ZURFIN CIKI hausa novels cmplt

 IKI book 4 part 1

ZURFIN CIKI book 4 part 1

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:42

Inna harira tace, Allah ya kyauta ku tashi mu tafi.

Suka mike Suka nufi dakin ummi. Duk da ummi a

da bata tunanin tana da lokacin bishira, yanxu

kam dole tasan zaman da zasuyi. Su inna saratu

suka ce ma ummi duk abinda zatayi don allah

kada ki kulata. Suka ce tayi harkokin gabanta tayi

biyayya wa mijinta shine abunda zai fisheta.

Ummi tace To amma a zuciyarta bata tunanin

zata zuba ido a rainata. Suna tafiya fatima ta

shigo yiman sallama, ummi tace don allah fati ki

dan tsaya ni kadai fa zan zauna a dakin nan. fati

tace wayace kada kisan kawaye? Ummi ta ce

wane kawaye, auren da a ka daura cikin yan

mintina? Fati tace, Yau zakiji abinda mata kaji.

Ummi ta damko mayafin fati, ni fa inajin turo, wai

da gaske da wahala ko kina tsokanata ne? Fati

ta kamo kunnen ummi tayi mata rada. Ummi ta

zaro ido tare da cewa, Da gaske? Fati ta sheke da

dariya tace sai nazo jin batun. Ummi tace sirrine

ya za'ayi in fada miki sirrina? Fati tace au ni

shine na fadamaki nawa ko? Ummi tace kinyi

haram da kika fada fati tace, "ke kuma kinji

haram ko? Suka sa dariya. Duk yanda ummi taso

fati ta tsaya amman taki, don haka sukayi

sallama. Fati ta shige dakin bishira don yi mata

sallama. Bishira tace, fati fitar min daga daki

bana wasa dake, tunda kema naga kin koma

jam'iyar waccan yar iskar, fati ta fita, cikin ranta

tana cewa ba zanki yar uwata ba don kishinki na

banza tayi tafiyata. Ummi tsuru tayi tanaji tsoron

abinda fati ta fadamata, amman sai wata zucia

tace keda ba sonki yake ba kila ma bazaibi ta

kanki ba, sannan ta samu yar natsuwa. Abba ya

fito zai nufi gida sai kuma ya fasa ya nufi super

market, ya siyo audugar mata yana tsammanin

gobe ne zata tashi da al'ada a lissafinsa. Tun

sanda ta soma bai taba mance ranar ba, haka in

ya chanza mata lokaci duk yana lissafe. Ya sai

masu yan kayan masarufi sannan ya fito, gida ya

nufa amman gabansa yana faduwa kila har

yanxun ba a kai ummi ba. Da yayi fakin sai kuma

ya nufi gidan su umma duk kowa ya watse. Yayi

sallama tsohuwa tana alwala ta amsa. Umma

daga kicin ta amsa, tsohuwa tace "wane kinibibin

kuma ya kawoka mai sunan malam? Bayan an

kai maka ita? Yace kaji tsohuwa da wata magana

da gurin ummi nake zuwa? Ni gidan mu ne. Tace

kadaiji shi, takwara dai kada inji kada in gani, don

nace mata duk abunda kuka mata tazo ta

fadamin. Yarinyar nan tana kuka wiwi tabar gidan

nan. Umma cikin dariya tace "toh ai tsohuwa in

don Abba baza ayi fada ba, ummin ce dai abin

jama kunnen. Tsohuwa tace 'a' a daina zancen

nan suwaiba kada ma ya samu nayi. Abba yace"

Toh bari in zo in hada maki kayanki mu tafi can

don kada wani ya zafin cewa. Kinga kyafi tare

mata. Tace ina gana nan din ma zanji. Yace

Alhaji sun shigo kuwa umma? Tace A'a basu

shigo ba. Yace toh bari in isa gida. Tace toh

Abba ummi ma dazun aka rakata. Don allah Abba

ka kara hankuri a kan na da, sannan matarka

kuma kada kace zaka nuna mata bambanci a kan

ummi yar uwarka ce. Ka kwantar mata da hankali

ka mata adalci, sannan kada ka bawa ummi kofar

da zata raina bishira. Yace zan kiyaye insha allah,

kuma don allah umma ki kara mika godiata gurin

alhaji. Tace haba Abba yaya kake fadin haka?

Alhaji ai mahaifinka ne karka dinga kallon

alakarka da ummi. Yace haka ne duk da haka dai

a min godia, tsohuwa tace yaki godia ya samu

mata a sama don rashin imani mai sunan malam

ko gyauto bai sa mata ba, toh kasani tana binka

bashin lefe. Abba Yace umma ni dai na wuce.

Umma cikin dariya tace "Toh Abba. Yace tsohuwa

ni nayi gaba, don in na cika tsayuwa a nan kila

mu dambace, Tsohuwa tace kai dai jeka na baka

amana ya tafi yana dariya. Koda ya kai kofar

gidan sai ya bude mota ya dauki kayan

masarufinshi ya nufi cikin gidan salam dai duk da

jarumta irin tashi gabansa ne ke faduwa. Bai san

wace irin masifar bishira ta tanada ba. Ya shiga

da sallama. Bishira tana zaune akofar daki tana

goye da muhibba, amman bata amsa ba. Duhun

magriba ya soma dan daf da a kira sallah a ke,

yace bishira ya ba a tada inajin ba? Tace tunda

kazo yanxun ai sai ka tada kai. Da kafin wata

tazo ai baka taba zuwa kace a tada inji ba. "Abba

ya kalleta a zuciyarshi Yace" mata kenan masu

manta alhaji. Ya aje ledodin hannunshi ya nufi

injin. Bishira ta mike ta nufi ledodin tana fadin

Tun yanxu a aka shigo mata da kazar, alamun ba

za'ayi ada ba kenan. Ni lokaci na sa wuraren tara

ya shigo ina lissafe da komai, ta bude ledodin sai

taga kayan masarufi d kuma audugar mata. Tsaki

taja tare da dangwarar dasu yana kallonta da ya

kara mai ya tada injin sa yazo ya kwashe ledodin

ya shiga falonta.vels / ZURFIN CIKI book 4 part 2

ZURFIN CIKI book 4 part 2

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:44

Kujerun da aka chanza mata masu kyau, amman

a ran abba yace ya basu sati biyu. Ya cire riga ya

fito yana son yayi wanka ne kafin a kira sallar

magana,yaja ruwa da sauri da sauri yayi ban daki

ya fito ya shiga falo ya kwalama bishira kira.

Tace minene kake damuna? Yace ina aka kai min

akwatuna na? Tace tace ina kuwa gasu can a

kicin da sauri ya fito, kicin din lafia? Ya tsaya

yana kallonta bani da mutuncin da za'a sa min

kayana a daki? Tace ni da aka guji dakina da

kayan a kace ni kazama ce, me zaisa in sake

kaine? Daga baice komai ba ya nufi kicin ya

kwaso akwatuna shi da takalmin shi ya kai

falonta. Bai tsaya chanza kaya ba, ya nufi

masallaci don zai rasa sallah. Bai baro masallaci

ba sai bayan isha'i amman bishira tana zauna.

Ummi kam ta kasa fitowa don tana kyankyamin

ban dakin, gashi al ada ta sameta da yamman

nan, sannan duk tanajin abin da sukeyi da

matarshi. Ya shigo gidan ya chanza kaya sabi fil,

ya feshe jikinsa da turarukkanshi wayar shi ta

soma ringing ya daga salis ne. Yace aboki in ba

sallama akwai daga hannu ko? Kace an kai maka

rabin ranka koda ba zamu rakaka ba ai kayi

mana sallama. Cikin dariya Abba yace na yafe

salis yace To Allah ya bada zaman lafia. Suka yi

sallama zai aje wayar kenan sako ya shigo. Ya

duba ummi ce da wayar nan da ya bata ajiya

cewa tayi, ina da matsala, ina bukatar taimako.

Gabanshi ya fadi, sai kuma ya tuna kila al'adar

ce, don haka sai ya saka hularshi ya dauki ledar

audugar ya nufi dakinta. Har lokacin bishira nan

zaune inda take, tace au tun daga yanxu za'a

soma rashin adalcin? An dauki leda an nufi

dakinta? Sam baiko waiwayo ba, yayi sallama ta

amsa tare da gyara mayafinta, ya shiga suka kalli

juna Cikin ido zukatansu sukayi fari kal. Cikin

taushin murya yace, wane taimako kike bukatar?

Ta lumshe ido sannan ta juya masa baya domin

kunya ta rufeta. Yace To karba ya mike mata

ledar ta waiwayo ta ansa da hannu biyu. Mamaki

ya cikata ganin audugar, ya yayi har ya san tana

bukatar audugar kuma a ina yake sanin lokacin

al'adarta har idan ya chanza? Tace nagode yayi

dan murmushi nima ina godia. Ya juya har ya

daga labule tace "Em na ce....." ya waiwayo yace

kika ce mi? Tace don allah inason maganin

wanke bayi ne, tayi maganar Cikin kyankyami,

sakamakon irin dattin da tagani a bandaki tare da

gamsa kuka. Yayi murmushi wane iri kikeso?

(IZAL) yace ai akwai amman yanxu Bai kamata ki

shiga wankin bayi ba. Tace zan wanke in dai

akwai. Yace bari in wanke maki, da sa tace a'a

yaya Abba zan wanke. Falon ya koma ya cire

rigarshi ya shiga jan ruwa. Bishira tana zaune ta

mike ina badai abokitaina ba, in zaka kwashe

mata rijiyar kwashe, amman a juye ko in baras

kuma in dai ruwan da za'ayi amfani dashi ne

kakeja, To kesani nima duk lokacin da zanyi

amfani da ruwa saika dibar min, ehee. Ummi ta

fito da bokitai don duk tana jinsu, tazo wurin

Cikin sanyin murya tace, Ya Abba don allah ka

bari in ja ruwan nan. Ya kalleta, take ya manta da

duk bakin Cikin da bishira ta kunsa mashi.

Yanxun daga zuwa saiki fara jan ruwa? Ummi

tazo ta kama igiyar gugar, ai ba zama nazoyi ba,

Ya Abba bauta nazo yi, Aljanna sai an dage. Ya

saki dariya bishira ta dakatar dashi da ce wa

"Karuwanci za'a gwadaman? Ta daga ruwan da

ya zuba a bukati zata watsama ummi, yace kina

watsa mata zan baki Mamaki. Cikin tsawa yayi

maganar ta tsaya cak da bokitin yace, Sakarya

mai kishin hauka. Yaci gaba da jan ruwan yana

zubawa abokitan da ummi ta fito dashi. Bishira

ta aje ruwan sannan ta hankadar dashi a kasa,

Bai ko kalleta ba. Ya zuba ruwan sannan ya fito

da izal da omo. Daki ummi ta koma ta dauko

tsinsiyar da aka sai mata don wankin bayi, kin

tafiya Abba yayi tana wankewa yana zuba mata

ruwa har sai da taga bayin yayi yanda take

bukatar sannan ta hankura. kyankyami jikinta

takeji don haka taje ta hada kayan wanka har

lokacinzurfin Ya Abba yana wurin rijiyar. So take

ya matsa taja ruwan amman yaki, don ya lura

bishira shi kadai take shakka zata iya zartar da

komai kan ummi. Shine ya sake zuba mah ummi

ruwan wanka, sannan ya coge har ta gama ta

fito rufe da hijabi tayi dakinta, sannan ya dauraye

jikinsa yaje ya maida kayanshi ya nufi wane.

Bishira tana nan wurin kofarta ta kasa zaune ta

kasa tsaye, bakinta kuma Bai fasa sambatu ba

sai kace sabon kamun hauka. Fadi take kuma a

zo a biyani duk basisikan da nike, ehee. Kuma in

yarinya tamin in murji bukina. Ummi kam ta

gyara jikinta tsab ta saka sabbin kaya ta feshe

jikinta da turarokan da umma ta sai mata. Tunda

ba lefe aka mata ba bare ta samu kayan shiga.

Kan doguwar kujera ta mike, salam yanzu taji

yinwa tana tsammanin rabonta da abinci tun

karin safe. Ta shafa Cikin ta ina ma umma na

aiko man da abinci. Ta furta a fili WAYA nan ta

jawo tana tunanin sanar da Abba cewa tana jin

yunwa. Sai wata zucia ta hanata wannan ba

girman amarya bane. don haka ta share ta bude

shafin game tana ta bugawa. Sai sha daya Abba

ya shigo gidan, ya rufe gidan. Nufinshi ya wuce

kai tsaye dakin ummi, amma sai ya tuna da kazar

da ita bishira ya sawo mata. Duk da baya tunanin

ta karba ga mamakinsa tana tsaye a tsakar daki

har yanxu da daurin kirji take. Wannan ya nuna

batayi sallah ba, bare wanka. Ya mike mata wata

harara ta zabga masa banaci, ya juya batare da

yace mata kala ba, ta biyo bayan shi, A bani

basussukana da nike bi malam. Ya nufi dakin

ummi taba biye dashi, ummi ta turo kofa dama

yana kokarin tura kofa dama yana kokarin tura

kofar bishira tana rike masa riga ta baya. Ya

waiwayo Cikin zafin nama zai wanka mata mari

sai taci sa'a ta tsugunna, Cikin azama ta yunkura

tayi baya da gudu. Banda tsaki da yaja Bai ce

komai ba. Ya shige dakin ummi da sallama, ummi

bacci ya dan dauketa saboda gajiya. A kan kujera

take da waya a hannunta. 4rm Shamsy bello

balarabe.IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 3

ZURFIN CIKI book 4 part 3

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:48

Niyyarta yau sai taji komai, don haka ta kai yarta

ta kwantar, dai dai lokacin ne abba ya fito don

kashe injin. Sake fitowar da tayi ne taganshi zai

koma. Wayan cewa tayi da daukar buta ta shiga

bandaki, shi kuma ya shiga daki ya kulle kofa,

tazo ta manne jikin kofar. Fitar abba shine yaba

ummi damar saka kayan baccinta, don bata iya

bacci da kaya masu nauyi. Fargabarta yaya

kwanciyar tasu zata kasance? Kan kujera ta

zauna tare da kwantar da kanta a hannun kujera.

Shima abba yana da jin zafi don baya iya bacci

da kaya sai da gajeran wando kurum, idanu ummi

ta kulle lokacin da taga ya abba ya soma cire

tufafinsa ga hasken cocilar da ya kunna. Filo ya

dauka ya jefa Kan doguwar kujera ya kwanta

rigingine, ganin haka sai ummi ta mike ta nufi

gado addu'a tayi sannan ta lumshe ido har bacci

ya dauketa. Fuskarta cike da murmushi zuciyarta

cike da godia allah yau gata dakin ya abba a

matsayin matarsa. Abu daya ya rage mata shine

ta koya masa yarda zaya sota. shima farin ciki

ne a ranshi yayi da idanuwanshi sukayi kuri a Kan

gado yana hango ummi ya ta zama halalinsa Abu

daya ya rage shine ya koya mata sonsa. Bishira

data labe bata jiyo komai amman kunnuwanta

suna jiyo mata magana kasa kasa,,hawaye na

zuba a idonta batasan iya adadin awanin data

dauka a kai ba. Koda ta koma daki juyi kawai

take a gado. Abbanta abun sonta yana can

kwance da wata, watar ma makiyiyarta wadda ta

tsana. Wata zuciya tace kije ki watsa masu man

petur wata tace ki bari da safe ki caka masu

wuka babu abinda bata rayaba har asubahin

farko. Labule ta daga ta shiga leke taga ko zasu

fito, lokacin ne kuwa abba ya fito yaja ruwa a

bokitai yayi wanka da alwala. Ba zata gane ko

wani Abu ya faru tsakaninsa da ummi ba don

wanka al'adarshi ce Koda bai dauki najasa ba.

Nafila ya shiga yi da rokon allah yasa ummi ta so

shi, ya kuma hada masa kansu. Koda zai tafi

masallaci bai tashi ummi ba tunda yasan ba

sallah zatayi ba. Bishira ta fito tasa kujera kofar

daki ta zauna, saboda tashi bai bar ummi bacci

ba, don haka ta tashi in tana al'ada yini take

wanka gaba daya sai ta tah ktankyamin jikin ta.

Ta fito da bokitai duk ta cika d ruwa, Bishira tana

kallonta sai da ta wanke bayi tas, sannan tayi

wanka. Sauri take tayi kwalliya don a cikin

nasihohin da umma tayi mata a safiyar da za'a

kawota gidan miji tace kada ta sake mijinta ya

ganta cikin kazamin yanayi. Kuma kada ta bari ya

shaki wari daga gareta, tayi shafe shafenta.

Atamfa ta saka riga da siket mai ruwan hoda

hoda da ruwan kwai. Daurin dan kwali ta kafa

sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshin

gaske, sannan ta shiga gyaran dakin duk da ba

datti yayi ba. kayan da abba ya cire ta ninke don

da jallabiya yake zuwa masallaci, sannan ta dau

kujera ta kishingida saida gari yayi haske sannan

ya nufo gida. Tsaki bishira ta jamashi maimakon

amsa sallamar ta kara da cewa an girma ba'a

san an girma ba, an kwana da yar ciki abin

kunya. Ai wallahi baka cika dan halas ba da ka

auri yarinyar datayi sanadin kulleka kaci duka har

aka ballaka ba. Ya kalleta dalilin kenan da ban

cika dan halas ba? Tace eh baka cika ba, yace

toh jeka naji ni shege ne, in don dai na auri ummi

ne, tace munafuki dama can kana sonta. Ya sake

wai wayoowa yace so kuwa mai tsanani. Takaici

ya cikata ta daga murya allah ya isa munafuki.

Ya nufi dakin ummi wadda ke sauraren duk

abunda ake. A cikin ranta tace ina ma son da

gaske ne? Tasan ya fada don kawai yaba

matarsa haushi. Da sallama ya daga labulen,

ummi ta amsa tare da tashi daga kishingida da

tayi, ya zauna tare da lumshe ido. Lokacin daya

kuma ya shaki kamshin turarukan data fesa. Ya

kalli Fuskarta labbanta da yake matukar so sun

sha jambaki ruwan hoda. Take abba ya manta da

duk wata damuna koh kalma marar dadi da

bishira ta fada masa. Daga inda take zaune ta

dan rankwafa don girmamawa tace ya abba ina

kwana? Lafia qalau ummin abba ya bakon wuri?

Ta lumshe ido saboda jin dadi sunan daya fada

mata. Alhmdllh ya sake karkatawa yana kallonta

sosai yace to masha allah, yanxu kinsan minene?

Ta tattara hankalinta gareshi tace a'a? Yace kiyi

hnkr nasan a al'adar ta hausawa amarya ta Kan

yi sati daya cir ba tare data yi ko cangal ba. Toh

hnkr zakiyi kinga ke tun daga kawoki jiya kin

soma da wanki toilet. Sannan yanxu ma ina son

ki ciro rishonki a hada shi a sa kalanzir mu karya.

Kin dai ga yanayin yanda matar gidan take

gudanar da nata kishin. Ummi ta gyara zama ta

tuna nasihar ummanta da tace in zaki yima

mijinki magana kalaman ya zamana kin zabo su

ne ba wai kin sakesu ba. Ta kalle shi, shima ita

yake kallo, tace ya abba don wannan ne kake ban

hnkr? Yayi murmushi tare da lumshe ido ya kuma

budesu lokacin guda, a yaran soyayya yana nufin

eh, itama ta fahimci yaren don haka taci gaba da

cewa. Ya abba ni dama ba zama nazo ba, neman

aljanna nazo kuma zanyi komai don na sameta.

Don haka kadaina bani hnkr umurni kawai zaka

bani. Tun daga tsakiyar Kan abba har zuwa

babban yatsansa sai da ya motsa, don sanyin

muryar da ummi tayi amfani da ita tare da

kyawawan kalaman ta. A zuciyarshi yace tabbas

ummi haihuwar ummanshi ce, duk rainon umma

dole zai zama daban ciki ya'ya. Ya kalli ummi

allah yayi maki albarka tace amin. Ta mike ya

bita da kallo taje gurin da a ka shirga mata

kayan aiki ta zakulo risho yace to muje kicin dinZURFIN CIKI book 4 part 4

ZURFIN CIKI book 4 part 4

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:13

Ta mike ya bita dkallo tje gurin da aka shirge mta

kayan aiki ta zakulo risho yce to muje kicin din.

Tkarya murya, ya Abba amin afuwa, bna son in

shiga kicin din can kmin hakuri insa rishona

akofar daki. Ykalleta, bazai tkura mta ba domin

ysan duk wnda yzauna da umma dole zai zama

me kyankyani, yce indai zai miki kiyi kawai , in na

smu ynd da nke so dga baya sai ayi miki kicin a

gurin, tce ngd. Shi kan da kanshi yfito darisho yn

budewa ya hadashi, tafito da tukunya tanufi rijiya,

ta dauraye sannan tazubo ruwa.Bishira kuwa

dma tazo talabe duk tji maganganun dsu kayine,

jin abba zai fito da risho sai ta gudu daki. Sintiri

ta dinga yi tna magana ita kadai, wato abban

walid nece mazai ce anga irin nawa kishin?

Yarinyar dya ce bsonta yke ba dole akayi masa

shine har ysoma kai mta gulmata. Har dawani shi

mata albarka , tunda uwarta ta kitso mata ynda

zata ce ai dole yashi mta albarka, to ni ya tsine

min kawai. Ummi ta amshi galan din kalanzir din

dga hannunshi tre da cewa ya abba kawo inzuba

zai ce ta barshi kenan wayarshi ta soma ruri,

yadaga. Anty ce, suka gaisa tce tna son yin

magana da bishira ya mike ytafi kaimata ummi

kam ci gbata yi dasa kalanzir dinta takunna

rishon tdora ruwan zafinta takoma daki, shima

yna bt wayar ydawo. Anty tce bishira dm na kira

kine inji bakuwar dta kwana a gidan da safennan

kin bta abin kari ko? Bishira tahade rai tamkar

tana gabanta, anty tome mexan bta, ina ruwana

ma da ita? Dazunnan fa suka gama gulmata wai

har yna ce mta tye hakuri tdai ga irin mtar gidan.

Anty tce hauka kike tyi shi ysa ai dole yce haka.

Ynzun dai sai ki tashi kibsu abin kari, hka da rna.

Karki sake yarinyar nan ta dora tukunya sai byan

sati daya, kina jina ko? Bishira tace to bdan

zancan ykai ranta ta amsa ba. Sai don tunanin

kada zancan zuwa makkanta yafasu . Sunayin

sallama ta aje wayar tre da cewa, koda uwarta

tke ywo bzan dfa mta abinci ba. Sai da ummi ta

wanke flas din shayin sannan tazuba ruwan, falon

bishira yje ydauko kayan shayin dbiredi. Tace,

itama kakai mta ruwan zafin. Yce ta dafa, ygama

yashirya tsaf don zuwa gurin aiki, harbakin kofar

daki tarakashi. Yce, ummi naroke ki koda bishira

tna zaginki ne don Allah kda ki kulata, sambana

ganin laifinta don nasan sboda sona tkeyi. Nan

da wni lokaci komai zai daidaita. Ummi tce kada

kadamu insha Allah ba abin dazai faru, allah ya

tsare yace amin nagode. Dakin bishira yaleka ya

amshi wayarshi, sannan yce mezakuyi drana?

Tzabga mishi harara, ina ruwana dawani abinci.

Ya aje mata dari hudu. Gashi kusai nama nasan

akwai komai ko? Tsaki taja, gara maka dauki

kudinka don bzan dafa ma munafukai suci suji

dadin zagina. Yakalleta, Allah yganar dke. Tdg

murya yganar dakai dai maci amana sainaga

bayanku. Bki yataba kafin yafita, baice mata kala

ba. Ummi ta kinkimi akwatinan kayan abba dya

kawo mt tgyara msu mzauni, sannan takwashe

'yan kofunan dasuka sha tea ta wanke. Sannan

takoma dki tna jin wsu kawayen bishira sunzo

sunata habaice dazage-zage, ummi bt fito ba

bare ta tanka. **** **** Bashir abin duniya ya

ishe shi, ykasa sukuni sbd son ummi, yzuga

ummanshi sun kai suka gidan su sahabi don

afasa auran anfasa kuma duk da hk ummin

tzama btashiba. Jinshi yke tamkar ykashe abba

don tsana, don hka koyaushe cikin zuga umma

yke dan kawai tatsani Abb. Guraran sha biyu

ummi bacci yasoma dibanta sai tji muryar

umman bashi akofar dakinta tna cewa ina ummin

tke munafauka, fitsararriya tadaga labulan kofar

tarike. ummi takalle ta. Kin kalle mi mna 'yar

makirai. Kin bar smun zman lfy a gidannan, kuma

uwarki ko tn tsafi dbakin kare dbakin dodo sai

kinbar gidan dana. Ke inzan tafi dazani daya

mtsawar bokaye da 'yan bori suna nunfashi kin

smun nutsuwa agidannan. Bishira tace, umma

shima munafuki ne shida yce bai sonta amma

dazun haryi dni sukayi. Umman bashir tce shi

Abba kimasa uzuri, duk abinda ykeyi byin knshi

bne, anriga an rikita shi, bakya ganin shi duk

afirgice yke? 'yar bori tafada min komai, ynzun

karya tambaya muke nema. Bishira tce duk dhaka

ma ynso, ai ance asiri yan tarad dahali. Umman

bashir tce hk ne, shi dinma ai ubansa zaici ba

dagin kafa. Ummi datna zaune kai duke, sam

zantukansu bsu dme tba, abu dya yagirgizata

btun asiri. Bta son ashiga tsakaninta da mijinta

tun kafin su fara son juna. Saidai kuma dta tuna

da addu'o'inta da takeyi bta fsa yi ba. Ga Azkar

safe dayamma, saitasamu ntsuwa tsan Allah

yafisu.ovels / ZURFIN CIKI book 4 part 5

ZURFIN CIKI book 4 part 5

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:33

Umman bashir tagama jarabarta tafita, karfe daya

drabi Abba ykira wayar dke hnnun ummi tdaga.

