Yayanmu amanarmu hausa novels cmplt

 [3/19, 7:32 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  1 ⚜ 5


    Bismillahir Rahmanirrahim.

Ina rokon Allah yanda zan fara wannan littafi lafiya Allah yasa na gamashi lafiya.


        JAN HANKALI.

   Banyi wanann littafin dan in cima kowa fuska ba, nayi shine domin gyaran rayuwar 'yan wa muslumai. Banaso wani ko wata su kalleshi ta wata fuska wadda zata iya nuna saboda wani ko wata nayishi. Allah yabamu ikon daukar darasin da yake ciki.


       SADAUKARWA!!!


Na sadaukar da wannan labari nawa ga dukkanin 'yan uwa musulmai, IYAYE, 'YAN MATA DA SAMARI, YARA MAZA DA MATA. Allah yakara shirya mana zuri'a amin.



Kamar kullum yau ma masallacin unguwar Dorayi dake cikin garin kano cike yake da matasa da magidanta har ma da Yara suna sauraron wa'azin da akeyi aduk larabar karshen sati a wannan masallaci me albarka.


Malan Adam shine malamin da yake gabatar da wannan wa'azi duk ranar laraba. A koda yaushe ana samun jama'a da dama suna zuwa wajen sauraron wa'azin da yake gabatarwa, hatta da yara kanana ba'a barsu abaya ba.


Wasu sune suke kawo kansu yayin da wasu yaran tare suke zuwa da iyayensu. Kamar kullum yau ma kowa ya nutsu yana sauraran malan Adam wanda yake bayani akan irin AMANAR DA ALLAH YABAMA IYAYE WAJEN KULA DA 'YA'YANSU.


Kamar yanda yazamo ala'ada ta mutane da dama idan suna sauraron wa'azi, zaka samu kowa jikinshi yayi sanyi saboda ana karanta maganar Allah, sede wasu da dama zukatansu sunayin sanyi ne kadai alokacin da suke zaune inda ake gabatar da wa'azin.


Suna barin wajen shedan yake samun damar shiga zuciyarsu ya kawar masu da duk wani imani daya shiga zuciyarsu. Wannan dabi'a ta zama ruwan dare a zukatan mutane, da wuya zaka samu cikin mutane goma asamu mutum 5 wadan da basa da wannan dabi'a.


Zaka samu ko makabarta mutum yaje, iyakar jimamin da zeyi na lokaci kadan ne, kafin wani lokaci kuma ya koma ga aikata sabon da yakeyi, duk da dan Adam Allah yayishi me saurin mantuwa.


Sede mutane masu karfin imani da jajircewa wajen aikin Allah basa barin shedan yasamu damar shiga zukatansu bare yayi nasarar tarwatsa imaninsu. 


Malan Adam ya cigaba da fadin kamar yanda kuka sani, yau kusan sati na 3 kenan muna magana akan abu daya, ba komai bane yasa muke maimaita ta saboda wannan abu shine babbar matsalar da mu iyaye muke fuskanta a wannan zamanin, kuma dole semun jajirce wajen yakar wannan musiba da shedan yake shigo mana da ita har cikin gidajen mu.


 Allah daya haliccemu ya damka amana dayawa agaremu, wanda kafin kowa yazo duniya seda yadauki alkawarin zeyi duk wani abu da Allah ya shar'anta mashi.


Tabbas haka yake, Allah ya saka AMANAR 'YA'YAN MU akan mu, kuma akwai ranar da kowa ze tsaya agaban Allah domin ya fadi wane irin kiwo yayi ma amanar da Allah yabashi. 


Kada kayi tunanin dan ka ciyar da Yaranka, ka tufatar dasu ka ilimantar dasu shikenan ka sauke nauyin da Allah yabaka.


Wallahi mu iyaye maza semun tashi tsaye, domin bayan amanar Yara datake kanmu hatta da Matan mu amana ne agare mu, kuma hakkinsu yana wuyan mu,domin idan kai me gida baka tsaya kai da fata ba wajen ganin matarka tana kula da Yaranku tabbas kaine aruwa.


Da yawa iyaye Maza muna yin kuskure wajen sakarma Mata taribiyar Yara, saboda muna ganin mu bamuda lokacin zama agida, duk ranar da Allah ya tsaidaka agabanshi ya tambayeka zaka fada mashi bakada lokacin zama agida ne? Hakika wannan ba hujja bace.


Dole Iyaye mu kula da ZAMANTAKEWAR IYALAN MU. 

 (LITTAFIN ZARAH B-B). Domin wannan shine kuskure na farko da ake samu wajen ta barbarewar tarbiyar cikin gida, duk yanda ka kai da son Yaranka dole ka koya masu yanda zasu zauna atsakaninsu, domin halaccin dayake atsakaninsu bashine yabasu damar kowace irin cudanya atsakaninsu ba.


Musamman idan akace kana da Yara Mata da Maza, dole kasa ido wajen mu'amalarsu koda kuwa sun kasance Hasan da husaina, wannan shine karshen kusanci ko?  To koda sun kasance Uwa daya Uba daya dole kasa ido wajen mu'amularsu.


Saboda shedan yana yawo ajikin mutum tamkar yanda jini yake yawo, illarshi tafi illar mummunar Guba, ze iya shiga gidanka ya tarwatsa duk wani farin ciki da kake dashi. 


Matukar Iyaye basu cire son zuciya suka kula da amanar da Allah ya basu ba, to hakika muna cikin tashin hankali. Ina kara jawo hankalinku bawai kula da yanda Yaranku suke fita waje shikadai ne hakki akan mu ba, ko kuma shikedai ne koya tarbiya ba.


Tarbiya tana farawa ne daga cikin gida. Dole se mun koyama yaranmu yanda zasu zauna da kowa acikin gida kafin mufara tunanin nuna masu yanda alakarsu zata kasance awaje.


Ka nunama yaro so  bashine kare amanar Allah ba, domin masu iya magana suna cewa Kaso naka duniya ta kishi, kaki naka kuma duniya ta soshi. Kuma wannan maganar haka take.


Ina fatan zaku fahimci wannan bayani nawa, domin dayawa abinda yake kawo rashin aiki da abinda Allah yace rashin saka fahimta, kowa ze iya daukar magana daya yabata ma'ana dayawa, kuma ba komai bane yake kawo haka illa rashin fahimta.


Abinda muka karanta da kuskure Allah ya yafe mana, abinda yake dede kuma Allah ya saka mana da mafificin alkhairinsa. Anan nakawo karshen wannan karatu namu na yau. 


Kuma ina me bakin cikin sanar maku daga yau bazaku kara jina ba senan da wani lokaci wanda bazan iya cewa gashi ba, domin nima Allah ya nufe ni da tafiya madina domin karo karatu.


Amma akwai yarana nasan zasu iya cigaba da karatun da kukeyi, duk da nasan ba kowane zezo wajen nan ba, amma ina  fatan asamu rabi daga cikinku suna halartar karatun. Domin ba'ason dan wani yabar waje kuma ace shikenan komai ya tsaya.


Da ana haka muma da ba muzo muka samu addinin Allah ba, da magabata sun so suma da basu kara daukaka wannan ilimi ba, da sun barshi daga kan wanda ya karantar kuma yatafi, amma se suka dage wajen tabbatar da wannan addinin Allah gashi munacin gajiyarshi, Yaranmu sunaci, kuma haka mukeso mutanan da zasu zo bayan mu ma su ci gajiyarshi.


Idan akwai me tambaya ze iyayi kafin mu rufe wananan karatu. Wani matashi ne yadaga hannu yana fadin Allah gafarta malan, kamar yanda kace akula da mu'amalar Yara ta cikin gida a tsakaninsu, shin shikenan bazamu bar Yaranmu surika wasa da junansu ba, idan suka kasance maza ne da mata? Gyara glass malan yayi yace.


Wannan shine rashin fahimtar da nake magana akai, na tabbata idan mukabar wajen nan za'asamu wadda ze iya cewa na haramta wasa tsakain 'yan uwa. To amsar tambayarka anan itace, bawai na hana wasa atsakaninsu bane, amma abinda nake nufi.


Ina jiye mana tsoro akan wannan zamanin, yaranku zasu iya wasa atsakaninsu, amma wane irin wasa? Wannan shine ainihin abinda nake nufi, kazamo me saka ido akan Yaranka musamman iyaye Mata, domin sune suke zaune dasu acikin gida.


Duk yanda ka koyama Yaranka ahaka zasu tashi. Ina fatan ka fahimci maganata? Tabe baki wani Alhaji yayi wanda yake kusa da wanda yayi tambayar, kallon agogon hannunshi yayi yana fadin gaskiya yau anci lokaci da yawa, kusan sati 2 ana maimaita abu daya haba.


Malan yace alaramma kayi mana addu'a naga lokaci yatafi, kuma ina rokon addu'a agareku, yanda zanyi wannan tafiya Allah yabani sa'ar karatu kuma yabani ikon dawo maku da wani sabon karatun, idan akwai wanda na bata mawa, ina neman afuwa, nide nayafe ma kowa.


Bayan anyi addu'a wani yatashi yana fadin za'a aje akwatin gudummuwa da yakamata ahadama malan, duk wanda yake da hali daga nan zuwa jibi ze iya kawo tallafinshi. Haka kowa yatashi yafita, wasu suna me jimamin tafiyar malamin.



Karar horn ce tasa megadi yayi saurin tasowa yazo ya bude gate, da gudu motar tashigo, rike baki megadi yayi yana fadin yau kuma waya tabo mana Alhajin Allah, wannan irin tada kura haka.


Yana rufe gate din ya ruga zuwa wajen Alhaji, bayan ya hude mashi kofa ya duka yana fadin barka da dawo wa Alhajin Allah. Hannu yadaga mashi yana fadin yauwa sannu Kallah ya gidan? Wanda aka kira da Kallah yace lafiya lau Alhaji.


Wucewa ciki Alhaji yayi yana fadin yayi kyau, rufe kofar motar Kallah yayi yana fadin gaskiya yau antabo Alhaji, amma kuma ai yau laraba daga wajen karatu yake, kai inajin de ahanyarshi ta dawowa nan aka bata mashi rai.


Da sallama Alhaji yashiga cikin gidanshi, wasu yara su biyu da suke zaune afalon suna kallo ne suka amsa sallamarshi, da gudu suka tashi suka nufi wajenshi, suna zuwa suka rungumeshi suna fadin sannu da zuwa Dady.


Dariya yayi yace yauwa yarana, yana ganku ku kadai afalon ina sauran suke? Dayar macen ce tace ai Aunty Mubina tana dakin Yaya Jameel suna kallo. Murmushi yayi yace to ina ita Mufida take? Na mijin ne yace sun fita ita da Yaya karami siyo ice cream.


Dariya yayi yace to Ina Momy? Wata farar matace take sakkowa daga bene fuskarta dauke da murmushi. Cikin muryar yara tace Ita kuma Momy tana sama tana jiran Dady. Saurin kallon saman benan sukayi, gaba dayansu suka sa mata dariya.


Karasowa tayi tana fadin sannu dazuwa, yace yauwa Momy ya gidan? Tace gida gashi babu dadi tun dazu muna jiran Dady yadawo muci abinci amma yaje ya tsaya awaje, ai nasan yau laraba  kuna tsayawa karatu, amma ai bakwa irin wannan dadewar.


Tsaki Alhaji yayi tare da zama kusa da ita yana fadin wallahi kema kya fada, aide daga yau na dena tsayawa karatun nan, dama can ni bawani zuwa nake ba, kawai dan de Alhaji Sambo ya matsa mani ne.


Amma dama irin wadannan malaman da kaga suna karatu to karshen maganar zakaji sun kareta da neman temako. Wannan malamin sati 3 kenan yana magana daya. Ni wallahi gani nake ma kamar dani yake,🤣 emana, yau satina 3 da fara zuwa amma beda magana seta kula da Yara se kace an fada mashi bana kula da yarana, yau daya gama shine ya rufe da maganar wai zetafi karatu Madina.


Kinga dama can ai yasan da maganar karatun shiyasa yazo yana mana karatu, ana gama addu'a kuma wani yatashi wai ana neman tallafin kudin da za'a ba malan, to da besan beda kudin ba kuma ya jajibo tafiyar.


Ya dage dole se mun koyama Yaranmu irin yanda suke tarbiyantar da nasu, ke ina kike ganin hakan ze yuwu? Murmushi Momy tayi tace ai dama tunda naga kafara tsayawa daukar karatu nasan wadannan malaman se sun canza maka akidarka.


Ta yama za'ayi tarbiyar Dan me kudi tazo dede da ta Dan Alaramma? Ai hanyar jirgi daban ta mota daban, sufa diyansu ko bacci yarinya zatayi to da hijabi ajikinta, acikin gida ma bazata cire hijabi ba, idan kaga tana magana da Dan Uwanta seka dauka da surikinta take magana.🤣.


Wai awajensu wannan duk iya rike amana ne, to aduniya idan 'yan uwa basu zauna sukayi fira awaje daya ba, ya akeso suyi? Idan basa zama suna cin abinci tare taya soyayya da shakuwa zata shiga tsakaninsu? Idan basa fadama junansu damuwarsu taya tausayawa zata shiga tsakaninsu? Nifa banyarda da irin wannan maganar ba.


Kai ne daka fisu har kawuce duk masallatan unguwar nan katafi wata unguwa can wai Dorayi. Alhaji yace wallahi laifin Alhaji Sambo ne, shine yadage wai malamin ya iya karatu. Momy tace ai ga karatu nan yana maku yana fakewa da zaginku. Wato yaranmu bazasu sake ba.


Alhaji yace nima haka nagani, shikenan yaran namu suna ciki daya amma ace wai seka kawo wani ta kunkumi kasa masu, idan ba dama can yaran ba yan halak bane taya za'ayi su iya neman junansu da wata lalata, ko kuma wata sha'awa tashiga tsakaninsu.


Ai duk inda kikaga anyi haka to idan kika duba dama can ba ciki daya suka fito ba, domin duk wata soyayya da take tsakanin yan ciki daya to wananan soyayyar ta jini ce. Momy tace dan Allah kadena biye ta maganar malaman cen, wallahi zasu iya canza mana kai, idan su suna tafiyar da yaransu tamkar suna prison ne mu su kyalemu da namu.


Domin duk wani ginshikin zaman lafiya to soyayyace take samar dashi, dama kuma idan kana neman zaman lafiya da soyayya tsakanin 'Yan uwa to kazo irin gidajen nan, domin mu soyayya abincinmu ce, dole yaran mu suyi rayuwar sakewa agidansu.


Idan suka fita kuma su nuna banbancin dake tsakaninsu da kowa, shiyasa nake kara godema Allah, yarana ko kawaye basu dasu sosai, kawayansu sune 'Yan uwansu, basuda abokan shawara sesu.


Duk lokacin da zaka samesu adakin mazan gidan nan to zaka samesu suna kallo, ko suna koyama junansu karatu, ko kuma suna cin abinci, shiyasa ni bazan iya yimasu shamaki atsakaninsu ba, dan kowa yana da ikon daze shiga dakin dan Uwanshi, kwana ne kawai bazan bari suyi ba, suma kuma sun san wannan ba me yuwuwa bane.


Alhaji yace to idan basu shiga dakin junansu ba so ake sutafi dakin wasu? Ai kinsan Allah koda ace wannan malamin baze tafi wani waje ba, daga yau nagama zuwa wajensu, ni dafarko ma da Alhaji Sambo yace mun karatu akeyi na dauka Qur'ani ake budewa akarantama kowa, ashe wa'azi ne sukeyi domin suruka samun abun kaiwa baki.


Dariya Momy tayi tace dan Allah manta da wannan maganar tashi muje kacire kayanka muci abinci, sallamar su Mufida ce ta katse su, kallonsu sukayi suna murmushi, atare sukace Dady sannu da zuwa.


Murmushi yayi yace yauwa kuma sannun ku da shan Ice cream, ina fatan de kun yima 'Yan biyu na tsara ba? Mufida tace sosai ma, ai dole musiyo masu, idan bamu siyo masu ba wazamu ba? Momy tasaki wani murmushi tace wallahi babu Mufida.


Su kadai kuke dasu, kuma su zaku kyautatamawa, tashi 'Yan Biyu sukayi suka rungumesu. Mufida taja hannun wanda aka kira da Yaya karami tana fadin muje kadauko mani dayar wayata.


Kamota yayi ya matseta ajikinshi yana fadin ai nace yau awajena zata kwana sede ki bari se gobe, tabe baki tayi tare da tureshi tana fadin Dady ka jishi ko, murmushi Alhaji yayi yana fadin kunfi kusa, kai kuma kaje kadauko mata wayarta, ka fadama su Jameel ku fito muci abinci.


Gwalo tayi mashi ta ruga da gudu yabita suka shige dakinta, Dariya Iyayen sukasa Momy tana fadin Allah kabarni da Yara na, domin sune farin cikina. Alhaji yace amin, muje nima kitayani cire kaya. 'Yan biyu suka ce to Dady kuyi sauri kada abincin yayi sanyi. Dariya sukasa suka haye sama.




Alhaji Sulaiman Dikko kenan, asalinshi dan garin Kano ne, tsohon ma aikacin gwamnati ne, ganin harkar kasuwanci tafi samu yasa ya aje aikinshi yakoma kasuwanci, yana da manyan gidajen Mai agarin Kano dama wajen kano, haka kuma yana da gidajen haya da manyan shopping malls.


Anfi kiranshi da Alhaji Dikko, yana zaune agidanshi da yayi amfani da makudan kudi wajen ginashi da yake G.R.A, hatta da bangaren masu aiki daban yake, haka kuma duka yaranshi kowa da dakinshi.


Matarshi daya me suna Rumaisa, anfi kiranta da Hajiya Shuwa, domin ita yar Nijer ce, yayarta me suna Ramatu itace tayi aure a kano inda ta auri wani babban dan kasuwa, shine yasa ta daukota ta dawo wajenta da zama.


Tana da kyau sosai, gata fara, hakan yasa aranar da Alhaji Dikko yafara ganinta beyi wasa ba yaje neman aurenta. Yaransu 6, ukku maza ukku mata. Babban dansu shine Jameel, se Mubina, Junaid, Mufida. Bayansu seda suka dade kafin suka haifi 'Yan biyu, ana kiransu Amir da Amira Sulaiman Dikko.


Gaba dayansu awaje sukayi karatunsu, Jameel yarigasu gamawa, yana aiki a Aminu Kano teaching hospital. A kwai soyayya da shakuwa sosai atsakaninsu, hatta da abinci tare suke ci, kowa yana da kayan kallo adakinshi, kuma duk wanda yaso yana shiga dakin dan Uwanshi suyi kallo.


Kowace irin shiga matan sukaga dama sunayi kuma basa jin kunyar mazan, domin abinda kullum iyayensu suke fada masu, basu da wasu yan uwa sama dasu, duk wata damuwarsu su fadama junansu.


Wannan dalilin ne yasa basu dauki rungumar junansu wani abu ba, zaka iya samun wata tayi matashin kai da kafar dan uwanta, zasuyi kallo tare, suyi kataru tare, suyi komai tare, ko karfe nawa zasu kai adakin junansu iyayen basa damuwa domin sunsan idan zasuyi bacci kowa dakinshi yake tafiya.


Hatta da karatun addini agida malami yake zuwa yana koya masu, idan kagansu da wasu baki to daga cikin Family dinsu ne, ba ruwansu da abota da wasu bare, kansu ahade yake, duk wata matsalarsu suna fadama junansu. Iyayensu suna matukar kokari wajen ganin sun hada kansu.


Ganin yanda suke bama junansu kulawa yasa iyayensu suke cikin farin ciki, kuma suke ganin kamar sun rike AMANAR da Allah yabasu.


Karar bude gate yaran da suke zaune afalo sukaji, hakan yasa wani saurayi da yake zaune a kujerar da take kusa data kanwarshi  yayi saurin tashi yana fadin ga Abba nan. Dayan kaninshi da yake kwamce kusa da Ummansu shima saurin tashi yayi.


Dariya  macen tasa tana fadin lallai dokar Abba ta fara aiki a gidan nan. Tsaki Ummansu taja tana fadin ni wallahi bansan inda Alhaji yaje yadauko wannan muguwar akidar ba, kuma acikin sati biyun nan ne yafara saka wannan dokar.


A ce kai da dan uwanka bazaku zauna kusa da juna ba,  se kace wadan da ba ciki daya suka fito ba, da anyi magana yace saboda zamani, to wane irin zamani ne zesa dan uwanka yaji sha'awarka.


Idan ma haka ne, ai bawani abu bane dan dan uwanka yazauna kusa da kai, kawai de rashin fahimtar addini ne, zesa yakawo ma mutane wata akida. Babban danta yace wallahi mude kam Abba yana takuramu, shikenan babu damar kazauna kusa da 'yar uwarka, to yama za'ayi kaji wani abu danka zauna kusa da ita, mude ba irin rayuwar turai muke ba,  bare yace yaga muna yan rungume rungume ko kuma yana ganin muna taba ta.


Sallamar Alhaji Sambo ce ta katsesu, shigowa yayi fuska adaure yace ashe kuna ciki baku fito ba ko bakuji karar mota ta ba? Sosa kai suka fara suna fadin sannu da zuwa Abba, waje ya samu ya zauna yana fadin ke Laila wane irin zama ne haka, tashi ki dauko hijabinki kisa, kuma wallahi daga yau idan nakara ganinki babu lillibi matukar mazan nan suna gida se ranki yabaci.


Kallon jikinta Laila tayi ganin doguwar riga ce ajikinta tace amma Abba wadannan kayan ai basu matse ni ba, pillow din kujera ya wurga mata yana fadin kinci gidanku, ni kike fadama basu matseki ba? Shi shedan ina ruwanshi da rashin matsewa.


Ko bargo kikasa idan yaso aikata shedancin shi ai se yayi, AMANRKU Allah yabamu dole mu kula daku, domin tarbiya daga gida take farawa, kaima Saleem daga yau bana son inkara ganinka kana zama cikin falon nan sosai, idan abinci zakaci kazo kadauka ka kai dakin ka kuma zansa maka kayan kallo da anyi magriba banason ganinka cikin falon nan.


Girmanka ya wuce ace kana zama cikin gida kana kallon kanwarka, duk lokacin da zaka shigo falo ka tabbatar kayi sallama an baka izini sannan kashigo, kuma koda wasa nakara ganin kafarka kusa da dakin Laila se ranka yabaci.


Kaima Hamza duk da kana karami banaso kana shige ma Laila, tunda yanzu zaka shiga jami'a kaima ka girma zan maidaka dakin Saleem na waje, wannan dakin naka na cikin gida zaka barshi.


Sakin baki sukayi suna kallon Abbansu yanda yazo masu da wani sabon salo, Umma ce tace Saleem kutashi kuje zanyi magana dashi. Bayan sun fita tace haba Alhaji, wai wane irin sabon addini ne kashiga haka? Wane irin tsanani ne kakeso ka kawo mana cikin gidan nan? Shikenan dan ance mu kula da yanayin mu'amular yaranmu shikenan se akace mu dasa zarginsu azuciyarmu.


Ni na tabbata koma wane malami ne yafada maka haka to kai kayi rashin fahimtarshi, babu malamin daze ce maka wai kada dan uwa yazauna da dan uwanshi suyi fira, duk da banje wajen karatun ba amma atawa fahimtar ba haka bane.


Murmushi Abba yayi yace ai dama ku mata karamin tunani gareku, duk wanda ya biye taku zaku kaishi kubaro, to bara kiji, ke kanki akarkashin Amanata kike, kuma ranar gobe kiyama se Allah ya tambayeni yanda na tafiyar da kiwonku. Alhamdulillahi malan ya haska mana wani abu daya shige mana duhu.


Kuma daga yau zan kawo sabon canji agidana ta yanda zan kaucema sharrin shaidan, ke idan kikayi wasa ma wallahi yaran nan maza zan hanasu shigowa cikin gidan nan matukar Laila tana nan sede idan tana makaranta sannna zasu shigo, idan zamu gaisa nizanje wajensu.


 Ko kuma ma nasan abinda zanyi, zansa afasa mani kofa ta wajen dakinsu kafin nafita surika shigowa muna gaisawa, kema se inkiraki ku gaisa kawai base sun rika shigowa ta cikin falo ba.  Kin ko san yanda shedan yake yawo ajikin yan adam?  Yau munsha babban karatu.


Kuma malan ya haramta namiji baligi yarika zama yana fira da mace baliga koda kuwa sudin 'Yan biyu ne, karewar uwa daya uba daya, saboda kema na bada wayata akamani recording wa'azin malan na yau, muje idan nagama abinda nake in kunna maki kiji nasan kema zaki tayani aikata aikin lada.


( 🤔Anya Alhaji Sambo ya fahimci abinda malan yace?🤷🏻‍♀ muje zuwa domin muga yanda zata kasance).



 Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263.


👂🏻👂🏻Waiting for ur comments.Tnx  Luv u all😘😘😘😘

[3/22, 9:06 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  5 ⚜ 10


Murmushi Umma tayi lokacin data gama sauraron wa'azin da malan Adam yayi masu Alhaji Sambo, kallonta yayi yace kema kinji abinda baki sani bako? Ai nafada maki, wannan malamin yana da matukar ilimi, shiyasa naja abokina Alhaji Dikko na kaishi wajen wa'azin saboda nasan kwarewar malamin.


Kuma naji matukar haushin tafiyar da malan zeyi karatu, amma duk da haka zan cigaba da zuwa tunda yaranshi zasu cigaba da karatun, wallahi kamar wasa wata rana naje wajen wani tsohon abokina a Dorayi bayan munyi sallah a masallacin yace in tsaya inji wani karatu na malan.


Tun daga ranar na dage wajen zuwa wa'azin, segashi acikin sati biyu da suka wuce yafara tabo mana yanda tsarin kula da iyali yake, se gashi wa'azin yau yafi na kullum girgiza jama'a. Kallonshi Umma tayi cike da mamaki.


Gyara zama tayi tace Alhaji dan Allah ka saurareni kaji abinda zan fada maka. Tabbas naji wannan wa'azi kuma nima yayi mani dadi, yanzun nan zaka tura manishi kuma na fahimci abinda malan yake nufi.


Amma Alhaji dan Allah inaso ka kara kunna wa'azin nan kaji, domin ka kara fahimtar abinda malan yake nufi, kwata kwata yanda ka fahimci maganar malan ba haka take ba. Ka saka rashin fahimta aciki.


Nasan nayi karatun addini dede gwargwado kuma agidan nan ina iya kokari na wajen kula da tarbiyar gidan nan, bana barin yarana suna aikata wani abu marar kyau,kuma ina kokarin nuna masu yanda tsarin musulunci yake, duk da irin kudin da kake dashi ban bari yaranmu sun lalace ba.


Mezesa yanzu ka kawo mana wata akida wadda bansan da ita ba atsarin musulunci, taya zaka hana zumunci atsakanin 'yan uwa? Idan baka sani ba wannan abun da kakeso ka kawo ze raba kan yaranmu.


Taya zaka hana yara zama suyi fira da junansu, shi shedan din ai yasan addu'a ko? Wallahi duk wanda kaga shedan yasamu damar tarwatsa mashi gida to tabbas yayi sakaci da koyarwar addini, bawai tsanani da raba kan 'yan uwa shine zesa shedan yaki shigowa gidanka ba.


Tashi zaune Alhaji yayi yana fadin ya isa haka, kada kibari rai na yabaci, ina tunanin kece baki fahimci abinda malan yake nufi ba, gida de gida nane kuma nikeda iko dashi, haka yara nawa ne, idan kinji zaki iya bin dokata zaki iya saka mani ido.


Idan kuma bazaki iya ba zan kawo wadda zata iya tayani neman lahirata dan wallahi zan iya auro diyar malan matukar yana da ita kuma ze bani, idan ma beda ita zan iya sawa aduba mani wata daga cikin diyan yaran malan.


