makauniyar soayya hausa novels 10

 MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽


 



*Wannan shafin sadaukar wa ce ga dukkan fans d’in Brigadier Faruk*

*Lallai Faruk ya ciri tuta a wannan littafin da yafi kowa samun mabiya, ni kaina Bregadier Faruk na burge ni, kuma fans d’in sauran jaruman ina mik’a gaisuwa ta a gare ku, wani shafin kuma zai zama sadaukar wa gare ku*


*Ina godiya ga dukkan d’aukacin masu bin wannan littafin*


*Allah ya bar mu tare*🤝🏽🤝🏽🤝🏽




_A wannan shafin nake sanar da makaranta wannan littafin cewa na tsayar da wannan littafin har sai bayan sallah in Allah ya kaimu saboda kusantowar azumi_


_Allah muke rok’o yasa mu fara azumin nan cikin kwanciyar hankali, ni’ima, lafiya da wadata_


_Ya Allah kasa muna daga cikin wad’an da z aka ba ma aron rai da za mu ga wannan watan mai alfarma, idan kuma kwanan mu ya k’are kasa mu cika da Imani_


_Allah kasa mu fara azumin nan lafiya, mu gama shi lafiya_

 




59&60


Yaya Faruk ne ya tako cikin takun k’asaita ya tawo gurin da nake, ni kuwa in ban da addu’a baa bin da nake yi a raina saboda ban san wani mataki zai d’auka a kaina ba.


Hannu na ya rik’e cikin d’aurewar fuska, yana min wani irin kallon da ni kaina bazan iya fassara shi ba.


Dr ne ya fara min wani hautsinannen kallo ganin hannu na a hannun yaya Faruk, hakan da na fahimta yasa na fara k’ok’arin k’wace hannu na amma ko alamar sake wa bai yi ba, ganin in na ci gaba da jan hannu n azan iya ja ma kaina ciwo yasa na hak’ura.


Direct motar shi ya nufa dani ya zaunar dani a kujera mai zaman banza sannan ya kulle motar.


Gurin motar Dr ya nufa wanda tun a lokacin da yaya Faruk ya rik’e hannu na yake kallo na.


Wani irin murmushi yaya Faruk yayi ya ci za gefen le’ben shi, kana ya kalli Dr da wani irin d’aurewar fuska ya ce "Dr Sadik ko?" ya tambaye shi.


Shiru Dr ya mishi bai bashi amsar tambayar da ya mishi ba, sai ma k’ara tamke fuskar shi da yayi.


Yaya Faruk bai damu da rashin amsawar shi ba, ci gaba da yayi da maganar shi.


"Warning nake so in maka, na ga alamar kamar ilimin addini bai gama wadatar ka ba, idan ba ka sani ba, ina so ka sani, ba kyau neman aure akan nema, hakan haramun ne kuma ya sa’ba ma addinin musulunci, ina so ka sani bikin mu da ita bai fi 2 month ba, ka fita harkar ta, idan kuma ka k’i… hmmmm" ya k’arashe maganar yana girgiza kai.


"Duk wannan maganganun da kake yi kana nufin zai sa in tsorata ne, ko in ja baya da neman Zarah, hakan bai girgiza ni ba, sai ma k’ara min k’arfin gwiwa da yayi, abin da nake tutiya dashi shine Zarah tawa ce, tun da ni take so, ka ga ni ke da power akan ta".


Jin wannan kalamen Dr yasa yaji wani irin ‘bacin rai ya ziyarce shi wanda yafi na da, yana ganin gwara ya koya ma Dr hankali yasan shi bat saran shi ba ne, don haka cikin fushi ya cakumo shi, Dr wanda ya ji hannun soja da kyar yake numfashi, har ya duk’ule hannun shi zai kai mishi naushi, ko me ya tuna ya sake shi ya bar gurin. 


Dr kuwa tun da ya samu yaya Faruk ya sake shi, ya shiga motar shi ya ja ta da gudu ya bar unguwar.


Ni kuwa tun da na ga abin da yaya Faruk ya ma Dr, na ji kamar ni aka ma wa, tun da ni na janyo mishi hakan, kuka kawai na fara yi mai tsuma zuciya.


Yaya Faruk na shiga cikin motar ya ji sautin kuka na ya cika mishi kunne, duk da kukan na ta’ba mishi zuciya hakan ba zai hana ya hukunta ni ba, gani yake yi in ya bar ni haka zan k’ara ganin lagon shi ne in raina shi.


Wata irin juyowa yayi ya kalle ni da idon shi da ya canza launi, ya daka min wata irin tsawa da na ji kayan ciki na sun kad’a.


"Fatima fitar min daga mota kafin in illata ki" ya fad’a cikin tsawa.


Saboda tsoratar da nayi yasa na kasa bud’e k’ofar, sai rawa da jiki na yake yi.


Tsawar da ya k’ara min ce yasa na fara k’ok’arin bud’e motar ko ta wani hali, ni dai in samu in fita daga motar, a yanayin yaya Faruk, in akwai abin da yafi illatawa, nasan zai iya.


"Ki fita nace…" Ya k’arasa maganar yana buga hannun shi a sitiyarin motar.


Ai ni ban ma san yadda aka yi na bud’e ba, ji na kawai nayi na fad’o daga motar, ban damu da buguwar da nayi ba na mik’e na fara tafiya da sauri ba tare da na juyo na kalli inda yaya Faruk yake ba.


Haka na ci gaba da tafiya har na k’araso layin mu, jiki na kuwa sai ciwo yake min saboda fad’uwar da nayi lokacin da na bud’e motar.


Lokacin da na kai gate d’in gidan mu, tsayawa nayi na goge hawayen da ke fuska ta nayi, ba na son kowa ya fahimci halin da nake ciki.


Da yaya Khalil na had’u a gurin shak’atawa yana waya, gani na da yayi ne yasa ya katse wayar da yake yi tawo guri na.


Cikin tsokana yace "matar Soja daga ina kike ina ta neman ki".


Ban ce mai komai ba, nasan idan na bud’ e baki zan mishi magana, kuka ne zai fito.


Ido ya tsura min yana kallon yanayi na.


Hannu na ya kamo ya kai ni gurin shak’atawa ya zaunar dani akan jurera, shi ma kujerar dake kallo na ya zauna.


"Fatima me ya same ki na ga idon ki yayi ja".


"ciwo idon yake min".


"Fatima nasan akwai abin da yake damun ki, tun dawowa ta daga service na lura da kin canza, da kina fad’a min damuwar ki, amma yanzu ban san me yasa kike so ki ‘boya min ba, baki san in na gan ki a damuwa ba, nima ina shiga damuwa, ki daure ki fad’a min kin ji Auta".


Maimakon in fad’a mishi abin da ke damu na, sai ma kuka da na fara yi mai ban tausayi.


Da ina da hali da na fad’a ma yaya Khalil damuwa ta kamar yadda ya buk’ata, nasan shi zai ba ni shawarar da ta dace da ni, amma a yanzu ina ganin ba bu wani amfanin fad’a mai tun da har na bar maganar ta kawo wannan lokacin da komai yazo k’arshe.


Tun da na fara kukan yake kallo na, yadda ya lura ina da buk’atar yin kukan a yanayin da ya lura ina ciki, sai da ya bari na gama kukan sannan ya taso ya zo gun da nake.


Farin handkerchief d’in shi yasa yana goge min hawaye, a lokaci d’aya yana girgiza min kai alamar kar in ci gaba da kukan.


"Fatima wannan kukan da kika yi, shi ya tabbatar min da kina cikin damuwa, amma ba zan matsa miki ki fad’a min a yanzu ba, yanzu ki tafi d’akin ki huta, anjima zan zo in same ki muyi maganar".


Tashi nayi na bar gurin, yayin da yaya Khalil ya bi ni da kallo yana k’issima abubuwa da yawa a ranshi.


