Title:None,Content:❤❤❤Soyayyar meerah👑❤❤❤
Gabatarwa
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai.tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (S A W)
Ina gabatarmuku da wannan littafi nawa mai suna soyayyar meerah
Marubuciya: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)
P 1🏤
Ta na cikin ɗaki ta na gugar uniform ɗinta ta mayar da hankalinta akan gugar bata Ankara ba ta ji a na ta famar rafka sallama a kofar ɗakin, yes shigo abinda ta fada kenan batare da dago kai takalli kofar ba. Farida ce ta shigo ɗakin ɗaure da fuska ta na cewa "Amma gaskiya ba ki da mutunci meerah, Meerah ta ɗan yi murmushi ta ce "Meyafaru kuma besty?
Farida tace "Tun ɗazu na ke famar rafka sallama ashe ki na ji na ki ka yi banza da ni. Yi hakuri bestyna ban ji bane ke kin san ban isa na kyale ki ba meerah ta faɗa tare da kamo hannun faridar ta zaunar da ita,yanzu dai ba wannan ba meye labari? Meerah ta tambaya. Farida ta ce "Wane irin labari? Habah besty! wane labari zan tambaye ki banda labarin mutumin,uncle wai? Cewar farida,ah! ya na nan ƙlau amma meyasa duk sanda muka haɗu sai kin yi zancensa,ko dai ki na son shi ne ƙawata? Meerah ta sha mur kamar da gaske ta ce "Haba besty! daga tambaya sai ki min wata fassarar ko kin manta cewa saurayin Meenah ne kuma Wanda zai aure ta?.
:❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
🏤 🏤P2🏤🏤
Kuma in haka ne ina zan kai uncle manish ɗina? ke manta da zancen muje ki gaida Ammi ko kun gaisa ne? Meerah ta fada tare da riƙo hannun Farida ta tayar da ita tsaye farida ta ce "mu je na gaida ta.
Suka bar ɗakin su ka nufi ɗakin Ammi,
Ammi na zaune ta na kallon TV su ka shigo ɗakin da sallama ammi ta amsa da fara'arta ta gaida ta ammi ta amsa tare da cewa ya mamanki ta na lafiya?ki gaidata,
Za ta ji sai anjima ammi ni zan tafi farida ta faɗa,ammi ta ce "Ki gaida gida. Meerah ta rakota har ƙofar gida ta ce "zan shigo anjima idan na dawo daga islamiyya,farida ta ce Allah yasa idan kuma ba ki zo ba wataƙil sai in mun haɗu gobe za mu je school bye,farida ta faɗa.
Meerah ta koma ciki Farida ta wuce gida.
kuwa a ka yi bayan ta dawo islamiyya ta je gidan su Farida da ya ke maƙotansu ne gida biyar ne tsakanin su da gidan su Faridar.
Da safe su ka haɗu su ka wuce school
Class ɗinsu ɗaya su na ss3 ne.
Wacece Meerah?
Cikaccen sunanta shine Ameerah Usman Lema haifaffiyar garin sokoto ce amma mahaifinta Dan Asalin jihar kano ne
Ya na zaune ne agarin sokoto shi da iyalansa a nan ya ke kasuwancinsa.
Matarsa ɗaya hajiya Karima wadda su ke kira da Ammi.
Ƴaƴansu uku kacal, biyu maza su ne manya Arif da Adil sai auta Ameerah wadda ta kasance ita kaɗai ce mace a gurinsu su na kiranta da Meerah su na matuƙar ƙaunarta.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
🏤🏤P3🏤🏤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
Ina mika sakon gaisuwata xuwa ga Aisha ridwan dahir(yar jos)
Haka ma yayyenta su na ririta ta, Ameerah yarinya ce y'ar kimanin shekaru goma sha takwas(18)a duniya ta kasance yarinya mai nutsuwa, hankali da tarbiya ga ta kyakkyawa ta na da kyau irin nata ita fara ce amma ba sosai ba mai madai-daicin tsawo siririya ce ba sosai
Tana da kyawun fuska gwargwado a taƙaice dai kyakkyawa ce.
Labarin soyayyarta ya fara ne a lokacin da ta ke ss1 a matakin karatun sakandire.
A lokacin su ka sami wani baƙon malami da a ka yiwa transfer daga wata makarantar zuwa tasu.
Baƙon malamin y kasance mai fara'a sosai da sake fuska ga dalibai duk da cewa ba ya daukar ss1 darasi ko daya ya na ɗaukar ss2 da ss3 ne amma duka ɗaliban makarantar su na son sa saboda fara'arsa,baƙon malamin mai suna Malesh Adam ya kasance aboki ga uncle Manish Aliyu tare suka yi Secondary bayan sun kammala ne ba su sake haɗuwa ba, sai da aka maido Malesh aiki a makarantar da Manish ɗin ke karantarwa.
Haɗuwar su ya tuna masu da tsohuwar abotarsu suka kuma ɗinkewa kamar da.
Uncle Manish malamin su meerah ne shi ke ɗaukarsu darasin English language yana da ra'ayi akan Meerah sosai kasancewarta yarinya mai ƙwazo da mayar da hankali ku san ita ce
Over roll a ajin ya na ji da ita sosai.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
🏤🏤P4🏤🏤
Safeenah mansoor yabo Allah ya shiryeki Ameen
A bangaren Meerah kuwa ta na mutunta Uncle Manish sosai, ya kan ɗan zo wata rana idan ɗalibai sun je break su ɗan yi fira shida Meerarsa ta haka su ka fara shaƙuwa.
Ana hakane wata rana uncle Manish ya zo fira gurin Meerah kamar yadda ya saba amma wannan karon ba shi kaɗai ba ne, ya zo ne tare da abokinsa Malesh .
Sallama suka yi atare tare da samun guri suka zauna akan teburin da ke gaban nata,
Ta amsa sallamar da fara'arta ta ce "Ah! Kace yau ba kai kaɗai ba ne tare ka ke da baƙon Uncle ɗinmu. Uncle Malesh ya yi murmushi bai ce komai ba, sai Uncle Manish ne ya yi magana ya ce "Wai ke har yanzu baƙo ne a gurinki? Ta ce "Baƙo ne mana don ko sunansa ma bansaniba, Uncle Manish ya ce "Wai da gaske baki san sunansa ba? Da mamaki a fuskarsa yay tambayar, ta ɗaga kai alamar tabbatarwa ta ce "Allah kuwa ban saniba, tab! lallai ma yarinyar nan da gaske ki ke cewar uncle Manish.
Shi kuwa Malesh da bai yi magana ba sai a lokacin cewa ya yi "Taya kuwa za ki san sunana?,ba dai kin san sunan wannan ba? Ya nuna Uncle Manish da yatsa.
Murmushi ta yi ta ce "Na sani mana, Uncle malesh ya ce "Meye sunansa?" ta ce "Uncle Manish namu, Manish ya yi murmushi kawai bai ce komai ba.
Uncle Malesh ya nuna kansa da yatsa ya ce "Ni fa ya sunana?" ta ce gaskiya ban saniba, ta na gama faɗa ya miƙe tsaye ya fara tafiya ya ce "Tab! to ni bari na tafi ka ji ma ko sunana ba ta sani ba kafin anjima ta ce bata taɓa ganina ba.
Uncle Manish da Meerah su ka dinga dariya daƙyar Uncle Manish ya tsayar da dariyar, ya ce "Ka ga dawo yanzu zan gaya mata sunan ka ga sai na sa ta haddace gudun mantuwa."
Uncle Malesh yace "A'a ka bari na tafi kawai ni da ba'a san sunana ba taya za'ayi fira da ni? Gwara na ba ku guri da alama ta na so ta kore ni ne,to na tafi.
Ya na kai nan ya cigaba da tafiya da sauri Meerah ta ce "Lah! Uncle yi haƙuri ba haka bane wallahi. Bai saurare ta ba ya fice abinsa.
Meerah ta bi shi da kallo Uncle Manish ya ce "Ke manta da shi wai shifa anan ya yi fushi ne amma zai ware ne,mu ci gaba da firarmu kafin nan sunansa Malesh Adam ya ci gaba da bata labarin malesh da abotarsu lokacin su na secondary school.
Amma hankalinta baya gurin ta tafi duniyar tunani sai leƙen waje ta ke ko za ta gan shi amma ya ɓace mata.
A haka suka tashi daga firar ranar firar bata yi armashi ba saboda hankalin meerah baya gurin.
:❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
🏤🏤P5🏤🏤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (ummu-inteesar)08109634202
Ranar har aka tashi tunani ta ke na fushin da uncle Malesh ya yi akan kawai bata san sunansa ba.
Ana tashi farida ta ja hannunta tare da cewa "mu tafi Meerah antashi fa na ga alama ba ki ma sani ba, tunanin me ki ke tun ɗazu? Tun dawowata break na lura da ke, meyafaru ne?"
Meerah ta ce "Bakomai mu je, Su ka tari napep suka yi gida.
Ta na shiga gida ta ajiye jakarta ta yi sallah ta ci abinci ta kwanta don ta huta.
Amma me?sai tunani ya dawo mata sabo nan take ta ji ta na so ta ga Uncle Malesh don ta ba shi haƙuri, a ranar ƙagara ta yi gari ya waye su je school don ta ga uncle ta bashi haƙuri.
Yau bayan ta je school ta shiga class ɗinsu ta zauna sai dube-dube take wajen window ko za ta gan shi amma ina! Har aka dawo break bata ganshi ba, duk da cewa yau har fita ta yi ta ɗan kewaya a makarantar amma bata gan shi ba,duk sai ta ji ba daɗi.
Sun fito ita da farida za su gida ta na ɗaga kai ta hango shi ya nufi Babur ɗinshi da alama zai wuce gida ne.
Da sauri ta ce "Farida ɗan jira ni kaɗan ina zuwa, bata saurari me Faridar za ta ce ba ta yi gaba.
Tun kan ta karasa gurinsa ta fara kiran shi Uncle Lesh! Ganin ya na ƙoƙarin tada Babur ɗin ta ƙara sauri tare da ɗan ɗaga murya Uncle Lesh!! bai ɗago ba da alama bai gane da shi ta ke ba,amma ya ji kiran sai da ta ce "Uncle Malesh" sannan ya ɗago ya kalle ta,ya gane ta sai ya ce "ya akayi ne?"
Ta sadda kai ƙasa ta ce cikin in-ina "Dama...dama hmmm!" Ya ce "Dama me meerah?."
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
🏤🏤P6🏤🏤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
Kuyi hkr kunji ni shiru kwana biyu abubuwa ne sukayi yawa.
Ta ɗago kai da sauri ta kalle shi dama ya san sunanta ne?a ranta take maganar,jin ta yi shiru
ya ce "Ki yi magana menene?" Ta ce "Dama jiya ne na ga kamar ranka ya ɓaci shine na zo na baka haƙuri,."
Ya yi murmushi ya ce:bakomai Meerar mu, raina bai ɓaci ba.
Ta kalle shi a ɗan razane jin sunan da ya kira ta da shi,wai meerarmu..to me hakan ke nufi?aranta ta ke zancen kamar ya karanci abinda ke ranta ya ce"Ina nufin Meerar Manish kin ga tamu kenan ko?"
Ta yi murmushi ta ce "Ka dai yi haƙuri
Don Allah Uncle Lesh,yanzu na san sunan kuma ba zan manta ba."
Murmushi ya yi shi ma tare da cewa "Maimaita sunan da ki ka faɗa yanzu."
Tace "Uncle Lesh na ce." Uncle Malesh ya ce "wow! Sunan yay daɗi kuwa,bakomai Meerah je ki Allah ya miki albarka." "Ameen Uncle Lesh nagode, ta faɗa tare da juyawa ta koma gurin su Farida da Meenah da ke tsaye su na jiranta.
Da murmushi a fuskarta ta ce "Mu tafi koh?su ka kalle ta Meenah ta ce "Da alama ki na cikin farin ciki me ku ka tattauna ke da wancan mutumin?"
Meerah ta ce "Ke bakomai ba ne kunji yadda akayi, ta kwashe abunda ya faru tsakaninta da su Uncle Lesh da Manish jiya har zuwa da ta je ba shi yanzu ta gaya ma su.
Murmushi suka yi su duka biyun tare da cigaba da tafiya.
Daga ranar Meerah da Uncle Lesh suka zama abokai,ko da yaushe ta gan shi ta kan je su gaisa,da ya ke Uncle ɗin mai fara'a ne ga raha nan da nan su ka shaƙu shi da meerah.
Ta bangaren Uncle Manish kuwa a yanzu ba yada sukuni *soyayyar meerah* ta yi kane-kane a zuciyarsa kuma ya kasa gaya mata.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
🏤🏤P7🏤🏤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
Kuyi hkr readers ina exam ne shiyasa bana post da wuri.
Ga shi yanzu sun rage haɗuwa su na hira kamar yadda suka saba. Abin na damunsa sosai ya rasa yadda zai yi akan haka ne wata rana ya je gun abokinsa Malesh, ranar Assabar bayan sun gaisa ne suka samu guri su ka zauna a ɗakin Malesh ɗin.
Anan Malesh ke cewa "Abokina meyafaru ne na ga kamar ka na da damuwa, meye matsalar? Manish ya numfasa cikin yanayin damuwa yace "Bari kawai abokina wallahi ina da damuwa ne, kuma na kasa solving problem ɗin shine ma abinda ya kawo ni gun ka don ka ban shawara.
Malesh ya tattara natsuwarsa guri ɗaya tare da maida hankalinsa ga abokin nasa ya ce "Meye damuwarka Manish?"
Manish ya numfasa a karo na biyu yace "Abokina na kamu da soyayyar wata yarinya ne kuma na kasa gaya mata na rasa yadda zan yi abin na damuna sosai.
Malesh ya yi murmushi ya ce "Wace yarinya ce abokina?" Manish yace "hmmmm! Meerah ce kuma na kasa sanar mata ,na kusa haukacewa akanta bani da aiki sai tunaninta duk ta dagulamin lissafi.
Malesh ya yi y'ar dariya sannan ya ce "Abokina kenan wai kai a tunaninka sai yanzu ne ka kamu? Hmmmm! Ai ka daɗe da kamuwa da son Meerah kawai baka gane ba ne sai yanzu, amma ni tuni na harbo jirginka,da na faɗa abaya cewa kayi a'a bahaka ba ne kai dai ka na ra'ayinta ne kawai kuma kawarka ce ,yanzu amma ka fahimci cewa "Masoyiyarka ce ba ƙawarka kawai ba,
Shiyasa ka ke damuwa da al'amarinta".
Manish ya ce "Bari kawai yarinyar nan ta gama dani,ni dai ba ni shawara ya zan yi? Dariya sosai malesh ya yi sannan ya ce "Ni kam a shawarata ka same ta kawai ka sanar mata,domin abari ya huce shi kan kawo rabon wani,na san ba za ka sha wahala ba gurin shawo kanta, domin akwai fahimtar juna atsakaninku,abin zai zo da sauki."
"Abu na biyu ka yawaita addu'a ni ma zan taya ka Allah ya zaba ma mafi alkhairi."
Manish ya ce "Ameen nagode abokina zan gwada insha'allah." Malesh ya ce "Ka je da ƙwarin gwuiwa za ka iya kar ka ji shakkar komai Allah ya bada sa'a abokina.👍🏻 ameen
Manish ya faɗa tare da miƙewa ya ce "Ni zan tafi."
