WATA KAWA cmplt

 👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻


  *WATA K'AWA* 


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀


It's very interested Story


(Labarin dake kunshe da cin amana,zanba cikin aminci)



Written by 2 stars



FIDDAUSI SANI(damsel feedorh)

&

RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu-inteesar)



✨✨Page1⃣


zaune take akan tabarma ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Hawaye ne ke bin kuncinta yayin da ta zuba ta gumi da hannayen ta duka biyu.

Da alamu tayi nisa acikin tunani,kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar tana cikin damuwa da k'uncin zuciya.


"Ashe za'a wayi gari aminci yayi k'aranci a duniya?"

"Me na tare miki a rayuwa da kika zabi ki ganni a cikin k'uk'untacciyar rayuwa?"

Kin ci amanata Aminiyata.............

Duk wannan tunanin a ranta take yinsa.

Tayi nisa acikin tunanin ta taji ana girgiza kafad'ar ta.


Dago kanta tayi ta zuba wa inna halima jajayen idanun ta da suka jazir dan kuka.


Inna Halima ta ce "habah Fatima! Wai sai yaushe ne zaki daina wannan tunanin?" "Tun ɗazu fa nake tsaye akanki ina maki magana, amma baki ma jini ba saboda tunani."


Sai zuwa yaushe ne zaki manta da wannan abun ki barshi ya wuce fisabilillahi?.


Share ƙwallar da ta gangaro daga idon ta tayi ta ce "dole nayi tunani Inna, suhaima ta cutar dani ta dasa mun baƙin ciki a rayuwa ta dana ke ji har abada bazan manta dashi ba"


Wasu hawaye Masu zafi ne suka sirnano a kuncinta,bata yi ƙoƙarin share su ba ta ce "wannan ai abun baƙin ciki ne Ni suhaima zata ci amana ta aure mun miji, tasa ya juyamin baya nida yarana?"


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "yarana da mahaifinsu a raye ta mayar mun su tamkar marayu".


Inna Halima ta zauna kusa da ita tana bata baki da cewa "kiyi hakuri Fatima, kanta tayiwa idan dai baki da hakk'inta tabbas sai Allah ya saka miki" 

"Ke fa ba ƙaramar yarinya bace, babbar macece ke wacce take da ƴaƴa,bai kamata ki zauna kina kuka a bayyane haka ba."


"Shikenan Inna insha'allah zan yi ƙoƙarin k'arfafa zuciyata. Allah ya bani ikon jurewa"

Fatima ta faɗa.


Ameen inna ta faɗa tare da mik'ewa tabar gun.

******************

KASAR INDIA.


Tafe take a motarta cikin kwanciyar hankali sai kid'a ke tashi a motar.


Wani makeken gate ta nufa tana isowa daf dagate ɗin tayi hon.

Cikin hanzari gate-man ya wangale mata gate ɗin makeken gidan.

Shigewa tayi sai da ta daidaita tsayuwar motarta kafin ta fito ta rufe motar.


Kana ganinta kasan Naira ta zauna mata Babbar macece wacce zata kai kimanin shekaru 35 a duniya amma saboda daular da take ciki zaka ɗauka yar 25years ce.

Hajiya suhaima kenan.

Fitowar ta ke da wuya masu aikin gidan maza suka fara gaishe ta.

Tana wani shan k'amshi Cikin takun k'asaitarta ta ke tafiya har ta shige tank'amemen parlourn gidan.


Tsayawa fad'ar kyau da tsarin parlourn b'ata baki ne sai dai kuyi imagining kawai.


Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa tayi wanka ta kuma shiryawa a cikin Pakistan masu matuƙar kyau parlourn mijinta ta  shiga.


Wani matashin mutum ne zaune  a parlourn yana kallon labarai,fari ne ba sosaiba, da ganin shi Kasan naira ta zauna.


Alhj Mubarak kenan, magidancin da duniya keji dashi saboda dukiyar sa, takun tafiyar da yaji ne ya saka shi d'ago kai.


 Wani killer smiling tasakar masa,tare da fadin "sannu na barka kai kad'ai ,wlh abun ne saida suka b'ata mana lokaci" baice mata komaiba ,yaci gaba da kallon shi.



Idan akwai abinda ke b'ata mata rai game da Mubarak bai fi miskilancin shi ba, kuma a da ba haka yakeba.


Tunda bahaka yake yi da iyalinshi ba.



