Wulakanci dodo ne hausa novels

 Copied By

YAYA HAYAT 

        (admin 

   Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

Cool novel, makeup and kitchen1⃣

                   AND 

Cool novel, makeup and kitchen2⃣) 


      WHATSAPP NO:

   +2347039625239

1

❤💜💚💛💙

Yafi dare duhu

💚💙💛💜❤

®zuwairat (ummumaryam)

0⃣1⃣

Alhamdullilah Allah yayi mani dawowa, before I thought it was over amma I can't do without you angels. Before nace sirrin wasu gayu zanyi amma that have to wait.

Amma pls bawai zan dingayi always ba amma I will try my best to make it up to you. So ko kunga ba post on time you should be patient Don commitments né da yawa. Thanks.

Wata yarinya ce wacce bazata wuce 18 to 19 years of age ba zaune kusa da wani magidancin mutum, sai dariya yake ita kuma Tana magana cikin kasaita, spoon ta daga ta Kai fruit bakin mutum ya bude ya amsa yana lumshe idanuwa

"Baby wannan mixture is so sweet...bana gajiya da shanshi..." Mutumin ya fada cikin muryan yan Hutu, dariya yarinyan tayi tace

"It's my pleasure daddy..." Wani spoon ta Kara kaiwa bakinshi ya bude yana sha, after like five minutes sukaji shewa daga bakin gate, mutumin ya daga Kai ya kalli masu shewan sai naga yanayin shi ya Chanza, kiss yarinyan tayi wa mutumin sannan ta ajiye cup din kan wani cristal table Tana cewa

"Daddy I have to go..." Fuskanshi daure yace

"Wai baby bakiji?... I have warned you ki rabu da wayan nan...because we live in USA does not make us Americans ....we are Africans and we will always be...." Ya fada mata yana kallonta, marairacewa tayi kaman zatayi kuka Tana cewa

"Daddy am sorry...there are my only friends daddy..."

"Dole Inyi wani Abu kan wannan..." Ya fada yana daukan bowl of fruit salad da kanshi do in sha,

"What did you say?.." Ta tambayeshi da alaman bata Jin hausan sosai, kauda kanshi yayi bai Kara ce mata komai ba, yarinyan fita yi cikin long fitted gown dake jikinta, kanta babu Dan kwali, gashintaya sha gyaran da babu bambaci Dana turawan dake jiranta wajen gate dinsu, bayanta dad dinta yabi da kallo abubuwan da yawa suna yawo cikin kanshi, he's feeling he's losing his only daughter ..only child dinshi, ajiyan zuciya ya saki tare da lumshe eyes

"I have to do something..." Ya fadawa kanshi, ihun da aka karayi yasa ya kalli gate din, hugging dinta suke ta koina suna

" rosey, rosey, rosey, " suke Chanting cikin ihu

"Stop...Dady is watching...." Ta fada masu, da sauri yan mata biyar din suka yi shuru amma still wearing a smile da alaman wacce suke tare daita is so special to them, mota Mara Kai suka shiga wasu suka zauna baya while wasu suna cikin motan, Dayan daga cikin baturiya taja motan with loud music suka bar gidan. Wanna mutumin ajiye cup din hannunshi yayi ya mike da hannunshi biyu cikin aljihunshi da gani he's lost in thoughts, Dan ajiyan zuciya ya saki yana takawa ahankali, kallon makeken gidan yayi kaman Mai tunani sai ya girgiza Kai ya cigaba da taka grass carpet da ke koina da gidan Wanda fadin kyau da tsaruwanta daga waje is a waste of time,

"Ko kadan banason loosing dinki...I lost your mom and I don't want to loose you...dole wannan rayuwan Wanda ba namu ba ki daina...Don harkoki ya kawo ni nan doesn't mean Inyi loosing only child Dina to the westerns...no way..." Ya fadawa kanshi, Dan takawa ya din gayi yana tsayawa after like each 5 to 7 minutes.

"What am I going to do...." Ya sake tambayan kanshi sounding so restless.

"Should I take her to Nigeria?..." Ya tambayi kanshi da sauri kuma ya girgiza Kai

"Sam...hakan ba Mai yuwa bane...bank da kowa da zan bawa amanar yata guda daya tilo da Allah ya bani..." Ya fadawa kanshi again,

"I wish now Ina da good siblings..da wajensu zan Kai Maryam har ta koyi aladan mu har Allah ya kawo miji tayi aure sannan tayi taking over companies Dina....amma ko ganina basu sonyi...all because am rich...despite duk taimakon da nake masu ..amma am still the bad one...the greedy one...the stingy one...the selfish one...the arrogant one...oh Allah..." Ya fada sounding very bitter, gani nayi eyes dinshi sun Chanza kala kaman bashi ba, kaman he's remembering something, something that makes him so sad,

"Wai mutum ke bawa kanshi arziki?... Then why is Mine different?... Me yasa nawa arzikin ya zama source of my sadness?... I don't have love ones...no trusted friends...and now the only companion and friend I have is trying to go astray..." Ya fada yana tuna yanda yayanturawa basu respecting iyayensu, yana ganin cases din da yara ke Kai iyayensu court ko wani law enforcement organizations in har wani Abu na bacin rai ya shiga tsakanin su, Sam bayason only daughter dinshi ta koma haka, yana son ta zama shoulder that he can cry on, not the other way round.

"Ya Allah what am I going to do?.." Ya sake fada kaman Wanda ke Neman urgent solution to a horrible problem. Agogon hannunshi ya duba yaga 5pm. Hanyan Kofan dake nan waje yabi ya sadashi da main falo Wanda girma ta ya wuce misali,falon bai da tarkacen Kaya da yawa amma its so beautiful. Kan wani resting Chair ya kwanta tare da lumshe idanuwa kaman Mai bacci. Wannan shine alhaj Mahmoud owner often maryama group of companies. Babban business tycoon me Wanda he's known all over the world, yana da companies a wurare daban2 Amman harkokin shi sun fi yawa a kasancen waje Wanda shiyasa yake zaune London. Alhaj Mahmoud is a nice person but a non nonsense person Don baya tolerating rubbish. He only tolerate his only daughter Don duk abinda ta gan dama takeyi duk da she don't do something bad except yawo da friends dinta which he don't like kuma daya yi kokarin gabanta dai tace she's lonely and bored. Abinda ke tada mashi hankali most shine yanda yarinyan bata da wani behavior da zaisa a gane she's from Nigeria , a nigeria maa arewa, komai nata kaman na turawan, alhaj Mahmoud na iya kokarin shi Don ta Dan gane aladansu amma its not working, kullum yana wishing he has good siblings da zai turata ta zauna wajensu a Nigeria Don ta koyi yanayin rayuwa amma ko kadan basu son ganinshi balle abinda ya Haifa Don last time da sukaje Nigeria saida suka kusa kasheta in the name of accident. Dan gyara kwanciyan shi yayi still with his eyes closed,

"Ya Allah...." Ya furta under his breath,saya daga cikin wayoyinshi yayi ringing, wani ya fito daga Dan corridor dake gefen inda alhaj Mahmoud ke zaune ya dauko wayan ya mika mashi, Dan murmushi ya saki gani Mai kiran, manager din company dinshi na Nigeria né, kuma ya fi ganin loyalty dinshi in sauran maaikantan shi. Picking yayi tare da sallama, daga chan bangaren aka amsa mashi, gaisawa sukayi cikin girma da arziki tare da tambayan family dinshi,

"Sir what's wrong with you?.." Wanda ya Kira ya tambayi alhaj Mahmoud, Dan ajiyan zuciya yayi tare dacewa

"Nothing..." Daga chan bangaren mutumin ya sake cewa

"Sir you sound worried...pls confide in me...nasan da akwai abinda ke damunka...pls sir let me share your burden..." Mutumin ya fada mashi daga chan bangaren, idanuwa alhaj Mahmoud ya lumshe tare da sakin ajiyan zuciya yana tuna irin halin Wanda suke magana, yasan he's a friend, his loyal, he's nice and above all he's among he's best workers, a kullum alhaj Ismail yana daukan damuwan alhaj Mahmoud so personal saboda yasan yayi mashi halarci a rayuwa, ko kadan baya son abinda zai tab lafiyarshi dukda ba a kasa daya suke ba, kaman Yanzu da suke waya yasan something is wrong, Don he sound so dull,

"Pls sir tell me what's is wrong...ka tuna problem shared is problem solved..." Alh Ismail ya sake fada mashi, wani ajiyan zuciyan alh Mahmoud ya saki before saying,

"It's something personal..."

"Ok.... I understand...but pls if you need my assistance in anyway...am around...call me and I will be in London for you...."

"Nagode da kaunar ka agareni..." Alh Mahmoud ya fada mashi, sallama sukayi sanna kowa ya katse wayan. Tunani alh Mahmoud ya cigaba da yayi inda yake tunanin ko yayi involving alh Ismail ko he will give him a good advice since he's older than him,

"How can I tell people I can't control my own daughter...my only daughter...no way..." Ya fada yana mikewa.2❤💙💚💜💛

Wulankaci dodone.....

❤💛💙💜💚






®Zuwairat(ummumaryam)


 Da sunan novel din was yafi dare duhu amma an samu Mai irin sunan littafin, so na Chanza wannan zuwa wulankaci dodone😀😀😀 pls don't worry about the name..you guys know am not Hausa so choosing suna yana bani wahala amma hope you will enjoy the novel. The name doesn't matter..it's what it contains. 


Godiya nake gareku masoyana, thanks for the prayers, mijina ya samu sauki sosai but still need your prayers.




0⃣2⃣





Wannan shine  suhail first son din alhaji Ismail, he's rude, arrogant, stubborn selfish and above all handsome Don tamkar shi ya hallici kanshi saboda komai nashi is accurate from his skin color to his foot, gashin kanshi kwance yake Don da wuya ka gane Dan bahaushe né saboda he looks exactly like his mother who is half Nigerian half Arab, itama mom dinshi ba a ganewa ta hada komai da Hausa Don itama tamkar uwarta take .  Lips dinshi is pink sannan yana da thick eye lashes and eyebrows , ta beautiful set of teeth, eye balls dinshi is something eyes Don in ya zaro su Kaman papers suke, muryanshi kaman waka in yana magana, inshort ya fi  sibling dinshi kyau kuma he's the only boy, yana da kanne mata guda biyu wayanda Yanzu sunyi aure suna gidajensu. A duniya mom dinshi bata hadashi da kowa ba haka kuma bata hadashi da komai ba, she can do anything to make him he happy, she's a professional doctor with a fat salary amma  kusan suhail  kadai ke cin kudin Don duk abinda yake so akeyi. Yanzu ya hada masters dinshi amma Yaki aiki wai shi dole Sai an samo mashi international job, ko ya zauna bai aiki wai he's too intelligent to work in Nigeria, gani yake he's too big for every thing Don ba karamin wahala masu aikin gidan su ke sha hannunshi ba, inshort you must be perfect to work in their house.Horn yayi bakin wani katafaren gate, daga ciki masu gadi suka mike Don sun San yanda yake horning, cos in yana horning tamkar an koroshi ko kuma Ana binshi, sannan yasa dokan in zai shigo dole security men suyi tsaye a both side na gate din, hakan yasan yana horn kome suke zasu dakatar dashi suje suyi tsaye suna jiran shigowanshi, yau ma yana horn duk su hudu suka taso da gudu suka kame kaman soldiers a both side na gate while daya daga cikinsu yayi ihanzarin bude gate, da gudu ya shigo cikin gidan da mota, sauran kadan daya bi ta kadan yabi ta kan maigadin daya bude mashi gate, yana huci ya tsaya ko parking baiyi da kyau ba , fitowa yayi ya kalle maigadin daya  bude mashi kofa ya fara cewa

"You stupid old fool wato tsayawa kayi in buge ka ka  jamIn Sharri kou?... To Bari in fada maka in da buge ka na buge banza...cos you are all nothing...banzaye zero behind decimal point..." Ya fada sannan ya juya still walking angrily yana cewa

"Someone should park my car...." Da sauri daya daga cikin su that looks younger ya nufi motan, yana shigewa duk suka saki ajiyan zuciya tare da watsewa, maigadin ya koma bakin gate looking carefree da alaman abinda suhail  yayi masu bai dame shi ba Don da gani sun Saba. Yana shiga main falo ya fara cewa

"Fall in!!!!!" Ya fada da karfi, da sauri masu aikin gidansu suka fito, yanmata né guda biyu sai wata matured woman guda daya, kalle2 ya danyifor like 5 seconds sannan yace

"Ina Dayan bitch din?" Ya tambaya yana kallonsu one after the other,  cikin cracking voice daya tace

"Tana...kewaye..." Wani irin yamutsa face suhail yayi before saying

"You..." Ya fada yana nuna daya daga cikin ya matan sannan yace

"Come and massage my leg...and you..." Ya sake nuna wata 

"Go mix my fruit salad and come and feed me...and you old woman je ki hada min intestine pepper soup...dashi zanyi dinner..." Ya fada yana komawa kan daya daga cikin kujeran dake cikin katafaren palour. Wacce ya Kira tayi saurin zuwa tayi kneeling gaban shi ta faracire mashi shoes while matured  woman da Dayan budurwan suka bar wajen. Tro pillow ya dauka ya jefa mata ta Kama ta ajiye kasa ta Kama gorgeous feet  dinshi ta Dora kan pillow kaman wani sarkita fara massaging ahankali, relaxing yayi yana lumshe idanuwa ahankali, after like 7 minutes Dayan yarinyan ta fito da bowl of fruit salad ta matso kusa ta debo fruit salad din ta Kai bakinshi, kaman baiso ya bude baki ya amsa, a haka tayi feeding dinshi while Dayan Tana massaging legs dinshi, ahankali ya daga hannunshi da alaman stop, da sauri suka dakata, hannu ya karayi masu da su tafi, still cikin hanzari suka bar wajen. Kitchen suka koma dukkansu, nan suka fara taya matar pounding pepper soup spice Don yanason spices sosai, 

"Allah yasa iyakar wahalal kenan yau...." Inji daya daga cikinsu, 

"Ameen..." Dayan Ta amsa mata, matured woman din batace komai ba sai su yan matan dake ta maganar yanda suhail ke treating dinsu, 

"Ni wallahi da Ina da daman sake gidan aiki da na sake...na gaji wallahi..." Inji wata Mai suna asabe

"Hmmm ni kuma wallahi ban Jin haushinshi....dama né ya samu...Sam ban ganin laifin shi kaman hajiya...itace ke daure mashi gindin yin duk abinda ya gan dama...wata rana sai labari..." Inji wata Mai suna murja, 

"Ni wallahi yayi aure ya bar gidan nan...ko mun samu sauki..." Inji ta ukun Mai suna 

binto, hararanta mature woman din wacce suke Kira da baba rabi tayi Tana cewa

"Ke baki fatan Allah ya baki miji kiyi aure?... Ko kinason ki dauwama a haka?..." Da sauri su uku suka girgiza mata Kai,

"To ku bar maganan shi, kuyi aduan Allah ya Baku mazanjen aure...sai ku bar mashi  gidansu..." Ta fada Tana kwashe cittadaga cikin turmin daka, 

"In mun tafi kefa?" Asabe ta tambayeta cikin sanyinmurya, Don su hudu dake aiki cikin gidan kansu hade, suna girmama baba rabi sosai saboda ta rike girmanta

"Ai nawa ba matsala bane...kawai ku Allah ya kawo mijin aure..." Ahankali suk amsa da ameen.


Suhail mikewa yayi, tare dacewata 

"Fall in..." Which is the general call da yake masu, da sauri dukkansu suka bayyana

"Follow me with my shoes...." Yayi commanding dinsu without pointing finger at anyone of them, da sauri murja ta duka ta dauki shoes din Don duk dakikancin in har kana tare da suhail you must hear English Don shi bai yarda da wannan aladan yin Hausa zalla ba, infactmostly da turanci suke magana da mom dinshi kuma haka na batawa dad dinshi rai matuka Don gani yake in har hakan ya cigaba har suhail yayi aure to yaranshi bazasuji hausan ba and suhail is his only son so bayason legacy dinshi ya mutu hakan yasan dad dinshi yake kokarin sanya shi on the right path amma mom dinshi Tana warware mashi aiki tunda she's the one staying with him always. 

Ahankali yake taka stairs while murja na biye dashi with his shoes. Daya daga cikin dakunan dake upstairs ya nufa, gefen Kofan ya koma murja tayi saurin bude mashi, nikam wondering nake wane irin sarauta suhail ke takama dashi Don ko yayan sarakuna basu kaishi mulki ba, in fact gane yake nobody is above him. Tana bude mashi ta koma gefe amma sai da ya bangajeta ya shiga ciki, dakin ya hadu matuka with foreign furniture da sauransu, wata makeken pics né jikin bango Wanda suhail né da mom dinshi, kallon dakin na yi Ina tunanin Anya dakinshi né? Because kan mirror dauke yake da Kayan Shafa da cosmetic kala2 which seems obvious tun dashi namijine, juyawa yayi ya Gallawa murja dake tsaye Tana kallonshi yayi, nan take tayi saurin sadda  Kai kasa tare da komawa baya ta  jawo Kofan, 

"Idiot..." Ya dada under his breath sannan ya nufi wata katuwa closet ya jawota, wasu files né cikin closet din, Dan daga su sama yayi sai bundle din 100k kaman guda 4, hannu yasa ya dauki bundle daya sanna ya fita, har lokacin murja Tana nan waje Tana jiranshi still holding his shoes, downstairs ya nufa Tana biye dashi, fita yayi ya nufi wata karamar flat dake cikin gidan. Daga Chan bakin gate Mai gadi ya kura mashi Ido yana kallon yanda yake tafiya full of confidence 

"Hmmm Allah ka shirya wannan yaron...ba Don halin uwarka ba...sai Don kirkin ubanka..." Mai gadi ya fada under his breath.  

Suhail na kaiwa bakin main door ya zaro key cikin aljihunshi ya mikawa murja, cikin sauri Ta amsa ta buda mashi  Kofan. Security men suna zaune suna kallo as always, sai da ya shige sannan suka Dan saki dariya daya daga cikinsu which is younger and handsome yace

"Ooohhh duniya...." Yafada yana dariya, sauran biyu suma dariya sukayi 

"Amma gaskiya har da yarinta ke damunshi..." Inji daya daga cikinsu, 

"Wallahi ba wani yarinta...kawai samun wuri né.....ya Salman ai shekarunsu daya...meyesa shi bai haka?.." Da sauri,matanshin  Mai kyau yace

"Ina ni Salman na samu daman behaving haka?... Ai shi Dan masu kudi né ni kuma Dan talakawa..."

"Ai kudi ba hauka bane...kaman gidan nan farau arziki?... Mu bamu huta ba haka yanmatan dake ciki basu huta ba...," Dan murmushi Salman yayi yana kallon Wanda ke magana, saida ya Kai aya sannan yace

"Ai da sauki tunda abun daga wajenshi da hajiya né kawai...ai da alhaji ke da bakin Hali da bamu iya zama gidan nan.. Jibi yanda yake kula da mu tamkar yayanshi...ya daukemu a matsayin bodyguards amma da wuya ya fita damu...mostly muna gida kuma wata na karewa zamuji alert...sannan bayan albashin da yake bamu yana kula da lafiyan mu da cin mu da Shan mu...ni wallahi ko me suhail zaiyi min alkhairin alhaji bai Barina inga laifin shi...." Inji Salman. Dan ajiyan zuciya duk suka saki sannan wani babban cikinsu yace

"Wannan haka né...ai alhaji karshe né wajen adalci...Amman hakan bai hanani fatan Allah ya hada wannan yaron da Wanda zaici ubanshi..." Ya fada yana dariya, duk suka ce ameen amma Banda Salman. 

Salman is kanuri by language amma shi da iyayenshi suna zaune a garin Kano, a Kano aka haifeshi nan yayi school from primary to diploma. Alhaji Ismail na sonshi sosai Don ya yarda dashi shiyasa duk important errand shi yake aika. 



Har karfe biyu na dare Maryam bata dawo gida ba, suna Chan suna party kaman ba dare ba, da dad dinta ya Kira sai ace leave a message. Alhaji Mahmoud ji yayi kaman hauwan Jininshi zai tashi saboda tsoron wani Abu ya faru, yan sanda ya Kira ya fada masu diyar shi ta fita bata dawoba suka tambayeshi tun yaushe ya fad masu sai cewa sukayi bazasuyi declaring nata missing ba sai bayan 24 hours. Wurgarda wayan yayi yana cewa

"Something have to be done..." Yqfada da karfi.  Shuru yayi for more than an hour yana tunanin, kaman Wanda ya tuna wani Abu sai yace

"Yesssss..." Ya fada on top of his voice. Komawa kwance yayi tare da relaxing yana jiran gari ya waye ya Kira alhaji Ismail dukda ba time daya bane. Maryam bata dawo gida ba sai wajen 15am. Tafiya take kaman Mai Jin bacci, da kyar ta Kai dakinta ta wulla kanta kan gado, nan take bacci yayi gaba daita ko shoes dinta bata cire ba. 

 




Karfe takwas driver ya maido alhaji Ismail da matar shi gida. Lokacin suhail yaci   intestines pepper soup ya koshi yayi sallah yabi lafiyar gado, ba bacci yake ba kawai yana kwance cikin blanket yana chatting da su Yusuf cikin group din da suka bude only for four of them wato suhail, Yusuf, sadiq sai aliyu. Kowanne na labarin new babe amma Banda suhail da sunyi magana sai yace har Yanzu bai gan yarinyan data dace da status dinshi ba, sauran kam Banda dariya babu abinda suke mashi and duk abinda zasuce mashi basu bata nashi rai Don an San halin juna.


Driver parking lot yayi parking hajiya da alhaji suka fito, Kaman kullum fuskan hajiya daure ta shiga falon ta while shi kuma alhaji ya nufi nashi part din. Tana shiga ta ajiye handbag dinta sannan ta daga Kai tare dacewa

"Kuna Ina?.."  Ta dafa da Dan karfi, daman dakin masu aiki yana downstairs, kuma tunda sukaga shi gan motan suke expecting kiranta Don sun San babu fashi, Tana cewa kuna Ina sai suka fito, dukkansu durkusawa sukayi sukayi suka gaidata amma ko daga ki batayi ba ta dauki wayanta, number datayi saving da my eyeballs ta fara dailing 

, ringing biyu suhail ya dauka tare dacewa

"My love kun dawo?..." Ya fada cikin shagwaban da mom dinshi ke mutukar so da Kauna, 

"Yes my eyeballs...where are you?.."

"In my apartment...am lying down..." 

"So soon?... Have you eaten?.." Ta tambayeshi sounding so caring 

"Yes mommy..."

"Baka zuwa mu danyi hira?" 

"Mommy no...kawai tomorrow...am exhausted..." 

"Alright...Allah ya tsareminka..." 

"Ameen my love..." Ya amsa with his eyes closed 

"And ka tuna kayi adua before sleeping..." Ta fada mashi kaman wani 8years old boy,

"Sure mommy" ya fada yana sauke wayan daga kunnenshi sai kuma ya maida yana cewa

"Mom are you there?" Ya fada kaman ya tuna wani abu, 

"Yes dear ..am here... Anything?.." Ta tambayeshi sounding so caring, ahankali yace

"Nothing mom...kawai inason fada maki na dauki 100k a locker dinki dazun..." Ya fada kaman the 100k is nothing, Dan bata rai mum dinshi tayi sannan tace

"Wai what are you doing with money...last week nayi maka transfer na 80k...and the money you took is not mine...dad Dinka ya bani ajiyan su..." Marairaice face yayi kaman yana gabanta sannan yace

"Ai motata ke consuming kudin...pls transfer the money into dad's account...banason fadanshi...." Ya fada cikin shagwaba, shuru mom dinshi tayi for a moment sannan tace

"Alright...amma pls minimize your spending..it's getting out of hand..." Ta fada mashi,

"Ok mom...good night..." Bata Kara cewa komai ba ta katse wayan, sai lokacin ta juya ya kalli su baba rabi dake durkushe Ta amsa gaisuwansu tare dacewa

"Hope kun yiwa suhail abubuwan da yake bukata?.."  Ta tambayeshi as usual Don bata da damuwa sai ganin suhail in a bad mood,

"Eh..." Suka amsa in chorus,

"Good...ku tafi... You " Ta nuna asabe,

"Kiji ki hadamin ruwan wanka..." Ta fada Tana mikewa

"To hajiya abincin fa?.." Baba rabi Ta tambayeta, harara Ta balle mata before saying 

"Kin taba tambayata kafin inci abinci?" Da sauri baba rabi ta girgiza mata Kai

"Ai in kin gan ban tambaya ba kawai bazan ci ba...amma get me a cup of tea..." Tana kaiwa nan ta kama hanyan stairs, bag dinta asabe ta bita dashi while ita kuma Tana gaba tana tafiya kaman bata son taka kasa. Duk Wanda zai ganta bazai taba tunanin zata iya ciza yatsa ko kashe fly ba amma she's so mean especially to people below her standards. 



The following day around nine suhail né zaune kan dining sanye da red three quarters sai red polo, yayi relaxing kan kujeran dining with his eyes closed sai kada legs yake kaman wani sarki at the same time Asabe Tana hada mashi tea while murja Tana zuba mashi chips da salad cikin plate, sai da suka gama ya mike zaune tare da bude eyes dinshi ahankali, tea ya fara kaiwa bakinshi yayi saurin saukeshi tare da kallon asabe data hada tea din

"Ke you want to kill me...ya zaa yi ki hadamin tea Mai zafi haka?... Kin San I don't eat hot food..." Ya fada cikin fada sosai, 

"Kayi hakuri..." Bata idaba yace

"Keep quiet before I leave a mark on your ugly face...I said kinason kasheni da wannan ruwan zafin?.." Ya daka mata tsawa, nan da nan jikinta ya fara rawa, hajiya ce ya fara saukowa daga upstairs Tana kallon dining da suhail da face dinshi yayi red saboda fada, 

"Eyeballs what's wrong?.." Ta tambayeshi tun kafin ta karasa inda yake zaune, kaman zaiyi kuka ya Kama cewa

"Mom wanna yarinyan wants to kill me...kawai ta bani extra hot tea insha Don ta kashe ni...." Da sauri hajiya ta karaso wajen Tana cewa

"Inna lillahi waina ilaihi rajuun....let me see...." Ta fada Tana saka yatsanta cikin tea din, da sauri ta Fido hannunta tare dacewa

"Wayyo...." Ta fada Tana kallon asabe, 

"Kuyi..." Asabe ta fara cewa amma bata karasa ba sai taji saukan Mari at the same time suhail ya dauki cup of tea din ya watsa mata a face Dinta, jumping asabe ta farayi Tana ihu saboda zafin dataji a face dinta.