"Au! tun yanzu angon meerah? ko tun yau za ka je gurin ta ne?wannan sauri haka?" Malesh ya faɗa a sigar zolaya ya na dariya.
Manish ya ce "Daɗina da kai shaƙiyanci, akwai abinda zan yi a gidan ne shiyasa bye." Malesh ya raka shi ya tafi.
A bangaren Meerah kuwa kusan abinda ke faruwa da Manish ɗinne ke faruwa da ita,Itama ta kamu sai dai bada shi ta kamu ba, ta kamu ne da soyayyar abokinsa Malesh, amma ta kasa yarda da zuciyarta akan cewa ta na son Malesh ɗinne ta fi yarda da cewa shaƙuwa ce kawai a tsakanin su ita da shi.
Komai zai faru da Meerah nan gaba?meye makomar uncle manish?uncle zai sota kuwa? Amsar wadannan tambayoyin suna zuwa a pages na gaba ngd.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
🏤🏤P8🏤🏤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
Sai dai me? Al'amarin na ba ta mamaki yanda ta ke damuwa da al'amarinsa sosai,bata da wani aiki sai tunaninsa idan ta hango shi sai ta ji ƙirjinta ya dinga harbawa,ta na tsananin jin kunyarsa, ta na so ta ji ana labarinsa,burinta a kullum ta gan shi.
Ya kasance ayanzu bata da wani buri da ya wuce ta je makaranta ko dan ta gan shi.
Wani zubin Idan ta hango shi har laɓewa ta ke ta na leƙensa. A yanzu bata yarda su haɗa ido da shi ko kaɗan saboda kunyarsa da take ji.
Ana cikin hakane suka fara 3rd term examination za su shiga ss2,
Murna agurin meerah ba'a magana za ta shiga class ɗin uncle Lesh ɗinta.
Wata rana sun fito daga paper farko kan ashiga ta biyu don biyu za su yi a ranar.
Farida ta ce "Ni fa yunwa na ke ji ga shi yanzu har 10 ta gota bari na je na nemo abinda zan sakawa cikina.
Meenah ta ce "Ni ma dai gaskiya ita na ke ji, ko break ban ba na fito tsabar sauri ku mu je mu nemo abinda za mu ci."
Meenah ta ja hannun Meerah ta ce "Mu je mana kin wani tsaya ko ke bakya jin yunwar ne?" Meerah ta ce "Eh ku je kawai zan jira ku anan."
Har sun fara tafiya Meerah ta ce "Dan Allah Ku siyomun donut, Farida ta ce "kut! ai wallahi ba za mu siyo ba,ba kin ce ba za ki ba?, ki zauna mu masu buƙata ma je."
Za ta yi magana suka yi gaba abinsu.
Ba su fi minti uku da tafiya ba Uncle Manish ya nufo gurin da take zaune ƙarƙashin wata bishiya nesa da class ɗinsu kaɗan.
Ya ƙaraso da murmushi a fuskarsa yace "Assalamu alaikum y'an mata."
Meerah ta ɗago da murmushi a fuskarta ta ce "Wa'alaikas salam Ɗan samari.
Ya kalle ta a mamakince da alamar tambaya a fuskarsa ya ce "Kut ni ne ɗan samarin?"
"Eh." ta ce ta na mai dariya, ya ce "Tab lallai yarinya kin samu guri." Ta kuma yin dariya bata ce komai ba.
Ya ce "Meerah yau ba tayin guri?, ina so mu yi wata muhimmiyar magana ne.
Ta ce "Zauna uncle." Ya dubi gurin da suke ya ga teachers da students nata kai-kawo agurin ya ce "Meerah ko za mu je can mu yi maganar?" ya nuna wani guri nesa da inda suke ya ce "kin ga nan hayaniya ta yi yawa."
ta ce "To muje."
Suka bar gurin, su na isa gurin da ya nuna ya ce mata zauna.
Ta zauna a ƙarƙashin wata bishiyar shima ya nemo guri ya zauna.
Cikin serious voice ya kira sunanta "Meerah!" Ta kalle shi ba tare da ta amsa kiran ba. Ya ce "kamar yadda na faɗa miki akwai magana mai muhimmanci da nake so na yi dake ki na saurare na?"
Tace "Eh!" Ya ce "Meerah yau zan buda ma ki sirrin zuciyata, ayau zan sanar dake abinda na Daɗe ina boyewa a zuciyata."
Menene uncle manish zai gayawa meerah?wanne sirri ne wannan? Ya meerah zatayi bayan uncle manish ya buda mata sirrin zuciyarshi? Ku biyoni a page na gaba Dan jin amsoshin tambayoyinnan. Taku har kullum ummu-inteesar.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
🏤🏤P9🏤🏤
Meerah! ya kira sunanta ta kalle shi
Yace "Kalli cikin ƙwayar idona me ki ka gani?" Ta kalle shi a karo na biyu sannan ta ce ban ga komai ba.
Ya ce "ƙara dubawa dai da kyau za ki ga zallar so da kaunarki aciki."
A razane Meerah ta dube shi tare da buɗe ido, da alama ta na neman Ƙarin bayani ne.
Ya ce "OF course I really love u Meerah ina matuƙar ƙaunarki, ƙaunar da ban taɓa kwatantawa wata y'a mace ba a duniya. Tunaninki ya hana min sukuni, ban san ya zan kwatanta miki irin son da nake miki ba, ki yarda da ni Meerah" ya faɗa a marairaice.
Meerah ta gama dasƙarewa a gurin ta zama tamkar mutun-mutumi bata ma san tunanin me ta ke ba, anya! Uncle na cikin hankalinsa kuwa, ta ɗago kai a daburce ta kalle shi.
"Uncle are you out of your sense?"
"Ni ka ke so?" Ta faɗa ta na nuna kanta da yatsa.
Ya ce "OF course Meerah I really do it."
Meerah ta rasa me za ta ce lallai uncle ya hauka ce ta faɗa a ranta Ashe a fili ta yi zancen bata sani ba, sai ji ta yi ya ce "ƙwarai na haukace amma akanki."
Meerah ta miƙe tsaye tare da juyawa kawai ta bar gurin cike da mamaki.
Ya yi ta kiranta amma bata kula shi ba ta yi gaba abinta.
Ya jima a tsaye kafin ya bar gurin, jiki ba ƙwari ya tafi ya na tunanin anyah meerah zata so shi kuwa? Da Alama abin ba ya da sauƙi kamar yadda malesh ya gaya masa.
A sanyaye meerah ta ƙarasa gurin da su meenah ke zaune su na jira suga inda za ta ɓullo masu, Ta zo ta zauna,.
Daga ina ki ke mun zo ba mu tarad da ke ba cewar Farida.
Meerah ta ce "Uhmm! Ina tare da uncle manish ne."
Meenah ta ce "Na gan ki a sanyaye meyafaru ne?" "Uhmm! Bakomai Ku tashi mu je ga can za'a shiga paper." suka rankaya zuwa class.
A ranar har su ka koma gida jikinta a sanyaye ya ke ta rasa tunanin me ma za ta yi zafin ya haɗe mata biyu ga tunanin Uncle Lesh ga kuma matsalar manish da ta kunno kai a rayuwarta.
Ta san cewa ya na jiran amsarta any time kuma haƙiƙa ba za ta iya cewa Uncle Manish bata son sa ba,ta na matuƙar girmama shi da mutunta shi kamar yayanta ta ke jin shi,
Ta na masa irin son da takewa yaya Adil ɗinta. Kuma idan ta ce ta na mai son aure ta yaudare shi, domin duk duniya a yanzu mutum ɗaya ne ta ke ji za ta iya aura ta rayu da shi ko da a bukka ne shine Uncle Lesh.
Yanzu kam ta gama yarda ta na matuƙar son sa.
Duk da cewa shi ma Uncle Manish ba ya da muni ko wani abunda za'a ƙi shi saboda shi domin shi kyakkyawa ne kalar fatar shi chocolate mai kyau dogo ne ba sosai ba, ya na da ɗan dogon hanci da kananan idanuwa ataƙaice dai yana da kyau irin na shi.
Amma da ta tuna Uncle Lesh sai ta ja dogon numfashi hmmm! Uncle Lesh ya haɗu dan ya fi Uncle Manish kyau nesa. Shi fari ne mai hasken fata sosai ga shi dogo dan ya fi Manish tsawo kuma ya na da y'ar ƙiba kaɗan ga manyan idanuwansa masu haske da dogon hancinsa kamar biro, bakinsa yana da ɗan girma ba sosai ba da ɗan sajensa da gemu kaɗan irin na gayu.
A takaice dai Uncle Lesh ya haɗu.
Sai dai ita Meerah ba dan kyansa ko dan wani Abu da ke tare da shi take sonsa ba, ta na son sa ne dan Allah kawai.
Meerah ce ke ta wannan tunanin a lokacin da ta ke kwance kan madai-daicin gadonta ta na juyi da dare a haka bacci ya yi awon gaba da ita.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
🏤🏤 P10🏤🏤
A makaranta kuwa yanzu Meerah ta na gujewa duk inda ta san za ta haɗu da Uncle Manish dan gudun ka da ya titsiye ta sai ta ba shi amsa ga shi bata shirya ba,ko na ce bata da amsar ba shi.
A bangaren Manish kuwa ya na zuwa duk inda ya ke tunanin zai ga Meerah dan ya ji ra'ayinta akan shi,amma INA! Ba ya ganinta sai a class ga shi ba damar ya mata magana acikin sauran students.
A haka su Meerah suka kammala exam ɗinsu su ka je hutun 1 month.
Bangaren Uncle Lesh kuwa wani baƙon al'amari ne ya fara ziyartarsa wannan al'amarin kuwa shine shi ma ya kamu da son kawar meerah wato Meenah, amma ya ɓoye a zuciyarsa bai sanarwa kowa ba, har ita Meenar kasancewar ba wani sabo a tsakaninsu iyakacin su gaisawa idan suka haɗu a lokacin da ta ke tare da Meerah.
A cikin wannan hutun ne za'ayi bikin babban yayan meerah wato Arif, Meerah ta yi matuƙar farin ciki da auren ya faɗo lokacin Hutu.
Ta gayyaci manyan aminanta wato Meenah da Farida wacca ta zama tamkar y'ar gida,dama sauran ƙawayenta na islamiya,ta kuma gayyaci rabin ranta uncle lesh da abokinsa Uncle Manish.
Uncle Manish ya yi murna sosai da gayyatar masoyiyarsa,ko ba komai ta kula da shi tunda har ta gayyace shi,kuma zai ga gidan su Meerarsa da danginta. Uncle Lesh ma yayi murna da gayyatar ƙawarsa kuma yana sa ran ganin meenarsa a can.
Yau takasance ranar alhamis a yau ne kuma za'ayi kamun yaya Arif da amaryarsa Airah. Tun ƙarfe goma na safe Farida ke gidan su Meerah suna ta famar shirye-shiryen kamun sai can zuwa 12pm sai ga Meenah ta zo.
Meerah ta ce "sai yanzu? Da kin koma ai mara mutunci sai da muka gama aikin saura kaɗan za ki zo?" Meenah ta ce "Yi haƙuri ƙawata akwai abunda ya tsaida ni ne ga unguwarmu da ɗan nisa zuwa nan."
Meerah ta ce "Shikenan bakomai ta ɗora da cewa kin ga Meenah don Allah share mana tsakar gidan nan mu zamu shiga ciki mu huta mun ga ji,in ki ka kammala sai mu je mu ƙarbo ɗinkin ankon mu koh?" Meenah ta ce "Shikenan ku je Ku jira ni. Ta na kammala sharar su ka je suka karbo ɗinkinsu.
3:30pm Meerah ta fito daga wanka ɗaure da towel ta na goge ruwan kanta da wani towel ɗin ta ce "Farida yi sauri ki yi wankan kinsan ba'a African time🤪🤪naga kowa ya shirya kar a bar mu anan. Farida ta shiga wanka yayin da Meerah ke shiryawa,ta na fitowa Meenah ta faɗa toilet din.
4:00pm suka fito a shirye cikin ankon atampa black mai zanen red flowers ajikinta an masu dogayen riguna fitted gown gaban rigar ya sha adon stone work ɗinkinsu iri ɗaya,takalminsu,jaka da mayafinsu kala ɗaya,kalar red yarinsu da sarkarsu suma red color ne sun sha red head,da ya ke red bai yawa a atampar ba sai ya bada ma'ana,sun haɗu sosai. Atare suka fito kamar dama su ake jira aka fara shiga motocin abokan ango ana wuce was gurin kamun.
Mota daya suka shiga su ukun sai N B A(Nigerian bar association) anan za'ayi kamun. Guri ya sha decoration masha'allah suna shiga suka zauna aka fara shagali, mc ya bada sanarwar isowar amarya da ango. Su Meerah da sauran yan mata da ke wajen suka je suka shiga da su.
Bayan sun dawo mazauninsu ne meerah ta dubi Farida ta ce "anyah! Kina ga su uncle za su zo kuwa? Farida ta ce "za su zo mana ba sun faɗa miki ba? Da damuwa a fuskar meerah ta ce" har yanzu ban gan su ba." Farida ta ce: ki kwantar da hankalinki yanzu aka fara na san za su zo.
Su Uncle lesh da Manish zasu zo kamun kuwa?
Me zai faru a Turin kamun? Ku biyoni a page na gaba danjin amsoshin wannan. Taku har kullum ummu-inteesar.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
🏤🏤P11🏤🏤
5:00 dot mc ya nemi ƙanwar ango y'ar auta shalele Meerah da ta zo kan step ita da kawayenta domin su nuna na su farin cikin a wannan ranar.
Daƙyar Meerah ta iya zuwa kan step ɗin domin ido sun yi yawa a kansu Farida ce ma tay mata jagora, adai-dai lokacin ne kuma Uncle Lesh da Manish su ka shigo filin bikin.
Suka nemi guri a ɗan gaba kaɗan suka zauna su na ɗan dube-dube ko za su hango su Meerah.
Ƙarar wakar da a ka sake ya sa hankalinsu ya koma kan step ɗin.
A can suka hango Meerah, Meenah da Farida da ke ta tiƙar rawa an sake masu wakar ado gwanja asha rawa-rawa sai takawa suke a tare kamar dama sun yi training.
Duk da cewa Meerah ba gwanar rawa ba ce amma a ranar ta cashe.
Nan da nan Uncle Lesh ya dauko wayarsa ya fara ɗaukar vidio.
A nan ango da amarya suka fito su na masu liƙi.
Ango Arif da amaryarsa Airah sun sha kyau masha'allah sun dace da juna sosai.
Su na gama rawar aka sa tafi,harda Uncle Lesh da Manish sai da suka tafa masu abin ya burge su sosai.
Su na dawowa daga gun rawar za su je mazauninsu su ka yi tozali da su Uncle. Dukkansu suka yi cirko-cirko,
Allah ya sa su Uncle ba su ga rawata ba Meerah ta faɗa a ranta. Uncle Lesh ne ya katse mata zancen zucin da ta ke da cewa "Sannunku y'an mata kun sha rawa kam." Uncle Manish ya ce "irin wannan kyau haka masha'allah kun yi kyau sosai.
Duka su ukun su ka rufe fuskarsu da tafin hannunsu wai sun ji kunya kenan.
Meenah ta ce "Lah! Uncle wai kun ga rawarmu? Uncle Lesh ya yi murmushi ya ce "Tun farko ma kuwa,kun iya rawa sosai Barin ma Meenah." aiko sai suka gudu wai sun ji kunya su uncle sun ga rawarsu.
