WUKA A MAKOSHI cmplt

 [9:06PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪  WUKA AMAKOSHI1⃣🔪🔪🔪🔪🔪🔪






Writter by 

Maman sadeeq





GARGDI

Wannan  littafin kirkirarran labarine banyarda kowa yajuyamani shiba kotakowace siga,duk wanda yayi hakan to bazan yafemashiba.



FARKON LABARI 




"Tafiya takeyi cikin sauri  harbataganin gabanta sosai,hannunta daukeda bokitin kunun aya wanda take sayarwa,tadade tana yawo amma batasaida koda rabibane,gamatsananciyar yunwar datake kwakularta 


Cikin sauri tacigaba datafiyarta burinta kawai taganta agida kotasamu abinda zatasakawa cikinta,


Sauritakeyi tatsallaka titi  saidatakai tsakiyar titi bataluraba damotar da take tunkarotaba saijitayi anbugi bolitin dake hannunta itama anyi wurgida ita gefe, 


Dasauri tamike tsaye ganin yamda kunun ayarta yake tagangarawa cikin kwalbatin dake gefen titi,sannan tamaida idanunta kan maimotarda yakadeta yanacikin motarshi azaune bashi daniyyar fitowa balle yabata hakuri,shitakaicinema ya isheshi na batamashi lokacindatayi


Bokitinta tadauka tafara tafiya ahankali kamar wacce kwai yafashemata aciki,

Cikin sauri yasha gabanta  tareda fadin malama kewace irin dabbace dakikiya dazakizowa mutane bisa titi kina abindakikagadama to wlh dakade kinayi toda nakade banza dan nni banida asara. 

Yanagama fadin haka yajuya batare dayasake koda kallontaba yahaye motarshi yatafi.

Kukane taji yakubcemata  tajuya baya taga irin mutanen dasuke kallonta taimaza tashare hawayenta takama hanyargida



Tana isa gida ta iske ummu tana sharar tsakar gida dagudu zuhra tanifeta tafada kanta tacigaba da risgar kikanta 


Ummuce tadago kanta tareda tambayarta ke lafiya meakayi maki kike kuka kowani ydakeki


Cikin kuka tagirgiza kanta alamun a ah ummu tace to meakayi maki, dakyar ummu tasamu tadaina kukan sannan tayimata bayani abinda yafaru,


Dukdaran ummu yabaci daabinda yafaru hakanan ta danne talallashi diyarta,


Zuhra tace kuma ummu yazamuyi da kunun ayar dayazube? Ummu tace karki damu zuhra allah shizaikara kawo mana wani jarin kinji,kaitadaga sama sannan tatashi tashiga kicin tadauko abincinta tafara ci,

Ummu kuma tacigaba da shararta


Sallama tarunkaji tundaga zauren gidan dagowar dazatayi taga anshigo da mijinta arurruke dasauri tasaki tsintsiar hannunta tasan ciwon mijintane yatashi tabude dakinshi sukashigadashi suka kwantar, 

Bayani sukema ummu akan abinda sukaga yayi amma hankalinta baya wajansu,tunaninta yafi tafiya akan indazatasamu kudin kaimijinnata asibiti dominkuwa idan harciwon yatashi asibitine kadai kan dantaimaka domin samun salama,saidai tarasa indaxatasamu kudin kaishi asibitin saboda abin yazamemasu jiki,harsunsan adadin kudin dazaabukata dag garesu idansundangano da asibitin,


Allah yabashi lfy yakuma tokari kafada".hakataji mutanen dasukakawoshi sunyimashi adduar samun lfy


Tayi karfin hali tace ameen angode allah yasaka da alkairi

Sukafita gabadaya suka kewayeshi yanadaga kwance zuhra takamo hannunshi tana kuka saidai takada cewa  komai


Mubarak yace "sannu baba",

Tsananin ciwo baibarshi yaamsaba 

Hamza yace ummu maizai hana mukai baba asibiti?

Saiyanzu hankalinsu yadawo sukatuna da wani asibiti,mubarak yace bari intaro dan adaidaita saimu tafi 

"zuhra tace mubarak bataro dan adaidaitabanematsalaba kudindazaabukata awajanmune matsala",.


Gabadaya saijikinsu yayi sanyi sukayi sororo ummu tace " zuhra daukomin hijabina inje wajansu innarsu sani

Tadauko hijabin takawomata,

Dasallamarta tashiga gidan innarsu sani ta amshe tareda fadin "lafiya aisha?".


Ummu tace dadai sauki inna, babansu zuhrane babu lfy shine nazo ki aramin dubu biyar dan allah idan daakwai""innatace subhanallahi jikin dai aisha?

Ummu tace wlh ko".

Inna tatashi tashiga daki ta dauko dubu biyar takawowa ummu, cikin jindadi ummu tadan sunkuya takarbi kudin tayi godia,.

Cikin minti talatin suka isa asibitin koyarwa na aminu kano,ambashi taimakon gaggawa  cikin ikon allah yafaradawowa hayyacinshi,

Bayan allurai daruwa daaka jona mashi ankuma rubuta magani mai yar tsada har na dubu biyar da dari bakwai gashi duka kudin dubu biyarne acikima suka fidda kudin adaidaita,

Kwana daya biyu baasayiba magani likita yasake fadamasu  asayi maganin dayarubuta masu,ummu tace zaasiya sai in har sunkoma gida saboda kudin dake hannunsu bazasu isaba likitan yace susayi koda biyune daga cikin biyar din inyaso sukakoma gida saisu sayi sauran


Kwana bakwai yamurmure yasoma fita indayake kwadago, 

Wata yacika yadauko albashinshi  nadubu bakwai yadauki dubu daya yabaiwa ummu sauran dubu shidan taware dubu biyar din innarsu sani tanemi izinin ahiga gidan taje takaimata ammatace bazata karbaba harga allah kyauta tabasu takoma totoshe wata kafar 

Ummu tace amma inna anahaka wataran aibama dawoba

Inna tace karkidamu aisha aizaman tare kenan 

Ummu tayi godiya sosai tadawo tafadama maigidanta yandasukayi  da inna murmushi yayi tare dafadin allah yayiwa wadannan mutwnen albarka domin koni sun mayemani gurbin yan uwana badan narasasuba ina dayakinin aisha inna da mijinta zasurukemani yayana ayadda nake da tabbas akan inna da mijinta banida tabbas akan salisu da rabi u sudasukazama tilas dina amma babu komai haka rayuwa tagada allah yasa mudace 


Tabbas ummu tanasan mijinta wanda yazamemata uwa da uba,hasalima halayyarsa ta jaraayinta fatanta daya ubangiji yajamata daranshi saidai tasan jinkirin mutum aduniya shine rashin gabatowar lokacinsa dan haka takejin duk ranar datawayi gari babu mijinta aduniya karshe itama barin duniyar zatayi 


Kai bata fatan ganin wannan bakarrana maitareda da bakaken abubuwa,










Maman sadeeq

[9:08PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪2⃣


Na 

Maman sadeeq





"Tarin takardune agabanshi yatasasu gaba yana kallo amma azahiri hankalinshi yatafi waniguri, idonshine kawai akan takardun amma basuyake kalloba 

Tunda abinnan yafaru yakasa mabcewa da fuskar yarinyar dukda ba itace irin ajinsaba,kasancewar babu wayewa atareda ita saidai tana daabu daya zuwa biu wanda hartake fusgarshi dasu abunadayadai allah yayishi mutumne maisan kyakyawar mace wadda taamsa sunankyau 

Sannan farar fata duka yarinyarnan tahadasu 

Ayanzu nadama yakeyiakan abinda yayimata duk da dai itace batada gaskiya

Amma dazai yi saar ganinta ayanzu tozai iya bintavharma yabiyata asarar dayayimatavalokacin daabin yafaru,

Bacin kyanta dasai ya fyalleta damari koma yabi takanta da mota saidai kyawunta yaceceta ammadai baiji dadin zaginta dayayiba,wani tsakiyaja tamkar zai tsinke harshensa kanwaya yadauka landline yamatsa wasu lambobi jim kadan yasoma magana 

Yawwa rabe dan allah idan babu aiki karaso inason magana dakai,

Yamaida kan wayar yaajiye, minti biu tsakani rabe yayi sallama yashigo, 

Rabe yagirmesa nesa bakusaba,atakaicema zai iya haihuwarsa,amma dayasjigo saida yarussina yace rankashidade incedai lfy? Yamuskuta yace lfy klw,dama dan incemaka  zankoma gida idan munnir yazo kace  yasameni agida dan banajin dadin jikina".


Baijira cewar rabeba yasabi jakarsa yanufi gida,

Rabe yayi murmushi dominyanason yaron  yadanga daga zuwa wani wuri yayagi abinda yayaga,musamman idan yatuno dayanda sukarabu damaidakinshi lubabatu akan kudin dasuka saraya takumace ita batagansuba,yanakuma databbacin itace tadaukesu  tunda baranar tasomaba, yaugadama tasamu dazaimaida asarar datayimasa.






Tana zuwa cikin katon falon maikamada fadar shugaban kasa, bisa wata kujera maibarazanar hadiye duk wani dake gigin hawa kanta.

Hannutavrike da remote control tana saita katuwar tibi plasmatana canza tashoshin datake muradin kallo,.

 Yar kwalisace tabugawa ajarida ta iya tsara ado nagaban kwatance ayanzu haka wani bakin leshine ajikinta maiyarfin goldin da blue,gawasu duwatsu dake raurawa ajikin leshin kala kala, gwanace wajan iya daurin dankwali,gakuma dankon nasara abakinta wato chewing gom tana tauna cikingwanancewa sai kara yake kas kas kas


Hajir kenan manyan mata maganin kananan kwari,tana canza tasha tajiyo kugin motarsa dasauri tatashi tazage labule taleka taga shine,.


Tokome yadawo dashi yanzu alhalin lokacin dawowarsa baiyiba?  Tananan tsaye yashigo takarasa gaanshi taamshi brief case dinshi tace,

Hubby lfya dai kadawo yanzu?" 

Yadubeta cikin kulawa yace  hajir banajin dadine shiyasa ina jawaheer ne?"

Tayimaza tatamke fuska kamar batataba faraaba tace""

"wai hubby meyasa kakesan wulakantani?"

Kafin yayi magana suka soma jiyo takunta itamavtasha ado, dayadaga cikin abinda tayi amfani dashi zaiyiwahala kabambance wacce tafi iya tsara ado da son kwalisa,.

Jawaheer kenan manyan mata masuyi dan kansu, sannu ahankali takaraso tasa hannu tasabule brief case din daga wuyan hajir takamo hannunsa suka nufi wata kofa,


Jajir tana tsaye wata kwafa tayi tareda dunkule hannu ta naushi dayan hannun.









Maman sadeeq

[9:10PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHi🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣



Na

Maman sadeeq








 Dani kike magana cewar hajir, takoma tazauna tacigaba da kallonta amma azahiri bakallontakeba hankalinta nawani wurin nadaban,


Tsawon awa daya jawaheer ta fito daga dakin maigidanta, kallo daya hajir tamata tadauke kai, itako bata ko kalli inda hajir takeba tayi shigewarta sashenta,


 Tamike tsam tanufi dakinshi,

Yana kwance bisa doguwar kujera singilet ce ajikinshi dagajeran wando yadora hannu bisa goshinshi idonshi arufe amma tasan babarcibayakeba 

" hubby " takira sunan data rasamashi yabude ido yadubeta,,.

Katashi magana nakeso muyi dakai tace dashi cikin gatsali,


Yace haba hajir nafadamaki banajin dadi shin bazakibarniba na hutaba?


" kaga idan gajiya kayi dani kafadamani insan abinyi,  nagaji da wulakancin dakakeyimani,danme zaka runka tambayata banxar matarka ko ajiyarta kabani?,

Ko gadinta nakeyi?,

 Saboda menene zakarunka hadani da shirginta,?

Tobanaso karka kuma yimin haka",.


Yayi tsai da ido yana kallonta tatakarkare sai sababi takeyi,

 " yace yanzu menene laifina imbaki hakuri?

Tambayar ta jawaheer ce daiko? to nadaina kin hakura ko?

Tayi shiru yace kobaki hakuraba?

 Yashiga yimata salon dayasan yana karya lagonta, tuni tamanta komai, tashiga yimasa salon da tasan kan mantardashi komai, shikam yadakatar da ita yakuma  tunasar da ita yau baranarta bace, ta jawaheer ce. 

"To menene?"

Tace dashi",inace kaidin mijinane,bakuma fasikanci mukayiba",


Yace nasan dahaka amma jawaheer tafimu gaskiya, dan babu mai son ashigar masa hakki, don haka jeki zan shigo,



Karar takunta suka jiyo mai makon tamike saima kara shige masa datayi, tashigo kanta tsaye bata kokalli hajir ba  taajiye kofin ruwa ta ballo kwayar maganin ta bashi ya watsa abaki tabashi ruwa ya kora , takamo hannunshi tsam tajashi suka kule uwar daki ta maido kyauren dakin bam ta datse hardasa key.,


Wannan abu yayiwa hajir ciwo matuka, gashi tacika fam kamar zata fashe.

Kunyar kanta takeyi akan abinda jawaheer  tayimata.



Tadauki lokaci azaune kana tatashi takoma falo tacigaba dasakawa dawarwara,

Daga karshedai tasama wa kanta mafita da kanta, gab dazaayi kiran sallar magriba  jawaheer tabaro dakin maigidan,


Anan tawuce hajir xaune tashige sashenta.

Wani murmushi tayi tare dafadin  


"Dani kike zancen.

Nakusa yadda kwallon mangwaro nahuta da kuda".

Itama tashige sashenta  danyin sallar magriba










Maman sadeeq

[9:11PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

4⃣



Na

Maman sadeeq













"Tana zaune tana dura kunun aya aro bobin faro, abbas yashigo gidan kai tsaye tare da sallama, ta amsa mashi, yakaraso inda take zaune ya tsuguna kan Katafunsa yakalleta yana murmushi yace kawo intayaki durawa,

Yafara bude murfiin robar tace, "lah! Karka bata jikinka yaya abbas aina kusan gamawa".

 Yace,  ina ummu ko sallah takeyine?

Tace eh sallah takeyi,

Yace " ke kinyi sallarne?

Eh saidanayi sannan nazauna dura kunun,


Umma tafito daga daki tace A"a abbas ne? 

Yace eh ummu,

Suka gaisa amutumce tace  tobani daurin kunun kishiga kidauko mashi tabarma",

 

Ummu tadauki bokitin kunin darobobin tashiga daki  dantabasu wuri suyi zancensu,



Abbas shine saurayin dake son zuhra,

Mahaifinshi aminin mahaifin tane,shiyasa aka yarjemasa yashigo hargida dansuyi zance,

Domin kuwa sun amince da nagartar abbas din 

Yanzu haka iyayansu sunbasu damane dan su fahimci junansu  sosai,saboda atsayar darana,



Sunyi firarsu tamasoya dukdadai shine karfin firar itakam daga eh sai a'a har yanzun takasa sabawa, 

Itadai kunya takeji, shikam burgeshi takeyi saboda kunyarta,

"Karfe takwas da rabi yatashi da niyyar tafiya gida, yadubeta yace " zuhra  ni zan wuce saikuma watarana",.

 Tace  to allah yakaimu,

 Yace babu ko yarrakiya,

Ta dukar dakai shima yasan dakamar wuya,wai gurguwa da auren nesa. 

Yayi murmurshi  yace,

To shikenan nina tafi:.

Tace to allah ya tsare :,.

 Yace ameen zuhra,

Sukayi bankwana tanade tabarma tashiga dakin ummu,. 



Washe gari tunda safe lubabatu tayo masu sammako kai tsaye dakin ummu tanufa.

Daga bakin Kofa tatsaya ta wakice labulen tace

" ina ingozin?

Koda yake aibaayi maki sallamaba tunda baki gajeta ba,

Ummu tayi murmushi tace shigomana kya tsaya anan,


A'a inani ina shiga dakin iyalan oduduwa?

Airamin kura sai yayan ta,

Fito nidai imfada maki abinda yakawoni, danmadai bakida fasaha aidaba saina tsaya wahalar da bakinaba,

Ya isa ace kin gane abin da yakawoni""


Tabbas maganar lubabatu sundaki zuciyar ummu saidai indasabo yaci ace tasaba,

Saidai shi bacin rai aiba asabo dashi, duk sanda akayimaka saikaji babu dadi,


Ummu ta shimfidamata tabarma tace "zauna lubabatu,"


Tatabe baki tace  nibazama yakawoniba, kudin haya rabe ya aikoni nakarba,

Yace yanzu aduk wata zaku runka biyan haya,


Ummu tace to insha allahu zamuyi kokari amma yanzu dan allah kuyimana arziki, kinga yanzu wata bai cikaba amma  da anyi albashi zan hado inkawo maki hargida". 


"wa?"kam ubancan"! Ai inkinga nabar gidannan to kudinku kukabada inko bahakaba imfitarmaku da ko matsanku indatse gida in wuce dan yau adubu nazo cikin biyu dole ayi daya,kodai kubani kudi kokuma inkarta maku rashin mutumci, saboda ni awannan fannin nafi kwarewa".

Ummu tace lubabatu dan allah kiyi hakuri wlh dawata yacika nidakaina zankawo maki kudinki har gida,

Tadubeta alalace  tace,

"ah tomekenan?

Ba magiya nazo kiyi miniba  idan da kudi kibani,idankuma babu sai kusan nayi ko mukadaine keda gidan haya,? 


" ummu tace to bari ingani ko wadanda ke gareni zasu isa imbaki,

Tashiga daki,

Lubabatu tatabe baki tace bayani zakiyi yar gidan oduduwa, tunda har kika tuna daakwai kudin adaki sauran ma safito,


 Ummu tafito dakudi naira dubu biyu  da dari biyar ta mikawa lubabatu,tayi maza ta tambayeta,

" Nawane?

Ummu tace dubu biyu da dari biyarne,

"ah me yacinye dari biyar din?

Ummu tace wlh lubabatu hada kudin abin cinmu dana kunun mu nahada maki, yanzun bansan yaya zamuyiba,

 Lubabatu tace ina ruwana dan kin hadomin da kudin abincinku?koma mezakuyi kuyi dari biyar sai kun Ciko mani ita yanzu idan bahakaba  inyi waje daku ko dole sainan zaa zauna?

Kenifa nafara gajiya dagayyar hakora dan bansaba da wahalaba"

Ummu ta kwalawa zuhra kira ta fito  da sauri  tagaida lubabatu bata amsaba saiwata harara  data dakomata,ummu tace shiga wajan salame ki aro min dari biyar,

Dasauri zuhra tafita  tadawo da dari biyar  ta mikawa lubabatu, fit ta fige kudin tare da jan tsaki mai tsananin karfi tabar gidan,

Ummu tayi shiru tana jinjina karfin rashin mutumcin lubabatu da mijinta rabekodayake aitace tanan fannin tafi kwarewa,allah ya kyauta,



Ayinin ranar basukai wani abuba bakinsuba, saboda babu ko sisi ahannun ummu saidai yandabaru wadanda basu wadacesuba,dole ummu takanyi hakuri tabarmq yayan duk da suma bai wada cesuba





Kafin wata yacika tuni har tatanadi kudin su lubabatu na haya bakin gwar gwado tana samu asanaar kunun aya,




Maman sadeeq

[9:13PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

5⃣





Na 

Maman sqdeeq








"" kwana biyu saiga mai gayya mai aiki wannan karon dakanshi yazo ba lubabatu yaturoba, babu kowa agidan sai ummu tana durin kunu arobii, kai tsaye ya shigo babu ko sallama,har umma tadan firgita,

"sannu dazuwa", tace dashi,

Yayimata kirr yana kallonta har tadan tsargu tadaure tace mashi " ina yini"?

Yayi wani murmushi, yace "kalau nake, aisha ya yara?

Abin yabata matukar mamaki,don baitababa russunawaba akan kiyayyar da yakemata,

Akullum kalamansa na batanci da aibatawa agareta,

Saidai gashi yau ya kwantar  da harshe har yana tambayar yara, koyasan annabi yafaku?

Kaikadaiji wata kila wata sabuwar yaudarace yashigo da ita,duk yanda akayi bayan gangami labari zaibiyo baya,


Ai indai mutum yafara furtamaka kalmar ki zayyi wahala yadawo ya furtamaka kalmar so, 

To komadai meneneallah yakareta da sharrinsa.


Yadubeta yace ina yaranne?

Ummu tace suntafi islamiya".

Yace to yayikyau,

Yazura hannu a aljihun rigarshi ya dauko wani dan karamin matajin kai yasoma sharce gemunsa cikin salona wadanda suka san duniya,

Abin duk yazomata abanbarakwai bakon al amarine agareta,dole tadakatar da durin kunun,dan taga yanda zasu kwashe,.



Yadauki lokaci yana shartar gemu yana kuma kallonta Cikin salo har takosa yayi abin da yakawoshi ya wuce, 

Yasake jeho mata wata tambaya "" ina awwalu?

Kodayake nasan antafi nema.

Kinsan abinda yakawoni?

"saikafada"

Tace dashi dan takosa yabar gidan,

Yace kudin haya nazo karba gashi kuma awwalun  bayanan Yanzu kuma yaya zaayi kenan?.

 Cikin taushin murya yafada mata haka, 

Cikin azama tashiga daki, yabibayanta da kallo,batajima da shigaba tafito dakudin ta dubu ukku ahannu ta jimka mashi,

Yacire hannu maimakon yakarbi kudin saiya shafo tafin hannunta sannan yakarbe kudin, 


Har ga allah batakawoba komai aranta ta dauka ajizancine irin nadan adam,

Ya kirga kudin yaga dubu ukkune cas yazurasu a aljihu, 

Maimakon ya mike sai yakara mike kafa,abin yadauremata kai,matuka ,saidai tazurawa sarautar allah ido,

 

"Aisha manya haka ake tarar bako babu wani dan ruwa ko abinci,?


Har yanzu mamaki takeyi tace aigani nayi tunda muke dakai bakataba bukatar haka daga garemuba,

Wani murmushi yayi yace to yau ina bukata,ai kanin miji shima mijine koba hakaba,?


Tace a'a daakwai bambanci kanin miji kani ne, shi kuma miji mijine,"

Yace toni ko dakeda lubabatu duk daya na daukeku,dan haka nima ki daukeni daya da awwalu,.


Tabbas ayanzu tafaravhasaso wasu abubuwa dangane dashi,

Idan kuwa harkane yayimata faduwar bakar tasa,duk da dai bawata kimace dashi aidontaba,

Bata yi tsammanin zaikasance hakaba,amma bari taji inda zancen zaifadi,


Tamike tashiga daki yasake  bin bayanta da kallo  harda kanne ido,

Robar kunu tadaukomashi  mai sanyi yakarba ya soma sha saida yadhanye tas sannan yayi gyatsa, sannan yace agaskiya aisha kinhadu tako ina,komai yayi ataredake, kinji yanda kunun ayarnan yabada wani dandano?

Kedinma nasan..........

Saikuma yawaske dacewa " zara ce acikin taurari,

 

Tagama gajiya dajin kala manshi tanaso ta koreshi  kuma tana gudun abin dazaibiyo baya,

 

Cikin ikon allah saiga zuhra da kannenta su hudu sun shigo agur aguje suka gaisa dashi  suka nufi daki, 

Yatashi tsaye saikuma ya sunkuyo  yana fuskantarta, har tadan ja baya  yasa hannu yashafi gemunsa cikin murya kasa kasa yaci "ni zan wuce"

Tayi sauri tace to agaida mutan gida,


Yamike  yanufi kofa yawaiwayo yadubeta tare dasake shafar gemunsa sannan yasa kai yabar gidan.


Ayanzu kam tagama gano indayasa gaba saidaitayi takai cin yanda yanunamata halinsa na dan akuya, 

Bawai tana jin takaicinsa nakasancewa ahakaba a'a  tanadai takaicin yanda yanunamata halinsa, 

Ajankasancewarta matar yayansa uwa daya uba daya,

To yanzu yadace ta fasa wannan maganar ga mijinta???????????????????







Maman sadeeq

[9:14PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

6⃣





Na

Maman sadeeq









"cokali mai yatsune ahannunta,tana dauko kayan marmari dashi tana kaiwa bakinta,

Indai kasan kama to daka kalleta ka ganshi to ba sai amfadamaka itace mahaifiyarsaba,

Fara ce tas kamar yanda yaje fari abu daya ya bambantasu kasancewarsa namiji,

Ita kuma mace dolene asamu bambanci,

Natsarin halitta musamman ma shidayake da saje afuskarsa da kuma gargasa ajikinsa,


Bacin wqnnan da macene zayyi wuya abanbancesu saidai idon girma,


Kasa Yazube saman kafet ya kwashi gaisuwa ga mahaifiyartasa,bayan sun gaisa yadubeta yace ""kai ""yau litinin ko?


Tace eh wani abu ne?


Yace tunawadainayi kinyi azumi yau""


Tace eh""

Yace nikan gani nakeyi hajiya kamar wahalarda kanku kawai kuke azuminnanfa ba farillah bane,amma kun kakabama kanku,duk litinin da alhamis sai kunyi shi,kudan bari hakanan ku huta mana,"


Tayi murmushi tace "lamido" kenan.

Yanzu kainan duk wawtata kake ganiko?

To bari kaji kaima dazakabi shawarata daka lazimci yinsa duk litinin da alhamis,

 Danzaka tsira da rabo mai girma,


Yace tabdijan ashe hajiya wayo kikeyimana? 

To insha allah daga alhamis zanfara zankuma jure,


Tace dadai yafi


Yasa hannu yadauki kankana, taturomasa  farantin  agabansa yana shan kankanar tana karemasa kallo saidayagama tajeho masa tambayar.

"lamido" bakada lfy ne?"

 Yayi saurin dubanta yace hajiya maikika gani?

Tace gani nayi kayi rama kodai matsalar matankane?

Yayi shiru yarasa abinda Zace da ita  shin zaifito fili yafadamata sirrin zuciyarsa akan yarinyar dake wahalar dazuciyarsa,ko akwai shawarar dazata iya bashi,

Amma shi ganinshi wannan zai iya zama abin kynya agareshi, kamarshi mai mata biyu zuka zuka  amma ace yabige da  son wannan yarinyar?


Saidai kuma babu yanda zayyi yayarda kuma ya amince da sanda yakemata,  

Dan akullum sai tayimasa gizo kusan sau dari,saidai abin haushi yarasa inda zai samota,

Indama yafara ganinta Alokacin da tsautsayinnan ya faru yaje yafi akirga amma babu wani lbr komai kama da ita bai ganiba,,


Aduk sanda zaiga mutum mai tsagen rumanci wato eleven ko mace ko namiji saitafadomasa aranshi,harma yarunkaganin babu wanda tsagen rumancin yakarba sama da ita,

Saidai zaita addu a allah yabayyana masa ita koda cikin mafarkine,yanada muradinyaganta ko zuciyarsa tarage radadi,wanda yasan bazata bariba saidai yakaru,. 


Tayi masa kyar da ido tana saurare taji abinda Zaice,

Tace kainake sauraro"


Ninasan matsalar matankace tamaida kai haka.

Imma banda rabon yaya "lamido shekarunka basujai nawanda zai ajiye mata biyuba, kaga tunyanzu da kuruciyarka zasumaidakai tsohon karfi da yaji, duka duka nawa kake,

Kodayake laifinkane ai idan gida yagyaru maigidane,

Idan kuma ya baci shiyabata,

Saikasan yadda zakayi kagyara gidanka tun ciwon zuciya baikamakaba,


Yayi karfin hali yace a'a aiyanzu suna dadewa basu samu sabaniba,wannan ramar kuma kwana biyune nadanyi zazzabi amma nasamu lfy,


Tadaiyi shiru amma bata yardaba dan haka tace to allah yakara sauki,

Ya amsa da ameen


Yace hjy wai ina zubaidane kwana biyu bana ganinta,? 

Tace tanacan sashin bilki inkashiga saika tambayeta


Abbafa yana ciki? 

Eh yana ciki?

Yayi mata sallama yanufi sashen mahaifinsa,

Sundade suna fira daga bisani yawuce sashin abokiyar zaman mahaifiarshi,,sungaisa hartana tambayarsa iyali sunyi fira sosai dayake akwai fahimtar juna da kyajyawar zaman takewa atsakani,


Zubaida ce tashigo Itada sakina yar bilki  suka zube suka gaidashi,yadubesu yace shikenan kuma sai akayimqnq yaji?


Sakina tace A'a yaya lamido bayaji mukayiba kawaidai makarantace amma zamuzo insha allahu,


Zubaida de batace komaiba danta tsani zuwa gidan dan uwannata, sabodagani takeyi bayyi dace da mataba,gasu da tsinannan kishi su din yan uwansane amma akwai abinda ta fuskanta akan matansa,basusan kowa yarabeshi saisu daga kwauri sai gwiwa,

Itamadai tabishi dazasuzo,

Yayima hajiya bilki sallama yanufi gida.











Maman sadeeq

[9:16PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI

🔪🔪🔪🔪🔪🔪

7⃣







Na 

Maman Sadeeq











"Rana zaune tana kallon tashar MBC 2 tana taunar cingom, Wanda yazamemata tamkar al 'ada,

hakoranta ko had sunsaba basama gajiya,

Yazauna akan kujera tareda fadin "wash".

Kwantawa yayi yamike kafafunsa, wayarsa yajawo yakira lambar jawaheer yagama magana saikuma yanufi sashenta,


Kwance take kanta kemata ciwo,yaranta sunazaune afalontacsuna kallon katun,su ukku,

Yashigo gabadaya suka baibayeshi yadauke su yayi wasa,sannan yaajiyesu yashiga cikin dakinta.

Tana kwance tadafe kai da hannu biu, ya is a kan gadon gaba daya  yatarairayota jikinsa yarungumeta ,dakyar ta iya bude idonta tadibeshi ,

Yadafa goshinta zafi rau! Cikin kulawa yace " jawaheer    tashi muje inkaiki asibiti"'.

"Dakyar tabude Baki tace  " bana iya zuwa"

Kadai samomani magani nasha tinda komunje asibitin magani kadai zasu bani, tunda ciwon Kaine,


"Bai aminta da abinda tafadaba yajawo mata hijabinta yakamo mata hannunta tamike tsaye saidai layi take saboda jigata da ciwon yayimata,


Yatallabota yarabata da jikinsa, dahaka suka fita daga dakin , yaran suka mike " Momy INA zakuje?


Yace asibiti zamuje Idan da maisan allura yataho muje?



Dukkansu suka noke kafada ,yace Abdul dauko munubiya, kaja hannun saifu,kuje wajan antynku kafin mudawo,


"Tana zaune Inda yabarta taga fitowarsu da alama babu lfy, tana kalloonsu batace dasu uffan ba,saima shine yace da ita  hajir zanje inkai jawaheer  asibiti,kanta ke ciwo,

Saida tatabe baki tare da taunar cingom dinta  yayi wata Yar kara sannan tace  " To" saikadawo"


Shima cikin ko inkula yafita yasata amota yanufi wata asibiti maizaman Kansa aka rubutamata magunguna suka koma gida,


Lokacin da suka dawo hajir bats cikin falon saidai yaran kadai,kallonma ta kashe, jawaheer tadauki munubiyya tasaba akafadarta, ta dura sauran zuwa daki,

Shi Kansas "lamido abinda hajir tayi baiji dadinsaba,tayaya zata barmasa Yaya afalo sukadai,amma ita ta mammala nata adaki,saidai baibari jawaheer ta luraba,


Yacire masu kaya yamaidamasu nabarci,sannan yajuya yanufi dakinsa,

Toilet yashiga ya watso ruwa,yana fitowa tana shigowa,rigar baccice ajikinta saitashin kamshi  takeyi,

Kai tsaye tahaye kangadon, saidayasa Mayan barci shima yahau gadon,

Kallonta kawai yayi  bai San abindayasaba hajir batada vikakken ilimin addiniba,

Idanda zaibiye mata Karya kalli koda dakin jawaheer ne  saidai itakadai,

Yanzuma ba girkintabane amma tazo tirakar maigida satar kwana kenan?



" gaba daya yajita jikinsa wani Sabon salo yashiga yimashi,

Yaso yayakiceta amma INA tuni ta mantar dashi komai tuni suka shiga shaanin gabansu,





Kiran sallar farko tatashi saboda babu ciwon kan, cikin sauri tanufi dakinsa,dantasan sai  sa a idan ba ashigaba hakkintaba tatura dakin yashiga,

   Yanayin yanda tagansu kwance taji kamar ta Dora hannu aka takurma ihu 

Meyasa hajir take mata hakane? Kodayake balaifinta bane,









Maman sadeeq

[9:18PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

8⃣




Na

Maman sadeeq











"Takai hannu tataa kafadarsa,yabude idon sa yaganta atsaye akansu,kunya takamashi dayake namijin duniyane sai yashare yamike tsaye yadafa goshinta yace "ya kan"?

Tadai daure tace dasauki"


Daya lura tana masa kallon tuhuma yakamo hannunta yace taho muje kitayani wanka,

Tamkar yawatsamata wuta saboda takaici,wannan ma airainin hankaline,banda cin amanarta dayayi shine kuma zaikuma cusa mata wani bakin cikin,


Takalleshi cikin kallonta na kankance ido tace

" katashetamana basaiku kauda kazantar tareba?


Sarai yasan maganace tafadamasa,saiya kama kame kame Yashige bandaki


Maganganunsu suka tasheta wani kallone sukewa juna,


Hajir tatashi taraba ta tafice daga dakin,

Tananan tsaye har yafito kunya duk ta baibayeshi, 

Yarasa dawace kalma zaiyi amfani da ita wajan lallashinta,

Hannunta yakamo yazaunar da ita kan gadon yakira sunanta cikin sigar lalladhi,

"jawaheer don allah kiyi hakuri nasan nayimaki laifi,saidai nikaina bansan yanda akayi jakan tafaruba,saidai farkawa nayi naganta babu wani abu daya shiga tsakanina da ita,.


Tace aibaxaka saniba saidai banso kaboyemin wani abuba nidin akar kashin ikonka nake,ashe ko bekamata ka boye minba tunda babu abinda zanyimaka,

Saidaikasani yin hakan agareka bakaramar musibaba xaijawomakaba,kaine abin tausayi,hajir kuma nizan dauki mataki da hannuna,tunda tafito fili tanunamin ita din karyace,




Haka yayi sallar asuba yadhiga shirin tafiya office shiru shiru jawaheer bataxo tasanardashiba yazo yayi karin kumalloba,har bakwai saura kwata,

Yagaji da jiranta yabita daki yatarar da ita dayaranta suna breakfast, cikintaushin murya yace "jawaheer  kefa nake ta jira gashi har bakwai ta kusa.

Tadubeshi cikin kulawa babu Alamun bacin rai atare da ita tace au ainadauka ba huruminabane,kaga kau bani zambaka abin karyawaba,jinake hajir ce?

 Yasani shagube tamasa dole yadanne tunda shine mai laifi,kuma yazama dole ya lallabata,yace nidai dan allah taimaka kibani sauri nakeyi".

Tace a'a nibazan shiga hakkintaba tunda ita kedakai jiya,toyau ma itace dakai inyaso jibi mahadu.


Yaci ace yanada dogon tsinkayeyandazairuka fahimtar al amurra cikin sauki,duk yadda mata zasu hudomasa dasalon kissa da tuggu zaiganosu, tosaidai bashida wannan baiwar,


Ahajan yayarda daabinda jawaheer tafadamasa yanufi sashen hajir, itama karin takeyi dayaranta guda biyu haleesa da siyama, yace tahadomasa karin kumallon,

Azatonta salonda tajemasa dashijiya shiya rudashi,har yamance da inda yake,

Dama ita haka tafi so,in sonsamunema har kwanan jawaheer dinma zata iya handamewa,don batavgajiya da gwarzin mijinta,

Dan haka dayace tahada masa kari batayi shayin komaiba,takanainayeshi da kissarta tahada mashi,


Saida yagama suka fito suka nufi dakinsa yadau laptop dinsa da breafcase dinsa,ta amshi jaka yakwashi wayoyinsa suka fito,


Jawaheer nazaune ita da munubiya a falon suka fito bata ko kallesuba,

Yakaraso inda suke zaune yace "sarautar mata muzamu wuce,"

Fuskarta asake tace to RANGIDA adawo lfy,


Itako hajir tabe baki take saboda sunannan yana bata mata rai duk sanda zaice RAN GIDA takanji haushi domin ko ita yadace yacewa ran gida,duk da tasan uwar gida yake nufi,amma ita aganinta fifitawa yake mata,



Har mota tarakashi saidataga tafiyarshi sannan ta dawo cikin gidan,aganinta cinyewar kenan tunda takwacewa jawaheer kwana saitakejin wani nishadi,

Cingom dinta takware ta wurga abaki tasoma tauna tadawo falon tazauna,

Hausa fim ne jawaheer take kallo itako hajir bata kallon hausa sai american ko kasashen turawa, dan haka tamike taje tadauko remote din dayakesaman table dindake tsakiyar dakin ta soma canza tashoshi zuwa na turawa,

Jawaheer batace mataba komai, ta lalubi tashar datakeso takoma tazauna tacigaba da cin cingom dinta cikin salo da kwarewa


Jawaheer ta kira  mai aikinta ladidi tabata umurnin tadafa mata kalar abincin datakeso narana,


Haka suka kasance harzuwa karfe  shabiu narana inda bamaicewa da yar uwarsa eh ko a'a





Maman sadeeq

[9:19PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

9⃣



Na 

Maman sadeeq





"laila sanqta ce tayi saallama,kawar hajir ce, cikin murna hajir tatashi tatarota,sukazauna kan kujera,

Hajir ta kwalawa mai aikinta kira tazo tace bakuwa nayi kawo mata dan abin tabawa,


Tuni aka cikawa laila sanata gabanta  dakayan ladhe lashe,

Hajir tadubeta tace kinzo adaidai lokacin danake bukatarki, saura kadan nabugo maki waya,ko inzo gidanki,


Laila tace kardai kice min haryanzu matsalar nance?


Hajir takyabe baki tace itace mana,ai duk duniya banida matsalar data wuce wannan


Tayi mata nuni da ido akan jawaheer,dake jwance jan doguwar kujerar falon,bata ko kulasuba kumatanajin abindasuke cewa,


Laila tace aisaken dakikayi kenan, aidama ance duk wanda yayi sake to zaiga sake,

Ai danzaki tunyana karami ake kaudashi,idan akasake yagirma to saiya gagari kowa,


Aiyanzu kan mata yawaye  sun daina dogin barci  idan shiga zakiyi kiyi shiri intarar wa zakiyi kiyi shiri,

Amma ke duk ambarki abaya to laifin wa?


Hajir tace laifinane amma aiyanzu zambi sahu


Laila tace dadai yafi nida mata zasubi shawarata aida sun mikevtsaye sun nunawq mazacewa kwace goruba ahannun yaro abune mai sauki,

Dadayawa maza wasunsu ki mutuwa matansu sukayi basu isaba sudubi wasu matan suce suna so,


To inda zaa runka samun mata irinki rafkanannu to dayawanku bakin cikin kishiya zai kasheku,

Aini nayi mamakin yanda kika kasance awannan gurbin,


Hajir tayi sauri tace gaskiyarki laila aidaganin wani abun zakisan babanzaba da walaki,


Laila tace ato yarage naki danni yanzu abin da yakawoni kinsan nacemaki ina so inje dubai to tafiyarce tataso,  wai kuda yaga mai kayan  nama,

Idan kina da sako  kya iya badawa,


Hajir tace toni wane sako zanbada  tunda bani da kudi,inafavsan sarka dama wasu abubuwan saidai babu wasu kudin kirki ahannuna,


Laila tace kinji ko kinji irinta ko,ke yanzu bakijiba kunyar fadar baki da kudiba? 

Kamarke zuwayanzu yadace ki mallaki kudin dazaki iya shirya ma kanki tafiya,badubaiba ko kewaye duniyakike sonyi, amma wai sakon da bai wuce dubu dari biyu zuwa ukkuba yagagareki, to alkah ya kyauta,


 Tamike tsaye tadubeta alalace tace  ni zan wuce, sai allah yayimani dawowa,

Amma ina mai tabatar maki cewa ankusan yi babu ke,


Hajir tatadhi tayiwa laila rakiya har wurin motartq,sun rabu da ita akan idan tadawo daga dubai zatarakata ayo mata aiki mai dan karen xafi





Aduk firar dasukayi akan kunnen jawaheer,wasu abubuwan ma duka kanta suke yinsu, ta kuma dade dasanin rashin mutumcin laila kawar hajir,tayiwa hajir din fintinkau,amma ita aganinta duk wani abu dasukeyi duk datasan da itacsuke hakan bazaizama hujjaba,abudaya zasuyimata wanda zainuna sunshiga gonarta, to anan laila zata gane bambancin dake ajwai tsakaninsu,amma yanzu duk har gagi sukeyi,

Kuma ita babu boka babu malam,abu dan tsubbu kodan bori,

Allah kadai tarike dan shi ya isheta abin dogaro,


Hajir tadawo tazauna tacigaba da tariyo maganganun dasukayi da laila sanata,,tabbas yaci ace ita din zuwa yanzu tana da kudin dazatayiwa kanta komai,tafita kasashen waje, amma wani abin kunyar dan sakon da bai wuce dubu dari biyuba zuwa ukku yagagareta,towai duk meyakawo haka?

Karyane dai tace mijin ta baida kudin dazaimata kyautar yan wadannan kudin,duk yanda ake zaton mijin nata  da kudi to ya shalla ke nan,abinda yasa tace haka kau tadora ayar tambaya akan hidimar dayakeyimasu,komai na amfani mai tsada yake siya masu,kan tufafi,sabulun wanka, akomai saiya kure adaka,ma ana mai tsada,to amma mai yasa baya bata kudi?


Yazama dole tajaraba tambayarsa kudi ko tatara abin duniya.




Maman sadeeq

[9:20PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

🔟



NA

Maman sadeeq




BAN HAKURI



Kuyi hkr bisa rashin samun postin dina akan lkc wadansu yan uzururrika ne suka shigo mania yanzu cikin ikon allah komai ya daidaita,zakucigaba da samuna kamar yanda aka saba,





JIN JINA



Najinjina maku masu kaunar littattafaina har kullum kaunarku tana kara shiga jinin jikina,kamar yanda kuke sona nima haka nake kaunar ku



GODIYA


Har kullum ina kara godemaku dan kun kula da al amurrana,

Masu kirana awaya da masu turomani text,nagodemaku allah yabar soda kauna allah kashiga tsakanin mu da makiyanmu,



BAZAN MANTA DAKEBA 


Kawata kuma aminiyata 


Momy son kiru kano state



CIGABAN LABARI

"larfe biyar na yamma lamido yataso daga wajen aiki,dirin motarsa tajiyo tafito domin tararsa,saida tarungumeshi tare da sakarmasa kiss atattausan sajensa wanda ke burgeta sannan ya mikomata yar jakarsa,suka nufo sashensa.

Hillatarsa takeyi don yamanta da jawajeer, aganinta zata cusamata bakin Ciki ayauma tayi niyyar kwace kwanan jawaheer din tunda jiyama ta kwace,inyaso bakin ciki ya kasheta,


Ruwan wanka tahadamasa.tadaukomasa kayanda zaisa,

Tambayarsa tayi wane irin abinci Yakeso adafa masa yafadamata takoma saahenta ta dora girki saboda tasan bayacin abincin yan aiki,


Agurguje tashiga bandaki tasheko wanka, tayi kwalliya tadaukar hankali,takira mai aikinta tace tashiya su haleesa da siyama takaisu dakin barcinsu,itakuma tanufi dakin lamido da kayan abincin data girka,


Cikin salo da yaudara dakissa dama kisisina taketa hillatarsa dandai karya tunatar da ita cewa yau ba huruminta bane,don jiya ita kanta tasan hillatarsa tayi da sababbin salonta abin datadauka salon datayimasa ne yadauki hankalinsa haryamantar dashi cewa yau baranar girkin tabane.

Danhaka yaudin zata bude makaman yaki, takudiri aniyar mantar dashi jawaheer  arayuwarsa matukar ita tana numfashi,zata kuma kara kaimi akan salon data nunamasa jiya,


Bayan yagama cin abincin ta shiga gwadamada da  gwalon gwaso saida ta tabbatar tagama kamashi ahannu babu abindayake bukata face ita din,saikuma tajanye jiki daga gareshi,dayanemi dalili saita bijiromasa da bukatunta,atake ya amsamata dakome zaiyimata babu kunya ko tsoron allah tasallama masa kanta,tun asuba tatashi takoma sashenta gudun kada jawaheer tayimasu irin najiya,bawai tsoro take tagansuba a'a tana dai takaicin tagansu awani hali itada mijinta, danko turakar maigida ai sirrice babu ko wanda yasan sirrin,


Karfe bakwai tashirya break fast tanufi sashenta,takaimasa itama tatsaya nan takarya,

Yayi shirinsa tsab tadaukomasa jakarsa shikuma yadauki computer suka fito atare,yashiga sa shen jawaheer fiskarta  asake suka gaisa babu bacin rai ko kankani afuskarta,kodayake ta iya boye bacin ranta duk da ance labarin zuciya atambayi fusaka to itakam zaiyi wahala kagane abinda ke cikin zuciyarta, kodako damuwarce fall Acikin zuciyartata to babu mai ganewa,shiyasa take konawa hajir rai dan ganinta babu abinda ke damunta,

Itakam bahaka takesoba sotake idan tacusa mata bakin ciki to tanuna kokumata runka yadda magana yadda za arunka kara cusa mata wani,


Yace jawaheer nizanfita babu wata matsala ko?

Tace babu wata matsala allah yakiyaye adawo lfy,


Yayi murmushi yace allah yasa,azo ayimani rakiya mana koda zuwa falo ne,


Tayi murmushi tace kayi sa a dazamfita falon,amma da bazanyimaka rakiyaba tunda banibaceba dakaiba,


Yayi sauri yace ayau din?

Tace a'a ayanzu dai,

Yace to naji mudaije""

Yakamo hannunta yafito,wani abu yacaki zuciyarta ganin yakamomata hannu,tatabe baki jawaheer tazauna bisa kujera tace to D allah yakiyaye"

Yace amn my "D".

Tacika tabatse ganin sun ambaci juna da "D" tadai daure tace my hubby yaya maganar da mukayi dakai?


Yace ah kinga har na manta amma yi min arziki har indawo sai imbaki kinji,?

Tayamuta fuska tace to sai kadawo din"


Tamika masa jakarsa,tun afalo taso agaban jawaheer yabata kudin dontajefata acikin tunani tosaidai hakan baisamuba,

Baidamuba yakarbi jakar yayi gaba Abinsa.

 Haka ta wuni taso ace tasamu kudin tayi gaggawar iske laila sanata  tun kafin tatafi,




Maman sadeeq

[9:22PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣1⃣






Na 

Maman sadeeq





Tun biyar jawaheer ta shiga kicindon tasamarwa maigidan abincin datasan yafiso.


Babu kunya ba tsoron allah itama hajir tashiga kicin don alissafinta,yaune ranar girkinta,su wadan can kwana kin datayi tayisune amatsayin shiga hakkin jawaheer don haka yau ranar tatace,ko ita jawaheer din zata yarda?



Kowaccen su tayi kwalliya taneman fitina,shikadai ake jira.

Jawaheer tana koyama Abdul da saifu karatun da aka koyamasu a islamiyya,

Yashigo yaran suka tareshi suna oyoyo shiyasa babu wacce tatashi  dontatareshi.


Yabude breaf case dinsa wacce baya rabo da kayan kwalam na yara yabaiwa,abdul da saifu,yace ina munubiya takene?


Saifu yace bacci takeyi""


Yabashi wata yace to ajiyemata""


Yadubi hajir yace ina su halisane?

Tace suna daki,

Yace da abdul kiramin su",

Yakirasu yace mekukeyi adaki ne?


Tace dady kallo mukeyi,

Yace toyayi kyau kuzo ga sweet kuna sha ko?


Sikace e suma yabasu nasu,

Yahade kan yaran dika yace to kuzo muje falona sai muyi kallo ko?


Ya dubi jawaheer yace zomuje "D "kihada mani ruwan wanka,


Wani kallo hajir tayi masa mai alamar tambaya,saidai baikulataba dukda yalura da abinda take nufi,yakada kan yayansa yanufi sashensa.


Jawaheer kuma tarufa masu baya.


Kan ubancan meyake nufi da haka? 

Koya manta yaudin ranartace?

Bari taji  jawaheer din ta gama gwalan gwason inya so itakuma tayi shigewarta dakin hubbynta,

Don atunaninta tagama siyeshi,da salon kissar da ta hudomasa dashi,

Shekaran jiya da jiya tasan zaiyi wuya bai nemetaba,imma bai nemetaba ita ta iskeshi,


Jawaheer tahada masa ruwan wanka ya shiga bandaki,

Dayafito ya umurci yaran da suyi alwallah sutafi masallaci,sukayi alwalla suka fice masallaci, 

Jawaheer tahada masa abin cinta takai ta shirya.

