[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
*Aunty Rukie*(Mmn Abduljalal.
♣♣♣
بسم الله الرحمان الرحيم
*Godiya ta tabbata ga Allah (S. W. T.) da ya bani ikon Fara wnn nvl ZUMUNTAR ZAMANI, cikin koshin lafiya. Alhamdulillah.*
*I want to use this opportunity to convey my gratitude to all those that congratulate me for the successful completion of my novel Gamon jini, most especially.*
*Halima Auwal.*
*Maryam A. I Gital.*
*Lubabatu kyauta.*
*Teemerhlurv.*
*Khairat Up.*
*Ummu D'alhat.*
*Amatallah.*
Dama sauran wad'anda ban ambata ba kuna da yawa, Allah ya bar zumunci.
*1*.
Kuka take rusawa mai tab'a zuciyar duk wani mai sauraronta ,babu kuma alaman tayi niyan tsagaitashi, dan abinda yake damunta, yake ci mata rai yayi zafin da a ganinta idan ba kukan tayi ba baza ta samu sassaucin damuwarta ba.
Kawunta dake zaune bisa kujeran palourn ya zuba mata ido cikin k'unar zuciya da matsanancin b'acin rai, wannan Kuka da take yi ba k'aramin tab'a mishi zuciya yake yi ba.
Ji yake inama da zai iya magance mata damuwarta da yayi ko da kuwa shi zai zame masa damuwa. Yanzu babbar matsalar shi bai wuci rashin sanar dashi takamemmen damuwarta ba.
Cikin dak'ushewar murya wanda yake ji kamar Shima yasa kukan yace "Rumaisa, Kiyi wa Allah ki fad'a min damuwar ki, kukan ki yana d'agan hankali ,ki taimakeni ki fad'an damuwarki ko Zan samu kwanciyar hankali. "
Volume na kukanta ta k'ara har tana shid'ewa ta kuma dad'a dukunkune kanta cikin katon hijabin da ke jikinta.
Cikin k'arin b'acin rai kawunnata ya dunkule hanunshi ya naushi kujera "Bull shit,"yace cikin karaji, Rumaisa Kiyi magana mana. "
D'ago kanta tayi da niyyar yi mishi magana wani kukan ya sake sarke ta tayi saurin mai da kanta.
Tasowa yayi daga kujeran yazo ya durkusa a gabanta, cikin sassauta murya yace "Maisa, kasheni kike son yi ko? "
Kai ta girgiza alamun A'a.
"To, Kiyi magana, fad'a min damurki Maisan Kawu. "
Ya k'arashe maganar da rarrashi.
Cikin cin zuciya da sarkewar murya tace," Kawu, Bobbo zai kasheni ,bazan iya ba na gaji ,wahalar ta min yawa kasheni yake son yi, bazan iya ba, bazan iya ba, na gaji Kawu, na....... " Tana fad'a tana jujjuya kanta.
Numfashinta ne taji kamar zai d'auke ta yanke maganar taci gaba da shessheka.
"Me KABIRUn yake miki, Maisa, fad'a min me ya ke miki. "cikin tashin hankali da tafasar zuciya yake magana idanunshi sun rine da b'acin rai.
Ci gaba yayi da cewa "Maisa fad'amin abinda ya ke miki Wlh zan kashe aurennan, dole zan karb'a miki takardarki. "
Maganarshi ta k'arshe tayi dadai da shigowar Kabeer, palourn idonshi a kansu.
Wani irin bugawa zuciyar Kabeer takeyi kamar ta fito, Kallon tsana ya bisu dashi dukansu biyu kafin ya yi hanyar d'akinshi.
"Kabiru! Kabiru!! kabiru!!!
Duk Wannan kira da yake jera mishi cikin b'acin rai da zafin zuciya baisa ya juyo ba shigewa d'akinshi yayi ya rufo k'ofa.
Bishi ya farayi Rumaisa tayi saurin tare shi "Kawu ka kyale shi zuciyarshi ba kyau kar Kuyi b'atacciya dashi. "
"Zuciya? Waye bashi da shi, muyi abinda yafi b'atacciya ma in yaga dama, ba fa Zan kyale shi ba, Wlh akanki Zan iya aikata komai Maisa. "
Ya na gama fad'ar haka ya tasamma d'akin Kabeer. Kwankwasawa ya shigayi yana kiranshi, idan ya amsa dutse ma ya amsa.
K'arshe ya shiga jijjiga kofar har ya gaji dan kanshi ya koma ya zauna yana huci yana surutai "Zaka fito ka sameni anan dan ubanka, ni ba sa'anka bane, badai kace kai d'an iska ba, Zan gwada maka kalar tawa iskancin. "
ita dai Rumaisa ganin abin yana neman yafi karfinta ta shige d'akinta ta takure gu d'aya.
Saida Kabeer ya gama duk abinda zaiyi tukun ya fito, ga mamakinshi sai yaga Kawu bai tafi ba yana zaune.
D'auke kanshi ya yi ya wuce zai fita, cikin zafin nama Kawu ya sha gabanshi ya rike kwalar rigar shi.
Kallo Kallo suka shiga yiwa juna cikin tsantsan tsanar juna.
kawu ne ya fara magana "Wato ga d'an iska ko, ina maka magana, Kayi wucewar ka, yanzu kuma kazo ka d'auke kai kamar bakasan da mutum a nan ba, wai kabiru me kakeji dashi ne? Ko Ubanka bai tab'a min rashin mutunci haka ba balle kai. "
Sai a snn Kabeer yayi magana "Shi dama mai mutunci ne, rashin mutunci kuma a wurinka na d'auko."
Fizge jikinshi yayi da karfi daga rikon da Kawu ya mishi yana cewa "Mind u, kada Ka sake yi min irin wnn abin, ko baka ga wanka nayi yanzu ba kake son b'ata min jiki da datti. "
Yana gama fad'an haka yayi waje da sassarfa ya bar kawu nan tsaye yana huci.
Motarshi ya shiga ya bata wuta.
Shiko kawu Kwafa yayi yace "Sai na raba aurennan dan Ubanka daga nan yasa kai Shima ya fita...
*Toh 🤔wai me yasa Kawun yake son kashe auren Maisan shi?*
*Me Kabeer yayiwa Maisa me zafinnan.?*
*Me yasa kuma yake cutar da ita?*
*Snn me yasa ya ciwa kawu mutunci?*
*Wnn amsa sai 'yar mutan Jalingo. Ku biyo Mmn Nuraini kusha labari.*
*Luv u all*😍😍😍
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
*Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Allah ya k'ara miki lafiya swt sis, Halima Auwal (Mmn Aisha.)*
*2*.
Gaba d'aya ya rasa yadda zaiyi Tunani yake wani irin mataki ya Kamata ya d'auka akan Kabeer, gida ya koma ya shige d'akinshi ya kwanta duk maganar da yaran shi da matarsa ke masa babu wanda ya kula cikinsu.
Kwanciya yayi, yayi pillow da hannayenshi, yana tunanin hanyar da zaibi ya raba auren Kabeer da Rumaisa.
Fitan kawu ba da jimawa ba Kabeer ya dawo gida, direct d'akin Rumaisa ya shiga, kwance ya sameta tayi rub da ciki ta kifa kanta a kan pillow.
kare mata Kallo ya tsaya yi daga k'ofar d'akin, wando ne dogo bak'i ta saka ya Matse ta sosae kamar zai fashe, rigar jikinta kalar pink ce mai doguwar hanu, ta d'an nad'e hanun rigar , rigar ta kama ta dam ,bak'in dogon gashinta d'aure da pink ribbon, sai kyalli gashin yakeyi. Tayi kyau iya kyau, duk inda kake neman kyakkyawar mace mai cikar halitta Rumaisa ta had'a.
Bakinshi ya hura ya fesar da iska, cikin taku Irinna zaratan maza ya taka ta isa gaban gadon.
D'ago ta yayi ta hanyar Jan wuyar rigarta ta baya ya finciketa da k'arfin da ya sata mugun razana.
Kuka ta fara, tana rokanshi yayi hakuri, saida ya sharara mata Lafiyayyun Mari guda biyu snn ya sake ta ya fara zare belt .
Cikin b'arin jiki ta durkusa a gabanshi, ta kama kafafunshi"Bobbo dan Allah Kayi min rai kada ka dakeni bani da lafiya Wlh. "
Ball yayi da ita wanda yayi sanadiyyar kifuwanta, tsugunawa yayi ya d'ago ta, cikin husky voice d'inshi yace "Ban hana ki saka wad'annan kaya a gidannan ba,? kuma uban me Bappa yazo yi min a gida, ehh?"
Rikon da ya mata da yadda yake bud'e mata ido ya hanata magana.
"Ba dake nake ba? Munafuka, sai zura ido take kamar mayya. Wato ke taurin kai ko? bakya jin magana ko? Yau Zan yi maganin rashin jinki a gidannan munafukai marasa mutunci. "ya fad'a cikin zafin rai.
"Bobbo Kayi hakuri bazan sake ba. "
Maganar da tayi ya k'ara harzuka shi tuni ya fara labta mata belt d'in hannun shi, tun tana kokarin Kaucewa har abin ya gagareta, Dakyar ihunta yake fita dan kukan da tasha, dukanta yake har suka fito palour, daga k'arshe ya takarkare yayi ball da ita wanda yayi sanadiyyar d'aukewar numfashinta.
Dadai shigowar yayarsa wacce yake bin mai bimata.
Cak ta tsaya tana binshi da Kallo ganin yadda ya ke huci idonnan jazur ga kuma belt a hanunshi.
Maida kallonta tayi kan Rumaisa'un dake kwance kamar ba rai a jikinta.
"Subhanallah, me Zan gani yau ni Binta. "Ta fad'a cikin rawar murya tana dafe kirji tare da durkusawa kan Rumaisa.
Tab'a ta tayi tana kiran sunanta amma shiru ba amsa.
Kallonshi tayi taga ya juya ya kama hanyar d'akinshi, da gudu ta isa wajen shi ta kama shi tana jijjiga shi "Ka kasheta Kabeer, ka kasheta ka huta, Wannan wani irin rashin imani ne? Ashe abinda ake fad'a min akanka gaskiyane? me yarinyar nan ta maka da ta cancanci Wannan hukunci daga gareka, Kabeer baka da imani. "ta fad'a tana matsanancin Kuka.
"Sakeni Adda Binta. "
Abinda yace kenan yana mata kallon banza.
Sakin baki tayi tana kallonshi, kamar kuma an mintsineta cikin azama ta damki kwalar rigar shi "Ashe baka mutunci Kabeer, ka kashe 'yar mutane kuma ko damuwa bakayi ba. "
"Sakar min riga. " Ya kuma cewa a dake.
"Bazan sake ba Kabeer dakeni sai in tabbatar baka da mutunci.
D'aga hanunshi yayi kamar zai shak'eta sai kuma ya fasa ya sa hannunshi ya cire nata hanun daga rikon da taiwa wuyar rigarshi.
Cike da takaici ta koma gun Rumaisa da yashe har yanzu babu alamun numfashi tare da ita.
A guje ta fita daga gidan cikin tashin hankali taje ta taro mai adaidaita, har cikin gidan suka shigo.
Jin tsayuwan napep cikin gidan shi yasashi fitowa daga d'aki, yana shiga falo Suna shigowa tare da mai napep cikin falon.
Hannayen shi ya hard'e a jikinshi ya tsaya yana kallon abinda zasu yi.
"Gata nan. "Cewar Adda binta tana nuna Rumaisa tare da nufar wajenta.
Biyo bayanta mai Napep d'in yayi tana cewa "Taimaka min mu d'agata ."
Duk'awa yayi dan taimaka mata yaji wata gigitaciyar tsawar da ta razanashi "Zan Karya kazamin hanunka idan ka tab'amin mata ."
Ai da sauri mai napep yayi waje yaja napep d'inshi a 360.yana jinjina rashin imani Irinna Kabeer, wai kuma har matarshi yake cewa ko kunya babu.
Haushi, takaici, bakin ciki suka had'u suka cika zuciyar Adda Binta.
Ruwan sanyi ta d'ebo tazo ta yayyafa mata, sai da ta d'au lokaci tana shafa mata ruwan sanyin snn ta farfad'o.
Yana ganin ta farfad'o ya koma d'akinshi ya banko k'ofa zuciyarshi na tafasa.
"Adda binta ki raba ni da gidannan, Bobbo zai kasheni. "tace tana fashewa da kuka.
"Shhh , yi shiru abinki Rumaisa, yanzu kuwa zaki bar mishi gidan. D'an iskan yaro kawai. "
Hijabinta taje ta d'auko mata, basu tsaya d'aukan wasu kaya ba taja hanunta suka fice daga gidan..........
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
*Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Dedicated to my besties.
*Maryam Mazad.*
$
*Lubabatu kyauta.*
*3*.
Jin shirun yayi yawa yasa shi fitowa palourn, duk a tunanin Suna cikin d'akine, yafi awa a zaune a falon da sunan Kallo yakeyi amma hankalinshi na gun d'akin.
A hankali ya je ya tsaya a jikin kofar bedroom d'in, ya jima yana tsaye, tsit yaji kamar ba mutane a gidan in ba T. V da yake karad'i ba babu alamun motsin wani a gidan.
D'aure fiska yayi ya tura k'ofa ya shiga d'akin cikin dakewa.
Ga mamakinshi babu kowa ciki sai wayarta dake kan gado kusa da pillow.
A sanyaye yasa hanu ya d'auka ya shiga bincike a wayar, Kwafa yayi ya cire sim card ya kakkarya, yana fadin "Sai Inga ta inda zaku rika communicating, 'yan iska kawai. "
Fita yayi da wayar snn ya fara duba ko ina a gidan ya kuma tabbatar bata nan.
Hannunshi na dama ya d'ora a lips d'inshi yana karkad'a Yatsunshi biyu, d'ayan hanun kuma ya rike kugunshi dashi. "Wato Adda binta tafiya tayi da yarinyar nan ko. ?Xanyi maganin ku dukanku."
Ya fad'a yana ciza leb'enshi na kasa.
Cikin sauri ya shige d'akinshi ya d'auki car key ya fice daga gidan bayan ya kulle ko ina.
Kofar gidan Adda Binta yayi parking, ya fito fiskannan a murtuk'e da ka ganshi kasan no mutunci .
Sallamar ma saboda sanin muhimmancin ta yasa shi yinta .daga ciki aka amsa mishi sallamar, kafin ya shiga.
K'ananan yaran Adda binta ya samu a gidan, babbar cikinsu bata wuci 11 yrs ba.
Oyoyo Uncle Doctor, yaran suke cewa suka nufo shi da gudu, k'aramin ciknsu d'an 3yrs ya d'aga sama, yayi pecking fore head nashi, snn ya kamo hanun D'ayar mai 5yrs yana tambayarsu Ina Maminsu.
"Sun tafi asibiti "Yaran suka had'a baki wajen fad'a.
"Waye ba lafiya. "ya tambaya yana kallon babbar ciknsu.
"Pendo Maisa ce Mami takai asibiti ."
"Kuma tana ta Kuka. "cewar 'yar 5yrs d'in.
Basarwa yayi kamar baijiba, ya ce, "wani asibiti sukaje?"
"Bata fad'a mana asibitinba tace mu zauna mu jirata Zata kai pendonmu asibiti ."
"Ina Umaimatu? "
"Tare suka tafi asibitin "
Sauk'e yaron yayi yace "Mu'allim, bari inje in dawo ko. "
Kai yaron ya gyad'a mishi yana tsotsar babban yatsar shi.
Federal Medical Center ya fara zuwa, duk zagayenshi baiga alamunsu ba, ya koma specialist hospital nanma basa nan.
"Toh ina suke? "
Ya tambayi kanshi bayan ya daidaita zaman shi cikin mota.
Wayar shi ya ciro yayi dialing no. Adda binta.
Da mamaki take kallon sunanshi da yake yawo kan screen d'in wayarta.
"Ko me d'an rainin hankalinnan zaice min yake kirana?"
Ta tambayi kanta.
Tab'e baki tayi ta d'aga wayar a zuciyarta tana cewa.
"bari dai inji kalar rashin Kunyar da zai min yanzu kuma.
"Meye kuma? " tace mishi tana yatsina fiska kamar yana ganinta.
"Ina kuke? " ya ce mata.
"Ban sani ba. "
Sassauta murya yayi, "wani asibiti kuke Adda binta?"
"Bazan fad'a ba sai naji shak'a. "
"Addana fad'a mukeyi ne? "ya fad'a yana dad'a sassauta murya.
"Ban sani ba ubana."ta fad'a a kufule.
Murmushi yayi mai sauti snn yace "Ina ce dai ba barin garin kikayi ba, I must find u where ever you are. "
Tsaki ta ja tace "Kanka ake ji. "
Kit ta kashe wayar.
Bin wayar yayi da Kallo yana tunanin ta ina zai fara, Gate way, city clinic, Doctor Aisha, khairan ko kuma Umma.
K'arshe ya yanke shawarar fara zuwa Umma clinc.
Yana parking ya hango 'yarta babba tana shiga cikin asibitin da flask a hanunta.
"Umaima. "Ya kwala mata kira bayan ya fito daga cikin mota .
Waige waige ta fara yi har ta hango shi, wajen shi ta kama zuwa Shima yana tahowa suka had'e a bakin gate na asibitin.
Gaisheshi tayi cikin girmamawa ya amsa tare da ce mata "Muje. "
Tana gaba yana binta a baya har suka shiga d'akin da aka kwantar da Rumaisa.
Idonshi akanta har suka isa gurin da take kwance.
Idonta biyu amma jin Kamshin turarenshi ya sa zuciyarta tsinkewa a take kuma ta rufe idonta kamar mai bacci. Duk da bata da tabbacin ko shine hakan bai sa ta bud'e idonta ba, gudun kada ta ganewa kanta masifa duk da kuwa tana son bud'ewan.
Kallonta ya tsaya yi nad'an lokaci snn ya nemi guri ya zauna ya fiddo wayar shi ya fara dannawa.
Adda binta da ta shigo yanzu da Ledar magani a hanunta da bag na pure water, ta bishi da kallon mamaki, saida ta ajiye pure water n snn ta sake kallonshi, taga ko d'agowa baiyiba balle ma ya nuna yasan tana wajen.
Dogon tsaki ta ja amma gogan ko ya d'ago ya kalleta, tsakin ta kuma yi snn tace.
"Me ya kawoka nan Kabeer. "
Ta fad'a tana harararshi kamar idanunta zasu fad'o k'asa.........
*A dad'e anayi sai gaskiya, Allah ya bar minke sistona Haleema Auwal (Mmn Ayshat) . 😍😘😍*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*4*.
Ci gaba yayi da danne dannenshi ko d'agowa baiyi ba.
"Kabeer tambayar ka nake me ya kawoka nan " ta fad'a a fusace.
Sai a lokacin ya d'ago ya kalleta "Kin dawo ne? "
Abunda yace mata kenan.
Shiru tayi kamar bata jishi ba.
Ganin a Kule take ya yi niyar kara Kular da ita "Ina kika je ne kika barta ita d'aya ."
Wayyo takaici kamar ya kashe Adda binta. Taso tayi shiru ta kyale shi sai kuma abun ya faskara, jin zuciyarta take kamar yana mata ciwo.
Harara ta zabga mishi tace "Inda ka Aikeni Marar mutunci. "
Murmushinsa mai kyau yayi har fararen hakoranshi masu d'auke da wushirya suka bayyana.
"Ya mai jikin?" ya sake cewa yana kallonta.
Banza tayi mishi kamar bata jinshi, ta nemi guri ta zauna.
Cikin nitsuwa ya Mike ya Iso kusa da Rumaisa, sunkuyowa yayi dadai fiskarta har tana jin hucin numfashinsa.
Bugawar zuciyarta ne ya k'aru lokacin da ya Kai hanunshi kan wuyanta, da gan gan ya maida hanunshi dadai inda zuciyarta yake ya tab'a, shi kanshi saida yaji wani iri jin yadda hrt d'inta yake bugawa da sauri kuma d'a ka'rfi.
Kallon ta ya tsaya yi yana nazarinta, tabbas ya gane ba bacci take ba, likimo kawai tayi kuma ya sani dan shi tayi hakan.
Tausayin ta ya kama shi da ya tuna dukan da ya mata, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, yayi shiru , can kamar ya tuna wani abu, lokaci d'aya ya had'e fiska, tare da yin Kwafa ya koma wajen zaman shi ya ci gaba da pressing phone d'inshi.
Har akayi Kiran sallar maghrib, babu wanda ya sake magana a cikinsu .
Tashi yayi ya fita dan zuwa masallaci, yana fita Rumaisa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sai da Adda binta ta kalleta.
"Ya dai? "
Adda binta ta tambaya.
"Ba komai."
Tace tana mikewa a hankali.
Kwafa Adda binta tayi snn tace "Wannan fitinannen ya zo ya takura ki ko? Mtss, ni rasa gane abin da ya maida Kabeer haka Wlh, har tsoro ya fara bani, yaro kamar mai shaye shaye."
"Hmmm. " kawai Rumaisa ta iya cewa, dan gani take kamar idan ta tofa wani abu ma zai iya jiyota.
Sallar maghrib sukayi, Rumaisa tayi saurin komawa bakin gado ta zauna ko addu'ar kirki batayi ba.
Jin muryarshi tayi yana magana, da alamu waya yakeyi, da sauri ta koma ta kwanta ta lullub'e kanta.
