AFSANA. HAUSA NOVEELS

 AFSANA*🌹 

   [ *LABARINA*] 

_*short true life story*_

🌹

🌹🌹

🌹🌹🌹

🌹🌹🌹🌹


     1⃣



   WRITTEN BY


 🌹AMEENA UMAR FARUQ🌹

OR

  🌹MEENAT🌹



  *GODIYA*


Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin halitta dayabani ikon   gama rubuta littafin *ZUCIYATA CE* lafiya, ya ubangiji ina sake rokonka da kabani  ikon rubuta wannan littafin me suna *ASFANA wato LABARINA,* ya Allah tsirada amincin ka su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalan gidansa DA sahabbansa da wayanda duk suka bashi gaskiya harzuwa ranan alkiyama ameen,




   *ALFAHARINA* 


Iyayena sune abun alfaharina Addu'a ta agareku bazata taba karewa ba har sai ranan dana bar numfashi, fatana Allah yasa kucika da imani ameen ya RABBI,



*SADAUKARWA*


Na sadaukarda wannan littafin ga duk wanda yai  biyayya ga ZABIN da iyayansa sukai masa", Ina nufin tafan'nin zaba masa "abokin rayuwa, mace KO" namiji Ina rokon Allah yadauwamar da farinciki tareda kwanciyar hankali agidajansu "aduk inda suke "afadin duniyar nan ameen ya Allah,🙏🏼



    *DOMINKI*


 Wannan Labarin dominki na rubuta shi _*HAJIYA AISHAT ABDULLAHI NIJAR Mrs MUHAMMAD SANI NIJAR LIVING IN GABON,*_ inafatan kina cikin koshin lafiya tareda farin cikinki I mean😀 you Hubby, da kuma sanyi idaniyarki 👉🏻👩‍❤‍👩Ina rokon Allah ya dauwamar da farin ciki agidan *AURANKI,* nagode sosai da kauraki gareni tabbas kauna kesa ayarda dakai har "abaka matsayi na musamman "a *ZUCIYA,* don haka kisani kinada matsayi mai girma "acikin *ZUCIYATA* fatana Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi Ameen,🙏🏼



*SHIMFIDA*


Wannan Labarin ba kagagge bane labarine Wanda yafaru da gaske, "asalima wacce abun yafaru da'itace tabani damar rubuta shi, don haka duk abunda zakaji ko" zakiji acikin labarin toh" yafaru ne babu wani abunda aka canja sai sunaye da kuma gari,



*JANKUNNE*


Banyarda acanjamin labari tawata siga batareda izini naba yin hakan babban kuskurene sai a kula,




*_ASSALAMU'ALAIKUM AL'UMMAR ANNABI MUHAMMAD_ _(S.A.W)_*

*_BARKAMU DA SALLAH DAFATAN MUNYI SALLAH_ _LAFIYA_* *_TO ALLAH YAKARBI _IBADARMU_* *_YA KUMA MAIMAI TAMANA_*

*_AMEEN_.*

_______________________


® _*PEN: WRITERS ASSOCIATION*_


_*only the exquisite and whizkid writers are opportunity to be pen writes*_





✍🏽


 _*Bismillahirra'hamaninrahim.*_



    _*Gabon city  Monday 11:00Am*_



Wata Kyakkawar macece fara tanada yarkiba kadan, kishingide take "Akan wani lallausan kushin tana kallon taurarin dan Adam. Duk datana "akishingide ne hakan baihana agane itadin doguwa bace, Kallo daya zakai mata kagane hutu dajin dadi sun zauna sosai ajikinta, musamman idan Kai la'akari da tanfareren falon datake ciki  wanda yaji kayan more rayuwa, wanda za'iya kiransa dasuna aljannar duniya.