Meerah ta ji daɗi sosai zuwan lesh ɗinta, a wannan ranar ne kuma soyayya ta kullu tsakanin Adil da farida.
A haka taron ya watse,wannan ranar ta zama ranar farinciki kuma ta shiga kundin tarihin matasan nan uku wato Adil Uncle Lesh da Manish.
Adil ya samu soyayyar farida da ya jima ya na dako a ranar, Lesh kuma ya samu damar yin doguwar hira da abar son sa Meenah duk da bai furta ba, Manish kuma ya samu amincewar Meerah duk da cewa ƙarya ta masa don ya titseye ta ne, amma shi a gurinsa ya yarda ta amince ne da gaske. Duk waɗannan abubuwan sun faru ne a wannan ranar.
Ranar Assabar ma su Uncle sun zo ɗaurin aure a nan suka yi abota da adil yayan Meerah har sukayi exchanging number waya.
*************
Bayan kwana 10 da gama bikin su Meerah suka koma makaranta, a ranar kuwa suka shiga ss2,murna gurin Meerah ba'a magana ta shiga ajin lesh ɗinta.
A nan fa Meerah ta zage da kyautatawa Uncle Lesh, komai ta ga alamar ya na so za ta mai, idan abin buƙata ne ta siyo ta kawo masa,sosai ta ke ƙaunarsa ko a labari ban taɓa jin labarin soyayya irin na Meerah ba,domin ta na son Uncle Lesh ne tare da duk abunda yake so,tana matuƙar son iyayensa da y'an uwansa duk da cewa bata sansu ba, amma ta na jin sonsu aranta.
Ko da akan hanya take tafiya ta na ƙara natsuwarta duk dattijo ko dattijuwar da ta gani ta na girmamasu ta na ji aranta kamar sune iyayen lesh.
***************
Meerah bata da wani aiki da ya wuce tunanin Lesh ko da barci ta ke mafarkinsa ta ke harda sambatu. Don ma Allah yasa ita kaɗaice a ɗakinta ba mai jin ta a lokacin da take sambatun.
Meerah ta na ji aranta cewa za ta iya sadaukar da rayuwarta da farincikinta akan na Uncle Lesh.
Me zai faru a makaranta? Shin uncle lesh zai bayyanar da soyayyarsa ga meenah?ya meerah zata kasance idan taji abinda ke ran lesh game da kawarta? Ku biyoni a page na gaba Dan samun amsoshin...
Taku har kullum (ummu-inteesar)
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)
🏤🏤P12🏤🏤
Masoya ina gdy agareku Allah yabar so da kauna a tsakaninmu
*****************
A wata ranar Monday ne bayan Uncle Lesh ya gama darasinsa na maths a ajin su Meerah ya na gamawa ana buga ƙararrawar fita break dama second period yake da.
Dalibai suka fara fita break uncle na nan tsaye har duka daliban class ɗin suka watse, ya rage saura Meenah, Meerah da Farida a class ɗin,
Uncle ya ƙaraso inda suke ya ce "Meenah ina son yin magana da ke." ta ce "Ni kuma uncle?" Ya ce "Eh ke." sa'annan ya maida dubansa ga su Meerah ya ce "Meerah don Allah ko za ku ɗan bamu guri kaɗan? Inaso na yi magana da ita ne."
Meerah ta kalle shi cikin so da ƙauna ta yi murmushin yaƙe ta ce "Me zai hana? ta ja hannun Farida ta ce "Mu je.", duk da cewa taji haushin maganar aganinta ya yi masu wulaƙanci ne,
Meye zai faɗawa Meenar da ba zai faɗa agaban su ba? Amma hakan bai hana ta duban Meenah ba tare da cewa "Idan kun gama kya same mu a waje mu mun yi gaba."
Kafin Meenah ta ce wani Abu har sun bar gurin, meenah ta ɗan bata rai kaɗan ta ce "Habah! Uncle ya za ka korar mun ƙawaye? Meye za ka faɗamun da bazaka faɗa agabansu ba? Su fa aminaina ne."
Ta dube shi a ɗan hasale.
Ya ce "Sorry ranki yadaɗe tuba na ke ba zan ƙara ba,dama da akwai wata magana muhimmiya da nake son na yi dake."
Ba tare da ta kalle sa ba ta ce "Ina jin ka
Murmushi ya yi sannan ya ce "Meenah ban san taya zan fara miki bayani ba ataƙaice dai ina sonki meenah."
Zabura meenah ta yi tace "What! me kace? Yace "ƙwarai ina matukar ƙaunarki Meenah,ni kaina ban san sanda sonki ya shiga zuciyata har haka ba, I really love u meenah."
***************
Miƙewa tsaye Meenah ta yi ta fara tafiya za ta bar ajin, domin bata ma san me za ta cewa uncle ba,ya zai zo mata da wannan maganar? kodai ya na so ya raina mata hankali ne? Eh kam rainin hankali mana ta faɗa a ranta,duk da ta san cewa Uncle Manish ya na son Meerah kuma suna tare, amma ita sai take ganin kamar ita Meerar ba shi take so ba Uncle Lesh take so, tabbas duk mai hankali zai iya gano cewa Meerah ta na ƙaunar Uncle Lesh don kulawar da take ba shi bata bawa manish ita,wannan kawai ya isa ka gane cewa ta na ƙaunarsa.
Amma me Uncle Malesh ke nufi da ya na sonta? ya na so Yace bai fahimci *soyayyar Meerah* agaresa ba ne ko yaya? Meenah ce ke ta wannan tunanin a lokacin da take tafiya har ta fice daga ajin.
Uncle Lesh na kiran ta amma ina ta yi zurfi a tunani bata ma jinsa. Uncle Lesh kuwa ya fi minti biyar tsaye a ajin sake da baki kamar dolo,to me Meenah ke nufi da tashi ta yi tafiyarta bako amsa don Yace ya na sonta?ko bai kai matsayin da za'a so shi ba ne?ya tambayi zuciyarsa tambayar da baya da amsarta,
A haka ya bar ajin jiki ba ƙwari ya na fatar Allah ya sa ta karɓi soyayyarsa.
******************
Su Meerah kuwa suna barin class ɗin suka je ƙarƙashin wata bishiya nesa da ajin suka zauna suna jiran meenah. Farida na bawa meerah labari amma bata fahimtar komai
Hankalinta na class ta na tunanin shin me Uncle Lesh zai gayawa Meenah da ya koro su? Ya wuce Yace ya na sonta? Wata zuciyar ta faɗa mata, damm gabanta ya buga da ƙarfi idan kuwa haka ta faru shikenan ni meerah farinciki na ya zo ,ta fada a zuciyar ta.
Ta na cikin wannan zancen zucin ne Meenah ta ƙaraso gurinsu ranta a ɗan ɓace, ta zauna kusa da su,farida ce tace "Meya faru ne meenah? Na ga ranki a ɓace."
Meenah ta ce "Hmmmm! Ke dai bari kawai, wai su maza meyasa basu da kunya ne?"
"Wani Abu kuma ya faru?" Meerah ta tambaya.
Meenah ta ce "Wai ni Uncle zai duba ya ce ya na sona?" Ras! ras!! dam!!! sautin bugawar ƙirjin Meerah kenan.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" ta furta tare da zabura da ƙarfi har sai da suka tsorata dukkansu har su na haɗa baki gurin cewa "Menene meerah?" Ta ce "Ah! Ba komai."
"kamarya bakomai? gashi kin firgita sosai." Farida ta fada.
Meerah ta ce "Ba fa komai ina ji wani ƙwaro ne ya shigar mun Riga bari naje class na duba." Ta mike ta na kakkabe-kakkaben ƙarya ta bar gurin.
******************
Ta na zuwa class ta je seat ɗin baya gaba ɗaya ta zauna tare da kifa kanta a desk ɗin seat ɗin.
Ta fara kuka a hankali ta na faɗa aranta "Shikenan farinciki na ya kare a duniya, koda kuwa zan yi farinciki kaɗan ne tunda na rasa soyayyar Lesh, Ashe dai ina yaudarar kaina ne da nake tunanin zai fahimceni,na ke mafarkin zai so ni watarana. Ashe shi Meenah yake so tabbas ba zan iya shiga tsakaninsa da farincikinsa ba.
Idan dai har Meenah itace farincikinsa tabbas zan taimaka masa ya samu soyayyar ta har ya aureta koda hakan na nufin mutuwa ta.
Na zaɓi farincikinsa akan rayuwata. Uncle nay maka alkawari insha'allah zan taimaka ma ka sami Meenah tunda har ka furta ka na sonta da bakinka,nima na ƙara sonta fiye da da ma."
Ta na zancen zucin ta na cigaba da kuka. A haka su meenah suka shigo class ɗin suka same ta,dama sun biyo ta ne da suka ga ta jima bata dawo ba.
A seat ɗin baya suka ganta ta kifa kai,da sauri suka nufo ta.
"Subhanallah! meya faru kuma Meerah? Kamar kuka ki ke fa?" A ruɗe meenah ta ɗago kan Meerah da hannayenta, atare suka zaro ido da farida.
"Kuka kuma Meerah harda hawaye? Meke damunki ne?" Farida ta tambaya a kiɗime.
Bata ce masu komai ba sai ƙoƙarin dakatar da kukan take ta kasa.
Meenah tace "kodai cizon ƙwaron kike wa kuka?" Nan ma shiru ta masu ta cigaba da hawaye.
Wai wai wai ya su meenah zasu kare da meerah? Zata fada masu damuwarta kuwa?
Muje zuwa😀😀😀😀😀(ummu-inteesar) ce ke nishadantar daku.
❤❤ SOYAYYAR MEERAH❤❤
Na: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(ummu-inteesar)08109634202
Dan Allah readers adinga comment ga numberta nan a sama duk Wanda yakeda wani sharhi dayaga yakamata yayi kofa a bude take,ina son inji ra'ayoyinku game da littafinnan.ngd saina jiku.
🏤🏤P13🏤🏤
Farida ta kalli Meenah tace "Meenah ko za mu je mu sanar da principal cewar Meerah bata da lafiya amana izini mu je mu kaita gida, Meenah tace "Eh Farida je ki ki yi report ni zan tsaya nan tare da ita bai kamata abarta ita kaɗai ba."
Sai a lokacin Meerah ta haɗo kalmomi daƙyar tace "A'a ku barshi kawai ba sai mun je gida ba cikina ke ciwo kuma kaɗan ne ma ,yama daina yanzu saura kadan." Meenah tace "Farida yi maza ki dawo mu je kafin sauran ɗalibai su dawo su tarad da ita Ahaka."
"Ba ku ji me na ce ba? na ji sauƙi fa ba sai mun je gida ba." Ko ta kanta basu bi ba farida ta wuce zuwa office ɗin principal ta nemo masu izini,suka ja ta zuwa gida don dole ta bisu.
A ɗakinta suka yi masauki bayan sun gaisa da Ammi suka sanar da ita abinda ya faru a makaranta. Akan gado suka zaunar da Meerah Ammi ce ta shigo ɗakin ta miƙo masu magani tace Su bawa Meerah ta sha.
Farida ce ta ɗauko glass cup da jug da ke bedside ɗin Meerah da ruwa aciki, ta tsiyaya mata a kofin.
Meenah ta ɓallo maganin ciwon cikin da ammi ta bata ta miƙawa Meerah. Farida ta bata ruwa a cup suka tasa ta a gaba dole ta sha, dukda ta san cewa ƙarya take kukan baƙin ciki take
Cutar soyayya ke damunta ba ciwon ciki ba.
Ta na gama sha ta kwanta akan gado ta rufe ido kamar mai barcin gaske,Ta na cigaba da kukan zuci da tunane-tunanenta. Su kuwa suna ganin ta yi barci suka bar ɗakin,suka je parlourn Ammi suna kallo kafin lokacin tashi makaranta ya yi su je gida. Suna taɓa hira sama-sama da ammi.
*****************
Adil ne ya shigo ɗakin tare da sallama yace "a'ah yau Ammi ke ce da yan fira haka?" Ya faɗa ya na kallon su Farida dake zaune a ƙasa kan center carpet ɗin ɗakin. ya ɗaura da cewa "Me ya dawo da ku gida dai-dai wannan lokacin? Bafa a tashi daga makaranta ba,ko kunyi dodging ne?"
Ammi ta yi murmushi tace "sun kawo Meerah ne bata da lafiya." "Subhanallah, ina take ne?" Ya fada.
Ammi tace "Ta na ɗakinta ta na barci." Allah ya sawwake yace:sannan ya mayar da dubansa ga farida yace "Meyasa baku koma school ba bayan kun kawota?" Farida ta yi murmushi tace "uhmmm! Yaya adil kawai dai mun ga saura kaɗan a tashi ne shiyasa bamu koma ba."
Shima murmushi ya sakar mata yace "Wato Ku ga dodgers koh?"
Ta kuma yin wani lallausan murmushin dake kiɗimar da shi,bata ce komai ba. Ammi na lura da irin kallo da murmushin da suke wa junansu.
Murmushi tayi aranta take cewa da alama masoyan juna ne. Adil ne ya katse mata tunani da cewa "Ammina ni zan ɗan fita kaɗan na katse maku fira."
Ya maida dubansa ga farida yace "Sister ina jiranki a waje, akwai abunda nake so na tambayeki game da meerah."
Ammi ta yi murmushi kawai tace aranta "oh! Su Adil angirma wai Amminsa zai wa wayo,wai zai tambayeta gameda meerah in HaKa ne ya tambayi meenah mana na ga duk ɗaya suke a wajen meerah. Oh ni karima yayana sun girma, har autata ma da alama ta kamu dan ina lura da ita bata da aiki sai tunani Allah dai shige mana gaba ya zaɓa masu mafi alkhairi a rayuwa."
Adil da ya ji ammi ta yi shiru sai kawai yayi gaba abinsa.
***************
Farida kuwa kunya ta hana ta tashi gashi Meenah sai dariya take mata ƙasa-ƙasa yadda Ammi ba za ta ji ba.
Sai can bayan mintuna biyu farida ta yi ƙarfin halin cewa "amm! Ammi bara na je na amsa kiran yaya Adil." Ta mike jiki a sanyaye .
Ammi ta yi murmushi kawai tace "to ta yaya Adil adawo lafiya." A kunyace farida ta bar parlourn
Da alama Ammi ta karto mu ta faɗa aranta.
Me adil zai fadawa farida ne HK?ya zasu kwashe da meerah zata fada masu gsky kuwa?
Muje zuwa❤❤❤.....
❤❤soyayyar meerah❤❤
Na:Rukayya Ibrahim lawal(ummu-inteesar)
🏤🏤P14🏤🏤
A kofar gida ta sameshi har ya fara kosawa da jiranta.
Tace:gani yaya
Yace: sai yanzu kikaga damar zuwa?har na fara gajiya da tsayuwa
Tace:yi hakuri yaya kunya ce ta hanani tashi,sai wani murmushi kake zabgamun a gaban ammi.
Itama ammin sai murmushi take tana kallonmu, ni fa ina ganin kamar ta harbo jirginka.
Yace: ta harbo jirginmu dai,kajimun ke zaki wani cire kanki,ince kedinma tun shigowata parlourn kike zabgamun murmushi.
Farida ta dan dubeshi tace: lah!yaya adil banda sharri fa,yaushe nama murmushi?