Saida aka gama sallar isha i sannan yashigo shida yaran, 

Shi ya nufi sashenshi  sukuma suka nufi sashen mahaifiyarsu.


Hajir naganin yashigo itama  tahada kayan abincin nata tanufi sashensa,abin yabashii mamaki ganin hajir dakayan abincin alhalin ga jawaheer ta soma bude kayan abincin tafara zubawa,shikam ya kame yakasa magana.


Jawaheer tasanyo kai ganin hajir nazuba abinci afaranti baisa tayi  wani yunkuri ba tazauna kusa dashi  suka sashi atsakiya.


Hajir tagama zuba aninci tace bismillah,"


Yayi wuri wuri da ido yayi karfin halin cewa hajir bar abincinnan kinsan yau ba girkinki bane, ina cewa yau kika fita daga naki,?

Tace banganeba wai dan allah hubby mai yasa kakeson tozartani a inda za amin dariya?

Yace bahaka baneba hajir ina dai sone in kwatan ta adalci,kinga idan bam mantaba kwana hudu kikayi kina  girki a maimakon kwana biyu,koda ace kwana hudu kukeyi atsakaninku aiyaune  girkin jawaheer bare kuma kwana biyu kukeyi,


Jawaheer tace "D" inajin mantawa tayi kasan ba kowace kwakwalwa bace ke jimirin ruke abubuwaba"


Yadubeta cikin kulawa yace zayyi  wahala tamanta, yaufa tafita daga nata girkin""


Jawaheer tabude nata kayan abinci taxuba suka soma ciyar da Juna Abincin,


Bakin ciki da ta kaici sun rufar mata  hartakasa cewa uffan,musamman maganar da jawaheer tafadamata,waiba kowace kwalwace ke juriyar rukon abubuwaba kenan ta dauleta mahaikaciya ko jaka?


Babu abinda kakeji saikarar  cokullah, tayi karfin halin cewa nagode hubby.

Da abinda kayimani.

Ayanzu na tabbatar dacewa namiji ba dan goyobane, ko amafarki banzaci haka daga garekaba,



Tabbas shima yakulu da abinda tafada,saidai ya Danne,

Harta mike tsaye saikuma ta juyo cikin gatsali tace daukomin maganar da mukayi dakai aicewa kayi saika dawo,


Yace toyimin hkr inkarasa cin abinci sai indaukomaki"


Takara kuluwa tace sai inyita tsayuwa har sai ka karasa cin abincin?


Baya son tashin hankali shiyasa yatashi yanufi kuryar dakinsa, 

Minti biyu ya fito da ra far yan dubu dubu ahannun sa har rafa shida,

Yawari ukku ya mika mata ,tamiko hannu daya tamkar zata amshi mugun abu takarba alalace,


Bai damuba ya mikama jawaheer  itama rafa ukkun  tace "D"  na menene?

Yace kyautace nayi maku  inafatan zata faranta maku?


Tace sosaima saidaini bana bukatar kudi ,inaga kabar kudinka,


Wani takaici yakama hajir don meyene zaimasu kyauta  kai daya?

Ai ita kadai tatambayeshi kudin dan yaja arainata shine ya basu atare? To bata so bari ta maidamasa tsia takunsa,zuciyarta ta dakatar da ita " akul kika maida kudinnan,

Damace tasameki ta mallakar mijinki atafin hannunki,idan kuma kika maida to anyi babu ke.

Maganar laila sanata ce ta dawomata,

Ta watsa kudin cikin kwandon kayan abincin datakawo masa,

"Deyasa bazaki karbi kudinba kodan tsaron lalura?

Tace A'a "D, ni gani nake hidimar fa kake yimana kadai ta isa mugode,

Yace tokodai inkaro maki sunyi maki kadan,?

Magan ganunsu sun ishi hajir  don aganinta cin fuskane sukeyimata,

Har ga allah bada itaba sukeba, taduri kayanta tayi gaba,

Itako jawaheer saida lamido ya dadomata wata dubu dari biyun akan ukkun,saida yanuna mata bacin ranta sannan takarba,




Washe gari hajir takira laila sanata,saidai ta bugi gurbi domin ayau kwanan laila biyu a dubai, dole ta hakura harzuwa lokacin da laila zata dawo.

















Maman sadeeq

[9:23PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣2⃣



Na

Maman sadeeq











"kwana biyu jawaheer tayi tana girki cikon na ukku hajir tayi nata,saidai abin yadauremata kai ayadda taga jawaheer tana shirya girki takawo saidai ayau ayi wacce za ayi don kuwa bazata yardaba,


Lokacin dayafito daga bandaki yaganta atsaye taruke kugu cikin daurewar fuska tace.

"hubby me kake nufi da matarka zata shigo hakkina?


Kafin yabude baki tajiyo muryar jawaheer na bata amsa.

"ko daya babu shiga hakki,inajidai ke kwalwarki bata jumurin rikon abubuwa,

Nikam kwana biyu ya isheni, bana bukatar handama da baba kere akan kwanan wata.

Idan har kwalwarki nada jimirin rikon abu buwa tokiyi tunani ki hango kiduba kwanaki nawa kina girki?

Kuma ni din kwana biune zanyi ko nawa?


Idan kuma le bazaki iya tunowaba saboda toshewar kwakwalwa ni bari na tuna maki.


Kwana hudu kikayi amai makon kwana biyu da mukeyi azatona ko kin sauya tsarin girkine,saikuma gashi tunkwananki baizoba ,

Ko dayake ba abun mamakibane in akayi la akari da Irin matsalarki ta kasawar kwakwalwa,

Danhaka sainan da kwana biyu zaki karbi girkinki tunda kimmaidashi kwana hudu,


Lamido yarasa maizaiceasu dama haka hada mata biyu yake?


Jajir tace babu wani canji danayi wa girki,yananan akwana biyu, dan haka janye kayan kazantarki,idan kuma kikace yau sai kin kwana as a kinnan saikinyi nadama harda dana sani,


Jawaheer tayi murmushi tace.

"zan koso inga kwarewarki kan rashin mitumcin don ninafison  mugwada kashi dake ko kya kiyayeni,inyaso ayi mutuwar kasko"


Gani yayi dagaske suke imba shiga tsakani yayiba  za ayi babu dadi


Yadubesu yace"


"kudakata haka".


Hajir tadube shi tace wane irin mudakata haka?


Wlh bazan sairarawa wannan ashawon ba (karuwa),

Tunda hartanemi ingwada mata rashin mutumcina to wlh saina nunamata nida nake jira.


Yace kinga hajir bazan yadda kaida min gida kamar kasuwaba,

Dukku saurara kuji tunda ke kwana  hudu kikayi,to itama kibari tayi nata hudun,idan hakan kuka maida kwanakin girkin to shikenan, idan kuma kwana biu zaku tsaya shikenan bana son tashin hankali"


Yana fadar haka yashige kuryar dakinsa.


"hajir tayi murmushi tana kallon jawaheer tace"

Kinyi nasara akaina saidai ina tsoron ranar da zan saka  fatsata  acikin ruwa don ta sha komin wuyanki, wlh saikin zama abin tausayi,

Bakuma zan taba tausaya makiba,dan haka kisaurari lokacin gamuwarmu bazatayi kyauba".


"jawaheer tace zansokuwa fatsarki tajawo maki ni,dan saikin tabbatarwa kanki fatsarki bala'i ta jawo maki.

Kin ganni nan ba boka ba malam bare tsubbu  da yan bori amma saina zame maki "WUKA A MAKOSHI"

Wacce idan bakiyi sa aba zata ratsa makoshinki,saikuma na nunamaki kissa tafi magani tasiri,

Tunda nake bantaba ganin karyar mace irinkiba, bankuma taba ganin maceba yar ina da maza ba irinki,ko alabari ba ataba kwata mace jarababbiya irinkiba,

Idan daza akyaleki akullum kuyi ta abu daya saikace karya, kodayaje babu mamaki ajininku abin yake,


Hajir tayi murmushin takaici tace,

Kifadi duk abin da kika so damarkice kuma lokacinkine,dasannu zaki fado komata,anan zancigaba da gasaki yanda raina yayimin,

Don haka kirubuta ki ajiye saikin zamo abin tausayi  agidannan,


Bata tsaya sauraren abinda jawaheer zata fadaba tafice daga dakin,


"Tawakkaltu alallah"


Jawaheer tafada  tatura kofar dakin  ta shiga wurin "D" dinta.







Maman sadeeq

[9:24PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣3⃣


Na

Maman sadeeq





















"yau kwanan sa bakwai dazuwa karbar kudin hayar gidansa,saigashi kuma ya kuma dawowa,

Ayau harda guzirinsa na shin Kafa tiya uku, da ledar taliya, guda ukku da macaroni laida biu,sai kus kus shima laida biu,


Ummu na duke tana ta tikar wankin kayansu hamza,yayi sallama tadago tare da amsa sallamar,

Allah yasa kayan jikintaasu yalwane,amma duk da haka babu dankwali akanta,da sauri ta jawoshi ta daure kanta tace dashi 


"sannu da zuwa".


Yace yawwa Aisha wanki akeyi?


Tace eh.


Yace dan bani wurin zama".


Dada jali da ta tambaye shi abinda yazo yi har yake neman gurin zama,to so takeyi su rabu cikin ruwan sanyi,

Tadauko kujera yar tsugunno ta miko masa,


Ina wuni? Tace dashi,


Ya amsa cikin kulawa,tayi shiru taji abinda ya kawoshi,

Babu mamaki kudin hayar shi yazo karba. 

Wata kila yaida karbar kudin hayar sati sati,

Tunda sai bayan wata ukku sike biya,to yanzu yamaidosu duk wata,babu mamaki yanzu yamaido shi sati,

Amma ita ara ayinta da yayi tayi mata kara kaina gara gara ya runka turomata lubabatu, duk darashin mutumcin data ke auno masu,  gara zuwanta danasa zuwan,

Saboda tasan babu alheri anasa zuwan.



"jin yayi shiru tadubesa tace.

"allah dai yasa lfy?

Rabe yayi murmushin da lubabatu tace yana karamasa kyau, azatonsa ya burge ummu yace,


"lafiya lau aisha,kawai dai naga kuna cikin matsin rayuwane, shiyasa nasayo maku wannan,


Yanuna mata laidar taliya da shinkafa daya kawo masu,


Ummu tayi godiya sosai  tare da addu ar jinkan iyaye,

Ya dubeta tareda shafar gemunsa yace.

"Aisha  babu zazzakan kununnan naki mai sanyi da dadi?

"Tace akwai?


Yace to kawomani roba daya'.

Tamike yabi bayanta da kallo,tareda kara shafar gunsa,

Allah yasani kugunta yana tafiya da hankalinsa,

Kallonsa kadai kan ragemasa damuwa,

Bare kuma zuciya tacigaba da wassafo masa  wasu abubuwa,atake yashiga tariyo surar matarsa lubabatu,bambancin abayane yake,

Babu yanda za ayi ahada Aisha da lubabatu.

Taimata nisa afagen kyau kai ko ta inama.


Ummu tadawo darobar kunun aya ta mika masa,

Yakarba ya soma sha cikin wani salo,

Yanayi yana kallonta.

Saida yashanye sannan yatashi da niyyar tafiya,

Ya dubi ummu yace 

Aisha nizan wuce idan zan zauna anan saiki shagaltardani immanta komai,


Dam! gabanta yafadi dajin kalamansa ashe duk karemata kallo yakeyi ita bata saniba?

Kodayake babu mamaki  ai tada de da hasaso wannan daga gareshi,

Tadago kai ta dubeshi saitaga yakafeta da idanunsa, tace,

To mungode kwarai allah kuma ya kiyaye,


Yashafi gemunsa yace amen"

Yajuya yabar gidan,

Batayi mamakiba tadayyi adduar allah yafidda ita daga sharrinsa,

Ta kwashe kayan takaisu dakin maigidannata ta ajiye tadawo tacigaba da wankinta.



"karfe bakwai nayi maigidannata yadawo,

Bayan tarba datamasa,saida ya kammala cin abinci,sannan ta nuna masa abinda dan uwansa rabe yakawo masu,

Yajinjina girman kyautar duk dacewa wannan ba wani abu bane na kuzo kuganiba,

Asaninsa dai yasan rabe bayayin kyauta haka siddan, matar sama bata wadataba daga dukiyarsaba, to ashe kuwa dole yayi mamaki akan kyautar dayayi masu 

Musamman idan ya lura da irin tsanar da sukayimasa shida dan uwansa sani harma da kanwarsu turai  

Amma dai yabar abin amatsayin tsananin rabo,

Tabbas idan rabo ya rantse to saifa maishi,


" To mungode inhar  yayi don Allah ",

Tadai yi shiru bata fasa masa abinda ke dunkuleba,

Yadubi ummu yace namance bamfada makiba ayau da karfe tara malam mande yace yan uwansa zasuzo nemarwa abbas auren zuhra, saidai ina jin wani kunci idanna tuna banida komai, ban ajiyeba ban bawani ajiyaba,shin aisha damai zan fita kunyar gudan jinina zuhra kadafa ta daukeni uba marar adalci"'',


Ummu tace  karkadamu malam allah shine gatan bawa,

Zuhra bazata tabayimaka wannan kallonba,

Nikaina inason inga nakai zuhra dakin mijinta,saboda ina kyautata zato akan abbas zai ruketa da gaskiya,ina so ta huta da gwagwarmayar nan haka,abin aure kuma bashine zaman aureba idan tabarma tasamu kakaita da ita,  kaidai kawai kacigaba da addu a allah yaja darai yakuma baka lfy 

Cikin sanyin jiki yace amn aisha.


Karfe tara daidai manema auren abbas sukazo gidan malam awwalu, yakira sani da rabe yasanar dasu zuwan bakin, saidai babu wanda yasamu zuwa,kowa yakawo uzirinsa wanda bashi da tushe bare makama,


Dan haka saiyakira mako cinsa malam lawal baban su sani da shi akayi komai aka tsaida ranar watan maulidi wata shida kenan nan gaba,

Ankawo kudin neman aure dubu goma da haka aka rabu vikin mutumci.






Washe gari ummu take sanar da zuhra antsaida ranar aurenta da abbas tadaiyi shiru bataceba komai saboda kunya.











Maman sadeeq

[9:25PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣4⃣








Na

Maman sadeeq















"'

Ayau asabar  babu aiki,

Aduk week end  yakan kwashi yaransa yakaisu gidan hajiyarsa su gaidota idan suka taho kuma yakam biya stores dasu jifatu ko sahad, donyiwa yaran  sayayya,

Kowa yana jidar abinda yakeso,

Saida suka gama sannan shima ya shiga jidoma iyayen  yaran dashi kanshi.

Saida yagama yatafi wurin da ake bian kudin,


Anacikin lissafine itama ta iso tazabio abinda takeso,

Saidai ita kananan kayane irin na turawa wato (english wears),tadauko kala hudu.


Takalleshi atake taji aduniya bqtataba arba da halittar data firgitataba irin sa, tabbas ya burgeta matuka, anan take takamu da a zababben sonsa.


Kamar ance yajuyo sukayi ido hudu dashi, da sauri tasauke idonta, shiko tsagar rumancin  dake fuskarta ita tatadomashi tsohon mikin  dake zuciyarsa, bawai yamance da itaba, ko yadaina santaba, a'a yadai samu saukin azalzalar dazuciyarshi take mashi, saigashi yanzu mikin yatasi ganin mai irin tsagarta,


Itakam saita wayance  da daukar munubiya tace.


"fine baby ya momy?

Yarin yar tayi dariya dantana da saurin sabo  da shiga rai  kasan cewarta mai kyau,


Ta dubesa cikin salo tace,

Ranka shidade niko zanso kabani babyn nan,


Yayi dan takaitaccen murmushi yace 

Ni idanna baki mamanta bazata bakiba"'


Tayi murmushi jin ya tankamata tace

Ai indai kabata magana to itama zata yarda tabar min ita"'.

Yace to kibari ayayeta saimubaki,

Tace to ina zaka ganni?

Yace muhadu anan".


Yakarbe diyarsa suka fito daga store din.

Tayi masu kuri da ido tana kallonsu, har yahau titi ya harba motar,


Wata ajiyar zuciya tayi akayimata lissafin yan kayanta tabiya tafito ta tsaida adaidaita sahu tanufi gida, 

Harga allah bayarinyar ce taburgetaba ubantane ya tafi da hankalinta,


Dahaka ta isa gida ta iske babanta rabe

Yahauta da masifar taje tayi zamanta akasuwa,

Ta zobare baki tayi shigewarta daki ta kyaleshi da sababinsa,

Daga karshe sai yajuya kan lubabatu wacce akullum sai sunyi imbata, indai ita bata jawoshiba toshi ya jawota.










"Shikam lamido darajar tsagenta taci har yatsaya yana musayar yawu da ita,bqdan wani abuba saida yataoma yake jin haushin meyasa baitambayeta kotasan wacce take wahaltar dazuciyarsaba?

Babu mamaki tasanta, wani tunani yayi kuma saiyaga wawtarsa,

Ta yaya zata santa daga sunkadance da tsage iri daya?


Mutane nawane suke da tsagen rumawa a kano?.aibasu kirguwa.


Da haka ya isa gida  ya sauke yaran kai tsaye yanufi sasjensa don yana son  yatunano yarinyar data dabaibayemasa zuciya,hardama ruhi gaba daya,







Yana begen ganinta koda jakurine yabata,akan abin da yayimata, inyaso daga baya kuma ya shigar da kansa agareta da kuma bulatarsa,duk da yadan zaiyi wahala ta karbi bukatarsa kasan cewar zalintarta dayayi,da farko,

Saidai duk dahakan ganin ta shine abu mai wahala.


Yayi alkawarin saiya samo soyayyarta koda kudi,koda kalamai.

Atake yashiga tariyo siffarta da kamanninta,fara ce tass tana da tsayi basosaiba, tana da dogon hanci da manyan idanu,

Sai tsagar rumawa wadda takarbi fuskarta tare da karamata kyau.


Tunda yake aduniya baitaba ganin wanda tsagar rumanci ta amsaba kamarta,

Duk da yarinyace shekarunta baza su wuce sha bakwaiba zuwa sha takwas ba.

dukda karancin shekarunta ta mallaki abubuwan dayakeso dadama,  saidai daganinta suna cikin matsin rayuwa.


Yagane hakanne ta hanyar suturar dake jikinta,

Bawasu kaya masu tsadabane ajikinta amma kasancewarta mai tsabta da iya  tsara ado yasa ba agane babun datake ciki.


Wata ajiyar zuciya yasaki tareda shafar sumar kansa  ya lumshe ido, sannu ahankali ya furta,

"Ubangiji katakaitamin wannan wahalar tahanyar sadani da farin cikina",.


Tadade atsaye bisa kansa, da ace dakarfi yayi furucin da babu abinda zai hanata taji, tadaiga yayi mimi da baki batasan abinda yake fadaba, gaba daya ta kwanta abisa gadon ta rungumoshi,


Yayi saurin bude ido  yaganta yace hajir yaushe kika shigo?


Tayi farr da ido tace yaushe zakasan nashigo naga kanata mimi da baki?


Yayi sauri yace kenake ta ambato saikuma gaki"'.


Ta tsura masa ido tana so tagano gaskiyar abinda yafada kokuma sabanin haka?

Tace to aigani na iso".


Yace to bacci nake son nayi yaza ayi kenan?


Tasan abinda yake nufi dan haka tashiga aikinta.

Tadauki lokaci tana masa tausa  har ta tabbatar yayi barci,sannan ta sumbaci goshinsa tafita ta koma falo.

Wayarta tajiyo tana kara da sauri ta isa ga wayar .

Sunan laila sanata tagani, dasauri ta dauka tare dafadin 

"Yan dubai  kardai kicemin kindawo?


Laila tace tunjiya naso inkiraki allah baiyardaba mene labari?


Hajir tace labarai kai don yafi gaban guda, dama amatse nake ki saurareni zuwa gobe"'.

Laila tace to shikenan ina saurarenki,

Sukayi sallama.








Maman sadeeq

[9:26PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣5⃣


Na

Maman sadeeq








"washe gari karfe shabiyu taje tasanar da lamido cewar zataje gidan laila sanata.

Yace saitadawo kudin dayabata kwanaki dubu dari ukku su ta kwaso,tazua ajaka.

Tadauki siyama tasa acikin mota tayi ribos aka bude mata gate tafita sai nassarawa G.R.A gidan laila sanata.


Bayan gaisuwa da tambayar bayan rabuwa, laila tace to menene bayani?

"hajir tace kedai bari laila yanzu sonake kiyimani jagoranci zuwa inda kikace don yanzun adubu nafito.


Laila sanata tayi murmushi tace yanzu kinji uwar bari kenan,imbanda abinki hajir yoshe zaki zauna ki mike kafafu, ai mata yanzu sundaina zama hakanan siddan, abin haushima waike maikamar lamido kice wai bakida kudi,abinnan yaani haushi,

Ai idan baki tashi kinnemi taimakoba akan jawaheer ba aikin tashi kinema akan lamido.

Ko dan yarunkabaki abin duniya,

Tunda kina ganin bakinki zai isa kaidin jawaheer.


Hajir tayi saurin cewa, wlh laila bakina bakina bazai ishi wannan yar iskar matar nanba, kusan abinda tayiminne yasa naji kwarin gwiwar naiman taimakon nan,

Dan innunamata cewa har gobe gawar giwa tafi karfin kiyashi yajata.



Sonake nasamo zuciyar lamido,yazamo nikejan linzaminsa,

Sai abinda nace zayyi,

Yazamana babu wata mace agabansa saini, tahakane shaidaniyar matarsa zata kiyayeni,



"laila tayi murmushi tace wayafadamaki barno gabas take?

Yanzune zakisan mekikeyi,

Yanzune zaki zamo big hajiya, big madam,

Ni bakin cikina daya da har yanzun bakitara tsiyar komaiba,

To wai jirama yanzu kina da kudin da zamuje a amso maki taimakon?


Hajir ta ce eh nasamu dari ukku shima saidanayi dan azancinnan namu namata sannan yabani, saidai wani abin takaicin nina roki kudin amma daatashi saidayabamu da matarshi.


Don wata salon kissa sai cewa tayi wai ita bata da bukatar kudi, atakaice dai laila saida yajara mata wasu akai.


Toduk ki arsu anzo wurin.

Kuma dani suke zancen.


Laila tayi wani murmushi natakaici tace.


"aike kinji matsalarki hauka da har gowa,wayagayamaki ana samun nasara cikin gatsali da hargagi?

Kinga ita dayake tasan kanta saitabiyo tajanyar kissa,

Tokema dazakiyarda sai ince kirunka hadawa da yar kissannan zakifi cin ribar abin.


Yo mace dama ai yar kissace, duk macen dabatada kissa nigani nake bata cika maceba, musamman ma tsajaninta da mijinta.

Ke tsaitsaye shi tsaitsaye to ina  nasara anan?




Nasan halinki sarai hajir bakya iya boye damuwarki, shiyasa aka sha gabanki,

Yanzudai tashi muje mukarasa ma ida bayanin acan.".




Amotar hajir din suka fita kabuga sukayiwa tsinke gidan wani dan tsubbu, wanda keyiwa laila aiki tayarda dashi sosai shiyasama takai hajir din wajansa.


Sunyi sa a basu iske kowaba awajansa .

Bayan sungaisa laila tashiga koro mashi bayani,

Yayi shiru zuwa can yadauko wani faifai ya zuba yashi akai yayi zane akai,

Yayi zane da yatsu yadubi  hajir yace.


"kadan yarage ayi babuke, don kishiyarki tayi nisa azuciyar mijinku,

Kuma ita din bahaka take siddan ba,

Allah yataimakeki dakika farko kika fito naiman taimako, yanzu maikikeso ayi maki?"


"hajir ta sauke ajiyar zuciya  ta dubi laila sanata  da aon jin abinda zatace, laila tace kiyimasa bayanin duk abinda kike bukata,

Dan kinzo inda za a sharemaki hawayenki, karkiyi shayin komai kifadamasa.


Hajir tace  malam idan zai yuwu zuciyarsa nakesan mallaka,

Ma ana yazamo sai abinda na tsaramasa.

Kuma akauda masa hankalinsa kan kishiyata shine kadai abinda nakeso.


Malam yayi shiru yasake yin zane akan yashi, zuwacan yanisa sannan yace,


To allah yasa zaki iya dan dakamar wuya gurguwa da auren nesa.



Laila tayi sauri tace masa zata iya komeye fada.


Yasake nisawa yace gaskiya zayyi wahala ta  iya,

Dan ko amaza bakowane zai iaba bare mace.

Kuma aikin ba abama wani yayi sai idan itace zatayi da kanta.

Shiyasa ma nake ganin bazata iyaba".


Laila tace malam zata iya aimacece maikamar maza kwarine  kawai bata dashi"


Malam yayi murmushi yace ainacemaki mai kwarinma ba kowabane zai iya ba.


Hajir kam jikinta ya sona yin sanyi jin abinda malamdin yake fada.

Tunda yace bata iyawa to bata iyawa din.

Dazata iya da baice bata iyawaba.

Tadaiyi karfin hali tadubeshi tace,

"gafarta malam afada idan zan iya sai inyi".


Malam yace  to shikenan kamar yanda kikayi bayani akan son mallakar mijinki aikin dazan yimakine nahanga.

Layace kingantanan zaki hada da kan koren kadangare (jan kwataki).

Zaki fiffisge kansa da ransa, batare dajin tsoro ko firgitaba,

Idan kika aikata haka to mijinki zai runkajin tsoron mata tamkar mace da kadangare.

Yaya kikagani?"


Tabbas dukansu sun karaya basuyi zaton hakavzata kasanceba.


Hajir ta kalli laila sanata,

Laila tarugata cewa "

" Yaya zaki iya?


Jajir  tadubi malam tace gaskiya gafarta malam bazan iyaba,

Aini yanda natsani kadangare ko mutuwata bana jin tsoro haka nan."


Laila tace bare kuma ni aini ko tsaka bana iya figewa kai bare koren kadangare.

Gaskiya malam asauya mata wani dai".

 Malam yayi murmushi yace sainajiko kamar kince macece maikamar maza?


Hajir tace agaskiya malam duk jarun tata  bazan iya wannan aikimba".


Yadubi laila sanata yace kinga kuwa anyiwa wata irin wannan aikin kuma ta aikata babu tsoro ko fargaba atare da ita.

Ayanzu haka tanacan tana shimfida  iko agidan  mijinta.

Anan inda kike zaune anan ta cisge kan kadangaren tayada gangar jikinsa.


Laila tayi sauri tatashi tana waige waige.

Malam yayi dariya yace meyabaki tsorone?


Tace yo malam cewa kayi nan tayarda gawar kadangaren?


Ya ce aiyamutu bashi darai"


Tace a'a baridai insake wuri,


Malam yace tunda nake bantaba ganin  tsabar tsana irin ta mata da kadangareba.

to dazakiyi da mijinki zai ruka tsoron mata kizama ke kadaice agabansa, bazaitaba duban maceba nayanke, saidai ansamu matsala kedin bazaki iyaba.


Hajir ta muskuta sannan tace to gafar ta malam yanzu ya za ayi?


Yace zan gwada nagani saidai asake imaki wani aikin amma azayyi tasirin na farko ba, ba kuma lallai bukatarki tabia dukaba.


Hajir tayi shiru zuwacan tace malam abani zan iya aibiyan bukata yafi dogon buri.


Malam yadubeta yace zaki iya?


Tace "eh"


Yace tokinji dai bayanin danayimaki idan har aka samu kuskure to kaikayi zaikoma kan mashekiya."


Batayiba sayin komai tace allah zai kiyaye".


Yace yana dai dakyau kakiyaye sai allah yakiyayeka,

Laila tace karkadamu malam aidama nafada maka zaka iya ai mace ce kamar maza kabata kawai".


Yace to shikenan


Yadauko wata laya yabata yace idan kin fisge kan kadangaren daransa saiki  bude bakinsa kisaka masa wannan layar aciki, saikisamu ruwa mai gudana saiki jefa kan kadangaren bayan kin ambaci sunan mijin naki  sau ukku.


Yadauko ruwa cikin wata yar batta ya ce


Wannan maganin kuma kizuba masa cikin abin cinsa, daruwan dazaisha lemu ko zobo, sauran lbr kuma keda kanki zakizo kibani lbr.


Hajir tayi ajiyar zuciya takarbi layar da battar maganin.


Laila sanata tace to malam mungode yanzu menene abin sadakar? Kawatace ina so ai mata abinda zata dawo gobe ko babu ni.


Yace to babu damuwa tabada dubu dari da hamsin, tunda wannan shine zuwanta na farko"


Hajir tabude jaka ta dauko kudin tabashi ta dora dafadin


Tokamar yaushene yakamata nafara gaba tar da aikin?


Malam yace yawwa ranar laraba koda asuba ko gefen magruba,


 Hajir ta jinjina kai sukayi godia dashara din kome kenan zaiji bayani dahaka suka baro  wajan malamin


Hajir tasauke laila sanata agidanta itama tanufi nata gidan.







Maman sadeeq

[9:27PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣6⃣


Na 

Maman sadeeq













Tadubi kawarta tace "zuwaira"  dama haka so yake idan yashiga baya shawara?


Itama xuwaira takalleta tace  "fa iza waidagaske son man dinnanne yamaida ke haka?


Fa iza tamirgina kai tace ".zuwaira ashe duk abinda nakeyi aikin banza nakeyi, ba sobane shiemene, yanzune nakeyin so wanda ya amsa sunansa so,

Inaji ajikina idan har narasa man dinnan to ko shakka babu zan iya rasa raina, kitaimaka min zuwaira yaya za ayi nasameshi?


" zuwaira tayi mata kuri da ido tace karkidamu fa iza zaki sameshi koyana so kobayaso, indai acikin kano yake saimun farautoshi,

Kedai sha kuruminki,

Matsala daya zamu samu shine rashin kudi ko kina da kudi ne agurinki?


Fa iza ta gyada kai tace a'a nibanida kidi, amma karkidamu naga inda baba yake ajiya.

Ammani matsalar danake gani inaxamu sameshi?


Zuwaira tace ke a'ina kikaganshi?


Fa iza tace a sahad naganshi"


Zuwaira tace tocan zamuje babu mamaki ko sunsanshi,

Kinga saisu kwatantamana , idanma basu sanshiba saimu yawaita zagayawa store din har allah yasa mudace daganinsa,


Da sauri zuwaira, ammafa saimumbi abin ahankali, dan sonake mubi komi asannu,


Fa iza tace to shikenan muma tafi yanzun mugani,


Zuwaira tace kingani ko?


Saifa kimbi ahankali babu abinda gaggawa zatamaki,mubari sairanar week end watakila ma aikacine,tunda airanar asabar kikaganshi ko?


Tace eh"


Tace to mubari sai asabar din sai muje kawai.


Fa iza tarangwadar dakai tace wato zuwaira idan ba man dinnan na auraba tosaidai immutu banyiba aure, donshikadai naji ina so

Ko habib da danakeso saiyanzu nagane ba sobane shirmene.

 

Zuwaira ta jinjina kai tace to yanzun yazakiyi da habib din?


Yakuwa zanyi dashi yakama gabansa kawai, aiyaci moriyar ganga tunkafin yayada korenta. Saimurabu,

Saiyanzuma nakejin  zafin yarda dawasu abubuwa dasuka faru atsakaninmu,


Zuwaira tace dan allah share kawai aikema kin rage zafiko,?tunda bashi kadai yaji dadinba,

Muture zamcen danni yanda nakeji ayanzu babu abinda zaihanani kula maza, saboda dai ina kawo wuta ,

Yanzu ke idan mutumennan yana da mata yazakiyi?


Fa iza tayi wani murmushi tace

"zuwaira kenan aikoda dakikaji nace bazan auri mai mataba bansaneye soba.


Matarsa kuwa ko ba afadamakiba aike maiba wa kanki amsace,

Nice dil akan yana da mata, tunda naganshi dayara har biyar,

Saidai bana tunanin duk yayansane don bai isa ajiye wadannan yayanba.


Matarsa kuwa karyarta duk takafin inshigoce ,dan danasamu nasarar shiga itajam waje rod,

Donhaka bari damun kanki dazancen matarshi ni bata gabana.


Zuwaira tace to allah ya kyauta"


Tamike tace ni bari in wuce sai asabar din.



Fa iza tace to muje in taka maki.

Sukafito tayimata rakiya saida takawota harbakin titi sannan ta koma.






Tana zaune tsaye tana jiran adaidaita sahu, shikuma yakaryo kwana cikin motarsa tundaga nesa ya hangota, don haka ya gyara  fakin yafito cikin fara a yace a'a zuwaira kece anan?


Tayi murmushi tace eh nice dama yanzu nake niyyar kiranka saigaka."

Yace to shigo mota muje kawai  dama cefanene ankaiwa lubabatu inyaso immun kammala da komai ankaimata.


Xuwaira tace nilam rabe ina tsoron kada fa iza tagane akwai wani abu atsakaninmu".


Rabe yace karki damu  zuwaira, 

 Uwar Fa iza ma akar karkashina take bare fa iza  kedai abinda nakeso dake karki kula kowa bayanni kinjiko.





Maman sadeeq

[9:28PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪1⃣7⃣


Na

Maman sadeeq












"Ranar asabar zuwaira da fa iza sukayiwa sahad tsinke,

Saidai rashin sani wanda yafi dare duhu, da acema sunsan gaibu dasaisunufi jifatu, dan wannan asabar din can yayiwa tsinke,

Suka shiga sahad suka cigaba da baza ido, ko allah zaisa suyi dacen ganinsa, amma bawani lbr sai suka dire dqwani security tayi masa kwatancen mutumin yace yaganeshi,kuma baizo wurinsuba.

Saidai yalarbi lambar ta da sunan idan yazo zai kirata, tayimasa ihsani mai yawan gaske.


Tana shiga gida Rabe ya dubeta yace wato.  Fa iza bazakiyi abinda na ke fadamakiba ko?


Har sainawa zamfadamaki banasan wannan yawan yawonnan da kikeyi?


To allah yasa inkara ganin kimfita ni inci mutumcinki.


Tavsoari baki ta shige daki, shikam rabe riga kafi ce yakeson yayi, yana tsoron kada ayi masa abinda yakeyi,

Shiyasa yake kaffa kaffa da fa iza.

Baisaniba yamakaro, don babu  yanda za ayia aiki yafadi sanransa.

Duk abinda kayiwa dan wani kaima dole ayima naka


Imbandama rashin tsinkaye aikamata yayi yarabata da zuwaira tunda shikeda tabbas akan zuwairar, to amma yamanta da hakan.






Yacigana da fadansa , ina dalili katiwa kamar fa iza tarunka ficewa yawonta?

Toninagaji idan har bata fito da mijiba to nizam bada sadakarta ga gardawan malam bukar, nikam nagaji bazaki daukomin maganaba.


"lubabatu tace haba dai sadaka sai kace " gyada amaro"?

Canza tunani fa iza auren soyayya zatayi, aikaidin ba doleba akayimaka ba.


"To shikenan allah yasa inkara ganinta tafita yawon ".

Cewar rabe.


Fa iza dai tana jinsu bata ce ko uffan ba,

Dontasan shima baban fada kawai yake yi, to ita kam ba da itaba, indai ba man dinnan bane tosai dai ta mutu ba aure.




Tana zaune tana daura kunun aya, yashigo kamar anjefoshi, ummu harta dan tsorata, yayi murmushi yace 


Har nabaki  tsoroko?


Yi hakuri na zaqu inganni agabanki".


Tace gabana kuma rabe?


Yace eh kardai ace baki fahimceniba?


Tace ni bam fa himce kaba indai kudin hayane ai wata baicikaba, bare kace sukazo karba, 

Idan kuma zumunci kazo aiwurin dan uwanka yakamata kaje, amma saikace waika kosa kaganka agabana?

To inyimaka me?


Rabe yashafi gemunsa yace babu mamaki idan kika ce baki ganeba sa boda ba gadon hausaba kikayiba,

 Haye kikayimata,

Toni bari nabaki abin abayane kuma awar ware,


Aganina kina bukatar taimako shiyasa nazo, don intaimaja maki,

Mukuma rufama junanmu bargon asiri.


Zanjiar dake dadi idan harkikayarda da bukatata,

Zan fito da martabarki da kimarki acikin yan uwanki mata,har ki manta mainene kadaici,

Dan nasan yayana lusarin namijine cutarki kawai yake.


Ammake kinki ganewa.

To kiyarda da bukatata. Kiga yanda zakizamo zara acikin taurari.


Danni wlh burgeni kikeyi  

Musamman idan nakalli surarki,

Dan dai kedin bakiwayeba. Yayana ya dinkimeki agida.

Ai mace mai kyau ribar kyawunta takeci dantasan akwai bambanci tsaka ninta da marar kyau.


Kekau da kyanki da komai amma ankasheki duk da dai kina da sauran mamora, nikam ina sanki ahaka.

Na tabata zakijini da bam banci ajan tala surin mijinki.

Wanda baya iya tsinanamaki komai sai minshari, da gur nani 

Yanzu me ake ciki?


Ainadauka kin gane abinda nake nufi, azatona kinanan kina jirana duk danasan bazaki bani matsalaba",.




Yasake shafar gemunsa yana lumshe ido azatonsa zai yaudari zuciyar ummu harta sallama mada kanta, wanda hakan yake jira daga gareta,

Wata sha awartace take bijiromasa.





Ummu taji wasu hawayen takaici suna zubomata dukda tadade da harbo jirginsa.


Tadubesa tareda kiran sunansa rabe kabani mamaki, wlh banyiba tunanin haka daga garekaba.





Maman sadeeq

[9:28PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣8⃣




Nq

Maman sadeeq










"Tuni na hasaso abinda yake nufi akaina,

Kasani ko gawata tafi karfinka dakiyayewar ubangiji,

Kayan ka kuma sunanan ba mutaba suba tunda ba abada da tsarkin zuciyaba".


Tatashi tashige dakin maigidan idonta yagama rufewa shiyasa bata lura dawanda yake tsayebA abakin kofar shigowa,


Tadauko kayan tadire agabansa tace dauki kayanka kafice daga gidannan tun banyimaka ihu kwartoba'".


Dayake dan duniyane baiko damu da maganar data fadaba, asalima sai shafar gemunsa yakeyi, yakuma yimata kuri da ido yana kallonta,


Tasake cewa katashi kabar gidannan tun muna mubiyu'


Baiko motsaba .

Gyaran murya yayi dasauri  suka juyo su duka ,

Wazasu gani?


Malam awwalune  tsaye abakin kofa.


Cikin sauri rabe yatashi yace a'ah yaya to gara da allah yakawoka, wlh bakayi dacen mataba, shiyasa mika kafe akan kin auren irinsu tubabbiya,

Saboda ba tubar allah da annabi sukeyiba,

Yanzu dan allah wannan aikin dame yayi kama wai matarka tanemeni saboda rashin sanin menene musulunci,

Ashe duk yaudarar mutane takeyi da kalamanta  masukama dana mai tsoeon allah,


Nikam sai dai ince allah ya isa kuma duk kai kajamin dakaje ka auro arniya takan dutse, wadanda basu san meye allah ba,


Kuka yake harda sharbe.


Atake ummu tadora hannu akai ta rushe da kukaai ban tausayi.


Nashiga ukku ni Aisha ubangiji kakawomin dauki dan alfarmar annabinka mai fiyayyan daraja.


Tacigaba da raira kukanta.


Malam  Auwalu yayi kuri da ido yana kallon dan uwansa,yana jinjina girman kinayar Rabe.


Ummu jin mijin nata yayi shiru yasa tatabba tar mujin nata yayarda,

Da sharrin da kanin mijinta ya lika mata.

Ko shakka batayiba shirun yana nufin laluben hukuncin dazaidauka akanta yake


Takara fadada bakin cikinta shikenan mutumen dayazamemata uwa da uba  yau anshiga tsakaninsu,

 To itakam wazata dosa.

Allah shine gatanta shikuma zaifitar da ita.

Dan haka tayi shiru taji hukuncin damijin nata zai yanke akanta.







Malam Auwalu yadubi dan uwansa rabe ya dage iya karfinsa sai tikar kuka yakeyi, kamar wanda yarasa iyaye .

Cikin wata irin murya yakira sunanshi.


"Rabe"  yayi saurin dagowa yace na am yaya"


"malam auwalu  yace kacuci kanka danni baka cuceniba .

Babu abinda zancema ka  saidai allah ya isa .

Kaje abunka babu komai aiduniyace,kudin kunzame mani WUKA A MAKOSHI, ammani bakayiminba kanka kayiwa  tashi kaje abinka Allah yayi min sakayyar abinda kayimin.


Aisha ko dayarda allah ko gawarta alla bazaibaka ikon cutar da itaba kuma da ikon All........"

Wani tari yasarkeshi yakasa karasa abindayakeson fadi abin kamar turi tunyanayi daga tsaye hartakaiga  yazauna, babu wani dagi bare afuwa 





Ummu tadauko ruwa tabawa mijin nata saiyazamo maimakon yasamu afuwa , sai abin yazamo tamkar wuta ake zubama fetur.

Ana cikin wannan halin Rabe yazare jiki yabar gidan".




Zuhra ce da kannenta suka shigo, ganin halin da baban nasu yake ciki yasa hankalinsu tashi.

Acikin daren ne suka nufi asibitin malam aminu kano.

Likitoci suka taru akanshi,saida suka shafe rabin sa a akansa  saidai saukin Allah.


Anyimasa allurar bacci wadda yasamu saukin tarin  saboda baccin daya daukeshi,



Zaune take kusa dashi gefen gado tanata  sharbar kuka.


Cikin karfin hali  yakamota yarungume yana bata hakuri .

Har saida tayi shiru,

Saidai hankalinta bai kwantaba, haka sukaita fira saikace baciwa yakeba



Karfe goma yace Aisha nikam barcinakeji,

Sai ince allah yabamu alkairi,



Karfe shida na asuba ta farka agigice, sakamakon mafarkin datayi,

Asukwane ta isa gaan gadon, takama hannunsa saidai babu wata jijiya datake aiki ajikinsa.

Tasaki hannun yatafi lakwaf.

Tasoma jijjiga shi saidai tuni an amsa kiran mai duka.


"sannu ahankali ta sulale akasa babu alamun numfashi atare da ita,


Su biyu ne  wadanda ke dakin, wata mata ce  ke jinyar danta ita kuma baccinta ta keyi, tsawon awa daya tayi asumi ta farfado,don kanta azatonta mafarkine tayi , tanufi gadon , saidai wannan karon ta tabbatar daba mafarkiba takeyiba,


Tadubadhi taga tabbas yakoma ga ubangiji,

Wata dan gana tasamu daga ubangiji, babu hawaye afuskarta,saidai tana jin jikinta tamkar babu lakka,

Dahaka tasanar da liki tocin aka hada mata shi acikin motar ambulance ta nufi fi gida,


 Malam  mande mahaifin abbas yazo ya shirya shi aka  kawo mankara  za asakashi, aka kira ummu tazo tayi mashi sallamar ban kwana.


Zuhra ma saidai bakinta yarufe takasa cewa komai,  dahaka su abbas da malam lawal suka dauki mankarar zasu fita da ita.

Anan zuhra tayi sauri tabi bayan abbas, takama mankarar ta ruke tareda rushewa da kuka.


Innarsu sani ce ta kamota ta ruke ita kam ummu takasa ko motsi, kyafta ido kawai takeyi,


Dagudu zuhra tabi mankarar saidai idonta tuni ya hangomata wasu kananan taurari,suka  baibaye mata idanu,

Kunnenta ko wani dammm taji , daga haka batasake  shaida komaiba saidai farkawatayi taganta akan gadon ummu, fatanta daya wannan mafarki yazamo kuma nakarshe.


Dirowa tayi daga kan gadon  tafito saidai  taron matan datagani shia tabatar mata da mafarkinta yazamo gaskiya.

Daga baya kuma sai tagane ba mafarkiba takeyi suma ce tayi, yanzu tafarfado akan kudingar dakin ta zauna tana kare wa matan  dasuke zaune karbar gaisuwa kallo,

Sai binsu da ido take.


Mata sukayi tashigowa sunayin gaisuwa, ahaka suka yini cikin alhini.












Maman sadeeq

[9:29PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪 WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

1⃣9⃣



Na 

Maman sadeeq


















" washegari  mata suka fara cika gida don karayin ta aziya,

Lubabatu ce tashigo tare da balaraba matar sani.


Lubabatu tace .

"mutanen annabi muhammad (S.A.W)yahakuri?


Saurqn matan dabasu fahimci metake nufiba suka amsamata hakuri sai ma aiki,


Lubabatu ta dubi balaraba tace to itakuma ta annabi isah ya akeyimasu gaisuwar?


Balaraba tatabe baki tace.

"yo Allah yakara masu nauyin kasa ko?


Kodayake aishi da musuluncinsa indai bakaza ta ja zakaraba",.


Lubabatu tace to saimuce kedudamma?


Balaraba tace to ke kya iya fada, nikam bazan tofaba,

Abintakaicima nibansaniba lada zamusamu ko zunubi?


Ummu tadukar dakanta kasa , inda sabo yaci ace tasaba, tosaidai yakamata suyimata adalci subarta taji da abinda ya isheta,

Sukuma sani gidan makoki sukazo ba gidan biki ko sunaba,

Saidai batace dasu ko uffan ba.



Innarsu sanice tayi masu magana dacewa haba bayin allah nanfa gidan makokine ba gidan bikiba,

Kubarmu muji da abinda ya ishemu mana,

Amma kunzo sai wadansu zantuka kukeyi kamar wadanda basusan allah ba".



Lubabatu tace a yo imbanda abinki ai wadan da suka san allah sune suke makoki idan anyi masu mutuwa,

Suko arna aishagali sukeyi idan anyimasu mutuwa,

Nidama yanzu zantambaya yaushe za afito da ashobe(anko)?

Don inada heade dina (gwaggoro)"


Innarsu sani tayi shiru don rashin mutumcin nashi mai girmane.


Balaraba tace 

Aimaganinshi kenan dayaje yadauko arniyar kan dutse shiga shehu mujaddadi.

Wai jihadi,yo arne ko yace ya musulunta ba karyar anza bace?


Aigashinan andamke mashi kurwa yasheka lahira, mukam kur warmu kur wlh"




Zuhra tadubesu tana girgida kai  tace 

"Dongirman allah inna kuyi hakuri kubarmu da rashin da yasamemu".


Lubabatu tayi sauri tace,

"ke naimi  uwarki tun wuri bai kuremakiba,


Tayi mata nuni da ummu 

Gatanan ialan oduduwa, itace uwarki nikam ina da diya,

Bana bukatar  diyan barbarar yanyawa gayyar  sodi su ingozi, koda balaraba kike?

Balaraba tayi wuf tace,


Wace ni?

Nima inada nawa diyan masu tsarki ba ruwa biyuba".


Lubabatu tace nikam nagaji dazaman gidannan gara muwucevgida kawai,

Balaraba tace ni aibammasan matsayin wannan zamanba , lada ko zunubi?


Aida wannan zaman dazaman ajo asuda bambanci,

Garama zaman ajo kinga karuwai da yan daudu wadanda suka kure duniya da iskanci, amma nanfa?

Sai karyar hijabin karya  da yaudara,dawata munafukar carbi kome ake fada?


Balaraba tayi dariya tace,

Yome za afada dayawuce YESU da JESUS dasu ALMASIHU?"


Lubabatu itama tayi dariyar  tace .

"To can gasu gada, gayyar sodi arna a idi........


Tashi muwuce  tunsu loma basu karasoba,


Balaraba tamike suka dubi ummu,

Sukace to allah yakara nauyin kasa,

Mu zamu wuce,


Dahaka suka fice daga gidam makokin innarsu sani tadubi ummu tace,

Kiyi jakuri Aisha rayuwace  duk yanda mutum yadauketa haka zata riskeshi allah ya shiryesu,


Ummu tace bakomai inna nidana rasa mijinama nakuma hakura yaushe zan zauna insauraresu?

Aikowa yayi nagari dan kanshi,


Ahaka akayi zaman makokin har zuwa kwana ukku, inda akayi adduar ukku, sun sami karamci daga mutanen unguwa.

Tunda akayi rasuwar mutane kekawo abinci musamman innar su sani da salame dasauran mutanen unguwa,


Haka aka dare akabar ummu dasauran yaranta su hudu, dagasu saisu har kawowar yanzu batagaba rabe da sani ba bare kuma turai,




Saida aka kwana biyar darasuwa sannan sani yazo 

Atsaitaye yayimata gaisuwa yakawo dari da hamsin  ya bata.

