UWAR GOYO hausa novels cmplt

 

Uwar goyo new book

Chapter1

wajen ya cika da Jama, a maza da Mata babba

da yaro

Kowa harkar gabansa kawai yake ba ruwan kowa

da kowa kasancewar gobe sallane yasa shagon

Mai Suna alfijir Super store cike da Jama, a

baban shagone yanada qofofi har hudu duk wani

nau, in sutura da kayan kyalekyale shagon

nadashi tsayawa fasalta yaddah shagon yakema

bata lokacine

You itace ranan da musulman duniya sukakai

azuminsu na 29 gobe Ko jibi kenan take sallah

Inka dubi fuskokin Jama, ar dake cikin alfijir

Super market din kowannensu cikin farinciki da

annashiwa yake kowa na sayen abinda yakeso

Jama, a sai kashe naira kawai yake a cikin

shagon kaika rantse kace bada guminsu suke

samo kudinba

A wanni vangare kuwa wata matace da yarta da

ba zata wuce year shekara shiddah a duniya ba

Kayane a kusa da Ita masu yawan gaske Wanda

ta saima

Year lelen nata

Kallo daya zakaima Matar Ka gane macece Mai

aji kuma naira ta zauna don alamun Hutu sun

bayyana a jikinta

Daaa ganin yanayin jikinta zaka gane tayi nisa da

talauci

Domin shiga Tai ta kece raini Kaya ta saka masu

tsada Ita da year tatata daga wuyarta zuwa

hannayenta wasu hadaddun danyen gwala

qwalaine a ciki wani siririn gyale ta yafa a

kafadar Tata wacce ake Kira da tayani gantali

Sam batai Kama da Matar aureba kasancewar

yanayin shigar Tata da tayi

Sai baza kamshi kawai take Tana wani hura hanci

irin na masu hannu da shuni

A zaune take a kan wani kujera ba qaramin kudi

ta kashema yar Tata ba duk tsadar Abu bata

shakkar siyama yar Tata inhar ranta naso kuma

Zai sakata cikin walwala

Dukda wannan uwar siyayyar da taima yar Tata a

banza ya tashi domin kuwa ita yar a duk cikin

himilin kayan da aka jibgo Mata din bataga

abinda yai Mata ba

Hasalima Ita wani Riga da siket takeso data Gani

a jikin wata yarinya a lokacin da sukaje Viki a

wani gida tun a lokacin taji kayan sun birgeta don

haka taketa rigima Kan sai momin Nata ta siyo

Mata kalan kayan sai kuma akai rashin sa. A ba,

a samu kalan kayanba don har Dubai abbanta

yaje don kayan Amman Ina Abu yaci Tara saidai

ya samo hadaddu Wanda sukafi wanNan kyau

Amman daya kawo Mata saita dinga ihu da tsalle

akan bataso Dole sai kalan wadancan

Daqar maman Tata ta shawo kanta da yin mata

alqawarin duk indai ake saidawa Ko, a inane indai

har a fadin duniyar nanne wajen yake to sai taje

ta sayo Mata su kuma Ko nawa suke hakan yasa

ta tashi ta nufi gidansu yarinyar da yar Tata taga

kayan a jikinta saidai anyi rashin sa, a domin

kayan ba a naija aka saima yar tasuba Tun daga

Saudi wata yar uwarsu ta kawo ma yar tsaraba

haka ta coma gida cikin sanyin jiki tanata tunanin

ta yaddah zata shawo kan yar Tata ba tare da an

samu matsalaba

Hakan kuwa akai duk wasu kalamai masu taushi

da kwantar da zuciyar da taitama yar tata basuyi

tasiri ba

Don rigima Kala Kala ta dinga tsirowa dAshi

hardasu yajin cin abinci na sati daya

Dadai maman ta fahimci yar Tata Tana cikin wani

haline yasa ta dauketa zuwa alfajir Super market

Wanda Ke cikin Garin Ko allah zaisa taga wasu

kayan wadanda sukafi wadancan Ita a nata

tunanin kantine babba kuma duk abinda kakeso

zaka iya samu a ciki

Don haka yasa ta taho da ita sai kuma akai

rashin sa. A a duk kantin saida suka zagaye ciki

da wajensa Amman Basu samu kalan kayanba

Yarinyace qarama wacce shekarunta Basu taka

sun karyaba Amman sai Dan banzan rigiman

tsiga kodon ita irin yarannanne da babu kwaba

balle harara_tunda Tai wayo komai sai abinda

ranta keso ake Mata komai kuma tsadar abu idan

aka saya Mata ba zatayi amfani dashiba matuqar

bai kwanta mataba

Mahaifinta yana matuqar Jin haushin halayyar yar

tashi saidai ba yadda zaiyi don Bashi da icon

hanawa sbd rayuwar auren nasu ba yaddah aka

sani suke gudanar dashiba Matar tashi Ita keda

icon komai a gidan Sam batason taga bacin ran

yarta shiyasa yar takecin

Karenta babu babbaka shagwaba Kala Kala ta

iyashi Ga qiriniya da rashin Jin magana da kuma

rashin Kunya duk wannan Abu da take a wajen

uwarta duk ado ne domin kuwa batasanma

tanayiba ballentana ta hanata

Duk shirin da kuke da ita kanaqin halayyar yar

tatta to yanxu zaku raba hanya da ita koda kuwa

jikinta nekai

Yarinyar an shagwabata da yawa duk abinda

zatai marar kyau to a wajen uwarta Mai kyau ne

kwarai da gaske Karna cikaku da surutu shin wai

wacece wannan matar

Hajiya fanne Kenan wadanda mutane sukafi sani

da hajia tsigala mafadaciyar matace a zamanin

quruciyarta duk a yarn anguwan nasu babu

Wanda ya kaita masifa

Mummunace sosai baqaqirin da ita babu Ko

alamun fari a jikinta

Yaddah fuskarta take baqa haka zuciyarta take

babu Ko alamun Imani a tattare da ita asalin

mahaifanta mangawane daga qaramar hukumar

nguru ta jahar yobe suka dawo garinda suke a

yanxu idan Suna yarensu kaika rantse kace kanuri

suke mahaifinta talakane Amman yanada Rufin

asiri

Domin kuwa yanada Sana, arsa wacce da ita

yake samun daukar nauyin iyalan Nasa kuma

dattijon arziqine don Jama. A na girmamashi don

halinsa na kirkine ba ruwansa da shiga shirgin da

Bai damesaba

Mahaifin fanne nada ilminsa na addini don da

yawa Jama. A a wajensa suke zuwa daukan

darussa mahaifiyarta da mahaifinta kusan halinsu

dayane don mahaifiyar tatama taso ta kereshi

wajen haquri

Su biyar ne wajen mahaifin nasu uku Mata biyu

Maza saidai duk yayyin Nata an musu auren

dangi Ga Yan uwansu a lokacin da akaxo yin

natanne ta qeqashe qasa akan ita ba zata aure

Wanda akeson a hadata dashiba akai juyin

duniyarnan taqi yarda dukda haquri na mahaifin

fanne Amman saida tasa ya kamata yai Mata

dukan tsiya don da alamun sunansa taqeson

batawa mahaifiyarta kuwa nasiha ta dinga Mata

akan tai haquri ta amince da zabin da mahaifin

Nata yai Mata gamida nasiha Mai ratsa jiki shine

mijin Nata da kalamai harta samu daman shawo

kansa amman da sharadin bata sati biyu tak

inhar sati biyu ya cika bata samo mijin aureba to

zai hadata da Wanda yai niyyah

Nanfa mahaifiyar Tata ta takura Mata akan ta

fitar da mijin da zata aura a cikin gwanon

samarin da suke zuwa wajenta Tun kafin lokacin

da mahaifin Nata ya dibar Mata don tasan halin

mijin Nata akwaishi da haquri amman duk sanda

ya fusata bashi saurin sauka saidai abinda ita

mahaifiyar fannen bata saniba shine duk cikin

samarin Nata babu Mai zuwa wajenta da niyyar

aure duk Yan I love u I love u ne Yan axo axo aji

dadi a Ware ne sai kuma masu nemNta da

fasiqanci Amman Sam bata taba Basu hadin kaiba

Yau itace ran da mahaifin Nata ya dibar Mata

suka cika din haka daya ya kirata domin Jin

Wanda ta tsayar ganin ganin ta faramai hanya

hanyane yasa yace to lallai Da Wanda yai niyyah

Zai hadata Dan Dan uwansa nanfa tai tsalle ta

dire gamida cewa wLlahi inhar aka hadata aure

da Wanda sukeson hadatadin to cikin biyu sai

anyi daya kodai ta kashe kanta Ko kuma tabi

uwa duniya ta salwantar da rayuwR Tata acan

kawai kalaman fannen ba qaramin girgixa

mahaifan Nata yaiba hakan yasa suka qaleta taci

gaba da zama a gabansu har aka dau lokaci mai

tsawo fanne sai qara gansamewa take a gaban

iyayenta don harta wuce minzalin aure don sa,

ointa yanxu wasu nada yaya2 wasu uku

Duk anguwan an santa batada kunya Kona

misqara zarratan ga fada idan Tana fada bakinta

har kumfa ke fita Ga zagi fanne ta iya zagi Lamar

bamagujiya sannan Ga shegen tonon fada Lamar

karya Kai fada koda bada Ita akeba Tana shiga

kullun sai an kawoma iyayenta qararta hakan ba

qaramin qonama mahaifin Nata rai yakeba

Hakan yasa Jama. A ke kiranta da fanne tsigala

fada da gaskia tsorone

Hakan ba qaramin damun mahaifinta yakeba

burinsa daya shine Yaga ya kawar da fanne daga

gabansa koda Zai iya samun kwanciyar hankali ta

wani bangaren

Ana cikin hakane mahaifin Nata ya bada Ita

sadaka Ga wani saurayi Dan anguwan nasu

kyakkyawan saurayine daga gidansu fannen zuwa

gidansu saurayin gidaje ukune kawai a tsakani. A.

Lokacin daya sanar da mahaifiyar fanne matarsa

kenan hukuncin daya yanke akan yar tasa ba

qaramin tashin hankali tashigaba sbd tuna furucin

yar Tata acan baya tashi kuma san mijin Nata

idan yahau baya saurin sauka kuma bai cika

alqawari kuma ya karyaba

Hakan yasa ta shiga wani Hali don Gani take

Kaman lokacin rasa yar tatace taxo gashi kuma

yace Mata karta sake ta fada Mata har sai an

kalmmala komai

Mahaifin fanne shine yadau dawainiyar komai na

game da kayan Viki da kuma Yan abubuwan da

baza. A rasaba Wanda addini ya tanadar a

bangaren mahaifiyar Tata kuwa Sam bata wani

amanna da wannan bikin don Gani take kamar

kashe kan Nata zata kamar yaddah ta fada a

baya shin waye Akabama fanne sadaka

Abubakar sadiq matashin saurayi ajin farko farine

tes dashi ga dan dogon hancinsa yarone Mai

ladabi da biyayyah Da sanin ya kamata ga ganin

Girman na gaba dashi Tun yana qarami

mahaifinsa ya rasu

Don haka Dan uwar mahaifiyarsa ya riqeshi shine

Tun yana aji uku na gaba da firamare mariqin

Nasa ya rasu hakan

Hakan yasa yake zuwa shagon wani a

anguwansu yana masa yan aikace aikace da

koyon Sana. A domin samun na kashewa don

daman abbakar din Mai zuciyar neman na

kansane

Don haka ya tashi tsaye wajen neman na kansa

ganin Hali da dabiun abbakar ne yasa mahaifin

fanne yai sha, awar Bashi yarsa sadaqa a lokacin

da yake fada masa saida ya tsaya sosai ya

tunani kamin ya bashi masa ta bangaren mahaifin

fanne kuwa murnane tattare a tare dashi don

yanada yaqinin abbakar bazai watsa masa qasa a

ido ba sbd dattakon yaron yaroneshi amman halin

manyane dashi

Duk da Bai farin ciki da kyautar da akai masa

kuma baiyi na, am da itaba amman ba zai iyama

tsohon gardamaba don yana ganin girmansa don

daman ance ai shaidanne kawai Ke maida hannun

kyauta baya hakan yasa ya amshi kyautar da

akai masa hannu bibbiyu gamida godiya tareda

wata yar guntuwar murmushin da zamu iya

kiranta da yaqe a ranan da mahaifin fanne ya

sanar da abbakar kyautar da yai masa ranan

wuni yai bashi da kuzari don Ko abinci kasaci yai

ya kasa fita shago mariqiyarsace ta leqo gamida

fadin abbakar lfy you baka fitaba Ko bakajin

dadine yace eh goggo zazzabine Ke damuna tace

to ina zuwa bari na samo maka magani don

nasan ba za, a rasaba nanta barshi ta fice daga

dakin

A daren ranan kasa barci yai ya saqa wannan ya

kwance wancan wai duk dandai ya samu mafita

Amman Ina a haka har gari ya waye abufa yai

qamari don har abbakar ya fara ramewa tunanin

irin zaman da zasuyi shida fanne kawai yake don

tuntuni yasan halin yarinyar ya tsani halayyan

yarinyar da kyamar abubuwan da take aikatawa

Domin shi Ko kadan baison Yaga yaro na Raina

na gaba dashi ita kuwa fanne ba ruwanta tsoho

Ko girman babanta yai idan ya shigo harkarta

yanxu zata yayyafa masa ruwan rashin Kunya kai

Ko kallone kai Mata wanda bai gamshetaba

yanXu saiku Debi Yan kallo kaida ita

fanne ba sa, an abbakar bace don da yayanta na

uku yake abota don akwai wata Rana da abbakar

din ya samu yayan ita fannen akan su dinga

tsawata Mata akan abubuwN da take domin duk

ba masu kyau bane sai ce masa yayi su Gani

suke kamar da shafar aljanu a lamarin fanne don

abubuwan Nata kullun gaba suke mun rasa

yaddah zamuyi da Ita saidai addu, a kawai da

mukasa a gaba kaima Ka tayamu da addu, a

abbakar yace Ina ba wani addu, ai yasin bataji

duka Bane kawai tsagwaron rashinjine Ke

damunta da yarinta kuma wlh Ina tabbatar maka

da duk sanda ta shigo sabgata saina Mata abinda

harta mutu bata Manta dashiba don wlh saina

Mata dukan da sai tayi satittika a kwance abokin

Nasa yai Daria yace abbakar kenan don ba tare

da Ita kakeba shiyasa kake fadin haka abbakar

yace to lallai zakasha mamaki Allah dai yasa tayi

gigin shiga sabgata Ka Gani

ita kanta fannen Tana mamakin yaddah akai take

shakkar abbakar din koda tayi niyyar sauke masa

buhun masifar Tata sai taji ta kasa dukda kuma

irin shishshige matan da yake don Kai tsaye yake

tunkararta ya fada Mata cewa abinda take babu

kyau ta gyra halinta da tayi niyyr mayar masa da

martani Ko zaginsa da zarar ta kalli kwayar

idonta duk saita daburce gaba da gabanta Kenan

wai aljani ya taka wuta

Ita da kanta idan ta zauna saita dinga tunanin

shin wai meye take gani a cikin kwayar idon

abbakar ne wnda Ke firgitata haka Amman har

izuw yanxu bata samu amsar hakan ba abinda

bata saniba kuwa shine akwai wani sirri da Allah

ya boyene Wanda sai shida kansa yasan ko meye

wannan

Jama. A da dama sunyu mamakin wannan Hadi

da akai domin abbakar salihin matashine kuma

natsastse Wanda Ke ganin darajar na gaba dashi

ita kuwa fanne kowa ya Santa batada Kunya

Kona misqara zarratan ballagazaace wacce

qaramin Abu zaisa yanxu Ku dambace kaida ita

bata ganin mutuncin kowa a idonta duk girman

mutun bata shayin angaza masa rashin mutunci

Ko watsa masa ashar hakan yasa Jama. A da

dama Ke zuwa masa jaje na rashin zabama

yayansa uwa ta gari da kuma Yan Bani na iya

dake zugashi akan karya sake ya yarda da

kyautar da akai masa

Mezai faru ta bangaren fanne zata amince Ko a, A

idanma ta amince ya zaman auren nasu Zai

kasance?