Cikin girmmawa tce, snnu da aiki ya Abba, ina ftn

kn cikin koshin lpy? Yyi murmushi cikin jindadi

yce, lpy nke ummi, am...in... Dama zan cene kin

ci abinci? Tce A'a, amma bna jin yunwa, dnaji

yunwa zn sha tea ai, kda kdamu kai fa kci? Yyi

dan tsaki, tsiyar bna cin abinci awaje ummi,

abincin umma kdai ke min dadi, Allah ys zki gjeta.

'yar driya ummi tayi, insha Allahu sai mna fita.

Yce anya kuwa? Tce insha Allahu ai nace. Kin

gma mgna yafadi tre dyin murmushi mai sauti,

yawwa bari in kirata ta turo miki da abinci, tce to

ngd. Yce, nima na gode, sai ndawo. Tce, to Ya

Abba kdawo lpy, ka kula min dkanka. Tkashe

wayar, yjima yna kallon wyar tre dmamakin ynda

ummi ta iya zantuka masu kwantar dahankali, irin

wdanda bishira da ta ba ta shekaru bta iya ba.

Ykira lyin ummanshi suka gaisa, yce ummana don

Allah kitura ma ummi abinci, umma tce, kan wani

dlili Abba? Tci gba dacewa, tbdijam!, bza ayi hk

dniba. Abba ymarairaice murya, don Allh ummana

yunwa tke ji. Umma tce, ta tashi tdora mna?

Abba tsaya kaji, dadai wta ce can kke aure ba

ummi ba sai na aika mta, amma ynzun ga

uwargidanka agidan shi kenan sai in aikamata da

abinci? Wannan ba gsky bne, sannan zgin da ake

min ai sai ya linku yfi nada, yce umma duk wnda

yzageki rshin fhimta ne. Kuma fana baiwa bishira

kudin cefane amma tki tdafa musu abinci, tce kila

tgaji ne, shiyasa bta dfa ba. Ita ummi dba saita

amsa tdafa musu ba? Yce, amma dai umma

tsakani da Allah kowacce amary bsai ta kwana 7

bsannan tke fara dfa abinci? Umma tce, ai ba

addini bne al'ada ce, don takama girki ai ba laifi

tyi ba, yce, shikenan umma tunda kin hna sai

anjima, tce mujima dayawa. Shiru abba yyi yna

tunanin mgangnun umma, ysan gsky tfada, amma

dmuwarshi ummi dbta ci komai ba. Ykalli agogo,

saura kusan awa 2 ytashi, wayarta yske kira,

tdaga yce ummi kisha tea din umma bta da

abinci kfin ndawo. Tce, to ya Abba, kkusa

dwowane? Yce, sai nan da awa 2. Tce to Ya

abba, sai ka iso. Bta wni sha tea bdon bta jin

yunwa sam, tshi tayi tasake kakkabe dkinta don

mutane suna tshigowa ganin dki yra dmanya. Tas

tkakkabe ko ina tafito tshare tsakar gidan lungu

dasako, bishira lokacin mbata gidan wsu yra

dsuka shigo tbasu kasko suka smo mt rushi

tzuba turaren wuta mai kyau dkamshi. Tnayi tn

kallon agogo, saura minti ashirin yaya Abbanta

ydwo ta wanke byi tsake wnka, sannan tdibar

masa ruwan wanka shima ta aje akofarta. Trufe

kafin ya iso, tshiga dki tna ta shafe-shafenta, sai

lokacin bishira ta shigo gida. Tna rike da 'yarta

akafada, ita kanta 'yar ba amata wanka ba bre

uwar, tkwabe hijabi trataye, sannan tzauna akofar

dakin tna kallon tsakar gidan. Duk da ita knta

gurin ybta sha'awa, amma bki ta taba tre dcewa,

wahalalliyar bnza. Ummi tayi mtukar kya cikin

wando da riga nawani ydin dshi Abba ydinka mta

a babbar sallar dta gbata. Tasaki gashinta sosai

tyi wani daurin dankwalin da ita ce ta iyashi

amma gshin nta duk yna wje. Tfesa turarukanta

sannan tfada kan kujera, tkalli agogo minti goma

takaru akan lokacin dya fada mta. Zuciyarta tdan

dmu tkosa sosai ta gnshi bta ki yzauna agida tyi

ta kallonshi tre da sauraron muryarshi ba. Sai

dkusan minti 20 sannan Ya Abba yshigo, tsayawa

yyi yna kallon tsakar gidan, yau kam farin cikine

ya mye gurbin bakin cikin dyake ji aduk lokacin

dya shigo gidan ykalli tsakar gidan. Kamshin irin

turaren wutan da umma ke cika gidanta dashi ne

yke shaka. Ysaki murmushi tre dyin sallama,

bishira dke zaune dabas atsakar gidan maimakon

ta amsa sallamar sai tsaki taje dogo tre da cewa.

Aikin bnza. Kallonta kurum yayi ranshi ya baci.

Bai cemata kala ba ynufi dkin ummi, tyi nisa cikin

buga game. Sallamarshi ceta sata yin jifa da

wayar akan kujera tamike tdaga labulan daidai

lokacin dyke cewa inshigo? Ta amsa sallamar

dwata murya wadda bta san ma tna da ita ba,

suka kalli juna cikin ido, lokaci 1 suka ski

murmushi tmika hannu kafadarsh rtaye da wta

jaka wadda bda ita yfita ba. Ya salubo jkar ymika

mt tre dcewa, kirike dakarfi, tce to, sannu

ddawowa. Yshigo rike da leda ahannunshi yzauna

tre dcewa. Yauwa, tnufi robar ruwa data dauraye

jug din data tnda don shi kadai, tzubo ruwa tzo

dakofi tadauraye kofin snnan tzuba ruwan tmika

msa tre dsake cewa, sannu dkokari. Ydubeta,

yauwa kema sannu dkokar, dud da byajin kishi

dole ne ysha ruwan, ybude bki ysoma shan ruwa.

Sai yaji ruwan yfi duk wani ruwa dyasha a tsayin

rayuwarshi gardi dkuma dadi, ydubeta ido lumshe

dama ruwan amare dadin shi dabanne?? ZURFIN CIKI book 4 part 6

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:37

Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa,

yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire

takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan dan

teburin da aka aje don dora abinci ko kofi. Tazo

takwashe tkalman tkaisu kusa da kofar fita tyi

musu ajiya mai kyau, sannan tadauko dan twul

tshare kasar gurin. Ykalleta, yi hkuri nshigo miki

dki datakalmi ko? Tce bkomai aranshi yce nsaba

shiga dakin bishira da tkalmi. Yjanyo ledar dya

shigo da ita tre dcewa ummana tki aiko miki da

abinci ko? Tace, kyi mta mgnane? Ya ciro take

away din yasiyo mata, zo kici, ai dole ta bmu na

dare, zan jene in tsaya mata. Ummi tdubeshi,

anty bishira fa ka bata nata ne? Yyi mta banza,

tduba ledar tga guda daya gakuma wnda yciro

mata. In kaima anti bishira? Ydaka mta tsawa tre

dharararta, ke! Ban aike kiba, tatsaya tna

kallonshi, meye ruwanki da mtata, kin fini snin

meye kamata nayi kenan? Yja dogon tsaki tare

djanyo jakar dta dora mishi akan gado, jikin ummi

yyi sanyi. Ta tuna damaganar da umma acikin

nasihar dta mta, kda kizama dga cikin mtan

dsuke btawa mzajensu rai. Hakan yna sawa miji

yatsani matarsa, kiyi tka tsantsan kinsan hlin

abba yna dsaurin fushi. Dsauri ummi tasulalo dga

kujera. Don Allah kyi hkuri ya abba, ban san

zakaji haushi ba. Ydubeta fuska daure, hwaye

ygni sun cika idonta yace, kda ki sake hawayen

nansu zubo, tsa ytsunta tdanna idnunta, tshi ki

zauna ki dauki abinci kici. Tzauna tarike abincin

tkasa ci. Ykalleta suka hda ido cikin ido, tariga

shi mgna kayi hkuri Yaya Abba, tausayinta

ykamashi amma sai ydake. Bnason kisake mgna

akan abinda yshafi mtata kinji ko? Da sauri tce,

bzan kra ba. Yyi dan murmushi ci abincinki.

Tasauke wta irin ajiyar zuciyar dhar ya klleta da

ido ya tmbayeta lpy? Dabaki tfurta lpy lau, yce ci

abincinki. Ummi tdauki abinci tn ci, jefi-jefi tna

kallonshi, shi kuma yna ta kokarin kunna laptop,

don ymantar da ita. Yce, kinsan menene wannan?

Ta a'a yace computer ce, agurin aikinmu aka rba

mna. Ummi tace, kyauta? Yce A'a za'aringa

cirewa acikin albashinmu, mtso kigani. Tdan

mtsa inda zta iya kallowa, ykunna yna nuna mta

abubuwa, yce ai nsan ki zaki iya sarrafata, tce

wai, bazan iya ba Yaya Abba. Yce, nima sai

nshiga mkarnta akwai tnan cikin gri zan shiga nyi

diploma, salis shi tuni yyi. Ummi tce amma gshi

ynzun mkana sarrafata, yce ina dan hwa ta office

dinmu ai tce tayi kyau Allah ysa albarka yce

amin. Ykashe komai ydauki take away din ynaci.

Sannan yce, bri infita. Tdube shi itakam bta son

yfita don umma tce mta tzama mai tsare mijinta

dga zaman majalisa koyawo. Indai ba mkarnta

yke zuwa ba, yma ztayi thana shi fita tatambayi

knta, tdube shi cikin tausasa murya. Ya Abba hka

zka fito bkayi wnka ba? Tmike gruwa nan nadiba

bari inkai mka, shima ymike. Sai anjima zanyi

ummi, ynzun shago nke sn zuwa. Akwai wsu

dinkuna da za a amsa yau ina son ingako yaran

sun gama snnan inson in yanka wsu dunkunan

ciki har dnaki, koda yke saina gwada ma tukunna.

Tce, tokadan huta mana ynzun faka dawo, ygane

bta son yfita ne, don hk yce kda kidamu dg shago

ba inda zanje. Har bkin kofa tarako shi tarike

labule, to sai kdawo, yce to, ynzun mbai kalli inda

bishira tke ba, yyi wje. Datsaki traka shi tre

dcewa, girma dai yfadi warwas, murmushi yyi mai

sauti yfice abinshi. Ita kuwa sai thau zntuka,

kinibibi a auran mka miji sannan a nuna anfi ka

sonshi, yrinya lokaci nabaki. Ummi dai sai tkaro

kofarta, koda dre abinci daidai cikinta bishira tyi

taci tba 'yarta shiko Abba bai shigo gidan basai

bayan sallar isha'i. Byan yje sun sha dirama da

umma, tce itafa bta yi abinci dsuba, yce umma

gskiya toki bmu na babanmu. Tyi driya, kasan

abin dakake fada kuwa abba? Inbaku abincin

mijina? Ai kuwa bkwaci ba. Tsohuwa tace, kai ina

mtarka ita bazata dafa fa? Kodon tsoronta

fakakeji ko? Abba yce eh bazata dafa ba ina

ruwanki ke tsohuwa kin cika sa ido. Tce, nasa

din, ai gskiyane kowa ysn uwargida ke yin girki

harsati guda. Abba yce, to mu tsarinmu bhka bne,

tkwashe da driya. Bwani tsarinku bhaka bne kila

ma kinyin girkin tyi, yce oho dai bza kiji bdai, tce

jeka intayi tsami mji. Umma dke tsheka driya tce,

abbana zoka dauka gashi nan yce, yauwa

ummana mungode, tce abba bka shiga gidan

nanne? Yce wai gurin umman bashir? Tce eh, yce

ina zuwa mna, tce todon Allah kadinga shiga, nan

yyi musu sallama ytafi. Lokacin dya shigo gidan

dindim! Sai daya tda injin, aranshi cewa yake yi

lallai mta dakíshi, jimatar dko darana tada inji tke

yi amma ynzun don kda wtan tga hske ko tji iskar

fanka shine taki tadawa.I novels / ZURFIN CIKI book 4 part 7

ZURFIN CIKI book 4 part 7

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:41

Ya aje kular kofar dakin ummi yaleka dakin

bishira, tana kwance kan gado, itafa bata jin cewa

zata dazama dakishiya, dole cikin biyu ayi daya,

kota tada ballin dazai saketa komuma tanemi duk

wata hanyar daza akori wannan 'yar iskar

yarinyar. Yashiga dakin, muhibba daketa wasa

akan gadon da baya zaton tun da aka kafashi

tasake kakkabe shi, yace hibba. Yarinyar ta

waiwayo cikin murna tanufo ubanta da dan

gwaranci, bishira tasa hannu tasuri 'yarta yace,

bishira duk wannan abin daki keyi fabashine

mafita agare kiba. Ki kwantar da hankalinki ki

nutsu ki kama girmanki, yarinyar nan zata biki

amma in kin zabi akasin haka kece zaki koko....

Kai malam! Ta katse shi, bafa wata sauran

magana fanasan komai, ni yanzun saki kurum nafi

muradi, ya ce sakin lafiya? Ni yanzun ma na

soma sonki, tadaga mishi hannu tare da daga

murya, nikuma nadaina sonka, karya ne makace

kana sona kuma kanason waccan banzar. Dole

acikinmu akwai wadda kafi so. Abba yace to ai

kece, ke nafi son kuma ita tasan haka, kalmar

tashi tadan sanyaya mata zuciya. Don haka bata

sake magana ba, yace kina bukatar wani abu ne?

Tace don Allah nidai ka fita kawai, yace to na

fita. Ummi lokacin tana canza kaya zuwa riga

dazani na leshi, sosai tayi kwalliya tamkar

kasureta ka ruga don kyau. Fuskarta sake ta tari

Abbanta dasannu dazuwa, ita ce tasa musu

abinci kowa da plate dinshi, amma sai ya aje

nashi yace suci nata. Dama taso yin hakan amma

tana tsoron kada ya gwasaleta, sai da sukayi

dam sannan yace bari yayi wanka tatashi takai

masa ruwan wanka tadawo. Kafin ya fito ta sake

gyara ko ina, jallabiya mai gajeran hannu yasaka

mara nauyi ya wadata jikinshi da turaruka tana

kallonshi cikin sha'awa. Taso taimaka mishi tun

agurin shafa mai, amma tana tsoron kada yaga

zakewarta, don haka tashare tare da cewa

dasannu za azo gurin. Ysake cewa zai koma

shago, tace haba yaya Abba yanzun kuma?

Yadauko tape dinshi nagwada mutane, zo in

gwadaki, har da kayanki zan yaka yanzun.

Yarannan 'yan shiriritane, badon naje dazun ba

dasun sani nasaba alkawari, dinkunan su kawai

suka yi tayi suka aje wanda nabasu. Ummi

tabata fuska, ya tausasa murya, come on zo in

gwada ki, bazan jima bakinji ko? Tatashi taje

gabanshi ta tsaya. Sai dai mamakinta duk

dunkunan da Ya Abba ya sha yi mata abaya bai

taba gwadata basai yanzun? Koya manta yanda

yake mata ne? Tsawon siket din ta ya soma

gwadawa, tana tunani sai taji ratsawar dan

yatsansa tare da tape din a kwankwasonta, duk

da cewa dariga ajikinta saida hakan yasa taji

wani yanayi ajikinta. Har ma takalle shi, haka nan

ya auna hips dinta da kirjinta, shi kanshi ya shiga

wani yanayi alokacin, haka nan yakoma shagon

cike dakewarta. Kayan bacci tasaka ta kwanta a

gadon tana da yakinin bazai mata komai ba,

tunda yasan bata sallah. Har kusan goma da rabi

tana jiran shigo warshi shiru, waya tadauka ta

rubuta mishi sako da cewa. Ya abba don Allah

kadawo ni dai tsoro nake ji. Ya karanta yayi

murmushi, azuciyarshi yace, don ita ya kwafe,

yayi dunkunan yana son kudin don ya sai mata

akwati da kayan shafa zuwa kayan ciki. Share ta

yayi sai kusan sha daya darabi sannan yatashi

tare da sallamar yaran, haka nan itama sai daya

hado mata duguwa rigarta ta shadda wadda

dama anriga anyi sirfani ajikinta. Dakin bishira

yasoma lekawa, bacci yadauketa sosai agefen

gadon take da alamun baccin yazo mata ba cikin

shiri ba. Abba yayi murmushi tare da cewa, wa ya

fada miki ana cin bashin bacci? Ina zaton matar

nan jiya bata runtsa ba, yau gashi yazo ba shiri.

Har ya gyara mata kwanciya itama 'yar ya gyara

ta amma bishira bata farka ba, don haka yakashe

mata wuta yafita. Yaso kashe injin amma garin

da zafi gashi basu kawo wutar nepa ba, gidan

yarufe yazo ya tura kofar ummi data rufe. Karar

kofar ne ya farkar da ita amma bata motsa ba,

tun daga kofar yatsaya yana kallonta, can

tsakiyar gadon takwanta bata dora kanta saman

filo ba. Amma tana manne da filo daya akirjinta

fuskarta yake kallo, a jikinta taji kallonta yakeyi.

Kusan minti 4 sannan ya aje ledar hannunshi.

Shirin bacci yake amma yakasa daina kollonta,

shikanshi yana mamakin wannar jarababben son

dayake ma ummi, duk da dakewar dayake don

kada yabada kanshi amma sai yadinga jin wani

abu yana fisgarshi. Tamkar yafito mata da zallan

sonshi gareta, tsoronshi inta gano kila tarainashi.

Kadan-kadan takan bude ido ta saci kallonshi, sai

daya gama komai a tunanin ta ya kwanta a

gadon amma sai taga yadauki filo yakwanta a

kan kujera. Haka suka rayu har tsawon sati daya,

ranar yabar dakin ummi ranar kuma tasoma salla,

ita ko bishira satin nan tayi shine tamkar

mahaukaciya sabon kamu. Ranar kuma da abba

yadawo dakinta bata runtsa ba shima bata barshi

ya runtsa ba, daga bisani dole yabar dakin

yakoma falonta yakwanta. Haka gidan yaci gaba

da kasancewa, in Abba yafita ummi bata da

sauran sakewa saboda zagi da habaicin bishira.

Wani sa'in har da kawayenta, ko makota 'yan

jam'iyarta su shigo suyi tayi, ummi bata kula su.qnovels / ZURFIN CIKI book 4 part 8

ZURFIN CIKI book 4 part 8

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:50

Duk abinda bishira zatayi kada takulata. To ita

duk bawannan bne damuwarta ba, damuwarta

ynda Abba sam yaki nuna sha'awarta gare shi,

duk dayasan tana sallah, hka nan duk lokacin

dakwananshi yajuyo kanta sai dai ya jefa filo

akan kujera ya kwanta. Takasa gane ma'anar

hakan, tun tanajin dadin ynda bai nemeta ba

saboda tsoronsa da take harta dawo tasoma jin

haushi. Ita ma fa mutum ce cikakka mai lafiya,

sannan tana kwana daki daya da san kacecen

abun sonta ya ya ba zata damu ba? Sai dai tayi

wa kanta alkawarin a yau in zasu shekara ahaka

ba za ta taba yi masa tallar kanta ba ma'ana

baza takai masa kanta ba. Sai dai zatayi masa

kyale- kyale taga karshen girman kai, ta kosa su

hadu da fati don ta bata sakon kananan kaya

tasiyo mata don ta bata labarin cewa ta kwashe

su a wambai. Kwananta goma taso ma girka, duk

tsawon kwanakin nan abincin siyarwa dana

umma suke ci, domin bishira taki dafa abinci.

Ranar da zata fara girki ta haukata gidan da

kamshi, tuwon shinkafa miyar shuwaka, tasan

Abba nason tuwon shinkafa. Tun kafin ya dawo

yamata waya ta aika shagonshi, 'yan shago sun

ci suna santi, haka nan ya gayyaci abokansa

kofar gida ya shimfida musu tabarma suka ci tare

da lemu, zobo da kunun aya. (reall ehem tazubo

mun nawa na koma 1 site ina kimtsa cikina lolx)

ga nama ya wadata a ciki, abba yaji dadin yanda

abokanshi sukayi ta santi, safiyar ranar kuma

kunun gyada ta musu da kosai. Duk wannan

abincin da ummi keyi bishira ko a harshenta ta ki

ci, cewa ma tayi ita fa kowa tayi girkinta don

baza ta ci abincin ummi ba. Kuma ba shegiyar

dazatai wa girki, hakan yayi wa ummi dadi don

nata ganin ta bakin tsohuwa ce, da ta ce ko kwai

bishira tadafa shine dai dai a cikin bawo to baza

ta iya ci ba bare wani abinci. Sun zauna tsawon

wata daya ahaka ummi bata taba leka ko kofar

gida ba, tana kewar ummanta gara ma tsohuwa

duk ranar juma'a in tadawo masallaci takan biyo

gidan taga takwararta. Dakinta Abba yake

yagama karyawa ya shirya zai tafi aiki, ummi ta

kalle shi tana son tambayar zuwa gidan umma

tna jin tsoro. Ya dubeta kamar kina son cewa

wani abu ko? Ta ce am dama inaso inje gida in

gaida su umma, yajuyo yadubeta suka hada ido.

Gabanta yafadi, ta sunkuyar dakanta, yace a'a

tadaga ido takalle shi, wani kunci taji aranta, ga

matanshi nan yini take garari a layi bata ko

tambaya amma ita ta tambaya shine ma zai

hanata? Ya dauki jakar shi, ta mike ta rakashi

har tsaka gida tare da yi masa addu'ar Allah

yatsare, yini tayi da takaici dama haka mata suke

ji in an hana su zuwa anguwa? Daran ranar zai

koma ga bishira don haka bata san dawowarshi,

tana kwance kan doguwar kujera tana karanta

littafin hausa ( naleka muku kozanga sunan

littafin amma bangano mukuba) kamshin turaren

shi ne yasa tasan yashigo, don littafin yadauki

hankalinta. Ta amsa sallamar daya sake yi tare

da mikewa zaune, yana sanye da kananan kaya

tamkar wani dan saurayi, yayi kyau a idonta

kamar ta rungumeshi. Tace sannu dazuwa yace

yawwa, dauko mayafinki muje tazura takalma

bayan tagoge sannan ta ciro mayafi, yace a'a

dauko hijabin. Ta maida ta dauko hijabi tafito

sannan yakulle kofar, saida suka fita waje sannan

yadubeta, hannu rabbana zakije musu? Tace yaya

Abba toni bani da kudi ai. Sukabi ta wani super

market suka sai sabulai da turare, akafa suke

takawa sannu ahankali suka jero duk da cewa

bawata hira suke ba, Abba ne yake amsa waya

jifa-jifa na jama'a masu sonshi. Tun daga nesa

suka hangi mahaifansu suna cin abinci a inda

suka saba. Alhaji babba dakarami. Cikin zumudi

ummi ta ce, yauwa gasu alh. Abba yaje haka

zakije musu da rawar kanki ko? Cikin shagwaba

tace, wanne rawar kai nayi toni yaya Abba? Yace,

na gani kinayi kamar zaki kwasa da gudu, kafin

tayi magana sun iso gurin dukkansu suka zube

akan tabarmar daga gefe. Abba ne yasoma cewa,

sannunku alh. Alh. Yace, a'a kune? Alh karami

yace, uwata harda ke? Tace, eh ina yininku?

Sukace lpy lau. Alh. Karami yace, uwata kunanan

lpy ba wta matsala ko? Ta ce, ba komai alh..

Yace to Allah yyi maku albarka, ya azurtaku da

'ya'ya ma su albarka wadanda kuma zasu biku.

Abba yace amin suka hada baki da Alhaji babba,

alh babba yaci gaba da cewa, Abba ya hakurin

shirmen ummi kuma? Ince dai bawata matsala?

Abba yakalleta mun gode Allah alh, amma bwata

matsala, ummi tamike dazumudi bari a karasa.

