DANGIN MIJINA hausa novels

 


* Zaune take akan tabarma .tana jera lemon

daxata fitar tasiyar. Inna tafito. Ke yannan

baki tafi ba tun daxu? sumayya tamike .tace

inna na tsaya jerawa ne saboda subada

shaawa. Anan tadora akanta. Tayi sallama

da innar tata. Bakin makaranta taje taxauna.

Suna fitowa break taje kusa dasu.don su

samu su siya. Hartama siyarwa cas tadawo

gyd .kasancewar lemonta fresh ne .kuma

tana wankewa tsaf tajera hakan yasa

mutane suke ganin tsaftanta harsu saya.

Kwanon tadire. Tashige bandaki. Innarta tace

yauma sun sayene? summaya tace ae inna.

Sallama majidadi yayi wato mahaifin

sumayya. Inasu adamu da nuru ne? suxo

muje masallaci.

Sumayya majidadi. Yata farko kuma ta mace

agun aliyu majidadi dakuma hauwau. Wacce

suke kira da inna. Tanada kanne biyu maza

adamu da nuru. Suba zaune cikin wadatan

xuci duk da bawai suna da arxiki bane. Anma

kam akwai na xuci. Sumayya har shekara

sha daya ce.tagama primary. Sai Allah bai

hore musu na secondry ba. Hakan yasa

tazauna a gida tana islamiyyanta kawai.

Hartaxo sukayi sauka. To ranan saukansune

makarantansu ta gayyaci manyan

yangwamnati suxo . Ahaka summaya taci

kaututuka. Aciki aka bata scholarship

nazuwa boardn skul. Aka bata daman xaban

kowanne. Murna agun sumayya kaman ta

rasu. Taje sa gudu gida ta sanarwa innanta

.sun kasance cikin murna a inda aka kawo

makarantu uku ta zaba. Ko spcl skul dake

garin baucgi. Ko hassan gwarxo dake kano.

Kokuma fggc dake damaturu. Ganin tana

bauchi yasa taxaba special skul abinta.a

satin admission dinta yafito. Inna tafara

kintsa mata kaya . Su kanxone. Su gari ne.

Su kulikuli. Aka xuba mata acikin akwatin ta

na gwangoro. Tadauko kayan sallanta

taxuba aciki. Ran lahadi suka shiga motan

kasuwa da ita da majidadi. Suna xuwa

majidadi yakai admsn dinta. Registrar

makarantan yayi sighn. Sannan yace

badamuwa zai iya tafiya ita kuma ta je

hostel.dakyar ta iya daukam akwatin.

Mutumin yace inkinje kice akaiki A.garba

anan hostel din zaki zauna.. Tana xuwa ta

xube agun da ita da kayanta.kowa sai

hidimansa yake. Taga kowa taci hijab tayi

hanyar wajen hostel. To ina zasuje? sai

tashare kawai. Tarasa agunwa zata samu

tayi tambaya. Tana haka saiga wata taxo

wucewa kawai tadan tabata. Baiwar Allah

don Allah inane A.garba? tayi mata wani irin

kallo. Sannan tce up ko down? sumayya

batare datasan me take fadaba ta amsa da

to.

Tace biyoni muje. Haka kuwa akayi tashiga

da ita sannan tamikata gawani gado. Kai

yan dakinnan idan Summaya Malanjo taxo

tkuce mata ni nakawo mata new cormer.

Sukace to .tafice tabarni agun. Nazauna

akan akwatina. Ina kalle kalle daga masu cin

abinci sai masu tadi .sai masu guga da iron

din charcoal.wasune suke shigo da gudu

suna cewa kaiii yan dakinnan bazaku shirya

kufuta arabic class ba? Sai yan dakin suka

rikice suka fara gudu suna fita sukuma

wannan matan suna binsu.ganin haka yasa

nima na rude. Indauki akwatinane intafi

dashi kokuma inbarshi? inacikin wannan

tunanin wata ta cafko hannuna ke kiyi gudu

mifita karsu miki duka. Nabita da gudu.saida

muka bar wannan fannin sannan muka dan

nutsa .tace meye sunanki? Sumayya

Majidadi.nikuma sunana zafyra Danbaba. Na

dan gyada kai saiga watama ta fancako da

gudu zafyra baza kuyi gudu ba! Zaarfe gate

ba shiri zafyra ta fincikoni mukabi wannan

din. Anma ina munyi latti donmu samu

anrufe gate din.anfara tarat latti. Nan

wannan tafara narai narai da ido. Sai zafyra

tace ke furyad wlh kincika tsoro. Bulala biyu

nefa. Furyad tace kut toki karbamin .kinsan

sarai Ba da dadi zasu manaba. Nikam dama

har kwalla tafitomun .zafyra ta kwashe da

dariya tace furyad kiga yaruwarki harda

hawaye nan akaxo kanmu. Zafyra tamika

hannu tashige. Aka kira furyad ana mata

daya ta doka tsalle. Ina ganin haka nakara

rudewa. Wata daga cikin seniours din kawai

tafara dariya nakalleta a kasafai. Tace

canavaro kixo kiga student dinki har da

fitsari. Nanfa aka taru akaina ashe nayi

fitsari bansaniba .hakan ya matukar basu

dariya. Sai dayan ta tambayeni meye

sunanki. Ido na fal cike da hawaye naje

Sumayya majidadi. Tace ayya awani hostel

kike? Sai na tsaya ina kallonta bance

komaiba. Tace yaushe aka kawoki nace yau.

Tana cikin magana saiga wacce daxu

takaini. Daki taxo wucewa da babban hijab.

Sumayya malanjo. Yar kwananki ne fa.

Sumayyan takalleta tace banganeba tace ae.

Daxu nakaita yar a.garba ce. Kayanta na

kwananki saiki duba mata gun zama. Shine

tajani tace badamuwa mukaje hostel. Tace

kayanki ne wannan! ? Nace ae nawane.

Tace to ga gado nan. Anan zaki zauna.

Inkina bukatar wani abu saikixo kuna ko

takwara na? Tafada tana murmushi wanda

wushiryarta saidaya fito nace tom.nazauna

na kimtsa kayana da jikina har aka dawo

anan naga ashe agefen zafyra da furyad aka

hadani. Tun daga lokacin muka dawo

kawaye tare muke yawo. Duk da cewa duk

sunfini auki ni tsayi kawai nafisu. Zafyra

anma tafi furyad jiki saidai furyad tafi zafyra

haske. Furyad irin matsoratannanne. Kuma

criminal ko aika zaayi saitace mu zalle

inbamu yaddaba sai ta zalle abunta.

Criminal ce sosai. Bata taba yadda taje aika

kullum a escaping take. Zafyra kuwa ana

cewa abu to zatayi .obeyer ce

sosai.acewarta duniyan nawane dahae zamu

takura makanmu? ajinmu daya sannan seat

dinmi daya. Tare muke wanki muke

guga.mudebo ruwa. Hatta abinci tare

mukeci. Duk dana fahimci cewa daga furyad

har zafyran yan gydan masu akwai ne.