Mu hadu a next chapter

Uwar goyo

Chapter2

Jama, a da dama na ganin rashin dacewar tasu

don babu yaddah za, ai tsuntsun dake yawo a

sama yai rayuwa da kifin dake cikin rigiya abinda

Basu saniba shine bakin alqalami ya rigada ya

bushe domin tuntuni ya rigada ya amsawa

mahaifin Nata yanxu kuwa babu ta yaddah za. Ai

ya koma yace masa ya fasa ba, a dau tsawon

lokaciba akasha Viki dukda dai angon ba son

auren yakeba don daqarma ya iya zuwa wajen

saurin auren don daman masu iya magana na

fadin lbrn zuciya a tambayo fuska

Bangaren amarya kuwa abin ba yabo ba fallasa

Don tunda aka fara hidiman bikin batacema kowa

komaiba don koda mahaifin Nata ya kirata

gamida sanar da Ita hukuncin daya yanke a kanta

din na hadata aure da abbakar shirun da tayi ya

nunar masa data amince da zabin da yai Mata din

don haka farincikine fal a tare dashi

Don haka ya tashi gadan gadan wajen ganin anyi

hidiman bikin lfy da kansa ya Kama musu gidan

haya saidai daki dayane kasancewar Mai qaramin

qarfine

Bayan an gamashan Viki yau washe gari amarya

da ago sukaje gaisheda iyaye daman Al, adar

Garin Kenan don haka Suna zuwa mahaifin

fannen ya jashi bangarensa domin su tattauna

ananne yake cema abbakar din abbakar don Allah

inaso kaimin wani Al qawari guda kuma wannan

alqawari ba komai Bane illa so nake Ka riqemin

fanne Amana abbakar duk runtsi karka rabu da Ita

idan har kaimin hada Ka gamamin komai a

rayuwa kaman asirinane Ka Rufe domin manxon

Allah yace duk waNda ya rufama wani asiri to

kuwa Allah Zai nisantar da fuskarsa Ga shiga

wutar jahannama

Nasan bakason fanne kawai girmana da

mutuncina yasa Ka amince akan ta zama

abokiyar rayuwarka domin jama. A da dama na

fadin aurennan nakuba jimawa zaiyiba to inaso

don Allah kabama marada Kunya inhar Kai haka

na tabbata Allah bazai barka hakaba Allah kuma

yasa maka albarka ya kuma saka Maka da gidan

aljannah

Yace Amin baba kuma nai make alqawarin duk

runtsi Zan riqe maka yarka bisa Amana sannan

sukai sallama

Viki ya waste kowa ya Kama gabansa akabar

abbakar dagashi sai amaryarsa sai muyi musu

fatan zama lfy da kuma Bashi icon cika alqawarin

daya daukarma baban nata

A ranan da abbakar ya fara shiga dakin fanne da

dare ya samu har tayi barci abinta tayi daidai

akan gadon basa banban inji bahaushe

Be abinda Ke damunta barcinta kawai take

Sharawa

Daman ba qaramin takaici takejiba idan Tana

kwance akan tabarman Karan dake dakinta

ranaku da yawa Ko runtsawa batayi don Tana

kwanciya ta barman zataita cizonta Kota Ina

Tana sha, awar taje gidan qawarta ta ganta akan

gadonta abin ba qaramin burgeta yakeba kuma

yana daya daga cikin dalilan da yasa bataima

baban Nata musuba alokacin da yace Zai hadata

aure da abbakar ayau ne ta kudiri niyyar fanshe

barcinta data dinga rashinyi a kwanakin baya duk

ta dalilin kwana akan taburman Kara tace in

banda talauuci mai zaisa mutun ya dinga kwana

Akan tabirman Kara duk wani juyi da zakai saita

sokeka

Alokacin data hayekan gadon natane taji wani

sanyin farinciki na ziyartan zuciyarta tace Ashe

daman haka kwanciya akan Gado yake da dadi

Aiko datasan hakane da tuntuni ta amince da

zabin da mahaifin Nata yai Mata na farko kilata

huta da rashin yin barci Amman Ka kwanta kan

tabirman Kara duk inda Ka juya saita sokeka da

wadannan tunanin tunanen har barci ya kwasheta

don batasanma angon Nata ya shgo ba

Dukda abbakar din ba sonta yakeba amman baiqi

shigo Mata da kazar amarciba ganin Tana barci

yasa Bai tashetaba ya aje mata a gafe shikuma

ya fita waje gamida dauro alwala Nan yaxo ya

fara nafiloli Bai tsayaba saida dare ya tsala

Donma wai ya farajin barcine ya dafe Kai shi

kadai yana tunani yace ohni abbakar shin Wai

tayaya zamu fara wannan zaman auren ne oho

Allah kadai shi yabarma kansa sani saida asuba

ya tashi bayan yai Alwala gamida shirin yafiya

masallaci itama ya tasheta don Tai sallah

Amman har yaje ya dawo bata farkaba hannunsa

yasa ya dinga jijiga gadon har saida Yaga ta

bude ido sannan yace Mata to ai saiki tashi kije

kiyi sallah kinga har gari ya soma wayewa ba

yaddah ta iya haka ta tashi gamida zumburo

bakinnan Yayo gaba wai donme Zai Mata

katsalandan alokacin da takejin dadin barcin Nata

harda mafarkai masu dadi

A gurguje taje tayo alwala tai sallan sannan ta

koma kan gadon abbabakar yai mamakin irin

wannan sallah na fanne Bai kamata ace yar

malam Mai farin sani Kaman fanne ace bata iya

sallah ba abinda kuwa bai saniba shine Tun

daman can fanne ba sallah takeba sai an takura

Mata take wani lokacinma idan tayi alwalan

dakinta take guduwa taje ta zauna Ko kuma Tai

kwanciyarta yanxu hakanma tadaiyinne kawai

don karya takura Mata adaidai lokacin da takeson

ta huta

Yace fanne Ga abin kari Nan a cikin ledar can

saiki dauka ki karya da Ita Nina tafi kasuwa

dukda taji abinda ya fadan Aman saitai burus

dashi abin yai masa ciwo Amman saiya nuna Bai

damuba ya kada Kai ya wuce abinsa

Ganin ya fita yasa Tai saurin saukowA tuni

miyonta ya tsinke da abinda ta Gani tace wai

dadi kasheni inji barawon takanta yau itace dacin

kaxa yaushe rabonta da taci kaza don haka nanta

bude ciki taita diban kazarnan har saida taji tayi

qat sannan ta saurara gamida aje saurAn agefe

tace anjima idan ta farka daga barcin ta qarasa

Hakan kuwa akai Tana farkawa misalin qarfe

daya na Rana taqarasa sauran lol

Da farko zaman doya da manja suke kodade daga

wajen abbakar shi bai nemi wani Abu daga

wajentaba baiso ya nema ya janyoma kansa jafa,

I da rashin kunya dukda kuwa iya qoqarinsa da

yake wajen ganin ya kyautata mata inda zasu

shekara a haka babu Mai tankama wani inhar ba

shine yai Mata maganaba to ba zatai masa ba

don wani lokutanma koda yai Mata maganaba

bata cika amsawaba don akwai lokutanda da

zaran taga ya shigo take fita waje ta zauna harna

tsawon wasu lokuta

Har yanxu girman kan fanne da Jiji da kanta babu

Wanda ya daya ballentana axoga yinma Miji

biyayyar aure

Abbakar Dai kallonta kawai yake da kuma jiran

ranan da allah zaisa ta gane gaskia yana qoqari

wajen sauke haqqinta dake kansa kasancewar

har yanxu yana zuwa shagonnan na anguwansu

da yake musu Yan aikace aikace

Ballentanama ganin gaskia da riqon Amana irin

na abbakar yasa Mai gidansa yasa yake shirin

dude masa wani babban shago wanda abbakar

Dinne Zai dinga Kula da komai abbakar wani irin

mutun ne Maison kyautatama iyalansa Kai

hardama Wanda suke tare dashi don baiqi ya

qarar da duk abinda yake dashiba a lokaci daya

don kawai ya biyama kansa buqata daman Ai

masu iya magana sunce biyan buqata yafi dogon

buri

Duk idan ya dawo daga kasuwa bai shigowa

hannunsa haka kawai dole saiya taho Mata da

wani abu dukda basonta yakeba da kuma

kyamatar halinta da yake gamida irin zaman da

suke to yana qoqaru wajen ganin ya farantamata

Rai kyautatawan da yake Mata da haquri Ga irin

zaman da yake da ita hakan yasa ta fara

saukowa harta fara masa magana gamida Bashi

duk wani kulawa da maigida ya cancanci ya

samu a wajen matarsa wannan sauyi da aka

samu daga wajen fanne shiya dinke barakar dake

tsakaninsu don daman ance mahakurci mawadaci

dukda iya qoqarinta da take wajen ganin ta

kyautata masa hakan baisa abbakar ya game

yarda da Ita Dari bisa dariba don masu iya

magana na fadin Mai Hali bai sauya halinsa

domin tsoron kar saiya Saki jiki da ita sannan ta

bullo masa da wani halin Amman dukda haka Bai

fasa yin Mata addu. A akan Allah yasa ta gane ta

gyara halaiyarta va

Har yanxu fanne bata gyara halaiyyartaba Kai

hardama Wanda abbakar din Bai San dasuba

wani lokacin idan abin ya taso Mata saiya baka

mamaki abin harya farabama abbakar tsoro sai

yanxu ya yarda da maganan yayanta da yai masa

a baya akan akwai shafar aljanu a tattare da Ita

don harya fara tunanin daukarta zuwa wajen

kalamai domin Ai Mata ruqiyyah

Abin mamakin shine ta bangarensu basa fada

jama, a da dama Suna mamakin yaddah akai

auren abbakar da fanne ya Dade haka ba tare da

samun wani matsalaba harda mahaifan fannen

kullun cikin sama abbakar albarka suke don yayi

namijin qoqari kasancewar Basu taba tunanin

fanne zata zauna gidan aure lfy Lau ba tare da

fitintunu sun biyo bayava domin sunfi kowa sanin

halin yar tasu

Don Mai haquri sosai ne Zai iya zama da ita duk

wani irin salon iskanci da zata bullo dashi

abbakar yasan ta yaddah zaibi ya shawo kan

lamarin wani lokutan idan ta taso da iskancin

Nata fita yake yabar Mata gidan don ya rigada

yayima mahaifin Nata alqawarin duk runtsi Zai

danne duk wani rashin mutunci da zatai masa

Ita kanta takan tazauna taita tunani tace haba

sai kace bada mutun nake zauneba kaita

tsokanan mutum Amman ya nuna baimasan

kanayiba Kai wannan mutumin inage Bashi da

zuciya kodai yabama kare ya cinyene oho

Kai Allah ya wadaran nake ya lalace ta girgixa

Kai gamida cewa wlh abbakar ba irin mijin da

nakeson aura Bane Ni Wanda idan na takaloshi

zai biyemin nakeso idan ta Kama mu dambace

duk Wanda ya kada wani to shine jarumin

Amman wannan wani solobiyo dashi tirr da irin

wannan Hali na abbakar

Abbakar kuwa tunani da irin zaman da suke d

fanne yasa harya fara ramewa a tsaytsaye bayan

Shiba ciwo yakeba sai yar waya Ita kuwa inka

ganta kumbura kawai take ba ruwanta yin abinda

takeso kawai take ba ruwanta game da mijina

kuwa ko ruwan wanka bata kai masa shida kansa

yake fita dibo ruwan da zaiyi wanka abinci kuwa

saidai idan ya dawo yaje wajen da ake aje

kwanuka ya dauka ya zuba da kansa Ko sau daya

Bai taba nuna Mata ya damu ba

Matan gidan da suke haya da yake gidan hayane

Ko wacce a cikinsu Suna sha, awar yaddah

abbakar ya maida fanne sarauniyar Mata masu

hassada nayi fatan Allah yasa Suma mazajensu

gane su dinga Basu irin kulawar da abbakar

kebama fanne nayi wasu kuma wautar fannen

suke gani akan abinda takema mijin Nata domin

kuwa Kaman wautane kullun idan ya dawo daga

kasuwa sai an kawo masa qarar fanne idan yai

bincike saiya Gano itace bata da gaskia wani

lokacin kuma itace keda gaskia Amman tabi har

qofar dakin macen su kacame da dambe Ko kuma

cacan bake sau da yawa dashi ake hadawa acin

musu mutunci abin na masa ciwo sosai saidai ba

yaddah zaiyi don haka Allah ya qaddaro masa

Bashida wata mafita daya wuce ya dinga addu, a

d kuma godema Allah

Domin alah na fadin Bai daurama nawa abinda

yafi qarfinsa sannan kuka bawa Bai kujema

qaddararsa saidaima yaje ya sameta

Sauda yawa abbakar kan zaunar da Ita yai Mata

nasiha akan ta daima abinda take domin ba Mai

kyau Bane ya kamata ta aje duk abinda take Ada

ta gane cewa yanxu ta girma ba yarinya bace ita

amman me a maimakon ta dauki maganan mijin

Nata Ina Ai a lokacin dayai maganan Tana tashi

Anan take bar magan ganin abin Nata bamai

sauqi Bane kuma ance Mai Hali Bai canja halinsa

yasa yasa Ma sarautan Allah ido

Don bazai iya kai qararta gurin mahaifintaba

kasancewar girmnsa da yake gani sannan duk

sanda suka hadu Kalman dai dayace shine Ka

qara haquri hakan yasa koda yai niyyar Kai

qararta wajen mahaifin Nata yana tune

kalamansa sai yai duk jikinsa ya mace sannan

koda yayi quri yakai qararta din ya tabbata marar

haqurin Kenan

Tunda sukai aure har izuwa yanxu ba, a tabajin

kansuba kasancewar abbakar din Mai haqurine

Bai biye Mata Amman ta bangarenta

Idan Sanrantane bataqi kullun su kwashi Yan

kalloba don daman abinda takeso Kenan

Sai kuma akai rashin sa, a mijin Nata mai

haqurine sunansa abbakar saddik

Komai zatai masa cikin tsiwa take masa Kai

hartakaiga idan yasata aiki kai tsaye take ce

masa ba zataiba Gar take mayar masa da

magana ba tare da taji shakkarsava Kota karanta

masaba a matsayinsa na jikinta Ko kadan batayi

masa biyayyah irin wanda aka sani mace

tanayima mijinta

Bata gaisheshi idan gari ya Wye haka kuma bata

masa sannu da zuwa din ya dawo daga kasuwa

Kai koda waje take idan ya shigo da Kaya bata

zuwa ta masa a hannun Nasa

Ga almubazzaranci duk abinda ya kawo haka

zata dinga watsar dashi Ko kuma idan ta tashi

firkawa saita dafa da yawa Wanda ba zasu iya

cinyewaba a maimakon idan sun rage Ko

almajirai tabamawa Ina Ai barin abincin take har

saiya lalace sannan ta zubar a bola Ga rowa

wohoho fanne akwaita da rowa kamar qanuwar

qaruna hatta Mai nemowan ya kawo bata barshi

a bayaba saiya jibgo Mata name ya kawo Amman

idan ta girka daqar yake iya samun yanka uku

Allah sarki saikace ya roqa Amman dukda hakan

Bai taba nuna Mata ya damuba

Abbakar sai zabgewa yake a tsaye kamar wani

Mai jinya bacin kuma lfyrsa qalau ba abinda Ke

damunsa sai rashin mutuncin da fanne Ke shuka

masa Kala Kala saidai duk rashin kirkin Nata da

take Mai bata taba zaginsaba harkar gabanta

kawai take Ga wata uwar kiba da tai kamar ta

fashe Ga surutu fanne akwaita da gulma da

tsugudidi ta saka wannan ta canja wancan

Shekararsu biyu d aure Amman Basu haihuba

shiru kakeji tamkar an shuka dusa lamarin ya

damu fanne sosai nanfa ta shiga sintirin zuw

gidan bokaye da kalamai harda asibiti taje

Amman ba, a samu nasaraba domin kuwa akwai

wani zuwa da tayi asibiti bayan likita ya gama

mata Yan gwaje gwaJensNe yace hajia saidaifa

kiyi haquri da yaddah allah ya halicceki bazance

ba zaki haihuba Amman zaki Dade kafin ki haihun

kuma ba lallai Bane ki samu zuri, a da yawaba

don bisa binciken da Naki koda zaki iya haihuwa

qarqari da dayane zuwa biyu bayan Nan kuma

saidai kiyi haquri hajia

Tur qashi Toya Kenan ya zatai da rayuwata Ita da

bataso abbakar ya kawo Mata kishiya tafison su

zauna su biyu sai kuma yaran da zasu Haifa lol

Tace Dole nasan abinyi Tun kafin ya sani hauka

don nasai idan abbakar da Yan uwansa sukasan

inada matsala a mahaifata lallai zasuyimin

saKiyar da babu ruwa don daman tasan ba sonta

yakeba duk a dalilin halinta marasa kyau Amman

ita bata ganin abinda takeyin musu

Shikam abbakar baimasan abinda ake tayiba

domin shi ya rigada yayi tawakkali Ga Allah ya

sani samu da tashi duk daga Allah suke hakan

yasa baima wani damu kansaba sannan kuma shi

, ain daman baso yake ya haihu da itaba don

lallai sai Dan data Haifa ya dauko halinta don

dama yaro a noon yakeshan hali sannan bashida

yaqinin zata iyama yaro tarbiya ta kwarai domin

kuwa ita kanta tarbiyyar ba ishenta yaiba

Fanne kuwa ba haqura taiba har yanxu neman

maganin haihuwa take duk Anan kudinta yake

tafiya tashi ba biyan buqata Amman wani

bangare na zuciyarta na fada Mata cewa taci

gaba da nem domin kuwa Mai nema yana tare da

samu haka kuma Wanda ya haji bau Saba Bane

Zuwa yanxu fanne ta fara damun abbakar akan

matsalan rashin haihuwarta da dare bata barinsa

yai barci sai Mita akan yaqi ya nema Mata

maganin haihuwa daman Aita gane ba Santa

yakeba Bashi Ita akai sadaq shiyasa Bai damu da

rashin haihuwar Tata ba maganganu dai marasa

dadi ta dinga fada masa shi kuwa Ko kallon inda

takema baiyiba balle ya tank mata wannan abin

da yake mata yana damunta sosai da yai shiru

yanajinta Tana magana yaqi tanka mata gwara

ya dauko sanda yaita rafka Mata da zaifi

Ana cikin hakane Allah yaima mahaifiyar fanne

rasuwa jinya Tai sosai Wanda har saida yakaita

Ga kwanciya a gadon asibiti jikin yai tsanami duk

yayanta wadand sukai aure saida sukaxo dubata

Tun daga garuruwan da suke auren jikindai ba

dadi sai, an kwantar an radar bata sanin Wanda

Ke kanta Ana cikin hakane ta soma samun sauqi

don har akan danyi hire da Ita a wani yammacine

da abbakar yaxo dubata don daman kullun sai

yaxo safe da yammah don ganin yaddah jikin

nata yake a lokacinne ta zaunar dashi Tana masa

nasiha Mai tsuma jiki gamida godia akan

riqemusu fanne da yai bisa Ga Amana don ta

tabbatar idan ba Mai haquri kamarsaba babu

Wanda zai iya zama da fanne zaman aure har

izuwa wannan lokacin sannan ta qara da damqa

masa amanar fanne a hannunsa daya riqe musu

Ita bisa amana sannan ya qara haquri domin duk

Mai haquri Allah na tare dashi a koda yaushe

yace insha Allahu goggo sannan ina godia da

wannan nasihar taki abbakar Ji yake kaman

wasiyyah take Bashi bayan ta gamane ya tashi

ya tafi hakan kuwa akai adaren ranar misalin

qarfe biyu na dare ciwon Nata ya dawo ta qara

birkicewa misalin asuba tace Ga garinkunan Allah

sarki Kullu nafsin za'ikatul maut washe gari aka

kaita gidanta na gaskia abbakar yai mutuqar

girgiza game da mutuwar baiwar allahn Nan

musamman idan ya tuna nasihun data dunga

masa a yammacin Jia sai yaji Hawaii na zubo

masa a fuska yace haqiqa duniya abin banzace

don duk Wanda yai damara sbd duniya to lallai

ya kamata ya kwance domin kuwa ita mutuwa

bat sallama

Su fanne anyi kuka Kaman rai Zai fita mutuwar

umar Tata ta girgizata domin bata taba ganin

mutuwa Kuru kuru da idontaba sai akan mamarta

saidai taji a bakin Jama a cikin yan kwanakin

ukunnan idan kaga fanne zaka rantse kace ba Ita

bace gaba daya ta sauya hakan ba qaramin dadi

yaima abbakarba donji yake kamar a jikinsa

kamar shiriyace taxo Mata saidai abinda Bai

saniba shine masu iya maganafa sunce mai Hali

baya sauya halinsa don a ranan addu, ar bakwai

din mamar Tata saida aka dubi yan kallo ita da

wata makwabciyarsu akan sosai lol

Chapter3

Haryanxu fanne bata sauko game da hayyarrArta

ba kullun qara gaba abin yake da zaran yayi

niyyar daukan mataki sai ya tuna da wasiyar da

mamar Tata ta Bashi a daren ran da zatabar

duniya hakan kesa gwiwowinsa na sanyi gameda

hukuncin da yai niyyar daukan har ya fasa cikin

halayyar fanne Abu dayane yafi qonama abbakar

rai shine rashin girmama na gaba da ita duk

girman mutun yanxu saita zumbudo masa ashar

wannan halayyah na fanne ba qaramin qonama

abbakar Rai yakeba wasa wasa abin Nata sai

qara ci gaba yake hakan yasa Jama, a ke kiranta

da fanne tsigalagala wasu su kirata da tsigai

wasu kuma su kirata da tsigala duk ta dalilin

halin fanne yasa basu dadewa a gidan haya ake

korarsu daga aurensu zuwa yanxu sun zauna a

gidan haya yafi Goma sha uku don akwai gidan

da sati daya sukai a ciki aka koresu waje duk ta

dalilin munanan halayyarta

Ba qaramin kudade abbakar Ke kashewaba don

ba duk gidan da suka Kama Bane idan sun tashi

ake maida musu da kudin nasuba haqiqa abbakar

Yaga rayuwa

Kodama Ana barinsu a gidan hayan

Halayyar fannema kawai ta ishesa

Ballentana yanxu data bullo masa da wani sbn

iskanci sai cikin dare zata tashi taita nemansa da

rigima idan yaqi tankata taita girgixa masa qafa

akan Dole saiya tashi wasu lokutanma a tsakar

gidan yake kwana nanma Bai mataba har tsakar

gidan take biyoshi saida Yaga alamun abin Nata

bamai sauqi Bane saiya soma kwanan qofar gida

Tun Bai sababa haryaxo ya Saba

Daga baya kuma suka sasanta Amman saidaya

bata dubu biyar abindai nasu Kaman ya lafa sai

kuma ta tsiro da wani sabon Salo wai indai har

Zai kwanta da Ita to yasin saiya biya kunji

shegiya sai kace karuwa. Da

Wannan baqin Halin irin na fanne ansha kaisu

police station

Sunje cargi office yafi a qirga don da zaran ta

tabo marasa haquri sai sace sai anje police

station wani banzan haline da fannen da zaran

sun fara cacan baki da Kai Ko fada to duk abinda

Ke kusa da Ita Ko meye saita sauka tace zata

maka makakoda kuwa menene

Akwai lokacin da fada ya hadasu da wata Mata

wacce suke haya tare gulman Matar akai da

kuma akabi diddigi sai aka Gano daga wajen

fanne gulman ta fito Matar da aka daurama

gulman kuwa tace Aiko ba zata taba yardaba

daqar abbakar yashawo kan lamarin Ashe Ita

fanne abin nanan a ranta Wai sbd Matar tayi

Mata tatas a cikin Jama. A kuma abbakar ya

tsareta akan karta Tofa komai hakan yasa ta

kasa daukar mataki Ashe abin na raNta saidata

Bari anyi Kwana biyu sannan taje ta samu Matar

a kicing kuma a daidai lokacinda take kici kicin

daura sanwan dare

Daman fanne da rikici ta shiga kichin din Tana

shiga sai cema Matar tayi Ke kuma meye na

hararata budar bakin Matar sai tace a yaushe na

harareki din? Daman abinda takeso kenan Matar

ta maida Mata da martini kafin kace me sun

kicime da fada fanne batai wata wata ba ta

rarumo tabaryar dake kusa da Ita ta makama

Matar a kafada zata qarane sai kuma akai rashin

sa. A kafin ta qara Kai Mata tabaryan itama

Matar ta rarumo tabaryar da take daka dashu

saiji kake gauuuuu a hannun fanne Aiko fanne ta

kurma wata mahaukaciyar qara Wanda ya janyo

hankalin Jama

Ar dake tsakar gidan har suka fahimci akwai

matsala a cikin kichin nanfa sukai kansu domin

su raba fadan kafin kace me har Jama, a sun cika

qofar kichin din Kai harda makwabta abbakar na

tsaka da kasuwancinsa yaro yaxo ya samesa

gamida fada masa abinda Ke faruwa nan ya Rufe

shagon Nasa ya taho a gigice saidai kafin ya

qaraso Ashe har mijin matar yakai rahoto a police

din Yan sanda suka hadoshi da yan sanda biyu

mace daya namiji daya domin awuce da fannen

police station don har wajen tafia da itanma

saidatama yar sandan rashin kunya Ita kuma ta

mammaka Mata kulki a kafada kafin abbakar ya

qaraso har an tasa qeyarta Ji yai Kaman ya Barta

Tai Yan kwanaki a hannunsu koda zatadan dawo

cikin hayyacin Nata Amman Ina bazai iyaba gashi

bawai wasu kudine a hannunsaba kasancewar da

damuunane market baya ja

Jiki ba kuzari ya Kama hanya ya nufi station din

babu ko kunya tadinga zaiyano abinda ya faru

saidai dagajin yanayin magananar zakasan duk

qaryane Ga hannunta harya kumbura da qar ya

samu a ranan aka Bashi belinta bisa sharadi

saiyakai wannan Matar asibity an Mata maganin

ciwukan da fannen taji Mata yace ba damuwa

bayan an kammala komai suka dawo gida itama

fannen abbakar ya Kira Mai dauri aka daure Mata

hannun Nata saidai tasha wuya don saidatai

nadamar biyema Matar ammanfa Matar ta zagu

ta uwa ta uba babu irin zagin da Matar

batashaba

Nan ne Mai gida yacema abbakar lallai saisunn

tashi masa a gida don Nan gaba matarsa zata

iya kisan Kai ba irin roke da magiyan da abbakar

Bai ma Mai gidanba Amman yaqi yarda yace Kai

ayau dinnanma zaku tashi inkuwa kaqi yanxu na

Kira hukuma da sauri abbakar ya miqe gamida

cewa Kai haquri ranka shidade badai gida baneba

zamu tashi ba saitakaiga hukuma sun shiga

cikiba nanfa abbakar ya tashi cikin sanyin jiki ya

shiga dakinsa abin duniya duk ya damesa yanxu

Ina zanje na samo kudin haya Kai gaskia na gaji

wlh na gaji da irin wannan hijiran da muke a

kullun sai kace tururuwA nanfa ya rasa abinyi

take shawara ta fado masa yace Mata gida kawai

Zan maidake har izuwa randa Zan sama Mana

wani gidan haka kuwa akai Ita kanta ta gaji da

wannan yawo na gidan haya da suke Aman me

maimakon ta tausayama mijin Nata ta gyara

halayen Nata marasa kyau Ina Ai saima wuta da

take hura masa akan lallai ya samo musu gidan

da zasu koma domin su huta da wannan

galantoyin da suke akanTiti. Kullun

Kuma su huta da takaicin duniya

Acan gidan nasuma data koma nanma ba a

hutaba don kullun sai an jita da matan yayyinta

duk kuwa da Jinyan dake hannunta sai kuma akai

sa. A matan daidai da itane basa qyaleta lamarin

ya fara birkita mahaifin Nata idan ya zauna yana

tunani saiya dunga jinjinama abbakar yace lallai

abbakar ya cika mai haquri don tunda sukai aure

Bai taba kawo qarartaba haka kuma nasan Dole

duk yaddah za, ai saita bata masa Rai lallai

abbakar ya cika Mai haqurin gaske

Rashin kunyar fanne ba akan matan yayanta ya

tsayaba harta yayyan Nata zuba musu rashin

kunya take

Musamman idan Tana fada da matansu da zarar

anga itace bata da gaskia Tofa ba daman ace

Mata itace batada gaskia don yanxu zatai tsalle

ta dire tace goyon bayan matansu suke kawai

don anga marainiyace Ita mahaifiyarta ta rasu to

komadai menene babu Wanda ya isa ya taka

Mata birki tunda ai gidan ubantane ,, ko abinci

suka girka suka kawo Mata bata sai tace Wai

sunsa Mata magani habaici Kala Kala nayau

Saban na gobe daban suma sun soma gajia da

halin Nata yasa daya daga cikin yayyun Nata

wanda yake abokin abbakar dinne ya samesa har

shagonsa domin ya tuntubeshi game da maganan

neman gidan da yace yana nema da ya samesane

yake fada masa gaskia cewa har yanxu yana

nema kuma dukda rashin kudi yasa yake Dan Jira

kafin komai ya warware kumama daman so yake

tunda hannun fannen Vai warkeba ta zauna Anan

har sai hannun Nata ya warke sarai sannan

abokin Nasa yayan fannen yai shiru yana

Tunani don shida kansa ya fahimci abbakar ya

fara hajia da zama da fanne a ransa yace lallai

dole asan yaddah za, ai don ganin fanne ta koma

dakinta idan kuwa ba hakan to sunaji suna Gani

zasu rasa aurensu don Ko Jia daqar yashawo kan

matarsa Amman da dabircewa Tai akan Ita

gidansu zata tafi don ba zata iya juran halayyar

fanneva abbakar Dunne ya katseshi da fadin to

yanxu ya kake ganin za. Ai Kenan yayan Nata

yace kawai hada kudi zamuyi mu ganganda a

samo Muku gidan haya don zaman fannen a

wannan gidan ba alkhairi Bane abbakar yai

murmushi gamida cewa tona gode hakan kuwa

akai ba tare da bata lokaciba suka samu gida

mutun dayane a gidan daga shi sai matarsa don

Ko Yaya Basu dashi Amman me abbakar yace Ai

lallai sai fanne ta watstsake sannan zata tare a

gidan da suka koman nanfa murna ta koma ciki

don har sun fara murna wato qaya zata bar musu

gida sai kuma gashi mijinta ya bullo da wani Salo

na saita wake don Gani suke Kaman wani lokacin

zata dauka mai tsawo a haka taci gaba da zama

saidai baban Nata Yaga alamun za, a bata Goma

daya bata gyaruba hakan yasa ya miqe tsaye

wajen nema Mata magani don hannun Nata

kullun ba sauqi don harya fara wani ruwa Mai

wari don ko wucewa kaxoyi ta kusa da ita to

sauka toshe hancinka Amman da yake Allah

majiqan bawansane da baban Nata ya duqufa

davyin Mata addu. Oi akan ciwon safe da ran da

dare ba fashi cikin ikon Allah ba, ai satiba ciwon

ya soma warkewa ruwan da yake ya qafe nanfa

fanne ta soma murnan komawa gidan mijinta don

ita kanta ta soma qosawa databar musu gidan

tace me za, ai da wani gidan da bana mijina ta

tafijin dadin gidan mijinta don Ko cimar da take

acan batayi Anan bata samun kudin kashewa

dukda dai yana bata Amman ba koda yausheba

Amman da a dakin mijinta take duk yaddah za, ai

kullun saita samu kudin adashi don koda Bai

bataba to saita Zara a cikin na cefane cikin ikon

Allah hannun fanne ya wake sarai suka koma

sabon gida a ranan da zasu koma ta dinga

yabama matan yayyaen Nata baqaqen

maganganu babu Wanda ya tanka Mata don

idanda Sabo sun saba a yammacin ranan da zata

koman ba Wanda taima sallama haka Suma babu

Wanda yai Mata rakiya sukace yafi non fari don

daman barinta gidan suke buqata

Fanne ta koma gidan abbakar ne da waNi buri a

Ranta Wanda Tai alqawarin lallai saita cimma

wannan burin nata sannan zata samu kwanciyar

hankali

Sun koma basufi da sati biyiba ta farama

abbakardin qorafi akan lallaifa saiya siya musu

gida sun koma su huta da biye biyen gidan haya

da farko Qin biye Mata yayi Amman kullun cikin

mitA take akan lallai saifa yasai musu gida sun

koma

Don akwai raNan da da safe bayan ya gama

karyawa Zai tafi kasuwa ta tsareshi aqofa ta tare

qofar gamida fadin wlh ba zakafitaba abbakar

tunda dai kaqi saurarata akan buqatata nason ka

siya Mana gida saidai Yaga abin Nata bamai

sauqi Bane nan ya soma Mata nasiha gamida

fadin

Wlh fanne Banda kudin da Zan siya gida koda

kuwa qaramine kinsan shagon da nake Kula dashi

a kasuwamafa ba shagona Bane kayan wanine

nake tsarewa don haka Ina zanje na samo kudin

da zanje na siya Mana gida yanxu?

Wanda yai nisa baijin Kira maganganun da yai

Mata duk ba Wanda ya ahigeta Ita gani take

kamar bason siyan gidan yakeba inba hakaba don

kuwa bajintar da yake musu ko wani Mai kudin

baiyi a gidans Gani take kaman zaman gidan

hayanne bai isheshiba shiyasa baison siya

musugidan tace lallaima abbakar Gani kake kamar

Banda hankali inba hakaba tayaya za, ai kacemin

baka da kudin siyen gida bacin Ina ganin irin

maqudan kudin da kake shigowa dasu gida duk

sanda zaka tafi sari haka kuma Ai kace Kana jefa

adashe acan kasuwar gashi kuma kacemin mai

gidanka na baka alawance duk qarshen wata Ina

kudin suke tafia?