Umma cike da mamaki tace dan Allah kayi hakuri ni ba haka nake nufi ba, tunda baka fahimceni ba shikenan abar maganar, nagode Allah da yasa Laila ita kadaice mace agidan nan, Allah yakawo mata miji tayi aurenta kowama ya huta.


Alhaji yace wacece zatayi aure yanzu? Laila da yanzu tashiga makarantar duka 200 level take kike kirawo mata aure? Kin manta acikin AMANAR da Allah yabamu hada ilimi aciki? To nide nine me aurar da ita, kuma bazan mata aure ba seta gama karatunta sannan.


Ko mutuwa nayi nasan na bata ilimi sosai, yanzu ma malami zan dauko mata yarinka koya mata agida suma su Saleem duk zan rika jansu muna tafiya wajen karatu a duk ranar laraba, tunda su maza ne karatunsu beda wani wahala.


Amma ita diya mace tafi rauni, amma bazan yi ma diyata aure yanzu ba. Umma tace shikenan Allah yakawo mana lokaci, ai karatu yana da dadi, kuma na islamiyar ma da tana zuwa shigarta makarantar nan ne yasa ta dena, amma tunda zaka dauko mata malami naji dadi, nima seya rika kara mani.


Murmushi Alhaji yayi yana fadin yauwa ko kefa, ai dole semun hadu wajen tarbiyantar da yaranmu dama hannu daya ai baya daukar jinga. Tashi ki dauko mani ruwa insha.




Alhaji Sambo kenan, shima dan garin kano ne, kuma dan kasuwa ne, yana harkar canji, ba laifi yana da kudi domin yana da gidajen haya. Matarshi daya me suna Hajiya Binta, itama 'yar kano ce. Suna zaune agidanshi me kyan gaske a unguwa ukku.


Yaransu 3, babban shine Saleem ya gama karatunshi yana aiki first bank inda yake rike da matsayin accounter, sede har yanzu beyi aure ba yana zaune agidan iyayenshi. Me bimashi itace Laila wadda take karatu a jami'ar Bayero a nan kano yanzu tana level 200, se karaminsu shine Hamza, yanzu ne zeshiga jami'a.


Gidan Alhaji Sambo gidane me matukar tarbiya, domin Umma tana kula da yaranta, kasancewar Mahaifinsu yana da kudi besa tabari yaranta sun lalace ba, domin itama tana da ilimin addini.


Sede shi Alhaji Sambo beyi zurfi acikin karatun addini ba, asalima ko karatun bokon beyi nisa acikinshi ba, kasuwanci kawai yasa agaba, yanzu ne Allah yasa hankalinshi ya karkata zuwa neman ilimin addinin inda yasamu wani abokinshi suka fara zuwa sauraron wa'azin Malan Adam.


A da babu ruwanshi da matsama yaranshi akan komai, amma zuwa lokacin daya fara jin wa'azi yasa ya bullo masu da wannan dokar wadda har take nema ta zarce abinda malan yake nufi.


************ **********


Zaune suke atsakar gida shida abokanshi suna ta fira suna dariya, kanwarshi me suna Maryam tana gefe tana ta yasu dariya jikinta riga da wando ne na pakistan ta saka hula.


Mamarsu tana kitchen tana girki. Tun daga waje yake jiyo sautin dariyarsu, har sauri yake yazo yaga suwaye suke wannan dariyar. Cak ya tsaya abakin kofa ganin abokan danshi ne se kanwarshi agefe, wani yana ta basu labari suna dariya.


Kara daure fuska yayi yashigo da sallama. Amsawa sukayi tare da fadin sannu da zuwa Baba, fuska a daure yace yauwa sannunku. Ke Maryam me kikeyi anan? Saurin tashi tayi tana fadin bakomai.


Kai Aliyu wane irin sakarci ne haka, taya zaku shigo cikin gida kurika wannna dariyar kamar kuna filin kallo, duk kofar gida be ishe ku ba sekun shigo har cikin gida. Saurin tashi abokan Aliyu sukayi suna safa kai sum sum suka fita.


Aliyu kuwa jiyayi kamar ya nutse dan kunya, shi so nawa yake zuwa gidan abokanshi kuma su shiga har cikin falon gidansu iyayensu basu taba masu magana ba seshi dan yashigo dasu tsakar gida shine za'a dizgashi.


Kallonshi yayi yace ina Abubakar? Cike da bacin rai Aliyu yace yana ciki, kai tsaye ya wuce jin sautin magana a cikin daki yasa ya nufi dakin, yana zuwa ya daga labulen dakin su Maryam, zaune Yayar maryam Amina take a saman kujera tafito wanka tana shafa suna ta fira da yayanta me suna Abubakar.


Se autarsu Halima dake gefe tana kwalliya, se Maryam data shigo yanzu. Tsawa Baban yadaka ma Abubakar wanda gaba dayansu seda suka tsorata. Saurin tashi Abu yayi cike da tsoro yana kallon Babansu.


Cikin masifa Baban yace ku sameni a waje. Hijab kawai Amina tasa tafito. Zaune suke su biyar yaranshi se Babansu agefe Mamarsu tana kusa dashi. Duk wanda ya kalli fuskarshi yasan cike take da bacin rai, wanda hakan yakeyi idan anbata mashi rai,


Gyaran murya yayi yace Saude, so nawa zan fada maki banaso inga Aliyu yana shigo mani da abokanshi cikin gida?  Duk fadin wajen gidan nan be ishesu ba harse sun shigo nan suna fira ke kuma kina kallonsu.


Ita kuma wannna ko hijabi babu ajikinta haka take zaune sunata fira suna dariya an maida mani gida kamar gidan maza. To wallahi daga yau idan nakara ganin wani abokinku yashigo gidan nan se ranku yabaci ku duka hada ke Saude.


Kai kuma Abu daga yau banason in kara ganinka adakinsu Amina, yanzu kai ko kunya bakaji tafito wanka amma kana zaune katasa ta kuna ta fira, idan ita tanajin kunyar cemaka katashi kai baka da hankalin da zaka bata waje tagama shiryawa.


Ni ban hanaku kuyi fira atsakanin ku ba, amma yakamata kurika lura da irin lokacin da zaku zauna dasu kuyi fira. Kuma daga yau na hanaku shigar masu daki. Idan wani abu kukeso ku tsaya daga waje kuyi sallama su fito su baku.


Amma wallahi koda wasa nakara ganin ku adakinsu ranku ze baci, ku ma matan banaso inkara ganin ku kunje dakin su. Kome suke so su fito su dauka, fira idan ta wuce falo ko tsakar gida to na hana.


Idan kuma dole sekun kawo abokanku cikin gida to zakuga bacin rai na.  Aliyu yace kayi hakuri Baba insha Allah hakan bazata kara fauwa ba. Amma Baba meze hana gobe idan Allah ya kaimu  ka kira Lauwali me gini yazo ya fasa mana  kofar da aka rufe ta  waje idan yaso se murika shiga kawai ta waje dasu.


Girgiza kai Babansu yayi yace Aliyu ina sane nasa aka rufe waccan kofar aka maidota cikin gida, domin ware ma yara bangarensu wata hanya ce da take kara bata komai.


Na fiso dani daku mu kasance kullum ta kofa daya muke fita, kuma in san cewar kofa daya ake kullewa agidana bana so ina ciki na kwanta bansan lokacin da kuke dawowa har kuke kwanciya ba.


Ni ba tsanani nake maku ba, sede ina kokarin kareku daga sharrin shedan da wannan zamani, mu da muke fita mune mukasan abubuwan da suke faruwa, ku kam daga wajen aiki se kallon kwallo abinda kawai kuka sani kenan.


Wannan zaminin abun tsoro ne, domin tafe yake da abubuwan bam mamaki, shedan kuma akullum babu abinda yakeso wanda ya halakar da bayin Allah. Abu daya zamuyi domin mu tserata daga kaidinshi shine mu kiyaye DOKAR ALLAH.


Kuma hakan baze faru ba harse munyi aiki da koyarwar Annabin mu. Ku dena ganin wadannan 'yan uwanku ne, Wallahi shedan babu ruwanshi da 'yan uwantaka, kai shedan ze iya hada Diya da Uba idan baku sani ba.


Kada ku dauki abinda nake maku kamar takura ce, inaso indoraku akan turba me kyau, wanda ko aure kukayi kuma zaku dora yaranku akanta, domin duk wanda yabi wannan turbar to ya tsira.


Shiyasa musulunci seda ya koya mana komai na yanda zamu rayu cikin aminci. Bawai ana nufin kadena zama kai da'Yar uwarka kuna fira ba, a'a yanda yakamata ku zauna kuyi firar shine musulunci ya koya mana.


Yau ko dakin mahaifiyarku zaku shiga yana da kyau ku farayin sallama, idan ta amsa kada kushiga harse ta baku izini, wannan shine koyarwar addinin musulunci.


Amma kai kana zaune kanwarka tana shafa kuna fira, e nasan azuciyarka bawani abu bane, kuma bazaka saka komai ba, amma kada ku manta shedan yana yawo ajikin dan adam kamar yanda jini yake yawo.


Kema Maryam da kike zaune babu mayafi idan kina tunanin Aliyu muharraminki ne sauran abokanshi muharramanki ne? Shifa musulunci yanaso kayi kokari wajen toshe duk wata kafa da shedan ze samu damar shigowa ya saka ka aikata banna.


Ina fatan kun fahimci abinda nake nufi? Daga kai sukayi jikinsu yayi matukar sanyi da bayanin mahaifinsu. Murmushi yayi yace naji dadi, kuma kada kusa wani abu aranku ko ku dauka ina zarginku ne ko kuma banyarda da ku bane, kawai nayi ne dan inkareku daga sharrin shedan.


Kema kuma Saude ina fatan kin fahimci abinda nake nufi? Murmushi tayi tace sosai na fahimceka, kuma naji dadin wannan tuni daka yi mana, Allah yabamu ikon gyarawa.


Ku ma se kuyi kokarin gyarawa, kada ku damu da dariyar da abokanku zasuyi maku dan kun hanasu shigowa gidanku, gara ace maka dan kauye da akiraka da wayayye, domin wata rana wadan da suke tare da kai sune zasu maka dariya idan wani abu ya sameka.


Abubakar yace haka ne Mama,  kuma mun fahimci abinda Baba yake nufi, insha Allahu zamuyi kokarin gyarawa, kuma munyi maka alkawarin babu wani abokinmu daze kara shigowa gidan nan, idan ma takama dole seya shigo to zamu fara zuwa muga halin da kannan mu suke ciki kafin mu barsu su shigo.


Sosai Babansu yaji dadin abinda sukace, yace nagode Allah yayi maku albarka. Sukace amin. Kallon Amina yayi yace wannan asabar din iyayen wannna yaro zasuzo kawo kaya, dan haka bawani rana zansa me tsawo ba se kizama cikin shirin barin gida.


Dariya suka samata, da sauri ta tashi tashige daki, Mamansu tace kai Malan hada kora, yace emana ai gara infada mata tasan da sani. Mama tace inde wannna zamanin ne kilama tarigaka sanin zuwansu.


Baba yace to Allah ya nuna mana, daga nan kuma sena Maryam dan naga su Aliyu sun tsaya ruwan ido, dama kuma nafiso infara kauda matan sannn, ku maza ne bakwa tsufa. Dariya sukasa gaba dayansu.





Malan Zakari kenan, yana zaune da matarshi guda daya me suna Saude a unguwar Dorayi, yaransu biyar, biyu maza ukku mata, babban danshi shine Aliyu, se Abukabar wanda suke kira da Abu,se Amina, maryam se auta Halimatu.


Malan Zakari yana daukar karatu awajen Malan Adam, duk da shidin karamin dalibinshi ne, amma duk inda Malan zeyi karatu to shima yana halartar wajen. Shima dan kasuwa ne, yana sana'ar saida yadudduka da shaddodi.


Yana da wada dede gwargwado, kuma yana wadata gidanshi da abinci, yaranshi duka sunyi karatun secondary, kuma matan daga nan basu cigaba ba, mazan ne kawai sukayi gaba. Inda Aliyu yagama Bayero ya karanci fannin kasuwanci.


Shi kuwa Abu ya gama Wudil, shi kuma yakaranci Geography, sede har yanzu cikinsu babu wanda yasamu aiki, hakan yasa suke zuwa kasuwa suna kasuwancinsu, kuma da haka suke rufa ma kansu asiri babu abinda kannansu zasu nema su rasa.


Malan Zakari ya dora yaranshi akan kyakkyawar tarbiya, kuma duk lokacin da yaga sunyi wani abu ba dede ba yana nuna masu fushin shi, sam baya yimasu da wasa idan yaga sun aikata wani abu marar kyau, sede daga baya yana kara nuna masu kuskurensu ta cikin sanyi.


Kuma yana matukar jan yaranshi ajiki, idan lokacin fada ne kuma yana zagewa yayi masu, hakan yasa sam basu rainashi ba, suna matukar kiyaye bacin ranshi, kuma suna girma mashi sosai.


Amina itace wadda za'a kawo kayan sa ranarta zata auri wani Ahmad shima dan kano ne kuma dan kasuwa ne. Ta fannin ilimin addini yaranshi mata sun sauke, kuma haryanzu basu dena zuwa islamiya ba.


Haka matarshi Saude macece meson addini, kuma tana da saukin kai, kuma tana matukar biyayya ga mijinta, haka kuma duk wani abu daze bata mashi rai tana kiyayewa, itama tana sana'ar saida kayan kulle kulle acikin gida.


Wanna shine takaitaccen labarin Malan Zakari.


Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[3/28, 9:16 AM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  10 ⚜ 15


Tunda safe Jameel ya tashi yashiga wanka  domin yau da wuri yakeson tafiya asibiti, yana fitowa jikinshi daure da karamin towel se wani a hannunshi yana goge jikinshi dashi, Mubina ce ta turo kofar dakinshi jikinta wasu kayan bacci ne doguwar riga me santsi  tana da siririn hannu iya karta guiwa.


Kanta babu dan kwali, murmushi Jameel yasaki yana fadin sweet Baby na har kintashi da wuri haka? Murmushi tayi tare da zama saman gadonshi tana fadin morning sweet Bro, hannu yasa ya shafi fuskarta yana fadin kintashi lafiya ko? Tace lafiya lau.


Turo baki tayi tana fadin haba Sweet Bro meyasa yau zaka fita dawuri? Mai ya dauko yazo ya zauna kusa da ita kafadarshi tana gogar tata yace am sorry, yau ina da patients da yawa shiyasa. Kanta ta dora saman kafadarshi tana fadin shikenan yau bazamuci break tare ba.


Man yafara shafawa yana fadin kinsan de bana iya cin abinci da wuri da na tsaya munci tare, kuma kema baci zakiyi yanzu ba, wai ya akayi ma kika tashi dawuri haka bacin nasan ba ki tashi da wuri? Kara turo baki tayi tace ai jiya naji kana waya da friend dinka wai zakazo da wuri yau.


Dariya yayi yana fadin dama jiya ba bacci kike ba kenan? To kiyi hakuri zan dawo da wuri kinji. Dago kanta tayi tace promise? Hannu yabata yace yes promise. Tashi tayi ta nufi drower dinshi tana fadin idan baka dawo da wuri ba zaka ganni ai.


Dariya yasa yatashi yana fesa spray ajikinshi tare da sharce gashin shi, kayan da zesa ta ciro mashi, juyowa yayi yace shiyasa nake matukar sonki Baby na, kinsan type dina, kin saba mani da komai duk ranar da kikayi aure nasan zansha wahala.


Turo baki tayi tace ni bazanyi aure in barka ba, sede idan ka yarda muyi a rana daya kuma duk matar da zaka aura se tayi mani zaka aure ta. Murmushi yayi yace na yarda, kema duk mijin da zaki aura se yayi mani.


Dariya tayi tace nayarda kaga se asa mana rana lokaci guda kuma ayi bikin mu rana daya. Amma fa kasani bazan taba aure a wani garin ba, kaima nasan a nan zaka zauna shiyasa duk wanda zan aura dole seya kasance dan garin nan ne.


Jameel da yake sa kaya agabanta sam be damu da tana kallonshi ba yace to idan kuma akayi mashi transfer fa? Tace ai ko sede yabarni anan yatafi. Dariya yayi yace ashe kuwa ze karo wata. Mubina tace inde ina kusa da kai ni ba ruwana.


Bayan yagama shiryawa ya kamota ta daukar mashi brief case dinshi suka fita. A falo suka sami Momy da Dady, murmushi Alh, yayi yana fadin ashe tana wajenka? Jameel yace wannan sarkin rigimar tun dazu tashigo ashe tasan zan fita office yau da wuri.


Momy tace nide nayi mamakin tashin mubina yau da wuri, ashe kai ne zaka fita. Zama sukayi tare da fadin Dady ina kwana? Yace lafiya lau, juyawa sukayi suka gaisheda Momy, murmushi tayi tace kuntashi lafiya ko? Sukace lafiya lau.


Tashi Mubina tayi ta hado ma Jameel lipton tasa mashi zuma ta kawo mashi. Amsa yayi yana fadin nagode Baby na. Alh, yace wannna shakuwar taku ina tausayin duk ranar da zaku rabu.


Jameel yace nima haka nagama fada Dady, shine Baby tace wai bazatayi aure ba sede ayi mana rana daya. Dariya sukasa Momy tace ai se ku maida hankali ku samo abokan auren alokaci guda. Dady yace sede kasamo mata acikin abokanka.


Mubina tace nima nice zan samo mashi. Dariya Jameel yayi yace aide ke bakida kawaye. Turo baki tayi tace Allah inde ba nice na zabo maka mata ba ba zakayi aure ba. Dariya sukasa gaba dayansu. Dady yace Allah ya nuna mana wannan rana, Momy tace amin.


Bayan Jameel yagama yatashi ya kamo hannun mubina yana fadin Dady, Momy zan tafi, murmushi sukayi sukace to Allah yabada sa'a, yace amin, idan wadan can sarakan baccin sun tashi natafi.


Nasan my twins sun tafi makaranta tun dazu ko? Momy tace kai ma ai kasan basa wuce karfe 7:00 tuni me aikinsu tagama shiryasu driver yatafi dasu, fita yayi yana fadin sena dawo. Har bakin mota Mubina ta rakashi tana ta mashi shagwaba da kyar yasamu ta barshi yatafi.


Lokacin da yaje asibitin haka yarika gaisawa da mutane domin Jameel akwaishi da jama'a, kai tsaye office dinshi ya nufa bayan yagama gaisawa da kowa. Wata kyakkyawar budurwace tashigo office dinshi fuskarta dauke da murmushi.


Daure fuska yayi ganin shigowarta, zama tayi tana fadin barka da zuwa Dr. Dago kai yayi ya bita da ido. Ilham kenan, itama 'yar kano ce mahaifinta shine Director na asibitin Aminu kano, kuma ita kadai gareshi


Tayi karatu a B.U.K a bangaren Nursing, bayan tagama Mahaifinta ya samar mata aiki a asibitin da yake. Ilham tun lokacin data fara ganin Jameel sonshi ya shigar mata zuciya.


Duk yanda taso Jameel ya gane tana sonshi yaki fahimta, domin shi sam batayi mashi ba, kullum seta shigo mashi office ta gaishe shi amma baya sakar mata fuska. Sosai takejin haushin Mubina.


Duk da cewar tasan gidansu daya amma tana jin haushin yanda Jameel yake bada kulawarshi a wajenta. Inde tazo office dinshi to kome yakeyi yana ajeshi ya maida hankalinshi akanta.


Sede idan yana tare da patients kawai take jiranshi, haka idan suna waya agabanta yake bata lokaci suyita fira kamar wasu masoya. Wannan abun ne yasa take tsananin jin haushin Mubina.


Gyara zama yayi yace lafiya lau, zaki iya tafiya wajen aikin ki. Murmushi tayi tace ko kanason tea? Wani file ya dauko yana fadin Baby na tabani, so zaki iya tafiya. Baki ta bude zata kara magana yadago afusace yace i said out.


Saurin tashi tayi jikinta yana rawa ganin yanda ya hade fuska, fita tayi lokaci guda taji wasu zafafan hawaye sun zubo mata. Hannu tasa ta goge tana fadin wallahi seka soni.



Laila ce ta fito dauke da jaka cikin  shirin fita makaranta, jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta yafa gyale a saman kanta dan karami kasancewar rigar me dogon hannu ce. A kitchen ta samu Ummansu ta fada mata zata tafi.


Kallonta Umma tayi tana murmushi tace lallai yau kin kusa makara, Laila tace wallahi kuwa. Umma tace to sekin dawo, tace to Umma. Fitowa tayi ta nufi gate, dan ta gaishe da Abbanta tun dazu.


Har ta kusa fita taji Abba yana kwala mata kira. Seda gabanta ya fadi jin muryar Abbanta dan jiya ta tsorata da yanayin daya shigo da kuma irin abubuwan daya fada masu jiya. Saurin juyawa tayi ta koma ciki.


Tana shiga ta sameshi a falo fuska adaure, dukawa kasa tayi kusa da kafafuwanshi  tana fadin Abba gani. Kamar wanda aka watsa ma ruwan zafi haka yayi saurin dauke kafarshi yana fadin Laila baki da hankali ne, dan zaki zauna sekinzo kusa da kafata? Daga yau banason kirika zama akusa dani, duk fadi falon nan be ishekiba se kinzo nan.


Kallonshi tayi amma shi ba ita yake kallo ba. Ummanta ce ta fito jin maganar Abba. Mamaki tayi ganin Laila bata tafi ba. Zama tayi tana fadin Laila lafiya baki tafi ba? Laila tace dama Abba ne yakirani.


Abba yace tashi ki koma kidauko katon hijabin da kike sallah dashi kisa, kuma ki dauko nikabi ki taho da safar kafa sannan kizo kitafi. Sakin baki sukayi ita da Umma suna kallonshi. Sede shi sam ba Laila yake kallo ba hankalinshi yana kan TV.


Umma tace Alh, zata makara fa, yanzu ina zata nemo wani nikabi a gidan nan ma ai bamu dashi, kuma hijabinta ai na sallah ne. Abba yace banaso in kara jin muryarki, idan har bata dasu to sede ta koma kada tafita yau.


Domin daga yau bazata kara fita bada irin shigar dana ce ba. Idan ko bazata iya fita haka ba, to daga yau bazata kara zuwa makarantar ba. Hawaye ne suka zubo ma Laila, wace irin rayuwa ce haka zata fara shiga? Duk gayunta amakaranta ace aganta da dogon hijab, ina ma laifin yace iyakar guiwa.


Wata irin tsawa Abba yadaka mata wadda tasa ta mikewar dole, kallonta yayi yana fadin idan bakida kayan ki koma zan siyo maki komai yau gobe sekije makarantar. Da gudu Laila ta shige daki tana kuka.


Kallonshi kawai Umma takeyi, da kyar ta iya bude baki tace amma Alhaji kana ganin wannan matakin daka dauka beyi tsauri da yawa ba? Kasan fa shi yaro duk da abinda aka koya mashi dashi yake tashi. Ina kai ne ka saka Laila makarantar da ko hijabi ba'a sawa ta secondary dinsu? Kuma tun tashi Laila agidan nan baka taba yimata magana akan shigarta ba.


Wani lokacin ma nice nake tsawatar mata amma baka damu da kasa baki ba, lokacin da take fita da karamin gyale kai ne fa me daukarta amota ka kaita makarantar. Karewa ma makarantar da take hade take da maza, meyasa tun can baya baka kawo gyara ba se yanzu? Uhm! Alhaji ina jimaka tsoron yaran zamani.


Shi icce tun yana danye ake tankwarashi, Laila tariga da ta girma, wani fada ko hargagi bazesa tayi abinda kakeso ba. Nasiha da lallashi shine abinda yakamata kayi mata idan kanason ka gyara kuskurenka.


Mikewa tsaye Abba yayi yana mazurai ya fara fada, babu ruwanki da sabuwar turbar dazan dora 'yata, ai ko zamanin sahabbai sun aikata abinda sukeso kuma daga baya da aka kawo gyara lokaci guda suka gyara.


Saboda haka nima dole Laila ta canza daga dabi'arta ta da ta dawo yanda nakeso. Murmushi Umma tayi tace a'a Alhaji, ai ko su sahabban ba kowane ya karbi gyaran da Annabi ya kawo alokaci guda ba, kuma shima beyi masu da zafi ba, a hankali suka rika shiga musulunci har sukayi yawa.


Da ace musulunci da zafi aka kawoshi bazaka samu mutane masu yawan yanzu ba acikinshi. Matukar mutum ya ai kata kuskure to dole se yayi ahankali sannna ya gyara, domin ba'a gyara zafi da zafi. Duk yanda kaso ka gyara Laila wayonka ko masifarka bazasu sa ta gyara ba.


Abba yace sede idan ba nine na haifeta ba, kuma bada sunana take amsa kira a makaranta ba, ai duk Uban da kika ga 'YA'YANSHI suna kin bin umarninshi to shiyaso. Kamar yanda Malan yace Allah yabamu AMANAR 'YA'YAN MU dole ne mutsaya kai da kafa muga mun gyarasu ta kowace hanya.


Wallahi kinji na rantse maki acikin gidana Laila ta gama fita jikinta abude, komai seta rufe, idan kinga ta bude fuskarta to acikin gida take, shima yaran nan suna zuwa zata saka hijabi ajikinta.


Wannan shine dokata daga yau, kuma ayau zanje insa a dinka mata kalar hijaban da nake so tasa. Nikaf da safa ma duk zansiyo mata. Idan kika bari na kama Laila tafita ba yanda nace ba daga ke har ita wallahi se ranku ya baci. 


Kema daga yau bazaki kara fita yanda kike fita ba, domin ku duka AMANA NE awajena. Idan kuma kika saba DOKATA zaki tabo lafiyar aurenki. 🤣. Daki yashige yana huci. Tagumi Umma ta buga jin wannan abun mamaki na Abba. Wato itama DOKAR tazo kanta. 


Tashi tayi taje tana lallashin Laila wadda take ta kuka. Umma tace hakuri zakiyi, Allah yabaki mahaifi me wata irin fahimta, nasan abinda yafada gaskiya ne, amma kuma ai ba haka ake gyara ba, tun farko laifin mu ne da bamu koya maki hakan ba.


Su sauran yaran da suke fita haka ai iyayensu sun koya masu tun suna yara, amma ada idan ina maki magana shine yake kareki, gashinan yanzu kuma yanaso yayi gyara sede besan ta yanda ze fara gyaran ba.


Shi addini ai dan fahimta ne, dan haka idan kinaso muzauna lafiya a gidan nan dole kibi umarnin mahaifinki, domin nima DOKAR hadani ta shafa, kuma kinji yace idan yaga mun saba zan taba lafiyar aure na.


Idan kuma kinaso intafi inbarku ya auro maku wadda yakeso to ki saba umarninshi. Cikin kuka Laila tace haba Umma, ta yama za'ace wai nice zan fita da wannan shigar? Kinsan kuwa yanda mukema masu irin wannan shigar dariya amakaranta? Ni kam gara in hakura da karatun.


Umma tace to idan kika hakura wa kikayi mawa? Kuma shikenan agida zakiyi ta zama bazaki fita ba? Kinsan de halin Alhaji, yanda wannan akidar tashigeshi lokaci guda wallahi mijin aure ma yana iya cewa shine ze zaba maki.


Laila tace haba de Umma, wannan kuma ai baze mun haka ba. Umma tace toshikenan, zakice na fada maki. Idan ma zaki cire wannan tunanin na barin karatu kicire. Ke mace ce dama kuma haka manzon Allah ya koyar da duk wata mace data fita cikin shigar mutunci.


Da kinyi aure shikenan kin fita daga takurar mahaifinki. Amma kisani dole zakiyi abinda yace matukar ina cikin gidan nan, domin bazan barki kijawo mani mutuwar aure na ba🤣.


 Kwanciya Laila tayi tana wani irin kuka. Tashi Umma tayi tana fadin idan kin gama kukan kifito kidora abincin rana tunda zuwa makarantar ya fasu.