Baabunda suka nema duka rasa. Anma

dangantaka dani bai damesuba.suna budewa

muci. Har ranar xiyartar iyaye tayi yakasance

nikadai ce baaxominba anma duka

anxomusu tare mukayi komai basu

gwadamin komai. Sannan ita anty summaya

malanjo tana lura damu sosai.ashe sunhada

dangantaka da furyad shiyasa bama wani

shan wuya

Har muka dawo gyda hutu. Inna tayi murna

sosai ganin ban rameba. Nima naji dadi. A

gun nabasu labarin makarantan dakuma

kawayen danayo innata taji dadi sosai haka

abbana. Lokacin komawa dayayi muka

shirya tsaf muka koma.a daddafe muka

gama shekarar mu tafarko.tabiyu .harta uku.

Yanxu mundawo jsce.inda zafyra da furyad

sunmin alkawarin xuwa nace musu to. tunda

nashiga secondry innata bata. Kara dauramin

tallaba. Acewarta na girma. Yanxu a gyda

muke sanaarmu.kuma ana ciniki. Watarana

nafito daga masai kawai naga takalmin yan

gayu adakin. Tare dajin muryoyi wanda

nasaba jinsu bakuma zanmanta dasuba.

Nashiga dakin su zafyra ne da furyad muka

fara ihuuu muna tsale.atake nadaura musu

abinci ba kyankyami sukaci .muka ci hiran

mu sannan suka mike zasu tafi.anan inna

tamusu goma na arxiki sukaji dadi. Mukayi

sallama.kwanci tashi muka koma aji hudu

inda muke ganin muma munfara girma hakan

bakaramin dadi yamanaba. Muka kama gun

zama tare mu ukunmu dama yanxu a

makaranta anshaidemu mu ukunmu muke

komanmu. Da sati biyu muka fara shiga aji a

lokacin aka kawo sabbin yan bautan

kasa.sukayi introducing dinsu a assembly

muka wuce aji. To ranar maths muke dashi

donhaka nafitar dakomai na na maths na aje

akan table.nice dama a tsakiyansu .zafyra

na gefena na dama furyad kuma

tahagu.yashigo da bakin glass a manne a

fuskarsa muka mike gaba daya muka

gaysheshi.bayan munzauna batare daya jiwo

yakallemuba yace yu knw d rgt tin cewa

maths zankoyar. A xuciya na nace yazaayi

musani mu almunsuru ne? kaman yaji

mezance yace saboda i said it a assembly.

Nan kowa ta nutsu saboda wannan ba

alamun wasa a tare dashi. Yamana drawing

shapes yaxubo calculation dinsu. Na dauko

pencil dina nazana sai naga nayi kuskure

namika hannu zandau cleaner zafyra tace

narigaki ai. Nikuwa nace wlh saibafara. Haka

akayi kuwa na fizge itama ta fizge munatayi

yajuyo yace meye kukeyi haka kaman

karnuka? raina yabaci dawannan kalman

yasa ko kallonshi banyiba idona a kasa.

Zafyra nema ta tsaya tana mishi bayani yace

will you shutup you black fool!! Kutashi

kubarmin aji. Nadago nakalleshi. Sai ya sare

alamun jikinsa yayi sanyi komeya gani oho.

Aa saiyakara bata rai. Meye kike xuramin ido

.da idanuwanki kaman na mage. Tashi ku

fice. Namike sulum sulum mukafita. Munafita

zafyra ta kwashe da dariya. Tace idon kulya

hehehe.

* Na cunno baki sannan nace waye idon

kulyan ? Tace ke mana. Bayan gashi anfada.

Abakacin mu nutsu amma ina nida zafyra

muka ma manta dawani malami abunmu.

Mukata hira. Can sai ga ummi manga ta

leko Sumy da zafyra wai kuxo. Muka mike

mukaje bakin kofan har zafyra tasa kai

yajuyo yace ke koma!! Jikina bari tadawo.