Abbakar kasan Allah na baka Nanda sati guda

kasai Mana gida mu koma in kuwa ba hakaba

wlh tallahi ruwama sai an tauna maka kaji na

rantse don haka idan kunne yaji gangan jiki ya

tsira

Uwar goyo

Chapter4

Tace wlh na baka nanda sati guda ka siya mana

gida mu koma in kuwa ba hakaba wlh ruwama

sai an tauna maka da yake yasan halin matar

tasa sai baice mata komai ba har sati guda taxo

ta wuce dadai taga alamun baida niyyyar yin

abinda take buqatar saita bullo da wata hanya

duk sanda ya dawo gida da zaran taga ya cire

rigar dake jikinsa zata lallaba ta zare kudin dake

ciki ta raba biyu ta aje masa rabi ta dauke rabi

idan yaxo yaga an dibar masa kudi yana

tambayarta zata haushi da fada tana fadin wai ya

maidata barauniya ta inda take shiga batanan

fitaba dukda yasan itadince amman saiya basar

kawai abu dai yaqici yaqi cinyewa har takaiga

kudin da yake zuwa sarin kaya dasu inhar zai

shigo da kudinnan gida tofa dole saita diba hakan

yasa ya daina shigowa da manyan kudi gidan duk

wasu bubuwa da zaiyi inhar na kudine to a shago

yakeyi ganin sauyin da yaine tace oho wato tanan

ya bullo lallai zai gane to tun daga ranan da

zarar ya dawo tun kafin ya zauna zata charge

aljihunan dake jikinsa sama da qasa ko nawa ta

gani a jikinsa saita zare abin na bama abbakar

mamaki ya rasa shin wai me fanne take da

maqudan kudin da take zara daga wajensane

shidai yaga ba sana, a takeba abinda bai saniba

kuwa wani adashi ta shiga na zubi kullun kai har

a cikin kudin cefanema ragetake inhar ya bata

kudin cefane raba kudin take uku tayi cefanen da

kashi daya sauran kuma ta tura a adashi

Wasa wasa saiga fanne ta samu kudin da zai iya

sawa tasai fili hakan yasa ta yanke shawarar

zuwa wajen babanta domin ya siyamata filin da

abbakar din tai niyyar va mawa ya siya mata sai

kum tace ina wlh bazan bashiba don har yanxu

ban gama yarda dashiba dagananne kuma tace

kodai yayyaina zan bamawa su siyamin can kuma

tace kai ina suma ta kansu suke ina basu miyar

gidansu zasu gyara su barni da kumfar baki

dagananne kuma dai ta yankr shawarar kawai ta

kaima daddyn nata don ta tabbata daddynta

baxai taba cin mata kudintaba a ranan da taje

wajen daddyn nata ko iznin abbakat din bata

nemaba ta tafi inda tana zuwa kuwa tai sa, an

samunsa yau yana gida bai fitaba vayan sun

gaisane yake cewa ahh yau su fAnne ne a gida

ince dai lfy tace lfy lau baba daman wata yar

mAgana nakeson muyi yace ina jinki nanta koro

masa zance gamida bude jaka ta zaro kudin ta

damqa masa yai shiru na wasu yan mintina

sannan yacecshi abbakar dinne yace ki kawomin

domin na saya miki fili? Tace a.a baba kawaidai

dacewar hakan na gani domin kuwa namiji bashi

da tabbas zai iya cinyemin kudin daga baya muxo

mu dinga rigima

Abban nata yai murmushi gamida cewa fanne

kenan wlh dukda ba tare nake da abbakar ba

amman na tabbata ba zai cinye miki kudinkiba

shine wandayafi cancanta daki tunkara da

wannan maganan gamida shawara don abbakar

mutum ne na gari nasan bazaiqi ci gabankiba

kuma hakanne ya qara tabatarmin da mijin naki

ba mugu bane don nasan duk wadannan kudin

daga jikinsa kika samesu kasancewar nasan

kedin dai ba sana, a kikeba

Don haka inaso ki koma gidanki daki nemi

shawarar mijinki kuma ina umartarki dakibi

abinda yace koda kuwa ya saba ga ke yaddah

kikesonne

BATAJIN dadin furucin abban nataba dukda kuwa

gaskia ya fada mata sai take ganin kaman

abbakar dinne yafi so amman ya ta iya dole tai

abinda yace din don tasan halin abban nata sarai

Tace to shikenab abba amman don allah kabar

kudin a wajenka inyaso idan na koma gida sai

nace kana nemansa idn yaxo saika bashi kudin ya

siyamin idan ka bashi kudin da hannunka zaifi

riqesu dakyau donni banso na bashine yaxo ya

salwantarmin dasu bayan saida nasha whl kafin

na samu

Yai murmushi gamida cewa to shikenan fanne jeki

karma kice masa ina nemNsa din zansa aimin

kiransa tace to na gode abba nandai ya qara

mata da nasihohi sannan ta tashi tai gaba don ko

matan yayyan nata bata shiga gidan domin su

gaisa ba ta koma gida abinta

Washe gari yasa akai masa kiran abakr din bayan

sun gaisane yake shaida masa abinda ke faruwa

murna abbakar din ya tayata sosai da mata fatan

allah ya sanya alkhairi sannan yace baba ai kaine

yafi dacewa daka saya mata filin don kuwa

dagani har ita duk a qarqashinka muke kuma

qasa dakai babu yaddah baiba akan abbakar din

ya amshi kudin domin ya siya mata amman yaqi

badon yasoba ya qaleshi ya tafi gamida tausaya

masa don yaga tsananin damuwa a tare dashi ya

fahimci abbakar baijin dadin zama da fanne ko

kadan saidai ance ai mai daki shi yasan inda

yake masa yoyo

Fuloti guda ya siya mata a waNi anguwa da babu

cikowan jama, a

Sannan ya kira abbakar da fannen ya shaida

musu gamida damqama abbakar din takardun filin

a hannunsa kaman jira take su fita suna fita tai

wuf ta kwace takardun tace bannan ai nima

nasan yaddah ake tanada tajardu kawai salon

lokaci guda kawai acemin fiki ya bata gabaki

daya murmushi kawai yayi yace fanne kenan

Tun kafin su qaraso gida ta fara masa maganan

gini yace kinada kudine isassu a wajenki? Donfa

kinsan aikin gini akwaishi da cin kudifa

Wani kallon raini ta bishi dashi sannan tace kana

nufin nice zan bada kudin da za, ai ginin to bari

kaji inma zaka dage damtse gara ka zage domin

kuwa sisina bazaiyi ciwon kaiba akan kayan da

za, a siya na aikin gidan

Kaiko kunya bakaji namiji kakkarfa kamarka ace

macece zata siya mata gida to wlh inma zaka

zage damtse gara ka zage ai namayi mai wuyar

da har na siya maka fegi

Tsugunne bata qareba saida fanne, ta matsama

abbakar lamma akan lallaifa ya fara gini a filinnan

domin su koma don kuwa badon yasoba ya fara

gini a filin a kuma shekarar ne alllah ya azurtasu

da haihuwa a ranan da fanne ta fahimci tanada

ciki a ranan batai barciba sbd tsabar murna

Kasancewar abbakar din bamai hali bane yasa

ginin bai tafiya da sauri gashi fanne tace irin ginin

masu kudi takeson ai mata don musamman

tajashi sukaje wata anguwa ta nuna masa wani

gida tace irin ginin takeso ayi gashi yanayin ginin

zaici kudi hakan yasa sai ai sati ba, aje ginin

gidan ba kasancewar gashi bamai qarfiba fanne

ta matsa masa lamba akan sai irin ginin masu

kudi ga sayayyar kayan haihuwa ga hidiman gida

abin duk ya taru ya cakude masa amman da yake

abbakar din jarumine yasa ko a fuska ba zaka

fahimci da damuwa a ransaba

Har yanxu ba, a gama ginin gidanba gashi cikin

fanne ya shiga watan haihuwa nanfa hankali ya

tashi

Don ita so take ta haihu a gidansu na kansu ba, a

gidan hayaba hakan yasa ta hurama abbakar din

wuta akan lallaifa yasa a gama ginin gidannan da

wuri tun abin baya damunsa har yaxo ya fara

damunsa ta matsa matuqa hakan yasa ya fara

fita ginin da kansa don daman da yana sacandire

yayi aikin leburanci sai yabar yaron shagonsa

yaci gaba da kula da shagon tun safe zai fito

yaxo ya fara aikin randa yakeda kudi ya dibi

jama, a aje shima ya shiga cikinsu aita aikin

randa bashida kudi kuwa shi kadai yake zuwa

aita fama donma wai allah ya taimaka ya gama

siyan kayan ginin kenan tun safe zai fita bazai

dawoba sai dare idan ya dawo ya kasa barci sbd

wlh sannan asuban fari zai fice abd rashin imani

irin na fanne ko dumame bata masa hakanan

yakeci da sanyinsa wai donma kar yunwa tai

masa illa kenan hannunsa duk sun kunkunbura

sunyi ruwa sbd tsaBar wlh. Lol

Uwar. Goyo

Chapter5

Saida tai fanne bata girl saidai ta saabinda ranta

keso taci bayan a kawai kayan abin cin wai ita ba

zata iya gikil ba sbd cikin dake jikinsa

Don wasu lokutan ko abincin darema batayi

saidai idan shi abbakar dinne ya dawo daga

shago yake girka musu ko a jikinta akullun idan

abbakar ya zauna yana tunamin yaddah rayuwa

ke tafiya saiyaji kaman ya daura hannunsa akai

yaita rusa ihu a kullun bai gajiya wajen yin ma

fannen addu.ar allah ya shiryeta kuma ta gane

gaskia amman shiru kakeijkaman an shuka dusa

a ransa yace ko tsaGoron jahilcin dake kanta ne

yasa har yanxu take ganin ita komai tayi daidaine

don a iysaninsa da fanne bai taba ganin ta saka

uniform bama balle ai tunamin zata makaranta

toma

To inama ta zauna kullun tana yawon bin gidajen

qawaye ai gulma anan a toni fada a can abinda

ta iya kenan

Duk wannan uwar wahala da abbakar Kesh a

fanne bata gani ita ga nima take bai qoqari tun

da gashi har e zuwa yanxu ba.a kammala aikin

gidan nasuba gaba daya bata jinjina masa da rin

qoqari da yake saidai ma idan ya dawone a

gadarance zata ce masa an gama ginin gidan

kuwa wanizubi yacemata tukunna dai wani lokaci

kuma idan abin ya tsaya masa arai ko kulata

baiyi

Idan hakan ta faru kuwa a ranan mitane da

rigima ya tashi kenan harma damai gorin

rashizuciya don ita ganinta rashin zuciyarsane

yasa har yanxu ba.a gama aikinba

Wannan rashin imani na fanne ba qara min bama

abbakar mamaki ya keba don kanta kawai ta sani

ta maidashi kaman wani bawanta data siyo da

kudinta a kasuwa duk tsadar abu inhar ranta

naso koda kuwashi abbakar din baiso tofa saiya

siya mata shi Sam bata lura da halin matsin da t

yake ciki ita a kullum abinda ranta ya raya mata

take yi gaba daya bata da Lissafi ballentana

Aje ga batun abinda zai amfaneta

Uwar goyo

Chapter6

Ba ruwanta ita burinta a duniya bai wuce taji dadi

kuma ta kasance abin kwatance a wajen

qawayentaba

Shiyasa a koda yaushe zaka ganta a cikim

kwalliya da shiga ta alfarma kaya duk tsadarsa

indai har yayi mata tofa saita matsama abbakar

yasai mata

Gata da qawaye kuma duk qawayen nata masu

kudine kuma gogaggun yan barliki kana ganinsu

zakasan babu Allah a cikin zukatansu

Abbakar da kansa na mamakin inda fanne ke

samo wadannan gogaggun yan barikin

Duk sanda wata ta haihu a cikinsu ko za. Ai mata

hidima to sai fanne ta matsama abbakar ya bata

maqudan kudade don takai gudunmuwanta a cikin

qawayen nata akwai wata da abakar yafi tsana a

cikinsu kuma duk ta fisu zuwa gidan nasu

malamace a wani asibiti kuma yar hakimin wani

kauyece gaba daya halinta yaxo daya dana fanne

a wani gidan biki suka hadu har suka kulla

qawance

Duk wasu halaye da fanne ke nunama abbakar a

yanxu ita take sata bata daukar maganan kowa

saina wannan qawar tata saude kenan jama, a na

kiranta da dashiya sbd munanan halayentane

yasa bata dadewa a gidan miji aurentake mutuwa

don a yanxu haka aurenta na bakwai kenan tana

shirinyin na takwas bazawarace kuma duk

mazajen da take aura masu hannu da shuini ne

munanan halayentane kesa a gidan miji akeyo

waje da ita ita ke kawoma fanne samfarin atamfa

duk tsadarta idan ta kawoma fanne sai tace mata

ta matsama abbakar ya siya mata don itamawai

ta dinga fasowa gari mutane su dinga bata

respect kullun itake zuwa yinma fanne awon ciki

don wani lokutanma anan takecin abinci duk

randa batazoba kuwa da zarar fanne ta kammala

girki zata zuba a kula ta umarci abakar akan ya

kaimata gidanta dake cikin asibiti

Abu dayane ta kasa rinjayan fanne akai shine bin

maza tayi tayi akan taja ra. Ayinta wajen harkan

bin

Amman firr taqi yarda don gani take kaman ba

zata samu fiye da abinda abakar ke mata ba

kumama bataso ana haka wani ya ganta yaje ya

shaidama babanta ta shiga uku don tasan halinsa

sarai babu yaddah dashiya ta iya dole ta qyaleta

amman gamida ce mata da kanta zataxo ta

amshi buqatar data nemeta dashi don namiji

baida tabbas kumama ai duk macen data maida

namiji uba to lallai saita mutu marainiya, inji

masu masu iya magana ba lol

Daqar dasidin goshi abbakar ya kammala bangare

daya na ginin gidan nasu wanda akai dakuna biyu

a ciki ko wannensu da bayinsa sannan da

bangaren kichin da sito ga makeken gate da yai

musu kaman sunada mota sannan yai fenti a

ranan da ya sanar da fanne cewa ai an gama har

anyi fenti ba qaramin dadi tajiba take ce masa

kaga gobe sai kawai mu koma don daman na gaji

da zaman gidan haya wlh

Koba komai ma samu kwanciyar hankali

Abbakar din yace a.a badai gobeba ki bari a

qarasa aikin gidan da kaina zan fada miki ranan

da zamu koma don akwai sauran yan aiyukan da

za. A qarisa amman fanne tace ina aiko ita

batasan wannanba ya za. Ai ita da gidanta

sannan ace wai sai wani yabata iznin tarewa a

ciki ba yaddah bai da itaba amman tai tsalle ta

dire gamida cewa ita batasan wannanba yakece

mata kingafa ko qofofi ba, a saka bafa na

winduna da qofofi a hakan kikeson ki koma ciki

tace wannan matsalarkace kaje kasan yaddah za,

ai a siyo qofofi a yau dinnan a saka gobe mu tare

ba qaramin fada sukaiba irinna wanda tunda

sukai aure basu taba yinsaba harsaidata kaisu

durkushewa a gaban mahaifin fannen fanne ce

takai qarar abakar din akan yaqi yarda dasu tare

a sbn gidansu gashi kuma ta kusa haihuwa don

ita tafiso ta haihu a gidansu bana hayaba

kasancewar tanason ai sunane na kece raini

wanda zai zama abin kwatanceca wajen

qawayenta wannan kai qara da fanne tai ba

qaramin qonama abakar zuciya yaiba yace wato

kenan shiba mutum bane da yai haquri na duk

tsawon lokacinnan da irin munanan halayyarta ba

tare da ya taba kai qararta koda sau dayaba sai

itace zata kawo qararsa akan wani abu da bashi

da tushe abinda bai taka kara ya karyaba ya

girgiza kai gamida cewa gaskia fanne sai gyaran

allah

A lokacin da abakar din ya iso gaban mahaifin

nata haquri baban nata yabama abbakar din

gamida cewa yai haquri su koma gidan tunda dai

hakan shine zai kawo zaman lfyrsu kuma idan

allah yasa kun koman koda ahankali a hankaline

sai kasai qofofin bai masa musuba yace shikenan

insha allahu zuwa jibi zan nemi motar da zata

kwashe mana kayan namu saimu koma abban

nata yace yauwa abbakar na gode allah yajiqan

mahaifinka kuma yasa ka gama da duniya lafya

yace amin sannan ya tashi ya tafi

A hanyarsa ta dawowane yake tunanin irin hali na

baban fanne gaba dayansa bamaison tashim

hankali bane gashi kuma kamilin mutum sai kuma

gashi allah ya azurtashi da tantiriyar yarinyar da

gaba daya bata tunanin allah zai iya daukan

ranta ko koda yaushe sheqe ayarta kawai take

tabbas allah yayi gaskia dayace ina fitar da

rayayye a cikin matacce sannan na fitar da

matacce a cikin rayayye

A ranan da su fanne suka tare a gidan sbd murna

har barci ta kasayi kwana tai tana zagaye gidan

taro tai sosai domin tayata murna da kuma

rakiya kusan duk qawayentane amman fanne ko

sallama bataima makwabciyaryaba wanda suke

zaune tare duk kuwa da quncin da taita turama

matar wai donma matar bamai son tashin hankali

bane kullun tana qofarta kai har saida takaiga

matar a qofar dakinta take girki sbd tsabar takura

mata da fanne tayi

Kwanansu goma da tarewa a sbn gidan nasu

allah ya azurtasu da diya mace ba qaramin

murna abbakar yaiba da samun kyautar da allah

yai musu ba qaramin hidima yaima mai jegon da

diyar tataba shima baban nata haka kai hatta yan

uwan nata suma ba, a barsu a bayaba kafin

sunane ya ari kudi yasai qofofi ya saka badon

komaiba sai don sanin halin matar tasa don zai

iya zama musu abin tashin hankali duk kuwa da

itace ta takura akan saisun dawo a hakan

Gidan kuwa kullun a cike yake da qawayenta su

dashiya sune akan gaba wajen aiwatar da

abubuwan da suka kamata don a gidanma yanxu

take kwana

Hatta kayan suna dashiyarce ta amshi kudi ta

shga kasuwa da kanta wai acewarta tafi abakar

din sanin kaya masu kyau da aminci itadai fanne

ido kawai take binsu dashi

Allah ya cika mata burinta nason samun haihuwa

saidai duk abin duniya ya dameta don kuwatun

washe garin ranan data haihu dashiya ta bata

kanwa tace ta shafe kan bre din nata dashi baYan

bayan wasu yan mintuna saita wanke sannan ta

fara bama yar tata nono tana aikata hakan yar

tata na kama bre din ya dare tun daga raNan ya

soma mata ciwo wai donma allah ya taimaka

guda dayane ba duka biyunba

A ranan suna an shagale qawayen mai jego sun

fiddah ita kunya don kaya sukai mata sosai ita

da babynta ta hannun damanta kuwa dashiya

makida da mawaqa ta dau nauyin daukowa

domin a chashe wuni ranan abakar baiyi a

unguwarba don bazai iya jurar ganin tabar gazar

da ake tafkawa a qofar gidanan nasaba sai kaga

mace da aurenta ta fito cikin jama, a tana kada

mazaunai babu kunya kojin tsoron allah lol

Ranan sunan raguna biyu abakar din ya yanka

mata kuma ya wadataya da abinci duk abinda

tace ya kawo saida ya kawo mata shiyasama

abinci suna ya wadatu saida kowa yaci ya bari

wasuma harda diba suna guzuri dashi masu

qaramin qarfi kenan sunandai sai san barka dukfa

wannan shagalin da ake ko loman abinci daya ba,

a dibama abakar ba hatta naman sunan da aka

soya ko yanka daya ba, a bashiba wakema ta

kansa ana hidiman biki da yake abakar din mai

haqurine sai ya maida komai ba komai bane allah

sarki admin kansa ya jinjina maka abakar

Taro ya tashi lfy ya rage daga fanne sai dashiya

da kuma tsohuwar dake kula damai jego don

daman abakar tun randa fannen ta haihu tace

masa yasan inda zaije ya dinga kwana don

dakuna yai musu qaranci saida komai ya lafa

sannan dashiya ta koma gidanta dondaman tunda

fannen ta haihu taxo ta tare anan amman kafin ta

tafin saidata bata shawarar ta saidai rabin

zannuwan da aka kawo mata don an kawo mata

da yawa kai hardama na jariran in yaso babanta

saiya sai musu wani sannan ta tafi gamida ce

mata nanda kwana biyu zata dawo ta dubata da

babyn nata

Ba tare data nemi shawarar abakar dinba ta kira

dillaliya sukai ciniki ta biya don daman tana burin

taga tasai kayan daki masu tsada irin wanda take

gani a gidan qawayenta sai gashi tsuntsu a sama

gasasshe itadai komai tasa a gaba allah na bata

sa, a shiyasa wani lokutan take cema abbakar

itadin ai mai qashin alziqice

Ba, a dau tsawon lokaciba fanne ta gyara dakinta

gunin ban sha, awa hardasa saitin kujeru dataga

kudin sunyi sauranema tabama dashiyasu tace ta

sayo mata sarqar gwal mai kyau

A satin da fanne ta kammala gyaran dakinta a

satinne bre dinta ya tashin mata ya kumbura yai

sumtum ga a zaba yaddah taga rana haka take

ganin dare ga yarinya ta fara damunta da rigima

abin ya taru yai mata yawa

Ganin hakane yasa tacema abakar ya dawo gida

da kwana don koba komai ya taimaka mata da

rainon yarinyar nanfa abakar ya dawo yaci gaba

da dawainiya dasu shi zaima yarinyar wanka yai

musu girki ya hadama fannen ruwan wanka itama

bayan ya tafasa yakai mata bayi idan kayan da

suka cire yayi datti ya wanke musu kana ganinsa

zakasan yana cikin tashin hankali itama duk ta

sauya tayi wani iri duk wanda ya ganta a wannan

yanayin saiya tausaya mata sbd azabar ciwo

allah sarki mutum ba, a bakin komai yakeba duk

halin fanne nada yanxu babu su to inama bakin

yake da har zatai masifan tanata kanta ganin

haka yasa abakar ya tashi tsaye wajen nema

mata magani bashi wannan qauyen bashi wancan

qaiyen kuma kullun saiya kaita taga likita

Saida akai wata uku fanne tana wannan ciwon

bre din sannan allah ya kawo sauqi wani

makwabcinsu ya kwantanta musu wani mai

magani a wani qauye yace indai sukaje da iznin

allah zata warke basuyi wata wata abakar yadau

mota suka nufi garin a lokacin da suka isa

sundan tarar da layi ba tare da bata lokaciba

layin yaxo kansu har suka kaiga ganin mai bada

maganin bayan mai maganin ya duba bre din

natane yaga duk yaddah yake yace da ita kedawa

kikaxonan tace nida mai gidanane yace to cemai

ya shigo ba tare da bata lokaciba suka shigo

yana duke da zainab a hannunsa mai magani

yace naga matalan dake tattare da bre din matar

taka kuma in allah ya yarda zata samu sauqi

saida kuma idan zaka barta anan harta warke

sumul abakar yace to malam amman ya za, ai da

zainab yarta wacce ko kwari bataiba mai maganin

yace karka damu da wannan akwai tsoffin dake

kula da jarirai a ciki

Sannan suka tsadance abbakar yasa hannu aljiu

ya biya kudin maganin a take mai maganin ya

janyo wata jarka mai cike da baqin mai yace ta

bude brez din nata sannan ya shafeshi gaba daya

da wannan baqin man ya kwalama wata tsohuwa

kira daga ciki ta qaraso yace dauki wannan

yarinyar da uwarta ki kaita dakin da ake aje

majinyata sannan kici gaba da kula dasu sannan

abakar ya miqe yaima fanne sallama a take taji

hawaye na gangarowa daga idanunta tace

shikenan y tafi ya barni a garin da bansan

kowaba wannan kngurmin dajinda ko mafarkin

zuwansa bata tabayiba wani katon daki mai

kama da zaure wannan tsohuwar takai fanne an

shimfide dakin da tabarmi ga majinyatanan mata

a ciki kowacce ra riqe kai sbd azabar ciwon dake

addabarsu itama fannen jiki a sanyaue ta nemi

waje ta zauna da rana aka kawo musu koko ko

sigari babu a ciki kofi daidaya gashi kaman ruwa

kallo daya taima kokon ta kauda kai da darema

aka kawo musu tuwo miyar kuka babu ko manja

fara fatal da ita nanma bataciba gashi cikin dare

ciwon nonon nata ya tasar mata nanfa ta tashi ta

dinga zagaye dakin tamkar mai safa da marwa

A darebn ranan batai barciba washe gari aka

kawo musu koko tace ta qoshi bayan mai bada

magani ya kimtsane yace kowa yaxo daya bayan

daya domin amsar magani sannan yacema fanne

taje tahau wani gado ta kwanta akai bayan ya

gama duba sauran matanne ya umurci da akawo

masa wuta da wasu qarafunan nanfa hankalin

fanne ya tashi tsoro ya soma kamata yace karki

damu sakiya zan miki kumama ga wani magani

nan zakisha kafin a fara zai rage miki radadin

zafin da zakiji hakan kuwa akai cikin ikon allah

yai mata sakiyan sannan ya umurci daya daga

cikin tsoffin dake wajen dasu maida ita dakin

nasu aikuwa suna kaita barci mai nauyi ya

dauketa har abakar yaxo dubata bata tashiba

ananne ake ahaida masa da matarsa bata iyacin

abincin da suke don haka saiya dinga taho mata

da abinci yace ba damuwa dukda nisan da

garinnan kedashi haka abbakar ke jigilar kaima

fanne abinci safe da yammah allah sarki abbakar

mutumin kirki satinsu daya a wurin mai magani

fanne ta samu sauqi nonuwan nata suka warke

sarai sannan suka tattaro suka dawo gida

Haqiqa fanne ya cancanci da tabama abbakar

lambar yabo don ya cika masoyi na gaskia don

ba duk namiji bane zai iyama mai hali irin na

fanne wannan dawainiyar ba kuma dukda bajin

dadin zama da ita yakeba wlh in wani namijinne

ko sannu bazai mataba ballentana har takaiga ya

nema mata magani

Shi kuwa abakar da zuciya daya yake mata komai

ba tare da duba duk wasu wulaqanci da tai masa

a baya ba

Fanne sauqi ya samu sosai itama yar tata da

take kira da momy ta murje kasancewar nono na

isarta yanxu ba kamar daba fanne nason yar

kaman ranta sam batason abinda zai taba mata

ita hatta kuda adan dole yake taba yarinyar

danba yaddah zatayine kullun yar cikin kwaliya

take kuma a goye in kaga fanne ta sauke yar to

barci tai yarinyar da fanne tai kama komai nasu

iri dayane sam batai kama da babantaba

Abbakarma nason yar don idan yana gida yana

daukarta sosai amman sond yake mata baikai na

momcyn nata ba lol su fanne an zama uwA

A kwana a tashi momy ta isa yaye sai dan

banzan rashinjin tsiya ga kuka idan ta fara kuka

ayi ayi ta tai shiru taqiyi wani zubinma sai cikin

dare take tashi tahau kuka suyi rarrashin

duniyannan taqiyin shiru fanne tace wai ba lfy ne

da itaba don haka kullun suna kan hanya zuwa

ganin likita

Wani rashin jinma saida yar ta iya tafia wohoho

komai ta samu zubarwa take ta balla wannan ta

watsar da wanccan ta rikito wannan wani abin

takaicin kuma fanne na zaune yar zataita barna

amman taqi hanata wai bataso ta hanata don kar

tai kuka lol saidai kuma bata barin yar tana

bannata mata kayan data siya da kudinta koda

kuwa kukan jini zatai

Amman abu indai abakar ne ya kawoshi tofa

zatabar yar ta barnata koda kuwa menen sannan

ba daman yai magana da zarar yai magana to

yinin ranan babu kwanciyAr hankali wai bayason

yarta bazai barta ta sakata a gidan ubantaba to

in batai barna a gidansuba ina zataje tayi hakan

na nufin abindaya kawo yafi yar tasa daraja

kenan a yinin wannan ranan ta dinga mita kenan

hakan yasa koda yana zaune yar ta fara barna

baice mata komai don shirun nasa yafi ace fanne

ta dinga yaba masa baqaqen maganganu

To yarinyadai haka ta taso cikin sangarta komai

tayi marar kyau a wajen uwar tata mai kyau ne

sam batason ganin bacin ran yar tata abbakar na

qoqari wajen bama yarinyar tarbiya ta kwarai

saidai me yanayine fanne na warwarewa don da

yarinyar tayi abu marakyau yana fara yin mata

fada zatace ina sam batasan wannanba gaskia

kuma ya daina takurama yarta duka duka nawa

take kumama yaushe aka haifeta harda zai fara

takura mata to wallahi inaso ka sani wanan

hanyar daka dauko bamai bullewa, bane don haka

tun wuri kwara ka dakata inkuma ba hakaba ta

murza yan yatsunta sukai qara lol

Mu hadu a nxt chapter jare donjin yaddah zata

kaya

Via. The. C.E.O @littafan hausa zallah

Duk wanda yaga anyi kicking dinsa out karya

zargi kowa ya zargi kansa don bamuce ai like din

wannan page dinba don kawai kaxo ka karanta

lbr kacwuceba anyine don idan akao post a dinga

comment don qarama admin qarfin qwiwa mu

kawai koment Mukeso idan mukai post ko meye

ku rubuta hakan zai tabbatar mana da lbrn yakai

gareku bafa roqon coment nakeba a, a if u like

coment if u like kar kayi I dnt care amman idan

nai kicking dinka waje karkaga laifina

Uwar goyo

Chapter7

Sauda tari a gaban yarinyar fanne zataita ma

abakar rashin mutunci hakan yasa yarinyar ta

taso cikin rashin tsoronsa don koda tana abu

yanacewa ke daina zatace ba za, a dainaba din

rashin mutunci kala kala babu wanda fanne

bataima abakar akan yar tasu hakan yasa abakar

din ya tattarasu daga ita har yar tata ya watsar

a kwandon shara don sau tari yar zata dinga

barna a gabansa amman ya kauda kai yai kaman

baimasan allah yayi mutum a wajenba

Hakan yasa momie ta tashi cikin gata da rashin

tarbiya ga rashin jin tsiya da rashin tsoro kullun a

anguwan sai anyi fada da fanne duk sbd rashinjin

tsiya akwaita da tsokana kuma yaran anguwa ba

kyaleta sukeba tana sokanansu suke kamata su

daka ita kuma fanne abinda bataso kenan aima

yar tata magana mara dadima aima yar sai inda

qarfinta ya qare inaga kuma an dakar mata ita

haba ai tuni zakuga ta zari gyale ta nufi gdan

iyayen yaron daya daki momin idan taga iyayen

nasa ta qare musu masifa da Zagi ta uwa ta uba

idan kuma tai arba da yaron ta kamashi tai masa

dukan tsiya a gaban uwar tasa babu yaddah ta

iya sannan ta zuyo shidai abakar ido yasa musi

gamida yin musu addu, a kullun bai gajia da

neman musi shiriya a wajen uban giji domin kuwa

shiriya a hannunsa take

A anguwar tasu akwai wani yaro taqadiri da duk

yaran anguwan tsoronsa suke idan yaro ya

tsokanesa to a duk inda suka hadu saiyamai

dukan tsiya fadarsa bata mutuwA

Wata ranan laraba da la, asar sule na cikin

abokansa a qofar gidansu makwabtansu fanne ne

saiga momi ta fito tana ganinsa tace aule

kunnuwa sannan ta fara masa daria shi kuma

yaron abinda ya tsana kenan a rayuwArsa kace

masa kunnuwa koka kalli kunnuwansa kana masa

daria habawa allah dawaka hadani inba da momi

ba nanfa tana cikin darianne bata ankaraba sai

ganinsa tai a gabanta ba tare da bata lokaciba

yahau kanta da duka saidayaga yayi mata lilis

sannan ya kyaleta yai tafiyarsa gamida barinma

anguwar dan yasan halin uwar tata momi ta

shiga gida cikin kuka fanne ta ganta hankali tashe

take tambayarta abindaya sameta cikin kuka take

fada mata cew kunnuwa ne tace kan ubannan me

kikai masa da har zai miki irin wannan dukan

harda fasa baki kodon yaga ya fiki qarfi lallai ya

taro ruwan bala, I baisan daya tabaki gwara yaje

ya rungumi transfomer ba tashi maza maza muje

gidan nasu

Nanfa fanne ta kama hanya harda tuntube riqe da

hannun momi saidai me da taje bata bata samu

suleba kuma uwar tasa itama akai rashin sa, a

taje anguwa nanfa fanne ta dinga sarfa ruwan

bala, I bakinta har kunfa yake saida tai mai isarta

sannan ta dawo gida ba, a sati da faruwan

abunbA

Momi da sule suka sake haduwa ita batama

gansaba ballentana ta tsokanesa ta bayanta ya

zagayo kafin ta ankar harya chakumota ya dinga

dukan bakin nata har saidaya fashe sannan ya

tsere gamida barin anguwan a lokacin da momi

ta isa gida ta shaidama fanne cikin bacin rai ta

suri tabarya idonta ya rufe don ko gabanta bata

gani sbd tsabar baqinciki ta isa gidansu salen a

bakin rijiya ta iske uwar tasa tana diban ruwa ba

tare da wani dogon bayaniba ta hau uwar tasa da

duka da tabarya tako ina saida taga ko moysi

bayayi sannan natsuwa yaxo mata

Tsorone da fargaba duka suka kamata don gani

take ke kamar matar ta mutu hakan yasa cikin

hanzari tabar gidan don kar azo a ganta abinda

bata saniba kuwa shine ashe tun shigowarta ashe

akwai yayar sulen dake can nesa dasu ganin za,

a kashe mahaifiyarsu yasa ta ruga can inda

mahaifinsu ke zama ta sanar dashi

Abbakar bai dade da dawowa daga kasuwaba sai

ganin yansanda sukai cike da mota ba tare da

wani bayaniba suka tasa qeyar fannen sukai gaba

da ita bayan sun tafi da itanne abbakar din kejin

abindaya faru girgixa kai yayi gamida mamakin

abinda fannen ta aikata kwana biyu yayi yana

sintirin zuwa station amman anqi barinsa yamaga

fanne a ransa yace wannan karon fanne ta dauko

ruwan da zai dafasu daqar da sidin goshi aka

bashi belinta wai donma ya dauki lauya kenan

don a tunaninsa akai lamarin koti a wannan karan

ba qaramin kudi abakar ya kasheba donshi yadau

nauyin jinyar matar da dannen takusa kashewa

don ata dalilin hakanne matar ta rasa rabin

kunnunta na gefe daya da manyan raunika wajen

fito da fannenma ba qananun kudi ya kasheba abi

ya taru yai masa yawa ga jinyar matar daya daka

ga kuma jinyar fanne don itama tundata fito

kasancewar ta daku fuskokinta duk sun kumbura

idanuwanta sukai jajir kana ganinta kasan ta

daku to tun daga ranan itama ta kama rashin lfy

hakan yasa yaci gaba da jinyar tasu su biyu

sauqi ya samu a wajen fanne saidai zuciyarta

cushe yake da baqinciki akan tozarcin da mijin

wannan matar yai mata taso ta daukaka qara

kotu domin abi mata haqqinta to saidai me

wanda take tunanin zai tsaya mata din har tao

nasara yace tai haquri don koda sunje kotu ita

za, a bama rashin gaskia tunda itace ta tashi taje

har gidansu laraban ta sameta badan tasoba y

haqura amman ta kudiri niyyah a ranta komin

daren dadewa saita rama cin mutuncin da akai

mata tun daga lokacin gaba ta kullu tsakanin

fanne dasu laraba ko magana bai hadasu daman

tun a station aka shiga tsakaninsu hakan yasa

yanxu sule bai taba momi hakanma itama tun

lokacin da yai mata mazgan farko ta soma jin

tsoronsa duk inda ta gansa a yanxu guduwa take

a tsakaninsu yanxu kowa jin haushin kowa yake

saidai kuma ba daman yin fada

Yanxu haka shekarun momi hudu amman fanne

bata sake daukan wani cikinba a tunaninta

tundata dade kafin ta haifeta kuma yanxu ta dade

bayan ta haifetan babu wani ciki sai take tunanin

kaman daman ita dayace allah ya rubuta zata

haifa hakan yasa ta janyota cikinta gamida bata

kulawa yaddah ya kamata tareda sangartar daita

ta bata freedom din yin duk abinda ranta yakeso

A duk fadin anguwan babu yaron dake samun

gatan da momy ke samu kullun cikin kwalliya

take ta saka wannan ta cire wancan kuma aka

sakata wata makaranta mai hade da islamiya ta

yayan masu dashi don a anguwan nasu ba ko

wane yaro bane ke makaranta allah sarki a

wannan shekarar ne allah ya sake budama

abakar mai gidansa ya kirasa sukai lissafin

abinda ke wajen abbakar din gida uku suka raba

mai gidan nasa yadau kashi daya yabama

abbakar din kashi biyi yace wannan mallakinkane

kaje na mallaka maka kaja jari daga yanxu ka

tashi daga qarqashina ka koma cin gashin kanka

hatta shagon da kake kula dashi shima na

mallaka maka wohoho ikon allah krnan daman

ance mahakurci mawadaci ba qaramin murna

abbakar yaiba harda hawayen farinciki mai gidan

nasa yace rabonkane abbakar kaje allah yasa

maka albarka a cikin kasnuwancin naka sannan

yace ameen ya tashi ya tafi

Yana tunkarar fanne da zancen uban gidansa ya

ware masa kudi masu tsoka domin jan jari saita

fara lallabansa akan yakaita makkah don duk a

cikin qawayenta itace kawai bataje hajjiba don

akwai wadanda duk shekara suke zuwa kumama

haji da umara zakaga mazajensu ke biya musu ka

duba qawata dashiya zuwanta uku gana hudu

tana shirin zuwa dukda batai aureba samarintane

ke boya mata baiyo mamakin jin kalaman rashin

hankali daga bakin fannenba kasancewar yasan

halinta sarai saidai shiru yai baice mata qala bala

ita kuma a wautarta tasha ai ya amincene hakan

yasa ta fara watsawa a gari da qawayenta cewa

itama wannan shekarar zata makka amman me

shiru kakeji shidai abbakar baice zai biya mataba

kuma baice bazai biyaba hakan yasa hankalin

fanne ya soma tashi don bazataso taji kunyaba

bayan ta gama shaidama qawayen nata zata

makkah wannan shekarar kuma zance ya sauya

salo don daman duk a cikinsu itace

maqasqanciya wai donma mijin nata na mata duk

abinda takeso kenan shiyasa har yanxu suke tace

tace ina ai dolenema abakar ya biya mata aikin

hajji taje don da taji kunyar duniya gwara taji na

lahira

Dadai abin ya dameta sai ta nufi wajen qawarta

dashiya domin nemo mafita don ta qare wajen

iya hada tuqqu kuma duk wani abu daya shigema

fannen duhu ita dashiyar itace ke shawo mata

kan lamarin cikin sauri tana labarta mata zancen

sai dashiya tace haba qawata ai wannan zancen

naki shi yafi komai sauqi kawo kunnenki kiji tana

rada mata fuskarta ta fadada da murmushi

sannan ta fara aiwatar da abinda dashiyar ta

fada mata washe garin ranan abakar na dadowa

daga kasuwa ko zama baiyiba balle yasha ruwwa

ta tareshi da zancen abbakar yace a gaskia fanne

banida kiudin da zan biya miki kujeran makkah a

yamxu ki bari zuwa gaba mu gani saina biya miki

inhar kinada rabon zuwa habawa aiji fanne tai

kaman abakar din ya watsa mata garwashin wuta

nanfa ta shiga surfa masa ruwan bala, I da

masifa tare dayin masa gore gore irin na jahilan

mata wadanda basusan inda ke musu ciwoba

Shidai shiru yai mata ba tare da yace mata komai

ba don idan da sabo ya isa ace ya saba da

wannan halin na fanne

Tun daga wannan ranan zaman lfy ya kaura a

gidan gaba daya zaman gidan ya ishi abakar don

inhar yana gidan fanne ta shiga yaba masa

baqaqen maganganu kenan tare dace masa

lusarin namiji wanda bai biyama matarsa

buqatunta in banda qaddara da rabon haihuwa da

mai zatai dashi

Wai sanin kansane ita ba tsaran aurensa bace sa,

ar manyace ya dubeta da kyau batayi kama da

irinsu yaku bayoba wanda baida zuciya irinta

zaruman maza kawai

Kaini fanne naga taskon duniya tunda har aka

hadani aure da wannan lusarin allaah dai yasa

kar yata momi ta dauko irin halinka na rashin

zuciya

A kullun ranan duniya sai fanne ta samu baqaqen

maganganun da zata sossokama abbakar tunda

yake a duniya bai taba ganin macen data raina

mijinta irinsaba

Yakan bata lokaci ya zauna yin tunanin abinda

yasa fanne ta rainashi haka backin kuma bai

rageta da komai ba duk wani nauyinta daya

rataya a wuyansa yana bakin qoqarinsa wajen

ganin ya saukesu suturan da yake sawama baikai

tsadar wanda yakesa kudi yana siya mata ba

gashi duk abinda ta nema yana mata

Kullin da akwai salon rashin mutuncin da fanne ke

bulloma abbakar dashi kai harya gaji dai ya biya

mata kudin kujerar makkan don ko abinci bata

barinsa yaci haka kuma bata barinsa yao barci

gashi ta dinga masa gori akan gidan da suke

cikima ai mallakintane

Abakar yana ahigowa gida kamar dai yaddah ya

sabanne da masifa aka tarbeshi saidaya bari tayi

mai isarta tayi shiru sannan ya zaro wata farar

takarda daga aljihunsa ya miqa mata wacce

shaidace na ya biya mata kujearar makkah

Zuciyar fanne tai ras nan da nan gumi ya karyo

mata cikinta yahau kuqi ta bude baki zatai

magana amman ta kasa domin bakin nata sai

rawa yake tunda takeca duniya bata tabajin

abinda ya kadata a duniya irin wannan ba a take

a wajen ta zuge da gudawa saidata shiga ban

daki yafi sau uku sannan ta dawo indacabbakar

din ke tsaye saidai har izuwa lokacin ta kasa ce

dashi komai tana tsaye a wajen ne saiga qawarta

dashita ta shigo gidan daqar fanne tayi qoqarin

nemo kalaman data amsa gaisuwar tata dasu

sannan tace zomu shiga daki akwai magana

Suna shiga fanne tasama dashi kuka gamida

cewa shikenan nikam na shiga uku asirina ya

tonu na shiga uku na lalace nikam ina zan saka

kaina naji dadi wayyo rayuwa yau duniya taimin

daurin dalmon minti ko kuma ince duniya taimin

atishawar tsaki dashiya dai kallon fanne kawai

take cikin rashin fahimta sanne ta sake bude baki

zatai magana dashiya ta rufe mata bakin nifa ban

gane me kike nufiba babankine ya rasu?

Uhhjm dashiya kenan idan babanane ya rasu ai

abin zai zomin da sauqi tunda nasan duk mai rai

mamacine

To meye ya sakaki shiga cikin wannan halin ni

wlh kin sani a duhu

Fanne taja ajiyar zuciya sannan tace daxun

abbakar ya shigo yana shihowa na taresa da

zancen tafiya hajji kawai sai ya miqomin wannan

takardan kuma yace waiya sakeni kunji qarya

jama, a allah e mana tsari daga biyema son

zuciya amin

Dashiya tasa hannu ta amsi takardar dA tace

abbakar dinne ya bata tana dubawa

Dashiya tace da gaske kike abbakar dinne ya baki

gamida cewa ya sakeki dashiya tace da ita

lokacin data kammala karantawan

Wlh kuwa shine ya bani dubamin ki gani saki uku

yaimin ko?

Don na sanshi da rashin imani tare da mugunta

ga kuma baqar zuciya

Dashiya ta girgiza kai gamida jan yar guntuwar

tsaki tace kai jahilci mugun ciwo. To wannan

takardar bata komai bace illa illah ta shaidar biya

miki kujeran makkah da abakar yayi fanne tace

wattttttttttttt

Uwar goyo

Chapter7

TACE WAT dan allah dashiya kibarmin wasa ke

komai saikin shigo da wasa cikinsa ki nemo mana

hanyar da zamubi domin samun mafita ya

maidani dakina tun kafin maqiya su faramin daria

don daman da yawa yan anguwannan bason

zamana da shi sukeba ke hardama yan uwansa

dondai na zame masa qarfen qafane kawai yasa

suke sauraramin

Dashi tace na rantse miki da allah abbakar ba

sakinki yaiba kinji rantsuwar dan musulmi kenan

makkah ya biya miki

Kaman daukewar ruwan sama tai cak da kukan

kuma sai aka koma murna harda bama dashiya

goron albishirin

Tace kai abbakar anyi mai baqar zuciya yana

ganina inata shige da fice a ban daki kuma

yaqice dani komai kai gaskia na yarda jahilci yafi

hauka ciwo yanxu da nayi karatu aida duk haka

bata faruba allahma ya taimaka babu wanda yaji

ballentana aomin daria dashiya tace aiko baki

tsiraba don sai ana taro ko biki qawaye sun taru

zan baje musu tabar gazan da kikai tace haba

hajia qawalli don allah kar muyi haka dake

wannanfa ba qaramin yarfi bane kiyi haquri

banson abinda zaisa mutuncina ya zube a idon

jama, a

Dashiya tace to naji amman da sharadi saikinban

wannan atamfar da abbakar ya dinka miki

kwanaki da sauri ta juyo tana kallonta azahirin

gaskia tanason atamfar sosai don duk cikin

kayanta tafisonta kuma sbd tsadar atamfar saida

suka kai ruwa rana kafin abakar yasai mata

Kuma bata dade da dinka kayanba don sawa uku

kawai tai musu amman babu yaddah ta iya dole

ta bata domin samun kwanciyar hankali don da

yawa a cikin qawayen nata sun dauka tanada ilmi

tayna miqama dashiya atamfar ta tashi tai gaba

inda tya barta da kuncin zuci na rabuwa da

atamfar tata sai takejinma dabatama fada mata

tabar gazan data afka ba

Watan tafin alhazai ya kama don wasu harsun

fara tafiyama hakan yasa su fanne aka sona shiri

taje taima babanta da yayyinta sallama amman

ta sananr dasu cewa itace ta biyama kanta ba

abbakar ba babanta yai mata addu, a gamida

nasihohi sosai sannan yace mata don allah ta

rage fadan da take da jama. A dimin kuwa

qasace xataje mai dumbin jama. A hade dayare

daban daban

A tanan da zasu tashi abakar ne ya rakata filin

jirgi lokacin da zasu tashin ba qaramin kukan

rabuwa da yarta momi taiba don tundata haifeta

yaune ranan farko da zasu rabu nadan wani

lokaci don hakanema yasa ta dauketa ta kaita

can wani gidan qawarta tace acan zata zauna har

saita dawo babu yaddah abakar baiba akan ta

kaita can vidansu wajen matan yayyenta ko kuma

wajen ummarsa domin kuwa baiga wani dalili

nakai yarinya can wani waje inda babu yan

uwanta na jiniba amman me fanne tai tsalle ta

dire tace ita batasan wannan ba abinda yasa taqu

amincewa shine bataso takaita can gidansu

wajen matan yayyenta daman sunada yara

qanana acan suyita gobje mata ya don nasan

bamai hanasu sannan tsanar umman abakar da

yan uwansa da tai yasa tace ba zatakai yarta can

ba don gani take kaman basason zamanta da

abakar din hakan yasa bata cika shiga

harkarsuba suma basa shiga nata

Amman ta tabbata yar tata zata samu kulawa

daidai gwargwado a wajrn qawarta hajia

hansatudon sun dade a tare akwaiqawance mai

qarfi a tsakaninsu

A ranan da jirginsu fanne ya tashi ranan taga abin

mamaki tun acikin jirgi ta dinga kauyanci tace

tab lallaine da ake cewa wanda ke zaune baiyi

kallo ba gaski masu kudi sunajin dadinsu ai wlh

nima kota halin qaqa sai nayi kudinnan kodan na

hucema kaina takaici

Cikin ikon allah akai aikin hajji aka gama sauran

dawo da ma aikatan aikin hajjin qasashensu to

fanne dai saidai muce allah e amsa ibadun nata

domin kuwa batasan komai na game da aikin

hajji ba ita yar abi yarima asha kidane ba

qaramin tsaraba taima yarta momie ba dan kusan

kudinta duk a sayayyar yar ya kusa qarewa

sannan taima qawayenta da yayansu suma

tsaraba mahaifinta da yayyanta da matansu

gamida yayansu amman abbakar kuwa ko hular

alhaji asallami dan banza bata siya masa ba

shida yan uwansa babu abinda ta siya musu a

matsayin tsaraba mahaifiyar abakar din kuwa ko

kallabi bata kawo mata ba dakinsu daya acan ita

da dashiya hakan tasa duk abinda zasuyi acan

din a tare sukeyi bayan sun dawo da kwana uku

ne ta fara bubbude tsarayba kai jama, a wanda

baida kunya yaji dadinsa a gaban idon abbakar

din ta gama rarraba tsaraban data kawo amman

ko ruwan zamzam bata bashiba wannan abu

damai yai kama ai koda ace bashine ya biya

mata kujeran hajjin nan ba kamata yai ace shi

zata fara yoma tsaraba don yafi kusanci da ita

amman ina saidai abin bai damu abbakar dinba

ko kadan sbd tuntun yasan bata daukeshi a bakin

komai ba ita kuma a nata wautar wai tasha

tsoronta yakeji shiyasa duk abinda tace masa

tana buqata yake mata kuma ta saki qafa tana

tsula tsiyarta a yanxu fanne ta gama tabbatar da

abbakar bazai iya sakintaba to inma ya saketan

aiba gidansa bane shine zai tattara yan

komatsensa yabar mata gidan sannan a duk

sanda yace zai qaro mata kishi wlh a ranan sai

anyi qaramin yaqi tunda ba gidansa bane kai

koma a wani gidan zai ajeta ba zata taba bari

abakar ya qaro aureba mutu ka raba ita dashi

domin kuwa ai itace tasha whlr zama dashi tun

baida komai sai yanxu da ya samu mai maiqo

shine wai wata zata shigo tace wlh na rantse

saina muzantawa duk wata mace datai gigin

shigowa gidannan kai bama itaba hardashima

abakar din saiya gane shayi ruwane ba, a

tabonibana nayi masifa inaga an shigo sabgata

Abinda kuwa bata saniba shine kullun sai jama, a

sun bashi shawarar qara aure ko wataqila allah

zaisa ya dace da mace ta kwarai a cikinsu harda

mahaifin fannen don yana sane da irin zaman da

suke amman abakar din yai biris da zancen

donshi gani yake kaman bazai iya ruqe mata

biyiba inma zai iya din baijin zasu iya samun

zaman lfy ita da fanne a gidan hayama ba, a

zauna lfy da utaba inaga kuma ace wannan

kishiyartace ai kullun an dinga tashin hankali a

gidan kenan masu ita magan na cewa zaman lfy

yafu zama dan sarki da ace kullun yana cikin

tashin hankali shida matansa kwara ya zauna da

daya inhar zai kasance cikin kwanciyar hankali

ballentanama ya tabbata fanne ba zata bari ya

qaro aure ba in kuwa kaga hak to saidai ian basa

tare ko kuma idan ya saketa abinda baya fatan

ya faru kenan don inhar ya saketa to bai cika

alqawarun daya daukarma kansaba

Inhar kaga sun rabu da fanne to saidai idan

dayansune baya raye amman har abada bazai

taba sakintaba saidai idan ita da kantane ta gaji

tace ya sauwaqe mata to sai yai mata abinda

take buqatan

Hajia fanne kenan tundata dawo daga hajji ta

zama cikakkiyar hajiya kuma naira suka qara

budema mai gidan nata tofa tun daga nan ta qara

bunqasa iya shegenta bata ganin kowa da gashi

hatta mijin nata gashi ta fara shafe shafen man

bilicin tayi wani fari kamar fatalwa sannan idan

zatai kitso sai an mata qari da atacment dukda

hakan ba kyau yake mata ba amman har yanga

take dashi

Ana cikin hakane abbakar ya kammala musu daya

bangaren na gidan nasu gamida canja musu fenti

gidan ba qaramin kyau yaiba flat ukune don haka

abbakar ya koma daya itama ta tashi ta koma

daya daga cikin sababbin tace tsohon zat

maidashi wajen sauke qawayenta

Dashiya uwar yan hadi tun da taga abakar yayi

flat uku ya koma daya fannema ta koma daya

don haka ta dinga zuga fanne akan ta tashi tsaye

inba hakaba kuwa sakiyar da ba ruwa zai mata

don tun da taga yayi flat uku to aure zai qaro

akullun fanne saina baki shawara akan mijinki

amman sai kiqi yarda wlh namiji bashi da tabbas

duk dadinki da namiji wataran sai yayi miki

kishiya muddun kika zauna kara zube ba tare da

kin nemi taimako daga wajen malamai da

bokayeba zauna garin kallon ruwa kwado yai miki

qafa idan kikai wasa kinaji kina gani matar zata

shigo ta dinga miki abinda taga dama idan kuma

kika takura ya baki rasit dinki takardar sallama

daga gidan kinga kin tashi a tutar babu kenan

tunda dake akasha wuya saida dadi yaxo sannan

wata zata zata shigo kenan tun wuri ki sake

tunani ki nutsu sannan kisan inda ke miki ciwo

yanxu lokacinkine kuma kinada damar yin komai

kar kiyi sake damarki ta kubce miki don daman

bature yace dama sau daya take zuwa

Hajia ki saki kudi kiga aiki da cikawa yanzu na

kaiki wurin wani boka mai suna lukum aikinsa

kaman yankan wuqa yake

Don na rantse miki saikin juya abbakar kaman

waina a tanda

Duk wani taurin kai da yake miki idan kin

tambayeshi kudi saiya dainaahi ke in tabbatar

miki inhar magani yaci kara idan kika aje kikace

karya qetara bai isa ya qetareba hatta harkan

kasuwancinsa kece zaki koma bashi umurnin

yaddah zai tafiyar da komai amman inkika tsaya

a haka to dan hakin da kika raina ina mai

tabbatarmiki da shi zaizo yana zokale miki ido

kixo kina kukan da baida amfani tunda kinbar gini

tun ran zane

Ai duk matan da kikaga suna yaddah sukaso a

gidajen mijinsu kuma su juya yaddah sukeso to

saida sukabi ta wannan hanyar ke bakyajin ana

fadin matambayi baya bata ba ne kuma qawata

wlh ba zaki tabbatar da abinda nake fada miki ba

sai nan gaba lokacin da zakiga kina juya mijinki

kaman yaddah kike juya tashoshin talabijin ki

murza naira a hannunki ki kerema sa, aninki wlh

qawata ni masoyiyarkice maison ganin kin

dauwama a cikin jin dadi kuma banso damarki ta

kubce mikine shiyasa kikaga ina baki wannan

shawarar a wannan lokacin fanne ta fara amanna

da abinda dashiya tazo mata dashi don a zahirin

gaskia itama tanason taga ta zama mace mai

fada aji acikin gidanta shiyasama batama abakar

din da sassauci idan abu ya hadasu don gani take

kaman hakan shi zaisa ya dingajin tsoronta

dukda sai ankai ruwa rana yake mata wasu

buqatun nata sannan takecin nasara wani

zubinma yaqi yaddah amman dole tabi hanyar da

dashiya zata daurata kodan ta magance matsalar

tata. Tai murmushi hmmmm abbakar ka kusa

shihowa hannu don saina juyaka yaddah nakeso

kuma zan iya kashe koma nawane don ganin

biyan buqatuna don daman masu iya magana ai

sunce saida kudi ake samun biyan buqatuuuuu

Sannu a hankali har dashiya ta koyama fanne bin

malaman tsubbu kuma ta fara ganin amfanin

abun domin a yanxu duk abinda ta tambayi

abakar din ba musu yake bata

Sai yanxu fanne ta qara tabbatar da maganan

dashiya ashe gaskia ne data sani aida tuntuni da

take fada take xijewa data amince komai da yaxo

mata da sauqi ganin nasarorin da take samu

wajen abbakar yasa fannen ta qara qaimi wajen

bin malamn tsubbu don ba qaramin kashe musu

kudi takeba kuma duk abinda sukace tai da sauri

takeyi ba tare da bata lokaciba don kawai samun

nasaranta

A yanxu kusan duk abinda ta samu a wajen

abakar a malamai yake qarewa shiyasama har

yanxu din ta kasayin abin kanta akace rashin

sani yafi dare duhu da fanne tasan duk asirin da

takema abbakar bai kamashi data daina jiqa

malamai da kudinta domin kuwa duk abinda taga

yana mata hakan ya samune ta hanyar budin da

allah yai masa don daman akace idan allah ya

buda maka saika gode masa harkar kasuwancin

tasace data qara bunqasa yasa shima yace bari

ya qara kyautatama iyalansa domin suma sunada

haqqi a cikin dukiyar mahaifiyarsa yan uwansa

dama wanda yake tare dasu kowa na samun

alkhairai a wajen abakar hakan yasa jama, a

kowa keson abakar din

Ba qaramin baqin ciki fanne kejiba idan abbakar

yai kyauta a gabanta kai koda kuwa yan

uwansane ita bataqi ace daga ita sai yartace

zasu dinga cin dukiyarba duk kuwa sanda yaima

wani kyauta a gabanta sai taji kaman tasa hannu

akai taita rafka ihu gashi ba daman tabi wanda

akaima kyautar ta kwace tace matsiyata kawai

lokacin da basu da komai waye yaxo ya taimaka

musu sai yanxune da allah ya buda masa sannan

za, azo a dinga manne mashi tace allah ita gani

take ma kaman abbakar bada guminsa yake

samun kudinnanba wlh domin bushashar da yake

dasu saika rantse kace shine yafi kowa tausayi a

duk duniya wasu lokutan idan anxo neman

taimako wajen abbakar din sai fanne tace bainan

ya tafi kasuwa idan kuma yan uwansane sai tace

musu yana barci kuma bai bada umarnin idan

yana barci a dinga tashinsaba koda kuwa waye

yaxo a haka suke haquri suna komawa

Saidai idan jama, a sun hadu da abakar din a

waje su fada masa abinda ya faru abin ba

qaramin cimai rai yakeba amman ko sau daya bai

taba mata magaba ba

Hakan yasa yan uwan abakar din basu damu da

zuwa gidan nasaba sbd wulaqancin fanne kai

hatta yan uwanta wanda suka fito ciki daya uwa

daya uba daya saida sukace mata ba zasu sake

zuwa gidantaba sbd wulaqantasu da take idan

sukaxo ta dinga binsu da kalllon raini hatta

dakinta bata bari su shiga saidai da zaran sunxo

ta shimfida musu tabirma a waje duk kuwa

buqatar mutum bata bari ya ahigar mata ban

daki wai kar suyi mata qazanta bayan a kullun

mai aikinta saita wanke bayin nata tatas sau

biyar a kullun

Lol

Uwar. Goyo

Chapter8

Lokacin da abban fannen yaji tabargazan da take

zubawa abinta hatta yan uwantama bata bariba

sai ya kirata gamida mata nasihohi akan

abubuwan da take din ba masu kyau bane koda

ace zataima wasu bai kamata ace yan uwanta na

jinima haka zatai musu ba kaman salihar arziqi

tace to shikenan baba na gode ta taahi ta tafi a

hanyarta ta dawowane ta dinga surutai kaman

zautacciya tace zuwa yanxu na fara gane shima

abbana ya shga sahun mahassadana tunda gashi

tun yanxu yana fadin inban a hankaliba bazanyi

kyakkyawan qarsheba harda wani fadin nabi

abbakar a sannu inba hakaba kuwa haqurinsa ya

kusa qarewa to ya qarw mana sai mene an gaya

musu ni inajin tsoron hukuncin da zai yanke akan

nawane idan har haqurin nasa ya' qare ko kuma

rasa mijin aure zanyi idan harya sakeni din a

yanxu yanda kaina ya waye idan har ya sakeni

suna zatan garari zan shiga banda qaddara da

kuma haihuwa ba yaddah za, ai na zauna da

abakar a matsayin mijin aurena wani kucaki dashi

wanda baisan tattaliba duk abinda ya samu

kashewa yake in banda wasu yan dalilai aida tuni

na takura masa ya sakeni ya kwashe

kwarmatsensa yabarmin gida don nasan yana

barmin gida bashi da inda zai koma shima ai

yasan da hakanne shiyasa yake bina a sannu in

banda inda wani buri a zuciyata wanda dole saida

aurensa zan cikashiba da wlh a yau dinnan saina

rabu daahi inga ta hassadan baban nawa adai juri

zuwa rafi don watarana tulun fashewa zaiiyi duk

wannan nasiha da mahaifin fannen yai mata babu

wanda ta dauka a ciki aban dakin nasa inda taji

anan ta zubar dasu tun daga lokacin ta daina jin

tsoronshi sam batajin tsoron gamuwarta ga allah

tun sanda baban nata ya kirata gamida yi mata

fada akan wulaqancin da takema yan uwan nata

tace daga ranan ba ita basu kuma duk sanda

suka sake zuwa sai tayi musu zagin qare dangi

sai kuma akai sa, a suma tun tafiyarsu sukai

alqawarin indai gidane na fanne bamai qara zuwa

a cikinsu koda kuwa garin sukaxo saidai idan ita

taje ta samesu

A lokacin data dawo tatas taima abakar akan

yanakai qararta gurin babanta wannan ai

munafurcine so yake ya hadata da babanta in

yaso yai mata baki ta lalace inba hakaba mai

takeyi masa wanda har zai kaishe zuwa gayin

qararta wajen mahaifinta in kuma gajia yai da

zama da ita ya gaya mata ba saiya tsaya yana

mata kwane kwane ba

Ko yana tsammanin idan ya saketa ba zata samu

mijin aure bane adama da takeda masoya

ballentana yanxu da ta qara sanin duniya

idanuwanta suka bude wanda basu kaitabama

suna samun mai sonsu ballentana ita ita?

