Soyayyar mutum da aljan hausa novels

    AHMED B. SARDAUNA

.

FACEBOOK ACCOUNT👇👇

(Ahmed bello sardauna)

WHATSAPP NUMBER👇👇

(08169047840)

.

NOTE: bana tura littafai a private, amma inada group na whatsapp da facebbok.


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 



*

Page *1*



_Bismillahir rahamanir raheem._


Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Alhamdulillah dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki. Wanda ya bani dama da ikon fara rubuta wannan takaitaccen labari mai ɗauke da rikicin soyayya. Labarin MARUBUCI labari ne da zai wayar wa masoya kan su domin gane yadda daraja da kuma kimar soyayyar gaskiya take. Da kuma yadda ake sadaukarwa kan soyayya da sallama rayuwa ga biyan bukatar masoyi. Jigon wannan labari shine soyayya darajarta da kimar ta. Da fatan masoya zasu biyo ni sannu a hankali domin kwasar romon dake cikinsa. 



Bazan iya kirga ku ba masoyana ko kuma groups da litattafai na suke zuwa, sai dai ina so ku sani sakonnin ku na zuwa gare ni bisa kari kuma ina godiya da kulawa. Sannan ina so ku sani ina kaunar ku ina kuma jin daɗin shawarwarinku gare ni Allah ya bar zumunci 🤝

__________

_______

____

__

_ farkon labari...




Zaune yake bisa wani dutse wanda da yayi sama kaɗan da kasa, karkashin wata bishiya mai yawan ni'ima da yalwar sanyi ga wata ni'mtacciyar iska dake kaɗawa. Wannan bishiyar a bayan gari take gurin da Muhsin ya mayar tamkar fadar sa ko wata majalisa ta zama musamman idan yana so ya jarraba fasaharsa. Yau ma kamar kowane lokaci yana jingine da jikin bishiyar hannun sa rike da farin littafi da alkalamin rubutu. Ya ɗora alkalamin bisa littafin kamar mai yin rubutun sai dai har yanzu ya kasa rubuta koda harafin 'A'  a jikin littafin. 


Tun yana yi da sauki har ya dawo yi da dukkanin karfin zuciyarshi amma abokiyar gwagwarmaya kwakwalwa ta ki ta bashi haɗin kai kamar kowane lokaci dai. Idanunsa suka cicciko da kwalla jikinsa ya hau kyarma yayi watsi da littafi har ma da alkalamin, tsananin takaici ya kama shi. Ya shiga kuka da takaicin kasancewarsa dakiki mai kunshe da babban buri. 


Allah sarki Muhsin. Ni da nake zaune a gefe ina kallon inda ke faruwa na share kwalla, tsantsan tausayinsa ya kara kama ni. Duk da cewa nasan baya gani na amma hakan baya sanyayyar min guiwa ko dakile zuciyata ga jin tausayinsa da kuma kara nutsawa a tafkin kaunar sa. 


Kuka yake sosai yana buga kansa a jikin bishiyar nan kamar yadda ya saba yi idan irin hakan ta kama shi. Da sauri na mike domin dakatar da shi tun bai kai ga illata min kansa ba. Cikin dabaru da hikima da kuma kwarewa irin tamu ta sarrafa bil'adama na dakatar da shi ga abinda yake yi. Sai dai har yanzu bai daina kukan ba. Yana yi ina yi an rasa wanda zai rarrashi wani. Ban san ya zan yi ba, damuwar Muhsin na tada hankalina kamar yadda zubar hawayensa ke haifar da fitar nawa hawayen. Tsananin so da tausayinsa na neman hallaka ni, rashin sanin hanyar da zan bi dan in taimake shi na neman illata zuciyata. Yau kimanin shekaru ashirin kenan ina bautar da rayuwa ta ga soyayyarshi. Duk da cewa bai ma san ina yi ba amma na taimaki rayuwarsa ta hanyoyi masu yawa... Muna haɗuwa da Muhsin har ma na labarta masa irin kaunar da nake masa amma cikin mafarkin shi ni kuma zahiri na. Har yau bai ji a ransa cewa da gaske ni ɗin wata ce ta gaskiya ba, ya ɗauki mafarkin da yake yi dani tamkar irin sauran mafarke-mafaken da ake yi a cikin bacci. 




*Wane ne Muhsin?*


Tsayayen saurayi kyakkyawa na gaban kwatance ɗan kimanin shekaru ashirin da biyar da haihuwa. Fari sal mai matsakaicin tsayi da faɗi.


Muhsin Al'hussain shine cikakken sunan sa. Ɗa na biyu a gidan sarautar garin gabas wanda yake cikin nahiyar birnin lumai. Garin gabas babban birni ne wanda ya kunshi mutane daban-daban maban-bantan akidu da addinai. Mahaifin Muhsin mai martaba sarki Al'hussain shi ne yake rike da mulkin kasar a yanzu, wanda shima gadon sarautar yayi a gurin yayansa yayan nasa kuma ya gada a gurin iyayensa haka tsarin yake. Mai martaba sarki Al'hussain shi da iyalansa duka ma biya addinin musulunci ne. Yana da mata biyu da ya'ya biyar inda Muhsin ya kasance na biyu a cikin su. Yayansa ɗaya Kabir sai Fatima karamar kanwar su. Su ne yan' ɗaki ɗaya, wato ya'yan uwar gida gimbiya Suhaima. Sai ya'yan ɗakin gimbiya Amrah su biyu Suhaila da Aliyu. 


Duk cikin waɗannan ya'yan Muhsin ne kaɗai ya fito daban. Dukkanin su suna da ilmi da kwazon karatu yana shiga kansu sosai, amma shi kam sam kansa baya ɗaukar karatu sau tari a magana ma in yaje wani matakin makalewa yake yi. A wasu lokutan yana magana yana kuka abin tausayi. Akwai kwazon maida hankali da tsare litattafai da ido yana karantawa amma duk abinda ya karanto sai dai ya tsaya iya bakinsa baya kaiwa ga kwakwalwarsa balle ta ajiye masa shi duk kuwa da irin ko'karin da yake na ganin ya saka karatun a kansa. 


Hakan ba karamin raini ya ja mishi ga sauran kannensa ba kai har ma da waɗansu ya'yan sarakan idan aka haɗu wawa dolo mai ɗanyen kai babu abinda basa ce masa. Matsalarsa ta gawurta tun iyayen na ɗauka laifinsa ne har suka dawo suka saduda suka fauwala al'amuransu ga Allah. 


Sai kuma wani iko na Ubangiji da ya yi a kansa, ya  kawo tsananin so da burin zamowa MARUBUCI ya saka mishi a rai, a duniya babu abinda yake burge Muhsin kamar rubuta  kirkirarren labari. Kamar yadda babu abinda yafi so kamar ya ga kansa a matsayin MARUBUCI.  Lokuta da yawa yakan ji kamar yana tsara labari a zuciyarsa amma idan yaje ya zauna da burin son rubutawa sai kwakwalwarsa ta hargitse ta dagula masa komai. Ya dawo kamar wani zautacce baya kula kowa ba kuma ya shiga kowace irin sabga sai dai ka ganshi yayi lamo yana nazari a kullum Muhsin cikin tunani yake a koda yaushe hawayensa zuba suke yi. Ya rasa abinda yasa ya kasance haka.


* * * * * *

Ni kuwa ikon Allah ne ya haɗa ni da Muhsin, da gani ɗaya naji na kamu da tsananin tausayinsa tun yana yaro ɗan kimanin shekaru biyar a duniya. Tun a lokacin na fara shiga rayuwarsa ina son taimakon sa amma matsalar sa ta sha gaban tunani da sani na.


Alakata da Muhsin tayi girman da duk wani ɗan'uwana na kusa da na nesa yasan ina tare da shi kuma ina matukar kaunarsa. Babu yadda iyayena basu yi ba dan ganin sun raba tsakani na da Muhsin amma abin ya gagara, tun suna jin haushi na har suka dawo suka hakura. 