Niko dama Allah yayini banson takuri hakan

yasa na tsuke fuska sosai don da alama

zamu kwashi rikici dashi. Zafyra tashiga

bada hakuri.nikuwa kyanm narike

kunkumi.hakan tasa yace tawuce tashiga

nikuma yabarni agun. Furyad tarinkamin ido

alamun inbashi hkr anma haka na bata

rai.bance komaiba.yana gamawa yace

kibiyoni office.saidana tabbatar ya isa

sannan nashiga ajin yan ajin sukayi caaaa

akaina.sumy majidadi bazakijeba? Ki rufawa

kanki asiri ki fice don Allah. Nadan nutsa

sannan nace naji abeg karku cinyeni.nace

zafyra tashi muje ki rakani. Tace chap.kalan

laifinki yashafeni? Jace matsoraciyar banza

matsoraciyar wofi.furyad tashi muje.nasan

kekam baki da tsoro.tayi dariyan mugunta

sannan tace wlh yamun wani abu zanci

ubanki.nace nayadda.muka doshi staff din

corpers.anan na wurga ido kozan

ganshi.yana zaune akan table dinsa baicire

glass dinba.donhaka baansamu sldaman

ganin cikar fuskarsa ba. Fatanshi yana

yanayi dana yan ethopia.gashin kansa ta

kwanta lufluf.dogone da faddadan

kirji.wannan kallon daya namasa naga

hakan.muna isa nayi sallama baice

komaiba.saida furyad takarayi sannan

yadago.yakallemu sannan yacewa furyad

kece mai laifi? Tace a a sir.yace to yu safe

journey.na damke hannunta anma dole ta

kufce tafice.nakai minti ashirin a tsaye agun

bai cemin uffanba.nima sainadan kishingida

nama manta dashi.can yace meye

sunanki.cikin sanyin murya nace Sumayya

Majidadi.ya gyada kai sannan yace.meyake

yawo akanki! !? Naga wannan tambayar

bana amsawa bane anma gudun abinda

zaifaru yasa nace karatu.wacce irin dariya

ne taso ta kufce masa.anma sai ya dan

daure.yacire glass din muka hada

ido.dasauri nakauda nawa shikyma kallona

yake tayi.harsai dawani malami yaxo

gefensa yace ahmed ina registernka? Anan

yafargo daga tunanin daya keyi.yace duba

can table din.nikuka gabana sai fadi take

.yace kije break idam andawo zanxo klass

dinku nabaki purnishment dinki.nace to

.thankyou sir.har na juya nafita yasa

nadawo sannan yace.nace zanyi purnishing

dinki sannan zakice thankyou? waini baki iya

bada hakuri bane? Abakacin nabashi

sainakara cewa thankyou.sir.kallona yayi

sannan yace Am gona deal wit these you

blocked head

Na murmusa sannan nayi shiru yace go for

break zanxo nasameki, nace o.k sir, nafice

nabarshi agun,A dinng ne nahadu das u

zafyra da furyyad ,zafyra naganina t ace ,

dafatan baimikii komai ba, nayi dariyan

mugunta sannan nace baminba anma zaiyin

da, habawa furyad ta tsure nifa wlh tsoro

yakeban , mutum fuska a toshe baya

murmushi? Zafyra tacce ke girmansa keanan

indai matan makarantanne, said a haka

inbahakaba sai arainashi, nkuwa namikee

tsabar iskanci shine baku karbamnnn bread

dinba? Ke daallah prefect sun tsare gun,

bahaliiiin karbawa wani, haka muka raba

abuncinsu mukaci tare, muka hadada

cornflakes sannan muka fito, harmunxo gate

dn shga classes zafyra tacee kuxo muje mu

tsnka guava a masallaci, muka nufi

,masallaci muka tsiinka guava muka dura a

jakan mu nahannu, anan mukaji anbuga

breakover muna tafiya wasu nagudu ,donkar

a taresu latti, muna isa mukaga anfara taran

latti, nanfa furyad t tsure, wlh kunjawo mana

matsifa, gawata katuwan dorina agun sister

mujahida adamu tsoho,haka muka karasa

akamana uku uku muka wuce, hannuna duk

saiya kumburo yatashi, narasaa yadda zanyi,

muna shiga aji batare dana lura waye bane

nashige , kaina akasa sai kuka nake, zafyra

tace kiyi shiru wlh wannan English corper

dinnne, cikin sheka nace b yayi English

dinshi daxuba? Tace sunyi canje da agric

teacher ne, wai bazaixo ba, ban dago ba,

kaina asaman benci, lokaci lokaci inajin

zafyra na muntsinina alaman natashi saboda

yana juyowa yakalleni , ko kulata banyiiba,

can yacee waye a kwance ana koyarwa?

zafyra ta mintsineni nabuge hannunta, tace

kanta ne yake ciwo sir, yace to ta wuce taje

dispensary, haka zafyrA tajanni muka fice a

ajn munafita na murkuda fuska ke hostel

zanje, kanuba wlh baki isaba kalan yaje

dispensary, nurse din tace bakjeba ahadu aci

ubamnmu, dole na naje, na xuwa matan

tafara banbani, sumayya majidadi ko? A sati

sakinyi ciwo sau uku, nace anty hannunA

Neda, tacre aemana, fatanki saivuban laushi

anatabaki sai yayi ja yafashe, gaki criminal

bakl avoding, kullum sai anbdukek latti, nace

kai anty wlh ba kullum bane, tana wAnkemn

cwon muna Magana, wani irin kara nadsaka

datasamin sprit anty vwlh akwa zafi, tace s

beta k nutsu, zafyra nev taciremun hijabna

wa injii iska taga alamun ina xufa, anamin

ina ihu itakuwa nurse din, sai dariya

takemun, Ina bataji ciwo sosaiba ,?

Magananan damukaji abayanmu kenan

wanda hakan yasa najuya donganin waye,

zafyra tace sannu sir, yace sannu zaki iya

komawa class, tafice nikuma na ce anty

samin hijabn, tace akanme zansamiki bazafi

kikejiba, tashi ki koma kan wancan kujeran ki

zauna, wani irin kallo yabiini dashi daga

sama har kasa gakuma gashina daya xubp

har baya abude, na tsargu sosai,dasauri

nazauna, saidana kalleshi sannan shi

yakauda kai, yace kina gama mata ta tafi

hostel tahuta, nurse din tace akan wannan

ciwon? Ai sumy tazaba xuwa nan, fatanta

laushi yake dashi duk kankantan cwo ko

duka to sai tasamu rauni, ya kalleni sannan

yace to sata wuce aj, yafice, ana gamamin

nafice nima

Har muka gama term din kullum matsala ke

hadani dashi anma kuma mutane sukanyi

mamaki yadda yake mana dariya dani da

zafyra da furyad anma inkaga dariyanshi to

acikin amalamai ne suma ba dukansu ba,

kasancewar yanada kyau yasa mata suka

fara shgemasa kowa tanaso yayi mutunci da

ita anma bai bada wannan damanba,

dayawa daga ckin seniours dinmu sai uka

farajn haushinmu, kuma duk laifi inmunyi

baya dukkanmu asalinsa bamai duka bane

sais a purnshment dayawa ana tsoronsa

saboda haka, mukaje hutu mukadawo second

term, wanda a lokacin nafara fuskantan

matsaloli

Ss2 sune seniours dinmu a lokacin dan wasu

akabawa prefectship saboda ss3 zasu fara

waec, yarinyan da kabawa head girl sunanta

Aisha Alka kuma dama tunmuna jeniours ta

tsaneni , nine dai nake turamata aniyanta, ,

mundawo daga prep ta aika akirani, cikin

sanyn jiki naje, nasamu su shida akwanansu

suna tadi da alamu na teachers , kuma

musamman na ahmed, sai data kase=he

akalla minti shabiyar sannan tace meye

tskananinki da AHMED G.nace bakomai,

karya kike munafuka, ni abin sai yadauremin

kai, to don muna mutunci dashi shine

yazama dole muna soyayya? Kuma ma

tsabar ni suka raina zafyra da furyad dinfa?

Lalle bazan zauna a rainamn hankalii ba,

nadan gyara murya don naga sai zage zage

suke nace ae soyayya muke , aisha alka ta

dura wani ashar, Kanuba yan dakinnan

kunajin metake fada ko? Suka hayyayakoni

daga mai naushi sai mai mari sai mai duka,

ranan haka na kwana ina purnishment ,wai

don nace musu ina soyayya d malam ahmed,

sster mujahyda tarika rokona wai donAllah

nabasu hkr, nayi kif naki bayarwa haka har

asuba muna zaunw dasu sai azaba suke

ban, fatana yayi narau narau, gani fara abun

sai wanda yagani, sallar asuba sukace naje

nayi, anma kif nagagara mikewa saboda

kafana danaji yarike, suka waste sukabarni

agun, watace dataxo wucewa nace

baiwarrrrrrrrr ALllah ki kiramin zafyra

Danababa dakuma furyad a masallac, minti

goma sai gasu suka daukeni, anan na sume

,wani irn kara naj furyad tasaka.

 Farkawa nayi naganni a despensary.ga

zafyra dakuma furyad a gefena.sai wasu yan

ajinmu dasukaxo gaysheni.nakalli jikina duk

yayi radau radau. Anan nafara kuka.furyad

ma kukantakeyi.zafyra ce ma take bani hkr.

Nace kubarni inje hostel.anan nurse

dintaxo.majidadi mekikayi musu? Anan na

zayyana mata. Tace uhm lallai.tosu mai

ruwansu? Zafyra tace kuma wlh anty ba

soyayya sukeba.kiyayye ne kawai na head

gal.meyasa to mu bata kiranmuba?nayi

caraf nace rainin wayo.furyad tace ke kina

da taurin kai.alum alum dakin basu hkr

dashikenan magana yawice.