"Serves you right..." Suhail ya fada mata, murja da binto suna tsaye suna kallon yanda abubuwan ke gudana, 

"Oya kiyi saurin gyara wurin nan..." Hajiya ta daka mata tsawa tare da kallonshi murja before saying 

"Ku kuma tsayuwan uban me kuke..." Ta daka masu tsawa, da sauri suka juya, cikin kuka asabe ta fara takawa Don dauko mopper daidai lokacin alhaji Ismail ya shigo Salman na rike da briefcase dinshi, nan ya hangi asabe that is wet Tana kuka, kallonta ya tsaya yi har zata shige kitchen ya kirata, suhail da mommy dinshi suna kallon shi, da sauri mom dinshi ta karaso wajen alhaji tare dacew

"Alhaji har zaka fita kenan..." Banza yayi daita har sai  da asabe ta karaso wajenshi sannan yace

"Meke damunki?.." Ya tambayeta, shuru tayi Tana kuka, Salman dake tsaye bayan alhaji knows something is wrong with her.

"Nace meke damunki...." Ya sake tambayanta, cikin kuka tace

"Ba komai..." Hajiya Dan murmushi ta saki Don tayi masu warning kan such issues. Bai Kara cewa komai ba ya fara taka stairs ahankali suhail ya mike yabi bayanshi yana cewa 

"Daddy good morning..." 

"Lafiya..." Kawai ya amsa mashi ya haye, direct dakin hajiya ya shiga while hajiyan Tana biye dashi, bayan sun shiga yace

"Dauko min wayan nan kudin...zan bawa Salman ya ajiye su a bank..."  Ya fada yana gyara zaman hulan shi, ahankali hajiya ta bude locker ta dauko 300k, ta mika mashi Tana cewa

"Bani specific account din in tura maka 100k...suhail yayi amfani da su..." Ta fada mashi in I don't care manner, bata rai alhaji yayi tare da daukan wayan shi daga cikin aljihunshi, number suhail yayi dailing yana piçking yace

"Meet me now.." Ya fada mashi atakaice sannan ya katse wayanshi. Suhai dake zaune yana cin dankali ya mike yana cewa

"Kome zanyi mashi?.." Ya fada yana hawan stairs. Yana shiga dakin hajiyanshi dad dinshi ya mika mashi hannu with out saying a word, suhail kallon dad dinshi yayi ya kalli mom

"Give me the money Yanzu nan kafin ranka ya baci...." Ya fada kaman bai taba dariy ba, hajiya bata rai tayi tan cewa

"Which money?.. Nace maka ka bani account in tura maka sai ka Kira Dan dake breakfast kana harassing dinshi?.. Gaskiya I don't like this ..." Ta fada sounding very harsh, ko kallon ta alhaji baiyi ba yace

"Suhail in nayi counting 3 Baka dauko kudin nan sai ranka yayi mugun baci Don I will make one call and your account will be frozen...maza je dauko min kudina..." Ya fada kaman hungry lion, da sauri suhail ya bar dakin, alhaji na tsaye with his hands in his pocket while ita kuma hajiya Tana zaune bakin gado sai murmuring take. Few minutes later suhail ya kawo kudin kaman yanda ya daukesu, fuskan shi Sam babu walwala, mikawa dad dinshi kudin yayi ya amsa ya juya zai fita alhaji yace

"Suhail come back here..." Ya daka mashi tsawa, ahankali ya dawo kanshi kasa amma da gani his angry 

"Yanzu suhail an't you ashene of yourself?... While all your mate are out there doing the right thing Kai kana nan sai wasting kudin uwarka kake...sannan ga zalunci Don nasan wannan yarinyan dake kuka. Dazun you are behind it...wai meyasa Baka da zuciya kaman abokan ka?.. I gave you the best education..amma it's of no use...why kakeson zuba min kasa a Ido....even your two younger sisters are better than you..." Hajiya ce ta katse shi dacewa

"Hana alhaji..why are you being harsh on him...kawai sai ka dauki Karan tsana ka Dora mashi?.. Gaskiya I don't like this...kudi né kuma ya baka...name zaka hadashi da  sisters dinshi dake gidan mazajen su..." 

"Ni daman dad never likes me...bayason ko ganina né....." Inji suhail, dad dinshi ya katse shi da cew

"Come on keep quiet...you should start acting responsibly ko kuma Inyi maka aure da Dan ubanka..." Inji alhaji, idanuwa suhail ya zaro da Jin zancen aure

"Allah ya sauwake....ni dai kawai dad ka nemo min aiki a NGOs zanyi...." Inji suhail, harara ya balla mashi before saying 

"Are your friends working in NGOs ?... Amma they are doing great..." Baki ya tabe

"Nidai dad I can't work my ass off for 100 or 150k...i need something better..." Ya fada sounding serious 

"Haka né gaskiya..."hajiya tayi adding, alhaji kallon hajiya yayi sannan yace

"You are not helping him...kina ganin so kike nuna mashi amma na sha fada maki ba haka ake nunawa da so ba...precise to much of everything is bad...ya yaro har ya Kai 29 amma yana behaving kaman he's 15... Allah dai na gani am trying my best..." Inji alhaji, yana kaiwa nan ya juya ya fita da kudin hannunshi. Suhail zama yayi gefen mom dinshi Fuskanshi babu walwala,

"Yanzu mom kudin shikenan?..." Ya tambayeta 

"No dear...I will transfer some into your account..." Ta shaida mashi. Dan murmushi ya saki tare dayi mata kiss ya mike ya barta nan zaune.





Around 12pm Maryam ta farka, duk gashin kanta  a bar baje, Tana bude tayi Ido hudu da dad dinta dake zaune yana sofa dake dakin, da sauri ta mike zaune tare dacewa 

"Good morning dad..." Ta fada Tana hamma,  ahankali dad dinta ya daga Kai ya kalli agogon dake jikin bango before saying 

"It's afternoon..." Ya fada cikin damuwa, duk Wanda ya ganshi yasan he's angry amma yana kokarin boyewa Don yasan in har ta gane yana fushi daita to plan dinshi ba zai yi aiki ba, 

"Good afternoon..." Sake fada mashi Tana mika sosai, kura mata Ido yayi yana kallon yanda kasan idanuwan ta sukayi ja, 

"Baby Ina kikaje jiya...." Ya tambayeta kaman bai damu ba,

" Sophie's house...she's celebrating her 18th birthday..." Ta fada ahankali kanta kasa Don tasan babanta bayason Tana dadewa waje, ahankali ya Dan Shafa beard dinshi sannan yace

"I was calling you...Bakiyi piçking ba..." 

"Yes dad am sorry..the party was loud..."  Shuru yayi for a moment before saying 

"Daman in fada maki kiyi hiding..." Bai idaba tace

"What happened?.." Ta tambayeshi cikin tashin hankali, ajiyan zuciya ya saki sannan yace

"Spy's sun fadamin anason kidnapping dinki..." Da sauri ta mike daga kan gadon tare da dawowa kusa da dad dinta, 

"Dad... Kidnapping...dad am afraid..." Ta fada kaman zatayi kuka,

"Nima...dear in wani Abu ya sameki ban San yanda zanyi da rayuwa ta ba...you are all I have got...", ya fada cikin muryan damuwa tamkar da gaske yake, kuka Maryam ta farayi Tana cewa

"Dad why would they want to kidnap me?... What have I done...." Ta fada cikin kuka, face dinta ya Shafa tare da goge mata hawaye

"Kinyi sallah?." Ya tambayeta, kanta kasa tace

"Aa..." Abinda ya tsana most about the whole thing kenan, bata dauki Ibada komai ba, in baa fada mata ba sai ta jera wata bata yi sallah. 

"Sorry dad..let me go and pray..." Ta fada Tana mikewa. Har lokacin gabanta bai bar faduwa ba, gani take ko a gida bata tsira ba, she's so scared, alwallah tayi ta fito ta Chanza Kaya tayi sallan asuba.


Fita alhaji yayi ya Kira alhaji Ismail, lokacin alhaji ismail yana zaune office, picking yayi suka gaisa, nan alhaji Mahmoud yake Gaya mashi he wants to see him, da sauri alhaji ismail yace

"Yaushe?.." 

"Zuwa next week..."alhaji Mahmoud ya fada mashi, without wasting of time ko tambayan reasons yace

"Tou shikenan.."3❤💙💜💛💚

Wulankaci dodone.....

💜💚💛❤💙



®zuwairat (ummumaryam)





0⃣3⃣





A week later 



Cikin sati daya alhaji Mahmoud yayi set up na kidnapping din Maryam inda she's lucky Tana escaping da taimakon guards din dad dinta,

"Dad am scared!!!" Shine abinda take fada lokacin da take Jin harbin bundiga a waje, Shafa kanta dad dinta yayi yana 

"Don't worry..babu abinda zai sameki,..I will protect you with my life..." Alhaji Mahmoud ya fada yana Shafa kanta, babu abinda take sai kuka, 

"Dear..." Ya Kira sunan ta 

"Yes daddy..." Ta amsa mashi

"Ina tunanin  yakamata a boyeki..." Da sauri ta daga kanta Tana kallon dad dinta

"Where?.." Ta tambayeshi cikin kuka

"Somewhere safe..." Ya fada mata

"Dad I can't stay far away from you...you know I can't do without you...pls dad let's hide together..." Ta fada cikin matsanacin kuka

"Dear just har a Allah yasa a gano people behind this...banason wani mugun Abu ya sameki...so kiyi hakuri zan sa a boye min ke inda nothing bad will happen to you..."  Ya fada yana rarrashin ta, 

"Pls daddy I can't stay with out you..."

"Don't worry everything will be alright...kinji kou?.." Ahankali ta daga mashi Kai.  Cikin ran alhaji Mahmoud tas saboda farin ciki, now sauran maganar shi da alhaji Ismail, he trust him, yasan zai kula da Maryam tamkar yar shi sannan zai tabbatar ta koyi aladansu yanda ya kamata, 

"Dad...where are you taking me tou..." Ta tambayeshi har lokacin bata bar kuka ba,

"Nigeria..." Da sauri Maryam ta zaro idanuwa 

"Dad why Nigeria...you know I don't like Nigeria..."ta fada Tana kuka sosai

"Ai ba inda kikeso zaa kaiki ba...inda zaki tsira zaa kaiki...inda nobody will disturb you...inda you will be save..." Dad dinta yayi assuring dinta, bata Kara cewa komai ba ta cigaba da kuka, ba komai takewa kuka ba sai rabuwa da dad dinta sannan the most annoying part shine Nigeria zaa kaita

"Dad pls take me to Italy or Spain...am sure I will be save there..."ta fada har lokacin bata bar kuka ba, 

"Pls baby ki manta da luxury...kawai remember your safety.." Ya fada mata, haka ta dinga kuka shi kuma ya biye mata yana rarrashin ta, few hours later tayi developing fever, saida Doctor yazo ya duba ya bata magani ta sha Sannan bacci ya dauketa.


Alhaji Ismail ya shaidawa family dinshi zai tafi USA inda suhail ke ce mashi 

"Pls dad in kaje wajen boss Dinka tell him ya daukeni aiki Chan kasan...I will gladly work for him..." Ya fada lokacin da yake ajiye dad dinshi a aminu Kano airport , banza babanshi yayi dashi, Don he's fed up da halin suhail. 

"Take care of your mom..." Alhaji Ismail ya fadawa suhail 

"Yes I will...and daddy greet yar boss Dinka...Maryam..." Ya fada kaman ya Santa, Don kullum yana tuna yanda duk loads of companies na alhaji Mahmoud is tied to Maryam, at times in yana zaune sai ya dinga tuna Wanda zai auri wannan yarinyan 

"Shegen yana nan kilan ko tuna ta bai taba yi ba amma mu da muke tuna ta ko ganinta kilan bazamu samu daman yi ba..." Ya fada yana tuki while heading back home from the airport 

"Ko kuma kilan suna tare suna soyayya...tab amma knowing such personalities is a privilege...Don ni Ina ganinta Yanzu babu abinda zan fara tambayan ta sai ta samo min aiki a daya daga cikin international company din dad dinta...or nata..." Ya fadawa kanshi, tunawa yayi da yanda yake binta on Instagram da Facebook amma the most annoying part shine baida pictures dinta ko daya, inshort bai taba ganin pics dinta ba. 

"Kilan ma am following the wrong account...Don even masu yankan fingers suna posting pictures balle yan gata..." Ya fada yana dariya, haka nan he was thinking why always talking about Wanda baisan kana existing ba, 

"It's call wahalal da Kai..." Ya fada this time yana dariya sosai har da beating staring din mota

"Maryama.... Enough about you for today ..." Ya fada under his breath. Har ya Kama hanyan unguwan su sai kuma ya juya kan motan yana cewa

"Let me browse this town..."




The following day, da dare alhaji Ismail né zaune a katafaren gidan alhaji Mahmoud, suna zaune kowanne dauke da glass of exotic juice, kallon alhaji Mahmoud alhaji Ismail yayi before saying 

"Sir...Yanzu am here...what can I do for you?..." Ya tambayeshi cikin girmamawa, murmushi alhaji Mahmoud yayi sanna yace

"Rest tukunna...kasha hanya...so ka huta gobe in Allah ya kaini sai kuyi magana..." Alhaji Mahmoud ya fada mashi cikin natsuwa

"Sir am not tired...not when you are involved..sir kasan kaine my life.. You..." Bai idaba alhaji Mahmoud ya daga mashi hannu tare dacewa 

"Pls ka bar flattering Dina haka nan..." Ya fada yana dariya, shima alhaji Ismail dariya yayi yana cewa

"Ai babu laifi Don mutum ya nuna godiyar sa...you have tried for me...dole in dinga Gide maka ..." 

"Naji....duk mu godewa Allah...ai Allah né ya bani ni kuma na Baka...so Allah né abun godewa..." 

"Haka né alhamdullilah..." Inji alhaji Ismail, kallon shi alhaji Mahmoud yayi sannan yace

"Kasan har kullum Ina Jin dadin yanda Baka nuna cewa ni Kanin bayan ka bane...kana respecting Dina despite am you are older than me...sannan ko kadan you are not greedy...hakan yaja na kirakamuyi wata serious magana..." Dadi alhaji Ismail yaji for such wonderful words

"Sir Nima kullum Ina Jin dadin yanda kana da kudi fiye da tunanin Mai karatu amma ko kadan Baka da dagin Kai....kowa naka né....you are simple..." Inji alhaji Ismail, dariya  alhaji Mahmoud yayi sannan yace

"Kai dai ke ganin hakan...some people basu appreciating...wasu ma gani suke kama you are hard on them..." 

"Hmmm that's human for you...daman baa iya masu..." 

"Haka né..." Inji alhaji Mahmoud, hira suka dingayi kaman wasu friends. Har 12am suna tare, alhaji Mahmoud yaji dadin zama dashi sosai, yau not as boss but as normal people not talking about work but talking about life, yanda harkokin kasa suke da ups and downs na Nigeria. Daga karshe kowanne yaje ya kwanta cike da annashuwa. Maryam kam Banda tunani babu abinda take, batasan how long zatayi a Nigeria ba, ganin bakon da dad dinta yayi ya Kara tabbatar mata dacewa dagaske yake Nigeria zaa kaita, 

"For how long?.." Ta tambayi kanta Tana kuka, 

"Until everything settles..." Ta sake bawa kanta amsa still crying, tunawa tayi da sexy clothes dinta, then lifestyle dinta na nan, ganin bacci bai da niyyan daukanta yasa ta mike ta nufi dakin masu yi masu aiki. Daman she's friendly with them, duk su biyar suna bacci amma shiganta ya tada su daga baccin da suke, 

"Are you alright?.." Shine tambayan da suke mata amma ta kasa fada masu abunda ke damu ta cos dad dinta yace it should be a secret wai saboda Ana iya tracking dinta. Shuru kawai tayi Tana kuka, a wannan ranar dukkansu babu wacce tayi bacci. 


The next day bayan kowa yayi breakfast Banda Maryam da tea Kawai Tasha, duk ta Kara ramewa daman ba weight gareta ba, dad dinta kallon ta kawai yake gani yake kaman bai kyauta mata ba amma he's thinking abinda   da niyyan yi is the right thing, yasan she will be greatful some day. Garden suka koma da alhaji Ismail inda alhaji Mahmoud ya cire glasses dinshi Sannan ya fara cewa

"Dan uwa abinda yasa na Kira ka ba Don komai bane Illah in Baka amanar yata..." Bai idaba alhaji Ismail ya zaro eyes yana kallon shi sannan surprise is written all over his face, bayason katse shi amma he's confused,  

"Relax..zan fada maka komai Don I don't feel like hiding anything from you..." Ya fada mashi, drink dake cikin tumbler ya dauka ya kurba while shi kuma alhaji Ismail is very eager yaji abinda alhaji Mahmoud zaice. Ahankali cikin natsuwa alhaji Mahmoud ya fara fadawa alhaji Ismail yanda environment ke nemen bata mashi only daughter dinshi da kuma yanda yake kokarin ganin ta dawo kan hanya madaidaiciya amma to no avail,

"She's my only daughter...ita kadai nakewa wahala...amma wannan western attitude bazai sa mutane na su amfane ta ba...she might end up married to a christain kuma hakan na iya zama ajalina...so pls inason ka maida ta Nigeria, ta zauna gidan ka...ta shiga islamiyya   Sannan I want you to be her guidance ...Don I want her to have all it take before she takes over from me dukda am still young..." Ya fada cikin sanyinmurya, alhaji Ismail is still confused, shuru né ya Dan biyo baya sannan alhaji Ismail yace

"Sir why did you choose me?" Shine tambayan da yayi mashi,

"Saboda na aminta da Kai....you're trustworthy..." Alhaji Mahmoud ya fada mashi babu wasa, idanuwa alhaji Ismail ya lumshe tare da sakin ajiyan zuciya before saying 

"Ita ta amince zata zauna Dani?.." Ya tambayeshi, dariya alhaji Mahmoud yayi yana cewa 

"Ba haka nan ba gaskiya..." Nan ya fada mashi plan da yayi yana dariya, shima alhaji Ismail dariya yayi, 

"So pls zaka rike min ita amana?..." Ya tambayeshi, ahankali alhaji Ismail ya gyada mashi Kai tare dacewa 

"It's an honor sir..so na amince..." Dadi alhaji Mahmoud yaji ya saki murmushi sannan yace

"Thank you for that...so that leads us to the second issue...banason kowa ya gane yata ce....inason ka boye identity dinta...for security purposes...even your family..." Alhaji Mahmoud ya fada ataikace,

"But sir...." Alhaji Ismail ya fara cewa sai alhaji Mahmoud ya katse shi dacewa

"Pls no buts...kawai kayi min alkawarin babu Wanda zaka fadawa she's Mai daughter...form something da zaka fadawa iyalinka...Don if my family knows Tana Nigeria kuma a wani wajen zai jawo matsala...kuma muddin mutum daya ya gane shikenan zaa sani tunda Yanzu we're in social media era..." 

"Amma sir ai kilan wasu sun Santa..." Kai alhaji Mahmoud ya fara girgizawa yana cewa

"Aa...sai dai people that she's together with...Don ko social media bana bari Tana ajiye pics dinta for security reasons...so babu Mai ganewa she's my daughter in ba fada masu akayi ba...Don haka Don Allah..." Bai idaba alhaji Ismail ya katse shi dacewa 

"Habasir... You don't have to beg...kawai matsalan shine zata yarda?.." 

"Wannan ba case bane...she's obedient sannan Tana da tsoro...so nasan yanda zanyi daita...after all nasa ta yarda zata Nigeria so Yanzu ma zan sa ko fita batason yi sai da izinin ka..." Alhaji Mahmoud ya shaida mashi, hira suka Dan taba amma deep down alhaji Ismail yana tunanin aikin daya bashi, yana tunanin me zai fadawa matarshi Don he don't owe suhail any explanation amma he owes his wife, the gal in question bata Kama da yar kauye balle yace yar dangin shi na kauye né.




A bangaren Maryam kam ko compound bata fita, Tana tare da masu aiki su har rana, a karshe ma sai bacci ya dauketa dakinsu, sai wajen 4pm ta farka, bathroom dinsu ta shiga tayi wanka sanna ta tafi dakinta tayishafa, wasu crazy Jean ta saka sai riga Mara hannu, gashin kanta baje a gadon bayanta kaman baturiyar gaske Don haske kawai turawan zasu nuna mata, amma hasken ta yafi nasu kyau Don she's always glowing. Bakin Kofan dakinta ta koma Tana kallon dakinta, kallon manyan teddy bears dinta kawai take sannan ta maido hankalinta kan decorations din dakinta Wanda ko Dan president sai haka, she remember da kanta tayi decorating dakinta dukda dad dinta yayi hiring masu hakan amma she insisted tayi da kanta, da taimakon su ta gyara dakinta to her taste. Ahankali ta koma bakin window Tana kallon farfajiyan gidansu that is like a football field, Ina ta lumshe tare da hugging hannunta a chest dinta, mosti da taji bayanta yasa ta juya ahankali, dad dinta né tsaye wearing a smile da sauri dawo Ta fada jikinshi tare da sakin ajiyan zuciya, face dinta ya daga daga kan kirjinshi yace

"Dear everything is set...wannan mutumin da yazo zaki bishi....he's your new dad...." Bai idaba ta fashe da kuka,

"I don't want a new daddy..." Ta fada cikin kuka, dariya dad dinta yayi yana cewa

"Ai Ina nan...kin ji dadi Yanzu you have two daddys..." Ya fada yana dariya 

,"Don't want new daddy..." Ta fada still crying 

"Ok...naji..." Ya fada mata, hannunta ya rike suka zauna kan kujera sannan yace

"Princess..." Ya kirata

"Yes daddy..." 

"Me yasa zaki tafi Nigeria,.." Ya tambayeta 

"For security reasons..." Ta amsa mashi cikin sanyinmurya 

"Very good..hakan yasa nake son kiyi laying low...kar kije koina...kar kije bank Don Ana iya gane inda kike...duk abinda kike bukata ki tambayeshi zai baki....sannan in kin je kar ki nuna you are my daughter Don baki San Who is watching ba...inshort zaa Chanza maki suna..." Maryam kallon shi kawai take Tana Jin duk abinda yake cewa deep down she's thinking Tana cikin babban matsala

"Kina jina kou?" 

"Yes daddy..." Ta fada Tana goge face dinta

"Sannan inason ki basu respect da kike bani...kar ki kuskure a fadamin kinyi ba daidai ba...kome akaceyi kiyi...in ance ki Bari still ki Bari....and kohmai naki ya koma irin na mutanen da zaki tadda...no fashion life kaman yanda kike anan...be a good gal..kinji kou"

"Yes daddy..." Ta Kara amsa mashi, 

"That's my princess...kinci abinci?..." 

"No dad...am not hungry..." dariya yayi tare da mikewa

"Muje kici...and gaskiya princess zanji dadi sosai in kin fara Hausa...." Ya fada yana Kama mata hannu Don ta mike, Dan murmushi ta saki tare dacewa 

"I...na....ji..." Ta fada daya bayan daya, dariya dad dinta yayi yana cewa 

"Haka zakije kina masu kou..." Ya fada laughing very loud. Suna dawo central palour ya nufi kan dining sai bin shi take a baya, zama yayi ta zauna gefenshi, nan masu aiki suka jera masu abinci Mai rai da lafiya. Few spoons Maryam tayi while dad dinta na kallon ta cikin so da Kauna.



The following day Maryam da alhaji Ismail suka Kama hanyan Nigeria cikin jet din alhaji Mahmoud, ba karamin kuka Maryam Tasha ba Don tamkar zaa kaita mayanka, ko Kaya daya dad dinta bai Bari ta taho dashi ba daga ita sai Arabian gown dake jikinta, har phone da laptop ya hanata daukowa, cewa yayi in sun zo Nigeria alhaji Ismail ya samo mata Dan karamin waya laptop kuma bata bukatar shi.4❤💛💜💙💚

Wulankaci dodone....

💛💚💙💜❤



®zuwairat (ummumaryam)





0⃣4⃣





Tun a hanya Maryam taji gabanta na faduwa, alhaji Ismail na kallon yanda ta susuce kaman ba ita ba

"Daughter..." Ya kirata, 

"Yes sir..." Ta amsa mashi kanta kasa

"I will prefer naam..." Ya fada mata in a loving tune,

"Naam..." Ta dauki correction nan taken 

"Kin kwantar da hankalinki...insha Allah you will love my home kinji kou?.."Alhaji ta gyada mashi Kai tare da goge hawayenta, 

"Yanzu wane suna kikeson a dinga kiranki dashi..." Ya tambayeta, shuru tayi for a while sannan tacel

"Anyone is okay " Ta amsa mashi in a cool tune, 

"No..ya kamata ki zabi Wanda kikeso Don in fada masu shine sunan ki...Sannan duk sanda aka kiraki ki San dake ake...so tell me wanne suna kikeso..." Ya sake tambayanta, 

"Choose for me..." Ta fada mashi kanta kasa

"No na baki dama... You choose...", shuru né ya Dan biyo baya Tana tuna sunaye data sani, after like minti biyar tace

"Fa...ti...ma..." Ta fada voice dinta na rawa, Dan murmushi alhaji Ismail ya saki tare dacewa 

"Nice name Fatima...so always remember Fatima kinji kou?" Ahankali ta daga mashi Kai, sadda Kai kasa tayi while pilot na aikinshi na tukin jirgi. Alhaji Ismail kura mata Ido yayi for a while deep down yana ganin she's gentle compared to wasu yaran zamani Don ko kadan babu rawan kai tattare daita, tunawa yayi da suhail sai ya Dan saki murmushi kawai.  Kafin su Isa Kano alhaji Ismail ya gama plan yanda abubuwan zasu kasance. A aminu Kano airport pilot yayi landing tunda alhaji Mahmoud ya Sanar dasu zuwan su, suna landing Maryam taji new alamari tattare daita Don it feel so weird. Motan cikin airport ya samu ya kaisu daya daga cikin gidanjen dake cikin garin Kano. Suna isa ya kalli Maryam tare dacewa

"Daughter relax kinji kou "?