Tana sanye da wata  atamfar super  exclusive koriya da ratsin yalo, sai Ta yafa gyale shima kore me duwatsu yalo, fuskarta daukeda kwalliya me tsari wadda takara mata kyauda kwarjini, hannuta dake rikeda remote Wanda yasha zanan lalle sanye da awarwaron gwal guda uku, dayan hannun kuma daureda agogo shima kallo daya zakai masa kagane zallar gwal ne, gaskiya matar Ta hadu sosai wanda kana ganin ta kasan irin isassun matan nan ne dasuke da matsayi mai girma a ZUCIYAR miji, saifaman kamshi take zubawa tamkar anyi barin turare ajikinta.


Agaban ta wani table ne me kyau daukeda wani kwali me walkiya cikinsa akwai farar takarda me taushin, Wanda bature yakirada suna toilet paper. Agefe kuma tsadardiyar wayarta ce kiran iPhone 7 , sai dan karamin farantin da ke cike da yankakku kayan itatuwa irinsu mangoro,tufa inibi dadai sauransu. Ahankali takai santalelen hannunta tadauki tufa takai bakinta, Cikin nutsuwa take taunawa tamkar bataso can sai wayarta tayi kara, "ahankali tarage karan t.v sannan tadaga wayar.


 Murmushi tayi ganin sunan daya baiyana akan gilas din wayar, daukar wayan tayi tareda bude karanta Cikin sanyi murya me cikeda farin ciki, Tace amincin Allah ya tabbata ga uwargida kuma amarya agidan "Alh Abeed. Dariya tayi harsada sautinsa yafito ta Cikin wayar sannan tace Kema amincin Allah ya tabbatar agareki uwargida amarya "Agidan "Alh "Ahmed, Dafatan kintashi lafiya?..tace lafiya lau toh" yakike  ya yarana" da "Baban su?.. tace duk lafiya lau suke suntafi makaranta shi kuma baban su yatafi gurin aiki.


Toh" nima yaya yaran nawa suke?..,tace suna lafiya suma suntafi makaranta babansu gurin aiki, tace toh" Allah yadawo mana dasu lafiya tace ameen. Inafata dai kin gama komai?.. tace tundazu ke kadai nakejira, tace nima nagama komai don haka gani nan zuwa yanzu insha'allahu, tace toh" Allah yakawoki  lafiya tace ameen sannan suka kashe wayar lokaci daya.


"Assalamu'alaikum masu gida inji cewar wata" kyakkyawa mece fara doguwa, Tanada jiki me kyau musamman ma mazaunan wanda yakarawa jikinta tsari da kyau, tana sanye da "atanfa sufa wax wadda kana ganinta kasan tsadadda ce, Me ruwan hodace atanfar tanada ratsin ruwan kasa, tayafa gyale me ruwan kasa takalmi da jaga masu ruwan hoda, fuskarta tasha kwalliya irin ta manyan mata masu "aji sai kamshin turare take zubawa, zama tayi kusada matar gidan wacce tuni ta amsa sallamar tareda tashi daga kishingidan datake.


 Saifaman doka mata murmushi take, cikin sanyi murya me cikeda farin ciki wanda da'alama yanayin takenan, 

tace sannu  dazuwa haj Asma'u.


Tace yauwa haj Aisha, dai-dai lokacin data ajiye jakarta saman table tareda cire gyale "aikam tuni sarkan wuyanta na zallar gwal yabai yana, tace haj Aisha wai d'an tafiyar nan danayi daga gida zuwa nan shine nakejin zafi, shin waiko dai nafara kiba ne?.. tafadi tareda daukar tufa takai bakinta.


 Dariya haj Aisha tayi cikin zolaya tace "aikuwa kinfara koma nace kinyi, dasauri tazaro ido😳 tareda cewa da gaske?.. dariya Haj Aisha take sosai tace haj Asma'u wai meyasa bakison kiba ne?.., Tsaki tayi tareda cigaba da taunar tufa din sannan tace hmm! haj Aisha kedai bari wlh banason kiba shima "Abeed dina mafa bayaso, yace" yafisona haka shiyasa banason nayi kiba wlh,


sai kuma ta kwantar da murya tace fadamun da gaske nafara kiba?..Cikin murmushi Haj Aisha tace kedai wasa nakeyi kina nan yadda kike. Ajiyar  zuciya tayi tareda cewa toh" amma meyasa kwana biyun nan nake yawan jin zafi?..,tace "eh gaskiya kwana biyu nan "anazafi kila munkusan samun ruwane, tace gaskiya kam toh" Allah yakawo mana masu "amfani tace ameen.