Yaya Khalil mik’e wa yayi ya shiga motar shi ya tafi gidan su Anisa.


San da ya isa gidan, bai shiga ciki ba, parking yayi a harabar gidan ya kira wayar ta ya sanar da ita zuwan shi..


Ba a fi mintuna 5 ba sai ga shi ta fito cikin shigar material kalar milk, ta yafa k’aramin gyale a kanta.


Da murmushi ta k’arasa side d’in kujera mai zaman banza tana murmushi.


Shima murmushin yake sakar mata yana ci gaba da kallon ta ganin kayan yanda suka amshi jikin ta.


"Sannu da zuwa yaya Khalil".


"Yawwa Anisa, sannun ki gimbiya ta".


Rufe ido tana dariya kana ta ce "kai yaya kana sa ni jin kunya".


Shima Dariya yayi yace "Au kunya ta kike ji, gwara ki daina wannan kunyar taki, dan b azan yarda da haka ba".


Sunkuyar da kai tayi tana ci gaba da murmushi.


Hira suka ci gaba da yi kafin ya canza akalar zancen da cewa "Anisa dama akwai tambayar nake so in miki, ina so ki ba ni gaskiyar amsar".


Mai da hankalin ta tayi gare shi tana sauraren shi.


"Anisa me kika fahimta a yanzu game da Fatima, nasan tana cikin damuwa amma in na tambaye ta sai tace min ba komai, ina son in kin san wani abu ga me da halin da take ciki, plsss ki fad’a min, nasan ba za ta rasa fad’a miki ba".


Ita kanta ba za ta iya cewa ga abin da yake damu na ba, tun da ban fito na fad’a mata ainihin matsalata ba, amma tasn duk wani halin da nake ciki, ba zai rasa nasaba akan magana ta da yaya Faruk ba, ba ta son a ce ta bakin ta za a ji komai, gwara ya gano me ke damuna da kanshi, don haka tace "gaskiya yaya Khalil ni ban san me yake damun Fatima ba, ni kaina na lura da canzawar ta, lura da nayi kamar ba ta son kowa yasan halin da take ciki, yasa nima ban matsa mata da tambaya ba, amma ni kaina ba na jin dad’in canzawar Fatima".


"Shi kenan Anisa, insha Allahu zan gano ko ma me yake damun ta, ba ri in k’arasa gida, sai mun yi waya, ki gaida Momi".


"Za taji, ka gaida Fatima da Ummu".


Motar yayi wa key, yayin da Anisa ke d’aga mishi hannu.


Yaya Faruk kuwa, tun san da na bar motar ya kwantar da kanshi a jikin sitiyari, wani irin zafi yake ji a k’irjin shi.


"Me yasa Fatima take son d’aura mishi damuwa da hayaniya, idan bai wasa ba zai iya kamuwa da wani ciwon duk a dalilin son Fatima, So ya zamar mishi babbar cuta a gare shi tunda wacce yake so ba ta damu da halin da zai shiga ba".


Sai da ya kusan kwashe mintuna 10 a gurin kafin ya ja motar ya nufi gida.


Yana shiga gidan ya wuce side d’in shi ba tare da ya shiga side d’in Momi ba.


Kwanciya yayi ya d’aga kan shi sama yana tunanin makomarshi a guri na, abin da yake k’ara d’aga mishi hankali bai wuce yadda bikin yake k’ara matsowa ba a lokaci d’aya kuma al’amura suna k’ara rinca’be wa.


Da yana ganin matsalar mai sauk’i ce, sai yanzu yake ganin abin ya wuce tunanin shi.


Yanzu wani mataki ya kamata ya d’auka? Wannan tunanin shi yafi mishi yawo a zuciyar shi.


Momi ce ta fito daga kitchen ta kalli Anisa da take faman buga game a wayar ta.


Kiran sunan ta Momi tayi ta amsa mata.


"Anisa yayan ki bai shigo ba, na ga motar shi ya dawo, nasan halin shi ba lallai ba ne in yaci abinci, d’auki food flask d’in nan ki kai mai".


"To Momi bari in je in kai mai".


San da ta shiga d’akin, samun shi tayi yayi zurfi a cikin tunani.


Tsayawa tayi tana kallon shi, yayin da wani irin tausayin shi yake k’ara mamaye zuciyar ta.


A hankali ta k’arasa kan center table ta ajiye food flas d’in kana ta wuce gurin shi.


Kusa dashi taje ta zauna tana kiran shi, amma ko alamar amsawa bai yi ba.


Ganin hakan ne yasa ta rik’o hannu shi.


D’ago kanshi yayi yana kallon ta.


Sanin ba zai mata magana ba a halin da yake ciki yasa tace "yaya Faruk me yake damun ka, plsss yaya Faruk ka fad’a min ko nima zan ji sanyi a raina". Ta k’arashe maganar hawaye na zuba a idon ta.


Yadda Anisa take damuwa da lumuran shi, yana ganin ba zai iya ‘boye mata komai ba.


Don haka yace "Fatima ce matsala ta".


Da sauri ta tare shi da cewa "Me ta maka yaya Faruk".


Zayyane mata komai yayi na abun da ya faru yanzu tsakanin shi da ni.


Wani irin haushi na ne ya kama Anisa, tana ganin lokaci yayi da ba za ta iya zuba ido yayan ta ya fad’a wani hali ba, za ta fito ta fad’a mata tasan me yake wakana.


"Yaya Faruk, ina ganin wannan maganar ya kamata a ce su Dadi sun san halin da ake ciki, ka ga bikin ku na matsowa, in ba an shawo kan matsalar da wuri ba, komai zai iya rinca’be wa, barin wannan maganar zai iya jawo maka wata damuwar".


"Kar ki damu Anisa, ni kaina ina tunain yin hakan, amma zan ci gaba da yin k’ok’ari na dan in ga komai ya zama normal, ba komai ba ne nake son in fad’a ma su Dadi su dinga ganin laifin Fatima, ina sa ran komai zai daidaita".


Anisa jinjina irin son da yaya Faruk yake min ta ke yi, tasan idan ya rasa ni zai iya shiga wani hali, fatan ta Allah yasa komai ya daidai ta.


Haka su ka ci gaba da tattaunawa akan matsalar.


Sai da ta tabbatar yaci abinci kafin ta mishi sallama ta bar d’akin.


Tana zuwa d’aki ta ga ba za ta iya jurar ganin halin da yaya Faruk yake ciki ba, shawara ta yanke akan taje ta nemi izinin zuwa gidan mu, tana ganin ta hakan ne za ta samu sassauci a yadda ta ke jin zuciyar ta.


Da zuwan ta, ta fad’a ma Momi tana son zuwan gidan mu, Momi ta ba ta izinin zuwa.


A lokacin da Anisa tazo gidan mu, ina d’aki na, ni kaina a lokacin ba zan ce ga abin da yake min dad’i.


Gaisawa da Ummu na ji suna yi kafin ta shigo d’aki na.


Da shigowarta ta nemi kujerar mirrow ta zauna tana kallo na.


Cikin murmushi na ce "Ashe manya ne a gidan namu, Anisa ya su Momi?".


"lfy lau" Ta ba ni amsa a tak’aice.


Lura da yadda ta ke kallo na da kuma yadda ta amsa min yasa na zargi ko akwai wata a k’asa.


"Fatima ina son mu yi wata magana da ke" Anisa ta fad’a.


"Ina jin ki" Na ba ta amsa.