Tana fita Laila ta tashi tana fadin wallahi kona fita da wannan shigar bazanje makaranta da ita ba, ai de baze bini har makarntar ba bare yaga yanda nake. Cab, Allah ya kyauta inje makaranta da wannan shiga ai se kawayena ma su rai nani, bacin dariyar dazan sha. Murmushi tayi lokacin da wata dabara tazo mata. Tashi tayi tashige bandaki ta wanko fuskarta ta nufi kitchen.



Maman su Halima ce ta fito zuwa gidan makociyarta domin ta karbo rariyarta da ta ara, dan bakowa gidan, Amina ce itama kuma taje kitso. Da sallama tashiga gidan. A tsakar gida ta iske mutan gidan dan su 3 ne agidan kasancewar na haya ne.



Da kallo tabi gidan aranta tana fadin zanga ranar da matan gidan nan zasuyi tsafta. Amsa mata sallamar akayi, murmushi sukayi suna fadin Maman Halima ce? Tace wallahi kuwa nice, duk ina kwanan ku? Suka ce lafiya lau.


Zama tayi tana kara kallon yaran da suke tsaye a tsakar gidan. Maza ne da mata wadan da a kalla mazan zasu kai shekara 14, matan kuma su 3 ne babbar cikinsu zata kai shekara 18, sauran biyun kuma zasu kai shekara 15. Se wasu yara guda 2 wadan da bazasu wuce shekara 10 ba.


Yakamata ace sun tafi makaranta amma gasu nan zaune agida suna jiran su dauki talla. Wata mata ce takira karamin danta tana fadin Audu zo ka kai mani nikan mana. Turo baki yayi yana fadin Allah Inna yau bazan je ba.


Ba ga Zainab nan ki aiketa mana. Wadda aka kira da Inna tace haba dan autana, Zainab ai itace zata kai tallar ko, taho ka kai mani. Tsaki yayi yana fadin to wallahi sekin bani 20. Dariya tayi tana kwance zaninta tana fidin inde 20 ce taho gata.


Amma kayi sauri kaji. Dariya yayarshi ta mashi, aiko ya gundumo mata wani uban zagi seda Maman Hailam ta rike baki. Kamashi Inna tayi tana fadin rabu da ita zan kamata ne, dauka katafi.


Yana dauka ya harareta yana fadin 'Yar shegiya, zabura Zainb tayi zata bigeshi Inna tayi saurin riketa tana fadin maza ka ruga, Zainab tace wallahi se naci Ubanka. Inna tace kibarshi so kike yaki kai mana nikan kizo kitafi tallar.


Turo baki Zainab tayi tana fadin ke wallahi Inna duk kece kike sawa wannna yaron yana rai na ni. Inna tace yi hakuri ki kyaleshi, kwallo tayi da wani bokiti tashige daki.


Maman Halima kuwa tagumi tayi tana kallon ikon Allah, can ma taji wasu yaran suna zage zage iyayen se lallashinsu sukeyi kamar sune 'ya'yan. Jinjina kai tayi aranta tana fadin lallai idan kana shiga gidajen mutane zakaga rayuwa. Wato kowa da kalar tarbiyar dayake bama 'YA'YANSHI.


Kamar ba AMANA Allah yabamu ba. Ajiyar zuciya tayi jin ana mata magana, murmushi tayi tana fadin maman Audu rariya nazo karba zanyi amfani da ita ne. Dariya Inna tayi tace kiyi hakuri wallahi tun jiya na bama Audu ya kawo maki ashe yana fita seya yardata a zaure, Allah yaso yara sun gani suka kawo mani.


Tashi tayi ta dauko mata, kallon wannan budurwar tayi yar shejara 18 tana zaune tana ta uban kwalliya mamanta tana kusa da ita tana hada mata kayan talla. Haka tagama kwalliyar ta tashi ta dauki tallar tana fadin Maman mu ta nawa ce? Murmuhsi Mamar tayi tana fadin ta dari 300 ce.


Yarinyar tace amma fa kinsan ina binki 200 ko? Mamar tace nasani idan kika dawo zan baki. Yarinyar tace to ga kudi nan ki bada asiyo mani waken suya dana dawo da rana zan badashi nika. Mamar tace to sekin dawoAllah yabada sa'a, dan Allah kishiga har can wajen masu bulo naga suma suna siya da yawa, yarinyar tace to.


Haka tafita da wasu matsatstsun kaya tasa wani karamin gyale se taunar cingam takeyi. Maman Halima kuwa da ido ta bita, wato da safe zuwa rana ta kaima Mamanta talla, da dare kuma tafita waje ta soya awararta.


Lallai ana rayuwa aduniya, aranta tace Allah nagode maka da kayoni a irin gidan dana tashi, kuma kabani miji tsayayye, Allah nagode maka da kabani shiryayyun 'ya'ya baka yoni a irin wannan rayuwar ta gidan nan ba.


Bayan Inna takwo mata rariyar tayi masu sallama ta fita tana me cike da al'ajabin abinda tagani. Duk yanda taji ana fadin halin yan gidan Ukku bata taba yarda ba se yau data gani da idonta, domin ita bata cika shiga gidansu ba seda dalili.



Gidan Ukku kenan, haka mutanan unguwar suke kiran gidan, kasancewar mata ukku ne agidan kuma kowa da mijinta, gida ne da kowa yake zaman kanshi, sam yaran gidan basu da tarbiya, makaranta ma se sunga dama suke zuwa, kowa tana da yaranta, manyan suna secondary amma befi asati suje so 2 ba, haka kananan da suke primary suma sam basu cika zuwa ba, koda zunje ma gudowa sukeyi.


Kowace mace da irin sana'ar da takeyi agidan, kasuwanci shine abinda zukasa agaba, mazajensu kuwa idan suka fita tun safe se dare suke dawo wa, shiyasa yaran sukeyin abinda suka ga dama. Zainab da Zarah sune manyan 'yan mata agidan, Zinab diyar Dije ce, ita kuma Zarah diyar Mariya.


Su duka suna da sana'arsu, bayan sunyi ta iyayensu da dare se suyi tasu, idan kaga yanda suke wasa da maza seka dauka wasu manyan 'yan mata ne, kullum kuma se sunyi tadi, babu ranar da wani namiji baze zo kofar gidansu ba.


Suyi awajen tallarsu, kuma idan sun dawo gida suyi, idan basuyi kasuwa ba wani lokacin se su kai har karfe 9 a waje, kuma sam iyayensu basa masu fada. Domin agidan kowace mace bataso aji tana ma yaranta fada koda kuwa karamin yaro ne. Sam sun manta cewar AMANAR 'YA'YAN Allah yabasu.


**** ***


Da misalin karfe 2:30 na rana motar Mubina tayi parking a asibitin su Jameel, dan tun dazu take kiranshi awaya be dauka ba, gashi har 2 ta wuce bedawo ba hakan yasa ta taho asibitin. Shi kuma yau aiki yayi mashi yawa, wayarshi ma a office ya barta.


Haka ta fito tana sanye da wata doguwar riga 'yar kanti me dogon hannu red colour, ta yafa siririn mayafi fari, kafarta wani takalmi ne me tsini shima fari, sosai tayi kyau, fuskar tana dauke da shade glass, sede gaba daya rigar tabi shape din jikinta, komai yafito.


Haka 'yan asibitin suka rika binta da ido, kai tsaye office dinshi ta nufa, tana zuwa masinjanshi yataso yana mata sannu da zuwa, ya tsuna fuska tayi tace yauwa sannunka. Kofar takama zata bude masinjan yace hajiya sede Dr. baya nan.


Kallon raini tayi mashi tace ina yaje? Sosa kai yayi yace yana dakin dayake duba marasa lafiya. Tsaki tayi tashiga office din, tebur dinshi ta duba anan taga wayarshi, tsaki takara ja tana fadin Sweet Bro baya son daukar wayarshi.


Wayar ta dauka tafita, kai tsaye ta nufi dakin da yake. Tun daga nesa wanda suke tare da Ilham ya tabota yana fadin ga mutuniyar nan. Saurin juyowa Ilham tayi tana kallon inda yake nuna mata.


Tsaki taja tana fadin banson iskanci Yaseer, dama wannan banzar ce kake nuna mani. Dariya Yaseer yayi yace kede kin tsani yarinyar nan, ni kuma wallahi burgeni takeyi, ina masifar sonta, dama Dr, ze bani ita ai dana huta.


Murmushi Ilham tayi tace da gaske kana sonta? Yaseer yace wallahi da gaske nakeyi, sede bansan ta yanda zan bullo mata ba. Ilham tace kawai kafada mata dan mutum ya tsaya yana boye son wani aranshi beda amfani.


Nima da tun tuni na fadama Dr, ai da yanzu mun wuce wajen, amma natsaya ina boye sonshi, kai me sauki nema kuna mutunci da Dr, idan kabiyo ta wajenshi ze shawo maka kanta, dan yanda take sonshi babu abinda zece mata bata amince ba.


Ance fa acikin yan gidansu gaba daya sunfi shakuwa, duk da suna sakon juna amma basa irin fadan nan, ni nasan da ace yaya yana auren kanwarshi babu abinda ze hana Dr, be aure taba. Yaseer yace kin kawo shawara.


Amma kema meze hana kibi ta wajenta kozaki samo kanshi? Ilham tace kabarni kawai, nasan yanda zanyi, amma ni banason yarinyar kwata kwata bazan iya mata magana ba. Isowar Mubina wajensu yasa sukayi shiru.


Murmushi Yaseer yayi yana fadin barka da zuwa ranki yadade, wani banzan kallon tayi mashi ta amsa ciki ciki, watsama Ilham harara tayi ta wuce, itama Ilham din harararta tayi ta kauda kai.


A hanya suka hadu da Jameel, yana ganinta yasaki fara'a zumburo baki tayi tare da juyawa zata koma inda ta fito, da sauri ya biyo bayanta, sunzo dede wajen su Iham yayi saurin kamota ya rungumota ta baya yana dariya.


Mikewa tsaye Ilham tayi, jitake kamar taje ta shakota, wani irin bakin ciki yake kamata aduk lokacin da taga Jameel yana taba Mubina, duk da tasan kanwarshi ce amma ta tsani taga yana taba ta. Tsaki Yaseer yayi, dan shima baya son wanna dabi'ar tasu da suka koyo a turai.


Hakuri Jameel yabata da kyar yasamu ta hakura, dariya suka sa gaba daya ya kama hannunta suka wuce office. Sosai wannna abu ya kona ma Ilham rai, har seda tayi kwalla, Yaseer ne yayita bata hakuri, kawai jakarta ta dauka ta nufi gida tana tunanin abinda zatayi ma Mubina. 


Shima Yaseer yaji haushi matuka, shima so yake yasamu ta amince mashi ko ya rabata da Jameel, yafiso wannan kulawar da take bashi ta dawo wajenshi, ko tazo asibitin se tafara zuwa wajenshi kafin taje gunshi. Tashi yayi yana fadin Allah de ya kai damo ga harawa.


Nikam nace ko beci ba yayi banna🤷🏻‍♀😂.


Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[4/23, 11:52 AM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  15 ⚜ 20


Kamar yanda Alhaji Sambo ya fada haka yaje kasuwa yasiyo ma Laila duk abinda yace, kuma yace dole haka zata rika fita. Haka Laila ta karbi kayan sam bata nuna damuwa aranta ba hada godiya tayi mashi.


Bayan ta koma daki Alhaji yace kin gani ko, ai dama nace maki bana saka Doka agida aki daukarta, amma da kin tsaya jayayya dani, duk megidan da kika gani iyalanshi suna juyashi to sakaran megida ne.


Hakkin kula daku akaina ya rataya, Malan ya ce matukar ban kula daku yanda ya kamata ba hakika Allah kona ni zeyi, saboda haka ki bani hadin kai mu tsira tare. Umma tace ai dama ni bance bazan baka hadin kai ba.


Kawai yanda ka dauki mataki ne abun yayi tsauri, shi gyara a hankali a keyinshi, amma fa ka hana yaranka maza shigowa gidan nan matukar Laila tana nan, me kayi kenan? Kamar fa ka raba kan 'Ya'yanka ne.


Ka manta yanda zumunci yake? Hannu tasa ta goge kwallar da ta zubo mata,tace Alhaji ina ji maka tsoron yaran mu su shiga wani hali, kasan yanda takura take maida Yaran zamanin nan.


Dan Allah Alhaji ka sauka ka masu, ba dole se anbi ta irin wannan hanyar daka kawo ba sannan zamu gyara gidan mu ba, wallahi na tabbata ko gidan malamin da ya fada maku wannan maganar ba zaka samu irin wannan tsatstsauran ra'ayin ba.


Tashi Alhaji yayi yana fadin zaki bata mani rai fa, tunda de su yara na sun fahimce ni idan ke baki fahimce ni ba bani da damuwa. Su kadai ne bazan iya canzawa ba, amma ke zan iya kawo 3 ma bayan ke.


Idan kuma naga dama zaki iya komawa gidanku kizauna acan inda baza'a sa maki doka ba, kinga ko mata 4 naso zan aura. Daki ya wuce yana masifa. Tagumi Umma tayi tana fadin to Allah ya kyauta.



**** ****


Washe gari haka Laila ta shirya kamar gaske, tsaf ta fito kamar yanda Alhaji yakeso. A falo ta sameshi, dukawa tayi ta gaishe shi. Murmushi ya saki gaba daya Laila ta gama burgeshi, kallonta yayi yace yauwa diyar albarka.


Yau kin matukar burgeni, Allah yayi maki albarka. Dubu 2 ya mika mata yana fadin gashi yau kinyi mani abinda nake so, tashi kitafi inaso ma in samu karamar mota se direba yarika kai ki.



Saurin dago kai tayi tace Abba kawai kabarshi nafison hawa Adedeta. Murmushi yayi yace shikenan, ai tunda kinyi abinda nake so kema zanyi maki abinda kike so. Tashi ki tafi Allah ya bada sa'a. Tashi tayi tana fadin amin.


Dakin Umman ta taje tayi mata sallama sannan tafita, da kallo ta bita cike da tausayi dan tasan yau a makaranta se anyi mata dariya, girgiza kai tayi tace Allah ya kyauta. Ta kofar dakin su Hamza tazo wucewa.


Dariya taji ana mata, tana juyowa ta ga Hamza se dariya yake mata hada rike ciki, matsawa tayi ta buga mashi jakar da take hannunta tayi tana fadin wallahi Hamza zanyi maganinka.


Dariya yayi yace wallahi kin bani dariya, ji nake kamar na biki dan naga irin dariyar da za'ayi maki ayau, amma dan Allah koda wasa kada ki bude fuskarki kowa ya gani. Ihu Laila tasa tare da kwada mashi jakar.



 Muryar Alhaji sukaji yana fadin wane irin sakarcin banza ne haka? Dama baki tafi makarantar ba kika tsaya kina wasa da namiji? Da sauri Laila ta fice, Hamza kuwa juyawa yayi ya koma daki yana fadin aifa mun shiga ukku da wannan sabuwar Dokar.



Laila tana hawa Adedeta tayi saurin cire hijab dinta da safar da nikaf din, dama tayi shigarta yanda ta saba, cikin jakarta ta saka kayan data cire. Duk abinda takeyi me Adedeta yana kallonta.


Juyowa yayi yace Hajiya lafiya de? Daure fuska tayi tace ina ruwanka? Kayi abinda yake gabanka. Murmushi yayi yace amma Hajiya ai naga ba haka kika fito daga gida ba, Laila tace wallahi idan baka rufe mani baki ba zan sauka. Me Adedeta yace Allah yashirya.



Zaune Jameel da Mubina suke a falo suna cin abinci, tana sanye da riga da wando 3 qaurter tana jingine a jikinshi yana bata abinci abaki suna fira, Karami ne da Mufida suka shigo suna guje guje.


Jameel yace wai ku se yaushe zakuyi hankali?  Mufida tace Yaya wai wayata ya karbe saboda na daukar mashi tashi jiya. Mubina tace sis rabu dashi ze baki ne. Momy ce tashigo tana fadin ku ma de bakin ku kuke son batawa.


Wa yake shiga tsakanin Karami da Mufida, ai ko kun shiga kune zakuji kunya. Dariya suka sa, Momy tace Mufida jeki gani idan an gama abincin Dadyn ku. Daki ta wuce, Karami yabi Mufida yana fadin jirani mutafi.


Jameel yace gashinan yanzu ma munji kunya. Wayarshi ce tayi kara yana dubawa yaga number din Ilham ce, tsaki yayi ya daga, bayan sun gama gaisawa Ilham tace Dr, kaci abinci kuwa? Jameel yace wace irin tambaya ce haka kuma? Zatayi magana ya kashe wayar.


Turo baki Mubina tayi tana fadin sweet bro wannan yarinyar ce ko? Murmushi yayi yace wallahi nima bana son wannan damun da take mani, ko zanyi aure ai bazan iya aurenta ba saboda bata da kamun kai. Mubina tace nide bana sonta, kabari zan sama maka matar da zaka aura.


Wayarshi ce ta kara ringing,saurin daukar wayar Mubina tayi tana dagawa Ilham tace haba Dr, Mubina tace dan Allah ki rika kama kanki, ya kina mace zaki rika kiran namiji, kawai yana cin abinci zaki wani dameshi.


Ilham tace se ki bari idan ke na kira sannan zaki fadi haka, koma menene ai Dr baze aure ki ba. Tsaki Mubina taja ta kashe wayar kamar zatayi kuka Jameel ya jawota ya rungumeta yana lallashinta.


Mubina tace Sweet Bro kajifa abinda tace, Jameel yace kibarni da ita, zanyi mata rashin mutunci kuma nayi maki alkawari bazan taba sonta ba. Murmushi Mubina tayi tace kayi alkawari? Yace sosai ma.




**** *****


An yi bikin Amina komai lafiya haka aka kaita gidan ta da yake unguwar Darmanawa, ba laifi Iyayenta sunyi mata kaya masu kyau, haka aka kaita gidanta tana kukan rabuwa da gida, haka kannanta sukayi mata sallama suma seda sukayi kuka.


Yanzu gidansu yarage saura su 4, cikin ikon Allah Aliyu ya samu aikin koyarwa a makarantar secondary ta mata, sosai Iyayenshi sukaji dadi, kuma duk da haka be saki kasuwancinshi ba, haka ya fara aikinshi cikin sa'a.


Kuma sosai suka gyara kuskuren da sukayi, sam abokansu yanzu baza shigowa cikin gidansu, idan har sunzo sede su tsaya awaje, har seda abokan suka fara masu tsegumi, amma basu damu ba.


Haka Babansu ya toshe kofar dakinsu ta waje ya maidota ta cikin gida, ya kasance ta kofa daya suka shigowa, haka idan dare yayi kofa daya ake kullewa. Haka suke rayuwarsu cike da kaunar junansu, suna matukar kula da kannansu.



**** ****


Lokacin da Laila ta gama lectures haka ta hau Adedeta tana shiga ta maida kayanta ta nufi gida, shide me Adede kallonta kawai yakeyi aranshi yana fadin Allah yashirya, da alama Iyayenta basu san haka takefita ba.


Yaso yayi mata magana amma seyayi tunanin kada tayi mashi rashin kunya saboda babban mutum ne hakan yasa yaja bakinshi yayi shiru yana fadin abunda babu ruwanka dadin kallo gareshi.



Tana sauka tashige gida tana murmushi aranta tana fadin Abba kenan, idan kasan wata ai baka san wata ba, amma wallahi bazan iya shiga makaranta da wannan shigar ba, haka kawai a rainani.


Kai tsaye dakinta tawuce dan bata son Umma taganta tana iya biyota, tana gama cire kayan tashiga bandaki tayo wanka seda ta gama shiryawa sannan ta nufi dakin Umma.


Murmushi Umma tayi tana fadin 'yan makaranta har kin dawo? Laila tace wallahi kuwa Umma yau da wuri muka gama, ina Abba be dawo ba? Umma tace ai kinsan tunda yafara tsayawa karatu yanzu baya dawowa da wuri.


Tashi kije ga abincinki can ki dauka, ni ban tambayeki bama, ya kuka kare da kawayenki? Laila tace name Umma? Murmushi tayi tace wai na sabuwar shigar da suka ganki da ita. Laila tace ai bazasuyi magana agabana ba, sede idan na tafi. Umma tace to koma sunyi ai zasu gaji ne, dan kin rika wannan shigar kenan har kibar gidan nan.


Tashi Laila tayi tana fadin Allah ya nuna mani ranar barin gidan, ai ba wani abu bane dan nayi wannan shigar, nima na huta da yawan kallon da maza suke mani, fita tayi domin daukar abincinta. Murmushi Umma tayi cike da tausayin Laila dan tasan hakuri kawai takeyi babu yanda zatayi da hukuncin Abbanta.


***** *****


Zaune Ilham take a office din Yaseer ta gama fada mashi wulakancin da su Jameel sukayi mata,seda Yaseer ya gama dariya sannan yace kema de Ilham, taya zaki kirashi yana gida, bayan kinsan dole yana tare da Mubina.


Ai yanda kuke aiki waje daya haka zaki samu ki shawo kanshi, ni yanzu haka shi nake jira yazo naje muyi maganar Mubina. Murmushi Ilham tayi tace kana ganin zata amince maka? Yaseer yace namiji ne fa ni. Kede kisa ido kigani.


Tashi Ilham tayi tana fadin gashi can ma yazo, na tafi. Murmushi Yaseer yayi yace Allah ya bada sa'a. 



Jameel yana shiga ya aje jakarshi. Da masinjanshi taci karo ze kai mashi coffee, amsa tayi tace zan mika mashi.


Tura kofar tayi bakinta dauke da sallama, be dago kanshi ba ya amsa dan yasan itace, kusa da tabur dinshi ta matso tana fadin Dr, sannu da zuwa ka tashi lafiya? Kamar baze amsa ba can kuma yace lafiya.


Mika mashi cup din tayi tana fadin ga coffee dinka. Dago kai yayi fuskarshi a daure yace bana bukata, murmushi tayi ta zauna tana fadin nasan kana bukata kawai dan ya fito daga hannuna ne yasa kace baka so.


Kallonshi tayi idonta cike da kwalla tace wai Dr, meyasa ka tsaneni ne? Dama so yana zama kiyayya ne, kasan tun lokacin da nake sonka kuwa? Hannu tasa ta share kwallar data zubo mata tace ban taba tunanin  zan bude baki ince ina son wani Da namiji ba.


A kanka kawai na fara fadar So, meyasa bazaka mani adalci ka amshi tayi na ba? Baka tunanin kaima wata rana Allah ya dora maka son wata azuciyar ka? Haba Dr, meye aibuna? Me na rasa? Idan ma baka sona ba haka ya kamata ka mani ba.


Kanta ta dora saman tabur din tasa kuka sosai. Saurin tashi Jameel yayi ya isa wajenta, gaba daya hankalinshi ya tashi, sam baya so yaga mace tana kuka, dukawa yayi yace Iham dan Allah kiyi shiru haka nan, idan wani yazo ze dauka wani abu nayi maki.


Shikenan naji, tashi ki goge idonki muyi magana, saurin dago kai tayi tana murmushi, tashi yayi ya koma saman kujerarshi ya zauna. Kallonta yayi yace Ilham ni bance bana sonki ba, sede nida Baby munyi ma juna alkawarin zaba ma junanmu abokan rayuwa.


Idan Baby taga na zabo matar da nake so da kaina bazataji dadi ba, idan har kinaso na amince dake to kije kisamu Baby idan har ta amince nima na amince. Saurin mikewa Ilham tayi tare da daure fuska tace saboda ina sonka se naje na nemi amincewar wata ban..........


Bata gama rufe bakinta ba taji saukar mari a fuskarta, idanuwan Jameel har sun canza saboda bacin rai, kallonta yayi fuska adaure yace idan har kika kara furta irin wannan kalmar abakin ki ina me tabbatar maki sena zubar maki da hakora.


Banza marar kamun kai, idan ba rashin aji ba taya kina mace zaki rika bibiyar namiji, fita kibar mani office, wallahi idan na kara ganin kafar ki a office dina se nayi maki wulakancin da ko kare baze dauka ba.


Marar tarbiya kawai, fita nace. Da gudu Ilham ta fita tana kuka, tsaki Jameel yayi ya dauki wayarshi yabar office din. Kai tsaye office din Yaseer ta nufa. Yana ganinta yasan ba'a dace ba.


Seda tagama kukanta sannan tabashi labarin abinda Dr, yayi mata. Jinjina kai Yaseer yayi yace lallai wadannan mutanan suna ji da kansu, wallahi idan har naje wajenshi yayi mani wulakanci sena gwada mashi asalin hali na.


Ilham tace wallahi nima bazan kyaleshi ba, nize kalla yakira da marar tarbiya, wallahi sena gwada ma duniya sune basu da tarbiya, mutanan da basu san mutuncin kansu ba, haka zerika rungumar kanwarshi wama yasani ko sonta yakeyi.


Yaseer yace kibar ni dashi, yanzu bazanyi mashi maganar ba, nasan zega kamar bakinmu daya, zuwa gobe zan sameshi da maganar. Ilham tace ai wallahi koda ya amince da bukatarka sena dauki fansa akan abinda yayi mani. Yaseer yace kede Allah ya kaimu goben.



***** *****



Dije ce ta fito daga daki da sauri jin yaronta yana kuka a tsakar gida, Mariya ta samu tana kokarin rabasu da Danta da suke fada, da sauri Dije ta karasa tana fadin haba Mariya, ya suna fada zaki kama Dana kirike kibar Danki yana dukanshi.


Wannan ai ba adalci bane, ina karfin Audu ina na Sale, Audu shine yakamata ki rike amma zaki kama Dana ki rikeshi yana dukanshi. Mariya tace dadina dake son kai, yanzu ba rabasu kika ga inayi ba.


Hannu Dije tasa ta kamo Sale tana fadin dan Allah kalli yanda ya yakusheshi a fuska, hannu tasa ta wanke Audu da mari tana fadin kai me yasa mugu ne? Uban meyayi maka zaka bata mashi fuska haka? Mariya ta cakumo Dije tana fadin wannan ai rashin adalci ne.


Agabana zaki mari Dana, fada suka kaure dashi suna zage zage, da sauri Zakiya tafito tana fadin haba jama'a, meyayi zafi zakuyi fada akan Yara, kokarin rabasu ta farayi. Zarah ce da Zainab suka shigo sun dawo daga talla.


Saurin aje kayan sukayi kowa yazo yana kokarin kwace uwarshi, da kyar suka rabasu, Dije tace ai dama na fada maki, duk ranar da Audu yakara dukan Sale sena rama mashi, ai Da befi Da ba.


Zarah tace haba Mama dan Allah meye na fada? Mariya  tace bazanyi ba da Ubanki, kina kallon yanda ta maida fuskar kaninki amma kike fadin inyi shiru. Zarah tace ai se kiyi tayi tunda ance kiyi shiru bazakiyi ba, ni wallahi dama ban tsaya raba ku ba.


Murfin bokiti tasa ta jefi Zarah dashi tana fadin to fitsararra, rashin kunya zakiyi mani? Daki Zarah ta wuce tana gungunai. Zakiya tace dan Allah kuyi hakuri, ba'a shiga fadan yara, yanzu se su baku kunya.



Hannun Dije ta kama tana fadin muje ciki kuyi hakuri dan Allah. Dije tace ai shikenan tunda na rama mashi, bazan kara barin Audu yaci zalin Sale ba, dan taga yafi karfinshi ne. Daki tashige tana ta masifa. Zainab ta dauki kayanta ta bi bayanta tana fadin kullum se anjiyo muryarku kuna fada kamar wasu kananan yara.



***** ****


Zaune Laila take adakinsu Hamza suna kallon wani american film, Saleem ne yayi sallama yashigo bayan yadawo daga aiki, Laila tace Yaya yau ka dawo da wuri. Saleem yace yau banyi over time ba shiyasa.


Hamza yace Yaya sannu da zuwa. Yace yauwa sannu sarkin kallo, wai tsaya ma, ke Laila ba Abba ya hanaki zuwa wajen mu ba? Turo baki Laila tayi tace wallahi Yaya gidan babu dadi, Umma taje gidan kawarta se ni daya aciki shiyasa kawai na taho nan.