Tun daga soro take kwala ma umma kira. Umma

tce, A'a muryar wa nake ji haka? Ummi tashigo

da gudu ta cakume umma, tsohuwa tafito tana

fadin lale. Dakin tsohuwa tasoma shiga suka

gaisa sannan tadawo dakin umma, sun gaisa

umma tasake mata nasiha, ummi tace umma ni

matsalata daya matarsa. Kullum saitayi min

habaici tana zagina wata rana r harda kawayentaRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 9 ZURFIN CIKI book 4 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:54 Ita ko bishira gidan su umman bashir ta tafi dakuka wiwi, tace Abba yamata duka takan sun taka hakkinta sun fita ranar girkinta. Tayi magana ummi ta mata tsaki shi kuma yazo yazo yahauta da duka, umman bashir tace duka! Duka akan ummi? Tabdi, tashi muje gurin wadanda suka daure masu gindi. Umma na kokarin shiga daukin alhaji taji sallamarsu sama-sama, gabanta yafadi ta amsa tare da dawowa baya. Sahura tace to suwaiba, abinda kuka shiirya yasoma tasiri. Abba yayi wa bishira shegen duka saboda 'yarku, umma tace haba sahura, yaya ki ke irin wannan maganar? Mu ne zamu sa Abba ya cutar da iyalinsa? Sahura kiyi nazari. Alhaji yafito, me yafaru ne ni kejin hayaniya suwaiba? Umma tace, oho. Sahura tace, bishira fada musu. Nan bishira ta shaida masu yanda ta tsara ma umman bashir, alhaji yadaga waya yakira Abba, Abba yana dagawa alhaji cikin zafi yace Abba maza kazo yanzun duk in da kake. Abba yace to alhaji, ummi ta mike zan bika tsoro nake ji ni daya, cikin zafin rai yace abin daki ke tsoro ya cinye ki, ya fita fuuu. Cirko-cirko ya same su a tsakar gida, sai muryar sahura kake ji tana rashin mutunci. Alhaji karami yadawo gidan shi sai ya jiyo muryar sahura a can gidan, ya nufi gidan don haka kusan tare suka shiga gidan da Abba. Alhaji cikin bacin rai yafada Abba da fada, abba bai katse shi ba har sai daya kai ga tambayarshi cewa me yasa yayi mata duka? Yace, banyi mata duka ba alhaji marinta kawai nayi, umma ta ce mari kawai ne Abba? Alhaji karami yace, to kan wane dalili ma zaka mare ta? Abba ya koro musu komai, ya kara da cewa, wannan har zata ce an mata tsaki, zata yi duka ni wane irin zagi ne bata min ina hakura darajar iyayenta? Ya nuna ta, wallahi in kika kai ni bango zaki koma gidanku don bazan iya ba na gaji, nan kuma su alhaji suka shiga bashi hakuri. Ita kuma suka bata rashin gaskiya, sai dai duk da haka umma tai masa fadan kada ya sake daukan ummi ranar girkin bishira ya fita da ita, yace to. Umman bashir taja bishira zo muje ai dama nasan baza suga laifin 'yar su ba. To wllh marin da yamiki ki tabbata bashine. Ko nan da yaushe ne ki rama shi kan ummin, in ba haka ba duk da banice uwar data haife kiba sai na tsine miki. Alhaji karami yace, to katuwa mara lissafi, ke dai kinji haushin rayuwarki, to ki sani duk randa ta rama duka akan ummi ni kuma akan ki zan rama wa ummin inga ta tsiya. Alhaji babba yace, kada kai ma kazama su mana aminu. Tsohuwa tace, gskiya ne, in har tazama silar dukan ummi itama sai ya mata taji. Umma tace, a'a duk abin ba zai kai haka ba insha Allahu, kai dai abba kayi ta hakuri sannan kadaina sa hannu kana dukan mace. Yace, umma dukana fa tayi, sai kace wani soko zan tsaya mce tna dukana, umma tace, to ai tace ummi taje duka, yace ummin 'yarta ce? Alhaji yace, tafi gidan kahadasu kayi masu nasiha, Abba yace ai baza ta tsaya ba, wannan yarinyar fa sai dai addu'a ni in nagaji kawai hakura za ayi, umma tace bana son jin wannan zancan, alhaji karami yace ai gskiyarshi ne, shi yasan irin zaman dayake da ita. Alhaji babba yace, ai kuma darajar mahaifinta za aduba, da mutuncinsa, Abba yace ai dama alhaji ni banda mahaifinta da tuni nayar da kwallon mangwaro na huta da kuda. Umman tace je ka gida Allah ya kyauta. Nan dai ya musu sallama yanufi gida. Ummi da gske tsoro ne da ita, da rana in ba kowa bta damuwa, amma da dare tfi son tdinga jiyo motsin bishira koda habaicin dta sabayi mata. Soro taje ta tsaya tana yi tana leka waje, can ta hango bishira, don haka takoma daki ta kullo kofa aranta ta ce kada tazo tayi min duka. Ummi tna jiyota lokacin data shigo tana cewa wllh kan yarinya zan rama marina, wannan dole ne koba dade saina ramashi. Abba kan bai nufo gida ba, shagonsa ya wuce lokacin goma ta gota, yaran sunyi shirin tafiya, don haka ya amshi makullin ya shiga shagon saman teburin da suke yin yanka da guga ya hau ya zauna. Tagumi ya zuba hummu biyu tare da sauke wata ajiyar zuciya mai karfi, me yasa ummi ta furta kalmar data tuna mishi cewa bata sonshi? Sakankancewa dayanda ummin kenuna mishi yasa shi jin kamar sonsa take ashe dai shi yake shermenshi. Ya tuno wani labari yaya tabaji na wani mutum da aka ara masa mata wadda bata sonsa, tazo tazauna dashi tsawon shekaru kuma tayi masa biyayya matuka. Ga 'ya'ya sun haifa yaran sun yi girma sosai, suma sun zama magidanta, sai wata rana mutumin nan suna hira da matar, yace oh, wance dafa ba kya sona, yanzun gashi harmun tsufa kin manta dawata kiyayyah. Tadubeshi, inji wa yace maka na manta? Biyayya kurum nake maka amma har gobe bana sonka. Abba yajinjina kai, lallai dole ne ya nutso, yadaina tunanin ummi tana sonshi kokuma zata soshi, shidai da kaddarar sonta tafada mishi sai yayi ta addu'a Allah ya bashi hakurin jure zama da ita ahaka. Bai san adadin lokacin daya dauka awaje ba kuma baisan adadin tunanin dayayi ba. Daga karshe yarufe shagon yanufi gida. Ganin yanda garin yayi tsit shine yasa shi kallon agogon hannunshi, daya da minti shabakwai, lallai lokaci yatafi. ZURFIN CIKI book 4 part 10

ZURFIN CIKI book 4 part 10

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:55

Yanufi dakin bishira aranshi yce da wanda yake

kinka gara mai sonka ko mahaukaci ne. Gdon

yahau tagefe ya kwanta suka saka muhibba

atsakiya, ummi kuwa duk tsawon lokacin nan

tkasa bacci domin bata ga shigowarshi ba. Idonta

biyu har sai daya shigo ta leka ta windo tana

kalloshi har yashiga dakin bishira ya rufo kofa,

sannan ta kwanta tare dayin ajiyar zuciya. A fili

tace ina ga fa har dani alaifin nan, amma bari

gari yawaye inba shi hakuri durkusa ma wada ai

ba gajiyawa bane. Bishira tafarka cikin dare taga

Abba kwance hannunsa na dama dore kan jikin

'yarsu, ta tsura mishi idanu tana son mijinta

sosai. Ban dahaka data kaishi koto ya bata

takardarta koda mahaifinta xaimata baki

sanadiyar haka, amma shi yanzun yadaina sonta.

Takai hannu tadora a kumatunshi, ahankali

yabude idanu, suka kura majuna ido yace bishira

me yasa kike yin abinda zai samu mu samu

sabani bayan kinsan sone ya hadamu?

Idanuwanta suka kawo ruwa, Abba dane ka soni

kaji dani har alokacin ina ganin ba Wata mace

data kai ni dacen gwanin iya soyayya. Amma

yanzun duk ka zuba ni a kwandon shara har kana

marina saboda ummi. Ya ce, a'a ba sbd ummi na

mare kiba, saboda kin dukeni ne amma kiyi

hakuri. Banason kina zubar da kanki a gurinta,

yawan fadanku zai sa raini ya shiga tsakaninku,

ni kuma ba zan so ta rainaki ba. Kuma da kin

kwantar da hankalin ki ummi fa ba wai tana sona

bane, ita fa an matsa ma tane, kuma su umma da

kike zagi na rantse miki masoyan kine. Ta ce

tokai kana son ummi ne ? Ya dan yi jim, sannan

ya ce ai dai kin san yanda auran namu da ita

yakasance bagatatan bai dace ace kinma tsaya

yin wannan tambayar ma. Tadan yi shiru, zancen

nan ya shige ta bakamar yanda ta zata da farko

ba, ko dadin baki zaimata? Sannan ta tuno da

ranar da fati tazo. Ta labe taji koza suyi

zancenta sai taji suna ta hirarsu, acikin harar fati

ke cewa wai kuwa ya kuka kaya ne ummi? Nasan

yanzun ai kin warke, kema kin goge. Ta ce

damefa? Fati tace, a'a ki gane mana, batun

kwanciya. Ummi tace, kin san cewa yaya Abba ko

gadona bai taba kwana ba? Fati tace kai haba?

Ummi tadinga yimata rantsuwa, tuno da wannan

sai bishira ta yarda mijinta ma baya son ummi,

don haka sai ta saki murmushi. Yace, tunanin me

ki ke yi? Tace da ina ga kamar dadin baki kake

min, amma dana tuno naji ummi tana fadama fati

wai baka taba ko kwanciya a gadonta ba, bare ka

hada jiki da ita sai na yarda. Abba ya zaro ido, a

ina kika ji suna zancan? Ta ce, a'a tazo mata

rakiyane naji suna maganar a soro. Abba ya

girgiza kai. Bishira tace, kuma da gske hakane,

yakai hannu yakama nata tafin hannun, wannan

wani sirri ne tsakanina da ummin. Ynda ba zan

fada mata komai tsakanina dake ba, haka itama

zan sakaya nata sirrin, tadai fahimci hakane, don

haka sai ranta yayi mata dadi har ma ta baiwa

Abban kanta a daran. Ynda taga yna rawar jiki ya

tabbatar ma ta ba wani angwanci da yayi, don

haka zuciyarta fes ta wayi gari. Duk da cewa

abba ya tashe ta cewa taje tayi wanka harda

Allah yahadata amma tayi niyar baza tayi hakan

ba sai gari yayi haske. Ummi ta fito don tanuna

mata cewa Abba ya kwana da ita. Bishira an dafa

ruwan tea an kai falo sai wannan rawan kai ake

yi. Sai data lura ummi ta dauko tsintsiya tasoma

sharar gidan kamar yanda tasaba, sannan tafito

da buta aka nufi bandaki, kai ko dankwali babu

aka yiwanka aka fito. Gashi yna ta digar ruwa,

ummi ta fahimta kuma tagane cewa tayi hakan

don ta nuna mata ne. Kuma taji zafi aranta

kamar ynda bishiran taso, ta amma azuciyar ta

sai tace na banza jiya nan yakora miki mari.

Lokacin da abba ya shigo gidan tagama shara

tana kwashewa, bai ko dubeta baya shige falon

bishira, kan ummi yasake daurewa, me yake

faruwane haka da zafi? Ta tambayi kanta. Data

koma daki tagumi ta zabga tana tunani ita da

suka yi kaca-kaca ma sun shirya bare ni? Kamar

tabi shi har falon bishiran ta gaida shi, amma sai

tafasa. Tazuba ido taga zai bar gidanne ba tare

daya leko dakinta ba? Sun gama karin

kumallonsu tsaf yayo wanka don tafiya gurin aiki,

sai dai kayan dazai saka suna dakin ummi. Ya

fito yanufi dakin. Ciki- ciki yayi sallama ita kam

tsoro ne ya tsirga mata, tasake tambayar kanta

mekuma yafaru? Ta amsa tare da gaida shi. Nan

ma a ciki ya amsa, yadauki kayan sai dazai fita

sannan yace ba kya bukatar komai ko? Tayi

karfin halin cewa sugata ceta kare. Ya dube ta

furka tsuke me yasa baki fada minba? Ta ce, na

manta ne, yace to sai kije gurin bishira da dibar

miki inzan dawo na siyo. Ba kya neman komai da

rana ko? Tace a'a sai nama kawai ya daga

murya, kullum ne ya zama dole a saka nama a

abinci? Jikinta har bari yake don tsoro, ta ce a'a

yaja tsaki ya fita. Ummi tasaka kanta cikin cinya

tana furta 'inna lillahi wa inna ilaihir raji'un.'

hawaye suka soma yi mata sintiri.KI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 11

ZURFIN CIKI book 4 part 11

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:57

Dadi tamkar yakashe bishira don tna labe tana

jinsu afalon ya saka kya yashirya tsaf, sannan ya

nufo dakinta don dauka jakar laptop dinshi. Jin

sallamarshi tayi mza tashare hawaye sannan ta

amsa, yshigo ya dauko dari biyu ya aje mata

akan gdo, ga kudin maman nan kura, kada fati

tzo kifada mata baki kudin nama kullum tunda

har kin iya shaida mta cewa ban tba kwana

agadonkiba. Kin kosa inkwanta dakene? Yadauki

jakar yarataya sannan yayi mata wani kallo sama

dakasa, to banga gurin kwana agadon naki ba.

Hakanan banga abin kwanciya ajikinki ba, yafice

yabar ummi tsaye tazaro idanunta cikin matukar

al'ajabi da kunya. Ina ya Abba yaji zancen nan?

Kodai fati ceta fada masa? Wata zuciyar tace fati

baza ta iyayi masa zancan nanba saidai in

ummarsu tafada mawa ita kuma tafada masa.

Inko hakane fati batayi mata adalci ba, ai hira ce

irinta aminta tsakaninsu, gashi ta bata kunya har

tasa ya Abba naganin tazaku. Tokuwa tasha

alwashin nuna mishi bahaka take nufi ba, afili

tace Allah yabamu rai da lpy. Sai kuma tasoma

kuka. Bishira tafadi kan dadi ashe gara data fada

masa zancen dataji suna yida fati, gashi yanzun

yayi mata rana. Lallai labe yayi mata amfani sai

kawai tasabi 'yarta tazari mayafi tafice makota,

yau kan tana da labari mai dadi sai yawon raba

shi take bata manta ko kalma daya. Sannan

darana tazo tahau kici-kicin dora girki, lokacin

ummi tafito don yin alwala, ita ko karyawa batayi

ba don tawuni da takaici ya Abba. Tana kallon

yanda bishira tazubu kayan miya tana jajjagawa

batare data wanke ba hancin kawai ta cire. Ummi

tayi alwala tashige daki, ranar har dare ummi

bataci komai ba, duk da tanajin yunwa. Zantukan

abba kawai kemata yawo a kwanya. Tayi kuka

harta gaji fuska ta kumbura. Tun uku yadawo

baiga ummi ba, bishira tagabatar masa da abinci

dakyar yayi cokali uku. Dama yazo dafura, yasha

sannan yanufi shago, yini yayi yana tunanin

kamar bai kyauta ma ummi ba, amma yana

mamakin yanda ummi ta iya cewa bai hau

gadonta ba. Kenan inyahau din dakuma abinda

yabiyo bayan hawa gadon duk zata ringa fesarwa

ne? Kai yafaji haushin abu biyun nan dacewa

bada sonta aka daura masu auran suba dakuma

fada ma fati sirrinsu. Saidai duk dahaka zuciya

da idanunshi suna matukar kewar ganin ummi,

sai shida yadawo gidan. Ruwan wanka ya diba

yanufi bandaki, man shafawarshi dasauran su

suna dakin ummi, don haka yakalli bishira. Bari in

dauko kayana can dakin ummi kozaki dauko min?

Tace, bazan jeba kaje da kanka. Tana kwance

kan doguwar kujera lokacin kanta yana matukar

sarawa, don kuwa yanda yayi sallamar da kyar

itama dinda kyar ta amsa. Saidai ita badon

wulakanci tayiba, saidai don yanda take jin

jikinta. Yashafa mai tare da feshe jikinsa da

turaruka. Idanunshi suka sauka kan darinshi biyu

daya aje mata. Yakalleta, ke ina abincin da kika

dafa? Batare data dubeshiba tace, bandafa ba.

Yace sbd me? Tace banjin yunwa, kaikuma naga

ba anan kake ba, baki ya taba yasa kaya yafice.

Har tayi sallar isha'i lokacin tasoma jin jiri, amma

bata da niyar shan ko tea tanajin ya shigo ya aje

mata ledar ta kusan minta 30 kafin tataso tazo

tatura kofarta. Sannan taduba ledar, nama ne

balango yaji albasa da tumatiri, sai sugar da

madara, nan ta aje su tayi kwanciyarta afili tace

natabbata kurar kenan indai naci maman nan.

Bacci yadauketa can kusan ukun dare fa yunwa

fatakai yunwa, kowa yasan yunwar dare yanda

take jigata bawa, a gigice ummi ta tashi tahada

tea tahau sha da gaggawa. Tagama kamar taci

naman sai kuma tafasa ( tamiko min ninkuma

nayi fuska nacinye au namanta madawani azumi

lolx) ta kauda kayan ta koma ta kwanta, aikonan

fa cikinta yahau hautsinawa. Dagudu tatashi

tanufi fita tana bude kofa kafin takai bandaki

tasoma sheka amai, tun bude kofarta abba

yafarka dasauri yafito. Riketa yayi ganin yanda

take sheka amai kamar zata amayar da hanjin

cikinta, sai sannu yake mata. Data gama yajanyo

ruwa ya wanke mata fuska ta kuskure baki.

Yawanke gurin gurin tana gefe tsugunne, cikinta

da kanta sai ciwo sukeyi tana mikewa sai jiri.

Nan tafadi ragwaf, shine yadauketa tamkar ya

dau jaririya don rashin nauyi yace duk kece kikayi

makanki sanadin wannan matsalar. Don kina

fushi saiki yiwa abinci yaji, ai gashi nan kema

kina ji ajikinki, kan kujer yadorata ya cire mata

siket din atamfar dake jikinta, don duk sun jike sai

na ciki. Yajuyata zai zage mata zif din rigar tana

son ta hana amma bata dawani karfin hanawa.

Tanaji tana gani abba yacire mata riga, gashi ko

best bata saka ba sai breziya. Takai hannuwanta

tarufe kirjinta. Shikam ganinta ahaka yasa tsigar

jikinsa tashi, tun daga karamin yatsansa har

tsakiyan kansa ruf da ciki ta juya tayi, shi kuma

ya kunna mata fanka yafita. Zaune ya samu

bishira atsakiyar gado, ta kalle shi da tuhuma, me

kaje yi dakinta? Yce amai naji tanayi shiyasa

nafita, bta dlpy ne, tsaki taja sannan ta kwanta.

Shi kam bai runtsa ba, kunnanshi da hankalinshi

suna can, dga bisani madayaga baccin yaki sai

yatashi yayi alwala yasomayin nafila. Dazai tafi

masallaci yske lekawa yaga IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 13

ZURFIN CIKI book 4 part 13

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:05

shikenan yanyun bata dawani aji agurin Abba

ummi da tsoron allura sam taqi tsayawa jiya ma

don agalabaice take Nurse din tace ke dai

shagwaba ta miki yawa A ce allura ma kin kasa

tsayawa kefa mace ce Wata rana ma haihuwa

zakiyi ummi fa taki tsayawa nurse tazo tace ma

Abba taki tsayawa abba yaleka dakin allura

menene haka ummi tsoron alluran ki yayi yawa

kitsaya mana Tadube shi fuska a shagwabe ya

Abba dazafi nikam na hakura da allurar nan Abba

ya shiga dakin ya kalli nurse din zo kimata ba

zanyi asarar kudina ba Ummi bata ankara basai

jinta tayi atsakiyar kirjin Abba shi kanshi sai jin

wani abu yayi yataso daga tafin kafarshi zuwa

tsakiyar kanshi Har yayi baya dasu tamkar zasu

fadi to bare ummi wadda jikin nata ya dauki rawa

Ya kalli nurse dinda idanuwanshi wadanda suka

canza kala nan da nan zo kiyi mata Yadaga

hajabinta tare dazame zanin daidai inda za ayi

mata allurar shigar allurar ta saka ummi cewa

wash tare da sake makalewa jikin Abba Don kuka

tasaka wanda daga jinshi kasan shagwaba ce

zalla ya lumshe ido lokaci daya ya kuma budesu

nurse din tace kai ke kam kin cika shagwaba

Abba ya dora yatsunshi guda adaidai gurin da

akayi allurar yana murza mata tare da rada mata

'sannu' akunnenta Rekicewa tayi sannan ta

kwace jikinta daga gare shi wani yanayi ta tsinci

kanta mai girgiza bawa Ya sauke ajiyar zuciya

sannan yace mu tafi suna cikin mota dukkansu

sunyi shiru Abba kasala ce da muradin matar shi

yasa shizama hakan Ita ko ummi mamakinta ba

yau Abba yasoma taba jikinta ba can baya yasha

rike ta yazane ta, yasha rungumeta ayi mata

allura, bata taba jin irin abinda taji yanzun ba Ta

jingina da kujera tare da lumshe ido sai take ta

tuno yanayin dataji lokacin daya mannata

ajikinshi. Tsayawar motar ne ya sata bude

idanunta, azatonta gida suka zo,sai taga ashe

gurin kayan kwalama ne Ya kalleta, ina zuwa Ya

fita ya nufi zuwa ciki jim kadan ya fito da ledoji,

kaji ya siyo da madara mai tsafta, har da

kankarar dayaji tana tambayar umma yasai

musu. Tace, gama fa kankarar umma tasai mana.

Bishira ta cika fam don takaici, kamal kaninsu

Abba yaduba mata ko ummi tana gidan umma, ya

fada mata bata nan. Ta tabbatar suna tare, ta

cema umman bashir tunfa safe suka fita tare

umma tace tun safe wane iri? Tace wai bta da

lpy yaje kaita asibiti Umman bashir tace Allah ya

tashe mu lpy Goben nan zan tafi kauye dama

gobe ta ce indawo gaje 'yar bori, ina fada miki

ummi dakanta zata bar gidan basai ance mata

ba. Bishira tace dahaka zata faru zanfi kowa farin

ciki, umman bashir tace kece aida shegen kyamar

'yan kauye bakison mutane Matsalarki kenan da

ace zaki jure muje tare kiyi kwana 2 'yar bori da

bokan tsauni zasu cika miki aiki Bishira tace

zanje umma. Biyan bukata ai yafi dogon buri

umma tace taki turo minshi ince masa sha'ani

zamu don kada yace zai hana, bishira tace to.

Sun sameta agidan ummi tayi dakinta da ledar ta

shikuma yashiga gurin bishira. Ranar daya dawo

dakin ta kuwa tayi kyau cikin doguwar rigar

shadda ruwan kunkumadi, tun yana kallon ummi

asace harya kasa dauke idonsa Ummi talura ta

birgeshi sosai don haka tazauna bakin gado tana

fuskantarshi hira ce suke yi jifa- jifa itace ma

tasoma sako zancen Ya Abba zance ma alhaji

yasai min TV nagaji dazama shiru Abba yace a'a

banason haka ina sane zansai miki, tace to

Bishira dake labe ta girgiza kai aranta tace ashe

za ayi bala'i duk randa yakawo TV ai itama ai

iyayenta suka sai mata. Tace to yaya abba

inason makaranta ya aje laptop din daya soma

budewa yamaimaita kalmar makaranta? Ta ce eh,

yace sai nayi tunani Ummi ta marairaice tunani

ya Abba? Kai dakake son inyi karatu? Yace

shikenan haka sukayi ta hira har lokacin

kwanciya ummi tayi shafa'i da wuturi tayi shirin

baccinta takwanta Abba yau yakasa nutsuwa

tamkar yaje ga ummi, amma girman kai ya

hanashi. Ranar sama-sama yayi bacci sau biyu

yna fita yana watsa majikinshi ruwan sanyi kozai

dan samu nutsuwa. Har lokacin daya tafi gurin

aiki bashi da wani kuzari. Ranar fati tazo lokacin

bishira ta tafi badadinta, ummi tahau fati

damasifa tare da fada mata yanda sukayi da ya

Abba. Fati ta rantse tamaya kan cewa ba wanda

yasan zancen nan don bata fada ma kowa ba,

sukayi ta tunanin ta ina ne zancan nan yafita?

Fati tace to ko kiyi hankali koda Anty bishira tana

miki labe? Ummi tayi shiru tna nazari, can tadubi

fati Bazan zargeta ba, domin ban taba ganinta ba

amma zansa ido fati tace gara kisa kam yanzun

harzuwa yau baku sasanta ba? Ummi tace aini

bana bukatar sasantawa dashi tunda yace baiga

gurin kwanciya agadona ba Fati tasaka dariya ke

dai kada kicika baki,ummi tace kedai mu bar

wannan zancen inbaki kudin kayan don Allah?

Tati tace kibani dan bnida matsala mijina she ne

yakaini nasai nawa zance yakaini insai miki

kinason wanduna Ummi tace kinjiki da siket zaki

debo min Ai har gajerun wanduna ki kwaso min,

wulakanci zanyi a gidan nan.vels / ZURFIN CIKI book 4 part 15

ZURFIN CIKI book 4 part 15

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:12

Saidatayi sallah sannan tazauna gaban madubi

duk da shirin bacci take yi Saida tashafa manta

da hoda sannan tadan goga jan baki. Tafesa

turarenta ta isa gurin kayan baccinta dake cikin

dirowar dora akwati, ta dauko duguwa tazira

sannan takama karshen kitsonta tahada su guri

daya ta tufke. Zata ha gado yace, ga nama kizo

muci. Ta fada gado tare da jan filo ta dora kanta

da kirjinta sannan tace nama saikace wata kura?

Dazun fana danci amiyar danayi. Yace nida na

siyo shine nazama kuran ko? Tace, a'a ya Abba

kaine ranar nan naji kace kura. Kullum ake cin

nama? Yayi murmushi aranshi yace, ok nan na

rama ne kenan, sannan yace toshi kenan bari in

ajiye miki naki. Nan tayi kwanciyarta. To 'yar

gidan tsohuwa, yafada danufin zolaya, tace kai

kuma dan gidan ummanka. Cigaba yayi dashiga

yanar gizonsa, ita kam a gajiye take bacci

yasoma fizgarta. Lokacin dayazo shima ya

kwanta akan gado, ta bude ido lpy Yaya Abba?