Yace: au tambayata ma kike? Yo dama yaushe zaki san kinyi bayan kin tsunduma kokin kauna?.
Farida ta shagwabe fuska tace: kai yaya gaskiya ni bana son sharri,wanne kogi kuma na shiga?
Murmushi yayi yace: kyaji dashi ni bana son gulma kidaina cemun wani yaya,ki sakamun wani suna mai dadi irin na masoya ya fada tare da kashe mata ido daya.
Tayi wani raurau da ido tace:kamar wane suna?
Yace: na masoya sai, misali kice sweety,hubby ko honey dadai sauransu.
Hannayenta tasa ta rufe fuskarta alamar taji kunya ashagwabe tace: ni bazan iya ba.
Ya dubeta sosai cikin sigar soyayya yace:aiko sai kin iya.
Tace: nidai gaskiya ya......
Kafin ta karasa ya tari numfashinta da cewa:kul naji kin cemun yaya sai munyi fada.
Tace:to me zancema?
Ki zaba daga cikin wadanda na fada maki yanzu.
Tace:bansan wane yafi dadi ba zabamun.
Yace:to kicemun hubby, fada naji.
Tace: uhmm
Anya kina sona kuwa?ya fada
Tayi saurin cewa sosaima hubby tana fada ta gudu cikin gidan.
Yana kiranta tamai banza,kunya dukta cika ta.
Wai ita da yaya adil ne yau suke wannan zancen haka.
Da yaga bazata dawo ba. Sai kawai yayi murmushi yace: Allah sarki farida ta akwai kunya shiyasa nake sonki da yawa.
Har ya manta da zancen rashin lafiyar meerah sai a lokacin ya tuna.
Yace:oh! Baby farida ta mantar dani sweet sister na ba lafiya ban ko duba ta ba.
Kuma Idan na koma ciki yanzu ammi zata dago ni.
Bari naje na dawo sai na ganta.
*****************
Karfe 2:00 su farida sukayi wa ammi sallama zasu gida. Kafin su wuce suka leka dakin meerah suga ko ta farka.
Adai-dai lokacin ita kuwa meerah tana kishingide ta tarye kanta da filo sai hawaye take wani na korar wani.
Tana jin sallamarsu ta kwanta da sauri gami da rufe ido dan bata so su fahimci halin da take ciki.
Meenah tashigo cikin dakin tare da cewa: kinga malama tashi dan muriga da munganki ba barci kike ba. Fada mana mekike boye kokarin boye mana? Ko kin manta mu aminanki ne? Suka zauna a gefen gadonta.
Haka ta tashi zaune a kunyace. farida tace: meerah meke damunki ne? Kin fa samu a damuwa ki fada mana dan Allah.
Bama son ganinki a wannan yanayin watakil ma iya taimaka maki koda da addu'a ne.
Kawai sai meerah ta kifa kanta a cinyar farida ta fashe da kuka. Tace: ku taimakeni aminaina Ku taimakeni da addu'a ayanzu ita kadai nake bukata daga gareku.
Aikuwa hankalinsu ya kuma tashi suna matukar son junansu sosai. Basa son abunda zai dame dayanzu.
Meenah ce ta fara hawaye tana cewa: zamu taimaka maki da addu'a insha'allah. Amma ki bamu amsa tsakaninki da Allah idan na tambayeki.
Tace:zan fada maku gaskiya inhar nasan amsar.
Meenah tace: tsakaninki da Allah meerah bakya son uncle? Tace wane uncle?
Meenah tace uncle malesh.
Hmmmm! Ko wace amsa meerah zata basu? Anya kuwa readers kuna ganin meerah zata fada masu gaskiya kamar yadda ta fada? Meye zai faru tsakanin wadannan aminan uku?
Ni kaina INA son jin amsar wadannan tambayoyi
Muje zuwa😄😄😄😄😄(ummu-inteesar) ce
❤❤Soyayyar meerah❤❤
Na:Rukayya Ibrahim lawal(ummu-inteesar)
🏤🏤P15🏤🏤
Readers adaure arika comment,comment dinku zai karfafani naji karfin cigaba da typing ko akasin hk.
Ras gaban meerah ya fadi meenah ta kartoni kenan,
Ta fada a zuciyarta a fili kuwa tasha mur kamar bata taba dariya ba. Tace: wannan wace irin tambaya ce meenah?
Meenah tace: tambaya ce mai ma'ana kuwa wacca take bukatar amsa.
Ko kin manta cewa nasan shakuwar dake tsakaninku.
Haka kuma dazu daga na fada maku cewar uncle malesh yace yana sona kika firgita har yanzu kuma bamu sake gane kanki ba.
Sai bayan munzo nan ne na tariyo baya na fahimci cewa shock ne ya kamaki a lokacin.
Tabbas kina son uncle malesh meerah, dan bakya ma wani kulawa da uncle manish. Pretending kawai kike.
Farida tace: kwarai kuwa ni ma ina kula dake tun farkon fara alakarki da uncle malesh. Ki kan kasance cikin farin ciki duk lkcn da kuke tare. Da alama kina matukar kaunarsa musamman idan aka lura da.......
Meerah ce ta katse ta da cewa: ya isheni Ku daina wannan game din bana so😡😡cikin karaji take zancen kamar da gaske.
Meerah ta cigaba da cewa: meyasa kuke abu kamar baku san komai ba? Ko kun manta soyayyar dake tsakanina da uncle manish ne? Ina hankalinku yaje kuka manta cewa uncle malesh manish aminan juna ne? Bana so karku sake mun makamanciyar wannan tambayar.
Ni manish nakeso kuma zan cigaba da sonsa har abada.
Tana kai nan a zancenta ta tashi fuuu tabar dakin tana fushin karya ko sallama basuyi ba. (Ku jimin meerah fa,🤔🤔an Sosa mata inda ke mata kaikayi.anaso anakai kasuwa🤪)
Meenah da farida kuwa baki suka sake kamar wawaye🤪🤪suka bita da kallo.da Alama kallon mamaki suke mata yadda ta fututtuke tana surfa masu masifa.
Wacca ada ko daga masu murya bata tabayi ba.
****************
Suna nan zaune a'inda ta barsu kowacce da tunanin da take aranta har kusan mintuna biyar.
Can meenah ta dago ta dubi farida tace: farida mekika fahimta game da meerah?
Farida ta nisa hmmm! Inaga kamar dagaske ba komai a ranta game da uncle malesh duba da irin yadda ta dage tana surfa mana masifa.
Inaga abinda yafi kar mu sake tada mata zancen idan muna san kanmu da lafiya.(yafi kam dan awannan karon meerah bazata raga maku ba🤪)
Meenah tace: hakane kawata mubarta tunda tace bakomai, idan masara ta gasu ita ke magana.(lallai kam meenah ke ma fa kin iya magana ita da kanta zata kawo kanta ahto😄😄)
Da haka suka kai karshen wannan maganar suka mike da niyyar barin dakin.
Sai ga meerah ta shigo da waya a kunnenta tana magana, da alama tana amsa waya ne.
Ko kallon side din dasuke batayi ba ta wuce ta zauna a gefen gadonta tana cewa: sosai ma kuwa nake kaunarka, ta danyi shiru nadan lkc can kuma tace: lah! Waya gayama haka? Ina fa kaunarka sosai.
Tayi danyi dariya kadan. Ta juyo ta wurga masu harara😏 alamar me suke jira da bazasu fita su bata guri ba.
Ai kuwa suka bar dakin kawai batare da since komai ba.(ah to me kuwa zasu ce lamarin meerah Sai dai a zuba mata ido.
Hmmm! Ko ya zata kaya tsakaninsu
Muje zuwa(ummu-inteesar) ce🥰🥰❤❤❤
❤❤Soyayya meerah❤❤
Na: Rukayya ibrahim lawal(ummu-inteesar)
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga
Feenat mansoor,zuwaira Ahmad muhd,Aisha ridwan dahir& maryam A d/daji ina godiya agareku Allah ya bar kauna.
🏤🏤P16🏤🏤
A kofar gidan farida tace: inaga da uncle manish ne take magana, ko yaushe fara waya?oho.
Meenah tace: ita tajiyo koma waye, sai anjima. Ta tari napep tabar unguwar.
Farida ta shige gidansu.
*****************
Kwanan meerah biyu a gida tana jinyar zuciyarta (wadda ta cika da so da kaunar lesh) kafin ta koma makaranta.
A wata ranar Thursday ne a makaranta bayan meerah ta dawo daga hutun jinyar da taje.
Meenah ta zo masu da Dan wake hadin salak da tumatir yaji dafaffen kwai da yaji ga mai.
Suna ci suna fira a aji lokacin break.
Dama sun shirya bayan tayi fushi dasu na kwana biyu saboda abinda ya faru tsakaninsu. Dama can ba'a taba jin Kansu ba wannan ne na farko.
Uncle malesh ne ya shigo ajin da fara'a a fuskarsa. bayan ya masu sallama yace: sannunku yan mata, abinci kuke ci bako tayi?
Meerah tayi farat tace: oh! Sorry uncle dinmu gashi kaci, mu zamu ma iya baka duka koh meenah? Ta karashe zancen tana duban meenah sai faman murmushi take.(kau jimun meerah da kyautar abunda ba naki ba da an labaki🤪🤪)
Meenah tace: tab ai sai dai ki bashi naki,tare da murguda baki kadan.😏😙
Uncle yace: iyyeah! Ni ake murgudawa baki akan abinci?
Lallai meenah kin iya rowa.
Eh andai ji ba za'a bayar ba meenah ta fada.
Meerah tayi kicin-kicin da rai gami da cire hannunta a kular tace: to nima bazan ci abin marowata ba,kuci kayanku.
Ta dubi meenah tace: ke kuma bakina takama ke kika kawo ba? To anbar miki ke jaka ki cinye.🙊 ta mayar da dubanta ga farida tace: kema ta koya maki rowa kina jin me take fada kinyi shiru,kuma a haka kikeso na baki yayana, to badani ba. Ta murguda masu baki. sa'annan ta mayar da dubanta ga uncle Wanda yake tsaye guri daya yana kallonsu yana murmushi. Tace: muje uncle dina muje waje muyi hira, tunda an mana rowa.
Uncle malesh ya dubeta yace: uncle dinki ke kadai meerah? Race:eh uncle lesh dina ni kadai banda marowata ko harsu? Ta mayar mai da tambaya.
Yace: a'a banda su.
Tace: yawwa uncle lesh dina muje.
Tayi gaba zata bar ajin da murmushi a fuskarta. Ya bi bayanta da kallo sa'annan ya maida dubansa gasu meenah sunyi wani sukui suna kallonsu.
Can farida tace: ah! Uncle da meerah abin baikai can ba kuzo gashi.
Meerah ta juyo tace: bama so sai da aka gama ja mana rai akan Dan waken da baifi karfina ba?.
Ai uncle yafi karfin wannan dan waken naku. Muje uncle. ta juya ta tafi yabi bayanta.
Meenah tayi murmushi kawai batace komai ba.
A ranta take cewa meerah kenan sarauniyar pretending.
Farida ce ta katseta da cewa: meenah sun tafi dagaske fa.
Meenah tace: ke rabudasu su suka jiyo,muci kayan mu kawai.
Farida bata ce komai ba taci gaba da cin dan waken.
*******************
A bangaren uncle lesh da meerah kuwa bayan sun fice daga ajin guri suka samu kusa da ajin suka tsaya.
Uncle lesh ya kalleta yace: kince muje waje muyi hira,to miye labari
Fuskar meerah ta bayyanar da farinciki karara cikin wani irin yanayi jin dadi ta kalleshi tace: wane irin labari?
Yace: kibani koma wane iri ne aike kika ce zamuyi hira Dan haka yau sai kin bani lbr.
Murmushi tayi sosai har dimple din dake Gefen kumatunta ya lotsa.
Tace:labari daya nake da idan kanaso labarin soyayyar wata yarinya. Yarinyar tana ban tausayi shiyasa ban manta ba.
Yace:ina jinki.
Ta sukunyar da kanta ta fara:
A wani gari anyi wata matashiyar yarinya yar gatan iyayenta da yan uwanta. Yarinyar tana da tarin masoya saboda farin jininta. Amma bata kula kowa acikinsu.Allah ya jarabce ta da tsananin son wani kyakkyawan saurayi. Tana yi masa so mai tsanani irin Wanda takeji zata iya rasa ranta akanshi.
Amma sbd girman saurayin a idonta ta kasa sanar dashi. Shi kuma yaki fahimtarta duk da cewa tana kyautata mai matuka. Daga karshe sai ta samu labarin cewa ya fitar da wacca zai aura. Gashi sonsa yay mata mugun kamu hakan yasa ta shiga wani yanayi,Wanda ta kasance tsakanin mutuwa da rayuwa......
❤❤Soyayyar meerah❤❤
Na: Rukayya ibrahim lawal(ummu-inteesar) 08109634202
🏤🏤P17🏤🏤
Ta na kai nan a labarinta ta dan tsagaita tare da satar kallonsa.
Tana so taga wanne yanayi yake ciki.
A ranta kuma fatar Allah yasa ya fahimci manufarta tabashi wannan labari,kuma ya tausayawa rayuwarta.
Shikuwa uncle lesh ya nutsu sosai yanajin labarin. Aransa kuma yana tasauyawa wannan yarinyar. Kwasam yaji tayi shiru sai ya dago kansa yaga ko lfy tayi shiru.
Sai idanunshi suka sauka akan wasu students dake Dan nesa dasu kadan sun tsaya suna kallonsu suna magana kasa-kasa da alama gulmarsu suke.
Yakuma duba dayan side din nan ma hk students ne a tsattsaye suna kallonsu.
Ya mayar da dubansa gareta
Adaidai lokacin itama ta dago sosai ta kallesa sai ko suka hada ido.
Sai yaga tana mai wani murmushi mai wuyar fassarawa.
Shiru ya gifta na yan sakwanni.shine ya katse shirun ta hanyar cewa: am.. Meerah ko zamu bar labarin zuwa wani lokaci sai ki iyarmin kinga sauran students sun sa mana ido.
Cikin tsananin jin kunya ta sauke idonta kasa. Ya salam! Me nake shirin aikatawa ne? Ta fada a ranta.
A fili kuwa cewa tayi shikenan uncle dama labarin yakusa zuwa karshe saura kadan. Amma yarinyar bata baka tausayi ba?
Ya nisa hmmm! Kafin yace: gaskiya na tausaya mata matuka. Wannan fa shi ake kira son maso wani. Da zan ganta shawara daya zan bata shine ta furta ko kuma ta hakura dashi gaba daya.
Yana gama fadar haka yace bye. Bai jira cewarta ba yabar gurin kasancewar lokacin komawa class tayi.
Meerah kuwa a haka ta tsaya agurin har kusan mintuna biyu.
Tana kokarin gano yanayin uncle.
Anyah! Ya fahimci manufarta kuwa.
Kamar bai wani damu ba bare yayi nazari akan labarinta har ya fahimceta.
Cikin rashin samun madafa da sacewar gwiwa meerah ta juya ta koma class dinsu.
A haka har ta dawo gida tunane-tunane kawai take tare da fatar Allah yasa yayi nazari akan labarinta dukda tasan cewa bata kwatanta mishi sosai yadda zaiyi saurin ganewa ba,amma ya kamata yaganen.
A haka ta wuni da wannan tunanin, wani bangare na zuciyarta najin haushin su meenah da suka mai rowa.
************
Ranar Friday tun safe meerah take kai kawo tsakanin kitchen da store tana kokarin hada Dan wake.