* Nace Allah sutura wlh.banyi laifiba nahau

bada hkr.anan nurse din ta ban

magani.kasancewar weekend ne ranar kuma

ba malanai yasa bawani staff dayasani.muka

koma hostel dakyar su furyad suka

matsamin naci abinci.gashi ranar wai

anyiwa ss2 laifi akataramu a field din

makarantan. Aka ware ss1 daban aka bamu

purnishment dinmu. Wata sister Yamina

muhammed muna shiri sosai da ita. Tace

majidadi kekan aibaki da lafiya jeki daki ki

kwanta.nan namike na je daki.nakwanta

kenan har bacci yafara kwasana kawai naji

saukan duka.wani irin firgit nayi saidatamin

sha biyu a jere tadaga bulalan.ta

kundumamin wani ashar meya kawoki hostel

.ban iyacewa komai ba sai wani hawaye

dayake fitamin.nace sister aisha wlh sister

yamina ne tace nadawo. Tace dakeda

yaminan malapar ubanku!!auxubillah nace

dakarfi. Wani irin kara tasaka tafara duka na

baji bagani.saida sandunan suka karye

dorinan ya mokade.anan metron tashigo ta

finciketa ta wurgata gefe. Aisha dama bakida

hanksli? Me yarinyan tamiki dazaki mata

duka har haka? Keda principal gobe Allah

yakaimu.tafice .metron kuma tajani takaini

kan gado.alokacin andawo daga purnishment

din.bawanda bai tausaysminba .mate dinmu

sai xuwa suke suna gaysheni.nayi narau

narau.ko ina a kumbure. Wani irin zazzabi

yarufeni. Haka narinka jinya har ran

monday.dayake english mukedashi first

period.Ahmed G.nashigowa yalura bananan

.a zatonsa ko lattin danasabayine. Anma

dayaga yagama first period baiganniba. Yace

wasu zafyra ina Mayah.dama Mayah yake

cemin. Sukayi narai narai da ido sai yan ajin

sukace batada lafiya. Meya sameta? Anan

kowa yayi tsit .kowa na tsoron fada daga

baya axo aci kaniyanshi. Ya buga musu

tsawa badaku nakeba?sai furyad tace sister

head gal ne tamata duka. Wani irin razana

yayi wat?!? metayi? sukayi tsit nanma. Yace

furyad tatashi tadaukoni.takaini

dispensary.shikuma yaje gun.anan nurse din

tabashi labari meya faru. Yaharxuka sosai

tunda take dashi bata taba ganin bacin

ransaba .adaidai nan muka shigo yana

ganina yace ashhaaa. Nurse shine baa mata

treatment ba! Zafyra tace a a. Tamata wani

dukan aka karayi.yace kuzauna anan amata

duk abinda yadace. Yakallen yayi murmushin

dole wanda nasan a dole yayi .sannu

mayah.Allah yakara sauki. Yafice. Bayan

angama wankemun ciwukan ina zaune

.kawai naga kaf ss2 wanda suka min duka

dawanda suka sabaki dawanda suka sa

hannu sunyi layi a kofan dispensaryn. Yaleko

mayah fitonan. Na fita ina kishingida.

Gatanan kufara. Abun yadauremin kai.daya

bayan daya suka taso sunaban hkr. Nayi

shiru a zuciyata nace don Allah ahmed

G.yarufamin asiri kar nakoma hostel suci

kaniya na. Ina wannan tunanin saiga aisha

alkan itama taxota taban hkr. Sannan tajuya.

Wani fincika yamata ya gaggaura mata mari.

Dan ubanki haka mukayi dake? Alkawarin

damukayi dake kenan? Zaki zaga kici

amana? dama haka kike? to a kunnen

umma. Wani irin kuka tasaka haba big bros

kayi hkr mana.abun yadaure min kai

matuka. Dama akwsi alaka tsakanin aisha

alka da ahmed G???? Yasa sukayi layi.

Tundaga admin block yakesasu tsalken

kwado har dinning hall. Yana binsu da

bulali.sunyi narai narai kam balaifi .duk

malamin dayaxo yamishi magana baya ko

kallonsu donhaka saisu juya batare da sunce

komaiba. Bayan sungama tsallen kwadon.

Yace yau anhutar damasu aikin makarsnta.

Haka yasa suka share

classes.hostel.dakuma admin block.yasa

suka wanke bayan gidan teachers .ranae har

karfe biyar suka kai suna aiki nikuwa yafita

yakawo abinci yakawomana mukaci mukayi

nak.hankalina a kwance.furyad kuwa duk

tabi ta tsure wai kar a koma hostel sumana

duka. Makaranta kuwa kowa sai yadada

tabbatar da zarginsa akan cewa muna

soyayya da ahmed g.inbahaka ba wannan

hukunci ai tsauri gareta. Bayan yagama sasu

aikin yakirani sannan yace gata agabanku

barin rantse muku kuji.wlh tlhy ko dauko

cokali kuja sata zaku wahala ahannuna.

Inada sunayenku.ba ita zata

fadamunba.securities nasaka donhaka saiku

kiyaye erhen.sannan dukka masu post

acikinku daga yau kutabbata kunyi bakwana

dashi zansa principal gobe yacireku.ku

bacemun.kowaccensu cikin sanyin jiki suka

mike .aisha alka ce tazauna.yace taxo

tataho tare da durkusawa yaya kayi hkr

bazan karaba. Na kalleshi shima kallon nawa

yake.sannan yace mayah. Wannan

kanwatace .cousin ditace .na gyada kai

sannan yace tatashi tatafi.bayan tafiyanta

ne yake cemin babanta da babana uwarsu

daya ubansu daya. A hatsarin jirgi babanta

da mamanta suka mutu.lokacin suna

dawowa daga aikin hajj.hakan yasa take

zaune a gydanmu har yai. Itada kanwata.

Itakuma tana fggc. Bansan meyake

damuntaba. Tana sona anma ni bana

sonta.ni akwai wacce nakeso .tun randa

nafara ganinita nakesonta.anma

bamgayamata bane.ina ganin kaman tayi

karama. Nayi kafaii ina kallonshi yau ahmed

G. Ne yake cemin hes in love. Lallai nayarda

duk jida kai na namiji a kasan takalmin mace

zai aje. Haka mukadanyi tadi sannan yace

natafi masallaci.a kishingide natafi.a

masallaci ne muka hadu dasu zafyra muna

zaune munadan tadi.sai aka dauke wuta.

Aka tada gene. Shima yadauke.muna jirane

ayi isha. Sai gasu aisha alka da yan

kwanansu sunxo mu munganesu.sukuma

kasancewar a duhu yasa su basu

ganmuba.anma mu mungansu.bayan sun

idar sai dayan tacewa aisha alka.wai ni

dama yasan kinasonshine? wlh yau anraina

mana hankali.ai wannan zaisa yarinyan ta

rainamu.aisha alka tace barshi. Wai adole ita

yakeson aura. Wancan hutun komawana naji

yana magana cewa akwai wata dalibarsa

yanaso .anma bai gayamataba. Dayan tace

hehe. Aikuwa idan aka aureta kin kade.

Aishan alkan tace kokuma ta kadeba.

Angayamata dangin miji wasane! ? Sukayi

shewa sannan sukacigaba. Nikan ganin

antashi sallahn ishai yasa muka mike. Muna

idarwa muka wuce prep. Awashegarin

bansan yadda ahmed G. Yayi da principal

ba. Aka tara assembly aka kwace green

dankwali aka bawa wasu.principal din yayita

korafi akan muguntan da prefect din sukayi.