Kenan da sauran aiki a gabanta saboda ta lura ya kasa cire damuwar iyalinshi aransa







 *Ya*ku *kaji salon labarin muci* *gaba* *ko* *mu* *dakata,,,comments* *dinku* *shizai* *nuna* *mana cewar* *kunason* *cigaba*






Feedorh&Ruky❤❤❤❤❤

👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻


*WATA ƘAWA*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀


It's very interested Story

(Labarin dake kunshe da cin amana,zamba cikin aminci)


*Written by 2 stars:*

*FIDDAUSI SANI (damsel feedorh)

& RUKAYYA IBRAHIM LAWAL

(Ummu inteesar)



✨✨2⃣


Guri Suhaima ta samu ta zauna kusa da Alhj. Ta na cewa "meke damunka ne Alhajina kwana biyun nan You look some how, meye matsalar?"


Murmushi yayi sannan ya ce "bakomai habibtie kawai dai wani ɗan tunani nake fama dashi kwanan nan."


Saurin kallon Alhj tayi tare da tambayar "wane irin tunani ne kake?"


A ranta tana addu'ar Allah yasa ba iyalinsa yake tunawa ba....

Tana cikin wannan zancen zucin ne ta tsinkayo muryarsa yana faɗin "Fatima nake tunawa da irin zaman amincin da mukayi abaya, da kuma cin amanar da tamun." "Wannan abun na damuna sosai."


Ras! K'irjin suhaima ya buga da ƙarfi,a zuciyarta ta ce kenan har yanzu da sauran aiki a gabana, kiyi hak'uri Fatima dole sai na nisanta tunaninki da ƙwaƙwalwar mijina hankalina zai kwanta.


D'agowa tayi ta mishi wani mayaudarin kallo tare da matsowa daf dashi, ta kama hannunsa cikin kwantar da murya da lallashi take cewa, "Alhajina kayi hak'uri ka cire wannan abun a ranka,komai ya wuce tunda yanzu bakwa kusa da juna."

"Ka cire Fatima a ranka yawan tunawa da ita shike haifar maka da Wannan matsalar ta tunanin abunda tayi."


"Fatima Aminiyata ce amma bata kyauta mana ba."

"Dan haka nake baka shawarar ka cire ta a ranka kwata-kwata, kafin ta ja maka hawan jini takaini ta baro."


Numfasawa yayi kafin ya ce "har yanzu zuciyata ta kasa gasgata cewa Fatima na taci amanata."


Tirkashi nan da nan wani k'ololon baƙin ciki ya taso ya tokare wuyan Suhaima, A ranta tace Fatima zaki san kiyi dani, nayiwa kaina Alƙawarin nisanta ki da farincikinki har abada.

Na tsane ki Fatima."

**************

NIGERIA

 Zaune take bakin murhun ita ce tana fitar da Alalen siyarwarta a wuta.


Bokitin tallar ta ɗauko tana saka Alalen aciki adai-dai lokacin da Almajirin dake mata tallar Alalen yazo ɗauka.


Sadeeq(yaron fatima na biyu) ne ya shigo gidan da sallamarsa,ya nufi inda mamansa ke zaune a bakin murhun yana faɗar "gaskiya nagaji da yawa mama kuma yunwa nake ji har yanzu fa banyi break ba..."


Wasu hawaye ne masu zafi suka zubowa Fatima a lokacin da take kallon yaronta, ba komai ya saka ta hawaye ba irin yanda yaron ta ya dawo duk ya fara fita kamanninsa saboda wahalar rayuwa da suke ciki.


"Allah ya isa Suhaima,bazan taɓa yafe miki ba."ta faɗa a bayyane.


Da sauri yaron ya rungume mamansa yana share mata hawaye tare da faɗar "kiyi hak'uri mamana Allah yana tare da masu hakuri."


Itama rungume shi tayi tafara kuka a hankali.

Shima yaron ganin mamansa na kuka sai ya fara kuka.

A haka Inna Halima ta fito ta samesu, tsayawa tayi cak a bakin Kofar ɗakinta tana kallon su cikin tausayi.


Tana so taje ta lallashe su amma sai zuciyarta ta tsinke kasa hak'uri tayi itama ta fashe da kuka tare da komawa cikin ɗakin da sauri..

************

INDIA


Wata karamar yarinya da ba zata wuce 8years ba, ce a durkushe tayi kneel down tana kuka.

Suhaima ce zaune a kan lumtsumemiyar kujerar parlourn ta hakimce.