Dauko wancan kwaba wannan yanka wancan. A haka ta kammala hada dan waken ta ta dauko kuloli masu kyau. ta zuba dan waken a babbar kular sai da ta kusa cika ta.
Ta dauko dayar kular karamar waccan ta saka hadin salak da tumatir da kwai aciki.
A Leda ta daura yaji mai dadi ta saka a kular da soyyen mai.
Sa'annan ta dibarwa ammi da yaya adil kowa ta masa nasa plate ta kaimashi.
Duk wannan abin da take ammi na lura da ita.
Sai murmushi take tayi tana aikin.
Tana kammalawa dama tayi wanka. Taje ta sako uniform din ta tafito tanata sauri.
**********"
Ammi da adil suna parlourn ammin suna cin dan waken tashigo rataye da jakarta ta makaranta tace: ammi na,yayana ni zan tafi.
Ammi ta dubeta tace bafa kiyi break ba meerah, a haka zaki fita ciki bakomai?
Murmushi tayi tace: ammi ina sauri ne nai latti har 8:20 fa,nayi break din idan naje can.
Adil ne yace: kanwata da kin daure kinci ko dan waken nan ne,yayi dadi sosai,wai da inji kikayi koda hannu? Ya karashe zancen yana kai wata lomar........
Muje zuwa
(Ummu-inteesar)ce
❤❤Soyayyar meerah❤❤
Na: Rukayya Ibrahim lawal
Readers adinga comment dan Allah
🏤🏤P18🏤🏤
Dariya meerah tayi sosai tace: a'a yaya bada inji bane
Wata sabuwar na'ura ce akayi da ka saka fulawarka aciki ka rubuta Dan wake ajikin na'urar kawai sai dai ka ganshi a plate an hadama komai aciki.
Adil ya fiddo ido waje yace: kai dagaske kanwata? Nawa na'urar take? A'ina ake siyarwa? Yaushe aka sameta anan gidan?. Ajere yayi wannan tambayoyin yana kara kai loma.
Dariya sosai meerah tayi tace: dagaske kuwa yaya, a wani gari mai suna Dan wake ake siyarwa.
Ta karashe zancen tana mai dariya.
Sai a lokacin adil yagane shakiyanci ne kanwar tasa take masa tana nufin yana santi ne.
Yace: ke nifa ba santi nake ba,kawai na tambaya ne dan naga kamar bada hannu akayi ba.ko ammi?
Ammi da tun sanda suka fara dramar take masu dariya sai a lokacin tace: kwarai ba santi kake ba,anan ma ba Wanda yace kayi.
Suka saka dariya atare ita da meerah.
Meerah tace: kaga yaya adil dan Allah taimaka ka sauke ni a school kaga nayi latti, idan nace zan tsaya tare napep zan karayin Lattin.
Yace: to, ajiye plate din yayi, suka yiwa ammi sallama ya fiddo babur dinshi.
Ta dauko kulolinta a Leda viva suka bar gidan.
***************
Sai 8:40 ta isa school yana sauke ta ta tarar ana tare late comers.
Sa'arta daya uncle manish ne on duty.
Kawai sai yace: an yafe kowa yaje aji.
Tana zuwa class dinsu ta tarar har malam habib ya fara darasin sa.
Ta shiga dakyar ya barta ta zauna.
Yace: ya daga mata kafa na yau dan bata taba yin haka ba.
Yana fita malama zainab ta shigo.
Meerah kam duk ta kagu a tashi break ta kaiwa uncle lesh dan wakensa.
Idanta na wajen window ko zata hangoshi.
Ana tashi break farida da meenah suka matso kusa da ita.
Farida tace: kawata me kika zo mana dashi ne? Kice yau ma lafiya qlau ne ba siyan fanke?
Meenah tace: aikam,ni kagu ma naga miye aciki.(😄😄😄 kaji uwayen kwadayi)
Meerah ta masu banza ko kallon arziki basu samu ba,bare su sa ran zata kula su.
Dama tun jiya take jin haushinsu saboda sun wa uncle lesh dinta rowa.(👍🏻👍🏻dakyau meerah,amma inkika hana su meenah ya zasuyi?)
Maimakon ta kallesu sai taci gaba da kallon wajen window.
Tana cikin kallon kuwa ta hangoshi yazo zai wuce zuwa office dinsu.
Da sauri ta tashi taje gunsa uncle lesh! Ta kira sunanshi.
Ya tsaya cak jin muryarta,ta karaso gunsa tace: ina kwana uncle
Yace: lafiya qlau,yakike?
Tace: alhamdulillah
Yace: ya akayi ne meerarmu?
Tace: jirani anan,kona sameka a office?
Yace: a'a bari na jiraki anan.
murmushi kawai tayi ta juya cikin ajin.
Tana shiga farida na kokarin rufe kular dan waken..........
Muje zuwa😄😄
(Ummu-inteesar)
❤❤Soyayyar meerah❤❤
Na: Rukayya Ibrahim lawal(ummu-inteesar) 08109634202
Ga numberta nan asama ga wanda ke sonyin comment
Wannan page din naku ne.
Farida lawal nuhu
&maryam s/fawa.
Ina yinku over Allah ya bar kauna.
🏤🏤P19🏤🏤
Yi tayi kamar bata ga me suke ba.
Ta zaro plate daya a ledar da spoon ta hada dan waken ta saka wani plate din ta rufe.
Ta rufe kulolin tabar ajin daure da fuska
Tana zuwa gunsa ta sake fuska tace: uncle lesh dina gashi, ta mika masa ledar.
Ya karba yace: miye aciki?
Meerah tayi murmushi tace: Idan kaje office ka bude zaka gani.
Yace:to,manish za'a kaiwa koh?
Tace: a'a naka ne.
Yace: ni da shi kenan?
Tace: eh amma dan kai na kawo.
Tana kai nan a zancenta ta juya tayi cikin class.
Yana ganin shigewarta shima ya juya ya fara tafiya da ledar a hannunsa.
Yana tunanin wai me yarinyar nan meerah ke nufi da shi ne? Tana yawan kyautata masa gashi tana girmamashi.
Abu daya ke daure mai kai game da ita shine: yadda take kiranshi uncle lesh dinta, wannan lesh din ma ita ta saka masa a'iya saninsa malesh ne sunansa ita kadai ce ke kiranshi da lesh.
Yayi-yayi kwakwalwarsa ta bashi amsar dalilin da yasa meerah ke masa haka, ya kasa samun amsa.
Da wannan tunanin ya isa office dinsu ya tarar da uncle manish a zaune a office din.
***************
Manish yace: a'ah malesh daga ina haka? Wannan ledar fa? Ya jero mai tambayoyin a tare.
Malesh yace: daga ss3 nake, wannan ledar kuma meerar ka ce ta bani,tace ni da kai.
Uncle manish ya washe hakora yace: habadai! Bude muga miye a ciki.
Malesh ya bude ledar ya fito da kulolin. Ya fara budawa ai kuwa sai yayi tozali da dan waken. Ya bude dayar kular yaga hadin salak da dafaffen kwai.
A ransa yace: tab meerah ke nan.
Shi kwata-kwata ya manta ma da anyi wani zancen dan wake jiya. Bare ya tuno yadda akayi aransa yace: oh! Meerah taji haushi abunda akamin kenan,shine tamun nawa.
Ashe shine dalilin da yasa tace danni ta kawo?
Manish ne ya katse mai tunani da cewa lallai meerah ta fara sona, tunda har ta fara damuwa dani haka.
Allah sarki! Kila ma shine abunda ya tsaidata har tai latti.
Shidai malesh bai ce komai ba sai murmushi da yayi. suka ci dan waken suna zuba santi.(adil part 2 kenan😄😄😄😄😄😄lallai meerah kina 🔥🔥gun girki)
***************
Bayan wata daya su meerah suka fara shirin exam din first term ss2.
Meerah ta dage da karatu mussanman subject din mutuminta.
Bata so ta fadi. Dan kar yaga kasawarta.
Adaidai wannan lokacin ne uncle malesh ya sako meenah agaba akan sai ta bashi amsar ko ta amince da soyayyarsa.
Domin har zuwa wannan lokacin meenah bata ce dashi komai ba.
Bata ma kulashi.
Yayi ta bibiyarta da zancen tayi kamar bata San meyake nufi ba.
Ya nuna mata so ta kowacce fuska da yake ganin zata fahimta. Amma taki kulashi.
Izuwa yanzu hakurinsa ya fara karewa. Yanaji kamar yayi gauka saboda meenah.
Akan hakane ya yanke hukuncin tinkarar meerah da zancen ko zata taimaka mai ta shawo mai kan meenah.
Hmmmm! Readers yakuke gani meerah zata kasance bayan lesh yayi magana da ita akan zancen meenah?🤔🤔🤔
Muje zuwa (ummu-inteesar ce)❤❤
❤❤Soyayyar meerah❤❤
Na: Rukayya Ibrahim lawal(Ummu-inteesar)08109634202
🏤🏤P20🏤🏤
Akan wannan dalilin ne wataranar Friday yaje ya sami meerah bayan sun fito daga exam. Tana tare da kawayen nata kamar kullum.
Yana karasawa gurin ya masu sallama. Suka amsa.
Meenah ta kawar dakai dan ta fara jin haushinsa zuwa yanzu. Aranta tace maye,yau ma ka dawo koh?
Ya dubi meerah yace: meerar mu ina son magana dake. Ko zaki bani time dinki kadan?
Meerah tayi murmushi sosai har hakoranta suka bayyana. Tace: ah! Eh, me zai hana. Ina jinka.
Yace: a'a kizo muje waje muyi sirri. saboda akwai wadanda bana so suji anan. Ya fada yana satar kallon meenah. Wai ko zaiga yanayinta ya canza. Amma baiga ta damu ba. Sai ma tafiyarta da tayi tabar gurin.
Meerah tace: shikenan muje uncle. Suka bar farida a tsaye gurin.
***************
Bayan sun samu gurin da bahayaniya sun tsaya. Uncle malesh yace: meerah wani taimako nakeso daga gareki. Zakimin?
Eh meerah tace: tare da sakarmai lallausan murmushin da ya dan kidima shi.
Yace: meerah ki taimakawa rayuwata ki tsamo ni daga halakar da zan fada. Ina gaf da fadawa rami mai tsananin zurfin da bazan iya fitowa ba.
Ke kadai ce nake ganin zaki iya taimakona a wannan lamarin. Kimin alkawarin zaki taimakeni.
Wani irin farinciki ne ya lullube zuciyar meerah,har ya bayyana a fuskarta. A zatonta uncle cewa zaiyi yana sonta. Shiyasa yake cewa ta taimaka mai. Kuma ita kadai ce zata iya.
Tana cikin wannan tunani da jin dadin. taji muryarsa yana cewa: meerah soyayyar kawarki meenah nake nema. Taki ta amince dani,ta karbi soyayata. Har ina neman zaucewa akanta.
Shiyasa nazo gareki dan ki taimakamin kuma kinmin alkawarin tunda kikayi shiru, Alamar zakiyimin kenan.
Ki taimakeni ki shawo min kanta. Zan zauce wallahi, meerah zaki rasa hankalin best friend dinki akan meenarki.(wai🤔🤔uncle kayi katobara fa,😳bari dai muga mezaifaru ga meerah)
Tun sanda ya fara maganar. Meerah tayi suman tsaye.
Sai ga hawaye suna sintiri a fuskarta.
Sai ji tayi kafafunta sun kasa daukarta ta durgushe a gurin.
Tana kokarin share hawayenta dan kar uncle yagani.
Abunda bata sani ba shine: ya riga yagani.
Sai ji tayi yace: subhanallah! Meerah meke damunki ne? A firgice yayi maganar.
Ta dago kanta tare da wayancewa,bayan ta gama goge hawayenta tace: bakomai fa uncle.
Yace: kamarya bakomai,bayan naga kina kuka. Ko zancena ne ya bata miki rai.
Tace:a'a uncle, kawai kaban tausayi ne halin daka shiga.
Amma ka kwantar da hankalinka,na maka alkawarin zan shawo ma kan meenah,tunda har ka furta da bakinka cewa kana sonta,
Insha'allah indai naci sunana Ameerah zanyi...................
🤔🤔🤔🤔uhmm! Readers kuji fa wani Abu. Me meerah ke shirin aikatawa kanta haka?wanne hali take shirin jefa rayuwarta akan soyayya?🤔🤔
Muje zuwa😄😃❤❤(ummu-inteesar)ce😄👍🏻❤❤❤
❤❤Soyayyar meerah❤❤
Na: Rukayya Ibrahim lawal(ummu-inteesar)
Wannan page din sadaukarwa ne ga dukkanin masoya wannan book din.
🏤🏤P21🏤🏤
Indai naci sunana Ameerah zanyi kokari naga ka auri farincikinka, koda hakan na nufin ajalina. Bazan gajiya ba gurin nemarma farinciki, ko da zan mutu akan wannan tafarkin.
Uncle lesh cikin rashin fahimta yace: bangane ko hakan na nufin ajalinki ba,mekike nufi?
Meerah tayi murmushin yake wanda yafi kuka ciwo, tace: bazaka gane ba uncle, ko zaka gane bayanzu ba, watakil sai lokacin da ganewar batada amfani.
Shi dai uncle ya shiga rudani.
Maganganun meerah sun rikita shi Ya kasa gane me take nufi. Kawai sai cewa yayi: to,meerarmu nagode.
Meerah tace: ina neman wata alfarma agareka,dafatar zan samu.
Uncle lesh ya amsa a takaice da cewa: tame fa?
Tace: ina Neman Alfarmar ka dinga kirana da,my besty. Zanji dadi sosai.
Murmushi yayi sosai sa'annan yace: wannan kawai kike so?
Tace:eh a kunyace tana sunne kai kasa.
Murmushi yayi a karo na biyu yace: angama my besty Ameerah.
Sosai taji dadi aranta jin ya alakantata da kanshi.
Cikin alamar jin kunya tace: nagode bye.
Uncle yace:sai anjima my besty.
Meerah tabar gurin.
***************
Tun daga lokacin meerah ta fara kokarin cire uncle lesh a ranta. Tare da tursasawa zuciyarta taso manish duk da tasan abune mai wuya a gareta. Da kuma kokarin shawowa uncle kan meenah.
***********
A haka rayuwar meerah tacigaba da tafiya ba wani armashi. Ko da a gida kowa ya kasa gane kanta Ta zama wani abu dabam.
Gashi ta kasa cire son uncle aranta. Duk iya kokarin da take na ganin ta manta dashi, ba abunda ya canza
Sai ma karuwa da sonsa yayi a zuciyarta.
Duk da cewa ayanzu tana kokarin bawa manish kulawa da nuna mai so.
Kullum suna makale a waya suna fira, wai ko damuwar dake aranta zata rage. Amma ina! Akasan ranta damuwa ce fal. Duk da fuskarta bata nunawa.
********
Uncle manish kuwa ayanzu yana cikin farinciki sosai.
Tunda meerah na kulashi kuma suna soyayyarsu a nutse. Bayada sauran damuwa a tare dashi. Kuma baya tunanin akwai abunda zai raba tsakaninsu a yanzu.
Tunda har yakanje zance gidansu meerah.
Har kowa na gidan ya sanshi. Har ma ta sadashi da abbanta sun gaisa ya kuma sanar dashi manufarsa akan meerah.