Wa sister yamina muhammed akabawa head

gurl. Mukam munji dadi koba komai

munhuta tunda muna mutunci da ita.

Muna shiga classes nanma wani gurmin

ake.kowa nafadan son ranshi.mutane

dayawa sun ce soyayya muke da ahmed

G.nikuma dariya suke ban. Inani ina ahmed

G. Ai yafi karfina. Maths teachrn mune

yashigo.tunda yashigo yake cara na. Hakan

yamin nuni dacewa jira yake nayi wani abu

kiris yamin rashin mutunci donhaka sai na

kiyaye.narufawa kaina asiri. Dama a

kaidanshi inyaasgigo lectures zaku mike

bayan gaysheshi har sai yayi settling.haka

zalika idan yagama. Zaku mike kubar ajik

har yafice daga fanninku. To yauma

hakanne.dataxo fita.natashi mikewa sai biro

na yafadi na tsuguna donna dauka. Naji

yabuga wani irin tsawa Su maeyah!!!!.dama.

Inyamurine bai iya pronouncing sunanba. A

firgice nace naam sir. Yace follow me to my

office. Nan nazaro ido. Zafyra tace

maganinki. Bake kinki tashiba.na tamke

fuska nace kuji iskaro biro nafa nadauka

zakimin tsiya.nabishi abaya har office yasani

nazauna akasa .nafi awa biyu agun.ahmed

G yadawo yashigo office din. Yajuyo ya

kallen baice komaiba. Nikuma kunya naji don

tunda nake baataba kawoni staff dasunan

nayi wani laifiba sai yau wanda natabbata

laifina bawani babba bane. Har aka fita

break aka koma bawan Allahnan baicemun

komaiba.ahmed G .kuma nazaune.shima

yaki fita yasa mana ido.kuma baice

komaiba. Harna fara tunanin da gayya

yakawoni.wato don ahmed G.yagannine yaga

matakin dazai dauka tashi yayi yafita can sai

gashi yadawo.minti biyar saiga zafyra.taje

gum maths teachern.sir barin tambayeta

inda ta ajiyemana test. Papers dinmu zaa

karba. Yace yo.taxo daidai kunnena sannan

tace. Inji mal.ahmed G.wai yasanki da taurin

kai.anma kiyi hkr kibada hakuri.na kalleta

sannan nace Allah sauwaka. Tayi tayi na yi

kwafa darai naki.hartagaji tafice. Sai shima

ahmed G.yafita. Hakan yasa maths

teachernmu yace natashi nayi kneeling.haka

har aka tashi sannan yace natafi shima don

wani teacher yace masa yabarni nayi sallah

ne. Ina fita naje bakin tanki nadebi ruwa

nazauna sai nayi tagumi. Maganansa naji

.Mayah! Yaushe zaki daina taurin kai!

Tsugunawa wada ba gajiyawa bane.anma ke

kokadan bantaba jin kinbada hkr ba. Na yi

murmushi sannan nace ana bada hkr ne a

lokacin da akayi laifi. Yace ba laifi kikayiba?

Nace ae. Wannan kuskurene.

 Ya gyada kai sannan yace kije nurse ta

dubaki nasan jikinki yayi tsami. Nace a a

daga zama kawai? yace God save yi anjima

nazo tacemun bakixo ba.zanmiki bulala.jin

ya ambaci bulala na tsorata donkuwa dukan

dayayi wasu aisha alka nake tunawa.yayi

dariya sannan yace matsoraciya . Nace

uhmn aibani kaunan bulala ne. Ahaka

mukayi sallama yafice nikuma nawuce

masallaci

Washe gari bayan chemistry teachernmu

yafita saiga maths yashigo. Na mugun bata

rai.anma abun mamaki saiwani dariya

yakemun yana lallamina. Bayan munkoma

hostel ne sister yamina muhd take bamu

labari.ashe dasu ahmed G.suka koma

quarters na teachers. Dare dare ahmed ya

kwankwasa kofa shikuwa maths teacher

yabude. Anan ahmed yatike shi da bindiga

yace idan baifita harkanaba to saiya

harbeshi yaga waye gatansa. Furyad ta

kwashe dawani dariyan mugunta hehehe

inyamuri yaga mutuwa. Aikuwa washe gari

mukaji labari wai yanemi transfer xuwa wani

branch din makarantan dake toro.anma shi

maza ne kawai. Munci dariya kam balaifi.

Laifin dadi karewa .mungama ss1 inda muka

shigo ss2. .kuma awannan watan ahmed

G.zasu gama servise dinsu bashiba hattani

nawani tsomare nadawo abun tausayi. Shine

gatana a makarantan. Yanxu yana tafiya

shikenan kuma. Duk da munshigo senior

class anma bazanji dadiba.

A satin aka hada wani thnksgvn wanda zaayi

a makarantan. Kowa zai hallata. Aka hada

drama dasu fashion parade.ahakane nafito

as fulani. Bakaramin kyau nayi ba. Nasa

kayan fulani.gashina ma nayi

kitson.munkimtsa tsaf zamuyi. Naleko tagun

don nakarbi takalmi.ashe ahmed

G.yahangoni. Wani irin. Gigiza yayi bashiri

yasauko. Nikuma nakoma gun damuke shiri

na tsaya don jira akiramu nima nafita. Yana

shigowa ya kutso kai. Ina mayah!!! Gaba

daya aka nutsu.nace gani. Yakaremin kallo

head to toe. Sannan yace craxy yu!! Kina

tunanin haka zaki fita!?? Nakalli jikina

dakyau sannan nace ai fashion parade

ne.will yu shutup? Ya ktseni. Baniba har

mutanen gun sun tsorata. Idan kika kuskura

kika fita haka i will deal wit yu.yajuya yafita

nikuka tsugunawa nayi ina tunani.furyad

dama a kanuri zata futo.zafyra kuma hausa.

Sukace nahakura tunda hakane. Nakallesu

sannan nace. Ubanane dazai hanani? ! Its

jex for fun. Furyad tace kinfi kowa sanin

halinshi is left for yu. Ana kiran fulani kuwa

nafice abuna. Nayi nadawo nahankalta da

yanayin dafuskansa yadawo wanda baya

shiga wannan yanayin sai in antabani.

Yaugashi nida kaina na batamishi rai. Ina

gamawa nakoma hostek.nasa check.saiga

wata kuwa taxo.waikixo inji malam

ahmed.nafice ina xuwa baiyi wata wata

ba.mari ya sharara min tassssss

Gud nyt.

* Nadago na kalleshi tare da rike fuskana.

Nabude baki zanyi magana yace

shhhhhhhhhh.taredasa hannunsa a bakina

alamun nayi shiru. Nayi kwaf ina kallonshi.

Mamaki alajabi komai yacikani. Wannan ma

ai rainin wayo ne. Ban idda tunanina ba

yace. Banaso koda baa gabanaba wani

yaganemin jikinki. Nace anma malam. ya

katse ni nadai gayamiki. Be warned .yajuya

yatafi. Hostel nashiga narinka

kuka.wannanma ai cin mutuncine ko

mamana data haifen bata taba marinaba

balle wani.su zafyra da furyad suka shigo.