Takarba tayi godiya,

Bata rainaba yakakkabe rigarshi yayi gaba










"tadubeshi ciki salon yaudararta  tace,

Hubby wai meyake damunkane kwana biyu?

Nagabaka walwala, kumani saiyanzun nake ganin ramarka?"


Tace to taso mushiga daga ciki ingusar maka dada muwarka".


Haka taja hannunshi suka nufi dakinshi,

Kamar yace mata indai zaki iya gusarmin dadamuwata tonemomin yarinyar dake wahalar da zuciyata, saidai bazai iyaba,

Idan ma yana so gayyar tawatse to yasako jawaheer bare kuma wata wacce ba matarshiba.


Sala salo take mashi waidan duk taja ra ayinshi, saidai takasa samun hakan.don zuciyarshi tayi nisa da begen watanta,


Baccin dole yakirkira don yasamu ta kyaleshi,tafito daga dakin 

Wayarta tadauki tsuwwa  taduba saitagavsunan laila sanata, tadaga bayan sun gaisa laila tace.


Najiki shiru, shine nakira donjin meyene lbr kin aiwatar da aikinne?


Hajir tace wlh laila banyiba.

Saina kudiri aniyar aikatawa sai tsoro yakamani, anyako zan iya?


Laila taja dogon tsaki tace.

Maizai hanaki iyawa?

Airufe ido zakiyi imbahakaba ko kya mutu atsaye kicire tsoro da shakku  kirufe ido,ki aikata aiki a aikace ,

To imma baki aikataba haka zakiyi asarar kudinki?

Kuma kizauna bakin ciki yakasheki.



Hajir tace tobari ingani idan zan iya.

Wlh dana tuno koren kadangaren nan sai inji gabana yafadi sai inga tayaya zan iya bin kadangaren in kamoshi har in cisgemasa kai?


Laila tace kibari nizanzo inkarfafa maki gwiwa  dan ayi abun cikin lokaci.


Hajir tace to kamar dayaushe zamuje?

Kinsan yace asubahi ko gefen magruba.


Laila sanata tace to muje da gefen magriba, danni da asuba bana tashi ko sallar asuba, bare intafi kamun kadangare,


Hajir tace nikuma kinga  adaida lokacin lamido kedawowa daga aiki. Gashi kuma jibin nikeda girki yaza ayi kenan?


Laila tace kina iya hakura da aikin kawai inyaso  saiki tarairayi lamidon tunda kina ganin abun zaizomaki dasau.....


Dif tadatse wayarta , hajir tayi shiru tana tunanin yanda zatayi ta iya aikata aikin dole zata rufe ido ta aikata, indai tana son mallakar lamido a hannunta.


Takira lailai tace yazaki kashe wayar laila?


To mezance maki alhalin kince bazaki iya barin mijinkiba?

Ai saikiyi tazama daddawa uwar aure,

Hajir tace kisaurareni larabar zanzo muje.

Amma im munje ke zaki kamo min kadangaren, nikuma sai in cire masa kan,


Laila tayi sauri tace.

Wlh bazan yiba ubanwa?

 Kidai yi kidanki kuma kiyi rawarki inkuma kina ganin baza ki iyaba to ki hakura kawai,

Nikam rakiya kadai zanyimaki karkisa ran zammaki wani abu,


Hajir tace to kidai saurareni.

Suka ajiye wayar.







"Ranar laraba tunkarfe ukku hajir takira hubbyn ta tasanar dashi zataje gidan yayarta munnira, yace saitadawo.


Tadauki hanya sai gidan laila basu tsaya komaiba suka fito.


Laila tayiwa hajir nuni dawani katon koren kadangare tace.

Kinga allah ya takaitamana wahala, inyaso saimu wuce hadeja road akwai wani ruwa mai gudana  saiki jefa kawai".


Jikin hajir yadauki rawa kyarma ta kwacemata.


Laila tace karkimanta hajir sai ansha wuya akanaha dadi,

Kituna abinda kikeso kizamo mijinki  atafin  hannunki, jawajeer ko zata zamo tamkar bola, itadaice abokiyar adawarki to saiki zaba".


Wani karfi yazowa hajir tanufi inda laila tanuna mata kadan garen,

Saidai wani abin mamaki  kadangaren baiko motsa daga indayakeba ,hasalima kallonta kawai yake, saidatazo gabdashi taji wani tsoro yadirar mata tadan jabaya.


Laila tace karasa mana?


Hajir tayi tsaye takasa karasawa duk abinda sukeyi akan idon wani dattijo,

Azatonshi wucewa zasuyi sukejin tsoronshi.

Yazo kusa dasu yace.


Yata wucewa zakuyine yatareku?


Hajir tayi shiru tana tsoron sanar dashi cewa, sotake ta kamashi,

Dattijon yace.


Inaga mutuwa zayyi shiasa yazo yatsare hanya."


Jin haka yasa hajir taji dan sanyi yasauko mata, yakora kadan garen yaka gefe ,shikuma ya wuce.







"gadan gadan hajir tatun kari kadan garen cikin  jarumta, dabushewar zuciya.tasa kafa tatake kadangaren, takama kanshi  tana kokarin fisgewa,

Saidai kan kadan garen tamkar dutse.

Tayi tayi, amma abu ya gagara, daga bisanima saikama danyatsan ta yayi da bakinsa.


Wata kara tafasa  tareda yarfe hannu amma yaki saki,tayi tsalle ta dira takara fasa kara,

Laila tayi tsaye takasa isa inda take,



Hajir tacigaba da kurma ihu tana tsalle tsalle, kadan garen yaki yasakar mata hannu, ta kwa so aguje ta nufo laila.



Koda laila taga tanufota  sai ta kwasa aguje, haka suka debi fili suna gudu, jardai hajir tacimma laila, itama karar ta fasa tareda ingiza hajir din.


Wasu matasa guda biyu suka isa ga su laila, suna tambayarsu dalilin abinda suke makara da tsalle tsalle,


Hajir tanuna yatsarta da kadan garen yakama yaki saki .

Suka duba hannunta basuga kadan garenba sukace ina yake?


Tace gashi nan yakusan ciremin yatsa"

 Suka sake dubawa basuga komaiba sukace gashinan babu komi a hannunki"


Tace wallahi gashinan bai sakeniba,

Daya yadubi dayan  yace kai inagafa matarnan sabon kamuce"


Dayan yace gaskiyarka baba mu ware kawai".

Suma aguje suka kwasa


Hajir taduba hannunta taga kadangaren yananan sai ma kara canza  kama yakeyi.


Itako laila gidanta takoma  taido kofa ta datse.


Wani mutum ne yazo wucewa yaga sai kuka take tana yarfe hannu .

Yatam bayeta abinda ke damunta, tanuna masa hannunta tana fada masa,


Shima ya duba sosai baiga kadangarenba,

Tarikice tana fadin waiyazakuce babu komai ahannuna, alhalin gashi ni ina gani,kuma inajin zafin cizon daya kemin?


Wani yaro ne yace mashi,

Kai malam mahaukaciyace.

Yadubi yaron ya kuma dubeta, ko shakka babu  sabon kamuce sai yanzu ya lura,

Dasauri  yabar gurin.


Abinnanfa yafara bata mamaki, tayaya kadangare  rike da ya tsarta amna mutane zasuce basu ganshiba?


Adai daita sahu tatara tahau ta nufo gida ko motarta bata tsaya ta daukaba.





Maman sadeeq

[9:29PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣0⃣


Na

Maman sadeeq





"Lokacin da hajir tashigo gidan,Lamido bai karasoba, sai jawaheer itada munubiyya.


Kai tsaye wurin ta hajir tanufo,da sauri jawaheer ta halasto addu o'in  tsari, azatonta wani mugun abunne hajir tanufota dashi,


Tamike tsaye ita da munubiyya tana kallonta,

Akallon da tamata tagano ba a hayyacinta takeba.


Hajir tace dan allah jawaheer dubamin kadan garen daya kamamin  yatsa ko kema baki ganshiba?


Jawaheer ta duba jannun saidai bataga  wani kadangarenba,

Tace babu kadan gare ahannunki,"


Hajir tace wlh gashinan inaganinahi sai sauya kama yake'".

Jawaheer tayi mata kyar da ido tana kallonta,

Ayanzun ta soma hasaso wani abu maigirma daga hajir din,

Tatambayeta ya akayi wannan abun yafaru,?


Hajir tace "iye na 'am"....


Saikuma tayi shiru dan dakunya tafadamata abinda yafaru.


Jawaheer tagama nazarinta gaba daya, takamo jannunda tanuna mata, 


Babu wani tsoro ko fargaba ta soma karanto wasu addu o i tana tofawa akan yatsanta.


Wata ajiar zuciya hajir tayi tace.

Kinga wlh ya fita".


Jawaheer ta dubeta tace to allah ya kyauta gaba'".


Hajir tayi saurin amsawa da amn".

Tacigaba da juya yatsan tace kin gani har ya jimin ciwo"



Lamido yashigo azatonshi fadane sukeyi , danetaba ganinshi sunayin wata mu amala atareba,

Daka gansu atare to fadane ko kuna  wani abu wanda bana arzikiba.


Jajir ta isa wurinshi tace "Hubby  sannu da zuwa,


Yace yawwa"


Ya dubeta yadubi jawaheer  yace ince dai lafiya?


Jajir tayi sauri tace lafiya klw.


Yace wai don allah maiyada bazaku hade kankuba ki zauna lfy ba?

Zan so indawo ma in iskeku kuna tafa tafa, ni kaina zanji dadi.



Hajir tace dawa za ayi tafa tafar?


Kaga taho muje karage kayan jikinka,kayi wanka kaci abinci, la ture wannan ta tsuniyar agefe don ba abinda zai yuwu bane".


Ya dubi  jawaheer yace  "D" yaya gidan?


Tayi murmushi tace gida lfy, ya ofis din?yace klw"

Yadauki munubiyya  yasabata akafadarsa ya nufi sashenshi,


Ruwan wanka ta hada mashi ,tadawo tace garuwan can yana jiranka,


Yace "Munu jeki wajan anty kafin  indawo"


Tace A'a nibazaka hadani da jidaliba, adai maidawa uwarta ita,


Yace to maida ita idanna fito sai in daukota,


Dahannu daya ta shuri yarinyar ta direta agaban jawaheer, batace ko uffan bata juya ta koma sashen hubbyn ta.


Bayan yagama wanka tagabatar mashi da abinci,saidai test din abincin yatabatar mashi daba nata bane, shikuma baya iya cin abincin yan aiki.

Ya dubeta yace amma wannan abincin bake kika girkabako,?



Tace eh kasan nacemaka  zanje gidan anty munirat, to nayi darene shiyasa ban girkaba,


Yaturo mata filet din abincin yace.

"gaskiya bazan iya cin wannan abin cinba , kidai sama min wani abu,


Talangabe kai tace wlh hubby nagaji, don bakasan irin wahalar  dana sha bane, kadaiyi hakuri kaci wannan.

Yace gaskiya bazan ia ciba jeki 

wurin jawaheer amso min abinci?


Tace haba hubby yazakamin haka?

Aisaikasa ta rainani, nidai kaci wannan,


Ranshi ya soma baci, yazata maidashi kamar wani danta,

Cikin zarewar ido yakira sunanta.

Hajir dube ni nan niba danki bane dazaki bani umarni.

Don meyasa kike son yin gardama danine?

Nace kije kisamamin wurin jawaheer donme xakiyimin gardama?

Tashi kije ki amsomin


Sanin halinsadatayi yasa tatashi simi simi tafito .

Kulan da munubiyya takeyi shiya kara kular da ita, don bata son hayaniya,


Alalace ta dubi jawaheer tace wai yace kibasa abinci"

Tace wakenan?


Tambayar databata haushi, tace, wazaice kibasa abincin, bayan wanda ya ajiyeki?


Jawaheer tace bani dashi, aibansan dashiba,


Tsaki taja takoma tafada mashi abinda tace,

Yasan abinda yasa tafadi haka saboda sanin ba ita ke da girkinba.


Ta sowa yayi yanufi sashenta abinda yayiwa hajir ciwo.

Yace jawaheer taimaka kibani abinci,


Tace yo itafa matar taka?


Yace batayiba kinsan ni bana cin abincin yan aiki"


Tamika mashi munubiyya tace tunda kamaidota  take kuka,


Yakarbeta ya rungume, ta hado mishi abincin a gyara zama tace,inaga kakoma sashenka zaifi,


Ya dubeta saikuma ya mike don tafishi gaskiya, yasabi munubiyya yace miko min abincin.

Tamika mashi yakoma sashensa.






Tana zaune ta cika kadan yahana tai bindiga.

Ya soma cin abinci tana kallonshi,

Koda yagama sai yashiga wasa da munubiyya,


Haushi duk ya cikata wato bashi dama lokacinta sai na yarsa.

Shiyasa ta tsani yarinyar saikace ita kadaice "ya" agidan.


Ta dubeshi tace yakamata ka kwanta haka amaida yar nan wurin uwarta".


Yadubeta cikin kulawa yace kiyi hkr tayi barci sai in maida ita,

Yanzu dana maidata kuka zatayi"


Tace amma ai ina ganin uwar yarin yar nan itace kishiya ta ba itaba,?

Ayanzu lokacinane, kukane idan tayi uwarta ta lallasheta,


Yace amma hajir baki da hankali, yanzu ke wannan yarinyar kikewa kishi?


Yace to bari kiji zan iya sauya ki amma bazan iya sauya wannan ba.

Ita din gudan jininace, dan haka idan zaki iya jira to kijira idan kuma baza ki iyaba  to kina iya tafiyarki.


Kallonshi take cikin takaici  da kunar zuciya, idan ko har yace haka zasuyi to itakam tana iya kawar da munubiyyar saitaga tasi.


Jawaheer tana jiyosu duk abinda suke fada , don aka da sauri tashigo falonshi, yarinyar tana kwance bisa kirjinshi tasa hannu ta daukota,

Yadubeta yace ina zaki da ita?


Tace lamido matarka tafika gaskiya, yanzu lokacin tane  bana munu ba, kabata hkr don ka bata mata rai".


Bata jira cewarsaba ta fice daga falon nashi,


Dogon tsaki hajir taja mai tsananin karfi,

Dayake yasan takanta  tuni ya mantar da ita. Harta shiga kyakyata dariya.

Dahaka ya shawo kanta harsuka shiga sha anin gaban su.


 Saidai wata datsa  taji anyiwa yatsanta irin datsar da kadan gare  yayi mata.


Wata kara tasaka tareda duban annun.

Ilaiko kadangarenne ya dawo, yaruke hannun takeyi ,amma yaki sakinta.


Lamido yatambayeta "lafiya?


Tanuna mashi  hannun ya duba baiga komaiba, yace menene?


Tace kadan garene

Yace yana ina?


Tace gashinan"

Yace ni banga wani kadan gareba".

Tasake nuna mashi amna shi bai ganiba.


Dagudu tanufi sashen jawaheer.

Cikin barci taji ana tashinta.

Tabude ido taga hajir daga ita sai rigar bacci tace " lfy?


Cikin muryar kuka tace wlh kadan garen nan ne yadawo,


Shikam ganin ta kwaso dagudu yasa shima ya biyota, sai yaga ta shiga sashen jawaheer,lokacin da ya iso saiyaga jawaheer tana tofa mata addu a.


Yayi tsaye yana kallon abin mamaki, asaninsa dai babu abinda ke hada hajir da jawaheer,

To koshiyasa yagansu daxu atsaye?

Ki shakka babu abinda jawaheer tayiwa hajir adaxu shine take yimata ayanzu, to meke faruwa da hajir din haka?


Can yatsinkayo muryar hajir din tana cewa kingani ko wlh harya sakeni,

Ohni wane irin bala "i ne na jawowa kain........


Tunawata tayi agaban jawaheer take, sai tayi maza taja bakinta ta tsuke.

Tadubi lamido tace hubby muje mu kwanta,


Azatonshi zatayiwa jawaheer din godiya akan abinda tayi mata amma sai yaji shiru .

Shikam abin yadaure mashi kai matuka, akan aabinda yasamu hajir , wanda  har jawaheer keyimata addu a akanshi,


Yazama dole gobe yatambayeta abindake  faruwa akanta da sana din dayajawomata hakan.



Tasake maimaita "Hubby muje mu kwanta,

Bantaba ganin butulu irin hajir ba.


Yadubi jawaheer datakewa hajir kallon tuhuma yace,

"D, angode allah yasaka da alkairi saida safe ko?


Tayi murmushi tace to D allah yatashemu lfy,



Kamar da gayya takama hannunsa suka baro sashen jawaheer din,

Lamido yashiga bakin duhun al amari gani yake kamar ba zai iya bari sai da safeba,yatam bayeta kuma sai ya kyaleta,

Saidai baikuma bi takantaba,

Itama bata matsaba,

Haka suka kwanta kowa da abinda ke damunsa.

Ita tana tunanin yanda zatayi tarabu da wannan sabin al amari datasamu ayau, shikuma  tunani barkatai yakeyi.






("maman sadeeq dai tace kalubalene ga mata masu mugun nufi ga kishiyoyinsu,

Yanzu kuyi duba zuwaga hajir tayi abin amma kaikayi yakoma gidan mashekiya,saidai ansamu akasi tagamu da ibilishin kadangare koya zasu kare?)







Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣1⃣



Na

Maman sadeeq
















"Tana zaune tayi shiru tana tunano rayuwar da sukayi daita da mijinta, da irin gudun mawar da yabada, wurin ganin ya tsamota daga cikin duhu,

Yakawota ahaske.

Yayi hakuri da jin duk wadan su abubuwa da ake fada akanta,

Duk yatoshe kunnensa amma yau gashi mairabawa tarabasu,

Ayanzune take marainiya tundata rasashi,

Shidin uwane agareta kuma uba.


Wasu siraran hawaye suka gangaromata akan fuskarta, tasa hannu ta share,





"Excuse me"


Yafada lokacin dayake shigowa, amaimakon sallama,


Tadago kai ta dubeshi saitaji gabanta ya fadi ras.

Don ganinshi babu aljeri agareta.

Rabon datasakashi a ido tun ranar da ya kulla mata sharri agurin mijinta,wanda sana diyyar hakane mijinta yakamu da cutar ajali.

Amma da yake bashida ta ido ko gaisuwa baixo mataba,sai yanzu yashigo komai zaifadamata ?


Kodayake bata raba dayan biyu waccan maganarce tasake kawoshi.



Tadubeshi shima din ita yake kallo yana shafar gemunsa, 

Tayi saurin tashi tsaye don ganin yana matsowa dab da ita, saida yamatso gabanta har sunajin hucin juna.


Yana samun saarta aduk sanda zaizo gidan ita kadai yake tararwa,

Koda yake yana daidaitar tafiyar yaran makaranta.



Yace Aisha yaudai allah ya aramin rana , gani gaki, nakuma xo adubu.

Walau kiyarda ta arziki kokuma innuna maki nidin namijine,


Xankara maimaitamaki abinda nafada miki afarko,

Idan kika yarda zan daga darajarki, da kimarki,

Zansiya maki situru na alfarma, kidaina yawo cikin tsumma,

Zam baki cima mai kyau, da kudin kashewa,masu kwari,

Ke ina mai tabbatar maki idannaji dadinki yadda yaka mata har wannan gidan zan iya malla ka maki shi kyauta,

Idan ko kikace bazakiyardaba to zanbiya bukatatane ko takarfin tsiyane,

Kuma zaki tashi atutar babu,

Garama kiyarda murunkayin abinnan cikin salama,

Kuma kema kidan faso gari cikin sutura ta alfarma,

Dan jaka fada min wanne kika zaba?



Tadubeshi cikin takaici tace babu wanda zan zaba acikin  su. Donko sabon allah ne.

 

Rabe kaji tsoron allah katunafa ni matar yayan kace amma baka ji kunyar nemana da zinaba.

Zambaka mamaki, nayimaka nisa, nazaka tabayin nasara akainaba dayardar allah.


 Yashafi gemunsa cikin salo yana wani lumshe ido, yace to shikenan tunda haka kika fada,

Ai bambaki arufeba, saidana baki zabi .

Saboda haka karki zargi kowa sai kanki.

Aike bakatako bace dabazaki bukaci namijiba ko katako ai yana bukatar abuga masa kusa"


Ummu tace kafadi abinda kake so  daidai dakaine.

Ai akwai allah nakuma kai karata gareshi"'.




"Yashiga kiciniyar  kwabe babbar rigarshi da hularshi,


Tana tsaye tana kallon ikon allah,

Yakwabe rigar yanufota kai tsaye, ya ware hannaye zai rungumota,

Tayi saurin ja da baya yakara matsawa ta kara ja baya.


Dasauri yanufeta.


Ganin intabarshi zai iya tsinkamata darajar ta da jakar  mutuncinta .

Tadunkule hannu iya karfin ta takaimai naushi abaki,


Cikin rashin sa a taballo hakora biyu na gaba,

Dama shi ba gwanin burosh  babe.

Da sauri yaja yatsaya yana dafe dabaki, ga kuma jini yana fita abakin ,

Batakoji dar  arantaba, bare tsoro.


Zuhra ta shigo itadasu mubarak, da hamza, ganin yaran sunshigo yasabi babbar rigarshi yayi waje, yamanta da hular.


Zuhra tace,

Ummu sai yau baba rabe yazo maki gaisuwa?


Ummu tanaso tazubar da hawaye ko taji sanyi,

Amma tana tsoron tuhumar da yaran ta zasuyimata.

Idan sukaga tana kuka to tace masu me?

Dole tamake kukanta tace.


Zuhra saiyau yazo".

Zuhra ta kalleta kamar bata yarda da abin da tafadamataba, amma sai tabar abin,

Amatsayin kalan batanci da yan uwan mahaifinta suka suke jifar ummu dashi.





Shikam rabe bai zame ko inaba sai asibiti, akayimasa allura tareda magani, kana ya wuce gida,



Kwana biyar da faruwar al amarin, saiga lubabatu tazo karbar kudin haya.

Batakoyi sallamaba, kanta tsaye tashigo tace da ummu.

       "To iyalan ododuwa, gani nazo , kosaina yimaki bayani tunda ba hausa garekiba?


Ummu tace nasan abinda yakawoki koba kudin hayaba?


Lubabatu ta gyada kai tace ras sunaxo karba"


Ummu tashiga daki tadauko dubu ukku tamikamata.

Takalleta shekeke tace.

Nawace wannan?


 Ummu tace dubu ukkune"

Lubabatu tace aiyace daga yau idan bazakibiya dubu biyarba to ki kara gaba.


Ummu tace dubu biyar?


Lubabatu tatabe baki tace "to dolene"?

Ai idan sunyimaki tsada kina ia karawa gaba,

Kasar allah ai mai yalwace,

 Yanxu idan akwai dubu biyu ki ciko idan babu zan tarkatomaku yan komatsanku,indatse gida,


Ummu tace da akwai, bari nadauko maki,tashigadaki



Asargafe ta hango hular mijinta,takai hannu tadauko ta duba dan gudun kokwanto, babu shakka itace .

Tomeyakawoshi nan gidan ar yamanta hularsa?


Ummu tafito taganta da hula ahannu,

Batayi maganaba tamikamata dubu biyunta.

Cikin tsawa tace "ke! Me yakawo hular mijina anan gidan?


Ummu tace inaga ai bani zaki tambayaba,

Shikeda amsar dazaibaki, harta gamsar dake, dan haka kitambayesji abinda yazoyi har yamanta hularshi.













Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣2⃣






Na 

Maman sadeeq












"lubabatu tace to abinda kikeyi haryazo kan mijina?


Dama ai batun yauba naji ance kina tara maza,kuna sheke ayarku,

Shine zaki yaudaro mijina?

Ti wlh kinyi karya mijina yafi karfinki,,

Wato dan kinkashe mijinki shine zaki runkabin mazammu suna rage mqki dare, to Allah yatoni asirinki.


Dama arnan kandutse yaushe zasuyi tuba ta Allah?

Ai arne arnene koda yashiga cikin musulmai bazai rasa arnan cinsaba.


Haka tagama cin mutumcin ummu da bakaken maganganu, tajuya da hular ahannunta tabar gidan.


Ummu tazauna jabar tanajin bakin cikin kazafin da lubabatu tayi mata, akaro nabiyu bayan mijinta shima yayimata,kuma duk dai na abu dayane.


Wani irin suka taji zuciyarta tanayi dasauri tadauko maganinta dan gudun hauhawar ciwonta.





Itakam hajir tunanin datake maiyakamata tacewa jawaheer akan tambayar datake mata.

Tabbas tanaso tasamu abinda zai rabata da wannan kadangaren,

Ayanzu ta yarda wannan kadangaren iskane(aljani)idanko haryakasance aljani zai iya cutarda ita fiyeda wadda yayi mata ayanzu,


To amma aida kunya tafadamata gaskiyar al amarin,

Tunda dai kaikkayine yakoma kan mashekiya,ita tanufa da mugun nufi sai Allah bai yardaba.

Tokodai jawaheer din tafita gaskiya datace kissa tafi magani?


Tabbas hakane, saidai bazatataba bari tazamemata WUKA AMAKOSHI ba,

Kamar yadda tafada.


Jawaheer tagaji da tsayuwa tace kinga jeki abinki,

Don talura tana jin mauyin abinda zata fada, tamaido kyaure zata rufe,

Hajir tayi sauri tace dan Allah jawaheer idanda taimakon dazaki bani, to kibani indai kinyi niyyar tai makona,


Jawaheer tace wane irin taimako zambaki alhalin bansan abinda ke damunkiba?

 

Kuma im banyiba niyyar taimakonki mai zaisa indamu da abinda yake damunki?


Idan har kina tunanin abin yazamo sirri toki boyeshi ki barwa cikinki,harsai lokacin dakika ga damar fito dashi,

Amma dazaki yarda sai ince ki ruke kissa dantafiagani tasiri,

Wata kila kuma zaki gasgata zancena, saidasafe.


Bam ta maido kofa tarufe.

Tabbas tasakata atararrabi,

Atake kuma ta harbo jirginta,

Anya kuwa batada sa hannu a al amarin kadan garennan?

Bata ko tantama akwai sa hannunta acikin lamarin, itace taturomatashi,shiyasa takeyimata waibuwa,da yin addu o'i to dole tadauki mataki akai,


Taja jiki takoma sashenta.

Bayan sallar asubahi tagabatar mashi da karin kumallo,

Yadubeta yace hajir ina son zanyi magana dake, kibani dukkan hankalinki"'.


Jikinta yayi sanyi dantasan abinda zai tanbayeta,


Waimeke faruwa dakene daga jiya zuwa yau?


Nidai nasan lafiya lau na barki ma alurardanayi sainaga kamar iska ya shageki, menene sanadin haka?


Tayi shiru tanajin kunyar sanar dashi gaskiyar al amarin da yafaru, shin gaskiya zata fada mashi ko yaya?


Yakatse mata tunani dacewa ke nake jira,






Tadubeshi tace nikaina ban san yadda akayi hakan tafaru da niba, kawaidai naga kadangare yakamamin hannu yaruke,kuma wai sai kuke cewa ku baku ganshiba,alhalin ni ina ganinshi,

Babu mamaki kuma aljanine zai shigeni, shiyasa yakeyimani wannan waibuwar,


Yace to shikenan tunda zato kikeyi bari inyatabbata sai asan abinyi,


Tace nidai idan magani zaka samamin kasamamin tayaya zantazama  da lalura kuma ace sai wani lokaci?


Yayata kyar da ido yana kallonta,don bai gamsu da hujjojintaba,yace to yazanyimaki?


Nidai nasan komai yana da sila,amma kekince baki saniba,to ni ai babu abinda zanyimaki"'.


Yayi karin kumallo yafita aiki agurguje.

Tashirya tadauki motarta agurguje sai kabuga gidan malam,

Takomashi bayanin abinda ke faruwa,

Yayi shiru zuwacan yanisa yace.

Shiyasa nace maki bazaki iyaba,

Saikuma kikayi sa a kika hadu da hatsabibin kadangare"'.


Tace niyanzualam wane irin taimako zakayimani akan wannan al amarin?


Malam yanisa yace .

Agaskiya wannan kadan garen yananan ajikinki,

kuma idan ba gaggawar rabaki alayi dashiba zai iya halakaki,


Gabanta yafadi ras!

Tace tomai za ayi akan rabamu?


Yace to inaga kije kisamu masu rukiyya surabaki dashi,nidai bana rukiya,

Saboda aljanun dasukemin aiki,idan nasake nayi to zasu iya daukar kowane irinataki akaina,

Donhaka kitashi kitafi.







Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣3⃣




Na 

Maman Sadeeq











"Dahaka sukayi bankwana  takama hangar gidan laila sanata,


" laila ta dubeta tace waiyya kikayi da wannan kadangaren hajir?


Itama tace yar iska wlh bakida mutunci,

Laila shine kika gudu kika barni, aini nadauka abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, shine harda rufe gida,


Laila tace Bahaka baneba hajir gani nayi kar ayi biyu babu,shiyasa nagudo gida

Ya......kinko cire kan?


Hajir tayi tsaki tace inafa nacire babu abindama nayi saijawowa kaina bala 'i danayi.


Laila tace banganeba?


Hajir tace kokinsan kadangaren nan ba kadangarebaneba aljanine?


Laila tazaro ido tadafe kirji,

Nashiga ukku, ya akayi kikagane aljanine?


Hajir tace kamamin hannu yayi yaruke kuma yabacewa ganin mutane,saidaini ina ganinshi,yanzu haka ance yana taredani,sai anyimin rukiyya kozai barni,



'"laila tayi ajiyar zuciya tace.

"wannan shine tsautsayi,

Yanzu kitashiutafi  inrakaki inda zaayimaki rukiyya yanzu"


Hajir tayi sauri tadubi laila tace inane?

Tace dorayi karshen waya akwai mai bada maganin musulunci,kuma sunayin rukiyya.


" dasauri hajir tamike,

Tace muje.


Laila tatashi suka nufi dorayi karshen waya,sun kumayi sa a sunga malamin,sunkuma yimashi bayanin abinda yakawosu.


Andan dauki lokaci ana karatun .

Zuwa can aka soma magana,

Adan takai taccen bayanin dayayi  yace.

Shinazai kyaletaba,tunda tayi mugun qudiri ga mutum biu, sai shi na ukku,,saboda haka shi saiyakasheta ko arage mugun iri.


Malamin yabashi magana akan yahakura yakyaleta, dukda tayi masa laifi mai girma,yace yanasone mata masu hali irin nata sudauki darasi akanta, shikam kasheta zayyi tunda batada kudiri na alkairi agareta,


Malam tasake bashi magana akan yayi hkr shizaijamata kunne.

Aljaninn yace akwai sharadin dazai kafa mata,kafin yafita daga jikinta,

Sharadin kuwa shine duk lokacin da tasake nufar wani da mugun nufi to zai dawo kuma idan yadawo kasheta zayyi, dan dama kudirinshi kenan tun farko,dan bayasan tacutarda kowa idan taki zayyi waiwaye.



Dahaka kadangaren aljanin yafita jikin hajir ,


Malam yagayamata sharadin aljani, tayi shiru tana tunani.


Tabas hkr yazama dole agareta,indai tana son zaman lfyarta,

Babu ko shakka jawaheer tayi nasara akanta.

Shikenan tayi faduwar bakar tasa,

Bisa tilas tayarda da sharadin  aljanin kadangaren.


Takawo abin sadaka taba malam.

Suka dauko hanya.

Saidai kowaccensu jikinta asanyaye yake musamman hajir,wacce take ganin bakin cikine xaikasheta daranta,


Haka dai sukaita sakawa da kwancewa har suka iso gidan laila sanata .hajir tasauketa itakuma tadauki hanyar gida.....




Takosa ta isa gidan tatam bayeshi abinda yajeyi gidan har ya manta hularshi,

Wayace manne akunnenshi suna fira shida zuwaira.

Jin sallamarta yasa yakatse wayar.

Kai tsaye dakinshi ta nufa.

Wurga mashi hular tayi.

Tabbas yatuna da inda yabaro hular alokacin dayaje gidan su ummu.


Tace meyakai hularka gidan tubabbiyar matar can?


Yayi shiru yana raba ido , yarasa abinda zaice mata, 

Danko bashida dabarar dazai kare kanshi agareta,

Tace kokuwa hularce takai kanta gidan?


Rabe yayi karfin hali yace gaskiya inajin ba hula ta bace,saidai in kamace kikagani"'.


Lubabatu tace rabe nagasan halinka sarai,

Kasan ranar dakazo da katon gibinnan maikama da kofar shiga gari,kace wai motace takadeka,aibabu hula akanka.


Ni wlh bamma yarda motace takadekaba.

Idan har mota ce takadeka maiyasa jikinka  baiji ciwoba?


Sai bakinka kadai?


Akuyan cin naka har yakai ga tubabbiya?


To wlh nizan dauki hukunci, ashe ni ka maida motar,

Itako sai tagane shayi ruwane, bakuma abinci bane. 

Tunda har tayarda take iskanci da mijina,

Ko dayake ai ita isketa akayi,to saidai kasani daga yau saidai kajoma gidanta.

Duk wani abu danake maka ita tayimaka, tundani ban ishe kaba,


Ganin tadage sai sababi take shima yabude tashi wutar,


Donme nace maki ba hulatabace zaki isheni da kwar mato?

Ko nikadai keda hula irin wannan?

To tawa dince ba gidan dan uwana najeba?

Duk abinda kike zato hakane saiki dauki matakin dazaki dauka.


Lubabatu da dubeshi tace "haka kace"?

Yace. 

Eh haka nace

Tace tozan dauki mataki ko tunda nasan halinka sarai,


Suna cikin hakane fa iza  ta fito daga daki tace.

"kai wlh ummani har kunya kuke bani,menene abin tada jijiyar wuya anan?


Yaci ace zuwa yanzun kumbar abinda kukeyi,

Yanzu idan yaya adnan yayi aure kenan bazaku iya yimasuba sasanciba shida matarsaba?


Kullum ku cikin fada da hargagi,don allah kuyima kanku fada,tunda kudai kun wuce asaku agaba ana maku,sai dai kukuyi mana.

Gashini inada damuwa ataredani, amma babu wanda yadamu dadamuwata.


Lubabatu tadubi rabe tace,

Tokaji yar cikinka tadamu da abinda kakeyi, saika gyara idan kana gyarawa.


Rabe yadubi fa iza yace meke damunkine?


Babu kunya tace baba wlh ciwon so Allah yajarab ceni dashi.

Akullim abin karuwa yake,

Inaji ajikina idan har narasa man dinnan to wlh mutuwa zanyi,

Don Allah baba kataimaka mani kar in rasa raina tareda nakin cikina,


Lubabatu tace haukan banza kenan. 

Kawai daga kinrasa namiji saiki  rasa ranki?

To dakin gane ki saukakama kanki don namiji da kike gani badan goyobane.


Duk wannan bare baren dakikeyi baimasan kinayiba, idan ma yasani balallai bane ya tausaya maki,


Kalmar da lubanatu tafada  ta namiji badan goyo bane ta bawa rabe haushi,

Ya dubeta yace  kikace maza ba yan goyo bane?


Lubabatu cikin sauri tace eh nace ba yangoyo da zane daya bane ku.


Yace amma ai ba duka akazama dayaba.


Tace duka halinku daya babu gwani acikinku.


Rabe yace idan kikace haka

Kenan hada gyatumi shima nadan goyo bane,


Lubabatu tace hada kuwa naka gyatumin, shima ba dan goyo bane. 


Iye!

Wannan ai wulakancine dama kaso zagin gya tumina.

Rabe yace A'a niban so zaginshiba kedai  kika zagi abinki, gobema saiki kara yiwa maza Jimla,


Yadubi fa iza yace inane sji wanda kike son yake?


Fa iza ta langabe baki tace wlh baba bansamba inda yakeba,

Hasalima sau daya nataba ganinshi asahad tundaga ranar bansake sake sake sakashi a idona ba"'.


Lubabatu taja tsaki  aikin banza imbanda shirme ina akataba yin haka?

Ni dai inaga aure kikeso fa iza  tunda kikasan zafin so".


Fa iza ta dubi lubabatu tace.

Tabbas umma zanso aure idan nagamu da man dinnan, ayanzuma zanso adaura min aure dashi,


Rabe yadubi fa iza yace nima sai yanzu nakula da aure kike so, fa iza kiyi kokari kigano shi wanda kike so din yake.

Idan kuma bajakaba nakusa badake ga duk wanda  Allah yacida,dan haka saikiyi  azama".


Lubabatu tatabe baki tace subadawa manya,kaima kasan fada kake aiyanda aka direma kowacce mace akwati itama sai andiremata,

Ailokaci baizoba da farashin mata zaizube wanwar.


Rabe yace har yaushe kuma?

Ina jin yanzu diyarki tagama cewa inbawani namijiba saidai ta mutu babu aure?


Shida ita wakebin wani?

Itace kuma kinga idan taganshi yadda zata azabtu da da radadin sonshi kinaganin zata jira saiya furtamata kalmar so?


Fa iza tayi sauri tace wlh ko babu sadaki zan iya aurenshi,

Ai anacin bashin sadakima, 

Idan anyi aure daga baya abiya.


Rabe yayi dariyar mugunta yace to kinji ko?

Tashi kije fa iza idan da rabo kun hadu.

Idan kuma babu aidole kikarbi wanda yasamu,


Fa iza ta mike tsaye tace nifa babu wanda zan aura imba wanda nake soba,

Tatashi  tashiga daki.



Zuwaira tayi sallama tafito tace shegiya sai yau ake ganinki.?


Tace kedai bari majago yayi yawa inata kiran numbarki akashe,

Fa izatace ke kashewa nayi saboda banasan hayaniya,


Zuwaira tace gaskiya fa iza kina da matsala,

Idan so cutane aihakuri maganine,


Faiza tace banyardaba, wlh sake dai saidai idan son bana gaskiya bane.

Kinko san yadda so yake?


Zuwaira tatabe baki tace ni ina ganin kukuke daurawa kanku abinda Allah bai dora makuba".


Aisaikiyi tayi wahalace bata ishekiba, tasi kirakani sahad inyo shoping, kinga daganan saiki tambayo lbrn man din naki ko.


Da sauri fa iza tatashi tashirya suka nufi dakin rabe don tafadama lubabatu zasuje sahad,


Zuwaira tazube har kasa tana kwasar gaisuwa, gurin lubabatu da Rabe.

Washe  baki yayi yana amsa gaisuwar zuwaira,

Itako ganin gibin dayayi yasa wata dariya na son kubcemata, saidai ta gumtse, suka fito suka nufi sahad.


Suna shiga wata mota tafita saidai rashin sani dayafi dare duhu,suka shiga cikin store din kai tsaye.


Fa iza ta isa wajan mutumen da ke amsar kudi, itako xuwaira saita wuce wajan abinda yakawota,


Bayan sun gaisa tacemashi kokaganeni?


Yace sosaima kuwa ai inata kiran wayarki akashe,

Lallai kindaki gulbi aiyanzu yanzu yabar gurinnan da kin kulama lkacin da kuka shigo da kinga wata range rover tana fita toshine aciki.



Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣4⃣



Na

Maman sadeeq













"fa iza ta dora hannu biyu akai tare da fadin "ya salam"

Baka kuma karbain lambarba?


Yace gaskia bazan iya karbar maki lambarsaba, don zai tambayeni mai zanyi da ita,tunda bawata alaka sai tacinikayya tsakaninmu, kingako bazan iya abinda zai dira ayar tambaya akainaba, yanzuma dan kin kashe wayarki datunima kin cimmashi.


Ga iza takwalawa zuwaira kira tataho tace yaya andace ko?


Za adai dace kinjiwai yanzu yabar nan""


Zuwaira tace nashiga ukku kice mundaki gurbi,?


 Fa iza tace " laifinane yakira wayata akashe".


Zuwaira tace to yanzu yaza ayi?


Fa iza tace binshi zanyi naga  titin da motar tahau kuma kirar range rover kinga bazatayi wahalar kwatanceba.


Zuwaira tace to inkinje kicewa kike nema?


Fa iza tace matamnayi aibaya nata, kuma bazan gaji da nemansaba kedai taho muje,


Xuwaira ta dubeta adage tace gaskiya nibazan iya wannan galboronba,

Danni yanzu jaka akwai wani gara yana can yana jirana, don jaka kedai da Allah ya doramawa kije nikam kasuwancina zani.


Fa iza tace to shikenan tunda butulci zakiyimin, minarakaki shine ke zaki kasa rakani?

Babu komai nina wuce,


Zuwaira tayi saurin riko hannun fa iza tace tace

"jirani mitafi don tunda kika laqabamin  butulu haka zakiyi tayimin mita, aigara inrakaki idannadawo naje can wajan wancan garan,


Azahiri kuma bahakabaneba taso susami sabani da ita, dan idan tazone suke haduwa da rabe babansu fa izar,yanzuma datace wani gara nacan najiranta Rabe neke jiranta, don haka tahakura tabi fa izar ne man man dinta.


Titin sukebi acikin adaidaita sahu .

Motoci guda ukku sukagani amma babu amma duk bashi bane,haka suka gaji dayawo suka koma gida.


Abakin titi zuwaira ta tsaya sukayi sallama  da faizar akan itama zata wuce gida.


Fa ixa tagangara zuwa gida itaka zuwaira ta lalubo wayarta ta lalubo lambar rabe, wacce tayi saving dasuna gara, takira sukayi yar magana sannan takashe wayar.


Adaidai kofar fita fa iza taga baban nasu ya fito yace har andawo?


Tace "eh".


Yace ina kawar taki?


Tace tawuce gida"


Yace "To...to yayi kyau"


Yafito yashiga motarshi dake kofar gidan  yayi gaba abinsa don zuwa yadauki zuwaira.



Ummu badai jikinba?


Dakyar tabude baki  cikin tsananin  jinciwo tace .

          "wlh zuhra inajin zuciyata tana min suka kamar zata fashe.


Yasub hanallah!


Abinda zuhra tafada kenan, tace to ummu tashi muje asibiti,aiba anzauna da ciwoba.


Ummu tace a"a zuhra basai munje asibitiba mikomin maganina dana jika gashi can, mikomin nasha.


Zuhra tace badai madaciba?


Ummu tace shi mana,


Zuhra tace a'a ummu shanadaci yana da matsala bareke dakike da ciwon zuciya mujedai asibiti kawai,


Ummu tace A'a  baridai nasha madacin kawai, idan ba adaceba sai muje  asibitin.



Ummu daitace da zuhra tayi hkr tabarta tasha madacin 

Bisa tilas zuhra tadaukomata gidauniyar maganin tasha,


Maimakon aga rangwamen ciwo saima karuwa yayi, tun ummu na boyewa gudun kada zuhra ta fa himta halin datake ciki, hartakai takasa daurewa, haka ta kwana cikin radadin ciwo.


 Karfe tara zuhra tataro  mai adaidaita sahu yakaisu asibitin



Likita ya duba ummu yayimata allurai nasa barci, yarubuta magani ya mikawa zuhra.


Saidataga takardar magani sannan tatunq da babu ko sisi a hannunta.

Ta mantosu agida saboda ganin ummu  nabarci shiyasa tayanke dhawarar komawa gida ta dauko kudin.


Dasauri tafito bakin gate din asibitin tana neman mai adaidaita sahu.


Kamar amafarki yaganta  tsaye , yasauke gilashin motar don yakare mata kallo ko shakka babu itace a indatake tsaye.


Ba hannunshibane dole in yana son zuwa inda take sai yaje  you town,

Da sauri yaja motar don ya isa  yakewayo, ya iso inda yaganta saidai wayam! Babu dalilinta, ya daki sitiyarin motar , wani takaici ya lullubeshi waiko dai yarinyarnan aljanace?


Kawai dai rashin rabone kesa sabani atsakaninsu



Ya dubi wani mai saida lemu yace malam yanzunnan naga wata yarinya tatsaya anan, kokasan inda tayi?


Mutumen yace eh nagadai tatsaida adaidaita sahu tashiga,


Yace dan Allah kokaji inda tace akaita?


Mutumen yace A'a taya zansan inda za akaita tunda ni ba adaidaita sahu nake jaba?


Lamido yace to na gode"


Yaja motarshi yayi gaba.



Dasauri tadauki kidin ta nufi asibiti, bayan tasallamu mai adaidaitasahu.


Wani kyamis  dake cikin asibitin tamika takardar aka jido mata magunguna ta tambaya nawa ne kudin?


Akace dubu daya da dari tara da hamsin, tadauko dubu biyu ta mika mashi,

Yabata cikon naira hamsin.


Ta isa dakin ummu.

Azaune ta iske ummu tayi tagumi da hannunta,

Zuhra ta isa gareta taciremata, tace ummu yajikin?


Ummu tace zuhra naji sauki, inakikaje na farka bangankiba?


Zuhra tace likita yarubuta magani shine natafi gida nadauko kudin  aka sayo maganin.


Ummu tace aida baki wahalar da kankiba tunda gashi naji sauki.


Zuhra tace kisha maganin ummu saikiga kinkara jin sauki.


Cikin hukuncin Allah tabude maganin  tabata kowane likita ya shigo  yaduna jiki atakema yabasu salla suka dawo gida.


Da daddare Abbas yazo yaduba ummu  har yayimata dan ihsani.


Abinda abbas yaba ummu dashi aka siyo aya  aka  kaiwa sani, ahaka suke samun nadan hidimar yau da kullum .


Lallai  rayuwa kenan!






Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣5⃣


Na

Maman sadeeq



"Kuyi hkr narashin ganin wuka amakoshi kwana biyu banajin dadin jikinane,amma yanzu cikin ikon Allah zakurunka samun littafina kamar yanda aka saba.




Jinjina ta musamman agareku masoyana,

Masoyan WUKA A MAKOSHI,

Har abada bazan tabamantawa dakuba ,

Nagode da kaunar da kuke nuna min👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻😁😁













"Itafa lamarinnan yana dauremata kai,

Bashida lokacin kowa saina yar  yarinyar nan,

Saikace itakadaice diya agidan,


Tarasa abinda yasa yasauyamata acikin dan lokacinnan,

Haka zaizauna yayi shiru yanata tunani,

Idan tatambayeshi abinda yake tunani yace ba komai,


Tadai lura munubiyya ce kadai ke debemasa kewa,

Idan yazauna shi da ita sai yayta sokana yana dariya.


Itakam ayanzu tafiyin kishi da minubiyya akan uwarta jawaheer.

Idan ko hakane aikawarda ita kawai zatayi ta huta, da bakin cikin datake kunsamata.


"Dadai tadauki shawarar da malamin laila yabata,kuma saidaga bayataga idan tasaka ido cutarta za ayi,

Tayi duk sharadin Aljanin kadangaren ayadda takeji idan hartabi sharadinshi, tobabu koshakka zuciyarta zatayi bindiga

              Shidin aiba Allah bane dazaiyimata abinda babu mai iya yimata.

 Bazaiyuwuba dole tasan abinyi koda barbadene idanma nazatayi binne bulinneba.



Ai itama tana da yaya idan yace kewar  yaya yakeyi, kokuwa sai munubiyya shafaffiya damai?


To takusa da tse wannan igiyar taso atsakaninsu sai taga rawar kafa,


(muna mancewa Allah shiyakesa so azukatan bayinsa, ka duk yanda mutum zai tara yaya dole yakasance yafisan wani. Duk da shidin baya banbanta su da diyanta,

Luma yanzin datakesan cutar da yarinyar ta mance Allah yaharamta zalunci akanshi ma bare ita,ta  kuma mance abinda yafaru abaya, tosai ta gwada idan zata iya,)




Tadauki wayarta takira laila sanata, basuko gaisaba tace,

Waini laila haka zanta zuba ido ayita cutata saboda Allah?


Laila tace "Hum basaiki yi tazamaba, tunda kindaiki tatsuniyar malaminnan,

Aljani dai aiba Allah bane  dazai shimfidamaki doka harki tsaya bata lokacinki abanza,

Dokar Allah ma abisa doron duniyarnan bakowane yake  bintaba bare Aljani kayan banza, wwnda ko gana wofi bai kaiba,

Kitashi tsaye ki kwaci yancinki, dokar Aljani ba dokar Allah bace yawwa.


Hajir tayi ajiyar zuciya tace to laila yanxun mekike ganin yadace ayi?


Laila tace abinda nake ganin yadace kekika san inda matsalarki take  kya iya zuwa kisameni,

Idan tabaki shawarace nabaki,idam ma zan iya magance maki ita sai inyi.

Idanma takama musauya sheka duk sai muyi, gari da yawa kuma ai maye bazaici kansaba"'.


Hajir tace to shikenan Aminiyata bani minti talatin gani nan zuwa,



Tadauki gyalenta da makulli tanufi gidan laila sanata.



Laila ta dubeta tace yanzuke yar jaririar ce kikarasa yandazakiyi da ita?