* * * * * 


Ni jinsin Alajan ce wadda ta fito daga babban gida mai daraja a can tamu nahiyar. Ni kaɗai Allah ya azurta iyayena da haihuwa kuma mahaifina babban Malamin addinin musulunci ne a can, shi yasa dukkan mu muka zamo mabiya addinin. 


Babu irin rokon da ban yiwa mahaifiyata da mahaifina ba kan su taimaka in sunada wani taimako ko masaniya akan lalurar da Muhsin ke ɗauke da ita su taimaka su gaya min amma sun ki. Duk kuwa da cewa inada yakini cewa babana Malam ba zai rasa masaniya akan maganin warakar wannan cutar ba. 


Wannan kenan. 



Cigaban labari... 


* * * * *


Dogon numfashi na koma ja a karo na barkatai, ina karewa masoyina Muhsin da bacci ya sace kallo. Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, yana fidda numfashi slowly. Na rufe dara-daran idona na koma buɗe su a kansa. Ga namiji har namiji amma wananan lalurar zata nakasa shi. Wani irin shaukin son sa ne ka kara ninkuwa a raina yana daɗa mamaye duk wata kafa ta sadar da tunanina. Nan da nan na yanke shawarar tafiya na mika ajiyayyun sakonnin soyayyata ta kafar sadarwar da na shirya mana ta haɗuwa da masoyina ba tareda ya san ko ni wacce ba a cikin mafarki.  Dama haka na saba a duk lokacin da shaukin kaunarsa ya motsa mini, nakan zama tamkar inuwa na ratsa jikinsa harma da tunaninsa sai ya ganni kamar yana mafarki ta nan muka saba da Muhsin sosai kuma ta nan ne nake sanar mishi irin son da nake masa. Ta wannan hanyar ne nake farantawa Muhsin ina ɗebe masa kewar rayuwar kaɗaicin da yake. Domin daga ni sai mahaifiyarsa gimbiya Suhaima mu kaɗai ne muke shiga rayuwarsa kuma muke ko'karin faranta masa domin mahaifinsa baya da lokaci koda yaushe yana cikin fada yana fama da talakawa da matsalolinsu. 


Na lumshe idona cike da shauki sannan na yunkura da nufin aiwatar da nufina, na shiga jikin masoyina domin sada zumuncin kauna. Kamar daga sama naji an yi gaggawar riko kafaɗata ta baya ana faɗin 


"dakata Na'eema" 











*Nasmat*  ✍

[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                     *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 



*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

Yar'mutan 

  Arkilla✍

____________






📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com




*Page 2*





*Alhamdulillah ina godiya ga Allah (s.w.a) kuma ina godiya gareku bisa yadda kuka kar6i wannan labarin kuma kuke kara karfafa min guiwa a kan sa. Na gode! Na gode! Masoyana Allah ya bar min ku a duk inda kuke. One love 🤝*








Wannan dakatarwar da aka yi min ba karamin 6ata mini rai tayi ba, na juyo a fusace dan ganin wane ne wannan da yayi min irin wannan katsalandan a cikin rayuwata. "Ummy"  na faɗa cike da mamakin ganin mahaifiyata a gabana, wadda ban ta6a tsammanin ta a yanzu kuma a nan ba. Ta zuba min fararen idanunta fuskarta cike da damuwa. Wannan ne ya kara sanyayar mini da ga66an jikina. 


"Ummy lafiya?" na tambaye ta cikin karfin hali da dakewa. "wai ke wacce irin kafaffiyar yarinya ce Na'eema?, kin kuwa san irin wahalar neman ki da aka sha yau? Duk faɗin nahiyar nan babu inda ba'a watsa Barade neman ki ba, ashe wai kina nan gun wannan bil'adaman kina gadin sa." maganganun Ummy basu bani mamaki sosai ba domin na saba da jin ire-iren su har ma da waɗanda suka fisu  daga gareta a kan Muhsin. Abu ɗaya ne ya tsaya min a maganarta inda take cewa 'babu inda ba' a watsa Barade nema na ba'. To yau kuma me na yiwa Sarki da har za'a baza Baradensa nema na?. 


Ummy ta kalle ni rai a 6ace "to tunanin me kike kuma? Maza ki zo mu tafi tsawon awanni Sarki da jama'arsa suna zaman jiran ki." tana kaiwa nan ta kama hannuna daga ni har ita muka 6ata 6at!. 


Al'amura sun cakuɗe a matashiyar kwakwalwata, ban gama warware sarkakiyar farko ba Ummy ta koma saka ni a wata. To me kuma zai sa sarki da jama'arsa jira na?. Ina cikin wannan tunanin ne nida Ummy muka bayyana a babban ɗakin baki na mahaifina Malam. Inda naci karo da wani sabon abin mamaki wanda ya haɗu da maganganun Ummy ya cure min a kwakwalwa. Duk da cewa waɗanda da naci karo da su ba bakin fuska bane a gurina, amma ina mamakin taruwar su a gidanmu kuma har ake nema na.


Babu yanda na iya haka na adana tambayoyi da mamakina, na zube kasa na kwashi gaisuwa ga sarkin Aljanu na nahiyar baki ɗaya sarki Shadad. Da uwar gidansa Ummu Haiman da kuma shi kansa babban ɗan nasu Haiman. Suka amsa mini gaisuwar cikin sakin fuska da kauna kamar dai yadda suka saba musamman Haiman wanda shi kallon so ne karara yake jifa ta da shi. Ni kuwa na basar nayi kamar ban san abinda yake ba. Sauran kuyangin gimbiya Ummu Haiman da fadawa yan rakiyar sarki suka zube kasa suna gaishe da ni. Na amsa cikin nuna kulawa sannan na mike na matsa can kusa da kujerar da mahaifina yake kai na zauna dab da kafafunshi ina mai sunkui da kaina alamar girmamawa gareshi. 


Baba Malam yayi gyaran murya ya 6oye 6acin ransa na nema na da aka yita yi tsawon lokaci, saboda yasan na wuce ayi mini faɗa a gaban sarki. Duk kuwa wanda yayi to zai ga 6acin ransa, domin sunan mahaifiyarsa gareni. 


Ba tare da ya kalle ni ba ya fara da godiyar Allah sannan ya fara magana kamar haka: Allah ya ja zamanin sarkin sarakai ga yar' taka nan an samo ta. Saboda haka sai ka yi mata bayanin maganar da ka zo da ita domin taji daga gareka. Sarki Shadad ya gyara zamansa ya dubi inda nake zaune fuskarsa ɗauke da murmushi yace "maraba dake ya'ta kuma uwa'ta Na'eema, kamar dai yadda kika sani yaron wajena Haiman yana matukar kaunar ki wannan ba maganar yanzu bace abu ne da kowannen mu ya sani. To bisa wannan ne yau na ɗauko kafa da kaina nazo neman auren ki yake wannan yar mai daraja da cikar kamala da fatan zamu sami amincewa, haɗin kai da kuma goyon bayanki." jin ya kai aya a zancensa yasa na ɗago a hankali na fara da kallon iyayena waɗanda nake ga kamar basu yi mini adalci ba, na nemo ni da suka yi suka zaunar a gaban sarki har ya tunkare ni da wannan magana a matsayinsu na waɗanda suka san sirrina sama da kowa. Sannan na rausaya kaina na kai duba ga yarima Haiman wanda yake jin kansa kamar a aljanna saboda tsananin daɗi da farin ciki na abinda yaji mahaifinsa ya ambata. Kasancewar a rayuwarsa babu abinda yake son ji da gani sama da ni. Wani kasaitaccen murmushi ya sakar min mai kunshe da sakonnin so da kauna. Hakan yasa nayi gaggawar kawar da kaina gareshi. Duk da cewa nasan yarima Haiman na tsananin kaunata amma hakan bai ta6a sawa na kalle shi kallo na masoyi ba, balle har na yi tunanin kasancewa mallakinsa. Ni kam bil'adaman nan da basa so Muhsin shi kaɗai na ta6a jin son shi a zuciyata kuma shi kaɗai nake ji zan yi farin cikin kasancewa da shi. 