"Tou..." Ta amsa mashi. Wayanshi ya dauka yayi dailing number Salman after ringing biyu ya dauka tare da sallama, nan alhaji ke fada mashi ya kaiwa baba rabi waya amma kar ya Bari kowa ya sani. Babu musu ya shiga cikin falo da sallama luckily ya shiga babu kowa falo sai murja dake mopping kan stairs, nan ya tambayeta inda baba rabi take Ta amsa mashi da Tana cikin kitchen. Nan ya shiga kitchen din ya kirata waje, mikawa mata wayan yayi. Nan sukayi magana da alhaji Ismail, da Jin yanda suke maganar kasan sirri suke Don ko Salman bai Jin abinda suke cewa, bayan sun gama ta mikawa Salman wayan sannan ta fashe da kukan karya tare da shiga falon. Direct upstairs ta nufa  da hannuwanta bisa kanta sai rusa kuka kawai take su murja sai binta suke a baya suna tambayanta abinda ke damu ta amma ko kadan bata basu amsa sai hawan stairs take hannunta biyu gida kanta, lokacin suhail na kwance kan three sitter sai latsa waya yake suna hira da mom dinshi Don mostly tare suke hira sai indai yana tare dasu sadeeq amma in har his not with them tou his with his mother. Ihun da suke ji ya doso su yasa hajiya dake zaune gaban mirror ta kalli suhail tare dacewa

"Eyeballs kanajin abinda nakeji?.. Ko kunnena né?.." Ta fada Tana sauraron ihun dake kussantosu, suhail daga manyan eyes dinshi yayi tare da cire ear phones dake kunnen shi sannan yace

"Kaman someone is crying kou?" Ya tambayeta 

"Yes..abinda nake ji kenan..." Bata rufe baki ba sukaji muryan baba rabi  Tana kiran 

"Hajiya!... Hajiya!!.." On top of her voice, daura face hajiya tayi tayi tare dacewa 

"Wai waye hakan...kina haukane?"  Ta fada a tsawace, cikin kuka baba rabi tace

"Hajiya nice...inna mu Ta rasu..." Ta fada cikin kuka kaman ba innan da 

Ta dade da rasuwa ba, suhail mikewa yayi zaune tareda saka slippers yana kallon mom dinshi,

"Ki shigo..." Inji Hajiya, ahankali Ta bude kofa ta shiga sai hada zufa take kaman da gaske take, suhail kallon ta yayi from head to toes sannan yace

"Shi yasa kike mana ihu cikin gidan kaman zaki tada mana gidan?.. Sai kace kanki farau rasuwa?... Annabi ma ya rasu anyi hakuri balle wata hagged old woman...after all kina sonta me ya Hana ki zauna ki kula daita?... Rubbish..." Y fada tare da Jan Dan guntun tsoki ya koma ya phi kwanciyan sa, kallon ta hajiya tayi sannan tace

"To ya zaayi...zaki tafi gida né ko daga kukan shikenan?.." Ta tambayeta In i don't care manner, cikin kuka inna rabi tace

"Ai dole in tafi..." Bata idaba hajiya ta daga mata hannu

"I don't want long story..." Ta fada atakaice sannan ta kalli suhail before saying 

"Eyeballs bata transport fare...", kaman bai so ya mike ya bude locker ya dauko kudi kaman five thousand, ta tako zuwa inda take tsaye har zai bata sai ya maida hannun baya yace

"Wai nawa né kudin zuwa garinku?.." Ya tambayeta kaman wata mate dinshi

"Dari bakwai ake kai mutum..." Ta amsa mashi 

"Duka nawa kenan?..." Ya sake tambayanta 

"Duhu daya da Dari hudu..." Kallon kudin hannunshi yayi ya zari dubu uku cikin kudin ya mika mata dubu biyu ahankali baba rabi ta sa hannu Ta amsa daga hannunshi tare dacewa 

"Nagode...", duk mom dinshi Tana kallon shi

"Eyeballs give her all..." Ta fada mashi, kallon ta yayi tare dacewa 

"Mommy why?... Ai the one I gave her is enough...she should manège it..." Ya fada tare da maida sauran cikin locker daya dauko su in the first place. Mom dinshi bata kada cewa komai ba ita kuma baba rabi ta fita. Dakinsu ta shiga ta hada yan kayanta as instructed ta fita su murja suna biye daita sai sannu suke mat kaman da gaske. Har bakin gate Suka raka ta sannan suka koma ciki Don hajiya bata yarda suna fita sai indai ita ta alike su Don cewa take bata kawo su Don su dinga kallon garin Kano ba ta kawo su né Don su dingayi mata aiki. Baba rabi na fita ta taka har bakin titi ta samu a daidaita ta hau Ta fada mashi address da alhaji ya bata. Cikin minti talatin baba rabi ta Isa gidan. Da sallama ta shiga ciki bayan Mai gadi ya bude mata gate. Tana sallama bakin Kofan alhaji ya bude mata kofa, durkusawa tayi zata gaida shi yayi saurin cewa

"Wai Dan Allah baba sau nawa nake fada maki ki daina durkusa min...." Da sauri ta mike Don ko kadan bata son ran alhaji ya bace. Shiga tayi suka gaisa, sai lokacin ta hangi wata kyakyawan yarinya dake zaune kan kujera with her head down, abinda ya fara zo mata shine kilan aure alhaji ya Kara bayason hajiya ta sani, wani irin dadi taji,

"Ki zauna mana..." Alhaji ya fada mata yana nuna mata wani kujera dake kusa Dana Maryam,  ahankali ta zauna sannan Maryam ta daga kanta ta kalli baba rabi tare da gaidata cikin hausan ta da bai fita, da sauri baba rabi ta amsa mata Tana kallon alhaji Ismail for a while sannan ta kauda kanta cikin tunani kala kala Dan gyaran murya alhaji yayi sannan yace 

"Baba wannan itace Fatima...." Ya fada mata ataikace, 

"To...madalla...." Baba rabi ta amsa mashi Tana dauke da murmushi,

"Ya uwa,...inason ki zauna da ita zuwa nan da sati daya...ki kula daita tamkar yanda zaki kula da suhail...sannan inason wannan ya zama Sirri tsakanin mu..."

"Ai alhaji komai ma zaa yi maka...." Ta amsa mashi, mikewa yayi tare da kallon Maryam before saying 

"Fatima zan wuce...." 

"Ok..." Ta amsa mashi  kanta kasa, cikin ranta sai tunanin Ina family dinshi suke daya kawo ta nan gidan, kallon baba rabi yayi sannan yace

"Anjuma zan aiko Salman da abinci sannan zan bashi kudi sai ya kaiki kasuwa ki samo mata atampopi da hijabai....sannan Dan Allah ki dinga tunatar daita in lokacin sallah yayi...in kun shiga kasuwa a samu tailor a bashi Kayan ya dinka mata su..." Ya fada yana kallon baba rabi,

"tou alhaji..." Ta amsa mashi. Fita yayi ya barsu nan. Maryam ji tayi kaman her world have come to an end Don Jin ta take so lonely Don babu waya da zatayi chatting da friends sannan babu wajen zuwa and the most annoying part shine gata a Nigeria. 

"Sannu yan nan" Inji baba rabi, daga eyes dinta tayi tace 

"Yau...wa..." Baba rabi kura mata Ido tayi Tana sauraron yanda take magana, cikin ranta Tana tunanin kilan ba yar kasar bace saboda yanda take amsa mata kaman ba bahushiya ba. Ahankali Maryam ta mike tare da cewa

"Bacci..." Ta fada Tana yi mata alaman kwanciya da hannunta, murmushi baba rabi tayi tare dacewa 

"Bacci.. Zakiyi?.." Da sauri Maryam ta daga mata Kai

"Tou...amma ai baa bacci bayan sallan asar...ki Bari sai bayan sallan ishai..." Ta fada mata ahankali, shuru Maryam tayi not knowing what to say, Don ita ji take babu abinda take bukata kaman ta watsa ruwa ta Dan kwanta, 

"Wanka....and hu...tawa....." Maryam ta  fada mata, 

"Tou...muje in hada maki ruwan wankan..." Ta fada mata Tana mikewa, ahankali Maryam ta girgiza mata Kai tare dacewa 

"Zan...yi...myself..." Dukda baba rabi bata San  maanar myself ba ta gane inda ta dosa

"Tou shikenan..amma dai kar kiyi bacci kinji kou?.."

"Tou..." Ta amsa mata, takawa tayi ta shiga corridor dake da dakunan bacci gida biyu, dakin right hand side dinta ta nufa ta bude taga well dressed bed da. Bed set, bata damu taga Yanda dayan  dakin yake ba ta bude bathroom Don taga how neat it is, luckily taga kaman baa taba amfani dashi ba, shiga tayi ta kunna tap Don gani in da akwai ruwa, gani tayi every thing is okey, tunawa tayi babu sabulu babu soso sannan babu towel amma she have no choice haka ta shiga ta sakarwa kanta ruwa ta fito daure da dogowar rigarta dukda bai ko rufe mata jiki sosai ba amma haka ta dawo daki ta kakkaba zanin gado ta jefa kanta kan gadon ko minti goma batayi ba bacci yayi gaba daita.


Alhaji Ismail na fita ya Kira Salman yana ce mashi ya kawo mashi mota, ba tare da bata lokaci ba Salman yazo ya dauki alhaji cikin ranshi yana tunanin ya akayi baya airport bayan kuma daga abroad yake. Gida ya kaishi inda suhail dake kwance under thatch  sanye da singlet da Jean was surprised, yana ganinshi yayi saurin mikewa zaune, 

"Dad...harka dawo?.." Ya fada sounding so surprised, murmushi dad dinshi ya saki tare dacewa 

"Yes son...ho have you been?.." 

"Alhamdullilah...." Suhail ya fada yana mikewa tsaye tare da Jan Jean dinshi dake Neman kwallewa. Alhaji tsaya kallon shi yayi sannan yace

"Are you out of belt?.." Ya tambayeshi yana kallon yanda yake tafiya Jean din na yawo waist dinshi

"No dad...kawai inason feeling free né...." Ya fAda sannan ya karasa ya amshi bag dake hannun dad dinshi, hanyan part din  alhaji sukayi, bayan sun shiga ciki suhail ya kalli mom dinshi data shigo ciki sannan ya kalli alhaji yace

"Dad ya trip?.."

"Lafiya lau..." 

"Dad ya Maryam...." Ya tambayeshi, kallon shi mom tayi before saying 

"Who is Maryam"

"Ask him..." Inji alhaji, Dan Shafa Kai yayi sannan yace

"Dad yar boss mana...." Ya fada kaman wani Mai kunya

"She's fine..." Ya amsa mashi cikin ranshi yana this days zaka hadu daita, it depends on you ka ja raayinta,

"Pls dad...." Ya bude baki zaiyi magana hajiya tace

"Pls eyeballs ka bar dad ya huta...he's just coming back..." Bai Kara cewa komai ba ya juya ya basu wuri, nan hajiya ta dinga fada wai ya dawo bai fada mata he's on his way ba, hakuri kawai ya bata yana kallon how glowing and beautiful she is. After yayi wanka ya yaci abinci shima ba sosai ba Don hankalinshi na kan Maryam Don yasan bataci Komi ba tunda babu wani Abu naci agidan. Hajiya na zaune kusa dashi ya rasa excuse da zai bata ya fita ya bawa Salman kudi ya sayo mashi abinci, labari take bashi amma he's so absent minded, 

"Bari in aiki Salman...." Ya fada mata yana kokarin mikewa,

"Aiken me zakayi  mashi...."  Hannu yasa a aljihunshi ya Fiddo atm sannan yace

"So nake ya amso min kudi a bank...." Bata Kara cewa komai ba ya fita.  Salman dake zaune kusa da masu gadi suna hira ya hangi alhaji ya nufosu da sauri ya mike shima ya nufeshi. Nan alhaji y mika mashi atm ya fada mashi ya amshi 100k yaje ya sayo abinci Mai rai da lafiya tare da drinks yanda mutane biyu zasuci, sauran kudin ya ajiye. Nan ya fada mashi address da zai Kai abincin.  



Bayan kaman hour guda Salman ya isa gidan, bayan Mai gadi ya bude mashi ya shiga ciki rike da manyan Leda guda biyu, door bell ya latsa few seconds later baba rabi ta fito, he was surprise to see her, gaidata yayi in a respectful way sannan yace ga sako daga alhaji, yana mika mata ledan yana leken dakin ko da akwai wata nan. Kaman ya tambayeta amma yayi shuru ita kuma ta maida kofa ta rufe without caring for the inquisitive look he's wearing.  Bayan ta shiga dakin ta jera abincin kan center carpet sannan ta shiga ciki nan ta hangi Maryam kwance daure da riganta Tana bacci, kaman ta tashe ta sai kuma ta kyaleta. 


Falo ta koma Tana zaman jiranta har magrib bata fito ba, komawa tayi this time ko tunani batayi ba ta tadata daga bacci, a firgice ta farka Don gani yake it's the end of the world Don tunda take baa taba tadata daga bacci ba, murmushi baba rabi ta saki tare dacewa 

"Dazun kinyi min alkawarin bazakiyi bacci ba...amma sai kika kwanta kou?.." Ta fada sounding so friendly, cikin karfin Hali itama Maryam ta saki murmushi tare dacewa 

"Yi...ha...kuri..." Ta fada cikin sanyinmurya, 

"Ba komai...tashi kiyi sallah sai muci abinci..." Babu gardama ta mike daga kan gadon sai hamma take Don ko kadan baccin bai isheta ba. Bathroom ta shiga ta cire riganta ta maida sanna tayi alwallah. Fitowa tayi bata ga kowa ba, lokacin baba rabi ta je tambayan Mai gadi Ina alkibla, bayan ya fada mata ta dawo ta tarda Maryam falo with her eyes closed 

"Kin fito Fatima?.." Ta tambayeta, Sam Maryam ta mance her new name is Fatima, hakan yasa bata ko bude Ido ba har saida baba rabi ta Maimaita same question sanna tayi saurin bude idonta.

"Eh..." Ta amsa mata ciin natsuwa, hijab baba rabi ta mika mata tare da nuna mata kiblah sannan itama ta shiga ciki tayi alwallah. Bayan sun idar da sallah, baba rabi ta kalleta, lokacin ta hada Kai da gwaiwa sai tunanin rayuwa take

"Matso muci abinci..." Ta fada mata, Maryam daga Kai tayi ta kalli abincin da aka jera taga babu abinda zata iyaci sai lean meat da juice. Ahankali ta Matso kusa da abincin suka faraci, bayan kaman minti biyu ta sha juice din, da sauri ta bata fuska Wanda yasa baba rabi tambayanta 

"Da...sugar..too much..." Ta fada mata, dariya baba rabi tayi Tana kallon ta cikin so da Kauna Don Tana da shiga  rai sosai, kaman ta tambayeta daga Ina take da bata iya Hausa ba sai kuma tayi shuru 

"Tou kici abincin..." Ahankali ta girgiza mata Kai. Duk yanda tayi magi ya Don Maryam ta Kara cin abinci ki tayi. Haka dai ta Ci ta koshi ta mikawa Mai gadi sauran ta dawo lokacin Ana kiran sallah ishai, da umarnin ta Maryam tayi sallah isha sannan ta koma ta kwanta full of tunani daga baya bacci yayi gaba daita.






One love💙💛❤💚💜

5💚💙💛❤💜 

Wulankaci dodone........

💙💛❤💚💜




®zuwairat (ummumaryam)




0⃣5⃣




Pls masu yi min flashing su daina if you can't recharge and call me then don't expect me to call you back. Sannan wasu zasu kiraka amma da nayi piçking ko magana basuyi sai su katse, I may not pick unknown number again. So pls don't be offended. Thanks 




The following day bayan alhaji yayi breakfast yayi shirin office, sai sauri yake saboda Maryam har hajiya taso ganewa something is wrong, ko suhail da ya raka shi har bakin mota sai da yace

"Dad are you meeting the president today...." Ya tambayeshi cikin zolaya, banza yayi dashi ya shiga cikin mota Salman yaja su suka bar gidan. Bayan sun Isa office ya Kara mikawa Salman atm tare dacewa 

"Ka koma bank ka amso 100k ...nawa na jiya suka rage?". Ya tambayeshi sounding calm,

"95k.. Sir,,,," ya amsa mashi, 

"Ok then...in ka amso 100k ka hada Dana hannunka zasu zama 195k kou?"

"Yes .." Ya amsa mashi kanshi kasa, 

"Tou ka saya masu abincin breakfast ka Kai masu sai ka jira su gama ka kaisu kasuwa zasuyi siyayya ..." Ciin respect ya amshi atm card din cikin ranshi yana tunanin abubuwa kala kala Don yaji yana using plural that means ba baba rabi kadai bace amma bai gan kowa sanda yaje ba, he lots of questions to ask amma waye shi da zaiyi tambaya, kawai he's happy alhaji yayi trusting dinshi yana nuna mashi abunda ba kowa ya sani ba, not even suhail. Da sauri ya fita yaje ba ka ya amshi kudin sannan yaje breakfast joint ya sayo masu abinci Mai dadi ya Kama hanyan gidan yana tunanin meke faruwa. 


Yana Isa gidan  maigadin gidan ya bude mashi kofa ya Kama hanyan parlor. Lokacin Maryam na zaune tayi relaxing kan kujera idanuwanta lumshe Don yau bata samu bacci yanda takeso ba saboda kiran sallan farko baba rabi ta tadata wai ta tashi tayi sallan nafila kafin a akira asalatu, bayan sallan asuba bata koma ba Don Tana bakin cikin a tadata daga bacci, hakan yasa ta hakura da baccin completely. Door bell da akayi ringing yasa baba rabi dake zaune mikewa, bakin kofa taje ta bude taga Salman tsaya rike da leathers gaisawa sukayi sannan ya mika mata ledan da sauran 180k yana cewa

"Baba ha sako daga alhaji..." Ya fada still yau yana Dan Neman leka dakin amma bai samu daman hakan ba saboda baba rabi ta tare Kofan da kyau, 

"Tou madalla..." Baba rabi ta fada Tana Amsan ledan, har zata juya yace

"Alhaji yace zan kaiku kasuwa...." Ya fada mata in a respectful way, 

"Tou..zaka shigo ka jira mu ko zata tsaya waje?.." Ta tambayeshi, kaman yace zai shigo Don ganin the third party amma sai yace

"Bari in jira ku a mota..." Yana kaiwa nan ya juya ita kuma baba rabi ta maida Kofan ta rufe. 


Bayan sunci breakfast Wanda baba rabi ta cinye almost all saboda yanda Maryam bata wanI damu da abinci sosai ba sannan all this new for babu vegetables yana damunta Don she loves vegetables sosai. Baba rabi ta  fara tattara wurin sai itama Maryam ta taimaka mata, ko kadan baba rabi bata hanata ba, tare suka gyara wurin sannan Maryam ta mike tare dacewa 

"Bacci...zanyi..." Ta fadawa baba rabi,

"Aa diyata...babu zancen bacci...kasuwa zamu...Don haka ki shiryo kizo mu tafi...." Ta in

Umarce ta, idanuwa Maryam ta lumshe sannan ta budesu ta kalli kanta from head to toe Tana son fadawa baba rabi bata da wata shirin tunda tayi wanka kuma bata da wasu Kayan amma ta rasa yanda zata fada mata, few seconds later sai cewa tayi

"gamawa..." Dariya baba rabi tayi sannan tace

"Ba gamawa zaki ce ba....na shirya zakice...." Ta fada Tana dariya, itama Maryam Dan murmushi ta saki tare dacewa 

"Na shir...ya...." 

" tou shikenan...mu je..." Ta fada mata Don itam by da wata shi da zatayi kuk her hijab is handy, da sauri Maryam ta shiga bedroom dinta ta dauko vail dinta ta daura kan gashinta, Tana fitowa baba rabi ta umarce ta data yafa vail din, babu musu ta yafa shi sannan suka fita. 


Ana buda gate Salman ya maida dubanshi kan Kofan, then he meet the shock of his life Wanda ya nuna karara a face dinshi, Maryam yake kallon, bai taba ganin yarinyan data hada komai na kyau a face dinta ba kaman Maryam, tafiyan ta na abun kallo né Don she walks majestically kaman wata saurauniya, har suka Isa bakin Kofan bai sani ba, sai da suka bude mota ya San sun iso,

"Na shiga uku...." Ya fada under his breath, daga Kai yayi yana kallon ta ta mirror lokacin ta shiga cikin motan, 

"Who is this...." Ya tambayi kanshi cikin ranshi,

"Mutum ko aljana..." Ya sake tambayan kanshi, 

"Ya rabbi save my job...." Ya fada cikin ranshi, ganin su shiga har sun rufe mota yasa yaja motan sai kasuwa, amma kafin su Kai ya kusa buge mutum har sau uku har saida baba rabi ta yi mashi magana kan ya kula da hanya sannan ya maida hankali Don bai minti daya bai daga Kai ya kalleta ta mirror ba, ita kuma ko kadan bata damu ta daga ki ta kalleshi ko wani abuba, ita kawai she's depressed. Lokacin da suka isa kasuwa rana ta fito sosai Don irin morning sun din nan né Mai haske, parking lots na kasuwan kwari  Salman yayi parking, baba rabi fita tayi amma Maryam ko alaman fita bata dashi, sai kallon ranar dake walkiya kawai take

"Ki fito mu tafi mana..." Taji baba rabi na fada mata, Kara kallon rana tayi sannan ta nuna shi Tana cewa 

"Ra...na....it's hot...." Ta fada ahankali, Salman kam mutuwan zaune yayi cikin motan saboda muryan da yaji Mai kaman waka,

"Ya zakiyi...ai sai hakuri...ki fito mu tafi kafin ranan ya fara zafi...." Baba rabi ta fada mata, with out choice ta fito daga cikin motan, da sauri shima Salman ya fito yana cewa

"In taho in tayaku daukan Kayan?." Ya fadawa baba rabi, 

"Da ka taimaka..." Ta amsa mashi, bayansu yabi yana tunanin wacece wannan duk da ya San da gani wannan ta fi ajinshi amma he can't stop thinking,tunanin da baba rabi tayi shima yayi wai kilan matar alhaji ce.  Da sauri ya kauda wannan zancen still yana tunanin 

"Who is she?..".


Cikin wata shago suka shiga inda baba rabi ta kalli Maryam before saying 

"Ki sayi atampopi da kike so..." Baba rabi ta fada mata, Maryam tsaya kallon shagon tayi Tana kallon abinda ita da kawayenta suke Kira da weirdos clothes, amma gashi itama zata saka, 

"Ki...saya..." Ta fadawa baba rabi, duk mutanen cikin shagon juyawa sukayi suna kallon ta, 

"Ki zaba....ai ke alhaji yace ayiwa siyayya...Don haka ki saya...." Ta fada mata, tsayuwan tayi bata ce komai ba, Salman na Jin shurun yayi yawa ya fada masu su kawo atampopi da materials masu kyau, sai lokacin Maryam ta daga Kai ta kalleshi for one to two seconds sannan ta kauda kanta, Kaya aka dauko Mai yawa aka ajiyesu gabansu, kallon ta yayi sannan yace

"Select..." Ya fada mata ataikace, Kara kallon shi tayi sannan ta maida duban ta ga tilin shadda, materials da atampopi dake gabansu, har ha Allah babu abinda take so ciki amma she have no choice haka ta zabi 3 daga each sannan ta kalli Salman tace

"I want gowns...like the one am wearing..." Ta fada Tana kallon eyes dinshi without anything, shikam ganin ta zufa mashi idanuwa yasa ya sadda Kai kasa Don bai am da budurwa balle ya koyi kallon mace eyeballs to eyeballs.

"Ok..." Ya amsa mata sannan suka bar shagon da Kayan da suka shiga, suna kan hanya alhaji ya Kira shi Don Jin halin da ake ciki, nan ya ke fada mashi komai shi kuma alhaji yace, a tambayeta ta sayi duk abubuwan amfanin ta.  Yawo sukayi a kausuwa tare da siyan duk abinda take so, ba Dan Tana son abubuwan da take saye ba sai Don bata da choice, nan cikin kasuwa suka mikawa wani tailor yayi mata dinkingowns Don ba iya daura zani tayi ba. Man shafawan ta ta nema amma bata samu ba, kawai  sai tayi settling for so white exclusive cream da sabulun, a gajiye ta  koma gida, Don duk jikinta zafi kawai yake mata. Direct bathroom ta shiga ta sakar wa kanta shower sannan ta dauki gown daya cikin wayanda suka saya ta saka, falo ta dawo ta bude wayan da tasaya  ta saka SIM card dinta ta jona charging.




Bayan sati biyu rayuwa ta sauyawa Maryam sosai Don har ita kanta ta Chanza, tayi pimples saboda man da take shafawa Sam bai amsheta ba, sannan hasken ta ya rage sosai, idanuwanta sun koma ciki Don duk kokarin kula daita da alhaji da baba rabi sukeyiis to no avail saboda ba abinci takeci sosai ba, she feels so lonely sannan bata fita koina, abun da ke Kara tada mata hankali shine dad dinta bai yarda ta dinga kiranshi always ba, ya fake kan security. Amma ba laifi ta Saba da baba sosai sannan babu laifi Hausa na Dan shiganta fiye da da kuma Yanzu sallanta kan lokaci. Duk sanda ta koma gaban mirror ta kalli kanta sai ta fashe da kuka amma baba rabi is always around for her. Kuma zaman datayi daita yasa ta fara  gane traditions na yan arewa saboda always suna kallon arewa24, sanna wakan Adam zango yana bata nishadi sosai Don if she's in the mood har takawa take. Kullum sau uku Salman ke kawo masu abinci amma iyakar shi bakin kofa, gurinshi ya Kara ganin wannan yarinyan just for once but no chance gashi bai iya tambayan baba rabi izinin shiga palour.