Ko uwarta tanemi kawomana matsala ai akwai yanda zamuyi da ita bare kuma wata karamar alhaki munubiyya, 

Dan Allah bari fadar haka kar haushi yasani indaukeki da mari".


Hajir tadubi laila tace niyanzu bani shawara inji ta ina zamfara?


Laila ta dubeta adage tace toke yanzu idan nakyaleki wane irin mataki zaki iya dauka?


Hajir tace wlh da niyyata intausa  kafura acikin tankin ruwa ta mutu ubankowa ya huta, idan kaunar tagaskiyave sai ya maidota kan siyama.


Laila tace karkiyi haka, ai idan kikayi haka kowa zayyi saurin ganoki, inaga abin da yadace kibata guba mai saurin halaka dan Adam"


Hajir tace a'a laila ai idannabatq guba taci toza ayi saurin ganoni kedai sake wata shawarar,


Laila taja tsaki tace aisaikijira kiji inda zancena zai fadi zaki katse min hanzari,

Aduk loka cin da kika samu sarari kisamu sweet dinki ki ajje, kitabbatar kin hadashi da guar, aranar da babu aikisaikice lamido yakaiki wani store zakiyo shopping, idan kinje saiki siyo sweet kibaiwa yaran,

Ita kuma tsinanniyar saiki bata mai gubar, kokuma kiba shi ubanta yabata, kinga datasha shikenan kinrabu da kaya kuma babu mai ganoki(sunmanta Allah)"


Hajir tace haka kuwa za ayi ,

To amma saidai kinaganin ba matsala gurin wannan iblishin?


Laila tace aiba wani abu ai Allah yafishi, idanma mukaga da matsala sai muhadashi da ayar Allah,

Ai baifi karfintaba don haka barin HALi sai mutuwa, 

Kowattuba dan wuya ba lada.


Hajir tace haka zancenki yake aminiyata,

Nagode kwarai da shawararki,

Daganan sahad zan wuce innemo sweet, ranar asabar kuma dani za aje shopping din,

Kinsan duk asabar yakan kwashi yara yakaisu sahad ya hadomasu kaya, kinga idannabisu saina aiwatar da aikina acikin salama,

Itako munubiyya saidai uwarta tasake haifar wata.


Laila tace to dadai yafi" 

Hajir tace to yanzu ina kike ganin zamu samu gubar?


Laila tace bari indaukomaki indai gubace bata hada fada, don bana rabuwa dakayan mugun abu saboda bacin rana"


Tatashi tasjiga daki jim kadan tafito da wata yar kwalba da wani abu akulle aleda tace,

Sai wanda kika zaba shiwannan na cikin yar kwalbar atake yake faska yan hanji,

Shikuma nacikin ledar, azababben ciwo yake sawa, daganan kuma lahira tayi bako"


Hajir tace duka zan hadawa yar banza mai luka lukan idanu kamar na uwarta"


Tayi godiya ga laila sanata tanufi sahad store, tasayi abindatake ganin lamido yana siyamasu, aduk ranar asabar,

Tayi sauri takoma gida saboda dora girki.













Kuyi hkr da wannan



Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣6⃣



Na

Maman sadeeq




" Ayau kwananta tara da sallamowa daga asibiti, sai kuma ga ciwo yadawo.

Awannan karen har suma takeyi, 

Cikin kidima zuhra tataro adaidaita sahu suka nufi asibiti,

Likita ya dubata ya rubutamata allurai, da magun guna yace zuhra tai sauri tasiyo,


Gabanta ya fadi dan batada ko sisi, hakama agida basuda ko asi, 

Tayiwa takardar kuri da ido tana kallo,kamar tana son gano abinda keciki,gani tayi ina zataje tasamo kudinnan?


Dasauri tafita tanufi kyamis din asibitin tamika takardar tace su mika mata kudin maganin,

Aka lissafa duka kidin dubu biyar ne da dari biyar.

Harsunfara dauko maganin tace duyi hkr babu kudin awurinta.

Dama dantaji yawan kudinne amma zata dawo.


Tadawo gurin ummu haryanzu tananan yandatabarta, tayi zugum tareda dora hannu akan fuskarta tayi tagumi,

Tarasa inazataje tasamo kudi, ko yan suturunta zataje tasayar?

Saikuma taga rashin dacewar hakan, wata zuciya tace mata,.



Yakamata kiyi hanzarin samo kudinnan, don karki rasa ummanki,ido daya daya rage maki aduniya, 

Tunda har likita yace maki kisamo kudi abin na gaggawane".


Dasauri tamike tsaye kamar wacce aka tsikara,

Tafito daga asibitin babu ko sisi ahannunta,

Dan haka da kafa ta doshi gandun Albasa, gidan kanin babanta sani,

Dukda tana dayakinin sai sa a tasameshi,

Dukdatana da yakinin sai sa'a tasameshi .

Agida ko tasameshi.

Bayan sun gaisa dashi, takuma gaida matarshi balaraba.


Cikin izgili da dagawa balaraba ta dubeta tace inasu  ingozi sabon tuba?

Incedai ko lfy?


Wani abu yacaki zuciyarta tadai daure tace.

"Dama ummu ce aka kwantar da ita asibiti,kuma yankudin mune suka kare shine nazo  baba ya agazamin da dan wani abu.


"wato ga mai kudin banza ko?

Cewar balaraba.

Tobari kiji kudin sani ko masu duban gabas banyarda yayi almubazzaranci dasuba,

Bare kuma iyalan oduduwa,

Xaifi kyau  kitafi ki rokamata jizos ko Almasihu, sune dai dai da ita".



Sani yana zaune baice ko uffan ba.

Balaraba tace tashi kitafi tun baki gayyatomin sauro ba".


Wasu hawaye suka biyo fuskar zuhra batako sharesuba,

Tamike tsaye tana shirin fita.

  Sani yazaro naira hamsin yamikamata yace kiyi hkr bamu karbi Albashi ba.


Tasani sarai yana da kudi anhanashi dai badawane,

Tunda ai yau ashirin datara kowa yakarbi Albashinsa.


Takarbi naira hamsin din tayi godiya ta fito,

Kai tsaye ta nufi gidan baba Rabe.

Tashiga da sallama,

Fa iza ce zaune tayi tagumi,

Tawaigo tadubeta,

Saidai bataceda ita uffamba,

Zuhra taduka  tace Anty fa iza ina yini?

A'a nemi Antynki tun wuri bai kuremakiba,

      Lubabatu tafito saitaga zuhra, tayi sauri tadaure fuska tace "lafiya?"


Zuhra tace dama ummu ce babu lfy, kuma yan kudin mu sun kare shine nazo ataimaka mana.


Lubabatu tace to bari inyi mashi magana tunda harta turo ki wurinshi,aida walaki, babu mamaki shine zai dauki dawainiyarta, dama ina zargin wani abu,


Xuhra bata fahimci abinda lubabatu take nufiba,

Fatanta dayababa Rabe ya dubi maraicinsu ya agazamata dawani abu,".


Rabe yafito shida lubabatu tace,

To gatanan tubabbiya ta aikota wurinka, yanzu kuma saikace min me?

   Idan ciki ne da ita gara kasanar dani, donni ina zarginku, kaida tsinanniyar arniyarcan,"


Ayanzu xuhra tagane abinda take nufi  lallai rashin mutumcinta ya doke na balaraba,

Tunda ita batace tana zargin ummu da kowaba,

Lallai wannan shine WUKA A MAKOSHI,

Inama ace wukarce aka kafa mata amakoshi,

Wlh dazata fiyin murna dan tasan kuskure kadan za asamu wukar zata ratsa  makoshinta,

Gara ace wukar tayimata sanadi nahanata jin kalaman lubabatu.


Rabe yadubeta yace ke ubanwa yaturoki wurina?


Zuhra tace babu wanda ya turoni nice nazo da kaina.


Yace totashi kibarmin gidana  ko inci  ubanki yar banza mai suffar yan ruwa.


Dasauri tatashi tabaro gidan ,

wani irin radadi taji zuciyarta nayimata,

babu ko shakka ta amince basu da kowa aduniya, sai Allah sai ummu .

Ubangiji katokari kafadun ummu don mutumcin ma aiki Allah.


Dahaka ta isa gidan turai, tashiga da sallama, turai ta amsa,

Tagaidata ta amsa.

Tadubi zuhra tace banganekiba daga ina?


Zuhra tace nice zuhra.


Turai tace ashe kuna gane inda mutane suke, kingani ban shaidakiba, lokaci ya yi daza akalato yan uwa ko?


Aikudai kam ubanku ya cuceku, kodayake harda uwarku,

Tunda takasance Ahlul kitabi, sun saka rayuwarku atsaka mai wuyame akeyi da kazanta?

Ai banjima abida ya kawo kiba, don nasan banza batakai xomo kasuwa,

Tabbas duk abin da su lubabatu da balaraba sukayimata shafar maine akan abinda turai tayi mata, sai yanzu tagano inda duniya tasa gaba, kowa kanshi kawai yasani.


Kenake saurare, turai takatse mata tunani,

Ta dago dakai ta dubeta tace ,

"inna dama wata yar matsalace ta kawoni".


"Ninasan babanzaba,don baki taba zuwaba,

Aito tsaya haka basai kin fadaminba abinda ya kawoki sawunki a likkafa, kibarmin .

Ko babu abida zanyimaki,

Ke ko Auwalune ya baro lahira yadawo duniya wurina yawun da zan zubar bazan tofa mashiba.

Ainasan dawalaki tunda baki taba zuwaba.

Tashi maza ki bace min dagani tun raina baigama baciba.


Wasu hawaye masu zafi suka zubomata wai meyasa ake cimasu mutumci hakane?

Wa ya isa ya kaucewa kaddararsa?


Sauri takeyi kamar takife kasa tana ta kukanta.

Jitakeyi kamar tayi fiffike ta isa ga ummu, saboda gananta ya tsananta faduwa ajan halin dazata iske ummu aciki.


Titi tara tsa da niyyar tsallakawa, shikuma ya danno motar, ko karin taka burki yakeyi amma ina!

Sai da ya isa gareta ya dauketa yayi gaba da ita,

Cikin sauri ya balle murfin motar ya fito kamar a mafarki,

Yayi tozali da fuskar da keyi mashi gizo, aduk lokacin daya tunota,

   Mutane suka taru akanta,

Yakamo hannunta saiyaga babu alamar rai atare da ita,

Gabanshi yafadi yace.

         "ya subhanallahi"

Kutaimakamin dan Allah insata amota.


Asibitin Aminu kano shine mafi kusa da su,

Saidai banan yaso yakaitaba yafi son asibiti mai zaman kanshi, yanda za afi kulawa da ita sosai,


To amma yanzu doyake tadawo hayyacinta,

Dole yanufi Aminu kanon,


Emergency yakaita aka dubata babu inda taji ciwo, saidai sumar datayi atake akayimata allura, likita yatabbatar mashi nanda awa ukku zata farfado in sha Allah,


Yaja kujera ya zauna , idan zata kwana a asibitin shima zai kwana,

Ayanda ya azabtu da begen ganinta,

Sai kuma gashi tsau tsayi ya gifta,

Maimakon yaganta ahayyacinta yabata hkr, akan abin da yayimata abaya, saigashi shima yakuma yimata wani laifin


Laifi kan laifi kenan.






Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣7⃣




Na 

Maman sadeeq










"Wayarshi tayi kara,

Yadauko ya duba,

Har ga Allah ya manta abinda ya fito dashi daga ofis,saboda faruwar Al amarin,


Yadauki wayar tareda bada hakuri,

Ya kumace gashinan zuwa nan da minti shabiyar,


Yadubeta har yanzun bata farkoba,

Yafito yanufi ofis din likitan yace zaije yadawo,yanzu ana jiranshi, tunda akwai sauran awa biyu da mintoci kafin tafarko,


Likitan yace to babu damuwa,

Yafito yadauki motarsa,


Minti shabiyar da barinsa ta bude idonta.

Ganinta akan gado yajefata Cikin tunani,

Meyakawota nan?

Ko tantama batayi asibiti ce.


Dasauri tadiro daga kan gadon,

Tabude kyauren dakin tafito.


Dakin tashiga.

Lullube take rub da zane, 

Gabanta yafadi,

Ta isa kanta da sauri ta yaye zanin.

       

Ummu!!!

Takira sunanta cikin fita hayyaci,

Shiru bata amsaba,

Tasake kiranta amma ko motsi batayiba,

Dasauri tafito tanufi ofis din likitan.


Koda yaganta yace kin farkane?

Kibari wanda yakawoki ya dawo yace yanzu zaidawo,


Tace likita kadawo dan Allah la dubamin mahaifiyata,


Yadubeta cikinamakin kalamanta daaji,

Wacece kuma mahaifiyarta?

    Shidai yasan ita akakawo amatsayin marar lafiya yace,

Ina majaifiyar taki take?


Tace tana word 3

Yace to muje"

Tayi gaba,

Yabi bayanta, suka isa dakin.

Yadubeta yace.

"itace mahaifiyarki?

Tadaga kai alamar eh"


Yace lkcn da nazo doctor afiz yafadamin matsalarta,kafin yatafi ,ganin bakowa tare da ita yasa nafara tunanin waya kawota, kuma yayi tafiyarsa,?


Tace "Ni nakawota, naje innemo kudin maganine saikuma naganni akan gadon asibiti,"


Likita yace wanine yakawoki yabankeki da mota, yanzu jaka yaje yadawo"


Tace likita ka duba min ita"


Yadubeta,yadubi ummu dake lullube, yayi shiru yakasa cewa komai ,


Ganin shirun yayi yawa  tace tamutu ko likita?

Kagaya min don Allah.


Cikin sigar lallashi yake bata hkr,

Daga karshedai yafada mata mahaifiyarta takoma ga ubangijinta.


Batakarasa  jin abinda yaceba ta sulale kasa.

Datai makon Allah dataimakon likitan ta farfado,saidai takasa cewa komai,


Haka aka saka gawar ummu Amotar daukar gawa, suka nufi gida.


Ganin yanda aka shigo dagawar ummu yasa su hamza da mubarak suka fasa kuka,

Zuhra kam takasa cewa suyi hkr, ko subar kukan,

Haka suka tasa gawar gaba susuna kuka itakuma tarasa tashar kamawa,


Innar su sani ce taji kukan yaran yayi yawa, tashigo dantaga abinda ke faruwa,

Gawar ummu tagani agaban yaran batasan lkcn da kuka ya kwace mataba,


Dasauri tajuya tabar gidan,

Minti biyar saigata da mijinta,

Malam lawal yashigo ya lallashi yaran,

Yajasu yakawosu nan wurin innar su sani,

Yakira malam mande,baban Abbas, aka kira matarda zata shiryata.

Nandanan aka shirya ummu.

Aka kira zuhra tazo tayi mata addu a

Saidai takasa cewa komai,

Bisa tilas aka dauki gawar ummu aka tafi da ita gidanta nagaskiya,

Dama haka duniyar take.


Abbas yataka yaje  har gidan sani yafada masa rasuwar ummu,

Yakuma je gidan Rabe  shima yafadamasa,

Sai dai abin da Rabenne   yafada ne  yayi matukar dauremasa kai,

Dan cewa yayi Allah yakara nauyin kasa.


Dan uwan ka usulmi yamutu kace Allah yakara nauyin kasa?

Allah ya kyauta.

 Haka Abas yadawo .

Innarsu sani ce tazauna amsar gaisuwar, itada yalwati mahaifiyar Abbas.


Kwana ukku aka share makoki,

Gida yarage daga zuhra.

Sai yankannenta suna samun agaji  daga malam mande,

Don duk wani abu na bukatar rayuwa sunayi masu,alhini kadai ketare dayaran,

Da malam mande da malam lawal sundau alhinin daukar yaran.

Shi malam mande zaidau su amza da mubarak.

Shi kuma malam  lawal zai dauki zuhra,

Idan biki ya kare sai yadauko daya daga cikin yaran ya rike saboda kwadayin ladar rikon maraya.


Amma sunbari suga abinda sani sa rabe zasu yanke akan yaran,

Idan sundaukesu shikenan,

Dama sune hakkun su ruke yaran,amma idan sunga basu da niyyar taimakonsu, to su zasu sa hannu sudauka, don da nakowane, 

Haka kuma da dadukiya ba a gwadamasu mugunta, saboda Allah ne kadai yasan wanda zai amfanesu.






Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣8⃣



Na

Maman sadeeq







"kwana bakwai dayin rasuwar Rabe ya diro gidan,

Bayan zuhra ta tagaidashi,

Tasaurara taji ko gaisuwa Yazo yayimata.

Saidai tasha mamakin jin kalmar da ta fito bakinsa,

Daga  baya kuma saitaga babu mamaki, idan tayi la akari da zuwan datayi gidansa,

Babu taisayi atare dashi,

Bayajin taisayinta, bakuma zaijiba yama za ayi yaji?


Tace  wlh baba babu kudi ahannuna, 

Ciwon ummu ne yadauki hankalina shiyasa na manta da wata yacika,

Amma insha allah wata nagaba  zan hada duka imbiya"


Yadubeta asheke yace ke dubanninan,

Karki maidani dan iska,

Gidan zambaku kuzauna amatsayin bashi har sai wani watan yaxagayo sannan kibani kudi?

Abinda muka guda kenan gashi yanzu iyayanku sunjefaku  acikin garari,

Sunjawo bala i sunkauce sumbarku dashi,

Yanzu ina irin haka keda dadi,?

Yanzu idan za akarade duniyarnan nabu wanda zainemo inda asalin uwarki yake,

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣8⃣







Na

Maman sadeeq










Kwana bakwai dayin rasuwar Rabe ya diro gidan,

Bayan zuhra ta gaidashi, 

Ta saurara taji ko  gaisuwa yazo yayi mata,

Saidai tasha mamakin jin kalaman da suka fito daga bakinshi, 

Daga baya kuma saitaga babu mamaki idan tayi la akari da zuwan datayi gidan sa babu tausayi atare dashi,,

Bayajin tausayinta kuma bazaijiba,

Yama za ayi yaji?


Tace wlh naba babu kudi ahannuna,

Ciwon ummu shi yadauki hankalina har na manta dawata ya cika,

Amma in sha Allah wata na gaba  zan hada duka nabiya,


Yadubeta shekeke, 

Yace ke dubarni nan karki mayardani dan iska mana

Gidan zambaku kuzauna amatsayin bashi har sai wani watan yazagayo sannan kibani kidin?


Abinda muka guda kenan.

Gashi yanxu iyayanku sunjefaku awani hali da garari,

Sun jawo bala 'i sun kauce sun barku dashi.

Yanzu irin haka keda dadi?


Yanzu idan za akarade duniyar nan babu inda za asamo wanda yasan asalin uwarki yake.


Adangin ubamma ninafita alissafi,

Ko su sairan bazasu yatda anunasu ace ku jininsaneba,

To ina riba a auren ahlul kitabi?


Yanzu bakiji bakin cikin kasan cewa RUWA BiYU ba?

Matsalarku ce ma wannan.

Yanxu zambaku noties, zuwa wata mai kamawa, idan kudi sunsamu to

Idan kuma basu samuba zan tarkataku zuwa gidan sani,

Nikuma insaka wadanda xasu bani kudi,

Don gaskiya bazan iyaba.

Koda zan  duba zumunci to bazanyi  zumunci da Auwaluba ko alahira""


Ya kade rigarsa yayi gaba.

Zuhra tayi ahiru tana jinjina girman kiyayyar da suke yima iyayansu.


Tasa hannu ta dafe kai, 

Tace

Ubangiji kasan yayamana wannan rayiwa,

Da abubuwa suka rincabe mana,

Lamarin yazamo rana zafi, inuwa kuna,

    Wasu hawaye suka biyo  fuskarta,

Tasa hannu tashare,

Tace,

Allah kana gani kakawomin dauki,

Don mutumcin annabi muhammad,(S.A.W).


Yadauki tsawon awa daya da yan mintina kana yajuyo asibitin,

Fatansa daya ya iske tafarka.

Akan hanya ya tsaya yayi mata sayayya irin tamarassa lfy.


Dasaurinsa yafito daga motar yanufi emergency.

Saidai tundaga nesa ya hango gadon datake kwance wayam.

Babu ita babu gurbinta,

Yazauna azatonshi ko tashiga bandaki, sjru babu ita.

Yatashi yanufi ofis din likitan. 

Bayan sun gaisa yatambayeshi ko ina mara lafiyar take?


Likitan yace tatafi gida dan rashi tayi babba na mahaifiyarta.


"subhannallah"

Yace,

Kodama mahaifiar tata tana asibitinne?

Likitan yace eh inagama tana kan hanyartane taxuwa tsautsayin ya afku,

Yadubi likitan yace.

Doctor kokasan inda takene,?

Likitan  yace gaskiya ban saniba,"

Yayi shiru zuwa can yace"To likita nagode"


Yamike tsaye yafito da ledar dayayi mata sayayyar, yashiga mota yayi gida,




Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣0⃣




Na

Maman sadeeq










"Jajir tace  toni ko inkoma saika nemeni?


Yayi sauri yace "A'a yi hkr hada mani abincin.


Ta jada masa abincin taturamasa agabansa,

Yasa hannu yadauki cokalin ya debo abinci yakai bakin yarinyar.


Baiciba saida yatabbatarda takoshi sannan ya somaci.


Hajir ta kuma kulewa wato itadai duk ranar da zata karbi girki sai ranta ya baci,yanzu me haka ke nufi?


Jawaheer tayi sallama ta shigo tataro hannu donta dauketa, 

Yace maiyasa baki bata Abinciba?


Tace bangane banbata abinciba?

Saiyau kakula da banbata abinci?

Yace yi hkr gani nayi nabata anan kuma taci sosai.


Tace kasan yaro shu umine.

Dontaga kaine shiyasa taci dayawa, yanzu haka abincinta na nan,

    Yace tonibari daga yau nizan runkabata da hannuna, tunda tafison imbata.

    Jawaheer tace kace imbar bata ki har sai kadawo?

     Ya harareta,

Hajir ko mikewa tayi tabar falon,

Jawaheer kuwatakai hannu daniyyar karbar yarinyar,  tamake lafada bazata zoba,

       Yace ki kyaleta mana tinda bata zuwa,


Ta  dubesa tace D, dan Allah kabar shiga hakkin matarnan meyasa kake haka ne,

Kaga yanzu ranta ya baci.


Yace D, ba shiga hakki bane meyena abin kishi da kan kanuwar yarinya  kamar wannan?

Karki manta cewa munubiyya diyatace. 

Gudan jinina,

Taya bazan kaunacetaba?

   Hatta dake uwarta zan iya sauyaki amma bazan iya sauya munubiyyaba.

To mai zaisa ta tsangwami kanta?


Jawaheer tace duk nagamsu da bayaninka saidai hakan zai iya  zamewa munubiyya matsala  nan gaba,

  Su duka kaine ubansu baikamata kana nuna bambanci atsakaninsu ba.

     Harga Allah nibazan nunama su abdool komaiba tsakaninsu dasu siyama,

Amma nasan hajir zata iya kullatar munubiyya, harma da yan uwanta, 

Nasan Allah shikesa so, 

Amma dan Allah karage nunama munu wannan fifitar,

Dan Allah yanzu kaje kaba ta hkr,

Yayi shiru yana nazarin maganganunta,

Tasa hannu ta dauki munubiyya ta fice daga falon,


Yadauki wayaersa ya kira hajir saidai har tayi ringin ta gama bata dagaba,

Yasan za ayi haka.

Yasake kiranta shima bata dagaba,

Yasake kira saiyaji wayar akashe,

Tashi yayi ya nufi dakinta.


Rungumota yayi cikin sigar lallashi yace,

Haba my  hajir sai ki  taho nadauka ma wata kwalliya za ashekomin,

Kuma ina kira saiki kashe wayar,?

Ayi hkr mana"


Tace me kayi min da kake bada hkr?

Aini babu abinda kayimin,

Natahone don imbaka wuri,

Idan kagama saika kirani,

Yace to maiyasa dana kira baki daukaba?


Tace banjibane

Yace to taso muje".

Tamike tabishi abaya, 

Batabari ya guskanvi da muwarda ke fuskartaba,

Sabida tasan gobe iyanzu yarinyar ta tsufa a lahira,


Dahaka tashiga yimasa salon datasan yana tafiyar da shi,


Washe gari takama asabar ko Wacce ta shirya yaranta zuwa shopping,

Halisa taje tace dady mun shirya.


Yadubeta yace halisa bazaku daga minba sai gobe?duk nagaji wlh

  Halesa tace dady fa jar min shirya!

Yace to muje".

Suka fito yadauki munubiyya,

Hajir tace hubby inaganin nima zam biku inhado kayan kwalliya,


Yace to babu laifi hjy karama,

Kema hjy babba kitaho muje.

Jawaheer tace A'a niba saina bikuba,

Yace nikuma nace saikinje maza dauko mayafinki mutafi.


Hajir tayi tsaye turus damba haka tasoba,

Itada take son ta aiwatar da shirinta cikin sauki,

Saigashi zai kawo mata tangarda,

Da haka ta sako hijabinta sika nufi sahad.


Yafaka motar suka fito suduka duka shiga,


Shika yana ganinshi yadauko wayarshi yakira lambarta yace togashinan ya iso saikiyi sauri kizo dan gudun dakar gurbi"

Yakashe wayar.


Hajir ta tsauno kayan kwalliya, 

Itako jawaheer wasu lasa asaine ta dauko guda biyu masu tsadar gaske,

Sukam yaran kayan kwalama duketa jida,

Saida suka gama sannan sukazo gurin wanda zai lissafa,



Kamar anje hota tashigo cikin sahad din,

Kallonsa tayi saitaji wani sanyi ya ratsata, tace. 

Hello beautiful baby"


Gaba daya suka juyo suka kalleta.

Takai hannu ta amshi munubiyya daga hannun lamido

Ta dubeshi cikin salo  tace, 

Inafatan dai kafadawa momyn baby ina so tabani ita?

Yadubeta yace aigatanan saikuyi magana"

   Cikin ko inkula yayi maganar,

Saboda bayasan wata Alaka tashiga tsakaninsa da ita,

Don bai aminta da tarbiyyar taba,

Itama din bataji dadin hakan dayayimataba,

Taso ace yanunamata kulawa,

Amma babu komi ai ita keso"


Ta dubi hajir ta dubi jawaheer tace bari ingani ko zan iya canko momyn babyn aciki?

Tafada tana murmushi,

Ta dubesu saita nuna jawaheer saitace yawwa  na canko, 

Dan Allah zaki bani baby wlh tana burgeni sosai?


Jawaheer tayi murmushi tace maixaihana nabaki ita?

Saidai idan babantane bai yardaba"


Ta dubi lamido dake mika kudin kaya tace to kaji momyn baby ta bani saura kai"

Yace tunda ta baki ai shikenan,

Yakado kan yaransa suka nufi mota,


Ita ko hajir sai tai amfani da wannan damar tayi sauri tabi bayan yaran tabar jawaheer da fa iza.


Sula shiga mota tacema yaran kowa yakawo ledarsa taga abinda ya dauka"

Suka bata tagani. 

Tace ina na munubiyya? 

Abdool ya mikamata tagani saitace subari tarukemasu, saboda kada suyi saurin cinye abinda aka siya masu,

Suka yarda da aninda ta fada masu,


Ta fakaici idon su ta dauko sweet din data gauraya da guba tasaka acikin ledar munubiyya,

 Ta maida sauran jakarta.


Shikam lamido harga Allah idan yaga mai irin tsagen  rumawa, suna dawo masa da bara bana, yakan tuno da yarinyar da har yanzun taki goguwa acikin zuciyarsa,


Fa iza taceomyn baby don Allah kibani nombarki, 

Mukulla zumunci dake,

Tunda nidai gaskiya baby ta burgeni,

Jawajeer tace to babu damuwa ai mai son danka mai sonkane, saidai ina fatan zumunci kadai zamuyi?

Fa iza tace insha Allahu karkiji komai,

Jawaheer takaranto mata nombar sannan ta amshi munubiyya  ta fito daga store din don ta lura da take takenta,


Wani bakincikine ya turnike fa iza wannan shine ga sa a ga rabo.

Lambar lamido taso tasamu bata matarsaba,

Shidin taso yatsaya suyi magana amma hakan bata yuwuba,

Wata zuciya tace mata bisu abaya kiga gidansu,

Inyaso saiki kaimasu ziyarar  bazata,

Tayanda zaki gudanar da shirinki cikin sauki,


Dasauri ta fito daga store din saidai wayam babu shi babu dalilinsa,

Wani takaici ya lullubeta anyako tanada sa a arayuwarta?

Matansa basa gabanta burinta dwya ta mallakeshi,

Saidai abubuwa sunzomata abaibai,

Yazama dole tasamo soyayyarsa kota halin kaka,

Don bazata iya hakura dashiba,

Tayi alkawarin saitasato zuciyarsa atafin hannunta,

Matsalarta daya shine batasan gidansaba,

Amma babu komai lokaci na zuwa.

Dahaka tajuya ta nufi gida.





Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

2⃣9⃣




Na 

Maman sadeeq









"Suna zaune afalo su duka,

Kawaheer tana ruke da munubiyya,

Siyama, da haleesa, da saifu,

Suka tashi sukayima dadyn shi oyoyo.

Ya ajiye ledar dayayi siyayyar kayan

Ganin marar lafiyan.


Ya dauki munubiyya, ya bude ledar yace.

"dauki abinda kk so".


Ta singumi kwalin madarar Dansa,

Yace da siyama kema zoki dauki abinda kk so"

Tazo tadauki kwalin 5alive.

Saifu ma yazo yadauka, haka haleesa.

Abdoola ma Yazo yadauka,

Ya rage daga cake sai dannot,

  Yadubi hajir yace,

Tokema hjy karama zoki dauka,

   Ayatsine ta dauki cake din,

Yadubi jawaheer yace to saurake hjy babba".

Jawaheer ta dauki dannot din,

Yace tau saurani ban samuba kuyimin karo-karo".


Jawaheer tace wai yau wannan sayayyar kamar me shirin zuwa dubiya?komai da ban daban?

          Yace wlh ko kamar kin sani, 

Wani naje dubawa natarar an sallameshi,


Jawaheer tace,

"Haba "D,

Aidasaika bayar kaga kasamu ladar da taniyya data bayarwa,

Kodayake yanzuma kasamu lada linkin balinkin,

Tunda mafificiyar kyauta itace wadata iyali".


Yace yawwa my D, shiyasa nake sanki, 

Akwai fadin gaskiya duk daci ko my hajir?

       Yafada yana kallonta tatabe baki tace A'ah ni inzaku kubar jirana".


Suduka sumfahimceta sai suka basar.

Jawaheer tace D, muje kayi wanka tun kafin magruba tayi ko?

       Yace shikenan D, mutafi sai ki tayani ko?

Yasabi munubiyya tace ina zaka da ita kaida zakayi wanka?

Yace ina ruwanki?

Tace babu".

Yayi gaba tabishi abaya,


Haushi kam yakashe hajir daga zaune, badan komaiba saidan madarar da munubiyya ta dauka, 

Saboda duk acikin kayan madarar tafi  tsada.

Aganinta yaso yanuna bambanci atsakamin yaran,

Imbajakaba taya zai iya baiwa yar kankanuwar yarinya abinda yashallake na iyayanta ma ba dangintaba.


Yazama dole tayi gaggawar bankawa tsinanniyar yarinyar guba, kota kauce tabata wuri.

Allah yasani taruke mata mara tahanata tayi fitsari, yadda take muradi,

Tayi kwafa tatashi tashiga daki,


Washe gari hajir takarbi girki, 

Kafin yadawo hartashiryamashi komai,

Lokacin dayadawo tana daki jawaheer ce kadai da munubiyya. 

Dan haka ya suri munubiyya yanufi sashensa.


Wayarsa yadauka yakira hajir yasanar da ita yadawo, dasauri tafito gudun kada cingom din talikemasa(munubiyya)


Ganin jawaheer ita kadai yasa ta tabbatar aikin gama yariga da yagama, ya dauketa,

    Ta isa dakin yana rungume da munubiyya, sai kyalkyala dariya sukeyi.

  Tadaure tace ashe kashigo bansaniba?

Yace eh shiyasa nayi kiranki

Tace ruwa nacan najiranka.

   Yamike tsaye ya dubi munubiyya yace,

"munu  jirani wurin Anti inje indawo kinjiko?

  Yadorata akan cinyar hajir,

Yashiga bandaki.

Jitayi kamar ya doramata garwashin wuta a cinya.


Ta dubi uarinyar takaici yakamata,

Datasan zata samu wannan damar da tataho  da gubar ta dura mata,

To ko komawa zatayi ta dauko?


Idan kuma yarinyar ta mutu ahannunta saitace yaya?

Dole ta hkr da aiwatar  da shirinta ayanzu,

Tayi hkr gobe iyanzu  tadade alahira.


Lamido yafito daga bandaki  yashigo yasaka jallabiya, munubiyya  ta soma mutsu mutsun tahowa wurinsa,

Yasa hannu yadauketa yace,

" munu"

Yayi mata kiss agoshi,

Tayi dariya,

Yasake yimata,

Takuma yin dariyar.

Hajir tazo iya wuya,

Tace,

Toni ko inkoma saika nemeni?

Yace a'yi jkr hadamini

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣1⃣





Na

Maman sadeeq







"tana zaune tayi tagumi tana tunanin halin rayuwa.

Ayau har an wayi gari ummu  tasa mu kwanan wata biyu ba yan kadan,

Lallai rayuwa wata kundice mai siffar littafi, mai daukeda shafuka masu yawa,



Yadade yana tsaye akanta amma bata luraba,

Dogon tunanin datakeyine yahanata jiyo sallamarsa,


Ke!" yadakamata tsawa,

Tayi firgigit tadawo natsuwarta,

Tadubeshi tace,

Baba sannu da zuwa,

   Bai amsaba yace ina kudina sun samu?


Tadukar dakanta, 

Ita harga Allah tamanta da yaune zaizo karbar kudin hayar,

Gashi kuma babu wani kudi nakuzo kugani ahannunta,

To yanzu mezatace dashi?


Cikin fusata yace basu samuba ko?

Tayi shiru takasa amsamasa, yace,

Tashi ki daukomin key din gidan"


Tayi saurin dubansa jin abinda yace tace,

Baba don Allah kayi hkr,

Wlh zankawoaka kudin har gida,

Idan munbarnan ina zamuje?


Yace kuje ko inama,

Ainafadamaki bambaki arufeba,

Tashi ki daukomin key idan kuma baki da niyya da akwai key ataredani,

Maza hado kan kannenki dan zan datse gidana.


Tafashe dakuka tana fadin,

Baba dan Allah katausayamana,

Bamuda kowa sai Allah sai ku,

Idan muntafi  bamusan inda zamujeba.


Yace karki damu rufe gidan sai inkaiku gidan sani.

Tace "To.

Tadauko makulli taashi takamo hannun kannenta, da kullin kayansu suka shiga mota yanufi gidan sani,


Balaraba ta na zaune afalo itada sani suna kallo,

Rabe yayi sallama,

Su zuhra suna biyedashi abaya,

Balaraba tayi sauri tadakatar dasu cikin tsawa,

Tace,

Kai kudakata anan,

Kar ku shigomin,

Kubariya gama abinda yakawoshi saikubishi,

Wannan gayyar ai sai su lubabatu,

Nikam tawa ta isheni,


Rabe yadubi balaraba yace,

Luabatuma babu wuri ke aibaki da yara dayawa,

Kinga ko aiki ne ke kyarunka saka su".

Sani yace waikai daga ina kadebosune?


Rabe yace daga gidana saboda ina san insaka yan haya agidan shine nataho nan dasu,

Saboda kai gidanka yafi nawa yalwa,

Dan haka gasunan.

Ke balaraba saiki runka kula dasu yanda ya dace".


Sani yace wai dagaske nan kakawominsu?


Rabe yace eh wlh"


Balaraba tace A'dasake wlh,

Banyardaba ina dalili,meyasa uban nasu yakasa sama masu muhallin dazasu zauna kafin ya mutu?


Tonan gidan yayanane suma suje inda ubansu yasamamasu,

Idanko babu ai duniya dafadi,

Kuma duk wqnda yarasa uba duniya ita take zame masa uwa harma da uba,

Dan aka sushiga duniya badai nan gidamba,


Wasu hawaye suka biyo fuskar zuhra ta durkusa kan gwiwa tace. 

Dan Allah baba ku tausayamana.

Bamuda kowa aduniya saiku,

Idan baku dubi zumuncia tokudubi girman Allah".


Sani yayi shiru dan yataisayawa yarinyar,

Dakuma irin halin dazasu shiga idan suka wofintqrda su, yazama dole susan abinyi,

Yadubi zura yace share hawayenki, yace bari kuka haka.


Yadubi rabe yace kasan abindaza ayi Rabe?


Yace A'a saikafada,

Inaga muduba zancen yarinyarnan, danko kan hanya yake,

Idan bazamuyi don zumunciba to mudubi girman Allah,

Inaganin kabarmin yan mazan anan,  Kadauki ita zuhran kakaita gidanka,

Idan makayi duba da nan da dan wani lokacin gidan mijinta zata tafi".


Rabe yace gaskiya lubabatu bazata yardaba, 

Kaikahada duka karike Allah saiyabaka ladar".


Sani yace kadai tafi da ita, 

Ita lubabatun gidan tane dazata hanaka abindakaga dama?

Tashi zuhra kibishi"


Wani kuka ya ballemata jin za arabata da yan uwanta,

Saidai nabu yanda zatayi dole tahakura, 

Suma yaran kukan sukeyi,

Dan zuhra itace tamaye masu gurbin iyayansu dasuka rasa.



Suka isa gidan Rabe.

Yana gaba tana niye dashi abaya,

Lubabatu takalleta tace,

"To yanzu kuma maiyakawoki?

Aikaruwar ta barmaku duniya bare kice ita ta aiko kikarbar mata wani abu,


Wani abu maikamar mashi ya soki zuciyar zuhra,

Jin kalaman lubabatu,saidai babu yanda zatayi kaddara taruga fata,

Tun yanzu za afara fada mata haka inaga tafiya tayi tagiya.


Lubabatu tace fadi abinda yakawoki kinsaka mu agaba saikace iyalan kamtaka(mayu)


Rabe yace kudin hayata naje karba, 

Babu kudi ahannunsu shine narufo gidana...............,

Lubabatu tatari numfashinsa tace to dababu kudi kuma sai akayi yaya?


Rabe yace saina dauko su yan mazan nakaisu gidan sani ita kuma zuhra sai nayo nan da ita,


A'ina lubabatu tafada,

Rabe yayi shiru,

Tace wlh badai anan gidanba,

Yo mekenan?

A'a dasake nibazan yarda adaukomin kazanta akawomani gidaba,


Yace kinga tunda dai sani ya amshi yarannan nasan abin mai girmane, kiyi hkr kawai tunda zaman nadan lokacine zatayi.


Lubabatu tayi shiru tana nazari,

Zuwacan tadubi Rabe tace,

To yanxun da kakawota ina  kake nufin ajiyeta?

Yace sai su zauna itada fa iza ada ki daya.


Lubabatu tace A'a bazata zaunaba daki daya da fa iza ba,

Inkace haka kenan babu bambanci atsakaninsu,

Saidai tarunka kwana asoro ko madafi(kicin)"


Rabe yace babu damuwa duk wanda kika zaba mata Shizatayi.



Washe gari tatashi takama aiki babu saurarawa,

lubabatu tace kinyiwa kanki alam nashraha, don bauta zakiyi agidannan, wadda ta amsa sunanta bauta,

Saboda bazaki bude kafarkiba saidai abaki


Rabe yace kinyi daidai, 

Ai yamacece dole ahorata tunda gidan wani zata ,


Ayinin ranar cikin aiki ta wuni, babu afuwa, saidai dayake baraguwa bace sai bata damuba


Adnan yayi sallama ya shigo,

Fa iza ta rugo da gudu tana yimasa sannu da zuwa,

Itama tayi masa sannu da zuwa yayimata kyar  da ido, 

Fa iza tadubeshi tace masa,

Kasantane?


Yace naso insaidata amma na manta,

Fa iza tace yar gidan Auwalucefa"


Yace to kice kofsi aiutumennan ya kwafsa mana"

Fa iza tace yadai kwafsawa kansa kosan ma yazarce mutuwa?

Yace yaushe?

Tace kai mubar zancen"


Suka nufi dakin lubabatu.


Magan ganunsu sundaki zuciyar ta saidai bayandazatayi


Haka taga ana tazuwarma Adnan barka dazuwa,

Tabbas tasanshi saidai batasan inda yajeba babu mamaki ko makaranta yakeyi,



Adnan ne zaune shida ummanshi suna fira yace,

Niko umma dazaki yarda dasai ayi yar gida....

Tayi sauri tace dawa?


Yace xujra mana wlh ina santa.

Lubanatu tace. 

Mafarki kakeyi,

Aiko bayan raina bakai ba auren iyalan ududuwa,

Bare kuma ina raye,

Habiba tananan ko kamanta da Alkawarin?

Yace A'a bam nantaba inda zakiyarda sai inhadasu su biyun.

Tace ban yardaba kuma bazan yardaba,

Kar insake jin wannan maganar daga bakinka.....tashi maza kabar gurinnan.




Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣2⃣






Na

Maman sadeeq







"Yafaka motar afarfajiyar gidan,

Suka fito suduka, 

Jawaheer batakawo komai araiba,

Ganin hajir da ledojin yaran ahannunta,

Suka shiga gidan ababban falo suka zube,

Yaran suka nufi hajir tace aikowa yasan tasa ko?

Suka ce eh, 

Tabawa kowa nasa,

Na munubiyya kuwa saida ta tabatar sannan tabata dan gudun akasi,


Duk yaran suka bude ledar suka soma cin kayansu,

Tana kallo munubiyya tadauki wani kek wanda ta murtsike da gubar takai bakinta.

  Wani dadi taji cikin zuciyarta,

Kuma tana cewa,

Haba yarinya yau saidai wata ba keba,


Lamido yace "munu dan yammin  kek din"


Tamikomasa yasa hannu yakarba zaikai baki,

Hajir taji kamar tace kada yaci, sai kuma tagaza takama kanta,


Itako munubiyya kodataga zaikai baki tayi sauri ta ruke hannunsa, alamar yabata abinta,


Ya mika mata kek din saida ta cinye kana tadauko wani sweet din takai baki.


Sannu ahankali munubiyya tacinye duka nata sweet din,

Amma bakota yamutsa fuskaba,

Saidai wani abin mamaki,

Siyamace take rike da ciki tanata mutsu mutsu.



Lamido shiya lura dahalin da yarinyar take ciki, yace"

Siyama ya akayine?


Tace dady cikina ciwo yakeyi".

Hajir tai saurin cewa cikinki ke ciwo?

  Tadaga kai".

Hajir takamota tana matsa matsamata Ciki,

Saiga gumi keta fesowa yarinyar.

     Lamido yace bara in kaita asibiti"


Jawaheer tace wannan shine ikon allah, 

Yanzufa take nan lafiyarta klw,


Hajir kam duk takidime, 

Hijabinta tadauka, tabi lamido suka nufi asibiti,

Saidai kafin su  isa  asibitin siyama ta amsa kiran ubangijinta.


Hajir tace da lamido "hubby dubata kagani ko tayi barci?"


Yataka birki, ya amshi  siyama, yaduba atake yagano babu rai  atare da ita,

Yarungume gawar wasu hawaye masu zafi suka biyomasa,


Koda hajir taga yana hawaye, 

Itama saitafashe da kuka,

Wayyo Allah nashiga ukku, wayyo narasa diyata.


Dasauri yajuya motar yanufi gidansu,

   Hajir bata tsagaita da kukanba,


Suka isa gidan hajiya,

Tadubesu yana dauke dagawar siyama, tace,

Subhanallahi yaya akayine?


Hajir tasake fashewa da kuka,

Lamido yace hjy siyama ce Allah yayi mata rasuwa, shine nakawotanan dan ayimata sutura,

Hjy tace Allahu akbar  rai bakon duniya,

Toyi sauri kasayo likafani kakai ahado.


Yafita hjy ta yitabawa hajir  hakuri,

Karfe biyu akayiwa siyama jana iza. 


Jawaheer ta kira lamido tace "D, yajikin siyamar,?

Yace "D, ai siyama Allah yayimata rasuwa,

Yanzi haka mina nan gidan hjy anan ake yin ta aziyya"


 Tace Allahu akbar siyama ashe duk bankwana takeyi?

To ganinan zuwa"


Yace kiyi hkr  hjy tace mutaho gida,

Saboda wadanda zasu zo wa hajir gaisuwa,

Tace to shikenan sai kunzo".



Karfe uku suka taho gida,

Hajir kam haryanxun takasa daina kuka,

Dan ganin abintake kamar amafarki,

Tayaya wannan bahagon al amarin zaizomata ahaka?


Saida tatabbatar gubar takayan munubiyya ce kadai bare tace ko ansamu sabani,

To amma ya akayi ita munubiyyan taci gubar amma bata mutuba?

Sai siyama.


Ayanzu kam ta jakikance cewa mai gubar  siyama taci.

Amma kuma wata xuciyar taki yarda da hakan,

Don duk cikin siyayar yaran babu me kek aciki sai na munubiyya,

Kuma shine kek din data zubawa gubar,

Kuma dai agabansu yaran sika saka kayan gaba suna ci bare tace ko jawaheer  ta amshi nasiyama tabaiwa munubiyya,

  Lallai duk yanda akayi akwai kullallen al amari, wanda batasan dashiba,



Jawaheer tace "D, yahakurinmu?

Yace hakuri mungode"


Tadubi jajir dake sjarbe hawaye,

    Hajir ya hakuri?

Bata tankamataba,

Donzata iyacewa itace takashemata diya,

Togai suwar mexatayimata?


Jawaheer tace "Allah yajikanta, kekuma Allah yabaki hkr".


Hajir taji wani bakin ciki yatokaremata zuciya,

Wato ankashemata diya shine ake bata hkr?

To zata dauki mataki, 

Wlh saita dauki fansa,

Tunda aka kashemata siyama itama saitakashe su Abdool ba munubiyya kadaiba, harda su saifusai takashe,.

   Ita daya akayimata amma ita idan tatashi saitayi ukku,


Dahaka tagama yanke shawarar yadda zatayi, 

      Tadauki wayarta tayi kiran yan uwa da Abokan Arzuki tana sanar dasu  rasuwar yar tata siyama.





Wash! Wash!wash!

Kuyi hkr dawannan Aradu hannuna yagaji🤡🤡












Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣3⃣





Na

Maman sadeeq






"A tun lokacin da yadawo ta lura yana matsa mata da kallo,

Itakam batasan wata alaka tashiga tsakaninta dashi,

 Amma duk da hakan yana yawan shigemata,

Musamman kai abinci, dayin gugar kaya,

Duk itace yake sawa,

Babu abinda tatsana irin kaimasa Abinci adaki.


Domin talura bashida kunya,

Don Yazauna daga shi saigajeran wando bawani abubane,

Itako bataso.

Saidai babu yadda zatayi,

    Don wata rashin kunyarma,

Yarinyar da zai aura habiba hargida take zuwa wurinshi susha firarsu,


Abin yana bata mamaki,

Tayadda mace ke zubar da kimarta, tabiyo namiji har gida,

Alhalin shi aka sani daya bi mace.


Abbas yafado mata arai, 

Yaushe rabon da su hadu?

Tun suna gida, 

Babu mamaki baisan suna nan gidan baba Rabe ba, tunda afujajan suka taso. 

   Ko su innar su sani basu samba suntasoba,

Tasan sunacan suna zulumi inda suka nufa,

Yazama dole inzataje dubo su hamza ta wuce tafadama innarsu sani, tafadamasu cewa rukonsu ya koma gun kannen mahaifinsu.


Haka tatashi tacigaba da yin ayyukanta,

Batasamu zamaba saida akayi kiran sallar mangaruba,

   Tayi Alwala tashiga kicin tadauko hijabinta tadawo tsakar gida tatayar da sallah,

Tana gamawa Adnan yashigo yace

"ke!

Sunan da yake kiranta dashi kenan,

Yace amsomin abincina wurin umma kikawo min daki".


Tamike tsaye tanufi dakin lubabatu tace "inna abada abincin Adnan,


Lubabatu tace wato  bashi da arzikin dazakice masa yaya saidai Adnan  gatsau ko kunya bakiji?


Tadukar dakanta kasa,

Fa iza tace,

Idan tace dashi yaya aitanuna halin dabata gadaba,

Ina danga arnan kandutse?


Lubabatu tamiko mata abincin,

Tadauka tanufi dakin Adnan,


Yana zaune akan gado tashiga tadora abincin kan center table din dakin, tajuya.


Ke!

Yakirata.

Tadawo yadubeta cikin wani kallo nakashe ido yace.

"kinyi wanka?