Saleem yace ai gara shi Hamza yaje can falo kuyi kallon da kizo nan, Hamza yace Yaya kasan de idan Abba yazo ya sameni a falo se raina ya baci, kawai kabarta idan muka gama kafin Abba yadawo zata tafi. Saleem yace katashi kutafi can falon kuyi kallon nima banaso tashigo mana daki.



Laila tace kai Yaya dan Allah, Saleem yace Laila nan fa dakin maza ne, abokan Hamza zasu iya shigowa bazasuyi tunanin kina ciki ba, amma idan kuna can falon dole zasu tsaya daga waje, bana son taurin kai kawai kitashi kitafi falo.


Tunda haka Abba yakeso ai gara mu kiyaye shima yana da gaskiya ta wani fannin. Hamza yace wallahi bawani gaskiya kawaide yashiga wata akida ce ta daban. Saleem yace ko ma menene Laila bazata kara shigowa dakin mu ba.


Tashi ki fita. Tashi tayi tana zumburo baki Hamza yatashi yana fadin muje in raka ki ai Abban se yayi isha'i ze dawo. Saleem yace oho de, kai kaji zaka iya da fadan Abba. 



Hamza yace rabu dashi, aide shima baya zama gida sosai. Suna fita motar Abba tana shigowa.



Yana kai dubanshi wajen dakinsu Hamza ya hango shi da Laila kanta ko dankwali babu sun fito daga dakinsu suna dariya. Ai ko parking be gama yiba ya bude kofar motar yafito ya nufi wajensu jikinshi har tsuma yakeyi.



Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263


Ina mika dubun godiya agareku masoyana. Allah yabar zumunci😘😘👍🏻👍🏻

[4/25, 11:37 AM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  20 ⚜ 25


Kamar Abba ze kifa saboda sauri, ganin yanda yake tunkarosu yasa Laila tashige dakinsu Hamza da sauri, alokacin Saleem ya cire kayanshi ze shiga wanka yana sanye da gajeran wando.


Abba beyi ta kan Hamza ba kai tsaye dakin yashiga dan yafison yafara hukunta Laila, Saleem ya bude baki zeyi mata fada kenan suka ga shigowar Abba. Cak Abba ya tsaya yana kallonsu, Saleem ma kallonshi yakeyi.


Hannu Abba yasa ya wanke Saleem da mari wanda yasa yakusa faduwa saboda besan da zuwan marin ba. Dayan hannun yasa ya wanke Laila da mari, hannunta ya kama suka fita yana fadin gaba dayanku kusameni afalo.


Hamza da yake abakin kofa yana jiyosu da sauri ya nufi hanyar falo jin abinda Abba yace. Saleem kuwa mamaki ne ya hanashi motsi, wai yau shine Abba ya mara, toshi ina ruwanshi shida yace ta tabar dakin amma baze tsaya yayi bincike ba kawai ze dauki mataki.


Rigarshi ya dauka jallabiya yasa yafita ranshi abace. Zaune suke a falo Laila se kuka takeyi. Cikin tsawa Abba yace ina Ummar ku? Hamza ne yace ta fita. Waya Abba ya dauko ze kirata se gata tashigo da sallama.


Seda gabanta yafadi ganin su gaba daya afalo, waje ta samu ta zauna tana fadin barka da zuwa Alhaji. Fuska adaure ya kalleta yace ina kikaje? Umma tace mantawa kayi dazu na fada maka zanje dubo diyar Hajiya Mairo bata da lafiya.


Amma ya akayi kika fita ahaka, ko kin manta abinda nace maki? Dukar da kai Umma tayi ganin yanda Abba yake mata magana kamar wata diyar cikinshi agaban 'Ya'yanta. Tsawa Abba ya daka mata yana fadin bada ke nake ba? Saleem ne ya dago idanuwan shi wadan da sukayi ja yace Abba da kun shiga daga ciki zefi.


Abba yace to marar kunya se kazo kashigar damu. Saleem yace kayi hakuri Abba, gani nayi baku taba haka agaban mu ba, be kamata saboda wani dalili na daban ba ace zaku fara haka agaban mu ba.


Tsaki Abba yayi yace daga yau idan har kika kara fita bada irin shigar dana ce ba wallahi zan dauki mataki akanki, idan kuma kinason igiyar aurenki ta ragu ki kara maimaita irin wannan abin da kikayi.


Gaba dayansu dagowa sukayi suna kallon Abba, Umma kuwa hawaye ne suka zubo mata, gyran murya Abba yayi yace ke Laila uban me kikaje yi dakin Maza? Dukar da kai Laila tayi, tsawa yadaka mata yace ba magana nake maki ba? Hamza yace Abba bafa waji abu taje yiba kawai sako ta kai mani.



Abba yace sako? Shine zata shiga har ciki shi wancan ko kaya babu ajikinshi haka tashiga dakin, idan akwai shedan adakin shikenan yayi maku hudubar banza daga kai har kaninka ku aikata........... cikin tsawa Umma ta tashi tana fadin A uzubillah! Wannan wane irin bala'i ne haka.


Kana matsayin mahaifinsu kake masu irin wannan fatan? Kasan bakin iyaye kuwa? Uwa daya Uba daya suke amma kake irin wannan tunanin akansu, yau idan yaranka suka shiga mugun hali waye zeshiga cikin damuwa idan ba mu ba.



Kada ka manta duk abinda yafito daga bakinka na alkhairi ko na sharri ze iya tasiri akan yaranka. Wallahi Alhaji ina jiye maka ranar da zakayi dana sanin abinda kakeyi, bafa kan ka farau ba, mutane da yawa sunje wajen wannan wa'azin amma ba haka suke yi agidansu ba.


Tashi Abba yayi yace akan wannan maganar zan iya batama kowa rai agidan nan, nine me iko da gida kuma dole insaka Doka duk wanda yakeson ya zauna agidan nan dole ya bi ta. Wallahi idan nakara samun ki adakin maza ko kuma kuna zaune kuna fira se ranki ya baci.


Ku ma haka duk ranar dana kara kamaku kuna zaune tare da Laika ranku ze baci, idan kuna son kuyi magana da ita to ku bari se mu duka muna zaune afalo sanan kushigo azauna gaba daya ayi fira, amma maganar ku ware kuyi labari banyarda dashi ba.


Kuma idan har zasu shigo ki tabbatar kin saka hijabi sannan ki zauna a falo. Daki ya wuce yana fadin aikin banza ni zaku jama fitina, hakanan ranar lahira kubarni da tsayuwar amsa tambayoyin da Allah zeyi mani akan AMANAR daya bani taku.



Daki Umma tashige itama tana wani irin kuka, sosai yau maganar Abba ta bata mata rai, tunda suke basu taba samun irin wannan sabani haka ba. Tashi Saleem yayi hawaye suna zuba daga idonshi saboda ya tsani yaga Ummanshi cikin damuwa.


Sosai yau Abba ya bata mashi rai, aranshi yayi alkawarin baze kara shiga gidan ba matukar yana gidan, ze rika kiranshi awaya suna gaisawa kamar yanda yafada daga farko, danshi bazeyi abinda yafada yanzu ba.


Idan ma yayi haka ne dan ya sassauta masu hukuncin daya dauka daga farko toshi bazeyi amfani dashi ba. Ummanshi kadai ze rika shiga yana gaidawa. Tunda ma haka abun yake aure zeyi yabar gidan gaba daya dama yarinyar da yake nema tace yafito shine be maida hankali ba.



Hamza kuwa abun dariya ya bashi, dama shi sam beda saurin fushi, matsawa yayi kusa da Laila yace dan Allah kidena kuka kina bata hawayenki abanza, duk abinda Abba ya fada kibarshi yabi ta bayan kunne, idan mukace zamubi abinda yakeso wallahi takura zamu shiga. Kawai mu nuna mashi bazamu kara abinda baya so ba.


Dago kai Laila tayi tace ni abinda yayi ma Umma ne yafi bata mani rai, tunda na girma Abba be taba duka na ba amma yau shine ya mare ni. Hamza yace kiyi hakuri, nasan shima Yaya ranshi ya baci ina nan dake baze kara dawowa gidan nan da wuri ba.


Wallahi bazamu bar fira ba, haka nan Abba yana so ya raba zumunci, mun riga mun saba muyi fira kawai se yanzu zekawo mana wata akida me wuyar dauka yace dole se mun bi.




Laila tace wallahi nima ban dauki hudu barshi ba, kaga ko wannan shigar da yace na rikayi dana fita nake cireta. Hannu Hamza yasa ya rufe mata baki yana fadin so kike ya jiyoki, kibarsu aide ba'a gidan zeta zama ba. Tashi kije ki lallashi Umma kada na shiga ya kara wani fadan.



***** *****



Maman Halima ce tashiga gidan wata kawarta domin duba ta saboda rashin lafiyar da tayi, da sallama ta shiga gidan seda tayi sallama so 2 kafin aka amsa, duk da akwai wata adakin farko kasancewar gidan haya ne.


Kuma su biyu ne suke zaune agidan, sede kawar Maman Halima dakinta yana daga ciki hakan  yasa bata jiyo sallamar ba. Shiga Maman Halima tayi ciki tana fadin Mamin Saudat ko duk ciwon ne yasa kika kasa amsa sallama ta? Fitowa Mami tayi tana fadin wallahi nama ji sauki, ina ciki ina gyara.


Sannu da zuwa kishigo. Bayan sun gama gaisawa Maman Halima tayi mata yajiki, Mami tace ai naji sauki dama zazzabi ne ya kamani tun da aka gama bikin Amina dana dawo gida na fara jinshi, kuma nasha magani kawai hada gajiya.



Maman Halima tace Allah ya kara sauki, ina su Saudat da Memah? Mami tace na aikesu gidan Kawunsu su fada mashi ina nemanshi kinsan me neman auren Memah yana so yaje ya gaishe shi.


Maman Halima tace Allah sarki ai gara ayi auren tunda tagama makaranta, itama Saudat ai wannan shekarar take gamawa ko? Mami tace wallahi kuwa, nima nafiso tayi auren kinsan halin dangin Babansu.


Tunda Babansu ya rasu nace abar mani su na rike suke tunanin bazan iya rikesu ba, saboda kudin makarantar su ne yasa na saka 'yan haya a wancan dakin tunda gidan yayi mana girma ace muzauna mu kadai, gashi yanzu muna amfana da kudin hayar.


Duk da haya tana neman zamar mani masifa, kina ganin fa yanzu sallama kikayi tana jinki amma taki amsa maki saboda tasan wajena kikazo. Ai nide wannan karon banji dadin masu haya ba, wallahi nafi jin dadin wadan da suka tashi su Maman Amira.


Amma wannan ga ta yarinya daga ita har mijin kar kiso kiga yanda suke rashin kunya agidan nan, wallahi dan na riga nayi amfani da kudinsu kuma shekarar da saura amma da maida masu sauran kudinsu zanyi su tashi.


Maman Halima tace to Mami me ya hadaku dasu? Mami tace mefa, kinsan idan akace maki yarinya kanta yana rawa babu abinda bazaki gani ba. Kuma fa ita ba dadin mijin takeji ba, Uban ta yakeci amma saboda rashin kunya har take iya fitowa tayi mani wani ji da kai.


So nawa ina shiga ina hana mijinta idan yana dukanta, matanshi biyu fa, amma sam baya kula da dayar kuma zaune take da mahaifiyarshi ga yara 6, amma haka zakiga idan kwanan wannan ne baya fita da wuri.


Wani lokacin ko kwanan waccan ne wallahi yana zuwa nan ya kwanta da amaryar, kuma idan ta tashi yimashi rashin mutunci haka zata zageshi ta Uwa ta Uba, sam bata ganin girmanshi, ta rainashi, gashi abun bakin cikin wallahi har maza take bi.


Kinsan dama aurenta 3 wannan ne na 4, sede Danta daya a wancan gidan na farko, yarinyar tana son kudi gashi mijin ta an koreshi daga aiki yanzu haka baya sana'ar komai, idan baya gidan haka zakiji tana waya da samarinta.


Wani lokacin har fita takeyi taje wajensu, wallahi abun duniya ya ishe ni, da ina da hali dana sallamesu, idan kinga yanda yake dukanta zakiyi mamaki, tun ina shiga har na dena, wani lokacin se sunyi fadansu zuwa anjima kuma ka jiyosu suna dariya.


Da tana shigowa har daki ta gaisheni daga baya kawai ta dauke mun kafa, daga ni har yarana bata masu magana, ke duk wanda zezo wajena ma bata mashi magana, mijin ne kawai idan ya ganni yake gaisheni.



Jinjina kai Maman Halima tayi tace lallai Mami kina kokari, ai dama can banji dadin 'yan hayar da kika sa ba, dan de kawai kina kula da karatun yaranki shiyasa banyi maki magana ba, amma wallahi kudinsu yana karewa kice su tashi, ke tun kafin ma su kare ki fadama mijin idan sun kare bazaki kara saka kowa ba.


Mami tace sede su tashi in saka wasu, amma bazan bar daki haka ba, kina ganin za'ayi bikin Memah duk da kafin su tashi ma za'ayi bikin amma gara na saka wasu, kinsan bana son zama haka kudi basa shigo mani.



Sallamar su Saudat ce ta katse su. Murmushi Mami tayi tace har kun dawo? Memah tace wallahi kuwa, bama mu sameshi ba, mun fada ma Inne. Dukawa sukayi suka gaishe da Maman Halima, amsawa tayi tana fadin Memah amarya ya gidan? Tace lafiya lau.


Tashi Saudat tayi tashiga daki tacire kayan jikinta tabar riga da wandon da suke ciki, dama after dress kawai ta dora asama, haka tafito kanta ko dan kwali babu ta nufi kitchen wanda yake kusa da nasu Nafisa wadda take haya agidan.



Tazo shiga mijin Nafisa yayi sallama, ta gefenta ya wuce yana fadin sannu da hutawa Mami, gaishe da Maman Halima yayi yashige ciki. Saudat kuwa ruwa ta debo tashige falo wajen Memah. Da kallo Maman Halima ta bita.


Mami tace kinga mijinta nan. Maman Halima tace gaskiya Mami akwai wani gyara da zanyi maki, taya kina zaune da namiji agida daya zaki rika barin su Saudat suna irin wannan shigar? Ba fa muharraminsu bane.



Kallarshi yaro dashi, yau ko tsoho ne ai be kamata ki rika barinsu suna zama haka ba. Kila ma hada wannan dalilin ne yasa ita Nafisar ta dena maku magana, kinsan halin zuciya, zata iya raya mata kinaso ya auri yaranki shiyasa kike barinsu suna irin wannan shigar.



Tubarakalla yaranki masu kyau dole zatayi kishi, nide dan Allah kidena barinsu suna zama haka. Mami tace abinda bazeyu ba kenan, gidan sune fa, taya wasu zasu zo su hanasu sakewa, hijab kike so surika sawa acikin gida? Duk duniya agidansu ne kawai zasu iya sakewa.



Idan nasa masu dokar zama da hijab ai ba zasuji dadi ba, awaje su saka hijab acikin gida ma su saka, haba ai abun da kwara, kin san fa yanda zaman gidan haya yake, kede kawai tunda Allah ya temake ki kina zaune agidan da ba na haya ba ki gode mashi.


Kuma ita kinga yanda take shiga acikin gidan nan? Ko kunya ta bataji haka take fitowa da gajeran wando da karamar riga, saboda me zan hana Yarana sakewa agidansu? Maman Halima tace Mami ita fa mijinta take yimawa kuma lada zata samu, su kuma wallahi zunubi zasu samu domin mijinta ba muharraminsu bane. Mami tace to hijabi zasuyi ta sawa kenan? To wallahi baze yuwu ba.



Maman Halima tace baki gane nufi na ba, bawai nace su zauna da hijab bane, ko da sunyi wannan shigar idan har zasu fita tsakar gida surika saka hijab ko doguwar riga musamman idan lokacin dawowarshi yayi ko kuma yana gida.



Kinsan fa ita zuciya bata da kashi. Mami tace ya isa haka, zaman gidan haya ne ya kama mu dole zamu rungumi duk abinda yazo mana, duk da gidan mu ne, amma muna da bukatar kudi dole musa masu haya.


Hakan bazesa kuma mu takura kanmu ba, idan kikaje WANI GIDAN ma ai abun yafi haka muni, mu fa tsakar gida kadai muka hada dasu, kowa da bagarenshi, A WANI GIDAN  zaki samu bandaki ma daya ne, kuma kusan mata 4 ne aciki su ya zasuyi? Kawai kigode ma Allah.



Nima wata rana zan sallami kowa nazauna ni kadai, amma sena aurar da yaran nan. Maman Halima tace haka ne, amma meze hana kisa amaida masu kofar su ta waje idan yaso ita Nafisar ta rika fitowa nan tsakar gidan saboda kitchen dinta yana waje.


Kinga mijin baze rika shigo maku nan ba, kema kin huta, amma fa ko abokanshi ne suka zo haka zasu shigo tanan ciki. Murmushi Mami tayi tace kede kawai Maman Halima mubar wannan maganar. Duk yanda rayuwa tazo maka kawai ka karbeta ahaka. Allah yasa mu dace.


Maman Halima tace amin. Ni zan tafi dama nazo duba ki ne. Mami tace nagode ina wajen amare? Tace duk suna lafiya, tashi Mami tayi ta rakata.



****** *****


Alhaji Dikko ne tare da Alhaji Sambo suna zaune a office din Alhaji Dikko, sunata fira, anan Alhaji Sambo yace wai ni Alhaji ban kara ganinka kaje wajen karatu ba? Tsaki Alhaji Dikko yayi yace wajen karatu ko wajen maula.



Alhaji Sambo yace subhanallahi, wane irin maula kuma? Haba Alhaji, kai da kanka kake fadin haka? Kasan kuwa waye Malan Adam? Nayi tunanin wannan wa'azin da yayi mana yashige ka, duk da baya nan ai akawai yaranshi.



Wallahi ranar da naji wa'azinshi kasa bacci nayi, domin abubuwan daya fada duk akwaisu agidana, nikam gaskiya naji dadin wannan wa'azin, kuma yanzu haka na dauki matakin gyara agidana.



Ya kamata kaima kayi gyara agidanka. Alhaji yace kawai yana neman temako ne ya bige da wa'azi, babu abinda yakeso illa yasa mu raba kan 'Ya'yanmu, domin wanna hayar daya kawo itace asalin hanyar da take raba zumunci.



Alhaji Sambo yace to se me? Daga lokacin da ka aurar da yaranka mata shikenan fa, yaranka zasu cigaba da zumuncinsu, domin alokacin kowa yayi hankali, amma yanzu kasan basu da hankalin da zamu barsu surika zama tare da junansu suna fira.




Zamanin yanzu da na lokacinmu ba daya bane, yanzu wannan zamanin banda shedanci babu komai acikinshi. Turawa sun riga sun shiga zuciyar 'Ya 'yanmu, bin hanyar da Malan ya kawo mana ita kadai ce zata sa mutsira ranar gobe kiyama.



Alhaji Dikko yace kai kaji zaka iya, ni kam bazan raba kan yarana ba, na tabbata yanzu agidan ka babu farin ciki, ko akwai? Kallonshi Alhaji Sambo yayi, Alhaji Dikko yace shikenan saboda muna tsoron zamani se mu hana yaranmu zama waje daya.



Idan basu zauna sukayi fira atsakaninsu ba waje akeso su fita? Ga newa ne baka yi ba. Sufa malaman nan babu abinda sukafi tsana kamar suga yaran masu kudi basa kula 'Ya'yansu, ganin yanda muke killace yaran mu agida basa fita waje suyi abota da yaran talakawa.


Da yanda suke shakuwa da junansu yasa suka kawo wannan maganar ta mu hana yaranmu zama waje daya. Kasan shi talaka, babu abinda yafi tsana irin yaga Yaran masu kudi sun taho suna farin ciki da junansu.


Duk inda yarana zasuje tare zaka gansu, koda siyayya zasuje tare zaka gansu, kai tunda kake ka taba ganin yaran talakwa mace da namiji sun fito tare wai zasuje siyayya? To irin wannan banbancin da yake tsakanin 'Ya'Yanmu da nasu shine babban dalilin da yasa suke so muma muraba kan yaranmu.




Murmushi Alhaji Sambo yayi yace Alhaji kai ne baka fahimceshi ba, amma Malan Adam babban malami ne, wannan maganar daya fada maganar Allah ce, babu son rai acikinta. Tashi Alhaji Dikko yayi yana kakka be rigarshi.


Hannu ya mika ma Alhaji Sambo yana fadin nizan je wani waje, idan kagama masinja ze kulle office din, agaishe da madam. Cike da mamaki Alhaji Sambo yake kallonshi, tashi yayi yana fadin ba seka koreni ba.


Naga alama baka son  wannan maganar, insha Allah bazan kara maka ita ba, nide na dauki maganar Malan, kuma tafara aiki agidana. Allah ya bamu sa'a. Alhaji Dikko yace amin, muje to na raka ka. Murmushi Alhaji Sambo yayi yace ka fasa fitar kenan? Dariya Alhaji Dikko yasa yana fadin tunda ka canza magana ai shikenan.



**** ****


 Yaseer ne ya fito daga motarshi ya dauko jakarshi yana ta sauri dan yau ya makara, tun kafin ya karasa office ya hangi Ilham tare da wasu nurses sun shiga wani daki hannunsu dauke da kayan aiki.


Office ya wuce bayan yagama ya fito domin yashiga wajen patients, seda ya gama dasu sannan yafito dan yau yayi alkawarin seya yima Jameel maganar Mabina. Da Ilham ya hadu ita ma ta fito.


Dariya tasa tana fadin ai yanzu nake shirin na fito na kiraka ganin yau bakazo dawuri ba. Murmushi yayi yace wallahi jiya ban kwanta da wuri ba na tsaya kallon wani shegen film me kyau.



Ilham tace nigerian film ne ko? Yaseer yace kema kinsan bani da film se nasu, domin sun iya film. Ilhma tace sun iya iskanci de, wallahi Yaseer kaji tsoron Allah. Dariya yayi yace kema dan baki taba kallo bane, amma kada kidamu gobe zan kawo maki wani kije ki kalla.


Ilham tace Allah ya kyauta, aini nafison indian film, ko ba komai zakaga love kala kala. Yaseer yace love din da ba'ayi practically ai shirme ne, wallahi idan kina kallon irin film dina zakifi son Jameel ma. Kallonshi tayi tace da gaske? Yace wallahi kuwa, ji zakiyi tamkar kina tare dashi.



Ilham tace shikenan, gobe ka kawo mun guda daya na fara kalla, idan yayi mani seka karo mani. Yaseer yace ki de bari na kawo maki biyu, dan zaki iya gama daya adare guda, kinga seki kunna dayan.


Ilham tace to shikenan naji, Yaseer yace kai nafiso ma kifara kalla ayau, idan muka tashi ki bini na dauko maki, Ilham tace kawai se aga naje gidanku. Yaseer yace to meye, amota fa zaki tsaya bance kishigo dakina ba. Ilham tace shikenan, yanzu katafi gashi can naga yashiga office kafin yafita.


Yaseer yace natafi kitayani da addu'a, dariya Ilham tayi tana fadin Allah yasa ya koroka nasha dariya. Yaseer yace wallahi da sena koya mashi hankali. Ilham tace Allah ya bada sa'a. Tafiya yayi yana fadin amin idan da gaske kike. Kai tsaye ya nufi office din Jameel.



Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO.

(Nabeelert Lady)

08028525263

[4/25, 3:32 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  25 ⚜ 30


Tura kofar office din Yaseer yayi tare da sallama, Jameel yana zaune yana duba wani file a gabanshi, dago kai yayi tare da amsa sallamar. Murmushi yayi yace Yaseer kai ne? Shigowa Yaseer yayi yace wallahi kuwa.



Zama yayi tare da mika mashi hannu suka gaisa. Jameel yace ni kwana biyu ma bamu hadu ba. Yaseer yace wallahi yanzu bansan me yake sani makara ba, sam bana zuwa da wuri yanzu.


Jameel yace kila kana zuwa firar dare ne. Yaseer yace haba de fira, ai har yanzu ban fara zuwa zance ba. Jameel yace Allah ban yarda ba, idonka kullum a kallon mata yake fa. Yaseer yace sede na kallesu na kauda kai, amma ban taba furta ma wata kallamar so ba.


Murmushi Jameel yayi yace ai yakamata ka samo mana wadda zamusha biki. Yaseer yace wai da kai nake jira. Dariya Jameel yayi yace haba, ai ni yanzu bani da wannan lokacin, ko zanyi aure se Baby ta zaba mani mata.



Murmushi Yaseer yayi yace ai Mubina akwai hankali, ya kamata ka bata dama ta zabo maka. Gyara zama Jameel yayi yana murmushin jin dadi an yabi Mubina. Yaseer yace kasan wani abu? Jameel yace seka fada.



Yaseer yace inaso kamun hanya wajen Mubina, na dade ina sonta na ce bara na fara maka magana na fiso kayi mata magana da kanka. Murmushi Jameel yayi yace ba komai zanyi mata magana.


Dariya Yaseer yayi yace kai amma nagode abokina, shiyasa nake sonka, nagode sosai. Jameel yace kadena azarbabi, nace zanyi mata magana, kasan halin Baby, matukar bata ga na samu budurwa ba bazata yarda ita tayi saurayi ba.



Bata fuska Yaseer yayi yace haba Jameel, taya zakace haka? Yanzu shikenan dan baka samu budurwa ba shikenan ita bazata kula kowa ba? Bayan kuma Ilham tana sonka amma kaki amince mata.


Daure fuska Jameel yayi yace dan Ilham tana sona shine aka ce maka dole na sota? Kuma ma Baby bata sonta, saboda haka kadena kawo mani maganarta idan muna magana. Zan fadi sakon ka kamar yanda kace.


Idan ta amince zanyi farin ciki, kuma idan bata amince ba ba zanyi bakin ciki ba, domin a kullum abinda Baby take so shi nake so. Bana fatan ranar da zanga bacin ranta. Tashi Yaseer yayi yana murmushi yace shikenan.


Nagode abokina, senaji daga gareka. Hannu ya bashi ya juya yafita. Tsaki Jameel yayi yana fadin daga kai har Ilham din ai duk jirgi daya ya kwaso ku. Ni sam bana son Baby ta amince maka ma.




Zaune Saleem yake agaban Ummansu, bayan ya kara bata hakuri akan abinda Abbansu yayi mata, kuma ya fada mata yana so ta fada ma Abbansu ya samu wadda ze aura. Murmushi Umma tayi tace lallai Saleem Abbanku ya bata maka rai da yawa.



Fada mani, meye ya saka yanke wannan hukuncin bayan nasan baka da ra'ayin yin aure yanzu? Kauda kai gefe yayi kwalla ta cika mashi ido. Hannunshi Umma ta kamo, hawayen da yake boyewa ne suka karasa zubowa.


Girgiza kai Umma tayi tace Saleem yau kai ne hawaye suke zuba a idonka? Me yayi zafi haka? Nasan baze wuce saboda abubuwan da Abbanku ya kawo agidan nan ba. Saleem idan har saboda wannan abun ne zakayi aure wallahi bazan barka kayi ba.



Nasan auren huce haushi ne kawai zakayi, kaga auren farko zakayi, banaso kaje kayi abinda zuciyarka bata natsu dashi ba, ita rayuwa tun daga farko mutum yake gina ta da farin ciki.


Matukar ka fara gina rayuwar auren ka da damuwa to haka zata tafi. Nasan ba dan ka shirya aure yanzu bane, kawai bacin rai ne yasaka fadar haka. Dago kai Saleem yayi yana kuka yace wallahi Umma mun dade tare da Jiddah.


Kuma muna son junan mu, abinda nasani de gaskiya ba yanzu nayi niyar aure ba, naso zuwa shekara me zuwa lokacin na gama ginin da na keso na fara yanzu. Amma dalilin wannan bakon al'amarin daya shigo gidan nan naji gaba daya zaman gidan ya fitar mani a rai.