Har ya shigo ya zauna bai gama wayar ba, ya dauki lokaci yana wayar kafin ya kashe ya maida dubanshi kan Adda binta dake zaune bisa sallaya Tana lazimi.
""Ita Wannan bata sallah ne? ko dai arniya takeso ta koma ne? "
Banza Adda binta tayi mishi, kallonta ya yi na d'an lokaci snn ya mayar da dubanshi kan Rumaisa.
"Ke, " yace cikin kakkausar murya.
Jin tayi shiru yasa shi cewa.
"Idan kika bari na same ki a gun zaki gane kiranki, nasan ba bacci kike yi ba munafuka kawai. "
Wuff ta tashi tana murza idanu "Nayi sallah fa Bobbo "
Ta fad'a har muryarta na rawa dan tsoro.
"Yaushe kenan. "
Yace tare da kafe ta da idanunshi masu razanata.
K'asa tayi da Kai "Kafin ka shigo nayi. "
"Shine kuma har kika kwanta ko Addu'a baki yi ba tsabar lalaci, ba abinda kika iya sai Kwanciya. "
Adda binta ce ta katse shi da cewa "wai Kabeer Lafiyarka kuwa, da, kullum sai ke yi mata sallar ko ko kabarinku d'aya ne, kai d'in me ya hana ka tsayawa Kayi addu'ar zaka wani ce batayi addu'a ba. "
"Bafa dake nake ba Addana da matata nake magana. "
Shiru tayi tana kallonshi a ranta take cewa "Anya ko Kabeer bai fara shaye shaye ba. "
Katse mata tunaninta yayi da cewa "Ba zaku ci abinci bane? "
"Cikinka ko namu? "
Ta bashi amsa.
"Bafa ke bace damuwata, Maisa ce damuwata, ina ruwana da cikinki idan mijinki ya damu yazo ya tambayeki mana. "
Bata San lokacin da "Ikon Allah "Ya sub'uce a bakinta ba.
Itako Rumaisa mamaki ne ya cikata har ta fara tunanin anya maganar Adda binta ba gaskiya bace. Ko dai da abinda ya shawo.
Satan kallonshi tayi taga ya maida hankalinshi ta wajen window ko me yake Kallo Oho .
Mijin Adda binta ne yayi Sallama ya shigo, Umaima 'Yar ta na biye dashi a baya hanunta d'auke da basket na abinci.
Amsa sallamar suka yi dukansu snn Kabeer ya tashi cikin fara'a ya Mika mishi hanu suka yi musabaha. Tare da gaisawa cikin mutunta juna.
Gun Rumaisa ya juya cikin zolaya yace "yau matar Doctor a gadon asibiti. "
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tana gaisheshi, ya jiki ya mata, snn ya juya ga matar shi yana mata ya mai jiki.
"Umaima sa mata abinci. "
Yace yana kallon Umaimar.
Zuba mata Abincin tayi ta Mika mata, kamar zatayi Kuka take tura Abincin ganin yadda ya kafe ta da idanunshi, Sam batajin dad'in cin Abincin amma babu yadda ta iya tunda dodonta yana wajen.
Rabi taci ta mikawa Umaima Plate, "K'ara. "
Taji yace, kamar zatayi Kuka ta Kalli Adda binta, da sauri Adda binta tazo ta karb'i plate d'in daga hanunta tana harararshi .
Kawar da kanshi yayi kamar baiga abunda tayi ba .
Maganar mijin Adda binta ne yasa shi Juyowa "Doctor ni Zan wuce, Allah ya Kara sauki."
"Amin "yace tare da Mika mishi hanu.
"Mun gode sosae, Allah ya kaika gida lafiya.
Fita yayi Adda binta ta bishi a baya.
"Ke ,bi iyayenki."
Yacewa Umaima.
Sumui ta fita daga d'akin.......
*Ina alfahari dake, Mira D'anfodio, Allah ya bar zumunci.Ana tare 👎*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: [9/8, 5:17 PM] Maman Abdul&Nurain.: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*5*.
Tana fita ya dad'a d'aure fiska ya cewa Rumaisa "Je Ki d'auki Abincin ki k'arasa ."
Babu yadda ta iya haka ta d'auka tana turawa dole kamar zata dawo da Abincin.
Tana cikin ci Adda binta ta dawo.
fiskar tausayi tayi tana kallon Adda binta.
Karb'a Adda binta ta sake zuwa tayi tana cewa "Iskancin banza, a cikin mutum zaki sa Abincin ne. "
"Amma dai Adda binta kinsan rashin cin abinci yana k'ara ciwo ko, kuma wa zai ta zama mata a asibitin ."
"Dama wa ya gayyato ka, Kiran ka akayi, ko ce maka nayi ka zo ka taya ni jinya. "
"Wnn kuma hakkinta nake bata."
""Allah, Ashe ma kasan hakki?"
Ta fad'a tana kallonshi shek'ek'e. "
Tashi yayi yazo ya rab'a ta gefenta ya wuce.
Ko kad'an basu yi tsammanin zai dawo ba, amma ga mamakinsu sai gashi ya dawo wajen K'arfe goma na dare.
Babu wanda ya kula shi cikinsu.
Tsabar rainin wayo irinnashi sai cewa yayi "Adda binta baki tafi ba dama, ina ta sauri nace ko an barta ita kad'ai. "
Shiru tayi masa.
"Adda binta garin akwai hadari fa ya kamata ki koma gida hakanan. "
Cikin takaici ta ce "Zo ka komar dani tunda kai ka kawo ni, bansan wani fitina ne ya dawo da kai ba, fitinannen yaro kawai. "
Zaman shi yayi ba tare da ya tanka ta ba dama burinshi yasata maganane kuma tayi hankalinshi ya kwanta.
A takaice ranar tare da shi suka Kwana a asibitin duk zagin da Adda binta ke mishi yayi kamar baya jinta har ta gaji ta yi shiru.
Asubar fari ya fita daga asibitin ya tafi, basu sake ganinshi ba sai K'arfe sha d'aya na safe ya shigo sanye da lab coat a jikinshi ta dukkan alamu daga wajen aikinshi yake .
Saida ya fara shiga gurin Doctor think ya isa wajensu .
Bacci ya samu Rumaisa take yi, ita kuma Adda binta tana zaune da pocket sized Quran a hanunta tana karatantawa.
Gaisawa yayi da mayar da ya gani kwance a gadon dake kusa da na Rumaisa ya mata ta jiki, ga dukkan alamu ba'a jima da kawo ta gurin ba.
Saida yaji takai aya snn ya gaisheta, harararshi tayi ta d'auke kai zata ci gaba da karatunta taji yace "Gaba dai babu kyau kinsani, nanma kuma Littafi mai tsarki kike karantawa. "
Jikintane ya d'anyi sanyi amma sai ta basar tace "Ka kiyaye ni Kabeer, nifa ba abokiyar wasar ka bace ka sani. "
Murmushi yayi mai sauti snn yace "Nama fiki sani, yanzu dai an sallameku Kiyi parking mu tafi. "
"Ina zamu tafi? "
Ta jefo mishi tambayar.
"Ina ya kamata mu je?"
Ya mayar mata.
"Gidan Abba Babba zaka kaimu dan can Rumaisa zata koma muga ta k'aryar rashin Kunya ."
Nuna ta yayi da yatsa yace "Kina nufin. "
Sai kuma yayi shiru yana ciza lips d'inshi na k'asa. "
With her full confidence tace" Eh, can Zata koma dan zamanta a gidanka kam ya K'are, idan baza ka kai mu ba kuma na kira Baban kalipha ya kaimu. "
Murmushin mugunta yayi dan ya gama tsara abinda zaiyi yace "To yi sauri ki gama parking na kaiku kar ku b'ata min lokaci ."
Zuciya d'aya ta juya ta kama harhad'a kayansu.
sand'a yayi yaje a hankali ya d'aga Rumaisa dake sharar bacci hankali kwance.
A hankali yake tafiya har ya fita daga d'akin.
Cikin mafarki take ji an d'aga ta ,sai taji kamar zata fad'o.
A firgice ta farka, ganinta rike a hannunshi kamar wata jinjira yasa ta zaro ido, tana kallonshi.
Had'e rai yayi ya sauk'e ta tare da b'alla mata harara yace "Muje. "
Gum tayi da bakinta ta bishi har suka isa wajen motarshi.
Shi ya bud'e mata motar ta shiga snn Shima ya shiga ya ta suka yi gaba.
***********
Adda binta na gama parking ta juyo tana kiran Rumaisa "Tashi mu tafi an sallamemu. "
Wayar ta gani ba kowa a kan gadon.
"Maisa. "Ta kira da karfi har matar dake kusa da ita ta bud'e ido.
Da sauri tayi waje aiko taga Kabeer yaja mota a guje, bin gurin take da Kallo, kafin daga bisani ta maida kallonta sama,tana kallon yadda hadari ya d'auro.
Komawa tayi ciki kafin ta k'arasa har ruwan sama ya sauko.
Mijinta ta kira ya zo ya maida ita gida.
Rumaisa kam kirjinta sai dukan uku uku yakeyi, ta rasa ta cewa.
Ganin ya Iso kofar gidansu yasata fashewa da kuka .
Kallonta yayi da mamaki "Kukan me kikeyi? Idan baki rufemin bakinki sai kinyi mai dalili. "
Mut tayi kamar Anyi ruwa an d'auke.......
[9/15, 3:06 PM] Maman Abdul&Nurain.: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
Wannan shafin musamman domin jin d'akinku ne.
*Halima Auwal.Mmn Aysha.*
*Aysha Ali Garkuwa.*
*Maryam A. I Gital.*
*Mira D'anfodio.*
*Xayynab*💤💤
*Ummin weedyan.*
*khairat Up*
*Teemerhlurv.*
Fasaha Online writers grp bna alfahari daku.
*5*.
Tana fita ya dad'a d'aure fiska ya cewa Rumaisa "Je Ki d'auki Abincin ki k'arasa ."
Babu yadda ta iya haka ta d'auka tana turawa dole kamar zata dawo da Abincin.
Tana cikin ci Adda binta ta dawo.
fiskar tausayi tayi tana kallon Adda binta.
Karb'a Adda binta ta sake yi tana cewa "Iskancin banza, a cikin mutum zaki sa Abincin ne. "
"Amma dai Adda binta kinsan rashin cin abinci yana k'ara ciwo ko, kuma wa zai ta zama mata a asibitin ."
"Dama wa ya gayyato ka, Kiran ka akayi, ko ce maka nayi ka zo ka taya ni jinya. "
"Wnn kuma hakkinta nake bata."
""Allah, Ashe ma kasan hakki?"
Ta fad'a tana kallonshi shek'ek'e. "
Tashi yayi yazo ya rab'a ta gefenta ya wuce.
Ko kad'an basu yi tsammanin zai dawo ba, amma ga mamakinsu sai gashi ya dawo wajen K'arfe goma na dare.
Babu wanda ya kula shi cikinsu.
Tsabar rainin wayo irinnashi sai cewa yayi "Adda binta baki tafi ba dama, ina ta sauri nace ko an barta ita kad'ai. "
Shiru tayi masa.
"Adda binta garin akwai hadari fa ya kamata ki koma gida hakanan. "
Cikin takaici ta ce "Zo ka komar dani tunda kai ka kawo ni, bansan wani fitina ne ya dawo da kai ba, fitinannen yaro kawai. "
Zaman shi yayi ba tare da ya tanka ta ba dama burinshi yasata maganane kuma tayi hankalinshi ya kwanta.
A takaice ranar tare da shi suka Kwana a asibitin duk zagin da Adda binta ke mishi yayi kamar baya jinta har ta gaji ta yi shiru.
Asubar fari ya fita daga asibitin ya tafi, basu sake ganinshi ba sai K'arfe sha d'aya na safe ya shigo sanye da lab coat a jikinshi ta dukkan alamu daga wajen aikinshi yake .
Saida ya fara shiga gurin Doctor think ya isa wajensu .
Bacci ya samu Rumaisa take yi, ita kuma Adda binta tana zaune da pocket sized Quran a hanunta tana karatantawa.
Gaisawa yayi da matar da ya gani kwance a gadon dake kusa da na Rumaisa ya mata ta jiki, ga dukkan alamu ba'a jima da kawo ta gurin ba.
Saida yaji takai aya snn ya gaisheta, harararshi tayi ta d'auke kai zata ci gaba da karatunta taji yace "Gaba dai babu kyau kinsani, nanma kuma Littafi mai tsarki kike karantawa. "
Jikintane ya d'anyi sanyi amma sai ta basar tace "Ka kiyaye ni Kabeer, nifa ba abokiyar wasar ka bace ka sani. "
Murmushi yayi mai sauti snn yace "Nama fiki sani, yanzu dai an sallameku Kiyi parking mu tafi. "
"Ina zamu tafi? "
Ta jefo mishi tambayar.
"Ina ya kamata mu je?"
Ya mayar mata.
"Gidan Abba Babba zaka kaimu dan can Rumaisa zata koma muga ta k'aryar rashin Kunya ."
Nuna ta yayi da yatsa yace "Kina nufin. "
Sai kuma yayi shiru yana ciza lips d'inshi na k'asa. "
With her full confidence tace" Eh, can Zata koma dan zamanta a gidanka kam ya K'are, idan baza ka kai mu ba kuma na kira Baban kalipha ya kaimu. "
Murmushin mugunta yayi dan ya gama tsara abinda zaiyi yace "To yi sauri ki gama parking na kaiku kar ku b'ata min lokaci ."
Zuciya d'aya ta juya ta kama harhad'a kayansu.
sand'a yayi yaje a hankali ya d'aga Rumaisa dake sharar bacci hankali kwance.
A hankali yake tafiya har ya fita daga d'akin.
Cikin mafarki take ji an d'aga ta ,sai taji kamar zata fad'o.
A firgice ta farka, ganinta rike a hannunshi kamar wata jinjira yasa ta zaro ido, tana kallonshi.
Had'e rai yayi ya sauk'e ta tare da b'alla mata harara yace "Muje. "
Gum tayi da bakinta ta bishi har suka isa wajen motarshi.
Shi ya bud'e mata motar ta shiga snn Shima ya shiga ya ta suka yi gaba.
***********
Adda binta na gama parking ta juyo tana kiran Rumaisa "Tashi mu tafi an sallamemu. "
Wayar ta gani ba kowa a kan gadon.
"Maisa. "Ta kira da karfi har matar dake kusa da ita ta bud'e ido.
Da sauri tayi waje aiko taga Kabeer yaja mota a guje, bin gurin take da Kallo, kafin daga bisani ta maida kallonta sama,tana kallon yadda hadari ya d'auro.
Komawa tayi ciki kafin ta k'arasa har ruwan sama ya sauko.
Mijinta ta kira ya zo ya maida ita gida.
Rumaisa kam kirjinta sai dukan uku uku yakeyi, ta rasa ta cewa.
Ganin ya Iso kofar gidansu yasata fashewa da kuka .
Kallonta yayi da mamaki "Kukan me kikeyi? Idan baki rufemin bakinki sai kinyi mai dalili. "
Mut tayi kamar Anyi ruwa an d'auke.......
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*6*.
Tunda suka shiga ciki, take ta fatan ya fita itama ta samu ta fice daga gidan. D'akinta ta shige, bini bini ta lek'a ta ganshi yana zaune a falon.
Sanyi, da niimar ruwan sama da aka zabga yasa bacci mai nauyi da dad'i ya kwasheta ba tare da ta sani ba.
Kiran sallar azahar ne ya tashe ta daga bacci, toilet ta shiga ta d'auro Alwala.
Tana shimfid'a sallaya idonta ya sauka kan Leda kan dressing mirror d'inta, bud'ewa taje tayi taga take away da drinks. "First in history ."
Tace tana kad'a Kai.
Saida tayi sallah, snn ta d'auki Abincin taci ta rage Saura.
Mamakin baccin da tayi take tayi, ita da take fakonshi ya fita Itama ta fita, amma har yaje ya sayo abinci bata sani ba.
Lekawa ta kuma yi ta hango shi zaune da remote a hanunshi yana canza channel a T. V.
A hankali ta koma ta zauna tsakiyar d'akin ta buga tagumi. Can kamar an mintsineta ta tashi ta fara neman phone d'inta.
Har ta gaji da nema ta koma ta zauna tana tunanin inda ta jefar da wayar.
Har dare bata samu ta fita ba k'arshe dai hakura tayi tayi wanka ta kwanta tana tunanin makomar rayuwarta har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari da sassafe bayan tayi sallah tana kwance kan sallaya, taji ya turo k'ofa ya shigo, da sauri ta tashi tana mutsike ido.
"Ina Kwana Bobbo. "
"Lafiya. " yace a takaice.
Yaci gaba da cewa "Ba sai na tambayeki ya jiki ba nasan kin warke, so zaki fara normal duties d'inki kamar yadda kika saba, kar kiga jiya na saya miki abinci Kiyi tsammanin Yauma hakane, Sam bazan yi wahalan banza ba gwara ma ki tashi Kiyi abinda kika San ya dace dake. "
Yana gama fad'ar haka ya fice daga d'akin.
Kuka ta fashe dashi tana fadin "Na shiga uku na, Bobbo yanaso yayi ajali na."
Tunawa tayi da inta sake ya dawo ya sameta bata fara aiki ba wuya zatasha.
Hakanan yasa ta tashi ta shiga toilet ta wanke fiskarta snn ta fito ta fara aiyukan gida kamar yadda ta saba, share ko ina tayi ta yi mopping har da d'akinshi da nata, da wankin 🚽, snn ta koma kitchen nanma ta gyara ko ina kafin ta d'ora abinda zata karya dashi.
Duk Gajiyar da tayi gashi tana jin jikinta so weak, hakanan ta fita ta share compound na gidan.
Girkin ta k'arasa ta juye duka a food flask, ta nufi d'akin ta dashi dan tasan ko ta zuba mishi ba ci zaiyi ba.
Zata shiga d'akinta ta tsinkayo sallamar Adda binta, da sauri ta dawo da baya fiskarta d'auke da fara'a zuciyarta fal farin ciki, tana yi mata Sannu da zuwa.
A falon suka zauna bayan sun gaisa take tambayar ta Kabeer, tace ya fita.
"Ba dai abinba ya miki jiya ko?"
"Ba komai Adda. "
"Kai ni jiya Kabeer ya ban mamaki, daga in tattara kaya sai kawai na juya naga dukanku biyu ba kwa nan. "
Saida ta waiga ta Kalli k'ofa kamar mai tsoron kada wani ya jiyota, tace "Hmmm, nima Adda am farkawa kawai nayi na ganni a hanun mutum, ni na ma d'auka mafarki nakeyi. "
Dariya Adda binta tayi snn tace "Amma Kabeer d'an duniya ne, sai da fa na kira Bbn kalipha yazo ya maida ni gida.
Barka dai da bai miki komai ba. "
"Hmmm, "Tace snn ta k'ara da cewa "Adda binta ga abinci.
Zaro ido Adda binta tayi, "Ba dai Sai yanzu zakiyi breakfast ba, wai tsaya ma ke kika girka Abincin da kanki, ke da aka sallamo jiya daga asibitin. "
"To ya xanyi Adda. "
Gyad'a kai takeyi "Al'amarin Kabeer ya ta'azzara babu tausayi Sam, lallai dole a d'au mamaki, dole Manya Suji maganar nan, ke idan an tambayeki dalilin wnn abinda yake miki, cewa kike baki saniba ,shi kuma idan an tambayeshi, ya Raina wa mutane hankali, toh abun ya ishe ni haka, dole Manya susa baki idan abin ya gagara ku rabu kawai. "
Har ta gama b'ab'atunta Rumaisa bata ce mata komai ba, cin abincinta take a tsanake.
Adda binta ce ta mata girkin rana tace ta kwanta ta huta.
Saida tayi wankanta da ruwa mai d'umi sosae snn ta kwanta tayi baccinta.
Haka rayuwa taci gaba kullum Rumaisa sai tayi dukkan Aiyukan gida, ga hantaranta da Kabeer yakeyi, kullum cikin gaya mata bakaken maganganu, bata da sukuni Sam a gidan, Gashi kuma sai ya fita ya barta ita d'aya a gidan . yanzu har ta saba, Kasancewar shi Doctor ba ko Yaushe yake Kwana a gidanba ,tun tana jin tsoro har ta saba da Kwana ita kad'ai a gida.
Kasancewar yau weekend babu inda yaje yana gida kamar yadda ya saba duk weekend sai dai in emergency ne ya taso mishi.
Wucewa tazoyi, ba tare da tasan ya fito palour ba, three quarter ne a jikinta fari da wata 'Yar bingilar riga bak'a, tafiya takeyi cikin nitsuwa Zata shiga kitchen, saida ta isa tsakiyar falon ta ji yace "Ke. "
Wani irin razana tayi har ta kusan sashi dariya .
Da hannu ya mata alamar ta zo gurinshi.
A tsorace tazo ta tsuguna daga gefe ta ce "Gani Bobbo. "
"Matso yace mata. "
Matsawa tayi kusa da shi a ranta addu'a take Allah ya kare ta daga sharrinshi.
Kamo rigar yayi ya ja, ya petta mata shi a jiki, yana bin duk ilahirin jikinta da Kallo.Kasancewar rigar rubber rubber ce, ta ko pettu pet, ta koma jikinta ta lafe.
A kasalance yace "Yaushe zaki fara jin magana ne Maisa?Bana hana ki saka wad'annan kaya a gidannan ba?"
Kallonshi tayi jin yadda yake maganar a sanyaye, suna had'a ido ya lumshe idanunshi, ba tare da ya bud'e su ba yace .