   Tambayar tadaure mata kai,

Tarasa abindazatace masa,

Don bata fahimceshiba, yace jeki kawai".


Tafito daga cikin dakin tanufi cikin gida ta amso abincinta ta nufi kicin taci abinta.

     Tatashi tadauro Alwala tayi sallar isha 'i.

Tagabatar da Addu o inta, sannan ta shimfida dan buhunta ta kwanta.

   Kasancewar ta wuni tana hidima  yasa tana kwanciya barci ya dauketa.



Dare yayi kafata dauke babu abinda kakeji sai kukan karnuka  da iskan sanyi,

Wanda ke kada itatuwa,

Azatonta mafarki takeyi shiyasa bata damuba,

Saboda shaikin datakeji,

Andauki lkc tana abu daya, acewarta mafarkine takeyi.


To amma aiyaci awuce wurin idan mafarkine amma abubuwa saidada karuwa sukeyi,


Jitayi ankai baki akan kirjinta ana tsotsa cikin salo,

Ubangiji yakawomata agaji tahanyar bude idonta,

Kicin din dundum yake da duhu ba ka ko iya ganin tafin hannunka,


Jitai ankankameta da hannu  biyu cikin jarumta tanemi kwacewa saidai takasa.


Cizo takawo batasan inda tadamka da hakori ba iyakacin karfinta tayi cizon, 

Ko shakka babu tajimasa ciwo,

Koma wanene jitayi ansaketa,


Tayi mazatatashi tanufi ma kyallin wuta,

Saidai kafin ta kunna kyallin har yafita daga dakin,

Tayi sauri taleka dantaga kowanene, yakeda mugun kudiri akanta saidai garin dundum yake da duhu, saboda rashin wutar nefa.


Tadawo ta makure aguri daya,

Babu batun bacci a idonta sai kuka takeyi kamar ranta zaifita meyasa za ayimata haka?

Meyasa baza a tausayawa maraicintaba?



Misalin karfe goma Adnan yashigo,

Tadubeshi shima ya dubeta,

Ciwon datagani akuncinsa shi ya tabbatarmata dashi yaso ya lalatamata rayuwa.


Yakuma dubanta cikin kunar zuciya, 

Baiyi wata wata ba yadauketa da mari.

Tadafe inda ya maretan  tace mainayimaka?


Yakuma hasala yace dan ubanki ni kike tambaya abinda kikayiminko?

Tobari idan jikinki yayi tsami saiki kuma tambayata,

Yazare belt yacigaba da jibgarta tamkar an aikoshi.


Lubabatu taji karar kukan zuhra dasauri tafito taruke belt din tana tambayar abinda yafaru.

Adnan yanuna mata ciwon dake kuncinsa, 

Tace subhanallahi garinya haka tafaru?


Zuhra tace jiya dadaddare ina barci sainaji mutum yana tabani nikima nacijesa,

Bansanba shibane saiyanzu kawai saiyahauni da duka.




Lubabatu tayi tafi tare da sallalami tace,

Yau abin har yakai haka?

To wlh bazan yardaba, 

Aini dama nasan arina aduk sanda yaronnan zai shigo idanki akansa,

Sjine saida kikayi yanda kikayi kika yaudareshi?

To Allah ya isa banyafeba.

Kuma daga yau zamanki yazo karshe agidannan,

Donbazakizo ki batamin yaroba, barima inkira Raben.


Zuhra ta rushe da kuka jin abinda lubabatu ta fada,


Fa iza tace kedaikam kinyi asara,

Kodayake babu mamaki idan akayi duba da tushenki, abinda yafi wannanma za ki iya aikatawa.


Rabe ya fito shida lubabatu karya dagaskiya ta fada masa,

Shima din jibgarta yashiga yi.

Saida yatabbatar ta bugu sannan ya kyaleta,

Ba haka lubabatu tasoba taso ace ya koreta gaa daya dan ita ta soma gajiya.

To amma da sannu tunda amfara haka.



Ahaka tawuce cikin radadin dukan da akayimata, duk da halin datake ciki, ba atausayamataba,

Akaragemata yawan ayyukamba.



Maman sadeeq

[9:30PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣4⃣





Na

Maman sadeeq







"Ayau yatashi dabegen  yarinyar data damke zuciyarsa.

Bakomai yasa hakaba sai magarkin da yayi  da ita,wai gashi  ga ita suna zaune guri daya,

Hartakamo hannunshi tasaka mashi zobe,

Saikuma tace wannan zoben nabakashi  sadakin son da kakemin,


Abin ya tsaya mashi arai,

To metake nifi da haka?

Ahaka dai yashirya yanufi ofis.


A ofis dinma tunaninta kawai yakeyi,

Shiyasa yakasa aikata komi,daga karshe sai yakira sakatarenshi Rabe,

Ya shigo ya zauna yadubeshi yace.


"Ranka ahi dade wai lafiya naga kamar baka lafiya?


Lamido yace kaidai bari Rabe.

Shiyasa nakiraka don imbaka wadannan takardun, kaje ku cikeminsu.

Wlh bana jin dadine,

Yakamatama nakoma gida amma zambari sai  antashi,


Rabe yace to ka koma gida mana tunda bakada lfy.


Lamido yace baridai imbari atashi kawai,

Tunda ba ciwon jikibane, laifin zuciyane.


Rabe yace koda naji ninasan laifin nazuciyane,

Wata kila data azabtu da bege ko kauna ko?


Lamido yayi murmushi jin Rabe yafarkemashi laya,

Rabe yace imbanda abinka ranka shi dade akwai yarinyarda zakagani kana so harta gagareka?

Aiko diyar shugabankasace kanema kasameta,

Fadamin ita ni innemoma ka ita duk inda take, ko yar inace"


Lamido yace tokai Rabe wayagayamaka  duk akan mace nashiga wannan halin?


Rabe yayi murmushi yace kaine dakanka,

Tunda kace laifin zuciyane, aibasaika karasaba "sone kawai,


Lamido yace to bazan iya yarda damaganarkaba,

Saidai ninawa son yazo da matsala,"

   Rabe yace wace irin matsala kuma?


Lamido yace Rabe inaga mubar wannan maganar tundadai ba maganin matsalar zakayimaniba.


Rabe yace "eh, saidai zan yimaka albishir kokuma ince huce haushi"


Lamido yayi maza yace dame zakayimin huce haushin?


Rabe yace da yayana sai wacce kazaba zambaka.


Lamido yayi dariya yace haba Rabe,

Kamar ni ace za ayimin huce haushi?


Rabe yace karkace haka kabari saikagansu kana ka yanke hukunci".


Lamido yace inaga mubar zancennan haka Rabe,

Kaje ka karasa aikinnan kawai"


Rabe yace gaskia ranka shi dade sainabaka daya daga cikin yayana, don ina so muhada jini dakai".


Lamido yace tonaji, yanzu dai jeka kacigaba da aikinka,


Rabe yatashi yanufi nashi ofis din


Azahirin gaskiya lamido yadauki zancen Rabe shirme,

Tayaya diyan Rabe zasu burgeshi,

Alhalin yana da lyawawan mata biyu agida?

Jawaidai yayi tsokanarshi yagama.

Shi idan ba yar budurwar da zuciyarshi kesoba to yarufe shafin aure,

Dan babu tsarin kara  aure arayuwarshi

Yanzu,

Amma idan tauraruwarshi ce da gudu zai amsheta.


Shiko Rabe gani yake idan yahada jini da lamido ta hanyar aure to kakarshi ta yanke saka, 

Tunkafin aje gabatun auren ma zai fara ta tsarshi,yadda yakeso,

Inama yace yana son rai zakai dashi, shilam yahaye har lubabatu,



Tosaidai yaga yafara kushe al amarin tun yanzun,

Kodayake bari yakoma gida saiyafadama lubabatu,

Inyaso saitanemawa fa izar taimako, koma da kwalline ko turare.


Lallai hakama za ayi tunkafin abin yayiwu har yakwadaitu da abinda yake sa ran samu.


Wata dariyayayi tareda shafar gemunshi,yadauki wayarsa yakira zuwaira yace tatanadarmashi Abinci dan zaixo yau.


Tace to ina jiranka"


Yayimata sallama yacigaba da aikinshi.







Kuyi hkr da wannan kunsan jiki dajini sai a hankali😁😁





Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣5⃣






Na

Maman sadeeq










"Haka yayi tasakawa da warwarewa, har akatashi daga aikin.


Yana zuwa gida yasamu lubabatu ya kwshe komai yafadamata,

Lubabatu tayi shewa tace.


Alhamdu lillahi, yanzu yanzu naji magana Rabe,

Idan yarinyarnan ta yi aure gidan mai akwai nikaina nasan zan huta,

Amma kacewani sadakarta zaka bada,saidaikace budurwqr daji,

Allah yakaimu gobe,

Ni kuma zanje insamomata taimako, 

Allah dai yasa mudace.


Itako fa iza yazama dole tature wancan tsinannan mutumen daya kamemata zuciya,

Wayasani ma ko Aljanine tayi gamo dashi?


Rabe yace "kuma kisani idan hartakafe bazata auri wannan ubangidan nawaba,to wlh saina bada kyautarta ga duk wanda naga dama,

Don bazata mayardani dan iskaba.


Lubabatu tace kwantarda hankalinka zatama aureshi, badai yanada kudiba?

Aizance yakare,

Saidai ina tsoron karyawatsa mana kasa A ido, yace batayimashiba, tunda bashine yaganta yace yana soba,

Kasan maza".


Rabe yace bashiyasa nace kinemamata taimakoba,

Koyana so kobayaso dolensa ya aureta.

   Kedai Allah yakaimu gobe,

Zambaki kudi kije ki karbomata dan taimakon, 

Dan idan komai yayi kyau zamfanshe kudin harma da riba"


Lubabatu tace to Allah dai yasa kartanamu kunya,

Dan inaga dakamar wuya fa iza ta yarda,bakaji yanda take cewaba,

Wai idan ba mutumennanba saidai ta mutu babu Aure".


Rabe yace saikifadamata abinda nace,idan harbata yarda da aurennanba wlh saina bada sadakinta,

Cikin biyu saitayi daya.


Lubabatu tace dolenema tabi abinda muke so, 

Dan da arziki agarin wasu aigara agarinku,

Kaidai Allah yakaimu goben,

Idan naje gurin malamin zance yabani lakani  na masu gardama, wanda duk abinda mukace tabimu da to".


Rabe yace hakama za ayi 

Dan idan ta botsare ai mutayiwa bakin ciki,

To garako ayi maganin abin tun wuri".



Dawannan shawarar suka kwanta.

Washegari tunda safe lubabatu tatafi amso taimako ta bar fa iza da zuhra acikin gida.


Fa iza ta kira zuhra  tazo, tadubeta a sheke tace,

"ke zoki gogemin kaushi dauko dutsen,


Zuwaira tayi sallama tashigo,

 Fa iza ta ce yar iska saiyanzu kikagadamar zuwa?


Zuwaira tace  kedaibari dan anacen nawane yamatsa mani shiyasa kikaga banzoba.


Fa iza tace wai waye wannan dan anacen?


Zuwaira tatabe baki tace karkiso saninshi kedai tsaya matsayinki".


Fa iza tace kwantarda hankalinki niyanzu babu low araina sai man dinnan.

Dama dan imfada maki yanda mukayidashi,

Bakima san wani abuba,

Zuwaira matanshi biyu fa?


Zuwaira tazaro ido tace mata biyu?


Fa iza tace wlh kau"


Tace to ke ahaka kike sonshi harki iya zama da matanshi?


Faiza taja tsaki tace,

"yoni ina ruwana da matanshi?

Aini shinake so

Kuma burina in mallakeshi atafin hannuna,

Dasannu sukuma matanshi zasu raina kansu".


Zuwaira tatabe baki tace lallai saikin dage,

Yanzudai kin karbi kodai lambarshi ko?

Dan tahakane zaki samu hanyar cusa kanki gareshi".


Fa iza tace inafa saidai tamatarshi na amsa, maidan saukin kai, kodayake itama saidatayimani kashedi cikin hikima,

Waidafatan daga zumunci babu wani abu  nadai bita da eh"

Zuwaira tace tayi abanza indai namijine.


Fa iza tace da Alla bar sakara yar iska,

Ai insukayi sake nasato zuciyar mijinsu  to sukam sadai sorry,

Dan hardiyar da nace ina so saita raina kanta,

Dama can shi nake so ba itaba,nafake da guzumane zan harbi karsana"


Zuhra tanajinsu sunata zancansu, 

Tana mamakin yanda mata suke haukacewa qkan maza,

Musamman mata masu tallar kansu ga maza,

Irinsu faiza dan ta fahimci wanine wanda shi fa izar takeso, 

Wanda shi bai san tanayiba.


Lallai zamani abin tsorone,


Saidatagama gogemata kaushin sannan tatashi,

Fa iza tace,

Ke shiga da kina kayana nanan ki kwasosu ki wanke mani".


Zuhra tace to"


Zuwaira tace faiza wai wannan kanwarkice?


Fa iza tace A'a yar aiki ce akakawo"


Zuwaira tace nadauka yar family dinkuce dan naganta da tsagen rumanci?.


Fa iza tace don Allah abar wannan zancen, 

Niyanzu kibani shawara yaya zan hudoma wannan  Al arin?


Zuwaira tace kuskuren dakikayi dayane dakinbi bayanshi kinga gidanshi, 

Todasai ince zaki sameshi cikin sauki,

Yanzukau ko aiki za ayi akanshi ai sai annemi indayake, kokuma gidanshi,

Yanzu abinda za ayi karki gaji duk asabar kirunka zuwa sahad,

Idan kinganshi saikisan yadda kika yi kika bi bayanshi,idan kingano gidanshi saimusoma bankomashi aikinmu".


Fa iza tace,

Taya zamu soma aikin?


Zuwaira tace zaki runka zuwa gidan dasunan  kin ziyarci yarsu,

Dahaka har yazo hannu,

Saidaifa kiyi  ahankali,

Dan wannan aikin dole za asamu hadari atareda shi

WUKA CE A MAKOSHIn ki da an kuskure to zata ratsa mako shinki, 

Saiki kiyaye dan gudun samun akasi".


Fa iza tayi ajiyar zuciya tace tabbas zuwaira haka zancenki yake,

Saidai ni bazanji wata matsalaba,

Indai zan samu man dinnan ahannu,

Kedai tayani da addu a zuwaira.

Zan wuce kuma saina dace".


Zuwaira tace  to Allah yasa mudace"


Fa iza tace amin.


Zuwaira tatashi tace ni inaganin zan wuce sai asabar din zanzo muje sahad din".


Fa iza tace " to sai kinzo


Tarakota nakin titi tatafi gida.




Kuyi manage dawannan don bana jin dadin jikina.





Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣6⃣




Na 

Maman sadeeq














" Laila sanata ta dubi hajir cikin tsana nin mamaki tace,

"ya akayi kikayi sakakin da hakan tafaru hajir?

Ni inaganin baki baima yarinyar nan abu mai guba ba,

Akasi akasamu kika baiwa siyama mai gubar,


Hajir tasauke tagumin datayi da hannu tace,

Wlh laila inada yakinin siyama bataci  abinda nazubama gubarnamba"


Laila tace yazakice haka idan siyama bata ci abu mai gubaba to meye ya kasheta?


Itakuwa munubiyya indataci kina ganin zatakai labari?


Hajir tace bari kiji laila. 

Aduk vikin kayannan babu mai kek sai na munubiyya,

Kuma saida natabbatar dana cakudashi da duk gubar da kika bani, 

Sannan nadauki nata nasaka mata mai gubar,

Da ace siyama taci kek din munubiyya da na sauya dasai ince taci gubar,

Kedai da akwai makarkashiyar da akashiryamani,

Kuma bazan yardaba tunda aka kashemin siyama nima sai nakashe duk yaran jawaheer,

Saidai duk abinda za ayi ayi"


Laila tace ai angaya maki baki yardaba saiyanzun darana ta bacin miki?


Tunda aka fara haka to halisa ma baza abarta ba abaya ba,

Daga kanta kuma sai ajuyo kanki,

Kinga maganata tatabbata,

Za ayi babu ko shawarata tarage gareki.

Allah yanada hakuri yakuma bada na aikawa".


Ta mike tsaye tace nina wuce.


Hajir tace to laila nagode,

Zanzo zuwa jibi insha Allahu".


Laila tace mexakixo yi?


Jajir tace kibari sainazo mayi maganar".


Laila tatabe baki tace sai kinzo,


Tasakai tabar gidan,


Jaka hajir  tazauna har tsawon kwana bakwai,

Ran kwana bakwaine kanwarta tazoai suna diyana.


Diyana budurwace,

Itama yar gayuce tagaban kwatance,

Hartaso takere hajir din iya ado dasaka sutura masu tsada.


Ahalayya kam tayima hajeer fintinkau,

Dan tace hajir bata iya rashin ta idoba,

Kodayake babu mamaki idan akayi duba da inda tayi karatu,

Wato kasashen masu jajayen kunnuwa,

Shiyasa babu ta ido atare da ita.


Tayi sallama cikin yaren nasara, tashigo gaba daya suna cikin falon,

Hajir tatada kai ta dubeta.

  Halisa tatashi tataro anty nta,

 diyana ta zauna bisa kujera tacire dan gyalenta,


Tadubi  hajir tace anti yagida  dakuma hakuri,


Hajir tace yanzu diyana inyi rashin kikasa zomin gaisuwa saida akayi kwana bakwai?


Diyana ta yamutsa fuska tace wlh abubuwane sunyi yawa shiyasa kikaga banzoba"


Hajir tace yaya su mama?


Tace suna klw sunce nadada yimaki gaisuwa".


Hajir tace to nagode".


Diyana ta dubi jawaheer data maida hankalinta akan talabijin tatabe baki tace".


Yoke anti har angama zaman makokinne da har ake kunna talabijin?


Hajir tace makoki aina wanda yayi rashine shikadai, keda kuka wanda bashida asarafa?


Diyana tace tonikam zaman makoki nazo,

Dan haka baza acikamin kunne da hayaniyaba".


Tatashi tsam takashe talabijin tadawo tazauna.


Jawaheer ta dubeta tace ya haka?


Diyana tace hakan take kibari idannatafi sai ki kunna kallonki,


Kawaheer tace saboda gidan gyatuminkine?


Diyana tace ko daya bagidan gyatumina bane gidan yar uwatane,

Danhaka saidai kiyi hkr har imbar gidannan,

 sannan mukam gyatumi Alhamdulillahi awadace yake, baya aurar da yaya dan kara jari hujja, bare wani bakon abu dazaisa amike kafa".


Jawaheer tace aiko gyatumi ya kyauta,

Saidai da akwai bibaya,

Dominko ina kokwanto akan wadatarshi,

Ko awane matsayi yake?


"bantan ubancan, 

Diyana tatafi dasauri tacakumi wuyan jawaheer,

Hajir tace".


"ke diyana karki sake kitabata

Munji kuma mungode dakazafinta,

Niyanzu ta yata da narasa nakeyi,

Batatashin hankaliba.



Diyana tayi tsaye tana kallon jawaheer cikin kaskanci.


Jawaheer tace maiyasa kika tsaida ita?


Aida kinbarta ta tabka irin kuskuren dabatataba bayin irinshi arayuwartaba.

    Wlh dakin yarda kin iso gareni dana shayarda ke mamaki,

Meyadameni da ke da har zaki shigo rayuwata?

To kashedina nakarshe dake, idan kuma kin musa bari  inkunna talabijin  kikasheta dan Allah.


Jawaheer ta kunna talabijin tadawo taxauna, 

Tacigaba da lallonta batasake bi ta kansuba,



Diyana ta dauki dan gyalenta ta dubi hajir tace".


Nagode anti, komai akayimin ke kika jamin, sai anjima".


Tafice daga gidan, 


Abinda jawaheer tayima diyana yabata ran hajir,

Saidai kamar yanda tace alhinin mutuwar diyarta shine agabanta ba hayaniyaba,

Kuma alkawarin da ta dauka na kawar da yaran jawaheer ya na nan.

Shiyasa ta kyale bata sauraraba, yama za ayi ta saurara?


Diyarta da aka kashe tadai bari akara kwana biyu sannan tasake wani sabon shiri,


 







Lamido ya dawo daga Aiki agajiye, duk dabawani aiki yayiba imbanda tunani.


Hajir tashigo tahadamashi ruwan wanka.


Saidayayi sallar isha i sannan ta hada abincinshi ta kai mashi,


Shikanshi yaga canji atare da ita,

Kodayake yasan abinda ke damunta,

Dan haka dayagama cin abincin saiyajawota yashiga dakin barcinsu da ita ya zaunar da ita akan gado,

Yakira sunanta cikin sigar lallashi yace,

" hajir dan Allah ki sanyaya zuciyarki, kibar tunaninnan haka,

Allah shiyabaki siyama kuma shiya karbeta,

Danko yafiki santa,

Kiyi hkr kiyimata adfu a shine gatan da zaki nuna mata,

Idan kikayi hkr saikiga Allah yasake baki wata,

Yin haka dayayi wa azine daba kowa keganewaba,

Wata rana kema za a wayi gari babu ke,

Kuma idan kika natsu ba akanki aka fara rasa yayaba.


Ina rokonki dan Allah kibar da muwarnan haka nima ba dadi nakejiba, idan naga kinshiga da muwar nan,

Konima kina so inshiga damuwar?


Tashare hawayenta tace hubby dolene indamu, 

Mutuwa farat daya saikace ansamin hannu?


Yayi sauri yarufe mata baki dan ya fahimci inda ta dosa,


Yace haba hajir idan kikace haka sai inga kamar bakiyardaba da kaddaraba,


Karki kuma fadin haka siyama dai lokacintane yayi,

Takuma koma ga Allah dama daga gareshi take,

Fatan kar inkuma jin  wata magana.


Hajir ta rushe da kuka,

Dan gani takeyi yana kare jawaheer ne baiso afadi laifibta.


Ganinta rushe da kuka yasa yashiga lallashinta hartayi shiru,


Washe gari tace mashi tana so suje gidansu laila kuma tana so yabata kudi,


Yadauko dubu dari yabata saboda yana son ya lallabata,

Aganinshi tahakane zai rage mata damuwar dake tare da ita tarashin yarta da tayi,


Itama jawaheer yabata dubu darin sannan ya nufi ofis,


Tashirya tanufi gidan laila sanata.


Laila ta dubeta tace wlh har kimfada, inaga kirage damuwa haja ki rungumi kaddara".


Hajir tace wlh laila bazan rungumi kaddarannan nikadaiba saidai muyi kama kama nida jawaheer,

Dan wlh tundata tunda ta kashemin  ya ni ma sai na kashe duk yayanta, yanda nayi kuka akan yata guda daya ita sai idanunta sun tsiyaye dan duk saina karar da yayanta gaba daya wlh"


Laila tatabe baki tace yanzu wane mataki kika dauka?


Jajir tace ni yanzu nazo kizo muje kikaini wajan wani wanda zai mini aiki shine mata kin dazan dauka,

Tashi muje".


Laila tace yanzu ko zan kaiki inda za a yayemaki damuwarki,

Tashi muje inafatandai kintaho da kudi?


Hajir tace eh inada kudi".


Laila tace to muje yau wajan bama guje zan kaiki".


Hajir tace Allah dai yasa babu nisa?


Laila tace mezai dameki da nisan guri kedai babiyan bukata kikesoba?


Hajir  tace bana so hubby yadawo bana gida,

Ga halisa tatafi makaranta karta dawo a ida kashe min ita.


Laila tace babu nisa sosai nanne wani dan jauye kafin akai dan batta".


Hajir tace to muje".


A motar laila suka tafi basuwani dade sosaiba suka isa kauyen,


Laila ta faka motar suka fito,

Suka nufi yar bukkar bamaguje,

Matane sukayi layi,

Abin yabawa hajir mamaki ta dubi laila tace"


Ashe mutane le taruwa haka?


Laila tace ai yauma babu layi, 

Kuma kinga duk matannan da kike gani kusan ciwonsu iri dayane".


Hajir tace banganeba?


Laila tace eh bari inyimaki jimla, 

Har dake kema irin  ciwonsu ne dake".


Hajir tace yimin yadda zam fahimta".


Laila tace menene matsalarki ke?


Hajir tace "inkawar da yayan kishiyata,


Laila tayi murmushi tace atakaicedai kishiyarce matsalarki dai, to suma tarin matan can  inda zakije ki tambayesu dukjan matsalarsu akan kishiya take  kinga kenan ciwonku daya,


Hajir ta gyada kai tace ashedai tuni mata suja farka daga dogon barci?


Laila tace aikema din saida kikaga wutar gasaki sannan kika tashi,

A inda kika gano layin matan can wata kishiyar ce za ayimata,

Wata tagida take son afitarmata, 

To kigayamin wacce ce kezaune siddan?


Kin ganninan ko mutuwa nayi mijina saidai ya rungumi taswirata(hoto)

Badai ya dubi  wata maceba,

Dominko nayi nisa akanshi,

Kema imbanda haka akayimaki da baki nemi taimakoba".


Hajir tayi jagale da baki tana kallon laila sanata,tace,

Ke yanzu ko mutuwa kikayi mijinki bazayyiba aure ba?


Laila tace kina mamakine?


To kibar mamaki wlh dagani ya rufe kofar Aure anan dai duniya saidai ko idan alahira in anayi".


Hajir tace toyazakiyi da matan Aljanna daza aba mijinki?


Laila tace mubar zancen haka".


Hajir tayi dariya haka sukayita zancen har layi yazo kansu suka shiga bukkar bamaguje".



Hajir ta dubeshi  tabas  zai iya aikata rashin imani donko babu haske ataredashi,(musulunci)Arnene irin nacikin daji.


Laila tace ran bama guje yadade ga kawata nan nakawo aduba mata matsalarta,

Ina fatan za ayimata aikin dazata yaba har gobe  takawo maka wata.


Cikin gurbatacviyar hausarshi yace angama indai zatabi ka idojin aiki meyene matsalarta?


Laila tace matsalar dai bata wuce kishiya saidai kafin azo kan kishiyar yayan kishiyar takeson kawar dasu kafi kishiyar,

Mekake ganin yadace ayi akansu?



Bamaguje yace akwai abinda za ayi, 

Abasu magani tazubamasu a abinci ko abasu hodar mutuwa?


Laila ta dubi hajir donjin zabin datayi,


Hajir tace inaga abani hodar mutuwar,

Tunda bansan  lokacin da sukecin abinciba".


Ba maguje yadauko wata yar kwalba yamikawa laila,

Yace ga hodar nan idan yaran sun kwanta barci sai ta zubata atafin hannunta, ta hureta da iskar akinta,

Saidai kartayarda ta shaketa tadaure hancinta.

Sukuma yaran suna shaka to angama,".


Laila tamikawa hajir hodar tace to nawane za abada tukwicin?


Dubu talatin ne,  

Cewar bamaguje,

Hajir tadauko dubu talatin tabashi,


LAila tace to bama guje idan taji dadi zatadawo ayimata aiki kan kishiyar".


Dahaka sukayi ban kwana da bamaguje suka  kamo hanyar gida.




Wash nagaji 

Aradu typing wahalaaa😛😛🙅🏼






Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣7⃣




Na 

Maman sadeeq









"Fa'iza!      Fa'iza!!

Wai ina takene tabarni ina tafaman yage baki?


Fa ixa tafito daga daki tana ya mutsa fuska tace".

Gani umna, saifaman kwada min kira kikeyi  saikace makauniya".


Lubabatu tace taho yar arziki kiji wani labari da dumi duminsa".


Fa iza tace Allah daiyasa alherine?".


Lubabatu tace sosaimakau Alherine bisa Alheri".


Fa iza tace fada mani inji ko hankalina ya kwanta".


Luabatu tace Arzikine yake nemanki inafatan tsiya bazata hanaki zuwaba?"


Fa iza tace umma ni kiyimin yadda  xam fahimta, dik kin barni acikin duhu,


Lubabatu tace dama Rabene yayi tallarki agurin agan sa na wurin aiki,

Saboda yasan idan ya aureki mukam kakarmu ta yanke saka,

Kuma kema zaki huta.

Don ko mai kudine na tashin hankali,

     Shiyasama ya bani kudi in amso maki taimako,

Kinga gasu na amso,


Wannan turarene,

Da kuma kwalli,kunayin arba da juna to angama,

Kokuma yashaki kamshin turaren,kingama kamashi to saiki kula".


Faiza ta dubi lubabatu tace yanzu babanne yayi tallata saikace narasa masoyi?



Lubabatu tayi maza tace bahaka bane,

Hutu yake nemamaki,

Shiyasa yayi maki haka,


Fa iza tace aini umma nafi karfin ayi tallata ga namiji don ya aureni,

Kuma ni yanzu Abinda nakeji babu wani namiji da zan duba da sunan so face mutum daya,

Wlh idam bashiba saidai immutu babu Aure.


Dan haka kubar wahalar da kanku da kuma kudinku,

Idan kuma kun kwadaitu  da abin hannunshi to kubashi yargidan tarbiyya(zuhra)

Inaga itayafi dacewa ayi tallarta, Amma baniba.


Kuma idan baba yazo kice mai idan har taimakona yake sonyi to yanemamin mutumen danake so.

Na yarda yabada ni sadaka indai ga wanda nake sone,

Amma idan dai wannan ne to kubar wahalarda kanku,

Dan wlh bazan Aure shiba".


Lubabatu tace yanzu fa iza abin Arziki zaizama na tsiya?


Shi Raben aiyasan da zuhran yace Keyakeso a aura, dande kawai yanemamaki gata,

Amma shine zaki watsa mashi kasa a ido?


Tobari kiji idan har baki yarda anyi abinnanba nidakaina zansa Rabe yabada ke sadakar ga kowama, 

Dan baza mu saka maki ido ba kiyi tazama babu aure ba din haka sai ki zaba",.


Fa iza tace umma kenan ai yanzu kai yawaye,

Ambar irin wannan auren kowa son zuciyarshi yake aure,

Kuma shi baban dayayi tallata gashi wancan  yanada tabba cin  zai soni?


Ai kokusa bazai soniba tunda bashi yaganni yace yana sonaba,

Tallata akayimashi,

Donme zan yarda ku auramin mutumen da baya sona?


Lubabatu tayi tsuru tana kallon fa iza

Lallai wannan shine taleko ta koma,

Dama tasan za ayi haka.

Saidai hakan bawai suna nufin zasu kyaletaba .

Tunda ta amso maganin hana gardama zata bankawa ja'ira cikin abinci,

Saita Aureshi kotana so kobata so".


Fa iza tayi shigewarta daki tabar lubabatu atsaye, da jimamin taleko ta koman datake shirin yimasu,


Lubabatu tayi kwafa,

Takwashi yan tarkacen turarenta da kwallinta tanufi daki.


Rabe yadawo daga aiki ya tambayi lubabatu ko an amso taimakon?


Lubabatu tace aina gayamaka bakaji ba abindatace wai ita idanba mutumennana to saidai ta mutu babu Aure,

Kuma idan har mun kwadaitu da abin hannunsa to mubashi waccan yarinyar,

Itace daidai da ayi sadaka da ita,

Amma ba itaba,


Daga karshe ma saicewa tayi idan gata zaja mata to kanemomata wanda take so,

Tayarda kabada kyautarta ga wanda take so".


Rabe yayi shiru yana tunanin abinda fa izar take shirin yimashi,

Ya dubi lubabatu yace yanzun tana ina?


Tace tana daki".


Yace kira min ita".


Faiza tazo, "baba gani".


Yace dama lubabatu ce tafadamin abinda kikace shine nakiraki dan ki maimaitamin Abinda kika fada".


Babu kunya babu tsoro faiza ta rattabo mashi abinda tafadawa lubabatu,


Ya dubeta yace abinda nake so dake faiza ki natsu ki gane mekikeyi,


Ayanzu dace tasamu, kiyi amfani da damarki, karki bari ta kubce maki,


Inaso ki duba abu guda daya,

Idan bazaki auri mutuminnan dan kankiba,

To kitaimaka ki aure si sabodani,

Don kinuna min biyayya irin ta yaya da iyaye,

Ina rokonki ki Aureshi, saboda ni tunda ke baki sanshi.


Kuma da kike cewa ga zuhra nan ainasan da ita nazabeki,

Saboda ko so  sone ai sonkai yafi.


Don haka kije kiyi tunani. 

Dankarkijekiyi wa kanki katan katan (mutuwar gabab almuru)nan baki ciba can kuma sungama rabo,


Tashi kije inafatan idanna kiraki zaki bani goyon baya?


Fa iza tace gaskiya baba nayi nisa ason mutumin nan,

Kuma kaigashi kazo dawani Al amari,

Gaskiya baba abar zancannan kawai".


Rabe yace kedai lije kiyi shawara.


Tace to tafice daga cikin dakin.







Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣8⃣




Na 

Maman sadeeq





"Lubabatu tace nifa inaganin yarinyarnan kamar bazata yardaba,

Kadatayi mana bakin ciki?


Rabe yayi shiru ya na neman mafita.


Zuwa can ya dubi lubabatu yace,

Kinsan yadda za ayi?


Inaga bazan yarda inrasa wannan damarba,

Idan fa iza taki  yin amfani da taimakon da kika amso saikiba zuhra,

Inyaso sai abin ya koma kanta,

Gudun kar muyi biyu babu,

Koya kikagani?


Lubabatu tace kwarai kuwa hakan yayi,

To amma tayaya zai ganta kasan bata kula kowa?


Yace karki damu kibani hotonta inkai mashi,

Idan yagani zance yakare,

Saidai zan so inkai mashi hoton guda biyu,

Na fa iza dana zuhran,

Kinga idan faizar batayimashiba wata kila zihran tayi mashi,

Abu yazo da sauki kenan

Idan kuma dai faizar yakeso sai acigaba da shirye shirye batare da tasaniba"0


Lubabatu tace kwarai arzikindai baibar gidam muba".


Rabe yace dauko min hotunanta inzabi wanda zai kayatar dashi".


Lubabatu ta daukomashi hotunan fa iza yazabi kala biyu,

Wadan da yake ganin zasuja ra ayin  oganshi,

Yace kinada hoton zuhra awurinki?


Tace wa?

Maizai hadani da hotonta?

Baridai inkiramaka ita idan tana dashi sai tabaka".


Tafita ta kira zuhran suka shigo tare".


Rabe yadubeta yace ke kinada hoto?


Tambayar tazomata abaibai,

Bata fahimci abinda yaje nufiba,

Tayi shiru takasa cewa komai,


Luabatu tace daukomashi hotunanki zai dauki guda".


Zuhra tadauko hoto guda biyu duk da bawasu kayane  masu kyau ajikintaba tayi kyau.


Tamika mashi ya karba yace".


To jeki abinki".


Tajuya tafita batako kawo komi arantaba.


Rabe yadubi hoton yace fatana dai acikinsu Yazabi daya,


Lubabatu tace bani na zuhran ingani".


 Ta duba hoton tace babu yqdda za ayi yaga hotunan fa iza yadau na zuhra.

  Dubifa yanda tasako hijabi kamar maitakaba,

Itako fa iza dubi har sharp da hips dinta sun fito".


Rabe yace Allah yakaimu goben harna kosa gari yawaye,

Allah dai yasa karya watsamin kasa a ido, yace babu Wacce tamashi,


Lubabatu tace kaidai kayi ta addu a nima kuma zantayaka, insha Allah hu saimu dace,


Rabe yace Allah yasa.


Ai idan nasamu yadda nakeso, har gida sai na sake, ko har Aur.....


"Dakata!" lubabatu ta katseshi,

Kasan Allah idan ban lalata shirin namba kace shegiyace ni,

Taya ya aga bana zaka runka kawomani zan can banza?


Yayi sauri yace yi hakuri lubabatu SUBUL DA BAKA ne,

Yaushe zan duba wata mace alhalin gaki?

Ai babu wata mace agabana saike,

Saki ranki,

Danyimin murmushi,


Lubabatu  ta dada tamke fuska,

Da wasa da gambaranci haryashawo kanta.



Washe gari  yayi sammako  fita daga gida, 

Tafe yake yana karanta yaladifu,

Har ya isa ofis yafara aiki,

Yayi tsawon awa biyu sannan yanufi ofis din lamido Yashiga da sallamar shi".


Lamido ya amsa ya zauna suka gaisa,

Ya zaro hotuna ya ajiye agaban lamido,

Tare dafadin gasunan kazabi wacce tayi maka".


Lamido yace wai Rabe dagaske kake?


Rabe yace duba kaga wadda tayimaka ranka shi dade".


Lamido yasa hannu ya dauki hotunan. 

Kamar amafarki lwayar idon shi ta sauka akan hotonta,

Ya mike tsaye sai kuma yakoma ya zauna,

Sai yanzu ya kare mata kallo.


Ashe baiga komaiba akyawunta,

Gabansji yacigaba da harbawa da sauri da sauri.


Rabe yace ka duba dayan kagani, naga kayiwa hoton zuru tun daxu".


Lamido ya ajiye hoton zuhra, 

Ya dubi hoton fa iza,

Itama ya shaidata, itace suka hadu a store, 

Baikarasaba kallon na fa izar  ba ya ajiye, 

Yadauki na zuhran  yayimasa kuri da idanu,

Hardai rabe yalura hankalinshi yafi karkata akan zuhra.


Acikin ranshi yace wahadas,

Da faizar ba sotakeba,

Allah yasa  zuhrace zabinshi,


Lamido ya kira sunanshi,

Rabe yayi saurin juyowa yace ranka shi dade, incedai kasamu wacce ta kwantamaka?


Lamido yace dukkansu yayankane?


Rabe yayi sauri yace "eh ranka shi dade".


Lamido ya Jinjina kai yace to wacce zaka bani daga ciki?


Rabe yace ai ranka shidade shiyasa na kawo maka hotunansu,

Duk wacce ka zaba ita zambaka,


Lamido yace wacce kake ganin zamu dace da ita?


Rabe yace inaga kazabi wannan,

Yanuna hoton fa iza,

Lamido yace nida nafi ganinta ga wannan".

Yanuna hoton zuhra,

Rabe yace ai duk dayane agurina".


Lamido yayi shiru yana tunanin ikin Allah,

Lallai tsarki ya tabbata  ga ubangijin daya halicci  rai da abinda rai ke bukata.


Yasha wahala gurinneman wannan baiwar Allah.

Amma Allah baisa ya gantaba,

Sai gashi dan hikimar ubangiji an iskeshi da ita har ofis.

Lallai godiya ga ubangiji marar adadi.


Ya dubi Rabe yace,

Rabe bantaba ganin mutum mai tsananin rabo irinaba".


Rabe yayi maza yace hakane........hakane ranka shidade,


Lamido yace kaga wannan yarinyar  to wlh itace aka jarrabeni da sonta,

Har kawo ranar da ka iskeni dazancen yayanka,


Harga Allah bandauki maganarka serious ba  saigashi ashe maganin matsalata ya na gidanka,



Rabe yaji dadi yakamashi, 

Dominko zai wasa wukarshi tundama haryazo hannu,

Ashe zuhrace yaketa haukan so?.


Rabe ya muskuta yace babu damuwa ranka shi dade ai kowani katuro, indai abin nawane to zan badashi bare kuma kai keso?


Karka damu,

Saidai wani hanzari ba guduba yarinyar nan marainiyace batada kowa sai Allah sai ni uwarta tamutu kaga ko abin atausaya ce,


Lamido yace karka damu daga yau duk wata hidima tata tadawo kaina,

Tunda kabani ita,

Inafatan kuma baza aja lokaciba?


Rabe yace duk yanda kace ranka shidade".


Lamido yace to shi kenan 

Zan iya zuwa mu gana?


Rabe yace sosaima kuwa".


Lamido yace to nagode baba Rabe bari inbaka dan wani abu ko?


Rabe yace babu damuwa"


Dubu dari biyar yadirewa Rabe tabbas kudin sumbashi tsoro suka rabu akan zaizo dadare.


Rabe yakoma ofis cikin rawar jiki saboda kyautar da akayimashi,


Yakosa atashi donyaje yafadawa lubabatu dunbin arxikin dazasu raraka🙊🙊🤣🤣





Karfe shida ya isa gida 

Lubabatu tatareshi da sauri  tace,

Rabe yakuka kare dan nazaku kazo inji kanun labarai?


Rabe yayi murmushi yace kwantar da hankalinki lubabatu,

Bana sai munje ziyarar ma aikin Allah Arziki ya waiwayomu".


Lubabatu tarike hanci tarangada guda mai tsayi da kara,


Rabe yace muje ki hadamin ruwan wanka sannan muzauna kiji yanda akayi",.


Dasauri suka shiga yayi wanka yaci abinci,

Ya dubi lubabatu yace Arziki yazo zamuyi abinda bamuyiba ada".


Lubabatu tace niyanzu nafison kafadamin wayazaba acikinsu?


Rabe yace ai ita fa izar dama tace bata so ko?

To sai akayi sa a shima baizabetaba,zuhra  yakeso kinga saita hutar da kanta,

Taje can tayi jiran tsinannen saurayin datake so".


Lubabatu tace baizabetaba kenan?


Rabe yace toko yazabeta aikin banzane tunda ita bata so,

Kinga ita zuhran Allah yabata,

Nidai burina insamu togashi ko har na soma samu.

Kinga nan dubu dari biyarne ya bani saboda kawai yaji dadi,

Nan  danwani abune akabani nangaba saidai kyautar miliyoyi tunda aka fara sharar gafe da dubu dari biyar".


Lubabatu tace dari biyar?


Yace eh kingansu nan".


Tace to waro min nawa".


Yayi sauri yatamke fuska yace babu nski anan ciki,

Saidai ko gaba idan yasake badawa".


Lubabatu tace wlh baka isaba saikabani,

Waikodan baka tona zuciyataba kaga bakin cikin da nake cikiba saboda rashin zaben fa izar da beyiba?


Wlh da duk abinda yabada saika direminsu  sai abinda nabaka amma yanzu tunda ka cusaasa waccan saidai muraba abinda yabada".


Rabe yace me ?

Wl baki isaba tayaya zamu raba abinda yabani?


Yadauko dubu dari ya wurgomata yace 

Gashi  nan idan kinaso inkuma bakiso bani kayana".


Lubabatu tadauki kudin tace airaba mugu da makami ibadane".


Ta fito ta nufi da kin fa iza.


Tadubi fa iza tace wlh kinyi asara".


Fa iza hakan yana nufin baki da rabo aduniya".


Fa iza tayi sauri tace A'a umma kadakiyi min mugun baki mana ,

Meyafaru harkike janyo min wannan bala in?


Cikin fusata lubabatu tace mema bai faruba,

Inbanda rashin rabo tayaya mutum kamar ogan Rabe zakice baki sanshi?


Togashi  nan yazabi waccan yar tubabbiyar .

Gakuma tukwici naira dubu dari biyar yaba Rabe,

Wai yanzuma kenan inaga tafiya ta mika,


Fa iza tace Alhamdllh tunda har yazabi waccan yayiwa kanshi farar dabara,

Dan dayazabeni dayakama tashar iska,

Danba zantaba karbarshi amatsayin mijiba.


Lubabatu tace wato ke babu abindama yadameki ko?


Fa iza tace yo maizai dameni.

Wlh ko akan farcena dama ai abinda kukeso kenan,

Yayi ta anko maku dukiya kuma gashi kun samu.


Lubabatu tace nangaba saikinyi nadamar kin karbar aurennan da kikayi,

Idan kikaga  yadda yarinyar can tazama lokacin kuma aki da tudun dafawa,

Kikuma rike  aranki  koni bazan tausaya makiba bare har intayaki damuwa".


Fa iza ta mike tsaye tadafa kafadar lubabatu  tace  kiyi hkr umma indai wannanne  wanda nake so yayagawa wanda yarinyarcan zata Aura don haka kwantar da hankalinki".


Lubabatu tace ,

Wato har yanzu baki rusunaba?

To shi kenan daga yau nikam nabar yimaki maganarnan,

Kije kiyi ta jiran saurayinki".


Tajuyo tafito daga dakin,

Fa iza tayi murmushi tayi kwanciyarta.


Washe gari Rabe yakira zuhra 

Tazo ta duka ta gaidashi,

Yadauko hotunanta yabata,

Harta mike yace dawo zauna magana zamuyi".


Gabanta yafadi ras!

Tazauna ta dukar da kanta don ta saurareshi,

Yakira sunanta,

Abinda ko baitaba bayi saidai yace ke!"


Tadago ta dubeshi jin yace zuhra, kinsan abindayasa nace kizo?


Tace A'a".


Yace to dama hotonki dana amsa wani ogana ne  nayiwa tallarku ke da fa iza ,

sai akayi sa a yace ke yake so don haka  atake  na bashi ke .

Dan haja zaixo koyau ko gobe ku zanta.


Tsananin kidimewar datayine yasa takara durkushewa agabanshi tace,


Baba wlh ina da ranar Abbas akaina yaya za ayi dashi?


cikin fusata yace ba Abbas ba ko mande  ne bazan basaba,

bare Abbas.

Ayanzu nike iko dake,

Kuma nazartas da hukunci akanki,

Na bada Aurenki ga ogana,

Bakuma wani lokaci zanjaba ,

dan haka tashi ki bani guri,


Cikin tsananin tashin hankali  tabaro dakin nasa ta nufi kicin,


Kuka takeyi iya kar finta,

Saida tayi mai isarta har tagodewa maiduka(Allah)

sannan tasamu damar  yin tunani".



Sai yanzu tagano illar rashin iyaye,


da ace tana da gata da ba ayimata hakaba.


Ita dake dasaranar wani akanta amma  wai har akayi tallarta gawani wanda bazai taba dubanta da mutumciba,


Tasake fashewa da wani kukan tare da dora hannu bisa kai tana fadin wayyo nashiga ukku ya zanyi da sa Auren Abbas akaina !


Yazanyi da soyayyar sa?





Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪 WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

3⃣9⃣




Na

Maman sadeeq







"Zuwaira tayi sallama ,

Faiza tafito daga daki,


Zuwaira tace nazo inji daga inda aka kwana?


Fa iza tace wlh zuwaira  jinake kamar immutu saboda rashin man dinnan,


Zuwaira tace kinkira matar tashi?


A'a bankirataba,


Zuwaira tace to kikirata kice gakinan zuwa gidan bakin san gidamba?


Fa iza ta ce wlh ban sanba gidan".


Zuwairatace kikirata kice mata zakizo sai ta kwatantamaki".


Fa iza tace habadai aisaita zargi wani abu,

Nina fi son naga no gidan dakaina saidai taganni kwatsam ,


Zuwaira tace kin san ma me za ayi yanzu ?


Zuwaira tace saikin fada".


Kitashi yanzu mutafi sahad tunda yau baranar aiki bane kila musameshi".


Fa iza tasa hijabi suka nufi sahad,


Cikin sa a kuwa yana siga suna zuwa,


Suka dubi juna itada xuwaira suka tafa,

Zuwaira taceenafada maki?


Suka shiga cikin store din,


Shima yacigaba da zaar abinda yakawoshi,


Saidai yau shikadaine babu yara,

Kuma kaya yake ta jida dangin sutura sabanin kayan kwalam dayasaba saye,


Zuwqira tace yaukuma sutura yake tasiya wa matanshi idan kina darabo watarana har dake za asiya".


Fa iza tace bari kedai zuwaira harna fara kishin matanshi,

Amma babu komai  lokaci na zuwa".


Akwatuna ya cika har goma shabiyu,


Abin yabasu mamaki matuka

Zuwaira tace".


Kardai lefene yahada?


Don wannan sunfi karfin kyautar mata da miji".


Fa iza tace haba zuwaira yoshe zaki ruka gayya tomin wannan bala in?

   Ni inanan zaune ina jiranshi, shikuma yanacan yana hangen wata?


Zuwaira tace to nikam saina tambayeshi,


Fa iza tace A'a karkije nina fi bukatar ingano gidanshi ayanzu,


Zuwaira tace ti muje mugaisa dashi kinga tanan sai mugane indayasa gaba",


Suka isa kusa dashi,

Cikin salo da gwangwalaso, fa iza  tace wannan kamar baban baby?


Ya juyo ya dubeta saiyayi kamar ya shareta,

Sai yatuna ai yar iwar matarda yake so ce,

Tunda alokacin da Rabe yakawo mashi hotunan harda hotonta aciki,

Din haka yasaki fuska suka gaisa,

Tace yau kuma ina kabaro baby?


Yace baby tana gida",.


Kamar ya tambayeta yar uwarta yaji ayatake ?

Sai kuma yayi shiru,


Zuwaira tace yallabai anata hidimane ko?


Yayi murmushi yace wlh kuwa".


Zuwaira tace to Allah yasa Alheri,


Yace Amin".


Azatonshi sun san komai itako fa iza sandarewa tayi atsaye jin ya amsa fatan Alheri da zuwairq tamashi,


Fa iza ta daure tace ,

"baban baby sai angoncewa?


Yayi mur mushi yace haka nefa.