Abban kuma bayada matsala a bangarensa tunda har meerar ta amince. Shi kuma yace ya bashi.
Jira kawai ake ta kammala secondary school a saka ranar aure.
****************
********
A wata ranar asabar ne meerah ta kaiwa meenah ziyara a gidansu dake lodge road kusa da government house.
Meenah taji dadin zuwa meerah sosai.
Bayan sun gaisa da maman aiman yanda ake kiran mamansu meenah kenan saboda sunan autan ta aiman.
Meenah taja meerah zuwa dakinta suka ci abinci. Daga nan suka hau firarsu irinta kawaye.
Anan meenah ke tambayarta labarin uncle manish.
Meerah tayi murmushin da ya zame mata jiki tace: habibty yananan qlau,har ma na hadashi da Abba sun gaisa saura maganar aure kawai da nayi candy.
Meenah ta Dan hangame baki tare da cewa: ah habah! Kawata kice kin kusa zama amarya.
Ta fada a sigar zolaya meerah tayi dariya tare da mika mata hannu suka tafa tace: ah to! Ki tsaya wasa zakiga yanda zamuje "muciya training centre"ni da farida mu barki,
Tunda ke bakya so.
Meenah tai mata dundu a cinya tace: mara kunya har fada kike zakuyi aure ku barni koh? Haka kikemin fata?
Meerah ta kuma yin dariya a karo na biyu sannan tace: ba fata nake miki ba,ke dince da abin haushi kinki bawa mai sonki dama. Ke har yanzu ko yar soyayyar nan da akeyi bakyayi.
Ki bawa uncle lesh dama ya shiga zuciyarki a wuce gurin.
Meenah ta dan bata rai tace: kinga abunda bana so ko......
Meerah bata tsaya jin me zata ce ba,ta katseta da cewa: miye bakyaso meenah? Uncle dinne bakyaso ko halayen kirki ne bashida shi? Ko shi mummuna ne? ki fadamun miye abunki a tare dashi? Ajere meerah ta mata tambayoyin.
Meenah tayi shiru kamar bata wajen. Dan gaskiya batada bakin da zata kushe uncle malesh aduka abubuwan da meerah ta lissafo.
Meerah tacigaba da cewa: uncle lesh yana matukar kaunarki, yanada wuya ki kuma samun dama irin wannan a rayuwa idan kika rasashi.
Yana sonki so mai tsanani da ya rufe masa ido har ya manta da cewa ni dalibarsa ce,ya tunkaroni da kokon bararsa yana neman na taimaka masa.
Ta danyi shiru na wasu sakanni sannan tacigaba da cewa: shawara daya zan baki meenah.shawarar kuwa itace kiyi amfani da damarki kafin ta kubuce miki.
Kinsan adadin yan mata nawa ne ke neman ko da kulasu ma yayi ko ya basu damar magana dashi?
Kinsan cewa daga cikinsu akwai wacca ke sonsa fiye da rayuwarta?
Tayi tambayar tare da bawa kanta amsa da cewa: baki sani ba,Allah kadai ya sani.
Amma ke har ya furta yana sonki shine kike wulakanta shi? To kiji tsoron Allah ki gyara.
Ina guje miki jarabawar ubangiji kar ya jarabceki da sonsa ko na waninsa bayan bakida damar samunsa.
A haka meerah ta dage tayi ta lurar da meenah,amma fa dauriya ce kawai take tana zancen.
Dan tsakani da Allah ta fara jin haushin meenah a yan kwanakinnan saboda wulakanta mata abun sonta da take.
Jikin meenah yayi sanyi sosai ta nutsu ta dau shawarar aminiyarta wacce tagama yarda tana matukar sonta tunda har ta fada mata gaskiya. Dama ance mai sonka ke fadama gaskiya.
Meenah ta nisa sa'annan ta dubi meerah tace: nagode da shawararki agareni kawata,kuma na dauki shawararki, insha'allah zan zama matar uncle malesh zan koyawa zuciyata kaunarshi duk saboda ke.
bari na fada miki abunda shi kanshi bai sani ba.
Dama naki kulashi ne domin a zatona kina kaunarshi ne saboda irin kulawar dana kina bashi, tare dakin duk abunda zai kuntata mashi ko ya Sosa masa rai.
Amma yanzu da kika zomun da wannan shawarar,sai na fahimce cewa hasashena kuskure ne.
Meerah murmushin yake kawai take aranta take cewa: hasashen ki gaskiya ne kawata,sai dai ya zanyi? Gaddara ta riga fata.
Jin meerah tayi shiru yasa meenah tacigaba da cewa: inaso ki yafemin bisa ga zarginki da nayi,kuma kisa aranki cewa koda na aureshi "kece sila". Shima zan sanar dashi wannan.
Nan take zuciyar meerah ta tsinke
Taji kuka na kokarin zuwar mata. Ga wani irin zazzabi na shirin dirarmata.
Dakiya ne kawai take dakyar tace: nagode da wannan alfarmar dakikamun kawata, ni zan tafi gida.
Meenah ta kalleta tace:ah! Tun yanzu?
Tace:eh,banajin dadi ne, inaga zazzabi ne ke so ya dirarmun bari naje gida.
Meenah tace:shikenan,muje kiyi sallama da maman aiman.
Meerah ta mata sallama ta fito.
***********
Tana zuwa titi ta tare napep sai koko road unguwarsu kenan.
Tana shiga gida ta tarar da ammi da abba a tsakar gida sun shimfida tabarma suna fira.
Dama da maraice ne lokacin karfe 5 na yamma dawowarsa kenan daga kasuwa.
Meerah ta durkusa ta gaida abba da ammi.
Abba yace: yar gidan abbanta ya kike? Ya karatu?
Tace:Alhamdulillah
Da wata matsala ne? Abba ya bukata. Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya cigaba dacewa: inda matsala ki sanar dani,kwana biyunnan bana gane miki duk kin wani susu ce.
Tace:bakomai abbana qlau nake.
Yace: to,ya sirikina ince yana lafiya koh?
Tashi kawai meerah tayi ta gudu daki batare data amsa shi ba.
Abba yayi yar dariya ya dubi ammi yace: autata ta girma,kinga wai kunya taji ta gudu.
Ammi tace:ai malam auta na cikin damuwa,sai dai na kasa gane meke damuntan.
Ko yanzu baka lura da yanayinta ba?
Ya nisa tare da cewa: gaskiyarki,nima kwannan ina lura da ita. Amma ke yakamata kiyi kokari ki gano mana meke damunta.
Tunda ke uwa ce kinsan hikimar da zakiyi kiji cikinta.
Ammi tace hakane,ina iya kokarina kasan zurfin ciki ne da auta shiyasa, amma bari yayanta yazo sunfi kusa.
Zansa ya bincikar mana ita.
Haka ya kamata dan adil dinne kawai zai iya da kanwar tasa. Abba ya fada
Da wannan zancen suka rufe babin meerah suka shiga hirar duniya.
****************
Meerah kuwa tun shigarta dakin ta fada kan gado rub da ciki. Ta soma kuka ahankali kanta ya fara ciwo ga zazzabi mai zafi daya lullubeta.
Har akayi kiran sallar magriba meerah bata tashi daga gurin ba.
Kanta yamata nauyi sosai.
Ammi ce taji shirun yayi yawa tazo duba ko lafiya meerah bata fito sallar magriba ba.
Kamar yanda ta saba a tsakar gidan take sallar magriba da isha, su danyi fira da amminta kafin ta koma dakinta.
A tsakiyar gadon ta hangota tayi rub da jiki. Ammi ta karasa dasauri taga ko lafiya meerah ke kwance har yanzu kuma a haka.
Aiko tana daura hannunta akan jikinta taji zafi sosai har tiri-ri yake.
Subhanallah Ameerah meke damunki? Ta tallabo kanta ta juyo da ita tana kallonta.
Taga idanta a rufe sai hawaye ke tsiyaya.sun kumbura fuskarnan tayi suntum.
Jiyojin kanta sai harbawa suke.
Ammi ta saki salati da karfi tana cewa: na shiga uku ni karima meke damunki auta?.
Hmmmm! Readers ko me yafaru da meerah? Wannan hali take ciki?.
Ya zancen aurenta da manish?
🤔🤔🤔🤔 Ku biyoni
(Ummu-inteesar)ce❤❤❤❤
❤❤Soyayyar meerah❤❤
na:Rukayya ibrahim lawal(ummu-inteesar)
masoyana godiya mai tarin yawa agareku ina alfahari daku
masoya meerah kuci gaba da hakuri da kuncin da take ciki insha'allah zai wuce
🏤🏤 p22 🏤🏤
Abba,yaya arif da adil da ayanzu suka shigo gidan dawowarsu kenan daga sallar magriba, suka ji karar ammi a dakin meerah.
suka nufo dakin cikin sauri har adil nayin tuntube.
suna shiga dakin suka tarar da ita rungume da meerah tana hawaye.
meke faruwa? suka tambaya atare. Ammi ta nuna masu ameerah dake rungume ajikinta batace komai ba sai cigaba da hawayen da take.
suka karaso suna ganin yanayin da take ciki suka rude. Arif ya fita da sauri yaje ya siyo allura yazo yamata. Dama bangaren kimiya ya karanta ayanzu haka nurse ne amma karamin ma'aikaci ne.
Ammi ta gyara mata kwanciyarta ta rufeta da blanket. Kasancewar taga tanajin sanyi.
Duk bidirin nan da suke meerah bata ma san sunayi ba.
kawai tana kwance kamar mara rai.
Adil ya zauna a gefen gadon yana kallonta kawai yana hawaye. Aransa yake cewa "meke damunki sweet sisterna"
Allah ya yaye maki damuwanki. San sakaki a addu'a.
Abba da ammi ma zaune suke akan kujerar dakin. Sunyi shiru kowa da abinda ke damunsa aransa.
Ita dai ammi tunanin abunda ke damun autarta take.
Ada tayi tunanin matsalar soyayya ke damun auta.
Amma yanzu da take ganin manish a matsayin sirikinta kuma wanda ameerah ta kawo a matsayin wanda zata aura.
sai take ganin bai kamata ace ameerah nada damuwa ba haryanzu Tunda sun amince da zabinta.
Idan kuwa har tanada damuwa har yanzu to ba wannan bace wata damuwar ce dabam. To meke damun ameerah da ya sakata a wannan yanayin?
wannan ne abunda ke damun ammi. Kuma ta kasa samo amsar wannan tambayar.
*******************
Shikuwa abba halin da ameerah ta shiga ke damunshi. Yanayin ciwon nata yakasa gano kanshi. Ya kasa gano meke haddasa mata wannan ciwon.Sai kare mata kallo yake tana akwance yana nazarin yanayinta.
Shikuwa adil yana zaune kusa da ita sai hawaye yake yana tausayin halin da kanwartashi take ciki yayiwa kansa alkawarin taimaka mata da zarar ya gano meke damunta.
*******"*****
Meerah kuwa bata farka ba sai 12am dama ammi na dakin anan zata kwana dan bazai yiwu abarta ita kad'ai ba.
Akan idon ammi ta farka. Ammi naganin ta farka ta taso daga kan kujerar da take kwance tana jera mata sannu.
Ta hada mata tea mai kauri tasha, ta bata magungunan da arid ya siyo mata ta hadiye ta kuma kwanciya. Ita ce bata kuma farkawa ba sai safe.
***************
Misalin karfe goma na safe arif da adil ne suka shigo gidan kusan a tare,sunzo dubiya.
Suka shiga dakin dan duba jikin meerah atare.
Bayan sun gaida ammi suka yiwa meerah "ya jiki"
Arif ya ajiye ledar hannunsa agaban ammi yace: abawa mara lafiya.
Adil ma ya ajiye tashi kana ya dubi ammi da yayansa arif yace:"yaya da ammi ko zaku dan bamu guri kadan ne?inaso nayi sirri da k'anwata.
Murmushi kawai ammi tayi tabar dakin. Yaya arif kuwa cewa yayi "munji mai k'anwa" ai kasan kanwar taka ce kai kadai bandani.
Ya dubi meerah yace: anjima sweet airah zatazo dubaki,Allah ya baki lafiya,ni zantafi kafin yaya adil ya mangareni.
Tayi yar dariya dan jin zancensa na karshe,sannan tace to yaya.
Adil dinma yar dariya yayi sannan yace: eyyeah! Anai mana kuri,ai dai muma munkusa aje honey ma karshen zak'i bare sweet.
Arif baice masa komai ba. Sai dariya da yayi yabar dakin.
************ Zama adil yayi kusa da ita yace kanwata tashi ki zauna muyi magana.
Ba musu meerah ta tashi ta zauna kusa dashi agefen gadon.
Sweet sis kimin alk'awarin zaki fadan gaskiya idan na tambayeki.
Tace: nama sweet bro. Adil yace kinsan banajin dadin ganinki acikin wannan yanayin na damuwa,haka kuma damuwarki damuwata ce.
Kece abokiyar shawarata kuma ke kad'ai ce y'ar'uwa ta mace aduniya wacca bana fatar wani mummunan abu ya sameta.
Ki daure ki sanar Dani meke damunki dan Allah kanwata. Jiyafa ko barci ban samuyi ba ina ta tunanin halin dakike ciki.
Yana maganar ne a marairaice kamar mai shirin yin kuka.
Meerah ta tausayawa dan'uwannata sosai. Ta riko hannuwanshi cikin nata tana cewa: sweet bro kayi hakuri da halin damuwar dana jefaka aciki,nima dan banida zabi ne da ya wuce hakan.
Ina cikin damuwa sosai,amma ni kaina bansan meke damuna ba. Ina rokonka daka tayani da addu'a Allah ya yayemun,idan kuma na mutu da wannan damuwar Allah yamun rahma yaji k'aina,ya dubi sadaukarwar danayi.
Tana kainan a zancenta ta fashe da matsanancin kuka. Acikin kukan tacigaba da cewa yaya ku yafemun komai na maku kaida su ammi watakil na kusa mutuwa. Ku yakemun😭😭.
Tana gama fadar haka tacigaba da kuka mai tsuma zuciya.
Shima adil sai ya tayata kukan ya rungumeta sosai suka cigaba dayi.
Acikin kukan adil yace "sweet sis Allah ya yaye maki damuwarki, ya mallaka maki abunda kikeso duniya da lahira.
Tace: ameen.
Taji dadin addu'arshi sosai.
Ahaka ammi ta same su ta dubi adil tace: meye haka kaida zaka lallabata sai kuma ka taya ta kukan? ta fada tare da rik'e hab'ah.
Baice da ita komai ba sai tashi da yayi yabar dakin yana goge hawayensa.(dan uwa kenan mai dadi)
*****************
Bayan watanni shida zancen soyayyar meenah da malesh yayi nisa har kowa yasan labarin a makaranta da gida.
Domin meenah ta dauki shawarar kawarta meerah. Ta bawa malesh dama ya zama rabin rayuwarta.
Ayanzu haka soyayya suke tsaftatacciya wacca ba yaudara acikinta.
Malesh na cikin farinciki sosai,yanata sakawa meerah albarka domin itace silar samun farincikinsa. Yana mata addu'ar samun dawwamammen farinciki saboda ta taimaka masa sosai.( Ni ko nace kai ne farincikin nata ai.lesh)
****************
Zuwa wannan lokacin makarantar tayiwa meerah zafi.
Bata jin dadin zuwa makarantar ko kadan kawai dan ya zamo mata dole ne.
Jin dadin ta daya sun kusa fara waec&neco dan ayanzu suna ss3 ne.