A bangaren alhaji ya rasa abinda zai cewa matarshi kafin ya kawo Maryam cikin gidanshi, kullum suna waya da alhaji Mahmoud, sannan ya fada mashi gaskiya alamari and alhaji mahmoud is ok by he's decision. Yau Friday suna zaune da hajiya ya kalleta wearing a smile sannan yace

"My hajiya I think tunda gobe weekend zanje katsina...na kwana biyu ban je ba..." Ya fada mata, Dan bata fuska tayi before saying 

"Kai Baka gajiyawa da zuwa wannan kauyan.." Ta fada sounding irritating,  Dan murmushi ya saki Don in da sabo ya Saba cos har kullum kauye take cewa katsina,

"Mutum ya taba gajiya da tushinshi?... Besides ni wurina it's as beautiful as London..." Ya fada babu alaman fushi tattare dashi, 

"Hmmm...Kai ka sani...amma dai gobe zaka dawo kou?" Ta tambayeshi kaman bata son yayi tafiya, pointed nose dinta yaja before saying 

"Why bazan kwana ba?.." Ya tambayeta sounding naughty kaman wani yaro, itama cikin shagwaba tace

"Because zanyi missing Dinka....." Dariya yayi before saying 

"Banason hajiyata tayi missing dina...so in naje gobe zan dawo goben insha Allah ...."dariya hajiya tayi tare dayi mashi peck a goshi sannan tace

"Thank you my alhaji...".


 Wace gari around 9am sadeeq, aliyu da Yusuf suka zo gidansu suhail, daman mostly weekend suna organizing meeting dinsu na shegantaka a gidan daya daga cikinsu, yau gidan su suhail suke, kowannen su yazo cikin motanshi da shiga ta alfarma. Alhaji na fitowa ya gan motocinsu, wayan suhail ya Kira tare da fada mashi yazo shi da friends dinshi. Nan dukkan su sukaje falon alhaji, kallon su yayi daya bayan daya sanna yace

"Wai Dan Allah meyasa Baku bawa friend dinku shawara?.." Ya tambayesu, suhail daure fuska yayi da ya gane the meeting is about him, sauran sadda Kai kasa sukayi, 

"Pls tell him tobe responsible ko kuma zanyi mashi aure this days...sai ya zaba..." Ya fada masu, 

"Wai dad why did you hate me this much...me nayi na irresponsible?..." Ya fada kaman zai yi kuka, 

"Salla malam keep quiet...." Inji sadeeq 

"Ashe bakasan you are not responsible ba...." Yusuf yayi adding 

"Na dai fada maka..ko ka fara zuwa office ko kayi aure...you can go..." Ya fada masu, afusace suhail ya bar wajen, su sadeeq suna baya sai dariya suke mashi,

"Ango ka sha kamshi...." Inji aliyu, juyawa suhail yayi yabishi da Palm sandals dinshi.


9:40am alhaji ya bar gidan in the name of zashi katsina, suna fita ya fadawa Salman ya kaishi office sannan ya aikeshi yaje chan agidan ya fadawa  Fatima ta shirya anjuma zai zo daukanta. 

 Bayan Salman ya shaidawa baba rabi ita kuma ta fadawa Maryam abinda sukace, ko kadan Maryam bataji dadi ba saboda gani take rabuwa zatayi da baba rabi. Shirya kayanta baba rabi tayi sannan tayi wanka, kafin karfe biyu ta shirya amma alhaji bai zo ba sai karfe biyar na yamma, tare sukazo da Salman. Kafin ya fito sai da yace wa

"Salman do you know why nake aiko ka nan gidan?.." Ahankali Salman dake zaune drivers seat ya girgiza mashi Kai

"Saboda na yarda da Kai...kuma banason kayi disappointing Dina waien yada abinda ka kani..duk da nasan bakasan komai game da abunda ke wakana ba...amma don't say anything to anyone.." 

"Sir you have no problem..." Ya fada mashi, fita yayi ya shiga cikin gidan Salman ya jira shi a mota. 

Kallon Maryam dake zaune wearing a dull look yayi sannan yace

"Daughter how are you...." 

"Lafiya ..." Ta amsa mashi cikin sanyinmurya, Dan murmushi yayi sannan ya sake cewa

"Hope kin shirya..." Kai ta gyada mashi, kallon baba rabi yayi yace

"Mu zamu wuce...ki Bari sai gobe ki dawo gidan...in kuma kinga baki iya kwana ke kadai ki dawo zuwa anjuma...amma pls ki tuna sirrin mu..." Maryam kura mashi Ido tayi, yana kaiwa aya tayi saurin cewa

"Nida...baba....gida daya?"" Ta fada sounding excited, dariya alhaji yayi sannan yace

"Eh...gida daya zaku zauna..." Bai idaba ta daka tsalle Tana nuna murnan ta a fili. Dariya baba rabi ta dingayi cikin ranta Tana farin cikin Fatima likes her. 


Tare suka Kama bag dinta da baba rabi suka saka cikin mota, gidan baba alhaji ya shiga ita kuma ta koma baya. Waving baba rabi kawai take kaman wata yar yarinya, alhaji kallon ta yayi ta mirror yaga ta Chanza dukda kyauwunta na nan wannan hasken da sheken ya ragu sosai,

"Daughter..." Ya kirata yana kallon ta ta mirror, daga Kai tayi ta kalleshi cikin mirror 

"In mun je gida,...duk abinda kikeso don't hesitate to ask kinji kou?.."

"Ok..." Ta amsa mashi kanta kasa. Wannan kalman na daughter ya sa Salman daina tunanin matar shi ce, amma har Yanzu bai bar tambayan kanshi

"Who is she " ba, sannan why alhaji ya kebe ta for a while before taking her to the family house,

"Da akwai wata kasa...amma it's not my business..." Tadata cikin ranshi, in silence suka is a gida, yaga yanda alhaji ya saki ajiyan zuciya kafin ya fita daga cikin motan bayan yayi parking a lot, Maryam dake zaune bayan sai kallon compound din da suka zo take, she's thinking tazo Sabon gidan ta,

"It's beautiful..." Ta fada Tana kallon the two mansions sai kuma one small one, da sauri ta Kara maida dubanta ga small one din Don wasu guys ta gani zaune su hudu, sai  dariya suke amma Banda daya, Dayan Wanda yafi da komai Don tun Tana nesa ta gama ganewa he's handsome and cute

"We're home..." Taji an fada, da sauri ta dawo hankalinta tare da kallon alhaji dake tsaye bakin Kofan, ahankali ta bude kofa ta fito sai taga guys din suma sun nufo inda suke, Salman bude booth yayi ya Fiddo bag dinta, Kara kallon guys din tayi tare da kallon suhail daya daure fuska, suma sauran guys din Dan kallon ta sukayi lokacin da suka karasa wajen alhaji, dukkansu durkusawa sukayi suka gaida shi amma hankalinsu wajenta amma Banda suhail dake cikin fushi Don tunda alhaji yayiwa su sadeeq magana suke yabbing dinshi hakan yasa ko kadan baiji dadin zuwan su na yau ba Don har koransu yayi amma sun San hali, mikewa sukayi alhaji yace

"Hope kunyiwa abokin ku magana?.." 

"Yes dad..." Suka amsa in chorus, suhail kadai né baice komai ba, sai Kara daure face yake, Maryam ta kasa dauke Ido daga kanshi dukda ta lura bai San Tana wajen ba Don Sam babu alaman ya ganta,

"Very good..." Ya fada Sannan ya kalli Maryam yace

"Let's go daughter..." Sai lokacin suhail ya daga Kai ya kalleta, kura mata Ido yayi without blinking kaman yanda sauran abokan shi sukayi, 

"Wacece?.." Aliyu ya radawa suhail cikin kunne bayan alhaji da Maryam sun juya sun bar wajen, Dan baki suhail ya tabe before saying 

"Kilan new house help ce..." Ya fada yana kallon yanda take tafiya kaman gimbiya, dukkansu kallon ta kawai suke kowa da tunanin da yake, Yusuf na Shafa  beard dinshi yace

"Kai I doubt that...wannan ba house gal bace...besides naji dad ya kirata da daughter..." Suhail da ko blinking baiyi saboda yanda Maryam ke tafiya yace

"Koma wacece to me she's an house gal...indai nan zata zaune she will be among my bitches..." Ya fada yana wani shuumin murmushi, hannu aliyu ya luka mashi ga baya har sai da suhail ya saki Kara cikin shagwaba

"Da ganin wannan yarinyan she's classy..so babu wani zancen making her your bitch..." Aliyu ya fada mashi, baki ya tabe 

"Sai in dai ba anan gidan zata zauna ba..." Dukkansu kallon yanda yake magana bai ko kifta Ido sukayi, wuri daya kawai ya kurawa Ido which is bayan Maryam da suke daf da shiga falon hajiya, sai da suka shige da alhaji sannan yayi blinking, dariya suka kwace dashi Yusuf yace

"guy kaman zaka daidaita da wannan Don ban taba ganin ka kurawa yarinya Ido for this long ba..." Bai idaba suhail ya saki tsoki,

"Wannan da face dinta ke da rashes kaman na masu karanbau?... Allah forbid..." Ya fada yana komawa part dinshi hannunshi biyu cikin aljihunshi while su sadeeq na biye dashi sai dariya suke aliyu na cewa

"Ko me wannan banzan ya dauki kanshi?... Nidai kilan na samu matar aure...she looks cute and adorable to me..." Yafada sounding serious' tsoki suhail ya Kara ja tare dacewa

"Your problem..."


Suna shiga falo Salman ya ajiye bag ya juya tare da satan kallon Maryam sannan ya bar falon. Su murja suna kin sallaman alhaji suka fito tare da durkusawa suka gaida shi, kallon su Maryam ta tsaya yi cikin ranta Tana murna 

"Am not going to be lonely after all..." Ta fada cikin ranta while Tana kallon yanmata dake age mate dinta. Bayan sun gama gaisawa da alhaji suka maida duban su ga Maryam dake kallon su Tana murmushi, gaidata sukayi itama ta gaishesu, alhaji kallon murja da asabe yayi sannan yace 

"Ku Kama wannan jakan ku biyoni dashi...." Sanna ya juya ya Maryam yace

"Daughter ki zauna and feel at home...Bari in kirawo new mom dinki..." Ya fada mata sanna ya kama hanyan upstairs su asabe na biye dashi. Falon Maryam ta kurawa Ido taga babu laifi dukda it can never be compared to her personal falo a gidan su na USA, kan wata two sitter ta zauna Tana Kara karewa gidan kallo. Bakin wata kofa alhaji ya nufa ya bude ya umarce su da su ajiye bag din sanna ya koma ya Kama hanyan dakin hajiya, yana bude Kofan kamshin perfumes dinta ya bugi hancin shi, idanuwa ya lumshe tare da ware mata hannu, ahankali ta mike daga bakin gado Ta fada jikinshi 






One love 💙❤💛💜💚

6💙❤💛💚💜

Wulankaci dodone.....

💙💜💛❤💚






® zuwairat (ummumaryam)







0⃣6⃣





Gaisawa sukayi cikin so da Kauna kaman yanda suka Saba Don kurawa da taje bashi at all times yasa duk yanda take misbehaving yake tolerating Don in suna tare she gives him all her time,

"My alhaji muje kayi wanka ka I abinci..I prepare your favorites..kuma da Kaina nayi maka tuwon da miyan..." Ta fada Tana Shafa beard dinshi kaman yau ta fara ganinshi, Dan murmushi yayi sannan ya Kama hannunta yace

"My hajiya ki zauna zamuyi wata magana..." Ba musu ta zauna Tana kallon shi, ahankali yace

"My hajiya nayi maki laifi amma saidai ki yafe min..." Gabanta né yayi mugun faduwa Don hankalinta wajen kishiya ya tafi, yanda ta zaro idanuwa yasa alhaji yin shuru for just one to three seconds before saying 

"Danaje gida naga wata yar cousin Dina..."

Bai idaba hajiya tafara

"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!!! Na shiga uku..." Da sauri alhaji ya rike ta Don yini ta fashe da kuka Tana salati,

"Stop kiji abinda zan ce mana...ba kishiya bace..." Ya fada mata Don yasan inda ta dosa, da sauri ta kura mashi Ido Don gano gaskiyar shi

"Yar cousin Dina na kawo Dan ta zauna damu for a while..." Nan take hajiya ta saki ajiyan zuciya tare da goge hawayenta 

"Amma alhaji ka shiga hakkina..." Dariya yayi tare dacewa 

"Kin dai shiga hakkin kanki..." Itam dariya tayi sannan tace

"Ina yarinyan take,..." 

"Down stairs..."

"Shekarunta nawa?" Ta tambayeshi, shuru yayi kaman Mai tunani sannan yace

"I think bata wuce 18"" idanuwa hajiya ta sake zarowa

"18 fa kace alhaji..ai ta Isa aure...why not a aurar da ita?... Haba alhaji yanda yaran Yanzu basu tsoron su aure tsoho?. Nidai I smell something fishy..." Ta fada cikin jelousy, dariya alhaji yayi tare dacewa 

"Hana my hajiya...don't you trust your Alhaji again?... Kin San ni ba irin wannan mutumin bane...kawai relax..abinda nake son kiyi min shine ki kula daita kaman I

Ke kika haifeta pls..." Ya roke ta, Dan tabe baki tayi tare dacewa 

"Let's see the gal in question...Don ni Ina tsoron yarinyan Yanzu...wai wait a minute..Ina iyayenta?.." Ta tambayeshi, daman yasan zaayi haka Don yasan halin matanshi da kyau and he's ready,

"Ai cousin din nawa ya rasu tun kusan 8 years back...sai yarinyan Tana zaune wurin mom dinta dake jos...so na samu labarin mom dinta Tana son aurar daita ga wani christain a chan jos... Sai nasa a kawota katsina..." Bai idaba tace

"Daman kayi plans tuntuni zaka kawota shine ko ka fadamin kou?.." 

"Sorry my hajiya...I thought bazaki yarda ba..." Da sauri tace

"Why not...abinda ga dakinta wasu ba baa taba kwana cikinshi ba?... And kasan ko masu aiki goma gare ba yawa sukayi ba...so more hands are always welcome..." Ta fada mashi, ya gane inda ta dosa, wato wata yar aiki aka kawo mata, bata San in future indai yarinyan ta rike business kaman ubanta sai sunanta ya fito cikin successful business women a duniya ba, amma Don kar tayi suspecting wani Abu bai ce komai ba kawai murmushi ya saki yana cewa

"Tou ki Kara goge face din kar a gane kinyi kuka..." Ya fada mata yana dariya. Mikewa tayi taje gaban mirror ta dauki tissue ya goge face dinta very neat sannan suka sauko downstairs, suna sauka Maryam dake zaune ta daga kanta, kallo daya rayiwa matan ta gane itace mahaifiyar wannan saurayin data gani dazun, mikewa tayi cikin respect sannan ta durkusa kaman yanda taga su asabe sukayiwa alhaji sannan ta gaidata, surprise look hajiya tayi mata sannan ta maida dubanta ta alhaji tace

"Why take Hausa haka?.." Ta fada sounding irritating 

"Ai I told you a Jos aka raineta..." Sai lokacin ta maida kanta Kaga Maryam tace

"Lafiya...." Ta fada Tana mata wani irin kallon kazanta, Maryam ta gane irin kallon amma sai ta sadda kanta kasa, hajiya bata Kara cewa komai ba sai ta Kama hanyan upstairs, alhaji kallon Maryam yayi yace

"Relax kinji kou?" Ahankali ta daga mashi Kai,

"Taso muje in nuna maki dakinki..." Ahankali ta mike ta bi bayanshi, suna yawa upstairs hajiya da ta kusa Kai karshen stairs din ta juyo ta kallesu tare dacewa 

"Ina zaka kaita kuma?..." Ta tambayeshi Tana kallon shi,

"Dakinta...." Ya amsa mata, Dan bata fuska tayi before saying 

"Haba alhaji...we have many rooms a downstairs....why zaka kawota har upstairs..you know it's all mine..." Ta fada Tana saukowa, ran alhaji ya bace amma ko kadan bayason rigiman ta sannan if he insist sai ta zauna upstairs Don yasan she may understand, 

"Ke ki biyoni...." Hajiya ta fadawa Maryam Tana saukowa, Maryam kallon alhaji tayi tare da sakin murmushi sannan ta bi bayan hajiya datayi hanyan dakin su murja, dakin ta bude tace 

"Kina iya zama dasu or kuma..." Ta rufe Kofan ta bude Kofan dake kusa dashi Sannan tacigaba dacewa 

"You can stay here..." Ta fada mata ataikace Tana kallon innocent face dinta, Dan murmushi Maryam ta saki sannan tace

"Zan zauna....chan...." Ta nuna dakin su murja, duk alhaji na tsaye yana kallon su,ka fada hajiya ta daga tare dacewa 

"Your choice..." Tana kaiwa nan ta juya, shima alhaji juyawa yayi ya Kama hanyan waje da alaman part dinshi zai koma, ahankali hajiya ta taka ta bi bayanshi. Bayan sun isa part dinshi ya juya yana kallon ta fuskan shi daure yace

"Wai me yasa kike nunawa duniya ban isa da ke ba?... Meyesa kike nunawa duniya ban isa da gidana ba?..." Ya fada sounding very bitter, cikin surprise hajiya tace

"Yanzu my alhaji Don wannan yarinyan kake wannan  maganan cikin bacin rai?.." Hannun ya daga mata tare dacewa

"Stop that...ba Don yarinyan ba amma ko na waye bai kamata ki nuna ban Ida dake ba...Yanzu yarinyan tan iya fadawa family ke ce kike controlling gidan...what sort of thing is that?.." Ya fada yana juya mata baya, rungume shi tayi ta baya tare dacewa 

"Am sorry my alhaji...amma ya kamata ta zauna da mate dinta...da kuma class dinta...." Ta karasa maganar in a low voice, baki alhaji ya tabe yana tunanin 

"Wannan yarinyan is more expensive fiye da tunanin ki..." Ya fada cikin ranshi, sannan yace

"Ke always matsalan ki class...bakisan talaka na iya zama Mai kudi ba shi kuma Mai kudi talaka ba...what goes up will surely come down...kullum Ina cikin fada maki Mai kudi baifi talaka da komai ba muddin bai tsoron Allah..." Bai idaba ta Dan tabe baki

"My alhaji naji..Yanzu dai muje Inyi fixing ruwan wankan ka...." Ta fada Tana wuce shi Don shiga bathroom Don ta San in zata tsaya bai daina maganar. Bayanta yabi da kallon tare da zama kan sofa yana aduan Allah yasa kar hajiya tayi abinda zaisa Maryam taga bakinta.


Maryam kallon dakin tayi Don lokacin su murja suna kitchen suna hadawa suhail da abokan shi dinner Don kaidarsu sai sunyi dinner sunyi sallan ishai sannan suke tafiya. Four student foam dake kasa ta kalla Tana tunanin Yanzu itama kan student foam zata dinga kwana, Dan murmushi ta saki before saying 

"Anything for my life to be save..." Ta fada kasan makoshinta, tsaya kallon bags dinsu tayi for a while sannan ta shiga dakin, direct bathroom ta shiga taga ba laifi it's neat, fitowa tayi ta Kara kallon dakin for few more seconds sannan ta fice ta koma falo. 

Tana fita falo suhail na shiga falon, har yayi hanyan shiga kitchen ya ji kaman Ana kallon shi, ita kam Maryam gani take tunda take bata taba ganin cute guy kaman suhail ba, Tana ganin mutane daban daban amma suhail is so cute, abinka da rainon turawa bata ko kauda Kai ba lokacin daya juyo yana kallon ta, suhail ganin yanda take kallon shi yasa ya juya ya nufi I da take tsaye, har lokacin ko blinking batayi ba, sai da yazo daf daita sannan ya tsaya ita kuma ta daga eyes dinta ta zuba cikin nashi

"Kan uban nan!!!..." Ya fada cikin tsawa Wanda yasa Maryam firgita

"Ke karuwar inace kina kallon mutum baki kauda Ido?..." Ya fada yana kallon ta from head to toe sannan ya Dan jingina Kai yana kallon bayanta, Maryam sadda Kai kasa tayi cikin ranta Tana Maimaita karuwa, bata taba Jin word din ba but it doesn't sound right, 

"Da kinkara kallona da wannan idanuwa sai na cire su..." Ya fada sounding very harsh,  Maryam dai couldn't believe her ears Don sun Saba ita da friends dinta suga cute guys su ce mashi 

"You're cute..." Shi kuma ya amsa da 

Thanks ladies and you look lovely too..." Ya fada masu haka ya wucewan shi babu wata matsala amma shine because ta kalleshi yake kiranta da sunan da bata sani ba, 

"Stinky fellow..." Ya fada mata, da sauri ta daga Kai ta kalleshi Don kaman ta nutse take ji, yau itace stinky fellow, ita dake amfani da designer perfumes, yanda ta kalleshi yasa yaga kaman taji abinda yace Don kallon irin yanmatan nan da ga kyau amma ba ilimin kirki yake mata 

"What!.. Ko kinji abinda nace né." Ya tambayeta yana yi aya irritating look, ahankali ta sadda Kai kasa Don sai taga bata taba ganin mutum Wanda ta tsana lokaci guda kaman shi ba, nan take tayiwa kanta alkawarin ko kallon inda yake bazata karayi ba. Barin inda take tsaye yayi ya Dan taka zuwa kusa da kitchen ya juya yaga kanta kasa amma he can see yanda eyes dinta suka chanza, baki ya tabe sannan yace 

"Fall in!!!..." Ya fada as usual, kan Maryam kasa amma she couldn't believe abinda take gani, Don su murja ta gani sun fito da gudu har jikinsu na rawa, kallon yanda each and everyone ke  shaking tayi sannan ta kalli yanda yake kallon su Fuskanshi kaman bai taba dariya ba 

"Is our food ready?..." Ya fada cikin  matsanacin fada, cikin rawan murya asabe tace

"Sauran kadan...." Disgusting look yayi mata sannan yace

"Filthy bitches...." Idanuwa Maryam ta zaro saboda word dataji ya Kira su daita

"If I come back here for the third time abincin bai dahu ba sai na sa ku gaba kun cinye tas...kuma da zafi...so kuyi sauri ku kawo abincin...." Yana kaiwa nan ya juya da niyyan barin falon, Maryam that's stoned da attitude din angel din data gani taji Ana cewa

"Next time da kinji fall in make sure kin shiga...or you will get what's coming to you...." Yayi directing maganan shi to Maryam sannan ya bar wajen, da gudu su murja suka koma kitchen Don sun San da gaske yake yana iya sa su cinye abincin duk zafintakuma babu Mai     Hanawa  tunda alhaji dake Hanawa ba kullum yake ganin abinda akeyi a part din hajiya ba, inshort mostly bai sanin abinda ke faruwa kuma hajiya da shi suhail sun gargadesu kan  dauka wata maganan gidan daga inda kayi ta. Maryam kallon Kofan da suhail yabi ya fita ta tsaya yi, she couldn't just believe it, ahankali take takawa ta shiga kitchen din su murja juyawa sukayi sauka kalleta tare da sakar mata murmushi Wanda she couldn't smile back, sannan suka maida hankalin su kan abinda suke, karasawa tayi cikin kitchen sannan tace

"Pls...me..ne...ne...karuwa?..." Ta tambayesu cikin slant Hausa language dinta Wanda yasa su murja kallon junansu, ahankali binto tace

"Yana nufin Mai bin maza..." Ta fada mata Kai tsaye, Maryam ji tayi her body is shaking Don at that moment ji tayi kaman ta Kira dad dinta ya nema mata wani wajen zama amma sai ta tuna da warning din shi sanna sai ta tuna da niceness na alhaji Ismail Don gani take fadawa dad dinta will make him hate alhaji Ismail, hakan yasa ta janye zancen fadawa dad dinta amma one thing she promised herself shine babu abinda zaisa ta shiga harkan shi, she will stay far away daga gareshi, sannan tayiwa kanta alkawarin ko word daya bazai taba hadata dashi ba. And one thing about Maryam shine she mostly keep to her words. 

"Kiyi hakuri...duk abinda yake ce mana kenan....amma babu abinda ya rage mana..." Inji asabe, hankali Maryam ta daga red eyes dinta ta kalleta tare da sakin murmushi karfi Hali. Gefe daya ta koma ta zauna Tana kallon yanda suke hada abincin cikin sauri, after kaman minti 15 suka gama suka Kai masu a part din suhail, lokaci Ana kiran sallan magrib, zagi suhail yabi su dashi Wanda yasa su sadeeq Jin haushinshi amma koma jikinshi. 


Bayan sallan ishai abokan shi suka tafi, zama yayi kafan  shi daya kan daya yana maida numfashi ahankali tare da lumshe eyes, ahankali ya daga Ido yana kalli wani latest American movie Mai suna the rich Italians, ganin yanda ake da kudi cikin film din yasa ya fara tunanin yar boss din baban shi, abinda ke bashi mamaki shine yanda ko sau daya bai taba ganinta ba amma he always think about her, at times in ya zauna sai yace in ba Don kar a ce ya fara hauka ba da sai yace in ba Maryam ba bai taba yin aure amma yasan hakan ba karamin zagi zai janyo mashi wajen dad dinshi ba sannan dariya wajen abokan shi, remote ya dauka ya kashe kallon tare da sakin short tsoki ya juya Kai one side, yarinyan main palour din su ta fado mashi a rai, tsoki ya sake ja tare dacewa 

"Mayya sai dai kici kanki...." Ya fada yana mikewa, kallon plates da food warmers dake kan dining dinshi yayi yana fita daga part dinshi. Hasken compound din kaman rana, cikin kasaita ya taka ya shiga falon mom dinshi, gani yayi ba kowa falo, ko wasting of time baiyi ba ya nufi dakin masu aiki, ba knocking ya bude kaman yanda ya sabayi at times, asabe dake daure da towel tayi saurin durkusawa kasa while Maryam dake kwance kan katifan da murja tace suyi sharing tayi saurin duba Kofan saboda yanda aka budeta da karfi, kallon asabe data durkusa kasa yayi tare da tsakin tsoki before saying 

"Ko uban me zan kalla da har kike wani nonnoke Kai?... Oho...." Ya fada face dinshi yamutse kaman Mai kyaman wani abu, ya Kara dacewa 

"Ni kukeson in kwace plates kou?..." Ya daka masu tsawa,  da sauri suka amsa mashi da

"Aa..." Amma Banda Maryam da tunda ya bude kofa ta ya shine ta juya kwanciyan ta tare da bawa Kofan baya, kallon Maryam yayi kaman zai wata magana amma sai yayi shuru 

"It's too early for that..." Ya fada kasan makoshinshi, sannan yayi banging Kofan ya bar wajen murja tayi saurin mikewa taje part dinshi ta dauko plates din sannan ta dawo ta kwanta, Maryam kam kasa bacci tayi Tana tunanin wannan awful guy din Don tamkar dodo take ganinshi.  Upstairs suhail ya hau ya tarda mom dinshi ta shirya cikin Kayan bacci amma ta daura wrapper sama, kallon shi tayi lokacin da yake zama in doguwar kujera tare dacewa 

"Eyeballs bakayi bacci ba?..."