Anisa cikin damuwa ta ce "Fatima ban ta’ba zaton hakan daga gare ki ba, tuntuni na lura da canzawar ki, ban san canzawar taki tana da alak’a da yaya Faruk ba, ban tsammaci za ki ‘boye min me ke tsakanin ki da yaya Faruk ba, Fatima yadda na d’auke ki, ashe ke ba haka ki ka d’auke ni ba, sai daga baya duk na samo amsar da nake buk’ata a gurin ki, shine kin min haka ne saboda kina ganin yaya Faruk d’an uwa na ne, zan goyi bayan shi, tabbas hakan ta ke a guri na, zan iya yin komai dan ganin yaya Faruk ya samu abin da yake buk’ata, ina gani ko da a ce yaya Faruk ba d’an uwan ki ba ne, ya ci a ce kin so shi saboda irin soyayyar da ya nu na miki na tsawon lokaci da ya d’auka yana rainon soyayyar ki, amma ke sai ki ka za’bi son zuciyar ki na ganin kin samu abin da kike so, ba tare da kin lura da halin da zai shiga ba, shawarar da zan ba ki shine yaya Faruk shi yafi dacewa dake ba Dr da kika d’aura ma so ba, wannan shawarar da nake baki ita, ina fad’a miki ne ba wai dan yaya Faruk yana matsayin d’an uwa na ne, sai don ina duba amincin da ke tsakanin mu dake, ko da yake nasan canzawar ki duk yana tattare ne da son da kike ma Dr, nasan za ki iya yin abin da yafi wanda ki ke yi, Dr shi ya janyo har ki ka canza, dan ni kaina nasan ba halin ki ba ne".


Duk da nasan abin da Anisa ta ke fad’a min gaskiya ne, yau da alama Anisa na kai ta k’arshe ne tun da ta fito tana fad’a min wannan maganar, kasancewar ta ba ta da fad’a, amma hakan ba zai sa in mata shiru ba ganin yadda take ba ma Dr laifi a maganar.


"Anisa ina ganin duk maganar da za ki yi, ki tsaya a iya kaina, Dr ba ruwan shi a wannan maganar, hasalima sai yau ne yasan me yake tsakani na da yaya Faruk".


Wani irin murmushin takaici tayi sannan ta ce "Ai ke ba za ki ga laifin shi ba, tun da kin yi nisa a son shi, duk yadda za a fad’a miki gaskiya ba d’auka za ki yi ba, dan haka bazan ga laifin ki ba, abin da nake so in tunasar dake, yaya Faruk kamar matsayin miji yake a gurin ki, tunda duk an yi abin da musulunci ya tanada, shaidu ne kad’ai ba su shaida ba, ya kamata ki san da haka".


Katse ta na yi da cewa "Ashe kin san ba a d’aura ba kenan, kin ga bai da damar hana ni kula Dr in ma shi ya turo ki".


Cikin ‘bacin rai Anisa ta ce "Yaya Faruk bai san zan zo nan gidan ba, bare har ya umarce ni da na zo na miki magana, ke kanki kin San Yaya Faruk ba zai aikata haka ba, ni da kaina na ga ya dace na zo".


"Anisa kar ki ga laifi na, ni kaina na rasa me yasa na kasa jin son yaya Faruk a raina, na san ya kuma cancanta da in so shi".


Wani irin kallo Anisa ta min kana ta ce "Son zuciya shi ya jawo miki haka, ba wai zuciyar ki ce mai laifin ba, Fatima ina guje miki ranar danasani a lokacin da ba ta da amfani a gare ki, Makauniyar Soyayya da ki ke ma Dr shi zai jawo miki hakan".


Kalamen Anisa sun min zafi, amma nasan ni ce mai laifi, ci gaba da tanka mata zai iya sa rai ya 'ba ci.


Ci gaba tayi da cewa "In har Yaya Faruk ya shiga wani hali, ke ce sila, da ma ai kin ta'ba fad'a min shi ba ya cikin tsarin Wanda kike so ki aura" Anisa ta k'arashe maganar tana mai zubar hawaye.


Kalamen ta sun sa jiki na yayi sanyi, nasan tun da ta fad'i hakan, ba zai rasa nasaba da halin da Yaya Faruk yake ciki a kaina.


Ba abin da ya dace da nayi a lokacin da ya wuce nima in zubar da hawayen ko na samu sassauci a halin da nake ciki a yanzu.


Duk wannan maganganun da suke yi Yaya Khalil yana bakin k'ofa yana jin me suke cewa, tun dawowar shi Ummu ta fad'a mai Anisa ta zo tana guri na, shi yasa ya taso ya tawo d'akin, wajen shiga d'akin ne yaji maganganun da Muke yi.



Ganin shi kawai muka yi a d'akin ya shigo yana min wani irin kallo da bai sa ba yi min irin shi ba.


Ganin irin kallon da yake min ne yasa jiki na ya k’ara sanyi, nasan yaya Khalil na ‘bata mishi rai, ba kasafai ka ke ganin ‘bacin ranshi ba, amma in ranshi ya ‘baci bai iya nuna fushin shi ba.


Anisa da ta lura da shigowar yaya Khalil yasa ta mike’ tana goge hawayen ta da niyyar tafiya.


Ta fara tafiya ne yaya Khalil ya kira ta cikin sanyin murya.


Juyowa tayi ta kalle shi kafin ta ci gaba da tafiya, da alamar ba za ta tsaya ta saurari mai zai ce mata ba.


Ci gaba yayi da kiran sunan ta, ko alamar juyowa ba tayi ba ta bar d’akin.


Shi kanshi yaya Khalil yasan yau Anisa ran ta ya ‘baci, kuma ko waye aka ma d’an uwan shi haka, fushin da zai nuna kenan.


Don haka ba zai matsa mata a yanzu ta saurare shi ba, yasan Anisa ba ta d’aukar abu da zafi, idan ta huce zai je ya lallashe ta.


Yasan yanzu gurin Ummu za ta, yana da tabbacin ba za ta fad’a mata halin da ake ciki ba.


Bayan fitar ta ne ya maida kallon shi gare ni.


Cikin d’aurewar fuska ya kira suna na "Fatima".


"Na’am yaya Khalil".


"Fatima abin da kunne na ya ji min gaskiya ne cewa ba kya son yaya Faruk duk tsawon lokacin nan da aka d'auka?".


Shiru na yi ban bashi amsa ba..


"Fatima kar ki bari raina ya ci gaba da ‘baci, zan miki abin da ba ki za ta ba, ki bani amsar da na tambaye ki".


Yanzu idan na fito na ce mishi ba na son yaya Faruk, nasan na k’ara ma kaina wani laifin ne, gwara na mishi shiru.


"Me kika mishi Fatima da har yake k’ok’arin shiga wani hali akan ki".


Cikin kuka na ce "Yaya Khalil ni ba abin da na mishi, Anisa ce take ganin kamar laifi na ne".


Watsa min harara yayi yace "Ba ma laifin ki bane ko? to laifin uban waye?" ya tambaye ni.


"Laifin waye tun da kin ce ba naki ba ne". Ya sake jefo min tambayar.


Kuka kawai na ke yin a yadda abu biyu suka had’un min, ga fushin yaya Khalil da yake yi da ni, ga kuma fad’an da yake min.


Ci gaba yayi da cewa "Fatima kar ki bari mu sa’ba akan wannan maganar, ba za ki ji dad’in hakan a waje na, kar ki ga ina miki wasa, zan mugun sa’ba miki idan har hakan za ki ci gaba da yi, so ki ke yi ki tarwatsa mana zumuncin da muke yi mai dad’i, gashi yanzu ma Anisa ta fara d’aukar zafi akan abin da kike ma d’an uwan ta, ki dawo hanya, in ba haka ba kuma ni zan dawo dake, in ban da isakanci ya za ayi bikin ki ya kusa ki ci gaba da kula wani Dr, ke a haukar ki duk cikin so ne, to wannan ba so bane, shirme ki ke aikatawa, ya kamata ki fuskanci gaskiya ki so wanda yake son ki da gaskiya da amana, nasan son da shi Dr Sadik d’in yake miki ba zai kai na yaya Faruk ba".


Rarrafo wa nayi na kama hannun shi ina ci gaba da kuka.