"Tashi ki bar nan. "
Still a sanyaye yayi maganar.
Tashi tayi tana Hamdala a zuciyarta bai mata komai ba, Zata shiga d'aki taji yace.
"dawo kici gaba da aikinki. "
"Ikon Allah."
Tace a ranta.
Wucewa ta zo tayi ya bita da Kallo har ta shiga kitchen d'in snn ya sauk'e ajiye zuciya.
Har ta gama ayyukanta ta wuce ta koma d'akinta yana zaune a gun bai tashi .
Wayar shi ce tayi Kara , yana dubawa yaga Adda binta ce ke kiranshi.
"Kabeer yanzu abinnaka har yakai ga Bappa khamis, ma yasan abunda kake wa Rumaisa?
To ka shirya amsa tambayoyi dan yakai karar ka wajen Abba Babba, yanzu ya ce ince maka kazo kai da Maisa. Da alama zaman Maisa ya K'are a gidanka, ita ma kuma ta huta. "
Baice komai ba ya kashe wayar yana maida numfashi.
A fili Yace "Bappa khamis ya Kai karata gun Abba Babba? Lallai ya kirawa kanshi ruwa. "
Toh fa 😳wai meke faruwane? ...
Zakuga yau ina ta suburbud'o muku lbr 🤣🤣🤣
To fa na bankwana ne ,sai had'uwa ta gaba dan Zan shiga vibration cikin yan kwanaki nan, hidimomi nake dasu, in Allah yasa na gama da Raina da Lafiyata zaku jini.
*Allah ya sada mu da alkhairi. Luv u all. 😍😍😘*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Alhamdulillah !Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!*
*Ma sha Allah.*
Allah ya bani lafiya,
Na gode da Addu'oinku gareni. Allah ya bar k'auna .
*7*.
Fitowarta kenan daga wanka, tana tsane gashin kanta da ta wanke da d'an karamin towel ta jishi yana kwala mata kira.
Amsa wa tayi tare da ajiye k'aramin towel d'in hanunta ta fito da sauri har towel d'in Jikinta yana faman fad'uwa rikewa tayi tana gyara zamanshi a jikinta har ta Iso ta durkusa.
"Gani Bobbo. "
Tace, tana raba ido, gaba d'aya ta tsorata da Kiran da yake mata.
Kallonta yayi na d'an lokaci daga sama har k'asa, ya had'iyi busasshiyar yawu da ta kusa sashi ya k'ware , snn ya Kawar da kanshi wani gefen.
Kije ki shirya yanzunnan zamu je gidan Abba babba, Saura kuma Kiyi banzan dressing da kika saba. Kar kuma ki b'ata min lokaci.
Da sauri ta tashi tayi hanyar d'akinta nanma da Kallo ya bita yana tunani a ranshi anya ba da gangan Rumaisa take zuwa gunshi da irin wad'annan shiga ba.
Kawar da tunanin yayi ya gyara zama yana tunanin yadda za'a kaya a gidan Abba babba.
Har ta fito yana zaune a gurin, K'are mata kallo ya shigayi ,sanye take da riga da skirt na atamfa, Nouvo, kayan sun mata kyau sosae d'inkin ya zauna mata d'as sai Gyale kalar kayan da ta yafa da takalminta high hill Shima kalar gyalen.
Saida ta Iso ta ce "Bobbo na shirya. "
Kamar wanda aka tasa a mafarki ya kalleta, sai kuma ya b'alla mata harara, "Wuce kije ki cire gyalennan wai ke bakya lullub'i mai mutunci ne? "
Da sauri ta koma d'akinta, kallon kanta tayi a madubi, ta tab'e baki, Meye aibun Wannan gyalen, ita dai bata gani ba, after all mota ma zata shiga,
"Sa ido ne kawai irin nashi "
Ta fad'a a hankali kamar mai rad'a.
A cikin manyan hijaban da ya sayo mata ta d'auko wanda ta ga ya dace da kayan jikinta ta saka ta fito.
Tafiya suke Irinna kurame ba mai yiwa wani magana a cikinsu, saidai ita takan saci kallonshi ganin yadda ya had'e rai kamar wadda aka Aikowa da sakon mutuwa.
Bata Zata ba taji ya kamo yatsunta yana murzasu a hankali.
Kallonshi tayi taga hankalinshi naga tukin da yakeyi.
"Maisa. "Taji ya kira ta.
Wani abu taji yana mata yawo a jiki wanda ta kasa fassara menene shi, dan rabon da taji ya kira ta haka cikin nitsuwa har ta manta.
Tsinkayo shi tayi yana cewa "Ina fata baki manta alk'awarin da kika tab'a d'aukar min a hospital ba.
Dama na sanar dake akwai lokacin da zan bukaci ki Fad'e shi."
Numfashi ya ja ya sauk'e, ya ci gaba da cewa "Lokacin yayi yanzu, so nake a yau ki fad'i maganar a gaban koma waye."
"Zaki iya? "
Taji ya jefo mata tambayar.
Wani irin juyawa taji cikin ta yayi, tuni taji hanjin cikinta suka Fara yamutsewa, hankalinta ya tashi.
No wonder, yake mata magana cikin taushin murya Ashe da manufa.
"Baza ki iya ba kenan?"
Taji yace.
"Oho, ruwanki da ki fad'a da karki fad'a duk uwar ubansu d'aya, kece cikin wahala, dan ni kome za'a min bazan sakeki ba, amma ki sani sai nayi trippling abinda nake miki.
Samun Kwanciyar hankalinki kawai kifito ki fad'a, idan kuma kink'i kece a wahale."
Dadai sun Iso yasaki hanunta ya nemi wajen parking yayi, suka fito.
Kallonta ya kuma yi yace "kindai ji abinda nace miki. "
Yayi gaba abinsa.
Itako gaba d'aya ta shiga rud'ani ta rasa inda zata Sa ranta taji dad'i, yanzu bata da wani burin da ya wuce taganta cikin toilet. 😂😂
Wuta sallau.
Koda suka shiga cikin gidan, cike yake da 'yan uwa maza da mata, wani kululu taji cikinta ya sakeyi sbd da haka duk Sannu da zuwan da ake musu babu wanda ta Kula ,buta ta Zara tayi hanyar toilet. ........
*Tuna baya.*
Familyn Alh.Abubakar manga,Wanda aka fi sani da Alh. Buba Manga Babban family ne wadda Allah ya azurtashi da yara da jikoki masu yawa.
Bak'i dogon bafulatani mai cikar haiba, mutumin kirki ya kuma San darajar d'an Adam, da kuma iya zama da mutane.
Sana'ar shi ya had'a da noma da kiwo dabbobi, most especially shanukai.
Matanshi hud'u ne, yaran da ya Haifa maza da mata a Sunkai ashirin da bakwai, acikinsu uku kawai suka rasu.
Ya tsaya tsayin daka wajen ganin 'ya'yanshi sunyi karatu, both Arabic da boko.
K'aramin d'anshi yana da shekaru goma sha biyu Allah ya mishi rasuwa.
Wnn babban family Sun ga tashin hankali, dan sunyi babban rashi ,ba familynshi kawai bama harda mutane makwabta, 'yan anguwarsu da sauran jamaar da suke huld'a tare. Rasuwan shi bai canza Komai ba na daga zaman lafiyar da akeyi a gidan sai ma k'ara had'a Kai da yaran sukayi ,suka rungume iyayensu mata ba bambanci .
Akwai had'in kai sosae cikin family dan Sam Alh. Manga bai yarda da raba kan yaranshi ba .
Yawancinsu sun taso da son harkar kasuwanci.
Sun taso da k'aunar juna, hakan yasa lokacin da suka girma suka Fara hayayyafa idan ba farin sani Kayi musu ba baka iya banbance Wannan d'an waye a cikinsu.
Yawancinsu kamannin Alh. Manga suka d'auka shi yasa suke kama sosae da juna kamannin kuma har yaransu da suka Haifa.
Kowani d'a a Familyn yana da 'yancin ya zauna a duk gidan da ya ga daman zama.
Asalinsu yan Jalingo ne Taraba state.
Musamman ya sayi filaye a anguwanni mabambanta ya rabawa yaranshi, tun kafin ya rasu. yakan d'auki fili ya ba yara biyu wanda basu had'a uwa ba duk dan gudun kada zumuncin su ya lalace .
Cikin yaranshi mata akwai wad'anda suka yi aure cikin jalingon akwai kuma wad'anda suke wasu garuruwa.
Kamar mahaifiyar Rumaisa kenan wacce aure ya kaita Jigawa state.
A can ta haifi yaranta takwas wanda ya kasance Rumaisa ce 'yarta ta biyar.
Tun tana 'yar karamar ta 'yar yayar mamanta wacce suke kira da Anty Hafsa, wacce ke aure a Abuja ta d'auketa riko.
Da fari Suna zaune lafiya zama mai dad'i, sai daga baya wata Kawar Aunty Hafsa ta fara bata shawarar ta mayar da ita gun uwarta ,idan ba haka ba Tana ji tana gani Zata rike ta ta girma mijinta zaice yana sonta.
Dan Rumaisa irin yarannan ne da tun suna kanana zaka gane zatayi cikar halitta.
ita kuma Aunty Hafsa ta nemi shawarar kawartata ne akan idan ta aiki Rumaisa gu mai nisa ko kuma ta ba ta aiki mai yawa mijinta yana mata fad'a akan hakan yana cewa tana bawa 'yar mutane wahala, shine kuma ita Kawar Tata ta fara zugata.
Wasa wasa zuga ya shigi Aunty Hafsa, ta zo Jalingo da Rumaisa akan Zata maidata gun mahaifiyarta kafin ta koma Abuja.
Jin haka kuma kawun Rumaisa wanda take kira da kawu khamis ,kanin mamanta wanda suke had'a uba amma uwa daban daban yace ta bar mishi ita zai riketa dan shi bashi da 'ya mace, yaranshi duk maza ne.
Mafari kenan zaman Rumaisa gidan Kawu khamis....
*Just d beginning.*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W..
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*8*.
Ba karamin shagwabata kawu Khamis yakeyi ba, duk wani abu da ya gani na yara mata yana saya mata, gatan da yake mata ko yaran da ya haifa ba ya musu.
Saida matar shi tayi da gaske ya barta take zuwa makarantar islamiyya da ta allo.
A cewarshi ana duka sosae.
Duk ranar data nuna bata son zuwa cewa yake a barta, sosae ya shagwabata.
Shi yake kaita makaranta ya d'auko ta sabanin yaranshi da driver yake kaisu.
Ko kad'an bayason b'acin ranta shi yasa yawanci tare da ita yake fita.
Maganar aiyukan gida kam babu su Dan ya kasa ya tsare. Shi yasa har ta girma ko tafasa ruwa bata iya ba.
Ta fannin sutura kuma saidai in ita tace bai mata ba.
Musamman yake kaita boutique nashi ta zab'i irin suturar da ta ke so.
Kayan kwalam kuma babu irin wanda bata sani ba.
Kowa gani yake dan bashi da 'ya mace shi yasa yake mata gata haka, amma abin mamaki Koda Allah ya ba matarshi haihuwar 'ya macen bata samu gatan da Rumaisa take samu ba.
Dalilin haka yasa matar shi ta fara jin haushin Rumaisa, amma fa saidai a zuciyarta bata isa ta nuna ba.
'Yan uwanta Sun zugata ta d'au mataki amma abin ya gagara dan kawu khamis irin mutanen nan ne masu zafin tsiya, amma fa banda akan Rumaisa.
Idan Kaga yayi wa Rumaisa fad'a tofa ya ganta da wani namiji ne Koda kuwa a cikin family members ne.
Batayi nisa sosae ba a karatun arabiyya ya hanata zuwa wai ana dukanta, shi da kanshi ma zai koya mata karatun.
Bokon ma ba wani damunta yayi ba,
Mutum d'aya ne yake sata tayi karatun ko taki ko ta so shine *Kabeer*. Wanda kannenshi suke kira da *Bobbo*.
Kabeer shima d'an Kawunta ne wanda suke neighbors da gidan kawu khamis.
Shi ya d'auko zafin ran kawu khamis, yawanci kuma idan yazo daga makaranta a gidan kawu khamis yake sauk'a.
*Kabeer shine second born a gidan su, shi yake bin Adda Binta.
Tun tasowarsu da Adda binta haka suke kullum cikin fad'a, a cewarshi ta cika sa ido, ita kuma tace ya raina ta.
Sosae Kabeer ke matsa mata akan karatu, tun bata sa hankali har ta fara fahimta.
A maiduguri yayi karatunshi.
Duk lokacin da ya samu hutu ya dawo, to Rumaisa tasan dole ta nutsu tayi karatu.
Shi yake kiranta Baby Maisa, Saura ma suka bi bakinshi suke ce mata Maisa.
Har kawu ma Maisan Kawu yake ce mata.
Ganin irin shak'uwar data shiga tsakanin Kabeer da Rumaisa
Yasa kawu ya fara sa musu ido, har ya fara kiranshi yana nuna mishi baya so.
Maisa tana ss2 kawu ya mata registration ta rubuta SSCE.
Sai ya zamto babu abin da takeyi sai bacci da yawo.
Ko kula matar gidan batayi, tsakaninsu Gaisuwa ce sai d'an abinda baza'a rasa ba.
Lokacin da Kabeer ya kammala komai na karatunshi ya dawo gida, sai ya ci gaba da zama gidan kawu khamis.
Lura yayi da bata damu da shiga dangi ba, ya fara sata ziyara Koda bata so haka yake tasata a gaba su ziyarci 'yan uwa.
Yawanci gidan Adda binta yake kaita tayi kitso, yana zaune tana mata kitso, suyi ta fad'an nasu na fama ,Itako Rumaisa Dariya abunnasu yake bata.
Koda kawu ya fahimci yawan fitarsu da kabeer, sosae ya nuna mata b'acin ranshi.
Duk yadda taso kin fita da Kabeer bata iyawa dan Shima bata so ta b'ata mishi rai.
Fahimtar hakan yasa kawu ya tsiri fita da ita duk kuwa da yanzu ta girma ba kamar da ba.
Kabeer baiso haka ba amma babu yadda ya iya, matarshi ma ta yi iya kokarinta har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.
Basa samun isasshen lokaci amma hakan baya hana Kabeer squeezing ya samu su d'an samu zama.
Kullum cikin yawon Sayan kwalam da makulashe suke, sune, Senate plaza, Ni'ima cool, Ostrich bakery da dai sauransu.
Yayyunshi ne suka ga abun yayi yawa suka kira shi suka mishi magana, snn aka samu ya rage yawan fita da ita.
A hankali soyayya mai ka'rfi ya shiga tsakanin Kabeer da Rumaisa, sosae suka shak'u, tsabtataccen soyayya suke gwada wa juna.
Tun kawu bai fahimta ba har ya gane, ba karamin tashin hankali ya shiga ba da ya fahimci soyayyarsu tayi nisa.
Duk yadda yaso ya rabasu abu ya gagara, sbd haka sai ya fara kuntatawa Rumaisa, kullum cikin zaginta yakeyi, wani lokacin har da duka yake hada'wa .
Koda aka tambayeshi abinda ya shiga tsakaninsu da 'yar lelenshi, cewa yayi tana yawan kula 'yan iskan samari,kuma idan ya kyale lalatata zasuyi.
ita ma matarshi da yaranshi mamaki abin ya shiga basu, amma matar fa taji dad'in yadda al'amarin ya Juyawa Rumaisa, dan gani take ta takurawa rayuwarta data 'ya'yanta.
Hanata fita ko ina yayi, snn idan ya fita Shima baya wani jimawa yake Dawowa gida, duk ya hana kanshi sukuni.
K'arshe ganin raba Rumaisa da Kabeer ya gagara sai yaje gurin mahaifin Kabeer yace mishi, yazo sanar da shine,
Muddin aka ga Rumaisa ta lalace ,to Kabeer ne ya lalatata, shi kam yayi iya kokarinshi abu ya gagareshi, dan haka BABAN Kabeer d'in ma ya jawa Kabeer kunne akan Rumaisa dan shi Sam bai yarda da tsakaninsu ba.........
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W..
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Wannan shafin nakine Habiba Muh'd Abdullah.*
Ke mai k'aunatace na sani, Allah ya bar mu tare.
*9*.
Tashin hankali sosae BABAN Kabeer d'in ya shiga, kiranshi yayi ya nuna mishi b'acin ranshi a kan tarayyarsu da Rumaisa, har yana ce mishi wai shi da ya kamata ya kula da ita ya hana ta Kula samari,amma shike kokarin lalata mata rayuwa, to duk abinda ya b'ullo yayi Kuka da kanshi.
B'acin ran da Kabeer ya shiga baya misaltuwa dan tabbas yasan aikin kawune, wanda su kuma suke kira da Bappa.
Daga nan suka shiga 'yar tsama da Bappan nashi, k'arshe dai da yaga zaman gidan ba mai yiyuwa bane a gareshi ya tattara ya koma gidansu.
Hakan kuwa yayiwa Kawu dad'i dan a cewarshi ya huta da ganin abin takaici.
Rumaisa ko bata ji dad'in hakan ba amma babu yadda ta iya, ta kuma tambayeshi dalilin barin gidan yace mata, haka kawai.
Yanzu ita ke yawan shiga gidansu Kabeer, duk yadda Baban Kabeer yasa hankali a kansu dan fahimtar irin alakar dake tsakaninsu, bai ga wani aibu a ciki ba, k'arshe dai ya bisu da Addu'a, Allah ya kare mishi su dukansu.
Da kawu ya gane yawan shiga gidan su Kabeer da ta keyi nanma Ya sa mata kahon zuqa.
Basu samu sukuni ba saida Kabeer ya samu aiki a specialist hospital, a Matsayin gyenea Doctor.
Zuwa aikin da yake yi ne ya sa ba ko Yaushe suke samun had'uwa ba.
Wani abin mamaki shine, yanzu duk gatan da kawu keyi wa Rumaisa, bai hanata Yunkurin guduwa ba, sau biyu yana kamata tana shirin guduwa, hankalinshi yayi bala'in tashi.
K'arshe ya kira meeting ya sanar da 'yan uwanshi halin da ake ciki, har ce musu yayi shi yana tunanin wani ne yake Hure mata kunne, ko kuma yawon banza take so ta tafi.
Da aka tambayeta cewa tayi ita gidan take so ta bari.ta gaji da gidan.
Cikin tashin hankali ya fara kumfar baki yana cewa, dan taga yana takurata yana hanata tsayuwa da samari shi yasa take so ta bar gidanshi.
Da kyar aka lallab'ata ta zauna bayan dogon nasihar da ta sha a gun Iyayennata.
Daga nan wata sabuwar kulawa take samu daga wajen Kawu,kullum cikin rarrashinta yake, komai nata daban ne a gidan, ya zamanto ko abincin da za'a dafa sai wanda ta zab'a.
Sosae hankalin matar kawu ya tashi taje ta fad'a wa iyayenta.
Kiranshi sukayi suka mishi magana akan hakan.
Da ya dawo gida kuwa saida ta gwammaci da bata kai kararshi ba dan sosae ya ci mata mutunci har Kaurace mata yayi na sati biyu.
Gaba d'aya gidan ya zama ba dad'i, yaran gidan yanzu Suma mugun jin haushin Rumaisa sukeyi dan a cewarsu ita take haddasa duk wata fitina dake Tasowa a gidan. Tun da yanzu kawu ko da yaran da ya Haifa yaga Rumaisa sai yayi ta zaginsu.
Ranar da Kabeer bazai tab'a mantawa ba a rayuwarshi, Ranar da ya sa mata suna da bak'ar rana, wata ranar talata, tunda Kabeer ya tashi yakejin jikinshi ba dad'i, sakamakon mafarki da yayi da daddare wanda ya gagara gane kanshi.
Sai kuma fad'uwar gaba da ya sashi a gaba.
Da kyar ya shirya ya tafi wajen aiki, ko da ya je ma ya kasa sukuni, aikin ma gaba d'aya ya gagareshi, jin jikinshi yake a mace.
Fitowa yayi daga asibitin ya dawo gida, gidan kawu ya fara shiga ya tambayi labarin Maisa, akace mishi yanzu suka fita da kawu khamis.
Gidansu ya shiga nan kuma Maman shi ta ce mishi d'azu Rumaisa ta shigo bata sameshi ba.
D'akinshi ya shiga ,ya zauna, ya rasa gane abinda yake damunshi.
Alwala yaje ya d'auro yayi nafila, tare da addu'a, kafin ya fita ya kama hanyar komawa asibiti, yana maimaita Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji uun, sbd fad'uwar gaba da ta dameshi.
Yana parking ya fito ya nufi hanyar office d'inshi.
Hankalinshi ne ya gagara Kwanciya ganin yadda mutane suka taru a emergency unit, ga dukkan alamu accident victims aka kawo.
Har yayi kamar zai wuce sbd in wnn ne Sun saba gani, amma abin mamaki sai wucewar ta gagareshi.
Gurin mutanen ya kutsa sai gani yayi ana daga wata da alama suma tayi ga jini kuma yana bin jikinta.
Dubawannan da zaiyi sai ganin Rumaisa ce a sume.
"Subhanallah. "yace da ka'rfi cikin azama kuma yasa hanu ya karb'eta bai damu da sauran da ake kokarin d'auka a gun ba.
Hankali tashe ya shiga da ita aka fara bata taimakon gaggawa, ba wani ciwo sosae taji ba, goshinta ne ya fashe, sai hannayenta da suka kwarzane.