Ya dubeta tsakaninsu mutum daya zai iya

kwanciya. Wace irin tambayace wannan mutum

da dakin matarsa da gadonta atambaye shi lpy?

Tatashi zaune, gani nayi ba guri agadona, yayi

shiru, wato ummi bata barin bashi, ta tsura mishi

ido tana jira jin mezaice. Yatashi zaune, idanunshi

akan lebunanta, toni dai ga guri na samu, ta

sulale itama takwanta rigingine tare dajan bargo

tarufe rabin jikinta. Shima hakan yayi, ummi

fargaba ce tasa tanemi bacci tarasa, shikam

addu'ar bacci yakaranta sannan yashafa

yalumshe idanu. Duk su biyun bacci sama- sama

sukayi koda Abba baisamu nasarar kama kayan

ummi ba amma aranshi yace wannan sharar fage

ce. Dasannu za'a kai ga muradi, ko washegari

daya kwana adakin dai bawani cigaba sai sake-

sake Abban yayi tayi azuciyarshi, na cewa

yakauda wata kunya ya fito mata amutum, amma

yakasa hakan. Musamman yanda yaga ummin

tana da shegen wayo, ba kamar yan yazata ba.

Sannan gashi ta iya yin ado irin na tsokana.

Hakan yasa duk ranakun girkinta Abba yana

zumudi amma yakanyi kwanan rashin sukuni.

Wata jumma'a tsohuwa ta riski ummi da irn

wannan shiga tariga da gajeren wando, ta kawo

mata ziyarar data saba inta dawo masallaci.

Salati tasaka tare da cewa, yarinyar nan kece

haka kinzamo sai kace arniya? Ummi ta tashi

tsaye tayi juyi tare da cewa. Ynzun tsohuwa ban

birge kiba? Ta ce kitson naki ne kurum yamin

kyau, amma wannan shiga dame tai kama? Kuma

shimai sunan malam yakasa hanaki koke ma

yasoma tsoron nakine? Ummi ta tuntsure da

dariya, ba tsorona yake jiba, shine ma yake son

kayan don shine ma yasai minsu. Tsohuwa tace,

oho! Eh lallai ta mike Allah ya taimaka, duk abin

ku dai baza ki koma baturiya ba, ummi tace oho

dai ke dai kuma baza ki iya wannan ba. Tace,

Allah ya tsare nida wannan shiga, ummi ta dauko

dari biyu ganin tsohuwa ta mike, nizan tafi in dan

zazzaga in ziyarci jama'a. Ummi ta kama

hannunta ta saka dari biyun, gana goron

jumma'a, Allah ya hadamu aladan ziyarar. Suka

fito tana cewa. Ke kullum nazo sai kin bani kudi

ummi, to Allah ya shi muku albarka, Allah kuma

yasa ki sauko lpy. Murmushi ummi tayi duk 'yan

gidan su kallon mai cike suke mata. Duk hirar

nan tasu bishira najinsu, ta cika tayi fam. Dama

Abba yana kwana da ummi? Ashe shine yake sai

mata kananan kaya? Ashe har tana da ciki shine

yamata karyar cewa baya sonta? Tana dawowa

raka tsohuwa, bishira ta kalleta, karamar yarinya

ta iya karuwanci, dube ki. Ummi ta kalleta babba

fa ya rike girmanshi inba haka ba inhau in taka,

kuma niba karuwa bace, kema kalle ki. Ta taso

zan zane kifa? Ummi ma tadaga murya. Sai kace

wata 'yarki? Ba ki isa ba. Bishira tazo zata

shakota, ummi ta daka tsalle taja baya. Karki

sake ki taba ni. Nan fa gidan ya kacame, bishira

sai ashar take zugama ummi, tana kiranta 'yar

matsiyata. Ummi tace, banga kamannin masu

arziki ba a jikinki, nan makota suka shigo yin

rabo. Ummi ko tana fada mata take ramawa, abin

da yafi yiwa ummi ciwo datace ummanki

matsafiya, nasan komai saboda bakin asirinta ne

sahabi yafasa aurenki aka mannawa mijina. Don

shima ya fada min ba ya sonki, har yanzun bai

taba kwanciya dake ba. Ummi tace, kazama mara

sallah me labe, kina labe min akofan don bakin

kishi, kuma insha Allahu sai Allah yasakawa

ummata tunda kika ce tana asiri. Maman amir

kawar bishira tuni taruga takira umman bashir,

sai dai cikin sa'a tanazuwa Abba nayin parking.

Ganin yanda mahaifiyarshi tashiga gidan cikin

hanzari haka shima agurguje yafada gidan, ranshi

yayi mugun baci yanda yaga gidan cike da

jama'a. Ga bishira mutum biyu sun rike ta tana

zambarmar asake ta ta lallasa ummi, ga ita kuma

ummi tsaye akofarta kanta babu ko dan kwali ta

sha gajeren wando ya dan gota gwuiwarta da 'yar

riga tana maida martani. Yace ma matan dasuka

rike bishira, ku saketa suka sake ta ya daka mata

tsawa da karfi, duk ku fice min daga gida,

magulmata tunda duk yawanku kun kasa sasanta

su. Sum-sum suka wucesuna tabe baki, duk

dahaka bishira bata daina magana ba.ZURFIN CIKI book 4 part 16

ZURFIN CIKI book 4 part 16

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:14

Haka umman bashar batasan yarda komai ya faru

ba. Amman ta shiga zagi da tsine ma ummi har

da ce mata karuwancin ne ya motsa, ai dama

nasan tun kafin kixo gidan nan kinsan maza.

Bishira ta ce umma wllhi ga babban mai laifin

nan, muna funtata sukeyi duk ire ire wadannan

kayan na jikinta shiya sai mata su, ni bai siyo

min ba. Na gaji da hakuri ana cutata gwara

yaban takarda ta. Umma tace daina fadin ya baki

takarda insha allahu saidai ita ya bata, Abba

yayima bishira wani kallo tare da cewa ki tafi

mana sai me? Yarda kika gaji da ni nima Haka na

gaji da ke, ya kalli ummi yace ke kuma mi nake

fada maki kullum? Itama cikin fushi tayi magana

toh shikenan saita ta zagina tana ma ummata

sheri don ita kake so? Bishira ta cafke dama ai

ya fadaman baya sonki. Ummi ta kalleshi ko zai

kare kanshi, amman baya kokarin Haka saima

kara zaro mata ido da yayi yana cewa. Ni kike ma

ihu ummi? Zuciya tazo mata wuya nata ganin an

daketa ne kuma an hanata kuka. Shi kanshi ya

tozarta ta da ya fadama kishiyarta baya sonta.

Duk da tasan da haka ta kalli bishira cikin daga

murya tace, an fada maki na damune don baya

sona bana son ya soni don nima bana son Shi....

Mari Abba ya sakar ma ummi da bayan hannu,

kalmar da ya tsana kenan, zafi yakeji a Zuciyarshi

ko tunowa yayi da ummi bata sonshi. Daki ummi

ta fada, ta fada kan gado tana kuka, ya kalli

bishira kije gidan ku sai nazo, umman bashar

tace ba inda zataje kuma in ka sake na samu

labarin ta tafi saina debe maka albarka. Tasa kai

fuuuu ta fice, tunda ka dauki hukunki mai kyau ka

duki marar kunya ai naji dadi. Bishira ma taji

dadin haka, Shi kuwa ba don su yayi ba zafin

furta bata sonshi ne yasa ya daketa. Yana shiga

dakin ummi lokacin ta mike tana kuka, ta dauko

zane ta daura tana kuka sosai. Ta zari hijabi ta

zura zata fita, yace ina zaki? Taki sauraronshi

zata fita ya rikota, ina zaki nake? Tayi magana

cikin daga murya cikin muryar kuka tace gidan

ubana kai kuma ka zauna da warda kakeso,

tunda ya mareta nan ya gane bai kyauta mata ba,

don yasan ba dole bane ta fahimce Shi, sai ya

samu kanshi da jawota ya rungume. Duk da suna

cikin bacin rai Duk kansu saida sukaji wani irin

yanayi. Yace kada kiyi yaji ummi kinsan dai koh

kinje su umma fada zasu maki. Cikin sanyin

murya yayi maganar, kan ummi ya sara, ta kwace

daga jikinshi ta sake fadawa kan gado. Sabon

kuka ta saki, ya zauna bakin gado ya kamo

hannunta ta sarke ya tsunshi da nata ya dan

matsa, ummi! Ummi!! Tashi kiji, cikin kuka tace

mi zanji yaya Abba, kawai ka rabu dani, ni baka

man adalci ba. Ya za'a yi kaje kana fada mata ni

baka sona kasa tana man gori, umman bashar

harda ceman wai ni nabi maza. Ya sake kwantar

da murya yace ki yarda ni ban fadama bishira

cewa bana sonki ba, kuma batun umma kisashi a

gefe kawai don ni nafi kowa sanin halinki. Nafi

kowa sanin tarbiyar umma na... Duk da haka ai

baka kare kanka ba lokacin da take fada ba,

ummi ta katse kiran da yake mata, yasan ummi

sarai yanzu kam bazata saurari komai ba, koma

ta saurara zata ta kalubatanshi ne, don haka sai

yace to Tashi ki bani abinci. Kin Tashi tayi don

kanta jinsa take kamar ya fado, mi kewa yayi ya

fita, ya rasa sukuni, koda yaje shago kasa yin

komai yayi, sai murza hannunsa da ya mari ummi

yake. Ya ciro wayarsa ya kira ummin tayi ta

ringing kusan sau 3 kafin ummi ta daga yace

haba ummi, inata kira kayi banza dani? Shiru dai

tayi bata tanka ba, ummi cikin disashiyar murya

tace, dama haka ne, sai an kwance ma mutum

zane kasuwa azo gida ace za'a daura masa. Sai

ta kashe wayar. Daga nan gidan umma ya nufa,

tace anya Abba lafiyarka kuwa? Naga Duk ka ya

mutse. Ya zauna suka gaisa yace umma ina fa

lafia, dazun bayan sallar jumma'a ina iso wa gida

da yunwa sai kurum na samu gidan tam d

jama'a. Ummi da bishira na tarar suna ta zage

zage har aka samu wata shedaniya taje ta kira

umman bashar. Umma tace subhanallah! To ya

akayi yanzu? Yace tarwatsa taron nayi, nasan

koda ban tsaya bin bahasi ba ummi ce mai

gaskiya. Domin bata kula bishira, Duk yarda akayi

ta kure ta ne. Tsohuwa daga can gefe tace, wai

bayan zuwa na gidan sukayi fadan? Abba yace

oho ni ban masan mafarin fadan ba. Umma tace

kai wannan abu allah ya dai dai ta maka su.

Amman kyanshi kana zuwa ummin ya kamata

kayi wa fada, koma ka zane ta, don itace karama.

Abba har suna hada baki da Tsohuwa gurin fadin

"Haba dai". Abba yace umma in itace da gaskiya

kuma ai na zalinceta, yanzun da haka fushi take,

Duk na tsorata bana son fushinta, sai taki cin

abinci. Don allah umma bari in kira maki ita ki

bata hnkr, umma tace ba zan bata hnkr ba, abinci

kuwa kada allah yasa taci. Sai dai ayi tunanin

abinda ke cikin ta, Tsohuwa tace, wannan

sakaryar matar taka dama na lura fada takeji.

Sanda nayi sallama tana zaune amman amsawa

ta gagareta, don haka ma ko gaisheta banyi ba

na wuce. Ita kuma takwara ka hanata saka

wadannan kayan na arna. Abba yace, su ake yayi

Tsohuwa, Tsohuwa tace, tafdi lallai yayi ya zama

banza. Abba yake cewa Don allah umma ga nmbr

bari in saka maki a waya, ya dauki wayar umma

ya saka mata lambar wayar da ke hannun

ummin, yace umma na roke ki lallasheta ba wai

fada zaki mata ZURFIN CIKI book 4 part 17

ZURFIN CIKI book 4 part 17

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:17

Duk jumma'a abba yana dawowa gida

musamman in ranar girkin ummi ne don cin

abinci na musamman. Jumma'a biyu kenan bata

fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis

taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin

tsohuwa tazo. Don haka suna gaisawa da umma

tace gurin tsohuwa nazo. Suka shige daki tace da

tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin.

Tsohuwa tace, name ummi? Ta ce na gyaran jiki

mana. Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu

abubuwa. Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari?

Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana,

bada ina fada miki kina sharewa ba? Ummi tace

haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani

shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja

hankalin mijina. Ta ce, toda farko ki dinga kula da

jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar

iska. Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga

tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba

dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da

ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi. Sannan ki

amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga

inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan

inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga

matsa farin miski a ehem dinki. Sannan ki samu

saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari,

mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari

dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi

biyu safe da yamma. Sannan ki aya garinta,

kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa,

sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar

ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai

ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale,

citta, lemun tsami, ki markada su kisha. In anan

maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum

daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta

musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban

da dukkan sauran mata. Ki hada da biyayya

tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi. Ummi

tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin

nan? Tace, bari zanba matar ado dake yawan

zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu. Amma

su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya

siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin

ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan.

Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje

gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi

tasan duk wadannan hadin matan? Tun ranar

alhamis din ta soma aiwatar da darussan da ta

debo daga tsohuwa, safiyar jumma'a ranar zai

bar dakin bishira. Ya fito tana sharar tsakar gida

ta gaidashi, ya amsa da fara'a, tare dawani kallo

mai fassarar in ba keba. Cikin muryar data adana

don shi kadai tace, ya abba ina son in je ayi min

zanen fulawa. Yace jiya kin fita yau kam a'a.

amma ki aika akira mai zanen tazo ta miki. Ta

marairaice, towa zan aika yaya abba? Yace aike

ni, ina ne gidan? Tace layin su umma ne yace to

za'azo ai miki. Bishira tafito daga daki tazabga

ma ummi harara, Tare dacewa kisisina. Abba

yakalleta, kema sai tayi miki. Tace bana bukata,

aikin banza, shikam yafice. Ummi kuwa tace gaba

da aikinta, ita ko sai tasa kujera tazauna tana

sakin zantuka, eh don kwalliyar tabanzanta tunda

ba a iya biyawa miji bukata. Allah dai yasa ya

fada min komai, to ni me zai dame ni don 'yar

aiki kawai na dauki yarinya. Tashare min gida,

tayi wa mijina abinci, daga nan fa? Saita saki

shewa, ummi ta ce aranta yau zan bambance

miki. Birabiskon shinkafa tayi da miya, ta wadata

birabiskon da kayan lambu, miyar ta dauki nama

da bushasshen kifi. Sannan ta hada musu kunun

aya yaji dabino da madara, ta aikawa ummanta

lokacin da kamal yazo daukar na ummarsu.

Tasheka wanka taci doguwar rigar shadda koriya

mai duhu, ta kafe dauri tamkar yau ne daurin

aurensu. Ga fulawar da yaje ya biya akazo aka

zana mata. Tanajin rigimar muhibba tafito tazuba

mata adan kwano tazaunar da ita akofar falon

mamanta. bishira tafito kicin baki tasaki tana

kallon ummi da tazo wucewa harda bangazar

ummi, nan ko kamshi ya bude ta na turarukan da

ummi ta fesa. Abba yana yin sallama ummi tafito

da sauri, oyoyo yayana, bishira tana daga kicin

dinta tana kallon su. Ummi ta rungume shi,

sannu dazuwa sahibina. Ta amshi ledar

hannunshi dajakar, yace yauwa sannu babyna

tace inazan kai ledar? Yace akwai ta bishira aciki

ki ciro. Ta mika mishi ledar ta wuce dajakar

dakinta. Ya mika wa bishira lemo da abarba da

yayo musu tsaraba sannan ya wuce danasu,

awulakance ta aje. Yana shiga ummi tadan karo

kofar yanda bishiran zata iya lekensu sosai ta

gefen kofan. Ta cire masa hula ta aje akan

madubi sannan ta kunna fanka. Ta shirya masa

abinci, yauni zan baka har ka qoshi. Haka suka

yita baiwa juna abaki har suka qoshi. Yakamo

hannunta mai qunshi yana ta sumbata, wai kamar

kada su goge. Kumatun shi ta shafa nima yau

kamin kyau, koda yake dama kai me kyaune, ina

sonka ya abba sosai. Cikin jin dadi ya mannota a

jikinshi, nima ina sonki, ina manta kowa da komai

in muna tare, tace ina tsoron kada wata rana ka

juya min baya. Ya saqalo hunnuwansa cikin nata

ina fata in mutu kafin lokacin. Ummi tasomayi

masa wasu irin darussa wadanda tasan yana

saurin tada sha'awarshi nanda nan kuwa tasa shi

fita hayyacinsa yakama surutai. Ummi ta tabbata

bishira tana wurin ta labe, don haka tai murmushi

ta bishi suka tafi duniyar ma'aurata. Bishira

tamkar tayi hauka sai kawai ta fado dakin tana

fadin, maciya amana, har yanzun ba afita daga

lokacin girkina ba munafiki. Abba ya tashi sannan

yaja riga yasaka, ok dama kina labewa ne kiji

sirrinmu? Da taga ya sauko da zafin rai saita

gudu dakinta. Yabita yamata tatas, kuma ya fada

mata cewa tazo ta shiga dakin ta zauna ba labe

ba, yanzun zai komane yaci gaba daga inda ya

tsaya. Tayi ta kuka gashi ba damar zuwa gurin

umman bashir dole ta tafi gidansu. Shi kam abba

shareta ya yi kosu umma bai fadawa ba. Sabuwar

soyayya ma ya balle agidan, su ci abinci tare,

wanka tare, su fita yawonsu a qafa ko amota. In

yana gurin aiki bini- bini ya kira waya, ita kuma

ko yaushe cikin kirkirar girki da kwalliya tare da

dadadan kalaman dazata fada masa take.ZURFIN CIKI book 4 part 18

ZURFIN CIKI book 4 part 18

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:19

Ummi tayi alalar gwangwani ta sauke kenan sai

ga aunty farida da yake tunda akayi auren ummi

batazo gidan ba. Har daki ummi ta shiga suka

gaisa tayi masu addu'a zama lafia, tayi mata

nasihar zama da miji. Umman taji dadi tare da

kwadayin ina ma bishira take da halin yayarta, ta

zuba alala ta kaima aunty falon bishira. Ta isko

su tana mata fadan kaxanta, cikin murna aunty

ta anshi alalar taci bishira ta cika fam. Tun tana

jurewa har tace aunty ai kin zubar min da kima,

ya ya za'a yi ki anshi abun kishiya kici. Aunty ta

kalli bishira fuska daure tace ke da ita akwai

bambamci ne? Bishira tace aunty bambamci ma

nifa jininki ce ita fa? Aunty tace a musulunci fa?

Bishira ta hade rai tana kallon aunty, taci gaba

da cewa, A musulunci tama fiki don tana sallah,

Haka nima ina sallah, kefa kin faru? In kin soma

sallar to kin shigo cikin mu ni da ita. Domin

addinin mu ya nuna muna dukkan musulmi dan

uwan musulmi ne. Inji mai tsira da aminci. Haka

zan iya cin abincinta banci naki ba don bakida

tsafta. Ta daka mata tsawa tashi don allah

malama kije kiyi wanka, ki wanke duk jirwayen

nan naki kafin In daukeki da motata. Da zasu tafi

har kudi aunty farida taba ummi, ummi kam

godiya ta dinga yi. Haka nan da abba ya shigo ta

nuna masa tace ai abba ya ciri tuta a zuri'arsu,

halin mahaifinsu ne da ita. Wata rana aunty ta

bugo ma abba waya cewa aisharsu ta haihu don

allah ya fadama bishira koda ya iso gida ya fada

mata nan ta shiga murna. Washe gari tace zata

gida tama mahaifiyarsu barka. Sannan taji randa

zasu abuja wurin aisha. Yace ta shirya ya

sauketa, ta samu aunty tazo nan dai sukeyi wa

juna barka, mahaifiyarsu tace dubi yar uwarki sai

yanxu ta haihu gwanin shawa. Amman kinje kin

gwarje miji ma yayi maki kishiya, dubeki kamar ba

yar gidan nan ba. Aunty tace mummy ai ita taso

ta zama Haka, tunda kaxanta ce sana'arta.

Hajiya zainu tace ni wani lokacin bana ganin

laifinta a kaxanta, don a gida bata saba aiki ba.

Laifinta daya a gurina wannan abba data nace ta

aura, data tsaya ta gama karatunta ta auri wanda

zai dobo mata yan aiki komai saidai ayi mata

tana daga zaune, amman ta likema talakan tela

wanda bashida ko sisi. Aunty ta katse mamarsu

da cewa In tana da yan aiki shine har wanka

zasuyi? Ta cire dan kwalin dake kan bishira kalli

fa mummy har kanta zasu wanke mata. Mummy

tace aiki gida ya mata yawa, yaushe har ta gyara

jikinta? Aunty tace kawai mummy kina goyon

bayanta ne. Bishira tace aunty mummy ta

fahimta kece baki fahimta ba saboda kina da yan

aiki. Mummy tace duk ba kece kika yima kanki ba,

ga kishiya an maki, bishira ta tabe baki nima duk

nadama ta isheni. Kuma shi da matar duk bana

raga masu. Don ban damu ya sakeni ba, yaji ne

dai nace na daina, daddy ko nazo cin mutuncina

yake gabansu. Mummy tace kin man dai dai.

Haka yake bishira kullum cikin tsokanan hayaniya

da ita da miji ko kishiya. Amman ummi yamxun

bata kulata Domin umma ta gargadeta. Bishira

bata bar gidan ba saida mummy ta zugata

Sannan tace mata jibi kizo za a kai su innarku

yin barka abuja kije ki dan huta kafin suna.

Bishira tace daman ban taba zuwa ba, ko anyi

suna sai na huta. Aunty tace kada ku yanke

hukunci ba tare da sanin mijinki ba kije kiji ta

bakinsa. Bishira ta ce ina ruwana da yardarsa

aunty. Haka kuwa data dawo ta shiga tattaro

kayan ta dake jibge a gefen gadonta, don ita zane

ko yau a aka dinka shi In tasa ta cire duk In da

tayar kafin ta dauke shi yaji jiki. Wani ma saita

goge ruwa ne, kamu ne, duk kyan zani saita goge

tsakar daki dashi. Ranar dama abba dakinta

yake, tace mashi jibi zamu abuja Inji mummy.

Taso ya dan sai mata zani sabo wanda zata

danci suna ya dinka mata. Yace akwai wani leshi

dan sai maku yana shago, Tun wancan satin

naso In zauna In dinkashi da kaina don mai tsada

ne. Tace nawa ka siyeshi, yace dubu biyar ko

wane daya, bishira ta tabe baki. Na zaci zakace

sha biyar wai dubu biyar, yace matsalata da ke

rainuwa yace bari zansa a dinka maku gobe ashe

sunan har yazo? Tace a'a jiya pha ta haihu, ya

sake kallonta jiya? Shine zaku tafi jibi? Tace eh

mummy ce tace mu tafi jibi. Yace a'a kibari sai

ana gobe suna kije. Kafin lokacin ma na samu

wasu kudi da nike sa rai. Sai na sai maki kayan

barka zanen maman da kayan baby. Bishira ta ce

gaskia gobe zamu tafi, In ka sayi kayan barkar ka

aika dasu can wurin mummy yan tafiya Ranar

suna su kai mata. Abba yace nifa ban amince da

tafiyar nan gobe ba. Ban yarda ba. Bishira ta ce

ba wai ina neman yardarka bane, ina fada maka

umurnin da mummy ta bani ne, ko ka mance

mahaifiyata ce? Mamakinta ya cika abba, yace

mahaifiyarki ita zata baki izinin tafiya ko ni?

Umurnina da nata yanzu wanene...? Bishira ta

katseshi kada kayi ganganci hada kanka da

mahaifiyata, ita ta haifeni ta raineni har ka ganni

kace kana sona Sannan ka dinga kokarin

kwatanta kanka da ita? An fada maka kowa

baisan darajar mahaifiyarsa ba irinka? Abba ya

mike ni ne bansan darajar mahaifiyata ba? Tayi

shiru yace nagode Kuma suna na hanashi ma

gaba daya. Zan gani Kuma Bishira ta ce zako ka

gani.ls / ZURFIN CIKI book 4 part 19

ZURFIN CIKI book 4 part 19

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:14

Duk ummi tana jiyo su amman bata fito ba, tana

ta mamakin yarda bishira batasan darajar

aurenta ba, bare tasan girman miji. Ranar da

zasu tafi kuwa ko a jikinta ta dibi tsummanta ta

nufi gidan su, Duk ta fadama mummy yarda

sukayi. Mummy tace kinman dai dai talakan

banza shine zai hada kanshi dani, tafiya zakiyi in

yaso in kika dawo ya ce baya auren. Abba ya

dawo ya samu dakinta a rufe, ummi na daka

sakwara a kofar dakinta yace ina bishira? Ummi

tace ina ga ta fita, don ina daki bansan fitarta ba.

Ya daga waya ya kira aunty yace bishira tazo?