Cikin kuka nake cewa "yaya Khalil dan Allah kayi hak’uri, kar kayi fushi da ni, kai kad’ai ne kake nuna damuwar ka a gare ni, kaima in ka juya min bay azan shiga wani hali, ni kaina na rasa yadda zan yi, ban san wani irin so nake ma Dr ba da na kasa hak’ura dashi, ina so ka taya ni da addu’a, ni kaina nasan ba na kyauta ma yaya Faruk"…….


Ganin yadda nake kuka yasa yaji tausayi na ya kama shi, yasan duk wannan abubuwan da nake yi, sharrin so ne ya jawo hakan, amma ba zai yi saurin nuna tausayawar shi gare ni ba, yafi so in gano gaskiya in gyara.


Mik’ewa yayi ya kalle ni yace "Fatima wannan kukan ba shi bane mafita gare ki, ki dawo hanyar da za ta fi miki shine ki nuna kulawar ki ga yaya Faruk sannan ki nuna mishi so, ina ganin wannan shine mafita a gare ki, gargad’i na k’arshe da zan miki shine in har ran Anisa ya ‘baci, to naki sai ya fi na ta ‘baci, dan ni nasan darajar soyayya, ba irin taki ta rashin madafa nake yi ba".


Yana gama fad’ar haka ya bar d’akin, yayin da naci gaba da wani irin kuka mai ban tausayi.





_Hmmmmm a min hak'uri da wannan ba yawa, sai bayan sallah in Allah ya kaimu za mu ci gaba da bin labarin Fatima_


_Anan nake ce mana Allah yasa ayi azumi lafiya_


_Allah ka yafe mana laifukan mu_


_'Yar mutan Paki na muku fatan alkhairi_


*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



      *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




_Wannan shafin naki ne namesake_. _Maryam Ibrahim Kusada_.

_Ban san irin godiyar da zan miki ba na irin yadda kike nuna min so da nuna yabawar ki akan novel d’ina, abin da zance shine Allah ya bar zumunci ya kuma kai mu lokacin bikin ki_.


_Ina miki fatan alkhairi_.🤝🏽



*INA SANE DAKU*


_Fans d’in Nana Khadija, gaskiya kun nuna mata k’auna_.


_Ana tare_.


_Gaisuwa ta musamman gare ku_.


*SAK’ON BARKA DA SALLAH*


_Alhamdulillahi ala kulli hal_.

_Yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da yasa muka yi azumi lafiya muka gama shi lafiya, Allah muke rok’o ya amshi ibadun mu yasa muna da rabon ganin na wani shekarar_.

_Anan ‘yar mutan Paki ke ma duk wani d’aukacin musulmi barka da sallah_.

_Allah ka maimaita mana_

_Taqabbalal lahu minna wa minkum_

_Happy Sallah 2 all my fans_


*BAN HAK’URI*


_Ina ba ma masoya wannan littafin hak’uri kan jinkirin da nayi wajen posting, sai a lokacin na k’ara tabbatarwa da wannan littafin yana da yawan mabiya da ni kaina ban san adadin su ba na yadda ake min magana ta Facebook, whatsapp, groups akan ci gaban novel d’in_.

_Ba abin da zan ce muku sai godiya da fatan alkhairi_.


_Ana tare har kullum_





61-62


Tun san da Anisa ta fito daga d’aki na take faman goge hawaye, ba hawayen komai take zubarwa ba sai na tausayin halin da yaya Faruk zai shiga in ya rasa ni, a yadda ta gama karanta ta tasan nayi nisa a Makauniyar soyayyar Dr Sadik da zai yi wuya in amince da yaya Faruk, duk abin da ka ga yaya Faruk na nuna damuwar shi a kai to ba k’aramin so yake mai, gashi yanzu na nuna cewa Dr ne za’bi na, fatan ta shine Allah ya sassauta zuciya ta in amince da yaya Faruk dan samun farin cikin shi da kwanciyar hankalin shi.


San da ta fito falon ba ta samu Ummu ba, hakan yasa ta nufi shashin ta dan yi mata sallama.


Samun Ummu tayi akan kujera da minhajil muslim a hannun ta tana karanta wa.


Sallama Anisa tayi kana ta nemi guri ta zauna akan carpet d’in dake shimfid’e a d’akin.


Amsa mata Sallamar Ummu tayi kana ta rufe littafin dake hannun ta.


Da fara’a Ummu ta kalle ta tace "ya aka yi ne Anisa".


"Ba komai Ummu, zan koma gida ne".


"Da wuri haka". Ummu ta sake tambayar ta.


"Akwai abinda zanyi ne in na koma gidan".


"To ina Fatiman?".


"Tana d’aki, mun yi sallama da ita"


Yanayin ta da Ummu ta gani ya nuna kamar akwai abin da ya had’a ta da ni, amma ganin ba ta fad’a mata ba yasa ba ta tambaye ta ba.


"Khalil ne zai kai ki? Ummu ta sake tambayar ta.


Cikin jin kunya Anisa ta amsa mata da cewa "A’ah ba shi zai kai ni ba".


Ummu ce ta fara fad’a "Ban son shashanci, me yake yi da ba zai kai ki ba, kira min shi…".


Da sauri Anisa ta kar’bi zancen da cewa "Ni na ce ya bar shi, yace in jira shi ya ci abinci yayi wanka, na ce kawai ya bar shi ya huta tun da yanzu ya shigo gidan".


"To ai shi kenan, ki gaida su Hajiya"

Nan suka yi sallama ta tafi.


Shi kuwa Yaya Khalil na fito wa ya nufi shashin shi.


Rasa me yake masa dad’i yayi, bai ta’ba tunanin zan makance akan soyayya irin wacce nake yi a yanzu ba, bai yi tsammanin in yaya Faruk ya min tayin soyayyar shi zan bijire mai ganin yanzu shak’uwa ta shiga tsakanin mu dashi a lokaci guda, ashe abin ba haka yake ba, hangen shi ne ya nuna mishi kamar ina son yaya Faruk, ashe yaya Faruk ne kad’ai yake d’awainiya da so na, ni ta Dr Sadik nake yi, da tun farko yasan yaya Faruk ne ya fara fad’a min yana so na kafin Dr, da bai nuna amince war shi ga Dr Sadik ba, da yasan yadda yayi ya raba mu dashi ta hanyar nasiha da lallashi da dubara, ko a yanzu lokaci bai k’ure mai ba, yana ganin zai iya juyo da hankali na in maida soyayya ta ga yaya Faruk dan shi yafi dacewa dani ba Dr Sadik ba.


Ko a yanzu ya samu makamin da zai yi amfani dashi tun da yana fushi dani, yasan bazan juri ganin fushin shi ba, dole ne in zo in nemi afuwar shi, ta wannan hanyar zai yi amfani yaga ya karkatar da akalar tunani na zuwa ga yaya Faruk.


Yanzu abin da yafi tsaya mishi a rai shine yadda Anisa ta nuna fushin ta, yasan ba k’aramin abu bane ya ‘bata mata rai kasancewar ta ba mai yawan fushi ba, zai bata time ta huce duk da yasan ba laifin shi ba ne, amma yasan yanzu laifi na zai iya shafar shi, shi bai ga laifin ta ba dan kowaye yaga ana ma d’an uwan sa haka iya nuna fushin da zai yi kenan.


Haka yayi ta sa’ka da warware wa shi kad’ai.


Tun san da yaya Khalil ya bar d’akin na ci da kuka na ba mai lallashi na, nasan na shiga tsaka mai wuya, wanda na ke sa ran zan samu sauk’i a gurin shi shima yayi fushi dani, ba abin da ke min yawo sai nasihar da ya min akan in nuna ma yaya Faruk so da kulawa, ni kaina nasan ya cancanci hakan daga guri na, "Me yasa ba zan ji shawarar da mutane suke ba ni ba akan yaya Faruk?" Na tambayi kaina.