Shikenan tafaru ta kare abinda fa iza tafada azuciyarta,

Ta kamo hannun zuwaira suka yimashi fatan Alheri,

Yadauko kudi har dubu goma  yabasu amatsayinsu na yan uwan Amaryarshi".


Fa iza tayi godiya shi kuma yace agaida mutan gida,


Abinda yabata mamaki koya kamune?

Inya kamu aibazaiyyi aure yabartaba.


Suka fito daga store din suka koma nesa da store din don kar yazo ya fahimci wani abu,


Zuwaira tace,

Tosaiki hutarda kanki dadakon wahalar dakikeyi, kinji dai da kunnenki".


Fa iza tayi shiru ,zuwa can tace ,

Yanzu abinda man dinnan zaimani kenan?

Ni ina hangenshi shi yana hangen wata?

Yanzu zuwaira yakike ganin za ayi?


Yafa za ayi banda kirungumi hkr?

Cewar zuwaira"


Fa iza tace wlh bazan yiba saina Aureshi".


Zuwaira tace tayaya zaki aurwshi?

Kuma cikin mata ukku zaki zauna?


Fa iza tace wlh ko acikin kwar kwarori saiyasakani,


Amma kowacece zai Aura tayimin yankan baya,

Kodayake bayanta ta yanka,

Zandau fansar abinda tayimin".


Kinganshi can yafito mubishi .

Cewar zuwaira,


Fa iza ta dago kai taga anata saka mashi akwatuna  dayayi siyayya acikin mota tace ,

"anyako zuwaira ma bishi?


Tace yo mai zai hana?

Mubishi tahakane zaki aiwatar da shirinki cikin sauki,idan mukaga gidansa mudawo akwai shawarar dazambaki".


Suka tsaida adaidaita  sahu suka nuna mashi motar dazaibi abaya suka bishi abaya ,

Har ya iso gidanshi dake court road,

Sukaga gidan daya shiga.


Zuwaira tace to munga gida sai mundawo,


Suka juya gida zuwaira ta dubi fa iza  tace 

Akwai kudi agurinki?


Tace  A'a  bani da kudi".


Zuwaira tace to kinga abinda zaisa kinaji kina gani kirasa man dinnan,


Fa iza tace karki damu ainaga inda baba yake ajiya,


Zuwaira tace to gobe zanzo in kaiki inda za ayimaki aiki,

Ki kaddara gakinan agidan mutuminnan ko".


Fa iza tace  to shikenan zuwaira Allah yakaimu gobe zanjiraki,



Sukayi bankwana aka  sauke zuwaira A unguwarsu aka wuce da fa iza  jiki asanyaye tashiga gida.



Dakin lubabatu tashiga,

Kai tsaye ta dubeta tawatsar.


Fa iza tace umma dan Allah ina tai makonnan dakika amsomin?


Lubabatu tace ai tunda kikace baki so na kwashesu na bawa zuhra,

Ya akayine kike nemansu?


Fa iza tace wlh umma ranace take son baci agareni wai mutumen danake sone  zaiyi aure .

Shine kafin abin yayi nisa zan amshi taimakon dakika bani injaraba",


Lubabatu ta kwashe da dariya tace Allah nagodemaka,

gara haka,

Wlh naji dadi ai namijin kenan".


Ke yanzunan taimako zandauko inbaki saboda bukatarki ce ta karan kanki,?


To kinyi kuskure,

Ko kudi kika bani bazan amso makiba,


Kin manta abinda kika cemin?


Bari in tuna maki,idan har kin mance,

Cewa kikayi,

Imbar wahalar da kaina kan amso maki taimako,

Saboda baza ki auri kowaba sai wanda kike so".


Kinga saiki dauki darasi a yau ,

Kinacan kina hauka akanshi shiyana can yana san wata,

Kinga kinyi biyu babu,

Bakiga tsuntsu bakiga tarko.


Gawaccan yarinyarnan  zata shige gidan arziki gidan daula, gidan hutu keko kinanan 

Bakinciki zai  yimaki jagora zuwa lahira, don haka tashi kibani guri ko zaki mutu babu abinda zammaki".


Fa iza ta soma kula tanabama lubabatu hkr akan tatausayamata, tace,

Ko daya bazan tausaya makiba, sabida nima baki tausaya minba,

Tunda ko na kyaleki nima kikyaleni,bahakaba saina nausar maki baki,

Tashi ma kibarmin dakina marar mutumci kawai".


Fa iza ta bari dakin lubabatu .

Saiyanzu tagano rashin kyautawar datayi wa uwarta ta


Tabas ko babu dadi ,baikamata tasagemata gwiwaba,

Gashi tayi fushi bare tasa ran zata taimaka mata,

Kodayake ai zuwaira nanan ,

Kudi yakamata tasamo zuwa goben".


Tashi tayi tanufi dakin Rabe cikin sa a  dayake taga sabon ma ajin dayake ajiye kudi,


Kudi tagani cun us  dami-dami tadauko guda biyu na yan dubu dubu tadawo daki ta boye kudin.



Tun jiya da lamido yahada kan matanshi  yafadama masu zancen Aurenda zai kara,

Hankalin hajir yakasa kwanciya ,

Kwana tayi tana kuka har zuwa waye war gari 

Takasa zaune takasa tsaye 

Itada take son ta fidda tacikin gidan kuma yanzu azomasu da zancan kara aure tabdi jam!

Dole tasan abinda zatayi don taga tahana yiwuwar auren,."


Ita kuwa jawaheer hankalinta baitashiba sosai itadai fatanta Allah yakawo wacce zasu zauna lfy da ita,




Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

4⃣0⃣







Na

Maman sadeeq





"Tadauki wayarta takira lambar laila sanata,

Ta dade tana kara saizuwa can ta dauka tareda fadin yaya sunsheka  lahirane?


Hajir tace ke bata yayanta nakeba, 

Yanzu gaggarumar  matsalace ta kunno kai.


Hodama tunda na amsota na ajiyeta kafin insamu damar hurawa yaran.


Sai dai kuma yanzu sawun giwa yabayyana wanda yatake na rakumi".


Laila idan kika zo gidanmu ayanzu abin saiya baki mamaki ma tuka,

Dominkau gyara maigidan  yake tayi komai sabo yake canzawa saboda Amaryarshi".


Laila tace amarya kuma?


Tace kindaiji abin kamar amafarki,


Laila tace 

Tobari kiji idan harkika bar amaryarnan tashigo saikinfi kowa kokawa,

Don kuwa ke za ayowa ita,

Saboda haka tun wuri bai kuremakiba kilalubo mafita,

Idan ko kin musa to sa ido ki kallo".


Hajir ta tace ina ko zan musa tunda nasan nixa ayoma kishiyarnan?

Kedai bari inzo ki rakani gurin bamaguje".


Laila tace to dadai yafi".


Minti talatin hajir ta isa gidan laila sanata,

Basu tsaya jiran komaiba suka dauki hanyar kauyen da bamaguje yake,

Sunyi sa a babu layi mata ukkune kadai suka iske.


Bamaguje   ya dubi hajir cikin gurbatacciyar hausarshi yace ya kikaga aikin?


Ina fatan dai baki samu matsalaba?


Tace wata matsalar ce tataso wacce ta doke waccan,


Ina so kabani magani wanda zai gisar da jankalin mijina akan  matar da zai aura,


Inaso yamanta da shafin rayuwarta gabadaya,


Yace angama,


Yadauko wani magani yabata yace".


Kisamu zuciyar zakara idan ta bushe ki dakata,

Ki hada dawannan maganin, kixuba mashi A 'a binci idan yaci  saidai wata macen".


Takarbi maganin ta cusa ajaka,


Laila tace menene abinda za abada?


Yace tabada dubu goma".


Tazaro kudin tabashi, suka kamo hanya,


Hajir ta dubi laila tace".


Ni a ina zansamo zuciyar zakara a yanzu?


Laila tace bani maganin in hadomaki nibazatamin wahalaba,

Idan nahada zuwa jibi sai in aikomaki".


Dahaka suka isa gidan laila sanata ta ajiyeta ita ka ta komo gida,


Tana shigowa gidan tayi arba da ajwatuna guda goma sha biyu afalo,

Batabi takansuba tayi shigewarta daki,

Bata fitona falon saida tayi sallar magriba.


Tana zaune yashigo yazauna,

Jawaheer ma tazo ta zauna.


Yadubesu yace ga kayan ku nan,

Ko wacce akwati shida da dubu dari biyu acikin kayan, 

Idan kuma da akwai mai wata matsalar to yafada".


Jawaheer tace aiko mungode kwarai.

Allah yatabbatar da Alkairi.

        Bacin kishiyace aida sai ince gobema adada".


Hajir ta auna mata harara tasandai da ita take".


Lamido yayi maza ya amsa da Amin,


Ya juya ga hajir donjin tata godiyar da du a in saidai batasu takeba hankalintanakan takaici,


Bawai batajiba A'a tsabar dagawace kawai


Yakira sunanta tawaigo tana kallonshi,

Yamaimaitamata abinda yafada tace Au hardani aciki?

To angode,



Kwana biyu tsakani laila sanata tadiro gidan da hadaddan maganinta,

  hajir tatareta da murna suka zauna,


Laila ta shiga duba yadda gidan keta annuri, ta dubi hajir tace,


Ashe haka gidan ya gyaru kamar fadar shugaban kasa?


Hajir tace kedai kyagani, laila abu kamar wahayi?


Lailavtace eh yagamu da zafafan mata,

Lallai kam abin nayine, 

Sai ataka ahankali, wata kila masu wurine sukazo".


Hajir tace candai bari yomin wannan Alkaba in,

Niyanzu bani hasashina dama yau nice da gadon.


Laila ta dauko maganin tabata, ta amsa tace,

Tundaga yau zan soma aika mashi da sinadarin bamaguje".


Laila tace ni har nakosa inga matar da ta dauki hankalin lamido dannasandai kyawu ba amagana".


Hajir tai tsaki tace gaskiya ni nagaji da jin zantujanki,

Wai kodama kinyi niyyar cin mutuncinane?


Laila tace ko daya girman amaryardai nake jinjinawa,

Ganin yanda Anti naira ke kokawa,

Dolene aso ganin amaryar da wuri, 

Ganin yanda gogan yakidime sai gyaran gida yakeyi".


Hajir tace nima abin yabani tsoro, 

Idannaga yadda yazage yana aiki, babu wacce yayiwa irin haka lokacin da zai auremu sai ita yar gwal".



Laila tace  to sai ki zage kema dondagani bayan gangami da labari".


Hajir tace kedai bari in jarraba wannan ingani,

Idanna samu yanda nake so to hanya ta bude tayanda zan mike kafa".


Laila tamike tsaye tace to indai kinyi sake to kyaga sakiya,

Nizan koma gida sai munyi waya".


Hajir tace to godiya dai uwar dakina komekenan zakiji,


Sukayi sallama.







Akwatuna oma shabiyu akakawo kaya na isa da kasaita,


Gakuma sadaki naira dubu dari biyar 

Da sabuwar mota kirar matrid, duk na amaryane.


Maza suka kawo,

Dan haka Rabe shida sani suka karba sukayi godiya,


Mutanen da suka kawo lefen suka mike da nufin tafiya,

Sani ya kirgo naira dubu ashirin yabasu,

Sukayi godiya suka tafi


Rabe yace kai yarinyar nan Allah yadubi lamarinta,

Dubi inda Allah yakaita,

Lalkai arziki kashi akafa ake takoshi",


Sani yace hakane yanzu waromin kudina danaba mutanencan".


Rabe yace haba sani yanzu dankabada dubu ashirin sai na baka?


Sani yace ih saikabani duk kudin da kake amsa wakataba bawa ko sisi?

Don haka bani kudina".


Rabe yace to dama haushi kakeji don ina amsar kudi banbakaba?

To bazan bakaba, 

Kuma wannan dakabada suma bazan bakaba,

Ai baka kawo taka gudun mawarba".


Sani yace wlh baka isaba indai baka bani wani abuba cikin arxikin yarinyarnamba to baza ka amshi nawaba".


Rabe yace wlh baxan bakaba komaiba,

Ai bance kaasuba,

Bajintarkace tasakaka ka basu,

Mutanen dasuka fito gida irin wannan meye nabasu kudi".


Rigima sosai tsakanin rabe da sani,

Daga karshe  dai Rabe ya  dauko kudin cikin zafin zuciya yawatsawa sani 


Haka suka rabu baram baram ya kwashe kayan yashiga cikin gida dasu.






Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

4⃣1⃣








Na 

Maman sadeeq



"Lubabatu tayi sagale da baki ganin lodin kayan,

Rabe yanunamata key  din motar yace,

"harda mota kinganta".


Takarbi key din tace,


Wannan motar sai kabani ita tunda kai kana da ita".


Rabe yace bakida hankali lubabatu,

Tayaya zambaki mota kamar matrix?


Kibarma zanvennan kawai,

Kiduba kaya kiga abinda aka narkowa zuhra".


Tabude kayan tagani,

Kayane irinnamasu akwai,

Tagama gani ta rufe,


Wani bakinciki yasoki zuciyarta da yanzu  duk wannan daular na fa iza ne da ita.


Kodai zatasake lallabar fa izarne ko zata yarda?


Sai kuma taja tsaki".


Zuwaira ce tayi sallama, 

Tashigo suka gaisa da lubabatu ta gaida Rabe,

Yayi kamar bejitaba,

Saida yace ana gaidaka".


Sannan ya amsa,

Tatashi tashiga dakin fa iza,


Zuwaira tace lefen waye nagani acan?


Fa iza tatabe baki tace, 

Na zuhra  ne".


Zuwaira tace  lallai yarinyar nan zata Auri done"

Wannan dukiyaa haka?


Fa iza tayi tsaki  tace, 

Don Allah  ni tashi muje kenake ta kira tun dazu".


Suka fito syka dauki hanyar gidan malamin".


Ka buga, zuwaira takai faiza, gidan malamin tsubbu,


Fa iza ta rattaba masa bukatarta,


Tana so ahaukatarda matarda lamido zai Aura.


Malam yabata laya yace  tasa amasai idan har matar tahau masan angama,


Fa iza tace to malam idanna karbi laya aiban san inda matar takeba

Idan da hali atura jinnu kawai su juyar mata da kwakwalwa,,

Tunda ni asalima bansantaba.


Malam yace idanko jakane aiki bazaiyuwuba, 

Kibari saikingano inda  take  dan wannan layarce kadai zataimaki abinda kika bukata".


Zuwaira tace A'a malam  abamu layar".


Fa iza tace idan mun amshi layar yazamuyi da ita zuwaira?


Zuwaira tace malam Abamu nawane abin sadaka?


Malam yace dubu ashirinne".


Ziwaira tace faiza bashi mutafi,


Jiki asanyaye fa iza ta bada kidin,


Zuwaira tace to malam agayamana yanda zamuyi da layar".



Malam yace wannan  babbar kujefa amasai,

Karamar kuwa kusamu wani guri inda ake hura wuta kullum lamar kicin, ko inda ake gasa nama tukuba, saiku binne akar kashi,



Zuwaira tace to mungode, 

Allah yasa adace".


Sika fito daga gidan malamin,


Fa iza tace meye hujjarki na amsar wannan layar alhalin bamusan  kowaceceba?


Zuwaira tayi murmushi tace ke haryanzu da sauranki,

Gaki afuska kamar wata me wayau amma wata irice ke,


Inace munsan gidan mutumennan ashe sanin wacce zai Aura bazaimana wahalaba


Kuma ko ba komai zai buga  invitation kinga dole abu zaizo dasauki,


Ma kin wani tsuke fusa ke kinji haushi donnace abada layar?


Fa iza tace A'a aiba haka bane,

Gani naidai bamusan kowacece ba to yaushe zamu amshi layar?".


Zuwaira tace waikinsan kowa yarinyarnan ta gidanku zata Aura?


Fa iza tace bansan shiba amma bana yace oganshine".


Zuwaira tace tonikam ina zargin wani abu kiyi kokari kisanshi".


Fa iza tayi shiru tace yoko mubiya ta ofis din su baban yanzu?

Zuwaira tace muje".


Sukata fi a adaidaita sahu sai sharada verse3,

Inda kamfanin lamido yake,


Suka shiga kai tsaye. 

Ofis din Rabe suka nufa.

Rabe yagansu yace, 

Daga ina kuma faiza?


Tayi shiru batace komaiba,


Zuwaira tayi sauri tace 

Dama munzo karbar kudin yan hidimomin yammatane,

Ganin aryanzu angon baice komaiba,


Rabe yayi murmushi yace to karkudamu kukoma gida zan karbo maku".


Xuwaira tace idan da hali dai angin mukeson gani,

Dan akwai abubuwanda zamu tattauna dashi,

Gashi biki saura sati daya amma har yanzu ba atsara komaiba".


Rabe ya ce eh kinyi gaskiya, kutaso inkaiku gurinshi sai kuyi maganar,


Suka tashi suka bi bayanshi,


Yana zaune yanata rubutu,

Rabe yasanardashi zuwan yayyen amarya yace su shigo".


Rabe yakoma yasanar dasu su shigo,


Zuwaira tashiga gaba, 

Itakam fa iza gabantane ya tsananta bugawa,

Tadai daure ta cusa kanta Acikin ofis din,

Gabant taji ya  fadi  sakamakon arbada tayi da fuskar data fi bukatar  gani arayuwarta lamido!


Cikin fara a yayi masu sannu da zuwa, 

Zuwairace ta amsa,


Fa iza kam har yanzu batadawo  daga hayyacintaba,

Suka gaisa cikin mutumci,


Faiza tace yallabai  munzo karbar kudin hidimomin  yammata munji shiru,".


Yace kai dan Allah kuyi hkr ,

Nima naso inzo muyi magana da amaryar saidai bansamu damaba amma tunda gaku  kubani lambarta,


Fa iza  tayi saurin karanto lambarta tabashi,

Saboda tasan zuhra batada waya,


Yakawo kudi har dubu dari biyu yabasu,

Sukayi godiya,

Sannan suka baro afis din nasa,

Basubi takan Rabe ba".


Faiza ta dubi zuwaira tace,

Narantse da Allah zuwaira saina auri man dinnan  koda zanyi yawo tsirara,


Ashe shine baba ya zabamin nace bana so?


To wlh saina aureshi,

Koda ko uwatace saimun gwada yar karfi da ita bare wata zuhra can.


Zuwaira tace tobari kiji abinyi,


Baga layu awurinkiba?


Kije ki aiwatar da aiki, 

Idan abu yayuwu sai musan abin yi,

Da haka suka rabu".


Fa iza tashiga dakin lubabatu  tazauna  tayi jugum takasacewa komai,


Lubabatu takalleta taja tsaki tace,

Fadamin abinda ywkawoki,

Kinzo kintasani  agaba saikace mayya".


Fa iza tace umma kiyafemin, nayimaku kuskure hakika duk abinda iyaye suka sa yayansu to basunufinsu da cuta agaresu,

Kuyafemin 

Umma ina maibakincikin sanar maki mutumennan dakuka zabamin naki karba kuka bashi xuhra


Lubabatu tazaro ido tace ke fa iza dagaske kike?


Tace wlh shine umma gashi yanzu lokaci yakure narasa yanda zanyi".


Lubabatu tayi shiru tana tunani zuwacan tace 


Lokaci bai kureba dama wannan damar nake tajira insamu, gashi kuma tazo".


Tadubi fa iza tace yanzu kin shirya karbar taimakona?


Fa iza tayi sauri tace wlh na shirya".


Lubabatu tayi murmushi tace hum yaro yarone,

To saidai ajwai wani sharadi guda daya idan har zaki amince zan iya taimakaki har sai kin auri mutumennan".


Zuwaira tace koma menene umma kifada zan amince".


Lubabatu tace idan har aurenku yatabbata duk abinda kikasamu zaki kasa biyu kidau daya indauki daya".


Fa iza tace karki damu indai wannanne niba kudinsaba nakeso shinakeso".


Zanyi ta tsaunomaki dukiya batare da mun rababa  burina na aureshi,


Lubabatu tace to shikenan kije kifara shiri, 


Dama ninafison lamarin akanki,


Bakin cikina daya motar can da aka kawowa yarinyar can keyafi dacewa da motar".


Fa iza tace idan har aikima yayi kyau  motarma kezan barmawa, ladar jajircewa dakikayi".


Lubabatu tayi murmushi tace ai har Rabe yafara nunamin iko akanta to saiya sauya shiri".


Fa iza ta mike ta fito ta nufi dakinta, 

Tabude jakarta ta dauko layunnan  tashiga kicin tadaga murhu ta binne layar  ta maida murhun,

Ta wuce bandaki shima tasaka daya layar  acikin  masan, bakin ta alaikum.





Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

4⃣2⃣






Na

Maman sadeeq



SADAUKARWA


Wannan shafin nasadaukar dashi ga daukacin masoyana, masoyan littafin wuka Amakoshi,


Hakika kuna birgeni matuka 

Ganin yanda kuke kulawa da  Al amurrana.


Nagode 

Nagode

Allah yabarmu tare 

Kuma yashiga tsakaninmu da makiyanmu



HAR YANZU KUNA RAINA,

Khadeeja usman talle (momy son kiru)

Badariya Adamu mlf

Sa adiya sani mlf

Xainab Abdullahi mlf

Aisha Adamu mlf

Haiwa u sanusi  mrs Abdullahi kalu


Rabi atu yunus mlf

Sa adiya muntari mlf



KAWATA TAKAINA

Zarah, mrs mutari dila,  katagum,

Kinfi kowa kaunar wannan littafin, 

Najinjinama soyayyarki gareni 

Allah yabar so da kauna💔❣💔❣












"karfe takwas na dare taji wayarta na kara,

Tadauko saitaga bakuwar lamba,

Ta matsa amsawa takai kunnenta,


Muryarshi taratsa dodon kunnenta,


Cikin salo da firirita ta amsa sallamar tasa,

Dan tagane kowaye,

Suka gaisa batare dayagane ba zuhra bace,


Yace Amarya inafatan kingane dawa kike magana?


Fa iza tace A'a banganeba,


Yace nasani nazakiganeba,

Saboda namaki laifi mai girma,

Kodayake damacan ni mailaifine,


Ga ixa tayi dan jum saboda batasan inda kalamansa sukasa gababa,

Saitayi sauri tace ai yaruga ya wuce,

Babu komai yanzu ka fadamin wanene kai?


Yace to Angonkine lamido Ahmad  tijjani kibiya".


Fa iza tace gaskiya nayi fishi tunda sai yau ka tuna dani,

Ko dayake nidin matar shigece,

Tunda cusamaka ni akayi

Laga kenan daraja bata idasu kaiwaba".


Yayi murmushi eanda tajiyo sautinsa yace,


Wa yagayamaki haka?


Faduwace tazo daidai daxama tun ranar da Abunnan yafaru kika shigemin zuciya,

Kinga ko ke ba matar shige bace,


Tace idan har hakane kazo sai in tabbatar da hakan".


Yace ina fatan hakan zaisa kiyarda dani?


Tace sosaima,


Yace to bani minti talatin"


Tace ina sairarenka,


Suka ajiye wayar atare,


Dagudu tanufi dakin lubabatu,

Tazayyanemata duk yanda sukayi da lamido,


Lubabatu tayi dariya tace da kyau yar gari,

Bari indaukomaki kayan hadin soyayya dole".


Kwalline da turare da kuma wata laya,

Lubabatu da kanta tashafa mata kwallin da turaren,

Layar kuma tace taruketa ahannu ta runka matsawa,


Tana cikin nuna mata yanda zata runka yimasa magana da fari da ido da gwalan gwaso wayar fa iza tayi kara,


Taduba saitaga lambar lamidoce, 


Tanunawa lubabatu tace kinganshinan ya iso".


Lubabatu tace to karki daga bari sai ya tsinke yasake bugowa".


Haka kuwa akayi ta tsinke yasake kira,

Sannan ta daga cikin kashe murya tace har ka iso?


Yace na iso kiran Amarya wasane?


Tace to ganinan fitowa".


Ta dubi lubabatu tace ya iso saidai ina tsoron yace  bani yake songaniba 

Zuhra yake san gani".


Lubabatu tace kada kisake kikawo shakku ajan wannan kwallin ko turaren,bare kuma uwar tafiyar  layar hannunki,


Bakiji abinda nakiraki da suba kayan hadin soyayya dole koda bayasanki darajarsu yasoki,

Fesa dan kamshinnan nabaki ki fita".


Tafito kofar gida yana zaune kan hadaddiyar motarsa,


Tunlafin takaraso yayimata kyar da ido,

Har ta iso wajansa yana kallonta,


Ta dubesa sosai takara matsowa kusa dashi tace sannu da zuwa".


Akasalance ya amsamata,


Wutar santace ke ruruwa azuciyarsa,

Tadubesa saitaga ya tsareta da idanu tace,


Dama naxo dannayimaka godiya akan hidimar dakayimana dazu,

Mungode kwarai Allah yabar so da kauna".


Yakada kai tare da lumshe ido jiyake kamar yajawota ya rungume, 


Itakau sai matsar laya takeyi tareda rausayar da jiki,


Yasake dubanta wani kayataccen kyau take masa,


Maiyasa lokacinda aka kawo masa hotunansu bai lura da hakaba?


Ko shakka babu tafi wacce yazaba komai........


Takatse masa tunani dacewa bari inshiga inkira maka ita,

Kada imbata maku lokaci,


Yace A'a aike da ita  duk dayane, tunda naganki ainaganta".


Tayi saurin cewa A'a da akwai bambanci,


Yace tonidai kar ki tafi dan ko kallonki kadai najefani cikin wata duniya mai wuyar fasaltuwa,

Bare kuma muryarki mai kama da ana busa sarewa".


Tace A'a bandafa zuga,

Ai yar uwata tafini komai".


Yace ban yardaba tserayyar dake tsakaninku kamar nisan sama da kasane, 

Kinga ko ba a hadaba".


Tace gaskiya wadannan kalaman bani yadace injisuba,

Yar uwata yadace kafadawa su dan haka sai incemaka saida safe,


Tajuya tashiga gida,

Jiyake kamar yabita cikin gidan,


Da shigarta saita  nufi kichin inda zuhra ke kwana,

Ta isketa zaune ta bude dan karamin Alqur ani tana karantawa, tace,


Ke kije waje ana kiranki".


Zuhra tace to".


Tarufe Alqur anin tasaka hijab, 

Gabanta nafaduwa tanufi kofar gida,


Yana shirin bude mota yaga ta fito,


Takalleshi shima yakalleta,

Ta isa kusa dashi tayimasa sallama saidai bai amsaba tace,


Kaine kake kirana?


Kadamata kai yayi alamar bashibane,


Tace to dan Allah kayi hkr".


Tajuya zata shiga gida yace idan kinshiga dan Allah kice yayarki tazo inasan ganinta".


Tace "to


Fa iza talabe tana kallonsu 

Ganin zuhra ta nufo soron ne yasa tayi ciki da sauri ta fada dakinta,


Zuhra tashigo tacewa fa iza kije yana san ganinki,


Fa iza tace yo har kungama gaisawar?


Zuhra tace A'a cewa yayi bani yake kiraba,


Fa iza tayi murmushi tace to ai shikenan ai,


Acikin ranta kuma tana tunanin yanda tashi daya tasato zuciyarsa atafin hannunta,

lallai komai zaizomata da sauki tunda har yakamu haka".


Tafita kofar gida,

 da sauri yataho ya iso gareta yace yazakiyimin haka?


Kodan kinga na azabtu da kene?


Tace haba dai kokamance yar uwatace zabinka?


Yace A'a nikece zabina ba yar uwarkiba,


Tace to yadda za ayi saikasamu baba da zancen donni ita nasani amatsayin wacce kakeso, 


Yace mata  to dhikenan inafatan zaki karbeni amatsayin masoyi?


Tayamutsa fiska tace to zan duba ingani".


Kudi yadauko masu yawa yabata yace sai akara hidima".


Ta amsa alalace kamar ta amshi kashi,


Sukayi bankwana tashiga cikin gida,

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

4⃣3⃣





Na

 maman sadeeq










"kai tsaye dakin lubabatu ta nufa


Tana shiga ta dorawa lubabatu kudi akan  cinya tace umma ga somin tabi kifara lasawa".


Lubabatu tace dhine yabaki wannan kudin?


Fa iza ta kwashe yadda sukayi da lamido tafadama lubabatu,


Guda mai tsanani karfi lubabatu ta rangado tace,


Allah nagodemaka,

Duniya tazama tamu,


Fa iza tace umma yanzu yaya zamuyi da eaccan yar gidan tubabbiyar?


Lubabatu tace barni da ita,

Nasan yadda zanyi  da ita,

Kedai bamuncika burinmuba nidake?


To uban kowa yarasa,


Kuma duk wani au da Rabe yayi sama da fadi dashi Yazama dole  yafitomin da kayana,

Mai wuri yazo mai tabarma saiyanade".


Fa iza tace to nidai zanje in kwanta".


Lubabatu tace to kadararmu saida safe".


Fa iza tayi murmushi ta fita".


Washe gari tunda Asuba tatashi tashiga bandaki, 


Kamar yandakika tafito agigece,


Saikuma ta kwalla kara mai tsananin karfi, tafadi kasa babu alamar  rai atareda ita,


Rabe ne yaji kararta ya fito,

Ganinta yayi akwance ta mimmike babu alamar rai  atareda ita,


Gaban Rabe yafadi,

Kardai ta mutu tayi masa taleko ta koma?


Dasauri yakamfato ruwa yakelayawa zuhra,


Yasake kamfatowa ya shekamata, saidai bata ko motsaba,


Dakin lubabatu yashiga,

Yakirata suka fito tare,


Lubabatu takamo hannu tagirgizata saidai babu alamar rai,

Tadubi rabe tace wannan yarinyar babu alamar rai atare da ita".


Yace da lubabatu kirawo fa iza kusata a mota  inkaita asibiti,


Itakau lubaatu aranta cewa take Allah yasama ta mutu  ubankowama ya huta,

Me akeyi da iyalan ododuwa,?


Takira faiza tafito ganin zuhra akwance yasa tagano shirintane ya soma aiki,


Lubabatu tace kamota musakata a mota".


Fa iza akamota suka sakata amota, 


Rabe yafigi motar aguje,


Asibitin murtala yakaita,


Hankalinsa ba akwance yakeba,


Fatansa daya kada ta mutu yayi asarar dukiyar da yakarba gurin lamido,


Saidai iya bincike likitoci sunyi amma basu gano matsalartaba,

Kuma bata farfadoba,


Daga karshe sai turasu akayi asibitin dala,

Can madai bata sauya zaniba,

Daga can kuma sai aka turasu federal medical centre dake zariya,


Washe gari shida lubabatu suka nifi zariya, 


Kwanansu biyu amma jiya iyau,


Babu dai wani cigaba da ake samu,

Kuma har zuwa yanxu bata far fadoba,


Likitan yace dasu gaskiya ciwon bana asibiti bane,

Saidai su koma gida ayimasu na gida,


Amma idan zasu iya akwai wani mutum dake nan zariya a unguwar gyallesu,idan suka kaita to insha Allahu zata samu sauki".


Daga asibitin suka nufi gyallesu,


Malamin ya dubi zuhra da ke kwance babu alamar rai atare da ita,


Zam zam roba daya yafasa,yayi addu o i acikin ruwan yabawa lubabatu yace tashafe mata jiki dashi,


Ta amsa tasoma shashafamata, saigashi ta soma motsi,,


Tashafe mata jiki da ruwan zam zam din sai gashi nfashinta yadawo,

Kuma tana motsa gababuwanta,

Daidai bata bude idontaba,


Malamin yasake yin rubutu yawanke yace ashafamata,

Akuma bude kanta ashafamata har cikin gashinta,


Lubabatu bata rai tayi alamar ta fara kosawa,


Tadai cigaba da shafamata har cikin kanta,


Cikin ikon Allah xuhra ta bude idonta,

Kallon mutane takeyi daya bayan daya,


Malamin yace mata sannu".


Ta dubeshi batace ko uffanba,


Yasake cewa inake maki ciwo?


Shima  batace komaiba,


Lubabatu tazaro mata ido tace tambayarkifa akeyi mekemaki ciwo?


Batadai tankaba,


Lubabatu tagaura mata mari tace,

Don ubanki magana akeyimaki kinyi shiru".


Malamin yace haba hjy ki tausaya mata mana,

Bakiga halin datake ciki bane?


Abita ahankali lalurace tatabuwa migodewa Allah ma da mukasamu dawowar numfashinta".


Rabe yace tabuwa kuma malam?


Yace eh kwakwal warta tatabu,


Wani dadi lubabatu taji shikenan komai yazo da sauki,

Fa iza tatabbata mai sa a


Wani guntun murmushi tayi,

Yayinda Rabe yadafe kai da hannu biyu,

Shikenan taleko takoma,

Ashe abinda yake gudu sai ya iskeshi?


Wasu hawaye suka xiraromasa,


Bawai yana tausayin zuhran bane a'a yana tausayin kansa ne akan dukiyar da ya kwadaita da san samu,

Amma bari sukoma ggidayalallaba fa iza don yabaiwa lamidon ita,

Idan kuma tasake kafewa akan bakanta saiya koreta daga gidansa".


Yakawo yan kudi yabawa malamin, 

Yadauko xuhra yadawo gida,

Gashi kuma yauvsaura kwana ukku  yarage  afaura auren dole ne yasamu lamido yasanar dashi dan asan abinyi tun wuri".




Washe gari Rabe yayi sammako zuwa aiki,

Kasancewar kwana biyu yana zariya ya iske aiki cinkushe a ofis din don haka  yasoma ragewa,


Yana cikin aikinne  wayar girke ta land line  ta soma kara yasan mai kiran danhaka yayi sauri yatashi yatafi ofis din oga.


Bayan sungaisa lamido yace

Kwana biyu bakaxoa wajan aiki dafatan dai lfy,?


Rabe yace to dadai sauki ranka yadade,


Wlh yarinyar nance takamu da ciwon hauka, shine natafi nemamata magani,


Subhanallahi wace daga ciki?

Lamido yafada cikin kaduwa,


Rabe yace anaryarce shine nake tunanin yanda za ayi".


Lamido yace karka damu rabe baga yar uwarta namba,

Amaida akanta kawai,


Rabe yace kanaganin hakan babu takura ko?


Lamido yace duk dayane tunda dukkansu yayankane,


Rabe yace to shikenan,


Da haka suka ajiye magana akan amaida auren kan fa iza, nanda jibi sai adaura kawai


Lamido yakawo kudi masu yawa yace akaima fa iza saitayi hidimar biki  kafin yazo,


Rabe ya amshi kudin yayi godiya,





Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

4⃣4⃣






Na

Maman sadeeq








."Rabe yadawo gida yakira faiza tasameshi adakinsa yasoma magana cikin lallashi".


Kinsan abinda yasa nakiraki fa iza?


Tace A'a 


Yace zan kuma neman alfarma akaro nabiyu,  awurinki inafatan zaki bani hadinkai?


Tace insha Allahu zambaka hadinkai".


Yace to dama maganar auren zuhra ne da ogana munyi  magana dashi amaida akanki, 

Keyakikagani?


Tace duk yadda kagani baba,


  Yace to ki amince kawai shine yadda nagani".


Tace shikenan na amince baba,


Yace yawwa  fa iza Allah uayi maki Albarka kinji,


Tace amn,


Yakawo kudin da lamido yabashi yabata,yamika mata ta ce name nene,?


Yace angonne yace imbaki kiyi hidimar biki,


Ta amsa tayi godiya ta fito, 

Tashiga dakin lubabatu tafadamata yadda sukayi da babanta,


Lubabatu ta warce kudin  tace,

Rabu dashi baisan dawan garinba,


Sha kuriminki auran soyayya zakuyi bakamar yanda yake nufiba,


Fa iza tace wlh harna kosa jibinnan tayi adaura aurannan,


Lubabatu tace  ke tsayama tukunna, bakosawaba

Aiyanzu zama baigammuba,


Mutashi tsaye don mu kara kameshi sosai,

Danni hankalina bai kwantabavdazamanki da matansaba,

Duk da bata san halayyarsuba,

Idan muka samu yanda mukeso to har su sai min iza keyarsu gaba,

Indai har inada rai mowa ceke acikin mowowi.

Dan haka wannan kudin taimako zan amso dasu,


Fa iza tace dadawasu kudin dana kara maki dankisamomin taimakon da zai runka ganin babu wata ya mace aduniya bayanni".


Lubabatu tace kwantar da hankalinki saikinyi yadda kikeso,


Harshi saikin juya tamkar sitiyarin mota,


Abudaya dai nake tsoro ki samu abin duniya kijuya min baya,

Kokuma soyayyar mijinki ta rufe maki ido kikasa bankadomin dukiya yadda yakamata".



Fa iza tace bana so umma kinasa kokwanto akaina,

Indai dukiyace duk abinda nasamo nakine,

Danhaka kishiga ki samomin taimako 

Nikuma zan shiga in ta bankadomaki dukiya".












Tadubeshi cikin bacin rai tace ashe ni ban isa dakaiba?


Nace kabar zancen aurannan shine katafi kaje kayi ta harkarka ga sakarya tanata babatu ko?


To naji komai da kuke ciki,

Dan haka tashi maza kakaini gidan da kakeneman aure inga iyayaenta,

Ingakuma ita yarinyar dakake nema,


Cikin rawar murya yace dan Allah hjy kiyi hkr kidauka komi mukaddarine daga Allah,  

Nasan nayi maki laifi  dan Allah kiyafemin".


Ta ce sosai nasan komi mukaddarine, saidai yadda nafadamaka magana bakaji,

Tonima bazakafadamin in saurarekaba,


Kuma bari imfada maka abinda zai kaini, 

Zanje in amso dukiyar da kanar ka masu,


Aure kuma kaje kayi tayi,

Idanda zaka birgenima dasai ince kacike suzama su hudu,

Amma yanzu tashi kakaini kawai".


Yamike tsaye  yafito tabiyoshi abaya,

Yabudemata marfin motar tashiga yanufi gidan Rabe,


Akofar gida yayi  fakin yafito itama tafito,


Ta dubi motar da akace hada ita yasako tace 

Wannan motar ce kasako da itako?


Yace eh cikin tausasa lafazi,


Tayi kwafa ta cusa kanta cikin gidan tayi sallama,


Babau wanda ya amsa daima zuhra datayimata kuru da ido tana kallonta batacemata komaiba,


Hjy tayi tsaye tana karewa gidan kallo vikin kyankyami da raini,


Lubabatu tafito daga bandaki taga mace  atsaye suka kalli juna,

Lubabatu tace bakuwa mukayi?


Hjy tace eh,


Lubabatu tace to shigodaga cik,


Bazamane yakawoniba .

Ina maigidan yake?


Lubabatu tace yana ciki,


Hjy tace kiraminshi,


Lubabatu tadubeta asheke tace  ke a wa dazankiramaki mijina?

Wace alakace tsakaninku?


Hjy Tayatsina  fuska sannan tace sunana hjy safiya nice mahaifiyar lamido dafatan kingane?


Lubabatu ta fadada fuskarta da murmushi tace,

To ashe sarakuwar fa iza ce sannu da zuwa bari inkira Raben,


Tashiga dakin suka fito tare.

Lubabatu tace sarakuwar fa ixa ce".


Rabe ya duka suka gaisa,

Tace dama  nazo saboda in amshi kaya,

Sabodani bandan wainar da ake toyawaba,

Sabodahaka kufitomin da duk abinda kukasan kun amsa".


Rabe ya dubi lubabatu suka kalli hjy,


Lubabatu tace hjy me yayi zafi haka?


Rabe yace A'a lubabatu mudauki kayansu mu basu,


Hjy tace babu abida yayi tunda jarkuka tallata yayanku saboda zurmewa da hadama,

Nibazan hana yuwuwar aurenba,

Saidai zan amshi duk wani abu daya tsaunomaku,

Ninasan abinda yadace inyi aakaidan haka kudaukomin kaya da dukiyar da kuka amsa".


Lubabatu tashiga daki tasoma jido akwatuna tana diresu agaban hjy cikin rashin zuciya lubabatu tace gasunankuma sai kuma me?


Hjy tace sai kuma makullin motavda kuma sadaki".


Rabe Yashiga daki yadauko makullin mota da kuma sadaki naira dubu dari biyar ya mikawa hjy,

Takarbi kudin ta duba tajinjina,

Tawaro dubu dari biyu tace ga sadakinan,

Kaya kuma akwati hudu zaku dauka sauran ta kwas zan koma dasu".


Lubabatu tace saidai ki kwashesu duka,

Aiba lallai saishi zata auraba,

Kije kizaba masa Wacce kike so ya aura  

Ni bantana ganin sakaryar uwa irinkiba

Wannan shine me?


Hjy ta ruke haba tace ni bazan hanaba tunda bansan abinda Allah ya shirya akaiba,amma dai kaya bazan bar makuba,

kuma inatakaici da dana baidace da sarakuwar arzikiba".



Lubabatu tace aini bansan shidin dan kananun mutanebane amma yanzu nagane,

Tunda harkika iya wanko kafarki kin biyo kudin  kayan da kuka kawo,

Lalkai akwai ayar tambaya akanki,

Watakila ko amai zaki iyayi kilashe abinki".


Rabe yayiwa lubabatu tsaki. 

Ke rufemin baki karki kawomin shirme".


Ya dubi hjy yace kiyi hkr ga kayanan ki dauki wanda zaki dauka,


Hjy tace babu komai dana yajamin duk  abinda akayimin".


Lubabatu tace dazaki birgeni da kin aureshi,



Rabe yace lubabatu yimin shiru bani son shashanci,


Hjy tasoma jidar akwatuna tana fitadasu waje har ta kwashesu, 


Lamido  yana kallonta tace budemin motar can,


Dasauri ya buda sabuwar motar aka zuba kayan aciki. 

Tace

Muje acikin  motar inyaso kadawo kadauki taka motar,


Jiki asanyaye yaja motar, 

Baiso hjy tayimasu irin wannan karantarba,

Yadda ya azabtu da san fa iza zai iya kashe konawane danyaga yafarantamata,

Dan saiya maidamata dakayan da hjy ta dauko,




Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪4⃣5⃣



Na

Maman sadeeq










"Lubabatu ta dubi Rabe tace,


Amma wannan mata akwai tsinanniyar uwa,


Nantaba ganin rashin mutumci irin wannanba,


Idanko hakane ko auren akayi bazatataba dagawa fa iza kafaba,

Dan haka abar abinnan kawai tunda har tafara haka tundaga yanzu, tumba aje gidan dantaba,


Nikam nasan matsalar rashin kaunar uwar miji,

Dan haka adau kayannan aidamata da tsiyatakunta,

Dama fa iza basan danta takeba biyayyace zatayi maka,


Tace to tunda kuwa jakane sai kabashi mahaukaciyar daua zaba da farko".


Rabe yaja tsakiai tsananin karfi, yace,


Duk yadda naso in tsara abinnan bazai tsaruba,

Tunda har matarnan tashigo cikin lamarin,


Babban bakincikina motarnan da ta sa na kwallafa raina  akanotarnan,

Dan haka zanje in lallashi ogana dukda tace baxata janashi aurenba,


Amma akwai yuwuwar tahana ruwa gudu agaremu,

Amma zansan abinyi,

Kuma keda kike cewa fa iza bazata aureshiba bakin ciki zakiyi mana?


Ai duk bala inta sai mun amshi wani abu agurin danta dan haka kizuba ido kiga yadda zamu kwashe,


Fa iza ta shigo ganin iyayenta atsaye tace baba lfy?


Lubabatu tasanar da ita abinda yafaru tace,


Fa iza tace karkudami baba aibadai auren zatahanaba ko?


To dasauki idana cewa tayi baza anadaba lefen ganadaya ba abindamuwabane,

Nidai biyayya zanyi ba lefene gabanaba".


Rabe yace yawwa yar Albarka zuwa gobe zan sameshi a ofis,mayimaganar,

Lubabatu tace to Allah yakau".


Wayar fa iza ce tayi kara dasauri tadubi kanwayar, 

Lamidone yake kiranta 

Tayi sauri ta daga yace tafito tasameshi akofar gida,


Tafada lubabatu cewar lamido yana kiranta awaje,


Lubabatu tadauko turaren hadin soyayya dole da kwalli, dakanta tashafawa fa iza sannan tabata laya tace tayi ta matsata,


Tasameshi jingine jikin mota,

Sai wani kashe mada ido takeyi,

Shikuma yanajin wani irin sonta aziciyarshi lamar ya rungumota yakeji,


Tace Ranka yadade,


Yayiurmushi yace tareda naki,


Nazo imbada hkr Allah yasa bakiyi fushiba,


Tayi far da ido tace wlh banyiba yoshe masoyi yake fishi daasoyi?


Yace to aike imbakiyi fushiba aisumama sunyi dan haka shiga kisanar dasu ganinan shigowa,


Tace to,


Tashiga tafadawa lubabatu abinda yakawoshi,

Libabatu tace tojeki ki shigo dashi,


Suka shigo shida fa iza yaduka yana gaida lubabatu yabasu hkr akan abinda majaifiyarshi tazo tayi masu,


Lubabatu tawashe baki tace,

Kai haba  aibakomai tanada gasakiya,


Ya dada bada hkr,

Kuma yaciremata kudi masu kauri yace da fa iza tazo gawasu kayannan takarba amaimakon wacce hjyrshi, takarba,


Lubabatu tayi godiya sosai,

Kamar tayiashi sujjada suka fito shida fa iza,


Akwati takwas ya diremata agabanta, kuma yace,

Tabari idan ta shiga gidansa zai siya mata, 


Sukayi fira wadda shi baiso surabuba,

Ahaka kuwa suka rabu yana matukar kewarta,


Fa iza tashiga gida da akwatuna 

Lubabatu takalleta tace dakyau".

Wato saidaya siyo wasu akwatunan?


Lallai yazo wuya dole intashi innemomaki gama didi yadda zaki ida damkeshi,


Fa iza tayi murmishi tace umma nadade ina jiran wannan lokacin ashe zaizo?


Lubabatu tace zaizo gashima yazo saidai akwai abu daya dazajiyi,


Kinga tsinanniyar uwarnan tashi,

Saikinyi taka tsan tsan da ita, 

Dominkuwa na lura bata maraba da aurenki,


Matanshi kuma duk sai munfitar dasu dannayi Alkawarin bazaki zauna da kishiyaba,(shin ko hajir zatabari?)


Fa iza tayo mur mushi tace Allah yabar minke umma kedai kibude asusunki,

Nikuma zanta ingizomaki abin duniya,


Lubabatu tace idanko kikayimin haka kin biyani,

Danda nasamu yanda nakeso tawwali zanyi tafiyata kasa mai tsarki,


Fa iza tace tawwali kuma?


Tace eh mana mai zan tsaya yi  a Nigeria,


Ahaka sukayi ta fira har dare yayi nisa


 washe gari Rabe  yasamu lamido a ofis,


Tunkafin yace wani abu lamido yasoma bashi hkr,

Akan abinda mahaifiarshi tayi,

Rabe yace,


A'a babu komai adai runka lura da hakkin iyaye,

Kasan lamarinsu mai girmane,

Sai anyi taka tsan tsan wurin kula da hakkin iyaye,

Idan sukace ayi to ayi idan kuma sukace abari dole adaure abari ko babu dadi".


Lamido yace insha Allahu zankiyaye,

Ina fatandai babu matsala?


Rabe yace babu idanma akwai yar kadan ce,


Lamido yadauko kudi har dubu dari  yabashi,


Rabe yayi godiya sosai,

Sannan yabar ofis din cinin tsananin farinciki,.


Muje zuwa








Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪4⃣6⃣




Na

Maman sadeeq







Tadubeta cikin kulawa tace,

"yaya kinzua mashi acikin abincin yaci maganinda  bamaguje yabaki?


Hajir tace yacimana kuma na soma ganin  sauyi,


Sai dai na lura yana rawar jiki  akan wannan auren nan da zayyi abin yasoma damuna,


Laila tace to tashi dazafi zafi akan daki karfe,

Indai da kudi mujega bamaguje,


Hajir tace,

Akwai kudi, namance ban fadamakiba ambamu kayan kishin laifi, harda kudi,


Laila tace daukosu muwuce,


Hajir tadaukosu suka nufi kauyen da bamaguje yake, 


Wannan karon wani  abu  yabata yace ta matsa shi agabanta,


Sannan yabata wata laya yace itakuma ta boyeta akarkashin filon da lamido zai dora kanshi,

Idan hartayi haka xataga biyan bukata,


Amma da sharadi saitadainayin sallar la asar gaba daya,


Hajir tace idan dai bukata zatabiya babu komai,

Idanma duka sallolin zata soke sai ta soke,(waiya zu billahi Allah ka tsaremu daga rudin duniya da iblis, amin ya Allah)


Takawo kudin da yabukata tabashi,

Tajuyo gida babu ko dar axuciyar hajir,


Cikin sa'a  kuma itace daranar girki,

Tahada abinci da sinadarin magungunanta,

Tayi wanka tare da kwalliya ta neman magana,

Ta matsa abinda bamaguje yabata, tawuce dakin hubbynta,


Tasamu filon dayake tada kai tasaka layar yadda babu mai ganewa ta koma dakinta,



Karfe shida ya duro agidan tareda abokinshi munnir da bada masi,


Hajir tafito cikin kidiferenta da firirita tatari hubby"


Badamasi yace A'a lallai yokai ana maka haka harkasamu zarafin karin Aure?