"Yes mom..just tired..." Ya fada yana hamma tare da Dora legs dinshi kan kujeran, Dan dariya hajiya tayi cikin son da kaunar danta tace

"Eyeballs kaman wasa dai you're lazy..,duk yau ko fita bakayi ba amma sai kukan gajiya kake...." Dan dariya shima yayi yana Shafa gashin kanshi tare dacewa 

"Ai momcy ko zama cikin su sadeeq is tiring...su sa mutum magana..." Ya fada yana relaxing kan kujeran tare da rufe eyes kaman Mai Jin bacci, 

"Sun tafi kou?.." Hajiya ta tambayeshi 

"Yes mommy..."

"Hope sun ci abinci kafin su tafi?"

"Yes .." Ya sake amsa mata idanwanshi biyu lumshe sai hand dinshi daya kan goshinshi, agogon dake hannunshi sai walkiya kawai take, 

"Mommy am so tired da abinda dad yake min gidan nan...he hates me so much..." Suhail ya fada yana tunanin yanda dad yayi downgrading dinshi gaban su sadeeq, 

"What did he do again?..." Ta tambayeshi Tana kallon shi tare da maida dukkan hankalinta kanshi

"Wai he's Insisting ko in fara aiki kaman friends Dina ko kuma yayi min aure...ni wallahi mom banga yarinyan data yi min ba kuma am not ready to work now..." Ya fada cikin shagwaba kaman Dan three years, hajiya sai kallon shi take cikin Kauna Don tamkar ta maida danta cikin ciki take ji saboda so, at times Tana Jin son da takewa suhail yafi son da takewa kanta, gani take she can't survive without him, kwantar da murya tayi sannan tace

"Eyeballs gaskiya I will not hide this from you...Nima I want you to start working..." Da sauri suhail ya kalleta, 

"Yes...am serious..." Ta fada calmly, 

"Yanzu mom ke da dad zamuyi teaming against ni kadai?..." Ya fada kaman zaiyi kuka, da sauri hajiya ta Baro inda take zaune ta dawo kusa dashi legs dinshi dake kan kujeran ta cire ta maida kan laps dinta sannan tace 

"Baby am not teaming against you...banason baki na tabamin Kai...so pls ka fara aiki kafin ka samu Wanda kake so...pls sweetest..." Ta fada Tana rike da Palm dinshi biyu cikin hannunta, suhail sai turo baki yake,

"Mom pls I don't want to work in Nigeria...ni nafison aiki abroad...na fadawa dad ya fadawa boss dinshi ya nema min aiki a abroad amma Yaki fada mashi...indai in na fara aiki dariya friends Dina zasuyi min...." Ya fada Kaman zaiyi kuka, mom dinshi shuru tayi Tana kallon shi bata ce komai ba,

"Ni dai help me talk to dad...pls momcy...." Ya fada kaman zaiyi kuka, nan take ya juyawa mom dinshi raayinta

"Ok son....naji...I will talk to him again...dukda nasan it's a lost cause I will still try it for you my love..." Tayi assuring dinshi, Dan murmushi ya saki tare da mikewa zaune,

"Thanks momcy..." Ya fada yana mikewa tsaye, kaman zai tafi sai kuma yace

"Momcy wai wacece dazun dad ya zo daita?..." Ya tambayeta, nan hajiya ta fada mashi exactly abinda alhaji ya fada mata, baki ya tabe yana cewa

"Ashe rainon jos ce...shiyasa dazun ta kura min Ido babu ko kiftawa....kaman wata mayya " 

"What!!!.. To duk ranar da ta Kara ka kifa mata Mari...banason a shanye mani Kai..." Ta fada babu wasa

"Trust me mom...ai ban daukan raini...." Ya fada ya Kara dacewa 

"Good night momcy..." 

"Good night my eyeballs...." Fita yayi daga dakin ya Kama hanyan part dinshi.





❤💙💜💛💚one love.....

8💙❤💜💛💚

Wulakanci dodone...

💚💜💛💙❤







® zuwairat (ummumaryam)






0⃣8⃣




Dearies dont forget to be voting ohhh, wai NA CUCE ta have over 220k views amma ko 20k vote ban samu ba😥😥😢😢, ni inyi wahala amma you can't take just a second kuyi voting 😭😭😭. Nidai Yanzu iya voting dinku iya samun new post 😾. 





Suhail fita yayi daga gida Don daman yana zuwa football field da su sadeeq ranar Sunday, a chan aliyu ke ta bayanshi Ina bakuwar gidansu, baki ya tabe sannan yace

"Inside my trousers..." Ya amsa mashi yana Shan bottle water, tsoki aliyu yaja tare da juyawa suhail baya, gabanshi suhail ya zaga sannan ya daga gaban gajeran wandon daya saka yace

"Kalli she's in side..." Banza aliyu yayi dashi.

"Ni dai pls kar kayi maltreating wannan yarinyan, she looks nice...." Yusuf ya fada mashi, suhail dake sanye da jessy na bacelona ya rufe marfin ruwan ya ajiye cikin bag daya taho dashi sannan ya tsaya kaman Mai tunanin wani abu, Kawai sai ya saki dariya, kallon shi sukayi ya fara cewa

"Allah wannan yarinyan muguwar yar rainin wayauce...wai ta hada min tea sai ta tuka min madara kaman tuwo...can you believe that?.." Ya fada fuskan shi dauke da murmushin da in ba friends din ba babu Mai ganinta, dariya sukayi Banda aliyu 

"Maybe haka ta Saba hada tea..." Inji sadeeq, baki suhail ya tabe tare dacewa

"Babu wani...kawai rainin hankali né...wallahi ni dai haka nan I feel like in kamata in dinga duka...Allah what I feel for her banajin shi kan sauran yan aikin...." Ya fada Fuskanshi babu walwala,

"Wai yar aiki ce?.." Aliyu ya tambayeshi 

"Yes...to me..."ya amsa mashi atakaice, 

"Amma seriously ka bar zaluntar wannan yarinyan...there's something about her...she look unique...Allah nidai yarinyan nan tayi min...if I have chance Ina iya aurenta..." Inji Yusuf, suhail kura mashi Ido yayi sannan ya kauda Kai without saying a word,Dan murmushi ya Kara saki yana cewa

"Allah dukda she's annoying ta iya ban dariya...yau da safe da gudu ta bar part Dina...." Ya fada wearing a killer smile,

"Me tayi a part Dinka?... Kar dai ka zama Dan iska..." Yusuf ya fada sounding surprised,

"Allah forbid...ko ina Dan iska ai duk wannan gidan babu mate Dina...dukkan su are under me..." 

"Enough about her..." Duk maganar da suhail keyi yana batawa aliyu rai amma yayi shuru kaman bai damu ba,  kawai he has his plans

"Ni daga nan gidanku zani..." Inji aliyu, 

"You're welcome..." Suhail ya fada mashi.



Da yamma alhaji ya shiga part din hajiya da Kaya cikin Leda, lokacin Maryam Tana dakin da aka ware mata tayi kwance Tana kallon ceiling idanuwanta lumshe amma ba bacci take ba, bude kofa da akayi yasa ta bude eyes, murja tagani 

"Alhaji yace kizo..." Ta fada mata, da sauri ta mike Don tamkar dad dinta ta dauke shi, falo ta tarda shi tare da hajiya, ahankali ta durkusa ta gaidasu Don duk ranar bata gan hajiya ba, alhaji kura mata Ido yayi yaga ta Chanza in just an instance. Alhaji né kawai ya amsa gaisuwanta while hajiya Tana kallon alhaji domin taga irin kallon da yake mata

"Daughter meke damunki?..." Dan murmushin karfin Hali ta saki tare dacewa 

"Babu...komai...." Ta amsa mashi kanta kasa,

"Daughter tell me meke damunki...ai ba haka kike jiya ba..." Ya fada kaman yana magana da yarshi ta cikinshi Amman hajiya babu abinda take sai kallon su sannan deep down she's boiling, 

"Nothing sir..." Ta amsa mashi still, Leda dake kusa dashi ya mika mata,

"Ga Kayan islamiyya...zaki fara daga gobe..." Ya shaida  Mata, ahankali ta taka ta dauki ledan,

"Na...go..de..." Ta fada sannan bar su nan, alhaji shuru yayi yana tunanin abinda ya sameta Don she was lively kafin ya kawota nan gidan, alhaji mikewa yayi ya fita daga falon hajiya ta raka shi har bakin gate dayake a kasa zai fita kasancewan da akwai majilisa da suke zama nan unguwan duk ranar lahadi. Hajiya na komawa ciki alhaji ya dauki waya ya Kira Salman, nan ya shaida mashi ya kirawo baba rabi amma kar ya Bari hajiya ta sani. Without wasting of time ya shiga falo luckily hajiya ta hau upstairs, nan ya Kira baba rabi ta sami alhaji waje. 

"Dan Allah baba...inason ki kulamin da yarinyan nan...amana ce aka bani...Dan Allah ki dinga kula da duk halin da take ciki...duk abinda akayi mata ki dinga fada min....kuma ki dinga tambayan ta abinda take bukata...kuma Dan Allah a dingayi mata komai...kar a barta tayi komai...zan bawa Salman kudi ya baki ki ajiye wajenki...duk abinda ta nuna Tana da bukatar sa sai ki saya mata Dan Allah...." Sai da ya Kai aya sannan baba rabi tace

"Shikenan alhaji...in Allah ya yarda zaayi yanda kakeso...kar ka samu damuwa..." Ta fada mashi cikin respect 

"tou nagode...".  Ya fada sannan ya wuce ya tafi majalisar su ita kuma baba rabi ta koma cikin gidan.


5:30 suhail da aliyu suka dawo gidan kowanne cikin motanshi, parking sukayi sannan suka shiga part din suhail. Wanka kowanne su yayi suka Chanza Kaya sannan suka fita zuwa main falo, aliyu zama yayi falo yana kalle2 while shi kuma suhail ya hau upstairs wajen mom dinshi, yana shiga ta ware mashi hannu ya fada jikinta kaman wani karamin yaro sai shagwaba kawai yake, 

"Eyeballs I miss you..." Ta fada Tana Shafa kanshi,

"Miss you too mom.,.tare muke da aliyu...he's downstairs..." 

"Ok..ka gaidashi...kasa a hada maku abinci..."

"Ok.." Ya fada yana mikewa daga jikinta, fita yayi tayi bayanshi da kallon so da Kauna. Downstairs ya koma yana cewa

"Mom tace I gaishe ka..." Ya fadawa aliyu yana zama, bayan yayi relaxing yace

"Fall in..." Nan take baba rabi da sauran yan gidan suka bayyana, aliyu daga Kai yayi ya kalli suhail tare da Dan girgiza Kai,

"Guy me zaa hada maka..." Suhail ya tambayi aliyu, harara aliyu ya Galla mashi tare da maida kanshi gefe, tsoki suhail yaja sannan ya juya ya masu aiki, kallon su yayi yaga babu Maryam 

"This gal is stubborn..." Ya fada before saying 

"Kirawo Dayan..." Ya fada ataikace, da sauri binto ta bar wajen, dakin Maryam ta shiga ta bude kofa, Maryam Tana zaune da wayanta hannunta, 

"Kizo..." Binto ta dada mata,  gabanta né ya fadi, tasan suhail né, jiki ba kwari ta biyo bayan binto, sai taka skirt dinta kawai take saboda tsawonta da kuma rashin sabo, aliyu daga Kai yayi ya kalleta, she looks so gorgeous to him, shima suhail daga Kai yayi ya kalleta na second biyu ya dauke Kai, 

"Ke bana Gaya maki in kinji fall in kiyi joining dinsu ba?..." Ya fada afusace, aliyu daure fuska yayi kaman bai tab dariya ba ya mike, sai da ya juya inda Maryam yake ya saki murmushi, 

"Sister....ya kike...ni na aika a kiraki...am aliyu kefa..." Ya fada sounding so polite, Dan murmushi ta saki Wanda ya Dan bayyanar da kyauwunta, suhail was so pissed off, ahankali ta mika mashi hannu tare dacewa

"Am..ma...Fatima...." Ta fada kaman wata baturiya, suhail was so stunned by her voice like wise  aliyu, hannu data miko mashi ya kalla, shima suhail kallon yanda tayi staighting hannunta Don musabaha dashi yayi, su murja da baba rabi couldn't believe their eyes, ganin aliyu bai mika mata hannu ba yasa ta sauke hannunta tare da sadda Kai kasa. 

"Dalla ku wuce ku hadawa mutane dinner..." Suhail ya dakawa masu aiki tsawa, da sauri suka bar wajen suka koma kitchen, a fusace ya bar falon kaman zai tashi sama, gaisawa sukayi sama2, so yayi tayi mashi introducing kanta amma sai tayi shuru saboda batason fadin abinda zai tona mata asiri. 

"Can we be friends?.." Shine tambayan da aliyu yayi mata, ahankali ta daga mashi Kai,

"Then let's exchange phone numbers..." Ya fada yana mika mata wayanshi Domin ta saka mashi number dinta, amsa tayi yana kallon yanda take typing numbers da sauri da alaman she's use to it, bayan tagama ta mika mashi, yana kallon numbers din yaga bana Nigeria bane, surprise look yayi mata tare dacewa 

"Wannan is abroad number..." Ya fada mata, idanuwa ta zaro tayi saurin Amsan wayan ta goge ta saka mashi na nan, Sam ta mance da wannan Sabon number Don ta Saba da number ta da take amfani sashi tun bata Kai 8 years ba Don ko idanuwanta rufe suke Tana iya typing dinshi. Waya ta Kara mika mashi while shi kuma aliyu yana tunanin wannan yarinyan is not from Nigeria, daman aliyu is very smart Don shi bai tsaya bata lokaci kafin ya gane gaskiya 

"Pls daga Ina kike?..." Ya tambayeta calmly, sunan garin da alhaji ya fada wata ta ambata 

"Jos..." Ahankali aliyu girgiza ya girgiza mata Kai,

"Ladies don't lie...at least not a unique lady like you...so pls tell me daga Ina kike...I am really into you..." Ya fada mata, Dan murmushi ta saki, 

"Gas...ki...ya..." Ta amsa mashi tana counting words din, ba Don ya yarda ba ya sakar mata murmushi tare da cewa

"Don't mind my stupid friend...he's nice but selfish..." Aliyu ya fada mata, murmushi kawai ta saki, bayan kaman minti biyar Maryam tace

"Zan...tafi...." 

"Tou sai na sake dawowa..." Ya fada mata yana mikewa daga inda yake zaune. Ahankali ta girgiza mashi Kai

"Pls don't come back...for me..." Idanuwa aliyu ya zaro yana sauraron yanda take magana Ina unique way, 

"Ai sai dai ki dinga dukana but I will come for you always...." Maryam bata Kara cewa komai ba ta juya ta bar wajen, shima bayanta ya bi ya Kama hanyan waje. Daga nesa ya hangi suhail dake zaune bayan mota yana huci, suhail bai taba ji ranshi ya bace game da aliyu ba sai yau, he feels so angry beyond words, bai San takamemen abinda yake bashi haushinshi ba amma ko word daya baison ya hadashi da aliyu, yana ganin aliyu ya nufo inda yake zaune ya sauka daga bayan mota ya nufo shi kawai sai ya wuce shi without saying a word, surprise look aliyu yabishi dashi, shima juyawa yayi yabishi har part dinshi, suhail na shiga kawai ya jefa kanshi kan sofa, aliyu na shiga yace

"Guy meye haka?.." Aliyu ya tambayeshi sounding harsh, suhail daga red eyes dinshi yayi ya kalleshi ya kuma sauke su yana Kara daure fuska, baki aliyu ya tabe ya zauna kusa dashi yana cewa

"Guy I just find out something about that girl..." Bai idaba suhail ya juyo a fusace yace

"From today henceforth..kar ka Kara disgani gaban workers din gidan nan...in fact ba workers din gidan nan Kai ba anywhere at all..." 

"Wai wane irin magana kake haka...in dai kana son wannan yarinyan you better say it..Don if I start there is no going back..." Wani irin tsoki suhail yaja ya mike ya shige bedroom dinshi ya barshi nan zaune. Shima aliyu tsokin ya ja ya juya ya bar falon. 

Suhail kwanciya yayi ya rada abinda ke mashi dadi sai kumbura yake yana batsewa shi kadai, duk juyin da zaiyi sai ya saki tsaki. Lokacin sallan magrib yaje yayi ya dawo ya shiga main part. Hanyan upstairs yayi sai kuma ya dawo falo, baki ya bude zai yi magana sai kuma ya fasa.  Haka ya karasa zamanshi ya koma bai Kira a bashi abinci ba. 


Maryam kam samun baba rabi cikin gidan Yanzu yasa taji dadi sosai, dakin masu aiki ta shiga suka sha labari dukda yawanshi sai dai ta saurara abinda suke cewa tayi dariya, sai wajen 10 na dare taje ta kwanta. 


The following day same thing da ya faru jiya ya sake faruwa, asabe taje gyarawa suhail daki ya korata wai ta Kira Maryam, Tana cikin bacci aka tadata taje tayi mashi aiki, yau ma bata gaidashi ba, kyaleta yayi  sai da ta gama sannan tazo wucewa gabanshi, har lokacin yana zaune falo, kawai sai ya samata kafa ta fadi, da sauri ta mike zata tashi galla mata harara

"Baki iya gaisuwa ba kou?.." Ya fada Fuskanshi kaman bai taba dariya ba, shuru tayi cikin ranta tan kome zai faru bazan taba bude bakina in gaidaka ba,

"Baki iya gaisuwa ba?.." Ya sake repeating question din, still banza tayi dashi, 

"Come here..." Ya daka mata tsawa, jikinta na rawa ta karaso inda yake, mikewa yayi ya Kama kunnenta, 

"Kunnen kanshi gareki kou..." Ya fada yana Kama kunenta da karfi, hannuwanta ta fara yarfawa Tana fashewa da kuka, bakinta ya buge tare dacewa 

"Shush..." Da sauri ta Dora hannunta kan bakinta hawaye na zuba,

"Dan ubanki ki gaidani ko in cire maki kunne..." Maryam kuka ta cigaba dayi amma batace komai ba, tsayawa yayi yana kallon yanda take zubar hawaye sannan yana tunanin why gaisuwanta matter to him, just two days a gidan amma kaman tayi shekara,

"Amma ke yar iska ce kou...tunda naga gaisawa ma kike da maza...tou mu gaisa..." Ya ski kunnenta tare da mika mata right hand dinshi,  Maryam Dora hannunta tayi kan kunnenta Tana kuka,  ganin bata da niyyan mika mashi hannu yasa ya daga left hand dinshi ya bugi keyanta, wani Abu yaji kulle awajen, San bata fuska yayi tare dacewa

"Me kika daukar min?.." Ya fada yana Kara Jin abinda ke kulle a keyanta, ko kasan bai yi zaton gashin kanta bane, 

"Wato daga ki gyara min bedroom har kinfara kulle min kaya kina fita dasu kou...now bring it out..." Ya daka mata tsawa, Maryam kuka kawai take Tana Jin yanda yake Kama gashinta data kulle baya yana ja da karfi, 

"Bude Dan ubanki!!', ya fada da karfi,  bata San lokacin da Ta fada hijab dake kanta ba, da sauri ta warware ribbon dake kanta, nan gashinta ya bazu bayanta, da sauri suhail yaja baya saboda tsoro Don bai taba ganin gashi a gabanshi haka ba,  still Maryam bata tsaya ba sai da ta saka yatsunta cikin gashinta ta bazasu yanda zai gan babu komai cikin kanta sai gashinta, baya suhail ya Kara ja, Maryam najin shuru tayi saurin tattare gashinta baya ta  dauki hijab dinta ta saka ta bar dakin, suhail yafi min goma bai dawo sense dinshi ba saboda abinda ya gani, 

"My Allah..." Ya fada under his breath, ahankali ya koma ya zauna yana kallon Kofa data bi ta fita. 


Da kuka Maryam ta shiga dakinta, baba rabi ta ganta, da sauri tabi bayanta Tana tambayanta abinda ke damunta, 

"Yace....ni...ba..ra..wo...me Maryam a thief" Ta fada cikin kuka, ahankali baba rabi ta Dora kanta kan shoulder dinta,

"Ki bar kuka...haka yake..sai hakuri..." Baba rabi ta fada mata sannan ta Kara da cewa

"Zan fadawa ubanshi...tunda ya bani amanarki..." Da sauri Maryam ta girgiza mata Kai, 

"Tsoro..." Ta fada mata atakaice, 

"Babu abinda zaiyi maki...zan fadawa babanshi ya ja mashi kunne,," still Kai Maryam ta girgiza mata, baba rabi bata Kara cewa komai ba ta shiga bathroom din dakinta ta hada mata ruwan wanka. Shiga tayi tayi wanka Tana kukan takaici da bakin ciki. Tea baba rabi ta hada ta kawo mata ba tare da kowa ya sani ba Don masu aiki basu Shan tea amma yanda alhaji ya nunawa baba rabi muhimmacinta yasa  ta sawa ranta zatayi duk abinda ya kamata don kar ta sha wahala kaman sauran masu aiki gidan. 


Karfe 8 alhaji ya tafi office nan ya fadawa Salman ya dawo gida ya jira Maryam ta shirya ya kaita islamiyya, dadi Salman yaji Don he will have a chance yayi magana da Maryam ko da word daya né. Karfe 8 p da rabi suhail ya  Kai mom dinshi wajen aiki, cos kullum shi ke kaita aminu Kano teaching hospital ya maidota gida. Yana tuki ya kalli  mom dinshi

"wai mom meye relationship din mu da wannan yarinyan?.." Ya tambayeta , Dan baki mom dinshi ta tabe before saying 

"Your father said yar cousin dinshi ce..." Shuru suhail yayi kaman Mai tunani,

"anything ?" Ta tambayeshi, 

"Nothing mom..." Ya fada cikin sanyinmurya, kallon shi tayi Sannan ta dauke kanta, suhail tuki kawai yake amma ya rasa abinda ke mashi dadi. 


Sallama Salman yayi lokacin daya shiga falo bayan ya ajiye alhaji a office, baba rabi ce ta fito, gaisawa sukayi sannan yace

"Dan Allah ki fadawa Fatima zan kaita islamiyya da Karfe tara..Yanzu sauran minti ashirin.." Ya shaida mata,

"Tou shikenan...Bari in fada mata.." Baba rabi ta fada sannan ta juya ta koma dakin Maryam, nan ta fada mata abinda Salman yace. Kaman Tana jira ta mike ta saka Kayan islamiyya tare da saka long hijab har kasa, tsayawa tayi Tana kallon kanta, kawai sai ta Dan saki murmushi Tana cewa

"Unbelievable...." Ta fada Tana fita daga dakin. Wurin baba rabi taje tayi mata sallama sannan ta fita waje, Salman na zaune cikin mota yana jiran zuwanta, yana ganinta yayi saurin fita daga motan ya bude mata ta shiga, shima ya shiga yayi suka bar gidan. Yana tuki ya kalleta ta cikin mirror tare dacewa

"Pls zaki iya fadamin sunanki?.." Bata yi wasting time ba tace

"Fatima...  " Ta amsa mashi babu wani Jan aji daman abinka da tashin turai

"Nice name,...am Salman...nine driver alhaji..." Ya fada mata yana kallon reaction dinta ta mirror, gani yayi bata wani Chanza face ba

"That's nice..." Ta fada mashi, Dan murmushi ya saki sannan yace

"Daga Ina kike?.."

"Jos..." Ta amsa mashi, cikin ranta Tana 

"I will surely visit this Jo's some day..."

"Ni kuma daga Niger nake...amma parents Dina suna nan Kano...kefa?.." Ya tambayeta yana tuki

"My mother is late...daddy kuma yana.....jos..." Ta fada kaman she doesn't want to talk. Shuru me ya Dan biyo baya sannan yace

"Jiya da yau naga kina fitowa daga bangaren suhail kina kuka...me yake maki?..." Ya tambayeta Kai tsaye, shuru tayi Tana wasa da yatsunta for a while sannan tace

"Don't want to talk about it...." Daga ki yayi ya kalleta ta mirror sannan yace

"Kin taba zama abroad né?.." Da sauri ta daga Kai ta kalleshi Sannan tace

"Why do you ask?" Dariya yayi sannan yace

"Naji kina turanci ta cikin hanci kaman turawa..." Itama dariya tayi bata Kara cewa komai ba,

"Pls in tambayeki wani abu?..."

"Yes.."

"Will you be my friend?.." Ya tambayeta, without wasting time tace

"Why not..." Ta fada ba tare da ta damu ba, turawa suna iya ajiye friends maza kala amma babu batun so, Don haka Don aliyu da Salman sunce suna son zama abokin ta bata dauke shi wani Abu ba, she feels it's normal, dadi Salman yaji

"Friend me kikeso in sayo maki  in zan zo daukanki?.." 

"Don't worry...nasha..tea..." 

"I insist..."  

"I love ice cream..." Ta fada Tana dariya kaman sun dade da sanin juna, dadi yaji tare dacewa

"Amma kina da kyau sosai...." Ya fada yana kallon ta ta mirror, murmushi ta saki ta kalleshi ta mirror tare da cewa

"Thanks..but I have heard that like a million times..." Tafada Tana dariya shima dariya yayi yana cewa

"Am jealous..." 

"Don't be...they're all friends..." Ta fada atakaice, kafin su Kai islamiyya har har sun sha hira kaman sun dade da sanin juna, daman  Maryam is lonely saboda rashin abokin hira Don ko jiya da ta zauna cikinsu murja ba dukan abinda suke cewa take ji ba. Tare suka fita kaman wasu couples suka isa office din shugaban makarantan. Nan yasa aka kaita aji sannan Salman ya koma yana tafiya yana murmushi. 