"Saboda zuciyar ki ba tayi marhabin da tayin soyayyar da yake miki ba, shi yasa ba ki d’au shawarar da mutane suke baki ba" zuciyata ta bani amsa.


Yanzu gashi yaya Khalil yayi fushi dani mai tsanani wanda tun tasowa ta bai ta’ba nuna min ‘bacin ran shi irin haka ba, nasan yaya Faruk bai iya ‘bacin rai kasancewar sa mai hak’uri, abin da yafi shine in bari ya huce da ga fushin da yake yi sai in bashi hak’uri.


Wata dabara ce ta fad’o min akan in fara kiran Anisa in ba ta hak’uri duk da nasan ba dole ba ne ta saurare ni, in na aikata hakan nasan zan yi saurin samun sassauci daga gurin yaya Khalil dan nasan yana d’aya daga cikin abin da yasa yayi fushi dani.


Trying d’in numbar ta nayi amma ba ta shiga, hakan yasa na hak’ura da kiran ta.


Ban san tsawon lokacin da na d’auka a zaune a d’akin ina karanta wasik’ar jaki, sai da na duba lokaci na ga ya ja.


Ummu kuwa shirun da taji yayi yawa ne yasa ta taso ta tawo d’aki na.


Tun da ta shigo d’akin ta lura da akwai abin da yake damu na ganin yadda na canza a lokaci guda, ga ido na da ya canza launi wanda hakan ke nuna da na ci kuka.


Kiran suna na tayi cikin sanyin murya "Fatima".


Sunkuyar da kaina nayi kana na amsa mata da "Na’am Ummu".


"lafiya kika zauna ke kad’ai a d’aki har na tsawon lokaci ba ki fito ba" ta tambaye ni.


"Ba ni da lafiya ne" Na ba ta amsa cikin rashin karsashi.


"Me yake damun ki?" ta sake jefo min wata tambayar.


Shiru nayi saboda ban san inda zan ce yana min ciwo ba.


Shirun da taji nayi ne yasa tabbatar da akwai abin da yake damu na.


"Me ya samu idon ki na ga kamar kin yi kuka" ta k’ara watso min tambaya.


Cikin daburce wa na amsa mata da "Ba…komai" Na amsa mata a tak’aice.


"Fatima! d’ago ki kalle ni" Ummu ta fad’a cikin bayar da umarni.


A hankali na d’ago na kalle ta kana na sunkuyar da kaina k’asa.


Kusa dani tazo ta zauna ta rik’e min hannu tana mai ci gaba da nazari na.


Da tasausassar murya Ummu taci gaba da cewa "Fatima yanayin ki da na gani ya nuna min akwai abin da yake damun ki, tun kwanaki na lura da canzawar ki, shiru na miki dan in ga iya gudun ruwan ki, amma na lura abin naki gaba yake yi, kin san a duniya ba wanda yafi cancanta da ki fad’a ma damuwar ki irin ni, fad’a min me yake damun ki Auta ta kin ji" Ummu ta k’arasa maganar cikin lallashi.



Nasan Ummu ba ta son gani na cikin damuwa, yanzu ita ma sai ki ga ta fi ni shiga damuwar.


"Ina ma zan iya fad’a mata halin da nake ciki?".


Zuciyata ce tayi saurin kwa’ba ta akan haka, nasan in akwai wanda ran su zai fi ‘baci akan tsakani na da yaya Faruk na bijire ma soyayyar shi bai wuce Ummu da Abbu ba, ya zamar min dole in ci gaba da taka tsantsan kar su fahimci akwai wata badak’alar a tsakanin mu dashi.


Wata dubara ce tazo min akan in ce mata ba ni da lafiya, nasan shi kad’ai ne zai iya sa ta yadda da magana ta.


"Ummu ni kaina ban san me yake damu na, kawai ba na jin dad’in jiki na ne" Na k’arasa maganar cikin rawar murya.


Ummu ba wai ta yadda da maganar da na fad’a mata ba ne, ganin ban son fad’a mata abin da yake damu na yasa ta k’yale don ba ta son ta takura min, ko ni na fahimci hakan a fuskar ta.


Murmushi tayi kawai ta ce "Shi kenan Auta tun da kin ce ba abin da yake damun ki, ki ci gaba da addu’a, Allah ya kawo miki sauk’i, Allah ya baki lafiya".


"Amin Ummu".


Mik’ewa Ummu tayi ta fara tafiya tana cewa "Ki daure ki fito falo, ba na son ki na zama a d’aki ke kad’ai".


"Toh Ummu gani nan fito wa" na amsa mata.


Ummu ba ta dad’e da fita ba na fito daga d’akin saboda ba na son ta tabbatar da akwai abin da yake damu na.


A ‘bangaren yaya Faruk kuwa, tun san da Anisa ta bar d’akin ya yanke shawarar ya koma Abuja kawai, hakan zai sa ya fi samun relief akan damuwar da yake ciki, da wannan tunanin ya samu ya kwanta.


Tuni bacci yayi awon gaba dashi, sai da ya kwashe kusan awa biyu yana bacci kafin ya tashi ya shiga band’aki ya watsa ruwa ko ya samu sauk’in da yake ji a jikin sa.


Ba laifi san da ya watsa ruwan yaji dad’i a jikin sa, hakan yasa ya canza shigar shi zuwa farar jallabiya ya nufo side d’in Momi.


Samun ta yayi a falo tana zaune, kusa da ita yazo ya zauna.


Hira suka fara yi da Momi, a cikin hirar ne yake fad’a mata gobe zai koma Abuja.


Mamaki ne ya kamata ganin bai dad’e da zuwa ba har zai koma, tafiya lokaci guda, ko ba komai yadda bikin shi yake matsowa ya d’an k’ara kwana biyu, ita a yadda ta lura kamar akwai abin da yake damun shi.


Cikin kulawa tace "Faruk da wuri haka, yanzu na lura tafiyar bazata kake so ka dinga mana, sai dai kawai kace wa mutane gobe zaka tafi, kai ba a sanin rananr tafiyar ka, sai kace wanda ake kora" ta k’arasa maganar tana kallon shi.


"Sorry Mommy, nima ban san da wuri zan koma ba, aiki ne ya taso aka kira ni, maganar shirye-shiryen biki duk mun gama magana da Daddy".


"Nasan dama haka za kace aiki ne ya taso, dashi kake fake wa in kana son koma wa, anya Faruk ba abin da yake damun ka kuwa?".


Murmushi yayi yace "Ba komai Momi, kawai dai yanayin aikin mu ne sai a hankali".


"Allah ya taimake ku, ya baku nasara a aikin ku".


"Amin Momi".


Suna cikin hirar ne Anisa tayi sallama ta shigo.


Amsa mata sallamar Momi tayi kana Anisa tazo kusa da Momi ta zauna.


"yaya Faruk sannu da hutawa, Momi sannu da gida".


"Yawwa Anisa har kin dawo, ya mutanen gidan, ya 'ya ta Fatima? Momi ta tambaye ta.


"Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ki".


"Ina amsawa".


Sai a lokacin yaya Faruk ya d’ago fuskar shi suka had’a ido da Anisa ya watsa mata harara.


Kallon da ya mata na nuni da alamar tambayar me taje yi a gidan yau.


Fahimtar hakan da tayi yasa tayi saurin sunkuyar da kanta.


Zuciyar shi ce ke raya mishi Anisa ta je ta min magana ne saboda taga halin da ya shiga, wata zuciyar na k’aryata zargin shi.


Tashi yayi ya nufi masallaci saboda kiran sallar da yaji ana kira yayin da Momi da Anisa suka mik’e dan ba da farali.


Lokacin da na fito falon, Ummu kawai na samu a dining area a zaune tana cin abincin.


Kitchen na wuce na zubo abincin na tawo da gorar ruwan faro na zo na zauna a d’aya daga cikin kujerun dining d’in.