Jin shirun  yayi yawa ne yasa mahaifina ya fara magana "kin yi shiru Na'eema?" na kara yin kasa da kaina dan ban san kalar amsar da zan basu ba, na tabbata yin shirun nawa zai fi buɗar bakina zama alkhairi domin bana so iyayena su yi kunya ta dalilina.


Can na jiyo murmushin mahaifina yace "Alhamdulillah dama na san ya'ta ba zata watsa mini kasa a ido ba. Allah ya taimaki sarkin sarakai a matsayina na mahaifin Na'eema na bawa yarima Haiman aurenta. Kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci a shirye nake da aurar da ita gareshi, yanzu wuka da naman suna hannunka."


Kaina na sunkuye a kasa ban san lokacin da na ɗago shi ba ina kallon fuskar babana Malam. Na rumtse ido cikin tsananin karfin hali da jarumta domin yadda naji saukar kalaman nashi sun fi kama da yayyafin ruwan narkakkiyar dalma bisa fatar jiki. Duk da cewa baba Malam ya gano halin tashin hankalin dana shiga amma sai yayi biris kamar ma bai san ina yi ba. 


Sarki Shadad ya saki fara'a cikin jin daɗin maganar ya kalli babana "na gode Malam Allah ya kara girma da ɗaukaka, Ubangiji yasa auren Haiman da Na'eema alkhairi ne." "ameen" fadawa da kunginsu suka amsa. Da haka suka yi sallama zasu wuce inda yarima Haiman ya nemi a bar shi yana son magana da ni. 


Takaici da bakin ciki kamar zasu kashe ni amma ya zan yi? Har in koma ga Allah bana fatan bijirewa umarnin iyayena. Wani ke6a66en lambu dake can bayan gidanmu muka tafi da yarima Haiman wanda duk wani motsi nawa bisa kwayar idonshi. Duk wanda ya kalle shi a yau ya san yana cikin farin ciki mara misaltuwa. Sa6anin ni da kallo ɗaya za'a gano ina cikin damuwa. Domin duk yadda na kai ga son farantawa iyayena ba zan iya danne damuwata in hana mata bayyana ba. 


Muka zauna kan lallausar shimfiɗar dake baje bisa korayen ciyayi a bakin wata korama. Na kalli wurin da ni'imarsa, hakika wannan shine wurin da ya kamata a ce masoya sun kasance a cikinsa yayin yin hira irin ta soyayya. Amma ni gani a ciki ni kaɗai ba tare da masoyina ba. Na koma kallon yarima Haiman idanunshi a kaina, na kauda nawa idon ina jin haushin kasancewa ta da shi a wannan wurin. 


Ganin banida niyyar yin magana yasa ya buɗi bakinsa cike da tsumi na soyayya yace "yake masoyiyata Na'eema shin har yanzu kina nan a kan bakarki ta ki na?, naga duk wannan batu da ake bai sa farin ciki ko kalilan a zuciya da kyakkyawar fuskarki ba."  


Na kawar da kaina gefe sannan na buɗi bakina wanda tun ɗazu nake ko'karin kulle shi, saboda na tabbatar duk abinda zai fita a cikinsa yau ba mai daɗin saurare bane. Nace... 










*Nasmat*  ✍

[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                    *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 



*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

Yar'mutan 

  Arkilla✍

____________



AHMED B. SARDAUNA

.

FACEBOOK ACCOUNT👇👇

(Ahmed bello sardauna)

WHATSAPP NUMBER👇👇

(08169047840)

.

NOTE: bana tura littafai a private, amma inada group na whatsapp da facebbok



📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com




*Page 3*





Alaka alaka ce kamar yadda so yake rikiɗewa ya zama kauna. *ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION* Na yarda da kaunarku GAREMU. Babu shakka aminci ne mai karfi tsakani mu *ZAMANI WRITERS* daku. Fatan mu a nan Allah ya bar zumunci da kaunar juna. Nasmat da ɗaukacin members na *ZAMANI* suna yin ku irin totally ɗin nan, ku huta 🤝 *Shamsiyyah Salis* naki daban ne Allah ya kara basira da zakin hannu. 






Cikin zafin rai da ɗacin zuciya "kaicon ka yarima Haiman, shin me ka yiwa wannan zuciyar taka ne da har take ingiza ka take tursasa ka son wadda kake da yakinin cewa bata sonka ba kuma zata ta6a sonka ba?." dama nasan a rina. A madadin Haiman yaji haushin kalamaina sai na tsinci wani lallausan murmushi a kan fuskarshi. 


Al'amarin da ya kara zafafa zuciya ta kenan, da har zan koma wurga masa wata mummunar maganar sai zuciyata tayi gaggawar kwa6a ta, tare da yi mini tuni a kan ko wane ne Haiman. Nan da nan sai na sassauta fushina na fara kirkirar abinda na san shi kaɗai ne zai sa Haiman ya saurare ni kan wannan batu. Kuka na fara yi ina zubda hawaye. Ai kuwa da sauri Haiman ya tashi daga kishingiɗar da yayi ya zauna da kyau ya fuskance ni, cikin tsananin ruɗani. 


Dama na sani idan kalamaina basu ruɗa shi ba kukana zai nutsar da shi. Sai ya shiga magiya yana roko na a kan in taimaka in daina kukan nan zai fahimce ni. Ni kaina ina mamakin tashin hankalin da Haiman ke shiga idan ya ga zubar hawaye na wannan shi ne dalilin da yake sawa na yarda cewa Haiman *son gaskiya* yake yi mini. Amma fa sanin  hakan bai ta6a sawa na ji tausayinsa ko da na rana ɗaya ba, wannan ne yake tabbatar min cewa bana son Haiman ba Kuna zan ta6a sonsa ba.


Na kalli yadda hankalin jarumin ɗan sarkin ya tashi saboda ganin zubar hawayena. Tabbas so na musamman ne, duk wanda kaga bai girmama so ba to bai tsinci kansa a ciki bane. 


"Haiman" na kira sunansa cikin muryar kuka. Ya amsa idanunshi da nutsuwarshi duk suna gareni. "Haiman wallahi bana sonka, ba kuma na tunanin zan so ka koda a gaba ne. Ban san ya zan yiwa zuciyata ta so ka ba da nayi Haiman. Dan Allah ka taimake ni ka bar ni, ina da wanda nake so. Muhsin shi kaɗai zuciyata ta yarda da shi a matsayin masoyi ka taimaka min yarima." na tashi na tsuguna a gabanshi ina ko'karin kama kafafunshi. 


Wani irin zafin kishi ne ya daki zuciyar Haiman ya mike tsaye hannunsa dafe da kirjinsa ya juya min baya. A lokaci ɗaya wani zazzafan gumi ya fara yanko masa ta ko'ina a jikinsa. "ki yi hakuri Na'eema tsakanin zuciyata da taki da akwai wata dangantaka mai karfi wadda na tabbata kema da sannu zaki santa, kuma kema zaki fara so na a lokacin da wannan dangantakar ta bayyana ga taki zuciyar. Ina son ki Na'eema ba zan iya rabuwa da ke ba. Zan iya zama dake koda bakya so na, zan jira zuciyarki har sai ta so ni koda kuwa lokacin zai kai ga lokacin tsufana ne, zan kasance mijinki har zuwa lokacin. Ni kam ba zan iya rabuwa dake ba. Zan aure ki in kuma baki dama ki ci gaba da zama a gidana har zuwa lokacin da zaki so ni. Zan zama bawa gareki Na'eema ina ji a raina saboda ke kawai aka halicce ni, na yarda da so ɗaya ne tak! Kuma shi nake miki Na'eema."


Yana kawowa nan a zancensa ya bar wurin ba tareda ya koma waiwayen inda nake ba. Wani wahaltaccen kuka ne ya su6uce mini, na shiga rera shi kamar wadda aka ce iyayenta sun cika. Ina cikin kukan ne iyayena suka bayyana a gabana cikin 6acin rai. Na kalle su sau ɗaya na sunkuyar da kaina. Malam wanda dama a cike yake da takaicina ya fara yi mini faɗa kamar zai dake ni. 