Tasowa tayi ta zo gun yarinyar tare da kama kunnen yarinyar ta murɗe.


Wani gigitaccen ihu yarinyar ta saka kafin ta ce kiyi hak'uri mama bazan ƙara ba.


Suhaima ta soma magana (ba tare da tasaki kunnen yarinyar ba) ta ce "wato kam ke ga mai kunnen k'ashi,sau nawa na gayamaki karki k'ara mun barna amma saboda kinyi gadon baƙin hali gun uwarki shine sai da kika fasa mun glass cup koh?."


Cikin kuka yarinyar ta ce "kiyi hak'uri momy ba da gangan na fasa miki ba...."

Ka sa ƙarasa maganar tayi saboda naushin da Suhaima ta kai mata a baki nan take bakin ya fashe sai jini.


Ko tausayin ta Suhaima bata ji ba ta ce "ai dole saina hukunta ki yau shegiya munafuka wacce tayi gadon munafurci gun uwarta.."

"Ki tashi maza kije ki share mun bedroom ɗina kiyi mopping ko'ina Sai kin gyara a ɗakin har toilet,kuma idan bai gyaru da kyau ba kin san saura."


Da sauri noor ta mik'e ta nufi bedroom ɗin saboda tasan halin momyn nata sarai zata iya karai-rayata akan haka.


Har ta kusa shigewa ɗakin Suhaima ta daka mata tsawa da cewa dakata ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba.


Suhaima ta ƙarasa gurin tana "faɗar yau kuma bazaki ci abincin rana dana dare ba a gidan nan,kuma idan dadynki ya dawo kika sake kika faɗa mashi na ma ki wani abu ko na hanaki abinci zakiga abinda zan miki."


Share & comment




Feedorh & Ruky❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻


*WATA ƘAWA*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀


It's very interested Story

(Labarin dake kunshe da cin amana,zamba cikin aminci)


Written by 2youngest writters:

*FIDDAUSI SANI (damsel feedorh)*

& *RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*



✨✨3⃣


"Munafuka maza ki b'ace mun da gani mai b'akin hali"ta faɗa cikin d'aga murya.


Ai kafin Suhaima ta gama rufe bakinta tuni Noor ta shige bedroom ɗin ta na kuka.


Ba ƙaramar tsana Suhaima ke yiwa Noor ba,wannan kuwa ya samo asali ne daga tsanar da take yiwa uwar yarinyar wato Fatima.


Bata son duk wani jini na Fatima duk kuwa da tarin alkhairan da Fatima ta mata a baya, Fatima ta zama haske a rayuwar Suhaima lokacin da take cikin duhun talauci da rashi.


Amma Suhaima bata taɓa son ta ba koda na yini ɗaya ne a kullum kwanan duniya wutar k'iyayyar Fatima daɗa ruruwa take a zuciyarta.


Shiyasa tasan makircin da tayi ta nisanta Fatima da ƴaƴanta ga Alhj. Mubarak.


Noor ce kaɗai ta rage a gabanta ta rasa yadda zatayi da ita duk makircin da ta k'ullawa yarinyar Alhj. Mubarak baya kamawa sai ya ce "ai ita noor ƙaramar yarinya ce sosai,aikin k'uruciya ne zata daina idan ta girma tayi hankali." Hakan na bak'antawa Suhaima rai sosai.


Gashi Alhj. Yafi son Noor duka acikin ƴaƴansa,yana nuna mata k'auna fiye da ƴaƴan Suhaima.


Wannan dalilin ne ya saka Suhaima ke bautar da Noor idan Alhjn ya fita ko yayi tafiya ƙasar waje.

*****************

Rayuwa ta ci gaba da tafiyar wa Fatima cikin k'uncin da bakin cikin, a kullum kwanan duniya bata da aiki sai tsinewa Suhaima da ja mata Allah ya isa.


Fatima tayi da na sanin sanin Suhaima a rayuwarta, *WATA ƘAWA* macuciya ce.


A haka Fatima ta ci gaba da rayuwa cikin talauci ita da ƴaƴanta biyu maza  da su ke zaune a gidan Inna Halima (k'anwar mahaifinta).


Abinda zasu ci ma yana neman gagarar su, tunda mijin Inna Halima ya rasu gashi bata da wasu y'ay'a masu yawa, ƴaƴanta biyu ne kawai maza.