Ta dora da fada masa

Kai bara na fada maka ni fanne nafi qarfin na

zamo matarka fin qarfi kawai akaimin a lokacin

aurenmu wanda baka wuce danxaikenabama nifa

matar manyace masu fada aji ko kuma masu

murza naira yaddah ransu keso ba irinka wanda

abu qanqani idan na nema a wajenka saika tsaya

kana jamin raiba duk wannan harigidon da kunfar

bakin da fanne keyi abbakar na kwance akan

gadonsa yana jinta ba tare da yace mata komai

ba harta gaji tai shiru domin idan da sabo yaci

ace ya saba shidai a iya zamansu da fanne bai

taba kai qararta wajen mahaifinta koda sau daya

ba koda wanine madai ya fada mata ya ganshi

wajen mahaifinta domin kai qararta to ya barshi

da allah ko kadan bazai bata miyon bakinsa

wajen fada ma fannen cewa ba shine yakai

qararta wajen mahaifintaba saidai baiji dadin

kalaman fataita faffada masaba don koba dadi ai

mijinta neshi

Shin yaushene fanne zata gane ta daina masa

abubuwan da tae masa ya dafe kai gamida cewa

shidai allah baisa yayi sa, an samun mace ta gari

ba haqiqa yasan allah ya jarrabeshi ta wannan

hanyar shiyasama a kullun yake addu, ar samun

cinye jarabawan da ake masa idan abokansa na

masa irin abubuwan da matayensu ke musu najin

dadi da karramawa sai ya dingajin inama shine

ke samun wannan garabasar ya dauki tsawon

shekaru yana da aure amman daidai da rana daya

bai tabajin dadinsaba gabadaya baisan menenen

dadin aure ba a yanxu tsoron halin matama yake

domin a tunaninsa duk irin halinsu dayane dana

fanne abbakar na mamakin rashin tarbiya irin na

fanne bayan yasan iyayenta sunyi iya bakin

kwarkwadonsu wajen bata tarbiya ita kadaice ta

fita zakka a cikin yan gidan nasu domin duk yan

gidan nasu babu wanda bai sauke qur, ani ba ga

ladabi da biyayyah ga duk wanda ya girmesu

Abinda yasa abakar ya qara tsanantar fanne sbd

rashin da, ar da take koyama mommy tare da irin

halinta da take koya mata har cikin ransa

yanason yarinyar domin kuwa jininsane kuma

akanta ya fara haihuwa koda ace nan gaba allah

zai qara bashi yaya itace gaba dasu amman sbd

halin uwarta da take daukowa yakejin tsanar yan

amman wani lokutan tausaya mata yake a bisa

halin data tsinci kanta na rashin samun uwar

goyo ta gari yaso ace fanne ta barshi ya bama

mommie tarbiya mai kyau sannan ya sata a

makaranta domin takoyo ilmi wanda shine

ginshiqin rayuwa daqar ya samu ya sata a

faramare nanma saida sukai qaramin yaqi domin

saidaya nuna mata bacin ransa amman da

kafewa taso tayi naqin son asa yarinyar a

makarantar babu yaddah ta iya dole ta barshi ya

sakatan amman duk sanda baya gari idan yaje

sarin kaya a legas ko kwatono to yar bata zuwa

makaranta kasancewar itama yar bada son ranta

aka sata makarantarba yasa uban ba tafia sarin

kaya zatacema uwar ba zatava fannen tace yi

zamanki yata damanni ba karatun nakeson kiyiba

salon kije aita dukarmin ke kamar jaka idan

mommie ta kawoma abbakar sakamakon

makarantar nata yakan bata lokaci wajen yin

mata fada akan ta dinga maida hankali ya kuma

nuna mata shi ilmi yanada amfani kuma ya zama

wajibi akan mutum ya nemi ilmi na arabi dana

boko domin shi ilmi kinshiqine na rayuwar dan

adam mutumin da yake rayuwa babu ilmi shida

jaki duk daya suke gaskia ne

Admin yace/living without walking is dying

wethout nowing/

Don zai iyayin abubuwa marasa kyau amman a

wajensa yaga ai masu kyau ne mutum mara ilmi

komai nasa kai tsaye yake ba tare da tunaniba

hakanan ya dinga samun sabani da mutanen da

yake zaune dasu kenan sbd rayuwarsu ba zata

zamo iri daya ba momie a yanxune kikeda damar

yin karatu sbd ke yarinyace kwakwalwarki bata

da wani damuwa a cikinta wanda zai hanatta

daukar abu cikin sauri a cikinta zaki dinga daukar

karatu matuqRar kin maida hankali ina jiye miki

danasani marar amfani anan gaba haka abbakar

ke zaunar da momy wasu lokutan yaita mata irin

wadannan nasihan wasu ta fahimci abinda yake

nufi wasu ku ta kasa fahimta duk kuwa da

kwakwalwarta nadaukar abinda mahaifin nata ke

fada mata domin ta zaiyanema fannen amman

saitacemata karta sake ta dauki abinda yake fada

mata domin kuwa ba sonta yakeba shiyasa

yakeson dode mata kwakwalwa da shirmensa ya

maidata mara yanci

Cikin ikon allah arziqin abbakar sai qara bunqasa

yake hakan yasa dashiya ta hurema fanne

kunnecakan lallai ta takura mata yasai mata

mota itama ta shigo gari ai kuwa ba tare da bata

lokaciba ta tunkari abbakar da zancen siyan mota

baiyi niyar siya mata motarba amman takura da

naci kawai saidayasa yasai mata sbw dal ba

qaramin wahala yashaba kafin ya samu ta iya

motar don shine ke koya mata harya samu ta iya

amman ba sosaiba tundata iya kuma fanne tabar

zaman gida akoda yaushe tana gidan qawaye

kasuwanci sai soma habbaka yake yanxu abbakar

dubai da chaina yake zuwa sarin kaya kuma idan

ya dawo gida naija sari yake badasu su hajia

fanne an zama masu fada aji ganini kudin da

abbakar ya qara qawar fanne ta fara nemansa ta

harkar banza domin taci kudinsa ta ware dashiya

kenan dayaqi amincewane ta nemi suyi aure

nanma yaqi yarda lokacinda ba kudin bata nemi

suyi auren bane sai yanxu ganin tayi tayi ta shiga

malamai amman ba sa, a yasa ta sallama masa

mahaifiyar abakar dinma taso ya qara aure koda

zai qara samun haihuwa amman sai ce mata yai

tai haquri idan lokaci yayi zaiyi da yake uwar tasa

mai hangen nesace yasa bata takura masaba taci

gaba da yi masa addu, a

Tajia tsigala wato fanne kenan na cikin katafaren

shagon alfijir ita da yar tata idan baku mantaba

sai siyayyar take mata. Bayan ta bude jaka zata

biya kudin siyayyar da taima yar yata kenan

momin tace laaaaa mama ga baba shima yazo

siyan kaya

Hajia fanne takai dubanta inda momy ke nuna

mata wani irin jirine ya dibeta wanda har saidaya

kusa kadata abinda ta ganin saidayasa

idanuwanta suka daina gani nadan wasu sakanni

dishi dishi take ganinsu sannan zuciyarta tahau

harbawa da sauri da sauri gashi duk jikinta ya

mutu daqar taje iya daga hannayenta duk wannan

abu ya sametane sakamakon ganin mijinta da tai

abbakar kenan dauke da wata yar matashiyar

yarinya a kafadarsa gefensa kuwa wata tsaleliyar

matashiyar matace wacce a qallah ba zata wuce

shekaru24 a duniyaba tana duba wani takalmi

inda suke hirarsu gunin ban sha, awa ita dashi

hankalinsu kwance fanne ta qara qurama yarda

abbakar ke rungume da ita ido taga yar dashi tai

kama sak farinne kawai ta dauko na uwar tata da

yake shi abbakar din ba za, ace masa fari tas ba

saidai ace masa wankan tarwada amman matar

dake gefen tasa farace ta da ita kyakkyawa

Hirarsu suke cikin kwanciyar hankali don da

alamunma sun manta a inda suke sbd hirar zance

Fanne ta dingajin zuciyarta tana mata wani irin

tuquqi sannan sai tafarfasa take sauran kadan ta

fashe domin ta kumbura sosai ji take kamar zata

faso qirjinta ta fito ga kuma wani abu da yaxo ya

tokare mata maqogoro mai daci wanda ta kasa

hadiyewa yawun bakinta gaba daya ya qafe a

rayuwa ta tsani taga abbakar na hulda da wata

mace bayan ita fanne nada tsananin kishin da har

ya wuce gona da iri shiyasama bbata sake masa

fuska da zaran yaxo mata da maganan zai qara

aure

Sannan ta kashe kudi da yawa ga malamai da

bokaye akan su masa maganin da zaiya yaji bai

sha, awar qara aure tayi zaton aiki yaci kuma ta

rigada ta gama dashi ashe ba haka abin yakeba

daman ance munafuki bashi da kama a duniya

yanxu ashe abbakar munafurtarta yake neman

mata yake bata saniba? To ina gaskiyar tasa take

da a kullun idan ka tabashi zaice maka shi mai

gaskia ne?

Tun yammah tai dashi akan ya dauki momie

domin yaxo yai mata siyayyah a wannan kantin

amman yace mata baijin dadi kumama a gajiye

yake ba zai iyaba sai gobe har fushi tai amman

yaqi fir yace bazai iya zuwa yau ba

Da dare yayi abbakar ya fita sallar magrib

mommy ta dammi fanne akan su tafi kanti ko za,

a iya dacewa a samu irin kayan da takeso ba

yaddah ta iya dole ta dauko key din mota da

kyale tacema direba ya kaisu kantin alfijir ashe

akwai abinda zata gani wanda zai tayar mata da

hankali watoma abakar ashe karuwarsa zai kawo

siyayyah shiyasama yaqi yarda da abinda tace

tunda hakane wlh yau zan nuna masa nima

macece mai yanci wacce nafi qarfin namiji ya

wulaqantani wlh sai yayi danasani marar amfani

a cikin shagonnan saina kunyatashi tunda daman

ai hausawa sunce kunyar mara kunya asarace

Tana cikin zancen zucinne saiji tai momie na

fadin laaa momy abba zai tafi habawa tabajin

haka tuni taji wani qarfi yaxo mata nan take cikin

sauri ta isa inda su abbakar din suje tasha

gabansu ba tare da bata lokaciba ta dau hannu

ta wankama matar dake tare da abbakar din mari

kwarara har biyu ita kuma matar juyowa tai

domin ganin wanda yai mata wannan aika aikan

don marin ya shigeta sosai gashi kuma ba

zatonta hakan ya faru shiyasama ta shiga cikin

rudu a karo n ukune da ta daga hannu domin

kaima matar abbakar ya riqe hannun nata nanfa

ta shiga kokuwar kwacewa daga riqon da yai

mata don kuwa so take taima matar dukan tsiyar

da saita kwana a gadon asibiti kuma saita bata

wannan kyakkyawar fuskar wanda shine ke rudan

mijin nata da taga ba zata iya kwace hannun

nataba daga riqon da yai mata dinba don riqon

bana wasa bane sai kuma ta shiga surfa musu

zagi yan iska masiyata duk jama, an dake cikin

kantin kowa hankalinsa ya dawo kan fanne a

ranan abakar yasha zagi masifa kawai take tana

kumfar baki wasu dattijun matane su uku suka

shiga bata haquri tare da tausarta amman ina

batasanma sunayiba don idanunwanta sunrufe

sbd tsananin masifa daqar suka samu hajia fanne

tai shiru jikinta sai tsuma yake daya daga cikinsy

tace baiwar allah ba wannan matar ya kamata ki

dakaba a matsayinta na karuwar mijinki shi mijin

naki shine babban mai laifi akansa zaki dau

mataki kai kuma ka cika mata hannu tundacan

samu tayi shiru

Abbakar yacema matar kije ki shiga mota ki jirani

ina zuwa tanaji yace ds ita haka ta fice daga

cikin shagon cikin sauri sannan ya sake hannun

fannen yana saki da axama ta rufama matar baya

so take ta cin mata tun kafin su isa inda sukai

parking din motar matannanne suka biyo bayanta

tare da riqeta suna mata kalamai masu tausasa

zuciya ganin sun riqeta abbakar din shima ya fita

daga shagon yai wajen motar cikin azama yai

mata key suka bar wajen hajia fanne na fanin

abbakar yai wajen motar yai kukan kura ta

watsar da matan amman ina tayi rashincsa, a

domin kafin ta isa har sun bade wajen da kura da

gudu ta bisu kamanxsbn hauka amman ina sun

mata nisa a kan tit ta tsugunna ta daura hannu

akai tana rusa ihu direbantane ya qaraso gamida

fadin hajia yi haquri ki tashi mu tafi kar jama a

su taru kinga har wasu sun fara zuwa tambayar

abinda ke faruwa

Fanne ta tashi cikim jin haushin rashin samun

nasara ta shiga mota direba ya jasu suka nufi

gida

Haqiqa hajia fannne ta fusata matuqa wanda har

tama rasa irin hukuncin da zata yankema abakar

din idan ya dawo gida

To nima anan zan dakata domin barin hajia fanne

ta samu nutsuwar zuci mu hadu a book 2 donjin

yaddah ZATA KAYA

Crews. U nw wat?????

This is just de begining yanxu book din zai fara

ldan naga ruwan comment sai mu fara gobe

Naku har kullun

Uwar. Goyo Book2

Chapter9

Cikin moyar yadau shirur babu mai magana face

aheshsheqar kukan matarnan da fanne ta mara a

kantin alfijir tunda ta shiga motar take kukan

takaici wannan ai cin mutuncine tunda take a

rayuwa bata taba tozarta irin na yau ba idan ta

qara tunawa da munanan kalaman da hajia fanne

taita fada mata saita sake fashewa da kuka

Ayau tai nadamar kasancewarta da abbakar a

yaddah taga mutanen dake cikin kantin suka

gasgata kalaman da tai a kanta din don har wani

kallo suka dinga binta dashi wasu daga cikin

matan dake gefenta kuwa harda ce mata

Ammanfa kinji kunya dukda kyaun fuska dana

suran da allah ya horeki dashi amman ki kasa

gode masa sai kinyi karuwanci tirr da wannan

halayyah taki yarinya qarama dake kin bata

rauwarki kin shafama rayuwarki baqin fentin da

bazai taba gogewaba har izuwa kan yayanki da

jikokinki domin shi abin kunya ko mutum ya jefar

dashi sai yayi tattali ya sameshi ke kuwa baiwar

allah mai yada kika zabama kanki irin wannan

rayuwar mai yasa kika bari namiji ya yaudareki

ya hure miki kunne gami da bata miki rayuwarki

ki sani duk abinda namiji yai a rayuwarsa adone

ita kuma mace ya zame masa abin kunya da gori

a wajen jama, a ki tunafa duniya ba matabbata

bace ki tunafa duk iya tsawon rayuwan da mutum

zaiyi a duniya ne haqiqa kinyi babban kuskure da

kika biyema zuciyarki haqiqa son zuciya bacinta

ne kuma inhar kana biyema kyale kyalen rayuwa

to ba zaka taba ganin haske a rayuwarka ba yar

uwa ke yarinyace shiyasa kika yarda da zaqin

bakin da namiji wanda kuma ba tabbas ne dashi

ba tunda dai ga idanuwanki sun gane miki

gaskiya ga matarsa ta sunnah harda yayansu

amman ya barsu ya tafi wajenki kuma karkisa a

ranki wajenki kadai yake zuwa mutumin da ya

yaudari matarsama bare ke da kuke dadiro tana

kawowa nan saita sake fashewa da kuka harda

buga kanta a jikin kujeran mota yar dake tare

dasu a cikin motar mai kimanin yar shekara biyu

tai shiru tana sauraron kukan mom din nata da

alamun batama fahimci me kukan mamar tata ke

nufi ba

Shi kuwa uban gayyah goga na fanne ya rasa

meke masa dadi a cikin ransa zuciyarsa sai

harbawa take da sauri da sauri kirjinsa yai masa

nauyi maqogoronsa ya qafe yanason yai ma

matar dake zaune a kusa dashi magana amman

ya kasa furta komai ji yake kaman ansa kwado

an bame bakin nasa kwakwalwarsa tadau zafi

tunanine sukai masa yawa so yake ya samo

hanyar da zaibi don warware wannan matsalar

data kunno masa kai amman ya kasa samu yaya

zaiyi da rayuwarsa waccce kalma zaiyi amfani da

ita wajen gamsar da fanne cewa abunda take

zargi ba haka bane

Ya juya a hankali yana kallon matar wacce har

yanxu kukan take tausayinta ya kamashi a

rayuwarsa sam ya tsani yaga mace tana kuka

tabbad yau ya dibo ruwan dafa kansa ubangijin

sammai da qassai ne kadai zai iya kwatansa a

hannun fanne kodai yaje wajen mahaifintane ya

sanar dashi gaskiyan lamarin kai haba kar kayi

haka addu, a kawai zakaitayi har allah ya doraka

a kanta abinda wata zuciyar ta sanar dashi kenan

zuwa yanxu ya kasa zure jin kukan da take

domin kukan na shiga har cikin kwakwalwarsa ya

juya gamida cewa don allah ruqayyah ki daina

wannan kukan da kike kar yaje yaja miki wata

illar sannan kukan naki na qara sani shiga cikin

rudani ba kuka bane maganin matsalarnan

tamuba ruky addu, a itace kawai magani domin

itace takobin mumini kaman jira take abbakar din

yai mata magana saita sake fashewa da kukan

tare da cewa

Na dade ina tunani tare da taraddadin da tsoron

zjuwan wannan ranan a cikin zuciyata na sani

babi wanda yasan abinda zai faru a gaba sai

allah amman hasashe ya fadamin irin haka zata

faru koma fiye da hakan nasha fada maka cewa

ka fito fili ka fadama matarka abinda ke gudana

a tsakaninmu tasan gaskiyan lamari tun kafin

abinda kake boye mata ya fito fili hakanan duk

tsawon darw sai gari ya waye to gashinan tun

ba, aje ko inaba magananr da nake fada maka ta

fara bayyana dukda cewa a lokacin da nake fada

maka din baka dau maganar tawa da

mahimmanciba a kullun sai nai maka nuni da

cewa wannan abin da kake aikatawa ba qaramin

kuskure bane kuma matsalace mai girma ka

dauko ma kanka saidai muyi fatan allah ya kawo

mana ita cikin sauqi na tabbata zaka fuskanci

bacin rai da bakinciki kunar zuci idan har matarka

ta gano abinda ka tona rami ka binne

Uwar Goyo

Chapter10

Abbakar din yace mata abunda zamuyi shine mu

natsu mu koma ga allah sannan mu nemi hanyar

da zamu bulloma lamarin ba kukane maganin

wannan abinba mai afkuwa ta rigada ta afku don

haka saidai muyi fatan wannan abu daya faru

damu shine mafi alkhairi a rayuwarmu

Ruky mumini baya taba zama a duniya ba tare da

allah ya jarrabeshiba ni a yanxu na damune da

damuwarki wannan kukan da kike basonsa

nakeba ada idan nace dake banason abu to kin

dainayinsa kenan har abada amman gashi a

yanxu kinason nunamun ban isa dakeba kuma

duk maganganun dana fada miki sun tashi a

banza kenan mai yasa ruky kikeson daukan

halayyar daban sanki dasu bA? Yayi furucinne a

daidai lokacin daya juyo yana kallonta hannu tasa

tana share hawayen dake fuskar tata sannan ta

tsagaita da kukan

Da alamar wannan karon ta yarda da kalaman

nasa don haka tausayinta ya sake samun

mazauni a cikin zuciyarta ryky macece mai

sauqin kai tare da bin duk wani abu daya gindaya

mata shi yasa a kullun yake sake jin sonta a cikin

zuciyarsa tare da kwadayin zama da ita da ace

ita ya fara aure to da babu abinda zaisa yai mata

kishiya domin ruky ta hada duk wani abu da

mace ta gari takedasu allah yayi mata baiwa

nakyau tare da kuma kyan hali ga kuma tarbiya

da iya zama da mutane gata da kyawawan dabiu

idan mutun ya zauna da ruky na kwana daya sai

yaso ace ya rayu da ita a waje daya sbd tanada

mu, amula mai kyau da mutane

Sam abbakar ya mace da tuki yake kuma akan

kwalta yake don zuciyarsa ta lula wajen tunanin

yaddah zai bulloma fanne cikin ruwan sanyi ba

tare dasun daga murya maqobta sun jiyosuba a

kullun yana ganar da fanne illar daga murya idan

har abu ya hadosu amman bata sauraranshi don

wani lokacin idan ta fara azalzalin bala, in nata

har sai makwabtan sun shigo bata haquri wani

lokutan ma gidan nasu cika yake da yara da

manya suna kallin fanne tana masa tijara idan

har hakan ta faru kunya ba qaramin lullubeshi

takeva don daqar yake samu yana fitowa waje

don kunya amman ita ko a jikinta ko allah wadai

da wasu mutanen anguwan nasu ke mata bai

damunta balle ta sake halinta sanin kowane

zaman aure ya kunshi jin dadi da kuma kishiyarta

akan samu rashin jituwa a wajen ma, aurata

wanda har saiya kaisu ga rabuwa ko zuwa wajen

magabata a sasantasu duk wannan abu yana

faruwane a cikin sirri

Qarar horn din da ake ta kwada masa shine ya

dawo da abbakar din daga duniyar tunanin da ya

shiga kuma a sannanne ya tuna da tukin mota

yake kuma akan kwalta yake a sanda ya gama

dawowa hayyacinsane ya lura da abinda ke shirin

faruwa

Innalillahi wainna ilaihi rajiun ya furta da qarfi sbd

ganin da yai ya nufi kan wata babban mota

gadan gadan saura kiris suyu taho mu gama

shine direban motar ya dannama abakar horn da

sauri abakar ya murza kan motar gefe guda

domin ya kaucema dureban motar rashin sani yafi

dare duhu kuma idan ajali na kiranka saika je

ruky dake zaune a gefensa ta rafka tagumi tana

tararrabin abinda zai biyo baya kaman daga

sama taji abakar na salati da qarfi don haka ta

dago idanuwanta don ganin abinda ke faruwa

salati ta shigayi tare da kabbara a daidai lokacin

da taga suna gab da mutuwa tsoro ya shiga

zuciyarta ta juya da sauri tana kallon inda yarta

ke zaune khadija ita batasanma meke faruwaba in

banda wasanta da take da yar bebinta ruky tasa

hannu zata dauko khadijan kena sai motar tasu

ta daki wani rami dake kan kwaltar tai tsalle

gamida hantsalawa ta fada cikin wani kwalbati

kusa da kwaltan sannan kuma ta kama da wuta

allah yasa akwai mutane a wajen lokacin da

hatsarin ya afku kuma dare baiyi sosaiba ai kuwa

cikin hanzari suka taimaka wajen cirosu daqar da

sidin goshi akai asibity dashu kayan dake jikin

ruky sun rine da jini kafin a isa asibity a dalilin

jinin dake fita daga jikinta abakar kuwa jinine ke

fita ta baki ta hanci yar tasu ko cikin ikon allah

ba abinda ya sameta sai dan buguwa da tai

ganin hakanne yasa ta fara kuka tana kiran

iyayen nata don ta firgita gashi kuma bataga

kowa a cikin iyayen nata ba

Hankalun fanne data koma gida ya kasa kwanciya

sai jima tai gaba daya duniyar tai mata zafi ta

rasa inda zatasa ranta taji sanyi don haka ta

kasa tsaye ta kasa zaune sai safa da marwa take

a falon nata sai kace wacce ta hadiyi tabarya da

taga ba zata iya zaman cikin falon nata bane sai

kuma ta fito tsakar gida hankalinta a tashe yake

ji take kaman qirjinta zaiyi bindiga ga kuma

haushin matannan da suka riqeta a alfijir wanda

ta dalilinsune abbakar ya samu daman guduwa

da karuwansa mai yasama ta yarda har suka

riqeta kai amman wadannan mutanen sun cuci

rayuwata kuma sunmin abinda baxan taba

mantawa dashiba a rayuwa shegu munafukai

wata qilama qawayentane allah ya tsine musu

albarka yan iska masu kwacen mazan mutane

kurama qofar shigowa tai babu ko kibtawa jira

kawai take taga shigowan abbakar din domin ta

cakumoshi ta shiga nada masa katon katon na

masifa da bala, I irin wanda tai taba gani

kojinsuba tunda yake a rayuwarsa lallai namiji

bashi da tabbas kuma badan goyo da zani bane

shiyasa tun farko bata bama abbakar din fuskaba

kuma bata amince dashiba ballentana bashi

sirrinta ayau tayima abbakar tanajin bala i domin

kuwa yayi mata abinda wani mai rai bai tabayin

mata shiba tabbas tayi sakaci sosai da har ta

bashi daman da yake fita har yake neman wasu

mata a waje

Da wani ido zai dawo gidan ya dubeta bayan ta

gama gano abinda yasa a rami ya binne lallai ta

yarda abbakar kyan dan macijine dashi mugu mai

halin dan akuya ni ya ajeni a gida bagidajiya

wacce bata da gata shi kuma ya fita waje sai

sheqe ayarsa yake da karuwansa ko babu ko

kunyar idon jama. Ar gari ballentana yaji tsoron

haduwarsa da allah haka zaka ganshi kaman

mutum ashe babban dabba ne shege wanda

bazai iya haquriba

Gaskia momie batai sa, an uba na gari ba domin

kuwa ya janyo mata abin gori a gari ne a kullun

maganan abbakar shine naji tsoron allah na daina

abinda nake toshi tsoron allahn ne yasashi aikata

wannan mummunan aikin? Ni kardai acena yana

tare da wannan cutar da ake fada wanda idan ta

kama mutun har mutuwa to indai hakane

Abbakar ka cuceni kuma kaci amanar mahaifana

tunda ai amanata suka baka allah ya isa

tsakanina dakai shikenan inaji ina gani zanbar

duniya tunda sauran kuruciyata abakar bazan

taba yafe makaba akan abinda kaimin don

saimun tsaya dakai a gaban ubangiji

Lallai ya zama wajibi naje gobe dashiya ta rakani

muje a gwada jinina wlh inhar ya tabbata inada

cutar qanjamau to saina kashe wannan shegiyar

matar datai sanadiyar cusamin cutar kuma shima

zai yabama aya zaqinta dani suke zancen

Idanun fanne suka dunga mata gixo waiga

abakar can da karuwarsa akan gado suna aikata

masha, arsu da sauri ta tuntse idanuwanta wai

ba xata juri ganin wannan abun ba tasa hannu ta

dafe daidai inda zuciyarta take jin zuciyar tata

take kaman zata futo da sauri da sauri

numfashinta ke fita gani take idan da za, a gwada

jininta ayau to sai nata yahau kai idan ana hawan

ruwama to sai tayi a yau don an bata mata rai

sosai

Wato daman abinda abbakar ke aikatawa kenan

shiyasa yakeqin kulata? Saisu debi tsawon

kwanaki ko sati bai gayyaceta zuwa

shimfidarsaba wani lokutanma sukankai wata

basuyi huldaba bata damuba a lokacin sbd

batasan abinda yake aikatawaba ita ta dauka ra,

ayine baidashi akan hakan shiyasama batabin

diddigin abinda ke hanashi rashin neman nata

kuma dadin dadawa abin bai damunta don bataga

amfaninsaba haka kawai mutum na cikin

hutawarsa a damesa bayan ba biyansa akeba

gashi kuma aita masa sukuwa akan ruwan

cikinsa sau kace wani doki duk kuma a kyauta

baza, a bama mutum ko sisiba ina amman ai ita

dadiron nasa biyanta kudi yake

Hajia fanne bata kushe tana tunanin abinda ta

gani a shagon alfijir super store ba saiji tai ana

kiraye kirayen sallan asuba da farko da taji tasha

ko kunnentane ke mata kizo dan abbakar bai taba

zuwa wanu waje ya kwanaba inhar ba sarin kaya

ya tafi ba tai gaggawan shiga falonta donta duba

agogo kuma ta tabbatar da abinda kunnuwan

nata kejin mata din ai kuwa hakane data duba

agofon qarfe hutu ne ba asuba harda yan mintoci

To ina abakar ya shiga har yanxu bai dawo

gidava kodai wani salon iskancinne ya sake

fitomin dashi kallai wuyansa yayi kwari kuma ya

sake bunqasa laifinsa a wurina tunda har yasan

ya kwana a gidan karuwa abinda bai taba

aikatawaba kenan daman ance ka tsoraci

mutumin da baya magana idan har ya tashi

kunsa maka baqinciki to saika rasa inda zakasa

kanka wato na kwana cikin baqinciki da tashin

hankali amman shi yanacan wajen dadirinsa ko a

jikinsa ko yau ni fanne na hadu da gamona wato

abbakar bai damu da damuwatava zuwa yanxy na

gama sanin cewa banida wata tasiri a cikin

zuciyarsa tabdijam lallai yau akwai rugiman da

bana fatan allah ya sauwaqeta inanan ina jiransa

zaizo ya sameni har gida koda kuwa ace shekara

zaiyi a wajrn nata ta gamacin burin wukaqanta

abbakar kuma ta nuna masa ita ba tsaransa bace

da zai mata wannan cin zarafinba

Tana kwance tana tunanin inda zata fara zuwa

neman abakar idan gari ya qarasa wayewa a

haka har bacci yai awon gaba da ita ta dade tana

barci batasanma gari ya wayeba sai zuba

minshari kawai take kasancewar ta kwana batai

barciba kuma ma daman ba sabonta bane rashin

barci

Bugun qofar gidan nasu da akene ya tasheta daga

nannauyan barcin da take tana murtsike idanu da

sauri ta nufi qofar gidan domin taga ko wanene

ke buga mata qofar gida haka kaman za, a cire

mata qofar gidan sai kace wacce ake bi bashi

tanada yaqinin abbakar ne hakan yasa da

azamarta ta nufi kiching gamida dauko muciya da

wuqa sannan ta koma zauren amman ina

zuciyarta bata amince da muciyarba don zata iya

karyewa kamin ta morema dukan nasa dashi don

haka ta juya can bayan gidan nasu taje ai kuwa

tai karo da wani faskaren itace nanfa tayo awon

gaba dashi cikin sauri ta sake dawowa qofar

gidan tana budewa bata tsaya duba wanene a

wajenba takai masa wawan duka da iccen

faskaren sauran kiris fannen ta gicciyema

makwabcin nasu gefen jafada da iccen don ita a

tunaninta tayi zaton wai ko abbakar ne ya dawo

daga yawon iskancin nasa da sauri mutumin ya

kauce don kuwa idan har ya bari wannen

faskaren ya samu mazauni a jikinsa

musammanma kansa don ya lura hajia fannen

nan take harin sama to sai buxunsa don dukan

data kawo bana wasa bane wannan dukan da

hajia fanne ta kawo masa ya dada bashi mamaki

kuma ya qara tabbatar da maganganun da jama,

a keyi akanta marasa kyau

Kai lallai kam abakar na fama da kuncin xuciya

mutum mai haquri da kamala amman allah ya

jarrabeshi da matsiyaciyar mata dashi ya dauka

duka qaryane akan abinda ake yamadidi dashi

akanta a cikin anguwa dukda yanajin ana cewa

masifaffiyace baiyi xaton lamarin nata yakai

hakaba domin ko magana bata hadata dashi da

itaba tunda allah ya kawoshi anguwan ballentana

aje ga batu na rashin jituwa suna mutunci sosai

da abbakar don bashi daga cikin masuma

abbakar din mummunan fahimta da yayi tunanin

komawa gidan nasa ba tare daya fadama fannen

abindaya kawoshiba wajen nata don iya jutewa

zai iya jure duk wani abu da zata gaya masa idan

kuwa har takaisu ga sa, insa to shine mara

gaskia tunda shine ya tako har kofar gidan nata

amman kuma daya tuna irin alkhairan da abbakar

din ke masa da kuma alkhairansa garesa ga

kuma haqqin makwabtaka sai yaga rashin

dacewar yin hakan ga kuma halin wahala da

abbakar ke ciki tun daren jiya har izuwa yanxu

sakamakon hatsarun motar da sukai wanda ake

ganinma da wuya idan zaiyi rai ya zama dole ya

daure ya fada mata domin taje taga irin halin da

yake ciki koda kuwa ace zata sakashi a cikin

turmi ta kirbashi to ya fita haqqinta ko a wajen

allah

Kai malam lfy kaxo kana bugamin gida da

sassafe kaman wanda kakebi bashi? Ko kuwa

dakai muka hada kudu mukasai gidan? Sannan ka

zubamin ido kana kallona tun daxu ka kasa cewa

komai sai kace wani maye wandayai shekara

baici namaba to ka bude kunnuwanka dakyau kaji

inhar kai mayene kaxo ka lashe kurwata toni

fanne nafi qarfinka

Kurwata kur take namana da daci nafi karfin

karamin maye kamarka don haka ka koma gida

ka sake shiri don yau babu sa, a a gareka inason

ka sani idan kanacin kasa ka kiyayi ta shuri

dominni murucin kan dutsece van fitoba sai daba

shirya kuma ni jeji ce babu mai iya min kyaure sai

mahaukacin kafinta gahon ari sai fanna ramin

kura sai yayanta daga yau nidakai mu zuba shege

ka fasa tunda fanne ta soma masifar bata dasa

ataba saida taxo iya nan shi kuwa mutumin shiru

yai yana sauraron maganganun da take yaba

masan cikin tsawa da tsiwa da kuma gatsali

dukda cewa yaji zafin maganganun nata saiya

danne zuciyarsa gamida cewa ina kwana hajia ?

cikin girmamawa daban kwanaba ka ganni ?

Bari kaji na gaya maka ni banason gaisuwarka ta

munafukai abindaya kawoka kawai nakeson ka

gayamin idan kuma halin naka na dan akuya daka

sabayima matan anguwannan kaxo kaimin to sai

kai da babban murya domin duk wannan nuku

nukun da kake babu inda zai kaika sannan inason

ka sani koda nidin yar iskace kamarka bazan

yarda dakai a matsayin kwartonaba ka dubeni

dakyau sama da qasa niba irin matan da kake

zuwa wajensu kana yaudara bane kai amman anji

kunya ba, aji dadin haliba dubeka tsofai tsofai

dakai amman ka rasa abinda zaka dinga

aikatawa sai bin matan mutane idanma iskancin

kakeso to ka tafi gidan karuwai mana tunda gasu

can a gari kaman jamfa ajos bawai ka dingabin

gidajen jama a kana lalata da matansuba

Haqiqa ayau da ace mijina yana gida da saika

raina kanka kuma daga kaina da ka daina zuwa

yin kwartonci gidan mutane kenan dukda bayanan

idan ya dawo saina sanar dashi abinda ke faruwa

don haka saika zauna cikin shiri na zuwa kotu

don ba yarda zanyiba ka batamin suna ina zaman

zamana ba mutane suna ganin mutuncina a cikin

anguwa

Fannen ta bude vaki zata qara magana kenab

mutumin ya dakatar da ita da hannu cikin fushi

ke dakata don allaha marar kunya wacce tarbiya

bai ishetaba ki sani niba abokin yinki bane kuma

wlh kinji na rantse kinci darajar mijinki vadon ina

kallonsa da daraja da qimaba a idonaba da na

rantse da wanda raina ke hannunsa daga kaina

kin dainama wani rashin kunya amman da yake

ko a lahira wani yanacin albarkacin wani yasa

zan kyaleki amman kici gaba da yima mutane

rashin albarka da sannu zaki hadu da daidai ke

kuma sharrin da kikaimin na barki da allah shine

kadai zaimin sakayyah abindaya kawoni wurinki

zuwa nai na sanar dake mijinki yayi hatsari tun

jiya da daddare kuma yayi mummunan rauni

wanda mutane da dama sun tausaya masa sbd

rayuwarsa tana cikin dayan biyu mutuwa ko

rayuwa allah ne yasa kwanansa na gaba shiyasa

har yanxu yake numfashi a halin da ake yanxu

yana general hospital na garinnan yana kawowa

nan a zancen nasa ya juya da nufin yabar wajen

tunda ya gama abinda ya kawoshi domin

tsayuwar da take a kusa da fanne hatsarine don

zuciya ba qashine da itaba kaman daga sama

yaji fannen cikin daga murya tace ahayye nanaye

allah na gode maka inama ace abbakar mutuwa

yayi yau da sai nayi qaramin fati sbd murna da

farin ciki shegu muna fukai ai halinku daya kai

dashi shiyasa taku taxo daya kai dashi banda

neman mata babu abinda kuka sani to gashinan

allah allah ya kamashi sauran kai ina mai

tabbatar maka da idan baka nutsu kayi hankaliba

a wajen kwartonci mijin wata zaiyi ajalinka

Wohoh wato dattijon ji yai kaman fannen ta dibo

ruwan garwashi ta watsa masa a jiki amman me

Mu hadu a next chapter donjin yaddah zata kaya

Naku har kullun

Uwar. Goyo.