Furyad ce tace meye kuma na kuka?

Saidana gama kukana mai isana sannan

nagayamusu abinda yafaru.furyad tana

dariya tace ke kishine. Kuma saida akamiki

magana. Kinfi kowa sanin halinshi anma kika

take kika fita. Haushi yasa ko kulasu

banyiba. Washegari munje prep. Dama ranan

shine on duty. Ya aika naxo. Nace yarinyan

tatafi. Saidaya aiko mutane hudu anma ina

zaune kif ko motsawa banyiba. Su furyad

kuwa sai lallami suke. Nace su rabu dani.

Haka kuwa akayi. Antashi a prep nadauko

buks dina zamu wuce islamiya. Naganshi

zaune a gate din classes din. Yadaura hannu

akai. Bayama cikin tunaninsa. Saina koma

nazauna.haka akata wucewa har aka watse

naga baida niyyan tashi. Sai nabata rai naxo

zan wuce. Mayah"!!!!! Yakirani.na tsaya anma

ban juya ba. Yataso yaxo daidai bayana

hakan yasa nadan kara gaba gudun zargin

students.tunda nagashi ba kunya bane ta

isheshi. Yace .meyasa zaki zabi ki hukunta

ni tahaka?shin baki lura dani bane? Wlh ina

sonki.nafara kaunarkine tun randa na hada

ido dake.kinada kwarjini.sannan a idonki

akwai wani sirri wanda bakowa bane zai

fahimta. Kece farin cikina. Farin cikinki shine

nawa haka bakin ciki. Kiyi hakuri abisa

marinki danayi .zafin kishine.saidana koma

gyda abun yadamen. Hawaye ne suka xuba

a idona batare dana kalleshiba dasauri

nafice agun.gudun karya biyoni.shima

juyawa yayi yabar gun. Danaje islamiyanma

ban fahimci komaiba. Har aka tashi.sannan

muka taho nida su zafyra mukayi alwala

mukaje masallaci don muyi magrib. Anan

suka takuramin har nagayamusu. Kowacce

jikinta yayi sanyi sannan furyad tace.

Majidadi kina sonshi aiko! ? Na kalleta

sannan najuya kai. Zafyra tace erhn

gud.shiru ma amsane.

A satin komai na yacanja kaman baniba.

Wani irin shaukin so ne yake kwasata. Ina

matukar son ahmed G.so na hakika. Babu

sirki awannan son. Zan iya salwanta

rayuwana akanshi.haka kuwa akayi suka

gama service dinsu bakaramin tashin hankali

nashigaba a satin dazasu kammala. Duk na

sukurkuce nawani rame. Karatunma bana

iyayi .lura dahakan yasa wata rana ya aika

akiran. Jaje office dinsu .nasameshi idona a

kasa. Yace mayah!! Nace naam. Yace

ayya.yanxu zan barki ko?! To jekiyi kukan

missing ungo. Yamikomin handkerchief

dawata takarda yace jeki share hawayen

naki. Nadan muskuta kaman bazan karba

ba.nace waya gayama zanyi missing dinka?

ka tattara katafi ko zan samu wasu.duk ka

kashemin kasuwa. Wani irin tsorattaccen

kallo yamin. Kafin yace komai harna ruga

waje. Ina zuwa hostel nazauna naci kukana.

Na jefar da letan cikin akwati.don a tunanina

ba wuce ban hakuri ba. Saida daredare nace

barin duba. Ko hankalina zai dan kwanta

nasan ahmed G. Da iya kalamu masu dadi.

Nadauko nafara karantawa

My Babyyyyy

Jex nasanar dake cewa nayi alkawarin zama

dake ta kowani hali. Bazan bari a cucekiba.

Donhaka nayanke shawaran applyn zama

permanent teacher don nazauna dake har

ranan dazaki kammala. Sannan albishirinki.

Nakai goron tambaya na gidanku.kuka an

amince min.

Your husband

Ahmed Galadima.

Wani irin tsalle da ihu nayi. Wanda saidana

farkar da mutane daga bacci.lafiya aka fara

tambaya nace babu.kowa tagama complain

dinta sannan takoma.dama furyad da zafyra

yan baccin mutuwa ne. Insun kwanta basa

tashi sai safiya. Shima da rikici suke

tashi.dasafe bayan munsa uniform nafito

musu da letan habawa sai akafasa karyawan

suka barni da hadawa. Zafyra tadauko iron

bucket.furyad tadauko slippers.anan suka

fara kida.suna waka.

::Yaune muketa murna Sumayya tazama

amarya.zataje gidan miji. Karki nuna

fargaba. Ahmadu zoka bata hakkinta na

sunna

Inna da baba sunyi murna matuka da

dawowa na.sunga yadda nakara girma.kyau

da haske.inna tace ana ramewa a boadn

kekam kyau kikeyi .

A wani dare ne. Inna tace yan nan. Wannan

malaminkun yaxo kwanaki yayi tambaya. Da

bamuso mubasu amsaba. Anma mahaifinki

yaga yadda yake lura dake a makaranta ya

tabbata cewa shi mai taimakonki ne .hakan

yasa ya amince.dafatan zabin yamiki?! Nace

ae inna badamuwa. Ahaka muka kare

hutunmu. Muka koma hutu.a lokacin aka

raba prefectship abin mamaki waini aka

bawa headgal.zafyra labour Furyad

kitchen.mukam mune da makarantan. Tunda

duk muhimman post a hannunmu suke.

Muka bi da yara yanda sukeso. Kowa ka

laluma yanason mu.shi kanshi principal yaji

dadin kasancewarmu. Prefect.a lokacim su

aisha alka suka zana jarabawa suka fita.

Ran fitansu takirani taban leta. Nakarba naje

na nutsu ina karantawa

Xuwa gareki

Ina mai tabbatar miki dacewa kuma baki

shawara ki guji shigowa gidanmu.don baguj

zamanki bane. Ahmed nawane har abada.

Idan kikayi garajen aurensa zakiyi dana sani

a rayiwanki.

Na tsaya na tsurawa letan ido. Yagawa nayi

atake.batare danasa komai arainaba.

Aganina razanana takesonyi.ahaka muka

kammala sec.ranan fita munyi kuka da juna.

Da masoya. Ahmed shima a ranan yayi

resighn.basuyi mamakiba.dama principal din

yasan don nine. Ahmed ne yadawo

damu.saidaya sauke zafyra a igbo

quarters.sannan muka sauke furyad a federal

low cost.don duk naga gydansu. Mukayi

alkawarin sada xumunci wa juna. Sannan

yadaeo dani gyda. Nashiga natarar gydan a

cike makil.abun yaban mamaki. Ko ina na

gifta ga amaryan taxo.haka inna takaini

gunsu gwaggonanina. Akafaramin gyran jiki.