Inda ƙaramin ne kawai ke taimaka mata kuma shima mai ƙaramin ƙarfi ne,babban ne mai arziki amma shi ya guje ta da dukiyarsa,Bama a garin ya ke zaune da iyalansa ba kuma baya zuwa bare ya taimake su.


Gashi iyayen Fatima duka basa raye both mahaifiya da mahaifinta duk sun rasu.

Yanzu Inna Halima ce kaɗai gatan ta,shiyasa da mijinta ya guje ta saboda 'kazafin da akai mata,ta dawo gidan Inna haliman da zama.


Yayin da Suhaima take India a babban birnin Mumbai tana watayawa da dukiyar mijinta.

*****************

Hankalin Fatima ya na matuƙar tashi idan ta tuna y'arta ƙarama na hannun Suhaima, tsoron ta ɗaya kada ta hallaka mata y'a.


Dan a yanda ta san Suhaima zata iya komai akan cimma burin ta.

Shiyasa fatima ta dage da addu'a sosai akan Allah ya kub'utar da Noor a hannun suhaima.


Tunda Alhj. Mubarak yaƙi ya dawo mata da y'arta kamar yanda ta bukata,dan a yanzu ma ko wayarta baya dagawa bare ya saurare ta.


Da wannan sana'ar Tata ta Alale take taimakawa Inna da ƴaƴanta yayin da innar kuma take siyar da su daddawa,Maggi,gishiri,kanwa da sauran su.

***************


Noor ta galabaita sosai alokacin da take aikin gyaran k'aton bedroom ɗin momy, dak'yar ta kammala,nan ma bai gyaru yanda ya kamata ba aikuwa tasha na jaki a gurin momy dan Saida ta lallasa ta da bulala duk ta farfasa mata jiki.

Tare da Faɗar

Ta ce "kuma wallahi sai kin kuma gyarawa kin ji na rantse ko yau na b'abb'ala ki a gidan nan,shegiya mai kama da Aljanu."


Noor ta sha kuka wani zazzafan zazzaɓi ne ya dirar mata a lokaci ɗaya ba yadda ta iya dole ta kuma gyarawa.


Anan kan tiles din d'akin ta kwanta bayan ta kammala,wani barcin wahala ne yayi gaba da ita.


Suhaima na shigowa ta tarar da ita tana barci akan tiles a ɗakin nata, "kutumar uban can! Ni zaki yiwa......


Share & comment


Ruky& feedorh❤🧡❤🧡❤🧡❤

👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻👩🏻


*WATA ƘAWA*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

It's very interested Story

(Labarin dake kunshe da cin amana,zamba cikin aminci)


Written by 2youngest writters:

*FIDDAUSI SANI (damsel feedorh)*

*& RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*






✨✨4⃣


"Kutumar uban can! Ni zaki yiwa barci a d'aki" Suhaima ta faɗa tare da saka ƙafa ta yi ball da yarinyar.


Noor da take barci cike da gajiya ba zato ba tsammani ta ji an yi ball da ita sai da kanta ya daki bangon ɗakin a take gaban goshinta ya fashe sai jini.


Firgigit ta farka tare da kurma uban ihu yana kuka.

Suhaima ta tako zuwa gabanta ta ce " Rufamin baki munafuka, uban wa ya baki izinin kwanciya a d'aki na?"

Kasa magana Noor ta yi saboda zogin da take ji a gurin ga jininta da yake ta zuba.

Falle ta da mari Suhaima ta yi cike da mugunta ta ce "Shine ma ina tambayarki kika min shiru tun da ga sa'ar ki koh?, Maza ki ta shi ki ɗauko mopper ki zo ki goge mun wannan k'azamin jinin na ki da ya b'atamun d'aki." Ta k'arashe maganar cikin bada umurni.


Jiki na kakkarwa Noor ta miƙe ta na dafa bango saboda jiri da ya fara d'ibar ta a haka ta je ta ɗauko mopper ta zo ta na goge da hannu ɗaya yayin da ta dafe gurin raunin da hannu ɗaya, ta na gamawa ta fice daga ɗakin ta na ƙarasawa tsakiyar parlourn ta zube a some.


Suhaima kuwa kwanciyarta ta yi a kan gado tana karkad'a ƙafa ta na ƙara k'issima abubuwan da zata kuma yiwa Fatima ta jefa ta a k'unci fiye da wanda ta ke ciki yanzun.