Tun da na yi lomar farko na ajiye cokalin saboda yadda ba ni da apatite a baki na kamar wacce tayi fama da rashin lafiya.


Ummu na lura da yadda nake wasa da cokalin dake hannu na a cikin abincin.


"Fatima ki ci abincin kin ji, za ki ji k’arfi a jikin ki tun da ba dad’in jikin ki kike yi ba, daurewa za kiyi".


Ni sai a lokacin na tuna ma da nayi k’aryar ciwo, ya zama min dole in ci abincin dan kar Ummu ta jefo min tambayar da ban da amsar ta.


Haka na dinga tsakurar abincin ina ci ba wai dan ina jin dad’in shi ba.


Muna cikin cin abincin ne yaya Khalil yayi sallama.


Amsa masa sallamar nayi, a lokaci d’aya ina addu’ar Allah ya sa yaya Khalil ya huce dan bai da wuyar sauka.


Guri ya nema ya zauna kana ya ma Ummu sannu da gida ta amsa masa.


Juyowa nayi da niyar yi mishi magana, yanayin fuskar shi da na gani ba annuri yasa na k’ara shan jinin jikina.


Cikin dauriya na daure na ce "yaya Khalil sannu da zuwa".


Maimakon ya amsa min sai ya maida hankalin shi kan wayar shi yana danne-danne.


Jikin na ne yayi sanyi da abin da yaya Khalil ya min, hakan na nuni da bai huce da abin da na mishi ba kenan.


Ummu ce ta ce "Khalil ba ka ji Fatima na maka sannu da zuwa ba ne ka mata shiru".


Sai a lokacin ya dakatar da danna wayar da yake yi ya kalli Ummu ya ce "Oh dani take yi, ban ji ba ne".


Dariya Ummu tayi ta ce "Ba na son shiririta Khalil, ya za ayi ace baka san kai Fatima take ma sannu da zuwa ba, kar kasa in muku dariya kai da mutuniyar taka".


Shima dariya yayi ya ce "A min afuwa".


Ummu ce ta kalle ni ta ce "Fatima jeki ki d’akko food flask a kitchen da plate, ki had’o mishi da maltina a fridge.


Da sauri ya katse Ummu da cewa "No, ta bar shi kawai, bari in je in d’akko".


Mik’ewa yayi ya nufi kitchen d’in.


Ban san lokacin da hawaye ya zubo min, ba zan juri irin wannan hukuncin da yaya Khalil yake min ba, zan iya shiga wani hali da wannan salon da ya fito min dashi ta hanyar hukun ta ni, abin da yafi shine in je in bashi hak’uri ko da bai huce ba.


Ganin Ummu na kallo na yasa na fara goge hawayen da ya zubo min.


Ummu ba ta ce min komai ba, nasan ita ma tayi zargin akwai abin da ya had’a ni da yaya Khalil wanda ba ma so ta sani.


Yaya Khalil ne ya dawo ya zauna ya fara cin abincin shi cikin walwala kamar ba shi ba ne ya gama d’aure fuska yanzu.


Hira suke yi da Ummu, ni kuwa shiru nayi kamar ba na gurin, da na gaji da zaman ma tashi nayi na dawo falo na kunna Tv.


Ido na akan allon Talabijin d’in yake, amma ni kaina idan aka tambaye ni akan me ake yi a Tv d’in ba zan iya fad’a ba.


Tunani na kawai nake yi akan yadda lamura suke canza min.


Bayan tafiya na ne Ummu ta kalli Khalil ta ce "Me ya had’a ka da Auta na ga tana maka magana ka share ta, sannan na ce ta zubo maka abinci kace ba ka so, to ba na son irin haka, da ka shiga kitchen har hawaye tayi, gwara ko me ta maka ka fito ka fad’a mata da wannan irin hukuncin da kake mata".


Bai so Ummu tasan me yake faruwa, yasan sai ta fi ci nuna ‘bacin ranta akan hakan, shi yasa ba zai fad’a mata me ya had’a shi da ni ba, jin bayanin da Ummu tayi ya tabbatar da na fara nadamar abin da na yi, shi yasa ya min haka dan yasan zan ji zafi a raina.


Murmushi yayi ya ce "Ummu ba abin da ya had’a ni da Autar ki, san da ta min sannu da zuwa ban ji bane ina faman danna waya, abinci kuwa da na ce ta bar shi na hutar da ita ne na ga tana cin abinci, ai ni da Fatima ba a jin kan mu" Ya k’arasa maganar yana dariya.


Jin wannan amsar da yaya Khalil ya ba ta yasa ta ji dad’i, tasan ba abin da ya had’a ni dashi, dama zargi take yi.


Tashi yayi ya bar falon, ko kallon in da nake bai yi ba.


Lallai fushin da yaya Khalil yake yi da ni mai girma ne, dan bai ta’ba min irin hukunci haka ba.


Sai da na bashi kusan minti goma da tafiya sannan na nufi sashin yaya Khalil.


Dariya Ummu tayi san da ta ga na nufi side d’in yaya Khalil ta ce "Kun fi kusa, ai ku ba a jin kan ku".


Yaya Khalil tun san da ya koma d’aki yake kiran Anisa, cikin sa’a ringing uku tayi ta d’auka.


Sauke wata ajiyar zuciya yayi saboda yadda yake kiran ta tun san da ta bar gidan su amma ba ta d’auka ba, sai yanzu ya samu ta d’auka.


Sallama ta mishi ya amsa mata cikin jin dad’in d’aukar wayar da tayi.


Khalil ne ya ce "Tuba nake yi, duk da ban san laifin da nayi ba ake k’in d’aga waya ta" ya fad’a cikin wasa.


Wata kunyar shi ce ta kama ta ganin yadda yayi ta kiran ta amma tayi biris.


Cikin sanyin ta tace "Ka yi hakuri yaya Khalil".


"Ba komai Sister, ni ke da ba da hak’uri, nasan ke aka yi wa laifi ke da yaya Faruk, kuma ko waye dole yayi kishin d’an uwan sa, ni ban ga laifin ki ba, sai dai laifin wani ba ya shafar wani Anisa, bai kamata ki yi fushi dani ba bayan kin san ba zan goyi bayan Fatima ba akan son zuciyar ta".


Tasan abin da yaya Khalil ya fad’a gaskiya ne, sai a yanzu take ganin wautar ta na k’in tsayawa ta saurare shi da d’aukar wayar shi san da ya kira ta, a nan ta k’ara gode ma Allah da ya ba ta yaya Khalil a matsayin wanda za ta aura saboda irin halin shi mai sauk’in kai da fahimta.


"Kayi hak’uri yaya Khalil na yi laifi, raina ne ya ‘ba ci a lokacin".


"Ba komai Sister, ni dama na fahimci dalilin fushin ki".


"Na gode yaya Khalil".


"Kin wuce hakan a guri na, buri na ki kasance cikin farin ciki".


Suna cikin hirar ne na shigo d’akin da sallama.


Juyowa yaya Khalil yayi ya kalle ni kana ya kau da fuskar shi ya ci gaba da wayar da yake yi.


Sai da na kwashe sama da minti goma a tsaye ba tare da yaya Khalil ya gama wayar da yake yi.


Gajiyar da nayi da tsayuwa ne yasa na nemi gefen gadon shi na zauna.


Sai da ya gama wayar ne ya juyo ya kalle ni cikin d’aurewar fuska kamar bashi ba ne ya gama kashe murya a waya.


"Ina fatan lafiya dan na ga yanzu muka rabu dake a falo"

 Yaya Khalil ya fad’a cikin d’aure fuska.


Cikin rashin karsashi na ce "Dama yaya Khalil na zo in ba ka hak’uri akan abin da ya faru".