"Nikam ban san yadda kike so ki maida ni ba Na'eema, da na ɗauka haukar da kike na son Bil'adama kuruciya ce sai gashi abin naki sai gaba-gaba yake, shin me kika maida kan ki ne? Ko dai bakida hankali ne Na'eema? Banda shi a ina kika ta6a ganin an haɗa auren Bil'adama da Aljan? Koko haka kike tunanin zamu zuba miki ido ki kare rayuwarki ta har abada babu aure kina bin bayan Bil'adama?."


Ummy ta kar6i maganar da cewa "Wata kila a kanta za'a fara, banza mara hankali to wallahi tun wuri ki nutsu ki dawo hayyacinki maganar aure babu fashi kuma nan kusa bada nisa ba."  a tare suka 6ace rayukansu a 6ace. Hankalina ya koma tashi damuwata ta koma ninkuwa ko kaɗan bana son ran iyayena yana 6aci ta dalilina, na shiga uku ni Na'eema ya zan yi da rayuwata?. 


Sai na koma fashewa da Kuka na faɗi kwance bisa shimfiɗar nan ina ayyanawa a raina cewa inama mutuwa zata zo ta  ɗauke ni da na huta bakin ciki da kallon kaina a matsayin matar wanin da ba Muhsin ɗina ba.










*Nasmat*  ✍

[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                   *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 



*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

Yar'mutan 

  Arkilla✍

____________






📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com





*Page 4*





Wannan shafin ga baki ɗayansa sadaukarwa ne gareki kawar kirki. *QUEEN HAFSY* aminta ta da ke ta musamman ce, ina yi miki barka da dawowa tawan Allah ya bar zumunci da kaunar juna. 








Lokaci mai tsayi na ɗauka ina wannan kukan ganin babu abinda zai kare ni da shi yasa dole na hakura na rarrashi kaina na mike na nufi ɗakina. 


Duk tsananin da nake ciki sai da naji saukar ni'ima da sanyi a zuciyata, lokacin da idanuwana sukayi tozali da manya-manyan hotuna na zanen fuskar farin ganina Muhsin. Waɗanda ke makale a kowace kusarwa ta ɗakin. Duk da ba can na nufa ba amma sai naji zuciyata ta jagoranci gangar jikina ta jani zuwa gaban hoton. Na tsaya kikam ina karewa Muhsin kallo wanda yake zaune da kayan aikinsa wato littafi da Alkalami yana son fara rubutu. Nice na zana wannan da hannuna saboda babu inda Muhsin yake min kyan gani kamar in gan shi a karkashin bishiyar nan yana gwada fasaharsa ta rubutu. 


Na shafi fuskarsa ta jikin hoton na fara magana cikin shaukin so dan a lokacin ji nake kamar Muhsin ɗin ne a gabana. "Muhsin kasan ina sonka ina kuma kaunarka. Amma gashi ra'ayi na yasha bam-bam dana iyayena. Muhsin bazan iya bijirewa iyayena ba, kamar yadda nake ji bazan iya rabuwa da kai ba. Ya kai masoyina hakika rayuwata tana cikin hatsari, wanda ni kaina ban san makomarta ba. Sai dai ina da buri a kan ka Muhsin. Koda ace ban aure ka ba, ban kuma kasance da kai ba, na so ace na cika maka babban burinka ta yadda har abada zan kafa hujja a zuciyata cewa na taimaki masoyina wajen zama abinda yake so ya zama. Muhsin in dai ban sami ko ɗaya daga cikin waɗannan ba zan iya mutuwa."


Na kifa kaina jikin hoton ina zubda hawaye. Can na ɗago kai na sumbace shi sannan na shiga tunaninsa shin ya tashi daga bacci ya tafi gida ko dai yana nan 'fadarsa'? Karkashin bishiyar nan nake nufi domin nan ne fadar masoyina. 


Nan da nan sai naji zuciyata ta kwaɗaitu da son koma ganin fuskarsa. Juyi ɗaya nayi na 6ata sai gani na bayyana karkashin bishiyar nan Amma ban sami Muhsin ba.  Wannan yana nufin ya tashi kenan. Ban jira komai ba na nufi gidansu. Kai tsaye ɗakinsa na bayyana nan ma wayam baya nan. Hakan bai sanyayar min guiwa ba na koma 6acewa sai ɗakin mahaifiyarsa gimbiya Suhaima. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke nan da nan fuskata ta wadatu da kawataccen murmushina. Badan komai ba sai dan ganin zumar rayuwata Muhsin. Yana kwance bisa wani lallausan kilishi wanda ke shimfiɗe a faffaɗa kuma kawataccen ɗakin. Yayi matashin kai da cinyar mahaifiyar tashi tana shafa kansa. farar mace mai farar zuciya.


Can na sami wuri na zauna gefen su ina kallon su kuma ina sauraron maganarsu gwanin sha'awa. Muhsin ya kalli mahaifiyarsa yace "yake ummana shin wai ni babu wata hanya za zan bi in samo maganin wannan lalurar dake damuna?" hawaye ne suka cicciko idon Suhaima, tayi saurin share su tun kafin su fito. Sannan ta kalli ɗan nata mafi soyuwa a cikin zuciyarta tace "koda akwai ta banida sani a kan ta Muhsin, ni kaina da ace na san wata hanya ta samun warakar ka wallahi da na bita na samo maka koda ko zan rasa rayuwata ne." da sauri Muhsin ya kai hannunsa ya rufe bakin ummansa "a'a mahaifiyata, da dai ki mutu kam gwara na tabbata dakiki in yi ta zama a haka har karshen rayuwata." Suhaima ta koma share hawaye tace "kawai dai babu ne ɗana amma wlh da babu abinda zai hana ni binta, Muhsin ina son ganin cikar burin nan naka, ina son ganin ka zama cikakken *MARUBUCI* Amma ban san ta yadda hakan zai kasance ba." 


Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "inaga hakan ba zai ta6a yuwuwa bane, inaga ba zan ta6a zama bane wannan shi ne dalilin da yasa Allah ya toshe min kwakwalwa. Amma kam ina son Rubutu Ummana." 


Ba umman Muhsin ba ni kaina saida hawayen tausayinsa suka zubo mini. Ta rungume shi cikeda so da tausayinsa "zaka zama ɗana, insha Allahu wata rana zaka zama." gaba ɗaya ɗa da uwar kuka suke yi wannan shine abinda ya kara zaburar da zuciyata kuka nake sosai ina tunani shin ta wace hanya zan iya taimakon Muhsin? Tabbas ya kamata ya zama amma ta yaya?. 


6acewa nayi daga ɗakin gimbiya na bayyana gidanmu. A wannan lokacin na gama yanke hukunci babu tsoro ko fargaba a tattareda ni. Na tabbata wannan ita ce damata ta samun abinda nake so daga gare su. Ganin babu kowa a mazaunin mai kama da fada yasa na kutsa kaina izuwa ɗakin baba Malam na shiga da sallama. 


Yana kishingiɗe bisa abin sallarsa ya amsa mini sallamar fuskarshi na kallon wani wurin daban. Hakan ya tabbatar mini cewa har yanzu mahaifina fushi yake dani. Na tsuguna ɗan nesa kaɗan da inda yake zaune. Nace "dan Allah baba kayi hakuri, ka sani sarai bana kaunar duk wani abu da zai zo ya 6ata min ranku kaida ummyna." nayi shiru ko zai ce wani abu amma baba bai ce komai ba. Hakan yasa na kara ɗorawa. "Baba dan Allah ina rokon wata alfarma daga gare ka, na yarda da za6in ku zan auri Haiman zan kuma so shi. Amma ni kuma ina bukatar ku cika mini burina kafin wannan auren." sai a lokaci baba ya ɗago ya kalle ni fuskarsa ɗauke da murmushi "dama nace ko canja min ke aka yi ne?  Domin ni a nawa sanin Na'eema na bata tsallake umarnina balle ta kai ga bijire mini." "ai har abada ba zan ta6a bijirewa umarninka ba baba." na koma faɗa cike da biyayya da nuna ya isa da ni. Mahaifina ya ji daɗin wannan maganar dan sai da ya tashi daga kishingiɗen da yake ya zauna yana fuskanta ta. Na saci kallon fuskarshi sai na ganta ɗauke da murmushi nima murmushin nayi bakina ɗauke da addu'ar Allah ya taimake ni yasa yau in sami nasara kan mahaifina. 