Munnir yacetoba mijin mace hudu bane?


Aitahakane Zaigane anasansa tahanyar kyautatawa".


Hajir tace to munnir kaida kanka? To aniyarka ta bika,


Yayi dariya yace aniyarmu tabimu dai nida mijinki,

Kuma bayan wannan dazatazo akwai Cikon daya nanan biyowa baya,

Kinga lenan mai karfi saita kwace miji,

Wai inama jawaheer ne kotafara shan kamshine?


Jawaheer ta fito tace aini tuni  nasha nawa kamshin,

Dan haka wannan karon ba kukana bane , wai uwar kishiya ta mutu".


Hajir tajuyo ta dubeta  dan tagano indatasa gaba,tace,


Barekumani danaci dubu sai ceto,

Tafiya kuma maganin gari mai nisa, 

Ajuri zuwa rafi hajir ashirye take tsab,

Allah yakuma bamu nisan kwana".


Lamido yace munnir dan Allah karkaja gobennan tazomin abaibai,

Karkajanyomin wutar dazata konemin gida".


Hajir tace har yaushe kuma?


Aitunda kayi kokarin hada mata ukku to kagayyatowa kanka masifa da tashin hankali agidanka,

Dan ba a taba sarki biyu abishiya dayaba,

Haka kuma duk inda mata ukku suke babu zaman lfy  atareda wanda ya ajiye su,


Badamasi yace haba hajir ai sai ai fatan zaman lfyr daga kanki,

Idan hankalin maigidan ya kwanta tokuma nakune ya kwanta, 

Tunda ko shine ku ku kune shi, dan Allah kuyi hkr,


Hajir tatabe baki tace,

To  za aduba idan da yuwuwar hakan,


Jawaheer kam bata tankaba,


Kiran sallar da akayi yasa  su badamasi sukabar gidan,


Hajir  tahadamasa ruwan wanka,


Bayan yafito daga wanka wasu sababbin kaya taga yasa,

Batataba ganinshi dasuba,

Tanadai kallonshi har yagama shiryawa,


Ina zakaje?


Yace kai namanta insanar daku yau ake gudanar da fati a daula hotel yimaza ki shirya mu wuce  tare bari na sanarwa jawaheer".


Hajir tace saidaiko itadin,

Nikam bazanjeba".


Yace sabodame?


Tace saboda nasan ciwon kaina,


Zakayimani kishiyar don hauka sai inkwashi kafa in bika gurin fati,

Mekakeso adau keni?

Kokana tunanin nima saunar matance?

Kadaije kawai".


Yace to shikenan  bari inje idan jawaheer zataje".


Yasakai yafita 

Yanufi gidansu amarya, 


Fa iza anyi kwalliya ta gigaggun yammata,

Tahadu hartagaji,

Dukda bawani cikakken kyaune da itaba,


Yamnatan amarya du zuwaira suma sinci ado daidai gwargwado,


Hidimarsu sukeyi ,

Yayinda zuhra ke zaune jikin bango, sai binsu take da ido,

Babu wanda yake shiga shirginta bayan lami,

Batacewa eh bare A'a saikallonsu takeyi,


Karfe takwas  lamido ya iso yakira fa iza awaya yace su fito,


Suka fito itada kawayanta,

Xuga guda munnir da badamasi suka kwashe kawayen amarya,


Shikuma lamido yadauki amarya duka wuce hotel,


Makadan zamani damawajan zamani sun baje  fasaharsu,


Amarya tana liki da angonta yayinda zuwaira ke cikin fili sunata bada himma awurin rawa,


Anraba abubuwan girma da girmamawa daga karshe aka gayyato amarya da ango dan du dan taka,


Shikam ango kunya bata barshi yadan rausayaba sosai,

Amarya tasaki jiki ta tiki rawarta har gwagwaronta na faduwa🤣🤣🤣🤣🤣


Karfe goma akatashi daga fatin 

Ya ajiye fa iza agida shima yanufi nasa gidan,


Tana zaune afalo yashigo ya zauna kusa da ita tadubeshi tace".


Har antaso?


Yace eh amarya tana gaidaku,


Ta kyabe baki dayasan yadda takeji azuciyarta duk lokacin da ya ambaci amarya da yadaina,

Dan ji takeyi kamar ta shakeshi".


Tace,

Uhum nidai bana neman gayyar sodi aname tagaidani?


Yakamo hannunta yace nidai zomuje nagaji dayawa".


Tace bari in hadaaka abinvi tukunna".


Yace dakin kyauta dan banci komaiba".


Tayi murmushi danta tuna da maganin data zuba, 


Tahada masa  abincin sannan takara  matsa maganinta tayo shirin bacci,

Yanagama cin abincin duka shiga bedroom.





Maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪4⃣7⃣





Na

Maman sadeeq





"washe gari yatashi yana ta hidimar daurin aure,


Babu fita ofis,

Karfe  biyu da rabi dubban mutane suka shaida daurin aurensu,


Rabe ansha babbar riga shida sani da abokan arxiki,

Sai tayasu murna akeyi,


Itako amarya sai kanta yakara girma,

Jitakeyi kamar amafarki,

Man dinnanne wanda ta azabtu da sanshi yau gashi yazamo mijinta,

Atansa kuma Allah yayanko masu kazar wahala tunda har yahadasu zama da ita,


Wani murmishi tayi tareda lumshe idanu,


Zuwaira tadana mata duka abaya tace,


Yar iska kedawa kike murmushi ke kadai?


Tadubeta tace zuwaira kenan natuno ne yadda  nawahala akan son man dinnan ne saigashi yau yazamo mallakina,


Zuwaira tace ke ni bawannanba,

Kinsan mutumennan yyanaa mata,

Kuma yasan alwai kuma yasan babu,

Baki gudun wani abu idan labari yasha bambam?


Rass Rass gaban fa iza yafadi tace,


Hakanefa, 

Kodayake ai umma tayimani tanaji karkiji komai zuwaira,


Zuwaira tace shiyasa nake tsoron auren mai mata,

Gara in auri yaro wanda baisan dawan garimba,

Amma masu mata sunsan rufe sunsan bude".


Haka akacigaba da shagalin biki gaban amarya mafaduwa,

Saboda tana gudun abinda zaije yazo tsakaninta da angonta.


Karfe tara motoci suka soma layi akofar gidansu amarya,


Bayan fada dayan nasihohi harma da yandabaru idan maigida yayi ajiya adan runka waro kudi

Duka dai aka kwashe tawagar mata da amarya zuwa court road gidan ango"



Uwar gida jawaheer anyi ado nakece raini, itada yaranta, duk suna zaune afalo".

Aigayya mai aiki itama tana zaune itada halisa,


Fadar adonta bata bakine,

Adage take kallon kowa tana taunar dangon nasara(cingom)


Guda tamatan dasuka rako amarya otace tafara yo sallama,

Sannan mata suka fara shigowa".


Amarya tana ruke ahannun turai,

Ganin girman gidan yasa dole ayi tambaya dan sashe hudune agidan,


Turai ta ce dasu hajir,


Don Allah inane dakin amaryar yake?


Jawajeer taimata nuni dayatsarta kaitsaye suka cusa kai, 

Azatansu dakine saisukaga ashe  gidane guda, 

Daki hudune da kicin da bandaki, 

Gakuma wani falo komai ahade aka saka amarya adaki,


Saikuma yankawo amarya suka shiga zagaye gidan dan su kashe kwar kwatar ido,

Suka gama kallon komai sukayi niyyar tafiya gida,


Atamfofine jawaheer ta rika rabawa yankawo amarya,

Kuma masu tsada, 

Dahaka suka watse akabar amarya kadai".


Itako hajir tashiga mamakin inda jawaheer ta samu atamfofi taraba,

Saidai tabar abin akan lamidone yasiyo yabata tarabawa matan".


Karfe tara da rabi lamido yashigo  gidan,


Hajir tashiga daki tamatso  sirkullenta,

Takuma bade abincin lamido damagani,

Sannan tanufi dakinshi, tace,

Ga abinci can yana jiranka".


Ya dubeta yayi murmushi yace uwar gida sarautar mata".


Tace yau kuma nice uwargidan?


Yace ehmana tunda kinyi kanwa girma yakamaki"


 Tace to nagode".


Yace waini jiya ya akayine meyene sirrin?


Tayi murmushi dan tagano inda ya dosa,


Lallai bamaguje yakuremata adaka, tace

"nidai taso kaci abincin".


Yatashi tahada mashi abincin,  yaci

Yanagamawa yakamo hannunta yace,


Inafatan yauma inji sauyin dayafi najiya?


Tace kabari kayi wanka tukunna".


Yace "Nadokantane dayawa,


Takuma yin murmushi tace,


Kaida kake da sabuwar amarya aledarta maizaikidimaka akan tsohuwa irina?


Yadubeta yace idan har amarya aleda take toke akwali  kike, kinga akwai bambanci,


Tayi gajeriyar dariya tace haba aininasan zakin bakin maza, kaidai kawai ayi sha ani,


Yace kensn baki yarda da abinda nafadamakiba?


Tace toya za ayi nayarda idan hakane ka gayyato min wata ka hadani da ita?


Yace baridai imfito sai innunamaki har kiyarda".


Yashiga bandaki yayi wanka adokance ya fito suka kule kuryar daki,


Washe gari akayi walima karfe biyar nayamma,


Turai takamo hannun fa iza ta shiga falon  dasu hajir suke zaune  tayi sallama,


Jawaheer ta amsa hajir ko ba tako dube su ba turai tace,


To ga amanar amarya don Allah  ku hade kanku ku zauna lafiya ayanzu  anbar  haukan kishi zaman lafiya shi kowa yake bukata,


Jawaheer tace to Allah yatayamu riko,


Hajir tayi maza tace yatayaki  riko dai,

Tunda ke kinji zaki iya karbar amanar kishiya,


Nikam bazan karbi amanar kishiyaba nida ita saidaina kafawa matsiyaciya WUKA AMAKOSHI


Turai tace ayi hkr dai WUKA A MAKOSHI mutuwa kenan adaiyi hkr azauna lfy".


Zuwaira tayi maza tace,


Baba airashin sani yafi dare duhu ba faiza bace?

Akafamata WUKA A MAKOSHI idan zai yuwu atsuntuwar fatalwa bazaitaba zamo ribaba".


Turai tace lerufemin baki bana son shashanci,

Muda muka kawo tamu aizaman lafiya Mukeso ba tashin hankaliba".


Fa iza dake lullube tace,


Hum ai baba abinda zuwaira tafada gaskiyane ninan nafi karfin wata yar iska takafamin WUKA A MAKOSHI,idan kuna zata iya to gafili ga maidoki,

Kuma ni banyi zaton gurin kishiyoyi zaki kawoniba wlh da bazanzoba...


Kafin tasake bude baki hajir tadauketa dawani wawan mari,

Takuma damki wuyanta ta watsar da ita tamkar kayan wanki takuma dora da fadin,


Ke har kin isa kice dani yar iska?


Ro wannan sine kuskurenki nafarko kuma na karshe,

Idan har kikasake kwata zagina wlh saikinyi nadama takarshen rayuwarki,


Zuwaira tayi sauri takamo fa iza tayayemata lullubi ga goshinta dayafara kumbura,


Faiza ta dubi hajir tace,


Wlh ayau saikinyi danasanin tabani dakikayi amarasa kunya waye ubanki?


Zuwaira ta ruko hannunta tace karkice komai kibari sai zuwa lokaci nagaba,


Karki mance ke amaryace idan kikayi haka  kin tabka abin kunya,

Mezaisa kiyi fada alhalin ke ba karya bace?


Fa iza tace wlh kudirati nazan kyale matarnamba, sainaga ubanta amarasa mutumci,

Abin kunya kuma andade ba a bugani ajaridaba,


Ta ingije zuwaira ta tinkari hajir da kokawa,

Saidai ance wanda yafika yafika,

Dan hajir tafi karfinta nesa ba kusaba,

Dan haka bata bata ba lokaciba wurin yimata kwabta daya saiga fa iza a sheme,


Dagudu turai tayi kanta,

Zuwaira tace, baba wlh ta suma,

Turai tace yimaza dauko ruwa dauko ruwa".


Dasauri zuwaira tadauko ruwa suka antayawa faiza saigashi takawo numfashi,


Jawaheer nazaune tana kallon  ikon Allah,


Itakam hajir ta dora kafa daya kan daya ta dubi fa iza tace".


Inafatan hakan zaizamomaki  darasi,

Ina mai tabatarmaki tunda kikafara leko rayuwar bar zahu, to watarana idan kika leka bazaki dawoba,

Kuma nan gidan wlh saiya zamemaki tamkar gidan maza,

Dan haka saikisan yadda zaki koyi yin ladabi da lafuzza masu taushi agareni".


Tana fadar haka tayi shigewarta sashenta,


Fa iza kam babu baki sai dai ido,

Ayanzu tatabbatarda rashin mutumcin hajir ya doke nata itadin uwartace,kai kakartace ma amma tasan yadda zatayi da ita".


Turaikuwa takasa magantuwa dan talura duk wanda yayi magana ciki fatar jikinshi ce zata fadamasa,

Shiyasama taja fatar bakinta tayi gum,

Suka kamo faiza suka dawo daki".


Turai tabata hakuri  takumace ta iya bakinta  karta kuma zakalkalewa hajir,

Idan tace tayi to tayi idan kuma tace tabari to lallai tabari,

Dahaka suka bar gidan akabar su zuwaira da sauran kawayenta wadanda kezaman jiran ango dansu karbi kudin sayen baki,

Inda kuma fa iza tayi mugun kudiri akan  hajir,

Saidai sanine batayi ba hajir tasha gabanta tayimata fintinkau,


Haka sukayi jugum babu mai cewa uffan,


Akayi magruba akayi isha i karfe takwas, tara, goma  shiru babu burbushin ango.


Goma darabi hardai shadaya saura zuwaira tace,

"nikam nagaji dazaman jiran tsammani fa iza,

Idan sunzo ki karbamin kudinmu zandawo gobe in amsa harma dasauran kazar amarci".


Fa iza dai bata tankaba,dan itamata ta mutu da rashin zuwan angon akan lokaci,

Haka sukayi mata nankwana suka bar gidan,


Tayi shiru tana tunanin abinda yahanashi zuwa har kawo yanzu, tayi tagumi,

Zuwacan tayaye lullubin,


Tadade azaune amma har yanzu babu ango babu duriyarsa,


Gyangyadi tafarayi tuntanayi intakusa faduwa ta bude ido hardai ta bingire kangadon,


Azatonta idan tafarka  zata ganshi kan gadon,

Saidai datafarkama batasauya zaneba,

Wayam taganta ita kadai ta dubi agogon dakin Karfe biyar  na asuba tagani, 

Karajan bargo tayi ta kudindine,

Sam batasaba tashi da asubaba,

Saikarfe tara tatashi tashiga bandaki tayi wanka sannan ta dauro alwala,


Rana na lallonta tayi sallar,

Tanagamawa takoma kangado shiru babu wanda yashiga sashenta bare yaga yata kwana,

Sai wajan shadaya sannan taga wata mata tashigo dauke da  fulas da kula wadda take kyautata zaton yar aikice,


Matar tagaidata kana ta aje fulas din da kular tajuya abinta,


Batadade da fitaba tadawo dawata leda ahannunta ta ajiye mata tajua abinta,


Tasauko daga kan gadon ta bude kular abincine fulas din kuma tasan ruwan zafine,

Tajawo  ledar ta bude kayan shayi ne aciki,

Tature kayan gefe dan basu take bukatar ganiba,


Lamido takesan gani dantaji dalilin dayahanashi zuwa wurinta,

Duk da sandayace yana yimata mai zafi 

Amma yawatsar da ita,


Gani tayi tunani bazaiyimataba tajawo kular abinci tasoma ci,  

Taja fulas tahada shayi tasha ta koma ta kwanta,


Wata dabara ce tafadomata tayi saurin dauko wayarta takira lambar  lamido saidai harta tsinke ba a dagaba,

Tasake kira gab dazata tsinke akadaga 

Shiru yayi bayui maganaba, sai itace tace hello".


Akace waye?


Tambayarda tabata haushi, 

Wane irin wulakancine wannan?

Yana nufin baigane maimaganaba?


Yasake cewa idan bakiyi maganaba zan kashe".


Saiyanzu tagane bashi yake maganaba,

Koshakka babu matarsace wadda sukayi rigima jiya da ita,

Satayi sauri tadatse kiran ta ajiye wayar tayi shiru,


Zuwairace tayi sallama tadago kai ta dubeta,

Suka gaisa, 


Zuwaira tace yakwanan farin dare?

Nasan dai angogu inafatan dai baki samu matsala daga gareshiba?


 Fa iza tace keni banasan  iskanci ga abin karin kumallonan idanzakici kici,  sirtin ma auratan zamfadamaki?


Zuwaira tace karki kaini inda banjeba waceni dazan leko sirrin ma aurata?

Nadai tamayekine dan karmushiga damuwa".


Fa izatace to babu wani abu karma ki damu".


Zuwaira tace to munyi tabarka,


Yanzu daukomin kudinmu najiya,

Alladai yasa yabamu abin kiri ganin babu idanmu,


Itako fa iza sotake taboye sirrinta,

Danbataso zuwaira ta fahimci har yanzu angonta bai zo indatakeba,


Zuwaira takatseta dacewa kardai kice baibadaba?


Fa iza tace ke namanta bari yadawo zan karbarmaku yama za ayi ya hanaku?


Haka dai sukayi ta fira ar karfe biyu,


Zuwaira tace nikam gida zanwuce wannan angon bazaidawoba dan yanzu ba,

Idan dai  yadawo kikarba mana kudin, kuma masu kwari zaki  karba,


Fa iza tace to shijenan,


Sukayi sallama akan gobe zata dawo takarba,.





maman sadeeq

[9:31PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪4⃣8⃣




Na

Maman sadeeq



"saida turai tagama bawa lubabatu labari tsaf duk abinda  yafaru  dasu agidan amarya sannan ta dora da,


Tokinji idan har yarinyar nan tacigaba dayiwa fa iza  haka ko sjakka babu itace ajalin auren,

Gagida har gida saidai masifaffiyar matarsa Ita zata hana ruwa gudu".


Lubabatu  tace amma dai ke yaya turai akwai yar iska,

Idan banda iskanci asumar da yarinyar kina kallo amma kikasa yin wani abu akai?

Toni kidhiyar fa iza bata batamin ba rai irinki,


Meyasamani kikazo kikafadamin?


Don inji haushi ko bakinciki yakasheni?


Turai tace yanxu lubabatu ni kike zagi dannazo nafada maki abinda yafaru?


Lubabatu tace kwarai nazageki, aida yarki akaduka dakin dauki mataki,

Wannan ko ta mutu kotayi rai badamuwarki bane,


Kodayake bakin cikinkine kika kasa boyewa saida kika fito dashi,

To fa iza dai tayi gaba wlh babu yadda za ayi saidai hkr,

Kuma ni da agabana akayiwa fa iza wannan kaskancin, wlh dasaita raina kanta, amma zamu hadu da ita, ba abinda zai gagareni bane inwanki kafa inje har gidan indauko mata fansa ba,,

Amma ke kina tsaye idan ma kasheta za ayi babu tsiyarda zaki iya tsinanawa mts".


Taja tsaki turai tace duk daya kenan yayi daidai,

Nakuma gode da abinda kikayimin".


Turai tajuya tabar gidan,


Wani takaici taji yakamata ,

Yaushene akayi auren da faixa zata fara fuskantar matsala?


Yazama dole takuma tashi tsaye tun wuri bai kuremataba,


Wani fitsari taji yana shirin kubcemata, ta fito dasauri ta nufi bandaki,

Saidai kadan yarage takifa sakakon tuntuben datayi da kafafuwan zuhra gakuma wani wari yana tashi babu ko tantama kashine tayi azaune,


Ran lubabatu ya kara  baci,

Taciri hannu tadauke zuhra da mari tace 

Shegiya matsiyaciya,

Kai nikam nagaji wlh ,

Ina dalili inazaune lfy za a hadoni da cuta?


Bari Rabe yadawo saidai yasan yadda zayyi dake, 

Kodai yakai turu koni inzubar dake can kan bola".


Zuhra dai saibinta take dakallo,


Kallo daya zakayimata saika tausayamata,

Babu wanka babu wanki,

Kayan jikinta dun cakude da kazanta,

Lamice kadai ke dan taimaka mata,

Ita kuma aiki yayimata yawa,

Bata samun sukunin yimata wanka da wanki,



Rabe yadawo lubabatu  takama hannunsa takaishi  inda zuhra take zaune,


Warin dayajine yada yayi saurin toshe hancinsa,


Lubabatu tace to wlh kasan yadda zakayi da ita wlh na gaji wannan aisaitasa kwalara takama mutum".


Rabe yace toni yazanyi da ita?

Lubabatu tace  ga turunan kakaita, ko kuma Kamaida itagidan sani dama aishi yayi wannan kasafin".


Rabe yace kwarai hadamin ita  in mikata can kawai".


Lubabatu tace kamar yaya in hada maka ita dakazantat atare da ita?

Kajata ahaka can balaraba ta wanketa".


Yakamo hannunta yasata a mota yaja motar suka nufi gidan sani,


Balaraba tace to ya akayi kuma?


Rabe yace ga yadda akayi nan kingani,


Tace me Kenan?


Wlh babu inda zata Zauna  anan kawai kakoma da ita".


Sani yace barima bata bakinki abanza,

Lokacin da yake samun abun duniya ta silarta  wa yanema, kowa yabawa wani abu?

Saiyanzu data haukace  sannan zainemi mutane da Ita?

To wlh bazan karbetaba saikasan yadda zakayi da ita".


Rabe yace kanku dai akeji nidai yarinya nakawota kuma bazan kima da itaba dan haka gatanan, 

Ya tunkudata gaban sani yajuya cikin sauri yabar gidan".


Sani yace balaraba kiyi hkr  don Allah ki karbi wannan yarinyar,


Kamarfa yadda tafada akwanakin baya,

Idan baza muduba zumunciba to mudubi girman Allah mutaimaka masu shin wake garesu sama damu?


Waye yafi karfin kaddara ko munsan yadda tsakiyarmu xata kasance?


Idan munsan farkon samuwarmu shin munsan tsakiyar?to dan Allsh kiyi hkr  muruke yaran nan,

Nisai yanzuma nakejin maiyasa muka kyale iyayansu cikin kangi  bamu tausaya masu ba?


Balaraba  tatabe baki tace


Aiyanzuma kanada damar dazaka fitardasu daga cikin kangin,

Nikam wlh bazan zauna da waccan kaddarar ba kai dai da Allah yadoramawa saika zauna  niyanzu zabinka nakejira".


Yadubeta yace duk abinda nafadamaki bakijiba?

Tokije nazabi yarannan akanki".


Tayi saurin dubansa danbatayi  zaton jin haka daga gareshiba tace kazabesu akaina?


Yace sosai".


Saita koma tazauna yace kitafi mana kinkoma kinzauna?


Batace ko uffanba ganin tazauna yasa  yatashi yabar gidan,


Tadubi zuhra da kudaje suka damaimaye ajikin ta tamkar anzubamata danyan sukari,


Saikallon balarabar takeyi,


Duban agogo tayi karfe goma da ace goma batayiba datasan abinyi amma gobe nanan,

Tayi wata kwafa tatashi tsaye tasa kafa ta mangare zuhra har ta kifa, tayi wucewarta daki tabarta nan".


Karfe shadaya sani yadawo gidan,

Ganin zuhra yayi ainda yabarta,

Yakama hannunta yashigarda ita wani daki da babu komi ya shimfidamata tabarma yakwantarda ita yafito yanufi dakinsa".


Washe gari yasa Aisha diyar balaraba yace tayimata wanka tabata kayan ta kala daya tasanyamata,


Aisha ta amsa dayake tanada saukin hali, kuma zasuyi sa annin juna da zuhra,


Tadebi ruwa ta kama hannun zuhran suka shiga bandaki, tayimata wanka tasa mata kaya saigashi tafito fes

Aishar tabata abinci sannan tanufi makaranta".


Gidan yarage daga balaraba sai zuhra,


Balaraba tafito daga dakin tadubi zuhra taja tsaki dasauri takoma daki tadauko mayafinta tafito takama hannin zuhra suka fito ,


Tatsaida mai adaidaita sahu suka nufi kundila aka saukesu".


Taja annunta zuwa wata bola mai tarin kaxanta dayawa, tazaunar da ita saman bolar tace nan yafi dacewa dake tsinanniya mahaukaciya abola, 

Nanne masaukinki,inda yan uwankikwankwamai suke ba inda mutane sukeba, daga nankuma Allah yasa masu satar mutane suyi gaba dake matsiyaciya,

Balaraba tajuya tatafi,

.

Hakatakasanceca bola har gefen magruba,

Tawuni zur babu abindatasakawa cikinta,

Ga sauro sai cixonta yaje amma batadamuba,


Wasu tsirarun matasane sukazo wucewa daya yace kai baba dubi   wata yar kyau can.


Dayan yadubi zuhra yace anya ba mahaukaciyabace?


Dayan yace aitaxo da sauki idan mahaukaciyarce,

Ruwan kashe gobara basu da tara,

Mudauketa kawai  muje dakina ,

Idan muka maida yadda akayi saimu maidota".


Dayan yace to kamota sai muwuce".


Yataka cikin bolar yadubeta tadubeshi yace kinacin abinci?


Tayimasa kyar da ido yakama hannunta yace  taso muje kici abinci".


Batayi musuba  tataso tabiyoshi,


Kirjinta yafara damka dayan yace haba aisaikasa atuhumemu kabari mukarasa kawai,


Yace to mu waremana,


Suka soma tafiya tana ruke ahannunsa,


Kamar daga sama yaganta jaye da hannunsa ,

Yayi saurin taka burkin mashin dinsa, yatsaya ,


Tabas  yasan Baho, yan iskane dasuka buwayi  unguwar ta kundila  da yan sace sace dabata yaran ja ma a,

To meyakawo zuhra wajansu?



Alurar da yayi tafita daga kamanninta,


Yana tsaye su baho suka iso indayake,

Ko tantama bayayi zuhrace,kuma su baho basudaniyyar alheri akanta meke faruwa da zuhran? 


Kai baho sakarmata hannu inazaka da ita?


Baho yace baxan saketaba inaruwanka da ita ko yar gidankuce?

Yanayi yana wani ciccije baki,


Yafinciki jannin zuhra daga gareshi,


Baho yaxaburo zai laimasa naushi,

Yayi sauri yasa hannu yadaukeshi damari,yasa kafa ya harbashi,


Da dai baho yaga dagaske yake sai yaranta a nakare abokinsama yarufamasa baya


Yadubeta yaga sai kallonshi takeyi yace zuhra  meyahadaki dasu kima ina zaki?


Shiru tayi batace ko uffan ba yace,

Meyafito dake yanzu?


Nanma shiru tayi,

Yayi shiru yana faman nazarinta,

Zuwacan kuma saicewa yayi hau inkaiki gida


Batakomotsaba,

Lallai babu lafiya yafada azuciyarshi,

Yatsaida adaidaita yasakata suka nufi gidan Rabe,


Yayi sallama kofar gidan aka amsa,


Rabe yafito kofar gidan.

Ganinshi tareda zuhra ne yace ya akayi kuma?


Yace dama zuhrace nagani cikin wani yanayi,

Nayimata magana shiru babu amsa,

Shine naga gara na maidota gida tunda bansan indazatajeba".


Rabe yace to shima tunda sanin yaji bazai iyaba kasaketa taje duk inda zataje,

Mahaukaci aiduk indayatafi shane,


Idan kuma kanaganin zaku iya kaida mande to kuje nabaku ita duniya da lahira,


Kodayakema aikace awwalun ma yabaka aurenta, to kaje ka aureta ahaka nikam nabarwa duniya".


Kan Abbas yayi matukar shiga duhu dajin kalaman Rabe,

Xuhrance ta haukace?


Anyako su Rabe suna da imani?


Yace yanzu a ina zuhran taje dazama nangidan ko gidan malam sani?


Rabe yace da nan takeda zama danaji ban iyawane, saina maida ita gidan sani,

To shima nasan yagaji shiyasa yawatsar da ita dan haka kajeda ita ka kaiwa mande  shima yadan fige kazar wahalar da Allah yayanka masa".


Rabe yashige gida yabar Abbas da zuhra,


Yadubetasai tausayinta yakamashi,

Tayanda ake harbasu kamar kwallo saboda basu da bangon dafawa,


Yadorata Amashin yanufi gidansu da ita,


Mahaifiar Abbas tagansu sunshigo yana ruke da hannunta tace,

Yau kaikuma maiyahadaka da matar wani?


Yace ummu dubi zuhra kiga yadda Allah yamaida ita".


Yalwati tace ba aure akace za ayimataba?


Abbas yakwashe abinda Rabe yafada akan zuhra yafadamata,


Tayi shiru tana duban zuhra zuwa can tace,

Babu komai akwai Allah,

Nibansan abinda mutanen zamaninnan sukamaida zumunciba,

Anyi watsi da zumunci duniya kadai ake duba".


Taja tsaki cikeda takaici,


Malam mande yadawo,

Maidakinshi takwashe komai tafada mashi,


Shima yayi mamaki abinda Rabe da sani sukayi,

Saidaishi yayi aljawarin nemawa zuhra lafiya dayardar  mamallakin halittu(Allah).




Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪4⃣9⃣



Na

Maman sadeeq










"yau kwananta hudu agidan amma har yanzu bata sakashi a idontaba,


Aduk yadda ta dauki lamarin ya shallake tunaninta,


Abinci kam batada matsala dashi,

Matsalar ta daya ce tarashin zuwan angon nata ,

Tarasa yadda zatayi tasamu koda magana dashi,

Wayarma datakira matarsace ke dagawa,

Dan haka tayanke shawarar fita babban falo tazauna har saitaga shigowarshi".


Tadubi agogon dakinta ,

Karfe hudu da rabi tadauki kwallinta ta rambada,

Takawo turaren shima tashafa,

Saidai dole zata hke da matsa layar tunda agaban matansane,


Kai tsaye tafito falon, babu kowa acikinsa,saboda kowacce tana ciki tana girki,

Tayi shiru tana karewa falon kallo yahadu karshen haduwa,

Babu abinda yafi daukar hankalinta irin faskekiyar talabijin din bango(plasma)wadda ta kusa mamaye Rabin bangon,



Jawaheer ce tashigo falon tace amarya bakya laifi, said yau ake ganinki?


Fa iza tayi mur mushi race aiko dai,


Maman baby shine kika ki turomin baby tatayani zama?


Jawaheer tayi shiru Dan said yanzu tagane fa iza,

Aranar da akakawota harsukayi sa insa da hajir taga  kamar tasanta  Ashe itace?


Tadai daure race",


Haba yazan turomaki ita alhalin kina bukatar kulawa",


Fa iza race to yanzu turomin ita,


Jawaheer tadauko munubiyya takawomata,

Ta kunna talabijin sukafara kallo,


Hajir tafito cikin shigarta Tamata masu duniya,

Tana taunar cingom said kara take abakinta, tadubi faiza tace,


Au hajiya ta boys ansamu fitowa?


Saita kece da dariya tacigabadacewa,


Amarya ta ango, Amarya mai dadin tuwo,


Alalace. Itama fa izar tace fadi ki kara babu kuskure azancanki,


Hajir tadubeta adage race Ashe bakikiyayaba?

Tomaida hankali ki fadamin wacce bats gamsheniba,

Yanzu jikinki yabaki lbr,


Fa iza tace Shaka?


Sosaima kuwa me ganewace bakiyi,

Bukatarkice ba ayi basaiki kauceba,

Indanice ke tuni zanyima kaina kiyamullaili,

Intafi inda ake bukatata,

Kodayake aikina dagaskiya gida irin wannan Ai ajuri wahalarsa, kodan samun nasiyawa tsofaffi kunu,

Saidai ke dakamaar wuya,

Yadda kikazo haka zaki koma,


Mijinma saidai ido atsakaninki dashi,

Kodayake bake kadaiba harda yar korenki, 

Duk zaman wucin gadi kukeyi,


Dams nasan dahaka akwai ranar da zansawo fatsata acikin  dohon ruwa mai yawan kifaye, Wanda duk wacce ta yarda fatsata tashakomin wuyanta sai  ta gwammace WUKA A MAKOSHInta".


Hajir!",

Jawaheer takira sunanta suka dubi juna,

Jawaheer race,

Wata wainarde amma bata wakeba,

Karki kuma sakoni acikin shirginki,

Sakanwarkidai gatanan,

Amma in wlh nafi karfinki,

Idan kuma kin MUSA yanzu innuna maki bambanci abayyane",


Hajir race A'a bazamu had a jikiba saboda me kisan mummuke zanuimaki,

Itako wannan jibgarta zantayi tamkar aikakkiya,

Duk dasannu zaku kama gabanku kubarni da hubbyna muna holewa".


Fa iza tace idanko har haka takasance to kiruke aranki nice ajalinki".


Hajir tace haba yarinya aini naci dubu said ceto,

Dan haka kitaka ahankali,


Lamido yayi sallama yashigo,


Hajir tayi Sauri tatashi tatareshi cikin firirita da is a,

Ta is a gareshi,

Tare da rungumeshi, tasakarmasa Sumba abaki taja hannunsa zuwa sashensa,


Tabbas hajir ta murda kambunta, Dan babu kowa azuciyar lamido said it's,

Hatta jawaheer yanzu bats gabansa,bare kuma amarya fa iza,

Amma ita hajir tahandame kwanakinsu suka,Kasai,


Jawaheer ko taxa idone sabodatasan kwanakin amaryane  tahandame tabarta,

Tayi kwanaki bakwai, idan itakuma fa izar tanemi hakkinta to shikenan,

Idan kuma batanemaba to da anti bakwai zata karbi  nata girkin,

Dan itakam bazata Shiga hakkin kowaba,

Dan haka kuma  baza ashiga nata hakkinba,


Fa iza tadubi jawaheer tace ,

Nan me sashin maigidan?


Tace eh nanne",


Fa iza ta mike  tsaye yanufi sashen,


Lamido yana kankame  da hajir tasawo kai,

Wani takaici yakamata ganinsu datayi ajone".


Yadago kai yadubeta yatashi tsaye,

Yakamo hannunta yahada ta dajikinsa,

    Aduk sanda sukayi ido hudu da ita 

Yanajin wani irin santa mai zafi,

Saidai babu wata sha awarta atareda dashi,

Wannan kam said hajir ita kadai yake son kasancewa da ita baya kuma gajiya da ita".


Yace fa iza ya gida?


Tayi far da idanu race lafiya klw".


Yace kina bukatar wani abune?


Tambayar tabata mamaki ta kuma bata mata rai matuka,

Tadubeshi tace 

"Inada bukatar ka ko kamanta matsayina agurinka?


Yace A'a kije zanzo said muyi maganar".


Ahasale tace babu  India zanje,

Wait wane irin aure mukayi saikace auren kiyayya?"


Yace ba haka bane  kidaije zanzo  idan kuma kina bukatar wani Abu to fada min".


Fa iza tayi shiru tana tunanin miryar hajir  ta tsinkayo tana fadin,

"Idankudi kike bukata ki fada masa zaiyimaki yayyafinsu,


Idanko shi ki ke bukatar,

To said incemaki zaki mitu datakaicin rashinsa,


Kikarbi kudin Kasai,

Saboda kudi ba abinda basayi saidai Abu daya",


Tana fadar haka tana hannun lamido suka Shiva uwar dakinsa sukabar fa iza zaune,


Takaicin magan ganun da hajir tafadamasa,


Bisa tilas tatashi tabaro sashen  takoma nata,


Zama tayi tana tunanin bakincikin data girba,

Azamanta datayi  agidan lamido,


Tanisa acikin tunanin,

Cantasoma jin karar takin hajir ce tashigo daga bakin kofa tatsaya tace,


Kinsan abinda zangayamaki?


Daga yau said yau,

Idan kika sake taka sashen lamido,wlh said kinraina kanji,kindaiji abinda nace dakeko?


To idan kudi kikeso kizo kifadamin zan amsarmaki,

Donhaka in kunne yaji jiki ya tsira".


Tajuya tabar falon.






Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA AMAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣0⃣






Na 

Maman Sadeeq





"kwana bakwai hajir na handamar kwanan amarya,

Azaton jawaheer hajir tace da ita wani abu,saitaga shiru batace da ita komaiba,


Tashiga shirin tarar D dinta,


Lolacin dayadawo hajir takasa ta tsare tabi ta kankame lamido,


Jawaheer tashigo tace D kayi wanka kuwa?


Yace "A'D, zoki hadamin ruwan wankan".


Hajir tace toni zan koma ciki saida safe kenan?


Yalangabe kai yace Yazakiyi kimin haka,

Bayan kinsan idan babu ke akusa dani bazan iya runtsawaba?


Hajir tace bagamatar kananba aizatayimaka komai.


Kafin yabudi baki jawaheer tafito daga andakin tace mashi gasucan,


Yashiga bandakin, 

Hajir tafito tana dariyar mugunta,


Jawaheer tahadomasa abinci,

Yaci saidai babu wata hirar kirki atsakaninsu,

Daga karshema babu wata alakar auratayya datashiga tsakaninsu,

Dan bayajin kowace mace aransa sai hajir".


Datayimasa magana saiyace bayajin dadi,

Tasani sarai yadai fadane kawai,


Saiyanzu tagano abinda hajir take nufi,

Babu shakka bokanta yaci kudin databashi harma dakari,

Dantayi nasarar kawarda hankalin lamido daga kanta,



Saidai zata iyacewa nasarar ta wucin gadi ce,

Nanda dan lokaci zatanemeta tarasa,

Da ikon Allah saitadawo dashi acikin hayyacinsa,

Tunda dai zaici abincinta aitazo gidan sauki,

Ayar Allah zatayi tasiri akansa fiyeda surkullen da hajir tamasa".


Tayi niyyar dawowa sashenta, kuma taga ai hajir zata iyaganin lagonta,

Dan haka tayi kwanciyarta adakin lamido,


Tunani tayi tayi hartadauki lokaci batayi barciba,

Can taga lamido yatashi cikin sanda yafita,

Azatonshi bacci take,


Dasauri itama tatashi ta rufamasa baya,


Sashen hajir yanufa tana biye dashi har ya isa dakin hajir,

Dan tsayawa tayi dan tajiyo abinda suke fada,


Jitayi sun kwashe dadariya harda kyalkyatawa,

Zuwacan kuma saitaji shiru,


Wani takaicine yadamki zuciyarta kai tsaye ta nausa kanta adakin hajir".


Da ace baha intarta dukayiba datayi nadamar ganinsu  datayi ahalinda  suke,

Saboda tana matukar kiyaye dokokin ubangiji,

Amma yanzu bataji ko dar ba,

Shikam haushi yakamashi,

Don me zata shigo masu awannan lokacin,

Kuma taga halin dasuke ciki,

Shine tashigo maimakon takoma baya".


Rigarsa yasa baiyi wata wata ba ya tsinketa da mari,

Yakuma hauta da fada kamar ya ari baki ya hada,


Batace ko uffanba, saidai tadafe inda yamareta datayi,


Abudaya data hakikance dashi shine hajir ta tasamo lamido fiye da yadda take zato,

Dan haka tajuya tabar dakin, tanaji hajir na kyalkyala dariya tare da jan tsaki,


Haka takoma sashenta zuciyarta na radadi,

Tadubi agogo karfe ukku saura,

Dan haka tafada bandaki tadauro alwala,tatayarda sallah,

Bayantagama laziminta saikuma ta jero addu o inta  masu matukar tasiri tareda rokon Allah ya tarwatsa mata wannan sabon Al amarin dayasameta".


Bayan tashafa saitadauko Al qur ani ta soma karantawa,

Batatashiba saida aka kira sallar asuba,

Tayi raka atul fijir, kana tayi ta subahi,

Baccine A idonta don haka tahau gado batajimaba bacci yayi gaba da ita sai wajan gima tatashi".


Tuni msi aikinta tashirya yaran suntafi makaranta,


Dan haka tana tashi tafada bandaki tayi wanka,

Tayi karin kumallo,

Takira wayar lamido,

Tadade tana  kara tamkar baza adagaba, zuwacan yadaga,


Shiru yayi bai yimaganaba,

Ita tafara cedashi "D, kanakan layi kuwa?


Eh inajinki,

Yace da ita cikin daurewar murya,


Tace barka da asuba,

Yace barka kadai,


Lallai lamarin mai girmane, tafada azuciyarta tace,

Dama dan insanar dakai zanje gida nasan yanzu ka tsufa a ofis,


"saikindawo, yafada tareda kashe wayar,


Tadubi wayar tayi murmushi tasaka hijabinta tarufe sashenta tafito,


Afalo ta iske hajir da fa iza, 

Tadubi fa iza tace amarya kin tashi lafiya?"


Fa iza tace lfy klw maman baby,

Yanzu nake cewa ko lfy baki fitoba?


Jawaheer tace wlh baccine yadebeni bantashi da wuriba".


Hajir ta dubeta asheke tatabe baki,


Fa iza tace kamarma shirin unguwa kikayi?"


Jawaheer tace eh gida zanje,


Hajir ta bushe dadariya sannan tadubi jawaheer tace,

Haba malama kedai fadi indazakije,


Ashe karyar banzace dakikace kissa tafi magani tunda gashi zakifita neman maganin?


Saidai kin makaro domin ni nayi nisa,

Kirule kissarki nikuma in ruke maganina dasannu za atantance waye keda WUKA A MAKOSHI,

Tsakanin nidake,

Wannan abin ma dakikagani ajiya shafar maice, bakiga komaiba,

Kodayake kema kinbi sahu saimu goga afagen daga".


Jawaheer tace ko shakka babu kuma nafadamaki kiruke  aranki kissar nan dana fada maki tafi magani tasiri,


Kuma ayanzu fitarnan wlh takice babu boka babu malam,


Sainanuna maki tasirin da kissa take dashi, 

Sati daya zanbaki tak!

Kikoma lissafi tundaga yanzu,

Natafi sainadawo".


Tasakai tabar gidan, 


Hajir tasake bushewa dadariya, tahuro cingom dindake bakinta,

Tayi kwai tace, 

Dasannu daya bayan daya duk zaku ci ubanku,


"ko kuma ubanki ba".

Cewar fa iza,


Hajir tadubeta tace "Ubana?"


Cikin dakewa fa iza tace eh ubanki bana gwal bane dazaifi nawa ubanba".


Hajir ta shako wuyan fa iza, tasoma jibgarta,

Ko kawa sukayi sosai,

Saidai fa iza tarama bugunda hajir din tamata ba ,

dan karfinsu badayaba,

Dole kowaccansu takoma sashenta dan sauya ksyan jikinta".






Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣1⃣




Na 

Maman sadeeq






GODIYA

Dole ingode maku masoyana, sakonninku yana samuna, nagode dayanda kuke nuna kulawarku agarene,

Kunzamo abin alfaharina,


Nagode Allah yabar so da kauna❣💔❣💔❣💔❣💔❣💔❣💔❣❣💔❣





"Yadubeta cikin bacin rai yace,

Ina yarinyarnan  tatafi  baki saniba?


Tayamutsa fuska tace,

Tayaya zakatambayeni inda tatafi?


Mahaukaci har wani wurin zuwane dashi?


Kumama aiba gadintaba kasaniba,

Yaushe zansan lokacinda xata zare jiki tafita,

Babu mamaki tashiga gari".


"wani wawan mari yadauketa dashi ,


Balaraba ashe bakida mutumci?


To bari kiji wlh narantse da girman Allah, idan har baki fitomin da zuhraba,ina maitabbwtarmaki da igiyoyin aurenki sunfara rawa,

Suna gab da tsinkewa,


Rashin zuhra rashin aurenkine,

Dan haka duk inda kika shiga da ita , kije kidawo da ita,


Ai Aisha tacemin tagamu dake da zuhran,

Wato tunda kin nuna adawarki tinfarko akan zama da yarinyar shine kika jata kikaje kika batar da ita,


To maza kije inda kika kaita kidawo min da ita,

Idan kuma babu ita karki dawo min nan,

Kiwuce gidanku zambiyoki datakardar sakin aurenki".


Balaraba tasauke hannu daga inda yamareta tace saime dan kasakeni?

Sai akace numfashina yayanke aduniya,

Indai akan tsinanniyar yarinyarnanne saidai kasakeni dan wlh bazan bitaba,


Sani yace bazakibitabako?


Tace eh".


Aisha tayi sauri tace A'a baba karkuyi haka,

Dan Allah mama fadamin indatake ni inje indawo da ita".


Balaraba tace rufemin baki bakar manafuka ,

Bazan fadaba".


Ahasale sani yashiga dakinsa jimkadan yafito da takarda ahannunsa yamikawa balaraba,

Saidai ta kasa amsa dan bata dauka dagaske yakeba.


Ganin taki karba yasa ajiyemata akasa,


Tunowa tayi dagidansu nagado, yazama kufai,

Batada indaxata zauna,

Saidai akwai wata kanwar babanta itakuma akauye take,

Itakam ayanzu baxata iyaba rayuwar kauye,


Hannu tadora akai takurma ihu tareda rike rigar sani tana bashi hkr,


Ai yanzu nakin Alkalami yaruga ya bushe har an dauke alkalamin babu kuma abinda zan iya yimaki yanxu, cewar sani,


Balaraba tace wlh zamfadamaka inda balarabar take tana kundila can kan bola nakaita,


Dasauri sani yanufi kundilan saidai wayam,

Yadungabin bola bola amma baigantaba,


Itakuwa balaraba kayanta tashiga hadawa, tafito bakin titi saidai tarasa inda zata dosa daga karshe  saitanufi wurin kawarta lubabatu".


Lubabatu tadubeta tace akan  mahaukaciyar  yasakeki?


Balaraba tace wlh bantaba zaton sani zaimin hakaba,

Gashi niyanxun bansan ba inda zan nufaba".


Lubabatu tace karkidamu kiyi zamanki anan,

Bari Raben yadawo sai incemashi nan zaki zauna har Allah yakawo makimiji  kiyi Aurenki".


Balaraba tace dako kin taimakamin,

Dan bani dawurin zuwa sai kauye nikam natsani kauye".


Lubabatu tace gadakin fa iza nan kishiga ciki,

Idan anjima xanje gidan fa izar naji shiru, har yanxu bata fara aikominda komaiba,

Idan na amso zandan naki wani abu saiki sayi laidar tsakar daki da labule".


Balaraba tayi godiya,


Karfe uku lubabatu tashirya tatafi gidan fa iza,

Fitarta badadewa Rabe yashigo,

Ganin balaraba adakin fa iza yasa yatambayi ba asi,

Balaraba tafadasa abinda yafaru, tsakaninta da sani,


Rabe yayi shiru, zuwacan yace da balaraba,

"To inhaka ne me zaisa bazamuyi abinnan ba kawai?"


Balaraba tace mekenan?"


Rabe yace idan babu damuwa murufawa juna asiri, kinga saikiyi zamanki anan dakin, 

Kinga dama lubabatu kawarkice, koyayakikagani?


Balaraba tace haba rabe,

Baka gudun musamu sabani da lubabatu?


Rabe yace to shikenan nidama awannan lokacin nake da niyyar kara Aure,

Idan ma bakeba to wata zan nema dan haka mubar zancen kawai".


Jin haka yasa balaraba tayi sauri tace to na amince tunda ba haram bane".


Rabe yace to idan kingama idda saiki sanar dani,

Ammakiyi shiru da bakinki,

Kada lubabatu taji ayanzu sai angama komai,

Dan idantaji ayanzu zata iya hana ruwa gudu".


Balaraba ta jijina kai tareda shigewa daki".


*****************************

Zuwanta gida tasamo sirrikan karya surkulle daga mahaifinta,kasan cewarsa masani akan ilimin addini, tadawo gida,


Bata gajiba ta shirya madhi abinci wanda tasan yana so,

Tahada abin sha,kunun aya da kuma sobo saboda tasan yana so,


Tahadasu da ayoyin Allah wanda zasu karya surkullen dake jikinsa,


Lokacindayadawo tahadamasa abincin dukda dauke kanda yakeyimata bai hanashi ciba,

Saboda kunun aya da sobon daya gani  yana cikin cin abincin,

Hajir tashigo da sauri tajanye  abincin daga gabansa,

Yadibeta yace ya akayine hajir?