Chapter11

Dukda yaji abinda ta fada din amman sai bai juyo

ya tanka mata ba zuciyarsa cike fall da baqin

cikin abinda hajia fanne tai masa wannan ai cin

fuskane rayuwa kenan kuma komai aida

sanadinsa haqiqa matarnan taci darajar igiyar

auren dake kanta inda kuwa ba hakaba wlh da

saina nuna mata da ruwa ake shayi don kuwa

bazai yiwu taci masa fuska ta kwana lfy ba kuma

da daga kansa ta dainama mutane fitsara da

rashin kunya kai duniya ina zaki damu bawan

allahn nan ya sadaukar da rayuwarsa wajen

samo mata abinda take buqata amman dukda

haka bai tsira ba kullun cikin tafiye tafiye yake

don kawai ya samu asirinsa dana iyalansa ya

rufu allah ya horema abbakar abubuwan jin dadi

ga kuma ilmin arabi dana boko

Hajia fanne mutumin ya tafi ya barta a wajenne

ta kasa aiwatar da komai domin jin maganar tasa

tai

tamkar a mafarki wai abbakar yayi hatsari har

wai yaji ciwo sosai wannan ai qaryane kumama

zancen banzane waya sanima qila hadabaki sukai

mutumin da yake cikin qoshin lfy jia da dare cikin

nishadi ga kuma mace a gefensa shine za, a wani

zo mata da zancen yayi hatsari kai gaskia nayi

sakaci da nabar wannan munafukin mutumin ya

tafi aida ta kansa na fara nuna musu abinda

zanma abbakar din inyaso yajema abbakar din

dashi don ya tabbatar masa da akwai bala, in

dake jiransa a gida kai mai yasa banbi

mutuminnan a bayaba domin na gano gidan

dadiron abbakar din don na tabbata gidan nasu

yanxu zai koma domin ya sanar dashi yaddah

mukayi

Amman abakar ya daukeni sakarya marar hankali

jiya mu rabu dashi lfyrsa qalau yau kuma da

sassafe axo acemin yayu hatsari dagajin

maganarma ai kasan zuqi ta malle ce sannan

kuma daga yaddah mutumin ya nuna da farko

zaka gane bashi da gaskia zuwa yanxu na harbo

girgin abbakar so yake ya nunamin ya fini sanin

duniya karka damu ai na gano shirin naka ka

gama zagaye zagayen naka zakaxo ka sameni

inanan zaune daram a cikin gidan ba asibiti kake

zauneba allah yasa a kabari kake indai har zakaji

sauqi to rigima nanan tana jiranka a gida aida

naso sanar da dashiyama abindaya faru amman

na fasa ai wlh sai naga abinda ya turema buzu

nadi don wlh abbakar ka tono tsuliyar dodo wlh

daga wannan lokacin na daina saurara maka

komai tunda nafahimci kaiba dan mutunci bane

gaba gabama inaga har gida zaka dinga kawomin

karuwan tunda naga alamun idanuwanka sun

rigada sun rufe akan aikata masha, ar taka ni

inanan zaune ina banga macen da abbakar zau

kawomin a matsayin matar da zai auraba ashe

mugun yanacan yana muna furtata a waje haqiqa

ina ganin wautar matan dake fadin da kishiyar

gida kwara ta waje kalmarma ba dadinji aini da

mijina ya fita waje neman karuwa kwara ya

auromin mata uku a rana daya ya ajemu a gida

daya ina ganin shige da ficensu Abbakar ka

cuceni harka mutu kuma bazan manta da wannan

cuta dakaimin ba haka kuma baxan taba yafe

maka haqqina daka tauyeminba

Sarkin iya magana kawai waya sanima ko shima

ta irin wannan hanyar aka sameshi tunda ni

bansan ubansaba haka tunda mukai aure ban

taba ganin dangin uban nasa sunzo wajensaba ta

kyalkyalr da daria sannan ta nufi dakin barcinta

ba tare da bata lokaciba nannauyan barci yai

awon gaba da ita bata farkaba har akai sallar

azahar wanda daman ko sallar safiya bataiba

daman can fanne ba sallah takeba bayan an idar

da sallar azhar dinne ta miqe zaune gamida

murtsuke idanu hade dayin wata doguwar hamma

cikin nutsuwa ta ture qafafunta kasa tare da

miqewa ta nufi hanyar falonta daga cikin kujerun

dake falon nata ne ta samu daya ta zauna

sannan ta shiga kwalama mai aikin nata kira da

sauri jummai mai aikin nata ta qarasao ta duqa

can nesa da ita tana kwasar gaisuwa sannan tace

gani hajia

Ki shiga bandaki ki hadamin ruwan wanka to

hajia sannan ta tashi ta nufi ban dakin domin isar

da umurnin hajiyan bayan ta gamane taje ta

sanar da ita cikin yatsine ta tashi tana wani taku

tamkar wacce takejin tausayin kasar sannan ta

fada ban dakin tana shiga mai aikin nata ta shiga

dakin nata domun gyara mata cikin kankanin

lokaci ta kammala sannan ta dawo falo nanma

ba tare da bata lojaciba ta kammala da yake mai

aikin nata akwaita da hanzari

Tsaf hajia fanne ta shigo falonta cikin kwalliya

kaman mai shirin zuwa wata liyafa sannan

jummai ta dinga jera mata abinci kala kala a

gabanta tare kuma da dauko mata lemuka irin

wanda takeso ina mommy take ta tambayi

jummai a lokacin da take zuba mata farfesun

kayan ciki tace da ita tun dazun ta farka nai

mata wanka gamida bata abinci sannan ta fice

tun sannan ban sake ganintaba

Kije ki nemomin ita aduk inda take kuma bance

kije ki zaunaba kamar yaddah kika saba idan na

aikeki ni na rasa mai yasa baki da hanxari kaman

na mutane kina tafiya kamar wacce kwai ya fashe

mata a ciki ina ganin idan na aikeki kalle kalle

kike tsayawayi shiyasa bakya dawowa da wuri

daman ai hausawa sunce komai akaima jaki sai

yaci kara yar kauye kawai wacce garinsu ko

kwalta babu

Itadai jummai batace da ita komaiba tashi tai

cikin hanzari domin aikatar da umurnin data bata

cikin zuciyarta kuwa tanajin baqincikin

wulaqancin da fanne ke mata idan da sabo yaci

ace ta saba da irin wannan cin kashin da hajia

fanne ke mata

Hajia fanne ta dauko lomai wainar kwai zatakai

baki kenan sai tsinkayar muyar mahaifinta a

tsakar gidan nasu yanayin sallama a haqiqanin

gaskia fanne bataso wannan ziyarar da mahaifin

nata ya kawo mata ba domin kuwa ta sani baya

zuwa gidan nata saida dalili bata ko shakkar

abbakarne yaje ya baibayeshi da zaqin baki akan

abinda ya faru jiya da dare shine yanxu ya debo

qafa yaxo gidan nata domin danne mata yanci

kaman yaddah ya saba ita tana ganinma fita

harkar baban nata zatai inyaso ta barshi da

abbakar din tunda yafi sonsa akanta fanne na

matuqar jin yinwa don rabonta da abinci tun jia

da yammah gashi kuma yanxu baban nata zai

katse mata cin abincin nata tana cikin hakane sai

jiyosu jimmai tai ita da momy taje ta rungume

kakan nata oyoyo shima cikin murna ya kamata

tare da tambayar maman taki tananan kuwa?

Tace eh tananan yace ti je kice da ita naxo ta

sakeshi sannan ta ruga falon maman nata domin

ta sanar da ita zuwan baban nata

Mama kixo banan cikin gida yaxo haka suke kiran

mahaifin fannen dashi tace ina xuwa momy ki

kaishi falon da ake sauke baqi saida fanne ta

tabbatar da cikints ya cika sannan ta fara tunanin

abinda zai wakana tsakaninta da mahaifin nata

wanda ayau ji take zuciyarta ba zata amince da

abinda zaizo mata dashiba idan har ya goyi

bayan abbakar domin ta gaji da danne mata

haqqin da ake haka kawai a daki mutum kuma a

hanashi kuka wai mai yasa jama a basa

ganewane a kullun daukar abbakar suke mutumin

kirki wanda ba haka bane dan akuyane mai

lullube da fatar kura wannan abin kadai idan ta

tuna sai taji ta qara tsanar abbakar din babanta

ya jima a zaune yana jiran fitowan fannen amman

shiru kakeji wanda har saida ransa ya soma baci

akan wulaqancin da tai masa daman kuma a

hasale yaxo gidan donma momy tana debe masa

kewa da irin zantuntukanta na yara ne saida

fanne taga lokaci na kurewa har yanxu bata samu

mafitaba sannan ta tilastama kanta fitowan cikin

nutsuwa ta shiga falon sannan ta qarasa wajensa

har qasa ta duqa domin gaishe dashi bai kalli

inda takeba haka kuma baice da ita komaiba a

lokacin da take gaishe dashi din ya dade yanajin

maganganu a bakin yayyun fanne game da

wulaqantasu da take idan sunzo wajenta dukda

yasan zata aikata hakan amman bai taba tunanin

shima zata aikata masa hakanba wannan shirun

da taga mahaifin nata yayi da kuma yaddah taga

fuskar tasa a daure tamau ta fahimci ba wasa a

tare dashi hakan yasa zuciyarta ta fara dukan uku

uku tsoro duk ya mamayemata zuciya bakinta na

karkarwa kaman mai zazzabi ko kuma maijin

sanyi tace

Kayi haquri don aallah idan na, bata maka raine

wlh na shiga wanka kenan momy taxo tacemin

kaxo shiyasa kaga nadade da yake shi mutum ne

mai saurin fahimta da zaran ya kalli fuskarka ko

yanayin maganar taka da sauri ya fahimci

maganan nata duk qaryane daman kuma tun

daya shigo falon ya tambayi mome me takeyi

tace dashi abinci takeci fanne ta tsugunna ta

sunkuyar da kanta qasa tana kallon qasa saiji tai

baban nata ya fara balbaleta da fada ta inda yake

shiga batanan yake fita ba yadau tsawon lokaci

yana abu daya ba tare daya saurara ba sai da yai

mata wankin babban bargo akan wulaqantashi da

tayi sannan ya umurceta data koma daki ta

dauko mayafi domin su tafi wajen abakar a asibiti

in banda rashin hankali irin naki ace mijinki yayi

hatsari tun jiya amman ki kasa zuwa dubashi to

idan allah ya dauki ransa me zakice? Yanada

ransama baki damu dashiba inaga ya rasa

wannan mugun halin irin naki na rasa a inda kika

samoshi domin kuwa dagani harmahaifiyarki babu

mai irin wannan halin naki

Zaki tashi kije ki dauko mayafin naki mu tafi ko

saina bata miki rai?

Jiki ba kwari fannen ta tashi ta nufi dakin nata a

lokacin data dauko gyalenne kafin ta fito daga

dakin nata take cewa ashe da gaskene abbakar

yayi hatsari allah na gode maka maganinsa kenan

allah ne ya sakamin a bisa cutar dani da yake

tare da munafurtata

Allah ya qara idan mutum shi bashi da aiki sai

zalunci aishi allah ba azzalumin sarki bane yana

kuma kallonsa akan duk abinda yakeyi allah yasa

da karuwar tasa yai hatsarin inaga mutane masu

goya masa baya idan sukaga abinda ya faru zasu

yarda da shidin munafukine daganan kuma

mutuncinsa ya zube mutane su dinga kallonsa da

abinda yake aikatawan

Shi kuma babana da yaxo yAnata wanimin masifa

ce masa akai nice sanadin hatsarin nasa ko

meye ? Da zaizo ya dingamin tsawa dolene sai

naje na gaishe dashi koko nice ke bada lfyn

daman ai hausawa sunce a wajen kwadayi kuda

ke mutuwa to gashinan ta faru akan abbakar

tunda ya biyema son zuciyarsa kuma ta kaishi ta

baro da danasani wanda bazai masa amfaniba a

motar hajia fanne direba ya tukasu daqar

mahaifin nata ya shiga motar donda shi cewa yai

bazai shiga motarba saidai su shiga ta haya

domin ya gama tsinkema da lamarin fanne don

gani yakema idan ya shiga motarma akwai

wulaqancin da zata sakeyi masa don haka yace

shi baxai shigaba daqar direban ya shawo kansa

sannan ya yarda ya shiga motan suka tafi a cikin

motarma nasiha ya dingama fannen akan tabi

duniya a sannu sannan tai hankali tun kafun

dunya ta koya mata duk abubuwan da mahaifin

nata ke fada mata bajinsu takeba don da tanajin

abinda yake fada mata da tuntun ta zama kamila

Sun isa asibitin mahaifin fanne ne yai musu

jagora zuwa dakinda abakar din yake duk mutum

mai imani idan yaga halin da abakar ke ciki saiya

tausaya masa akan mummunan halin da yake ciki

ko ina a jikinsa ciwone duk an nade jikin nasa da

bandeji yana kwance akan gado kaman matacce

numfashima saida akasa masa abin janyowa

karaya hudu ya samu tare kuma da manyan

rauniya a jikin nasa allah kenan mai yaddah yaso

da bayinsa jia da kamar haka abbakar na cikin

qoshin lfy sai gashi kuma yanxu yana gadon

asibiti a kwance yawan raunikan dake kansa da

kuma zubar jinin da yakene likitoci ke zargin koya

samu tabin kwakwalwa yan uwansa da

abokanansa duk sun cika dakin ko wannensu idan

ka kalla fuskarsa babu walwala amman dukda

wannan mummunan hali da abbakar ke ciki

matarsa hajia fanne bata tausaya masa ba ita a

tunaninta duk sakayyah ce gameda abinda yake

mata allah ya kamashi fanne ta shiga gamida

samun kujera ta zauna fuskarta cike da walwala

tana taunan cingam din dake bakinta tare dayin

kas kas ko kunyar idon jama, a bataiba balle ta

rage abinda takeyin kowa a wajen ya fahimci

jinyar da abbakar keyi bai damu matar tasa va

domin babu abinda ya dameta harkar gabanta

kawai take kunya duk tabi ta lullube mahaifin

nata akan abinda fannen keyi qanwar abakar da

suke uwa daya tazo zata wuce bata saniba ta

taka fannen kamin fannen tace wani abu matar

tace don allah kiyi haquri bada sanina na takaki

ba habawa kin tabo zuliyar dodo fanne cikin fushi

tahau qanwar abakar din da masifa harda kumfar

baki daman me neman kukane sai kuma aka

jefeshi da kashin awaki hankoron da fanne ke a

wajenne ya janyo hankulan jama, a har suka

fahimci abinda ke wakana a tsakaninsu

Mahaifintane cikin fushi yace da ita kekam

malama ki rufe mana baki ke kam fanne kinji

kunya a rayuwarki wlh me za, ai da hali irin naki

ki duba ki gani dukkanin mutanennen dake

tsaitsaye hankalinsu ya kasa kwanciya duk ta

dalilin halin da mijinki ke ciki amman ke ko a

jikinki da yake duniya na zugakine koya mutu

koya rayu ko a wannan halin da yake ciki wai har

kinada bakin yin masifa na dade ina miki fada

akan ki guji bakin mutane tofin san barkama daya

mutum ya qare ballentana tofin ala tsine nandai

fanne tai tsuru tsuru ta kasa cew komai har saida

baban nata yai mata masifan iya yinsa yana

gamawane likitocin dake duba abbakar din suja

fito yan uwansa dake bakin qofar suka tarbi daya

daga cikinsu doctor ya jikin abakar yace dasu jiki

da sauki kuma cikin ikon allah in allah ya yarda

zai samu lfy nan bada jimawa ba sannan ya wuce

cikin sauri fanne ta dafe kirji donjin kalaman

docton tai kaman saukar aradu tace kan kaza

kazan can tayayama za, ai haka ta faru nida

nakeson a qallah yai shekara a gadon asibiti yana

jinya kafin ya qarasa kuma shine dan tsinannar

doctorn nan zaizo yace mana zai warke nan bada

jimawaba ai wlh da sake nanfa cikin tashin

hanakali hankalin kowa ya dawo kan fanne

gamida zare idanu lol

Uwar goyo

Chapter12

Kwanan abbakar hudu a asibityn amman har

yanxu baisan wanda ke kansa ba domin har

izuwa yanxu bai farfado ba mahaifiyarsa

hankalinta ba qaramin tashi yaiba don a

tunaninta kawai mutuwa yai ba, ason a fada

matane a kwanakin da yayi babu mai shiga

dubashi in banda likitoci duk sanda likita ya shiga

ya fito sai mahaifiyar tasa tabi likitan domin taji

ya jikin dan nata da sauki kawai suke ce mata

amman har yanxu bai farfado ba a yaune

akesaran zai dawo hayyacinsa don haka jama, an

dake gurin suka duqufa dayi masa addu, a a

kullun sai mahaifin fanne yaxo asibitin domin

duba abbakar din kuma itama fanne yasa mata

dokan zuwa dubashi a kullun dukda zuwan nata

bashi da wani amfani kasancewaR duk zuwan da

take bata taba tambayar ya jikinsaba a kullun

idan taxo saidai ta samu waje ta zauna taita cika

tana batsewa idan kuma da kayan ciye ciye taxo

taita ci kamar jaka

A duk sanda dereba ya kawo mata abinci

batayima kowa tayi kasancewar a aaibitin take

wuni hatta mahaifinta bata bashi abinci ita kadai

take zama ta nade kayanta

Wannan abu da hajia fanne take ya sake tabbatar

mada yan uwan abbakar bata damu da rashin lfyn

nasa ba a kwana na shidane abbakar ya farfado

don haka likitoci sukai cai akansa domin ceto

rayuwarsa kasancewar jinin dake fita daga

bakinsa ta dalilin taunan harshensa da yake an

dau tsawon lokaci kamin su samu daman tsayar

da jinin sannan sukai masa allurar barci kamin

kace me barci mai nauyi ya daukeshi

numfashinsa na fita daya bayan daya washe

garin rana ta bakwaine abbakar ya kammala

dawowa hayyacinsa wanda har yakan shaida inda

yake a kwance abubuwan da suka faru ya dinha

dawo masa daya bayan daya cikin fargaba yace

ina ruky da khadija kardai ace suma sun tsinci

kansu kaman yaddah shima ya tsinci kan nasa ne

yace allah yasa dai suma basuji ciwonba addu, a

ya dingayi a cikin zuciyarsa akan allah ya kare

masa yarsa da matarsa

Can kuma yace allah sarki ruky nayi sanadin

fadawarki cikin tashin hankalinda kika dade kina

gudu kiyi haquri insha allahu komai zai zamo

daidai da zaran mun samu lfy fatana allah yasa

bakuji rauni sosai ba likitoci sun sanar da yan

uwan abbakar cewa ya gama dawowa hayyacinsa

don har yana gane a inda yake don haka suka

basu daman shiga dubashi mahaifiyarsace ta fara

shiga dubashin saidai kash tana shiga ta tarar da

har ya fara barci sai misalin bayan sallar magrib

ya farka qannensane a cikin dakin duk sunyi

zugum sai kace wadanda aka aikoma sakon

mutuwa saida ya kira sunan daya daga cikinsu

sannan suka tabbar da ya farka nanfa suka

nufeshi ya kuresu da ido ko kiftawa baiyi yace ina

ruky da khadija suma sunji ciwon irin nawa ne?

Babu wanda ya bashi amsa har ya gaji da

tambayar tasa yai shiru don yaga alamun ba

maganan ruky ce ke gabansu ba ba yaddah ya

iya dole ya koma ya kishin gida gamida rufe

idanuwansa ba barci yakeba kawai tunanin irin

halin da ruky da yarta suke ciki yake

Shin meya hana ruky zuwa inda yake?

Abbakar yanajin muryar mahaifiyarsa tana

tambaya akan har yanxu barcin yake? A hankali

ya bude idanuwansa yana kallonta wanda itama

kallon nashi take nan ta qarasa wajensa tace

sannu dannan ya jikin naka? Da sauqi ummah ya

bata amsa allah ubangiji ya baka lfy kuma ya

tashi kafadunka amin tana dasa aya yace

Umma don allah ina ruky da khadija kodai suma

sunji raunin ne kaman yaddah naji? Wannan

tambayar da abbakar yaima mahaifiyar, tasa a

yanxu bata da amsar ko daya daga ciki kuma ma

bayanxune lokacin dayakamata a amsa masa su

ba

Umman tasa tace ruky da khadija suna nan lfy

babu abinda ya samesu daxun bada jimawaba

ruky ta koma gida domin canjama khadija kaya

kasancewar ta bata na jikinta amman nan bada

jimawaba zat dawo bai bata amsaba saidai harga

zuciyarsa ya amince da maganan mahaifiyar tasa

domin tunda yake da ita bata taba masa qaryaba

A kullun idan ya tambayi ina ruky taje sai

mahaifiyarsa ta nemo wata maganan ta toshe

kunnuwansa dasu tun yana yarda har ya soma

raba daya biyu rannan dai ya dameta da magiya

gamida kuka akan don allah ta taimaka ta fada

masa ta taimaki rayuwarsa ta fada masa inda

ruky take ko ya samu nusuwa ga tunaninta daya

hana zuciyarsa sukuni

Da mom din tasa taga ya tashi hankalinsa da har

yake son shiga wani hali saita yanke shawarat

gaya masa gaskiyan abinda ke faruwa kawai

saida tai masa nasiha sosai sannan take shaida

masa da saidaifa kayi haquri abbakar domin

wanda ya fika son ruky ya karbi abinsa a dalilin

hatsarin da kukai don daman ita ba, a fito da ita

a motan da rai ba amman khadija tananan da

ranta babu abinda ya sameta yanxu haka tana

wajen kakar rukyn addu, a kawai zaka dage dayin

mata don a yanxu babu abinda tafi buqata a

wajenka da ya wuce addu, arn

Tunda aka sanar dashi cewa ruky ta ra su ya

shiga rudanin da bai taba shiga irinsaba duk wani

zogi da radadi da yakeji a sakamakon raunikan

dake jikinsa daina jinsu yayi tun sanda ummansa

ta sanar dashi mutuwar matar tasa haqiqa yaji

ciwon rasuwan ruky ba kadanba ita kanta umman

tasa ta tausaya masa don tasan ba qaramin

rashi yai ba ranan da yaxo mata da batun auren

nasa sanin mummunan halin da yake ciki a

gidansane yasa tai farinciki sosai da auren nasa

me za, ai da halin fanne wacce tunda mijin nata

ya farfado har izuwa yanxu bata leqo ta

dubashiba balle har aje ga batun tai masa ya jiki

ko ta taimaka masa da wani abu shidinma bai

nemetaba ruky kawai yakeda muradin gani a kusa

dashi saidai hakan ba mai yiwuwa bane don ruky

ta dade da zama a kabarinta

Abbakar ne kwance a kan gadon asibitin kansa na

sama yana kallon silin din dakin da yake ciki yayi

nisa cikin tunani tunda akace dashi matarsa ta

rasu ya daina magana da kowa saidai ya kwanta

yai shiru yana tunani wasu lokutan kuma kaga

hawaye nabin kumatunsa kaman wanda aka bude

famfo

A halin da ake ciki yanxu ya tsani yaga fanne

kwata kwata ta gama fita a cikin ransa ko hanya

bayaso su hada ballentana ace gida daya zasu

zauna shima tunda ya dawo hayyacinsa bai

nemetaba sam yanxu baison ya ganta a kusa

dashi dukda yana jiyo muryarta a waje idan halin

nata ya motsa amman bai taba cewa a kira masa

ita ba toma mai zataxo tai masa komai

muqaddarine daga allah sanadin ganin fuskarta

zai iya dawo masa da hotunan duk abubuwan da

suka faru a baya duk ta dalilin masifarta itace ya

kamata ta shigo dakin domin jin yaddah ya qaraji

bawai ahine zai zaisa a kirawo masa ita ba

A bangaren fanne kuwa baqincikin farfadowan da

abbakar yayi ne ya sata rashin shiga ta dubashi

don ita ba hakan tasoba mutuwa kawai taso yayi

a ganinta hakan kawai shine zai huce mata

baqincikin daya kunsa mata tayita bincike akan ta

samu lbrn matarnan da taga abbakar tare da ita a

cikin shagon alfijir amman bata samu damar gano

ko wacece itaba haka kuma a kullun idan taxo

sai tayita baza idanu ko allah zaisa taganta taxo

duba abbakar din sai kuma aka samu akasin

hakan

Fanne tayi tanajin boma bomai da nukiliya tare

da makaman qare dangi akan wannan karuwar ta

abbakar so tai kawai ace matar ta dauko qafarta

mai kama da lauje taxo asibitin

Fanne so tai ace matar taxo asibitin ayita ta qare

in yaso daga ranan kowa ya kama gabanshi don

tayi niyar idonta idon matarnan wlh wlh saita

baqunci lahira in kuwa har batai sa, an kashetaba

to saita sauke mata wani sashi na jikinta dalilin

da yasa kullun take zaryar zuwa asibitin kenan

bataqi ace sun rabu da abbakar ba don tanada

qadarorin da zata iya riqe kanta dasu ba tare da

tasha wahala ba saidai ba zataso hakan ya

faruba don bata gama cika burintaba don so take

ta mallake duk wani dukiya da qadarori na

abbakar gaba daya su dawo hannunta ya zama

sai yaddah tai dashi kenan hakan yasa takebin

abbakar din a hankali don daman hausawa sunce

idan mage zata kama bera likimo take wato

sanda take har allah ya bata ikon damqarsa a

hannunta

Uwar. Goyo

Chapter13

asibin. sai ya tsinc mata ya kuma cire ta daga

cikin jerin ‘ya’yansa da ya haifa, kuma ko

mutuwa ya yi karta kuskura ta je kan gawarsa,

tunda dai shi bai isa ya gaya mata magana

tajiba. a wannan karon Fanne. ta ga Bacin ran

mahaifmta irin Wanda ba ta taBa gani ha, don-

haka ne ma ta yarda da dokar daya kafa mata,

sai dai kuma kwalliya ba ta hiya kudin sabulu ba,

saboda wanda take zuwa asibilin dominsa bai

ishe ,ta kallo ha ma balle ta iya budar baki ta ce

da shi ya jiki, k0. kuma ta'taimaka masan kamar

'yadda mahaifinta ya ce da ita. A kan hakan ne

ma dayawa daga cikin- ‘yan uWan Abbakar din

suke cewa, ba su ga’ amfanin zuwanta asibitin

ba, tunda ba gaishe da marar lafiyar Wanda 'take

zuwa dominshi. ' cin mutunci da neman husuma

ne kawai suke kawo ta aSibitin ba komai ba, ga

shi kuma kullum za ta zo sai tasha wanka ta

dauki ado: kamar wadda za ta je wajen' biki,

haka ma Momi da sauran qawayent masu zuwa

yi mata jaje Dashiya kam tare suke wuni da yake

a asibitin ta ke aiki, za ka gansu suna ta hirar

duniy'a cikin kwanciyar hankali tare da nishadi

babu abin da ya dame su rayu’war jin dadi kawai

sukasa a gaba. . Hajiya Fanne bilayinta , kawai ta

ke- zuwa a asibitin wai bara a kufai inji wani

mawaqin Hausa. ‘Yan uwan Abbakar sun fara

gajiya da zuwan nata, hatta da mahaifiyarsa

yanxu abin ya fara damunta .a cikin zuciyarta,

duk da hakuri tare da kawaicin da ta ke da shi, ta

kuma gano cewa akwai wani abu da ya faru a

tsakaninsu shi da ita kafin Allah ya dora masa

wannan jinyar, sai dai ba ta mat’sa wa Abbakar

:da tambayar mene ne ke faruwaba don ba ta so

ya sake shiga wani hali bayan Wanda ya ke Ciki,

koma mene ne idan ya yi' tsami za ta ji, don ko

ta tambaye shi ma bai zama lallai ya’ sanar da

ita' ba, saboda shi mutum ne wanda Allah ‘ ya

halicce' shi da zurfin ciki, ba kowanne magana ba

ce za ka ji ya fada wa mufum ita ba. . ‘ A" yau

ne aka ba ‘wa Abbakar Sallama daga asibiti, don

haka suka. tattara yanasu-yana-su suka yi gida,

a cikin zuciyarsa bai so a ce an mayar da shi

gida ba, inda tanashi za a bi to da' an kai shi

gidan da suka zauna da Rukayya'ya yaje ya yi

jinyarsa a can, don gani yake yi zai samu sauqi

cikin qanqanin lOkaCi a can din, sabida babu

Wanda zai dinga tayar masa da 'hankali. Ji yake

yi kamar kabari za a 'kai shi, k0 kuma kurkuku

don shi a halin 'da ake ciki yanzu ganin gidan da

suke shi da Fanne yake yi kamar wata maqabarta

Amma dukda halin da yake ciki ya zama dole ya

yi hakuri a mayar da shi can din, idonsa a rufe

yake tun lokacin da aka dauko shi daga cikin

dakin da yake kwance asibitin, hatta sanda suka

iso gidan bai bude idonsaba kuma bai ce .‘d'a

kowa komai ba, a bangaren da yake aka ajiye shi,

don Fanne cewa ta yi ba za a kawo mata wari da

dattin asibiti dakinta ba. Kannen Abbakar guda

biyu maza su ne za su zauna a wajensa domin

sudinga kula dashi tunda har yasamu ya warware

zuwa yanzu akwai, sauran ciwuka ‘a jikinsa,

kuma ga shi yana tare da Karaya har guda

shiddah mahaifiyarsa ce ta kawo wannan

shawarar, don ta San halin Fanne ba za ta kula

da shi ba, sai dai ya rube a zaune Mahaifiya‘r

tasu ta ja musu kunne sosair a kan su zauna da

matar gidan lafiya, kar su kuskura su shiga

shirgin da ba nasu ba, duk abin da za ta yi musu

na Batanci su yi hakuri tare da jurewa tunda ba

don ita suka zo b a, kuma dalili‘ ne ya kawo ku

gidan ,,ba wai kun zone don jin ‘dadi ba, haka

kuma zaman naku a gidan na dan lokacineDan

uwanku za ku duba da irin hal'in da yakeciki, ba

biye mata za ku dinga_ yi ba, kullum ana jinku a

makotaba, na yarda da halayyarku nagari shi ya

‘sa na zabe ku cikin ‘yan uwansa da zaku zauna

a wajensa, ina fata ba ba zaku watsamin qasa a

ido ba cikin kulawa sukace mata insha allahu

zasu kula sannan sukai sallama ta fice futarta

dakin fanne ta nufa inda ta sameta tai daidai

akan doguwar kujera tana taunan cingan ga sauti

na tashi daqar fanne ta amma sallaman da uwar

abbakar din tai mata sannan tai mata sallama ta

wuce fitarta keda wuya fannen taja wata doguwar

tsaki mtwwww shegu matsiyata kawai kina

tsammanin kawo wadannan matsiyatan da kikai

domin kula da abbakar shine zai hanani aiwatar

da abinda nai niyyah lallai bakisan wacece fanne

ba matsiyata kawai kai matsiyaci baib ko a cikin

mai ka sanyashi ka tsami haka zaka tsamoshi ba

tare daya dangwalo manba shiyasa nake gudun

zama dasu don kana sake zasu shafa maka

talauci da baqin halimutanen unguwa wadanda

suke zaune layi daya suka yi ta shigowa suna

duba jikin Abbakar din maza da mata, tare kuma

da yimasa ta’aziyyar mutuwar matarsa, da yawa

daga cikinsu daman sunje asibiti sun duboshi a

lokacin da yake kwance .a can, an Samu kusan‘

kwana uku da dawowarsa gida, .amma har

.yanzn gidan nasu bai rabu da ‘yan zuwa dubiya

ba, wanda duk bidirin da ake yi Hajia Fanne tana

daga Bangarenta a zaune k0 kallo ba su ishe ta

ba, balle ‘tace dasu wani abu. ' Jira kawai take yi

mutane su tsagaita da zuwan nasu ta samu

damar sauke wa 'Abbakar boma boman da ta yi

,masa tanadinsu, domin ba ta so kowa ya san da

abin da zata yi masa, saboda kar sukawo mata

cikas a cikin lamarin. Wannan yasa shige da ficen

da mutanen suke y'i‘ a gida'n zuwa yanzu ya

.Hajiya Tsigala, domin a 'dalilin zuwan nasu ba ta

samu» damar cikar burinta ba, wand. ta isawon

kwanaki tana dakonsa a' cikin ‘ zuciyarla, da ma

tun sanda ta je 'asibiti ranar da mahaifinta ya

tusa keyarta ta ke ta kissa rashin mutunci da

wulakanci tare da. tozarcin da Za ta yi masa idan

aka ba shi sallama ya daw'o gida, idan kuma ya

mutu kamar yadda ta ke fata shi kenan ya

tsallakerijiya da baya, ya huta daga tijarar da za

ta sauke masa. ’ '

. sai kuma akai rashin sa, a bai mutu ba

kuma gashi har an sallamo shin wankin hula yana

neman kaita dare, don haka ya zama dale ta dau

matakin da za ta dauka tun kafin lokaei ya kure

mata

A kwana na biyar ee mutanen da suke zuwa

wajan nasa suka dan tsagaita, ganin wunin ranar

babu wanda ya zo duba shi har aka yi. sallar

la’asar, wannan ne ya ba wa Hajiya Fanne damar

tunkarar inda Bangaren Abbakar din ya ke, domin

ta ida nufinta wanda babu ko sallama haka ta

shiga dakin cikin daurewar fuska kamar wacce

aka aikoma da mutuwa

Cikin karaji ta ceda qannen Abbakar, din Malamai

ku fice ku aa ni wuri, akwai abin da zanyi dakin”;

« ' ‘

Daya daga cikinsu ya yi mata kallom biyu taro

uku aha, salman ya ce da ita, “Ba inda za mu je,

duk abin da za ki yi, ki aiwatar da shi muna

kallonki domim ban yarda da keba, tunda na ga

alamar babu imani, a cik‘m zuciyarki”. ' '

Kai don Allah daka‘ta, niba sa’arka ba ce; don

haka nake umartarku da ku ficemin min daga daki

tun

kafin na sauke maitar fushin nawa a kanku har

daya daga ciki ya bude baki zai ce da ita wani

abu’ Abbakar ya kira sunansa a hankali tare da ce

masa, “Karka sake cewa da ita wani abu, ba

yayarka ba ce zaka tsaya kana fadi in‘fad'a da

ita? K0 kun manta da abubuwan da Umma ta ce

da ku ne? Ku yi haquri' don Allah ku je daga waje

11a dan wasu mintina, ina ga akwai maganar

data ke son ta fadamin na sirri” ne

Cikin sanyin .jiki suka fice daga dakin, Fanne tana

ganin haka ta juyo suka fuskanCi juna da shi,

kallo daya ya yi mata ya dauke kansa, dimin. ya

’hango zallar masifa a cikin Ruwayar idsanun

nata , a yadda ya ga ta birkice ta dawo kamar

wata zautacciya sai muzurai ta ke yi kamar

Zakanyar da ta dauki tsawon kwanaki ba ta samu

abinci ba, .sam babu annuru a fuskanta, ya

tabbalar wa kansa cewa, ba zaman Iafiya ee ya

kawota Wajensa ba, a karo na biyu ya sake.

'kallon cikin idonta, numfashinsa ne ya ji yana

shirin daukewa, .saboda tsorata da‘ y'ayi- da

abin da ya hango .a ‘cikin idon‘ta. ~ Ko dai ace

ta zone don ta kashc sh? K0 kuma. ta haukacene

bai ‘sani ba? Wad'annan tambayoyi ne .da ya

yiyiwa kansa, wanda kuma ba shi da amsarsu,

sai yanzu :ya gano cewa ya yi babban kuskurc

da ya ce da kannensa su fita daga waje , domin

kuwa duk abin da Fanne zata yi masa na

mugunta ba zai‘iya kare kansaba yanxu ya ZAiyi

da kansa kenan don yasan koda kira ya kwala

musu baji zasuyi ba don da alamun sunyi nesa da

dakin nasa kai nimadai nayi rashin tunanin toya

kenan!?

Mu hadu anjima da yammah donjin yaddah zata

kaya ina ganin daga yau zamu fara post sau biyu

a rana

Uwar. Goyo

Chapter14

kare kansa ba, to yanzu ya ya zai yi da

rayuwarsa ya sani k0 kira ya kwala wa kannensa

ba za su ji bu, don da alama sun tafi da nisa. Shi

ma dai ya yi rashin tunani, shi ya’ s'a ake son

idan mutum zaice wani abu ya yi nazari kafin ya

furta. ' ‘Hasbunallalm Wa'niimal warhl3. ya

sh‘iga furtawa a hankali, domin Allah ya kawo

masa agaji, ya‘kuma kare shi daga mugun

shar'rin Fanne, don ya gama Sadaukarwa zai iya

cewa, Allah ne kad'ai zai iya kuButar da‘shi

'dagadukkan abin ‘da ya kawo "*Fanne dakinsa.

Domin ya Allah buWayi ne gagara misali, kuma

da wannan addu’ar da' yake yi ne Allah ya

kuButar da Annabi Ibrahim (AS) a lokacin

dakafurai suka hura Wuta za su jefa shi a ciki, a

dalilin ya karya musu allolinsu, wanda suke yi

musu bauta. Suna’jefa shi kafin ya karasa.

cikinta. sai'ya ambaci wannan addu’ar, sai Allah

ya ce da wutar ta yi sanyi amma bamai 'cutarwa

ba a gareshi. 'Haka kuma ita ce. addu’ar

da;Aimabi Yusuf (A.S) ya yi a sanda ‘yan

.uwanSa suka jefa shi a cikin ri'jiya, don haka

yana da kyau musulmi mumim' ya dinga tunawa

da' Uba'ngijin ya- halicce shi a kowane irin hali'

ya tsinci kansa Abbaka’r ya ci ‘gaba~ da

maimaita kalmar a bakinsa tare da-jiran'

hukuncin' 'd‘a Allah (S.W.T) zai yanke masa.

Ita‘kuma uwar ‘yan rigima tunda ta taje ta tsaya

a kansa ta zura masa na mujiya ba ta ce da shi

komai ba‘ An dau tsaWon lokaci a haka babu

wanda ya yi wadan uwansa magma, da ma shi

Abbakar b'a son~ yawan magana yake ba, ‘kuma

shi da yake neman mataimaki wace magana zai

yi mata?

Fanne tsayuwar da ta yi tana kallonsa rasa ta

indazata fara abin da ya; kawo ta dakin ta yi, don

laifmsa- a wajenta yana da girman gaske. Tana

tsaye a wajen da take har yanzu, k0 me ta tuna?

Kawai

sai ta bude bakinta ta shiga zuba masa ruwan

ashar masu maiko, zagi ta uwa ta uba ta shi

masa tare da‘ warwarw masa irin jahilcin nata.

Saida tai masa tatas sannan ta shiga maida

numfashj, haushi duk ya; cika mata zuciya, domin

kuwa shiru ya yi mata kamar ' ma baisan abin da

ta ke yi‘ba, ya manna mata bajin hauka,-bai ce

daita ta 'tafasa balle ya ce ta kone, da ma

wannan ko’in kul'a da Abbakar yake yi .wa Hajiya

Fanné‘ idan tana yi masa- masifa tare da kumfar

yana yi mata ciwo sosai, shi yasama wani lokacin

bata saurara masa idan rigima ta hadosu Abbakar

maki ne ya cika masa . cikin zuciya, tare da yin '

godiya ga Allah da ya kuButar da . shi, saboda

bai taBa tsammanin abin nasu' afatar baki zai

tsaya ba. yana cikin tunani sai‘ ya ga Fanne ta

sake kusantowa inda ya ke sai da cikinsa ya

bada wani irin sauti kululu don tsoron abin zai

biyo baya, amma kuma tana zuwa, daf da shi sai

ta d'aga hannunta ta nuna shi da yatsa daya‘,

tare da cewa, “Da ma ance qarshen munafuki jin

kunya, to ga shi kuwa kaji tunda-duk duniya ta

fahimci abin da ka dad'e kana aikatawa a boye.