Suhail na dawowa daga inda ya Kai mom dinshi ya shiga main falo, kiran da yasaba yayi masu suka fito, 

"Ina Fatima!.." Ya tambayesu atakaice 

"Ta tafi islamiyya..." Binto ta amsa mashi, daure fuska yayi tare da Jan tsoki ya Kama hanya ya bar falon. Falon shi ya koma ya kwanta kan kujera tare da Jan tsoki. Bai fin minti biyar sai yaja tsoki. Ahankali na taka zuwa inda yake kwance na danyi tapping shoulder dinshi ya daga manyan eyes dinshi  ya kalleni 

"What's wrong?.." Na tambayeshi, tsoki ya sake ja tare dacewa 

"Ban sani ba!!!"




One love 💜💛❤💚💙

7💙❤❤💚💜

Wulakanci dodone...

💙💜💛❤💚






® zuwairat (ummumaryam)





0⃣7⃣







Cikin kasaita ya sauka ya tafi part dinshi, kawai he's thinking about new comer dinsu, yaga daya shiga dakin masu aikin ko juyawa batayi ba balle ta kalleshi, hakan ba karamin bata mashi rai yayi ba.

"I will give you special treatment...." Ya fada yana kwanciya. 

 The following day, Maryam ta tashi taji jikinta babu dadi saboda kwanciya kasan katifa, daman kan katifan baba rabi taji, tun da sassafe su murja suka shiga kitchen ita kuma zama tayi jikinta duk ciwo

"For how long...." Ta fadawa kanta Tana ragumi, Yanzu kuma taji yanayin ya Chanza mata kan da don before Tana Jin dadin tsohon gidan da take da baba rabi kan nan gidan especially data lura mutanen gidan are rude. Ahankali ta shiga bathroom tayi alwallah ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta fito falo lokacin gari ya fara wayewa kadan2, Tana tafiya ahankali ta shiga kitchen, gaisawa sukayi da su sannan ta samu stool ta zauna tare day in tagumi, Tana kallon yanda suke hada breakfast cikin gaggawa. Karfe 6 daidai binto ta kalle sauran Tana cewa

"Bari inje in wanke mashi  kewaye kar a samu matsala..."  Ta fada Tana barin dakin, Don daman kullum da karfe shiga suhail yasa dokan su dinga wanke mashi bathroom, hakan yasa suka rana atsakanin su amma Banda baba rabi. Da sauri binto ta Isa part din suhail, yana zaune  da pure white jallabiya hannunshi rike da counter, idanuwa shi lumshe sai bakinshi dake motsi ahankali, Ana bude  Kofan ya bude idanuwa ahankali, binto ya gani, da sauri ta durkusa ta gaidashi, bai amsa ba ya daure fuska, ahankali ta mike Don she's not expecting him to answer Don bai taba amsa gaisuwansu su ba saboda he feels he's far above them, hanyan bedroom dinshi tabi ya daga mata hannu alaman ta tsaya, chak ta tsaya kanta kasa, 

"Je ki Kara sabuwar zuwa nan..." Ya fada kaman baison magana Don in Baka kasa kunne ba bazaka ji abinda yake cewa ba, da sauri ta juya ta koma, har lokacin gari bai gama wayewa duka ba, ba kowa compound din balle wani yasan abunda ke faruwa. Binto na bude Kofan kitchen Maryam ta Dan daga weak eyes dinta ta kalleta, Dan murmushi binto ta sakar mata sannan tace

"Yace kije..." Tayi directing maganar ta ga Maryam, Maryam kallon ta ta tsaya yi for a while sannan ta nuna kanta tace

"Ni?.." 

"Eh...yace kije...." Ta sake fada mata, Maryam ji tayi gabanta na mugun faduwa saboda bayan tsana Tana tsoron shi, 

"Waye?..." Ta fada Don ta tabbatar da Mai kiranta

"Suhail ...." Binto Ta amsa mata

"Ina....ya...ke...." Ta fada cikin slant, 

"Zo in nuna maki...." Binto ta sake fada mata, ahankali ta diro daga kan stool da take zaune ta biyo ta, sai da suka isa falo binto ta juyo ta kalleta Sannan tace

"Da kin saka hijab kan Kayan baccin ki...." Ta fada mata, Don Kayan bacci ta saka Mai Riga da wando cotton, 

"Tou...." Ta amsa mata sannan ta koma ta dauko hijab cikin wayanda aka saya mata ta saka ta fito, har bakin flat din suhail binto ta rakata sannan ta koma ta barta nan tsaye, juyawa Maryam tayi Tana kallon compound din don ganin in da mutane taga wayam yake. Suhail kam har ya fara zama in patient Don har ya mike ya kuma zama, sai baya kaman minti biyar sannan Maryam ta bude, gabanta sai faduwa kawai yake, lokacin suhail ya Dora kafa daya kan daya yana girgiza su ahankali, Tana shigowa ta tsaya daga Dan nesa dashi kanta kasa, ahankali ya daga Kai ya fara kallon daga beautiful feet dinta 

zuwa kayanta then fuskan ta, da gani she's frightened Don daman bata Saba da tashin hankali ba, kura mata Ido yayi amma yaga ko kadan bat daga Kai ba balle ta gaisheshi kaman yanda su murja ke ke durkusawa sun gaida shi,  relaxing yayi yana kallon ta while ita kuma Maryam gabanta na dukan uku2 saboda tsoro, sun fi minute biyu a haka yaga bata da alaman gaida shi, afusace ya mike ya je inda take tsaye ya rike bayan wuyan ta ya dukar daita in a forceful manner, Dan Kara Maryam ta saki Tana fashewa da kuka Don ko a wurin dad dinta haka take, she easily crys, 

"Dan ubanki baki iya gaisuwa ba!!" Ya daka mata tsawa, kuka ta cigaba dayi bata amsa mashi ba, cikin ranta Tana yau dad dinta wani banza yake zagi, 

"Wato ke tashin jos kou?... You don't have respect...now kneel...." Ya sake daka mata tsawa, da sauri ta tashi daga durkushen da take tayi kneeling Tana kuka hannunta rike da bayan wuyanta, 

"Zo nan..." Ya fada mata in an irritating way, mikewa tayi niyyan yi Don zuwa yayi sauri cewa

"Koma kiyi kneeling then crawl to me..." Yayi commanding dinta, da sauri ta sake kneeling Tana rarrafawa zuwa gabanshi, har lokacin hannunta bayan wuyanta sai kuka take, sai da tazo daf dashi ta dakata, kura mata Ido yayi for just a second sannan yace

"Kin San ni?..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta girgiza mashi Kai, 

"For your information nine suhail...wannan tsohon daya kawoki gidan nan is not the boss...ni né boss...you do what I ask you to do ...Don in na so ko abinci bazaki samu gidan nan ba....." Ya fada sounding very rude and harsh, ahankali Maryam ta daga wet face dinta ta kalleshi cikin ranta Tana cewa

"You will pay for this...." Ta fada cikin ranta, the next thing nataji shine Mari

"Don't ever look at me again..." Ya fada cikin tsiwa, ihu Maryam ta farayi Jin face dinta on fire, hannu tasa ta rike cheek dinta Tana hawaye

"Daddy....." Ta Kira cikin kuka, 

"Me kika ce?.." Ya tambayeta Don bai taba Jin murya ta ba amma sai tayi share shi ta cigaba da kuka, 

" close your mouth..." Bai idaba tayi saurin hadiye kuka Tana sauke ajiyan zuciya, 

"From now  henceforth ke zaki dinga wanke bathroom Dina....ke zaki dinga gyara gado na...inshort ke zaki kula da part Dina kuma I I see any dirt you are in trouble...am I clear?!!!" Da sauri ta daga mashi Kai Tana sauke ajiyan zuciya, 

"Kije ki fara da bathroom Dina....and make sure you fix ruwan wanka na..." Ya fada yana relaxing..." Mikewa tayi daga gabanshi ta Kama one door dake wurin, nan ta tarda bedroom dinshi, Tana ganin bi kusa ta fashe da kuka sosai, yau ta godewa Allah ita ke komai na dakinta da bata San yanda zatayi ba, tana kuka ta bude Kofan bathroom dinshi, gani tayi bathroom dinshi is nothing compared to hers Don ita har da jacuzzi cikin nata, batayi wasting time ba t wanke mashi kaman yanda takewa nata cikin ranta Tana tunanin abinda zatayi mashi ta huce Don tunda take baa taba sata kuka da duka ba sai yau wai har mari. Cikin few minutes ta gama ta fito ta dawo bedroom, gadon shi ta gyara dukda bai watse sosai ba, bayan ta gama ta tsaya ta kasa fitowa saboda tsoro, har garin ya ida wayewa bata fito ba, suhail né ya gaji da zama ya mike ya shiga bedroom din, nan ya ganta tsaye jikin bango, gadon ya kalla yana cewa


"Stupid gal ko iya gyara gadon bata iya ba...sai iya kallon maza...idiot..." Ya fada yana shiga bathroom, Maryam sake Sabon kuka tayi dataji abinda yake cewa, Tana ganin ya shiga bathroom ta fito falo da gudu ta wuce waje har lokacin bata bar kuka ba. Lokacin security sun fito likewise Salman, yana daga Kai ya hangi Maryam ta fito daga part din suhail Tana kuka ta shiga part din hajiya, tunda yake ganin su murja suna fita daga part din suhail bai taba Jin abinda yaji yau ba, ji yayi he's heart is beating so fast,ahankali ya zame ya zauna yana tunanin me yayi mata take kuka. Maryam na shiga ta wuce bedroom dinsu, Sabon kuka ta fara, Tana kiran daddy dinta, murja ce ta shigo dakin ta zauna bakin katifan da take kwance Tana kuka,

"Yar uwa kiyi hakuri...karkiyi kuka Don in alhaji yazo ya ganki cikin damuwa ya tambayeki dalili kika fada mashi ..tou wahalal ki sai ta ninka haka...Don haka ki bar kuka kinji kou...." Ahankali Maryam ta daga mata Kai Kai Tana  goge face dinta. 

"Ki taso muje muci abinci...." Murja Ta fada Mata , ahankali Maryam ta kalli agogon dake jikin bangon dakin taga it's just 7:20am, ahankali ta girgiza mata,

"Zamu ajiye maki naki...." Murja Ta fada mata sannan ta mike ta bar dakin, komawa Maryam tayi ta kwanta Tana tunanin Suhail da irin kalaman dake fita daga bakinshi, bata taba ganin Wanda ta gani yayi mata kyau kaman shi ba likewise bata taba ganin Wanda ta ga munin halin shi kaman shi ba, yanda yake magana cikin command ta tuna dukda she's angry bata San lokacin da murmushi ya zomata ba, Don gani take inda ita yar wata matsiyaciya ce da bakin ciki ya kashe ta amma thank Allah she's among the rich young ladies kaman yanda dad dinta yake fada mata, Tana tuna at times in tayi ba daidai ba sai yace

"Baby the person who is worth billions of dollars shouldn't behave like such...." Takanyi murmushi in ya fadi hakan and she do reply da 

"Dad am I really worth billions of dollars?.." Shima sai yayi dariya yace

"in kinyi hankali zan fada maki ko ke wacece....". Idanuwa ta lumshe Tana tunanin if Tana iya zaman gidan, tasan ko kadan she's not the lazy type Don dad dinta baiyi training dinta tobe lazy ba

"The boss shouldn't be lazy..." Shine abinda yake fada mata duk sanda ta nuna gajiyawanta kan wasu abubuwan, 

"Always be strong in any situation you find yourself..." Ta tuna maganar dad dinta kafin tazo Nigeria, tunani tayi ko ya San da halin suhail kafin tazo gidan

"No way...." Ta fadawa kanta Don ta San her dad will do anything to make her happy and not the other way round. Tunawa tayi da alhaji Ismail, ji take kaman Ta fada mashi abinda suhail yayi mata just in a day a gidan sai kuma ta tuna da maganar murja, ko kadan batason abinda zai taba mata lafiya jikinta, 

"Let's see your game....then it will be my turn..." Ta fadawa kanta sounding firm and strong. Cikin tunani bacci yayi gaba daita. 


Suhail na shiga bathroom yaga bata hada mashi ruwan wanka ba, a fusace ya fito amma sai yaga bayanta har ta fita daga part dinshi, kawai sai ya saki dariya

"Idiot..." Ya furta under his breath sannan ya koma ya hadawa kanshi ruwan wanka ya shiga cikin bathtub tare da sakin ajiyan zuciya.


Bayan alhaji yayi breakfast ya kalli agogon hannunshi, karfe 9 da yan minutes, kallon hajiya yayi ya kalli wayanshi, babu abinda yake bukata Yanzu kaman yaji ya Maryam ta kwana a gidanshi, duk sanda ya tuna alkawarin daya daukawar dad dinta sai gabanshi ya fadi Don wani irin nauyin alamarin yakeji, ji yake Ina ma yana iya fadawa family dinshi ko ita wacece Don anyi treating dinta like a princess that she is amma babu daman haka, yasan ko special attention ya bata Yanzu zai sa hajiya ta zargeshi, Dan ajiyan zuciya ya saki tare dacewa 

"My hajiya I think zan saka wannan yarinyan a islamiyya..." Irin kallon da hajiya tayi mashi yasa yayi shuru, 

"Hana alhaji...do you mean dadewa zatayi gidan nan da har zaka sata islamiyya?... Gaskiya ni shawarata is a kaita wurin wasu family sai ka dinga tallafa mata har tayi aure...amma ni gaskiya I don't feel comfortable with her around..." Ta fada babu wasa, daure face alhaji yayi ya fara cewa

"Hajiya kin San I have given you too much hand da Yanzu kike son maidani mijin hajiya?"" Baki hajiya ta bude zatayi magana alhaji ya daga mat hannu tare dacewa 

"Let me finish..." Ya fada tare da sauke hannunshi sannan yacigaba dacewa 

"From now henceforth I don't want you making commands....in kuma Dan kishiya kike wannan abun sai in auro so that hankalinki ya kwanta..." Bai idaba hajiya tq Dora hannu bisa kai 

"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!!!...alhaji..." Still daga mata hannu yayi tayi saurin yin shuru hawaye na taruwa eyes dinta

"I want you to know ba tsoron ki né yasa ban Kara aure ba da zaki hanani taimakawa family Dina saboda kishi...if I want sai in jero uku bayanki amma bani da wannan raayin..but if you continue like this I might change my mind..." Ya fada yana kallon yanda tears ke rolling daga idanuwanta 

"Am sorry...ban karawa..." Ta fada gabanta na dukan uku uku Sannan Tana tunanin why alhaji ke mata harsh words saboda wannan yarinyan, Don har ta gane bayason ta soki maganar ta, hannu yasa ya goge mata face yana cewa

"Stop shedding those expensive tears..." Sai da ya tabbatar ta goge face dinta ta dawo mind dinta sannan ya mike yana cewa

"Bari in aiki Salman ya shiga cikin gari ya nema mata good islamiyya..." Ya fada yana kokarin barin dakin, ahankali itama ta mike Tana cewa

"Nima Bari inje part Dina..."

"Ok..in na gama da Salman am coming to your part..." Ya fada mata Don abinda yake so kenan Don yana son ya shiga part dinta yaga Maryam and how she is. Tare suka fita compound ita tayi part dinta shi kuma ya yiwa Salman alaman ya zo da hannunshi sannan ya koma ciki, da sauri Salman ya taho ya bi bayanshi, bayan sun zauna alhaji yace

"Ka dauki mota kaje wannan islamiyya na modibbo kayi wa shugaban makarantan magana...just tell him ni na aikoka kan maganar wannan yarinyan...zasu Baka uniforms ka kawo...sannan pls ka tabbatar kana kaita kullum kana maidota..." 

"Ok sir ..." Salman ya fada mashi sannan ya tashi ya fita, cikin ranshi ya jidadi da Maryam ba gida zata zauna ba balle suhail ya takura mata. Sai da ya fita shima alhaji ya fita ya shiga part din hajiya, sai da ya tabbatar hajiya bata downstairs sannan ya leka kitchen yaga binto Tana aiki Don mostly cikin aiki suke saboda kowa da irin kalan abincin da zaici especially suhail Don har time table yayi masu na abincin shi sannan yakan Chanza ta after some weeks. Gaidashi binto tayi ya amsa sannan ya tambayi inda Maryam take, nan binto ta shaida mashi Tana bacci, agogon hannunshi ya kalla yaga few minutes to ten, 

"Ina ta kwana?.." Shine tambayan da alhaji yayi mata,

"Dakin mu..." T amsa mashi kanta kasa, daure fuska yayi sanna yace 

"Ima sauran yanuwnki?"

"Suna sama suna gyaran wurin hajiya..." 

"Shikenan in kin gama ki shiga dakin dake kusa da naku ki gyara...in kin gama ki maida jikkanta dakin..sannan duk abinda dakin ke bukata ki fadawa Salman ya fadamin..."

"Tou..." Ta amsa mashi cikin ladabi. Wucewa yayi upstairs ya tarda hajiya kwance while su murja na aiki, yana shiga sukayi saurin fita daga dakin. After kaman minti talatin ya koma part dinshi hajiya na biye dashi.  


Sai karfe goma da rabi Suhail ya shiga part din mom dinshi, upstairs ya hau ya gan mom dinshi bata nan yasan Tana part din dad dinshi, downstairs ya dawo ya wuce kan dining ya hakimce yana jiran breakfast, suna ganin shi kan dining sukayi saurin fara jera mashi breakfast dinshi kan dining sai da suka gama murja tazo serving dinshi ya daga mata hannu alaman ta dakata, tsayawa tayi Tana jiran next command dinshi Don tasan ba da kaishi zai zuba abincin ba. 

"-–-11222222222222Kirawo Dayan...." Ya fada mata atakaice, murja ta gane abinda yake nufi, da sauri ta bar wajen while binto da asabe suka kalli juna. 

Daki murja ta shiga har lokacin Maryam Tana bacci saboda kukan data sha, ahankali murja ta Dan bugi shoulder dinta, cikin kasala  Maryam ta bude idanuwanta,

"Yace kije...." Murja Ta fada mata, da sauri Maryam ta wace idanuwa Tana cewa

"Waye..again..." Ta fada gabanta na faduwa,

"Suhail..." Ta amsa mata,

"Na...shiga....uku..." Ta furta kaman zatayi kuka, nan take ta hada Kai da gwaiwa gabanta  na Kara dukan uku2, 

"Ki taso..baya son jira, Ta fada mata, jiki ba kwari ta daga Kanta da idanuwan ta da suka kada sukayi ja, kaman Mai maye ta biyo murja har lokacin Tana sanye da Kayan bacci da hijab, duk ta susuce suna fita falo ta hangi suhail dake zaune kan dining fuskan daure kaman bai taba dariya ba, daga Kai yayi suka hada Ido ya Kara murtuke fuska haka nan yanajin wani Abu game daita dake sashi ji kaman ya dinga dukanta, so he thinks. Yanda ta Saba tafiyan ta ta taka ta karaso inda yake zaune, kusa dashi tazo ta tsaya, daga inda yake zaune yana ganin yanda jikinta ke rawa, 

"Save me..." Yayi commanding dinta, jikinta na rawa ta isa kan dining din ta bude abincin, hannunta sai rawa kawai yake, daga Kai yayi ya kalli sauran yan aikin sukayi saurin watsewa, jikinta na rawa ta fara zuba Irish potatoes, rabi cikin plate rabi kan dining, suhail harde hannuwanshi kan kirjinshi yayi yana kallon ikon Allah, Kwai ta zuba mashi sama Tana kyarma, hannu tasa zata dauki flask da ruwan tea ke ciki kamshi ya bugi hancin shi, dukda ta dade bata yi amfani da perfumes dinta ba she doesn't smell bad saboda ya Kama mata jiki already, ruwan tea ta zuba cikin cup Dan kadan kaman yanda ta Saba Shan nata, madara ta bude ta fara zubawa cikin ruwan, sai data cika Dan karamin ruwan da madara ya koma Kama custard sannan ta tura gabanshi, suhail zama kawai yayi yana kallon abun mamaki tea kaman koko, saida ta gama ta mike tsaye, ahankali yayi mata hannu alaman tazo, Dan Matso kusa dashi tayi sannan ya kalli tea da dankali dake kan dining yace

"Daman haka matsiyata suke...nasu dukiya na mutum banza,... Dan ubanki kin taba ganin tea haka?..." Ya daka mata tsawa, jikinta na rawa ta girgiza mashi Kai dukda ita paste takeyi da tea dinta ta dinga lashewa ahankali kaman Tana Shan ice cream, lumshe idanuwa tayi Tana sauraron abinda yake cewa

"When am talk about to you look at me...." Ya daka mata tsawa, da sauri ta bude red eyes dinta

"Nace haka ake tea?..." Ya sake tambayan ta cikin fada, da sauri ta sake girgiza mashi Kai,  tsaya kallon tender hands dinta data rike cikin juna yayi sannan ya maida idanuwashi kan face dinta yana cewa

"Kin San ba haka ake tea ba shine kika hadamin haka Dan ubanki?... Wato tunda bana ubanki ko uwarki bane even if it's wasted babu komai kou?.. Tou tunda na lira ke yar raini hankali ce special treatment zan baki gidan nan...and now kin kwace wannan Irish din kin cinye..." Ya fada yana nuna mata na kan dining, hannunta na rawa  ta saka ta fara daukan daya tana kaiwa bakinta, rike mata hannu yayi, cikin second daya ya saki hannun saboda abinda yaji, ha shocking sannan hannunta kaman cotton wool dukda bai taba hannun mata yasan ba haka hannunsu suke ba, 

"Park all and eat..." Ya umarce ta, da sauri ta  kwace duka ta Kai bakinta, Dan karamin bakinta ta bude ta fara turawa cikin bakinta, shuru suhail yayi yana kallon ta, Abu guda saya da bai gane ba shine at this moment he don't mean what he's doing to her amma kuma he enjoys watching her, 

"Get out..."  Ya daka mata tsawa, da sauri ta bar wajen, direct bathroom ta wuce ta saki abincin cikin sink Tana fashewa da kuka, she can't just believe yau tayi kuka sau biyu because of same person. Bakinta ta wanke ta dawo dakin ta zauna bakin katifan, wayanta ta dauka tayi dailing number dad dinta, ringing ya dingayi amma baiyi piçking ba, bayan kaman minti biyu sai ya message cewa yana meeting that he will get back to her, tasan ba lallai bane ya kirata a wannan ranar Don mostly excuse da yake bata kenan.


Salman ya dawo da Kaya cikin Leda ya bawa alhaji, lokacin still suna tare da hajiya, nan yake fada mata Kayan islamiyya Fatima ne, batace komai ba taja bakinta ta tsuke. 


Har karfe biyu Maryam bataci komai ba, wanka tayi ta Sam gown ta koma ta kwanta. Alhaji bai samu kadaici ba sai da zashi sallan zuhr, sai lokacin ya dauki wayanshi ya Kira Maryam yana tafiya, Tana piçking ya gane something is wrong 

"Daughter meke damunki?.." Shine tambayan da yayi mata,

"Babu...komai..." Ta amsa mashi muryan ta narawa sannan hawaye na forming idanuwanta, 

"No..ya zakice babu abinda ke damunki while you sound dull...pls daughter ki fada min..." Ya daka yana tafiya ahankali,

"No...just missing my daddy...." Tana kaiwa nan sai ta fashe da kuka

"And baba rabi...." Tayi adding, 

"Am so sorry daughter...zansa a maido baba rabi nan ba da dadewa ba...have you eaten?.." Ya tambayeta, sai lokacin ta tuna da ko ruwa bata sha ba yau, shuru tayi babu response 

"Daughter kinci abinci?.." Ya sake tambayanta, 

"No...Yanzu...zan...ci..." Ta fada mashi, 

"Daughter pls kar ki zauna da yunwa...and duk abinda kikeson ci just contact me directly kinji kou?..." 

"Yes sir..." 

"Nasa an gyara maki dakin kusa da Wanda kika kwana...ki koma chan..sannan duk abinda kikeso ki sa ayi maki...don't stress yourself...hope am understood?..." 

"Yes sir..." 

"Yes ma'am..." Shima ya fada cikin zolaya, San murmushi ta saki sannan ya kashe wayan, relaxing Maryam tayi Tana tuna irin kirkin alhaji Ismail, 

"He's so caring..." Ta dada under her breath, ahankali ta mike ta fito falo tare da shiga kitchen, 

"Baki ci abinci ba har na rana y kusa dahuwa..." Binto ta fada mata, murmushi kawai ta sakar mata sannan ta bude fridge, yourght ta gani ta Fiddo, 

"Tab ki maida shi..kika sha tou kin shawowa kanki..." Bata nemi Jin ko na waye ba ta maida ta ajiye, cabbage da asabe ke yankawa ta deba ta wanke, ta fara ci haka nan, kallon ta kawai suka tsaya yi

"Bazaki ci abincin da aka ajiye maki ba?.." Binto ta tambayeta, ahankali ta girgiza mata ki Tana Kai cabbage bakinta.


Karfe hudu baba rabi ta dawo gidan, suhail dake zaune compound harara ya bita dashi batare saya amsa gaisuwanta ba. Maryam Tana ganinta taji wani irin dadi Don har hugging dinta tayi saboda farin ciki. Nikam nace baba rabi bata iya Hana Suhail yin what suhail do best.



One love💙❤💙💛💚9 💛💜❤💙💚

Wulakanci dodone 

💛💚💙💜❤






® zuwairat (ummumaryam)





0⃣9⃣








Juye2 ya dingayi har bacci yayi gaba dashi. Maryam kam islamiyya is fun, mostly young ladies dake gurin are civilians and friendly, especially wata Mai suna Aisha.  Sit daya suke zaune da Maryam. Karatun was fun. Around 12 suka tashi, tare da Aisha suka fita zuwa bakin gate, sai lokacin suka samu  daman introducing junansu, suna fita ta hangi motan Salman tsaye daga gefe, Dan tsoki Aisha taja tare dacewa 

"Driver dinmu bai zo ba...he's always late...." Ta fada Tana turo baki, kallon motan Salman dake faman saki murmushi yayi Sannan tace

"Will you join us?..." Ta fada mata, ahankali  Aisha tace

"Nasan he's close...kawai ku tafi...zamu hadu da yamma...." Ta fada mata, sai lokacin Maryam tasan da yamma zasu sake dawowa 

"You mean we're coming in the evening too?.." 