Wallahi Umma gara nayi aure ace gaisheku nake zuwa da Abba yace baza murika shigowa gidan nan ba koda yaushe, se kace wasu barayi. Haba Umma, a ina kika taba ganin anyi haka?  Kawai de Abba be fahimci bayanin da Malan yayi masu bane.



Amma ni ban taba jin haka ba, domin raba zumunci ne. Nide dan Allah kije ki fadama Abba zanyi aure, na fasa gina filina dama ko farawa banyi ba. Inada kudin da zan sayi gida zuwa gaba sena gina filin.



Umma tace yanzu Saleem ba zaka bari ka gina gidan ka ba zakaje ka sayi wani? Idan har kana son kayi auren yanzu to ka kama hayar shekara daya mana, kafin kudin ka su kare ka gama ginin ka kaga se kawai ku koma can.



Saleem yace Allah ya sani Umma bana son zama agidan haya. Kibarni na sayi gidan tunda ina da kudin da zan siya. Shi MUHALLI  DARAJA gareshi, kuma baya taba yawa, idan nasaya yanzu, zuwa gaba idan na gina wani kinga na hada biyu kenan.


Kinga nima sena bada nawa haya, amma yanzu ni ban sayi wani ba, nazo na kama haya kuma sauran kudin suna ajiye a haka zan cinye su ban sayi wani abu me amfani ba. Kibarni dan Allah na sayi gidan.



Murmushi Umma tayi tace kai ma ka kawo magana me amfani, hakika MUHALLI YANA DA DARAJA, bakomai, Allah ya sanya alkhairi acikin gidan da zaka siya, kuma Allah yasa ayi bikin a sa'a.



Ba komai na fahimceka, kuma yin hakan shi ze hanaka fadawa wata damuwar, domin kai de kana da saurin shiga damuwa ba kamar Hamza ba, shi kafin abu ya bata mashi rai da wuya, dan haka zan fada ma Abban ka maganar yarinyar Allah yasa alkhairi. Saleem yace amin.



Kema Umma dan Allah kiyi hakuri da duk abinda Abba zeyi maki, tunda har wannan akidar tashiga ranshi gara ki bishi a haka, idan ba haka ba wallahi gidan nan ze zama tamkar gidan yaki, kullum cikin fada ze kasance, abinda ba'a taba yi agidan nan ba amma jiya anyi shi.



Idan kika kalli maganar Abba ta wani fannin yana da gaskiya, kawai rashin fahimtar abinda ake nufi shine yasa yake haka, amma dun ta ke kin fahimceshi dan Allah ki kiyaye duk wani abu da zesa yarika maki fada.



Wallahi bana jin dadi ace wai irin abinda yake faruwa A WANI GIDAN yau shine yake faruwa a gidan mu. Umma tace haka ne, kuma nima tun jiya na dauki alkawarin zan kiyaye duk wani abu daze rika kawo sabani tsakanina dashi.



Bakomai zanyi yanda yace, dama ai haka annabi yace mata su rika fita, nasan zan samu 'yan gulma amma da komai ya wuce shikenan, me nake bukata yanzu? Ina gidan aurena, ga yara Allah yabani, babu wanda yafi kamata na bayyana ma kwalliya kamar mijina.



Kawai de rashin sabo ne da fita da irin shigar da yace ne yasa zanji wani iri idan na saka, amma da na saba shikenan, kuma itama Laila zanyi kokarin ganar da ita, kaga ko aure tayi bazata sha wata wahala ba idan tasamu miji me irin ra'ayin saka wannan shigar.



Kuma tunda baya son ta rika zama da ku an gama daga yau, idan zakuyi fira nima zan zauna a falon ko da baya nan se kuyi firar gaba daya, ai bawani abu ake fada ba wanda za'ace baza'a fada agabanmu ba.


Nima banga amfanin zuwanta dakin ku ba, saboda akwai abokan Hamza da suke zuwa kasan kowa da irin tarbiyarshi. Insha Allah zan kiyaye, Allah yakara rufa mana asiri. Murmushi Saleem yayi yace amin, har naji dadi.



**** *****



Maryam ce zaune a dakinsu Aliyu ita da wani saurayin ta da yazo wajenta dan basa tsayuwa a waje musamman idan saurayi ya nemi izinin tsayuwa da yarinya agidan, to basa tsayuwa suyi fira awaje, sede suyi shimfida a zaure.


Ganin an maido kofar dakinsu Aliyu cikin gida yasa Mamansu tace su shiga dakin maza tunda yamma ce gashi mutane suna shigowa kada ayita wucesu. Hakan yasa Maryam ta kai saurayinta dakin.



Bayan sun gama firarsu suka fito domin ta rakashi, alokacin Babansu yadawo daga kasuwa yazo daukar wani abu, dasu ya hadu suna kokarin fitowa daga dakin suna dariya. Cak ya tsaya yana kallonsu.



Basu kula dashi ba ma haka suka shiga cikin gida Maryam ta yima Mama magana ta leko yayi mata sallama, seda suka juya zata rakashi suka hadu da Baban akofar shigowa. Saurin dukawa yayi yana gaishe shi.


Amsawa yayi fuskarshi babu fara'a, ciki yashiga sannan suka fita, bayan ta rakashi ta dawo ciki, tunda taga Babansu taye a tsakar gida gabanta ya fadi tasan anyi wani abu.  Har zata shiga daki ya kirata.



Dukawa tayi tana fadin gani. Kallon Mamansu yayi yace meyasa Maryam tashigar da saurayinta dakinsu Aliyu? Mama tace wai gani nayi yazo da yamma babu dadi su zauna a zaure mutane surika shigowa ta gabansu shiyasa nace su shiga dakinsu Aliyu tunda ya nemi izini.



Murmushi Baban yayi yace Saude kenan, har yanzu bakisan sharrin shedan ba. Ai gara su shiga falo su zauna yafi ace sun shiga har cikin daki su biyu, bawai dan ina zargin Maryam bane na fadi haka.


Shi kanshi yaron na yarda da tarbiyarshi shiyasa ma na amince mashi, kuma nasan Ubanshi nasan cikin gidansu, amma bazanyi amfani da wannan sanin da nayi masu in basu dama har haka ba.


Duk yanda ka kai da yarda da yaronka shedan ya fika dabara, abu daya zakayi ka kaucema sharrinsa shine kadau matakin hana shigowar barna agidanka, har ga Allah na yarda da irin tarbiyar da na bama yarana. Amma duk da haka semun kiyaye domin shedan ajinin dan adam yake gudu.



Ba izini yazo ya nema ba, ko rana aka sa masu ni banyarda su kara shiga daki su kadai  ba, mude bamu da wani karamin yaro dazamu hadasu dashi kinga kuwa bazan saka ido shedan yayi wasa da iyalina ba.


Matukar ya kara zuwa da yamma to yashigo falo su zauna, idan kuma da dare ne su zauna a zaure tunda akwai haske kuma idon mutane na kansu, amma daga yau Maryam na hana kushiga daki kina jina? Kai ta daga.


Sassauta murya yayi yace bawai ban yarada dake bane, sede ina tsoron sharrin Shedan ina fata zaki fahimci abinda nake nufi? Murmushi tayi dan taji dadin yanda ya saki ranshi yana mata magana cikin taushi, dago kai tayi tace na fahimce ka Baba.



Kuma insha Allah hakan baze kara fauwa ba. Nagode da tunasar warka agareni. Yace bakomai, tashi kije Allah yayi maki albarka, shima kuma zanga mahaifinshi idan ya shirya gara manya su shigo azo ayi magana, tashi kije.



Murmushi Umma tayi tace Malan ina jin dadin yanda kake ma yaran nan, duk yanda kayi masu fada cikin zafin rai seka dawo kayi masu cikin hankali kwance. A yanzu naga farin ciki a fuskar Maryam lokacin daka tausasa muryarka wajen yi mata fada.



Baba yace ai ba wai tsanani bane yake sa yara suji magnar ka ba, zafi baya kawo komai se bata al'amura, tsanani baya kawo gyara, nasan ina yima yaran nan fada da zafi, amma nasan yanda nake tafiyar dasu.



Kinsan yanzu ko yaro karami baya son yaga ana mashi fada, to yanzu yaran mu sun girma yawan yimasu fada ze iya sa masu jin haushin mu aransu, shiyasa ba'ason karika yima yaranka fada batare da kana yimasu nasiha ba. Allah de ya kara shirya mana su, ya bamu ikon sauke nauyin daya rataya awuyan mu. Mama tace amin.



**** *****


Zaune su Mufida suke a falo gaba dayansu suna cin abincin dare, 'yan biyu suna daga gefen Momy, Mufida da Karami se labari sukeyi. Dady ne yace wai ku kullum kamar wadan da suke aiki gidan redio sam bakinku baya iya yin shiru idan ana cin abinci.



Murmushi Momy tayi tace inde Karami da Mufida ne sun saba, labari baya kare masu. Mubina tace ai wallahi dama aikin jarida kukeyi. Jameel yace da duk yafi sauki de. Karami yace kai Yaya, aini babu abinda na tsana kamar aikin jarida.


Kullum mutum bakinshi baze huta ba. Dady yace waya fada maka surutu sukeyi kullum? Kawai de yanayin aikinsu ne haka yasa ake masu kallon masu surutu, amma taya mutum ze zauna yayita zuba kamar redio.



Amira tace Dady nima idan na girma aikin gidan redio znyi. Dariya suka sa Jameel yace kada kidamu insha Allah zakiyi, Karami yace waze barki kiyi wannan aikin, sede idan ba'anan gidan ba.



Amir yace Allah shi zamuyi ko Dady? Momy tace kwarai da gaske, abinda kowa yakeso shizeyi, shima ra'ayinshi ai yakaranta, ku ma naku ra'ayin zakuyi.


Dariya Mufida tasa tana tsunkulinshi, sauran ma dariya suka sa mashi, ruwan da yake hannunshi ya watsa ma Mufida, kara ta saki da gudu yatashi yana dariya yashige dakinshi, tashi tayi ta dau robar ruwan ta bishi tana fadin wallahi sena rama.



Dariya suka sa masu Dady yace ai gara ki rama kinga seki sashi gyaran daki. Momy tace dan karshenta se sun jika gadon. Mubina tace ko ta bata ai ita zata gyara kunsan halin Karami da shegen son jiki.



Jameel yace kai, Baby nifa na manta ma an bani sako na fada maki. Kallonshi tayi tace wane sako ne? Dariya yayi yace bara mugama ba agaban su Momy zan fada ba. Dady yace idan tayi wari ai zamuji ne.



Momy tace muna zaune kuwa, dariya Mubina tayi tace nasan ma bawani abu Yaya ze fada ba kawai tsokana ta yakeyi ai yasaba mani haka. Jameel yace shikenan tunda haka kikace, tashi yayi bayan yagama shan ruwa yace na tafi naje na kalli series film nasan yanzu sun fara.



Lemu Mubina ta shanye ta tashi tana fadin yi hakuri muje ka fada mani, Jameel yace bazan jira ba, kuma bazan fada ba tunda kince tsokanarki nakeyi, da gudu ta bishi ta rike hannunshi tace plsss mana sweet bro.



Murmushi yayi ya lakace mata hanci yace muje. Murmushi Dady yayi yace ina matukar farin ciki a duk lokacin danga yarana suna cikin farin ciki. Nagode Allah daya hada mani kansu, sam basa tunanin sufita fira wajen abokansu.



Kannansu sune abokansu, ina matukar farin ciki da irin zuri'ar da Allah yabani. Momy tace nima kullum cikin farin ciki nake, suna matukar son junansu, kuma kowa da abokin hadinshi, idan wani baya lafiya acikinsu kamar zasuyi kuka haka sukeyi, aranar sam zakaji gidan shiru.



Gaskiya nima ina godema Allah da wannan kyauta daya bamu. Tashi 'yan biyu sukayi suna fadin Momy mun gama, murmushi tayi tace kushiga ciki Asabe ta gyara maku wajen baccinku kada ku tsaya kallo fa kuce ta kashe fitilar da kayan kallon.



Dady yace seda safe ku kwanta da wuri kada ku makara makaranta, kuma kuyi wanka. Sukace to Dady, ciki suka shige da gudu suna kwalama Asabe kira. Dady yace nima Momy bacci. Dariya tasa tana fadin tashi muje to. Suna tafiya dayar me aikin Laure tazo ta kwashe kayan ta gyara wajen kamar ba'aci komai ba, sannan taje ta wanke kayan ta rufo kitchen din.



Tana fitowa ta hadu da Asabe itama ta fito zata wuce dakin barcinsu. Murmushi Asabe tayi  tace hajiyar kitchen har kin gama? Laure tace wallahi kuwa yanzu haka daki zan tafi na dauka ma kin kwanta.


Asabe tace nima yanzu na gama da kyar ma suka kwanta sannan na kashe kayan kallon wai se sunyi kallo, kuma nasan idan na barsu bacci zasuyi bazasu kashe kayan kallon ba, kinsan kuma ni zasu jama fada.


Mufida ce tafito daga dakin Karami kayanta duk ajike ya fito yana mata dariya yana sanye da gajeran wando yana fadin kizo ki goge dakin, harararshi tayi tawuce dakinta. Wajen su Asabe yaje yace dan Allah Asabe dauko mooper kizo ki goge mani daki waccan sarkin rigimar ta jika mani daki, Allah ma yaso banda gadon.


Wucesu yayi ya nufi dakin Mufida yana kiranta. Girgiza kai Laure tayi tace kai duniya idan kana da kudi babu abinda ba zakayi ba. Asabe tace wasu masu kudin de, amma ba ko wane yake barin 'Ya'Yanshi suna irin wannan abun ba.



Gani suke wannan rayuwace ta 'yanci, ace ka bar baligan yara surika cudanya atsakaninsu, ku kuma iyaye babu abinda yayi maku zafi kun shige daki kuna tunanin burgewa ce. Yanzu ina amfanin wannan wasan da sukeyi, kalli yanda ta fito kayanta duk ajike, shima ko riga babu ajinkishi.


Kuma ya bita daki nasan yanzu tana can zata sake kaya haka kuma zeshiga. Laure tace rannan fa wajen karfe 1 na fito shan ruwa naga Mubina ta fito daga dakin likita ba kiga karamar rigar da take jikinta ba, kanta ko dankwali babu wai se alokacin take fada mani kallo sukayi.



Asabe tace inde wannan ne ai kadan kika gani, mude namu ido ne, neman kudi ya kawo mu gidan nan, idan munaso mu zauna lafiya to mu sama bakin sakata, domin mutanan gidan nan baza suji wa'azi ba. Bara kiga naje nayi aikin daya sani tun kafin sufito.




Mubina tana jingine jikin Jameel se shagwaba take mashi wai ya fada mata abinda yace ze fada mata, shiko yayi shiru yana kallonshi, saman gadon ta kara hayewa ta kwace remote din ta kashe TV, saurin kamota yayi yana fadin bani.


Dariya tasa takara matsawa tana fadin Allah seka fada mani zan baka, binta yayi suka fara kokowa yana fadin ta bashi, itako ta rike remote din da kyau se dariya takeyi. Duk yanda yaso ya kwace ya kasa, gaba daya sun gama hargitse gadon.



Hatta da rigarta ta tattare ta dawo ciki saboda kokowa, duk sun gaji haka suka zube suna maida numfashi, Jameel yace wallahi ke muguwa ce, duk kin gajiyar dani, shiru tayi ba tace komai ba se nishi takeyi ta kulle idonta.



Tashi yayi yana kallonta, tsayawa yayi yana kallon yanda take nishi da sauri idonta a kulle, ya dade yana kallonta, ya kasa dauke idonshi, bude ido tayi jin yayi shiru, hura mashi iska tayi tana murmushi.


Komawa yayi ya kwanta dan tsigar jikinshi yaji ta tashi, Mubina tace Yaya dan Allah ka fada mani, runtse ido yayi yace kibari seda safe zan fada maki yanzu nagaji, zata kara magana yasa hannu ya jawota ta kwanta gefenshi yana fadin kibari se gobe.



Mubina tace Yaya me yafaru? Yace bakomai, kawai kin gajiyar da nine, tace to tashi na kunna mana kallon, yace bacci zanyi ki kalla ke daya, turo baki Mubina tayi ta buga mashi pillow tana fadin Allah seka tashi.



Saurin tashi yayi yace Baby dan Allah kitafi dakin ki ki kalla, tsayawa tayi tana kallonshi, kauda kai yayi yace zan fada maki amma se gobe, yanzu da mukayi kokowa naji kaina yana dan ciwo.


Saurin matsowa tayi cike da damuwa tace Yaya sannu, hannunta ta kai ta shafa goshinshi tana fadin bara na kawo maka magani, murmushi yayi yace wasa nake maki. Dariya tayi tace ka ganka ko, to zo muyi kallon, yace shikenan kunna amma bazamu dade ba? Tace e naji.



Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[4/26, 3:57 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  30 ⚜ 35



Tunda asuba Jameel ya tashi dan ya kusa makara, sam beji karar alarm din wayarshi ba, nauyi yaji a jikinshi  hakan yasa ya  dauko wayarshi ya kunna fitilar dan tun jiya suka kashe ta dakin.


Cak ya tsaya yana kallon Mubina wadda duk rabin jikinta akanshi yake, wayarshi ya kara dubawa yaga ko karfe nawa dan yasan Mubina bata taba kwana a dakinshi ba. Karfe 5:30 dan anyi sallah tun dazu.


Kallonta kawai yake yana mamakin yanda akayi har sukayi bacci bata tafi dakinta ba, kuma ga TV nan a kunne, murmushi yayi yana girgiza kai ganin yanda Mubina take bacci kamar wata karamar yarinya.



Hannu yasa ya fara bubbugata, juyi tayi takara rungumoshi, hannu yasa ya tsunkuleta da sauri ta tashi, hannu tasa tana murza idonta tana kallonshi, turo baki tayi tace kai Sweet Bro, shine zaka zalince ni.


Dariya yayi yace ki tashi muyi sallah, zaro ido tayi tace wace sallah kuma? Yace asuba mana, kallonshi tayi tace wai anan na kwana? Yace nima se yanzu nagani. Dariya tasa tace lallai jiya mun kwanta da wuri.



Tureta yayi yace ai seki tashi muyi sallah, tace to bara naje dakina idan na gama zanzo ka fada mani sakona. Dariya yayi yace wato baki manta ba ko? Sauka tayi daga gadon tana fadin emana, kai de kaje kayi sallah.



Tana fitowa suka hadu dasu Asabe a kitchen, risnawa sukayi suna gaisheta, amsawa tayi tana mika ta wuce dakinta. Laure ta rike haba tana kallon Asabe, girgiza kai Asabe tayi tace da alama Mubina ba'a dakinta ta kwana ba, Laure tace Allah de ya kyauta, ina tsoron ranar da za'ayi abun kunya agidan nan.



Asabe tace kin jiki da wata magana, Uwarsu daya Ubansu daya fa kike wannan maganar, Laure tace idan ma Uwarshi ce ita ai Shedan ba Ubansu bane daze sa masu ido. Kede Allah ya kyauta kawai. Asabe tace amin.




Bayan ta gama sallah Mubina ta koma dakin Jameel tana jiranshi yafito wanka dan  wanka ya farayi kafin sallah. Yana fitowa ya kabbara sallah,seda ya gama sannan ya shafa mai ya saka kaya.


Mubina tace Yaya kai fa nake jira, turare ya gama fesawa yace to kawo mani Lipton nasha. Turo baki tayi tace wai yau da wuri zaka fita ne? Murmushi yayi yace wallahi yau meeting zamuyi karfe 7:00 kinga dole na fita dawuri.



Kamar zatayi kuka tace kuma se yaushe zaka dawo? Zama kusa da ita yayi yace kije ki kawo mani abinda nace sannan. Tashi tayi tana bubbuga kafa ta fita, dariya yayi yana girgiza kai yace Baby sarkin rigima.



Bayan ta kawo mashi ta zauna tace wai Yaya bazaka fada mani ba? Murmushi yayi yace kome na fada maki zaki amince? Kai ta daga, yace ko da miji na zaba maki? Saurin kallonshi tayi tace miji? Yace sosai ma.



 Kamar zatayi kuka tace Yaya waye? Dariya yayi ya fada mata sakon Yaseer, saurin tashi tayi tana fadin wane Yaseer bade abokin wannan kazamar ba? Dariya Jameel yasa ya kamo ta yana fadin abokin nawa shine baki gane ba? Tace na ganeshi mana, ai dama naga yana yawan kallona idan nazo asibitin ku.


Kuma wallahi bana sonshi domin tare suke da wannan yarinyar. Jinjina kai Jameel yayi yace nima beyi mani ba domin tare suke da Ilham, kullum suna tare abokinta ne sosai ni kuma bana son ki auri namijin dayake da abokiya.



Hakan yasa naki amincewa da Ilham saboda bata da aboki se namiji. Murmushi Mubina tayi tace yauwa Yayana tunda beyi maka ba nima bana sonshi. Jameel yace nima Baby tunda ya fada mani naji ban amince ba.



Zan samo maki miji da kaina, tashi muje ki rakani nasan bacci zaki koma. Jakarshi Mubina ta dauka suka fita, Jameel yace idan su Dady sun fito kice na tafi, wadan can sarakan shiriritar kuma nasan basu tashi ba. Seda yatafi sannan ta koma daki ta kwanta.



**** ****



Laila ce ta fito cikin shirin fita makaranta, sallama tayima Umma ta juya ta nufi dakin Abbansu, bayan tayi mashi sallama ta fito, har ta kai bakin kofa Umma ta kirata. Cak ta tsaya gabanta yana faduwa.



Kusa da ita Umma tazo tace ya naga dankwali biyu akanki? Laila tace na'am? Umma tace baki lura bane gashi nan yafito daga cikin hijab dinki? Hannu Laila tasa tana taba saman kanta.


Santsin gyale taji, murmushi tayi tace oh! Dankwalin ne yayi mani nauyi idan nasa hijab shiyasa na daura gyalen. Umma tace ai na dauka hada dankwalin kika daura? Murmushi Laila tayi tace a'a. Umma tace shikenan Allah ya kiyaye, ki kula da kanki.



Ajiyar zuciya Laila ta saki tace nagode, fita tayi da sauri tana hamdala, seda ta shiga dakinsu Hamza dan tasan Saleem yatafi aiki, labulen tagar ta bude haske ya cika dakin, saurin tashi yayi dariya tasa tana fadin tunda na tashi kaima dole katashi.



Fuskarshi ya rufe yace ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, dariya suka sa gaba daya, Hamza yace wallahi kamar wata Ninja, Laila tace ai iyaka cikin gida ne kawai, ina fita shigata tana ciki.



Allah yaso ni Umma ta kusa ganewa, Hamza yace ai seki kara kula idan ba haka ba kin kusa fara shiga makaranta a haka. Laila tace wallahi bazan taba shiga makaranta a haka ba. Ni natafi kafin Boss ya fito. Dariya Hamza yayi yace adawo lafiya kidawo da wuri yau akwai kallo, tace to.




Bayan Abba ya gama cin abinci Umma ta fada mashi abinda Saleem yace. Murmushi Abba yayi yace amma naji dadin wannan magana, dama ya kamata ace kamar Saleem yabar cikin gida haka nan, baligin namiji ace yana zaune agaban mu ga babbar budurwa acikin gida.



Dama kullum hankali na atashe yake dan nafi tsoron haduwar Laila da Saleem akan Hamza danshi kaninta ne, kuma har yanzu yaro ne yanzu ma zeshiga jami'a. Gaskiya naji dadi sosai, yanzu hankali na ze kwanta.



Idan yadawo ki fada mashi ina son ganinshi, zanji yarinyar diyar waye dan muje ayi magana, kuma tunda yace ze sayi gida ba matsala idan ma beda kudin siyen zan bashi daya daga cikin gidaje na su zauna, dan bana so bikin ya dauki lokaci.



Gara ya tafi gidanshi kowa ya huta. Tunda ya fara magana Umma ta saki baki tana kallonshi, sam batayi tunanin ze amince da wuri haka ba, wato saboda yana tunanin zaman Saleem da Laila waje daya wani abu zefaru.



Girgiza kai tayi, ta san idan ba Laila tayi aure ta bar gidan nan ba Abba baze taba saukowa daga wannan muguwar akidar tashi ba. Kallonta Abba yayi yace ko bakiji abinda nace ba? Murmushi Umma tayi tace naji.



Ai nima nayi matukar farin ciki da auren Saleem, dama na dade ina mashi magana yafito da mata zamanshi haka ba aure komai yana iya faruwa. Murmushi Abba yayi yace yauwa Hajiya, haka nake son ji daga bakin ki.



Yanzu nasan kina goyon baya na, kinga idan Saleem yabar gidan nan zamu samu kwanciyar hankali, bana jin Hamza. Umma tace shikenan zan fada mashi idan yadawo. Abba yace shikenan ni zan fita sena dawo. Umma tace Allah ya tsare.




***** *****


Sauri Saudat takeyi zata shiga wanka dan Mimah ta fito tun dazu tana jiranta zasu fita. Kasancewar Bandakinsu a tsakar gida yake dole se sun bi ta gaban falon su Nafisa sannan su shiga.



Haka ta fito daure da towel iyakar cinya, dede lokacin mijin Nafisa ya shigo dan ba'a gidan ya kwana ba adayan gidanshi ya kwana, Saudat bata kula dashi ba haka tashiga kitchen tasha ruwa yana tsaye yana binta da kallo.



Har ta fito yana tsaye, ganin tayo hanyar bandaki yasa yayi saurin yin sallama ya karasa shigowa, gaishe shi tayi tashige bandaki, baki ya lasa aranshi yana fadin yarinyar nan akwai diri, shigewa ciki yayi yana fadin Allah ya kai damo ga harawa.



Duk abinda yakeyi Nafisa da Kawarta Ummy makociyarsu suna kallo, yana shiga Ummy ta mike tana fadin bara naje sena dawo. Tashi Nafisa tayi tare da daure fuska tace muje na raka ki, gaishe dashi Ummy tayi suka fita. A zauren gidan suka tsaya, Ummy tace kinga abinda nake fada maki ko.



Wallahi se kinyi da gaske idan ba haka ba matar nan so take mijinki ya auri daya daga cikin yaranta, in banda iskanci tasan mijinki ze iya shigowa amma ta bar diyarta tafito haka.



Shiyasa nace kema kidage da saka kana nan kaya idan ba haka ba zasu kwace maki miji. Nafisa tace ai shiyasa na nuna masu nasu iskancin karami ne, yanzu bakiga irin shigar da nakeyi ba. Ko Uwarsu bana jin kunyarta, gidan miji na ne dole na sake, koda agidanta muke haya aide kudi muke biya.



Idan kuma taji haushi ta maido mana kudin mu mubar gidan, danni wallahi duk yafitar mani arai. Ummy tace kema de kinsan bata da kudin da zata maido maku, kawai ki iya kanki kada akwace maki miji kada kije kina zaune kwado yayi maki kafa.



Nafisa tace kibar ni dasu, shima zan sameshi ne, ya wani tsaya yana kallon waccan banzar. Dariya Ummy tasa tace nide na wuce, anjima kizo kifada mani yanda kukayi dashi. 



Tsaki Mimah taja dan duk abinda suke fada tana jinsu, dan tazo zata je siyen wani abu taji suna magana azaure.



Fasa fita tayi ta komo ciki. Mami tace Mimah har kin dawo? Tsaki ta kara ja tace wallahi Mami kiyima Saudat magana, dama dazu nayi mata magana akan tarika yafa zani ko tasa hijab idan zata shiga wanka amma bata ji ba.



Yanzu bakiji abinda Nafisa da Ummy suke fada ba, wai mijinta yashigo yaga Saudat zata shiga wanka ya tsaya yana kallonta, wai kece kike sawa muna fita haka dan yace yana son mu. Me zamuyi da wancan banzan mijin nata.