 Haj Asma'u tace hmm! Haj Aisha nifa jiyada mamakin ki nakwana, cikin mamaki! tace mamakin mekuma?.. tace dakikace waikin taba shiga kuncin rayuwa domin nidai atunanina bakimasan me'ake kirada kuncin rayuwa ba,


tace Kai! haj Asma'u dadina dake "akwaiki da "abun dariya toh" meye "abun mamaki Dan nace maki nataba fuskarta kuncin yaruwa ummh?.., Tace saboda naga  babu "abunda kikarasa najin dadin rayuwar duniya musamman "abunda kowace mace take burun samu agurin miji, dasauri tace haj Asma'u mene ne shi?.. 


tace soyayyar miji, da'yan'uwansa" dariya tayi tareda cewa haj Asma'u kenan toh" ke! yanzu "acikin "abubuwan nan mekika nema kika rasa?.. dasauri tace wlh Haj Aisha babu "abunda na nema narasa musamman ma soyayyar miji data yan'uwansa wanda kullum mamakin yadda suke sona nake, dakuma yadda shi "Abeed din yake sona kamar yacinyeni saidai fakisani saida nasha bakar wahala, sannan nakai ga samun wannan soyayyar me cikeda matsayi.


 tace toh" nima haka Saida nasha wahala, dasauri tace "a ah haj Aisha Sam ke! bakiyi kama da wacce tasha wahala arayuwa ba, dariya tayi tareda cewa toh" ai abun bata gakama kuma kisani babu wani dan' "Adam din daza yace" maki baitaba fuskantar matsala arayuwar, saba saidai kawai nawani yafi nawani. tace hakane toh" yanzu bani labarinki da kikace nazo yau zakibani, domin dai zanso naji irin wahalar dakika sha "arayuwa, tace zanbaki labarina kamar yadda nace  amma saikin farabani Labarin ki tukun, 


dariya tayi tareda cewa "au hakane?..tace "eh  tace aiko yanzu zanbaki labarina don haka sai kigyara zama kiji. Dariya tayi tareda cewa toh" nagyara dai-dai lokacin data cire gyale ta ajiye, sannan tadauki yankakken mangoro takai bakinta saida ta tauna sannan tace" toh Ina saurarenki bani nasha, dariya haj Asma'un tayi sannan ahankali tafara dacewa?..





Muje zuwa



daga



Alkalamin



✍🏽



🌹Meenart ce🌹

[9/11, 4:28 PM] ‪+234 816 334 9332‬: 🌹🌹🌹🌹

      🌹🌹🌹

           🌹🌹

                🌹

🌹 *AFSANA*🌹 

   [ *LABARINA*] 

_*short true life story*_

🌹

🌹🌹

🌹🌹🌹

🌹🌹🌹🌹



 🌹 _*TRUT LIFE STORY*_🌹



Page2⃣




WRITTEN 

      BY

🌹AMEENA UMAR

 FARUQ🌹  


 OR

🌹MEENAT🌹



  *DOMINKU WANNAN PAGE DOMIN KUNE MASOYANA IDUK INDAKUKE, INA KAUNARKU SOSAI FIYEDA YADDA KUKE KAUNATA ALLAH YABAR KAUNA, TAREDA ZUMUNCIN ME DOREWA AMEEN.*



_______________________


® _*PEN: WRITERS ASSOCIATION*_


_*only the exquisite and whizkid writers are opportunity to be pen writes*_





✍🏽



    



Kamar yadda kika sani sunana Asma'u Jibrin ni haifaiffiyar garin Niger Minna ce, Amma "a Kwantagora muke da zama awata unguwa mai suna Nasarawa, kasan cewar  mahaifina haifaffen kwantagora ne dan haka duk yan'uwansa suna can kwantagora.