Anan inna take gayamin tun wancan

jummaan aka daura aurena da ahmed G.nayi

mamaki kwarai dagaske.to meyasa bai

gayaminba..?bangama mamaki ba

saidayyama danaga zafyra dasu furyad

dakuka wasu yan ajinmu da ashogbensu

kowa takure adaka. Anan suke gayamin

ahmed G.ne yadauki nauyin komai.kuma

yasanar dasu yace karsu gayamin.yanxu ma

shiyabada motoci akawosu.mukayi walima.

Sannan dare dare ahmed G.da abokansa

suka shirya dinner .munje mundawo lafiya

washegari inna takiranit tarinkamin

waaxi.hakama baba. Dare dare aka kaini

dakina. Dake gra.

Katon gidan da aka shiga dani.shiya

matukar bani tsoro.haka muka shiga. Da

misalin karfe sha daya bayan kowa ya

watse. Angona yashigo .

Washegari da asuba bayan munyi sallah sai

namike da xummar nemana abunci .yace

inazaki ? Nace abinci zan daura mana. Yace

dawo kizauna.nadawo. Haka yasa muka

koma bacci.da misalin karfe 8 nafarka nayo

wanka na tsara kwalliyata. Nadaurawa

maigidan nawa. Bayan mun kammala. Ne

aka kawomana abinci daga gidansu ahmed

G.muka karya. Sannan na nufi palour

nazauna ina kallo. Yace bari yaje gun

hajiyansa su gaysa zai dawo. Anan namike

nazaga gidan. Nayi mamaki kwarai dagaske.

Dama ahmed G.nada wannan arxikin? don

ko yar minista albarka. Nasanshi yamin

wannan kayan.gydanmu bamuda arxikin

dazaamin kayan dakin danaci karo dasu .don

har gun swimming da gym nagani . Bayan

nazaga. Ina dawowa naji anbuga kofa

axatona maigidan nawane.saidana budre

nasha mamaki. Bakowa bane illa aisha alka

dakuma wata wacce suke kama daga gani

yaruwart ce. Sannan tayi murmushi. Ta

rungumoni. Yauwa yar albarka amarya ta

ango. Yakike? nayi mamaki matuka anma

sai na hadiya nakirkiro murmushi.muka

shiga tarinka xolayana. Ina bros din yake?

nace yaje gayda hajiya. Tayi murmushi

sannan tace toh.Allah dawo dashi lafiya

.kekuma yu r welkm to the family nayi

murmushi sannan nace thnx.mukadanyi tadi

kafin nan ahmed yadawo. Ganinmu muna

tare yasa yayi murmushi little sis? tace

naam big bros. Yakike? Lafiya lao.naxo

ganin amarya ne. Aiho

Nan mukayita dadi.harsuka tafi.

Cikin sati uku kullum sai aisha alka taxo tun

ina dar dar da ita har nasake raina. Komai

tare muke. Zaka zata mu kishiyoyine.

Matsalaj tafara tun watana daya da rabi a

gudan ahmed G.

Ina zaune ina karanta jarida saigata tashigo.

Sis ya akayine? Nace sis wlh inaduba

wannan newspapern ne. Ohk tom.

Mukadanyi tadi.sannan nace bara naje nayi

sallah. Nafice nabarta agun. Fitowana naga

bata falon.kasancewar gidan babba sai nayi

zargin kotana wani gunne.donhaka sai

nazauna. Can saiga ahmed G. Yadawo

.narungumeshi tare damishi sannu da

dawowa.nadauko riwan wankanshi da

xummar nakaimishi bandaki. Baki a

bude.ruwan zafin nasake agun. Ahmed

nagani rungume da aisha alka. Wani irin

kara nasaka ayayinda nasake butan. A

razane yajuyo.idonsa tayi jajur.nikuma ashe

ruwan yadan zubemin tagefen kafana.fadi

nayi agun.

Bayan gwaje gwaje likita yayi wa ahmed

kashedi akan akiyaye sannan aka yi drippn

gun ciwon. Kallonsa nayi idona na zubar da

hawaye. Ya kalleni cikin sanyin jiki. Mayah!!

Meyasa kike da saurin fushi? Mekika gani

dazaki tsorata har ki xuba ruwan zafi

ajikinki.?! Wani irin kololon bakin ciki

naji.wannan wacce irin musiba da rainin

hankali ne? Nagansu sannan yamayar dani

shasha.juyar dakai nayi.ahaka mutane

sukayita xuwa suna gaysheni hardasu furyad

da zafyra.da inna.dakuma kannena su

aliyu.su hajiya dasauransu.uwar jinyan kuwa

aisha alka ne duk tarude.wani irin tsananta

naji. Ana gobe zaa sallameni. Tace majidadi

nasan zakimin kallon maci amana.anma ba

abunda kike tunani bane. Nadaga mata

hannu.alamun tayi shiru a sanyaye tamike

tabarni agun. Bayan ansallamoni su zafyra

suka xo gaysheni.anan muke tattaunawa da

kawayen nawa. To ke majidadi.wani irin

yarinta ke damunki? matarda kinfimu sanin

makiyarki ce sannan kisake mata?! Nace

bahaka bane. Taxomin da fuskan lumana

shiyasa gaba daya nasare da ita.furyad

kuwa taja tsaki.ke sai uban xuciya anma da

saurin amincewa da mutum. Tanaso

tacuceki ai dole ta lallameki.kai furyad bahak

bane. Shikenan kya mutu da bakin ciki.Allah

baku zaman lafiya suka mike suka barni

agun. Ahmed ne yashigo da gudu naxo da

xummar namar oyoyo .wani irin hankadanani

yayi.yanunani da yatsa kishiga

taitayinki.saiga aisha alka tafito cikin

rangwada da kissa.gajeran wando da vest a

jikinta.dagudu ta rungumeshi shima ya

lalumota kawai suka hau kiss.auxubilla nake

fadi.mikewa nayi nabargun

Abin bakinciki yadameni.yanxu watana biyu

da aure anma duk na sukurkuce

narame.nadawo wani iri.ahmed yajuyamin

baya.kamar bashiba.daga hantar sai mari

sai zagi sai duka. Aisha tadawo tamkar

matar gydan. Daya bayan daya ta rinjaye

danginsa .baa ganina da gashin ido.ko taro

zaaje anrika zamba dani ana nunani.abin

yadameni.gshi innata tamin horo dakar na

kuskura nagayawa kowa sirrina. A dangin

ahmed .hajiyarsa ce kawai take sona. To

itama tana canada sunje aiki itada da alhaji.







Jinine ya kwaranyo a jikin fuskana. .a gigice

ya iso kaina. Zai tsuguna aisha alka ta

fuzgoshi karkayi kuka don Allah karkafara.