Tace hubby wannan abincin banyardaba dashi, 

Kabarshi kazo inhada maka wani".


Jawaheer ta mike tsaye tace saidai kijirayi zuwan ranarki,


Karya wadda namiji bai isarta,

Bantabaji ba ko atarihi mace jarababbiya irinkiba".


Hajir tayi murmushi tace zanko nuna maki halin karnukanci, domin nasha gabanki,


Lamido yace kinga hajir ajiye min abincina kuje can kuyi hayaniyarku".


Cikin mamaki tadubeshi jin abinda yafada tace,


Gaskiysa bazakaci wannan abincinba, daboda ban aminta dashiba,


Jawaheer tadubi lamido tace "D bai ishe kaba abincin?


Ya gyada kai,

Tamikomasa hannu yakamo, tace zomuje in hada maka wani babu mamaki itama tana bukata".


Bai gardamaba yabi bayanta sula nugi sashenta,


Tana tsaye da faranti ahannunta suka fice,

Ko shakka batayiba jawaheer tana gab da rusa mata asiri, dan haka yazama dole tasan matakin dauka,

Tafito daga sashen lamido tanufi sashenta,


Dai jitayi ankece da dariya,

Tajuyo  taga fa iza ashe ta lura da duk abinda ke faruwa,


Hajir tadawo baya  tadubi  fa iza,

Faiza tasake ballewa dadariya,

Wuyanta tadamka tareda fadin ubanwakikewa dariya?


Ubanki nakeyiwa dariya,

Cewar fa iza,

Idonta rufe ta shiga jibgarta,

Cikin rashin sa a ta gotata ahannu,


Wata kara tasaka wadda tasa su jawaheer fitowa da sauri,

Ganin fa iza dage da hannu yasa jawaherr ta kamota,

Shiko lamido kallondu yake cikin rashin fahimta,


Jawaheer tace "D inaganin kamar da akwai matsala ahannunta kadauketa kuje adubata,


Yace badai yanxua dan nagaji saidai ko gobe,


Tace haba "D kadai daure kakaita,


Yace toshikenan tunda kince  akaita".


Yadubi fa iza yace taso muje".


Wajan gyara yakaita akagyaramata hannun suka dawo gida, 


Sashen jawaheer  ya wuce  kai tsaye daga karshema can ysyi niyyar kwana,


Itako hajir tazo dakinsa dan taji shiru bai biyotaba, saidai baya dakin,

Tazauna jiransa saidai shiru, 

Atake tagane jawaheer tayi nasarar watsamata shiri,

dolene takoma ga bamaguje gobe dan atara kusa.


Itako jawaheer  bayanta sauke nauyin da ke kanta namaigidanta,

saisuka fada bandaki  sukayi wanka,


Yadubeta yace,

wai "D laifin menayimaki kika shareni kwana biyu?


Tayi murmushi dan Allah yaso karjato dashi bisa hanya,


Tace kaxo mu kwanta barci nakeji".


Can wurin karfe ukku tatashi ta dauro alwala ta tada sallah sai gab da asuba  takoma ta kwanta,

bayan ta tofe lamido da laifafan addu o 'i,


Washe gari jawaheer tashiga sashen fa iza ta dubata  tadawo falo tazauna,


Hajir ta dauko ado ta nifi gidan laila sanata,


Jawaheer tayi murmushi  tareda godiya ga Allah dayabata rinjaye akan hajir.








Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪

5⃣2⃣




Na

Maman sadeeq








"Sallama ta doko ta amsa tareda yimata sannu da xuwa,


Tawashe baki suka gaisa,

Jawaheer tace banganekiba?


Lubabatu tace eh gaskiya bazaki ganeniba nice uwar fa iza".

Jawaheer tace oh Allah sarki zomuje inrakaki sashenta,


Lubabatu tabi bayan jawaher har cikin dakin fa iza tace,

Umma kece agidan?


Lubabatu tace eh nice tunda kimmanta da Alkawari,

Dama ninasan saikinmin butulci,

Togani nazodakaina hadomin kan abinda ke akwai,


Fa iza ta dubi lubabatu tace wlh umma nayi dana sani akan aurannan danayi,

Bani ko tantama Alhakin yarinyarnanne yake bibiyata,



Tunda nazo gidannan bantaba tsintar fatin ciki ko si dayaba,

Yanzu dubi hannuna agoceya ke".


Matarsa ce tahanani sakewa,

Nikam dai nagaji wlh auren ma  nagamashi saiyasakeni".


Lubaatu tace wacece wadda tamaki wannan aikin wadda tarakoni?


Fa iza tace ba ita bace".


Lubabatu tace tashi likaini inda take,

Ni indaukarmaki fansa,

Wlh bazan yardaba dama inada cikinta yau zan haifeta,


Fa iza tace A'a umma kada azo ayi abin kunya,

Kibarta kawai indai mijine to zan barmatashi".


Lubabatu tayi sauri tace badai yanzuba, 

Aure yanzu kika somashi,

Yomekenan idan kika tafi yanzu?

Aisai mun warci abinda muka warta,

Kuma kedama sondakikke masa kodama laryar banzace?


Fa iza tace umma dan bakisan irin  bala in da ke gidannanba,

Babu yadda za ayi mu cimma burinmu daga ni harku domin matarsa tayi mana zarra".


Lubabatu tace karya takeyi kedai bakiyi amfani da kwalli da turaren nanba?


Fa iza tace wlh umma ina yi kedai kawai munzo inda aka keremu".


Lubabatu tace yanxu akwai wani abu agurinki?


Fa iza ta gigiza kai babu komai agurina sai takaici".

Lubabatu tace toni zansan matakin dauka,

Natafi saina dawo".


Fa iza dai bata tankaba harta fice daga gidan,






Kina yadda kikeso gimbiyar lamido".


Cewar laila sanata,


Hajir taja tsaki tace, 

Laila tashi muje ina san ganin bamaguje,


Laila tace incedai lfy?


Inafa lafiya tsinanniyaratarcan tafara rusamin shiri tunba ajeba ko inaba".


Laila ta zaro ido tace kamar yaya?


Hajir takwashe komai ta sanar da ita,

Laila tace tashi maza mu wuce,



Takorowa bamaguje bayani yayi yan tsubbace tsubbacensa,

Zuwacan yace da hajir, 


An bata Aiki,

Ayanzu kuma aiki bazaiyi tasiriba inba kin kauda mai bata aikinba,


Ayanxu komai ya lalace,

Saboda addu o indatakeyi, 


Kawarda itane kawai zaibaki damar sa ar mallakar mijinki,

Dan haka saikisan abinyi".


Suka dubi juna itada laila sanata sukace yanzu mainene abinyi?


Bamaguje yace akwai maganin da zaki buba a abinci ko kuma guba,

Yazamodai kin kasheta tabar duniya".


Laila tayi sauri tace ai hodar da ta amsa ta nanan zatayi amfani da ita".


Yace zaifi sauki,

Saidai zan kara gargadinki, dakada kiyarda ki shaki hodarnan, 

Dan idan kika shaketa to kema zaki mutu,


Laila tace zatakiyaye".


Dahaka sukabaro dajin da bamaguje yake,

Suladawo gida,

Laila tace,

Wai ita amaryar yayakuka kare?


Hajir tayi malalacin murmushi tace,

Ai yadda kikasan jaka haka na maida ta,

Dan matsayinta bai kai yadda zamu jada kafada da itaba,

Saidai ido tsakaninta daamido,


Kuma alurardanayi itama yan biye biyene tayi tasamo kan lamido,

Saidai sanin da batayiba ni uwartace koma kakarta akomai,

Laila tace to yanzu takan wazaki fara?


Hajir tace yo ga wacce taruguzamin shiri aikema kinsan takanta zamfara,

Ke har diyan sainaga bayansu".


Laila tace to kidaibi asannu".


Hajir tace karkiji komai uwar dakina sainaxo".


Sukayi bankwana hajir tanufi gida cikin murna".


*********************************

Tawatsa mata ruwan afuska,

Lokacin dataji ta soma surutun sokanar,

Tadago kai tadubeta,

Saidai bata kuma cewa komaiba,


Ganin tayi shiru yakumasa tadauki ruwan ta kuma watsamata,

Daga karshema saita kelayamata ruwan aka".


Mamakine yajamata ganin hayaki nafita taka fafen gashinta,


Yalwati tayi tsaye tana kallon ikon Allah,

Hayakin yayitafita da sauri,


Ganin haka yasa ta daurara da xuba ruwan Addu o in,


Kamar minti biyu hayakin na fita zuwa can yadaina,


Yalwati tasake zuba ruwan akanta saidai babu yhayakin,


Wata atishawa zuhra tahau jerowa,

Tamkar hanvinta zai cire,

Xuwacan kuma sai ta limshe idonta tatafi luu kamar zata fadi,

Yalwati tatarota takwantar da ita abisa gadonta,


Wasu addu o i yalwati ta tofawa zuhra,


Yalwati tayimata kyar da ido tana tausayawa zuhra,


Kamar minti biyar zuhra tatashi  daga dan guntun barcin datayi tareda fadar,

~Alhamdu lillahillazi ahyana, ba adana amatana, wa ilaihinnushur~.



Tadubi yalwati kuma tadubi indatake kwance tace inna maiyakawoninan harnayi bacci?


Yalwati tace zuhra kaddara ce takawoki harkikayi barci".


Ina ya abbas koshine yadaukoni dan yaji baba Rabe zaiyimin Auren dole?

Idanko hakane ya abbas yajyautamin,

Kuma bazan koma gidan baba Rabe ba".


Tadubi yalwati tace inna dan mutumcin Annabi larki bari a aurardani gawanda baya sona,

Tafadi haka cikin muryar ban tausayi,


Yalwati tace Allah nagodemaka dakataimaki wannan baiwar Allahr taka Allah kayi dubun salati ga shugaban halitta ,hamdan kaseeran".


Zuhra dai sai bin yalwati da ido take,

Yalwati ta dubeta tace kinsan abinda najeso dake?


Tace A'a".


Yalwati tace sonake kiyi godia ga Allah kuma kiyi salati ga annabin rahma,


Zuhra ta bi umarnin yalwati,

Saidatagama sannan tace inna mainene hikimar yin haka?


Yalwati tace kibari babansu abbas yadawo zakiji kome kenan".


Zuhra tayi shiru tana tunani,

 malam mande  yayi sallama zuhra ce ta amsa masa,

Abin yabashi mamaki yace zuhra?


Tace na am baba".


Shima godiyar yayima ubangiji kanta yashiga duhu, batasan abinda sukeyima godiyarba".


Tadubi malam mande tace,

"baba inna tace nabari kadawo zaka fadamin wani abu?


Yace sosai zuhra".


Yalwati tayi tsaye tana kallonshi tace "to yi masa arziki ya huta tukunna".


Zuhra tayi murmushi ta amshi laidar da take hannunshi, takaimasa daki,


Bayan ya natsu yakwashe labarin komai  akan haukan datayi, 

Yasanar da ita,

Saidai bai fadamata watsi da yan uwan ubanta sukayi da itaba".


Tayi shiru tana tunanin yadda tayi hauka acikin rashin hankali,


Lalkai sumalam mande sunyimata halacci iya halacci,

Dolene tayimasu  biyayya tamkar su suka haifeta,


Hamza da mubarak suka fadomata azuciya,

tadubi malam mande tace baba ban san da abinda zan saka makuba akan halaccin dakukayimani kaida inna,

Saidai ince Allah yayimaku sakamako dagidan Aljanna,


Malam mande yace amn zuhra Allah kuma yajikan Auwalu da Aisha".


Tayi murmushi tace "Amn baba".



"goron menene haka rabe?"


Yayi murmushi yace na daurin Aurene".


"Nawa?"


Yace  nawa"

Kan ubancan wannan shine karya,

Wlh nina wuce kayimani kishiya,sake dai......

Wai tukun ma da fari wace tsinanniyace ka Aura?


"A'a karki zageni mai nayimaki?


Lubabatu tace balaraba bangane abinda kike nufiba?


Rabe yace totaji kin bankomata ashar shiyasa tafadamaki karki kuma zaginta".


Lubabatu tace balaraba dama kun shiya cin amanata?


"A'a kar kice haka meyene nacin amana anan,

Dadiro muka daura?


Aurene kamar kowane aure, 

Dan haka kada kikuma cewa naci amanarki,


Tadubi Rabe tace honey taho muje inyimaka tausa".


Takama hannunsa duka shige daki, 

Sukabar lubabatu atsaye kamar andasata,


Matsala tazama biyu kenan ga tata ga ta fa iza menene abinyi?


Abinyi dai kudi sune jagaba akomai to babusu,

Wani tunani tayi saita dariya tashiga dakinta tana murna".




Muje zuwa😛😛😛😛😛

Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣3⃣





Na

Maman sadeeq




"Tadubeshi tace,"D, inaga gara kuyi maiyywuwa dawannan baiwar Allah nan,

Idan ko bahakaba ina mai tabbatarmaka ranar gobe zakatashi  acikin maza marasa Adalci,masu shanyayyen jiki niko bazanso hakaba,

Garakasan abinyi".


Yakamota yarungume yace "D, zan iya ce maki bansan  ya akayiba,

Saijinayi kince Wai matatace,to A'ina tazama matata,

Nidai inaga zankirata imbata wani abu in sallameta kawai,


Jawaheer tace tokazauna dai kai da ita idan zata iya zama dakai,

Idan kuma bazata iyaba sai kusan yadda zakuyi".


Yace ko in wakiltaki ki tambayar min ita danni banaso tana rabata?"


Jawaheer tace A'a nibazan shigaba,

Wake dhiga tsakanin miji damata?"

Kaidai zakaje da kanka".


Yace to Allah yakaimu goben...."D,fa bacci najeji".


Tace to kayi baccinka mana".


Yace hakama zakice?"

Tace tuba nake my D, muje".


Washe gari tunda safe ta lalubo hodarta tayi shiri ta fito daga sashinta ta nufo sashin jawaheer,

Saidai adatse tatarar da sashen, saita juya akalarta sashen fa iza, 


Cikin sa 'a tasamu sashen abude,


Tana barci tana ta sharar barci,

Hajir tatoshe hancinta ta hurowa fa iza hodar twmayo baya dasauri, takoma dakinta,



Fa iza tashaki hodar sosai,

Firgigit ta farka sakamakon radadin da jikinta yakeyi mata,


Ta bude tarasa yadda zatayi, dasauri tafada bandaki tawatsa ruwa saidai babu  wata afuwa data samu".


Takasa zaune takasa tsaye,

Daga karshe saitasaka hijabinta ta fice daga gidan tanufi gidansu,


Itako jawaheer sai karfe takwas ta bude sashenta ta shirya yara sukatafi makaranta,


Hajir ko sai goma ta fito  falo tazauna tana taunar cingom,tadubi jawaheer taja wani tsaki taredayin kwafa,

Jawaheer dai bata tankaba".


Tace Rabe tunda dai har kuka iya cin amanata to nikam wlh bazan zaunaba,saidai kasawwakemin,


Balaraba tace ta kwana gidan sauki nidama aka nafi so,


Ta dubi Rabe tace inaga kabata jan katin datake bukata".


Rabe ya dubi lubabatu yace kada muyi haka lubabatu,

Kiyi hkr kawai zan kwatanta adalci".


Lubabatu tace idan harko kana so in zauna saidai kasaki waccan bitulun,

Wlh baxan zauna da itaba danni inada gidan uba baizama kufaiba".


Balaraba tayi saurin cewa kada ki kuskura kiyi min gori,

Aini tunda na aure maki miji naga gurin zama dan haka kafafuwa zan mike".


Rabe yayi juyin duniya lubabatu takiya,

Yarubutamata takardar saki daya yabata,


Balaraba ta rangada guda, 

Tadubi rabe tace,

"honey zo muje mudan huta".


Takama hannunsa suka shige daki,

Lubabatu tayi murmushin mugunta tashiga daki,


Duk wasu kudi da Rabe ke takama dasu saida tatattarosu ta kulle,

Sannan tadau akwatin kayanta tafito tsakar gida  tace, 

Kufito muyi bankwana ni zan wuce".


Balaraba tace basai mun fitoba tunda yasallameki kije abinki kawai".


Lubabatu tayi murmushi tace to saduwar alkairi,

Taja akwatinta tayi gaba".


Fitarta bada dadewaba fa iza tashigo kai tsaye dakin lubabatu ta nufa saidai  ata gantaba, takira lambar libabatun saidai akashe take,

Ga azabar da takeji sai karuwa takeyi, 

Dan yanzu ji takeyi numfashinta yana barazanar daukewa, saitayi da kyar take samun jawoshi,


Takwashe tsawon awa hudu batagaba lubabatu tadawoba,

Abinda takawo wa ranta shine lubabatu tatafi karbomata taimako,


Wani tsaki taja itakam tagama zaman Aurannan,tafito tsakar gida ta zauna,


Balaraba tafito itada rabe,

Sai ganin fa iza sukayi,

Rabe yace ke fa iza ya akayine?


Tace baba banida lfy".


Dan bakida lfy sai akace kidawo gida?

Ai zaman auren kenan, cewar balaraba,


Abin yabata mamaki ganin balaraba da babansu,


Rabe yace shi mijinnaki yasan kin taho gida?


Tayi saurin cewa Eh yasani".

Dan tayi alkawarin bazata koma gidamba".


Rabe yace to shikenan".


Yadubi balaraba yace toni zan fita,

Tace to "honey karkadade,


Honey faiza tamaimaita sunan abakinta,

Wai meke faruwa?

Tadubi balaraba tace Anti wai ina umma taje?


Balaraba tatabe bali tace saki tanema kuma ansaketa,

Tatafi gidan tsoho mai dattin hula".


Fa iza tazaro ido tace akan wane dalili baba yasaketa?


"Akaina yasaketa, cewar balaraba,

Saiyanzu fa iza tagano abinda ke faruwa,

Wato cin amanarta tsyi balaraba ta auri babansu,

Shiyasa  lubabatu tayi tafiyarta,

Itayanzu yaxatayi, 

Gawayarta akashe,

Idanko hakane tasan zata sha wuya agurin balaraba,

Gashi itakuma yanzu lafiyarta take nema".


Wai D kasan inda matarka tatafine?

Duk yinin yau banganta talekoba?


Yace nashiga dazu nima ban gantaba".


Jawaheer tace aisaikaje gidansu kagani, 

Babu mamaki tagaji da abinda kakeyimata,


Yace ni ainagama yankewa kaina hukunci gatakardartanan, dama ita nashiga imbata,

Yanzu bari inje gidansu inkaimata,


To Allah shi kyauta cewar jawaheer.








Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣4⃣



Na

Maman sadeeq





"yayi fajkin akofar gidansu yayi sallama Adnan ne yafito,

Suka gaisa yafadamasa yana son ganin fa iza,

Yashiga yakira masa ita,


Wqni kallo ta watsomasa, sai huci takeyi,

Gakuma kumburi da jikinta yafarayi,


Yadubeta da kyau yace yagida".


Bata tankamasaba, 

Yasake cewa bakida lfy ne?


Dakyar ta iya bude baki tace kaga kafadi abindayakawoka,

Nidai zaman gidanka ya isheni dan bazan komaba,


Yadaga kafadunsa yace babu matsala, yazaro takarda yamikamata,

Yadauko kudi masu dama yabata yayi gaba abinsa,


Tashiga cikin gida tamikawa Rabe takardar yace yayi kyau kema kinkashe naki auren tunda uwarki takashe nata,

Kun kyautawa kanku, yanxu zo bani kudinnan dayabaki".


Fa iza tace A'a baba asibiti zanje,


Yau naga yar iska ubannaki?

Yo sai kinbashi su ko in hardeki inkarba".

Cewar balaraba,


Dasauri tamikamasa kudin wannan rashin imani har ina?

Babu yadda ta iya,


Rabe yace da balaraba amshi wannan kudin kidan ibi kadan kikashe wutar gabanki ki ajiyemin sauran adaki,

Ta amsa tare da kashe ido daya tace "honey nagode,

Suka shige daki gaba dayansu sukabar fa iza, 

Da tsayuwa ta gagareta dole takoma tajingina jikin bango,


Agigice Rabe yafito daga cikin daki,

Balarabata  rufamasa naya tana tambayarsa, 


Bai iya tankamataba kudinsa kawai yake tunawa, don ba kananabane sama da miliyan biyar ashe ko dole ya kadu,


Balaraba tace waimele faruwa maga sai gumi kake kamar wanda yahadiyi kunama?


Balaraba lubabatu ta kasheni daga tsaye tayashemin dukiyata tatafi,


Balaraba tazaro ido tare dafadin munshiga ukku,

To mubita gidansu kakarbo dukiyar tunkafin tasal wantarda ita,


Rabe yatashi da sauri sukatafi gidansu lubabatu, mahaifiyarta tace ita twodade rabonta datasakata a idonta,


Rabe yarunga kiran lambarta akashe,


Lungu lungu sako sako dik indayasan lubabatu tana hudda dasu sai yaje amma sai ace batazoba haka yahakura yadawo gida da zummar middin Alkah yahadashi da lubabatu to saiya kusan zama ajalinta


Waini hubby bansan maikake son maidaniba,

Sam kasauya min idan laifi nayi maka kafada min mana".


Yaya mutsa fuska yace,

Idan kinyimin laifi ai zan fadamaki,

Kawai banasan kina zuwa kusa dani,

Dan inajin wani wari duk sanda kikazo wurina,

Inagadai kina zubar da mugunya toki hakura da zuwa wajena,har saikindaina zubarda mugunyar".


Sandarewa tayi atsaye,

Lallai lamarinnan babbane,

Dole tasan abinyi,

Kodayake ai dama bama guje yafada mata saitakawarda mai bata mata aiki sannan zata samo kan lamido".


Tace  yau nice nake wari ko?

Baitankamataba saimatashi yayi daga wajanta yanufi sashen jawaheer,


Wanibakin cikine taji ya tokaremata zuciya dasauri takira wayar laila sanata dan tanemamata mafita,


Bugu daya tashiga tadauka kamar tana jira,


Saidatakwashe duk yadda sukayi da lamido tafadawa laila sanata,



Laila tace tokema hajir maikike jira, 

Bahodar nan tanananba kawai yau ki aiwatar da aiki,


Hajir taja ajiyar xuciya tace karkidamu laila,

Yay yau dinnan matarnan saitabar duniya,

Zan kawo iyakar matsalata dakaina,

To dadaiyafi cewar laila sanata,


Tadawo falo ta zauna tana dakon taga ta inda jawaheer zata billo,

Ganin ranar tatace yada take ganin zatayi komi cikin sauki,


Tagirka abinci  takaimasa,

Dukdatasan bazaiciba kyan kyaminta yakeyi,

Batatsaya saurarenshiba tadawo falo tazauna,


Dare ya nisa,

Takasa barci sai juye juye take natakaicin da lamido ya kunzugamata,

Dole tadauki mummunan mataki akan jawaheer, 

Yanzudai tasan tayi barci,

Tashi tayi ahankali tadauki hodar tanufi sashen jawaher,


Ahankali taturakyauren dakin tashiga,

Kwance tasameta tanata barcinta,tatoshe hancinta,

Tadauko hodar tazazzagata ahannunta,

Saidata daidaici fuskarta sannan ta hura,

Saidai tana hurawa gaba daya hodar tadawo afuskarta tamkar ita aka huramawa,

Gabadaya kamar tayi wanka da ita".


Nandanan wani radadi yaziyarci fuskarta da jikinta gaba daya ,


Motsintane yatada jawaheer,

Tadubeta taga yanda tayi budu budu  dawani farin abu afuska,


Bama wannanba maiyakawota dakinta awqnnan lokacin?

Ko shakka batayi ba Alheri ne yakawotaba,

Dasauri takaranto adduo in tsari,


Hajir ko saimurza fuska takeyi,

Batace da ita ko uffanba,

Tatashi tsam ita da munubiyya ta baromata dakin ta nufi dakinsu Abdul ta kwanta".


Gari nawayewa hajir ta fara kumbura,gawasukuraje da suka fesomata,


Tabaro sashen jawaheer din takoma dakinta,


Jawaheer tashiga dakinta ta ta iske hajir sai soshe soshe take ga wani kumburi da jikinta yafara,

Taje dakin lamido tace yazo hajir bata da lafiya,


Yace maiyasameta?


Tace  wani abune yafitomata afuskarta,


Afalo suka isketa akwance bisa kujera,

Sai nishi take dakyar,


Dasauri lamido  yatunkareta ,sai kuma yatsaya cak sanadiyyar warin da yaji yana tashi ajikinta,

Yajuya yalalli jawaheer yace "D taimaka kikamata mukaita daki".


Tace to,


Takama hannunta itama ayanzu taji warin da lamido ke fada,

Suka isa daki kangado aka dorata,

Saidai wata farar takarda lamido yagani yadauka yawarware,


Wani dogon bayanine takardar ta kunsa,

Yasoma karantawa kai tsaye kamar haka,



Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣5⃣




Na

Maman sadeeq



Wannan takardar tinice da matashiya agareki,*

Idan baki mantaba kinyi mugun kudiri akan bayin Allah,

Hardani dakikaso tumbikemin kai,

Kirabani da raina,

Kikuntatawa yan uwanki,saboda cikar burinki ke kadi,


Idan bakimantaba nakafa maki sharadi,nacewa aduk lokacin dakikayi niyyar cutar wanda bai cucekiba,

To zam bayyana agareki,

Kuma idan nabayyana saina kasheki,

Saboda haka kikayi kudira akaina,

Saidai nadaga maki kafa ne akan waccan(fa iza)

Harkikayi nasara akanta.


Abindayasa nakyaleki kika cutar da ita,saboda itama ta cutardawata akan burinta.


Ayanzu kuma wannan da kikaso cutarwa babu kudirin curar ki aranta,

Danhaka muka juyarda sharrinki zuwa gareki.


Karki wahalar dakanki wurin neman magani,

Danko Allah baya zalinci ahaka zaki kare rayuwarki,


Saidai kina dadama  guda daya,

Zaki iya neman gafarar wanda kika cuta,

Idan sunso suyafemaki,

Idan kuma basu soba subarki da Allah,

Nidai zan iya yafemaki,

Bakuma zan cutardakeba,

Saboda nasan Allah yaharamta zalinci,


Allah yasa kinkoyi darasin duniya,

Dafatan kingane wanda kemaki  JAN KUNNE.


Lamido yadubi hajir yace waye me wannan takardar?


Ko tan tama babu Aljanin kadangarene keda wannan fallasar,

Taganeshi sarai,

Tayi shiru bata tanka masaba.


Ya girgiza kai dan ya fahimci komai.


Yadubeta yace,

Ni bazance kin cuceniba,

Saidai zance kin cuci kanki,

Dan haka daiki tattare kayanki immaida ke gidanku,

Dan nikam bazan iya zama dakeba kina matsayin mushrikaba, don tsafi shirkane".


Jawaheer tace karkace haka kayimata uziri".


Babu wani uziri da zammata kozatace dani batasan me wannan takardarba?


Hajir tayi saurin cewa nasani".


Ta soma rattabo zance tundaga kan malamin dayabata shawara,

Harzuwa kan kadangaren da yalikemata a hannu,

Dakuma sharadin daya kafa  mata,

Har kawo yanzu da komi ya kwabe mata.


Suduka sun kadu da abinda ta zayyana masu,


Jawaheer tace "D, kaga idan kamaidata ga iyayanta zasuga kamar kayimasu butulci,

Kataimaketa anemamata magani".


Babu wani maganin dazanyimata itatajawa kanta,

Kuma ke bakiji abinda tayi niyyar yi akankiba?


Tace saikuma Allah ya gwada mata shine mai iyawa,sai kuma yayarda sannan komai yake tabbata".


Yace to saita koma gidansu zambata kudi taje tayi magani,Allah yabata lfy".














Yakusan wata biyu yana neman layinta amma shiru,

Dan haka yayi niyyar zuwa gidansu,

Dan yana bukatar sudan sheke ayarsu kamar yanda suka saba.


Yayi fakin akofar gidan yatura yaro yayi masa kiranta,

Kakarta ce tafito tace wake sallama da zuwaira?"


Rabe ya gaidata sannan yace nine baba"


Tace saidai taje asibiti tundazu,

Amma haryanzu batadawoba kome yatsayar da ita?"


Tana rufe baki mai mashin yasauke zuwaira,


Rabe yadubeta ganin muguwar ramar datayi,

Gawasu kuraje dasuka fitomata,

Ga lebenta sunyi jawur,

Hakan yasa gabansa yafadi.


Yadubi zuwaira da iska ke kadawa kamar zai kayar da ita yace,

Zuwaira ashe baki da lfy?


Yace meke damunki?


Tamika masa file dake hannunta,

Yakarba yasoma duba rubutun dake ciki,

Idan sa yakafe akan  inda aka rubuta AIDS,gabansa ya fadi ,

Yasaki file din kasa,

Gumi ya karyomasa.

Yadubi zuwaira ko shakka babu kanjamauce ajikinta.

Idan ko hakane shima bazai tsallake wannan siradinba".


Zuwaira tadanyi murmushi da motsatsiyar fuskarta,tadubeshi tace,

Karka damu wannan cutar ba ita bace mutuwa ba sai lokaci yayi,

Idan har zajabi dokokin shan magani,

Nima banbi dokokin yanda yadaceba,

Shiyasa kaga nakoma haka.

Tunda har kana da kudi zaka iya yin rayuwa batareda wani ya fuskanci kana da cutarba".


Takarbi file din tashige gida,



Asanyaye rabe yadawo gidan ya iske balaraba sai jibgar fa iza take yi,akan ta daukar mata kofi tasha ruwa.


Rabe  yace ya akayi ne balaraba?"


Tace imbanda iskanci dan iban yarinyar nan,tadaukarmin kofi tasha ruwa,salon tasakamin kwayoyin cuta?

Kadubi yadda take dada kumburewa kamar ana hura balo".


Tabbas fa iza tayi kumburi sosai har idonta ya nutse cikin fuskarta, 


Shi kansa  Raben yatausaya mata,

Saidai shima yanxu abin tausayine.


Yadubi balaraba  yace dauko mayafinki  muje wani guri,


Bata musaba suka nufi asibiti,

Ganin ya shigo asibiti yasa tatambayeshi abinda zasuyi a asibiti.


Kedai kixo  muje kome kenan ai kya ji".


Wani lab din awon jini duka shiga,


Balaraba kam tashiga duhin Al amarin,saidai tabishi da ido,


Akayimasu gwaji aka basu sakamakon,

Balaraba ta duba ganin abinda ke ciki yasa ta kurma ihu tareda dora hannu  aka ta sona gaza.


Rabe dai yakasa motsawa,likitan dayayi musu awon shiya basu hkr tare da yan sjawarwari,

Dahaka ya lallabasu sukatafi".





Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣6⃣





Na

Maman sadeeq


"Tayi sallama ita da zubaida,

Jawaheer tataso da sauri tatareta,tareda yimata sannu da zuwa,

Bayan sungaisa hajiya tadubi jawaheer tace,


Ashe haka A'amari yafaru da abokan zamanki?


Jawaheer tace "wlh ko hjy,

Allah ne ya gwada karfin ikonsa".


Hajiya takara cewa "To sai akara dagewa da addu a

Allah ya kyauta gaba kuma".


Ta amsa da amin,


Sukatashi, 

Jawaheer tadauko turare tabawa surukarta,

Hjy tace idan yadawo kicemasa baba malam yana san ganinsa,

Yaje akwai maganar dazasuyi dashi.


Jawaheer tace in Allah yayarda zansanar dashi,


Tayi masu rakiya sukatafi,


Lokacin da lamido yadawo tafadamasa sakon hjy,yace,

Sairanar asabar zaije,


Jawaheer tace "D,waikadubo hajir kuwa?


Yace banjeba kuma bazanjeba".


Tace to Allah yabaka hkr,toni ka daure kakaini indubota".


Bazan kaikiba yace da ita".


Tace to ka amince min inje?"


Yace "eh kije ammani baxanjeba,


Yana kallo tasako hijabinta taja jannun munubiyya,tace saitadawo,


Yace adawo lfy,


Taja motarta ta isa gidansu hajir,

Dukda kasancewarsu masu abin hannu,hakan baisa suntallafi rayuwartaba,


Kumburin datayi shiyafi bawa jawaherr tsoro,


Tayi wani irin kumburi,wanda haryasa gabobinta shafewa,gawarinnan yananan saima karuwa dayayi,



Tana zaune acikin wani dan tsukakken daki marar fadi,

Lokacin da munubiyya taganta saita fasa kara tareda kankame mahaifiyarta saboda tsoro dataji.


Jawaheer tadubeta tace sannu hajir".


Ta amsa cikin sanyin murya,

Suka gaisa amutumce,


Jawaheer tayimata fatan samun lfy,


Hajir tace jawaheer kiyafemin dan Allah, kingadai yadda Allah yayi dani,

Tabbas ayanzu nayarda magani aikin banzane,

Gaskiya itake sawa ayi karko,


Dawannan cutar ajikina wlh gara WUKA A MAKOSHI,duniyar nan ta ficemin arai".


Takarashe da zubarda hawaye,


Jawaheer tace kadakice haka,kidauka dama can haka Allah yakaddara,

Nikam nayafemaki,

    Kuma cutarki anemi magani daga Al qur ani za adace da ikon Allah".


Hajir tace babu wanda ya kulani tundanadawo gida,

Abinvi kadai ake bani, babu wanda yadamu da ciwona".


Jawaheer tatausayamata,tace,

Bani ruwa inyimaki tofi,


Tadebo ruwa tabatavtayimata addu o i tamikamata, tace tasha rabi saurankuma tashafe jikinta dashi".


Tayi yadda ta umarceta,

Cikin ikon Allah saitadaina jin ciwon,harma kumburin yadan soma sauka,

Taji dadi sosai,tayi godiya harda kuka,


Jawaheer takawo kudi masu yawa tabata, sannan sukayi sallama ta juyo".



Taso ace tasan gidan su fa ixa itama da takaimata ziyara,

Tonatasan unguwarsuba bare gidansu,


Haka takoma gida tasami lamido tasanar dashi halindatasamu hajir,


Allah yasawake mata"

Abinda yace kenan,

Yayi ficewarsa.


**********************************************************"zuhra ce duke agaban malam mande,

Dayan gefen kuma yalwati ce azaune itama,

Malam mande yace da zuhra ,

Zuhra ki natsu kiji abida zamfadamaki,


Hakika naso Abbas yazamo miji agareki,

Tosaidai Allah bai tsara hakaba,


Alokacin da Rabe yayi  niyyar aurardake yafada wau bazayaba shi auren kiba,

Jin haka yasa malam lawal yace da Abbas yaje  wurin nana yarsa sudaidaita.


To Allah da ikonsa suka daidaita,

Uanzu haka saura wata ukku biki,

Ganin kusancinki da nana shiyasa nazan yardaba ya hadaku ya auraba.

Idan har kin amince toni zan xaba maki miji dan asali,

Wanda zakiyi alfahari dashi,

Idan ka inbari  saikin samu wani da kanki to babu matsala".


Zuhra tayi murmushi tace,

Baba duk yadda kayi dani wlh xanyaka biyayua.


Maganar abbas kuma da nana wlh naji dadi,

Dama matar mutum kabarinsa,dama Allah ya tsara ni ba matar ya Abbas bace,

Nayarda kazabamin duk mijin dakaga yadace dani.


Malamande yayi mirmushi yace,

Allah yayi maki albarka xuhra,tashi kije zakiyi farinciki dazabin da zanyimaki ko bayanzuba.




Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣7⃣


Na 

Maman sadeeq






"yadur kusa agabansa  yagaidasji cikin ladabi,

Bayan sungaisa ya dubeshi da kyau yace "kaji kirana ko?"


Lamido ya gyada kai".


Yace "to ita safiyar  tayimaka bayani?"


Lamido yace A"a batafadamin komaiba".


Yace to wata Alfarmace kuma gata agareka,

Inaso kuma idan kaji ranka bai daukaba karka kwari kanka kafadamin gaskiyar abinda ke ranka,


Bari imbaka abin abude ko ince abayyane.


Aure ne nakeson imbaka,wanda nake kyautata zaton zaja rikemin amana".


Dasauri yadubesa yace "Aure?"


Yace "eh,


Shikam yasoke babin aure arayuwarsa matarsa daya ta ishesa,

Dan yayi baiji dadadiba,

Saidai baya iyayiwa tsohon gardama,

Yana da kima a idonsa,zaikarba kodan yafarantamasa,


Yadubesa yace karka damu malam nayarda dazabinka,

Kuma ina godiya ,

Allah yasaka da Alkairi".


Malam yayi murmushi yace,

"Ameen babana,

Abinda yasa nazabeka acikin yayan dangi,saboda nayarda da nagartarka.


Yarinyarda zambaka marainiuace,

Tasha wahala arayuwarta,

Shiyasa nakeson tasamu salama agidan Aurenta,

Saikuma naduba naga kaikadaine hakan zata yuwu,shiyasa nakira safiyya mukayi maganar dan haka tunda ka amince sai ahada dana dan uwanka ayi gaba daya,

Amma yanzu bari inturo maka ita ku dan zanta".


Har zaice akyaleta kuma saiyayi shiru,

Malam yashiga gida, 


Jimkadan tayi sallama tashigo.


Cikin sanyin murya,

Jin muryarta dayayi yasa yayi saurin dago kai suka hada ido.


Dam-dam!  Yaji gabansa ya fadi waiya akayi haka?


Mikin sonta yasake dawowa sabo,

Ya akayi yananta da abinda yake bege dare darana?"


Saigashi acikin dafawar ubangiji yasake hadasu akaro nabiu.


Yamatsa kusa da ita kamar zai rungumeta yace,

"kurratul aini(sanyin idaniyata)m, ashe zansake ganinki?"


Daigashi Allah ya kaddaro aure atsakaninmu,

Kina sona?"


Kidubi girman Allaj kisoni ko yaya,

Dukda dai nabaki hkr akan abinda nayimaki,kuma kince kinyafemin  daure kive dani kina sona".


Tabbas tashaidashi abu yadda za ayi ta mantashi,


Haka kuma yazamar mata dole ta karbeshi,

Tundashi malam mande ya zabamata amatsayin miji,

Kuma ma aibadhida makusa,

Yana da kyau daidai shi......


Yakatsemata tunani dacewa kinyi shiru".


Tayi murmushi tace,kaikana nifin harka karbeni?


Sosaima kuwa,

Yace da ita,


Tace baka gudun ko inada aibu?"


"ko kina dashi wlh ina sanki".


Tace badai tiladtakaba akayi ko?"


Yace A'a saidai yabani zabi kuma nazabeki,

Inafatan nima zaki soni koda rabin sanda nakemakine,

Kitaimakeni ki soni".


Tayi murmushi tace,

"inadanka zankuma yimaka biyayya,gaduk abinda zaka umarceni,

Inafatan zaka tallafeni danni marainiyace,

Bani da kowa sai Allah saikai, da baba malam, da inna yalwati,sai kannena guda biyu".


Yadubeta cikin kulawa yace karki damu, sanyin idaniyata,

Dayardar ubangiji ni zanantardake maraicin iyayen dakikayi,

Saina shafemaki duk wata wahala da kikayi na mayar maki da ita farinciki".


Tayi murmushin jin dadi tace,

"Allah yasa".


Yace bari inje infara shiri tun yanzu,


Zandawo anjima lamar dame dame kike bukata?"


Tace babu komai".


Yace banyardaba".


Tace Allah babu".


Yace to nari imbaki kudi saiki soma shiri ko?"


Tace A'a kabar kudinka daga zuwa sai indoramaka hidima?"


Yayi mamakin jin lafazinta,

Yadade baiga mai irin halin taba,

Kodai jawaheer dayake yabo inyabata kudi amshewa takeyi,

Lallai Allah ne yayimasa kyauta".


Ajemata kudin yayi yace idan har baki karbi kudinnanba to baki karbeniba kenan?


Tace to nagode".


Yayi murmushi ya juya,

Tadauki kudin  tashiga gida tana godewa  Allah.








Maman sadeeq

[9:32PM, 10/27/2017] ‪+234 803 383 3485‬: 🔪🔪🔪🔪🔪🔪WUKA A MAKOSHI🔪🔪🔪🔪🔪🔪5⃣8⃣





Na 

Maman sadeeq




SADAUKARWA


Wannan littafi kacokan na sadau karda shi ga  mahaifana,Abin Alfaharina,

Allah ubangiji yasakamaku da mafificin Alkairi, 

Yakareku daga sharrin mahassada kuma yakara maku lafiya💔💔❣💔💔




MASOYAN WUKA AMAKOSHI,

Hakika kun cancanci ayaba maku, nagode da irin kaunar da kuka nuna mani, da littafina, 👍👍👍👍👍👍🤝

Ummu aleesha wa waleed,

Maman shaheed,

Maman sayyid,

Mrs Abubakar,

Haj  sadiya s. Fata,

Zainudden zain,

Zainab muhmd inuwa,

Zainab Abdullahi loya,


BAZAN MANTA DA KUBA,

Khadeeja usman talle kiru, (momy son)


Badariya Adamu mlf,


Amina Aminu(maman khadey)baure.



INA TARE DAKU


WUkA AMAKOSHI FANS,

ZAMAN AURE,

P.M.L.WRITTERS FANS,


PEN WRITTER ASSOCIATION,

MUTAI MKI JUNA GRP,


CLASICAL FINES LADIES,


MD,MD FANS NOVELS


M.SHAREEf FANS,

SADAU FANS,



JINJINA,

Jinjina agareki maman isham,(zara dila kata gum)


Bazan manta dakeba, 

Nagode dayanda kike nuna kulawa dani, 

Allah yabarmu tare👏🏻👏🏻💔❣💔❣




LAST FAGE,




"gaba daya sun zuke sun tsomale,

Dagani basai ka tambayaba,cutarsu nada nasaba da kanjamau,

Gababu abincin kirki,

Garashin shan magani,

Ga kuma rashin tsafta.


Itako fa iza ayau ciwon yafi na kullum,

Danko tashi bata iyawa,


Kakari ta somayi saidai babu wanda ke iya taimaka mata,kowa takansa yakeyi,


Allah da ikonsa fa iza ta amsa kiran mai duka,babu wanda yasan ta mutu,saidatafara wari, sannan aka farga,akasadata da ma kwancinta.


Kwana biyu tsakani nalaraba tabi bayan fa iza,


Sani yazowa rabe gaisuwa,yakuma sanar dashi daurin Auren zuhra,

Dan malam mande yazo hargida yasanar dashi saboda fita hakki".


Rabe yace yanzu zuhra tana gurin mande?"

Din Allah sani kaini innemi gafarar yarinyarnan kafin mutuwata tazomin".


Yatashi iska nakadashi suka nufi gidan malam mande,


Kuka yasaka yana rokonta tayafemasa.


Batajaba tace, 

Nabu abinda kayimin baba".


Yace kayya dai Alhakinkine yake dawainiya dani".


Tace babu komai baba Allah yabaka lfy,


Yace kayya dai babu wata lfy da zan samu,lokaci kawai nake jira,

allah yajikan  auwalu da Aisha,Allah yada suyafemin,,


Malam mande yabasu hkr ya lallabasu sukatafi,

Sani yakawoshi gida.


Lubabatu tashigo gidan kamar anjehota,

Rabe yadubeta duk tafita ahayya cinta gawata rama datayi,


Itama dubansa tayi cikin takaici,

"ina kudina dajika sace min?"inji Rabe,


Tace bansaniba,

Rabe ka cuceni,

Allah ya isa ban yafemaba,

kudi kuma bazan badaba,xuwa zanyi inyi takarbar magani dasu,

Tunda ka hanani yin Aure,

saboda cutarda kajefamin matsiyacin banza".


Tazageshi tas sannan tafita ta tsaida  dan acaba ta nufi gidansu,


Saidai tsautsayi ance baya wuce ranarsa,sunzo dai dai rawun din ta sirmiyo kasa,

Cikin rashin sa a kuma wata mota tabiyo takanta,

Atake lubabatu tamutu ko shurawa batayiba,

Aka kwasheta aka kaita asibiti gurin adana matattu(mutuware)

Saboda ba asan ko yar ina ceba,


Tayi sallama tashigo cikin sanyin murya,

Dasauri haleesa tataso ta rungumeta,

Tadubi haleesa anyimata wanka angyarata kaibakace batada uwa avikin gidanba,


Haleesa tace mama ashe kinji sauki?"

Tayi murmusji tace naji sauki haleesa ina momin taku?"

Tana ciki tace da ita,

Tokisanar da ita zuwana".


Jawaheer ta fito taga hajir tace A'a hajir kece atafe?"

Wlh nice jawaheer,

Suka gaisa jawaheer tayimata yajiki,

Tace jiki da sauki,tunda gashi kumburin duk yasabe,

Saidai ina fama da barazanar daukewar lumfashi,

Naje asibiti ambani magani amma babu wani sauyi,

Shine nazo ki taimakamani da Addu o i ki tofamin aruwa,

Saboda naga adfu a tana da tasiri sosai,

Dan itace tazamo silar sabewar kumburinnan".


Jawaheer tace to bari inrubutamaki kinga saiki runkayi da kanki,


Hajir tace wlh bazan iyaba, kedai kitofamin aruwa insha,


Mamakine yakama jawaheer lallai hajir batada ilimin addini akanta,


Ta dauko riwa ta tafo mata tabata tasha sannan tabata shawarar idan tasamu lfy taje ta nemi ilimin addini,

Hajir taji dadi sosai da shararta, ahaka harsukayi bankwana,


Jawaheer tajinjima girman Al amarin rayuwa,

lallai duniya rawar yammata ce,

Nagaba yakoma bbayako a mafarki batatana tunanin hajir zata russunaba bare har tace tafiyemata yan uwanta,

Harma da kawarta laila sanata,

allah kayimana dacewa.



Gagarumin biki akeyi,

Wanda ya amsa sunansa biki,

Abbas ya dubi zuhra yace amaryar lamido".

Kingako yanda kike sheki?"


Tayi murmushi tace Allah angon nana, kaima kaga yanda ka hadu,

Gaskiyani inyayana yayi ado irin naka bazan barshi yaje fatinnanba".


Abbas yace kajita kamar duka kenan,

Kunyar zatabarki kifadawa lamido haka?"


Tayi murmushi tace to karkafadamasa,


Sukayi dariya su duka,


Lamido yasawo kai cikin  hadaddiyar motarsa,

yafito suka gaisa da Abbas. 

Yadubeta yace kurratul aini nabata maki lokaci ko?"


Abbas yace A'a baka bata lokaciba,

Tadaice idan layo ado sosai bazata yarda kaje gurin fatyn ba,saboda batasan yammata su kallemata kai".


Kunya duk ta rufeta lamido yace wai hakane zuhrata?"


Kasa dago kaitayi ta kalleshi, 

yayi  murmushi yabide mata gaban mota tashiga sukatafi wurin faty.


Shagali akayi sosai andaura aure amarya tatare agidanta, 


Soyayya kala kala lamido yake nuna mata,

zuhra harta manta dawasu wahalhalun rayuwa da tasha, 

Tajawo kannen ta ajikinta,

Lamido yanemamasu makaranta maikyau yasakasu,


Zamansu da jawaherr kuwa gwanin ban sha awa bakataba ganinsu kace masu kishiyoyine daidai ya da kanwa,


Watansu ukku da aure zuhra ta fara lailayin ciki, fadin

Murna awajan lamido ma bata bakine hala yayi ta riritata jar Allah yasauketa lafiya tayi baby boy mai sunan baban ta wato(Awwalu)amma suna kiransa da isham.


Ganin zaman lafiyar da sukeyine yasa suka matsa masa akan yadawo da hajir dakinta,

Dafarko dai yakiya amma daga baya yaje gidansu akadawo da auren nashi da ita,


Zaman lafiya sukeyi sosai bakataba cewa kishiyoyine komai tare sukeyi, suyi girki tare baka banbance dan wani acikinsu,

Hajir ta natsu duk ta ajiye maka man yakinta ta koma ga Allah.


Rabe kuwa ciwo yakici yaki cinyewa yarame yalalace  yafita daga hayya cinsa mutuwa kawai yake tsammani akowane lokaci.


Laila kuwa alkadaritane yakarye mijinta yayimata dukan tsiya tareda takardar saki ukku ayanzu haka tazamo abin tausayi ,

Iyayanta da yan uwanta dun gujeta ,yanzu haka ta loma bara atiti.




TAMMAT BI HAM DILLAHI




Anan ne nakawo karshen  littafina kuskuren danayi aciki Allah kayafemana Allah yasa mugama daduniya lfy


Nanda dan wani lokaci zakujini a sabon littafina mai suna

🍀🍀🍀SONE KO KISHI?🍀🍀🍀



Nagode ,nagode, nagode👏🏻🤝






Maman


sadeeq


Post a Comment

0 Comments