Kai bayan jin kunyar ma hatta sakamako ka

samu, donAllah ya saka min“cutata da kake yi,

tunda gashinan ka zama nakasasShe, musaki

wanda ba shi da amfani in ban da bar'a‘ a bak'm

titi. Shi din ma sai dai ka samu mai turaka a kan

keken guragu, inyaso ku, dinga raba abin ida kuka

samu. Na yarda a yau da ake cewa mutum

mugun icce ne, .wallahi ko kur’ani aka ba ni zan

iya dafawa na yi ‘rantsuwada shi akan cewa kai

ba ka neman mata, _ashe abin duk ba'haka yake

ba, ba a gane mutum ta ‘fuskarsa ko kuma ta

jikinsa, domin duk wani hali mamar kyau da yake

yi a cikin zuciyarsa yake Boyewa.

Abbakar ka ji kunya, kuma" ka ba .ni mamaki, a

ko yaushe kana cikin .aibata 'ni kayi min

inummunar fassara, ba ka‘ da wanihira da za ka

yi min~sai wa’azi, yau ka ce min Allah ya ce

kaza, gobe ka ce da ni Manzon Allah (S.A.W)' ya

cé‘mu mata mun fi yawa a cikin Wutar

jahannama, idan mutum ya Zauna yana

sauraronka sai ya rantse dacewa duk duniya babu

abin halittar da Yake jin tsdron mahaliccinsa

irinka. Ai kamata ya yi ka fara yi wa kanka

wa’azi kamin ka yi wa wani, ‘ koda yake an ce ka

ji fad‘ar Malam, amma kar ka yi aiki da abin da

yake aikatawa. Allah ai ba azzalumin Sarki ba ne,

sai bawan .da ya zalunci kansa, ga shinan kuwa

mun ga ishara a kanku kai da karuwar taka. ~ Ita

kam ma nata abin ya yi muni,’ tunda jiya na

samun labarin cewa tare da ita kuka yi hatsarin, '

ita ta sheka barzahu garin da ake arhar gyada,

kuma idan an tafi ba a dawowa, ba na k0 shakka

a ’ halin da ake ciki yanzu tana can cikin wutar

jahannama, kuma a ciki za ta dauwama, tunda ta

aikata Zunubi mai gilman gaske, da ma yanzu an

ce idan ka‘ yi wa Allah laifi tun a cikin gidan

duniya ya ke fara yi make hisabi, ba sai ka‘je can

ka same shi ba, ashe da gaske suke yi, dan ga

shi nafara gani da idona abin da suke fadamin ya

fara a kusa'da ni,. don haka ya kamata 'mutanen

dum'ya su yi taka tsantsan da rayuwa'r, kuma su

guji aibata :‘yan uwansu' a kan abin da ba su‘ da

masaniya a kai

Abbakar kasa hakuri ya yi da jin wannan shirmen

na Fanne da take yi wa Rukayya, domin kuwa k0

da ace ita din kamwar ce da gaske, bai kamata ta

ce da ita ‘yar wuta ba, domin ba a shiga tsakanin

mutum da ubangij'msa, .haka nan akwai karuwar

data shjga aljanna don Allah (S.A.W) mai ‘yawan

gafara ne, kuma mai jin Kai, kuma Yana yafewa

bayinsa’wanda Ya so zunubansu matukar ba su

yi shirka ba, ya Allah ka yi mana tsari da yin

shirka qarama da babba, amin. sannan

Rukayya salihar mace ce mai halin matan kwarai,

wanda idan mutum ya mallake su ya huce

takaicin duniya, kuma ya samu jin dad'm rayuwa,

amma Fanne ta ke yi mata qazafi tare da

aibatata, kuma da yi mata mummunan fata'

wanda shi a nasa tlmanin “rahamar Allah ya. ke

mata fata ba azabarsa. ba, tunda ta mutu me a

kan tafarkin gaskiya, ga shi ‘kuma a sanda

numfashinta zai ,d'auke ya ji ta da kunnensa

tana maimaita kalmar shahada a bakinta, sanna

Manzon Allah (S.A.W) ya ce,‘ “Duk wanda ya

mutu da kalman shahada a bakinsa to babu

makawa zai shga aljannah

1 Da ace lafiyarsa qalau, kuma. ana hukunci ne

da qur’ani a kotunan garinmuto da sai! ya kai

Karar Fanne’ an Mawa Rukayya haqqinta na

qazafin da ta yi mata, sai dai yanzu ba'shi da

ikon y'm komai, dOn haka ya barta da Allah shi

ne zai yi musu hisabi Abbakar yana cikin tunani

ya ji Fanne zata sake yin magma, sai ya yi saurin

ya ce da ita.

“Dakata Fanne abin naki ya fara isa ta, ina so na

sanar da ke wani abu da ba ki sani ba, duk wani

rashin kunya da cin muttim'ci idan za ki ki yi min

shi ni kadai, amma-kada ki kuskura ki 'saka da '

Rukayya a ciki, domin ita babu ruwanta kuma ba

ta yi miki wani Iaifi ba, haka kuma aAhalin da a

ke; ciki, ba ta ma san kina'yin wannan haukan

ba, saboda ta .riga ta bar miki duniyar ma gaba

d'aya, ‘ sai ki d'auki abin da za ki d'auka a ciki.

Da a Ce kin san gaskiyar yadda lamarin yake da

ba za ki tsaya a kaina kina ta BaBatu harda da

kunfar baki ba.

Zuwa yanzu Fanne ya kamata kiyi karatun ta

nutsu, ki yi sani' da cewa, duniya ba matabbala

ba ce, ki duba‘ ki gani lokaci daya Allah ya mayar

da ni haka,_bacin aranar na wuni cikin koshin~

lafiya'babu wani waje a jikina inda ya ke yimin

ciwo, amma sai kuma kika wayi gar kika ganni

cikin lalura; duk ireiren haka Allah yana nuna wa

bayinsa aya ne‘ko za’ 'su hankalta su daina

abubuwan da suke munana; tabbas maganarki

gaskiya ne da kika ce darasi ne Allah ya nuna a

kaina, amma kuma ba ta hanyar da ke kike

tunaniba

_ ' Don ita Rukayya da’ kike masifa a ‘kanta‘ kina

kiranta da sunan karuwa, to bari yau na gaya '

miki mene ne gaskiyar abin da’ ke tsakaninmu.

Matata ce wadda ita ma. na biya kudin sadaki

aka daura mana aure‘da, ita, shaidu suka shaida,

kuina muka yi zama‘a' tare irinna ’auratayyah, a

bisa 'yadda shari’ar imu§ulunci tatana’darwa

koWane mutum Wanda haihu da zuria a

tsakaninmu,“Allah ya. azurta mu da haihuwar

Khadija Wannan yarinyar da kika gani a tare

damu kuma mun same tane ta aure ba wai ta

hanyar ,da kike nufiba. "Na yi miki rantsuwa da

Allah ni ne namiji na farko da na fara sanin

Rukayya ‘ya mace, kuma bayan haka ma ita ba

mai , yawan zuwa unguwabace, k0 da kuwa zata

nine ke kaita kuma na dawo da ita belle ma ace

_tana munafunta‘ta idan ta fita unguwan , ba

yaddahban 'yi da ita ba akan na saya matamota

'ta dinga .amfani da ita idan za ta jewani

wajenba, amma fir taqi Yarda; saboda ita ba

mace ce mai burin samim abin duniya ba Babu

abin da zai sa na zarge ta, tunda ban

taBa samunm da’ wani. laifi Makamancinsa ba,

kai ita k0 kawaye ba ta da‘ su kema Fanne ban

zaxgeki ba da .kike'da Kawaye masu mummunar

akida balle ita

'Rukayya bane shi ya sa kiké’fad'ar abinda

kikaga dama a kanta". Sai da Abbakar ya saurara

na wasu yan mintina kamin nan ya ci gaba da

cewa; “Munanam halayarki da kike gwada min

Fanne su ne suka kai ni ga sha’awar qara aura,

wanda ni ba tsarina .ba ne ajiye mace fiye da

daya a ' qarkashinaba Fanne ba kya ganin

darajata da mutumcina a matsayina na mijinki,

magana: da kike furta min na tabbata k0 kawarki

ba kya yi 'mata. irinsu, kuma sanin halinki da na

yi shi ne yasa nai aura ba tare da saninkiba

saboda’ na sani ' sarai idan na gaya miki ,a

lokacin‘ba amincewa za ki yi ba, wanda ni kuma

a sannan din na matsu kwarai don son nayi auren

don bana Samun nutsuwa a wajenki. Bai kamata

ki dinga jin haushinaba don wai na yi .aure, za

karki abun da, nayi don kece, kika yankan min

tikiti tare da ba ni lasisi na yin aura, n_ *.Tunda

muke da keban taBa sanin dadin aureba a

‘kullumr shan wuyarsa nake wanda mutane da

dama suke daukata akan ban san mene ne

rayuwa‘ba, wasu k'uma suke ganin cewa, asiri

kikayimin shi ya sa ki ke :cin ’karenki' babu '

babbaka, 'dukda nasan da haka baisa na

wulaqantakiba k0 cimiki fuska ba,

Mu hadu gobe da safe idan allah mai kowa mai

komai ya kaimu domin jin ci gaban lbrn

Naku har kullun

red a profile .

Uwar. Goyo

Chapter15

Fanne da na dade da cutar da ke, tunda a

karRashin ikona kikce kuma da yawa daga cikin

Kawayenki wanda kika dauke su aminnai ba ki da

kamarsu, duk wani sirri naki kin d'ebe kin gaya

musu, su ne kuma masu zuwa wajena suna kawo

min tallar kansu ‘kan na auresu, amma na Ki

yarda da‘tayin nasu don idan na yi haka ban

kyauta ba, kuma kamar na‘tozarcine , duk da

cewa na sani Allah bai haramta min su ba, s'ai

dai ana barin halak k0 don kunya. ~ ‘ ‘ . Saboda

haka nake so ki gane, na yi aure ne ba don na

wulakantaki‘ba, kuma Allah ya ga abin da‘ na

kudurta acikin zuciyata, Fanne ke dafa kanki kin

San cewa ba kya-kyautata min, kuma ba ki dauke

ni a bakin komai ba. ba ni da qima balle daraja a

idonki, duk wata kalma da za‘ki furta min. da

bakinki mummunace, a tun Sanda Allah ya nfemu

da yin aure zuwa yanzu da nake yi miki' wannan

maganar'ba zan iya cewa‘ga rana daya wadda ki

'ka taba yi min ladabi da biyayya ,a rayuwarki ba.

Ba kya‘yarda da abin da nake gaya " miki,

sannan ba kya bin umarnina, unguwa idan za kije

ba kya tambayata, haka kawai'kike fita sai ka Ce

zaman kanki kike yi, duk wani abu da mace ta, ke

yi wa miji domin ta 'samu karbuwa a wajensa ba'

kyamin amman ban taBa nuna miki damuwataba

a" kai ba, hasalima a k0 da yaushe na zamanto

mai haquri da juriya a. kan abin da‘ kike yi min,

kuma k0 dasau d‘aya ne ban taBa tunanin na kai

Kararki wajen mahaifinki ba, k0 kuma na yi

tunanin ' rabuwa da ke bacin kuma ina da 'ikon

sakin‘naki‘ babu kuma wanda ya isa ya tsare ni

da tambaya a kan me ya sana sake ki,~ k0 kuma

ya sa ni na dawo dake

Ki sani Fanne bafa kudi ake biyana domin

nazauna da ke'ba, haka kum‘a .ba ni da wani buri

da zancim' masa Wanda shi ne makasudin

zaman da nake dakein nai hakuri na jure duk

wani' -wulaka.nci da .kike min, "saboda nasihar

da mahaifmki yake yi’ min, kullun da kuma

amanar da mahaifiyarki ta ba ni, don ko a lahira

mutum ya kan ci albarkacin dan uwansa, balle a

nan duniyda

Ba yabon kai ba, duk wani hakki naki da ya

rataya‘a‘ w'uyana ina kokari‘ na sauke, kuma ina

,binki a yadda kike so, ba don kOmai ba sai' don

mu zauna lafiya ba wai tsoronki nakeji 'ba, kamar

' yadda kike zato har kina tunkaho da hakan a

cikin Rawayenki, ba haka abin yake ‘ba;.abubuwa

guda biyun nan da na lissafo a baya su ne suka

saka nake daga miki qafa ki.yi duk abin da ranki

yake: so, ina kallonki ba tare da nace dake komai

ba, amma. ba tsoronki ‘nake ji ba, domin kuwa

bana

samun qaruwa k0 kad'an a tattare da zaman da

nakeyi da ke‘, kuma ba ke ce kike daukar

dawainiyataba balle ace don haka ne ya zame

min dole sai mun zauna ba.

Rukayya kuma da kike tunanin cewa tana cikin

wutan jahannama, insha Allahu makomarta mai

kyau ce :a wajen Alllah' (S.W.T) dan'ni ta

Bangarena ba ta da wata matsala, saboda mace

ce ta gari. Da ace za ki yi dace Allah ya

mikibaiwa da rabon kaso daga cikin kashi dari na

halayyarta mai kyau, da wallah kin, ci ribar

zamanki na du'niya. Kai harma da lahira, a yadda

na. fahimci Wannan zama'n namu samun mace

kamar Rukayya sai an yi bincike sosai, domin

tunda muke' da ita b’a ta taba Batamin rai‘ba,‘

‘shi ya sa nake yin kukan rashinta'a tare dani

,'ko sau daya Rukayyah bata taBa daga murya

sama da tawa ba, duk abin da zata ce dani a

cikin lumana da kwanciyar hankali ta keyi min

magana, sannan kuma bata so ta ga raina ya

Baci, don ,haka nema sam ba ta yi min abin da

raina ba ya so duk wani abu da ta san cewa

banasonsa, tana gudun aikata shi k0 dakuwa ace

itan tana da muradin abin. ' , '

Kullum abin da raina yakeso ta keyimin, ga haquri

da sanin ya kamata, kuma ga fara’a tunda muke

da ita ban taBa ganin fuskarta a d'auke da

fushiba kai, a maimakon ta dau fushi da zafin

zuciya ta hau ka'ma da masifa irin yadda kike'yi,

zaunar da mi ta ke yi ta gaya min lafin' da na yi

mata cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ya

ji kanmu ba, duk kuskuren da nayi ita ke nuna

min hakan ba daidai ba ne. ‘ - '

Sannan kuma ba sai na nemi da ta yafe min

laifukan da na ,yi mata ba ta ke yafe min,

Rukayya ta kan yi min uzuri ' idan har na yi mata

ba daidai ba, don sai nayi mata laifuka

masu‘yawa‘sannan ta ke sanar' da ni. Ba irin

yadda ba ta yi da ni ba a kan na sanar da‘ke

gaskiyar abin dake faruwa a tsakaninmu, amma-

naqi saboda gudun masifarki.

, .Ni Abbakar ko da ma a ce akwai wani laifin da

Rukayya ta yi min wanda‘ ban sani ba, na yafe

mata duhiya da lahira‘. Haqiqa na sani ruky ta

rasu ne a daidai lokacin da nake tsaka da

begenta tare da kwadayin zama da i‘ta, amman

Ubangiji’n daya halicceta

,ya karbi abinsa banda haka da , inaga babu wani

mahalukin da ya isa ya. raba ni da ita,_a‘ dalilin

halayenta 'kyawawa nake mata fatan shiga cikin

gidan aljanna, domin kuWa ni ne kad‘ai na rage

mata wanda zan yafe mata abin da ta yi min,

Allah ya ‘ jikanta da rahamarsa, kasancewana

marainiya gaba da baya mahaifinta ya rasu tun

tana

:cikin mahaifiyarta haka nan mahaifiyartama ta a

lokacin haihuwarya , shi yama wani lokacin nake

jin tausayinta don bata dandana dad'm mahaifa

aa.

Allah Ubangiji ya jikanki Rukayya tare da yi miki

rahama, ya kuma albarkaci abin da kika bari a

doron qasa, ya kare ta daga sharrin mahassada”.

Yana kawowa nan a maganama saiya runtse

idnnunsa tare da cizon leben bakinsa da

hakoransa, wannan alama ce da take nuna hr:

cikin zuciya'yana jin ciwon rabuwa da matarsa.

Wasu hawaye masu dumi suka shiga yi masa

zarya a kan kuncinsa, haqiqa ya yi rashi babba

wanda ba zai taBa mantawa da shi ba, har'izuwa

qarshen rayuwarsa, hakanan kuma da ace Allah

zai bashi lafiya ya dawo kaman yadda ya ke bai

yi tsammanin zai sake samun mace mai irin.

halin Rukayya ba, sai dai ko wata rahama ta

ubangiji mai kowa mai komai, don balalle nema

ya samunba shiyasa a kullum yake addu’ar Allah

ya jiqansa Ya dube shi da fuskar rahma Ya azurta

shi da mace waddn za ta iya riqe masa Khadija,

don yasan da qyar ne Hajiya Fanne in zata iya

rike masa amanar ma'rainiyar ‘yarsa, kai k0 za ta

rike ma ba zai so a ce Khndijan a hannunta ta

tashi ba, dom'm a kullum burin Rukayya Allah ya

taimake ta, Ya

kuma ba ta. ikon, ba wa Khadija tarbiyya irin ta

addinin musulunci, to ta ya ya ma Za ace ya

dauki , Khadija ya ba wa Fanne ta riqe ta bacin

kuma nata’ data tsugunna ta haifa ma ba ta

zauna ta ba ta‘ ‘ tarbiyyar tar da ita ba, kai ita

ma Fanne yaushe' tarbiyyar ta. wadacetaballe a

Ce zataba wa wani? K0 ta Wannan wajen ma. ya

sanda‘ cewa ya yi‘ rashin Rukayya, haqiqa ta riga

ta Zama wani Bangare babba na rayuwarsa. _ , '

' Rashinta a rayuwarsa giBi ‘ne babba wanda ‘

bashi da tabbacin ga ranar day zai ciko, haka

kum ; ya sani ba zai dain'a tunawa ita ba, har

iya kwanakin da suka rage masa wanda zaiyi a

duniya Sam ba yajin ciwon, raunikan' da_ ~suke

a‘ jikinsa, kamar yadda yake jinzafin mutuwar

matar. da ba don Allah ya _ sanya shi mutum' ne

mai ’taWakkali da kuma yarda da qaddara‘ ba, da

bai san wane hali‘ zai shiga ba; kuma dadin abin

Allah ya bashi mahaifiya mai kaifin basira gata da

hangen 'negsa, a duk sanda ta zo duba‘s'hi sai

ta‘ sake, .yi- masanasiha a kan ya yi‘ hakuri ya

fauwala' wa _ AlIah‘ lamarin. su ma qannensa

da‘ Suke Wajensa, ba su-da hira sai na

rarrashinsa da ba'shi magana masu dadi, don

haka ne ma yake samun ’ sassaucin kuncin ‘da

zuciyarsa takeyi‘, kuma ko- ganinsa suka'. yiya

zauna shiru yana kallon sama

yana tunani to sai sunsan hanyar da sukabi suka

dauke masa- hankali daga barin tunanin da yake

yi, saboda ba sa son ya fada wani hali, kuma ,da

ma likita ya kafa masa doka a kan yawan tunani,

don ‘jininsa ya hau da yawa, tun a sanda ya ke

asibiti a kwance, shi ya sa ,ma Kannensa suke

'yawaita karanta masa -qur’ani a kusa da shi,

domin ‘ shi qur’ani waraka ne ga dukkan cuta da

ta ke damun mutum, yawan karatun dasuke yi

masa ya yi matuqar tasiri a rayuwarsa, domin

kuwa da'ga cikin abin da yake damunsa a

cikin'zuciyarsa da dama ya samu sauqinSu. ' ‘ '

Kuma bai cika damun kansa da tunani ba, duk da

cewa abu ne mawuyaci ya sake mikewa da

Kafafunsa 'ya yi tafiya, saboda tsananin ciWon da

zogi' da. suke yi 'masa, Wanda tunda yake ‘a~

rayuwarsa bai taBa jin irinsu ba. To gwara :ace

ya rasa komai na rayuwa a kan ya rasa RuKayya,

duk Wani abu da'yake ji a yanzu mai sauqi ne a

kan rashin nata, ina ma ana mutuwa a daWO,

kokuma wani yan'a fansar ran d'an uWansa, sai

dai kash! Hakan ba zai taBa faruwa ba, wanda ya

mutu bashi dawowa gidan duniya

mutuwa ta riga ta raba su, Shi ita kuma sai

a~lahira idan Allah yasa da rabon za su gana."

Ya Ubangijin daya halicci sammai‘ da qassai, ina

roRonka da ka had‘a fuskokinmu cik'm gidan

aljannah, amin”. ~ ’ r ‘

A Iokacin da Abbakar ya yi nisa a cikin tunanjnsa,

ita. kuma Fanne , tana tsaye qikam a kansa

kamar wata gunki, tabudee baki glalala tana

mamakin Abbaka: tare da alajabin maganganun

da suke fitoWa daga bakinsa', wanda-ta'ke jinsu

kamar saukar aradu a cikin zuciyarta , tunda take

bata taba. tunanin jin makamancin wadannan

kalaman daga bakinsa ba, 'domin a yad'da ya ke

wanda ba ya son hayaniya ko ‘rigi‘ma; ta d'auka

maganar ce bai iya, ba shi ya.‘ sa ba ya biye

mata su yi inta nemeshi 'da. wata magana ashe

da ma haka ,mutum matum mara magana ya ke’?

Ita kuwa taya akai tayi saken da Abbakar

ya‘dainajin shakkarta tareda tsorontane ,‘wanda

in da da ne k0 giyar wake ya ke sha ba zai taBa

tunkaranta da irin wannan kalaman nasa

masu‘ciWO ba, babu kuma k0 dar 'a cikin abin da

yake fadan, lallai ya zame mata dole ta tashi

tsaye domin cimnm burinta Wanda ta dade tana

yi, don a yanzu k0 Abbakar yamutu ba ita da

Momi ne kadai zasuci gadonsa ba,

tunda naji ya kira sunan wata tsinanniyar yarinya

wai ita khadija lallai dolene nasan abinyi wajen

ganin na kauda yarinyar daga doron qasa kodon

samun cimma burin nawa cikin sauqi lol

mu hadu anjima saidai yau it lukz like i, m so

busy amman idan na kammala komai in time

zanci gaba karku damu ku kasance tare damu

akoda yaushe

a profile .

Uwar. Goyo

Chapter16

Kai daga dukkan alamu asirin da take yi Wa

Abbakar din ya daina tasiri a jikinsa; tunda ga shi

nan ya nuna mata a zahiti ita a haukarta ta

d'auka ta riga ta gama da shi, wanda ba zai iya

wani kataBus ba, saboda asiran da take sawa

bokayenta suke aika masa‘ da shi, ashe abinha

bahakaban'e, domin ta manta da cewa ta

kashe’maciji ne bata ta sare masa kaiba, saboda

haka tana da aiki ja a gabanta wanda Sai tasha

damara tare da zage damtse da'kuma bud'e

bakin aljihunta‘ a wadanda suke yi mata aiki, don

kawai ganin ta mallaki Abbakar tare da duk, wani

abu da ya mallaka a duniya.

“Domin ni da ‘yata kad'ai nakeso mu gaje

dukiyarsa, tunda da ni aka sha wahalar néma, na

yi haqurin zama da Shi cikin baKin talauci, Wani

irin wahala ne ban shaba. a lokacin da bashi da

komai? K0 da_ takaicin yawan gidajen haya da

muka yi aka bar ni kadai ya? aishe ni, balle' a je

ga ‘batun sauran wahalhalun gida da nasha tun

daga farkon aurenmu har ixuwa lokacin da yayi

kudi”.kuma sai da dadi yaxone za, ace da Wata

za su ci‘ Ina ba zai ba, zai taba yiyuwaba dolene

nai duk wani abu da nasan zai taimakamin wajen

mallakar dukiyar yasa amman bazai taBa

saBuwa ba bindjga a ruwa, kura da shan bugu

gardi kuma da kwace kudi. ' ‘ . _ Zuwa da

Dashiya ya kamata; tayi domin’ ita- kadai ce za

ta iya magance mata wannan matsalar da ta

kunno mata kai, tunda ga shi nan Abbakar ya

furta mata da bakinsa. cewa, akwai‘ qawayentar

‘wanda suke kawo m'asa h'ari, _~wannan ma ‘

wani sabon‘tashin hankali ne a gareta, doinin

kuwa ta sani sarai akwai da yawa daga cikin

qawayenta ‘ wanda suka fita masifa kai hata da

bin bokayen ma, dama ace Abbakar din zai yarda

ne ya gaya mata sunan qawayen nata da suke

zuwa wajen nasa da duk abin zai zo mata da

sauki; sai dai tasan cewa‘ ba zai taBa gaya

mataba, ko da kuwa~ za ta kwana, tana masa

magiya a kai, don shi mutum ne mai zurtin ciki, in

har kaga ya furta‘a'bu, to abu ne mai girma,

kuma mai muhimmanci. -. . * “Fanne tayi nisa

cik"n zancen zuciyan sai ta tsinkayi muryar

Abbakax yana cewa da ita. ._“Ina so ki nutsu ki

yi tunani cikin kwanciyar ~. hankali, za ki gane

cewa wannan abu da ya faru dani akwai darussan

da zaki dauka a ciki masu yawan gaske; a nawa

tunanin wannan jarrabawace da Allah ya dora min

ya ishe ki ishara a iya rayuwarki, don‘daga nan

za ki gane mutum ba a

bakin komai yakeba, haka kuma ita rayuwar

duniya tana da iyaka, duk lokacin da ajali ya zo

wa mutum ba a jinkirta masa ko da kuwa na

sakan daya ne, saboda haka ya zama dole

mutum ya tashi tsaye wajen neman lahirarsa,

ayyukan da mutum zai yi ya shiga aljanna suna

da wuya tare da sauqi, don manzon Allah (S.A.W)

ya ce, ‘kayan Allah yana da tsada, wato shine

aljannah

Ni ina da yakinin cewa, wannan'abu da ya same

ni Allah ubaagijin da ya halicce ni ne yake so ya

jarraba imanina, ba wai kamar yadda 'kike nufi ba

ne, Wanda kike ikirarin sakayya ne Allah ya miki

a kan abubuwanda nake miki na cutarwa, wanda

kuma ba haka ba ne. Bazan kuma taBa _ cewa

haka ba, donin ni na yarda da 'Raddara mai kyau

k0 marar kyau, saboda haka ne a kullu'm kwanan

duniya nake godiya ga Allah da ya halicceni a

cikin jinsin mutane kuma ya saka zan fito a cikin

bayinSa musulmai wanda suke cikin al’ummar

AnnabinSa Muhammad (S.A.W), da yawa daga

cikin Ann'abawa suna cewa, ina ma a cikin

al’ummar Annabi Muhammad (S.A.W) aka halicce

su, domin’ irin gatan da Allah ya yi wa al’ummar

tasa . Ina neman sauqin halin da nake

ciki awajcn Allah, domin na sani Shi kad‘ai nc zai

. iya ya‘yc min wannan laluxar da ta kc damuna:

Wanda da'ma shi ne Ya dora min ba wani abi;n

halitta ba, don ba a so bawa yana cutar da’rai

daga rahama‘: Ubangijinsa, in kuma ma ya bar ni

a haka har izuwa Rarshen rayuwata ya zame min

dole na yi masa godjya, saboda ina tunanin

barina a hakan ma wata ni’ima ce ta Ubangiji, sai

dai ina fatan Allah ya sa ya zamanto kaffara ne

ga dumbln Zunuban da na aikata a rayuwata,

inasoki bade kunnuwanki da kyau ki ji abin da

zan gaya miki, duk da cewa kina ' ganin na

zamanto musaki, nakasasshe wanda bani da ikon‘

taimakon kaina kamar yadda kike'furta, wa insha

Allahu da yardar 'Ubangijin‘ musulunci ba zan yi

bars a bakin titi ba, Allah daya dora min shi ne

ya. san kuma hanya: da zai bullomin da ita na

dinga cin abinci, domin bakin da Allah ya tsaga

ba ya hana shi abin 'da zai ci, kuma idan barewa

tana ciwon ciki a jeji Allah da ya halicce ta shi ya

ke ba ta magani. allah shi ne kad'ai ya kejin

karatun kurma, sannan kuma abu na gaba da

nake so ki 'sani shi ne, Khadija za ta dawo nan

gidan da zama don a halin yanxuu ita kadai nake

gani wanda ta ke" d'ebe min kewar marigayiya- a

anan ne ya kamata ta zauna, tunda ni kad'ai na

rage mata,- ni ne .kuma ya cancanci na ba ta

tarbiyya da kaina, ’domin Shine babban burin

mahaifiyarta

ina ga zatafi samun kwanciyar hankalu ' da

nutssuwar zuciy'a idan tana tare da ni lnsha Allah

idan Allah ya ara min rai har zuwa lokacin da za

ta girma na yi mata aure ba zata taBa yin kukan

rashin uwa ba, don zan zame mata‘uwa da uba a

dukkan abin da zatayi

A yau Fanne ina so na rake ki wata alfarma,

wadda nake fata za ki yi qokari ki yi min ita, ga

Khadija nan na baki amanarta, ina so ki sa hannu

biyu ki amshe ta, ki rike min ita tamkar ‘yar da

kika haifa a cikinki, domin kuwa da ita da ,Momi

duk abu daya ne ya- Yi sanadin zuwansu duniya,

don Allah ko don wannan dangantak'ar da take '

ts‘akaninsu da Momi nake rokonki da kar kicutar‘

da ita, k0 kuma ki dinga nuna mata bambanci a,

tsakaninsu, wanda yin ‘hakan zai iya kawo

rabuwar kansu ita da ‘yar uwarla, Allah ne kadai

Zai sakamiki idanhar kika daure zuciyarki kika yi

min wannan alfarmar,‘ tunda kin ga Khadija '

marainiya cce kuma yarinya ce qarama wadda

bata san inda yakeyi mata ciwo ba. , duk abin da

' kike so na daga cikin dukiyata zan ba matuqar

kika yi min Wannan alfarnar da .na nema a

waienki

.‘shiru neya biyo baya na d'an wani lokaci a

dakin, kowa a cikinsu yaha nasa tunanin tare da

neman mafita a lamarin, shi Abbakar ya yi‘ wa

Fanne haka ne domin ba ya son idan an kawo '

Khadija gidan su dinga takura wa rayuwarta tare

da tsangwamarta, don yana ji a jikinsa‘ ba zai iya

rabuwa da ita ba, saboda haka ne ma ya ce da

Ummansa ta yi hakuri a lokacin da ta ke cewa da

shi, ita ce ya kamata ta dauki Khadija don ta ci

gaba' da zama a wuri'nta, haka nan Kakar

Rukayya ma ta nemi wannan alfarmar a

wajensa,.ita’din ma hakuri ya ba ta, don ba zai

iya ba su Khadija ba, sai dai ida'n da shi duka za

su had‘a su dauke.

Duk da cewa hatsari ne babba a rayuwar yarinyar

zamanta tare da Fanne, amma zamanta a kusa

da shi ‘ya fiye masa komai najin, dadin rayuwa,

shi yasama yaima fannen hannunka mai sanda

don y'a santa a kan kudi za ta iya yin komai

saboda tana amsifar son ta tara dukiya , shi a

nasa. tunanin idan ya ce da' ita haka' za ta

rangwantawa Khadija wani abin,‘ k0 duka

dukiyarsa fanne tace tana so zai iya mallaka

mata muddin ba za ta dinga takura wa

marai'niyar ‘yarsa 'ba,

don so yake ta zauna gidan ubanta ubansa cikin

walwala da sakewa tare da jin dadin rayuwa mai

doréwa;

Wannan tunani na Abbakar da shin'eya tafka

babban kuskure a rayuwarsa.

Fanne ‘kuma da ta yi shiru ‘farin ’ciki ne ya

mamaye mata zuciya, saboda gam'n cewa

bunrinta ya kusa cika, sannan za ta samu abin

da ranta keso cikin sauqi ba,tare data sha wahala

ba, k0 kuma ta daga jijiyoy'm wuya ba, kuma k0

sulenta ba zata kai wa boka ba. Wannan shi ake

cewa, tsuntsu daga sama gasaSshe, _da ma ance

'tsuntsu mai- wayo ta wuya ake kama shi,

wannan shegiyar yarinyar da ita ce zan dana. wa

Abbakar tarko har ya shigo hannuna, inyaso k0

ma mene ne zai faru ya faru' tun’da na cinma

burina, kwanton Bauna zan yi wa abbakar na

nuna masa cewa na- yardada bayanansa, duk

wasu sharuda da zai kafa min a kan shegiyar

“yarsa yarda zan yi, amma kuma da zarar

kwalliya ta biya kud'm sabulu ‘shi kenan sai na yi

watsi da su, .dan ta"r'iga ta samu abin da ranta

yakeso,‘wa.nda ta ’dauki‘ tsawon lokaci tana

neman hanyar da‘zatabi don ta mallake shi, sai

ga shi yau cikin ruwan sanyi Allah ya tarfawa

gayanta nono ta same shi.

Idan har ta bijire masa daga baya iyakacin

hukuncin da zai 'yi mata shi ne saki, to kuwa

idan ya yi hakan tafi nono fari a wajenta, don ba

shi da

Wani amfani a wajenta' a: lokacin domin tanada

hatimin nasara a hannunta masu huce lakaicin

duniya, don haka ne ta ke ganin za ta iya duk

abin da ranta keso, kuma duk mai son zama da

ita ya zama dole ya yarda da abinda ta keso, ya

kuma yi mata biyayya a kan hakan. ‘

Allah sarkindadi, in ji Barawon'takanda, dama

ance komai da sanadinsa, wato da ma sanadin

arziqina kenan, ashema‘ gwara da suka. hadu u

da su a shagon na alfijir, kai rabo sai mai shi. Da

fa ha: ta kl tablyc wa Momi, sai da ta Sakata a

gabada rigima sannan (a yarda, ashe ita arziqi ne

yake kiranta, Allah neya taimake ta da ta tafka

uban asara, wadda ba ta taba yin irinta ba a

rayuwarta.

“Allah na g'ode maka da ma an ce dare daya'

Allah kanyi bature”

‘ Fanne tana zuwa daidai nan a tunaninta,’sai ta

sakarma abbakar din wani murmunin mugunta

gamida samun waje ta za‘una a kusa da shi, ta

kuma fuskanceshi cikin fara’a da yaIWar lfuska

irin na makirci, sannan ta ce da shi.. .

“Na ji dukkan bayananka, kuma na gamsu da 'su,

da 'ma abin' da ya sa ka ga ina yi maka hankoro

a kanka, rashin sanin gaskiyar al’amarinnce‘

kuma duk wata mace mai hankali takan yi kishin,

mijinta idan ta ganshi da'watamacce shi yasa

amma yanzu da ka wayarmin da kai na gane

cewa ba karuwa ba ceita, sai dai kuma mene ne

dalilinka na Boye min kana da auré tsabar, sOnka

da nake yi Abbakar shine ya sa ka ga ina

tsananin kishinka”. -

. Wannan magana da Fanne ta 'farta ta matukar

ba wa Abbakar-mamaki, wanda har sai daya

dago ido ya kalle ta, sai kuma aka yi sa’a ita ma

shi din ta ke kallo, don haka ta sakar masa da

wani yalwataccen murmushi mai sace'zuciyar

wanda aka yi mawawa, habawa Abbakar yana

ganin haka sai yake zaton cewa ko dai mafarki

yake yi ne, saboda tunda suke da. ita ba ta taBa

yi masa in'n wannan murmushin ba.