Saudat ce tashigo dakin ta fito daga wanka. Mami zatayi magana kenan suka jiyo ana zage zage. Muryar Nafisa sukaji tana fadin E na fada, idan ba iskanci ba Uban me ka tsaya kana kallo ajikin waccan banzar.



Wallahi banajin tsoron kowa bazan zauna wata tsohuwa tasa yaranta surika shigar banza saboda mijina ba. Sautin mari suka jiyo mijin yana fadin ke wace irin marar kunya ce? Ni kike zagi saboda bakida mutunci.



Ai gara ni namiji ne, ke fa? Kina matar aure kike bin maza, banza fasika. Zaginshi ta karayi hakan yasa ya dauko belt ya fara dukanta. Mimah tace Mami dan Allah kije ki hanashi. Mami tace wallahi babu inda zanje.



Ada da muna zaman mutunci nayi, amma yanzu kinaji da kunnanki tana zagina saboda bakida kishi zaki ce naje na hanashi, sunfi kusa, nan da anjima daya lallabata zaki jiyosu suna dariya, ni bana shiga tsakaninsu.




Kuma bazan hanaku sakewa agidanku ba. Saudat tace Mami kema kika tsaya biye mata, wallahi bazanyi zaman takura agidanmu ba, yanda take takama da gidan mijinta nima gidan mu ne. Mezanyi da wannan kazamin mijin nata, wallahi damma yana gaishe dake shiyasa nima nake gaidashi, amma da babu ruwana dashi. Mimah tace Allah ya kyauta, Mami tace amin.



**** ******



Tsaye Yaseer yake abakin office din Jameel yana jiranshi ya karaso, dan tunda suka fito meeting be dawo office ba ya wuce cikin asibiti, ya dade yana jiranshi sannan ya hangoshi ya taho.



Tun daga nesa Jameel yake murmushin mugunta, yasan Yaseer yana jiran amsar shi ne. Yana karasowa yabashi hannu suka gaisa, bude office din yayi suka shiga, gyaran tebur dinshi ya fara Yaseer yace haba abokina kafa san dalilin zuwa na.



Dariya Jameel yayi yace amsar ce bata bukatar afadeta shiyasa nayi shiru. Yaseer yace nide ka fada mani, koma menene zan dauka. Jameel yace tace kayi hakuru. Shiru Yaseer yayi na kusan minti 5.



Kallonshi kawai Jameel yakeyi, murmushi yaga yayi yace shikenan babu damuwa, dama nace maka koma menene zan iya dauka, Allah yazaba mana abinda yafi zama alkhairi. Jameel yace amin.



Amma ka burgeni abokina, ban dauka zanji haka daga gareka ba. Yaseer yace haba se kace wani karamin yaro, kowa yasan dama soyayya ta gaji haka, dan haka karka damu na dauki Mubina tamkar kanwata tunda kanwar abokina ce.



Bara naje office, Jameel yace nagode. Hannu ya bashi yafita. Yana fita ya daure fuska, kai tsaye office ya nufa. A zaune ya iske ilham. Tana ganinshi tasa dariya dan taga yanda fuskarshi ta canza.



Zama yayi yana kallonta fuskarshi a daure. Ilham tace dan Allah ka saki ranka, sam ba kayin kyau idan kana fushi. Murmushi yayi yana kallonta, Ilham tace fada mani, baka dace ba ko? Yaseer yace ki barni dasu.



Wai bata amince ba tace nayi hakuri. Ilham tace me kace mashi? Yaseer yace mefa zance mashi, ai nima inada wayau, bazan nuna mashi naji haushi ba, amma tabbas sena dauki fansa akan wannan abun.



Ilham tace wallahi ina goyon bayanka. Daga ni har kai bamu samu abinda muke so ba. Kallonta Yaseer yayi bece komai ba. Ilham ta hure mashi ido tana fadin wannan kallon fa? Murmushi Yaseer yayi yace ko tuwo na mai na zamuyi? Ilham tace ban gane ba.



Tasowa yayi ya matso kusa da ita yace tunda bamu samu abinda muke so ba meze hana kawai mu dedeta kanmu? Daure fuska Ilham tayi tace bana son irin wannan maganar, dan ka samu ina sakar maka fuska shine zaka samu karfin guiwar fada mani wanan maganar.



Yaseer yace to se me, banyi maki bane? Tsaki taja ta tashi tana fadin wallahi zamu bata, hannunta ya kamo yana fadin wasa nake maki, Allah ya huci zuciyarki. Zoki fada mani ya kikaga wannan film din dana baki? Murmushi tayi ta zauna.


Hannunta ta kwace tana fadin wallahi baka jin magana, ashe dama haka film din yake? Wallahi jiya da kyar nayi bacci, lokacin dana fara kallo har na kashe ganin abubuwan da akeyi, amma sena kara kunnawa.



Da kyar fa na tashi sallah dan nasan da wuri zamu fito, amma yanzu bakaji baccin da nakeji ba. Dariya Yaseer yasa yakara matsowa kusa da ita yana fadin zan baki wasu yau, idan aka tashi muje ki karba, amma yau zaki shiga dakina ki zaba da kanki.



Ilham tace 'yan gidanku fa? Yaseer yace har seki shiga part dina ki fito babu wanda yasan kinshiga, nafiso kije ki zaba da kanki. Amma dan Allah ya kikaji ajikinki jiya? Dariya tayi ta kaimashi duka tana fadin ban sani ba. Tashi tayi tana fadin bara naje wajen Dady, Yaseer yace sekin dawo.




Tana fita Yaseer ya daga kanshi sama yana murmushi.



**** ****


Zarah ce da Zainab suka fito dauke da tallar zasu kai wajen masu gini, dama kullum da rana suna kai abinci da dare kuma kowa da abinda yake saidawa. Zarah tana soya awara, Zainab kuma doya da kwai.



Sunci kwalliya kamar masu shirin zuwa wajen biki. Zainab ce tace waini Zarah ina Ado? Zarah tace kede kibarshi, daga fa nayi mashi maganar ankon bikin Aisha shikenan ban kara ganinshi ba.



Jiya ma da naje inda suke buga  bulo dana tambayi abokinshi cewa yayi bezo ba. Zainab tace lallai, kinga ni jiya har Bashar ya bani nawa, bana fada maki kidena tsayawa wajen saurayi daya.



Bakiga jiya ban dawo da wuri ba, ina gama saida doya ta na bishi shagonshi yabani. Zarah tace lallai, nima Ado yace wai nazo dakinshi na karba nice naki zuwa, Zainab tace ai ko sede ki fidda cikin kudin ki kiyi ankon.



Kinsan de duk wadda batayi anko ba ba ta sakewa a wajen biki. Zarah tace nifa tsoro nakeji. Zainab tace tsoron me? Ni me ya sameni? Kawai baki zeyi kifito. Zarah tace kinsan fa Ado akwai son taba mace.



Zainab tace to se me? Tunda bazakije ba ke kika sani, kina gani Bashar hada sabuwar waya ze kawo mani kafin bikin. Zarah tace da gaske? Zainab tace wallahi, ke de ki tsaya anan. Zarah tace aiko zanje na sameshi. Zainab tace yauwa ko ke fa.




Seda yamma sosai suka tashi daga asibiti, Jameel yafito ze tafi gida ya hango su Yaseer da Ilham sun nufi wajen motarsu suna dariya, Ilham hada  kaima Yaseer duka, tsaki Jameel yayi aranshi yace aikin banza, ahaka ka keson Baby, Allah ya kyauta na baka.




Yaseer yace amma fa se na saka maki kin fara gani sannan kizaba. Ilham tace kaide kanaso ka sa na kara dadewa, kabani idan naje gida zan zaba da kaina. Yaseer yace kede mutafi kawai, kuma kiyi tuki da sauri kada na wuce ki. Dariya Ilham tayi tace muje zamuga wanda ze riga wani zuwa. Yaseer yace muje. Mota suka shiga suka nufi gidansu Yaseer.



Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[4/27, 1:56 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  35 ⚜ 40


Tsaye Ilham take a dakin Yaseer tana jiranshi ya bata film din, kallonta Yaseer yayi wanda yake duke gaban TV yana kokarin kunna film din daya saka. Murmushi yayi yace ki zauna mana kamar wadda ake kora.



Gefen gadonshi ta zauna tana fadin nide kayi sauri, nace kabarshi kawai idan naje gida zan kalla. Yaseer yace ke de ki bari kizaba. Bayan ya kunna ya dauko mata ruwa ya zuba a kofi tare da zama kusa da ita ya mika mata.




Harararshi tayi tana fadin ce maka akayi kishi nake ji? Dariya yayi yace ai ko ba kijin kishi sekinsha ruwan dakina domin ke bakuwata ce. Murmushi tayi takai hannu zata amsa, janye ruwan yayi yace bara na baki.



Daure fuska tayi tace wallahi Yaseer ka rai na ni. Yaseer yace kefa kawata ce, haka nima abokin  ki ne, na tabbata bakida wanda kike fadama sirrinki da damuwarki sama da ni. Kinga kuwa mun zama daya.


Domin nima ina jinki kamar wata 'yar uwata, bana shakkar fada maki damuwata domin Ilham na yarda da tarbiyarki da hankalin ki, bana tsoron fada maki komai nawa. Murmushi tayi ta kamo hannunshi tana fadin nagode da wannan yarda dakayi mani.



Kauda kai Yaseer yayi yana murmushi, kofin ya mika mata abaki ta amsa seda ta shanye sannan ya dauke kofin ya aje. Hannunta ya murza yace kalli can, juyawa tayi ta kalli TV, saurin kifa kanta saman cinyarshi tayi tana dariya.



Hannushi yadora sama bayan ta yana fadin tashi ki zaba mana, kara tusa kanta tayi cikin kafarshi, kokarin dagata ya farayi tana kaucewa se dariya sukeyi, nan suka fara kokawa yana fadin dole seta kalla.


Tun suna kokawa azaune har suka fada saman gado, sun dade suna kokawa, karar wayar Ilham ce ta tsaidasu, tashi tayi tana gyara rigarta ta dauki wayar, sunan Ummanta tagani, saurin dauka tayi tana fadin gani nan a hanya.



Ture Yaseer tayi tana fadin kaga har Umma takira ni, Yaseer yakara jawota yace wallahi har bana son kitafi, banida abokin fira shiyasa yau kadai senaji wani irin dadi. Kanshi ta shafa tana fadin ai muna haduwa asibiti.



Gashi yanzu duk ka gajiyar dani. Dauko mani film din natafi bazan iya kalla tare da kai ba, ko ni daya nake kallo kunya nakeji. Yaseer yace ki samana rana muzo mu kalla tare ina me tabbatar maki sekinfi jin dadin kallo.


Ilham tace bawani, yace da gaske fa. Tashi tayi tana fadin shikenan, ranar da bamuda aiki semuzo mu kalla. Saurin tashi yayi yana fadin nagode sosai, my Friend for ever. Dariya tayi tace muje. Films ya bata suka fita domin yarakata. Seda ta tafi sannan ya shafi kanshi yana murmushi ya juya.




Zaune Saleem yake a falo shida Abbansu da sauran mutanan gidan, Laila ta dauka ma fada Abba zeyi, sede yanda taga yana fara'a tasan ba fada zeyi ba. Kallon Saleem Abba yayi yace naji sakon ka a wajen Ummanku.



Naji dadi sosai, Allah ya sanya alkhairi. Dukar da kai Saleem yayi yana murmushi, Hamza yace Yaya me yafaru? Harararshi Saleem yayi. Abba yace suruka ya samo mana, dariya Hamza da Laila suka sa, Hamza yace Abba ashe mun kusa shan biki.


Abba yace sosai ma, yanzu inaso naji yarinyar 'yar wane gida ce? Dukar da kai Saleem yayi yace Abba diyar Alhaji Abu Galadima ce na unguwar Sharada ma aikacin gidan redio freedom. Murmushi Abba yayi yace kace abokina ne ma.



Sanadiyar Alhaji Dikko na sanshi, gaskiya yana da mutunci, bakomai zan samu Alhaji Dikko muyi maganar, wannan ba wani abun damuwa bane, kaje ka fara shirin biki domin bana so bikin ya dade.



Idan ma baka da kudin da zasu isheka hidimar bikin zan bama Ummanku wanda zata hado lefe kai kaji da siyan gidan, dama yakamata ace kabar gidan nan haka hankali na zefi kwanciya idan katafi saboda Laila.



Umma tace yanzu de abar maganar tunda de yace zeyi aure, Saleem yace Abba ni koda banyi aure ba ma ina ruwana da Laila, kanwata ce fa. Abba yace koma Uwa ka ce,  dariya Hamza yasa, Saleem ya magareshi. Abba yace kutashi kuje dama abinda zen tambayeka kenan.



Tashi sukayi Hamza yana dariya, Abba yace kai kuma sarkin dariya, yaushe zaku fara lectures din? Hamza yace zuwa sati me zuwa. Abba yace to Allah ya temaka. Tashi Laila tayi ta nufi daki dama tagaji da hijabin da tasaka.



Suna fita Hamza yace wato Abba saboda kabar gidan yaji dadin aurenka, Saleem yace nima ai zaman gidan ya ishe ni, shiyasa ma na kawo maganar auren, amma yanzu gidan nan beda dadin zama.



Hamza yace kai ne kake daukar fadan Abba da wani abu. Saleem yace kai dama ai fada baya damunka, idan ka kara girma ya fara kafa maka doka akan Laila a nan zaka gane rashin dadin fadan Abba. Dariya Hamza yasa yace wallahi ni fadanshi baya damuna.



 Saleem yace ka huta ai, nide na bar gidan nan sede nazo gaishe da Umma, Hamza yace ai nima nasamu wajen zuwa, murmushi Saleem yayi yace nima zan saka Dokar zuwa mani gida, saboda kaima baligi ne. Dariya suka sa gaba daya.




***** *****


Bayan kwana biyu su Abba sukaje akayi maganar auren Saleem da Jiddah, babu bata lokaci aka tsaida rana nan da wata daya, dama su ashirye suke kawai dan Jiddah tace Saleem yace ta jirashi ne.



Yanzu tsakanin Ilham da Yaseer sun zama tamkar masoya, sosai suka kara shakuwa, duk wata hanya da Yaseer zesa Ilham takara sabawa dashi seda yabi, yanzu koda yaushe suna tare matukar ba aiki suke ba. Basa jin kunyar taba juna.



Duk abinda sukeyi Jameel yana kallonsu shide ya kara ma Allah godiya da Mubina bata amince dashi ba. Yanzu har a office Yaseer yake kunna mata film din batsa suke kallo. Ranar da sukaje dakinshi suka yi kallo kuwa haka Yaseer yafara wasa da Ilham, kuma ta kasa hanashi dan itama tana bukatar hakan.




Tun daga lokacin suka manne, babu abinda Yaseer baya yi mata, dan idan basu hadu ba har kewarshi takeyi, kusan kullum setaje dakinshi a office ma suna wasan su matukar babu mutane, har office din Jameel aka kai mashi gulmar abinda sukeyi, shiko yace ina ruwanshi sun fi kusa.


Duk da har yanzu son Jameel be fita daga zuciyar Ilham ba amma yanda Yaseer yake debe mata kewa yasa ta rage zuwa wajenshi, amma wani lokacin tana kiranshi awaya, sede sam baya daukar wayar ta dan yanzu yakara tsanarta.




***** *****


A gidan su Maryam ma an kawo kayan sa aurenta, itama nan da wata 2 za'ayi bikinta, sosai Mama take cikin farin ciki dan yanzu saura Halima kadai zata rage mata, ga Aliyu shima an kai kudin neman aurenshi.



Haka ta raba ma mutanan unguwa kayan sa ranar Maryam. Mariya ce da Dije sukazo gidan Mama domin suyi mata murnar sa auren Maryam. Bayan sun gama gaisuwa Mariya tace Maman Halima munga kayan sa rana, Allah ya sanya alkhairi.



Mama tace amin, Dije tace ikon Allah itama Maryma ta samu miji da wuri haka, gashi ko shekara ba'ayi da auren Amina ba itama zatayi aure. Mama tace ai haka abun yake shi aure da yazo baya jira.




Mariya tace haka ne, amma shi mijin aikin me yakeyi? Kallonta Mama tayi tace yana da sana'a tunda har ya jawo aure ai yana da aikinyi. Dije tace amma de gidan kanshi ne bana haya ba ko? Mama tace ko gidan haya ne ai kudi mutum zesa ya kama.



Tabe baki sukayi Mariya tace aini wallahi duk wanda zezo neman auren Diyata se yana da gidan kanshi, da kuma sana'a me karfi, dan baze yuwu ina gidan haya Diyata ta zauna agidan haya ba.




Ina fama da talauci ace Diyata ta auri talaka, idan ta auri me kudi koba komai nima zan huta. Dije tace wallahi kuwa, shiyasa idan kinaso ki gane saurayi me saki ne tun daga neman yarinya zaki gani. Idan wani ankon biki ne shine zeyi mata.




Siyan kayan kwalliyarta duk shine, idan bata da lafiya ma shine ze kaita asibiti, sannan da wuya yazo fira be riko wani abu yakawo mata ba. Amma kaga saurayi yana zuwa hannu biyu ai kasan ba wani abun arziki zeyima Diyarka ba koya aureta.



Murmushi Mama tayi tace ku ne de kuka dauka ahaka abun yake, wani saurayin ko be kashe ma yarinya kudi agidansu ba idan taje gidanshi ze kashe mata ne. Ina amfanin ka bari saurayi yana daukar nauyin Diyarka, ace ko asibiti ma shine ze kaita, idan ya saba kashe mata kudi a waje duk ranar da ya aureta beyi mata abinda ya saba yi mata ba shikenan se afara fada.



Wallahi iyaye muna kuskure wajen tarbiyantar da 'Ya'yanmu, kashe ma yarinya kudi ba shine yake nuna saurayi yana da kudi ba, kada ku manta azamanin nan akwai masu karya, wani baya da kudin daze ci ma cikinshi amma saboda ya burge budurwa haka ze biya mata bukatar ta saboda kawai ta amince dashi, idan ba'ayi sa'a ba daga haka ya hure mata kunne aje ayi abun kunya.




Mariya tace Allah ya kyauta, abun kunya ku ganshi acan, amma munsan irin tarbiyar da muka bama yaranmu, koda ana ganin suna talla amma sunfi mutane da yawa da basa yi, Allah kadai yasan irin abinda masu saka manyan hijabai sukeyi.




So nawa ana kama yaran unguwar nan masu saka hijabai wadan da basa talla da abun kunya, aikede ba anan take ba, kuma duk saurayin da baya kashe ma budurwarshi kudi to matsiyaci ne. Dije tace gane mani hanya. Kede Allah ya sanya akkahiri, ya nuna mana lokacin bikin. Mama tace amin, nagode, tashi sukayi suka fita.




***** ******



Mijin Nafisa ne yashigo da sallama, a tsakar gida ya iske su Mami, risnawa yayi ya gaisheta, su Saudat ma suka gaishe shi ya bude falon su da mukulli yashige. Tsaki Mimah tayi tace wai Mami ba matarshi bata nan ba me kuma yazo yi? Mami tace shida gidanshi.



Saudat tace amma fa yana da wani gidan mezesa yanzu yazo tunda yasan bata nan taje unguwa, haka wancan karon da tayi tafiya duk da a wancan gidan yake haka yarika zuwa nan hada su dora abinci yayi yaci kuma ya kwanta. Mimah tace ai be dace ba wallahi.




Mami tace ikon Allah, kudinshi fa yasa ya kama haya, duk inda yakeso ai anan ze zauna, ni bana son saka ido. Mimah tace Allah Mami baki son laifin wannan mutumin, kuma fa abinda yakeyi baya kyautawa.




Mami tace ni ina ruwana dashi, tsakanina dashi ya bani kudi na bashi gida, kudinshi yakeci, duk abinda yayi bani da damuwa, kamar yanda na kauda kaina daga garesu kuma kuyi haka. Ni kin sa ma naman na fada maki.





Jiya munyi waya da Kawunku, yace sunje sunyi bincike akan saurayinki, kuma komai lafiya lau, saboda haka idan yazo ko ya kiraki ki fada mashi zasu iya kawo kudin neman aure idan ma hada saka ranar za'ayi zasu iya hadowa da kayan sa rana.




Murmushi Mimah tayi ta dukar da kai, Saudat tace wallahi naji dadi, muma za'ayi biki agidan mu, aiko zamu sha party, wallahi. Mimah tace ni ba wani partyn da zanyi. Saudat tace wallahi se munyi. 




Dama bikin Maryam din gidan Maman Halima basa party haka na yayarta da akayi haka mukaje wai sede walima, to Allah naki se munyi. Mami tace to meye dan anyi party, ranar farin cikin ku ne fa. Mimah tace nide bana so Mami.




Saudat tace ai nice zan hada, Mami dan Allah kada asa bikin da nisa. Mami tace dama baza'a kaishi da nisa ba, nagama komai, kawai su muke jira, kilama ayishi rana daya dana gidan Maman Halima. Mimah tace kai Mami abari se munyi bikin Maryam sannan.




Mami tace to se abinda Kawun ku yace, kada kimanta ki fada mashi. Mimah tace to. Fitowa Mijin Nafisa yayi dagashi se gajeran wando da vest ya shiga kitchen ya dora abinci. Tsaki Mimah tayi ta tashi tabar wajen tana kunkunai. Dariya Mami tayi tace aiki ya ganki, mutum baze sake agidanshi ba.



Lekowa yayi yace Saudat dan Allah ko zaki karbo mani maggi? Mami tace kawo seta karbo maka mana, tashi Saudat ki karbo mashi. Mikewa tayi tana kun kunai ta dauko gyalenta ta fita. Daki ya koma Mami ma tashige daki. Bata dadeba ta dawo, falonshi tashiga yana kwance tayi sallama yace Saudat shigo mana.




Shiga tayi ta mika mashi, amsa yayi yana fadin amma kinyi sauri, nagode kinji, murmushi tayi tace bakomai, yace idan na dafa zaki ci ko? Dariya tayi tace nikam ba zanci girkin namiji ba, yace shikenan, ni kuma idan nagama zan kawo maki, juyawa tayi tafita tana dariya.




***** *****


Zaune Jameel da Mubina suke a dakinshi suna kallon wani series film tana jingine da gado tana shan tea, tana sanye da kayan bacci. Jameel yace Baby kinsan mutuminki yanzu shida Ilham soyayya sukeyi. Mubina tace Yaya kana kishi ne? Tsaki yayi yace Allah ya kyauta.




Murmushi tayi tace kaide yaya, idan ba kishi ba bazaka fadi haka ba. Jameel yace bawani kishi kawai fada maki nayi. Mubina tace ni ina ruwana, dama baya burgeni dagashi har ita. Jameel yace toni se yaushe zaki samo mani budurwar? Mubina tace to ai ni kaga banida wasu kawaye.




Amma zan duba acikin friends dina na whatsapp akwai 'yan nan garin se muje gidansu. Jameel yace nima inaso na fara soyayya, dariya Mubina tayi tace kace de aure kake so kayi ka barni. Hannunta ya kamo yace Baby tabbas inaso nayi aure.




Bana so na cigaba da zama haka babu mata. Turo baki tayi tace Allah yaya da ana auren 'Yan gida daya kai zan aura. Dariya yasa hada rike ciki yace lallai Baby har yanzu akwai yarinta akanki.



Bata fuska tayi tace nifa banaso katafi ka barni, shikenan idan kayi aure zaka dena sona, zaka dena kula dani, ko gidanka nazo kaida matarka zaku shige daki ku barni. Hawaye ne suka zubo mata. Saurin matsowa yayi yace Baby, me yayi zafi haka? Turo baki ta karayi.




Jawota yayi ya rungume yana fadin kinaji ko? Duk macen dazan aura bazan sota kamar ke ba, domin ke jinin jiki nace, Uwar mu daya Uban mu daya, kuma zan cigaba da kulawa dake, shiyasa nace nafiso na zaba maki abokina wanda nake da ikon zuwa gidanshi a koda yaushe.




Karar bude kofa sukaji, Amir ne yashigo yana fadin Yaya wai ana maka sallama awaje. Jameel yace waye kuma? Amir yace nima ban sanshi ba. Jameel yace kace yashigo. Hannu yasa yana goge ma Mubina fsuka yana fadin bana so ki kara zubar da hawayenki saboda wannan maganar.




Turo kofar dakin akayi, juyawa yayi, Yaseer yagani tsaye yana kallonsu. Murmushi Jameel yayi yace yau wace rana kazo gidanmu. Shigowa Yaseer yayi ya tura kofar yana fadin wallahi nima unguwarku nazo shine nace bazan kiraka ba bara nayi maka ba zata.



Zama yayi Mubina ta daure fuska tace ina wuni? Murmushi yayi yace lafiya lau kanwarmu, kallo akeyi? Jameel yace kasan ai Baby bata iya yin kallo da kowa seda ni. Baby tashi kidauko mashi abinci da lemu. Tashi tayi tana gyara wandonta daya tattare ta fita.




Yaseer yace haba abokina, se ka ce mace zaka tsaya kana kallon indian film, gaskiya ka bani kunya. Dariya Jameel yayi yace ai tun bana sonshi har Baby ta samani sonshi, domin tana matukar son su.




Shigowa tayi dauke ta tray ta aje tace Sweet Bro zanje daki, yace shikenan Baby amma fa kada kiyi bacci da wuri, tace to. Kofar ta ja ta fita. Yaseer yace kanaji da Mubina sosai, Jameel yace duk cikin kannena itace Allah yafi hada jininmu.




Yanzu ma rigima tagama mani wai bataso nayi aure na barta. Dariya Yaseer yasa yace nima ai ina tunanin ranar da zaku rabu, kun shaku sosai. Jameel yace walkahi kuwa.



Yaseer yace amma kana kokari, ai ni bazan iya bata lokacina wajen kallon irin wannan films din ba, haba abokina ga films can masu kyau wanda akeyi yayi amma ka tsaya kana bata ma kanka lokaci.



Jameel yace wane iri ne? Yaseer yace ka bari gobe zan taho maka da guda biyu kazo ka kalla, ammafa sede ka kori Mubina dan film din maza ne. Jameel yace aiko sede idan bazan kalla ba, Baby da rigima cewa zatayi itama seta kalla.



Yaseer yace idan zata iya kallo ai se ku kalla, amma wallahi zakaji dadinshi sosai, Jameel yace shikenan, kada kamanta. Yaseer yace bazan manta ba. Mikewa yayi yace nizan tafi.




Jameel yace bakaci abincin sosai ba ma. Yaseer yace akoshe nake ne. Fita sukayi seda ya rakashi har bakin motarshi sannan yadawo gida. 



Wata irin dariya Yaseer yasa tare da girgiza kai, a fili yace wallahi A WANI GIDAN. De ana shirme, wai kamar Jameel da Mubina arika barinsu suna kebewa su biyu adaki. Lebenshi ya cije yana murmushi ya kunna motarshi yayi waje.



Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[4/28, 6:39 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  40 ⚜ 45



Zaune Yaseer yake a office ya baza films akan tebur dinshi yana rubutu a jikin wata takarda yayin da wasu mata da miji suke zaune agabanshi. Da sallama Ilham tashigo tana sanye da wata doguwar riga me hade da mayafinta purple colour, sosai tayi kyau.



Dago kai Yaseer yayi yana kallonta, sam ya manta da mutanan da suke gabanshi haka yacigaba da kallonta, takowa tayi tana murmushi tashigo ciki, gaisheta mutanan wajen sukayi hakan yasa Yaseer yadawo daga kallon da yake mata.



Karasa rubutun yayi ya mika masu takardar tare da yi masu bayani. Godiya sukayi mashi suka fita. Suna fita ya taso ya rungume Ilham yana fadin gaskiya yau kinyi matukar kyau. Tureshi tayi tana fadin a office fa muke.



Shafa kai yayi yana murmushi yace dan Allah yau mutashi da wuri muje muyi kallo. Zama tayi tana fadin babu inda zanje, kana gani jiya badan Allah yaso ba da yanzu ka rabani da......... turo kofar da akayi ne yasa tayi shiru.