Aunty tace bata fada maka zasu tafi abuja bane,

Abba yace ta fadaman amman nace a'a sai ana

gobe suna zataje, ya kwashe komai ya fadama

aunty. Aunty tace kayi hnkr don allah idan ta

dawo da kaina zan hadata da daddyn mu, Abba

yace kiyi hnkr aunty na gaji da halin bishira inga

wannan karo gwara kowa ya huta ni da ita. Aunty

tace kayi hnkr Abba yace sai anjima ya kashe

wayarsa. Zama yayi kan kujera dakin ummi yace

gaskia wannan karo bazai fadawa kowa ba ya

gama auren bishira. In bai nuna mata kurenta ba

nan gaba zata masa abunda yafi wannan don

Haka yabar komai sai ta dawo. Ummi kam

batason ya rabu da matarsa, amman kam saida

taga tarairaya cikin kwanu kan nan matsalarsu

daya, Abba yace ummi kodai asibiti zamuje ne,

ummi tace muce masu mi? Yace muyi masu

bayani mana, ummi tace a'a. Yace to muje mu

fadawa umma, ummi ta zare ido yanxu sai kama

umma wannan zancen? Yayi murmushi. Ai da zan

iya mata wannan maganar da tuni na mata,

asibiti ma abunda yasa banson zuwa sai likita ya

bukaci ganin wurin. Ni kuma ina kishin wani

namiji ya kallan mi al'aurarki, ummi tace nima ai

shine, ya sake janyota jikinshi. Yanzun Haka

zamu zauna? Shine nakeson in fada maka naji

kana ka gaji da aunty bishira kila zaka saketa ne.

Toh don allah ka rabu da ita tunda ko ka saketa

sai ka auri wata. Tunda nasan zama Haka bazai

yiwu ba. Ta soma hawaye ya shiga lallashinta

yace Allah zai yaye masu. Haka sukaci gaba da

rayuwa cikin kwanakin da bishira bata nan, ummi

tanason kalolin wasanin da Abba ke mata,

amman da yaso kwatantawa ko allah ya amshi

addu'a su ta warke saita kwace jikinta ya hau

bari tayi ta kuka. Don Haka sai ya hnkr da

bukatarsa amman ya takura sosai, kuma yana

ganin dole yabar batun bishira yanxu don Haka

ya jaye batun saki amman sai dole ya nuna mata

kurenta. Ranar data dawo kwananta takwas

Ranar ma bata da niyar dawowa sai da aunty ta

kira mahaifinsu ta sanar dashi, ya kirasu a waya

ya zagesu tas gaban mahaifiyarsu harda mai

jego. Tace bishira ta dawo shine ya kira Abba da

waya ya bashi hnkr yace Duk irin wannan ta faru

ya kirashi ya sanar dashi. Abba ya shigo da T. V

guda 2 daya ya kai dakin ummi, daya ya kai falon

bishira wanda ya yanke kwadon. Ummi tayi ta

murna bishira kuma ta daki Duk rashin kunyarta

gabanta sai faduwa yake, batasan ya zasu

kwashe ba. Sai da taga baiko kalleta ba daga ita

har yar sannan ta dan saki jikinta, tasan ba zai

tsaya a fushi ne in taci sa'a. An dauki sati guda

Abba baya ko kallon inda bishira ta ke ko Ranar

girkinta sai dai yayi kwanciyarsa a falonta. Duk

da yana bukatarta Haka kuma ya janye yan

wasanin da yake da ummi don wahalce yake

bacci, ita kuma sai ta damu don ya saba mata

sai tayi tunanin ko laifin tayi masa ne. Ita kam

bishira ganin zura ido ba zai kaita ba, don Haka

ta sauke zafin kai ta iske Abba a falonta wani

dare harda kukanta take bashi hnkr. Wai sherin

shedan ne ba zata sake ba, Abba ya dubeta mi

kikayi? Tace nidai ka yafeman, yace ashe kinsan

kinyi ba dai dai ba? Ai inda ke ce saikin kara,

amman bari kiji na rantse maki duk kika kara

zuwa wani wurin bada izinina ba wllhi sai kinsha

mamaki. Tace na yarda, abun mata da miji nan

dai suka sasanta, hakan nan dakin ta ya kwana,

suna shiri cikin satin don bishira ta fahimci mijnta

ita kadai a matarsa, yarda yake rawar jiki lokacin

kwanciyarsu. ***ummi na zaune idonta kan tv

Abba take kallo yarda yake watso turanci cikin

kwarewa. Kullum kara sonshi take, ta kwantar da

kanta a hannun kujera, kusan sati guda kenan

tana lura da Abba. Baya son ko taba hannunta

sannan ga wani shiri da yake da matarsa, sai dai

yazo yaci abinci ya dauki laptop dinsa ya raba

dare. Inko yazo kwanciya saidai ya juya mata

baya sabanin kwanaki da yake mata makwanci da

hakarkarinsa, lokacin tasan babu inda keda dadin

kwanciya ga matar aure irin hakarkarin mijinta,

sam bata iya bacci sai tunanin abunda tayi masa,

amman yau din nan zata tmbysa ko laifi tayi

masa, Bayan yaci abinci yayi wanka ta dauko mai

zata shafa masa ya amsa da murmushi yace

barshi kawai nagode, ta dawo ta zauna, zaya fita

tace ina zaka ya Abba, yace aski zani, ko zaki

rakkani tace eh yace taso muje. Suna tafe suna

hirar aikin shi, yace An koma kirkirar wani filin

kuma An saka shi ciki, yanxu abubuwa zasu kara

mashi yawa. Sun isa babu layi An suma mashi ya

mika mata wayoyinsa guda biyu tana danne

danne kira ya shigo. Nan take ta hade rai ganin

sunan dake jiki zainab dina, ya tmbyta da ido

waya kira ta sake hade rai, sannan ta mika masa.

Ya kalli sunan zainab sannan ya daga cike da son

ya zolayi ummi yace zainabuna. Can bangaren

Duk da kallaman Sun mata dadi tace da ba

amman yanxu ta wani ce. Yaya salis ya kawo

maka katin aurena? Yace eh yabani tace ya

amarya? Yace gata bari in bata ku gaisa, ummi ta

kauda kai tare da jan tsaki, yayi dan murmushi

yanason yanda ummi ke nuna kishinsa, salon da

take wurin kishinta daban ne. Yace zainab Wai

tana gaisheki, zainab tace to ina amsawa. Ka

gaida umma sannan ka sai masu anko kalla biyu

ne. Abba ya naji ko kalla goma ne zan saya tace

to gobe kazo gidan mu nan ake sai dawa. Ya kalli

ummi yasan kadan ya rage ya kaita bango. Ya

danne dariyar da ta taso masa yace gobe kikeso

nazo gidanku zainab? Tace eh don gobe za'a

kawo wasu kayan, yace to zanzo, ummi ta zaro

ido ta mika tsaye dai dai lokacin da aka gama

askin. Yayi sallama da zainab din sannan ya

shiga karkabe jikinsa. Ummi kam tuni ta kai bakin

kofa. Ya sallami mai askin ya isketa Sun jera

yanxu ba kamar daxun da suke fira ba. Sun kusa

layinsu yace muje mu gaida su umma tace ni

bacci nakeji baice komai ba, Sun iso hijabi kawai

ta cire ta kwanta, yace Wai lafia don zainab ta

kirani tun dazun kin kasa sukuni?URFIN CIKI book 4 part 20

ZURFIN CIKI book 4 part 20

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:17

Ummi ta taba baki, Allah yakawo ta lpy. Ya ce ni

ban soba gsky. Sbd ke ummi tadafa kirji, sbd ni?

Ni ya abba, kada kasa duniya ta zage ni, Tare fa

nasameku? Yace to ni dai kada kiga kamar da

son raina, tace don Allah ya Abba kabar zancen

nan. Kaje kagyar mata dakunanta don su kamal

bazasu iya ba, yanufi gurinsu ganin kamar ya

damu yasa itama taje tasa musu hannu don dai

ya saki ranshi, sun gyara tsaf ummi ta goge

sannan ta rufe dakin. Har magriba bishira bata ji

an ce za'a maida taba, sai ta dauki wayar

kanwarta ta kira shi wai yazo don Allah

yadauketa. Tsakanin mata da miji sai Allah, nan

ya tausaya mata yace zaizo, kafin ya isa sai daya

sai mata waya irin dai ta hannun ummi. Har cikin

gidan ya shiga suka gaisa da babanta, yayi

murna sosai yayi tawa Abba godiya, tare da ba

shi hakuri yace yasan yanda ta horu zai gata

canza da yardar Allah. Yasa aka turo ta yayi

mata nasiha, sannan ya gargadeta da cewa inhar

ta bari mijinta yakawa kararta zatayi mamakin

abinda zai mata. Tace, insha Allahu baza ta kara

ba, yakawo kudi yaba Abba, da kyar ya amsa ita

kuma ya bata wasu zannuwa acikin leda, yace su

raba da abokiya zamanta. Taje tayi wa hajiya

zainu sallama suka tafi, tamkar baquwa haka ta

koma, sai kace basu taba zaman aure da Abba

ba, nauyinsa take ji. Suna tafe ya ciro waya ya

miqa mata, tasa hannu ta amsa yace taki ce, tayi

ta godiya yace ba komai. Sallamarsu tasa gaban

ummi faduwa, ta dake ta fito ta amsa, wani kishi

ya tasho mata amma saita danne. Ta kalli bishira

tare dayi mata sannu dazuwa, ta amsa tana

kallon ummi tayi kyau tagoge daga ka ganta

kaga wayayya 'yar gatan miji. Ta dauko makullin

dakin ta ba bishira, abba kuma ya nufi dakin

ummi. Bishira ta dinga kallon yanda abba ya

gyara gidan yaja gini ta gefen ummi yayi mata

falo da kicin, sannan tsakar gidan an gyare shi da

tiles. Haka bandakin su yagyara shi, nan dai

bishira ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana

yi wa allah godiya tare dayi wa kanta alkawarin

har abada bazata ta kara yin yaji ko ta janyo

abinda zaisa mijinta ya sake ta ba. Ummi tana

kan gado tana karanta wani littafi yazo ya zauna

bakin gadon bata ko kalle shi ba don haushi take

ji. Sai take ganin kamar rawar kai yake yi da

dawowar bishiran, kuma tuntuni yana zuwa gurin

ta ya boye mata. Yace madam ina son in yi

magana da ku ne ke da bishira, ummi tace ina jin

ka, yace can zaki zo muje. Tace, gsky nagaji, kayi

maganar da safe. Yagama gano kishi ne ke

damunta, don haka yayi murmushi yace yanda

kikace hakan za'ayi. Ya fita kamar minti 30

yasake shigowa ya aje mata leda tare da cewa

saida safe aciki tace Allah yabamu alheri. Yana

tafiya taje ta banko kofarta, yau kam bacci ya qi

idanun ummi sbd tayi sabon bacci a haqarqarin

Abba. Dukkan filolinta ta rasa wanda zai maye

mata madadin haqarqarin mijinta, ynzun yancan

da wata tasan yanda yake wannan rawar jikin

ynzun ya manta da batunta. Tarasa me yake

mata dadi, littafin datake karantawa kuwa sam

bata fahimtar abinda ke ciki. Hka ta dinga zubda

hawaye har nisan dare, ganin bata da wata

mafita, tashi tayi ta bude kofa lokacin 2 saura

taje tayo alwala tazo ta kama nafila. Abba jin

bude kofarta ne yasa shi leqowa ta window

aranshi yaji tausayinta don yasan bata iya bacci

sai ajikinshi, ita bata san ya leqo ba don ko

hanyar dakin bata ishe ta kallo ba. Yakalli bishira

wadda bacci yayi gaba da ita ya tausaya mata

sosai yanda tayi tarawar jiki alokacin

auratayyarsu dazun. Yadauko wayarshi yarubuta

ma ummi sako. KI KWANTA KIYI BACCI BABY,

TARE DA QISIMA CEWA KINA LAFE

AMAKWANCINKI (WATO JIKINA) INA CIKE DA

KEWAR LEBUNANKI Tana sallah taji shigowar

saqo amma bata yi ko marmarin dubawa ba, haka

tai sallah har zuwa lokacin da bacci yasoma

fizgarta. Tayi adduo'o'i sannan ta kwanta, saida

asubahi ne datayi sallah sannan ta karanta, dan

tsaki taja tare da cewa, Karya kawai, kishi yasa

ta fadin haka don tasan Abba sosai baya boye

mata komai ynzun. Sai dai abinda yasake qular

da ita da asubahin nan yanda tana fita shi kuma

ya fito wanka, duk da tasan dole wani abu yafaru

tsakaninshi damatarsa, amma sai taga tamkar da

gayya ya tsaya don tafito taganshi. Tna idar da

sallah ta dora ruwa akicin dinta, tadafa ruwan tea

taje kicin din bishira tadauko flask tazo ta wanke

ta zuba musu ruwan zafi taje kofar bishira tayi

sallama bishiran ce ta bude ummi tamiqa mata

tare da cewa an tashi lpy? Cikin sakin fuska tace,

lpy lau, nagode. Ummi ta ce ba komai takoma

dakinta ta kulle kofarta don yau bata da darasin

safe. Abba ma yau bada wuri zai fita ba, don

haka yadan samu baccin safe sai 8 yayi wanka

ya karya, sannan yanufi dakin ummi. Kofarta tana

rufe, ya kwankwasa ta share sai can dai dataji

yaqi tafiya sannan tazo tabude. Takalle shiya yi

kyau cikin kananan kaya, ta kauda kai tare da

cewa, an tashi lpy? Yace lpy lau, kin karya? Tace,

um'um sai anjima, zata rufe kofar yace,

makaranta fa? Tace sai karfe 2 nake da darasi.

Ta maida kofar ta rufe, yayi dan murmushin

takaici sannan yafita. Kwananshi 2 dakin bishira

yayi niyyar dawowa dakin ummi, don ya kosa

yadawo ya lallasheta bazai iya daukar wannan

shariyar da take mishiba. Tsakaninta da bishira

lpy lau amma shi sai tana wani share shi. Ya

shigo da zumudi zai nufi dakinta, tamiqe cikin

fara'a daga wanke-wanken da take yi ta amshi

ledar hannunsa da jakar laptop ta nufi dakin

bishira. Shida bishira suka bita da kallo, ganin

zata shiga bishira tace ummi yau ai dakinki yake.

Ummi tace injiwa? Anty bishara ai kullum ke ce

dashi har sai kin rama duk kwanakin da kika

dauka agida. Kinga kenan kusan wata goma sha

daya kenan. Abba cikin sauri yace ke

mahaukaciya ce? Ina ki kasamo wannan fatawar?

Ta kalle shi, sannan tashiga dakin ta ajiye ta fito

taqara kallonshi gurin malamai, yace to ban

yarda ba, don haka zanci gaba dayi muku kwana

bibbiyunku, ummi tace to ni na yafe mata nawa

kwanakin bishira tace nagode ummi. Haushi ya

cika Abba, amma shi bazai dauki wannan horon

da ummi take shirin yi masa ba. Yadawo dakin

bishira a fili yafurta kema saina baki haushi zakiyi

dakin sanin wannan furucin. Sharewa yayi yaci

gaba da kwana dakin bishira tare da nuna kulawa

ga bishiran. Ummi ta jure duk da duk daren Allah

sai taci kuka ta gode Allah, sannan tashiga zargin

cewa shi ma ya Abban dama can yana son

tarewa dakin bishira, inba haka bame zaisa yayi

saurin yarda kuma yayi ta nuna mata soyayya?

Ganin ummi tana yi tamkar bata damu ba yasa

shi qa rajin haushi, yadawo da yamma suna

zaune kowa A qofarshi. Ummi tayi kwalliya cikin

qananan kaya, bishira kuma tana sanye da leshi,

karatun littafi bishiran keyi ita kuma ummi tana

yin gyaran qumbunanta. Bawai suna wata hira

bane amma suna kula juna sosai musamman

bishira tana son su saba da ummi. Ummin ce.

bata cika son fitowa ba, bishira ta tashi ta masa

sannu dazuwa tare da amsar kayan hannunsa

don yanzun tana koyi da ummi gurin kyautatawa,

ummi ta kalle shi sannu dazuwa, ya amsa da

yauwa baby. Yakalli bishira sweety zanyi wanka,

tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai

tazo tace masa takai nan k sweety zanyi wanka,

tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai

tazo tace masa takai nan kuma yajanyo bishira

jikinshi. Ba wai yana da bukata bane, amma don

ya shaqar da ummi sai ya banko kofar, qaran

kofar ne yasa ummi kallon gurin dakin. Ta duqar

dakai taci gaba da abinda take yi, kusan minti

arba'in suka fito, Abba ya matsawa bishira wai

suyi wanka tare, tace ni bazan iya ba akwai ummi

dama da dare ne inajin kunya. Kuma kada taga

kamar cin fuska ne, yace kenan don kada ki bata

mata rai ni mijinki bazaki faranta min ba ko? Dole

ta bishi suka shiga bayi. Baqin ciki yasa ummi

tashi tashige daki, kuka sosai tayi daga nan bata

fito ba sai magriba, tanayin alwala tarufo kofa,

washegari ma qin bude qofar tayi daga alwalar

asubahi. Abba yayi ta raba ido ya ganta amma

bata fito ba, yasan fushi take, ya kira wayarta

taqi dagowa yayi mata saqo cewa in zata

makaranta tafito inkuma sai darana ta bude ta

amshi kudin mota. Tana gama karantawa tayi

wuri da wayar ba tare data bashi amsa ba, haka

ya tafi. Bishira ta qwanqwasa ma ummi ta bude

suka gaisa, tace naga baki fito bane ina fata lpy?

Tace lpy lau bacci ne, tace yau baza kije

makaranta bane? Ummi tace, zanje sai sha biyu.

Bishira tace kinji dadinki ni gashi nan ina tayi

masa zancen karatun amma ya share ni, ummi

tace inkin matsa zai yarda, tace ko za ki dan sa

min baki? Ummi ta riqe baki, ni a wa? Ke da yake

hannunki ai ke ce zai saurara, ni kin zo ne ma ki

zage ni. Bishira tace wane irin zagi? Ni dama ki

amshi mijinki ummi don gangar jikinshi ce kawai

agurina, amma ruhinsa yana gurinki. Ummi ta ce,

ngd da zagi, bishira ta ce zancan gsky ne ba

wani zagi. Haka suka yi ta rayuwa cikin kwanakin

ummi kam har rama tayi shima Abba ya rage

walwala don wanda yasan kan kula da shi

kamarta. Yayi missing din abincinta. Amma ya

gaji bazai jure ba. Ya tuna bishira tace masa zata

ta yini gidan ummanshi. Don haka yana gama

muhimman abubuwan da zai yi agurin aikin

yanufi gida. Ummi tana shirin tafiya makaranta ta

dauko jakarta sai kurum taga mutum kamar an

jeho shi. Ta daure fuska tamkar bata taba dariya

ba, yace ummi nagaji kin ji ko, na gaji da wannan

horon naki. Laifin me nayi miki? In don na dawo

da bishira ne sai in saketa, duk ba kece kika

takura min sai na dawo da ita ba? Ummi tace, ni

karka doran jakar tsaba kasa kaji su bini, ka saki

matarka sbd ni? Ba ruwana. Yace, to ki dawo

yanda kike, kuma ki janye batunki na wai kin

haqura dani, niban haqura ba. Ke ma kuma nasan

dole ki kasa kanki, ummi ta ce ni ban damu ba,

ya ce qarya ne gashi nan duk kin rame? Ya

canza daga fada zuwa lallashi, ummi don Allah

na roqeki mu koma kamar da, haba bebyna. Ya

lalubo hannunta ta qwace, don Allah ka tafi kada

bishira ta dawo ta same ka anan ta zargi wani

abu. Haushi yakamashi sosai, ya daga murya da

qarfi, kin san Allah ummi zan hadaki da umma, ta

nufi hanya fita, nikaga kada kasa ni yi latti don

lokaci yayi nisa. Ya ficiko ta ta dawo ba zaki

makarantar ba, ke an ma daina karatun tunda yafi

ni. Ta zubar da jakar da hijabi ta nufi gado shi

kuma ya fita cikin zafin rai, gidan su umma yaje.

Bishira tana dakin umma tana sallah yabi umma

kicin, umma gurinki nazo, ta dube shi lafiya

Abba? Ya turo baki, alamun ranshi bace baki,

yace umma ki sallami bishira, tace kamar yaya?

Yace taje can gidan ko muyi maganar agabanta?

Tace, kyale ta muje dakin babanku. Abba ya fada

ma umma komai da ummi ke masa, tun dawowar

bishira ran umma ya baci tace ka barni da ita.

Banda shashancin ta da ita kadai take son

azauna? Baga bishirar nan ba gidan nan ta gane

kuskurenta ko yau yarinyar nan sai da tace in

yafe ta nace ni dama ban riqe ta da wani abu ba.

Shine ita zata qirqiro fitina? Yace, umma ai ba da

bishira take yi ba dani take yi, tace to zata gane

kurenta da dare kuzo kai da ita. Umma ce ta kira

ta awaya tace tazo ita da abba, jikinta ya mutu

don tasan qararta aka kai, tana idar da sallar

isha'i taje gidan. Can tasamu abba, nan ko umma

ta rufe tada fada, koda tsohuwa ta jiyo tazo

umma tafada mata komai sai ta shiga fada. Wai

ai kishi halas ne, ke suwaiba tsakani ga Allah ko

ke bazaki so kishiya ba, bare ita yarinya. Abba

yace to gata nan ita ce fata dame ne nida batun

in dawo da bishirar, yanzun na dawo da ita kuma

ni abin ya qare akaina? Nan fa umma tayi mata

tatas, ta kuma sata anan ta ba Abba Haquri, aka

kira shi awaya ya fita. Umma ta samu dama

taqara yi mata nasiha da cewa, in bnda shirmenki

yaushe zaki bar ladanki, hanyar aljannarki kice

kinyi fushi da ita kin barwa kishiya? To kada in

sake jin haka, ki riqe darajarki da mijinki, ke

ganinki da ita. Ta jima tana bata shawara kafin

Abba yadawo suka nufi gida. Ya shiga gurin

Bishira ya fada mata cewa yau gurin ummi zai

kwana, nan ya bar ta da kewa yanufi gurin ummi,

tamkar yaune daren farkonsu hara sukai rayuwa

s / ZURFIN CIKI book 4 part 21

ZURFIN CIKI book 4 part 21

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:19

Kwanci tashi asarar mai rai, shekara ta zagayo

lokacin bishira da tsohon ciki, Abba nason yara

don muhibba taqi dawowa tafi son umma dole

suka haqura suka bar mata. Ta haifi 'yarta

budurwa tubarkalla ranar suna ta ci sunan sahura

inda suka sa mata walida. Ummi nason yara, don

haka in tana gida to tana manne da walida, Abba

yana damuwa da rashin samun cikin ummi,

wanda ita ummin ta barma Allah komai. Shekaru

uku sun sake biyo baya, lokacin Bishira ta sake

haihuwar habiba takwara Abba yayi wa ummi.

Tsohuwa an qara tsufa, 'yan rigingimu sun qaru

tace ita Abba yama takwara amma bata son ya

duke ta irin yanda yayi wa ummi. Abba kullum

qara son ummi yake, umma ta matsa masa sai

da yayi qoqari ya sai fili rabin filoti tace kuma a

rage ciye ciyen dadin nan agina shì. Haka kuwa

ya gina flat mai daki hudu, daya ummi daya

bishira, sai nashi sannan na yara. Yayi qoqari

gurin gyaran falon ita kuma ummi ya canza mata

kayan daki don bishira an canza mata daza su

tashi agidan su. Yace tabishi bashi in ya samu

zai bata kudi amadadin kayan daya saima ummi,

tace ta yafe. Ummi dake karantar (BUSSINESS)

har ta hada (H.N.D) dinta kuma tayi bautar qasa.

Abba dai yace baza'ayi aiki ba amma ya yarda

tayi kasuwanci, Alhaji babba ne ya bata jari inda

take saro kaya zannuwa, lesuna, takalma zuwa

jakunkuna. Abin ya amsheta don har kayan aure

tana hadawa, tana yin saqo irin su kwatano da

chaina, india, pakistan ko dubai, ta hanyar wani

wan kawarta. Haka kawai ummi ta samu kanta

da zaban abinci, yawan bacci kasala da dai

sauransu, sam bata san takamaiman lokacin

al'adarta ba. Don bata wani lissafi in yazo shi

kenan in bai zo ba bata damu ba tama cire ranta

daga batun ciki. Abba ya kalli nonuwanta, baby

kwanan nan kirjinki ya cika sosai, gashi kinyi

haske ko kin canza mai ne? Tace yaya yaushe

kazama likita? Yace, ummi kin fa canza shirya

muje asibiti, ta ce ya Abba don Allah ka bar ni

nagaji dazuwa asibiti. Yace, to ni zan je inya

tambaya game da yanda ki ka canza. Cikin jin

haushi tace sai ka dawo. Ga yara atsakar gida

sun ishe mu, yace ni naki nake qawar in gani

nasan addu'ar da nike yi bazata fadi kara banza

ba, sannan ga qoqarin danake yi, shiru ta masa.