Amma abinda ya basu mamaki shine bleeding d'in da takeyi ba kakkautawa.
Kabeer ne ya shiga dubata da kanshi, dan tun d'azu tsaye yake yana kallonsu ba tare da ya sa musu hanu ba.
K'arshe dai ya yanke shawarar ya mata scanning dan gano abinda ya sa ta bleeding.
Abinda ya gani ne ya yi bala'in tayar mishi da hankali, har tuñaninshi ya shud'e na wucin gadi..........
..Toh fans Me Bobbo Kabeer ya gani ne?
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W..
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*10*.
Unbelievable, office d'inne ya shiga juya mishi, take yaji duhu na mamaye idanunshi.
Hanunshi duka biyu ya dafe kanshi dasu tare da rintse idonshi tamau.
Tuni ya fara jin kanshi kamar zai tsage, ya rabu gida biyu.
"Wai Rumaisa da ciki?"
Abinda ya ke maimaitawa a ranshi kenan.
Toh ta ina ta same shi?
Duk Wannan tsaro da Bappan yake mata amfanin me yayi?
Wani shegen ne ya mata ciki?
Wad'annan tambayoyi su yayi ta jerawa kanshi, duk da bashi da amsar ko d'aya daga cikin su.
Ya jima yana zaune a gurin, kafin daga bisani ya yanke shawarar yayi flushing na cikin kawai tun da ya fahimci kamar lalacewa yake sanyi.
Hakan kuwa akayi harda wanki ciki ya mata.
Ward aka kaita, aka d'aura mata drip.
Sai sharar baccinta take, alluran bacci na ta aiki a jikinta.
Office d'inshi ya kulle, yadawo kan kujeran ya zaune tare da d'ora kanshi kan table.
Wasu hawaye masu d'umi da rad'ad'i suka Fara zubo mishi.
Kuka ya yi sosae, kafin yad'an ji sauk'in abunda ya tokare mishi kahon zuciya.
"Why, Baby Maisa, why? Me yasa zaki min haka?
Laifin me nayi da na cancanci Wannan sakamako mai muni?
Me ya kaiki zubar da mutunci da darajar ki ta 'Ya mace a titi.?
Menene amfanin tsaron da Baffa yayi ta miki?
Me zaki cewa Allah ranar gobe k'iyama.? "
Surutai yayi ta yi cikin kukan bakin ciki.
Ranar yayi kukan da bai tab'a yin irinshi ba.
Dakyar ya samu yayi controlling na kanshi ya goge fiskar shi, snn ya bud'e drawer ya d'au bak'in eye glasses d'inshi ya toshe idanunshi da shi.
Inda aka kwantar da ita ya je ya tsaya yana K'are mata Kallo.
Ya jima yana zaune yana kallonta yana rasa gane wace irin Tunani zaiyi akan ala'marinta.
Yarinyar da ya zab'a ta zamo uwar 'ya'yansa.
Yarinyar da tun tana k'arama yake mata matsanancin so.
Yarinyar da ya rayu da k'aunarta.yau itace d'auke da cikin wani kuma ba ta hanyar aure ba.
Hawayen da suka sake zubo mishi ya sa hand kerchief ya goge.
Sai daga baya ya yi tunanin ya kira gida ya sanar da su.
Anan suke fad'a mishi Suna hanya, yanzu aka fad'a musu Maisa da Kawu khamis sunyi accident.
Sai a lokacin yasan tare da kawu abin ya faru dan shi baima Kalli sauran victims d'in ba ,hankalinshi na ga Rumaisa.
Dakyar ya ja kafafunshi ya fita don uwa duba Baffanshi.
Acan suka had'u da iyayenshi suka shiga tare dan dubashi.
Daga bisani suka koma wajen Rumaisa.
Bai sanar da kowa ba saida ta warke bayan an sallameta, ya samu mahaifinshi ya sanar da shi abinda ya faru.
Iya kad'uwa da tashin hankali Babansu Kabeer ya shiga.
Kallon Kabeer yake kamar wadda yaga bakuwar fiska hardai Kabeer ya tsargu da kallon da Babbannashi yake mishi, ya fara tunanin ko dai bai yarda da zancen shi bane.
Numfasawa, Babanshi yayi kafin ya fara jera kalmar Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji uun.
Har sau uku.
Kafin ya bi da.
Allahumma ajirnii fii musiibaty wa'akhlifnii khairan minhu.
Sai da ya kuma d'aukan lokaci kafin yaji mugun bugun da zuciyarshi keyi ya sassauta.
"Muhammad Kabeer. "
Yaji babanshi ya kirashi da dakusasshiyar murya.
Tsinkewar zuciyace ta ziyarce shi da yaji yadda babanshi ya kirashi.
"Na'am Baba."yace tare da d'agowa yana kallon Babbanashi.
"Ka tabbata abinda ka fad'i gaskiya ce "
"Wlh iyakar gaskiyata kenan, abinda na gani na fad'a maka, ni na mata scanning da hanuna. "
Kura mishi ido baban ya kuma "Kabeer, Kaji tsoron Allah ka fad'a min gaskiya, kana da wata masaniya akan cikin nan ko babu. "
A gigice ya d'ago ya kalleshi, "Masaniya kamar ya Baba?"
"Ina nufin, ko kanada alaqa da samun cikin Rumasa'u, dan ku 'ya'yan yanzu an haife ku ne ba'a haifi halinku ba, sbd haka babu yadda za'ayi a shaide ku, more especially idan akayi la'akari da yawan kawo karar ka da Baffanka yakeyi game da tsakaninka da Rumasa'u.......
*Wnn shine ana wata ga wata, Bobbo Kabee yashiga tsaka mai wuya.*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal )*
♣♣♣
*11*.
A take wani irin b'acin rai, bak'in ciki, da kuma tsantsar kiyayyar da tsanar kawu da Rumaisa suka ziyarce shi, more especially, Baffa khamis, ji yake kamar ya shakeshi sai yaji Kamshin lahira tukun ya sake shi.
Jajayen idanunshi da suka rine dan bakin ciki ya d'ago ya saukesu kan babanshi.
Still kallonshi yakeyi ba kakkautawa dan amsar Kabeer kawai yake jira a halin yanzu.
"Baba idan na rantse zaka yarda da ni? "
"Wallahil azeem bani da masaniya akan cikinnan, idan ba Ranar da tayi accident ba, babu wata alaqa makamancin haka data tab'a shiga tsakaninmu. "
Ya k'arashe maganar yanaji kamar ya rushe da Kuka.
Ko ba komai Baba ya d'an samu relief, tunda yaji Kabeer ya rantse, amma abin tambayar anan.
Wa ya aikata Wannan aika aikar?
Numfasawa Baba yayi "Naji abinda Kace Kabiru, na kuma yarda, sai dai abinda ya kulle min Kai wa ya lalatawa Rumasa'u rayuwa? "
Cikin takaici Kabeer yace, "Abinda ban sani ba kenan Baba saidai ko tambayarta za'a yi aji daga bakinta. "
"Hakanma yayi, tashi Jeka, Allah ya maka albarka, zamu san abin yi.
Musamman Baba ya shiga gidan kanin nashi kawu khamis, cikin lumana ya fahimtar dashi abinda ke faruwa snn ya bukaci a kira mishi Rumaisa.
Cikin tsananin tashin hankali, kawu ya shiga har d'akin Rumaisa ya kirawota.
Tambayar duniyar nan Baba ya mata, amma taki magana sai kuka takeyi, Kuka mai ban tausayi. Har ya gaji ya ce ta tashi ta tafi.
Maida hankalinshi yayi kan d'an uwanshi dake zaune kamar mutum mutumi, da ka ganshi kasan baya cikin hayyacinshi ya shiga Tunani mai zurfi.
Dafa shi Baba yayi.
"Khamis, ina so ka kwantar da hankalinka akan wnn abu da ya faru, kada ka sashi a rai ya jawo maka wata cutar, ka d'auka wnn abu kaddarace babu wanda ya fi karfinta, sai dai muce ,Allah ya kiyaye gaba, amma ni a Tunani na mai zai hana a d'aga Rumasa'u daga wnn gida, ta koma gidana ko gidan yaya saboda wasu dalilai da Basai na tsaya zayyanasu ba yanzu, ko ya ka gani. "
Hankali a tashe Kawu ya kalleshi.
"Kana nufin wai Maisa ta bar gidannan? "
Gyad'a mishi kai yai tare da cewa "Eh, haka nake nufi. "
Girgiza kai ya shiga yi "Bazai yiyu ba Yaya, Maisa baza ta bar gidannan ba, yadda na raineta tun tana yarinya haka zata ci gaba da zama har ranar da Allah zai rabamu, wato idan tayi aure ko dayanmu ya mutu. "
Wani Kallo Baba ya mishi "Wannan magana kakeyi Hamisu, dole Rumaisa tabar gidannan ko don ta samu kula da tarbiyar da ya dace ace ta samu daga wajen uwa wadda babu shi a gidanka, muna da masaniyar tsakanin mai d'akinka da Rumasa'u babu wata shiri, Wannan Kuma ba laifin kowa bane sai naka, sbd haka dole mu sama mata wnn kulawar kafin komai ya gama kwab'e mana. "
"Yaya Kai ka bani Maisa ne? "
Ya fad'a cikin b'acin rai.
"Ko ba Nina baka ita ba, dole insa hankali akan tarbiyarta, dan nima 'ya tace, ka tuna wani hali mahaifiyarta Zata shiga idan taji abunda ya faru da 'yarta?
Me kake tsammani Zata tuna? Barin Maisa gidannan dole ne ko don ta samu kulawar da ta dace. "
"Dan Allah yaya ka barni naji da abinda ke damuna, Zan gyara komai da kaina. "
"Khamis nifa mamaki ma kake bani, duk kulawa da takurawar da Kayi wa yarinyar nan, ya akayi haka ya faru da ita, me zaka iya gyarawa wadda bakayi shi tun da.
Wai ina zafin naka yake?
Ya akayi wani ya lalata mata rayuwa ba tare da ka sani ba?
Waye kuma ya aikata hakan?"
Katse shi yayi da cewa "Nima abunda nakeso na gano kenan, dole na tsaurara bincike dan gano wanda ya aikata Wannan aiki. "
"Good, amma kafinnan tau Rumasa'u Zata bar gidannan na gaya maka. "
A zafafe yace "Wai yaya so kake ka nuna min ba ciki d'aya muka fito da mahaifiyar Maisa ba, kana nufin bani da cikakken iko akanta ne, ko a tunaninka ka fini jin zafin abinda akayi mata ne. "
"Ko d'aya Khamis, idan ka manta in tuna maka ,nima ba ciki d'aya muka fito da mahaifiyarta ba.
Saboda haka ina magana ne a Matsayin d'an uwan mahaifiyarta wanda yasan zafin ta kuma babu bambanci tsakaninta yaranta da yaran da na Haifa, duk d'aya ne a guri na, so kasan abinda bakinka zai rika furtawa."
Sosae sukayi ta sa in sa ,kowa ya kafe akan ra'ayinshi.
K'arshe dai yayannashi ya fita ya bar mishi gida dukansu ransu ba dad'i.
Washegari da sassafe sai ga Abba babba da sauran yan uwansu sunzo gidan kawu khamis.
Ganinsu ba k'aramin tayar mishi da hankali yayi ba.
Baban Kabeer yaso ayi komai cikin rufin asiri ba tare da kowa yaji ba, amma abin ya faskara, dole ya nemo sauran yan uwanshi, dan ya kudurta a ranshi dole Rumaisa tabar gidan kawun .
Sosae Maganar ta girgiza su,lokacin da ya gama yi musu bayani, snn ya d'ora da buk'atarshi naso a d'aga Rumaisa daga gidan da kuma dalilanshi.
Dukansu sun gamsu da dalilanshi, sun San mai afkuwa ta riga ta afku, amma dole su d'au mataki saboda gaba.
Sam kawu yaki amincewa, tun Suna magana kasa kasa har hayaniyarsu ta fara shiga kunnen matar kawu, da sauri ta kora yaran su tafi makaranta, snn tazo ta lab'e dan jin abinda yake faruwa.
Ta kuwa Jiyowa kanta abinda ya d'aga mata hankali, ga kawu ya dage baza'a d'aga Rumaisa daga gidanba.
Bata San lokacin da tayi Wuff ta shige falon kawu ba, sai jinta suka yi cikin masifa tana cewa, " gwara ma ka barta ta tafi dan wallahi bazan zauna da karuwa a gidana ba."
Tass kawu ya d'auke ta da Mari, cikin b'acin rai, jikinshi har rawa yakeyi .
"Ba Mari ba ko kasheni zakayi bazan zauna da itaba, idan kuwa Zata zauna saidai ni nabar maka gidan. "
Ta fad'a cikin Kuka, kuma tana dafe da kuncinta da yasha Mari.
Yana huci yace "Uban wa ya hana ki tafiya, ga ki ga hanya, Alla raka taki gona,indan Rumaisa kike cewa baza ki zauna ba, Kiyi tafiyarki, Wannan matsalarkice. "
Cikin b'acin rai da d'inbin mamaki, Abba babba yace "Hamisu kana da hankali kuwa, Akan Rumaisa zaka rabu da uwar 'ya 'yanka, to, ba damu za'a yi Wannan rashin hankalin ba, Rumaisa kuma dole tabar gidannan. "
Da gudu ta fita daga d'akin taje ta kira mamanta a waya.
Gaba d'aya kawu ya fita hayyacinsa ya rasa wani mataki zai d'auka akan raba shi da Rumaisa da ake son yi.
Zama yayi dab'as a k'asa yace "Na yarda Zata bar gidan amma ku barni na maidata gurin mahaifiyarta da hanuna. "
"Idan ka mayar da ita Kace mata me, fad'a mata zakayi dan baka da hankali, idan abun bai baka kunya ba mu abun kunya ne a wajen mu ace duk yawan mu mun gagara rike Rumaisa, mun kasa bata Tarbiya, saida ta lalace muka mayar da ita, babu inda zata Je, mu nan zamu riketa mu aurar da ita da yardar ubangiji kuma cikin rufin asiri."
Suna cikin haka sai jin Maman matar kawu ta shigo tana bambami, ita dole a fitar da Rumaisa idan ba haka ba ta tafi da 'yarta.
Fita suka yi zuwa inda take ta fad'a suka shiga bata hakuri, shi kuwa kawu zama yayi cikin falon ya dafe kanshi.
Baban Kabeer ne ya shiga d'akin Maisa dake kwance tana ta Kuka kamar ranta zai fita, duk abinda suke yi tana jiyosu.
Abubuwa uku ne suka had'e mata,.
Ga takaicin abinda ya faru da ita .
Ga fita harkarta da Kabeer yayi. Snn
Ga kuma rikicin da iyayen ta sukeyi, wanda tunda take bata tab'a gani ko jin labari ba kuma duk ta dalilinta ake yinshi........
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*12*.
Da Sallama ya shigo d'akin, duk da ta gane mai sallamar hakan bai sa ta d'ago ba, sai wani sabon Kuka da ya kufce mata.
Duk da yaji zafin abinda ya faru amma Yana tausayawa Rumaisa dan cutuwa kam ta riga ta cutu, abin haushin shine rashin sanin wanda ya cutar da itan.
Zama yayi kusa da ita ya dafa kanta.
"Rumasa'u."
Bai saurari amsar ta ba, itama kuma bata amsa ba amma ta sassauta kukan.
"Kukan ya isa haka, sai kijawa kanki wata cutar, yanzu ba lokacin Kuka bane, dan kin riga kin b'ata wayonki, kin lalata rayuwarki, Kin cuci kanki da yaran da zaki Haifa nan gaba dan Suma abinda kika aikata saiya shafesu, tunda koyaya sai an gaya musu abinda uwarsu ta aikata, kuma dole ya musu zafi, idan ba wani ikon Allah bama su tsane ki. "
"Shawarar da Zan baki a yanzu itace ki dage da yawan istigfari, ki roki Allah gafara dan shi gafurur raheem ne.
Snn sharrud'an tuba sune, yin nadama akan abinda ka aikata, bayan haka ki k'udura a ranki baza ki kuma komawa zunubin da kikayi ba, kuma ki tsaya akan hakan har k'arshen rayuwar ki.
Wnn shine shawarar dazanbaki a matsayinki na 'yata. "
"Sai kuma abu na gaba yanzunnan ba sai anjima ba nakeso ki tashi ki tattara kayan ki Zan maida ki gidan Abba babba. "
Ba musu ta tashi ta fara tattara kayanta, tana sauke ajiyar zuciya, tass ta kwashe duk wani abinda ya zama mallakinta, ta cika akwatunanta uku , da babbar jaka d'aya.
"Na gama kawu."tace kanta a kasa, dan ita yanzu Kunyar had'a ido da kowa ma takeji.
Tayata yayi suka tattara kayan kaff, suka shigar cikin motar k'anin Su d'an autansu, daga nan ya umurceshi da ya kaita gidan Abba babba.
Saida suka ga fitanta hankalinsu ya kwanta suka daina tada jijiyoyin wuya, kafin mamanta ta tafi saida ta k'ara zugata akan kada ta sake a kuma dawo mata da Rumaisa gida.
Tunda kawu ya fahimci Maisa bata gidan ya tabbata Sun d'auketa, daganan ya tsiri fad'a akan banza da wofi, k'arshe ma Boys quarters ya koma a can yake Kwana.
*************
Tunda ta koma tabi ta takura kanta, ko yaushe tana kunshe cikin d'aki.
Sosae Mamma matar Abba babba take kokarin janta a jiki da kwantar mata da hankali.
Abu na farko da ta fara lura dashi game da Rumaisa shine, ko d'aurin zani bata iya ba.
Kullum cikin skirt, tops wando, three quarter, English gown, mostly kayanta English wears ne.
Idan ka ga atampa ,lace ko material, to d'inkin gown aka mata ko kuma riga da skirt.
Abu na biyu shine, babu abinda Rumaisa ta sani ta fannin girki, ko tafasa ruwa bata iya ba, ga d'an banzan ganda, bata son aiki sam.
Musamman Mamma ta aika aka saya mata atamfofi guda hud'u ta bada aka dinka wa Rumaisa.
Lokacin da aka nunawa Rumaisa kayan kamar ta fashe dan haushi, ji take kamar ta rusa ihu.
Gun koyon d'aurin zani, abin takaici abin dariya, idan ta d'aura ta fara tafiya saidai Aga ta wuntsila, sbd yadda zanin yake hard'e ta.
Saida aka dibi kwanaki masu yawa ta iya d'aura zani.
Maganar girki kuma saida da kyar ta yarda take shiga kitchen tare da masu aiki tana ganin yadda suke sarrafa kayan Abinci .
Shara, wanke wanke, wnn duk bata sansu ba, dan ko d'akinta tana da mai share mata shi a gidan kawu.
Hakan yasa Mamma ta hana kowa share mata d'akin da aka bata a gidan, gata kuma Sam bata son datti.
Tun tana Shara da mopping tana Kuka har tazo ta saba .
Wnn ba komai ya jawo mata shi ba sai rashin kula daga b'angaren mace wacce Zata zamo mazamin uwa,koda bata tare da Tata uwar, wacce Zata bata tarbiyyar da ya dace ace ta samu daga wajen Tata uwar, wacce Zata bata shawarwari game da abinda zai amfaneta a rayuwa.
Snn idan taje hutu Jigawa kuma mamanta bata damu da tasa 'yar tata a gaba dan ta gano matsalarta ba, sai tasata tayi ta zaga dangi 'yan uwan babanta, dan Ita a tunaninta Rumaisa tana samun kula da tarbiya yadda ya kamata, Shima Baban ta hankalinshi kwance dan gani yake 'yarshi bata da wata matsala, dan ba alamun hakan tattare da ita.
Sauk'in abunma Kabeer ya tsaya tsayin daka akan karatunta da haka zata taso ba sanin addini sosae, tunda malamin da kawu ya d'auko yake mata lesson a gida ma ya koreshi yace Shima bai yarda da shi ba.
Kewar Kabeer take sosae kamar tayi yaya, amma ganinshi ya gagareta, ko ta kirashi a waya kuma baya d'auka, kullum cikin zullumi da tuñaninshi take.
Gashi ba damar fita dan kwata kwata an hana ta fita ko kofar gida.
**********
Kabeer kam gaba D'aya ya koma wani iri, so yake lallai sai ya yakice Maisa daga zuciyarsa amma abin ya faskara. Wani irin zafi da rad'ad'i yake ji a zuciyarshi du lokacin da ya tuna da halin da ta jefa kanta ciki.
Duk iya kokarinshi, har da Addu'a ya ke had'awa Allah ya cire mishi Maisa a zuciyar shi, all to no avail ...........
Kawu ko ba karamar matsala ya shiga ba sanadiyyar barin ta gidan, ya zamto ko bak'i yayi, suna hira kallonsu yake kawai amma hankalinshi baya garesu.
Ko wani gurin yaje sai an gane yana cikin damuwa.
Gaba d'aya ya daina ma d'an uwanshi baban Kabeer magana, ko ya mishi baya amsawa.
Halin da matar kawu khamis ta shiga baya fad'uwa, dan gaba d'aya gidan ya zama kamar gidan makoki, duk yadda taso su daidaita da kawu ya ki saurararta.
Ba abinda yafi d'aga mata hankali irin yadda ya maida ita matar kulle ka'rfi da yaji, kwata kwata ya hana ta fita, ba damar taje gurin 'yan uwanta, ko gidansu ya hanata zuwa.