"Ni ai ba ni kika yi wa laifi ba, wanda kika yi ma laifi ya kamata ki je ki ba hak’uri ba ni ba, ina ganin za ki iya tafiya in wannan maganar ta kawo ki, ina da abin yi".


Kuka na fashe dashi mai ratsa zuciya, kafad’ar shi na je na kwanta ina mai ci gaba da kukan da nake yi, nasan zan samu sauk’i a halin da nake ciki.


Tausayi na ne ya kama yaya Khalil, bai so ya nuna min ya hak’ura da wuri, yafi so yaga mun daidaita da yaya Faruk.


"Wannan kukan da kike yi bai da amfani Fatima, abin da yafi shine ki yi abin da ya kamata ki yi shine nuna ma yaya Faruk so, da kin aikata hakan ina ganin ba ki da sauran wata damuwa".


Cikin kuka na ce "Zan kiyaye yaya Khalil, kayi hak’uri".


Shima a lokacin zuciyar shi tayi rauni, ba zai juri ganin kuka na ba.


Hawaye ya fara share min ya ce "Is ok Fatima, kukan ya isa haka, plsss ki daina abin da ba na so, ya kamata a ce yanzu kin san abin da ya dace dake ba bin son ranki ba, ya kamata ki kula ki gyara".


"Toh! yaya zan gyara".


Murmushi ya min yace "Shi kenan Auta, komai ya wuce".


Dad’i ne ya kama ni ganin yaya Khalil ya daina fushi da ni.


Hira muka ci gaba dayi da yaya Khalil kamar ba abin da ya faru tsakanin mu.


Washe gari yaya Faruk ne ya zo gidan mu.


Gaisawa suka yi da Ummu ya ma sallama akan cewa zai koma Abuja, add’ua ta mishi kamar yadda ta saba yi mishi in zai koma Abuja.


San da ya shigo ina juyo maganar shi, tsoron fito wa nake yi nasan bai gama huce da fushin da yake yi dani.


Kiran wayar shi ne ya shigo waya ta, ganin sunan shi a jikin screen d’in waya ta yasa gaba na ya fad’i.


Cikin ladabi na gaishe shi, ya amsa min kamar ba ya so.


"Ki same ni a waje ina jiran ki, kar ki ‘bata min lokaci" ya fad’a cikin bayar da umarni.


"Gani nan zuwa" na bashi amsa a tak’aice.


Hijab kawai na sa na fad’a ma Ummu yaya Faruk na kira na a waje kana na fita.


Ko da na k’arasa inda motar shi take bai da alamar fito wa daga motar, knocking d’in glass d’in kofar nayi.


Sai da ya gama jan ajin shi kafin ya fito daga motar.


Gaishe shi nayi ya amsa min da k’yar.


Sai da ya gama shan k’amshin shi kana ya ce "Yau zan koma, nasan za ki yi farin ciki da hakan, kar ki yi tunanin dan ba na nan za ki aikata abin da kike so, nasa a dinga lurar min da takun ki ko ba na nan, ki guji had’uwar mu in na kama ki da bijire ma umarni na, idan buk’atar wani abu ya taso kya iya ma Khalil magana ya amsar miki gurin Aminu, na bar mishi komai, ina k’ara gargad’in ki, ki kiyaye, ina fatan kin ji abin da na ce".


"Na ji" na amsa a tak’aice.


"Ki fad’a min in akwai abin da kike buk’ata akan hidimar bikin, ba na jin zan shigo Kaduna sai a satin bikin, in akwai event d’in da kika tsara sai ki fad’a min ko ki turo min ta waya, ni ba zai wuce walima da Dinner zan yi ba, nasan sauran friends d’ina ba za su rasa organizing d’in nasu event d’in ba".


"Ba na buk’atar komai".


"Wannan kuma ruwan ki, Sauri na ke yi ina so in biya ta gurin Aminu, maganar kayan akwati za mu yi waya dake sai ki fad’a min kalar kayan da kike so duk da Dadi ya ce in barshi zai min akwatin, nima zan had’o nawa sai a had’a".


Lallai yaya Faruk ba k’aramin shirya ma bikin nan yayi ba yadda yake maganar abubuwan da za a gudanar a bikin, gashi yanzu Dadi ya ce zai yi akwati, nasan kuma ba k’aramin kud’i zai kashe a had’a akwatin, amma a haka yake cewa shima sai ya had’a nashi akwatin, nasan duk son da yake min ne ya jawo haka.


Katse min tunani na yayi da cewa "Za ki iya koma wa ciki".


"Allah ya kiyaye hanya" abin da na ce kenan na koma ciki.


Hak’ika ya ji dad’in addu’ar da na mishi, sai da ya ga komawata ciki kana ya ja motar shi ya tafi.


Bai zarce ko ina ba sai gurin aikin yaya Aminu, kiran shi yayi a waya akan ya k’araso kasancewar sun yi waya zai zo ya same shi.


Yaya Aminu ne ya fito daga office d’in shi ya zo ya same shi a mota.


Musabaha su kayi kafin su nemi guri su zauna a harabar company d’in.


Tattauna wa suka yi game da yadda yaya Faruk yake so bikin ya gudana.


San da yaya Khalil zai tafi ne ya nemi alfarma a gurin yaya Aminu akan yasa ido a kaina da lura da taku na da wanda nake mu’amala, ciki har da Dr Sadik.


Yaya Aminu ya mishi alk’awarin zai sa ido a kaina.

Da haka suka yi sallama dashi ya tafi.



Zaman kad’aicin da yake damu na yasa na tambayi Abbu zuwa gidan su yaya Aminu in yi kwana biyu saboda yanzu yaya Khalil bai cika zama ba yana zuwa kamfanin su Abbu kafin ya fara aiki.


Da k’yar na samu Abbu ya amince min kasantuwar yadda biki na ya matso kusa, ni ko a jiki na, gani nake yi kamar ba ni za ayi wa auren ba.


Shirya wa ayi cikin wani less kalar ruwan madara, an mishi ratsi da kalar army green, d’inkin an min riga da skirt six pieces, gyale ma da takalmi da jaka duka ruwan madara na sa.


Kwalliyar da nayi ba k’aramin amsar jiki na tayi ba.


Sallama nayi ma Ummu na fito yaya Khalil shi zai sauke ni a gidan.


Bayan mun k’arasa gidan ne yayi parking d’in motar shi a waje, muka jera a tare muka shiga gidan.


Anty Jiddah muka samu a falo da su Humaira suna kallon cartoon.


Lokacin da muka gaisa da ita ne take tsokanar shi da cewa ina ya bar Anisa muka zo ba tare da ita ba.


Ba ta amsa yayi da cewa ba tasan za mu zo ba, da ta biyo mu.


Sun d’an ta’ba hira da Anty Jiddah, yayi ma su Nabil da Humaira wasa kafin ya mana sallama ya tafi.


Tun da na zo Anty Jiddah ke tsokana ta da amarya kin sha k’amshi.


Fad’a min hakan da take yi sai in ji takaici ya kama ni.


Nasihohi da jan hankali akan zamantakewar aure had’e da sirrin gyaran jiki duk sai da Anty Jiddah ta zauna ta koya min.


Wasu littattafai ta bani in karanta mai suna Ki gyara da kan ki, Sinadarin Ma’aurata, Mu san kan mu Maza da Mata da sauran littattafan girki da ta k’ara had’a ni dasu duk da nima ba baya ba ce wajen iya girki.


A cikin nasihar da take min ne cikin dubara take ta k’ara nuna min in yi hak’uri in yi ma yaya Faruk biyayya, ko ba komai shi d’an uwa na ne kuma wanda zai zama miji na.


Ni dai kawai sauraren ta nake yi ba dan na ba nasihar ta mahimmanci ba, a wannan lokacin tunani duk yana gurin Dr ne da kwana biyu ba mu had’u ba, gashi ina son ganin shi amma ban san wace hanya zan yi amfani da ita ba wajen ganin shi, ina tsoron hukuncin da zan fuskanta a gurin yaya Faruk duk da nasan ba ya gari, nasan tun da yace ya sa a lura da taku na har zuciyar sa ya fad’a, matsalar dai ba ta wuce ban san wa ya sa ba.