 Saida ita mahaifiyarmu ba fullatanar Bauchi ce, karatun allo ne yakai mahaifinmu Bauchi can yahadu da mahaifiyamu me suna maryam, sukai aure har Allah ya azurtasu" da haihuwar yara biyar.


 Saida kuma mahaifiyar mu wacce muke kira da "Umma ta kasan ce meyin irin haihuwar nan, da'akekira haihuwar rakunma dan haka kowa ni akwai tseraiyya tsakaninsa da dan'uwasa sosai, yaya "Auwal shine babba wanda koda nayi wayo na iske yagama karatunsa haryana koyarwa "Awata secondary school maisuna Girls day secondary school, yana da matarsa da yaransa biyu.


 Sai Aunty "Khadija itakam tana gama secondary tayi aure, Amma kuma kasan cewar mijinta yana koyarwa a f.c.e sai yabarta taci gabada karatun asibiti a Jega, Sai yaya "Usman shikuma yana n c e 3 sai ni Asma'u ina secondary s.s 2, sannan "Auta Aliyu, shi kuma yana j.s.s  3, Af namanta "mahaifinmu  yakasan ce manomi ne kuma malamin makarantar allo ne wanda  yake da "Almajirai dayawa, don haka dukka mu "agurinsa mukai karatunmu kuma duk munsauke alkur'ani.


Don haka mun taso Cikin tarbiya da biyayya tareda girmama junanmu, Cikin rufin asirin Allah babu abunda mukanema agurin mahaifinmu mukarasa, yawa data mu da abunda Allah yahore masa, lokacin da nagama S.S 3 shekarata goma sha shidda komai na cikakkiyar budurwa, ya baiyana agareni don haka samari sukai mani cha! saidai kuma bana kulasu, kwata-kwata domin basu" ke gaba naba nidai burina nayi karatu nazama malamar makaranta.


Ganin  hakane yasa Malam baikawo maganar aurena ba, da result dina yafito kasan cewar yayi kyau sosai don haka  sai "Malam yasa "Baban Abba wato Mijin Aunty "Khadija yasamo mun Admission, a f.c.e saina fara zuwa makaranta kasan cewar dama na rubuta jam, Ina level 2 wata mummunan kaddara tafada Mani.


Ranan wata lahadi da bazan taba mantawa da'itaba arayuwata, nadawo daga gidan Aunty "Khadija dake dadin kowa kasan cewar duk two weeks take dawowa daga Jega to nikuma sainaje can nayini, to ranan banwuho gida dawuri ba sai bayan sallah isha'i kuma Aunty Khadija, tayi-tayi dani na tsaya har "Baban Abba yadawo yakaini gida nace mata A'ah nidai gida zantafi,


 Dan haka sai tabani kudi nahau mashini, saidai kuma wani abun mamaki shine aranan sai mashin yaimani wahalar samu, Dan haka sainai ta-tafiya ahankali Wanda nayi tafiya mai nisa sannan nasamu mashin, mun isa wata  Unguwa wadda daga ita sai Unguwar mu sai mashin din ta tsaya, mai mashin yayi-yayi ta tashi amma bata tashi ba ganin lokaci sai tafiya yake tunda harkarfe 9:00pm tayi saikawai nabashi kudinsa,


 Nafara tafiya atunanina idan nasamu wani sai yakarasa Dani Unguwar mu, saidai kuma bansamu wani mashin din ba.


 Ga gari yayi duhu kuma hadari yataso sosai kasan cewar lokacin damuna ne, dan har anfara iska tareda walkiya don haka saina fara sauri sosai, Wanda idan kaganni sai karantse tafiya kawai nake ba sauri ba, saboda yanayin tafiya ta kenan saida kuma ni sauri nake sosai.