Babana ya katse mini tunani da tambaya. "Mene ne wannan burin naki da kike son cikawa kafin aurenki da Haiman Na'eema?" duk yadda naji na dake d'azu sai da nayi jim kaɗan ina tunanin makomar abinda zan faɗa. Na sake jin muryar baba yana faɗin kar kiji tsoron faɗa min ko mene ne ya' ta, tabbas zan yi miki adalci. Na lura babana ya kagu yaji mene ne burina wanda cika min shi zai sa in kar6i auren mijin da nayi ikirarin bana son sa. 


Kaina na sunkuye a kasa na fara magana. "baba, nasan matsayin saninka da yawan shekarunka mawuyacin abune ace bakada masaniya a kan maganin lalurar nan ta Muhsin da na daɗe ina gaya muku. Baba ka dubi Allah da girmansa, ka dubi darajar Ma'aiki (s.a.w) sannan ka dubi daraja da karfin soyayya ka taimake ni in dai har kanada masaniya akan abinda nake tambayar ka baba ka gaya mini. Kar kaji shayin sanar min ko mene ne, idan har na samawa Muhsin waraka ya sami cikar burinsa ta dalilina to zuciyata zata sami nutsuwa zan kuma yi alfahari da soyayyata domin na taimaki wanda nake so. Sannan cikin kwanciyar hankali zan amshi auren za6in ku."


Shirun da naji babana yayi ne yasa na ɗago kaina dan ganin makomar magana ta. Ai kuwa abinda naci karo da shi ya yi matukar Razana ni ya kuma tashi hankalina... 













*Nasmat*  ✍

[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                   *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 


                      👩🏻‍💻👩🏻‍💻

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

'Yar mutan 

  Arkilla✍

____________






📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com





Dedicated to the loved Frnds 'yan uwa abokan aiki:

King Boy Isha 

Kamala minna 

Bamai A Dabuwa Kkm. 

Zaidu Ibrahim. Mr. Zaid 

Ramadan Mubarak (Mubson) 


Mu gudu tare mu tsira tare. I am proud of you guys. Always 🤝




*Page 5*





* * * * * 

Hawaye ne na gani fall sun ciko idon baba Malam, kasancewar kansa a sunkuye ya kara bawa hawayen damar surnanowa suka biyo kuncinsa. A take zuciyata ta harba hankalina ya kara tashi. A 6angare ɗaya kuma naji ina nadama da danasanin tunkarar mahaifina da wannan maganar. Kaico na da wannan rayuwar tawa, tunda na kasa samawa iyayena farin ciki. Gashi yau har na kai ga zama silar zubar hawayen Babana. 


Sai na fashe da kuka na karasa ga mahaifina na rungume kafafunshi kasancewar yana zaune ne bisa kujera. Cikin kukan na fara magana "na shiga uku babana ka yafe min, dan Allah ka min aikin gafara. Da na san magana ta zata kona ranka da ban zo maka da ita ba baba. Wannan wace irin rayuwa ce dani? Ina son ku ina son yi muku biyayya baba dan Allah kayi hakuri wlh zan janye wannan kudurin nawa koda kuwa zai zamo sanadin fitar numfashi daga gangar jikina. Baba ka yafe min nayi alkawarin kawar da bukata ta Na rungumi taku bazaka koma zubda hawaye akai na ba, sai dai ko in na mutuwa ta ne."


Ahankali baba ya ɗago ni ya zaunar da ni bisa kujerar dake gefensa. Na lura da sauyi sosai a tattare da shi, jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karaya. Tsawon dakiku babu wanda ya koma yin magana a cikin mu. "Na'eema"  baba ya kira suna na cikin sanyi da alamun tausayi a fuskar shi. Ban iya ɗaga kaina ba saboda wata kunyar mahaifina da nauyin sa da nake ji. Na amsa "na'am baba." baba ya fara magana cikin jimami da mutuwar jiki yace "Na'eema kin tuna min da ɗan uwana Jamal ne ta dalilin wannan yunkurin da kike yi akan soyayya. Nasan kinada labarin inada ɗan uwa guda ɗaya jal a wannan duniyar." yaja numfashi tareda sararawa niko nayi nutso a kogin tunani tabbas inada labarin yayan babanmu mai suna Jamal wanda aka ce ya bar gida tun yana saurayi kuma har yau ba'a koma ganin sa ko jin labarin shi ba.


Tsayawar tunanina yayi dai-dai da cigaba da maganar baba. "na san baki san cikakken tarihin wannan ɗan uwan nawa ba, baki san bisa dalilin da ya bar gida ba to yau zan gaya miki. Wannan labarin da zan baki shine dalilin mu ni da mahaifiyar ki na hana ki wata masaniya akan maganin cutar wannan bil'adaman da kike so.


Na tabbatar koda ke ce a matsayin mu irin matakin da zaki ɗauka kenan." baba ya sarara kafin ya fara bani labarin yayansa wato babana Jamal wanda labarinsa kawai na sani ban san shi ba. 


"Kamar yadda kika daɗe kina ji Jamal yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, wanda mu kaɗai ne Allah ya azurta iyayenmu da haihuwa. Ba tare aka haife mu da Jamal ba, amma muna da matukar kama. Kasancewar ba wata tsera ce tsakaninmu ba yasa nayi kusa iso shi a girma. Hakan ne yasa da yawa idan suka ganni sai su ɗauka Jamal ɗin ne, gurare da dama nakan amsa sunan shi ga duk wanda ya kira ni da shi. Saboda son da muke wa juna yasa ko kaya za'a yi mana sai iri ɗaya muke sakawa. Haka muka taso har zuwa girman mu. Inda a nan ne mummunan lamarin ya afku."  


Baba yai shiru yana share hawaye cikin tsantsan kunan rai ya ci gaba... "soyayya!" ya faɗa da karfi da kuma nauyin gaske. Kafin ya ɗora "soyayya da kike gani abu ce mai matukar hatsari Na'eema, wata irin rikitacciyar soyayya ce ta 6alle tsakanin yayana Jamal da wata gimbiya 'yar sarkin birnin Durgas mai suna Sunita. Sunita ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance wadda masu ittafaki sun faɗa a wannan zamanin babu wata kyakkyawa kamarta a duk faɗin nahiyar nan. Ɗan uwana Jamal ya mace sosai akan son Sunita wadda tunda take bata ta6a jin murya ta wani ko wata ko kuma wani sauti a duniya ba.


Hakan kuwa ya samo asali ne ga kasancewarta kurma, da cutar aka haife ta. Babu wanda ya ankara da haka har saida ta girma ta kai munzalin yi da kuma jin magana. Sai a lokaci kowa ya fahimta da Sunita kurma ce bata ji daga nan mahaifinta sarki Ashwar ya shiga fafutukar nema mata magani tun yana yi da malamai har ya koma kan bokaye, na ruwa dana tudu. Amma ina biyan bukata ya gagara. A cikin haka ne ya sadu da wani hatsabibin boka wanda ya gaya masa Sunita fa bazata ta6a warkewa ba har sai an ɗiga mata sihirtaccin ruwan nan na (ma'al dawa'u) waɗanda can binne a tsibirin Darul iks a cikin kunnenta. Ruwan ko yana can bangon duniya ne a karkashin ikon shahararre kuma azzalumin sarkin nan na bakaken sheɗanu sarki Dawwaz, wanda a wannan duniyar har izuwa yanzu ba'a sami na biyunsa ba a karfin sarrafa miyagun dodanni da sheɗanu na jinni. Baya ga tsagwaron karfin tsafi dana dantsen da yake da su. Jin hakan yasa mahaifin Sunita sarki Ashwar ya saka wata doka ga manema auren tauraruwar 'yar tasa


Cewa duk mai son ya mallaki Sunita da gaske to ya je ya nemo mata waraka ta hanyar samo mata wannan sihirtaccen ruwan na ma'al dawa'u.  Wannan ne yasa duk masu tururuwar neman gimbiyar suka ja da baya saboda sanin ɗinbin hatsari da masifar dake cikin tafiya nemo wannan ruwan.