"eh mana...zamu dawo...." Gira daya Maryam ta daga sannan tace

111"Alright...na tafi...." Ta fada Tana takawa ahankali, kafin ta Kai bakin motan har Salman ya fito ya bude mata mota yana cewa

"Bestie welcome..." Ya fada yana bude mata bayan motan. Murmushi ta sakar mashi tare da daga mashi gira Tana cewa

"What's up dude...." Dariya Salman ya saki yana cewa

"Dude kuma?'" Ya fada yana dariya, gaban  motan  ta bude ta shiga Sannan tace

"Ina my ice cream..." Salman maida bayan mota yayi ya rufe sannan ya shiga, Leda ya mika mata, kaman hungry lion ta amshi Leda Tana cewa

"I love you...." Ta fada bata damu da maganar as anything ba, kallon ta Salman yayi yaji kaman an soke heart dinshi, ko Kara daga Kai batayi ba ta Fiddo roban ice cream din ta bude, da sauri ta Kai spoon daya bakin ta ta lumshe idanuwa tare da sake cewa

"You're the best dude...I miss this..." Ta fada idanuwanta lumshe, Dan murmushi Salman ya saki yana kallon lashes dinta sannan yace

"Da alaman kina sha kuma kin dade baki Shaba...." 

"Getting to three weeks...." Kara sha tayi Tana saki santin havila ice cream, mota Salman ya tada  ya ja ya Kama hanyan gida, Maryam tanashan ice cream Tana yi mashi surutu which he loves so much, batasan anan budurwa Tana Jin kunyan cin Abu gaban saurayi ba sannan ita bata dauki Salman more special than female friends ba, the only person da yake da amfani a rayuwanta kafin ta bar USA shine Erick, Wanda bai da gurin da ya wuce yayi sex da ita, and ba wai batason bashi ba illa tsoron da Helen ta bata kan Ana Shan wahala on first time. Kullum in sun hadu sai yace tayi kokarin Fidda tsoron ta so that ta suyi bonding kaman yanda yake kiran sex, haka bai faru ba har ta Baro USA, she remembered lokacin data fada mashi zata bar kasar, yayi kokarin su hadu amma tsoron fita ya hanata Don ita gani take Tana fita Ana iya harbeta ko kuma ayi kidnapping dinta.  Har kullum ce mata yake at 18 ya kamata ta zama full woman and he's willing to make her a woman, wai she's still a kid since she's a virgin. At times if she's lonely Tana son kiranshi a waya amma Tana tsoron maganar da dad dinta yayi mata kan cewa Ana iya tracing calls dinta a gano inda take sannan she should be careful Don batasan wayanda suke da hannu kan abinda ake son yi mata ba.

"Just laying low...." Ta fada under her breath amma sai da Salman ya juyo ya kalleta,  

"Me kika ce?.." Ya tambayeta calmly,  

"Nothing..just enjoying the ice cream..." Ta fada Tana licking ice cream din da tip of her tongue kallon ta Salman ya tsaya yi har ya manta tuki, Tana daga idanuwanta taga bump gabansu, da sauri ta bugar mashi laps tare dacewa 

"Look out...my daddy still loves me..." Kai kawai Salman ya maida gabanshi batare dayace komai ba, 

"At first nayi tunanin you are alhajis wife..." Bai idaba ta zaro idanuwa tare dacewa,

"What the hell...an old man...Allah forbid..." Ta fada sannan ta nuna shi Tana lumshe idanuwa tace

"Kai how old are you?.."

"28.." Ya fada mata Kai tsaya

"Well you are old for me...." Bata idaba wayanta ya fara ringing, bayan few ringing  tayi piçking, aliyu me yayi sallama daga chan bangaren, Tana Jin muryan ta gane shine, gaisawa sukayi, yana Jin yanda take magana cikin excitement yace

"What are you doing?.." Ya tambayeta, 

"Licking ice cream..." Ta fada kaman she's sounding naughty, idanuwa ya zaro yace

"Licking kuma?...hmmm kaman you love..licking...the ice cream..."

"A lot..." Ta amsa mashi, 

"Wa ya saya maki..." 

"My friend Salman..." Daure fuska aliyu yayi kaman yana gabanta yace

"Who is he..," 

"Non of your business..." Ta amsa mashi not too harsh, dariya yayi 

"Ok Nima zan kawo maki ice cream..hope zakiyi licking sosai..." Itama dariya tayi sannan tace

"why not..."Ta fada not caring yanda yake furta word din. Suna cikin hira dashi har suka Isa gida, Salman ji yayi kaman ya fashe saboda bakin ciki, suhail dake bacci yana in karan shiga motan yayi saurin mike wa zaune da eyes dinshi da sukayi ja, kaman Mai layi ya mike yaje bakin window,  nan yaga Maryam ta fito daga gaban mota hannunta daya rike da roban ice cream sai daya rike da waya a kunnenta, Salman ya gani ya mika mata Leda da alaman wasu Kayan dadin né ciki, haka nan dai ya ji ya cika yayi dam. A fusace ya fita daga dakin yayi waje, da sauri Maryam ta daga Kai ta ha mutum ya nufosu, sadda Kai kasa tayi ta Kara sauri 

"You zo kayi min wanki..." Ya fadawa Salman babu wasa, Maryam taji abinda yace amma ko Kara juyowa bata karayi ba har ta shige falo

"Alhaji yace in dawo office in na maidota daga islamiyya..." Salman ya fada mashi atakaice, bai idaba suhail ya daga hannu ya nuna shi da Dan yatsa sannan yace

"Don't you ever in your peasants life argue with me...ni da Kai dayane da inayi zakayi?... Allah yasa ka karayi min gardama you will see what happens...." Ya fada cikin wani irin anger da shi kanshi bai San yana da shi ba, juyawa yayi ya Kama hanyan part dinshi looking so furious, Salman Fiddo waya yayi tare da dailing number alhaji, baya yayi piçking yayi mashi sallama ya amsa sannan yace

"Sir I will be a little bit late..."

"Why?.." Alhaji ya tambayeshi atakaice, ahankali yace

"Suhail yace Inyi mashi wanki.." Bai idaba alhaji yace

"Come to the office right now ..." Alhaji ya fada tare da katse wayanshi. Salman bai jira tsaya jiran suhail ba ya shiga mota ya tada ya bar gidan. Suhail sake tsaye cikin daki gaban closet dinshi yana Fiddo Kayan da ko sawa bai tabayi ba saboda zalunci ya ji Kara mota, da sauri ya leka ta Window yaga Salman né ya fita, hannu ya dunkula ya fara dukkan bango da karfi, zuciyan shi kaman ta fito saboda ya da yake harbawa , he's so restless for unknown reasons, bakin gado ya zauna ya Dora  Kai kan gwaiwan shi,  ajiyan zuciya ya saki ya mike ya Kama hanyan waje, kallon agogon dake falon shi yayi yaga daya sauran yan mintina amma ko ruwa bai sha ba. Maryam na shiga ciki suka gaisa da yan gidan, ledan dake hannunta ta mikawa baba rabi ta shige dakinta. Sauran ice cream dinta ta ajiye ta cire Kayan jikinta, Dan mika tayi tare da shiga bathroom wearing only pant and bra. Bayan ta gama wanka ta fito daure da towel, har zata Shafa Mai sai ta tuna wani Abu ta mike, bathroom ta koma ta fito da alwallah sannan ta Shafa Mai. Tana gamawa asabe ta shigo 

"Yace kije..." Shine abinda Ta fada mata, 

"Ki fa..da...ma...shi...am wearing my clothes..." Ta fada fuskanta daure, 

"Kiyi sauri...ya dade zaune..." Ta fada mata kafin ta fita, baki Maryam ta tabe amma gabanta na faduwa Don batasan abinda zai sata ba, taji dazun yana sa Friend dinta Salman aikin wanki and she's not happy about it, kawai she feels Ina ma she can do something. Doguwar Riga tasa ta rufe kanta da dankwalin kaman vail ta fito, daga nesa suhail ya hangota ta taho, ji yayi gabanshi na faduwa kaman zata fito, 

"Who is this!!!" Ya fada cikin ranshi Don gani yake wannan yarinyan ba mutum bace da take néman kashe mashi zuciya, ahankali ta karaso inda yake ta tsaya daga Dan nesa dashi, ahankali ya daga idanwanshi ya kalleta tare dacewa 

"Wato ke baki iya gaisuwa bako?... Now kneel and greet me..." Ya fada atakaice Fuskanshi dauke da annoying look, ahankali Maryam tayi kneeling amma bata bude baki tayi magana ba, 

"So bazaki bude baki ki gaida ni ba kou?...to is either ki gaida ni ko kuma wallahi in aikaki inda babu service..." Ya dada kaman wani Dan daba, bata gane maganar shi ta karshe ba, amma it doesn't sound ok, gani tayi yayi mike da gudu tace

"Ina...wu...ni..." Ya fada  gabanta na dukan uku2, 

"Ashe you can talk...ai da kin nuna taurin Kai na baki visan zuwa lahira Yanzu nan....iya go and serve me..." Ya fada yana relaxing, ahankali ta mike ta Kama hanyan kitchen, baba rabi ta gani labe kaman she's listening to their conversations, Tana shiga baba rabi ta mika mata tray na abinci da suka shirya tun safe Amman baizo yaci ba. Falo Maryam ta dawo ta ajiye kan dining, kaman baison tafiya ya mike ya dawo kan dining Don farat daya yaji he's famished. Tan ajiye ta juya zata tafi, 

"Ubanki zai zo yayi serving Dina kou?" Ya tambayeta atakaice, still tayi for a moment sannan ta juyo Don duk abinda yake mata bai mata zafi kaman zagin ubanta da yake. Serving dinshi tayi in a unique way Don yau ko daya bata zubda ba, juyawa tayi ta bar wajen ta koma dakinta. 

Spoon na abinci ya Kai bakin ci amma to his surprise sai yaji duk ba dadi, still daurewa yayi ya Kara Kai wani spoon din amma still babu dadi, 

"Fall in!!.." Ya fada da karfi kanshi kasa while yana murza hannunshi da juna, da sauri suka fito har baba rabi, Maryam taji amma bata tashi ba,

"Waya dafa wannan abun?.." Ya fada yana nuna plate of abinci dake gabanshi, 

"Nice..." Inji baba rabi, bata fuska yayi tare dacewa 

"Da uban me kika dafamin abinci?.." Ya tambayeta Kai tsaye kaman yana magana da age mate dinshi. Dan runtsunawa baba rabi tayi sannan tace 

"Abinda na Saba dafawa dashi né....."

"Karya kike...you're lying...ga  abinci babu taste...it tastes awful kuma kice da abinda kika Saba dafawa dashi?... Now ki koma nan cikin kitchen ki hadamin wani abincin....if you like ki dafa babu dadi sai kin Kara dafawa..." Ya fada atakaice, mikewa yayi ya Kama hanyan dakin Maryam, ba knocking ya bude Kofan, luckily she's decent, Tana kwance tayi rub da ciki, Tana Jin an bude Kofan juyo suhail ta gani, da sauri ta mike zaune, nunata yayi da yatsa sannan yace

"Wallahi kika karajin fall in baki fito ba sai na lahira ya fiki Jin dadi....I know kina wasa Dani because you don't know what am capable of...amma ki cigaba..." Bai idaba yaga Tana bashi wani irin blinded look, irin kallon nan na na nothing you said matters take mashi

"Ni kikewa wannan kallon?.. " Ya fada  yana taking a step zuwa inda take zaune, da sauri ta mike  tana ja da baya tare da girgiza kanta,  

"Kika karayi min irin wannan kallon sai na nakasa ki..." Ya fada out of anger, shi kanshi yasan he's bluffing sannan yana mamakin why he's so furious today, mostly abinda ke hadashi da masu aikin gidansu shine batun aikinsu amma bai damu da wani Abu nasu that doesn't concern him ba amma wannan yarinyan is different, yi mata magana gives him fun da bai San ko na miye ba. Yana fita Maryam tace 

"Saddest frike...." Ta fada Tana koma ta zauna, wayanta né ya fara ringing Tana dauka taga daddy dinta né, da sauri tayi hugging wayanta tare da piçking, kiss Ta fada jerewa wayan, daga chan bangaren dad dinta yace

"Sweetheart wato babu Salam sai kiss kou" ya fada yana dariya, da sauri tace 

"Salamun alaikum..." Amsawa yayi yana Jin dadi, 

"My love how have you been..." Bai idaba tace 

"Daddy am tired...daddy pls take me back and I promise I won't step out of the house...pls daddy..." Ta fada kaman zata fashe da kuka, Dan murmushi ya saki before saying 

"Dear har Yanzu baa Kama people responsible for the attacks ba...sannan ko jiya they was an attack on the house..." Bai idaba tace

"Daddy I don't believe that....daddy you can make them pay in a day if you really want to...kawai you are tired of seeing me...." Ta fada Tana fashewa da kuka

"Don't ever say that...yara nawa gareni da zan yarda ki?... I have only you...kuma kin San cewa bani da gurin daya wuce in ganki cikin farin ciki..."

"But daddy am not happy here without you...pls Daddy take me to another country..." Ta fada cikin kuka,

"Baby if you keep crying when ever I called I might stop calling...and har yanzu banji kina zuba min Hausa ba.." Ya fada yana dariya 

"Na...iya..." Ta fada still crying 

"Good..gaya min me kikayi yau?..." 

"Nothing much..kawai...na..je...islamiyya...and am going back by four..."

"That's good to hear... Hope you love it?..."

"Yes daddy..."

"To da akwai abinda kike bukata?.." Y tambayeta, shuru tayi for a while Tana tunanin abinda zata ce, sai da ya Kara Maimaita tambayan sannan tace

"Daddy.."

"Yes love..

"Birthday Dina sauran...3 months...pls..I want to celebrate it with you...." Ta fada cikin low voice, shima dad dinta shuru yayi yana tunanin yanda duk shekara take grand party na birthday dinta and ko Yanzu he don't want to say no to her, yan missing dinta kaman hauka amma he's pretending he don't care. 

"Ok dear...how do you want it..in zo Nigeria ko yaya?..."

"No daddy...pls I want to come ..with my friend..." Ta fada cikin sanyinmurya, dariya dad dinta yayi tare dacewa 

"Daughter har kinyi Friend?"

"Yes daddy...."

"Mace ko namiji?.." Shuru tayi batace Komi ba

"I guess namiji né..." Dad dinta yayi adding daya ji tayi shuru.

"Kou shine mister right din?.." Y fada babu wasa Don bai da gurin daya wuce Maryam tayi aure Don already babu abinda barin ya mace babu aure ke haifarwa sai balai,

"No..daddy...I just want to show him my home...." Ta fada kasan2

"Alright then...Allah ya kaimu lokacin...I will make some arrangements...sai ku zo...amma ba dadewa zakiyi ba..." 

"No problem daddy..." Ta fada cikin ranta Tana Jin dadi, Don bata San dad dinta zai yarda so easy ba kasancewan bayason yana ganinta da namiji,

"Behave well kinji kou and listen to your new daddy and mommy..." Ya fada mata

"Ok daddy..." Ta fada Tana tunawa da maman suhail Don mostly bata ganinta sosai like yau ma bata ganta ba. Kashe waya dad dinta yayi ta ajiye wayanta ta koma ta kwanta, Tana tunawa da plan dinta, 

"How did I get this plan in the first place..." Tafada Tana dariya , tsalle ta daka tare dacewa 

"Am a genius...." 



Ganin gidan duka is not conducive for him yasa ya shiga wanka ya fito, ko Mai bai Shafa ba kaman yanda ya Saba ya Zauna gaban mirror kaman mace yana Shafa wannan shafa wancan. Black Jean ya saka da white polo ya dauki makullin motanshi ya bar gidan. Straight ya wuce office din mom dinshi Don Karfe biyu yake zuwa daukanta kullum except in da akwai emergency. Yana zuwa ya tarda ta tashi Tana sallah shima masjid dake nan kusa yayi alwallah yayi sallah sannan ya daukota suna kan hanyan zuwa gida yake bata labarin abincin da baba rabi ta dafa and tasteless it is. 

"Rainin hankali né....Bari I will warn her..." Mom dinshi Ta fada amma maimakon yayi ji dadi sai kuma aka samu akasin hakan. Dan tsoki yaja mom dinshi ta kalleshi tare dacewa 

"Eyeballs what's wrong?.." Dan karamin tsoki ya karaja sannan yace

"Don't know mom..kawai am restless..." Kallon mamaki mom dinshi tayi mashi sannan tace

"Ban gane you're restless ba?... Ai restlessness baya zuwa haka nan...sai if there's a reason for that..." Ta fada Tana gyara zaman glasses sake fuskan ta, 

"Nidai momcy bansan am restless ba...kawai nidai ban Jin dadi..." Ya dada atakaice, 

"What's..." Mom dinshi ta bude baki zatayi magana yayi saurin katse ta da cewa

"I don't know mom..." Ya fada. In silence suka isa gida, bayan ta sauka yayi Kai motan parking lot har ya bude mota zai fita sai kuma ya koma ya zauna yayi relaxing with his eyes closed. Zuciyan shi na tafiya wajen da bai sani ba, sannan bai San abinda haka ke nufi ba, he's 29 but has never given his self chance to fall for any body, ko da ya gan yarinyan da tayi mashi daya kura mata Ido sai ya Tsinto aibunta daga nan kuma shikenan but wannan na néman zaman above him. Mata da dama sun nemi hallaka kansu because of him including cousin sisters amma ko kallo basu isheshi ba, kuma the most annoying part har rashin mutunci yake masu Don he remembered wata school mate dinshi a secondary school, babu irin zalunci da bai mata amma yarinyan ta rufe Ido wai shi take so, har zuwa gidan su take, he remembered the last time data azo gidansu, suna tare da su sadeeq, part dinshi ya kaita, he can still see the look of excitement a face dinta Don she was happy yau suhail ya kulata, the nest thing sai clipper ta gani hannunshi, kafin ta ankara ya Kama vail dinta ya cire ya saka clipper ya kwace left hand side hair dinta.  Murmushi yayi tare da juya kanshi,

"Allah yaisa mugu...." Ta fada mashi kafin ta bar gidan crying. Tafi wata bata zo school ba, kullum da gashinta yake zuwa junior section Don ya bata cikin mutane ya dixga ta amma daya gaji ya yarda gashin. Sadeeq was so furious saboda wannan abun to the extent suka rabu da some months kafin su shirya. Ahankali ya fito yana tafiya cikin kasaita ya shiga part din mom dinshi. Hajiya Tana shiga falon ta direct ta shiga kitchen Tana fada

"Wane irin rubbish abinci kuka fadawa dana gidan yau?.." Ta fada sounding so harsh and rude, durkusawa sukayi duka suka gaisheta, bata amsa ba ta sake cewa

"I said me kuka bawa Dana gidan yau?.."  Ta sake tambayan su, 

"Ko so kuke ku kashe min Darin cikina?." Da sauri baba rabi tace

""Aa wallahi...abincin daidai na dafa..." 

"Close your dirty mouth...daidai kika Dafa kuma yake complaining...to hakan kar ya Kara faruwa...kunji ko bakuji ba?..."

"Mun ji!!!." Suka amsa in chorus, kallon su tayi Dayan bayan daya Sannan tace

"Ina Fatima?" Ta fada Tana ya mutse fuska, 

"Tana dakinta..." Baba rabi ta amsa mata, fita tayi daga dakin ta bude next door which is dakin Maryam, yanda tayi banging Kofan yasa Maryam firgita, da sauri tace

"Ina...wuni..." Harara ta balla mata sannan tace

"why baki cikin kitchen wurin sauran masu aikin gidan?.. Or do you think you're better than them?..well for your information you are not up to them to me..Don baki da wani amfani...kuma daga yau kar in kuskura in ganki nan while work is going on...kinji kou?..." Ahankali Maryam ta daga mata kai still sitting, juyawa hajiya tayi ta kata har bakin kofa ta juya still taga Maryam zaune 

"Why are you still sitting..come on get your dirty body out of here..." Ta fada afusace, da sauri ta mike har jikinta na rawa Don ko kadan bata kaunar tashin hankali. Tana fita falo suhail na shiga falon, hajiya tsayawa tayi tare da bin bayan Maryam da harara, haka nan sai suhail ya daure fuska, hannun ta  ta mika mashi ya Kama su hau upstairs tare amma sai ya wuce kaman bai gan hannun ba, bayan shi dake hauwan upstairs ta kalla itama ta hau. Bayan ta ajiye bag dinta Tana cire agogon hannunta ta kalli suhail dake zaune kan three seater tace

"Allah wannan yarinyan is so annoying...tunda tazo gidan nan ban taba ganin Tana aikin komai ba...sai ta wani kwanta kaman wata princess..inshort ko irin gaisuwan da su murja ke zuwa yi min da safe ita batayi...and the most annoying part shine dad Dinka bai yarda a taba ta ba..." Duk surutun da hajiya yake kallon ta kawai suhail yake, sai data Kai aya sannan yace

"Hmmmm..." Juyawa hajiya tayi ta kalleshi tare dacewa

"Hala Baka ji abinda nace ba?.." Cikin kasala yace

"Naji mana...." 

"And all you could say shine hummmm?." Ta fada sounding surprised Don he doesn't sound like her suhail, ahankali yace

"Nifa momcy am hungry,...duk yau banci koma..so let me eat first..." Ya fada yana rufe idanuwanshi, kallon shi hajiya tayi for a moment sannan ta juya ta cigaba da abinda take.  

Wajen Karfe uku lunch ya hadu, Maryam zama tayi Tana kallon yanda suke Kai kawo, in ta dauki wani Abu zatayi sai baba rabi ta hanata, she really wants to help duk da dafa abinci baya cikin abinda ta iya kuma she don't want to learn Don cooking bai cikin hobby  dinta ko kadan, 

"Why should I spend hours preparing food while I can just walk into a restaurant and eat what ever I choose to..." Take fadawa kanta duk sanda akayi maganar dafa abinci ko kuma friends dinta sukace su je catering school. Kallon su kawai take har aka gama lunch aka jera a dining, upstairs baba rabi ta hau Ta fadawa ha jiya lunch is ready, banza tayi daita kaman bataji ba ta kalli suhail tace

"Eyeballs muje kaci abincin..." Ta fada mashi, cikin kasala ya mike itama mikewa tayi suka sauko downstairs tare. 


Cikin katuwar tray su murja suka suka abincin  su kaman yanda suka saba, Maryam zama tayi ta kurawa abincin Ido Tana kallon jelofdin daya sha cray fish tayi Tana tunanin weight dinta Don ko kadan batason kiba, 

"Ki sauko muci abincin mana" Binto ta fada mata, 

"Na...ko..shi.." Ta amsa mata wearing a smile, kallon juna sukayi sannan baba rabi tace

"Ban gane kin koshi ba...maza ki sauko kici abinci..." Ta umarce ta, murmushi ta sake saki tace

"Aa..na..sha...ice cream..am ok..." Ta fada mata, 

"Ikon Allah...wai me kike ci?.. Din tunda kika shigo gidan nan ban taba ganin kinci komai ba...sai ganye..." Inji asabe, 

"Fall in!!!" Sukaji daga falo, da sauri suka saki abinci suka Kama hanyan falo, itama sauka tayi daga stool tabi bayansu. Ahankali ta daga Kai ta kalli  hajiya da suhail, kawai sai suka hada Ido da Suhail, 

"Kun ajiye mana abinci kun koma bakuyi serving ba..to uwayenku zasuyi mana serving?.." Inji hajiya, suhail kallon hannunsu dake maiko yayi yace

"Ai da gani har sun fara ci mu masu gidan bamu ci ba...." Ya fada yana bin hannunsu da kallo Dayan bayan daya amma hannun Maryam ba komai,murja ce ta karaso domin serving dinsu sai suhail ya watsa mata kallon banza tare da cewa

"Wannan dirty hand din zaki zubamin abinci?... Get the fuck out of my sight..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta ja baya

"You..." Ya nuna Maryam Sannan tace

"Serve us..." Ya fada atakaice. Ba musu ta zo ta ajiye  plates gaban su sannan ta zuba masu abinci kowanne spoon uku, kallon juna hajiya da suhail sukayi Don abincin tamkar zaa bawa baby, coslow ta zuba a gefen abinci shima not much. Still kallon juna suka tsake yi, suhail fashewa yayi da dariya yana kallon Dan abincin dake cikin kwano 

"Amma wannan yarinyan anyi matsiyaciya...wato inda kika fito babu abinci...tou albishirinki...muna ci mu koshi gidan nan...so pls zubamin abinci...." Inji hajiya, shi kam suhail Banda dariya babu abinda yake, Don daya kalli abincin dake gabanshi kaman na Mage sai ya sake fashewa da dariya, su murja sai kallon juna suke sannan suna kallon suhail Don suna iya rantsuwa basu taba ganin dariyan shi ba sai yau,Maryam Kara zuba abincin tayi wannan Karin da yawa, sannan ta koma baya inda su asabe ke tsaye. Hannu yayi masu alaman su bar wajen. Kitchen suka koma suka cigaba da cin abincin su while Maryam ta koma mazaunin ta Tana kallon yanda suka maida hankali suna cin abinci kaman ba Yanzu aka gama zaginsu ba.



Suhail kurawa abincin gabanshi Ido yayi bai ko,dauki cokali ba balle yaci, sai da hajiya tayi spoon biyu sannan ta lura da suhail dake kallon abincin gabanshi kaman mirror 

"Eyeballs why are you not eating...kuma kace kana Jin yunwa...." Ta fada mashi ahankali, cikin kasala ya dauki spoon ya debi abincin ya Kai bakinshi, bata fuska yayi ya daure ya hadiye tare dacewa 

"Mommy this food still taste awful..." Ya fada yana bata fuska,  kallon shi hajiya tayi for a few seconds sannan ta Kai abincin bakinta Tana taunawa ahankali,

"Baby the food is okay.. Kodai you are sick?..." Ahankali ya girgiza mata Kai

"Then maybe Baka da apetite.." Bai Kara cewa komai ba ya ja kujera baya ya mike, kallon shi kawai tayi yana tafiya, har yayi hanyan fita sai kuma ya koma baya ya Kama hanyan kitchen..