Dagaske yake yi yaje yayi wa likita bayani, yace

yadai kawo fitsarinta. Sai da suka yi tsiya da qyar

bishira ta lallasheta ta yarda ta bada fitsarinURFIN CIKI book 4 part 23

ZURFIN CIKI book 4 part 23

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:22

Sam bishira bata damu da barin mijinta da zatayi

gurin ummi ba, tunda ta jima da sanin cewa

ummi bata da wani ammafni. Wannan ne ma

yasa tasha alwashin in taje zatayi addu'a Allah

yakara toshe ummin kada ta warke sam, tunda

umma Bashir ta fada mata duk addu'ar da tayo

kafin ta dawo an karba mata. Ta kuma kara bata

shawara ta roko musu rigima suyi tayi har su

rabu, Bishira tace duk zata roko. Ko ranar da

zasu tafi sai da ta yi wa ummi habaici, kawyenta

sun shigo wato makotansu a tsakar gida take

fada musu cewa mijinta kurum take tunani. Wai

zai sha wahala kafin ta dawo. Wata cikin su tace,

wahalar me ga shi da amarya? Ta ce amaryar da

ta ke a toshe, ai bata da ammfani. Ummi duk

tana ji, takaicin duniya ya isheta sai dai ita zata

so ace bishiran take ta roko ma kanta shiriya ko

Allah zai sa ta dawo ta kama sallah. Dayar tace,

to Bishira ki roko mata sauki mana, cikin zolaya

tayi zancen, Bishira tace ba abinda zai kaini

makka in roko ma kishiya abin arziki. Ummi ta

fito ta ce Anty Bishira zai fi kyau ki roko ma

kanki shirya ko in kin dawo kya fara sallah da

tsafta. To ban san ma yanda zaki kwashe da

ibadar ba ko za a karba tunda ba yin sallah ki ke

ba. Ta taso fuuu, kawayen suka reketa suka ce

kyaleta bakin ciki ne. Abba ya fito wanka yana

cewa, Ok, za kuyi na bankwana ko? Yana da kyau

hakan. Ummi ta koma dakinta. Tun bayan tafiyar

Bishira Abba ya shiga takura musamman irin

wannan lkc na sanyi. Ya dawo da yiwa ummi 'yan

wasanni da ya daina, sai hakan yakara sa shi

damuwa don haka ya shiga lallashin ummi ta

fadawa umma....... Kuyi hkr da typing din banda

lafia sstr dita nake sawa tana maku.els / ZURFIN CIKI book 4 part 24

ZURFIN CIKI book 4 part 24

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:24

Tace ita kam ba zata iya ba ranar wata juma'a

suka tafi da nufun su fadama umma matsalarsu,

sai dai har zuwa bayan isha'i da abban yazo don

su tafi sun kssa sanar da umman komai, har

sunyi sallama abba yayi kunar bakin wake yace

umma ta fada maki matsalarta? Umma tace wa?

Yace ummi tace a'a suka koma suka zauna. Abba

kanshi na kasa Yace umma dama bata da lafiya

ne? Umma tace mike damunta kuma? Yace ummi

fada mata. Ummi ta sunne kai cikin cinya tare da

cewa shiya fada. Cikin sa'a aka kira wayarshi,

nan yayi waje ya barsu, umma tasa ummi saita

fada. Ummi ta rasa ta inda zata dauki zancen,

umma ta soma yi mata fada har tsohuwa ta leko

tambaya take lafiya ba sunyi sallama dama basu

tafi bane? Umma tace wai bata da lafiya ne,

kuma ita da abban sun kasa fadaman shi yayi

waje, ita kuma ta kunshe kai cikin cinya wai injira

ya dawo ya fadaman. Tsohuwa taja hannun

ummi zuwa dakinta, suka zauna bakin gado ta

riko hannunta. Takwara fadaman abunda ke

damunki. Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa

magana. Tsohuwa tace inda baki fadaman ba

akwai wanda zai taimaka maki ne? Tunda naga

duk yarda mijinki yake da umman ku ya kasa

fadamata to abun mai girma ne. Ummi ta daure

tace "Gabana ne fa a toshe....." tsohuwa ta rafka

salati, sannan tace yannan badai angurya ba?

Cikin tsoro ummi Tace, ni ma ban sani ba ko

shine. Salati tsohuwa ne ta jawo hankalin umma

tazo dakin da sauri. Tsohuwa Tace ina ga

yarinyar nan angurya ne a gabanta. Umma Tace

shine don wauta daga ke har abban kukayi shiru,

dubi tsawon watanin da kuka dauka, tsohuwa

Tace yanzun yaya za'ayi umma tace ni ina nasan

yanda za'ayi, ai ni na zata yanzun babu masu irin

wannan ciwon. Rabon da inji labarinshi tun muna

yan mata. Tsohuwa Tace kai nima na jima banji

ba, amman kinsan dama wanzamai ke aikin.

Alhaji ya dawo daga sallar isha'i yaga abba tsaye

a waje, Yace a'a babana dama baku tafi ba, Abba

yace eh yanzun zamu wuce, ya biyo bayan Alhaji

suka shigo suka riski zancen dasu dasu umma

keyi. Alhaji Yace lafiya? Umma Tace yaran nan

ashe zaune suka da lalura, tame inji Alhaji, umma

Tace angurya ce ashe ta fito ma Ummi wai suka

zaune. Alhaji yace meye kuma angurya Tace wani

abu ne dake toshe mace. Nan fa suka shiga

tattauna yanda za'a shawo kan abin, tsohuwa

Tace wanzami za a kira ya yanka mata. Alhaji

yace to gobe zai kira wanzami. ZURFIN CIKI book 4 part 25

ZURFIN CIKI book 4 part 25

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:26

Abba da jin haka sai ya fito, kishi fal da

zuciyarshi, ya ce umma wanzami kuma? Ta ce

eh, aikin sune. Yace gsky umma ba za a kai ta

gurin wani wanzami ba , bagara muje asibiti ba.

Tsohuwa ta ce, kaci gdanku da asibiti komai ku

ce asibiti to wannan ba aikinsu ba ne. Abba ya

ce, Nifa gsky ba xa a kai min mata gurin wani

wanzami ba, umma asibiti zamu. Yanzu kai ya

waye wanzamai ba duka suke dafa kayan aikinsu

ba, haka kawai taje ta hadu da wata cutar? Alhaji

yayi murmushi yasan kishi ne ke damun Abba, ya

ce Babana kada ka damu, goben sai kuje asibitin,

in sun ce ba su san shi ba to sai a zo a yi na

wanzam ko ? Kunya ta kama Abba, Sam ya

manta Alhaji yana gurin ya ce to Tsohuwa ta ce

kuje in kun je ma dawowa za Ku yi dan me taurin

kan tsiya. Abba ya ce naji kin ji ummi taso muje

gda Tsohuwa ta ce oho dai, kuyi ta tafiya in dai

akayi mata aikin ai dole ka barta ta warke . Alhaji

da umma dai dariya sukayi ta yi musu, shi kuma

yayi musu sallama, ummi kam kasa magana tayi

don duk ta tsorata. Suna fita ta rike hannun Abba

gam tana cewa. Don Allah ya Abba kada kabari

wanzam yayi mini aikin nan, zan ji zafi. Ya

rungumota, Ba zan amince ba wani ya ganmin

al'aurar mata, likita ma mace zan nema ko nawa

zan kashe . Ummi ta ce, to zan ji zafi ya Abba?

Ya ce, made ki damu, in asibiti ne kila suyi miki

allurar kashe zafi amma in wanzami ne ina za ya

ga wata allura yayi mini. Ummi sarkin tsoro ranar

kwana tayi cikin damuwa, washegari kuwa tun

bakwai suna asibiti. Babban asibiti suka je sun

yanki kati likita me kula da fannin mata aka tura

su. Mata dayawa suna ta kallon su ummi

musamman yanda Abba ke nan-nan da ita,

sannan wasu sungane shi kasan cewar shi dan

jarida mai farin mini. Wasu mazan kuwa sai zuwa

suke suna gaida shi. An kirata dakin ganin likitan,

ta mike zata Shiga Abba shima ya mike, wata

Nurse ta ce, malam jira mana, ya ce ai duk Mu

biyu ne bamu da lfy, ya shige likitan namiji ne ba

yanda ya iya dole ya yi masa bayani likitan yayi

ma ummi tambayoyi in da duk ta bashi amsa/ ZURFIN CIKI book 4 part 26

ZURFIN CIKI book 4 part 26

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:27

Sannan ya bukaci ta kwanta kan gado ya saka

safar hannu, juya kai abba yayi don gaskia ranshi

ya baci, lallai ya kamata mata musulmai su dage

suyi karatun likitanci don su taimaki yan uwansu

mata. Sai da likita ya gama dubata sannan ya iya

dubansa, likita yayi wani rubutu ya mika abba

tare da cewa, an baku gado zayi mata aiki gobe

ko jibi. Abba yace likita zan iya sanin wane ciwo

ne wannan? Likita yace tsirone dake fitoma mata

dai daiku. Sam abba bai fahimta ba don haka yayi

mashi sallama. Umma ce a wurin ummi tana

shan magani kafin ranar aiki inda abba

hankalinshi ya rabu biyu rabi gurin aiki rabi garin

ummi. Don ma umma ta koreshi da so yayi ya

rika kwana, addu'a kam yana yinta. Ranar da

za'ayi aiki abba hankalinshi duk tashe. Yana

zaune bakin gadon da take kwance ita kuma tana

can ana aikin. Wayar umma ce a hannunshi yana

ta danne danne, ba don nishadi ba don kawai ya

rasa me zaiyi. Dript ya shiga yana ta bin abinda

ke ciki, mamaki ya cikashi lokacin da yaga irin

text din da ummi tasha rubuta mashi don ta tura

ma abba, sai kuma ta fasa. Tamkar cikin mafarki

abba ya rika karanta sakwanin dama ummi tana

sonshi zurfin ciki ne tayi? Ya sake bude wani

rubutu cewa, Ya Abba ina sonka, ina kaunarka

duk wani motsi na numfashina kara sonka nake,

ka tausaya mun sonka zai zama ajalina, duk

ciwon da nakeyi na sonka ne. Ko na rantse ba

zanyi kaffara ba, in kaji haushin kalamaina ka

yafeni, nasan ni ba ajinka bace, amman ka daure

kace kana sona koda bada gaske bane. Gama

karanta sakon yayi dai dai da dawowa da ummi

dakin, da sauri suka nufeta idonta biyu saidai

daga gani tasha azaba. Tayi wujiga wujiga. Abba

ya kama hannunta cikin matsanancin sonta da

tausayi. Sannu suka dinga yimata, nurse tabasu

magungunan da za'a rika bata, umma kuma ta

dauki wayarta don sanar da alhaji an gama aikin.

Abba yasa bakinshi dai dai kunnenta yace ina

sonki ummi, ina matukar sonki. Duk da tana cikin

wani hali taji kalaman nasa har a tafin kafarta.

Ta bude jajayen idonta ta dubeshi, ya sakale

hannunshi cikin tafin hannunta ya hade su. Ta

girgiza kai dai dai lokacin da nurse din ta sake

shigowa tace ga kayanta, ya amsa zaninta ne da

siket da sauransu. Tace ka barta tayi bacci kafin

ta tashi zafin gurin ya ragu, kila zuwa dare a

sallame ku. Umma tace to mungode. Nurse tace

yarinyarki nada dauriya, anyi mata allurar kashe

zafi bata kama jikinta ba amman bata yimuna ihu

ba. Likita ma ya yabata da kokarie ta, Abba ya

kalli ummi cikin tausayi. Sai gurin karfe ukku ta

farka wurin kam ya dan lafa da radadin, abba ne

yaje gida ya dafo masu abinci sannan ya nufi

wurin aikin shi. Don ranar bada wuri zashi ba.

Tunda ummi ta farka take ta kokarie tunowa shin

kalaman da taji cikin mafarki ne ko kuwa ido biyu

ne? Bakwai na dare likita ya shigo ya kara duba

ummi sannan yace suna iya tafia gida. Ya basu

maganin sha sannan yace ta rika shiga ruwan

zafi da dettol. Umma ta kira abba ta fada masu

batun sallama. Yace su jirashi yana zuwa. Ummi

tace da ummansu su alhaji pha? Tace sunxo kina

bacci harda ummanku sahura.els / ZURFIN CIKI book 4 part 28

ZURFIN CIKI book 4 part 28

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:30

Bansan lokacin dana dauka ina rigimniya da sonki

danqare a zuciyata.Ummi da ban sameki ba da

tuni bana garin Kano domin lokacin yanke

shawara nayi in nemi canjin aiki zuwa wata jihar

har yau ban daina yiwa Salisu addua ba wanda

shine mutum na farko da ya soma tsegunta min

kin zama mata gareni So, Ummi baya raina

abinda yake so da nayi zaton zubar da kima ne in

furta maki kalmar so musammam in na tuna ke

baki soma, zurfin a so bashida wani amfani don

na sha wahala.Ba zan Qara boye dimbin son da

nike maki ba Ummi ko gaban wa zan nuna kina

jina matsala? Ummi wadda ke zaton mafarki take

sai taji bakinta yana furta wayyo dadi Ya Allah

kada ka farkar dani in har bacci nike Abba yace

ciji yatsanki zakiji zafi Ummi nine Abban ki mai

sonki wanda ya reneki tun kina zanen gobe.

Hawaye suka soma zubo mata cikin muryar kuka

tace Ya Abba da gaske kana sona? Nafi zaton

tausayina yasa ka furta haka, Amma koba gaske

ba ne na gode kuma naji dadi Amma ka sani Ya

Abba ina sonka mai tsanani sai tasa kuka. Yace

ummi yi shiru, in kukan takaici ne kukan ya kare.

Nima na jima ina sonki jiya naga sakonki a wayar

umma da kike rubutawa mai dauke da nuna sonki

gareni. Sai zurfin ciki ya hanaki, don allah ummi

kada ki koma zurfin ciki a sona, ki zazzage min

duk irin sonki gareni. Ummi tace yau kam ji nake

kamar a mafarki. Sun nutsa a cikin hirar so suna

ta baiwa juna labarin halin da suke shiga a baya,

a lokacin daya ganta da wani namiji yace

hankalinsa yayi mugun tashi. Sai lokacin daya

fuskanci bashir na sonta, ita kuma Tace ta tsani

koh mace ta kira layin shi, zainab kuwa data

samu labarin ta kamar ta mutu. Tace ko bishira

bata kishi kamar yarda take kishin zainab, sunyi

nisa basu san sun kwana zance ba, sai da ummi

taji kiran sallah. Tace ya abba kaji abunda naji,

yace sallah ake kira naji, kin sani kwana zance.

Ban gaji dajin muryarki ba amarya tah. Ummi

tace gari yayi saurin wayewa kaje kayi muna

godia ga allah ta hanyar nafita, yace to matata.

Hamdala ta rikayi har bacci ya dauketa, muryar

umma taji tana cewa ummi ki tashi kiyi wanka ki

gasa jikinki. Tana zaune cikin baho wanda umma

ta zuba ruwan dimi da dettol, tsohuwa ta shigo

cikin bandakin. Ummi tace don allah tsohuwa fita,

tace don allah ja can anki a fita din, ta saka

hannu cikin ruwan wankan ummi dake gefe a

bokiti. Tace ina suwaiba? Ai karo mata ruwan

zafi, wannan ruwa yaushe zata gasa jikinta, idan

da dan tawul dauko in danna mata jikin. Ummi

tace nidai tsohuwa ki barshi don allah, sai kace

wata mai jego? Tsohuwa tace tafi can kuda baku

san darajar jikinku ba. Wannan rawar kan da mai

sunan malam keyi idan ba'a gyara kiba saiki ba

sai zance ya dawo baya, idan anyi magana ku

yan zamani kuce bamu waye ba. Alhali ku

wayewarku itace kwalliya amman jiki ba'a san a

gyara ba, umma tazo ta kara mata ruwan zafi a

cikin bokiti. Tsohuwa tace yau a sawo bagaruwa

a tafasa ruwan shigar tata da ita don tayi saurin

warkewa. Kuma ko ina zai hade, in kin koma

gidanki kin kwana biyu ki dinga hada bagaruwa

da alim kina tafasa su kina shiga.IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 29

ZURFIN CIKI book 4 part 29

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:31

Umma Tace xa'asiyo tafita tabar su ummi

nacewa to tsohowa kije mana tace bantafiya sai

naga yanda xakiyi ganin ummi tabata lokaci nan

tsohuwa ta dauki tawul din tashiga nadar ruwa

tana dannama Ummi, Ummi tanacewa itadai

abata tayi da kanta. Tsohuwa tace gaddamace

daku ya'yan yau kinga duk macce dake rufe

jikinta tafita daban damasu tallar jiki. Ita macce

anfison a sameta ko yaushe da dumi a jikinta,

yawo babu takalmi ko a tsakargidane yana

ragewa mace dumi sbd sanyinda ke ratsa tafin

kafarta har ni'ima yana ragemata. Sannan zama

atantagaryar suminti shima yana rage mace, da a

ace zaku gane kunga masu saka hijabinnan da

safa? bakaramin wayo suke yimukuba. Inda za'a

banbance za a samu sunfiku ni'ima da kyau fata,

don haka sai kin dage Ummi dai tayi shiru, amma

aranta cewa take wannan tsohowa ko ina tasan

wannan duk bayanin? Filo aka ajewa Ummi ta

zauna tana karin kumallo, duk takosa taga

abbanta, koda ta tsinkayi sallamarsa tamkar

tamike ta taroshi. Amma dole yaje yagaida su

alhaji, tsohuwa tace aefa mu kuma bana munga

takanmu don nan zaka dinga likemana. Yace

dadin abundai nima nan gidan ubanane, da

uwata. Umma tana kicin tanamasu dariya. Tunda

ya zama idanunsu sunsarke da juna sun kasa ko

magana Ummi ce tayi karfin halin lumshe ido

sannan tabude tace sannu daxuwa. Tasowa yayi

ya tsugunna kusa da 'its, yajikin babyna?sunan

yamata dadi, naji sauki bari in kawomaka abun

karinka. yamika mata tafin hannunsa tasaka nata

yahadasu ya yasarke, murya kasa kasa yace

barshi na' amso. Ta kula abba mutum ne maison

wasa da tafin hannu. Ita kanta tanason hakan da

akwai wani sako da tafin hannu ke isarwa acikin

duniyar ma'abota so, kila wannan dalilin ne yasa

abba ke kashema tafin hannusa kudi da mayukan

da ke saka laushin hannu har ita mah ya

saimata. Koda umma ta shigo Ummi tayi kokarie

amshe hannunta amman abba yaki saki, kuma a

hakan ya karya. Umma kasa zaman dakin tayi

domin a baki abba yake ba Ummi abinci, umma

nafita taceels / ZURFIN CIKI book 4 part 30

ZURFIN CIKI book 4 part 30

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:33

Daren ranar duk suna kan kujera doguwa a dakin

umma ya bude mata laptop wai yana koya mata

kanta kwance a cinyarsa, umma ta shigo dakin

tsohuwa tace tsohuwa zaifi kyau mu sallami

yaran nan na gaji da ganin wannan aiki nasu ai

tasamu sauki. Tsohuwa tace suwaiba ina laifin ta

kwan goma ma, umma tace anya zasu kwan

goma nan? Gobe bakwai guda ta koma dakin ta,

tsohuwa tace shine nan. Abba yace Ummi kinfa

samu sauki ba zakizo mu koma gidan mu ba?

Tace su umma ne zasu maidani ai nima ya abba

inason in koma yace yau nan zan kwana in sunga

haka sun kuramu, Ummi tace ya abba kayi hnkr

kada ka kwana, shine yace kin yarda goma inxo

mutafi ko ba sanin su umma? Tasa dariya tace

taf inajin kunya bazan iya binka ba yace to kuwa

zan kwana a nan. Suna cikin haka umma ta leko

tace abba bazakaje gida ba yanxo fa sha biyu

saura, yace umma nima nan zan kwana. Ta rike

haba nan din lafia? Yace to umma nima ba gidan

mu bane? Ummi tace dama yafi umma kada yaje

wani abu ya rudashi, umma tace a'a abba tashi

ka tafi insha allah gobe Ummi zata koma yayi

murmushi tare da cewa nagode umma.nan dai ya

tattara yanashi yanashi ya tafi gida cike da

kewar matarshi, itama Ummi lamo tayi a gado.

Bayan umma ta gama yimata fada ta bari ta

warke taki ko, sai cewa tayi umma ni fa na

warke. Umma ta kalli Ummi cike da mamaki tace

yaran yazo saidai a barsu. Shiyasa akace idan

macce ta isa aure ayi mata a huta. Ita kam Ummi

tana ganin a barta tabi mijinta ta faranta mashi

shine abinda yafi dacewa don yanxu ba inda ya

kai mata dakinta dadi bacci. Duk da kashedin da

tsohuwa tasa abba dakinta tayi mashi na cewa

ya bar Ummi sai ta kara sati kafin yace zai

kulata da sunan auratayya, bai sa abba jin zai iya

ba. Don haka koda ta fada mashi cewa yayi kadai

da huruminki da wanda ba naki ba duk sai kin

shiga? To nidai ki lafa man haka. Ya fice a dakin.

Ita kuma tana ta fadanta tana cewa "Na shiga din

dan neman yaro, da kyar ya barta ta kara kwana

biyu ya afka mata don shi hkr sa ya kare, ta

nuna mashi ita fa tsoro take ji kada ta wahala, ya

lallasheta yace ba wani wahala. Ummi tana son

faranta ran mijinta. Don haka ta jure duk da

yarda yazo mata ba sauki, sai dai tasha albarka

kuma ta kara samun wani matsayi na

musammam a gunsa. Cikin satin ta zama yar

lelenshin kafin sati biyu ta hardace duk wani

darasi da abba yake koya mata, abba jinsa yake

kamar wannan lokacin ne ya fara rayuwar

angoncinsa. Sam ya manta yana da wata mata

uwa duniya saida Aunty ta kirashi tace lafia baya

kiran matarsa sai ga abba da girman shi ya girba

karya. Wai ya kira ya kasa samunsu Aunty ta

yanda tunda farkon tafiyarsu yana kiransu sun

gaisa da bishira tana tmbyrshi ina hibbarta? Sai

lokacin ya tuna kwana biyu bai ganta don tana

gidansu umman bashir, amman sai yace tana

lafia in yaje zai kirata taji gwarancin yar tata.

La'asar sur suka jero ita da abba don su dan

zaga kurum. Sun shigo gidan ahmad da muktar

duk basu rabu ba saida sukaji sun saba da ummi.

Don ita haka take yana da wuya kayi zaman awa

guda da ita bakaji ta kwanta maka a rai ba. Abba

yaji dadi yarda Ummi ta nuna kauna ga matan

abokanin nasa, yasan bada jimawa ba matansu

zasu zama kawaye kamar yarda yaso da bishira

amman taki. Daga can suka nufi layin su gidan

su umman bashir Ummi tace su fara shiga su

dauki muhibba abba yace bazata yarda dake ba.

Ummi tace zata yarda muje a ran abba tsoro

yake gada umman bashir ta gwasaleta Ummi, sun

sameta tana shara da sauri Ummi ta amsa ta

soma sharewa hakan ya faranta ran abba sai dai

da ya kalli umman bashir yaga tana hararar

Ummi, saida ta gama taxo ta zauna suka gaisa

abba na rike da hibba tayi kaca kaca da kunu

gashi duk ya dunkule dama ko lokacin da bishira

tana nan haka zakaga yar duk kazanta. Ummi ta

bude post dinta ta cire dari biyu guda biyu ta

mikawa umman bashir gashi umma kin sai goro

saida ta tabe baki ta amsa babu ko godia, sai dai

abba cikin jin dadi yace angode, da hibba taki

binsu Ummi tace kamal xo ka siyo wa hibba

alawa, kinga baba kamal baya nan xo muje in

sayo maki. Cikin sa'a sai taxo zasu fita sai ga

bashir dauke kai yayi tare da jan tsaki daya shiga

gidan sai ya hau umma da fada Wai ta daina

barin Ummi da wannan abba suna zuwa in ba

haka ba zasu kawo mata wani asiri. Umman

bashir tace suta zuwa ma indan ta nine mi jiya

tayi bare yau, ka gansu dari hudu yanxu ta bani

don haka bazan hana zuwa ba amma fa ina nan

yarda nake bazan canza ba, suna shiga gidan su

umma kicin ta wuce ruwan zafi ta zubu ta cude

muhibba tas, ta wanke mata kai ta chajeshi ta

shafeta da mai nan ma basu jima ba suka nufi

gida zanen umma ta ansa ta goye muhibba, shine

ya bude dakin bishira duk kayan yarinyar sun rine

da datti, Ummi dai ta zazzaba yace .ba maidata

za'ayi ba, Ummi tace ta dan kwana biyu mana.

Yace tana fitsari fa. Ummi tace kasawo muna

pampers Yace shikenan duk da ya nuna bayaso

yarinyar ta zauna gurinsu amman yaji dadi sai

lokacin bacci daya shigo ya shigo da pampers din

ta saka mata Sannan ta kwantar da ita can gefe

ta azama mata pillo guda haba guda baya, su

kuma suka kwanta a nasu makwancin suka

cigaba da soyewa. novels / ZURFIN CIKI book 4 part 31

ZURFIN CIKI book 4 part 31

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:36

Ummi tana son yara don haka hibba ta dinga

samun gata, satinta guda umman bashir ta dinga

jaraba sai an dawo da ita. Wai kwadayi ne don in

bishira tadawo ta bata tsaraba, amma koda ta

tafi da hibban yarinyar sai taqi sai kuka har dasu

amai. Dole aka dawo da ita, don alhaji karami

cewa yayi atattara mata kayanta duka inyasake

samun an maido da ita sai ya saba ma umman

bashir. Hakan da babbar sallah abba yakashe

musu kudi ita da hibba, sai dai duk abinda yasai

ma ummi to ya aje ma bishira nata. Ita kam tana

can duk addu'arta akan ummi ne, kafin ta dawo

ummi tafita, don haka data dawo da kwarin

gwuiwarta ce wa bazata samu ummi agidan ba.