Tun tana tunanin abin na d'an lokaci ne har taga dai abin da gaske ne.
Kuka tayishi har ta gode Allah, har ciwo ta kwanta, yace ciwon na gulma ne ba maganin da zai sayo mata.
Kannenshi mata biyu wanda suke ciki d'aya ne suka zo gidan, suke tambayar basu ga Maisa ba .
Nan ta kwashe komai ta sanar dasu.
Salati suka shiga yi dukansu biyu kafin d'aya daga cikin su tace anya Dadda ta bar yaya Khamisu banza kuwa.
D'ayar tace, "Kuma fa da gaskiyarki, haka kawai bazai shiga damuwa dan an d'auketa daga gidanshiba, saidai in asiri ta mishi.
Subhanallah wato ma ba cikin da tayi ne ya damesu ba, damuwar d'an uwansu ya damesu.
Nan sukayi ta surutansu Suna cewa ya kamata ace Sun fahimci hakan tun farko dan gatan yayi yawa ko yaranshi basu samu gatan da suka samu ba, .
Har cewa suke idan ba asiri ba me yasa ba ya kulawa da 'yayansu Su da suka fito ciki d'aya.
Yanzu ai da tabar gidan zasu gane inma wani irin munafurcin suke kullawa asirin Su zai Tonu.
Har D'ayar tana cewa idan 'yar riko yake nema a cikin nasu yaran zasu bashi.
haka sukayi ta maganganu marasa dad'i akan Maisa da mamanta, kamar ba yan uwan da suke bala'in son juna da nunawa juna kulawa ba.
Musamman taje ta sameshi, yana ganinta had'e girar sama data k'asa.
Magana ta fara yi mishi a sanyaye kan Indan barin Rumaisa Gidanne ya ke damunshi haka, yaje ya dau d'aya daga cikin yaran kannenshi mata, ko kuma ita ta d'auko a yaran yan uwanta.
Hayayyako mata yayi kamar zai dake ta yana cewa babu wata shegiyar da za'a kawo mishi gida, kada ma ta kuma kawo mishi wnn zancen banzan.
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*13*.
Wata uku curr tayi a gidan ba tare da taje ko ina ba, tun abin na damunta dan ta saba da yawo har ta hakura.
Sosai take istigfari, tana me kaskantar da kai wurin ubangiji mahaliccin sammai da kassai.
Kawu kuwa duk lokacin da ya kira ta, ta d'auka bata iya yin magana mai tsawo dashi idan tayi kokari ta gaisheshi, daganan yayi ta surutanshi shi d'aya wani lokacin ta sa mishi Kuka, daga yaji tana Kuka kuma sai ya shiga rarrashi dan kukan ta ba k'aramin tab'a mishi zuciya yake yi ba.
Mamma kuma bata daina sata a hanya duk abinda tasan ya kamata ta sani, tana iya kokarinta wajen ganin ta koya mata.
Koda mamanta tazo daga Jigawa babu wanda ya sanar da ita abinda ya faru saidai tayi mamakin ganin Rumaisa a gidan Abba babba maimakon gidan kawu.
Da ta tambayi Mamma, sai ce mata tayi, sun fahimci kawu ya sangarta Maisa da yawa shi yasa suka d'auko ta idan ba haka sukayi ba haka zata ta zama ba tare da ta iya komai ba, dan can matar kawun bata koya mata komai.
Bata kawo komai a ranta ba, ta yarda da maganar Mamma dan itama shaidace akan irin shagwab'a Rumaisa da kawu yayi, ko Yaushe tazo sai tayi ta mata fad'a akan irin zaman da sukeyi da matar kawu, ita komai sai kawu ,matar da ya dace Su shaqu ta koya mata as abubuwa na mata, sam dukansu biyu sunki, ita matar kawu Tana jin haushin Rumaisa, Itako Rumaisa Tana biyewa kawu.
Shi yasa Maman Rumaisa take ganin wnn hukunci da suka yanke daidai ne.
Lokacin da tazo komawa Jigawa babu abinda ya canza na daga alkhairan da yake mata, wnn al'adar Su ce duk wacce tazo daga wani gari cikin yan uwansu idan Zata koma, kowa a cikinsu zai mata alkhairi dadai gwargwadon iyawanshi, kawu kuwa dama ya saba kyautatawar da yakeyiwa yayarshi wato mman Rumaisa ta daban ce, haka ma wnn Karon har yafi na kullum, har ta koma basu bari ta fahimci akwai wata matsala ba .
Gidan kawu yanzu ya gama watsewa dan duk yaran yan uwanshi samari da suke zama a gidan da masu zuwa su kwana biyu su tafi duk ya koresu daga gidan, yace a cikin su lallai baza'a rasa wanda ya lalata rayuwar Maisa ba, zargi harda d'an cikinshi akan Rumaisa.
Saida Maman matarshi tace za'a jisu a kotu idan ya kuma d'aurawa jikanta sharri, tukuna ya bar maganar .
Bayan komawar Dadda( Mmn Rumaisa) da wata guda, Baban Kabeer ya kirashi.
Saida ya mishi nasiha mai shiga jiki ya gama d'aure shi da jijiyoyin jikinshi snn ya sanar da shi kudurinshi nason had'a shi aure da Rumaisa, dan shi tsakani da Allah tausayi suke bashi daga Rumaisar har Kabeer, sbd ya tabbatar akwai k'auna mai ka'rfi tsakanin su, saidai shi yanzu Kabeer d'in abinda ya faru yasa ya fita harkarta, amma fa duk wanda yasan shi idan ya kalleshi da kyau yasan yana cikin damuwa duk da kokarin b'oyewar
da yakeyi.
Ta b'angaren Rumaisa ma ya fahimci abin haka yake dan ko Yaushe yaje gidan Abba babba sai ta tambayeshi labarin Bobbonta, hakan yasashi yin wnn shawara har ya sanar da mai Mahaifiyar Kabeer d'in, Tare da nuna mata amfanin yin hakan, da yake ita mai fahimta ce, kuma bata da Matsala yasa ta amince ba tare da nuna wata damuwa ba.
K'arfin hali Kabeer yayi ya nuna wa mahaifinshi ya amince.
Albarka yayi ta sa mishi kafin ya sallameshi.
Fita yayi ya koma d'akinshi yanaji zuciyarshi Tana mishi zafi, gaba d'aya fitar ma ta fice mishi a Kai.
Wani irin ciwo yake ji zuciyarshi nayi, bugawa takeyi kamar zata fito ,wani abu yaji ya tokare mishi mak'oshi, har wani d'aci d'aci yakeji.
Ba wai bayason Maisa bane, a'a, takaici da bak'in cikin abinda ya faru ne ya gagara barin zuciyarshi, ko a yanzu akace Maisa Zata auri wani bashi ba, yasan dole ya shiga damuwa, amma yanzu da aka ce shi zai aureta sai yaje jin ya shiga tashin hankali.
Ko da ya samu mahaifiyar shi da maganar, hakuri da ban baki ya samu daga gareta, k'arshe ta bishi da nasiha wanda ya sanyaya mishi jiki da zuciya.
Ba tare da b'ata lokaci ba suka je Jigawa wajen dangin mahaifin Rumaisa.
Sun samu tarba na karamci da mutunci.
Cikin mutunta juna suka gama komai na neman aure, basu ja lokaci mai tsawo ba suka sa watanni biyu masu zuwa.
Kayan lefe ma saidai Kabeer yaji labari ankai .
Sai da aka kai lefe, Mamma ta kirashi, akan tana da magana dashi.
Sam baiso haka ba amma babu yadda iya, dan yana mutuntata ba kad'an ba, ganin mahaifiya yake mata.
Ada ko wani bayan Kwana biyu yake zuwa gaisheta, amma tunda Rumaisa ta koma gidan ya daina zuwa, ko ya kama hanyar zuwa yana karya Kwana da Zata Sada shi da gidan ya ke jin matsanancin fad'uwar gaba, wadda yake tilasta mishi komawa babu shiri.
Daurewa yayi ya je gidan domin amsa Kiran Mamma.
Bayan ya gaisheta cikin girmamawa ta amsa cikin kulawa, shiru ya d'an biyo baya.
Nisawa tayi tace, "Kabeer. "
"Na'am Mamma. "
Yace ba tare da ya d'ago ba, dan jikinshi na bashi ko ya Akayi wnn kira yana da alak'a da Rumaisa.........
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie "Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
Wannan shafi nakine dan jin dad'in ki *Saudat Muhammad.* Fasaha online writers grp.
*14*.
"Da farko abinda Zan ce maka shine, Kayi hakuri, ka k'ara akan wanda kake dashi.
Ko ba'a fad'a min ba nasan baka ji dad'in hukuncin da iyayenka suka yanke akanka na auren Maisa ba.
Ka sawa ranka cewa haka Allah ya kaddara maka, idan ka yarda da kaddara sai Kayi hakuri kayiwa iyayenka biyayya sai Kaga abin ya zamo maka alkhairi.
Kai mai ilimi ne, ko ban tsaya fad'a maka ba kasan cewa mai cikakken imani shi ke yarda da kaddara, Walau mai kyau ko akasin haka.fatana dai shine Allah ya baka ikon cika burin iyayenka na ganin Rumaisa ta samu farin ciki da rufin asiri, wanda kuma ta wajen ka suke fatan hakan. "
"Bayan haka, sai kayi hakuri da halayen Rumaisa dan har yanzu yarinya ce. "
A ranshi yace "Yarinya indeed. "
Haka dai tayi ta bashi shawarwari da kwad'aita mishi falalar biyayyar da zai wa iyayenshi, har yaji zuciyarshi tayi sanyi.
Har ya tashi zai tafi, ta tambayeshi, bazaiga Rumaisar bane?
Sosa kanshi yayi cikin jin kunya ya ke tambayar ina take.
D'akin ta ta nuna mishi.
Tana cikin d'akinta taci Kwalliyar ta da dressing nata na fama. Body hug da trouser.
Taje sumarta take yi ta rabashi gida biyu, ta gama taje b'ari d'aya tanayin d'ayan b'arin taji muryar da baza ta tab'a mancewa ba a rayuwarta, muryar da ko cikin bacci taji zata gane maishi ,muryar da take kewa,da muradin jinsu a dodon kunnuwanta, muryar da take jin yafi ko wane murya dad'i. Yana Sallama kamar baison yi .
Wuff ta mike ta tsaya tana raba ido, kirjinta sai bugawa takeyi, tana fatar Allah yasa da gaske Bobbonta ne yazo gareta ba mafarki take ba.
Sallama yayi a karo na uku, snn ta amsa muryar ta yana shaking.
Wani abu yaji yana masa yawo a jiki, ba shakka yasan yayi missing wnn golden voice d'in.
"In shigo? "
Yace a dakile. Ba tare da ya san lokacin da maganar ta fito daga bakinshi ba.
"Bismillah tace tana jawo gyale domin rufe jikinta.
A hankali ya d'aga labule ya kutsa kanshi cikin d'akin.
Wani sassanyar kamshi ne ya Marabci hancinshi har yasashi lumshe idanunshi.
Bud'esu yayi ya sauk'e su kan fiskar ta, da ta Kara mishi kyau.
Kallon juna suka tsaya yi ,ji suke kamar sun d'ebi shekaru basu ga juna ba.
Shiru d'akin yayi kamar babu mai rai a ciki, sun jima Suna kallon juna kafin daga bisani ta katse shirun da cewa.
"Sannu da zuwa Bobbo. "
Sai a snn hankalinshi ya dawo jikinshi.
Saurin kawar dakai yayi ba tare da ya amsa mata Sannun da ta mishi ba.
Sallaya ta d'auka ta shimfida mishi tare da mishi Bismillah. Kallonta ya kumayi ya Kalli sallayar snn ya Tab'e baki, a ranshi kuma cewa ya ke, " dube ta kamar wata mutuniyar kirki. "
K'asa tayi da Kanta ganin yadda lokaci guda ya canza fiska, yana wani yatsina kamar yaga abin kyama.
"Waya ce miki zama nazoyi cikin wnn kazamin d'akin naki,
Idan zuciyarki tana raya miki cewa son ganinki ne ya shigo dani nan gara ta dena, dan banga abin gani Anan ba.
Da yake kuma kin cika cikakkiyar 'yar iska shine kikasa wad'annan kaya a cikin gidan mutane, ko wani d'an iska ma ya ganki a haka ko.
Kuma dan rashin sanin ciwon kai shine da nace in shigo kika wani ce Bismillah kamar dama jira a shigon kikeyi, haka kenan kike barin ko wani Gardi yana shigo miki d'aki kina sanye da irin wad'annan sutura ko kunya babu sbd rashin kamun Kai.
Kai nidai Su Abba sun gama dani da suka rasa wacce zasu aura min duk yawan matan garinnan saike Maisa. "
Ya k'arasa maganar yana nunata da yatsa tare da yi mata kallon kaskanci.
Durkushewa tayi a gun ta fashe da kukan bak'in ciki ,ji take kamar ta hadiyi rai ta mutu akan irin munanan kalaman da Bobbonta yake jifanta dasu.
Cikin sauri ya fice daga d'akin, dan bazai juri jin kukan ba. Har yana tuntub'e .
Sai da taci kukanta ta koshi snn ta mik'e taje ta wanko fiskarta tare da d'auro Alwala, dan nemawa kanta sassauci a gurin Allah Ta'ala.
A hanyarsa ta komawa gida yake zancen zuci,"Allah ne ya taimakeni da ba'a ce za'a bawa wani ke ba Maisa da bansan yadda rayuwata Zata kasance ba.
Sajenshi ya shafa yace "I really love you Baby Maisa. "
Sai can kuma yaja tsaki, shi Sam ya rasa yadda zaiyi da wnn b'acin rai da yake zuwa mishi duk lokacin da ya tuno ta," Allah ka kawo min sauk'i. "
Ya ce a fili.
Tun daga ranar basu kuma had'uwa ba sai lokacin bikin su.
Sun yi kokarin ganin Sun b'oye duk wata damuwa da suke ciki a gaban Jama'a, sbd da haka har akayi bikin aka gama babu wanda ya fiskanci akwai wata matsala.
Lafiya akayi biki aka gama, aka kai amarya gidan angon ta dake anguwar Millennium suite....
Har kawaye suka watse ba'a ga idon ango ba sai abokanshi, haka suka bar amarya ita kad'ai cikin katon gidanta.
Tsoro duk ya isheta,tun tana Kuka har idanun suka bushe daga baya bacci yayi awon gaba da ita.
Tun da tazo gidan yau Kwana biyu bata sashi a ido ba, bata da masaniya akan gidan take Kwana ko kuwa, ita dai sunanta matar gida, kuma amarya.
*Toh ko wani irin zamane Bobbo Kabeer zasuyi da Amarya Baby Maisa.*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Wannan shafin nakune masoyan Zumuntar zamani duk inda kuke, na gode da k'aunarku gareni.*
*15*.
A ranar da ta cika Kwana uku da safe tana kwance kan sallaya dan tun da ta idar da sallar Asubah bata tashi ba.
Sai ji tayi an turo k'ofa.
A razane ta tashi tana kallonshi dan jin da wanne ya shigo dan itakam yanzu halayenshi tsoro suke bata kamar ba Bobbonta da ta sani mai sonta da k'aunarta ba.
Murmushi ya sakar mata, wanda ya saukar mata da kasala.
kasa maida mishi martani tayi dan tasan yanzu ya dizga ta ba damuwarshi bane.
"Baby Maisa Amaryar Bobbonta. "
Taji yace still bai bar murmushin ba. Ita dai nata ido, tana jira taga k'arshen rainin hankalinshi.
"Well, kina ta murna kin zama matar Bobbo ko? "
Ya fad'a yana d'age girarshi d'aya.
Sai kuma ya girgiza kai yace "Saidai ni kuma akasin hakanne dan ina cikin bakin cikin had'a mu da akayi, hakan ya sani zazzafar zazzabi, duk sbd aurenki da nayi.
Kin cuce ni Maisa, kin kuma cuci kanki.
A da ,bani da wacce nake k'auna da so da kuma burin ta zamo uwar 'ya'yana kamarki Rumaisa."
"Amma yanzu" Saida ya tab'e baki yana girgiza kanshi snn yace "bani da wacce na tsana nakejin kamar na shake na kashe ko Zan huta da bak'in ciki sai ke. "
Zaro ido tayi tana kallonshi hawaye har sun fara wanke mata fiska, a ranta take cewa "abin har yakai ga kisa? Lallai yanzu ba k'aramin kiyayya Bobbo yake min ba."
Cikin Kuka tace "Bobbo dan Allah ka gafarceni, idan bazaka iya zama dani ba, kada mu bawa kanmu wahala, ni daga nanma ko gida bazan koma ba, balle ayi tunanin sake dawo maka dani, Zan yi nesa dakai ta yadda bazaka kuma ganina ba balle ranka ya rika baci."
Ta k'arashe maganar cikin matsanancin Kuka.
"Really, zaki iya nesa dani Ashe. "
Ya tambaya yana kallonta.
Gyad'a kai ta shigayi kamar kadangaruwa. "Zan iya Indai hakan zai kawo maka kwanciyar hankali. "
Jikinshi ne yayi sanyi, a zuciyarshi yake Tunani, yanzu Maisa Zata iya yin nisa dashi kamar yadda tace, idan Zata iya shikam bazai iya ba, gwara suyi ta zama a hakan.
Kallonta yayi yaga har yanzu kukan take amma k'asa k'asa.
Zama yazo yayi tare da hard'e k'afa yana fuskantarta, ji yake kamar ya yi hugging d'inta ya rarrasheta amma wancan muguwar zuciyar tashi tana hana shi aikata hakan.
Basarwa yayi da cewa "Well, niba dogon surutu nazo muyi dake ba, na zo ne dan na gindaya miki sharrud'an zama a gidana. "
Na farko, kinsan bana son kazanta, ko kad'an kika kuskura naga datti a gidannan ranki zai b'aci .
Dan naji labarin, babu abinda kika iya na aikin gida sai shashanci, har wani cemin ake min ke yarinya ce tsabar ke shagwababbiya ce.
Na biyu ban yarda da yawan fita ba kuma bazan lamunci a shigo min da k'ato gidana ba.
Idan zaki dafa abinci ki dafa dadai cikinki banda ni, dan bazan ci jagwalgwalo ba.
Idan kina bukatar wani abu, zaki iya tambaya, ko Meye shi.
Lastly wnn 'yan iskan sutura da kike sakawa, bana son ganinki dasu dan nan ba gidan 'yan iska bane.
Idan kunne yaji........
Yana gama fad'ar haka ya tashi yayi ficewarshi ya barta da tunani.
Duk abinda ya lissafa tasan Zata jure ta yi, amma banda sutura, dan takurar zaiyi yawa.
ita kad'ai cikin gida ace ta takura kanta tayi ta saka manyan kaya, wnn ne kawai za'a samu matsala.
Haka zamansu ya kasance kullum da kalar bak'ar maganar da yake yab'a mata.
Ayyukan gida kuwa tun tana yi jikinta na mata ciwo har wahala yabi jikinta, ga gida ba k'arami ba. Kuma babu mai taimako.
A haka yan uwansu suke zuwa su sameta kullum cikin aiki ba hutu, har wasu suka fara magana akan hakan.
A cikin hakanne kawu khamis yaji labari yayi tattaki yazo har gidan Kabeer dan ya ganewa idanun sa abun da yake faruwa.
Da fatan baku manta abinda zuwan kawu ya jawowa Rumaisa ba.
*Mu koma labari.*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*16*.
Tana fitowa daga toilet, ta had'a Zufa tayi sharkaf, tana gaisawa da mutane be amma Sam hankalinta baya jikinta.
Ba abinda yafi d'aga mata hankali sai da taji Mamma tana cewa," Maisa kam bata San Amminta tazo bane?"
Da sauri ta fara dube dube tana neman ta inda Ammin tata take.
Kakaro fara'ar dole tayi, tana nuna farin cikin ganin Ammin.
Sai lokacin ta gane taruwar 'yan uwansu a gidan bazai rasa nasaba da zuwan Ammin ba . Relief ta d'an fara ji yana shiganta.
Bata ida tunaninta ba, Faisal autan Abba babba ya zo yace mata ana Kiran ta a falon Abba babba.
Cikin sanyin jiki ta tashi taje. tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ganin haka ne yasa Mamma ta tashi ta bita a baya.
Saida aka bata izini snn ta shiga falon.
Kawunanta ne da pendonayenta dankam a cikin falon.
Wani sauti cikinta ya bada, kamar ta zura a guje take ji.
Ta waiga ta Kalli bayanta taga Mamma na biye da ita, hakan ya d'an bata kwarin gwiwar isa gurin da suke zaune.
Gaishesu tayi d'aya bayan d'aya, snn tayi k'asa da kanta.
Kurr kawu ya kure ta da ido yana mai jin takaicin yadda ya ganta kamar bata cikin hayyacinta.
Iyakacin Su iyayen ne kawai babu Yara a cikinsu sai Kabeer da Rumaisa.
Da Addu'a aka fara snn Abba babba ya fara magana kamar haka:.
"Kabeer, Babanka Hamisu ya kawo mana karar ka, akan kana wulakanta Rumasa'u.
Duk da dai bamu san laifin da ta yi maka ba, amma abin bai mana dad'i ba, shi yasa muka kira taron gaggawa, sbd musan wani irin zama kukeyi,gani ga sauran iyayenka."
Babu abinda Baban Kabeer yakeyi sai zabgawa Kabeer harara, Shiko Kabeer ya Duk'ar da kanshi, tun ganin farko bai kuma yarda sun had'a ido da Babbanashi ba.