Ya kasance babu kowa a manemanta sai yayana Jamal. Saboda shi tashi soyayyar ta sha bam-bam da wadda sauran suke mata. Wato shi son gaskiya yakewa Sunita."


Babana yaja numfashi yana sharar kwalla. Wannan karon hadda ni kukan nake yi domin jin inda soyayyar gaskiya take, kasancewata ma'abociyar soyayya ina son mai maida hankali gareta da kuma bata muhimmanci. 


Tunanina ya yanke ne lokacin da naji baba ya numfasa zai ci gaba da bani labarin... 












*Nasmat* ✍

[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                   *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 


                      👩🏻‍💻👩🏻‍💻

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

'Yar mutan 

  Arkilla✍

____________






📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com





Dedicated to my sweet Sister *Maryam (Ummu Hanan)* banida wata kalma da zata isa wajen yin godiya ga karamci irin naki. 'Yar uwa ta gari, ɗaya bayan ɗaya kika dinga saudaukar min pages gaskiya Nasmat bazata manta dake ba. Allah ya kara ɗaukaka min ke yasa kifi haka. Sabon littafi 👄SURAYYA👄 kuma Allah yasa an fara shi a sa'a yasa a gama shi lfy. 'Yar mutan arkilla na yin ki Maryam ki huta ta wajena. 🤝








*Page 6*





* * * * * 

"To a lokacin ne Sunita ta kamu da tsananin son Jamal domin bayyanar mata da yayi a matsayin masoyinta na gaskiya. Ya zamana bata son rabuwa da shi, kullum suna tare dare ne kawai yake yi musu shamaki. 


Cikin wannan hali ne ɗan'uwana ya yanke hukuncin tafiya nemo wannan ruwan domin samun Sunita ta zama mallakinshi na har abada. Fama sosai yasha da iyayenmu a kan wannan tafiyar domin su basu lamunta ya tafi ba. Har saida ya haɗa da turo musu manyan garin nan da dattijan da ya tabbatar suna jin kunyar su sannan ya samu suka amince bisa dole badan ransu ya so ba. A wunin da ya samu amincewar su a wunin ya shirya tafiyar domin dama ya daɗe da fara shiri." hmm baba ya sauke numfashi yana daɗa matso hawayen dake idon shi sannan yaci gaba "a wannan ranar nayi kuka irin wanda ban ta6a yin irinshi ba na shiga tsoro da ɗimuwa musamman da naji babanmu na bashi karin haske gameda inda zai tafin. Tunda naji jerin hatsarurrukan da babanmu ke lissafowa yaya Jamal na kan hanyar ma kafin ya kai ga isa tsibirin na darul iks wanda can kam sai abinda Allah ya yi. Sai na kankame shi ina kuka kamar zan mutu, nace babu inda zai tafi dan na tabbata yadda naji labarin wannan hanya in ya tafi ba zai dawo ba. Na tabbata mutuwa zai yi. Domin ni a gani na gwara ka kashe kanka da kanka yafi ka tunkari tsibirin darul iks. 


Amma ina kukan ina karawa yaya Jamal yayi sallama da dangi da iyayenmu ya rungume ni ya sumbaci goshina yana faɗin "inda rabon ganawa wata rana Jamal zai dawo gareka Uffar" wannan ita ce kalma ta karshe d'aya furta kafin tafiyarsa. Bai koma cewa kowa komai ba ya juya yana mai karanto addu'ar nan ta neman tsari ya 6ata 6at!. Wannan shine gani na na karshe da yaya Jamal da ni da duk wani dangin mu. Iyayenmu har suka koma ga Allah maganar Jamal suke yi kullum sai sunyi maganar sa. Tun muna koke-koke muna tuna yaya Jamal har muka dangana ga Allah muka daina kukan sai dai addu'ar Allah ya dawo mana da shi. Domin har babanmu ya cika yana gaya min cewa ɗan'uwana yana nan a raye bai mutuba, amma yana cikin mawuyacin hali. Wasu lokutan har ji nake kamar nima in fita inbi bayan Jamal dan nemo shi, amma idan na tuna ni kaɗai na rage a zari'ar mu sai inji ina son zama donmi tada gidan nan. 


Sunita ma tun daga lokacin ta shiga kunci da kunan zuciya na rashin dawowar masoyinta. Ta kuma yiwa kanta alkawari har ta mutu ba zata so wani namijin da ba Jamal ba. Yanzu haka ita take mulkin birnin Durgas saboda tsufa daya riski mahaifinta sarki Ashwar.


Masu ganin ta sun ce har yanzu tana nan da kyawun nan nata kamar na da, sai dai shekaru da suka ja. Ance kuma har yau tana kan bakar ta na jiran masoyinta Jamal inko ya mutu ta yi alkawari itama sai dai ta mutu a hakan nan amma itada aure har abada." 


"Wannan shine cikakken labarin ɗan'uwana Jamal. Shin kin san me yasa na baki wannan labarin, har ma na ce miki yanada nasaba ga hanaki labarin maganin cutar Muhsin da muka yi?"  na girgiza kai cike da jimami nace "a'a" ina sharar kwalla. Domin gaskiya labarin soyayyar baba Jamal da gimbiya Sunita ya ta6a zuciyata ba kaɗan ba. 


Babana ya gyara zama ya fuskance ni da kyau yace "Na'eema maganin nan na warakar cutar Sunita shine maganin warakar Muhsin ɗinki. Babu wani magani a duniya da zai tashi kwakwalwar Muhsin tayi aiki yadda yake buri sai wannan ruwan na tsibirin darul iks wato ma'al dawa'u." 


Sororo nayi ina kallon baba wanda ya dasa aya a maganarsa idonshi a kain na.  Matsanancin tsoro da tashin hankali ne su yi min dirar mikiya. Zuciyata ta shiga dukan uku-uku ina kara juya maganar baba ina jinjina ta a ma'aunin tunani. 


Lokaci ɗaya naji jiri na ɗiba na tunanina ya gauraya kaina yayi mini nauyi sosai har ina ji kamar zai rinjayi gangar jikina... 











*Nasmat*  ✍

[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                   *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 


                      👩🏻‍💻👩🏻‍💻

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

'Yar mutan 

  Arkilla✍

____________






📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com




Sadaukarwa ga

Ama Alhj Kabir

Zeenat Deen (Shazee) 

Beauty Queen 

Zuwaira Madara 

Zeety Mmn Hanan 

Mmn Noor 

Mom Heebah 

Mum Namma 

Ina son ku Sisters thanks for the love and support. 





*Page 7*





* * * * * 

Cikin dauriya da cijewa na mike tsaye lokacin da azababben bakon ciwon kaina ya kara tsananta. Ban ko dubi inda baba yake ba na danna kaina ta cikin bangon ɗakinshi na bayyana nawa ɗakin. Hannuna na dafe da kaina da ke juya min wanda nake ji bisa dukkanin alamu yau nema yake ya faskare ya rabe gida biyu. Na zube kan gadona ina mai ambaton sunan Allah, daga nan kuma ban koma sanin komai na duniya ba. Na dai ji ni kamar ina bacci sai na shiga addu'ar Allah ya tashe ni ya kuma sanya duk abinda na jin nan ya kasance mafarki ne. 


Lokaci mai tsayi na shafe a yanayin fitar hayyaci ni ban mutu ba ban kuma suma ba, dan sama-sama nakan ji motsin shigowar iyayena har ma da maganganun da suke a kai na. Wasa-wasa na ci gaba da rayuwa a haka har na tsawon mako guda bana magana da kowa, ba kuma na iya cin komai. Babu abinda ke kai komo a rayuwata sai soyayya, tunanin Muhsin da lalurar sa ne suke kara yi min babakere a kowane lungu da sako na zuciyata. Tunanina ya gagara kawo komai gameda hanyar da zan bi in taimakawa Muhsin, a saboda haka na koma kamar mai cutar mutuwar 6aren jiki, bana iya yiwa kaina komai sai ummy ta yi mini. Iyakacina bin su da ido in na gaji kuma in sufe idon. 