Dasauri na shiga wani lungu wanda zata sadani da wata Yar karaman titi, To kuma Dana tsallaka titin saina shiga layin dazaya kaini layin gidan mu, tsaye nayi bakin titin inajiran wata mota tazo tawuce saina tsallaka, saidai kuma fitilar motar ta haske mun ido sosai dan haka sainai saurin kare fuskata, da hannu tareda kauda kaina gefe Ina gun-guni haske mun fuska da me motar yayi.


Saidai kuma wani abun mamaki! konace abun al'ajabi! shine jinai anyi sama dani, Cikin matsanancin tsoro da firgici nabude baki zanyi ihu, sainaji an rufemun baki tareda ido jinayi kirjina yana dukan tara-tara,


 Saka makon wata muguwar dariya danaji ankasaki dakarfi, Wanda nidai tunda nake arayuwata ban tabajin sautin dariya irin wannan ba, dan haka dasauri nafara addu'a domin atunanina gamo nayi da aljanu sosai nake addu'a, 


Don banyi tsammani acikin mota nakeba. Saida naji an zaunar dani akan kujerar mota dakarfi sannan nagane wato hannun mugayen mutane nafada ba aljanu ba, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin fuskata kirjina kuwa wani irin matsananci bugawa yake tamkar zaya fito waje saboda tsanani tsoro da tashin hankalin Dana tsinci Kai aciki, don haka sai na tsananta addu'a ta yayinda nakai hannuna da sauri zan konce kullin da'akai mani,


 Saidai me jinai anyi caraf anrike Mani hannun dakarfi anmayar dashi tabaya, andaure dan haka saina fara mutsu-mutsu "aikaim tuni akadaka mun wani uban tsawa Wanda yasa na tsunu, yayinda nacigaba da  zambada addu'a tareda kai kukana kurin Allah domin dai nasan babu mai fiddani daga hannun wayan azzaluman sai shi. 


Munyi tafiya mai Dan nisa sannan naji antsaya, karan bude kofa naji, can kuma sai naji anfin ciko ni  dakarfi harsai danaji hannuna yaikara Katttt!, acikin zuciyata nace wayyo Allah "Ummata domin wani irin radadin zafine ya bakunce ni, 


Still fincikata naji ansake yi dakarfi tareda jana, idona rufe yake dan haka jefa kafata kawai nake ba tareda nasan inda suka nudosa dani ba,


Karar bude kofa na sakeji, sai kuma naji ansance mun kullin hannuna da fuskata sannan aka turani wani daki dakarfi, Har saida nafadi kasa sannan naji anja kofar aka rufe da karfi.




Dasauri natashi tareda bude idona yayinda kirjina yacigaba da matsananci bugun tara-tara Cikin tsoro tareda gigita nafara juyi atsakiyar dakin da babu hasken fitilar lantarki saita fitilar barci,


Motsi naji ta bayana don haka na juyada sauri sai naga wani mutun dogo majiyi karfi a tsaye, duk da dakin babu gaske sosai hakan bai hanani ganin damtsen hannusa ba yana sanye da  riga vest da wando boxes, saidai banga fuskar shiba sam kasan cewar fitilar barci batada gaske sosai,



Jinayi tsoro yasake kamani don haka dasauri najuya nanufi kofar, nafara bugawa da iyakarfina Ina kuka tareda ihun fadin abude, saida kuma Ina babu wanda yajini balle nasaran zaya taimaka ya budemun nafita.


jinayi an" fincikoni tareda dagani sama, aikam nasaki wani uban ihun, dai-dai lokacin da naji asaukeni saman gado tareda fisge hijab dina akai jifadashi,  jikina ne yadauki kerrrrrma! sosai gani mutumin yahau saman gadon tareda cire vest din jikinshi yai jifada ita gani mugun abunda yake shirin aikatawa agareni yasa Cikin matsanancin tsoro da firgici nace?....



Muje zuwa


Post a Comment

0 Comments