Bakomai ne yasa meerah bata son zuwa makaranta ba yanzu,sai dan ganin meenah da malesh da take atare koda yaushe.
Gashi malesh baya jin kunyar nuna mata so agaban kowaye.
Shiyasa meerah take gujewa duk inda zata gansu atare. Da taga uncle lesh ya nufo su in suna tare zata bar gurin. Gudun kar taga abunda zaisa zuciyarta ta buga.
*************
Wata rana bayan antashi daga school meerah da farida sun fito zasu gida atare kamar kullum. Sai ga uncle lesh yana ta zabga sauri.
Yazo ya tsaya agabansu yace: my besty tun dazu nake nemanki bangankiba sai yanzu.
Meerah tayi murmushi tace gani uncle. Yace dama ina so na miki godiya ne da taimakon da kikamin. Nagode Ameerah Allah ya saka miki da mafificin alkhairinsa,ya dawwamar dake acikin farinciki.
Sosai meerah taji dadin addu'ar tace ameen a bayyane. Aranta kuwa cewa tayi kai ne farinciki na uncle,in har ban sameka ba bawani sauran farinciki atare dani.
Da fara'a sosai a fuskarsa yace my besty ni zantafi,nagode miki sosai. Ayanzu ina cikin farinciki sosai,kuma kece silar shiga ta wannan yanayi najin dadi. Bazan manta dake ba.
"Ameerah usman lema I like you"
Bayan meenah Ayanzu acikin mata ba wadda nake ra'ayi sama dake. Yana fadar haka yabar gurin bai jira cewarta ba.
Zo kaga murna agurin meerah har bakinta baya rufuwa. Har suka isa gida tana cikin farinciki.
Ko da taje gida ma farin cikinta bai boyu ba.
Har ammi ta lura cewa yau meerah na cikin farinciki. Abunda ta dad'e bata gani ba atare da meerah shi tagani ayau wato fara'a har sai da ammin ta kasa hak'uri tace wa meerah
"Autata meke faruwa ne yau,ko ammaki albishir ne?" Meerah tace mekika gani? ammi tace: naganki ne cikin farinciki sosai.
Eh kawai meerah tace da ammi tasa dariya tashige d'akinta.
Ammi tace: Alhamdulillah a bayyane.
Meerah kuwa da tashiga d'aki zama tayi akan kujera tace "alhamdulillah" a bayyane a ranta kuma cewa take:
Na godewa Allah yau naga farinciki a fuskar masoyina. Kuma har yana fada cewa nice silar sakashi farinciki har cewa yake yana ra'ayina sama da kowace y'a. Ko bakomai yau burina ya fara cika,kuma na fara cika alk'awarin da nay masa na nemar mai farinciki komai rintsi da wuya. Tana kai nan a tunaninta taji kiran sallar la'asar ta.Ta tashi ta doro alwala tayi sallah.
Muje zuwa:(ummu-inteesar)ce.❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤Soyayyar meerah❤❤
na:Rukayya ibrahim lawal(ummu-inteesar)
jinjina ta mussamman zuwa gare ki Asma'u zayyan(asmeenat zeeyan)
marubuciya yar baiwa ta kungiyar brilliant writers association.
B.W.A suna alfahari dake.
🏤🏤 P23 🏤🏤
Dawowa daga labari
lokaci na kara ja kwanaki suna shudewa.
yau takasance itace ranar baikon meenah da malesh.
Inda aka kai matsaya akan maganar aurensu da zarar ta kammala secondary school.
Gashi bai fi saura wata uku ba su kammala.
A ranar baikon meenah, meerah tashiga tashin hankali ba kadan ba. Ganin cewa shikenan fa yanzu uncle lesh ya kubuce mata. Gashi itama wani satin mai zuwa za'ayi baikonta da manish.(meerah ta manta cewa Allah yana jujjuya al'amarinsa yanda yaso, akuma lokacin da yaso.)
koda meenah takira meerah suje rabon alawar da ake kira"i see i love" kamar yanda al'adar mutanen garin sokoto take,na raba wannan kayan ga y'an uwa da abokan arziki dan su tayaka murna.
meerah tana cikin dakinta ita kad'ai ta rufe tana kukan bakin cikin rasa masoyinta da tayi.
kiran meenah ya shigo wayarta,har bugu biyu meenah ta mata amma bata daga ba. sai ana ukun shima har takusa tsinkewa sa'annan ta daga, Bayan ta dakatar da kukanta. bayan sun gaisa ne meenah kece mata tazo suje rabon minti,kuma ta gayawa farida dan bata sameta awaya ba su zo tare gobe.
wani sabon kukan ne yazowa meerah ta maza ta kashe wayar batare da tace uffan ba.
meenah kuwa da taga meerah ta kashe wayar batare da tace komai ba. Sai tabi wayar da kallo baki sake kamar taga meerar aciki. Aranta tace meke damun meerah ne? bafa tamin magana ba ta kashe.(ni ko nace kishinki take yarinya)
sai kawai ta koma kira akaro na hudu. Meerah ta daga wayar, meenah tace meerah bakice komai ba kika kashe.
Meerah tace "to,zamuzo ai ba gobe ba?"cikin wani yanayi mai kama dana kuka tayi zancen.
meenah tace sai kunzo ai hasale nake dake,ko Allah ya kyauta baki kira kin mun ba, Yau kwana hudu kenan da kawo kayan. Inata kiwon hankalinki naga ashedai dagaske bazakimun Allah yasanya alkhairi ba.
Meerah taji kunya aranta gaskiya bata kyauta ba,to,amma kishi ke damunta shi yahanata tayiwa meenah Allah ya kyauta.
Aganinta wannan baikon na meenah da'akayi tamkar an rufe kofar farincikinta ne gabadaya.
Domin ada tana saka rai,yanzu kuma ta cire ran zai zama nata ko yaso ta.
Cikin rawar murya meerah tace: Allah ya sanya alkhairi kawata yasa ayi damu. Ameen meenah tace hade da kashe wayar.
***************
A ranar asabar da misalin karfe sha biyu na rana meenah da kawayenta uku suka fita rabon minti a motar yayan meenah(ma'aruf).Sunje gidajen kawayensu da dama sun kai masu. Karfe hudu na yamma suka biya gidansu afnan(d'ayar k'awar meenah da suka fita tare) da ke unguwar polo club.
Sukayi sallah suka ci abinci suka kuma fita. Abokin yayan meenah wato rashid shine ke jan motar.
Suna cikin tafiya a motar saiga kiran malesh ya shigo wayar meenah. Cikin fara'a meenah ta daga wayar.
Acan bangaren malesh ne ya mata sallama cikin zazzak'ar muryarshi yace:
"Amincin Allah ya tabbata ga gimbiyar mata".
Meenah tace: Amin tare dakai sarkin masarautar birnin zuciyata.
Malesh yayi murmushi mai sauti yace nakira ne naji ko gimbiyata tana cikin walwala da koshin lafiya?
Itama murmushin ta mayar masa sannan tace lafia qlau nake taurarona,abun alfaharina,malesh na Meenah.
Murmushin yakumayi kana yace hakane,Meenah kuma ta malesh. Ya dora da cewa ke kad'ai na bawa makulin zuciyata,sauran yan mata sai suyi hakuri dan ke kadaice zaki iya bud'e zuciyata kishiga cikinta kiyi yanda kikeso. Daga ke ba wata,kece cikon burina Amaryata!.
Meenah tayi yar dariya tace harda wani fadar amaryarka ko?
Yace eh saura kiris ki zama mallakina sai yanda nakeso nayi dake.
Meenah tace lah! Kafara wuce guri,sai anjima, ina tare dasu meerah ne muna rabon minti.
Lallai anyi mara kunyar amarya dake ake rabon mintin? Idan kunje mekike cewa to?.ya fada.
Meenah tana dariya ta kashe wayar kafin ya kuma tsokanarta.
Meerah kuwa tun lokacin da meenah ta fara waya da malesh zuciyarta ke bugawa da karfi. Kanta ya fara matsanancin ciwo.
Dama ita ke kusa da meenah a bayan motar. Kuma taji duk abunda malesh din ke fada. Kasancewar wayar China ce lol🤪.
Kafin su ankara sai karar meerah suka ji tana cewa "wayyo kaina, zuciyata, zan mutu.
A firgice rashid ya taka burki a gefen hanya. Meenah da farida dake kusa da ita sun sakata a tsakiya. Suka maida hankalinsu gurin meerah har ta tafi zata kife farida tayi saurin tallabo kanta.
Da sauri farida ta janye hannunta sakamakon zafin da taji ajikin meerah kamar ta taba garwashi.
Kan meerah ya bugu a seat din direba dake gabanta. Meenah ta rungumo meerah ajikinta sai taga kamar meerar bata motsi. Ta buga kara tare da dora hannu akai tace mun shiga uku,bata motsi fa.
Farida da afnan suka fara innalillahi wa inna ilaihir raji'un,ya zamuyi yanzu?
A rude rashid yace bara muje asibiti,wanne zamu kaita?
Meenah tace: muje uduth yafi kusa da nan. Ya tada motar cikin hanzari ya nufi hanyar asibitin.
Farida da meenah kuwa sun kasa magana tsabar tashin hankalin da suke ciki,sai tsare meerah da ido da sukayi. Ko waccensu da abunda ke damunta aranta.
Ga jikinta zafi rau amma tunani suke kota mutu ne ko suma tayi?.
***************
Da isarsu asibitin basu zarce ko'ina ba sai emergency.
Da gaggawa aka shigar da meerah wacca har a lokacin bata motsi.
Su Farida kuwa sun kasa zama,sai kai-kawo suke a wurin. Kowannensu a rude yake kowa da abunda ke damunshi a ranshi.
Ita dai meenah abu daya ke damunta shine: idan sunje gida me zasu ce ya samu meerah, idan kuma ta mutu fa?
Gabanta ya buga da karfi, na shiga uku na ni aminatu! Ta fad'a abayyane hawaye suna tsiyaya a idonta.
Farida kuwa tashiga wani irin yanayi na tashin hankali da yasaka har takasa tunanin komai. Sai hawaye dake bin kumatunta.
Rashid ma sai kai-kawo yake a harabar asibitin.
Duk da cewa baisan miye silar ciwon nata ba,kuma a iya saninsa yana driving dinsa akan tsari,amma sai yake ganin kamar shine sila.
Suna cikin wannan halin ne likita ya fito daga d'akin da aka shigar da meerah yace ina wadanda suka kawo ta?.
Afnan ce tayi saurin tashi tsaye tare da kiran su meenah suka CE mune muka kawota.
Doctor yace bakwa tare da wani babbane? Ina iyayenku?
Meenah tace tare da yayanmu muke,bara akirashi. Suka kira rashid,doctor yace muje office nama bayani.
*******"******
A office din doctor rashid ya nemi guri ya zauna a kujerar da aka tanadar dan zaman bak'i.
Doctor ya zauna a kujerarsa hade da cire gilashin dake sanye a idonsa. Yace kai yayanta ne?.
Rashid yace eh meke damunta ne doctor?. Maimakon doctorn ya amsa mai tambayarsa sai ya kuma jefo masa wata tambayar yace me ya sameta har ta suma?.
Rashid ya koro mai bayanin iya abunda ya sani. Doctor yace OK na dubata,bincikena ya nuna mun cewa tana dab da kamuwa da ciwon zuciya saboda yawan tunani da damuwa da take ciki. Yanzunma ina tunanin akwai abunda taji ko ta tuna wanda yake tayar mata da hankali shi ya haddasa mata hakan. Sai kuma buguwa da kanta yayi, dukda gurin baiyi rauni ba amma ya kumbura.
Dole ta kwana anan domin tasamu kyakkyawar kulawa daga garemu dan har yanzun bata farfad'o ba daga suman da tayi.
Kuma da kwai magunguna da zamu daurata akai.
Yanzu kaje gida ka sanarwa iyayen naku abunda ke faruwa.
Rashid yace nagode likita bari na je.
***************
Nan fa rashid yazo ya sanarwa dasu meenah halin da ake ciki,tare da tambayarsu yanzu miye shawara.
Farida cikin karayar zuciya tace ayanzu bamuda wani zabi da yawuce mu koma gida mu sanar da iyayenta ,tunda abun ya hada kwana asibiti.
Rashid yace hakane yanzu acikinku wace zataje gidan saina sauketa? Kunga bazai yiwu abar mara lafiya shikad'ai ba.
Farida tace meenah kije ni zan tsaya anan, daga nan ma saiku sauke afnan agida,kinga dare yayi kar amata fad'a.
Meenah tace gaskiya a'a bazanje ni kad'ai ba muje tare,kinga kece yar gida sai afnan ta duba mana ita. Idan muka dawo saita tafi gida.
Farida cikin sanyin jiki tace shikenan,amma kafin nan muje muga halin da take ciki.
Suka shiga d'akin su hudu har yanzu tananan asume. Wasu sabbin hawaye ne suke fita a idonsu.
Meenah ta dubi afnan tace kawata pls kijira mu anan muje mudawo.
Afnan tace bakomai kuje Allah ya bata lafiya. Ameen suka ce tare da barin dakin...
Hmmmm! Allah sarki meerah 😒😒ko yaya zata kare?
Muje zuwa❤❤(ummu-inteesar)ce.
❤❤Soyayyar meerah❤❤
na: Rukayya ibrahim lawal(ummu-inteesar)
🏤🏤 P24 🏤🏤
Bayan sunje gidan sun sanarwa ammi da abba abunda ke faruwa atare suka dawo asibitin dasu abba. Sune sukama su abban jagora har dakin da aka kwantar da ita.
Ammi na ganin halin da y'ar tata ke ciki hankalinta ya dungunzuma sai tafara hawaye tana cewa "Allah sarki autata Allah ya baki lafia,kinga jarabawar rashin lafiya a wannan shekarar. Allah ya yaye maki.
Abba kam bai samu cewa komai ba sai zama dayayi yana kare mata kallo gata akwance ba motsi tamkar gawa. duk sai yaji hankalinsa yana neman barin jikinsa.
Rashid yace to abba mu zamu wuce gida Allah ya bata lafia.
Ameen Allah ya maku albarka mungode Abba yafada.
Dakyar su meenah suka yarda su bishi zuwa gida nan ma saida ammi tasa baki sannan suka mata sallama suka tafi rai ajagule.
sai tsakiyar dare meerah ta farfad'o likita ya kara dubata.
**************
Da safe ma meenah tazo tare da maman aiman rashid ne ya kawosu dan shima yanaso ya k'ara ganin jikin ko taji sauki domin yarinyar tashiga ranshi sosai.
farida ma tazo ita da mamanta sun dubata, domin a daren jiya ba wanda yayi barcin kirki tsakanin su ukun mussanman farida da meenah da suke cike da tashin hankali ganin suna shirin rasa aminiyarsu dasuke matukar so.
Uncle manish da abokinsa malesh suma sunzo dubiya. Manish dinma baiyi barci ba adaren da ya samu labarin tana asibiti. Ya hakura ne kawai dan bashida mafita dare yarigada yayi alokacin da labarin ya riskeshi da ba abunda zai hana mishi zuwa asibitin aranar.
Yaya arif, anty airah da adil ma sunzo da safen.
Kwananta biyu a asibiti aka basu sallama suka koma gida.
A haka lokaci ya cigaba da ja har gashi yanzu saura 1 week su fara waec. Meerah jiki yayi kyau sosai sai karatu da suke ba kama hannun yaro.