Babu abinda yake burge ni dangane da abinci, da kyar ummy na take matse bakina ta zuba min ruwan kwakwa a safe da rana da kuma yamma, a yadda nake ji waɗannan ruwan sune suka taimaka min wajen hanawa 'yan cikina mannewa su bushe saboda rashin cin abinci. 


Ranar da na cika sati da kwana biyu a ranar yarima Haiman ya zo shi gidanmu cikin matsanancin tashin hankali da kaɗuwa na jin halin da nake ciki, da kuma irin lokacin da na ɗauka a hakan. Allah sarki so, ni kam na sallamawa soyayya. A ranar yarima ya bani tausayi duk da babu ɗingon son shi a raina, amma na jinjina mishi saboda bawa soyayya muhimmanci. 


Lokacin da yayi arba da ni da kuma halin da nake ciki sai ya fashe da kuka, yayi zaman dirshan a gaban gadona kamar yaro ya ci gaba da kuka yana rero mini baitoci na zallar soyayya da bege. A ranar da kyar baba maalam ya lalla6a yarima ya koma gidansu. Washe gari aminiyata Rumana ce ta zo ta ganni itama cikin halin bakin ciki da nuna damuwa da ni. A nan suka wuni ita da yarima Haiman suna famar ɗawainiya da ni. Ana gab da sallar magariba ya fita domin halartar sallar jam'i shi da baba. Ɗakin ya rage daga ni sai kawata Rumana


Wadda itama take shirin tashi tayi tata sallar. Tana mikewa nayi saurin riko hannunta bayan na tattara dukkan karfi da kuzarina, Rumana ta juyo da matukar mamaki tana kallona. Dawowa tayi ta zauna bakin gadon hannunta rike da nawa, tace "sannu Na'eema kina bukatar wani abin ne?" na girgiza kai lokacin da idona suka kawo kwalla buɗar bakina na farko cewa nayi "Rumana Muhsin, nayi kewar masoyina Rumana." shiru tayi tana kallona da yanayina, hatta maganar a wahale nake yinta cikin ɗan lokacin duk na rame na fara fita hayyaci na. Hawayen dake fita daga idona ta fara share min. Tace "ki kwantar da hankalin ki Na'eema Muhsin yana nan lafiya, kar ki karawa kanki damuwa yar'uwa Allah ya baki lafiya." na girgiza kai ina kallon kawata aminiyata Rumana wadda bama 6oyewa juna sirri nida ita. Mahaifin Rumana da babana abokan juna ne wanda zan iya cewa amintakar su ce ta haifar da tamu. 


Nace cikin sanyi da raunin murya "Rumana ki taimake ni ki je ki gano min halin da Muhsin yake ciki, ni kam ina jin karshen taka kasa da kafata ne ya zo." Rumana tayi gaggawar kai hannunta ta tsoshe min baki "a'a kawata, kar ki cire rai da rahmar Allah, ai cuta ba mutuwa bace da iznin Allah zaki tashi har ma ki taka kasar." ita kanta cikin dauriya take maganar tana shanye hawayen dake ko'karin zubo mata. Na yi murmushin karfin hali nace "ba zaki gane ba kawata, ni kaɗai nasan yanda nake jin jikina. Gani da rai amma banida damar mikewa ko tankwasa ga66aina, Ruma tunda nake ban ta6a jin ciwo makamancin wanda nake ji yanzu ba. Ke koda Allah ya tashe ni ma na san rayuwata batada wani amfani. Rumana ba zan rayu da Muhsin ba, ba kuma nida hanyar nema masa warakar cutarsa."  hawaye masu zafi suka zubo mini yayinda wani kululun bakin ciki ya tokare mini makogwaro. Kuka nake son yi amma ya gagara sai wani tukuki na zafi da nake ji a makoshi na, wanda nake ji kamar in fasa ihu. 


Rumana ma kukan ne na tausayi na ya kwace mata kallo na take irin kallon tausayi tace "ki hakuri kawata komai da kike gani a wannan duniyar mukaddari ne daga Allah, Na'eema kina da ilminki kar ki bari sheɗan ya ribace ki. Ki dage da gayawa Allah matsalar ki na tabbata zai ji6anci lamarin ki. A matsayin ki na musulma ki rungumi kaddara a yanda ta zo miki, ki yarda da yarima Haiman matsayin abokin rayuwar ki ki..." duk da cewa ina cikin yanayin ciwo mai kama da mutuwar sassan jiki, amma jin kalmar kawata saida yasa na yi karfin halin motsa jijiyoyina na ɗaga mata hannu alamar dakatarwa "ya isa haka Rumana, na gode da kauna da kike min. Amma ki bar maganar nan haka domin in kika ci gaba da yinta na tabbata cikin biyu zaki kaini ga rasa abu ɗaya. Ko dai in rasa ji na, ko kuma in rasa rayuwar gaba ɗaya. Barni da wanda nake ciki yanzu ma, na roke ki kije ki aiwatar da abinda na nema a gurin ki. 


Ki nemo min labarin masoyina ko zan sami sassauci na halin da nake ciki." Kawata bata koma cewa komai ba ta mike. Sai da ta fara gabatar da salla tukunna sannan ta nufi birnin lumui ta kuma sauka a garin gabas. A lokacin yarima Haiman ya dawo daga salla shi da baba, baban ya wuce turakarsa yariman kuma ya iso gurina. Maganganun da naji daga bakinsa su suka tabbabar min da babana ya riga ya gaya masa dalilin kwanciyata a yanzu ya san abinda ya assasamin ciwon da nake yi wanda ban ta6a yin irin shi ba, ban kuma san ranar warakarsa ba. 


Bayan shigowar tashi tsayuwa ya fara yi akai na na tsayin lokaci, sannan daga baya ya juya ya nufi gaban madubin dake ɗakin nawa yana karewa kansa da halittar jikinsa kallo, ya juyo ya kalle ni cikin kunci da ɗacin rai yace "yanzu saboda Allah kin min adalci kenan Na'eema?" ban tanka masa ba sai ma binsa da nayi da kallo ya ci gaba da magana "me wancan bil'adaman yake da shi wanda ni bani da shi? Ni ɗin nan fa nine jinsin ki, bayan wannan ina da martabar da za'a so ni dan ita, a halitta ma Allah bai hana ni komai na cikar kamala ba. Amma Na'eema ke duk ba kya ganin waɗannan. Na ɗibi tsayin shekaru ina nuna so da kaunata gareki amma hakan bai ta6a burge ki ba. Na'eema na yarda so ɗaya ne kuma kin bada shi ga jinsin da ba naki ba, na san har abada ba zaki soni ba." ya tsagaita maganar yana matse kwalla a idonsa. 


Ni kuwa ido kawai na zuba masa kalamansa na yawo a kwakwalwar kaina ina kuma mamakin raunin zuciya irin na Haiman, shi ba wahala yayi kuka sai kace mace. Ci gaba da maganarsa ne ya katse min tunani 


"Na yarda ba kya so na Na'eema, ba kuma zaki so ni ba. Amma ni zan tabbatar da soyayya ta gareki, da dai in kalle ki a haka gwara na rasa rayuwata saboda ke. Na'eema nima na shirya sadaukar da rayuwata gare ki ga soyayyar da nake miki. Gwara na mutu kan tafarkin son ki da na kalli taki mutuwar. Ki sani nan da sati ɗaya zan gama shirina na zuwa tsibirin darul iks domin samo ruwan ma'al dawa'u wa cikar burinki."


Sai naji saukar maganar yarima kamar an shimfiɗa wani hijabi ya lullu6e a kaina, kamar dai wanda yake tsaka da nannauyan bacci kuma yana mafarki... 