“Abbakar na yarda ka dauko Khadija ta

zauna'tare da mu, kuma zan riqe ta kamar yadda

na ke rike da Momi, sannan kuma ba sai ka ba ni

.wani abu daga dukiyarka ba, zan rike ta ne

tsakaninada Allah, , saboda ba ka san wanda za

ka mom ba, kuma k0 b'a komai jininsu daya da

‘yatane ka ga kuwa nima‘mun hadu da ita ta

Bangaren haifayya, kuma ba fata ba

' k0 rabuwa muka yi ni dakaji .ai su 'suna tare

tunda

mahajfmsu daya. A halin da ake ciki yanzu

addu’a kawai nake so ka taya ni da ita a kan'

Allah ya ba' ni ikon rikesu da kuma yi musu

tarbiyya' mai kYau,

kai kuma Allah ya baka lafiya tare da ba ka ikon

daukar nauyinmu gaba daya”. ‘ Kai duniya, abin

al’ajabi ba ya qarewa Abbakar bai gama dawowa

daga inda ya tafiba‘na mamakin abin da Fanne ta

yi masa ba, sai kuma ga wasu kalamai masu

taushi da laushi tare da dadinji da ta sake yi

masa. ' Allah gwani a kan kayanSa, kuma sai ya

bar mutum zai saba maSa. ‘Abbakar yana cikin

tunani sai ga qaninsa wanda ya ce' da fanne ba

za su fita ba, ya shigo cikin dakin yana ta

muzurali Fanne tana ganin haka ta mike tsaye ta

ce da Abbakar. “Ni zan koma mu love me kakeso

yau na dafa maka?” ‘ ' Zuwa yanzu abin na

Fanne ya daina ba wa Abbakar mamaki, dOn haka

ya ce da ita. ' “Duk abin da kika dafa min. mai

dadi zanci

“To shi kenan, sai anjima”. Tana fadar haka ta

kama hanya ta yi tabar dakin, ta bar Abbakar da

sake-saken zuciya tare da jin dadin ganin Allah

ya ba shi sa’a a kan Fanne ta fahimce shi cikin

ruwan sanyi ba tare da sun kai ruwa rana ba,

ashe da ma Fanne zata "zamanto mutuniyar

kirki? Lallai rahamar Ubangiji tanada yawa a kan

bayinsa, tunda yake bai taBa tunanin zai iya

shawo kan fanne cikin ruwan sanyi ba

dangane da riqe Khadija ' amana, a wajentaba da

‘ a tunaninsa ma ba za ta yarda da dawowar

Khadija gidan ba balle aje ga batun ta rike ta

amana. Allah ne ya dubi zuciyat'sa tare da

maraicin da yarinyar take ciki ya amshi addu’ar

sa. Godiya ya shiga jera 'wa Ubangiji ba iyaka

tare dayi masa kirari da sanayenSatsarkaka,

kuma yana me addu’a a kan Allah ’ ya'sa Fanne .

ta dore da wannan kyakkyawan hali da ta bijiro

da shi. Allah kuma ya musu tsari daga

mahassada masu saka ido a kan ’ abin dabai

shafe su ba‘," Ya kuma dora shi a kan qawayen

Fanne ya samu nasara a kansu 'kamar yadda ya.

samu ta bangarenta , domin ya sani da

shawararsu ta ke amfani, duk abin da suka ce da

ita ta aikata shi take yi; musammgn ma Dashiya

wadda Fanne ta dauke ta kamar ita ceta

tsugunna ' ta haife ta, k0 maganarmahaifinta ba

ta ji idan ya gaya mata, sai na Dashiya

, Wannan shi ne ake cewa an rufe qofa da

barawo, domin shi Abbakar har cikin zuciyarsa ya

gama yarda a kan cewa, Fanne da gaske ta ke yi

da amanar daya ba ta, abin da bai sani ba rufa-

rufa ta yi masa, duk maganganun data gaya

masa a iya fatar bakinta ta tsaya baikai ko

makogoronta ba balle yakaiga qarasawa

zuciyarta

Hmmm mudai yan kallone allah e bama mai rabo

sa, a

WACECE RUQAYYAH ????? OHO NIMA BAN

SANIBA

MU HADU A NEXT CHAPTER DONJIN ko wacece

ita da kuma YADDAH ZATACI GABA DA KAYAWA

TSAKANIN FANNE DA HAJ ABBAKAR SARKIN YAN

HAQURI

naku har kullun

Uwar goyo

Chapter17

WACE CE RUKAYYA?

Malam Inusa wani manomi ne wanda ya shahara

a harkar ta noma, mutane da dama sun sanshi ne

ta dalilin noman da yake yi. Yana da mata guda

daya mai suna Dije wadda aka yi musu aure tun

sun: saurayi' da budurwa har suka fara

manyanta,sun dau tsawon lokaci a tare amma

Allah bal nufe su da samun haihuwa ba duk da

haka suna zaune lafiya da juna'zaman 'rufin asiri

babu mal jin kansu. ‘Yan uwan Malam Inusa sun

dame shi a kan ya qara aurr k0 Allah zai sa ya

ga jininsa a duniya, amma sam yaqi karBar

shawararsu, domin shi a nasa tunanin Allah ne

mai bayarwa, kuma mai hanawa dunia idan kama

raye‘ baka core rai daga samun axziki ko wanne

A haka hat suka gaji suka daina yi masa

maganar. A Bangaren Dije ma ta kan ce da shi. .

'

“Malam ka yarda da zancen yan uwanka wata

kiln rabonka na haihuwa a jikin wata yake ba ni

ba".

ldan ta‘gaya masa haka shiru yakeyi'ba tare

dayace da ita’komai ba. '

Malam Inusa mutum ne masanin addini, ya yi

zurfin karatu sOsai a cikin islama, d0n haka ya ke

yawaita addu’a a kan Allah ya azurta shi da

zuri’a dayyaba wanda za su iya ba su tarbiyyaglh

ta gari; idan kuma rashin haihuwar tasu ita

:ce‘mafi alheri a rayuwarsu Allah Ubangiji‘ ya ba

‘su ikon yin haquri.dadangana

- Kwatsam wata shekara sai 'Allah ya nufi Dije-

da samun ciki, sun matuqar farin *ciki da yin-

godiy‘ ga Allah da ya ba su kyautar da kudi ba ta

iya‘sayenta, tun daga lokacin suka shiga tattali'

da nuna kulawa abin da' yake cikin Dije, kuma

malam' Inusa ‘ya shiga tanadin abin da zai

yi'hidiman suna dashi idan Allah ya sauki matar

tasa lafiya. .

Cikin Dije yana da watanni takwas Allah ya dauki

rayuwar mijinta Malam Inusa,'lafiya qalau suka

kwanta, can cikin dare ya tashi da wani

matsanancin ciWon ciki wanda kafin a kira sallah

har rai'ya yi'halinsa. Dije ta shiga

mawuyacin’hali, Wanda har ya kai ta ga

kwanciya rashin lafiya tai sbd rashin mijin nata

har cikin cikinta ya shiga watan haihuwarsa ba ta

yi lafiya‘ba. .Ta sha Wuya 'sosai a sanda nakuda

ta kamata, don duk ta fita hayyacinta, sai wani

abu ta keyi irin na masu ~borin haihuwa ana

shirin kai ta asibiti Allah cikin ikonsa ya kawo

mata sauki ta haifi ‘yarta mace kyakkyawa da ita,

Katuwa fara sol.

An gama shirya yarinyar cikin kaya irin na jarirai,

jikin Dije ya sake dawowa, a wannan karoh abin

ya yi' muni sosai sai suma ta ke yi ana zuba

mata ruwa, ba .ta dau'tsawon lokaci ba ita ma ta

ce ga garinku. Allah ‘mai ‘ yadda yaso, 4‘ haka

aka shiryata itama aka je' aka binne ta. Ga kuma

yar jaririyatta nan da ranta, sati guda aka dauka

ana zaman makoki kafin nan kowa ya watse. A

rananne kuma aka rada wa jinjira suna Ruqayya,

wanda da ma'tun mahaifinta nada rai yace da

Dije idan ta haifi ya mace Rukayya yake so a sa

mata, idan kuma namiji ne Muhammad.

Rikon yarinyar .ya koma hannun kakarta ta wajen

uwa, wanda da ma ita ma ‘ya guda' daya Allah

ya nufe ta da haihuwa mai rai, duk sauran ‘yan

uwan Dije .da aka haifa babu rai suke zuwa, k0

kuma a haife. su da‘rai kafin suna su koma, shi

ya sa ma wasu suke cewa da Dijen Ajuji.

Madara aka dinga ba wa Rukayya har Allah ya sa

ta rayu, hakika yarinyar ta taso cikin kulawa da

tsabta tare da tarbiyya mai kyau duk da cewa a

gaban .Kakarta take hakan bai sa ta tashi

sangartacciya marar jin magana ba. allah’ ya

horewa Rukayya kyau na baiwa kwatance, da ma

duka

mahaifanta kyaWaWa ne, fulani ne su. .Wata

baiwa da Allah ya yi wa Rukayya shi ne tanada

Kwakwalwar daukar karatu, don haka ta tashi

cikin hazaka, ba a sanya ta makarantar boko ba,

amma tana makarantar . islamiyya har biyu, tana

da matuqarr haKuri tun tana qarama, ga kuma

nutsuwa ‘bata cika yawan surutu ba, idan mutum

bai Santa. ba ma sai ya dauka kurma ce, saboda

ta kan dauki' tsawon lokaci ba ta bude baki ta yi

magana ba sai ka ce mai‘ ciwon baki» Haka'

Allah ya halicCeta, rashin .maganarta‘ nema yasa

bata da Kawaye, domin ba‘ta shiga ’shirgin kowa

k0” kuwa~a makaranta' ne, abin da ya kaita

kawai ta ke yi. ' " -

’ "‘Tunda ta ke a rayuwarta ba ta taBa fada da

kOWa ba,‘ “tun sanda .shekarunta suka ja ta

zamanto

budurwa'sai' samari suka yi mata' caaa, hatta

malamanta »‘Wanda Suke koya mata karatu Suna

sonta da aure, don babu wani namiji 'da zai dubi

Rukayya' kai. tsaye Ida baiji sonta ya shiga cikin

zuciyarSa’ba;- Saboda baiwa'r kyau 'da Allah ya

yi »

mata ta ko’ina ta hadu,~ akwai wani malami a

makarantarsu da yake matukar sonta, don da

alama 'duk yafi sauran fadawa ‘cikin kogin

begenta, amma‘ ita sam bata san ma yana yi ba.

Duk cikin'samarin da‘ su’ke zuwa' wajenta da

su‘nan suna sonta Habu‘ mutum daya dataji ya

kwanta mata' a rai,‘don haka,

nAN

yasa bata fita wajensu idan wani lokaci sai

kakarta ta yi ta mata surutu tukunna ta kan fita

ta saurare su, amma duk da haka bata wani

dadewa take koma wa gida.

Haka nan daga gaisuwa ba ta sake cewa dasu

komai, Wannan abin da Rukayya ta keyi yana

damin kakarta sosai, sai dai ta rasa ta inda za ta

Billo wa- lamarin domin k0 magana ta keyi mata

bata cewa da ita komai, harta gaji da sumbatunta

taja bakinta tayi shiru Da yawa daga, cikin

Samarin .da suke zUwa wajenta sun yi mata'

mummunan fassara, don gani suke yi tana

wulaqanta sune don tanada kyau, wanda kumapa

a Wajenta ba haka bane, 'kwata-kwata bata '

wulakanta su, kawai dai-har yanzu Allah. bai

kawo mata irin mijin da takeso take kuma burin

aure bane’ ita ba qyale-qyalen. duniya ta ke da

bukata ba, so take a ce Allah yabata mijin da zai

rike ta tsakani da Allah, kuma su yi zaman

amana da 'fahimtar juna. Wanda ta ke ganin

kuma kusan dukkanin wanda suke zuwa wajen

nata,duk kusan basusan inda yake musu ciwo ba ,

har gwarama malaminta za ta iya amence mass

su zauna tunda' Allah ya hore masa baiwar

karatu, amma kuma shi ma

tana ganin akwai cikas a cikin lamarinsa, don

haka

hakan yasa ta mika gaba daya lamarin nata a

wajen Allah a domin yayi .mata zaBi na gari. ‘

‘ . A wani yammacin ranar-juma’a ne Rukayya ta

“fitodaga gidansu zataje bakintititayiwa kakarta

cefanen kayan miya, a anan Abbakar ya ganta

nan take yaji ta caja masa kwakwalwa. a Cikin

lokaci qanqani ta kwanta masa‘ male-male a ,

cikin zuciyarsa, : tsayawa yayi_ yana kallonta

tana> tafiya cikin nutsuwa, ga kuma shiga ta

kamala da tayi. Sannu a hankali har ta karaso

inda yake, habawa tana zuwa kusa da inda yake

sai ya qara rikicewa, a dalilin kyau da Allah ya

hare mata

’ “Tsarki ya tabbata‘ ‘ga ~Ubangijin da ya “

halicci wannah kyakkyaWar budurwa”. Abbakar

ya"

fadi haka' a cikin zuciyarsa. — ‘ ' Har Ruliayya ta

Wuce 'inda‘ Abbakar yake tsaye bai sani ba,

saboda ya lula duniyar gajimare; tunda' yake a

rayuwarsa bai taBa jin son wata mace ya shiga

Zuciyarsa a cikin lokaci kanqani ba, Sai yau ~da

Allah ya nuna' masa

Rukayya. ‘ ' ‘ .

Fanne matar dayake aure ma suna zauge ne

zaman aure, amman babu soyayya a

tsakaninsu...

Dirin wani' mashin ne ya dawo da‘shi daga

duniyar tunanin da yake kai juyawa ya yi yana

waige-waige ko Allah zaisa ya .sake katari‘ ya

hango budurwar data sace masa zuciya,~amma

bai ganta ba Saboda haka ya sama waje_ ya

gyara tsayuwarsa yana zuba ido a. kan hanya k0.

Allah zaisa ya sake ganinta ta zowucewa. ' _ ";

Ya jima a tsaye . yana 'jiran‘ gawon Shau kamin

daga bisami ya hango. ta tana daWowa, da bar

ya ‘fara tunanin tafiya ganin lokaci yana‘ qurewa;

a 'sain da'yaganta ta dawo sai ya ji Wani farin

ciki - tare da saukw wata‘ ajiyar zuciya, nan da

nan ya saki fara’a zuciyérsa tai fari'_bai yi mata

maganaba a ' ‘lokacin da ta zo kusa dashi

saidaya Bari : hakan tayi‘ dan nisa data inda yake

tsaye, . ‘ sannan ya‘fara binta a baya har: zuwa

lokacin da ya ‘ gata_ shiga wani gida wani yaro

ya tambaya wanda yake wasa a 'qofar “gidan

yana “Don Allah kasan' wannan budurwar da' ta

shiga gidan? yace eh na santa, Rukayya "sunanta

kuma nan gidan data shiga shi ne gidansu”; ‘ __ _

,GOdiya Abbakar yayi ma yaron harda yi masa

kyautarkudi, yaron yai godia gamida soke abinSa

a cikihm‘aljihu, shi- 'kuma Abbakar ya juya yanufi

inda za shi, zuciyarsa cike da farin ciki _ da

murna sai ‘ka‘ce wanda aka'yi wa'babbar kyauta,

dama wajen wani abokinsa zai je a‘ can kasuwa

Uwar goyo

Chapter 18

Allah ya hadashi da ‘Rukayya. A sanda ya isa

wajen abokin nasa bayan sun gaisa tare da

tambayar juna wasu abubuwan da suka danganci

kasuwancinsu, sai suka shiga_ hira irin ta abokai,

Sun Ja tsaWon lokaci suna hira kai daga bisani

Abbakar ya bijiro masa da zancen Rukayya, tare

da tambayarsa k0 ya santa? Eh-na santa farin

sani ma, domin mamata gidan mahaifanta a

maqotan. gidansu yake. ‘ Nan dai ya kwashe duk

wani' abu da ya sani a game da Rukayya ya

sanar da Abbakar, shima ya Sanar da abokin

nasa abin da yake cikin zuciyarsa, ' da kuma

niyyar ,da yake da ita. akanta. ‘ ' . 'Haqiqa

‘Abbakax da ace Rukayya za ta amincc da

batunka da ka more, kuma qarshen wahalar da

matarka ta ke baka da ya20, ni a nawa Bangaren

na baka goyon baya a kan ka nemeta, domin bata

da wata matsala, insha' ‘Allahu idam abin ya

tabbala zakayi farin ciki sosai, kuma ' aurenta zai

zamo maka alheri. don yarinya ce mai nutsuwa"

tare da .ladabi da biyayya, a kaf fadin unguwar

Rukayya‘ ta doke sauran sa’anninta a tarbiyya,'

sai dai. kuma na ce dakai ka dage da addu’a‘,

‘domin kuwa. na samu labarin tana da manema'

da yawa; amma har yanzu bata fitar da

‘ .gWaniba, mutane suna yi mata zaton tana da

Wulaqanci ne, k0 kuma ruwan ido ne DA ita shi

yasa ta gagara tsaida zuciyarta waje daya ta

zaBi mutum daya a cikin dubban wadanda Suke

zuwa wajenta, amma ni. kuma , ban yarda da

Wannan batun bu, kawai dai Allah ne bai kawo

mata mijinba shi 'yasa har yanzu ba ta ce ga

wanda take soba”.

Dab da magriba Abbakar ya yi wa abokinsa

sallamar zai tafi amma ya ce dashi, nan ‘da sati

mai zuwa zai dawo domin ya raka shi wajen

RuRayya, insha Allahu. - .

Tsawon sati Abbakar ‘ya dauka yana, yin sallar

istahara don neman zaBin Allah a tsakaninsa da

Ruqayya kamar yadda manzon Allah (S.A.W) ya

koyar damu, ba Wai mutmn ya tashi ya taii .

wajen malami yana da buKata kaza a taimaka a

yi masa istihara a gano masa abin da yake alheri

a, ciki ba, wannan ba shi ba ne ,mafita, kai da

kanka za kayi abinka kuma ka bar wa Allah zaBi,

ba sai kaje wajen malami ka basu kudi ba. 1 .

' A tun lokacin da Abbakar ya fara yin sallar

istihara' kullum Kara son Ruqayya yake yi a

zuciyarsa, wanda har ya gagara daurewa "satin

yayi, domin yaje wajen abokinsa ya raka shi

wajenta ~

Dakyar da sudin goshi ya danni zuciyarsa ta

yarda satin ya yi, wanda a wajensa gani yake yi

kamar ya .

wata rabonshi' da unguwarsu Rukayyan

Ranan juma’a da wuri ya 'shirya ya nufi anguwan

abokinsa don yayi masa rakiya wajen‘- mutuniyar

tasa , yau tun da safe yake ta dokin '“ zuwa don

yaje yaga kyakkyawar fuskar‘ Rukayya', wanda ya

ke kasa yin bacci a dalilinta, cikin nasara da

kwarin gwiwa ya nufi unguwarsu, a cikin

zuciyarsa yana jiyoWa alamun dacewa a game da

abin. Yana zuwa gidan abokin naSa bayan'

sun‘gaisa sai suka dunguma sai gidan su

Ruqayyy sun yi sa;a kuwa sun same ta‘ bata, fita

k0, inaba, da daman ba.ma’abociyar yaWo bace,

idan ka ganta a waje aikenta aka yi,'ko kuma za

taje makaranta:

,A' sanda suka aika yaro ya yi musu sallama da

ita cewa ta yi a koma a ce musu bata nan. Har‘

yaron ya juya zai tafi, sai kakarta tace masa, “Je

kace tana zuwa”.

Sannan ta juya wajenta ta dinga mata fada, ba a

son ranta ba ta dauki mayafi tayi waje tana

mai zumBura baki tare da'yin qunquni. Gaisuwa

ce kawai ta shiga'tsakaninsu da ita, sai taja

bakinta'ta tsuke, abokin Abbakar ne ya shiga

gabatar'mata da shi, da kuma makasudin

zuwansu wajenta a

m’atsayinsa na wanda'ya ganta ya ji'yana sonta,

so-kuma na auree in Allah ya nufa shine mijinta'.

‘ ‘ Sun dan tana hira zuwa wani lokaci kamin nan

.suka yi mata sallama 2asu tafi, wanda duk cikin

hirer Rukayya ba ta. ce dasu 'komaiba iyakaci

idan sun Sako ta :1 ciki ne ta amsa musu da“

‘eh, ko a’a, Wannan hali nata na rashin magana

‘da kunya yayi bala’in burge Abbakar, kuma mi

sonta ya sake yin matsugunni a cikin zuciyarsa.

Yau da gobe tafi qariinwasa kuma ,-yawan naci

da kulafuci' da juriya tare suke bawa mutum

Karfin gwiwa wajen,.,cimma, nasara'a kan abin da

yake nema yawan' yimA'- Rukayya ziyara da

Abbakar yakeyi tare kuma da, kyawawan dabi

unsa sune‘ suka taru waje guda suka dunkule

harta ji sonsa ya shiga cikin zuciyatta, soyayya

mai tsabta suka dinga gudana‘rwa a tsakaninsu

Basu dau . tsawon lokaci da haduwaba komai ya

kammala a tsakaninsu, kasancewarma Abbakar

din a matse yake, haka ita ma Rukayyan

magabatanta sun matsu data fito da miji ayi

mata aure ‘ An, gama shirin komai na biki, anma

Abbakar bai sanar wada Fanne ba, saboda gudun

rigimanta don ba yason ta kawo masa wani cikas

‘a

akin lamarin, yasan qaramin aikinta ' ne ta nemi

gidansu RuKayya ta je ta yi musu rashin ,nutumci

wanda zai sa su ce sun fasa. ba shi . Rukayya,

domin ba kowane mutum ba ne zai yarda ya

dauki ‘yarsa ya had'a ta kishi da Fanne ba‘, shi

da kansa yanajin tsoron tasan abinda yake niyyar

yi, don ta sha gaya masa maganganu masu muni

da‘za ' ta aikata wa macen‘da tayi gangancin

aure‘; : mata'miji, ‘don haka né ma_ ya Boye

matacewa Zai ' qara aurene, kuma zai ci gaba da

Boye mata tare da nema musu tsari a wajen Allah

‘daga dukkan mugun ' nufin da za ta nufe su da

shi, har" zuwa lokacin da Allah zai ganar da ita

gaSkiya ta saduda ta daina munahah halayyar da

take yi, inyaso a lokaci‘n ne zai sanar da ita abin

da ke faruwa ya zama dole ya yi taka tsantsan

don gudun tonon asirinsa. Mahaifiyarsa yaje ya

samu ya sanar da ita. abin da ya tsara dangane

da akeciki ita kuma taba shi goyon'baya a kan

hakan, sai dai ta ce da shi ya zama dole a kansa

ya yi mata kayan fadar kishiya tunda dai ba

munafurtatta za a yi ba. , _ Hakan kuwa aka yi,

duk abin da Abbakar ya ‘yi wa Rukayya na' kayan

aure sai da ya yi wa Fanne; sai dai ya fake ne da

ce mata, da ma kullum yanada burin yi mata,

domin a da can da suka yi

Wancen Lokacin da sukai aure kasancewar

baidashi yasa bai Samu yay1 mata

wani abin kirki ba. . _ '

Fanne baki har kunne don har ciki, zuciyatta bata

kawo cewa kishiya Abbakar ke shirin 'yi mata ba,

don haka ne ma ba ta nemi tayi bincike a kaiba.

Abbakar ya sanar wa Rukayya cewa, yana da

mata da ‘ya guda ‘daya a tun farkon zuwansa

wajenta, Allah ya yi aure da marar kobo,‘ dubban

jama’a ne suka shaida daurin auren Abbakar da

Rukayya, Wanda yawancin - ‘yan unguwar suke

kiransa da mai sa’a, domin shi ne Wanda ya zo

daga ' . baya ya ce yana son Rukayyah ' kuma

shi ya yi nasarar aurenta An yi biki an tashi

lafiya, amarya da ango" sun kasance da juna cikin

farin ciki, zaman lafiya da,kwanciyar hankali tare

da so da Raunar juna su ne suke gudana a

tsakanin ma’auratan. A wani sabon gida da

Abbakar ya saya a can wata unguwa wanda ta ke

bayan gari nan aka kai Rukayya, unguwar

sabuwa ce shi yasa ba ta cika yawan mutane ba,

kasanceWar dagonaki, ne yanzu kuma aka yanka

su suka dawo plotai

Sati guda yayi a gidan yana cin amarci, kafin nan

ya koma gidan Fanne a kan cewa ya. dawo daga

tafiyar .da ya yi, da- ma da haka ya sallameta”

kwana biyu yake yi a gidan Fanne, ita'

itama amarya ya20 ya mata, biyu idan bai ya

samu dama, idan kuwa hakan bai samu ba, sai

ya dinga zuwa yana mata yini daddare ya koma

wajen fanne. Wani lokaci ma ya kan yi kwana

hudu a gidan Rukayya koma tiye‘da haka, idan

yayi wa Fanne Karyan: ya yi tafiya, itama Fanne

hakan tana faruwa da ita, don wani lokacin sai ya

doké sati a gidanta ba tare da yaje gidan

Rukayyaba _ ya kwana ba, haka ya yi tayi idan

yana nan, yau" gobé yana can. _ ’

An dau tsawon lokaci ana haka 'kafin nan daga

baya Rukayya-ta gano cewa Abbakar 'ya aurata

ne ba tare da sanin uwargidansa ba, hakan da

yayin ya yi mata ciwo sosai; wanda harta kaita»

ga zaunar da shi ta yi masa nuni 'da cewa, hakan

da ya yi ba daidai ba ne, kuskure ne

babba'wanda Zuwa. gaba'idan ta gane Wata

sabuwar rigimacé don haka ya sanar da ita a

yanzu ‘shi ‘ne mafita, domin duk‘ kishinta bata

isa ta hana’abin da Allah ya hukunta ' ba. .' ' '

Hakuri Abbakar ya ba ta tare da kawo masa

hujjojin da ya sa ya Boye wa Fanne cewa zai qara

aure, amma ba da niyyar don ya wulakantata ba,

ya dora da cewa.

Kuma da kike kallona ina So a ce iyalina a

.wajé daya suke‘ a zaune, domin ina bukatar

hadin

kansu, kuma tarayyarsu waje daya shi zai sa su'

fahimci juna, sai dai kash hakan ba zai yiwu

yanzu '- ba, don akwai wani shinge da zai hana

ni hada ku; ' Kwaraii da gaske ta_ gamsu da

bayanansa, kuma har cikin zuciyarta ta yarda da

‘su, domin tana da yakinin cewa iya gaskiyama

ya tito ya fada mata, amman; duk da haka'sai da

ta sake yi masa

sharhi a kansu, ta cedashi. duk, Naji‘ bayananka,

amma kuma hakan. da ka yin ba daidai ba ne,

duk da cewa'kana da hujja, don . komai daren

dadewa sai an yi walkiya haske ya bayyana,

matarka ta gane cewa kana da wata mata a

'gefe, in kuwa ka kuskura ta gano hakan da kanta

ba tare da ka sanar da ita gaskiya ba, to wallahi

kaji na maka rantsuwa za ka ga abin da ba ka.

taBa tsammani ba, domin a lokacin zata dauke

ka makaryaci, kuma girmanka da take gani zai

zube, za ka zamanto ba ka da kima balle daraja a

idonta, sannan kuma'abin da-ka ke gudun

faruwar tasa sai ya faru... Kai sai ma ya zarce

don a lokacin ne za ka san da ruwa a ke shayi-

babu wanda zai ba ka goyon baya, kowa cewa

zaiyi munafuntarta ka yi, amma idan yanzu ka

gaya mata ta tada hankalinta, mutane cewa za

su yi da ita

kishi me ya sa ta ke maka haka”.

Tunda abakar ya auri rukayyah ya samu nutsuwa

DA kwanciyar hankali Wanda idan yana tare DA

ita had baison KO kadan baison matsawa kusa

DA ita kumama mantawa take DA wata Mai suna

fanne a duniya don har abokan huldarsa su

Kansu sunga canji a tare dashi wasu data ciki

sukan tsokanesa sauce Kai abakar me

amaryarnan taka take bakane DA kake narka

uban qiba haka murmushi kawai take binsu dashi

a duk sands suka tasoahi DA tsokana dob shi

kansa yana mamakin qiban DA yayi a dan

qanqanin lokaci bayan kuma ba qarawa take akan

abinda yakeci a kullun ba

Uwar goyo

Chapter19

Wani lokacin idan ya zauna yana tunani sai ya

dinga tamb’ayar kansa da ma. ashe haka abin

yake da dadi, Wanda yake daukarsa a matsayin

wani abu daban, a wannan lokacin ne ya sake

tabbatar wa kansa cewa, lallai yana da hakuri’

tunda'ya iya zama da Fanne na tsawon 'shekaru

masu yawa; ya kuma jure duk ‘wata tsiya da‘

take yi masa, shi da a nasa tunan'ma 'namiji

bawan mace ne anayin aure ne kawai' domin "ya

dinga yi wa matarsa hidima, ashe abin ba haka

bane, shi din ma yana da nasa ‘yancin, kuma shi

ne‘ jagora a kan - dukkan komai na rayuwar

matar sannan yana da ikon sanyata‘da hana ta; _

Uhm’lallai gWama da'yaYi'auren ya dandani

zumar‘ da a‘keji Wanda a da madacinsa kawai

yake ji, da daya mutu bai aureba da shi kenan‘ ya

yi babbar asara. Allah mai rahama ‘ da ya yi

masa, gaskiya ne da ake cewa mutum yana

samun kwanciyar hankali ne'idan ya azurta shi

da mace ta gari.“kullum Rukayya cikin kwantar

masa da' hankali ta keyi,ko Fanne ta Bata masa

idan ya zo gidanta sai ya manta da duk wani

bakin ciki da ‘yake cikin'zuCiyarsa, domin ta iya

kula da shi; sam bata da lokacinta na kanta idan-

yana gidan, k0 barci yake yi tana zaune a kusa

da shi tana maSa '

fifita duk wani motsi idan yayi sai ta tambaye shi

k0 da akwai abin da yake so, ga shi a koyaushe

tana cikin girka masa abinci mai dadi sannan

kuma ga tsafta ta ko’ina kamshi ne ke tashi a

jikinta da kuma gidanta. Abinda yake sake sa

masa sonta a“ cikinzuciyarsa kenan, aduk sanda

zai zo gidan zai same ta cikin kwalliya, kamar da

ma ya sanar da ita zuwan nasa.

Ba kamar Fanne ba daba zatayi kwalliya ta saka

kaya mai kyau ba, sai idan zata. je unguwa,

duk da kuwa tarin suturun da ta ke dasu. '

Shekararsu daya da aure Allah ya nufi Rukayya

da “haihuwar ‘ya mace, Abbakar yayi murna sosai

da wamman kyauta da Allah ya ba shi. Yayi

hidima sosai ga maijego da jaririyarta.

Ranar suna data zo aka sawa yarinya suna

Khadija,’ Wato ta ci sunan kakarta' ta wajen uwa,

ba zata Abbakar ya yi wa Rukayya, sai ranar

suna ta ji sunan kakata ya saka. Tayi murna‘

sosai kuma har cikin zuciyarta ta ji

dadin’karamcin' da ya yi mata, da ma ita ma

sunan data keson a sa wa ‘yar kenan, amma

kuma kunya ta'hanata sanar da Abbakar din,

kuma‘~ wani Bangare na zuciyana yana tunasar

da ita'ko akwai wanda Abbakar ya yi niyyar saka

wa suna. A halin da akeciki yanzu Sam Abbakar

ya daina damuwa da abin da Fanne ta ke

yi masa‘ don haka ya debeta gaba daya ya Zubar

da, ita a kwandon Shara, sai'dai bai daina

kyautala mata ba kamar yadda‘ya saba yi a da,

kuma har zuwa wannan :lokacin yanayi‘ mata

addu’a kan Allah (S.W.T) ya shirye ta Ya dawo

da ita hanya mai kyau, ta kuma gane cewa ita

duniya ba matabbata bace ta tuba ta koma zuwa

ga Allah, inyaso 'a lokacin ne zai tone mata askin

da ya dade da binnewa.

Har zuwa wannan lokacin Rukayya ta kan

yawaita yi wa Abbakar magana akan ya' zama

dole ya sanarwa matarsa uwargida‘ cewa yana

da wasu iyalin a gefe, saboda rayuwa ba ta da

tabbas idan mu ne yau ba mune gobe ba, ba fata

ta keyiba idan ta,Alla ta kasance da wanne idon

zataje tama da matarsa'ita ma matarsa ce har

sun haihu, kuma ma sai yaushe ne zai hada kan

yaransa suyi zumunci, kuma. fahimci juna ba cin

ba su taba k0 da kallon juna ba. . _ ‘

“Ni wallahi naf1. so ka hada mu waje daya mu

zauna, k0 Allah zai sa mu fahimci juna nida ita.

Insha Allah na yi maka alkawarin zamu zauna

lafiya bazaka samun Baraka ta wajena ba, kuma

ko da,‘ace ita ne tanemi ni‘ bazan kula ta ba, da

ma niba halina ba ne hayaniya, haka kuma ban

Saba da yin fada ba, ka ga kuwa ba zai yiwu ace

Rana tsaka na dauki halin karnuka na dora wa

kaina ba, duk wani gida da kake ganinn kishiyoyi

suna fada su duka biyun ne ba su da haKuri,

amma idan aka yi dace aka samu mai haquri a

cikinsu sai ka ga sun 'zauna lafiya, suna ta haife-

haifensu a . haka. ‘ Abbakar‘ hakuri kala-kala ne,

akwai mai hakurin da zai’iya zama da

dayuw‘ansa duk masifar da mutumin yakeda ita,

k0 da‘kuwa a ce shi din wuta ne”. '

Idan Rukayya ta gama gaya wa Abbakar

wadannan maganganun sai kawai ya kalle ta yaYi

murmushi baya cewa da ita komai, lallai Rukayya

ke har yanzu da sauranki‘domin kuwa ba kisan

kowace ce Fanne ba shi ya sa ki ke nemAn ki

zauna tare da ita, ’duk haqurinki da iya zama DA

mutum sai Fanne ta yi miki wani abin da zai

jawo kinyi fada da ita, kai ko koyi ne yake zaune

da ita watarana sai ya yi baKi, SBD abubuwan da

zata dinga yi masa. ' . kaI A rayuwa bana fata k0

maqiyine ya zauna da Fanne a yanzu, domin

kuwa‘ itan‘ dakalin~ majina ce duk wanda ya

hauta saiya zame, kuma itazuma ce zama da ita

sai da wuta ko kuma da

magani "maganama bata wadace ki ba, yaushe

Zan hadaki

in hadaki damasifatu wacce bata gajiya, k0 da

kuwa kwana za ku yi kuna abu daya, wani

lokacin har mamaki takd bani a yi mutum baya

gajiya sai kace inji, ni‘dama da nake tare da ita

dole ce ta sa nake zaune da ita, ba

wai don ina son zama da ita ba, ko kuma tana

mini

abin da raina’yakd, so shi yasa na kd zaune da

itaba .matar da zamana da ita ban qareni da

komai ba sai tarinwahala da baqin ciki, ba don

ma Allah'ya taimake ni ba, ai da yanzu ina

kwance hawan jini ya kada ni”. ,

Duk yadda mutum yake tunanin Fanne ta wuce

nan, haka nan kuma k0 kai wane ne zata ci maka

mutumci bata ganin kan kowa da gashi

baran ma shi data gama raina shi, Wanda ta ke .

kallonsa kamar wani bawanta mai mata hidima

take biyansa albashi, k0'kuma kudi ta saka ta

sayo shi, domin kuwa dada namiji mai zafinrai

aka hadata lallai data dandana kudarta, don a

kullllun sai ya jibge ta idan ta Bata masa rai, k0

kuma ta tsaya a‘ kansa tana masa tsageranci'

irin wanda ta

saba yi masa yake hakuri da ita, to

lallai ba zasu

dauki tsawan lokaci’suna tare ba; shi ma Wani

lokacin duk haqurinsa idan ta yi masa Wani abun

sai yaji kamar zai doke ta don haushi. Da ,Kyar

yake samu ya danne zuciyarsa, kuma ma idan ya

“ya hada su gida daya’ytabbata 'ba zai iya yi

musu adalci a tsakaninsu ba, kuma k0 da' ya

kwatanta Fanne ba za ta barshi yayi ba. ita

Rukayya da take neman a hada su waje daya, ita

fazata dawo bora don sai yayi da gaske sannan

zai samu ya dinga shiga wajenta, 'ko kuma ta

dauki makami rana daya ta shiga har dakinta ta

kashe ta, don yana da yakinin Fanne za ta iya

komai domin ta samu biyan bukatarta, shi yasa

ma maganin kar ayi kar a fara, saboda ya gama

sanin cewa ba ta da imani k0 kadan a. cikin

zuciyarta, kuma ba lta zama ta yi .tunani idan

har Zuciym‘ta ta raya mata wani abu mummuna.

A take ta ke aikata shi, sannan kuma bai taBa

ganinta ta yi nadama koda na sakan a kan

abubuwan da ta ke aikatawa ba, shi ya sa ma

yake dada tsorata da al’amarin nata, domin kuwa

duk mutumin da ya' girma ya mallaki

hankalinkansa, yana da masaniya a kan

abubuwan da yake aikatawa mai kyau ko marar

kyau. Amman ban da Fanne har yanzu bata san

inda yakeyi mata cijwo ba.‘

- Rayuwa .taci gaba da .gudana a haka, Ruqayya

yanzu abubuwa sun fara yi mata yawa, saboda

haihuwar da tayi, don haka Abbakar ya

nemi shawararta akan cewa ta.samo wata ta

dinga ‘ taya ta k0 da da ayyukan gida ne,

inyasosai a dinga

biya Shiru kawai tayi masa batace dashi komaiba,

a dama haka ta ke ‘idan abu bai dametaba, idan

ya gaya mata sai ta yi shiru ba Zata ce dashi a’a

ba, don ba ta so su yi jayayya da shi, babu yadda

Abbakar bai' yi da ita ba akan maganar ‘yar aiki,

amma tace dashi ita ba ta so, ita zaman mata

keyi a gidan da har sai an kawo mai taya ta

ayyukan gidan, kuma ma duka nawa aikin yake

da har za a, tsaya rabawa mutane, ,lalaci ne ace

da mace aikin da baifi karfinta ba,,sai ta saki‘ jiki

ta zauna sai an nemo 'mata mataimakiya, harga

Allah akwai yawan aikinda zai sa a daukar wa

mace ‘yar aiki, amma ba irin nata ba, wanda bai

taka 'kara ya karya ba, dole Abbakar ya hakura

da maganar ‘yar aikin kamar yadda aka yi a

lokacin da ya saya mata mota, fur Rukayya ta

kekashe qasa ta ce ba bazata yi amfani da ita ba,

ina ma take zuwa da har za a saya mata mota?

Kuma idan ta yi yawo a cikin mota aceda ita ‘yar

waye a garin?

Motar ta dade a ajiye kafi nan daga bisani

Abbakar ya sayar da ita ya kawo mata kudin yace

gasu nan idan ta ga dama ta qona suma, tunda

ya riga ya ba ta ya rantse ba zai karBa ba.

Da taga alamar ransa ne ya Baci sai ta karBi

kudin ta jeta ajiye su, daga bisani ta ba shi

hakuri.