Bugeta yayi yajuya yana kallonta wani irin

kallo cike da alajabi. Hawaye ne suka

kwaranya a idonshi. Yarike goshinshi wani

irin salati yayi tayi a jere sannan yajuyo ya

kalleni a tsorace ya gigice mayahhhhh!!! Ido

na akansa anma nagagara motsi. Daukana

yayi muka shiga mota sannan yanufi asibiti

dani. Anan suka bamu gado. Aka wankemin

ciwon sannan liktan yasanar damu inada

juna biyu. Murna kam kaman zai hadiyeni

nikuwa sai kallonshi nake. A lokaci guda

yacanja bayan munkoma gyda muka tarar

aisha a zaune kaman yadda ta saba. gajeren

wando da bra top. Wani irin salati yayi

sannan yace ke !!! Kinada hankali kuwa?

mekikemin a gyda tsirara? ta tashi a

sanyaye alamun wani abu yabata mamaki

kiwuce kibarmin falo.kije ki suturce jikinki.

Anan haj. Takirashi.yafice dasauri nikuma

nashige daki.nayi wanka bayan nafito naji

wayana yana kara alamun kira. Naje dasauri

.nadauka furyad ne take cemin daga gun

malami suke ya karya asirin. Dama anyi ne.

Akan wannan koyin xuciya na ahmed ne.duk

randa kwan yafashe to xuciyan ahmed

zaifita daga ikonta. Dadai sauran

tsibbu.sannan wannan gunkin yazama busar

da xuciyanshi agareki.zai na miki kallon

namiji. Kuma asirin zata karyene kawai duk

randa yazubar da hawaye akanki donhaka

saiki san yadda zakiyi jikina a sanyaye nace

kuka kam yayi daxu bayan tafiyarku. To

yanxu kidage da addua. Munsa yayi saukan

alqurani. Nace to.yaushe zakuxo! tace

kinmanta maigidanki yace karmu kara xuwa?

nace zanyi masa magana .tace tom.

Ina juyowa gabana yayi mummunan.

Faduwa sakamakon abunda nagani

Muhadu dare dare

Aisha nagani da wuka a hannunta kanta a

yamutse kaman mahaukaciya.yau zan

kasheki kihuta. Nima nahuta. Baxan zauna ki

auri wanda tun ina karama nake

mafarkinshiba .nazaro ido. Hannu nasaka ina

rokonta anma wani irin kara tasaka tayo

kaina. Tana kururuwa. Tuni na sadaukar

darai.wani irin salati nakeyi saboda a

tunanina mutuwa ce taxomin kawai.shiru

naji. Banji wukaba banji kuma muryarta

ba.donhaka saina fara tunanin kona mutu

ne. Tafdi ma. Dama haka mutuean take? sai

nabude ido .a tsorace namike don ganinsu

akaina. Hajiya ce rike da wukan da aisha tayi

niyyan cakkamin. Suna tsaye sai kallon kallo

suke. Namike a sanyaye zanyi magana

hajiya ta dakatar dani. Kwantar da

hankalinki. Basai kinmin bayani ba. Kafin ta

idda magana. Aisha tadaura hannu aka. Sai

wani ihu take. Tana cewa

Tun a makaranta nake son raba ahmed

dakuma sumayya.bansamu damaba shiyasa

dana dawo.na ziyarci boka kilu. Yabani

maguna. Ni na asirce ahmed da xuciyansa

tazama nawa. Komai nasashi yayi.sannan

nina asirceki harkike son aurena da ahmed

kuma kike hantarar sumayya. Ni na asirce

dangi.kowa yana mata kallon kurciya. Don

bokan dakanshi yamin wanka yakuma sadu

dani.yace in anfasa kwai acikin kwalban

dayaban asirina yatonu. Zan haukace .kuma

komai zaidawo kamar da. Gashi inada cikin

boka .wayyo nashiga uku na lalace.

Kutaimaka min. Wayyo ni.yakurtu boka.

Auxubillah nida hajiya mukayi tayi wacce

kuka yaci karfinta. Anya aisha ke jinin alhaji

ne? gaskiya ina kokonto.dagudu aishan

tafice.nayi xummar nabita don nakamota

hajiyan tace.akanme? matar da zatasa ki

nakunci lahira?


8Jinine ya kwaranyo a jikin fuskana. .a gigice

ya iso kaina. Zai tsuguna aisha alka ta

fuzgoshi karkayi kuka don Allah karkafara.

Bugeta yayi yajuya yana kallonta wani irin

kallo cike da alajabi. Hawaye ne suka

kwaranya a idonshi. Yarike goshinshi wani

irin salati yayi tayi a jere sannan yajuyo ya

kalleni a tsorace ya gigice mayahhhhh!!! Ido

na akansa anma nagagara motsi. Daukana

yayi muka shiga mota sannan yanufi asibiti

dani. Anan suka bamu gado. Aka wankemin

ciwon sannan liktan yasanar damu inada

juna biyu. Murna kam kaman zai hadiyeni

nikuwa sai kallonshi nake. A lokaci guda

yacanja bayan munkoma gyda muka tarar

aisha a zaune kaman yadda ta saba. gajeren

wando da bra top. Wani irin salati yayi

sannan yace ke !!! Kinada hankali kuwa?

mekikemin a gyda tsirara? ta tashi a

sanyaye alamun wani abu yabata mamaki

kiwuce kibarmin falo.kije ki suturce jikinki.

Anan haj. Takirashi.yafice dasauri nikuma

nashige daki.nayi wanka bayan nafito naji

wayana yana kara alamun kira. Naje dasauri

.nadauka furyad ne take cemin daga gun

malami suke ya karya asirin. Dama anyi ne.

Akan wannan koyin xuciya na ahmed ne.duk

randa kwan yafashe to xuciyan ahmed

zaifita daga ikonta. Dadai sauran

tsibbu.sannan wannan gunkin yazama busar

da xuciyanshi agareki.zai na miki kallon

namiji. Kuma asirin zata karyene kawai duk

randa yazubar da hawaye akanki donhaka

saiki san yadda zakiyi jikina a sanyaye nace

kuka kam yayi daxu bayan tafiyarku. To

yanxu kidage da addua. Munsa yayi saukan

alqurani. Nace to.yaushe zakuxo! tace

kinmanta maigidanki yace karmu kara xuwa?

nace zanyi masa magana .tace tom.

Ina juyowa gabana yayi mummunan.

Faduwa sakamakon abunda nagani

Muhadu dare dare

Haka muka zauna nida ita saiga ahmed

yaxo. Nikuwa natashi domin naje na kimtsa

Komai ya dawo daidai.{[Wannan labarin

na.xuwa muku daga Saje novels nd sales.

Domin kaima kasiya labari kaima kabuga

donka zama marubuci nakanka.saika

tuntubemu a sajenovelss@gmail.com ]}. Nida

maigidana sai son barka. Lalle aure da dadi

musamman inkunason juna. Kaso a soka

shine so. Daga baya ahmed yabiyawa inna

da baba makkah. Bayan sundawo lokaxlcin

muka fara shirin bikin zafyra. Rayuwa sai

godiya wa Allah. Donko bakomai na dandana

radadi da azaban dangi miji batare da

hakkina ba. Anma daga baya ninafi moran

dagin mji.Mijina nasona nima inasonshi .

Dangin mijina sun maidani kamar kwai.

Ahaka na haifi tagwaye. Wanda yakara

samin farin jini a dangin mijina. Nagode

Muhadu a labari nagaba. NIDA KISHIYATA



Post a Comment

0 Comments