*Nasmat* ✍

[24/1 20:39] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                   *MARUBUCI...*

                

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari. 


                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_____________________________________

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 

_____________________________________


       ©

'Yar mutan 

  Arkilla✍

____________






📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽

Zamaniwriterassociation@gmail.com





Dedicated to lovely Sis 💋

Layuza Kabir 

Rahma Dawaki 

Aysherh 

Besty Nana

'Yar Auta 

'Y@r @mana

U guys means more to me  💋






*page 8*






* * * * *

Maganar babana malam da ya shigo ce ta kara tabbatar min cewa lallai ba mahafarki nake ba. Zumbur na mike daga kwance zuwa zaune ina kara yiwa yarima kallon mamaki da al'ajabin abinda naji ya fito bakin sa. 


Nayi nisa ga abinda nake yi na kallon shi da wani irin yanayi wanda na kasa gane kansa. 


Cikin tsawa da 6acin rai baba yace "ashe baka da hankali yarima? Ka kuwa san abinda kake furtawa? Maza fice, ka fita nace" ya karashe maganar yana nuna masa hanya da hannunsa wanda har karkarwa yake saboda tsananin tashin hankalin da maganar yarima ta haifar masa. 


Yarima bai koma cewa komai ba ya 6ace. Yana aika min wani irin kallo mai nuni da cewa 'abinda na faɗa gaskiya ne' bayan fitarsa baba ma ya fita. Ya rage saura ni kaɗai zaune a kan gado na tamkar wadda aka dasa ta cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa, ta ciki da waje kai harma da gangar jikina naji sauyi a cikin kankanin lokacin. Sai dai na kasa gane ainihin halin da nake ciki shin na farin ciki ne ko akasin hakan? Alhamdulillah dama tazo abin ya wuce wasa dan daga zaunen naji na Mike tsaye da wani irin karfi da ban ta6a jin irinsa ba. Kai kamar ma ban ta6a yin ciwo ba. 


Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Na rika na nata kalmar a bakina da karfi nayi salati ga Ma'aiki (s.a.w) wanda ni kaina bansan adadinshi ba. Sannan na taka cikin irin takuna mai kama da tafiya akan ruwa luuuuu. Na isa gaban katafaren hoton nan na zanen masoyina Muhsin, sai a lokacin na tabbatar da abinda nake ji farin ciki ne irin wanda zuciya bata ta6a cin Karo da shi ba. Maganganun yarima Haiman suka shiga dawo mini, a lokacin kuma naji kwarin guiwar da ban ta6a jin irinshi ba tun daga ranar da baba ya sanar mini hanyar samun maganin cutar kwakwalwar Muhsin da kuma tsantsan haɗarin dake cikinta. 


Na kalli hoton masoyina nace "Muhsin yau kukana ya kare, yau damuwa ta ta zo karshe a ya burina ya ɗauki hanyar cika..." bayyanar kawata Rumana ne ya katse min magana ta. Na mayar da kallona gareta


Wadda itama ni take kallo cikin tsananin mamakin gani na a tsaye. Ni da ta bari kwance cikin halin rayuwa ko mutuwa. Har ta isa gareni mamakin dake fuskarta bai kau ba ta riko hannayena duka biyu tace "Na'eema kece kuwa?" lallausan murmushina na sakar mata tareda jan hannunta zuwa kan ma dai-daitan kujerun dake jere a ɗakin muka zauna. Har yanzu dai idonta a kai na. Ta koma yunkurin yin wata magarar amma sai na dakatar da ita ta hanyar toshe bakinta da tafin hannuna nace "kar kina mamakin ikon Allah Ruma. Zan gaya miki komai a nutse, shin ina labarin masoyina Muhsin?" Rumana ta sauke ajiyar zuciya tareda dafa kafaɗata nan take naga sauyi sosai a fuskarta, ta canja daga yanayin mamaki zuwa na damuwa da kuma alamar tausayi. Wani irin bugu zuciyata tayi da karfi, kar dai wani abin ki ne ya sami Muhsin, "lafiya Ruma me ya sami Muhsin ɗina.?" Ta juyar da fuskarta gefe, wato ta ɗauke ta ga barin kallo na tace "bazan 6oye miki ba 'yar'uwa Muhsin ɗin ki yana cikin wani hali na damuwa, in takaice miki zance dai shima kwance yake yana kar6ar kulawa ta majinyatan bil'adama."  "Innalillahi! Wa inna ilaihi raji'un"  na faɗa da karfi ina share gumin da ya fara yanke mini tun lokacin da naga sauyin fuskar kawata. 


"Muhsin ba lafiya? To wai ma me ya same shi?."  "soyayya" kawata ta bani amsa a takaice. Na kara zaro ido wannan karon tsagwaron tsoro da kishi ne suka bayyana karara a idona "soyayya?!" na tambaye ta da karfi ina kara zaro ido "kina so ki ce min Muhsin yana soyayya da wata bil'adama?" Rumana tayi murmushi na ganin sauyi na lokaci ɗaya. Ta kara dafa ni tace "kwantar da hankalinki kawata, ina taya ki murna cewa Muhsin da kike fafutuka a kan sa shima ya damu da ke. Ya kuma kama da matsanancin son ki duk da har yau bai san cewa ke ɗin zahiri bace." na kasa gasgata abinda bakin kawata ke faɗi, tabbas na san mun shaku da Muhsin a mafarki amma taya zan yi tunanin zai kamu da so na ta wannan hanyar? 


Na koma kallonta wannan karon cikin sanyin murya nace "taya kika san haka kawata?" ta koma yin murmushi a Karo na biyu sannan ta fara bani labarin data samo mini kamar haka: "Lokacin da na sauka cikin masarautar garin gabas da masoyin naki na fara cin karo kwance magashiyan a ɗakin ummasa, wasu likitoci na musamman mai martaba (mahaifinsa) ya ɗauko dan kula da lafiyarshi. Sun kuwa dage suna ta bincike da yi masa gwaji (aune-aune) amma shi majinyacin sai sambatu yake yana ambaton sunan ki da kika gaya masa a mafarki. Kalaman bakin shi ne suka tabbabar min da cewa ya kamu da son ki kawata, cewa yake, Na'eema kawata ta duniyar mafarki ina kika shiga? Ina ji a jikina wani abin ki ya same ki. Na'eema ina son ganin ki amma ban san ta wacce hanya hakan zata samu ba. Ina kaunar ki kawata Na'eema mene ne yake faruwa da ke da har yayi mana shamakin da kika daina zuwa gareni? Fatana ace lafiyar ki kalau masoyiya ta da zan san hakan da na rage jin raɗaɗi da zogin da nake ji a zuciyata. Tabbas idan na sake kasancewa da ke sai kin gaya mini inda zan rika zuwa in same ki duk lokacin da baki zo gare ni ba domin zuciyata ba zata ɗauki rashin kusanci da ke ba. Me yasa ina kwanciya ina rufe ido, ina tilastawa kaina bacci amma baki zuwa Na'eema ina kika shiga?"


"waɗannan sune kalmomin dake fita daga bakin Muhsin cikin tsananin zafin zazza6in da yake ciki. Amma 6angaren iyayensa kuma sun fara gano gaskiya tunani suke ko dai yaronsu yayi gamo da aljanu ne? 


Kawata Na'eema ni kam ina cikin shakku da tsoro anya kuwa soyayyar mutum da aljan zata yuwu?"





🤔 to nima dai Nasmat abinda nake ta tambaya kenan, bari in bar sauri sannu-sannu dai. 




Muje zuwa yanzu ne wasar zata fara. 


Alhamdullah hakika dukkan godiya ta tabbata ga allah (s.w.a) da ya nuna mana karshen wannan littafin cikin koshin lafiya.

A matsayina na wanda yake tattara littafai na wannan marubuciyar dama sauran marubuta littafan hausa ixuwa document, wato AHMED SARDAUNA nake muku fatan alkhairi sai munhadu a cigaban littafin idan mawallafiyar wannan littafin ta saki cigaban daga naku AHMED B. SARDAUNA

👇👇

 08169047840



Post a Comment

0 Comments