Sadiya yar aikinsu ce ta fito daga kitchen za ta wuce taga Noor yashe a ƙasa, da ɗan gudunta ta ƙaraso ta jijjigata ta ji ta a some, ihu ta kurma sai ga Suhaima ta fito a hanzarce ta na tambayar lafiya, da hannu kawai sadiya ta nuna mata Noor da ke a some.


Da gudu ta ƙaraso gurin cike da firgici ta ce "Subhanallah me ya same ta sadiya? Ki gayamun me ya sami y'a ta."


A dai-dai lokacin ne kuma Alh Mubarak ya ƙaraso cikin parlourn ya na tambayar lafiya.


Ganin abunda ke faruwa ne ya saka ya d'auko wayarsa a kid'ime ya kira doctor Rahul Akash (dama shine likitan su na ƙasar).

********************


Firgigit Fatima ta farka daga mummuna mafarkin da ta yi, ta tashi zaune ta na addu'a, "Ya Ubangiji na abin dogaro na, ina rok'ar ka akan ka kare mun y'ata Noor daga sharrin wannan shu'umar matar." 


Mummunan mafarki ta yi da Suhaima ta zo zata kashe Noor da wuka ,Noor sai ihu ta ke tana kiran sunan ta ta na faɗar "mama ki zo kicece Ni Mommy zata kashe Ni," dariya kawai Suhaima ke yi tana matsowa sai da ta zo har gaban yarinyar ta d'aga wuk'a za ta chaka mata kenan, Fatima ta yi firgigit ta farka.


Kasa komawa barcin ta yi kawai sai ta tashi ta d'oro Alwala ta zo ta ɗinga nafilfili.


Har safe hankalin Fatima ya kasa kwanciya saboda mafarkin jiya da ta yi.


Tun 7 na safe take so ta kira Alhj Mubarak Amma ta kasa saboda tasan ya daina ɗaukar wayarta yanzun.


Jujjuya wayar kawai ta ke a hannu daga karshe ta ajiye wayar, tana ta zullumi a ranta.



 Ƙarfe 9 na safe Fatima ta yi shahada ta d'aga waya ta kira number Alhj Mubarak, Ringing kawai wayar take Amma har ta katse ba a d'aga ba.


Bata hak'ura ba ta kuma kira har sau biyar sai ana biyar ɗin ne aka d'aga, nan ma har ta kusa tsinkewa.


Sallama ta yi ta na cewa "Abban Sadeeq don Allah ka taimaka ka maido min da Noor a gurina."


Wata mahaukaciyar dariya ta ji anbushe da ita, hakan ya sa ta ciro wayar daga kunnenta ta na ƙare wa wayar kallo.

Ta na mamakin waye mai wannan dariyar? Mayar da wayar ta yi a kunnenta da nufin ta yi tambaya, kawai sai ta jiyo Muryar Suhaima na cewa:

" Da na yi niyyar sakawa a maido miki da ita ba tare da kin roƙa ba, Amma gaskiya yanzun na canza shawara, naga idan har na bari aka maida miki ita za ki ji daɗi, Ni kuwa bana son ki ji daɗi na tsani naganki kina farin ciki, don haka zan riƙe Noor a hannu na in cigaba da gana mata azaba son Raina, Kuma ba yanda kika iya dani."


Cike da tsanarta Fatima ta ce "Allah ya fiki, insha'allah ba Abinda za ki iya da Ni, daga Ni har ƴaƴana mun fi ƙarfin ki da yardan Ubangiji."


Wata dariyar Suhaima ta kuma shek'ewa da ita sa'annan ta ce " Eyyeah Lallai Malama Fatima ashe fa kinyi baki bayan rabuwar mu koh? Wow! Abin ya burgeni mu zuba Ni dake, Na tsane ki Fatima."


"Ni ma na tsane ki sosai Suhaima ba na son tunawa da Rayuwarmu ta baya Ni dake bazan taɓa yafe miki ba,kin cutar da ni ba tare da kin tuna d'umbin Alkhairan da na miki a baya ba." Fatima ta faɗa.


Har Suhaima ta bud'i baki zata yi magana ta ga Alhj Mubarak ya fito daga bedroom ɗin sa ya nufo parlourn da nufin ɗaukar wayarsa.


Saurin katse kiran ta yi ta goge lambar da duka misscalls ɗin ta ajiye wayar.


Ta ƙarasa gurin shi tana murmushi tare da Faɗar "Sannu da fitowa pyaary...."



SHARE & COMMENT







RUKY & FEEDORH❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤



Post a Comment

0 Comments