"Bismillah, muna sauraronka. "
Cewar Abba babba.
Kanshi a kasa yace "Babu abinda tayi min. "
A kufule Babanshi yace "Tsabar cin zali ne kawai kake zalintarta? Ko kuma.....
Dakatar da shi Abba babba yayi ta hanyar d'aga mishi hanu. Ya sake maida dubanshi ga Kabeer.
"Ina jinka, babu abinda take maka auran ne baka so, ko itace bakaso?"
Girgiza kanshi kawai yayi ba tare da ya yi magana ba.
"Idan baya sonta ,ai ba dole ba sai ya sawwake mata ba."
Cewar kawu Yana huci, ji yake kamar ya makure Kabeer ko zai samu sassaucin abinda yake ji.
Shima Kabeer cikin jin haushin Baffan nasa ya ce "Ba Zan rabu da Maisa ba, sai dai..... "
K'asa ya sake yi dakai yana jin nauyin maganar da yake so yafad'a.
"Sai dai me? "Abba babba ya tambaya.
"Abba, ku gafarceni, amma inason aja wa Baffa kunne kada ya kuma zuwa gida na, Wlh banaso na sake ganinshi kusa da Maisa......
Maman Maisa da hankalinta ya gaza Kwanciya da wnn meeting da akeyi ba a gayyaceta ba, ga kuma sauran yan uwanta a ciki, ga gudan jininta.
Sulalewa tayi ta nufi falon, tana isa K'ofar taji Abba babba na cewa.
"Bamu fahimceka ba Kabeer, mu iyayenka ne bakaso muje gidanka ko yaya?
Kad'a kanshi yayi ba tare da ya d'ago ba yace "Baffa khamis ne bana so yaje gidana, sbd yana so ya kashemin aure. "
Hayayyako mishi kawu yayi "Kaji d'an iskan yaro, ni d'in ne zan kashe maka auren, bayan wulakanta matarka da kikeyi, ka kiyayeni Kabeer, Zan b'alla ka in b'alla banza wallahi. "
Gaba d'aya jikin baban Kabeer ya gama mutuwa ,zuciyar shi ta fara halarto mishi da wani bahagon Tunani.
Suko matan har sun fara zagin Kabeer, a ganin Su raini ne irin na d'an yau, idan ba haka ba mutumin da Maisa ta girma a hanunsa, ya zamo kamar mahaifinsa, ya nuna mata dukkan gatan,yace bayaso yaje inda take.
Abba babba ne ya dakatar dasu daga surutan da sukeyi har sun fara d'aga murya.dan shi ma ya fiskanci kamar akwai matsala mai girma dan shi a iya saninshi bai San Kabeer da rashin Kunya ba balle kuma ga iyayensa.
A nitse yace "Kabeer, kada ka kuskura ka mana wasa da zumuncin mu, ba'a tab'a irin haka a wnn family ba kuma a kanka baza'a Fara ba, so nake a yanzu ka fad'a min dalilinka na muzgunawa yarinyar nan da kuma dalilin cewa kada Baffanka ya kuma zuwa gidanka. " ya k'arasa maganar a zafafe.
"Abba, duk dalilan Maisa ta sansu ,zata kuma yi bayani da bakinta. "
A harzuke kawu ya Mike "Kaga, bamu son iskanci, kai aka tambaya ba Maisa ba sbda haka Kai muke jira ka bada amsa d'an iskan yaro mara mutunci, wanda bai San girman na gaba dashi ba. "
Tafasa zuciyar Kabeer yakeyi sbd jin irin tijarar da kawu yake mishi, ita ko Maisa cewa take a ranta inama da Zata iya b'acewa daga gurin da tabbas za'a neme ta a rasa.
Bata ida tunaninta ba taji Kabeer yana cewa "Maisa, a yau, a wnn guri, a yanzu a gaban kowa nake so ki fad'i wa ya miki ciki.........
*Turkashi.😳😳*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Dedicated to my other half.
*Nafeesat Abdussalam (Mrs Bashir Bello.)*
*17*.
Wani irin tsinkewar zuciya da fad'uwar gaba Mmn Rumaisa ta tsinci kanta ciki, kamar yadda ya kasance Maisa.
Sauran wad'anda basu san da labarin cikin bama maganar tazo musu a bazata, ciki, a cikin familynsu, babbar magana.
Tunani Maisa ta shiga yi lokacin da tayi accident tana kwance a hospital bed .
Shigowa Kabeer yayi fiskarshi a murtuke kamar bai tab'a dariya ba, sosae yanayin fiskar shi ya tsorata ta dan bata tab'a ganin shi cikin wnn yanayi ba.
Idan ba idontane ya gane mata ba daidai ba kamar ma Kuka yayi dan idonshi yayi ja sosae.
"Tashi ki zauna. "Yace da ita.
Ba musu ta mik'e ta zauna.
"Zan tambayeki, wallahi idan kikayi min karya ,kinga wnn?"
Ya fito da wani ruwan magani yana nuna mata.
"Kasheki xanyi dashi kuma in kashe kaina , kina jina?"
Kai ta gyad'a tana kallonshi a tsorace.
"Ya akayi kika samu ciki, ubanwa ya miki shi?"
"Ciki? "
Ta fad'a gami da zaro ido.
"Kada ki ce min baki sani ba, nasan kin san dashi."
Wani irin juyawa taji d'akin yake mata, take taji jiri na d'ibanta daga zaune.
ita da mutuwar ma tayi a yanzu zai fiye mata akan wnn ritsata da Bobbonta yayi, kuma abun takaice babu wanda ya gano cikin sai shi.
Amma zancen ya kasheta da hanunshi kam bata taso ba.
Katse mata tunanin taji Kabeer yayi da cewa "Ba zaki fad'a ba kenan? "
Binsu Abba babba tayi da Kallo ta maida kallonta kan Kabeer ya galla mata muguwar hararar da yasata Duk'ar da Kai ba tare da ta shirya ba.
Tunowa tayi da alk'awarin da ta d'aukar mishi, lokacin da ta sanar da shi uban cikin.
Da ta nemi yi mishi k'arin bayani yayi saurin dakatar da ita da cewa "Ba nason jin komai daga gareki a yanzu, alk'awari d'aya nakeso ki d'aukar min. "
Cikin sauri ta d'aga Kai.
"Duk lokacin da na bukaci ki bayyana wanda ya miki ciki, zaki fad'a ko da a gaban wayene. "
"gyad'a mishi kai tayi.
"Da baki zaki yi min magana ba da kai ba munafuka, kinyi alk'awarin? "
Da sauri ta ce "Nayi. "
"Rumasa'u. "
Abba babba ya dawo da ita daga kogin tunanin da ta afka.
"Kinyi shiru, ke muke saurare?"
"Kawu ne. "
Tace bayan ta sunkuyar da kanta jikinta kuma sai b'ari yakeyi.
Difff gurin yayi, kowa ya zuba mata ido kamar Suna jiran k'arin bayani.
"Wani kawun? "
"Kawu khamis. "
Tace cikin rawar murya.
Salati kowa ya d'auka banda kawu da ya kafe Kabeer da ido kamar ya cinyeshi d'anye .
Cikin kid'ima Baban Kabeer yace "Garin ya haka ta faru, me yasa baki sanar mana ba tun da farko. "
A sanyaye tace "Cewa yayi zai kashe Bobbo idan na fitar da maganar. "
Salati aka kuma d'auka, masu inna lillahi, suna yi, masu, Hasbunallahu ,suna yi, masu Subhanallah Suna fad'a duk dai addu'ar da ta fito daga bakinsu yi sukeyi, dan ba shock suka ji ba.
Kabeer kallon Rumaisa ya shigayi da mamaki, wai dan shi ta bari aka lalata mata rayuwa.
Bai Ankara ba yaji an mishi mummunar shaqa.
Kawu ne ya shaqeshi yana surfa mishi zagi "Shege tsinanne, nasan wnn duk munafurcin ka ne, kai ka shirya wnn munafurcin. "
Cikin azama da b'acin rai Abba babba ya d'auke shi da wata lafiyayyar Mari, ni da nake labe saida na dafe kumatuna.
"Sakar min wuyan d'a khamis tun ban baka mamaki ba,
Kaiconka khamis Kayi asara, 'yar cikinka?ka b'ata mana sunan Zuri'a."
Shi yasa yarinyar nan tayi Yunkurin guduwa har sau biyu, da yake Kai munafuki ne, Ka taramu ka mana k'aryar cewa wani ne yake hure mata kunne, ko tsoron Allah babu, kasa muka takurata muka sata zama a gidan ka ka cuci yarinya a banza, ka zalince ta. "
Ya k'arashe maganarshi da kukan bak'in ciki.
"Ba shakka biri yayi kama da mutum. "
Abinda Baban Kabeer yake ta maimaitawa kenan yana karkad'a k'afa.
Kowa a wajen jikinsa yayi sanyi zuciyar su baki Kirin.
Niko nace, yo dama me kuke tsammani, wnn irin Mulki da Maisa take zubawa a gidan kawu na banza ne?
Ina Kuka tab'a ganin namiji kad'ai yayi tarbiyar 'ya mace ba tare da mace 'yar uwarta ba.
Wnn shak'uwa tasu ta banza ce,?
Wa yafi qarfin sharrin shaid'an ,sai wadda Allah ya tsare.
Allah kasa mu fi qarfin zuqatanmu.
Da k'arfi Kabeer ya fincike daga rikon da kawu ya mishi da su biyu ne kawai a gurin shima babu abinda zai hana ya shakeshi har sai yaji Kamshin lahira.
Fad'uwar da suka ji daga k'ofar falon ne yasa su duka maida hankalinsu wajen.
Maman Rumaisa ce ta yanke jiki ta fad'i tsabar yadda maganar ta kad'a ta.
Kusan a tare duka sukayo kanta,
Maisa dake rusa Kuka tun d'azu, ta sake k'ara k'arfin kukan ta tana kiran Amminta.
Kabeer ne yasa hanu ya......
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W..
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*18*.
Ciccib'eta ya fita da ita, sauran suka rufa mishi baya.
Da mamaki mutanen cikin gidan suke binsu da Kallo, har suka fice.
Adda binta tayi saurin binsu tana tambaya, ina duk hankulansu sunyi nisa, babu wanda ya kula ta cikinsu, da gudu ta juyo Zata shiga gida sukayi karo da Maisa.
Rik'e Maisa tayi tana tambayar abunda ya faru, Maisa ba magana sai kuka.
"ya salam ."tace snn ta kuma cewa "Maisa me ya sami goggo? Kabeer ya sakeki ko?"
Dan ita a tunaninta Kabeer ya saki Maisa ne yasa mmnta shiga wnn hali.
A ranta take cewa "Ba dole ba kwata kwata ma auren wata nawa ne har an rabu, dole goggo ta shiga damuwa. "
Fad'awa jikinta Maisa tayi tana mai ci gaba da kukanta.
A sanyaye tace "Kiyi hakuri Maisa, Allah yasa hakan alkhairi ne, Allah ya ba goggo lafiya. Amma Kabeer bashi da mutunci Wlh. "
Da sauri ta shiga girgiza kai "Ba laifinshi bane Adda, laifi na ne. "
"Ke dalla tafi can wani irin laifinki, duk zaman hakurin da kikayi dashi ya rasa sakayyar da zai miki sai ta saki. "
"Adda, Bobbo bai Sakeni bafa."
Ta fad'a cikin Kuka.
"Ha'a, to me ya farune wai fad'a min man Maisa. "
"Ammi na, zanje na ga halin da take ciki. "
"Yanzu ina kikasan suka nufa da ita. "
"Adda, bazai wuci asibitin su Bobbo bane."
"Jirani mu tafi tare. "
Ko da suka isa basu sha wahalar nema ba dan kusan rabin familyn duk suna wajen har da wad'anda basu je gidan Abba babba bama sun ji labarin ciwon Dadda.
Kowa ka gani hankalinshi tashe sai jajanta zancen ake tayi, wad'anda basu san abunda ya faru ba sai Tambaya sukeyi.
Sun d'auki lokaci mai tsawo kafin aka samu ta farfad'o dan mata kam har sun fara Kuka, mazan ne, suke ta kwantar musu da hankali tare da tabbatar musu tana raye da yardar ubangiji kuma zata samu lafiya.
Tare suka fito shi da wani doctor dukansu share gumi sukeyi, mutanen gurin kaff suka zuba musu ido Suna jiran su karaso Su musu bayanin halin da take ciki.
************
Gida kawu ya koma, cikin tashin hankalin da bazai misaltu ba, sosae yake jin haushin Kabeer dan shine silar tonuwar asirinshi, snn a tuñaninshi Kabeer shi ya jawowa 'yar uwarshi ciwo.
So yake ya bisu asibitin amma Yana tsoron abinda bin nasu zai jawo.
Dan yasan yanzu kowa yasan abunda ya aikata, kuma sun gaskata hakan tunda daga bakin uwar gayyar maganar ta fito, kenan ba damar musu.
A b'angare d'aya na zuciyarshi kuma har yau har yanzunnan yana jin bak'in cikin raba shi da Maisa da akayi, sbd har yanzu shaid'an bai bar kawata mishi Maisa ba, har yau k'aunarta da sha'awarta Suna nan manne cikin zuciyarshi shi yasa ka bai ji zafin tona mishi asiri da tayi ba, duk laifin Kabeer ya daurawa.
A zuciyarshi ji yake inama da aure tsakaninsu da Maisa da babu abinda zai hana shi aurenta.
😲wnn irin bala'in da me yayi kama.
Allah ka tsare mu da sharrin shaid'an kasa Mufi qarfin zuqatanmu.
Gaza hakura yayi ya d'au wayarsa ya fara dialing numbers d'insu d'aya bayan d'aya, abin da takaici babu wadda ya d'auka a cikinsu.
Dan Suna can hankali a tashe duk wanda yaji wayarshi tayi ringing idan yaga shine sai yaja tsaki yayi ignoring. Sbd dukansu zafinshi suke ji.
Haka yayi tayi har ya gaji gashi hankalinshi ya gaza Kwanciya, so yake yaji halin da take ciki.
"Hindu. "Ya kwala wa matarshi kira da karfi kamar muryarshi zai tsage.
A guje ta Iso tana amsawa da jin yadda muryarshi take babu alamar Rahama a cikinta, duk a tsorace take, tana tunanin yau kuma da wanne ya shigo.
Gashi dama tasan tayi mishi laifi dan yace taje ta Marabci Daddanshi, har ta amsa zata je, yana fita ta kama harkokinta tana mitar, tunda ya hanata zuwa wajen danginta ita ma babu gurin d'an uwanshi da Zata kuma zuwa har sai ya gaji ya barta ta fara zuwa wajen nata.
Fiska a had'e shi nan baya so ta raina shi.
"Shirya kije ki duba min Dadda a specialist hospital, idan kin isa kuma immediately ki kirani ki gaya min halin da take ciki. "
"Dadda bata da lafiya ne?"
Ta tambaya tana nuna alamun tausayawa.
A masifance yace "Ban sani ba Hindu, kin tab'a ganin inda lafiya yakai mutum asibiti, malama idan zaki je ki tafi kawai idan baza kije ba kuma ki sanar da ni. "
Har itama zata mayar mishi da martani akan baza taje ba d'in sai kuma wani tunani ya fad'o mata ta fara tambayar kanta.
"Me yasa shi bazai je ya dubo ta da kanshi ba?
Cikin sauri ta tashi tana cewa a ranta koma menene idan naje Zan ji.
Har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo da baya.
"wani ward take?"
"kar ki dameni Hindu ban sani ba. "
Tab'e baki tayi ta tafi ta kama shiri sauri sauri ta gama tazo ta tsaya a kofar falon shi, kallonta yayi zaiyi magana ta rigarshi da cewa "Transport. "
'yar karamar tsaki yayi kafin ya zura hanu a aljihu ya ciro dari biyar ya jefa mata.
Isa tayi ta d'auka a ranta take cewa "Masifaffe kawai. "
Ta fice.
***********
Gurin mazan d'ayan doctor ya nufa Shiko Kabeer ya k'arasa wajen matan, dukansu suka yo ca akanshi Suna tambayar ya take dadai Isowar matar kawu wajen.
"Alhamdulillah da sauki, sai dai BPn tane ya hau sosae yanzu bacci take, insha Allah Zata samu lafiya. "
Ya fad'a fiskarshi ba walwala snn kuma yana binsu da Kallo d'aya bayan d'aya.
Akan Adda binta ya Tsaida idon shi, da idon yake tambayarta Maisa.
Ganin bata fahimceshi ba ya mata da hanu.
Waige waige ta fara yi alamar neman Maisar da mamaki d'auke a fiskarta dan ita duk tunaninta Suna tare da ita.
Gefe ya koma ta bishi a baya.
"Kabeer tare fa muka zo da ita, d'azu dazunnan ma na gama bata baki dan Kuka take tayi tunda muka zo. To ina ta shiga,?ko ta koma gida ne? "
Duk ta jera tambayoyin a kid'ime.
Shiru yayi kamar yana tuna wani abu sai yace mata "ina zuwa bari inje masallaci. "
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
This page is yours .
*Jamila U.Nyaja.(Mmn Al-Mustafa.)*
Allah ya bar zumunci.
*19*.
Sosae yayiwa goggonshi addu'ar samun lafiya, bayan yayi sallah, snn ya k'ara da neman zaman lafiya tsakaninshi da Maisa da kuma addu'ar Allah ya sanyaya mishi zafin da yakeji game da ita.
Kamo hanya yayi dan dawowa cikin asibitin yana mai fatan Allah ya sa ya samu Maisa agun Su Adda binta.
Idonshi ne ya sauk'a a kanta tana zaune a kasan wata bishiya ta gefen masallacin, kanta a kasa ta k'urawa k'asa ido ko kiftawa bata yi.
A tsanake ya isa wajenta, har ya isa bata d'ago ba balle ta nuna tasan da mutum a gurin.
Dafata yayi ta d'ago ta kalleshi, Suna had'a ido tayi saurin Kawar da nata.
Saida ya tsorata ganin yadda idanun ta suka kumbura suka yi Ja da alamun Kuka tayi ba kad'an ba.
Ta gurin da ta maida fiskarta ya koma tasake Juyawa d'aya b'arin ,wasu Sabbin hawaye suna sake fitowa daga idanunta.
D'agota yayi ya mik'ar da ita, gaba d'aya ta saki ba ka'rfi a jikinta, dama jirine yasata zaman gurin bayan tayi sallah.
Hawayen ya shiga d'auke mata da yatsunshi, snn ya kamo hanun yana kallon cikin idonta.
"Kinyi sallah? "
Tambayar da yayi mata kenan.
Kai kawai ta gyad'a mishi. Ba tare da Shima ya sake magana ba ya fara tafiya still yana rike da hanunta, hakan yasa ta kama binshi kamar rakumi da akala.
Har suka isa wajen babu wanda ya kuma cewa uffan a cikinsu, ba tare da ya Kalli kowa ba ya jata suka wuce inda aka kwantar da Mmn Maisa.
Binsu da Kallo mutanen wajen dukkansu a sanyaye suke sun zama abin tausayi.
Har bakin gadon ya isar da ita snn ya saki hanunta ya jawo kujera kusa da ita ya mata nuni da ta zauna.
Kurr ta k'urawa mamanta ido tana tunanin duk a kanta mmnta ta shiga wnn hali.
Tana kallon mamanta shi kuma yana kallonta.
Wa yaga kallon mai Kallo.
Tun tana kokarin mayar da kwallar da suke shirin zubo mata har suka yi nasarar zubowan.
Sosae take kukan bak'in ciki halin da ta shiga ta kuma jefa mahaifiyarta ciki.
Ji yake kamar ya tayata kukan dan dai shi namiji ne bai kamata ya dad'a karya mata zuciya ba.
Ba tare da yayi mata magana ba ya sake d'agota ya jata suka fita daga d'akin.
Direct gurin motarshi ya nufa da ita, saida ya bud'e mata ta shiga snn Shima ya zagaya ya shiga.
"Maisa."Ya kira sunanta cikin dakusasshiyar murya, bata amsa ba amma ta d'an Tsagaita kukan da takeyi.
"Kalleni nan. "
Ya kuma ce mata.
A hankali ta d'ago tana kallonshi hawayen kuma basu daina tsere kan fiskarta ba.
Handkerchief yasa yana goge mata hawayen.
"kukan kike so nima nayi ? "
Ya tambaya still yana goge mata hawaye.
Girgiza kai tayi alamar A'a.
"To ya isa haka Kiyi hakuri ki bar kukan haka nan, da wanne kikeso muji da ciwon goggo ko kuma da wanda kikeso ki jawo mana yanzu. "
Shiru tayi tana kallon hanunshi dake rike da hand k. D'in.
"Nasan kina jin yunwa muje kici abinci ko? "
Girgiza kai tayi snn cikin disasshiyar murya tace "Bana jin yunwa, Zan zauna gurin Ammi na. "
K'ara d'aure fiska yayi yace "Idan kinga kin dawo wajenta kinci kin koshi ne."
Shiru tayi dan bata da ta cewa.
Saida ya biya ya musu take away snn suka wuce gida.
Kusan d'uren Abincin ya mata duk da shi d'in ma ba dad'in Abincin yake ji ba.
Da lallami da fad'a haka suka yi ta fama har ya samu taci ta koshi.