La'asar sakaliya, direban gidansu ya iso da ita

gidan kamar yanda mahaifinsu ya umarce shi

cewa in ya dauko su kada yaso dasunan, ya dire

kowa agidanta. Kasancewar unguwa uku suka

soma zuwa sai anty ta taya bishira diban kaya

su shiga. Daidai kofar dakin bishiran abba na

kwance rigingine, 'yar T-shirt ajikinshi fara kar.

Dawandon jeans gajere iyaka gwuiwa. Ummi

kuma dogon wando ne irin mai kama jikin nan

dariga mai kamar singileti kanta yasha kana nan

kitso, tayi filo da kirjinshi yana bata labarin wata

mota da yake son yabada tashi yayi ciko. Ita

kuma tana ce masa ya dai je ya shawarci umma,

muhibba kuwa tana ta faman wasa da sabbin

kayan wasanta da ummi tasai mata. Ita ma cikin

'yar shimi mai kyau, kanta kuwa ummi tayi mata

kitson (3 in 1). Sororo bishira ta tsaya tana

kallonsu, sam bata tsammaci a irin addu'ar

datayi zata dawo ta samu ummi agidan ba. Basu

ganta ba saida anty tayi sallama tare da cewa, ya

naga kin tsaya? da sauri suka waiwayo duk suka

mike. Gaban ummi yayi wata muguwar faduwa,

amma duk dahaka cikin fara'a ta nufe su, bishira

ta hade rai matuqa sannan taqi ko kallon ummi

ta nufi 'yarta. Anty kam cikin fara'a suka gaisa da

ummi harta zage jakarta dake kafadarta tabawa

ummi wani dan agogo mai kyau. Nan dai ummi

tayi ta godiya shima abba ya mata godiya. Abban

ne ya shigar mata da kayan daki, ummi tana

cewa anty kin mana dawowar bazata, dakin fada

da an share miki dakin. Nan ma bata tanka ba,

ummi dai data gaji dayi mata sannu bata amsa

ba sai kurum ta nufi dakinta, zuciyarta babu dadi,

tasan yanzun ya Abba zai raba jin da yake da ita

zuwa su biyu. Bishira tayi kyam tana ta qamshi

don anty baza su barta tazauna masu da qazanta

ba, ga haqorin makka an sako ana ta qwambo.

Ranar dakinta Abba yakwana, yanda bata ga

wata rawar jiki daga gare shi ba tayi zargin ummi

tasamu lafiya. Hakan ya qara dagula mata lissafi,

tayi rabon tsarabarta daga kawayenta sai

maqota, don ko umman bashir daga zam-zam

bata qara mata komai ba. Dama tana cike da

haushin umman data bari ummi ta daukar mata

'ya gashi nan muhibba ta liqe ma ummi. Hakan

ya shaqar da umman bashir har tace amaida

mata zam-zam dinta ita bata sha. Wato don taje

makka shine zato zo ta canza hali? Ita kuma

bishira ta amsa tare da cewa, ai ba ita ta aike ni

makkan bada har sai tazabi abinda zan bata.

Ummi ko zam zam din ba abata ba, kuma ko

ajikinta. Abba kam shita kawo masa dogayen

riguna da T-shirt masu kyau, amma su anty ne

suka matsa mata sai ta saya. Ranar daya dawo

daga dakin bishira ummi tana fashin sallah gashi

yanuna yana dalarura alokacin. Sai tace ta yafe

masa yau dagobe yaje gurin anty bishira, yace

A'a tace ba haramun bane nina amince, yace

nasani. Shiba yason sai yatafi tafara damuwa ko

tazo tana jin haushinsa, tace ba komai saida

yatafin kuwa har kuka tayi don kishi. Amma

tabawa zuciyarta hakuri tasan wata rana wannan

jarumtar datayi zata zame mata alkhairi. Ita ko

bishira koda yazo mata sam bata damu ta

bincika ba, tunda taga ba girkinta ba, saima ta

hau murna yayo satar kwana ya bata musamman

dataga dayayi wanka yakoma dakin ummi, haka

washegari. Don haka sai tashiga daga hanci har

da 'yan habaice habaice, kafin tadawo tun da

dama da namiji dan uwansa yake kwana. Tana

nufin ummi bata ba tayi masa amfanin komai

wannan yasa ummi ta daura aniyar cusa mata

takaici, aranta tace tunda cinikinki labe nikuma

zansa miki hawan jini. Kamal yazo daukar abincin

da ummi ta saba sawa yau har da kunun gyada

tayi. Bishira ta kalle shi, wai kai wannan abincin

na waye kullum kake zuwa dauka? Yace na

ummarmu ne. Ta taba baki, ummar nan taku

kwadayinta yayi yawa, ko kuwa itama asirin ya

kamata ne? Kamal kuwa yaje yafada sai ga

umman bashir agidan suna zage zage da bishira,

tana ce ma bishira dadin abin gidan dana nazo

kwadayin ba gidan ubanki ba. Marowaciyar bnza

ai dama ina da cikinki, lokacin da Abba yasai

maku TV, yace ki bani naki sai ki kace gara kiyar.

Bishira tace, Eh na hana TV aiba wani shegen ya

sai minba, ubana yasai min, kuma nace mai

kwadayin yarinyar daki kace uwarta mai asiri,

menene na amsar abincinta kici banda kwadayi?

Shiyasa kika bata 'yata ashe don asami abinci

ne, umman tasa kuka ni ke ke zagi? Yau ko abba

zai zo gidan nan zai zaba ko ni ko ke. Ummi dai

tana daki tana jinsu. (aranta tace dadi na da

gobe saurin zuwa). Bishira tace dama ya darajaki

ne shine za kice haka, yazo din nace mai kwadayi

harda rainawa na baki zam zam butulu duk

abinda na miki kin manta kece kika aikeni

makkan? Umman tace, zuwa makkan naki dashi

gara babu, don nasan da kyar ne in za akarbi

wannan aikin nani ke da bakya sallah arniyar

banza qazama. Ummi harda riqe ciki don dariya,

haka dai suka yi tayi wajuna gori har dai 'yan

kallon da suka taru suka soma bda haquri,

umman bashir tayi gida cikin kuka. Tagayawa

'ya'yanta komai su bashir dasunce sai sunje sun

zaneta umman bashir din tace barta ku barta

kawai bari abban yadawo. Da dare ta ritsa shi

agidan yasha mamakin wai yau mahaifiyarshi da

bishira ne suke fada yace hakane dama duk

zamantakewar da ba'a kafata don Allha ba wata

rana sai ta rushe. Nan yayi tawa bishira fada da

cewa uwarshi sa'arta ce dazata tsaya ta dinga

gaya mata magana? Nan fa aka sake kacamewa

har abba. Yakai ga kwasa wa bishira mari,

sakamakon irin rashin kunyar data rike qugu take

tsulawa umman bashir din. Ummi ganin abin yana

tsawo ta fita taja umman bashir tana bata haquri

ta zaci zata hantare ta amma sai taji tana cewa

ba komai ummi sakayya ce tunda na nuna ina

sonta dole tamin haka. Abba yace ummi tasa

mayafi taraka umma gida, hakan ya qara qona

ran bishira gashi yanda taga Abba ya bata rai zai

iya yin komai, dole ta koma daki tana cizon yatsa

tare da tunanin mafita. Ummi kuwa ahanya sai

lallashin umman take tare dayi mata alqawarin

cewa duk abinda take so ta tambayeta zata mata

shi tarakata har gida sannan tadawo. Sabon kuka

umman bashir tazauna tanayi, takaicinta yanda

bishira ta zage ta taci mata mutunci agaban

ummi, tashare ido tare dayin ajiyar zuciya a fili

tace dani take magana. Ynzun ummi tasan kishi

fiye da baya, don ta hau turbar ma'aurata kuma

tasan muhimmancin abinda ake yiwa kishi, don

haka zatayi komai na jan hankali don ganin taja

mijinta gareta. Kuma inta lura cewa bishira ta

maqale mata aqofar daki sai tayi ta jan abba da

wasanni, don ta quntata ma me labe. Amma

hakan baisa ta daina ba, don haka ta daura

aniyai saita mata abinda zata tona kanta ha abba

yasani. Duk jumma'a abba yana dawowa gida

musamman in ranar girkin ummi ne don cin

abinci na musamman. Jumma'a biyu kenan bata

fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis

taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin

tsohuwa tazo. Don haka suna gaisawa da umma

tace gurin tsohuwa nazo. Suka shige daki tace da

tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin.

Tsohuwa tace, name ummi? Ta ce na gyaran jiki

mana. Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu

abubuwa. Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari?

Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana,

bada ina fada miki kina sharewa ba? Ummi tace

haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani

shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja

hankalin mijina. Ta ce, toda farko ki dinga kula da

jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar

iska. Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga

tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba

dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da

ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi. Sannan ki

amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga

inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan

inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga

matsa farin miski a ehem dinki. Sannan ki samu

saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari,

mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari

dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi

biyu safe da yamma. Sannan ki aya garinta,

kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa,

sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar

ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai

ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale,

citta, lemun tsami, ki markada su kisha. In anan

maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum

daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta

musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban

da dukkan sauran mata. Ki hada da biyayya

tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi. Ummi

tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin

nan? Tace, bari zanba matar ado dake yawan

zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu. Amma

su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya

siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin

ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan.

Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje

gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi

tasan duk wadannan hadin matan? Amma data

tuna cewa 'yar katsina ce sai tace ba mamaki.

Tun ranar alhamis din ta soma aiwatar da

darussan da ta debo daga tsohuwa, safiyar

jumma'a ranar zai bar dakin bishira. Ya fito tana

sharar tsakar gida ta gaidashi, ya amsa da fara'a,

tare dawani kallo mai fassarar in ba keba. Cikin

muryar data adana don shi kadai tace, ya abba

ina son in je ayi min zanen fulawa. Yace jiya kin

fita yau kam a'a. amma ki aika akira mai zanen

tazo ta miki. Ta marairaice, towa zan aika yaya

abba? Yace aike ni, ina ne gidan? Tace layin su

umma ne yace to za'azo ai miki. Bishira tafito

daga daki tazabga ma ummi harara, Tare dacewa

kisisina. Abba yakalleta, kema sai tayi miki. Tace

bana bukata, aikin banza, shikam yafice. Ummi

kuwa tace gaba da aikinta, ita ko sai tasa kujera

tazauna tana sakin zantuka, eh don kwalliyar

tabanzanta tunda ba a iya biyawa miji bukata.

Allah dai yasa ya fada min komai, to ni me zai

dame ni don 'yar aiki kawai na dauki yarinya.

Tashare min gida, tayi wa mijina abinci, daga nan

fa? Saita saki shewa, ummi ta ce aranta yau zan

bambance miki. Birabiskon shinkafa tayi da miya,

ta wadata birabiskon da kayan lambu, miyar ta

dauki nama da bushasshen kifi. Sannan ta hada

musu kunun aya yaji dabino da madara, ta

aikawa ummanta lokacin da kamal yazo daukar

na ummarsu. Tasheka wanka taci doguwar rigar

shadda koriya mai duhu, ta kafe dauri tamkar yau

ne daurin aurensu. Ga fulawar da yaje ya biya

akazo aka zana mata. Tanajin rigimar muhibba

tafito tazuba mata adan kwano tazaunar da ita

akofar falon mamanta.bishira tafito kicin baki

tasaki tana kallon ummi da tazo wucewa harda

bangazar ummi, nan ko kamshi ya bude ta na

turarukan da ummi ta fesa. Abba yana yin

sallama ummi tafito da sauri, oyoyo yayana,

bishira tana daga kicin dinta tana kallon su.

Ummi ta rungume shi, sannu dazuwa sahibina.

Ta amshi ledar hannunshi dajakar, yace yauwa

sannu babyna tace inazan kai ledar? Yace akwai

ta bishira aciki ki ciro. Ta mika mishi ledar ta

wuce dajakar dakinta. Ya mika wa bishira lemo

da abarba da yayo musu tsaraba sannan ya wuce

danasu, awulakance ta aje. Yana shiga ummi

tadan karo kofar yanda bishiran zata iya lekensu

sosai ta gefen kofan. Ta cire masa hula ta aje

akan madubi sannan ta kunna fanka. Ta shirya

masa abinci, yauni zan baka har ka qoshi. Haka

suka yita baiwa juna abaki har suka qoshi.

Yakamo hannunta mai qunshi yana ta sumbata,

wai kamar kada su goge. Kumatun shi ta shafa

nima yau kamin kyau, koda yake dama kai me

kyaune, ina sonka ya abba sosai. Cikin jin dadi

ya mannota a jikinshi, nima ina sonki, ina manta

kowa da komai in muna tare, tace ina tsoron kada

wata rana ka juya min baya. Ya saqalo

hunnuwansa cikin nata ina fata in mutu kafin

lokacin. Ummi tasomayi masa wasu irin darussa

wadanda tasan yana saurin tada sha'awarshi

nanda nan kuwa tasa shi fita hayyacinsa yakama

surutai. Ummi ta tabbata bishira tana wurin ta

labe, don haka tai murmushi ta bishi suka tafi

duniyar ma'aurata. Bishira tamkar tayi hauka sai

kawai ta fado dakin tana fadin, maciya amana,

har yanzun ba afita daga lokacin girkina ba

munafiki. Abba ya tashi sannan yaja riga yasaka,

ok dama kina labewa ne kiji sirrinmu? Da taga ya

sauko da zafin rai saita gudu dakinta. Yabita

yamata tatas, kuma ya fada mata cewa tazo ta

shiga dakin ta zauna ba labe ba, yanzun zai

komane yaci gaba daga inda ya tsaya. Tayi ta

kuka gashi ba damar zuwa gurin umman bashir

dole ta tafi gidansu. Shi kam abba shareta ya yi

kosu umma bai fadawa ba. Sabuwar soyayya ma

ya balle agidan, su ci abinci tare, wanka tare, su

fita yawonsu a qafa ko amota. In yana gurin aiki

bini- bini ya kira waya, ita kuma ko yaushe cikin

kirkirar girki da kwalliya tare da dadadan kalaman

dazata fada masa take. Duk lokacin datayi masa

zancen bishira sai ya ce, don Allah ta bar ta ta

huta, ummanshi kuwa 'yar bin qwaqqwafi sai da

tabi ta gano bishira bata nan. Don haka koda ya

shiga gaisheta sai tace kada ya yarda yaje yama

bata takardarta. Ita ko tana can uwarta tace ma

mahaifinta abba sakinta yayi, shi kuma yace to

sai tazauna tunda zaman gidan take so. Amma

su sani daga abinci sai ruwan gidanshi ya amince

tayi amfani dasu sai ko gurin kwana, amma bnda

wannan ko makilin dinshi ta taba bai yafe mata

ba, wannan hukunci yayi musu tsauri. Ko wata

bata rufa ba taji gidan ya isheta don hajiya zainu

taso maidata makaranta amma yace tagama

boko. Bishira na zaune ta zuba tagumi hajiya

zainu ta shigo dakiki tace tagumin menene kuma?

Tace, su sumayyah ne wai nace suyi ma muhibba

wanka sukace Allah yakiyaye. Wai tunda nazo

dakinsu ya lalace da kazanta, hajiya zainu tace

aiba karya suka yiba, don haka ma maida

yarinyar nan za ayi ke kuma ki koma gidan

antynku ko ki tafi abuja gidan aisha. Tace

baxanje gidan aisha ba, don itama bama shiri,

gara gidan antyn amma gsky ni abarmin 'yata

kuma fakinsan bai sakeni ba. Tace, inda ubanki

yasan ba saki bne da tuni bai kora kiba? Don

haka mubarshi haka amma batun 'ya nice zan

maidata. Ranar da ummi takira ummansu tafada

mata cewa bishirafa tuntuni tayi yaji amma Abba

yaqi zuwa, umma ta kira shi tace inya dawo gurin

aiki tana son ganinshi. To kafin yadawo ma saiga

hajiya zainu da direba tazo gidan su umma tadire

musu 'yar, sannan tashiga gidan umman bashir

tace, in kin haifi danki na halas ne ba shege ba to

kisa shi ya aiko wa 'yata saki. Umman tace zoko

kiga dan halas ne in yaso kuje ku nemi arne mara

sallah dan uwanta kazami kubashi. Nan fa zage-

zage ya tashi har su umma dasauran makota

suka shigo. Dakyar aka tura hajiya ta tafi, tace

kuma saita kira 'yan sanda anzo antafi da umman

bashir. Alhji qarami ma cewa yayi maza abba

Abba yarubuta takarda ya aika ma bishira.ZURFIN CIKI book 4 part 32

ZURFIN CIKI book 4 part 32

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:37

Shiko alhji babba da umma suka ce a'a abari

qura ta lafa sannan aje. Koda aka kwana 2 abba

kin bin alhaji yayi sai wani abokinshi alhaji

yasamu suka tafi tare. Mahaifin bishira yaji

mamaki cewa ba sakinta abba yayi ba. Kuma bai

san sun maida 'ya ba, tadai ce mishi kunzo kun

amshi 'yarku, to yanzun tunda haka ne kunga

kenan bishira da uwarta basa son takoma gidan

mijinta ko? Su alhaji suka ce eh, yace to ku sa

shi ya rubuto takardarta ku kawo min, su alhaji

sukace ba za'ayi haka ba. Yace, to kuje ku barta

zata gane gidan ubanta bananne yadace tazauna

ba. Sukai godiya suka tafi. Harta koma gidan

anty farida mahaifinsu yace tadawo nan gidanshi

badashi take takama ba? Wato ta kashe auranta

zata je ta kashe na yarta dole ta dawo, tsohuwar

dake musu aiki yace ta koma gida tahuta amma

duk wata tazo ta amshi albashinta. Sannan yace

bishira itace zata dinga wannan aikin duka ita

kadai, lamarin yayi wa bishira tsauri da yawa,

gashi ba fita duk ta rame ta lalace ga tunanin

'yarta. Muhibba kuwa tana gurin umma, ummi

ma takan daukota sannan ummi tasamu nasarar

rufe bakin umman bashir, ta hanyar yi mata

kyautuka ko me sukace sai ta aika mata. Tasa

Abba ya canja mata gado don nata ya lallace,

sannan da fati ta haihu tasa Abba ya sai mata

garar abinci, ita kuma tasa zani da rigunan yara.

Nan fa sai ga sahura babu ko kunya tana shima

ummi albarka, ko bashir ne yakawo gulmarsu

ummi sai tace ai ita bata yo halin uwarta ba.

Tafi-tafi ma in ya kawo sai tace ai su umma da

ummi sun gane kuransu. Haba sahura kodai ki

gane kuranki? Abba yasoma damun ummi da

batun ciki, wai shifa yana tsoro kada su gaji su

umma, ummi tace su dai yi addu'a sunje asibiti

ba wata matsala, likita yace in rabonsu yazo zasu

haihu. Da kyar ummi ta shawo kan Abba ya

amince ta zana (JAMB) don ci gaba da karatu,

sannan ta shiga islamiya. Abba yayi kyau yayi

kiba ya kara gogewa, haka nan ummi duk wanda

yaganta saita birge shi, daka ganta kaga wayayya

wadda mijinta yasan da ita. Taci nasarar samun

(POLY) saboda bata samu abinda take so don

zuwa (UNIVERSITY) ba, sai dai ba tasha dokoki

kafin ta fara zuwa. Bayason kawaye baya son

abokai, irin wanda wasu matan keyi sannan

yadinka mata manyan hijabai, kuma banda hawa

acaba, inya samu sarari zai dinga zuwa da kansa

yana daukarta. Sai kuma gargadi na karshe kuma

da babbar murya, in har ya daina samun kular

datake bashi ta kowane fanni wai saboda karatu,

to kuwa za adaina karatun gaba daya. Tace,

insha Allah sai abinda yai gaba. Ya canja mota,

umma tayi ta fada wai tafi son yasai fili yayi dan

gidanshi irin na zamani yace za'azo gurin

ahankali kada ki damu umma. Bishira ta sulale ta

tafi na'ibawa gidan anty da kukanta wiwi don

Allah ta taimaka mata taba Abba hakuri ya maida

ta, wlh tagane kuskurenta. Anty tace, nifa bazan

iya kiran Abba ba don kin riga kin bmu kunya, sai

dai in ke ce zaki kira shi ga waya can. Ta dauko

ta kira, shikuma ganin kiran anty sai yayi parking

yadauko ummi daga makaranta, ya daga sai yaji

muryar bishira. Cikin kuka tana cewa, don Allah

abba nice, kayi hakuri indawo dakina, wallh zan

canza, yace ok baki riga kin canza din ba, to bari

inkin canza din sai muyi magana. Yakashe haka

tayi ta kuka tagama anty tabata wasu kayan

sawanta sannan ta tafi. In lokacin labarai yayi

haka take zuwa ta tasa TV tayi ta kallonshi tana

kuka, kullum kara sonshi take gashi yayi kyau

idanunshi sun qara haske. Wata ranar jumma'a

wuraran karfe sha daya ta saci jiki tanufi gurin

aikin Abba, yana fitowa dakin daukar labarai

akace wata tana nemanshi. Baiji wani mamaki ba

don mata kanzo neman shi wasu suce suna

sonshi wasu suce ganinshi kurum zasuyi don

yana birge su. Yana zuwa sai yaga bishira, nan

take ya daure fuska tamkar bai taba dariya ba,

duk da cewa acan kasan zuciyarshi yatausaya

mata. Ta tsugunna gwuiwa 2 tana rokonsa, yace

ke tashi kada ki janyo min mutane, jeki zanzo.

Koda ta tafi cikin murna shi ko harkokinsa

yakama. Shiru-shiru tana saka rai bashi ba

alamarsa. Nan kuma tashiga daukar waya

kannanta tana kiranshi, harma yadaina dagawa.

Wataran taje tasamu ahmad tana kuka, ahmad

yace taje zai ganshi. Rannan kuwa har gida

ahmad yiyi sallama da abba yashiga rokon Abba

ya maidota. Abba yace taje taroqi mahaifiyarsa

dasu umma insun yarda shikenan. Har gida

ahmad yaje ya fada mata, bata yi sanyi ba tanufi

gurin umman bashir. Umman tana zaune da

'ya'yanta suna shan farfesun kifin da ummi ta

aiko musu dashi, tana ganin bishira ta hade rai.

Tace, lapiya? Bishira tace lpy lau umma zuwa

nayi in roqi gafararki. Tace nime kika min? Tace

don Allah dai ki yafe ni, ina son indawo dakina

Abba yace sai kin hakura, tace oho, yanzun kin

yarda ina da kima agurinsa? To bari kiji bazaki

dawo ba, mai baqar rowa kince nimai kwadayi ke

kuma mai rowa ko? To kin gani wannan ummi ce

ta dafo mana ta nuna mata kular kifi, sanda

kinanan bana cin komai bansan dana yana samu

ko baya samu ba. Yanzun abin arziki iri-iri

kidawo ki toshemana kofar samu? Tace, wlh

bazan toshe ba, umman bashir tace dukda haka

dai bazaki dawo ba. Tayi takuka sannan tafita,

har zata wuce gidan su ummanshi sai ta tuna

kada suyi mata dariya sai tace baridai ta shiga.

Kyakkyawar karba umma tayi mata suka gaisa,

tazauna umma ta kawo mata ruwa ta amsa

tasha. Muhibba tana ta tsalle tsallenta kan kujera

zuwa jikin umma, umma tace ji hibba ki gaida

mamanki, ga mamakin bishira sai yarinyar ta

kalleta tace. Umma niba wannan bace ba

momina, momina sun tafi da babana zaya kaita

makaranta. Umma tace, wannan ma ummarki ce

yarinyar taruga dakin tsohuwa tana cewa, ita ba

ummarta bace. Bishira ta bita dakallo, yarinyar

tayi bulbul gata cikin shiga mai kyau da tsafta

kanta yaji kitso da 'yan duwatsu. Saita soma

kuka tana fadin mahaifiyata ta cuce ni, umma

tace a'a kece kika cuci kanki, inbaki dauki

damuwarki kin kai mata ba yaushe zatasan anyi?

To ynzun dai dubi 'yarki tana gudunki sbd bata

sanki ba, ina amfanin wannan? Tsohuwa tace

kukan wanikeji ta shigo tana kallon bishira cikin

mamaki tace. 'yar nan kece haka? Ciwo kikayi ko

ko duniya ce ta juya miki baya? Kai jama'a dubi

yanda kika kare kikayi bikinkirin. Ita da tadukar

dakai tare da cewa bnyi ciwo ba nidai nazo ku

yafe ni, sannan ku roqa min abba ya yafe min in

dawo dakina. Yace, bazan dawo ba har sai kun

yafe min, amma naje gurin umman bashir ta kore

ni tace bazata bari in dawo ba. Kuma gidanmu

wuya nake sha, kusan rabin aikin gidan nikeyi ga

qannaina duk sun raina ni. Umma tace, yi shiru

share hawayenki bari zaki koma. Tsohuwa tace,

ke dai kin cika sa kai a uku suwaiba, gashi abin

kirki bai karbe kiba. Kina yi ana zaginki ana zagin

'yarki, bishira ta ce wlh duk na daina, yanzu na

gane kune masu sona, umma tace ba komai.