Cak ta tsaya tana kallon wanda yake bakin kofa, jitake kamar ayau ta fara ganinshi, ba karamin kyau yayi ba, takasa dauke idonta daga kanshi, jitake kamar taje ta shige jikinshi. Daure fuska Jameel yayi ganin kallon da take mashi.



Murmushi Yaseer yayi yana sosa kai ya matsa daga jikin Ilham dan ya shige mata da yawa. Hannu ya mikama Jameel yana fadin abokina ka ganni shiru ko? Murmushi Jameel yayi yace shine nace bara nazo na karba da kaina ai.



Gyara zama Ilham tayi tace ina kwana Dr? Ko kallonta beyi ba ya amasa a ciki, mika mashi films din Yaseer yayi yana fadin gasu nan guda biyar ne, idan ka gama dasu zan karo maka wasu. Jameel yace nan da sati 2 kila zan gama.



Kasan Baby bazata yarda ayita kallonsu ba, dole se mun kalli films dinta. Yaseer yace bazan ce maka komai ba, idan kaje kafara kalla zaka bani labari. Dariya Jameel yayi yace baka da kyau Yaseer, ni natafi ina da aiki a office da acan ma zan fara kalla.




Yaseer yace rufa mana asiri, taya zaka kalli wannan film din a office, ai ko gida kaje kada ka kunnashi da rana, kabari sekayi sallama da kowa sannan ka sama dakin ka key kayi shirin bacci ka kunna abunka, dan idan kafara kallonshi bazaka iya tashi ba daga haka bacci ze dauke ka.



Daga kafada Jameel yayi yace shikenan, semunyi waya, hannu yabashi ya fita. Tura kofar Yaseer yayi yadawo ya zauna saman tebur yana dariya. Ilham tace bakada kyau, kana so kasa bawan Allah yafara neman mata ko? Yaseer yace ba wasu matan daze nema, ai abokina akwai karfin hali, yanda kikasan waliyi haka yake.




Dariya Ilham tayi tace wane irin waliyi kuma? Yaseer yace idan ba waliyi ba taya namiji kamar Jameel ace har yanzu baya soyayya. Ilham tace ai duk jirgi daya ya kwaso ku, kaima gashi har yanzu baka soyayya.



Yaseer yace nikam da ban nake, domin ina rage zafi. Ilham tace wato kana da wasu 'yan matan kenan? Sosa kai yayi yace wai ina nufin ke. Duka Ilham ta kai mashi tana fadin nima daga yau bazan kara biye maka ba tunda kana so kasani shiga damuwa.



Yaseer yace yi hakuri bazan karaba, jiyama akasi aka kusa samu kuma Allah ya takaita. Kema nasan fadi kikeyi bazaki iya rabuwa dani ba. Murmushi Ilham tayi tace kawai kasa na saba da kai ne, ko bacci nakeyi ina tunaninka. Gaskiya duk matar daka aura zata more.



Yaseer yace kema haka, kin iya kula da mutum, Allah yasa ke rabo nace. Shiru tayi tana kallonshi, hure mata ido yayi yace wannan kallon fa? Lumshe ido tayi tace ai ba soyayya muke da kai ba.




Murmushi Yaseer yayi yace hakane, nasan har yanzu kina son Jameel, ni kuma na cire Mubina azuciyata domin nasan bazan taba samun ta ba, yanzu daukar fansa shine kawai arai na, kuma na fara dauko hanya. 



Ilham tace wace irin daukar fansa zakayi? Tashi Yaseer yayi yana dariya yace kede ki zuba ido kiyi kallo, amma bazan bari wannan yarinya tacigaba da cin mutuncin maza ba. Ilham tace nikam banga ranar da zan dena son Dr, ba.




Yaseer yace zaki dena ne, akwai ranar da zakicire sonshi aranki kisaka na wani, ai sabo ake yimawa ba wai soyayya ba. Ilham tace me kake nufi? Daukar kayan aiki yayi yace zaki gane nan gaba. Muje ki rakani cikin asibiti.





Mami ce take ta kwala ma Mimah kira, da sauri Mimah ta fito rike da hijab tana fadin Mami takalmina na tsaya dubawa, Mami  tace ina Saudat din? Mimah tace tana can tana bacci.



Daki Mami ta koma tana fadin Saudat tashi zamu tafi ki gyara gidan kuma ki dafa farar shinkafa akwai sauran miyar jiya ki kara albasa da attarugu se ki kara maggi. Juyi Saudat tayi tace to Mami se kun dawo kuyo mani tsaraba.



Juyawa Mami tayi tafice haka suka fita ita da Mimah. Nafisa ce tafito sanye da gyale ita da mijinta zasuje unguwa, gaishe da Mami mijin yayi yana fadin unguwa zakuje ku ma? Mami tace wallahi kuwa. Yace Allah sarki ashe rufe gidan za'ayi? Mami tace ai Saudat tana nan.



Yace to se kun dawo, Mami tace Allah yasa, fita tayi dan Mimah tun dazu ta fice. Mimah tace wai kema Mami kin tsaya kina masu bayani ita ko se wani daure fuska takeyi. Mami tace ni ina ruwana da ita, mijinta yana bani girma dole na kulashi.




Ai babu dadi yana mani ladabi ni kuma saboda fushin matarshi na ki kulashi, hakan da nake mata shine ze kara sawa taji haushi. Mimah tace ita de ta sani. Bayan su Nafisa sun fito mijinta yace amma de bazamu dade ba idan mukaje ko? Nafisa tace haba Dear, kai fa kace idan mukaje seda dare zamu dawo.




Shiyasa fa ko girki banyi niyar dorawa ba. Murmushi yayi yace ai nima akwai wani waje da zanje shine nake tunanin mudawo da wuri. Nafisa tace shikenan, ka barni acan idan ka dawo se mu dawo tare. Murmushi yayi yace shikenan, yanda kikeso haka za'ayi. Tace nagode.




Seda Saudat ta gama baccinta sanna ta tashi tana sanye da rigar bacci iyakar guiwa kanta babu dankwali ta fito, brush ta farayi sannan tafara gyaran daki sannan tafito tana share tsakar gida.



Turo kofar gidan akayi tare da sallama, dago kai tayi tare da amsawa, mijin Nafisa tagani,  murmushi yayi yana fadin Saudat aiki kikeyi? Shara tacigaba tare da fadin ina kwana? Yace lafiya lau.



Ai mun gaisa dasu Mami ashe unguwa suka tafi? Saudat tace sunje Gwarzo. Yace amma yau zasu dawo ko? Saudat tace E zuwa anjima zasu dawo, dakinsu ya bude yace itama Nafisa taje cikin gari suna.



Shiru tayi batace mashi komai ba, bayan tagama shara ta dauko wanke wanke tayi ta share wajen sanna taje ta cire kaya tafito zata shiga wanka, fitowa yayi sanye da gajeran wando yana fadin Saudat yau fa maza ne a kitchen.




Dariya tayi tace ai gara arika barinku kuna shiga zakufi tausayin mata. Kallonta yayi yace ai mun fiku iya girki kawai aiki ne yayi mana yawa shiyasa bama tsayawa muyi amma da babu abinda zesa narika barin mace tana mani girki.



Ko yanzu nasan nafi mata da yawa iya girki. Dariya Saudat tayi tace wallahi nide baka fini iya girki ba. Yace ko za'a gwada? Saudat tace ai wanka zanshiga da angwada, yace to nima ai zan sake wankan kije ki sako rigar da kika cire idan muka gama se muyi wankan.



Sede idan tsoro kikeji kada nafiki iyawa, juyawa Saudat tayi da sauri tana fadin wallahi baka fini iyawa ba, ka jira yanzu zan fito za'aga wanda yafi iya girki. Murmushin jin dadi yayi.



Tana fitowa yace to me zamu dafa me sauki? Kai ta daga tana tunani tace adafa indomie dama ban karya ba. Yace shikenan. Haka suka shiga kitchen tare suka dora indomie yana ta bata labarai masu ban dariya.



Haka suka gama yace atare zasuci, sosai Saudat ta sake dashi haka sukaci abinci suka wanke kayan, kallonta yayi yace to wayafi iya girkin? Saudat tace ai tare mukayi baza'a gane ba. Murmushi yayi yace haka ne.



Gaskiya yau naji dadi sosai, ashe haka kike da sakin jiki da mutane? Na dauka kina da girman kai ai. Murmushi tayi tace kaima ai ka iya bada labari me dadi. Murmushi yayi yace kinji dadi kenan? Tace sosai ma.



Hannunta yakamo yace amma fa kada ki fadama kowa, kinsan Mami zatayi fada. Lumshe ido tayi tace babu wanda zan fada mawa, yace yauwa, wallahi  jinake kamar ace bada wuri su Mami zasu dawo ba kinga yau da mun yini tare kinsha labarai.



Saudat tace ai seda dare zasu dawo, nima abinda yasa ba'a tafi dani ba saboda na tsaya nayi mana abinci kuma ma zuwan na Mimah ne shiyasa. Amma yanzu idan nayi wanka zan dora abinci.



Kamata yayi suka mike yace to idan kika gama wankan zan tayaki aikin, tace to. Daki tashige ta ciro kaya tafito, yanda ta barshi haka ta iske shi. Murmushi tayi tace baka shiga wankan ba? Yace ke nake jira.



Dariya tayi tace rufa mani asiri kada Nafisa ta yankani, a hakama ya muka kare tana kishin mu. Tsaki yayi yace wannan ai rashin hankalinta ajininta yake, kin fita komai, murmushi tayi tace to bara nayi wanka.



Jawota yayi ta fado jikinshi, kasa yayi da murya yace Saudat tun ranar dana fara ganinki naji kina burgeni. Kinada matukar kyau, dan Allah inaso daga yau na zama abokinki amma na sirri. Murmushi tayi tare da kara lumshe ido ta daga kai.




Kiss yayi mata a kunci yace nagode, kuma daga yau zamu fara jin dadin mu, kada kibari kowa yasan tsakaninmu. Tace to. Sakinta yayi tashige bandaki tana dariya. Iska ya hura tare da sakin murmushi ya shige daki hada dan tsallanshi.





Se wajen karfe biyar su Mami suka dawo, suna sauka daga adedeta Mami tace ma Mimah ki wuce da kayan zan shiga wajen Maman Halima nayi mata murnar sa auren Maryam ban samu naje ba. Mimah tace muje kihuta gobe se kizo kiyi mata mana.



Mami tace kede gara nashiga yanzu bana so mu hadu da ita banje nayi mata Allah yasa alkhairi ba ai da kunya. Mimah tace to sekin taho, wucewa tayi ita kuma tashiga gidansu Maryam.



Tana shiga da sallama mijin Nafisa yashiga dakinsu, ciki tashiga tana fadin Saudat bakijin sallama ne? Gaban Saudat ne yafadi jin muryar Mimah, Allah yaso yanzu mijin Nafisa yafita yaje ya dauko wayarshi.



Fitowa tayi tana fadin amma kunyi saurin dawowa. Mimah tashiga tana fadin shi kuma wancan me yakeyi agida ba ya ce unguwa zasuje ba? Saudat tace ina ruwanki dashi, ba gidanshi bane, Mimah tace dole na tambaya ai tare muka fita dasu.



Tsaki Saudat tayi tace wallahi ke Mimah kin cika daukar ma kanki abinda be dameki ba, ina ruwanki da wadan nan mutanan duk kinbi kin sa masu ido, yanzu zakiji dadi idan ke akema haka? Kika sani ko ita ya baro shikuma yadawo.



Sakin baki Minah tayi tana kallon Saudat, wai yau itace take goya masu baya. Mimah tace e babu ruwana, amma taya ze dawo gida bayan yasan ke kadai za'a bari? Saudat tace ina ruwana dashi, tunda nagama girki ina daki, shima ko minti 20 beyi da dawowa ba. Mimah tace ai na dauka ya dade. Ajiyar zuciya Saudat ta saki.




Bayan Mami sun gama gaisawa da Mama tayi mata Allah yasa alkhairi, anan take fada mata itama Mimah an kai kudin neman aurenta wajen Kawunsu. Mama tace kai amma naji dadi, Allah yasa alkhairi, saura su Saudat.




Mami tace ai ita bayanzu ba, kinsan halin Saudat bata cika kula samari ba. Mama tace aiko gara ki matsa mata tarika sauraronsu, data gama karatu mezata zauna tayi, tunda ba wata makarantar suke wucewa ba ai gara suyi auren hankalin kowa ya kwanta.



Mami tace ai Saudat bata da girman jikin Mimah, ina tunanin ma na barta ta wuce wata makarantar. Mama tace dan Allah Mami kada kice haka, idan mijinta ya nason tayi karatun ko agidanshi zatayi ai. Nifa wallahi da yara sun girma hankalina yake tashi.




Kinsan yanzu wannan zamanin abin tsoro ne. Mami tace haka ne, Allah yakawo nagari to. Mama tace amin, kamar daga unguwama kike ko? Mami tace wallahi Gwarzo mukaje nida Mimah yanzu muka dawo nace Mimah ta wuce na shigo bana so mu hadu banzo nayi Allah sa alkhairi ba.



Mama tace ina kuka bar Saudat din? Mami tace gida muka barta ina zan tafi dasu su duka ga aikin gida kuma ga kudin mota. Cewa nayi ta zauna tayi mana girki, kudin motar ta ai semuyi wani abun dasu. Mama tace amma Nafisa tana nan ko? Mami tace tare muka fita dasu unguwa sukaje ita da mijin.




Jinjina kai Mama tayi tace gaskiya daga yanzu idan zaki je unguwa matukar bada dukansu zaki tafi ba to kirika turo dayar nan gidan, da ace ku kadai ne agidan babu laifi dan kin bar Saudat agida, amma akwai namiji fa.




Mami tace ai bawani abu bane tunda shima yafita shida matarshi, koda yana nan ni babu ruwana tunda kowa yana wajenshi, shikenan saboda akwai wasu agidan bazan bar yara agida ba, dan nice Uwar 'Ya'ya shikenan se nayita daukarsu muna fita unguwa.





Idan muka fita duka shikenan babu wanda zeyi aikin gidan. Gaskiya baze yuwu ba, kowa yazauna a wajenshi, nasan Yarana babu abinda ze hadasu da mijinta, mema zasuyi dashi mutum kamar wada ga muni





Murmushi Mama tayi tace gaskiya Mami akwai gyara acikin gidanki, bakisan illar da take cikin wannan zamanin ba, wadan da suke muharraman juna ma shedan yana ribatarsu bare kuma wadan da basu hada komai ba. Nide shawara na baki. Tashi Mami tayi tana fadin nagode Allah yasa alkhairi nizan wuce. Mama tace ki gaishe da yaran.





***** ******



Da gudu Hamza ya fito jin maganar Laila, abakin gate sukaci karo, dariya yasa yana fadin kiyi sauri kada Umma tasan kindawo wani abu zaki gani. Rufe kofar sukayi da gudu suka shige dakin su Hamza.



Hijabinta ta cire tana fadin wallahi har ka bani tsoro, kai kullum kana gida kamar wani mace. Hamza yace zaki gane ne idan nafara shiga makaranta, wallahi sekin rika kewata.




Dariya Laila tayi tace yi hakuri idan kadena zaman gidan nan ai banida abokin fira, gashi Umma ita batason kallon films din zamani kuma ni banida kayan kallo dakina. Hamza yace kinsan wani abu? Tunda yanzu kina yima Abba abinda yakeso kawai kije ki sameshi.




Laila tace mezance mashi? Hamza yace kice mashi kinaso asa maki kayan kallo adakin ki bakison kina zama a falo tare da mu, ina me tabbatar maki da gudu ze saya maki.




Laila tace aiko ka kawo shawara bara yadawo anjima zanje har daki na fada mashi. Yanzu de meye zaka nuna mani? Wayarshi ya dauko  yana fadin wani hoto zan nuna maki.




Dazu muna chart da wani abokina da nake fada maki mun hadu ta facebook, shine ya dora wani hoto me kyau nace zan nuna maki nasan kece meson namiji me kyau. Dariya Laila tasa tana fadin da gaske? Yace gashi ki gani.



Amsar wayar tayi, gefen gadon tasamu ta zauna tana kallon hoton, kusa da ita Hamza ya zauna yana fadin ya kika ganshi, gayen ya iya wanka shima dan kano ne daga ganinshi kasan yana cikin hutu. Laila tace kai, gaskiya Hamza wannan gayen ya hadu.




Hamza yace kina sonshi? Murmushi Laila tayi, yace ki fada mani ni kuma zan hada ku, amma idan har kika wankeshi inada kaso aciki. Laila tace gaskiya yayi matukar burgeni, ina sonshi.




Dariya Hamza yasa ya kai mata duka yana fadin ai nasan dama zaki soshi. Laila tace bana son iskanci nifa Yayarka ce. Hamza yace yi hakuri kin bani dariya ne, amma yanzu ai nine Yayan tunda ke mace ce. Laila tace nide ba wannan ba, yaushe zaka hada mu?  Hamza yace kawai kituro mani hotunanki masu zafi, ni kuma nasan yanda zanyi.



Hannu Laila ta bashi suka kashe tace yauwa dan kanina, bude wayarka na tura maka dama jiya nayi wasu hotuna masu kyau, amma dan Allah kada ka tsaya sanya. Hamza yace kada kiji komai, inde zan samu kudi banida damuwa.



Tura mashi tayi tana fadin nida kai ai bata baci, kabari musamu shiga zaka more, dama shegun samarin yanzu da sunga kana fitowa daga gida me gate shikenan se su rika matse hannu. Dariya Hamza yayi yace kila kema baki iya kula dasu bane.



Duka ta kai mashi tace nizaka ce ban iya kula da maza ba? Yace emana, to wallahi wannan idan baki kula dashi wasu zasu kwaceshi dan dan soyayya ne. Laila tace kaide ka bari kasha mamaki. Wai ya sunanshi ma? Hamza yace Mujittafa Galadanci, amma anfi kiranshi da Mujee.




Laila tace sunanshi akwai dadi, wayar tace tayi kara tana dubawa taga sunan Ummansu, saurin tashi tayi ta saka hijabinta tana fadin idan kayi magriba kazo dakina ka san Umma idan tashiga bata fitowa se tayi isha'i, ko da tafito nasan yanda zaka fita batare data sani ba. Hamza yace to.



Tana shiga Umma tace yau naga kin dade har ankusa kiran sallar magriba. Laila tace zan shigo kenan naga kiranki shiyasa ban dauka ba. Lecture 4 to 6 mukayi shiyasa. Umma tace sannu da hanya, kishiga ciki idan kin gama abincinki yana kitchen. Tace to Umma sannu da aiki.






Amira ce tsaye ajikin dakin Karami tana leken jikin kofarshi, Amir ne ya taho yana kiranta, hannu tasa abaki tana yi mashi nuni da hannu akan yazo, yana zuwa yace mekike kallo anan? Dariya tayi tace Yaya Mufida ce ita da Yaya Karami suke rawa.



Matsowa Amir yayi yana fadin mugani, bayan ya leka shima ya gani, dariya suka sa. Mubina ce tazo wucewa ta gansu, kusa dasu taje tana fadin kai me kuke leke anan? Rugawa sukayi da gudu suka shige dakin Momy, lekawa taje tayi taga suna rawa, girgiza kai tayi ta nufi dakin Momy tana fadin wallahi bakuda aikin yi.



Tana shiga suka haye saman gado bayan Momy suka boye, Momy tace kunyo jan fada ko? Mubina tace kuzo ku fada mani abinda kuke leke, Momy tace me sukayi? Dariya Mubina tayi tace wai kawai dakin Karami sukaje suna lekawa, ashe wai rawa  suke ta yi shida Mufida.




Dariya Momy tayi tace inde su Karami ne ai sun saba, kullum dakinshi cikin jin sauti suke, idan kika ga Mufida tana rawa kamar itace tayi wakar. Amira tace wallahi Momy Yaya Mufida tafi Yaya Karami iya rawa.



Mubina tace ai sena fada mashi, Momy tace ku kyaleta ko ta fada babu abinda zeyi maku. Momy tace wai har yanzu Dr, be dawo ba gashi har anyi magriba? Turo baki Mubina tayi tace nima yanzu nagama kiranshi wayarshi  akashe, Allah binshi zanyi kawai yaje ya dade.




Momy tace yi hakuri nasan yanzu yana hanya kila wani aikin suka tsaya yi. Karar motarshi sukaji da gudu suka fita hada Mubina sukayi waje, Amir da Amira ne suka riga isa wajenshi, suna zuwa suka rungumeshi.




Dariya yayi yana fadin 'Yan biyuna ya school? Sukace lafiya lau, sannu da zuwa Yaya. Yace yauwa, ku bude bayan mota akwai Sweet da ice cream ku dauko, sakinshi sukayi suka nufi motar.



Dariya yayi daya ga Mubina ta tsaya daga baya tana fushi, matsawa yayi wajenta ya kamota yana fadin haba Baby yau dani ake fushi? Kamar zatayi kuka tace ba kai ne ka dade ba. Jawota yayi jikinshi yana fadin aiki ne ya tsaidani.



Murmushi tayi tace na dauka ko fira ka tafi? Hannun ta yakama suka fara tafiya yace haba de fira, ni yanzu babu inda zanje fira idan ba wajen Baby ba. Hannu tasa ta karbi jakarshi tana fadin to muje kayi wanka.




Bayan yashiga wanka ta bude jakarshi films din da ta gani tayi saurin cirowa tayi ta dauka india ne. Tsaki tayi ta wurgar dasu. Murmushi yayi yana tsaye bakin kofar bandaki. Mubina tace Yaya yau kuma wannan film din zamu kalla? Matsowa yayi yace abokina ne yabani yace suna da kyau.




Mubina tace Allah nide banaso. Jameel yace shikenan yau kowa se yaje dakinshi yayi kallo, amma ni yau shi zan kalla. Tashi Mubina tayi tace shikenan tunda haka kace, fita tazoyi yayi sauri kamota yana dariya.



Tureshi ta farayi tana fadin kasa keni. Matseta yayi yace wasa fa nake maki Baby, kibari muci abinci yau da wuri zamu shigo daki se ayi kuri'a. Murmushi Mubina tayi tace nayarda. Jallabiya yasa ya jata suka fita.




Bayan sun gama cin abinci Mubina tace tashi muje Yaya. Dady yace wai ni saurin me ku keyi haka? Jameel yace wani sirri zamuyi. Momy tace idan ya cika maku ciki zakuyi amanshi mu gani. Karami yace Yaya dan Allah arama mani film mana.



Jameel yace kaima kasan bana kallon irin films dinka, ace kullum kana kallon harbi da fada. Mufida tace wallahi sunfi dadi. Mubina tace nide katashi yaya. Dady yace Dr kana ganin ga Saleem nan dan gidan Alhaji Sambo zeyi aure kai kana nan zaune cikin mata. Sosa kai Jameel yayi yace Dady zanyi ne.




Momy tace nima de inaso ace zanyi biki agidana, idan ma kai bazakayi ba to kabar Mubina ta fiddo miji, nasan kaine kake hanata kula kowa. Jameel yace Allah Momy ba ruwana, nace zan zaba mata miji de.



Dady yace to me kake jira ai yakamata ace yanzu Mubina tana gidan mijinta. Mubina tace nide bazanyi aure nabar Yaya ba. Dariya suka sa Momy tace ai shikenan Allah ya nuna mana ranar da zakuyi auren.




Hannun Jameel takama tana fadin muje. Momy, Dady seda safenku. Karami yace muma da ba'ace mana ba seda safenku. Murmushi tayi tace sorry, Karami, seda safe. Sis bye.



Dady yace Allah ya kaimu, dan nasan se wajen 11 zakifito kwanciya tunda kallo baze bari ki kwanta da wuri ba. Momy tace inde Mubina ce seta kai karfe 12 ita da Dr, suna kallo. Dariya sukayi suka shige dakin Jameel.




Da kyar Jameel ya shawo kan Mubina ta yarda su fara kallon Film din dayazo dasu. Saman gado ya haye yana fadin Baby nasan bazaki iya kallon film din ba zokiyi bacci idan nagama zan tasheki mu kalli wancan. Mubina tace ai nasan Nigerian film basu da kunya.



Kuma wallahi nima sena kalla. Jameel yace zonan idan naga zasuyi wani abu sena rufe maki ido. Zatayi magana film din yafara, jawota yayi ta fado kanshi, suka sa dariya.



Dun daga fara film din kunya ta rufe Jameel, hannu yasa ya kulle ma Mubina ido yana murmushi. Mubina tace Allah sena kalla, wayace ka kunnashi. Jameel yace Baby kunyarki nakeji. Tace ni banajin taka kawai ka bude mani fuska.




Kwanciya yayi ya sakar mata fuska yace toni ahaka zan kalla. Haka sukaci gaba da kallon film din, gaba daya jikinsu seda yayi sanyi, pillow Mubina ta jawo ta kwanta kusa da Jameel tana lumshe ido. 



Jameel yace Baby yanaji kinyi shiru, murmushi tayi tace bacci nakeji. Hannunta ya kamo yana murzawa yace bawani baccin da zakiyi kitashi mugama kallo, murmushi tayi batace komai ba.



Haka yacigaba da kallonshi dan tuni Mubina tayi bacci, jitayi wani abu yana mata yawo ajiki, hakan yasa tashige jikin Jameel bacci ya dauketa. Jameel kuwa kafin yagama jiyayi cikinshi yafara ciwo.




Da kyar yatashi yashiga bandaki, seda yayi wanka sanna yafito, wutar dakin yakashe ya koma kusa da Mubina ya gyara mata kwanciya ya kwanta kusa da ita tare da rungumeta yaciga da kallonshi yana murmushi tare da lumshe ido. A fili ya furta dole nazo nayi aure.



Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[4/29, 5:28 PM] nabilalady5: 👨‍👩‍👦‍👦'YA'YAN MU AMANARMU👨‍👩‍👦‍👦

    👨‍👩‍👦‍👦       👨‍👦‍👦👨‍👦‍👦                  👨‍👩‍👦‍👦


              Nah

   Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO

      (Nabeelert Lady)


 www.NabilaLady5@gmail.com

Facebook...Nabeela Ladeey


        Part  45 ⚜ 50



Hasken daya shigo cikin dakin ne ya tashi Mubina, juyi tazo yi se taji nauyi ajikinta, saurin kallon gefenta tayi, Jameel ta gani yana rungume da ita hannunshi daya yana cikin rigarta saman kirjinta.



Saurin lumshe ido tayi, kara juyi yayi ya kara jawota jikinshi, hannu tasa ta kara rungumeshi tana murmushi. Cikin bacci yaji ana mutsu mutsu ajikinshi, saurin bude ido yayi, Mubina ta najin ya tashi tayi saurin rufe idonta.




Kallonta kawai yakeyi yana murmushi, zuciyarshi yaji tana bugawa da sauri. Hannu yasa yayi sauri zareta daga jikinshi, juyi tayi tare da mika tana fadin Sweet Bro film din yakare? Duka ya kai mata suka sa dariya.




Tashi yayi yana fadin kinsa mun makara, kallonshi tayi tace wai ya akayi cikin kwana biyun nan nake kwana a dakin ka? Jameel yace ki tashi muyi wanka muyi sallah. Tashi zaune tayi tana fadin mu fara sallah sannan muyi wanka de.




Kamota yayi yace jeki daki nide senayi wanka, Mubina tace to meyasa zakayi wanka Yaya? Murmushi yayi ya juya yana fadin idan bakiga komai ajikin ki ba kada kiyi wanka, Mubina tace ban gane ba Yaya? Dariya yayi yashige bandaki.



Dariya tasa ta fice daga dakin, da Momy suka ci karo a falo zata shiga dakin Dady, Momy tace sarkin naci yanzu haka kece kika tashe shi. Sosa kai Mubina tayi tace ai yau babu aiki shiyasa naje na duba ko yayi sallar asuba.