Tana gama ci ta mik'e "Bobbo na koshi mu koma to. "
Girgiza kanshi yayi "Sai kinyi wanka, in fact ma sai muyi sallar maghrib zamu koma, dan naga alamar ciwo kike so ki kirawa kanki.
Babu yadda ta iya haka ta shiga d'akinta da niyyar Wankan kamar yadda yace.
************
Bayan matar kawu ta kirashi ta sanar da shi abinda Kabeer ya fad'a game da Mmn Maisa, sai ta fara tunanin yadda zatayi tambaya taji musabbabin ciwon.
Ta d'an d'auki lokaci tana jira taji ko wani zaiyi k'arin bayani yadda Zata fahimta amma shiru ,hakan yasa ta kamo hanun kanwarshi d'aya ta mata alamun zasuyi magana.
Saida suka keb'e gefe matar kawu ta tambayeta musabbabin ciwon tunda dai tasan ance tazo kuma lafiya qlau.
D'an jimm Kanwar tayi tana tunanin kamar kada ta fad'i gaskiya sai kuma ta tuna watakil matar kawun ma ta sani tunda cikin gidanta abin ya faru, ta iya yiyuwa shi yasa ta dage sai Maisa ta bar mata gida.
Cikin Jimami tace "Nikam Hindu da gaskene ya khamis shi ya wa Maisa ciki?"
Zaro ido matar kawu tayi kamar zasu zazzago su fad'o k'asa.
Dakyar ta iya bud'ar bakinta tace "Ke zali ina Kika jiyo wnn labari. "
Zali da ta tsorata da yanayin matar kawu sai ta waske da cewa, "Share kawai jita jita ne irin na mutane muma ji mukayi. "
Tana gama fad'ar haka ta fara k'okarin barin wajen.
Da sauri matar kawu ta riko"Dan Allah zo kimin bayani yadda zan fahimta, to ko shi yasa yaki zuwa duba ta ya turo ni."
"Ba dole ya turoki ba an mishi k'azafin da yafi qarfin shi. Wai Maisa dai 'yar da ya fifita akan 'ya'yanshi ake mishi k'azafin shi ya lalata ta. "
Zali ta k'arasa maganar kamar zata yi Kuka dan itama abun ya dameta, kuma tsakaninta da Allah tana tantamar cewa kawu ne ya aikata gani take abin kamar shiri ne amma ba damar ta furta tunda sauran yayyunta sun yarda da maganar.
Da dai matar kawu bata samu takamemmen abinda takeson ji ba sai ta kyaleta.
Komawa sukayi suka zauna a inda sauran 'yan uwansu suke.
Mamma da mamar Kabeer ne suka Iso da Manya manyan kulolin abinci dan Mamma ta koma gida dan kawo Abincin data nan suka had'u da mamar Kabeer da tazo yiwa Dadda Sannu da zuwa bata samesu ba taji labarin sune asibiti Zata fita kenan Mamma kuma ta shigo.
Nan tace mata ta jirata tad'aukowa mutane abinci shine suka zo tare.
Bayan sun shiga sun duba ta, sun fito, tun kan Su koma inda sauran suke matar kawu tayi saurin zuwa ta tare su daga hanya idonta ya rufe, ba abinda takeson ji sai gaskiyar al'amari.
08161594233
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
Wnn shafin nakine Kakus.
*Amina Saleh Muri.*
Allah ya barmu tare.
*20*.
Tana isa ta sake Gaishesu tare da musu ya mai jiki.
"Mamma wai nikam Maisan ce da kanta ta fad'i maganar nan. "
Ta fad'a da son bugar cikin Mamman.
Cikin takaicin abinda ya faru Mamma tace "Ita ta fad'i sai akayi yaya?"
Duk da fad'uwar gaban da taji bai hanata cewa "Abinne da mamaki Mamma, wai Maisa tace Kawunta da kanshi ya lalatata. "
Shek'ek'e Mamma ta kalleta "Meye abun mamaki a wajen,mutum da halinsa ,ko ba akan irin hakan Kuka tab'a rikici ba har kika koma gidan ku, ba kama shi kikayi da me miki aikiba.
"
"In ko hakane mutumin nan ya cika cikakken munafuki, shine harda Koran yara a gida harda Amir fa yace yana zargi tsabar ya raina min hankali. "
Cewar matar kawu cikin b'acin rai.
"Kemafa da laifinki Hindu, ta yaya za'a baki rikon 'ya baza ki jata jiki ba, baki san matsalarta balle ki bata shawara, baki saki jiki da ita balle tayi tunanin tunkarar ki da damuwarta, baki damu kisa hankali a kanta ba balle ki fahimci wani canji a tattare da ita, ke sunan kuna gida guda ne kawai, shin Tsakaninki da Allah idan 'yarki ce ko 'yar uwarki zaki mata haka?"
Sosae jikin matar kawu yayi sanyi,a sanyaye tace "Tabbas nasan yana da wnn hali amma ban tab'a tsammani hakan zai iya faruwa tsakaninshi da Maisa ko don yadda yake mutunta Dadda. "inji matar kawu.
"Sharrin shaid'an dana zuciyar fa,ke kike tare da su kinfi kowa sanin kusancin dake tsakaninsu, abinda ya faru ya riga ya faru sai Allah ya kiyaye gaba, ita kuma uwar yarinya Allah ya bata lafiya da hakuri. Ke kuma sai ki dage da yiwa mijinki addu'a dan al'amarin shi kam sai addu'a, tunda ko kwanakin da kika kwanta rashin lafiya ma 'yar aikinki na yanzu ita tace min khamis yace mata ciwonki na gulma ne, me ya kaishi wnn maganar da 'yar aiki.
Mamma tace, ga dukkan alamu sosae take jin haushin matar kawun.
"Allah ya shirya, Mmn Kabeer tace tana jinjina abin a ranta, mamakin kokari da kuma kwarewar kawu wajen munafurci dan bazata manta lokacin da ya d'aga musu hankali akan wai Kabeer zai lalata mishi Maisa.
*************
Sai bayan sallar isha suka shiga asibitin dan saida ya kuma ritsata taci abinci snn suka fito.
Mamma da Mmn Kabeer kawai suka samu a asibitin sauran duk sun tafi.
Lokacin da suka shiga idonta a bud'e, Kabeer ya fara gaisheta, dakai ta amsa snn Maisa ma ta gaisheta.
Rintse idanunta tayi ba tare da amsawa Maisan gaisuwar da tayi mata ba.
Kukane ya taho mata hakan yasa ta toshe bakinta da hanu ta fita daga gurin a guje.
Da sauri Kabeer yabi bayanta yana kira.
Sai da yayi da gaske ya samu ya Cafkota ,Kuka ta sake fashewa da shi tana cewa "na shiga ukuna, banga amfanin rayuwata ba, tunda na zamo silar sa masoyana cikin damuwa. "
Sosae take Kuka tana surutai har maganar ya daina fita sai sautin kukan.
Jin kukan yake yi har cikin ranshi.
Riko hanunta yayi har cikin office d'inshi .
"Maisa nace kukan ya isa haka, ko sai kema kin kwanta ciwonne?"
Ya fad'a yana zaunar da ita kan kujera.
Cogewa tayi taki ta zauna tana ci gaba da kukanta.
Hanun shi ya hard'e a kirjinshi yana kallon ta tare da tunanin abinda zai yi tabar kukan.
Sai ganinta yayi ta durkushe a wajen tana Kuka mai cin rai cikin kukan take cewa Allah ya dauki ranta ta huta.
"Subhanallah. "yace da sauri.
"Me haka Maisa, kina da hankali kuwa?kin tab'a ganin inda mutum ya mutu kwananshi basu K'are ba?
Ashe shi yasa da Baffa yace miki zai kasheni kika biye mishi Kuka tabka rashin hankali?
Mutum mai cikakken imani bai kamata wnn kalma ta Zan kashe ta bashi tsoro ba, Indai ya riga yayi imanin Allah ke rayawa da kashewa. "
D'agowa tayi ta kalleshi "Bobbo ya zanyi,? Kai kana fushi dani Ammi na ma haka, Allah yasan yawan wad'anda suke jin haushina cikin family dan nice ta farko da ta fara b'ata mata Suna.
Ya zanyi ta k'arashe cikin Kuka kamar zata shid'e.
D'agota yayi ya rungume ta yana d'an bubbuga bayanta a hankali.
"Neman gafarar Allah shine babba dan ta namu mai sauk'i ne.
In don tani kam na yafe miki Allah ya yafe mana. Dama zafin Kishine ne yake sa nakeyi nake b'ata miki rai, ki rikemin amanar kanki, ki kaucewa duk wani abinda zai sake kawo irin Wannan matsala, wallahi ina kishinki sosae Maisa har bansan yadda zan rika controlling kaina ba, ki kiyaye dan Allah. "
Itakam sai gyad'a kai takeyi, ko ba komai ta samu sauki tawani b'angaren, tunda Bobbonta ya yafe mata.
"Ina fatar kema zaki yafe Min musguna miki da nayi tayi. "
Kai ta kuma gyad'a wa tana jin relief na shiganta .
"ita kuma Ammi ki bata lokaci komai zai daidaita.taji abinda bata zata ba dole abin ya buge ta. "
Kankameshi tayi tana sauke ajiyar zuciya "Na gode Bobbo, na gode. "
Take ta maimaitawa.
"Ya isa haka, zauna ki huta, kukan ya isa haka. "
Ya fad'a yana sake ajiyeta kan kujera. "
Sai pass 11 suka bar asibitin har zuwa lokacin Maisa bata samu tayi magana da mamanta ba.
************
Komawar matar kawu gida ta tarar dashi yana zaune a kofar gida kamar jiranta yakeyi.
Tana isowa yana cewa "ya jikinnata.
Wani Kallo ta Watsa mishi tayi wucewarta.
Sai a snn ya tuna wautar da yayi na tura ta asibiti, daga kallon da ta mishi ya tabbatar da taji komai.
Bin hanyar da tabi da Kallo yayi snn yayi Kwafa..
*Gaisuwa da fatan alkhairi gareku masoya, kabeer da Maisa sun gaisheku.*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
♣♣♣
Dedicated to my sisters.
*Hajiya (Mmn Affan)*
*Ummi*
*Hameeda*
*Zahra*
*Shafa*
Allah ya barmin ku k'annena.
*21*.
Zama yayi a gun na d'an lokaci kafin ya tashi ya shiga yana wani cin magani.
"Ke ana miki magana kina wani share mutane, nace ya jikin Daddan?"
Kallonshi tayi a d'age snn tace "Marar kunya dai baiji dad'in rayuwarshi ba. "
Kamewa yayi "To to, na gane, rashin kunya dai kikeso ki min yanzu, ki kiyayi ranar da zaki shiga hanuna dai. "
Ya fad'a yana tafiya.
Shima kanshi abun ya kashe mishi jiki, sai yanzu ya fara jin Kunyar abun, yanzu da wani ido zai Kalli Dadda.
Washegari ma tun safe yace ayi breakfast da 'yan asibiti.
Bata kula shi ba ya gaji da tsayuwa ya tafi.
Sai can bayan yaran Sun tafi makaranta ya kuma dawowa.
"Wai nikam Hindu baza kije asibitin bane? "
Dama Kiri's take jira, ai kuwa ta Kankance ido ta fara Watsa bayani.
"Dakata malam, Bafa ni na saka d'irkawa 'yar mutane ciki ba, ka jawa uwarta damuwa snn ni kazo kana damuna. "
"Abinda zaki ce kenan? "
"Eh, an fad'a ko karya aka maka baka yin bane? "
"Tsiyata daku kenan ku mata daga kunji magana sai ku hau Kai ku zauna ba tare da bincike ba. "
katse shi tayi da cewa "Ku kuma mazan idan aka barku sai ku rainawa mutane wayo ba, idan ba haka bane ka Musa mana, an daiyi abin kunya.
Maisan Kawu Maisan Kawu Ashe kawu da abu a kasa. "
"Ki kiyaye ni Hindu, ina raga miki dan yarannane fa."
Ya fad'a yana kifkifta ido.
"Kada ka raga min Abban Amir, Kayi duk abinda Kaga dama, babu abinda zaka b'oyemini yanzu babu kuma barazanar da zakayi tayi tasiri a kaina. Kaje mana da kanka ka dubata in dai kana da gaskiya. "
Ta K'arasa maganar tana murgud'a mishi baki.
Fuu ya wuce kamar zai yi abin Kirki, sai naga kawu kam ya taka birki a kofar gida.
Kan dakali ya zauna ya buga tagumi yana ta shawara a ranshi ko ya shafawa idonshi toka ne yaje ya duba ta.
Sai ya Mike kamar zai tafi sai kuma ya fasa. Yadda zai had'a ido da Dadda yake tunani.gaba d'aya jikinshi ya gama yin sanyi, sai yau yake nadamar abinda ya aikata.
Da ya koma tunanin yadda yabi yaci zarafin baiwar Allah Maisa kuma gaba d'aya sai yaji ya tsani kanshi tausayinta duk ya cika shi.
Tabbas yasan ya cuce ta ba kad'an ba Ammafa duk sai a yau yasan da haka.
Bai Ankara ba yaji hayawe na d'iga daga idanunshi.
Sosae ya shiga nadamar abinda ya aikata,Tunani yakeyi yanzu idan yaranshi Sun San da maganar nan yaya zasu d'auke shi.
Niko nace daga baya kenan.
yanzu babban damuwar shi yadda zai iya had'a ido da Daddan shi wnn kuma ya zama dole tunda yana da niyyar neman gafarar ta.
Wani tunani yayi, da sauri ya tashi, gidan Abba babba ya nufa,
Ko daga tarban da ya mishi da mummunar Kallo ya ishe shi amsa.
Da kyar ma ya amsa gaisuwar shi, daga yayi ta zuba yana bada hakuri da cewa a nema mishi gafarar Dadda.
Nan ne Abba babba ya hayayyako mishi "Khamis kada ka raina min hankali mana, lokacin da kake aikata abinda ka ga dama ka nemi shawarata, tunda ka fitsare kafafunka, nasan itama Daddar taka ba kunyarta zaka ji ba, saboda haka Kayi duk abinda zaka yi kada ka had'a dani cikin al amuran ka, babu ruwana da kai. "
Babu yadda ya iya jiki a sanyaye ya bar gurin yana tunanin mafita, baiyi tunanin zuwa wajen Baban Kabeer ba tunda ya daina mishi magana, amma ya kudurta a ranshi zai fara mishi magana yasan bazai ki amsawa ba tunda dama can shine mai bakin halin.
*************
A b'angaren Maisa kuwa duk iya kokarinshi na gani ta kwantar da hankalinta taki Sam, dan muddin Amminta bata mata magana tasan haka zata dawwama cikin bak'in ciki.
Ganin haka yasa Kabeer ya samu Mamma da maganar, itama ta lura da hakan amma tayi wa Mmn Maisa Uzuri dan tasan dole taji ba dad'i akan abinda ya faru. Saidai tace mishi zatayi mata maganar.
ita kuwa Mmn Rumaisa duk lokacin da taganta abinne yake zame mata Sabo sai taji kamar a lokacin take jin mummunar maganar .
Shi yasa take rufe idanunta idan ta ganta, amma a can kasan zuciyarta tausayin Maisar take ji, dan tasan tabbas an cuce ta, ga dukkan alamu kuma bata samu kwanciyar hankali a gidan aurenta ba.
A tausashe Mamma ta mata magana tana nuna mata illar fushinta ga Rumaisar.
Sai da tayi da gaske snn Ammi ta fara kula Maisa saidai ko Yaushe ta tuna tana jawa kawu Allah ya isa.
Bata tab'a tsammanin yadda suka riki zumuncin su akwai wanda zai iya cutar wani cikinsu ba, sai gashi kawu ya wa 'yarta tabon da bazai tab'a gogewa ba.
Kabeer yana iya bakin kokarinshi ganin ya kyautatawa Rumaisa wadda hatta Mmn Rumaisa saida ta fahimci hakan, shi yasa tad'an samu kwanciyar hankali.
Kullum Rumaisa take zuwa ta wuni a asibiti ,sai dare suke komawa tare da Kabeer.
Kwanan Mmn Maisa shida a asibiti aka sallameta, tana komawa gida tace Zata koma Jigawa Dakyar Abba babba ya matsa mata ta k'ara kwanaki.
Koda kawu ya nemi Iso gurinta cewa tayi bata son ganinshi ,babu wanda ya ga laifinta dan ya cancanci fiye da haka ma.
An sami sabanin raayi cikin Familyn dan wasu Sun yarda da abinda aka ce kawu ya aikata yayin da wasu suke ganin k'azafi kawai aka mishi.
Ba ma kamar wad'anda suka fito ciki d'aya cewa suke saida Dadda da Maisa suka gama morar kawu snn suka mishi muguwar sakayya.
Zali kanwarshi har cewa tayi zata mayarda 'yarta Fauziya gidan kawu dan huce haushi.
Kafin ta koma Jigawa saida ta kira Kabeer da Maisa tace mishi tana son tasan Ra'ayin shi game da Maisa, Indai yasan takura kanshi zaiyi ya rabu da ita kawai Zata koma da ita Jigawa.
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
Wannan nakine maqociyar kirki.
*Khadija ( Mmn Buhari.)*
Allah ya barmu tare.
*22*.
Ce mata yayi, ba takura, yana son matarshi, komai kuma ya wuce.
Har cikin zuciyarta taji dad'i bazata so auren Maisa ya mutu ba bare har abinda ya faru yaje kunnen dangin mahaifin ta.
Nasiha sosae tayi musu mai shiga jiki.
*************
Fitowa Baban Kabeer yayi cikin shirin tafiya sallar Juma'a, sai ganin kawu yayi tsaye kofar gidanshi.
Da mamaki ya bishi da kallo, ko kafin yace wani abu sai gani yayi kawu ya Mika mishi hanu, yana kuma yi mishi Sallama.
Mika mishi hanun yayi shims tare da amsa sallamar.
"Bismillah ".kawu yace mishi yana bud'e motarshi, dan Baban Kabeer ya shiga kamar dai yadda suka saba tafiya masallacin tare.
D'an jim yayi kamar bazai shiga ba
Me kuma ya tuna, sai kawai ya shiga.
Hira sukeyi jefi jefi, Sun gagara sakin jiki da juna,sun zama kamar wasu bak'i, har suka je suka dawo ba wata sakewar kirki kamar ba yan uwan juna ba.
Saida suka zo rabuwa kawu yace "Yaushe Dadda zata koma. "
"Ta koma. "Baban Kabeer ya fad'a a takaice yayi gaba.
Jinjina kai kawu yayi yana tunanin shi kenan yanzu Zumuntar Su ta lalace.
Niko nace wa ya jawo 😏
Har gida Abba babba yazo ya samu matar kawu ya bata hakuri tare da shawarar ta rufawa mijinta asiri Su zauna lafiya ta kuma rufa maganar kada yaranshi suji.
Dansu yaran ba kanana bane Sun girma suma, Babban ya gama sec. School.
Sai na biyu da yake ss2
Shi kuwa na uku ss3
Sai auta Farida Jss 3.
Shima kawun ya Sauko daga borin Kunyar da ya hau, nan ya lallaba matarshi suka zauna lafiya.
Amma fa yanzu Sam bata yarda dashi dan mugun sa mishi ido tayi.
More especially kan mai mata aiki.
*************
Kabeer da Maisa yanzu zama suke yi na mutunta juna, suna zaune lafiya ba maijin kansu, saidai itama yasa mata dokar zuwa gidan kawu, ko gidansu zata je tare suke zuwa, da yake itama haushin kawun takeji ko kallon gidanshi batayi.
Dad'i Adda binta take ji idan suka je gidanta ko taje gidansu ta gansu Suna wasa da dariya ,kwarai abin yake mata dad'i.
Har mai Shara da wanke wanke Kabeer ya nemawa Maisa idan ta gama aikinta ta koma gida, girki da gyaran dakunansu kawai Maisa keyi yanzu.
Basu da wata matsala yanzu sai na rarrabuwar kan Family.
***********
Tunda Mmn Maisa ta koma bata kuma Zuwa ba yanzu ana neman shekara guda kenan. Sai Maisa da Kabeer da Adda binta ne suka je mata.
Gaba d'aya garin ne ya fita kanta bata sha'awar ganinta a garin,duk da tana cike da Kewar yan uwanta.
Kamar yadda suka saba zuwa gidan Abba babba mostly weekends haka yau ma matar kawu da Farida suka je.
Hira suke amma hankalin Mamma yana kan Farida, har itama Farida ta fara tsarguwa da irin kallon da Mamma take mata.
Can dai Mamma ta shiga d'aki ta d'auko wayarta ta kira kawu.
Yana dagawa ko gaisuwarshi bata amsa ba tace "Khamis kar dai wani abin kunyan ka kuma yi mana. "
"Kamar ya Adda A'i?"
Cikin b'acin rai tace "Ba ciki nake gani jikin Farida ba? "
"wace Farida. "
Ya fad'a da ka'rfi bakinshi na rawa.
"Farida nawa gareka khamis ? Farida nake nufi 'yar cikin ka. "
"Innaalillahi. "
Yake ta nanatawa, jikinshi babu inda baya rawa.
"Ciki? A jikin Farida, yar karamar yarinyar da bata wuci 14 yrs ba?
Kuma ma wai shi Adda A'i take zargi. "
Lallai yanzu ya tabbatar da tabon zina bata gogewa.
Allah ne ya Iso dashi gidan Abba babba lafiya sakamakon gudun da yayi ta shararawa a hanya.
Yana shiga ya fara Kiran Adda A'i.