Abbakar yana mamakin hali irinna rukayya, sam

ita ba ta dauki wyale—qyalen duniya tasa a cikin

zuciyarta ba, bata da wani buri mai yawa, kuma

babban burinta shi ne Allah ya ba ta ikon

tarbiyyanta: da Khadija a bisa yadda shari‘ar-

musulunci ta tsara, sai kuma yi wa mijinta

biyayya da kuma fatan‘ cikawa da kyau da imani

Khadija tana da shekara daya da Wata uku

Rukayya ta yaye ta, kasancewar a wannan

shekarar ne Allah ya nufe ‘ ta da zuwa aikin hajji

wanda Abbakar ya biya mata, a tun farkon

aurensu ya so taje sai kuma Allah bai nufa ba,

saboda tana dauke da qaramin ciki, kuma yana

ba ta wahala shi ne Abbakar ya mai da kujerar ta

zamo ta kakarta wanda- ta goyata.

RuKayya sun yi hajji lafiya har ma sun dawo,

yawancin tsarabar da ta yi daga can Abbakar ta

yiwa sai kuma Ummansa da sauran ‘yan uwansa,

har da Hajiya Fanne da Momi ta yiwa' tsaraba,

don haka ta kudiri niyyar insha allahu a wannan

karon sai ta samu nasara a kan Abbakar ya kai

ta sunga juna, inyaso sai ta kai musu tsarabar da

ta yi musu, amma kuma sai me? Tana gaya wa

Abbakar abin da yaksle cikin ranta, ya kalallameta

da dadin zance irin wanda ya saba yi mata idan-

har ' irin hakan ta dasu. Cikin sauki ya samu ta

yarda da batunsa har ta amince taba shi kayan

da ta sayo

musun don ya kai musu, shi kuma yana ganin ya

cimma nasaya dauki jakar ledar yayi waje, cikin

zuciyarsa cike, da farin ciki. fanne ya kai 'wa

kayan amma sai dai ya boye mata gaskin

lamarin, ya ce da ita‘, wani abokinsa ne ya je

aikin hajji ya kawo musu tsaraba. .

Khadija ta taso cikin kulawa da gata daga dukkan

Gangaren mahaifanta, suna matukar' ji da ita, da

kuma tattalinta yarinya kyakkyawa da ita, ruwaa

biyu ta ke da shi, kamansu daya da Abbakar ta

.fuska da hannu da qafa, amma fatar jikinta irin

na mahaifiyarta ‘ne, fara ce sol ga gashi har.

gadon bayanta, tana‘ da dara-daran idanu masu

kyau da haske, fararr A kullum zaka ga idanunta

kamar ‘ mai jin barci, akwai ta da yalwar gashi

gira kuma baki sidik, yawancin halayyarta yayi

kama dana - mahaifiyarta har cikin ransa

Abbakar ya sani yana qaunar Khadija,‘ Sam baya

iya hada soyayyarsu waje daya da Momi, haka

nan kuma halayyarsu ba irin daya ba ce, Khadija

na da shekara biyu Allah ya sake bawa Rukayya

ciki, wanda Allah bai nufa za ta haife shi ba, ta‘

rasu adalilin hatsa’rin motar da ya rutsa da su_ a

kan hanyarsu ta komawa ,gida daga shagon alfijir

Wanda ko shi Abbakar din bai san tanada shigar

qaramin cikin ba, domin ba ta gaya masa ba

kuma

A tun lokacin da Allah ya yi wa Rukayya rasuWa,

sai rikon Khadija ya dawo hannun kakar

mahaifiyarta, a‘koyaushe za ka ga yarinyar tana

cikin alhinin rabuwa da mahaifiyartta, domin

kuwa a kullum suna tare basa rabuwa da juna,

kuma tayi matukar shakuwa da mahaifiyar tata

shi yasa a ko yaushe take cikin‘ damuwa,

batakuka, amma a koyaushé. -za ka sameta a

zaune jigum babu walwala a tare da ita, kuma

tana yawan‘ .ambaton sunan mahaifiyarta, kai

harda mahafinta tana da muradin ganinsu, duk da

’cewa tana samun kulawa ‘ Sosai a wajen' kakar

Rukayya, amma tafiso ce tana kusadasu

Kakar Rukayya tuna-tausayawa halin maraici da

yarinyar ta shiga,~tana‘ kuma so a ace Abbakar

ya haqura yabar mata rainon.yarinyar ya dawo

hannunta kona shekaru qalilanne, amman a yadda

ta alamu‘shine yaf1 ta bukatar kasancewa tare

da Khadijar fiye da ita, domin daga 'dukkan

alamu . yarta shiga damuwa a kan mutuwar

Rukayya, don haka 2atayi haquri ta. bar masa

ita‘a wajensa,‘ inyaso ta dinga zuwa lokaci zuwa

lokaci tuna duba ta, fatanta Allah yasa 'matarsa

ta yarda ta rike yarinyar tsakani da Allah, ko dan

maraicin data ke

tare da yar da alamn kuma matar ba ta da illa

tunda ita dai Rukayya ba ta taBa kawo min wani

. aibu nata ba, hasalima ni ba mu taBa yin.

hirarta da Rukayya ba, yaushe ma ta bude: baki

tayi zancen nata" balle har aje ga batun ta gaya

mata abin da yake damunta a cikin zuciyarta,

yake da nasaba da gidan aurenta.

' Allah ‘kenan mai yadda yaso, ya dauke wa

Abbakar‘ Rukayya ‘a lokacin da yake tsaka da

muradinta, ya kuma bar masa Fanne wadda yake

zaune da ita a bisa qaddara

..... ..... ......

hajiya fanne kuma tunda Abbaka: ya ce

da‘ ita ‘yarsa za to. dawo hannunta da zama,

kuma a ’dakinta ta zauna ta shiga qullah yadda

zata yi ta mallaki dukiyar da Abbakar yake dashi,

cikin’ ruwan sanyi ba tare da ya gane nufinta ba,

ya zama dole ta bishi kuma ta shiga yin duk abin

da ya ce da ’ita, .kuma ta janyo yarinyar da yace

zai kawo ta zauna'da ita a jikinta, ta nuna mata

kulawa sosai iya da yadda take bawa Momi, in ba

haka_ ba bata ga hanyar da za ta biba don

cimma hurinta, duk da cewa tana jin Kiyayyar

yarinyar tun kafinma a kawo mata ita, shegiya

mai kama da aljanu.

“Matukar‘ ina raye ba zan taBa bari ki samu

komai a dukiyar Abbakar ba, haka kuma bu zan

“taba barinki ki ji dadin rayuwa ba, sai na zamo

miki bakin takobi wanda zan dinga sare dukkanin

farin cikinki da shi, yadda uwarki ta aure min miji

kuma ta shiga ta 'fita wajen boka da malamai ta

mallaki zuciyar Abbakar‘, ta kunsamin min bakin

‘ciki a rayuwata, haka ni ma zan shiga taki

rayuwar na dinga kunna miki wuta a cikinta,

dama nayi niyyar rama abin da uwarki tamin

tunda kuwa bata nan, to a kanki zan' rama. Kai

‘kuma uban munafukai ka shiga ukunka a

hannuna, bari ka gani burina ya cika a kanka idan

dai ni Fanne ‘yar halak

ce a cikin uwata da ubana na fito to sai na rama

wulakancin da

cin mutunci wanda ka dade kana yi min shi, ta~

wannan hanyar ce kawai zan bi na musguna

maka, kamar-yadda ka yi min wai har da yin aurc

ba tare da sanina ba, shi ne kuma yanzu za ka

dauko min yarta ka kawo min cikin gida? Ina! Ba

zai’yiwu ba, da sannu zan nuna maka cewa,

shan-shayin‘ da akeyiwa kanwa‘ba za a yiwa

barkono ba, mu zuba ni da kai shege ka fasa.

Kuma wallahi idan burina ya cika ba sani ba

sabo, rufe idona zan yi na ci maka mutumci 'iya

son raina, inyaso naga da wa kake taqama,

‘sannan naga uban ‘yan rashin

kunyar da'zai zo ya tuhumeni a kan me ya sa

'nayi

maka "bala'i saina‘ bashi amsa daide da

tambayarsa, daga ni sai ‘yata nake so mu gaje

dukiyar Abbakar, domin kuwa mune muka

cancanta mucita ba, wasu can ba dabasu san ta

y aaka same ta ba". "Bayan kwana biyu da

maganar dawowa, Khadija gidan Abbakar yace

don Allah ta kawo masa ita‘ domin Zamanta

akusa da shi Zai debe'masa kewar mahaifiyarta.

Hakan kuwa aka yi washegari da safiya Kakar

Rukayaya ta sako Khadijn gaba da akwatin

kayanta, ta dawo da ita gidan ubanta. , " ' A 'kan

hanyarsu 'ta zuwa gidan Kakar Rukayya tana‘ta

sake saken zuci, tun jiya'da Rana , Abbakar ya

jure ya sanar da ita sakonsa harzuwa yau da

zuciyarta taketa cike da zullumi da tunanin halin

rayuwar da yarinyar zata shiga. Taso ace Abbakar

ya haKura ya bar mata Khadija ta raineta kamar

yadda ta goya uwarta, koba komai zata dinga

kallonta kamar Rukayya, amma fa yaqi yarda don

tun yana kwénce a gadon asibiti yaketa yi mata

magiyar ta kawo masa ‘yarsa

, ya hada ta da Allah ya had at a DA Allah, ya ce

da ita ' yana so neya dinga 'ganint‘a a kullum

tana zaune a! kusa da shi, k0 Zai dinga samun

sassaucin rashin

Rukayya da ya yi, wanda a koyaushe yake

addabarsa a cikin zuciyarshi, kafin nasa lokacin

yazo, don yanzu ma yana raye ne amma kusan a

mace yake, tunda wasu sassa na jikinsa sun yi

mummunan raunin da baya iya moisa su, kuma

suna da matukar muhiinmanci a rayuwarsa, din'

haka yake ganin nan ba da dadewa ba shi ma zai

iya bin nata ; dayazo nan a zancensa sai ya fashe

da kuka, domin tausayin Khadija daya jiya ‘ cika

masa zuciya, shi'kenan ita kuma ta zama babu

uwa ba uba, ta zama marainiya gaba da‘baya,

Allah ne gatanta watakila ita ma irin; rayuwar da

mahaifiyarta tayishizatayi; ’

- Kakar Rukayya" ta share: wasu hawaye DA

suka zubo mata a~ lokacin da suke shirin shiga”.

gidan Abbakar, Kaninsa ne yamusu’ .-

jagora har zuwa' inda Bangaren Abbaka'r din

yake

tare da‘sallama suka Shiga ‘dakin a lokacin’

qaninsa ‘dayan ya mikarda shi zaune ya sa masa

filo guda

biyu a bayansa ya ‘tokare . A :sanda suka shiga'

dakin Khadija nayin tozali da mahaifintar ta saki'

hannun Kakar Rukayya .wanda take riqe da shi ta

ruga da gudu- ta’ nufi wajensa. Tana -‘ isa ta

fada

kansa tare da rungume ~abinka da yarinta bata

k0 lura ‘da raunikan da suke jikinsa ba, duk da

cewa

ta fama‘shi bai tsaya bitakan zafin ciwon da

yakeji ha;

sai kawai shima yahau murnar yana ta ‘

kiran‘sunanta amma ba ta amsa ba, Sai ta ce

dashi, “ “Abba ina Ummina?’ A ‘ '

‘ Habawa yarinya tana fadar haka Abbakar ya

fashe dakuka, daman me neman‘kuka ne; kuma

sai aka jefe shi da késhin ‘awaki'

‘ “Don Allah kayi hakuri ka daina wannan ‘ kukan,

Wanda baida wani amfani a wajenka, sai ma ‘ya

janyo maka wata‘cuta 'daban, kayi tawakkali‘ ga

Allah, shine: "ya ‘rubuta ita kuma ya kar6i

abinsa, haka—nan duka muma zaman jiran

’lokacinta muke yi, ka tuna cewa dukkan ,mai' rai

mamaci ne, sai dai idan lokakacin'sa bai yi ba.

abban Khadija ni ce ya kamata na shiga wani hali

a game; da mutuwar Rukayyah sabod ita kadai

ta- rage min a' cikin‘Zuriyata, sai kuma wannan

‘yada kuka haifa, amman haka nake danne

zuciyata‘ ,

na bar wa Allah ikonshi shi kadai ne ya isada‘

bawansa. haka, Ba wai’ bana jin ciwon

mutuwarta bane a:a sai

don babu yadda na iya ne

zab damqa maka khadija a hannunka kaman

yadda‘ka, buqata, amma badon inason rabuwa

da- ita ba, domin ita kadai ta rage min wadda

zan dinga kani inajin dadi, kuma ita kadaice ta

rage min "; wadda ta fito daga‘ tSatsona ma’ana

jinin jikina”. ,

Adaidai nan Hajiya Fannee; ta yi sallama ta'

shigo dakin, cikin girmamawa tarda durkusa ta

gaishe da kakar Rukayya, ita ma, cikin sakin

fuska ' ta amsa mata tare da tambayarta me jiki.

“Da sauki”. Ta ba ta' amsa.

“Allah ya qara kaqo sauki”.

“Amin”. Su duka suka amsa harda qannen

Abbakar din

Da ma tun shigowar su’ Khadija‘ Hajiya Fanne ta

gansu amma taqi zuwasu gaisa, don jin zuciyarta

takeyi kamar ta yi bindiga don qunan take mata

da qyar ta taushi zuCiYarta ta‘ tashi ta nufi dakin

..,Abbaka.r. din Bayan sun gama gaisawa ’da

Hajiya. Fanne n sai kakar Rukayya ta ca da

inta“Hajiya don Allah ki rike amanar wannan

,yarinyar, kin ganta. marainiya ce, kuma yarinya‘

ce qarama wadda bata san ciwon kanta ba, akwai

tarin lada mai yawn wanda Allah zai baki idan

har kika yi mata riwo na gaskiya, amma hakan ba

zai yiwu bu sai kin hada da hakuri,kin danne

zuci‘yarki, domin a.kwai cin rai wahalar rikon dan

wani”.

Hajiya Fanne dai ba’ ta ce da ita‘komai bai harta;

dasa‘aya ga maganan nata,,tana tsaye ne kikam

tun ‘sanda ta shigo dakin tana kallon Abbakar shi

‘da yarsasunarungume dajunaa

_' Takaici ne‘tare da baqin ciki suka taru suka

lullubeta, tun daga‘yatsan qafarta babba har-

zuwa ‘tsakiyar kanta, haushin Abbakar din ya

kamata ji ta keyi, kaman taje ta dauko taBarya ta

mammaka musu musu a kansu-shida yar‘ tasa,

lallai ma Abbakar ya gama rainamin hankali, a

gaban. nata-zai rungume

- ‘yar-sa yana wani nuna mata so ta

musamman, abin da bata taBa gani ya yi wa tata

yarba, a _koyaushe cikin hantarar.Momi da nuna

yana kyamarta yake. Kai-lallai DA sake

ya"zama"dole ta'bazana zuwa wajen ’masana,

dominta‘ samu abin da- zata .ma wannan

soyayya 'da yake ma yarnan daga gani ma ‘asiri

ne yake dawainiyada shi, don kuwa ba a cikin

hayyacinsa yakeba. , “Kai amma wannan tayi

min‘abin da harna: mutu bar'zan manta da shi

ba, kuma wallahi nima sauna rama, domin cin

tuwon'kishiya ramakone.‘ Sannu a .hankali zan‘

bisu' a yanzu, nai mudu duk abinda suke bukata

zan musu har na cimma manufata, sannan ne

zasu gane dawa suke zancen. Abbakgr kénan;

zakai kuka- kamar yadda kasani”; Ta. ambaci

hakan da a cikin zuciyarta

«Hajiya riqon yaro sai an hada da hakuri, . Kakar

Rukayya ta katse wa Hajiya Fanne tunaninda ta

ke yi.

“Babu komai Iyah, insha Allahu zan rike ta

abisa'amana kamar yadda zan rike ‘yar da na

haifa' a cikina, balle ma ai ita da Momi duk daya

ne ba su da wani bambanci» a wajena', tunda dai

daga tsatso daya suka fito, uba daya ai ya fi

qarfin wasa. A dalilin Momi da Abbakar ni ma

Khadija ta zamo : wani Bangare na jikina, idan

har na cutar da ita na cutar da ita kamar kaina

na cutar, kuma 'ai da na kowa ne, haka kuma' da

.da da'dukiya ba a musu mugunta don ba ka san

Wanda za ka mora ba”. ‘

Wannan magana da Hajiya Fanne ta furta ta yi

wa kakar Ruqayya dadi, kuma ta faranta mata

rai, haka kuma ta goge duk wani dar da take ji a

cikin zuciyarta dangane da irin rikon da- za ta yi

wa Khadija. ' _ . Shi ma gogan Abbakar yayi farin

ciki da wannan‘ bayani na matarsa, don haka yayi

murmushin jin'dadi da samun nasara a

kan.Hajiya Fanne. Sai dai kuma maganganun

Hajiya Fanne na munafunci bai yi wani tasiri a

cikin zukatan qanncn Abbakar ba, domin sun

gano inda ta dosa.

“Yauwa Hajiya na ~ gode a bisa wanna ‘

karamcin ’da kika yi min,_ kuma ‘ina mai tayaki

addu’a a kan Allah ya ha ki ikon riRe su tare da

baSu tarbiyya mai kyau”. “Amin summa amin”.

Abbakar ya amsa addu’ar kakar Rukayyan da ta

yi wa Hajiya Fanne. “Ya ‘ki 20 nan Khadija”.

Fanner ta ce da ita ‘tare dakama hannunta.

Khadjja kuwa sai ta sake lafewa a jikin

mahaifinta alamar ba za 'ta 20 ba kenan, 'dama

yarinyar akwai ta da qiwiya, matukar ba saninka

ta yiba.to ba zatazo.wajenka ba, duk da cewa

Hajiya Tsigala taji haushin abin da Khadija ta yi

mata, sai Bata daddara ba ta sake kai hannunta

duka biyu za ta dauke ta, yarinyar tana ganin

haka sai ta fashe da kuka tare da qankame

mahafinta.

Abbakar yana ganin ta fara kuka nan da nan sai

ya rikice ya rasa inda zai sa ransa, shima kawai

sai‘ ya fara. hawaye, wannan abu .ya baqantawa

Fanne, rai , sosai, wanda har sai' data gagara

dannewa a cikin zuciyarta, bacin ran nata ya fito

karara a kan fuskarta, babu wanda ya kula da

hakan sai Kannen Abbakar. '

, Da taga ba zata iya jure tsayawa, a dakin ‘ tama

ganin' bakin; ciki ba, sai kawai ta_ cewa Kakar '

RukaYya; “Bari na je daki na duba k0 Momi ta

‘tashi daga bacci”.

Bayan fitarta sai kakar Rukayya ta shiga lallashin

su Abbakar, tare, da gaya masa magangaui masu

taushi. Ita kuma Hajiya Tsigaln. dakinta ta nufa

ta zube a kan kujera tana maida nunfashi na

baKin ciki, kamar wadda ta yi gudu. Me Abbakar

yake so ya nuna min? Yana nufin cewa ya fi son

Khadija da mahaifiyarta a kanmu? Lallai ma

namiji- sai a gajshe shi, yau ,ta debo ruwan dafa

kanta, ya ya za ta' yi ne- da wannan tsinanniyar

yarinyar da aka hada ta da ala qaqai, amma ba

komai, ni na san abin da zan yi mata”.

'Fanne zamanta ta yi a falonta taKi komawa

wajen su Abbakar, domin , ba ‘zata je ta gano

abin da zai hanata . 'bacci ba, ko kuma ta

kasa'cin abinci a wunin ranar,

‘saboda abin na Abbakar ya wuce misali, duk

yadda

ta dau ha haka bane ya nuna. Soyayyar da

Abbakar yake yi wa matarsa da ‘yarsa tana da

yawan‘ gaske.

Har dakin Fanne kakar rukayya ta shiga .

don ta yi mata sallama a lokacin da za ta ta tafi

nanma ta jima tana yiwa Fanne nasiha tareda

kuma bata hakuri a game da zama da yaro, .

.“Hajiya ya Zama dole ne sai kin ,yi hakuri

da Khadija, domin zaman naku mai

,daukartsawon

lokaci ne k0 da kuwa ace ke kika haife ta, domin.

yaro akwai shi da rashin jin magana

Lah ba komai Iya, kar ki ji komai‘fatana ku

dinga taya ni da addu’a a kan Allah ya ba ni ikon

rike amanar da na dauka, kuma Allah ya yi musu,

albarka”.

. “Amin Hajiya, na kuma gode ni zan tafi sai ' an

kwana biyu zan sake zuwa na duba ku. ' '

“To shi kenan”. ' 7,

Har harabar gidan Hajiya Tsigala ta raka ta tare

da yi mata alheri, sabulun wanka da na wanki har

da man shafawa a cike da leda Fanne tabata.

A kan hanyar Kakar Rukayya‘ta‘ komawa gida

taketa tunanin halin kirki irin na Fanne, kai

wannan mata akwai ta da kirki, daga yadda na ga

aluamu zata yi kirki, kuma za ta rike min Khadija

cikin~ aminci ya‘ Allah ka bata 'ikon tarbiyyantar

da yaran a bisa yadda shari’a ta tanadar, sannan

kuma Allah ‘ka kare su daga sharrib makiya da

muyagun qawaye, don wasu qawayen ba basu da

dadi da zarar'sun ga halayyar mutum mai kyau

ne, sai su nemi hanyar da za su bi su canza

maka.

Allah ya sa dai kar ta dinga daukar zugar

mutane, amin.

Kash masu karatu sai 'nace muku sai mun had‘u

a gaba. ‘ book3 kenan donjin yaddah zata kaya

To nima sai nace daku Allah Ya bama Hajiya

Fanne ikon_’rike amanar Khadija da aka bata da

fatan za zakuci gaba da ban dakinkai mu hadu a

book3 don jin yadda za ta kasance a tsakaninsu,

komu aje book dinner my Fara wani don't naga

DA yawa kaman basajin dadun book din said naji

data gareku muci gabane komu canja wani????

Na gode‘ sosai da hadin kan da kuke'banii

naku ha'kullum mai burin faranta muku

zuciya

Uwar. Goyo

Chapter20

"WAR GOYO. book3

Rayuwar Khadija a sabon wurin da ta tsinci

kanta, rayuwa ceda ta keyi cikin qunci da takura,

saboda ita yarinya ce wadda ba ta da saurin sabo

da mutane, k0 don ba su cika yawan zuwa

gidajen mutane ba ne a lokacin da mahaifiyarta

ke da rai? Don haka ne a yanzu ta ke fuskantar

matsala, don ma tana ganin mahaifinta a gidan,

kuma a koyaushe zaka same ta a wajensa har

zuwa yanzu da ta ke da sati daya a gidan, ta qi

yarda Hajiya Fanne ta dauke ta, k0 kuma wata

mu‘amala ta shiga tsakaninsu da ita, sam

yarinyar ta tsani ta ga Fanne ta shigo dakin da

suke, ko wasa ta keyi idan ta ganta ta shigo za

ta bar abin da ta ke yi ta ruga da - gudu ta Buya

a bayan mahaifinta, kai k0 muryarta ta jiyo daga

tsakar gida tana magana sai ta firgita ta kuma

daina abin da ta ke yi, wannan abu da Khadija ta

ke yi wa Fanne yana mata ciwo sosai a cikin

zuciyarta, yarinyar ta maida ita sai ka ce wata

dodanniya ko mayya mai cin naman mutane?

Gashi kuma a ‘dalilin tsoron nata da ta ke ji‘ shi

ne ya hana Fanne cimma burinta a kan Abbakar.

Abin duniya duk ya taru ya yi- wa Fanne yawa,

gaci ga qoshi, sannan kuma ga

kwanan yunwa. Ta rasa ta yadda za ta bulloma

lamarin

duk abin duniya ya taru ya camera ta rasa

yaddah zatai ta

samu yarinyar ta saki jiki da ita ta’ amma

shegiyar yurinyar taqii yarda, don haka cikin

gagguwa ta gurzaya gidan Dashiya don neman

mafita. A lokacin da Fanne ta ke Sanar da

kawallinta abin da ya ke damunta .shiru ta _yi

tana jinta‘ har ta gama. sannan ta numfasa ta ce

da ita. " ' “Wannah ai abu ne'ma'i sauqi,’ da yaro

da’ dabba duk hanya daya»'akebi a‘samu kanSu

cikin ‘kwanciyar hankali- ba tare'da: an sha

Wahalaba ammafa ‘sai kin" yi hakuri domin‘sai

kin bi abin da zan gaya miki a hankali sannan'

kuma saurin fada ‘ba naki ba.ne';'.don intasan

halinki da sauri' karki dinga hantararta‘, jawo ta

jikinki 2akiyi ki; dinga nuna’ ’mata' kulawa kina

sassauta magana sannan ki daina yin mata

mummunan ‘kallo'wanda‘ kuWa idan; kina

harararta kokuma kina' bata tsoro da idonki ba‘

za‘ta taba sakin jiki da keba, ki dinga 'lallashinta‘

da ‘tarairayarta kamar kwai

dolé ki danne'Zuciyarld don ki samu‘ "daman

cinma‘ burinki sannan kuma ‘sai kin hada da

malamai' _‘sannan haqarki zata cimma ruwa,

.shirya na ra‘ka‘ki ~wajen wani wani boka wai

mai gani har ha'nji', wannan boka babu abin'da

,ba ya'”gani,aikinsa kamar yankan wuqane . Nima

wata kaWata ce- ta raka ni wajensa

naji dadin haduwa da bokan sosai gashi kuma ba

wani kudi ake bashi masu yawa ba. mutukar za

ki bi umaminsa to bukatarki saita biya".

naji bayananki, kuma zan yi amfani da su, amma

batun zuwa wajen bokan mu bari sai nan da sati

biyu. kafin nan Kannen Abbakar masu jinyarsa

sun tafi, domin kuwa idan suna nan ba zan samu

na sake na aiwatar da shirin nawa- ba, don akwai

su da sa ido gashi, kuma duk sun bi sun toshe

min hanyar da zan bi na‘ cimma burina”..

Dashiya ta ja tsaki, ta ce.

“Kar wannan abin da suke yi miki ya dame ki

Fanne, ke dai ki Ci gaba da haquri dasu har zuwa

‘lokacin da komai zai daidaita, inyaso daga nan

sai mu san' abin yi a kansu”. -

Fanne ta taBe baki, ta ce.

“Uhm, Kyale ni da su Dashiya, da sannu zan dinga

cin'ubansu cikin ruwan sanyi zan dinga dafa su,

ina dai da ni suke'Zancen, sai na daidaita musu

zama, ina nan ina musu tanadin wUlaqancin da

zan yi musu idan harhakana ya cimma ruwa, ke

dai kaWai mu'yi fatan Allah ya kai damo ga

harawa’

“Kawallina ke nan, har yanzu kina nan ‘da

'halinki”,

“To meza a fasa, mutuwa ko'hisabi? Kamar

yadda ki ka sani ne, ni Fanne ba na yafiya ba na

yi wa mutum afuwa, k0 ida kuwa a ce ya nemi da

na ‘yi masane

Sannan kuma ba na taba manta ranar daukar

funsa idan a ka yi min abu na Bacin rai wanda

har yasa rains ya baci komai daren dadewa sai

na rama shi, saboda ba zan taba samun

kwanciyar hankali ba . idan ban rama ba.'ko da

kuwa. ace ya dauki tsawon ; shekarune Wannan

abu da— Abbakar ya yi min tunda na. ke a duniya

ba a taBa yi min irinsa ba. Shi ya sa na ; lashi

takobi duk wuya duk runtsi sai na rama, domin:

shi ma ya ji irin abin da' na ji, i‘dan har ni ‘yar

halak‘ Ce a cikin uWata da ubana na fito sai na

tozarta Abbakar‘ kamar yadda-ya tozarta ni a

cikin dubban mutane. A ranar zai yi kuka da

haWayensa, kuma ya yayi' ‘nadamar'abin da ya

aikata min”. '

Cikin hikima da. kissa irin ta gogaggun‘mata'

wadanda suka kware a'harkar bariki, Fanne ta

samu; .ta shawo kan Khadija ta daina jin

tsoronta, ta saki jiki da ita, wanda yawancin

lokutazaka sameta zaune wajen Fanne, wani

lokacin ma wuni takeyi a wajen nata - ‘tana

wasanta' sai idan' dare ya yi ta nemi inda’

maha‘ifinta ya ke ta je kusa da shi ta kwanta.

A hankali a hankali ta dawo dakin Fanne da:

‘ kwana, ayanzu Khadija tazamo ‘yar’ dakinta a

wajenta take kwana abinci ma a baki Fanne ta ke

ba ta, sannan kuma ita ta ke yi mata wanka da

kanta, ta yi mata kwalliya sannan ba ta bari _mai

aikima ta yimata, hakama idan .- sunzo

kwanciaya sai Fanne ta lallaBa Khadija tayi bacci'

sannan ita ma ta ,ke yi, har goyata Fanne takeyi

kuma ba‘ta barima ta zauna a kasa,‘ ko a kan

kujera sai dai a kan cinyarta. Duk wata hanya da

fanne ta san 2a ta bi domin ta 'faranta mata rai

shi ta kebi, sam ba ta so ace an Bata wa Khadija

rai.

Wannan abubuwa da "Fanne ‘ta keyi wa Khadija

yana matukar Bata wa Momi rai, shi ya‘sa ma ta

ke jin tsanar"yarinyar a cikinzuciyarta, ga shi

kuma‘Fanné ta hana ta dukanta, duk wata kulawa

da Fanne ta ke ba wa Momi a da a‘yanzu ta

daWo da ita kan Khadija, Momi 'ta tsani ta bude

ido ‘ta ga Khadija "tana' rayuwa a - gidansu, Sam

bataga amfanin dawowar Khadija gidan nasuba

Sau’ da‘yawa idanta yi niyyar 'yi mata-mugunta

sai Fanne ta yi mafa waigi don ba‘ta yin. nisa da

inda Fannen take ‘zaune, haka kuma k0 unguwa

Fanne'za ta je tare ‘da ’ ita‘suke tafiya, ba ta

barinta a gida balle Momi‘ ta samu hanyar da za

ta ci 'zalunta. Sai dai tana yawan tsokanarta

da'baki, k0 kuma ta dauki' kayan wasanta ta

je‘waje. ta jefar, tana yin hakan ne duk danta

bakanta wa Khadija rai ita kuma da ya ke tana

da' ,sau‘rin‘ kuka idan irin hakan ta ‘faru sai ta

samu‘ waje ta zauna ta yi ta kuka har da birgima

irin na: sakakkun yara.’ Feanne‘ ce take dauke ta

ta‘yi ta aikin .rarrashinta har sai ta, ga ta

hakura, ta daina kukan ~Wani lokacin kuma

takama Momi da fada ‘kamar za fa doke ta;

wunin ranar duk za ta yi shi: ne tana mitar abin

da MOmi ta yi Wa Khadija.

abbakar kuma yanajin dadin hukuncin da

Fanne ta ke yanke wa Momi. sai dai kuma daya

daya daga cikin qannen .‘abbakrkar Wanda suke

jinyarsa a zuciyarsa bai yarda ’da wannan sauyin

da aka samu a gidan dan uwansa ba. domin

yana-zargin Fanne a kan akwai'wani munafurci

da ta ke qulla “ wa Ahbakar wanda ya lura kuma

shi din har yanzu _ - hai fahinci inda matar tasa

yasa a gaba ba, kuma ko'da a . ce ya gaya masa

ba yarda zai yi ba kasance warsa mutum ne shi

wanda ba .ya son gulma k0 tsegumi; kuma bai

cika daukar abu da muhimmanci ba idan ' wani

ne ‘ya20 ya'gaya masa. “yaf1 so ya‘ga abu da

idonsa, k0 ‘kumaya ji da kunnensa'kafin nan ya?

’ dauki mataki a‘ kai, saboda gudun aikata ba

daidai ba daga baya’ sanin‘ halayyar dan uwansa

shi ya' sa ya ja bakinsa ya tsuke, sai dai yana

binsuda addu’a-a cikin kowace sallarsa idan

ya‘yi, amma kuma yaqi yarda ya saki jiki da

Fanne kamar yadda ta ké so, ‘a‘_ wajen Allah

yadinga neman kariya daga 'sharrinta; wanda ya

lura da’cewa so take yi ta shirya musu gadar

zare idan sun hau kai' su fada ciki‘. Itakuma

anata‘bangarenba ta damu da‘ abubuwan da

yake-yi nata ba. dOmin jira‘ta ke yi lokaci ya ‘yi

tanuna, nasa cewa. ita din ba kanwar lasa bace

watanni uku hajia fanne ta kwashe tana

rike da Khadija, riko na 'amana da gaskiya,‘ ba‘

ta kaunar abin da Zai bata wa yarinyar rai, k0

quda ba , ta so a ce yana sauka aljikinta.

Yarinyar ta gama sakin jiki da ita, da ya ke ba ta

da wayo sosai a lokacin har ta .fara

manta'mahaitiyarta ta asali, sai Kibartala ke yi,

domin ~ba tada damuwa.

Mama take kiran Fanne kamar yadda ta ji

Momi‘tana‘cewa da ita, ita kuma duka. gidan

Gimbiya suke ce‘ mata, bakin Abbakar suka bi da

ma tun can baicika kiranta da sunanta na asali

ba, sai. dai ‘ya ce da ita Gimbiya, wani-

lokacinkuma idan. yana cikin nishadi har yana

Kara mata da_ gimbiya yar sarki, a kai guda daya

a karbo dozin, sai mai gudan ya yarda. ’Zuwa

yanzu Abbaka‘r ya gama yarda’da cewa, k0 ya

mutu'Fanne za, ta iya riRe. masa amanar‘

gimbiyarsa, a wani' ,Bangaren kuma godiya ya ke

yi wa Ubangiji da Ya amshi addu’arsa da ya

dauki tsawon' lokaci yana yi' a kan Fanne, wani

lokaci Sai ya afka Cikintunani. Oh Allah mai

iko,'Mai kuma‘ yadda _Yaso duk shekarun daya

shude yana ’zabga addu’a a kan Allah ya shiryi F

anne ba ta shiryu ba sai a yanzu da‘ wannan

abun'ya faru, lallai Allah shi ne ubangijin gaskiya.

" . ‘

‘Sai ‘dai kuma wani kayan‘ haushi har yanzu

tana nan da iya shegen nata data Saba, babu

babu abinda ya ragu na data cikin halayyarta

‘saima karuwa da

ya yi. A bangaren momi ne’ Abbakar ya ke ganin

cewa‘ akwai matsala babba ma kuWa. don sau

da _yawa;

Gimbiya ta. kan kawo~ masa Kararta, akan ta

taba_. mata kayan‘ wasanta k0 :kuma yana daga

daki 'a, kwance ya dinga jiyo muryar gimbiya

tana kuka,‘ duk kuma yawanci ita da Momi ce

domin bamai Bata mata rai a gidan sai ita Idan

irin haka ta faru rarrashin' Gimbiya ya ke‘yi tare

dA'ba ta‘ hakuri, a‘,duk l0kacin da: ta shigo

wajensa. A can Kasan zUciyarsa kuma haushin.

Momi ya ke ji .tare da yin 'Allah wadai da'

wannan hali nata na cin zalin, don ya sani haka

kawai ta ke musgunawa marainiya ba‘tare da ta

yi mata laifin ko‘mai‘ ba haKiqa abin yana

matukaqAr yi'masa Ciwo, don dai ba shi da

yadda zai yi'ne ya rama wa gimbiya abin da ta yi

matanne kawai saboda‘har-zuwa- wannan

lokacin ba' ya iya miKeWa tsaye da’ kansa,

amma kuma jikin nasa da sauki, domin raunukan

‘da. suke jikinsa duk .sun warke, hatta karayar da

ya yi a‘ hahnunsa ya‘ warke, sai' dai

’qafafuwansa ne kawai da ba suwarke ba, 'shine.

ma dalilin da ya sa ba ya‘ iya. mikewa tsaye,

ammna yana yin kokari ya yi ja da‘ gindi idan

yana jin matsuwa ‘zai je bandaki, shi ya" sa ya

ce da qannensa su tafi gida tunda 'ya ji sauki,‘

wani lokaci idan' Momi .ta tsokani Khadija. tana:

kuka, sai .ya ji' kamar‘ ya kirata ‘ya yi mata fada

tare da mata nasiha a kan ta dai‘na aikata wa

‘yar uwarta abine

da ta ke yi, domin kuwa qanwarta ce da suke

tsatso daya, wanda duk dUniya ba ta da ,wata

‘yar uwa da ta keda alaka da ita Khadija, amma

kuma sai wani Bangare na zuciyarsa ya hana shi

aikata hakan.

“Ka yi hakuri, watarana sai labari, yarinta ce ‘ta

ke damun Momi shi ya sa ta ke yin abin da ta ga

dama,'duk ranar da suka girma irin hakan ba zai

dinga 'faruwa 'ba, kuma ma ai idan har ka kira ta

ka yi mata fad‘a a kan Khadija uwarta za ta iya

fassara‘ maganarka da Wata manufa daban,

wanda kuma' kai I ha haka ka ke nut] ba,

watakila ma a je gandun da za ta ce ka dauki

‘yarka ka kai ta Wani waje ita ba .za ta iya riqe

maka ba, don haka maganin kar a yi, kar a fara,

domin kuwa ka san matsayin da Momi ta ke ' 'da

shin cikin Zuciyar Fanne ka bi ta a hankali cikin

'nutsuwa‘ ku zauna 'lafiya, saboda ka san' ‘halin

mutuniyar taka sarai, kamar yunwar cikinka, dan

qaramin aikinta ne ta botsare “maka, duk da‘

cewa A yanzu ta yi laushi

A kullum F anne. ta je unguwa Sai' ta-sayo wa

Khadija kayan wasa, don haka ta ke da su kala-

kala, bebin wasa kuma tana da shi ya kai goma.

duk da cewa Momi tana dauka ta kai waje ta

jefar- mata, k0 kuma ta ba wa yaran makotansu

ammana, hakan bai

hana Fanne sake sayo mata wasu



Post a Comment

0 Comments