Tadaga waya ta kira alhaji ta fada masa komai

yace to yana zuwa donshi ya qosa asulhunta

yarinyar ta koma dakinta saboda darajar

tsohonta. Yana zuwa yaji komai nan ya daga

waya yakira Abba, yace yana zuwa yana hanya

ne yace to ya same su gida. Abba yana shigowa

ganin bishira yahade rai ya zauna nan dai alhaji

ya hada su yayi musu fada da nasiha, sannan

yace baya son abba yace komai komai kuma ko

sun koma gida banda tashin tashina. Bishira tayi

ta godiya alhaji babba yace su tashi ashiga gurin

umman bashir din tana ganinsu tahau cewa alhaji

dakanka? Maimakon ace in zo? Umma tace, a'a

keda zamu zo baki hakuri ai mu ya dace mu

shigo. Nai dai alhaji yayi bata hakuri tace taci

albarkacinta na hakura, amma da sharadi inta

sake maimaita halin da tayi abaya ko taje ta

takurawa ummi tofa saita tabar gidan. Bishira

cikin kuka tace ta daina insha Allahu, nan itama

umman bashir din tace dasu umma su yafe mata

sharrin shaidan ne da qaryar barayin imani wato

bokaye da 'yan tsibbu suka ce ba komai. Nan

alhaji yace da abba yakai bishira gida, ba don son

ranshi ba yadauke tazuwa gida, sam bata damu

da daure fuskarshi ba, dadi da murna fal ranta.

Yana sauke tazai wuce tace, don Allah ka yafe

min sannan ka gaida min ummi, yace zataji. Tace

to yaushe zan dawo? Yace, duk lokacin dasu

alhaji suka zo gurin dadynku. Nan yatafi, ita

kuma ta shiga gida, hajiya zainu ta tsareta wai

sai ta fadi inda taje, tunda ta kira anty tace, bata

can. Bishira tace naje ba mijina da surukaina

hakuri ne, hajiya zainu tace ni dazai maida ki ai

sai nafi kowa murna. Na gaji da zamanki da

qazantarki, tunda babanku yaqi ki koma

makaranta yakashe miki kudi ki goge ko kya

samu mai kudin dazai aure ki, to gara kin koma

can kin qarata. Abba kam shi tunaninshi ta ina

zai soma sanar da ummi dawowar bishira? Don

baya son ko kusa hankalinta yatashi, baya son

wani abu yayi musu katsalandan a cikin

daddadan zamansu, don haka ya share bai fada

mata ba. Da dare alhaji da umma suka je, an

sasanta sannan suka taho da alkawarin cewa

gobe zata dawo dakinta. Washegari umma ta kira

Abba tace ya share ma bishira daki yau zata

dawo, yace umma nifa gsky dabata hankalina yafi

kwanciya. Sannan ina ta tunanin yanda zan

tunkari ummi da wannan zancen, umma ta riqe

baki tare da rafka salati, yace ynzun tsoron

ummin ka koma ne? Yace, a'a umma kin gata

sakankance ynzun hankalinta yakwanta sai kuma

taji nazo mata da zance dawowar bishira? Tace,

shi kenan nina fada mata. Awaya ta kira ummi

tafada mata cewa bishira zata dawo, duk datasan

cewa matar mijinta ce dama, amma sai da

gabanta yafadi. Umma taja mata kunne da cewa

kada taji kada tagani, abba ranar sai kusan sha

biyu zaije gurin aiki. Don haka yace kannanshi

suje su soma fito da kayan kafin yazo sunzo sun

fada ma ummi, ita ce ta bude musu dakunan don

abba ya canza makulli bayan tafiyar bishira. Abba

ya shigo tana zaune kan kujera sai tunani take yi

na irin zaman dazasu yi in bishira tadawo.

Yazauna tare dariko hannunta, tunanin me ki ke

yi? Takalle shi, halin rayuwa nake tunani, yace

yanzun umma ta kira ni jiya sun je gidan su

bishira wai yau zata dawo. Ummi ta taba baki,

Allah yakawo ta lpy. Ya ce ni ban soba gsky. Sbd

ke ummi tadafa kirji, sbd ni? Ni ya abba, kada

kasa duniya ta zage ni, Tare fa nasameku? Yace

to ni dai kada kiga kamar da son raina, tace don

Allah ya Abba kabar zancen nan. Kaje kagyar

mata dakunanta don su kamal bazasu iya ba,

yanufi gurinsu ganin kamar ya damu yasa itama

taje tasa musu hannu don dai ya saki ranshi, sun

gyara tsaf ummi ta goge sannan ta rufe dakin.

Har magriba bishira bata ji an ce za'a maida

taba, sai ta dauki wayar kanwarta ta kira shi wai

yazo don Allah yadauketa. Tsakanin mata da miji

sai Allah, nan ya tausaya mata yace zaizo, kafin

ya isa sai daya sai mata waya irin dai ta hannun

ummi. Har cikin gidan ya shiga suka gaisa da

babanta, yayi murna sosai yayi tawa Abba

godiya, tare da ba shi hakuri yace yasan yanda ta

horu zai gata canza da yardar Allah. Yasa aka

turo ta yayi mata nasiha, sannan ya gargadeta da

cewa inhar ta bari mijinta yakawa kararta zatayi

mamakin abinda zai mata. Tace, insha Allahu

baza ta kara ba, yakawo kudi yaba Abba, da kyar

ya amsa ita kuma ya bata wasu zannuwa acikin

leda, yace su raba da abokiya zamanta. Taje tayi

wa hajiya zainu sallama suka tafi, tamkar

baquwa haka ta koma, sai kace basu taba zaman

aure da Abba ba, nauyinsa take ji. Suna tafe ya

ciro waya ya miqa mata, tasa hannu ta amsa

yace taki ce, tayi ta godiya yace ba komai.

Sallamarsu tasa gaban ummi faduwa, ta dake ta

fito ta amsa, wani kishi ya tasho mata amma

saita danne. Ta kalli bishira tare dayi mata sannu

dazuwa, ta amsa tana kallon ummi tayi kyau

tagoge daga ka ganta kaga wayayya 'yar gatan

miji. Ta dauko makullin dakin ta ba bishira, abba

kuma ya nufi dakin ummi. Bishira ta dinga kallon

yanda abba ya gyara gidan yaja gini ta gefen

ummi yayi mata falo da kicin, sannan tsakar

gidan an gyare shi da tiles. Haka bandakin su

yagyara shi, nan dai bishira ta shiga dakinta ta

zauna bakin gado tana yi wa allah godiya tare

dayi wa kanta alkawarin har abada bazata ta

kara yin yaji ko ta janyo abinda zaisa mijinta ya

sake ta ba. Ummi tana kan gado tana karanta

wani littafi yazo ya zauna bakin gadon bata ko

kalle shi ba don haushi take ji. Sai take ganin

kamar rawar kai yake yi da dawowar bishiran,

kuma tuntuni yana zuwa gurin ta ya boye mata.

Yace madam ina son in yi magana da ku ne ke da

bishira, ummi tace ina jin ka, yace can zaki zo

muje. Tace, gsky nagaji, kayi maganar da safe.

Yagama gano kishi ne ke damunta, don haka yayi

murmushi yace yanda kikace hakan za'ayi. Ya

fita kamar minti 30 yasake shigowa ya aje mata

leda tare da cewa saida safe aciki tace Allah

yabamu alheri. Yana tafiya taje ta banko kofarta,

yau kam bacci ya qi idanun ummi sbd tayi sabon

bacci a haqarqarin Abba. Dukkan filolinta ta rasa

wanda zai maye mata madadin haqarqarin

mijinta, ynzun yancan da wata tasan yanda yake

wannan rawar jikin ynzun ya manta da batunta.

Tarasa me yake mata dadi, littafin datake

karantawa kuwa sam bata fahimtar abinda ke

ciki. Hka ta dinga zubda hawaye har nisan dare,

ganin bata da wata mafita, tashi tayi ta bude kofa

lokacin 2 saura taje tayo alwala tazo ta kama

nafila. Abba jin bude kofarta ne yasa shi leqowa

ta window aranshi yaji tausayinta don yasan bata

iya bacci sai ajikinshi, ita bata san ya leqo ba

don ko hanyar dakin bata ishe ta kallo ba. Yakalli

bishira wadda bacci yayi gaba da ita ya tausaya

mata sosai yanda tayi tarawar jiki alokacin

auratayyarsu dazun. Yadauko wayarshi yarubuta

ma ummi sako. KI KWANTA KIYI BACCI BABY,

TARE DA QISIMA CEWA KINA LAFE

AMAKWANCINKI (WATO JIKINA) INA CIKE DA

KEWAR LEBUNANKI. Tana sallah taji shigowar

saqo amma bata yi ko marmarin dubawa ba, haka

tai sallah har zuwa lokacin da bacci yasoma

fizgarta. Tayi adduo'o'i sannan ta kwanta, saida

asubahi ne datayi sallah sannan ta karanta, dan

tsaki taja tare da cewa, Karya kawai, kishi yasa

ta fadin haka don tasan Abba sosai baya boye

mata komai ynzun. Sai dai abinda yasake qular

da ita da asubahin nan yanda tana fita shi kuma

ya fito wanka, duk da tasan dole wani abu yafaru

tsakaninshi damatarsa, amma sai taga tamkar da

gayya ya tsaya don tafito taganshi. Tna idar da

sallah ta dora ruwa akicin dinta, tadafa ruwan tea

taje kicin din bishira tadauko flask tazo ta wanke

ta zuba musu ruwan zafi taje kofar bishira tayi

sallama bishiran ce ta bude ummi tamiqa mata

tare da cewa an tashi lpy? Cikin sakin fuska tace,

lpy lau, nagode. Ummi ta ce ba komai takoma

dakinta ta kulle kofarta don yau bata da darasin

safe. Abba ma yau bada wuri zai fita ba, don

haka yadan samu baccin safe sai 8 yayi wanka

ya karya, sannan yanufi dakin ummi. Kofarta tana

rufe, ya kwankwasa ta share sai can dai dataji

yaqi tafiya sannan tazo tabude. Takalle shiya yi

kyau cikin kananan kaya, ta kauda kai tare da

cewa, an tashi lpy? Yace lpy lau, kin karya? Tace,

um'um sai anjima, zata rufe kofar yace,

makaranta fa? Tace sai karfe 2 nake da darasi.

Ta maida kofar ta rufe, yayi dan murmushin

takaici sannan yafita. Kwananshi 2 dakin bishira

yayi niyyar dawowa dakin ummi, don ya kosa

yadawo ya lallasheta bazai iya daukar wannan

shariyar da take mishiba. Tsakaninta da bishira

lpy lau amma shi sai tana wani share shi. part 33 the end

Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:45

Ya shigo da zumudi zai nufi dakinta, tamiqe cikin

fara'a daga wanke-wanken da take yi ta amshi

ledar hannunsa da jakar laptop ta nufi dakin

bishira. Shida bishira suka bita da kallo, ganin

zata shiga bishira tace ummi yau ai dakinki yake.

Ummi tace injiwa? Anty bishara ai kullum ke ce

dashi har sai kin rama duk kwanakin da kika

dauka agida. Kinga kenan kusan wata goma sha

daya kenan. Abba cikin sauri yace ke

mahaukaciya ce? Ina ki kasamo wannan fatawar?

Ta kalle shi, sannan tashiga dakin ta ajiye ta fito

taqara kallonshi gurin malamai, yace to ban

yarda ba, don haka zanci gaba dayi muku kwana

bibbiyunku, ummi tace to ni na yafe mata nawa

kwanakin bishira tace nagode ummi. Haushi ya

cika Abba, amma shi bazai dauki wannan horon

da ummi take shirin yi masa ba. Yadawo dakin

bishira a fili yafurta kema saina baki haushi zakiyi

dakin sanin wannan furucin. Sharewa yayi yaci

gaba da kwana dakin bishira tare da nuna kulawa

ga bishiran. Ummi ta jure duk da duk daren Allah

sai taci kuka ta gode Allah, sannan tashiga zargin

cewa shi ma ya Abban dama can yana son

tarewa dakin bishira, inba haka bame zaisa yayi

saurin yarda kuma yayi ta nuna mata soyayya?

Ganin ummi tana yi tamkar bata damu ba yasa

shi qa rajin haushi, yadawo da yamma suna

zaune kowa A qofarshi. Ummi tayi kwalliya cikin

qananan kaya, bishira kuma tana sanye da leshi,

karatun littafi bishiran keyi ita kuma ummi tana

yin gyaran qumbunanta. Bawai suna wata hira

bane amma suna kula juna sosai musamman

bishira tana son su saba da ummi. Ummin ce

bata cika son fitowa ba, bishira ta tashi ta masa

sannu dazuwa tare da amsar kayan hannunsa

don yanzun tana koyi da ummi gurin kyautatawa,

ummi ta kalle shi sannu dazuwa, ya amsa da

yauwa baby. Yakalli bishira sweety zanyi wanka,

tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai

tazo tace masa takai nan kuma yajanyo bishira

jikinshi. Ba wai yana da bukata bane, amma don

ya shaqar da ummi sai ya banko kofar, qaran

kofar ne yasa ummi kallon gurin dakin. Ta duqar

dakai taci gaba da abinda take yi, kusan minti

arba'in suka fito, Abba ya matsawa bishira wai

suyi wanka tare, tace ni bazan iya ba akwai ummi

dama da dare ne inajin kunya. Kuma kada taga

kamar cin fuska ne, yace kenan don kada ki bata

mata rai ni mijinki bazaki faranta min ba ko? Dole

ta bishi suka shiga bayi. Baqin ciki yasa ummi

tashi tashige daki, kuka sosai tayi daga nan bata

fito ba sai magriba, tanayin alwala tarufo kofa,

washegari ma qin bude qofar tayi daga alwalar

asubahi. Abba yayi ta raba ido ya ganta amma

bata fito ba, yasan fushi take, ya kira wayarta

taqi dagowa yayi mata saqo cewa in zata

makaranta tafito inkuma sai darana ta bude ta

amshi kudin mota. Tana gama karantawa tayi

wuri da wayar ba tare data bashi amsa ba, haka

ya tafi. Bishira ta qwanqwasa ma ummi ta bude

suka gaisa, tace naga baki fito bane ina fata lpy?

Tace lpy lau bacci ne, tace yau baza kije

makaranta bane? Ummi tace, zanje sai sha biyu.

Bishira tace kinji dadinki ni gashi nan ina tayi

masa zancen karatun amma ya share ni, ummi

tace inkin matsa zai yarda, tace ko za ki dan sa

min baki? Ummi ta riqe baki, ni a wa? Ke da yake

hannunki ai ke ce zai saurara, ni kin zo ne ma ki

zage ni. Bishira tace wane irin zagi? Ni dama ki

amshi mijinki ummi don gangar jikinshi ce kawai

agurina, amma ruhinsa yana gurinki. Ummi ta ce,

ngd da zagi, bishira ta ce zancan gsky ne ba

wani zagi. Haka suka yi ta rayuwa cikin kwanakin

ummi kam har rama tayi shima Abba ya rage

walwala don wanda yasan kan kula da shi

kamarta. Yayi missing din abincinta. Amma ya

gaji bazai jure ba. Ya tuna bishira tace masa zata

ta yini gidan ummanshi. Don haka yana gama

muhimman abubuwan da zai yi agurin aikin

yanufi gida. Ummi tana shirin tafiya makaranta ta

dauko jakarta sai kurum taga mutum kamar an

jeho shi. Ta daure fuska tamkar bata taba dariya

ba, yace ummi nagaji kin ji ko, na gaji da wannan

horon naki. Laifin me nayi miki? In don na dawo

da bishira ne sai in saketa, duk ba kece kika

takura min sai na dawo da ita ba? Ummi tace, ni

karka doran jakar tsaba kasa kaji su bini, ka saki

matarka sbd ni? Ba ruwana. Yace, to ki dawo

yanda kike, kuma ki janye batunki na wai kin

haqura dani, niban haqura ba. Ke ma kuma nasan

dole ki kasa kanki, ummi ta ce ni ban damu ba,

ya ce qarya ne gashi nan duk kin rame? Ya

canza daga fada zuwa lallashi, ummi don Allah

na roqeki mu koma kamar da, haba bebyna. Ya

lalubo hannunta ta qwace, don Allah ka tafi kada

bishira ta dawo ta same ka anan ta zargi wani

abu. Haushi yakamashi sosai, ya daga murya da

qarfi, kin san Allah ummi zan hadaki da umma, ta

nufi hanya fita, nikaga kada kasa ni yi latti don

lokaci yayi nisa. Ya ficiko ta ta dawo ba zaki

makarantar ba, ke an ma daina karatun tunda yafi

ni. Ta zubar da jakar da hijabi ta nufi gado shi

kuma ya fita cikin zafin rai, gidan su umma yaje.

Bishira tana dakin umma tana sallah yabi umma

kicin, umma gurinki nazo, ta dube shi lafiya

Abba? Ya turo baki, alamun ranshi bace baki,

yace umma ki sallami bishira, tace kamar yaya?

Yace taje can gidan ko muyi maganar agabanta?

Tace, kyale ta muje dakin babanku. Abba ya fada

ma umma komai da ummi ke masa, tun dawowar

bishira ran umma ya baci tace ka barni da ita.

Banda shashancin ta da ita kadai take son

azauna? Baga bishirar nan ba gidan nan ta gane

kuskurenta ko yau yarinyar nan sai da tace in

yafe ta nace ni dama ban riqe ta da wani abu ba.

Shine ita zata qirqiro fitina? Yace, umma ai ba da

bishira take yi ba dani take yi, tace to zata gane

kurenta da dare kuzo kai da ita. Umma ce ta kira

ta awaya tace tazo ita da abba, jikinta ya mutu

don tasan qararta aka kai, tana idar da sallar

isha'i taje gidan. Can tasamu abba, nan ko umma

ta rufe tada fada, koda tsohuwa ta jiyo tazo

umma tafada mata komai sai ta shiga fada. Wai

ai kishi halas ne, ke suwaiba tsakani ga Allah ko

ke bazaki so kishiya ba, bare ita yarinya. Abba

yace to gata nan ita ce fata dame ne nida batun

in dawo da bishirar, yanzun na dawo da ita kuma

ni abin ya qare akaina? Nan fa umma tayi mata

tatas, ta kuma sata anan ta ba Abba Haquri, aka

kira shi awaya ya fita. Umma ta samu dama

taqara yi mata nasiha da cewa, in bnda shirmenki

yaushe zaki bar ladanki, hanyar aljannarki kice

kinyi fushi da ita kin barwa kishiya? To kada in

sake jin haka, ki riqe darajarki da mijinki, ke

ganinki da ita. Ta jima tana bata shawara kafin

Abba yadawo suka nufi gida. Ya shiga gurin

Bishira ya fada mata cewa yau gurin ummi zai

kwana, nan ya bar ta da kewa yanufi gurin ummi,

tamkar yaune daren farkonsu hara sukai rayuwa

aranar. ** ** ** ** Kwanci tashi asarar mai rai,

shekara ta zagayo lokacin bishira da tsohon ciki,

Abba nason yara don muhibba taqi dawowa tafi

son umma dole suka haqura suka bar mata. Ta

haifi 'yarta budurwa tubarkalla ranar suna ta ci

sunan sahura inda suka sa mata walida. Ummi

nason yara, don haka in tana gida to tana manne

da walida, Abba yana damuwa da rashin samun

cikin ummi, wanda ita ummin ta barma Allah

komai. Shekaru uku sun sake biyo baya, lokacin

Bishira ta sake haihuwar habiba takwara Abba

yayi wa ummi. Tsohuwa an qara tsufa, 'yan

rigingimu sun qaru tace ita Abba yama takwara

amma bata son ya duke ta irin yanda yayi wa

ummi. Abba kullum qara son ummi yake, umma

ta matsa masa sai da yayi qoqari ya sai fili rabin

filoti tace kuma a rage ciye ciyen dadin nan agina

shì. Haka kuwa ya gina flat mai daki hudu, daya

ummi daya bishira, sai nashi sannan na yara.

Yayi qoqari gurin gyaran falon ita kuma ummi ya

canza mata kayan daki don bishira an canza

mata daza su tashi agidan su. Yace tabishi bashi

in ya samu zai bata kudi amadadin kayan daya

saima ummi, tace ta yafe. Ummi dake karantar

(BUSSINESS) har ta hada (H.N.D) dinta kuma

tayi bautar qasa. Abba dai yace baza'ayi aiki ba

amma ya yarda tayi kasuwanci, Alhaji babba ne

ya bata jari inda take saro kaya zannuwa, lesuna,

takalma zuwa jakunkuna. Abin ya amsheta don

har kayan aure tana hadawa, tana yin saqo irin

su kwatano da chaina, india, pakistan ko dubai,

ta hanyar wani wan kawarta. Haka kawai ummi

ta samu kanta da zaban abinci, yawan bacci

kasala da dai sauransu, sam bata san

takamaiman lokacin al'adarta ba. Don bata wani

lissafi in yazo shi kenan in bai zo ba bata damu

ba tama cire ranta daga batun ciki. Abba ya kalli

nonuwanta, baby kwanan nan kirjinki ya cika

sosai, gashi kinyi haske ko kin canza mai ne?

Tace yaya yaushe kazama likita? Yace, ummi kin

fa canza shirya muje asibiti, ta ce ya Abba don

Allah ka bar ni nagaji dazuwa asibiti. Yace, to ni

zan je inya tambaya game da yanda ki ka canza.

Cikin jin haushi tace sai ka dawo. Ga yara

atsakar gida sun ishe mu, yace ni naki nake

qawar in gani nasan addu'ar da nike yi bazata

fadi kara banza ba, sannan ga qoqarin danake yi,

shiru ta masa. Dagaske yake yi yaje yayi wa likita

bayani, yace yadai kawo fitsarinta. Sai da suka yi

tsiya da qyar bishira ta lallasheta ta yarda ta

bada fitsarin. Rungume likitan yaya lokacin da

yake fada masa ciki ne in dai har fitsarinta ne.

Afalo gaban bishira da yara abba ya rungume

ummi yana murna, ji tayi tamkar tsokana amma

ganin ya zauna yana ta buga waya yanata

yadawa ta amince cewa gske ne. Don haka ta

tashi ta shiga dakinta tayi alwala tazo tayi nafila

raka'a 2 cikin kuku take godewa Allah tare da

addu'ar ya raba lpy. Ya bata mai albarka.

Tsohuwa ma kuka ta saka lokacin da labarin ya

riske su. Ummi taga gata musamman daya

kasance cikin yazo da kumburi tayi sumtum. Duk

kowa ya tsorata sbd tunanin ko hawan jininta ne

ya tashi. ALLAH cikin Ikonshi data tashi haihuwa

saita santalo danta cikin gajeriyar nakuda, sak da

abba kwabo da kwabo. Rungume ummi abba yayi

don murna, sunan alhaji babba ya sake maida wa

kuma walid din dai suke kiranshi. Watan yaron

bakwai ummi ta sake rasa kanta, kuka wiwi ta

dinga yi shiko abba murna kamar yayi rawa.

Tasake samun da namiji inda yaci sunan alhaji

karami suka sa masa hibban. Haka suka ci gaba

da rayuwa cikin haquri da juna, tsakanin bishira

da ummi, bama irin bishira saboda abba baya iya

boye son ummi. Kan 'ya'yansu ahade ba kya

gane bambanci, bishira ta gane umma uwa ce

guda har da rabi, don haka hatta shawara saitaje

gurin umma kuma ko sabani suka samu da abba

gurin umma take zuwa. Ita kuma umma ta dauke

ta babu bambanci da ummi, don bata taba fada

ma ummi sirrin bishira ba. Sahura yanzun ta

yarda umma da alhaji sune rufin asirinsu, kuma

gatan Abba, bashi ma da yayi aure gidan dasu

ummi suka tashi nan ya zauna. Dangin bishira

yanzun sunga bishira ta samu natsuwa sun

sulhunta. Abba agurin aikinshi yana ta samun ci

gaba, lamuran sai godiya. Ummi tashafa addu'ar

da takeyi sannan tamiqe tana linke dardumar tace

kallon me ka ishe ni dashi ne ya Abba, yace ina

kallo ne na kusan samun da na uku wannan

karon takwara zan ma kaina. Ummi ta jefa masa

dardumar hannunta, daina min fata ni, yace ban

karanci likitanci ba amma ni likitanki ne. Ta fada

kanshi, ya rike fuskarta yana kallonta cikin ido,

ummi lokuta da yawa ina zama inta tuna da,

musamman in na kalli 'yan yaranmu wadanda

suke matuqar kama dani, tace me kafi tunawa a

baya? Yace, yanda kikayi ta kirana awaya kina

tsara ni suhaylan kaduna. Suka sa dariya. Ni kam

nafi tuna yanda ni da kai muka yi ta 'ZURFIN

CIKI' dason juna. Yace Allah yabarni da ke har

abada matata. Ta kwantar da kanta

amakwancinta ''Amin mijina''. Muma Allah ya bar

mu da masoyanmu har gidan aljanna, ya bamu

lafiya dazama lafiya. Ya zaunar mana da 'yan

uwanmu lafiya, Amin ya rabbi. ** ** ** ** Bayan

shekara goma naje nasamu yaya Abba nace

inason muhibba yace badamuwa yabani kyautar

gida da mota. Ummi kuma ta hada mun kayan

lefe saboda namijin kokarin danayi na rubuto

maku wannan littafin aka daura mana aure da

muhibbata muka tare muka cigaba da soyayya

fiye dasu ummi ma.



Post a Comment

0 Comments