Palourn Abba babba tace suje.
Ido jazur yake kallonta tana tabbatar mishi da lallai ita taga alamun ciki gun Farida.
Hindu ya kwala wa kira, tana isowa cikin hargowa yace "Wani d'an akuyan ne yama Farida ciki. "
A gigice tace "Ciki? "
Tana zaro ido kirjinta yana Lugude.
"Eh, ciki. "
Ya fad'a yana muzurai.
Maida kallonta tayi kan Adda A'i kamar tana neman k'arin bayani.
"Ciki gareta Hindu, ke bakya gane mai ciki ne. "
Dab'as, tayi zaman yan bori a tsakiyar falon, Kuka take tsakaninta da Allah, kukan bak'in ciki.
Cikin kukan take cewa "Kaga abinda ka jawo mana ko,Wnn jinjirar yarinya ace cikine da ita. "
"Farida. "
Ya kwala mata kira cikin b'acin rai, sai da taji cikinta ya d'uri ruwa, dama daga yadda taga Ya shigo a fusace da jin Kiran da yayiwa mamanta tasha jinin jikinta, jikinta ya bata akwai abinda ke faruwa.
Duk'awa tayi kusa da mahaifin nata, kan tayi magana ya d'auke ta da wata mahaukaciyar Mari.
"Wa ya miki ciki Fareeda, nace wani d'an akuyanne ya Miki ciki. "
Hhhhh su kawu manya, ka manta ba d'an akuya bane d'an bunsuru ne.lol.
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
In dedication to my swt sis.
*Halima Awwal.( Mmn Ayshat)*
Allah ya kara miki lafiya.
*23*.
Cikin gigita da zafin Mari ta fashe da kuka.
Ganin zata ba'ta masa lokaci yasa ya shakota, har idanunta suka fiffito.
"Nace wani tsinannen ne ya miki ciki, kashe ki xanyi Farida idan baki fad'amin ba. "
Dakyar ta iya budan baki sbd shakar da tasha tace "Hamma Siraj ne ."
"Wani Hamma Siraj d'in. "
Suka fad'a dukansu da ka'rfi.
Jiki a sanyaye kuma Babanta ya sake ta ta fad'i kasa tana rike da wuya tana tari.
Matsowa ya kuma yi kusa da ita, a sanyaye yace "Farida, wani Siraj kike nufi?"
"Hamma Siraj d'in Goggo Nenne. "
Ta bashi amsa still tana rike da wuya..
Salati suka d'auka baki d'aya.
Basu matan ba shi kanshi wnn Suna da ta kira ya bashi mamaki.
Yaron da baya d'aga ido ya Kalli mutum.
Yaron da suke ganin ko yatsa aka saka mishi a baki bazai ciza ba.
Zama yayi ya dafe kanshi zuciyarshi na tafasa, shiru falon ya d'auka.
Can Mamma ta matso kusa da Farida ta dafa kanta.
"Farida 'yata gaya min gaskiya, Siraj ne ya miki ciki ko kin fad'ane dan kinga baya magana. "
Cikin Kuka tace "Wlh shine, ku tambayeshi, Wlh shine. "
Shiru sukayi dukansu sun rasa ta ina zasu fara.
Tashi kawu yayi ya figeta ya fita da ita ko takalmi babu a kafarta.
Jefata yayi cikin matarsa kamar kayan wanki.
Snn ya shiga yaja.
Asibiti ya kaita ya roki a fitar da cikin, amma abin takaici aka bashi tabbacin cikin ya Kai wata shida, idan ance za'a fitar zata iya rasa rayuwarta.
Cikin bakin ciki suka dawo gidan Abba babba, zuciyarshi kamar zata yi gobara.
A inda suka barsu nan duka dawo suka samesu sai dai yanzu Abba babba ma yana falon.
Zama kawu yayi yana huci, ji yake kamar yaga Siraj a hanunshi, shi kanshi baisan irin hukuncin da zai mishi ba.
Shi kanshi Abba babba yaji mamakin cewar Sunan Siraj da ya ji an fad'a a matsayin wanda ya kamata wnn mummunar aiki, amma da ya tuna sharrin zuciya da na shaid'an sai yaga ba abin mamaki bane.
Goggo Nenne ya kira ya ce wata ta tambayi mijinta tazo gidanshi yanzu.
A kid'ime tazo gidan amma da taji musabbabin Kiran, sai ta fututtuke ta fara masifa, ita an ma d'anta sharri tasan bazai aikata.
Kiranshi Siraj d'in akayi, bai wani b'ata lokaci ba ya Iso gidan.
Ganinsu harda Farida cikin su yasa ya fahimci dalilinta Kiran.
Zama yayi ya Gaishesu duka kanshi a kasa, duk suka amsa banda Baban Farida.
Ko da aka tambayeshi baiji ko d'arr ya amsa shi ya mata.
Tsananin tsoro da mamaki suka bayyana a fiskokinsu, Shiko Siraj ko kallonsu baiyi ba bare yasan halin da fiskokinsu suke ciki.
Da aka tambayeshi dalilin cutar da kanwarshi, sai cewa yayi ya rama musu ne sharrin da Kawu ya ta musu akan Maisa duk ya jawo ana musu kallon yan iska.
Kure shi kawu yayi da ido, lallai mutum sai a barshi, bai tab'a Tsammanin yaron nan zai d'auki abinnan da zafi ba.
Dan ko lokacin da ya koresu daga gidanshi bai nuna b'acin rai a kan haka ba sai ma hakuri da ya bashi.
Ashe akwai abinda ya shirya.
Dukansu saida jikinsu yayi sanyi da amsar da ya bayar.
"Siraj, ba'a rama sharri da sharri, ba haka ya kamata kayi ba, yanzu ita yarinyar nan Meye laifinta, ai ba ita ta maka laifi ba, gashi yanzu sanadin fushi da d'aukan fansa ka lalata mata rayuwa, ka kuma b'ata mana sunan Zuri'a, shi kuma d'an da za'a Haifa ya rayu cikin bak'in ciki, shin idan ya girma ya tambayeku Kuce mishi me.
Bama Wannan ba, me zaku cewa mahaliccin ku?
Kai kana ganin Wannan hujja da ka bayar ya ishe ka hujjar kare kanka a gurin Allah ne? "
Fad'a sosae Abba babba yayi tayi cikin damuwa da b'acin rai, kawu kam ba baki sai ido.
Shi kuwa Hamman namu ko d'agowa baiyi ba .
K'arshe dai Abba babba yace ma Goggo Nenne taje su shirya idan Farida ta haihu za'a d'aura musu aure da Siraj.
Daddagewa goggo Nenne tayi akan baza'a aurawa Siraj wacce baya so ba, ko da aka tambayi Siraj baiyi kasa a gwiwa ba yace baya sonta sbd da haka bazai aureta ba.
Sosae maganar ta shigi kawu, kallon yayarshi wacce suka fito ciki d'aya yakeyi, yau ita ke kyamar had'a jini da shi, lallai duniya abar tsoro ce, nadama ya dada shiganshi, ko me ya faru da 'yarshi shi ya jawo mata.
Haka suna ji Suna gani Goggo Nenne taja d'anta suka fita.
Saida suka koma gida tasa shi gaba ta zage shi tass.
Washe gari Abba babba ya kira sauran yan uwansu Meeting nan suke jin abinda ya faru, duk da basu ji dad'in abinda ya faru ba amma Sun hakikance alhakin Rumaisa ke bibiyar Kawu.
Nan Abba babba ya kafa dokan kar d'an wani a cikin su ya kuma zuwa gidan wani da sunan zai Kwana biyu ko hutu kowa ya zauna gidan ubanshi. Ya k'ara da cewa, "Ke kuma Zaliha, naji har tura yarki kike gidan khamis dan ki huce mishi takaicin k'azafin da kuke ikrarin an mishi ko?
To kisani cewa duk abinda ya faru da ita ba ruwan kowa anan kada ki neme mu.
Dama yaya zumuncin nasu yanzu ya riga ya zama ana kallon juna ne kawai, kowa da abinda ke kasan ranshi.
Allah ya kare mu da sharrin ZUMUNTAR ZAMANI.
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Dedicated to all fasaha novel group members at large, luv u all.😍*
*24*.
Haka taro ya watse ba dad'in rai.
Kulawa sosae Hindu take bawa yarta don tausayi take bata,banda Mmn Hindu babu wanda ya san da maganar cikin, cikin dangin Hindu.
Shi kuwa Siraj daga baya sai yaji ya fara tausayawa Farida, Ammafa baya ganin zai iya auranta dan shi yana da wacce yakeso.
A Kwana a tashi ba wuya har cikin Farida yakai haihuwa.
Wata ranar alhamis ta tashi da nakuda mai zafi bada jimawa ba jini ya b'alle mata.
Cikin tashin hankali suka kaita asibiti, sai bayan sun isa asibitin ne kawu ya sanar da Abba babba.
Suna gama waya Abba babba ya kira Goggo Nenne yace ta sanar da d'anta Farida tana nakuda yazo maza ya karb'i d'anshi idan ta haihu.
Haka kawai taji zuciyarta ya tsinke, da sauri ta kwala wa Siraj dake hanyar fita kira.
Yana zuwa ta fad'a mishi abinda Abba babba yace.
Cikin sauri ya fita daga gidan tana kiranshi ko waiwayo wa baiyi ba.
"Kana nufin baza ka je ba kenan. "
Ta d'aga murya ta fad'a.
Ina yayi gaba ko waiwaye babu.
Abba babba ya kira yaji asibitin da suke.
"Medical Center ."
Ya ce mishi.
Yana isa yaga nurse ta fito da gudu ta nufo su Mamma da Hindu.
"Ina mijinta?"
Nurse d'in take tambaya.
"Gani. "
Shine amsar da suka ji a bayansu .
Da sauri duka suka waiwaya dan ganin waye.
Siraj suka gani ya kure nurse da ido k'arin bayani yake jira.
"Doctor yana son ganinka. "
Tace tare da Juyawa da sauri.
Bin bayanta yayi shima da saurin kamar zai tashi sama.
Takarda Doctor ya bashi yayi signing dan bazata iya haihuwa da kanta ba.
Ba gardama yayi signing snn ya nemi izinin ganinta.
Dakyar suka yarda dan cewa suka yanzu zasu yi aikin, sun bashi minti biyar su gana ya fito.
Nurse ce a gaba yana binta a baya har suka shiga d'akin da take.
A sanyaye ya k'arasa bakin gadon yana kallon yadda ta galabaita duk ta fita kamanninta.
Gani yayi ma kamar an canza ta.
Fita nurse d'in tayi taja musu k'ofa.
Hanunta ya riko yana kiran sunanta, duk jikinshi ya gama sanyi.
Nadamar abinda ya aikata ne ya shige shi ga tausayinta da yasa idanunshi suka cika taff da k'walla.
"Fareeda. "
Ya sake kiranta muryarshi na rawa.
A hankali take bud'e idonta da ta Rintse har ta gama ware su kan fiskarshi.
"Fareeda, ki yafemin, ki gafarceni, na tuba."
Matse hanunshi dake cikin hanunta tayi ta kuma Rintse idanunta tana cewa "La Haula wala quwwata Illa billah. "
Tayata yayi suka k'arasa tare.
Saida abin ya Lafa mata snn ta sake bud'e idonta ta kalleshi.
"Ina mummy na? "
Tace mishi a hankali.
"Tana waje. "
Ya bata amsa.
"Daddy na fa?"
"Yana waje Shima. "
Yace mata.
"Hamma Kace su yafemin, mutuwa zanyi."
A gigice yace "Baza ki mutu ba Fareeda, zaki haihu lafiya, ki daure dan Allah. "
Girgiza kanta takeyi a hankali "Ni dai nasan mutuwa zanyi."
"Baza ki mutu ba nace Fareeda, Kiyi hakuri ki tashi Wlh Zan aureki. "
Murmushi ta d'an yi kad'an snn tace "Na yafe maka Hamma, Kace kowa ya yafe min. "
Kuka yanzu kam yakeyi sosae maganar ma ta gagareshi.
"Inna lillahi wa innaa ilaihirraji uun. "
Ta fad'a da dan ka'rfi snn ta koma yi a hankali, tun yana jinta har ya koma bakinta ne kawai yake motsi.
Hanunta dake cikin nashi yaji yana sakewa da sauri ya rike hanun yana cewa "Kar ki min haka Fareeda, Wlh zan aureki. "
Turo k'ofa akayi bai ma d'ago ba surutan shi yaci gaba da yi har likitocin suka karaso.
Kallo d'aya suka ma Fareeda suka gane rai yayi halinsa.
Dafashi babban Doctor yayi cikin karaya yake cewa "Kad'an bamu waje zamu dubata. "
Fiskokinsu kawai ya kalla ya girgiza kai ya kama hanya fita.
Yana Kai bakin k'ofa ya juyo, sai gani yayi ana rufe ta har fiska.
Fad'uwar shi suka jiyo suka dawo kanshi.
Kawu yana jin Tilon yarshi mace ta rasu Shima ya fadi, take a gurin stroke ya bugeshi.
Har aka kaita makwancinta Siraj bai dawo hayyacinshiba.
Saida ya Kwana ya wuni snn aka sallameshi, tunda ya koma gida ya shige d'akinshi babu abinda yake fito da shi sai sallah, sosae mutuwar ta shigeshi.
Hindu kam abunne ya had'e mata, ga rashin yarta mace tilo ga kuma ciwon mijinta ,gaba d'aya ta rame ta zabge ta zama abar tausayi..
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie. (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Dedicated to my lovely son *Abdurrahman Bashir Bello.*
Allah ya rayamin ku tafarkin addinin musulunci.
*25*.
Rasuwar Fareeda ne yasa Maisa zuwa gidan kawu, sosae itama rasuwar ya shigeta tayi Kuka har ta gode Allah.
Kawu kam ya zama ba baki ba k'afa,
Sai ido kawai.
Mmn Rumaisa ma tazo, tana ganin halin da kawu yake ciki ta fashe da kuka, Kuka tayi tayi na tausayin d'an uwanta, ya zamo kamar ba shine lafiyayye kakkarfannan ba.
Rayuwa kenan.
A cikin zuciyarta take cewa ta yafe mishi abinda ya mata.
Wata guda tayi kafin ta koma, lokacin kawu ya d'an fara magana amma idan yanayi zakaji kamar fizgar maganar yake da ka'rfi.
A hakan ya Nemi yafiyarta ta yafe mishi .
Ya kuma roketa ta ta roka mishi gafarar Maisa, dan tunda ya kwanta ciwo sau d'aya tazo dubashi lokacin kuma bai fara magana ba.
Kabeer yana zuwa dubashi amma ba sosae ba.
Har gida Mmn Maisa ta samesu ta roka wa kawu gafara, suka yafe mishi.
***************
Hirar su suke cikin shauqi da ishqi, kwanciyar hankali da nishad'i, da ka gansu Kaga masoya masu matukar k'aunar junansu, masoyan da suka yi bala'in dacewa da juna.
Jinsu suke tamkar su kad'ai ne masoyan da suka rage a fad'in duniya.
Sallamar Adda binta ce ta katse musu hirar duk suka yi tsit kamar masu so su tabbatar da sallamar.
"Bobbo kamar Adda Binta ce take Sallama. "
"To ki amsa mana Maisa. "
"D'agani in tashi kafin ta shigo. "
Idonshi a lumshe, ya dad'a narkewa kan cinyarta yana kwance kamar wani k'aramin yaro,yace
"Sai an tashi ake amsa sallama ne, amsa Kice ta shigo. "
Sallama Adda binta ta sake kwadawa a karo na biyu .
Ware murya Kabeer yayi ya amsa sallamar tare da cewa ta shigo.
Tura kanshi ta farayi "dan Allah Bobbo ka tashi kafin ta shigo. "
Gyara kwanciyarshi yayi tare da saka hannayenshi k'ark'ashin cinyoyinta ya Matse saida ta d'an yi k'ara .
"Me nake ganin nan god'od'o dakai ka wani kwanta mata kan cinya, karyata zakayi?"
Adda binta da ta shigo yanzu, take fad'a bayan ta Waro idanu kamar wacce taga abin mamaki.
"Nifa takurace bana so, ya daga zuwanki gidan mutane zaki fara damunsu da surutu idan kinsan sa ido ne ya kawo ki ki koma. "
Kabeer ya fad'a yana kallon Adda binta.
Maisa duk kunya ta gama isarta.
"Dama ka kirani nazo ka min wulakancine, ina ce min Kayi Maisa ba lafiya ka d'agamin hankali Ase karya kake. "
"Ah, Haba dai Adda binta da girma na Kice ina k'arya, ki tambayeta kiji da gaske bata da lafiya. "
"Me ke damunki Maisa. "
K'asa tayi da Kai takiyin magana.
"Tunda taki fad'a ni barin in fad'a miki, baby na ke damunta, Wlh Kwana biyunnan duk amai takeyi. "
Ya fad'a yana mik'ewa zaune.
"Inna lillahi. "Maisa tace.
"Ma sha Allah, Allah ya inganta. "Adda binta ta fad'a fiskarta d'auke da fara'a.
"Amma shine kuma ka kanainayeta kamar kaine Marar lafiyan."
Turo baki yayi irin na shagwab'abbun yarannan yace "Ni d'in kika San abinda take min, Wlh ko rabin son jikinta bani dashi. "
"Na banu. "
Maisa tace tana sunkuyar da kanta.
"Dan tayi son jiki ba laifi bane, kai kuma god'od'o dakai abu ba kyan gani Sam, kada ki yadda Maisa ke zaki wahala. "
"Tare fa kika samemu Adda binta kuma haka zaki tafi ki bar mu, idan kika shiga tsakanin mu ma kunya zaki ji. "
Kabeer ya fad'a yana dariya.
"Naji, yanzu da ka taso ni daga gida me kakeso na maka? "
"Kitso fa zaki mana Addanmu, tun shekaran jiya wancan muka tsefe kuma mun gaji da ganinshi a tsefe."
Tashi Rumaisa tayi ta nufi fridge dan samowa Adda binta abin jik'a mak'oshi.
"Kabeer Kaifa d'an rainin hankaline, da kullum ni nake zuwa na muku kitson?"
Langab'ar da Kai yayi snn yace "A'a mu muke zuwa yau dinma bamu son mu wahalar da baby ne yasa muka nemeki Addanmu. "
Ladabin Kule kenan.
Gaisheta Maisa tayi bayan ta ajiye mata abinda ta kawo mata, ita kuma ta mata ya jiki.
Snn ta koma wani kujera daban ta zauna.
"Yauwa Adda binta kisa mana date muje shopping. "
"Shopping na Meye kuma ni 'ya su. "
"Na kayan babies mana. "
Ya fad'a yana kashe mata ido.
"Oh Allah, ni naga zarb'ab'i, har wani shopping na kayan babies daga yanzu Kabeer. "
D'aure fiska yayi "Point of correction ,Baban Abdurrahman daga yau. Ko ya Maisa?"
Ya sako Maisa cikin zancen jin tayi shiru, ya sani Sarai Kunyar Adda binta takeji.
"Hmmm." kawai tace tana d'an murmushi.
"To, ya Adda zamujenne? "ya sake tambayar Adda binta. "
Rike baki tayi "Oh, ni binta, zamu je Kabeer shi kenan. "
Hararan wasa ya mata, tayi saurin cewa "Sorry Baban Abdurrahman. "
"In sha Allah. "Yace yana shafa fiskarshi yana kallon Rumaisa fiskarshi d'auke da murmushi.....
*Tammat bi hamdillah.*
Alhamdulillah, hamdan, katheeran, d'ayyiban, mubaarakan fiih.
Anan na kawo k'arshen littafi na *Zumuntar zamani.*
Godiya ta tabbata ga Allah (S. W. T) mai kowa mai komai da ya bani ikon kammala wnn labari, lafiya.
Kurakuran da na yi a ciki Allah ya gafarta mini, Allah ya sa labarin ta zamo mai amfani ga al'umma, ya bamu ikon amfani da koyarwar dake ciki.
Wannan labari sadauqarwa ne ga duk macen da aka lalata mata rayuwa sanadiyyar zumunci.
Tukuici ne ga
d'aukacin masoyana duk inda suke, ina k'aunarku kamar yadda kuke kaunata.
Ya Allah Mammallakin sammai da kassai, kai kad'ai muke rok'o kuma a gareka muke neman biyan buk'ata, Muna tawassuli da sunayenka kyawawa tsarkaka, ka d'aukaka musulunci, musulunci da musulmi a duk inda suke, Allah ka karya kafurci da kafurai, Allah ka shirya mana Zuri'armu baki d'aya, Allah ka shirya mana 'ya'yan musulmai baki d'aya.
Marasa lafiya Allah ka basu lafiya, masu lafiya Allah ka Kara musu mai albarka, wad'anda basu da abinda zasu ci ,ya Allah ka hore musu.
Allah ka azurtamu da arziki mai albarka.
Allah kasa mu fi qarfin zuqatanmu.
Allah ka rufa mana asiri duniya da lahira.
Wad'anda suka rigaye mu gidan gaskiya Allah Kaji kansu da gafara.
Mu kuma in tamu tazo Allah kasa mu cika da imani.
Allah kasa mu gama da duniya.
Alfarma annabi Muhammad (S. A. W).
*Luv u all.*😍😘😍
Sai mun had'u a sabon nvl d'ina *IN SO CUTANE.*
Allah ya Sada mu da alkhairi.
BISSALAM
*Daga alqalamin Mmn Afrah 💞.*
*08161594233*.
0 Comments