One love 💙💜💛❤💛10💚💜💛💙❤

Wulakanci dodone....

💜💛❤💚💙






® zuwairat (ummumaryam)






1⃣0⃣




👻👻👻👻👻👻👻👻👻👻👻👻 ghost mode activated. They want me dead before my time. Ina godiya ga wanda ya rubuta don ko ba komai nasha adua. Mutuwan is compulsory we're all waiting for time.


"Ina zaka kuma?.." Hajiya Ta tambayeshi 

"Inason ruwa..." Ya amsa mata while heading for the kitchen,

"Ga ruwa nan .." Hajiya Ta fada Tana kallon bottle water dake kan dining,

"I want cool one..." Ya amsa mata, Dan taba ruwan tayi taga it's very cold amma bata Kara cewa komai ba, shiga kitchen din yayi ya hangi Maryam dake zaune Tana kallon su murja dake cin abincin kaman ba gobe, tsoki yaja yana cewa

"Irritating creatures...wata rana dole ku bar gidan nan...Don bazaku dawwama anan ba...." Ya fada yana nufan fridge, binto na zaune kusa da fridge din ya daga kafa ya harbeta tare da cewa

"Come on move your skinny self from here...", da sauri binto ta matsa daga wurin giving him enough distance, fridge ya bude ya tsaya yana kallon Kayan sha dake ciki, rufewa yayi ya bude na sama yaga still drinks né, cikin kasaita ya taka zuwa Dayan fridge din yaga duk Kayan Miya né da sauran kayan amfani wajen Miya, tsoki yaja ya rufe, Maryam dake zaune Tana kallon shi taga zai juyo tayi saurin dauke kanta ta koma kallon su murja kaman bata San yana wajen ba, 

"Ke..!.." Ya fada yana kallon ta, ahankali ta daga Kai ta kalleshi, suna hada Ido yaji tsigan jikinshi na tashi, daure fuska yayi yace

"Come and give me something to drink..." Ya fada mata without looking at her, mikewa tayi ta bude fridge ta dauko mashi hollandia milk sannan ta dauko cup ta zuba mashi kadan ta mika mashi, tsaya  kallon Dan drink din yayi yace

"Ke da alaman marowaciya ce ke...take a like at the drink da kika zuba min..in my own house...in gidan ki ko badawa bazakiyi ba..." Ya fada cikin tsiwa, cika cup din Maryam tayi Tana sauraron abinda yake cewa bai San she don't eat or drink much ba, shi yasa ko friends suka zo gidanta she make them serve themselves. Amsan cup din yayi hannun su suka hadu yayi saurin sakin hannunta tare da cup din, ji kake tassss, da sauri baba da sauran aikin suka taso Don ganin abinda ke faruwa, haka hajiya dake cin abinci a falo ta mike da sauri ta shigo kitchen Tana

"What the hell is happening..." Tumbler ta ganin tarwatse a kasa, suhail daya kurawa Maryam Ido ta kalla tare da juya shi Tana kallon jikinshi to make sure nothing happens to her eyeballs, 

"Ubanwa ya fasa min tumbler?.." Ta fada afusace, cikin rawan murya Maryam tace

"Ni...ce...sorr...." Bata Ida sorry din ba hajiya ta dauke ta da Mari, har sai da ta fadi kasa,   Ko motsi bata iya yi Don ji tayi komai nata ya tsaya in an instant, suhail tsayawa yayi yana kallon ta from head to toes, baba rabi da sauran yan aikin sukayi kanta, lokaci daya ta saki Kara tare da Kira daddy da karfi sannan ta fara kuka daga inda take kwance, tunda suhail yake bai taba Jin mom din shi tayi wani Abu Wanda shi ya gani bata kyauta ba Don they're bird of the same feather they flock together amma yau sai yaji abinda tayi ta bata mashi rai beyond words, 

"Daddy...daddy..am not staying here..." Maryam ta fada cikin matsanacin  kuka, Banda kallon ta babu abinda suhail yake, just like that he's feeling her pain then yaji yanda take cewa she's not staying here, ji yayi mom dinshi ta Kama mashi hannu, har falo ta rike mashi hannu, farat saya ya fixgehannunshi daga nata tare dacewa 

"Mom what did you do that for?..." Ya fada yana nuna hanyan kitchen Fuskanshi kaman bai taba dariya ba, mom dinshi tsaya kallon reaction dinshi tayi Tana mamakin is this her suhail Don ta sha cin uban masu aiki kuma ya taimaka mata amma yau ya daure fuska yana tambayanta 

"Is not as if it's her fault...sannan  nothing happened to me..." Ya fada afusace, zata bude baki tayi magana ya hau upstairs da gudu ya dauko car keys dinshi , hajiya kasa tafiya tayi tabi bayanshi da kallo, Tana tsaye ajen ya sake saukowa da gudu ya bar falo. Motanshi ya fige shi ya bar gidan a guje. 

Hakuri baba rabi ta dinga bawa Maryam amma sai kuka take Tana dirza kafanta da kasa, wayanta ne ya fara ringing luckily alhaji Ismail né datayi storing da second dad, har ta gama ringing baa dauka ba sai da ya Kara Kira for the second time sannan baba rabi tayi piçking, Ana picking alhaji yaji kuka Maryam, 

"Lafiya?.." Ya tambaya cikin tashin hankali Don ji yayi kujeran dayake zaune sama tayi mashi zafi saboda tashin hankali, baba rabi naji muryanshi ta gane alhaji né, sallama tayi mashi amma bai amsa ba yace

"nace meke faruwa?.. Ba Maryam...aa Fatima ke kuka ba?.." Ya tambayeta cikin tashin hankali, 

"Hajiya ta doketa..." Inji baba rabi, alhaji bai Kara cewa komai ba ya kashe wayanshi, har ya fara dailing number hajiya sai kuma ya kashe wayan ya mike, Salman ya kwalawa Kira suka Kama hanyan gida. Yafi hour kafin ya dawo gida amma Maryam na zaune inda take babu abinda take sai kuka har muryanta bai fita, fuskanta ya kumbura sosai sannan kanta sai zafi yake, duk yanda baba rabi tayi kokarin hanata ki tayi, Don tunda suhail ke zaluntar ta na yau yafi su duka, Don Tana marinta taji kaman an sakar mata wata irin Karfe a fuska.  


Part din hajiya alhaji ya wuce direct, yana shiga ya fara Jin nishn Maryam daga kitchen, da sauri ya shiga kitchen din, Maryam ya gani zaune fuskanta kaman ba nata ba, yan aikin dake kanta sukayi saurin mikewa Don bashi daman zuwa kusa daita, inda take zaune ya durkusa ya daga jaw dinta yana kallon face dinta, yatsu biyar yagani kwance a face dinta, 

"Pls...tell my daddy...to take...me out of here...." Ta fada Tana shessheka kaman wacce ta shekara Tana kuka, kallon ta ya tsaya yayi tare da Kama hannunta 

"Am sorry daughter..pls am begging unbehalve of my family...pls ki yafe masu...they don't know who you are...pls forgive them..." Ya fada sounding out of words Don yasan inda ubanta zai ganta a haka da babu abinda zai hanashi jailing entire families dinshi, still cikin kuka tace

"Pls I want to go..."  Shuru alhaji yayi yana kallon yanda hawaye ke fita daga eyes dinta, hannu yasa ya goge face dinta,

"Your body is hot..." Ya fada yana dafa goshinta, bata ce komai ba sai kuka take, hannu yasa cikin aljihunshi  ya dauko wayanshi yayi dailing number family doctor ya fada mashi yana da patient ya so ya dubata. Mikar daita tsaye yayi ya Kama mata hannu har dakinta, da kanshi ya shiga bathroom dinta ya hada mata ruwan wanka cikin ranshi yana tunanin me zaiyi wa hajiya da zai Rama abinda tayiwa Maryam Don Maryam is more precious to him than diamond and golds, Tana shiga wanka ya fito daga dakin,  falo ya koma ya zauna yana karkada kafafawa, he's so,lost in thoughts. Bayan kaman minti talatin ya koma dak n, lokacin Maryam ta fito daga bathroom ta Chanza Kaya ta koma ta kwanta, bakin gadonta ya zauna ya Kama hannunta ya rike cikin nashi

"Daughter ke amana ce a gareni...I promise dad dinki zan kula dake..and am going to keep that promise...zan samo wacce zata kula dake...but pls don't tell your daddy about this...kinji'pls.." Ahankali Maryam ta daga mashi Kai Tana kifta idanuwa kaman Mai Jin bacci.

"That's my daughter...just give me two weeks...komai zai yi daidai..but before then be patient just for me.." 

"Ok sir..." Ta fada ahankali , murmushi ya saki tare da Kama cheek dinta before saying 

"That's my boss..thank you for being compassionate...kinci abinci?.."Ahankali ta girgiza mashi Kai tare dacewa 

"Salman bought me an ice cream..nasha...am okay..." 

"I will get you more..."  Ya fada sannan ya mike yana cewa

"Am coming..." Hannunta ya saki ya bar dakin, sai lokacin ya hau upstairs, hajiya na zaune sai chatting take, yanayin da alhaji ya shigo dakin ya bata tsoro Don tunda take da shi bata taba ganin yanayin shi haka ba, gaidashi take amma bai amsa ba yace

"Me wannan yarinyan tayi maki kika yi mata irin wannan hukunci?...tsakanin ki da Allah kin kyauta kenan.." Ya fada sounding a little bit normal kaman he's not so mad, 

"Yo alhaji sai in kyaleta ta kashe min tumblr danayi ordering daga China?... Ai ko yarana basu isa su lalata min Abu ba balle ita...." Ta fada in I don't care manner, 

"Ok shikenan...I have been telling you wannan yarinyan amana ce a gareni Amman baki so in ci jarabawan da aka bani...no problem..I will look for someone that will help,me win..." Ya fada atakaice sannan ya bar dakin, surprise look né kwance kan fuskan hajiya din bata gane last statement dinshi ba. Yana fita Doctor na isowa, dakin Maryam data fara bacci suka shiga, ahankali ta bude idanuwanta ta kalleshi tare da sakin murmushi, nan Doctor ya dubata ya rubuta mata drugs. Tare da doctor suka fita ya mikawa Salman prescription da doctor yayi sannan ya wuce part dinshi. Falon shi ya zauna tareda cire hulan kanshi. Wayanshi ya dauka yayi dailing number mom dinshi dayake Tana nan da ranta, bayan sun gaisa alhaji yace

"Inna..batun salima...nace kin taba yi mata maganar kinason in aureta?" Ya tambayi mom dinshi,  

"Ya zaayi in fada mata tunda kullum cewa kake Baka da raayin mata biyu?.."  Inji inna, Dan Shafa Kai alhaji yayi sannan yace

"Inna...Yanzu inaso...kuma Dan Allah inason kiyi mata maganar yau ko zuwa gobe né Don in ta amince nan da sati biyu a gama komai..." Nan da nan inna ta fara guda, sallaman hajiya daya ji yasa ya katse wayan. 



Salima wata cousin sister dinshi da bazata wuce yar 36 ba, mijinta ya rasu ya barta da yara hudu, tun rasuwan mijinta innan alhaji ke cewa ya aureta Don ya tayata rike marayunta amma sai yace bashi da raayin mata biyu. Yanzu kimani shekara 6 ke win da rasuwan mijinta kuma bata sake aure ba Tana zaune a Dan karamin gidan da mijinta ya bar masu kafin rasuwanshi. Tana da kyau iya nata Don wasu masu San kyau ba, kawai da sunga mutum fari dogo sai ace ai yana da kyau, meanwhile da akwai manyan kyau sanna da akwai kananun kyau. Bathroom hajiya ta wuce ta hada mashi ruwan wanka,

"My alhaji ruwan wankan is ready..." Ta fada mashi, ba musu ya mike amma Fuskanshi Sam babu walwala. Kokarin cire mashi Kaya tayi as usual amma ya Dan ture hannunta ya shige bathroom. 



Suhail bai tsaya koina ba sai gidan su sadeeq, ,Mai gadi na bude mashi kofa yayi parking, ko part din iyayen sadeeq bai je ba ya shiga dakinshi dake kusa da gate, kulle take amma duk sun San inda dukkansu ke ajiye keys dinsu, karkashin carpet ya da dauko key ya bude ya shiga, bedroom ya wuce ya jefa kanshi kan katuwar katifa dake kasan dakin. Tunanin Maryam kawai yake da statement dinta wai she's not staying here, yayi mamakin Jin irin wannan fluent English a bakinta sannan she's calling her daddy, from abinda mom dinshi ta fada mashi tace she's from jos Sannan daddy dinta ya rasu. Yana nan kwance har sadeeq ya dawo daga aiki, yana zuwa ya tarda dakin shi bude, bai tsaya bata rai ko waye ba Don yasan cikin friends né, yana shiga bedroom ya hangi suhail kwance yayi rub da ciki hannunshi biyu rungume da pillow,

"Mr lazy Ashe kaine..." Ya fada mashi, ko daga Kai suhail baiyi ba ya cigaba da karkada legs ahankali which indicates he's not sleeping, zama sadeeq yayi gefen katifan tare da dafa bayanshi, da sauri suhail yasa hannu ya buge hannunshi daga cikin shi kaman wani Kaya,

"Guy meke damunka?.. You looked disturbed..." Ya fada mashi yana kallon yanda yake kada kafa ahankali 

"Suhail..." Ya Kira shi, 

"Dan Allah Dan Annabi ka rabu Dani...ni Kaina ban San abinda ke damuna ba...kawai I need to be left alone shiyasa na so nan gidan...in kuma kana ganin hakan it's not possible sai in tashi in bar maka gida..." Suhail ya fada kaman zaiyi kuka, hannu sadeeq ya daga sama  tare dacewa 

"Ok..sorry...just relax..." Ya dada mashi. Mikewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya sake Kaya sannan ya fita daga daki. Part din iyayenshi yaje yaci abinci sannan ya dawo dakin ya dauko car keys dinshi ya bar gidan without saying a word to suhail Don ya San halin shi. 



Bayan Salman ya kawo drugs alhaji ya bar hajiya nan ciki ya fita ya bashi atm tare dacewa 

"Kaje kasuwa ka samo min bedside fridge sai drinks masu kyau. In ka kawo ka mikawa baba rabi sannan ya Kai fridge din daki Fatima..." Ya umarce shi, da sauri Salman ya amshi atm card dinshi amma sai kishi yake Don gani yake kilan da akwai wani Abu tsakanin alhaji da Maryam Don yanda yake maganar kullum is becoming unbearable. Ciki alhaji ya koma lokacin hajiya ta shirya mashi dining domin yaci abinci, yana zama wayanshi ta fara ringing, inna ya gani, yana piçking yace

"Inna Bari abinci zanci..anjuma zamuyi magana..." Tun daga nan hankalin hajiya ya fara tashi Don tasan inna bata kaunar ta ko miskala zaratin sannan Yanzu da take ganin alhaji is mad at her suna Sirri da inna tasan da akwai matsala

"Alhaji..." Ta kirashi, ahankali ya daga eyes dinshi ya kalleta without saying a word, 

"In abinda na yiwa wannan yarinyan ya bata maka rai kayi hakuri..." Ta fada cikin sanyinmurya, 

"Ok..." Kawai ya fada atakaice yacigaba da cin abincin shi. 


Around 5:30 Salman ya dawo daga kasuwa da Kayan da alhaji ya bashi sautu, bai je wurin alhaji ba  ya wuce main part dasu, nan ya nemi dakin Maryam bayan ya mikawa baba rabi manyan ledan dake dauke da Kayan sha kala kala. Tare suka shiga dakin da baba rabi, har lokacin Maryam Tana bacci Amman suna bude kofa ta bude idanuwanta, Kayan data gani hannunsu yasa ta mike zaune, face dinta Salman ya kurawa Ido har yana kusa faduwa da fridge daya dauko

"Sannu yar nan..Allah ya saka maki..." Inji baba rabi, daga weak eyes Maryam tayi ta kalleta tare da sakin murmushi, fita baba rabi tayi bayanta ajiye Kayan cikin Leda, shima Salman ajiye fridge yayi yana Fiddo ta daga cikin kwalin ta amma Maryam yake kallon, 

"What happened..." Ya tambayeta yana cire Leda daga jikin fridge, shuru Maryam tayi bata amsa mashi ba, kallon yayi yace

"Pls tell me what happened to you?.." Ya sake tambayan ta,

"Nothing..." Ta amsa mashi atakaice, bai Kara cewa komai ba ya gama hada fridge din ya ajiye Kayan da ya sayo ciki har suka rage ya ajiye mata saman fridge sannan ya mike ya dawo kusa da inda take zaune yace

"Friend your face look dull...meke damunki?.." Ya sake tambayan ta cikin kulawa, Dan hararanshi tayi Tana cewa

"Stop asking ...I said nothing..." Ta fada Tana turo mashi baki. Kallon Kofan yayi Don ya tabbatar babu Mai shigowa sannan yace

"Dazun na tambayeki abinda suhail keyi maki kince nothing...Yanzu ma your eyes are swollen na tambayeki abinda ke damunki kince nothing...haka friends suke daman?.." Ya fada gwani ban tausayi, daga eyes tayi ta kalleshi for just a moment sannan tace

"But friends respect each other's privacy..." Ahankali ya daga mata Kai, bai Kara cewa komai ba ya mike,  sai da yayi step biyu sannan yace

"Ko me ake maki kiyi hakuri...we're have been bearing too...wata rana sai labari..." Ya fada sannan ya bar dakin,murmushi Maryam ta saki sannan ta koma ta kwanta. 


Bayan alhaji ya bawa Maryam drugs ta sha ya wuce masjid, Akan hanya yayi maganar salima da innan shi. Bai the way he was talking komai zai zama possible.


Bayan sallah ishai Maryam tayi wanka tayyi sallah ta kwanta without eating anything, wayanta yayi ringing, picking tayi alhaji ya tambayeta if there's anything she needs amma Ta amsa mashi da aa. 

Ita kuma hajiya sai nan nan take da alhaji dayake tasan ta bata mashi rai kuma bai nuna mata komai ba but he's not going back on what he has decided. 

Hajiya sai trying number suhail take amma bai piçking, zama tayi Tana tunanin what is he mad for?, gani take he's being angry for no reason at all.

Har Karfe Tara na dare suhail da kwance dakin sadeeq, kuma har lokacin baifi komai ba, lokacin daya tashi yayi sallah sai yaji kaman iska na kada shi, fridge dake dakin ya bude yaga babu komai, tsoki yaja ya fita waje ya dauki motanshi ya Kama hanyan gida. Wani su ya joint ya tsaya ya sayi kadan ya ajiye yana tuki yana ci, shima ji yayi kaman yana cin tsaki amma bai daina ci ba ya dage sai tauna yake kaman yana taunar paper. Yana Ida gida ya bar sauran cikin mota ya fito yana tafiya kaman wani patient da akayi discharging daga hospital. Part dinshi ya shiga ya zauna ya daga Kai ya kalli agogon dakin yaga goma saura, mikewa yayi ya fita waje, tsakar gidan ya tsaya yana kalle kalle, babu kowa sai security dake duty post dinshi, waist dinshi ya rike da hannu biyu yayi tsaye ya kalli nan ya kalli chan

"What's wrong with me?.." Shine abinda ya fada under his breath, ji yake nothing matters to him now, nothing at all. He's so depressed for no reason, Abu daya kawai ke yawo a ranshi itace Fatima, yana mamakin yanda take hawan yawo cikin brain dinshi.

"Get out of my head....and my heart..." Ya fada yana cije lebe, shuru yayi for a while kaman Mai tunani sai ya Kama Hanyan main part. Tsaye yayi cikin falon da babu motsin komai, har ya Kama hanyan upstairs sai kuma ya tsaya ya koma bakin Kofan Maryam, hannu yasa sai kuma yayi saurin cire hannunshi 

"Allah ya sauwake,..." Ya fadawa kanshi, juyawa yayi ya bar wajen sai kuma ya sake dawowa bakin Kofan kaman wani Mara hankali yanda yake acting. For the fifth time ya dawo bakin Kofan, hannu yasa ya murda ya bude idanuwanshi lumshe, amma kafin ya shiga dakin sai ya daure fuska kaman ba shi ba. Maryam bata San an bude kofa saboda drugs da tasha, kaman Barawo ya shiga dakin, hasken dakin na kunne so yana ganin face dinta daga inda yake tsaye, hannunta daya kan cikin ta sai daya wurin kanta, Tana sanye da Riga da wando na bacci masu kauri, sanyin dakin yaji da yawa, ahankali ya taka yaje wajen ac ya rage sannan ya koma baya ya tsaya yana kallon ta kaman mirro, da sauri ya girgiza Kai ya juya ya bar dakin ya jawo Kofan har ta danyi Kara Wanda yasa Maryam juyawa. 


Komawa kitchen ya shiga ya dauki juice data bashi da rana ya kafa Kai ya shanye sannan ya koma part dinshi. Atakaice yanda ya ga rana haka ya ga dare  Don ko,kadan bacci bai dauke shi ba, sai bayan ya dawo daga sallan asuba yaji bacci na néman daukanshi, mikewa yayi ya kulle kofanshi tare da kashe wayanshi ya shiga cikin blanket, nan take bacci yayi gaba dashi.

      Da wuri alhaji da Salman suka fita dayake katsina zashi amma bai fadawa hajiya komai ba. Itama around 8 ta shirya Don zuwa wajen aiki taga babu suhail, wayanshi ta Kira taji switch off, har bakin Kofan shi taji tayi knocking tajishi kulle, dole ta taka da kafa zuwa bakin titi ta nemi abun hawa ta hau ta tafi hospital Don ko,kadan batason tuki da Kanta, she's use to sitting beside her eyeballs while he drives.

Lafiya lau Maryam ta tashi kaman nothing happens, sallah tayi ta bude fridge ta sha juice ta koma tayi relaxing, number dad dinta tayi dailing ya dinga ringing amma no response.  Wanka ta shiga ta fito tare da saka doguwar gown, kitchen ta shiga taga su asabe suna aikinsu as usual Don tunda ta shigo gidan kullum cikin aiki suke kaman agogo.  

"Kun...gaida...hajiya?" Ta tambayesu, 

"Ki kwantar da hankalinki ta tafi aiki...." Baba rabi ta fada mata,  

"An...yi..aikin...part..din...shi?.." Ta sake tambayan su Don Yanzu she have decided to be careful, 

"Naje amma Kofan rufe kuma bai yarda a kwankwasa mashi kofa ba...." Inji binto, sai lokacin taji ta free ta zauna. Tana nan zaune har Karfe tara da rabi Amman ba a zo daukanta domin zuwa islamiyya ba, and she feels bored waya ta dauka ta Kira alhaji Ismail, 

"Daughter kin tashi kou?.."

"Yes...good morning..." Ta fada cikin sanyinmurya 

"Morning ma'am...how was your night?..."

"Fine sir...am I not going to islamiyya today?" Ta tambayeshi,

"No ma'am...ki zauna gida yau since you're on drugs...." 

"Sir pls stop calling me ma'am...and am ok now..." Ta fada mashi kaman zatayi kuka

"Ai ke ma'am ce...dole in Kira ki da hakan...well ki huta da yamma sai kije tunda mu yi tafiya da Salman..." 

"Ok..." 

"Kinci abinci?.." Ya sake tambayan ta

" eh..."

"Me kika ci?.."

"I drank juice...." 

"Juice ba abinci bane...tell me me kike so kici""" ya fada kaman wani yaro, Maryam cire wayan tayi daga kunnenta ta kalli wayan sanna ta maida kunnenta 

"Meatballs...or hot chocolate..." Dariya alhaji yayi tare dacewa

"Ai ni ban San abubuwan da kika lissafa...da Nama ake ball din ko da bournvita ake hot chocolate din..." Ya fada ciki dariya, itama Maryam dariya tayi 

"Give baba rabi the phone..." Ya umarce ta, mikewa tayi daga inda take zaune ta mikawa baba rabi wayan, nan alhaji ya fada mata suyi wa Maryam yamball amma kar su saka doya suyi na Nama zalla. Sallama sukayi ya kashe wayanshi. 


Gogan bai farka ba sai Karfe kusan goma, mika yayi tare da salatin Annabi, bathroom ya shiga ya fito sanye da jallabiya, bakin gado ya zauna kaman minti biyar sannan ya mike ya Kama hanyan main falo still wearing jallabiya, yana shiga falo yaji kamshi ta koina, lokacin sun gama meatballs, sunyi rolling kanana yanda za a ci at a time. Cikin wani nice plate suka zubawa Maryam sai ta dauko toothpick Tana daukan daya ta saka baki, direct kitchen suhail ya shiga, nan ya hangi abinda ke gaban Maryam, ita kam bata ganshi ba ta dauko zata Kai bakinta sai ji tayi ance

"Ke!..." Ya daka mata tsawa, da sauri dukkan su suka juya zuwa bakin kofa, shiga kitchen din yayi ya yana cewa

"Uban me kuke?..." Ya fada yana nufan Maryam, mikewa tayi tsaye Tana ja da baya, gaban plate din ya tsaya yana kallon abinda ke cikin plate din Don tunda yake bai taba ganin meatballs ba, same toothpick ya dauka ya dauki daya ya Kai daya bakinshi, duk sun zuba mashi ido suna kallon ikon Allah, wani dadi yaji har cikin system dinshi, daure fuska yayi yace

"Wato kunga babu kowa gidan shine kuke ya da kuka gan dama kou..." Ya fada yana tauna na an dake cikin bakin shi, dukkan su sadda Kai kasa sukayi saboda babu abinda yake basu sai dariya, plate din ya dauka, sannan yace 

"Ke follow me....." Ya fada mata yana juyawa da plate din a hannunshi, bayanshi tabi da harara tare da bin shi. Kafin ya Kai falo ya Kara Kai wata meatball cikin bakinshi, yana ci yana lumshe Ido. Haka suka is a part dinshi. Zama  yayi kan kujera dining  ita kuma Maryam tayi tsaye, ajiye plate din yayi tare dacewa

"Feed me..."

    




Pls zakujini silent kwana biyu thanks....





One love 💚💜❤💛❤


Copied By

YAYA HAYAT 

        (admin 

   Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

Cool novel, makeup and kitchen1⃣

                   AND 

Cool novel, makeup and kitchen2⃣) 


      WHATSAPP NO:

   +2347039625239





Post a Comment

0 Comments