Momy tace leka ki duba idan Karami yayi sallah, Mubina tace to, Momy tana shiga dakin Dady itama tayi saurin shigewa dakinta.




Tunda Jameel ya gama sallah ya kasa tashi daga inda yayi sallar, tunanin abubuwan da suka faru jiya tsakaninshi da Mubina kawai yakeyi, murmushi yayi ya shafi kanshi, tunda yake betaba tsintar kanshi cikin jin dadi irin na jiya ba.




Tagumi yayi aranshi yace Kanwata ce fa? Hannu yasa ya dafe goshinshi. Wayarshi ce tayi kara yana dubawa yaga Yaseer ne, yana dauka Jameel yace shegen kaya, dariya Yaseer yayi yace menayi kuma? Jameel yace tunda ka sani wankan asuba ai dole zaka fadi haka.




Dariya Yaseer yasa yana fadin haba abokina hada kai ma? Nasanka fa kaidin jarumi ne. Jameel yace irin wannan films ai kyau ace mutum yana da Mata, amma kawai ka hada ni dasu, jiya ba kaga rigimar da mukayi da Baby ba.




Yaseer yace kada kafada mani tare kuka kalla? Jameel ya sosa kai yace kasan halin Baby ai, damma tayi bacci da wuri. Yaseer yace to dakinta ka maida ta? Jameel yace bansani ba, kai ka kacika tambaya.




Dariya Yaseer yasa yace kai de ka fada mani gaskiya, nasan bazaka iya barinta ta tafi ba. Jameel yace koma de menene ba ruwanka. Ina Ilham? Daure fuska Yaseer yayi yace me zakayi da Ilham kuma? Jameel yace laifi ne dan na tambayeta.




Yaseer yace Ilham ai ta dade da hakura da kai har ta samu wani, Jameel yace bana son haka, kasan ajiya naji ina matukar son na fara soyayya, babu wadda ta fado mani arai se Ilham, nasan tana sona zata iya debe mani kewa.




Yaseer yace idan zaka iya shawo mani kan Mubina nima zan shawo maka kanta. Jameel yace kasan halin Baby, idan har tace bata son abu to bazata canza ra'ayi ba. Kawai ka share. Yaseer yace shikenan, kai ma ka samo wata.




Jameel yace shikenan, dama temakonta zanyi naga tana matukar sona ne, amma ka samo mani wata mana. Murmushi Yaseer yayi yace abokina zakasa kanka cikin damuwa.




Ka ganni nan tunda na rasa Mubina na hakura da soyayya, gara nashige daki na kunna film dina na kalla na rage ma kaina zafi, kawai abokina ka share kacigaba da jin dadinka. Murmushi Jameel yayi yace shikenan, anjima zanzo gidanku dan jiya na kalli 2, nasan kafin dare zan gama.




Zanzo na karbi wasu. Dariya Yaseer yasa yace ina indian film din? Jameel yace haba share kawai, yau babu inda zan fita key zan sama dakina. Yaseer yace shikenan se kazo. Kashe wayar yayi. Wani ihun dadi Yaseer yasa yana fadin yanzu wasan ya fara.





Tura kofar dakin Jameel  Mubina tayi ta jita a kulle, kwankwasawa tayi tana fadin Yaya ka bude, shiru yayi ya kyaleta dan ya kunna kallo baya son damu, Mubina tace Yaya bazaka bude ba? Tsaki yayi yatashi yana fadin Baby da takura kike.




Bude kofar yayi ya tare hanyar, Mubina tace matsa mani na shigo, Jameel yace kinsan yau babu aiki inaso na huta, Mubina tace to kazo muci abinci su Dady suna tambayar ka. Jameel yace lipton kawai zaki kawo mani.




Idan nafito anjima zamu gaisa dasu. Turo baki tayi tana buga kafa tace nide kazo muci. Yace Baby na fada maki yau hutawa zanyi, Kallonshi tayi tasa murmushi tace kallo kake ko? Daure fuska yayi yace wane kallo kuma? Tace idan ba kallo kake ba ka matsa mani nashiga.




Fitowa yayi yaja hannunta yace muje na gaishe dasu amma bazanci abinci acan ba. Mubina tace Allah sena biyoka. Bayan sun gaisa dasu Dady, Momy tace yau week end shiyasa baka fito da wuri ba? Jameel yace yanzu ma Baby ce ta tasoni.




Bazanci abinci yanzu ba, kallon Mufida yayi yace zuba mani lipton shikadai zansha. Karami yace Yaya anjima zan je Abuja an tura mu wani aiki, Jameel yace na kwana nawa ne? Karami yace 2 days zamuyi.




Dariya Jameel yasa yace ashe shiyasa naga wata tana ta bata rai. Dady yace wai tace seta bishi, Jameel yace babu inda zataje. Mufida tace haba Yaya, kaima fa idan zakaje wani gari kana tafiya da Yaya Mubina ni kuma se ka hana ni. Jameel yace ai tafiyar ba tashi shi kadai bace.




Kuma nasan a hotel zasu sauka kinaso kije kiyi shiru cikin maza? Karami a wace mota zaku tafi? Karami yace ai tafiyar ta gaba daya ce. Matsowa Jameel yayi ya dafa kafadar Mufida yace kinaji ko? Kiyi hakuri idan zeje wani waje shi kadai zaki rakashi.




Turo baki Mufida tayi ta tashi tabar wajen. Dariya suka sa mata, Momy tace ka barta zata sauko ne, kallon Mubina yayi yace ki hado mani Lipton ki kawo mani, yau bana son takura kada wanda yazo mani daki. Amir yace Yaya yau fa zaka koya mana wannan game din daka ce.




Jameel yace kije Momy ta koya maku amma yau hutawa zanyi. Amira tace Yaya dan Allah, Dady yace kunga yau babu aiki, ku barshi yaje ya huta. Itama Mubina kunga yace bazata je mashi daki ba. Turo baki Mubina tayi tace Allah Dady ba bacci zeyi ba.




Saurin kallonta Jameel yayi, Dady yace to mezeyi? Mubina tace wani film........... hannu yasa ya rufe mata baki yana fadin wai dan nace taje dakinta tayi kallo shine take fadar haka. Dariya Momy tayi tace yaude mun ganku arana, tunda tace adakinka zata kalla kabarta mana.




Kasan halin Mubina idan tafara fushi yau babu me iya sakko da ita. Dady yace Mubina daukar maku kayan break din kutafi, gwalo Mubina tayi mashi ya juya yana murmushi. Dady yace idan baka zauna tare da kanwar kaba dawa zaka zauna? Wannan ai shine zumuncin.




Wasu ma suna so suga yaransu suna haka amma Allah be hada kansu ba, WANI GIDAN idan kaje babu wata shakuwa tsakanin yaran gidan, kullum se fada tsakanin sako da sako, shiyasa nake ma Allah godiya, tsakanin ka da Mubina kamar ba itace take bi maka ba.




Kun hada kanku gwanin sha'awa, kowa ya ganku sekun burgeshi, ina alfahari da yarana, domin bantaba jin kuna fada ba, kuna matukar son junanku, shiyasa bana fatan abinda ze raba kanku. Momy tace kawata kullum fadi take wai harso take tazo gidan nan.




Babu abinda yake burgeta se irin yanda yarana suke zaune lafiya, kowa yana kula da Dan Uwanshi, dan Allah ku kara hada kanku, kada kubari wani abu yashiga tsakanin ku har ya raba kanku. Shiyasa nakejin dadin yanda baku da kawaye, nasan sune zasu iya raba kanku.




Jameel yace insha Allah Momy, hannun Mubina yakama yana fadin muje 'yar kanwata. Dariya suka sa, Karami ya tashi yana fadin bara naje nayi lallashi. Dady yace ai kunfi kusa.




Suna shiga dakin yasa key, Mubina ta kalli TV, murmushi tayi tace ai dama nasan abinda kake kallo kenan, murmushi yayi yace kawai inajin dadin kallonshi. Aje kayan dake hannunta tayi tace Yaya nima jiya ko? Kallonta yayi yace meya faru? Murmushi tayi tace bakomai.




Zauna muci abinci. Murmushi yayi ya zauna yace ni kallo zanyi sede ki bani. Zama tayi tace angama Yayana. Dariya suka sa.





Acikin kwana biyu Jameel da Mubina a daki daya suke kwana, shedan ya samu damar shiga zuciyarsu, sam Jameel bayaso Mubina tayi nisa dashi, gaba daya week end din tare sukayi shi, ko sallah acikin daki yake yinta.




Cikin kwana biyu kadai Jameel ya canza, ta gefe daya kuma Yaseer yana kara ingizashi akan kallon film din batsa, daya gama wani yake kawo mashi,  har Mubina ta saba da irin abubuwan da Jameel yake mata.



Yanzu sam yadena jin kunyarta, basu da film din kallo se na batsa, sam Iyayensu basu lura da halin da suke ciki ba, Asabe da Laure kadai suka san cewa Mubina tana kwana a dakin Jameel. 




Ranar monday da Jameel ze tafi aiki rigima Mubina tasa wai se sun tafi tare, jawota yayi ya rungume yace Baby idan kika bini hana ni aiki zakiyi, kuma idan ina kallonki bazan iya tafiya nayi aiki ba.




Nayi maki alkawarin da wuri zan dawo. Zatayi maga ya hade bakinsu, murmushi tayi ta dora kanta saman girjinshi, dagota yayi yace kinyarda ko? Kai ta daga mashi, yace yauwa my Baby, muje ki rakani. Seda ya tafi sannan tashige,  kai tsaye dakinshi ta koma ta kulle ta kunna kallo ta kwanta.







Da Yaseer suka fara cin karo, hannu ya bashi suka gaisa, Yaseer yace wallahi gani nake kamar sabon ango, kaga yanda kake sheki, fuskar ka tana wani fitar da annuri? Jameel yace bade zakaji komai ba, muje yau akwai meeting. Yaseer yace to muje.




**** ******



Gidan su Saleem ana ta shirye shiryen biki, cikin ikon Allah ya samu gida me kyau a hotoro, duk wani gyara yayi, Umma da kanta ta hada ma Jiddah lefe, sosai kaya sukayi kyau, lokacin da suka kai kayan kowa seda ya yabasu.



Hamza da Laila se shirin party sukeyi dan sunce se sunyi party, shide Saleem jinsu kawai yake dan yasan halin Abbansu. Zaune suke a falo hada Umma, Laila tana zaune kusa da Umma tasha hijabinta kamar kullum.



Hamza yace Allah Yaya mude semunyi party, kawai ka bamu kudi mu hada da kanmu. Laila tace gaskiya de, amma ace za'ayi biki a gidanmu babu wani party. Saleem yace babu wani party da zanyi, nasan kona ce zanyi Abba baze bari ba.




Umma tace to meye amfanin party din? Ku barshi kawai ayi walima auren ma zefi albarka, dalilin dayasa auren yanzu baya albarka saboda yawan shagulgulan da akeyi sune suke kwashe albarkar auren.




Hamza yace Umma rana daya ne fa kawai, kuma kowa yana alfahari da irin wannan rana ta bikinshi. Turo kofar dakin Abba akayi, saurin kallon wajen sukayi, Abba ne yafito yana fadin to sarkin 'yan surutu.



Sosa kai Hamza yayi yana murmushi, zama Abba yayi yace Hajiya kinyi dede, babu wani party da za'ayi a gidan nan, walima kadai za'ayi, kuma koda wasa naji ance kunyi party ko ba a garin nan kukayi ba wallahi se ranku ya baci.




Dama nasan Saleem beda matsala, Hamza da Laila sune masu matsala, bazaku taba daukar abinda nake fada maku ba, idan zaku cire ma ranku rudun shedan gara kucire.




Hamza yace Allah ya huci ranka Abba, insha Allah bazamuyi ba tunda baka so. Laila tace ayi hakuri Abba bazamu kara ba. Murmushi yayi yace yauwa yaran albarka. Hada ido sukayi ita da Hamza, gira ya daga mata suka saki murmushi.




Laila tace Abba maganar mu ta jiya. Murmushi yayi yace ina sane dake, ayau zan ba Saleem kudi ya hada maki kayan kallon, amma kirika sanin irin films din da zaki kalla, kinsan bana son kallon marasa kyau. Laila tace angama Abba.



Umma tace yanzu duk kayan kallon da suke falon nan basu isheta tayi kallo ba se an hada mata nata adaki? Kasan irin illar da hakan take haifar wa? Nide idan zakabi shawarata abar saka kayan kallon nan, inde film na Allah ne mutum ze zauna ya kalla a falo.



Abba yace koma menene nafiso tarika zama cikin dakinta, nima bana son yawan zaman falon da takeyi, idan tana dakinta zefi, amma idan ta zauna a falo kowa yashigo seya ganta. Nima naji dadin maganar kayan kallon data kawo mani.




Yin hakan shine zefi, suma su Hamza ai suna da nasu. Umma tace Alhaji yanzu saboda ita kadai se an sa mata kayan kallo? Kabarta ta rika kallo a falo mana. Abba yace ya isa, bana son yawan surutu.




Kudi de nawa ne. Kai Saleem anjima kazo ka karbi kudi kasiyo mata kayan kallo. Saleem yace to Abba. Mikewa yayi yana fadin anjima kije gidan Alhaji Dikko ki kaima matarshi kayan sa ranar Saleem.



Jiya da na bashi IV yake tambaya ta ina na matarshi, duk se kunya ta kamani, yakamata ace yanda muke abota ace kema kuna kawance da matarshi, amma ke kin ki zuwa gidanta, gaba daya zuwanki gidanshi befi so 3 ba.




Umma tace kasan ni bana son zuwa gidan masu kudin nan, kasan halin matar abokin ka, tafi son kula 'yan uwanta akan kowa. Abba yace koma menene kije ki kai mata, bana so mukara haduwa yakara tambaya ta. Ni na fita.




Baki suka hada wajen fadin adawo lafiya Abba, yace Allah yasa. Umma tace Laila kishirya anjima muje akai masu tunda yace haka, Laila tace gaskiya Umma inde da irin shigar da Abba yace na rika fita zanje na hakura.




Umma tace aiko bazaki rika fita ko'ina ba, domin wannan shigar babu ranar dena ta. Saleem ka bama Hamza mukullin motarka anjima ya kaimu. Saleem yace to Umma. Inaso ma bayan bikin nan nama Abba magana ya karo mota daya, kodan saboda Hamza.




Kinga zasu rika tafiya da Laila makaranta, kuma idan zaki fita wani waje zerika kai ki. Umma tace nasha fada mashi haka, kasan halin Abbanku da kudi ai. Amma yanzu tunda yaga kuna bin Dokarshi kome kukeso zeyi maku.




Laila tace Hamza ya maganar mu? Murmushi yayi yace komai yazama dede, zuwa anjima zakiji bayani. Tsaki Saleem yayi yace munafuncin banza, Umma tace kai kuma ina ruwanka, maganarsu ce fa. Saleem yace wallahi Umma wadannan yaran akwai munafuncin da suke kullawa.




Umma tace koma menene sunfi kusa, kaninta ne fa, banaso kana sa masu baki, so kake sudena sakewa da kai? Hamza yace kibarshi Umma nasan yafara bakin cikin rabuwa da gida ne.



Pillow ya wurga mashi yana dariya, Laila tace ka rabu dashi idan yayi aure baze rika ganin mu ba. Saleem yace nima bana son kuzo kada kije ki hurema mata ta kunne. Murmushi Umma tayi ta tashi tana fadin kaima da ba kaji dadi ba ace kannan ka basa zuwa gidanka.




Hamza yace ai wallahi idan na kwaso yunwa can zanrika zuwa, Laila tace ai mun samu wajen zuwa. Saleem yace duk inda da dakin ku. Tashi yayi yabar falon. Hamza yace ke, munfa gama magana da Mujee, lokacin da yaga hotonki kinga yanda ya rude.




Yana tambayata nace mashi yayata ce, tun jiya yake kirana, nace mashi yabani lokaci na shawo kanki dan baki kula samari, dariya suka sa yace ai dole na kankaro maki aji. Laila tace nagode, daga yau zan fara shigow gari. Hamza yace Allah de ya kauda idanun su Abba da Umma, tace amin.




******* ******** 



Maryam, Maryam, wai kina ina ne naketa kwala maki kira haka? Fitowa Maryam tayi tana fadin wallahi Halima na tsaya jira, Mama tace yamma tanayi gara kuyi sauri ku dawo kada Babanku yazo yasamu bakwanan.



Maryam tace kinsan ma me dinkin nan be gama ba, Mama tace aiko gara kije ki sameshi yaufa saura sati 2, gara ki hada kayanki waje daya. Halima tace Mama daga can fa gidan Yaya Amina zamu wuce. Mama tace me kuma zakuyo, ba shekaran jiya kuka je ba? Halima tace wai wani sako zata bama Yaya Maryam.



Mama tace ai fa, inde Amina ce bataki kullum kuna gidanta ba, tunda bikin nan ya matso, Maryam tace tashi muje kada muyi dare. Mama tace ku gaishe su, dan Allah kada ku zauna, suka ce to.




Mimah ce ta fito daga kitchen ta dora abincin dare, Mami tace Mimah idan kin gama dora miyar zo ki karbo kuka can gidan Ukku. Mimah tace Mami me Saudat takeyi ne? Mami tace wanka ta fito shiryawa takeyi



Mimah tace Allah Mami bana son shiga gidan Ukku, dan Allah Saudat taje ta karbo. Mami tace to jeki fada mata tayi sauri. Nafisa ce tafito daga daki tana ta 'yan wake wakenta daga ita se karamin wando da wata riga iyakar cibi.




Kanta kitson kulu ne ta sakeshi har baya, kitchen tashiga ta fara kokarin dora girki. Mijinta ne yafito cikin shirinshi na fita. Kallonshi tayi tace Dear ina kuma zakaje? Hula yasa yana fadin yanzu zan dawo wani abokina ne yayi mani waya yana bakin titi zanje na sameshi.




Tasowa tayi ta kama hannunshi tace muje na raka ka. Tsaki Mimah ta ja Mami tace aikin banza, ahaka da kike mashi wannan rawar kan baya hana idan ta hado ku ya kamaki ya zane kamar diyarshi.



Mimah tace ni wallahi dariya ma take bani, ta maida mu kamar wasu kishiyoyinta. Dan Allah Mami idan kudinsu yakare kada ki kara amsar wasu, kice sutashi, Allah banason zamansu agidan nan. 



Mami tace haka kawai, ina samun kudi zaki ce na koresu, banga ruwa ba na kama shuka, idan nasamu wani ze kama zan barsu su tafi, amma matukar ban samu kowa ba babu inda zasu je.




Duk bala'in ta iyakarta damu kallo, bata isa tace zata fada mani magana marar dadi ba bare kuma duka. Saudat ce ta fito tana fadin Mami kide na biyema Mimah, bansan me suka tsare mata ba, duk tabi ta sa masu ido. Baki sani ba zunubi kike kara ma kanki tunda kullum sekinyi gulmarsu.




Keda zaki bar gidan ma ina ruwanki da zamansu. Mimah tace dama ai ke killum goyon bayansu kikeyi. Mami tace ya isa haka, amshi ki siyo kuka ta hamsin. Karbar kudin tayi tafita, a zaure taci karo da Nafisa, kusan tureta tayi   hakan yasa Nafisa ta bata hanya tafice.





Dede tasha kwanar layinsu ta hadu da Mijin Nafisa, murmushi tayi tace me kake anan? Yace ke nake jira, matsawa tayi kusa dashi tace ya akayi kasan zan fito? Yace inajin lokacin da Mami tace a kiraki ki siyo kuka ai.



Nima banyi niyar fita ba kawai inason naganki ne yasa nafito. Saudat tace muje kada 'yan sa ido su ganmu. Kallonta yayi yace se wani kara kyau kikeyi, wallahi inaso musamu lokaci mudan kebe amma babu dama.



Saudat tace gobe Mami zataje kauyensu, Mimah kuma naji tana fadin zataje gidan kawarta kuma tace zan rakata, murmushi yayi yace dan Allah kada ki bita, nima zansan yanda zanyi na tura Nafisa wani waje, kinga gobe semusha firara mu.



Saudat tace shikenan, katafi banaso wasu su ganni tare da kai, hannu yasa aljihu yaciro dari biyar ya bata yana fadin gashi kisa kati, Saudat tace nagode, juyawa yayi yatafi ita kuma tashige gidan Ukku.




Tana saka kanta murfin bokiti yayi mata sannu da zuwa, saurin kaucewa tayi har seda ya sameta a kafa, dambe ta iske ana yi agidan, tsakanin Zarah da Zainab. Saurin karasawa tayi dan Saudat awai son jin gulma.




Dije da Mariya se kokarin rabasu sukeyi, da kyar suka rabasu. Zainab tace banza me bin maza, Zarah tace ga kinan mebin maza, ko jiya seda aka kamaki keda wani a wani kango. Mariya tace dalla kiyi mana shiru haka nan, so kuke ku tara mana jama'a.



Dije tace ai da gaskiyarta, wayace taje wajen mazan? Mariya tace ai ba kanta farau ba, itama diyarki ai tana bin mazan, Zarah tace kuma wallahi idan kika kara kula saurayina sena tona maki asiri.




Zainab tace ki tona mana, haushi kike ji Bashar beyi maki anko ba shiyasa kike neman hanyar da zakiyi fada dani, karya akayi maki baki bin maza? Gara ni Ado ne kadai nake bi kuma saurayina ne aure zamuyi.




Sallama Saudat ta karayi ganin fadansu bame karewa bane. Mariya ce ta amsa, ganin Saudat yasa sukayi shiru, Saudat tace abani kuka, karbar kudin tayi tashige daki ta dauko mata, fita Saudat tayi tana dariya.




Tana zuwa gida ta fadama Mami, Mimah tace inde gidan Ukku ne sun saba fada, babu ranar da basa fada shiyasa bana son zuwa gidan, sam yaran gidan basu da tarbiya, banda neman kudi babu binda suka sa aransu.



Mami tace ai 'yan iska ne, wata rana se sun kwaso ma iyayensu abun kunya saboda neman kudi, inama amfanin haihuwar irin wadannan yaran, kana da 'Ya'Ya mata amma ka kasa tarbiyantar dasu. Tashi Saudat tayi tashige daki jin abinda Mami take fada.




****** *******



Se wajen karfe 6 Umma da Laila suka je gidansu Mubina, har ciki Hamza yashiga dasu, Umma tace muje Laila, Hamza yace kawai Umma kije ki fito, Laila tace Allah bana son zuwa irin wannan gidan shiyasa ma ban taba biyoki ba.




Umma tace ai shikenan, idan ta rakoni ta ganki zakiji kunya. Hamza yace Umma irin matan masu kudin nan basa rakiya, Umma tace to bazan barku ba gaba dayanku kufito mushiga. Fitowa sukayi Laila se tattare hijabinta takeyi dan ba tasa nikaf din ba Umma tace tabarshi tunda a mota zasu tafi.



Hamza se dariya yake masu yana fadin wallahi kamar irin matan nan masu Da'awa. Umma tace zan ci maka, haka suka shiga gidan da sallama. Amir da Amira kawai suka samu afalo suna kallo.



Bayan sun zauna Umma tace 'yan biyu kallo akeyi? Da ido suka bisu, Hamza yace ina ma amfani, ace kamar wadannan yaran basu iya gaisuwa ba, Laila tace inde gidan masu kudi ne zaka ga fiye da haka.



Umma tace ina Momyn taku? Basu kalleta ba suka cigaba da kallonsu. Asabe ce tafito daga kitchen tana fadin sannunku da zuwa, Umma tace yauwa, bayan sun gaisa Asabe tace bara ayi ma Hajiyar magana.



Amira jeki kira Momy, hararta tayi tace ni kallo nakeyi, girgiza kai Asabe tayi ta juya tace bara nayi mata magana. Tsaki Hamza yayi yace shiyasa bana son zuwa gidan 'yan gayu. Momy ce ta sauko daga bene tana fadin wai Hajiya ce nake gani yau agidan mu? Murmushi Umma tayi tace wallahi kuwa.



Bayan sun gama gaisawa Momy tace Hajiya wannan katon hijabin fa? Umma tace me yayi? Dariya Momy tayi tace bakomai, ina Laila? Umma tace gatanan itace kuka gaisa ai, Momy tace ikon Allah, wallahi ban gane taba.



Yanzun kema Laila irin wanna shigar kika koma yi? Dukar da kai Laila tayi, jitake kamar tayi kuka. Umma tace kayan biki na kawo maki. Momy tace bade Laila za'ayi ma biki ba? Umma tace Yayansu ne Saleem. Momy tace Allah sarki, yaushe ne? Umma tace nan da sati 2.



Karbar ledar tayi tana fadin Allah yasanya alkhairi, a wane Venue za kiyi Mother's day dinki? Murmushi Umma tayi tace walima kawai zamuyi anan filin cikin gida. Tabe baki Momy tayi tace to fa, walima? To Allah ya nuna mana.



Mubina ce ta fito da gudu daga dakin Jameel, tana sanye da riga da wando kanta babu dan kwali ta bazo gashi, su Amir da suke zaune suma jin karar motar Jameel yasa suka tashi da gudu suka nufi waje.




Umma tace ikon Allah, ashe Mubina tana ciki, Momy tace tana dakin Dr, tana kallo, tun dazu taki cin abinci wai shi take jira, ai tsakanin Mubina da Dr, akwai shakuwa, inde baya gida to bata da walwala.




Umma tace ikon Allah, da sallama suka shigo Mubina tana makale da hannun Jameel, falon yashigo ya zauna yana gaishe da Umma, hannu ya mika ma Hamza suka gaisa, Laila kuwa tunda yashigo take kallonshi.



Ta kasa gaishe shi ma, gaishe da Umma Mubina tayi tana fadin Yaya katashi muje. Hannunta yakama yana fadin ina Mufida? Momy tace tana daki kasan yau Karami baya gida taki kula kowa, so nake Alhaji yadawo ya tayani lallashinta.




Ga abincinku can a akan tebur, Jameel yace Baby kinci naki?  Momy tace kaima kasani ai, murmushi yayi yace dauko mana ki kawo mana daki acan zamuci. Amir yace Yaya mungode, kanshi ya shafa yace kuje kusha kada ku bama Mufida.



Jakarshi ya karba yana fadin Baby dauko mana abincin. Sakin baki Umma tayi tana kallon ikon Allah. Kallon Momy tayi tace Hajiya amma be kamata kirika barin Mubina da Jameel suna zama acikin daki daya ba.



Kalli kayan da suke jikinta fa. Daure fuska Momy tayi tace ai kinsan kowane Gida da nashi tsarin, mu yaranmu haka rayuwarsu take, cike take da soyayya, suna kula da junansu, shiyasa kullum zumunci su yake karuwa.



Umma tace amma kuma........... Momy tace ya isa haka dan Allah, haka tsarin gidan mu yake, rayuwar 'yanci mukeyi. Murmushi Momy tayi tace to Allah ya kyauta, mu zamu tafi. Momy tace to nagode ki gaida gida.



Ko rakata batayi ba tashige daki tana fadin kaji mani mata, ina ruwanki da rayuwar gidana. Suna fita Hamza ya fashe da dariya hada rike ciki. Umma tace dalla bude mani mota mutafi. Hamza yace kema Umma da karfin hali kike, ba ko ina bane mutum yake wa'azi ba.



Umma tace gaskiya ce kuma na fada, ina me tabbatar maka wata rana se tace na fada mata gaskiya itace bata dauka ba, amma wannan sam ba rayuwa bace, wallahi se yanzu nake ganin gaskiyar Abbanku, hakika bedace ace murika barin Yaranmu suna kowace irin cudanya atsakaninsu ba.




Hamza yace amma de mu Umma bama irin wanna shedancin, kawai zafin Abba ne. Umma tace Allah ya kyauta, muje. Wata rana itace zatayi kuka da idonta, Allah de ya bamu rai da lafiya, ba fata nake mata ba, amma wannan hanyar da suka dora Yaransu wallahi bame bullewa bace.




Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263



Post a Comment

0 Comments