Lokacin da yaya Aminu ya dawo ya ganni yayi murna da zuwa na, haka muka zauna muna hira dashi.


Yaya Aminu sai wata kulawa ta musamman yake ta bani, nasan hakan baya rasa nasaba da auran da ya ga zanyi, sai tambaya ta yake me nake so ya siya min.


Har gajiya nayi da bashi amsar ban a buk’atar komai, da ya dame ni da tambaya ne nace mai komai yayi min ina so ba ni da za’bi.


Da haka muka yi sallama dashi na wuce d’akin su Humaira.


Wahegari bayan na taya Anty Jiddah aikace-aikacen gida ne nazo na zauna ina kallon wani indian film mai suna "Ok Jaoon".


Kiran Dr ne ya shigo cikin waya ta.


D’auka nayi yake sanar dani ya za ayi mu had’u, yana so muyi wata magana ne, ni kaina zan so mu had’u, sai dai hanyar da zan bi mu had’u ne zai zaman min wuya tun da mun gama makaranta, gashi ba inda nake zuwa.


Sanin yaya Aminu ba ya nan yasa na kwatanta mishi gidan yaya Aminu na ce ya zo ya same ni a can.


Ba a d’au wasu mintina ba sai ga kiran shi ya shigo yana sanar da ni ya k’araso.


Tashi nayi na je na sanyo hijab, na wuce d’akin Anty Jiddah na mata k’aryar yaya Faruk ne ya ba ma wani abokin shi sak’o ya kawo min.


A Gaban gidan yayi parking d’in motar shi.


Ina zuwa ya bud’e min d’ayar k’ofar na shiga.


Musayae kallo muka yi ni dashi, kowa da irin sak’on da yake so ya isar ma d’an uwan sa.


Ni na katse shirun da cewa "Dr ina wuni, ya aiki".


"lafiya lau Zarah".


Shiru ne ya k’ara ratsa wa a tsakanin mu kafin Dr ya fara da cewa "Zarah ina ganin wannan had’uwar da muka yi dake ne nake son mu yanke decision, ban a son mu tsaya muna ‘bata wa kan mu lokaci, kin ga dai abin da yayan ki ko in ce masoyin ki ya min akan ya ganni dake, duk tak’amar shi ke zai aura, ina so yanzu ki fito ki fad’a min me kika yanke game da ni, in har kin za’bi auran shi to ni gwara in hak’ura duk da son da nake miki, in kuma ni kike so kamar yadda kike fad’a min ina so ki tabbatar min mu samo maslaha a yanzum lokaci na dad’e k’urewa ba mu nemar wa kan mu mafita ba".


A tunani na zan iya hak’ura da Dr in auri yaya Faruk ko da ban jin son shi a raina, sai dan son da yake min da kuma ‘yan uwa na da suka nuna sun fi son in aure shi.


Sai a yanzu nake ganin wauta ta na yanke hukuncin hak’urin auran yaya Faruk da zanyi, alhalin ga wanda zuciya ta take da muradi, take mishin son da ba zai misaltu ba, wanda son shi ya gama dabaibayi a cikin ta, kullum dashi take kwana tana tashi da tunanin sa.


Yanzu maganar da Dr yazo min da ita tayi min tsauri, za’bin raina zan bi ko za’bin abin da ‘yan uwa na da iyaye na suke so zan bi?

Ni kaina na gaji da wannan al’amarin da yak’i zuwa k’arshe, gwara ayi mai yiwuwa tsakanin yaya Faruk da Dr.


"Anya kin ma yaya Faruk adalci? Duk irin son da yake nuna miki amma za ki za’bi son ran ki" abin da zuciya ta take fad’a min kenan.


Wata zuciyar kuwa cewa take min "Ba wani maganar adalci, zan ba wa zuciya ta abin da take muradi".


Sadik ne ya katse min tunanin da nake yi da cewa "Ke nake saurare Zarah, me kika yanke". Ya k’arasa maganar yana kallo na.


Ajiyar zuciya na yi kana na ce "Dr kai kasan kai nake so, ni kaina ban san irin son da na ke maka maka ba, tuntuni nake neman hanyar da zan samar mana mafita dan mu samu mu ci ribar soyayyar mu ta hanyar yin aure amma na rasa, na bar maka komai Sadik, duk hukuncin da ka yanke ya yi min".


Wani lalausan murmushi yayi yana jinjina irin son da na ke mishit un da har na bashi za’bi ya yanke hukunci ba tare da tunanin wani irin hukuncin zai yanke ba.


"Kenan za ki iya hak’ura da auran Faruk d’in ki aure ni". ya fad’a yana min wani sihirtaccen kallo.


Jim nayi ina tunanin irin hukuncin da zan fuskanta na k’in auran yaya Faruk alhalin komai ya zo k’arshe tun da bikin bai wuce wata d’aya da satittuka ya rage ayi bikin, idan na duba halin da zan shiga in na rasa Dr na gwammance in fuskanci kowane irin hukunci ne in dai za a barni da shi.


Da wannan na samun k’arfin gwiwar amsa mishi ‘Zan hak’ura da auran shi in dai a kan ka ne".


"Good, abu na gaba shine ya za ayi ki guje ma auran shi".


Nan na tsaya tunanin hanyar da zan bi wajen ruguza auran amma ban samu ba, k’arshe dubarar da ta fad’o min shine in bar garin har bayan bikin, idan aka ga ba na nan za a hak’ura da auran, in yaso in komai ya lafa sai in dawo in ba su Abbu hak’uri da yaya Faruk hak’uri, in yaso sai a d’aura mana aure da Dr Sadik, wannan shawarar ce tayi tasiri a kaina.


Fa’da ma Sadik nayi shawarar da na yanke, shi kan shi ya ba ni go ahead akan hakan, wannan ita kad’ai ce hanyar da za mu bi dan ganin mun cin ma burin mu.


Shawarar da ya k’ara ba ni ita ce kar in nuna ma kowa komai a game da plan d’in da muka had’a, in ci gaba da shirye-shiryen bikin har lokacin da muka gay a kamata in yi tafiyar.


Muna cikin wannan maganar ne motar yaya Aminu ta shigo layin, ban wani tsorata ba tun da ina cikin mota, nasan ko ya tambayi Anty Jiddah, za ta fad’a mishi k’aryar da nayi mata ne.


Yaya Aminu na shiga falon ya nemi guri ya zauna, Anty Jiddah ce ta d’akko mishi abinci da driks ta kawo mai, ya fara cin abincin ne yake tambayar ta ina nake jin shiru ban fito na mishi sannu da zuwa.


Sanar dashi tayi abokin yaya Faruk ne yazo kamar yadda na fad’a mata, dakatawa yayi da cin abincin yace mata bari ya lek’a ya ga ko waye.


A lokacin ni kuma na fito daga motar ni da Dr muna ta kawo idea yadda komai zai tafi ba tare da an samu matsala ba, sauran dubarar mun barshi ne akan sai mun had’u a waya.


Yaya Aminu shi kuma a lokacin ya fito ya tsaya a bakin gate yana kallon mu, juyawar da zanyi muka ha’da ido dashi.


Sai a lokacin ya lura da san da ya dawo ya ga motar amma baisan ni ce a ciki ba.


Sallama na yi ma Dr akan cewa zan koma gida yaya Aminu ya dawo, nan muka yi sallama dashi ya tafi.


Ni duk a tunani na yaya Aminu bai ga fuskar Dr ba, shi yasa na fara tafiya ta cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fargaba ba.


Ganin ina tawowa yasa yayi saurin koma wa cikin gida.


Post a Comment

0 Comments