Amma a k'asan zuciyarta damuwa ce fal domin har izuwa yanzu ba abunda ya ragu a zuciyarta na son lesh.
A kullum soyayyarsa da kaunarsa dad'a linkuwa suke a zuciyarta, bishiyar kaunarsa tayi rassa a birnin zuciyarta. Sonsa ya mamaye ko'ina a zuciyarta har yakai manish yarasa koda gurin da zai makale ne azuciyartata.
Kawai tana kulashi ne a dole domin batada zabin da ya wuce hakan ta hakurtadda ranta da malesh din kamar yanda ya bata shawara a baya cewa idan ba zata iya furtawa ba kawai ta hakura dashi.
Tabbas ta hakura ta sadaukar da farincikinta wa nashi. Tana so ya rayu cikin farinciki koda ita zata rasa rayuwarta ne.
Dama ace ba meenah yake so ba da tayi iya kokarinta taga ta mallakeshi, amma yanzu kam ta hakura ta rungumi kaddararta ayanda tazo mata.
Zata auri mai sonta da gaskiya wanda bai damu da k'arancin kulawar da take bashi ba. Koda kuwa ita bata sonshi tasan zata samu kyakkyawar kulawa daga gareshi tunda shi yana matukar kaunarta.
**************
Shirye-shirye ya kankama a duka bangarori hudun. Ayayin da su meerah suke zana jarrabawarsu ta neco.
Gidajensu amaren kuwa sai shiri ake domin kowacce an tsayar da date din aurenta bayan ankawo lefensu.
Jira kawai ake su kammala exam din asasu a lalle.
Meenah dai antsayar da date din aurenta a ranar 29-december-2018.
Na meerah kuwa za'ayi bayan sati biyu dayin na meenah wato 12-january-2019.
Suma angwayen anasu bangaren sai shirye-shirye suke mussanman ma manish da yake akwai aikin da har yanzu bai k'arasa ba agidansa shiyasa ma za'a riga yin na malesh,da yake shi ya kammala nashi aikin fenti kawai ya rage. Da atare suka so ayi.
***************
Biki ya matso sosai a wata ranar laraba saura sati daya cif a wanke amarya meenah.
Tasha gyara sosai tayi kyau dama can ita kyakkyawa ce da yake kuma farace sosai dan tafi meerah fari sai haskenta yakara fitowa sosai.
A ranar ne kuma k'awayen meenah na kusa da ita suka taru zasuje rabon I.V(invitation) da mintin gayyatar bikin.
**************
Ango malesh ne ya turo masu wani abokinsa mai suna hayat ya kwashesu a motarsa suka fita ,su biyar ne har ita meenan sai hayat cikon na shida.
Farhana ce a gaban motar sai hayat dake driving.
Meenah,farida,afnan da meerah sune a bayan motar, sai fira suke abinsu daga gani kasan dukkanninsu suna cikin farinciki inka dauke meerah wacca sai can ba'a rasa ba take samasu baki a firar. Kana ganin fuskarta kasan akwai damuwa mai yawa atattare da ita. Wannan fitar ma ta dole ce tayi dan idan bataje ba idanun mutane zasu dawo kanta da kuma son sanin meya hanata zuwa,sanin irin amincin dake tsakaninsu shiyasa ta daure ta biyosu dan kar su fahimci abunda ke ranta.
Hayat ne yasaka masu baki a hirar inda yake cewa meenah: mutumina fa yana matukar kaunarki amarya,kinga yanda yake rawar kafa da bikinnan? Sai kace kanshi aka fara aure, har cewa fa yayi musanar da dukka abokanmu duk wanda bai zo mashi daurin aurenshi da honeyn shi ba bashi ba wannan mutumin. Ku ji fa?
Meenah batace dashi komai ba sai dariya da tayi.
Farida ce ta cafe zancen da cewa: ah nifa banga laifin uncle ba yanada gaskiyarsa,ko ni idan aurena da yaya adil ya tashi zanyi abunda yafi wannan ma. Ai da masoyi ake rawar kafa.
Dukkansu suka sa dariya banda meerah wacca takejin saukar muryoyinsu a kunnenta tamkar suna kwadamata guduma a tsakiyar kai. Runtse idanuwanta tayi gam jin maganganun nasu take tamkar suna watsa mata ruwan zafi.
Tayi iya kokarinta ta yakice sonsa aranta takasa sai ma karuwa dayake akullum kwanan duniya,tare da tsananin kishin meenah da take.
Bata san sanda taja tsaki ba idan ta arufe. Jan tsakin da tayi yayi daidai da lokacin da suke dariyar.
Dukkaninsu suka juyo suka kalleta idonta a rufe yake har yanzun.
Farida tace lafia malama kike mana tsaki?.
Cikin tsananin jin haushinsu su duka ta tsuke fuska tace Ku maidani gidanmu.
Saboda mefa? Suka bukata amamakince.
Meenah tace yanzu fa gida biyar kawai mukaje shine zakice amaidaki gida?
Meerah ta bud'e idonta a d'an zawace tace nace ku maidani gida koh? Idan kuma bazaku iya ba ku ajiyeni anan,ni yar gari ce bazan bata ba ai.
Mamaki yakara cikasu mussanman meenah da farida da sauyawar halin k'awarta su na lokaci daya yake basu mamaki.
Hakannan ba yadda suka iya dole suka sauketa a kofar gidansu.
Ta fita azuciye ko sallama bata masu ba ta shige gida.
Farida ta d'aura hannu a hab'a cike da mamaki take kallon meerah tace "sabon salo".
Meenah dai batace komai ba mamaki da takaicin meerah sun cikata sai ta fad'a duniyar tunani. Meyasa meerah ta sauya lokaci d'aya? Meyasa duk lokacin da akayi zancen uncle malesh dani take shiga wani hali? Ko dai tanamin bak'in ciki ne? Bayan itace tazomun da shawarar aurensa. Mutum,mutum sai Allah ta fada a ranta.
Tun daga wannan ranar kuwa meenah bata kuma d'aura idonta akan meerah ba dukda bikin ya matso sosai a gobe ne ma za'a sakata a lalle.
Amma tayiwa meerar uzuri kasancewar itama amarya ce saura sati biyu bikinta watakila abubuwa ne suka mata yawa shiyasa bata shigo ba.
Sai kuma ta tuna ranar da suka rabu a hasale take,kawai sai ta d'auko wayarta tayi dialing number meerah har ta tsinke ba'a d'aga wayar ba.
Ta kuma k'ira har sau uku ba'a d'aga ba.
Cike da mamaki da haushin meerah meenah tabi wayar da kallo sake da baki,can kuma ta ajiye wayar tare da Jan wani uban tsaki " wannan ma ai iskanci" yarinya duk ta sauya lokaci daya ta fada a ranta had'e da mikewa tabar gun.
A bangaren meerah kuwa ciwo ne ya farmata tun ranar da suka rabu da su meenah bata kuma fita ko'ina ba.
Tana gida akwance
Duk ta fige ta lalace,sai uban tunanin da take. komai rashin imaninka idan kaga yanda meerah ta koma acikin kwanaki bakwai kacal dole ka zubar mata da kwallah.
*************
Ammi da Abba kuwa hankalinsu ba karamin tashi yayi ba,ganin wannan lalurar data samu autarsu gaf da za'ayi bikin aurenta.
Anata shan magani kamar ba'ayi ciwo sai habaka yake, to a yan kwanaki biyunnan ma anga sauk'i har tana fitowa tsakar gidan da kanta.
Yan uwannata biyu suma sundamu matuk'a sai kashe kudadensu suke gurin nemar mata magani.
************
A bangaren manish ma haka take yadamu sosai da rashin lafiyar abar kaunarsa.
Koda yaushe yana zarya agidansu meerah dan ganin lafiyarta. yana kuma yin duk wata hidima dayake ganin yakamata yayi dan samun lafiyarta.
Ranar wankin amarya meenah,farida taje gidansu meerah dan tak'ara duba jikinta daga nan kuma zata wuce gidansu amarya.
Yanda taka meerah
Ya d'aga mata hankali sosai,tamata fatan samun lafia tabar gidan jiki a sanyaye. Dan tasan duk yanda suka kai da buk'atar meerah a gurin bikin hakan bazai samu ba "ciwo ya kauda komai"
Anyi shagalin bikin amarya meenah cikin nasara da kwanciyar hankali, komai ya gudana kamar yanda aka tsara. Abu daya yaso kawo cikas shine rashin walwalar amarya sosai sakamakon tunanin halin da k'awarta take ciki da yay mata yawa.
Kasancewar farida tasanar da ita halin da meerar take ciki tun ranar da aka sakata a lalle,gashi badama taje dubata.
**********
Rana bata karya, yau takama ranar asabar, kuma ayau dinne za'a daura auren meenah da malesh.
Tun cikin dare jikin meerah ya rikice da asuba ta daina motsi,numfashinta ya dauk'e ita kad'ai a dakinta bawanda ya sani.
Misalin karfe bakwai na safe ammi ce ta shigo d'akin dan duba yanda meerar ta kwana.
Tun daga bakin kofa bugun zuciyarta ya k'aru,sakamakon hango meerar da tayi rufe acikin blanket ba alamar motsi atattare da ita.
Da sauri ammi ta k'arasa bakin gadon, tasaka hannu ta yaye blanket din.
Abunda tagani ne yasanya numfashinta daukewa na wucin gadi kafin yadawo.
Ta saki salati da karfi tare da furta "innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
A hankali ta sulale kasa azaune dabas.
Zaman dabas din datayi akan floor din d'akin yayi daidai da shigowar Abba d'akin. Cikin sauri ya karaso zuwa gareta har muryarshi na sark'ewa gun tambayar lafia? Meke faruwa ne?
Hawaye kawai ammi keyi bata iya cewa komaiba sai nuni da tamasa da yatsa zuwa inda meerah ke kwance.
Ya karasa dasauri yakai hannunshi kusa da hancinta yaji bata numfashi.
A rikice ya ciccibo ta yabar d'akin tare da cewa hajiya d'auko hijabinki muje. Bai saurari cewarta ba yayi gaba rungume da meerah a kirjinsa.
Yana karasawa gurin motarsa ya bud'e baya yasanyata aciki.
Dai-dai lokacin ammi ta fito sanye da hijab d'akyar ta iya cewa ina zaka kaita kuma? Ta mutu fa...ta karasa zancen cikin kuka.
Shiga mota kawai yace da ita bai kuma cewa komaiba tashiga yaja motar sai asibiti......
Yawan comment dinku shi zaisa naci gaba ko akasin hakan..
Share & comment
Muje zuwa.
(Ummu inteesar) ce.
________________________________
❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤
Story & written by Rukayya Ibrahim lawal(ummu-inteesar)✨✨✨
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa Ginshiƙin Al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/109559843864286/?app=fbl
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
🏤🏤 P25 🏤🏤
A cikin dakin majiyanta Likitoci ne suka duk'ufa gurin ceto rayuwar meerah. Yayin da ammi da Abba suke waje suna jiran sakamako.
Abba ne ya d'auko
Wayarshi ya kira arif yasanar mai
Halin da ake ciki sa'annan ya kashe ya nemo adil shima ya sanar mai,dukkanninsu a rikice suka karasa asibitin.
*********
K'arfe tara na safe farida tafito daga gida zata gidansu meerah dan k'ara duba lafiyar ta, daganan kuma zata wuce gun amarya.
Tana isowa kofar gidan tayi kicibis da adil yana k'ok'arin bud'e gidan.
Da mamaki a fuskarta tace a'ah! Ina mutan gidan ne? Naga kamar yanzu ne kake bud'e kofar gidan?
Murmushin k'arfin hali yayi yace suna asibiti ne,ni dinma daga can nake ammi ce ta aiko ni d'aukar kayan meerah da yan wasu abubuwa da za'a buk'ata a can.
A d'an razane tace jikin meerar ne? Eh yace tareda fad'ar anbata gado ma.
Tace subhanallah! Allah yabata lafia. "Meerah kinga jarabawa"
Ameen yace hade da cewa yawwa my farida dan Allah taimaka mun mu shiga ki debowa meerah kayan da za'a buk'ata, kinga kece mace zaki fini sanin abubuwan buk'atar mata.
Dan ni Ban masan ta Inda Zan fara ba wallahi, dukda Tana cikin damuwa hakan bai hanata yin murmushi ba tashige gidan Bayan yagama bud'ewa.
kai tsaye d'akin meerah ta shiga yayin da shi kuma ya shige d'akin ammin sa.
*************
A can d'akin meerah kuwa farida ce ta shiga sauke akwatunan meerar tana bud'awa dan nemar mata kayan da zatayi amfani dasu a asibitin.
Tana cikin dube-duben ne takai kasan wata babbar akwati ta meerah inda take ajiye muhimman ababenta na sirri.
Ai kuwa sai taga wani d'an madaidaicin diary ta d'auko shi, ta duba bangon diaryn aranta take mamakin na mine.
Har ta mayar dashi ta ajiye sai kuma taji tana kwad'ayin ganin abunda ke ciki.
Wata zuciyar ta kwab'eta da cewa uhm! Uhmm! Farida karki duba abun mutane,bincike fa bashi da kyau.
Har ta kuma ajiyewa zuciyarta ta azalzaleta akan ta duba bakomai ai na aminiyarta ne.
Ai kuwa ta kuma d'auko shi ta bud'a ta fara dubawa daga shafin farko, taga anyi heading da manyan bak'i ga abunda ke rubuce kamar haka.
"SOYAYYAR MEERAH "
Farida ta mayar da hankalinta sosai,ta kurawa diaryn ido cikin zak'uwa da son jin wannan labarin da meerah tayiwa take da "SOYAYYAR MEERAH"
Ta bud'a Page na gaba ta cigaba da karantawa kamar haka.
Sunana Ameerah usman lema wacca akafi sani da MEERAH ni yar gata ce gaba da baya, ba abunda na rasa na dangane soyayyar iyaye da y'an uwa da k'awaye.
Sai dai kash! Abu daya na rasa Wanda ya matukar illata rayuwata da gangar jikina, Wanda nakeda tabbacin dana rashi zan iya hallaka.
Wannan shine dalilina na rubuta wannan labarin domin bayan na mutu ina tsammanin wannan diaryn zai shiga hannun d'aya daga makusanta na.
Ina son iyayena da y'an uwana su san abunda na dad'e ina b'oye masu,
Kuma abunda suka jima suna kwadayin sani.
Wato abunda ke haddasamun damuwa da rashin lafiya har yay silar mutuwata.
Dalilin kuwa da yasa nayiwa wannan littafin nawa take da "SOYAYYAR MEERAH" domin A rayuwata ban taba gani ko jin labarin wanda yayi soyayya irin tawa ba.
Soyayya wacca take cike da sa rai da jiran tsammani,soyayyar masu wani,sadaukarwa ga masoyi da kuma cutar dakai.
Wadannan abubuwan duk sun taru acikin wannan labarin nawa.
Nasan idan ka/ki ka karanta za/zaki yi kuka saboda tausayawa wani gurin kuma ya baka haushi. Duk acikin labarina.
**********
Lokacin da farida Takai nan a karatun da take sai ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sa'annan tacigaba da karatun.
Sam tama manta abunda ya shigo da ita d'akin.
Tana karatun tana sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci,wani lokacin kuma ta share k'wallah har takai ida yafi jan hankalinta da bata tausayi a labarin.
Inda meerar ta rubuta"ina matukar k'aunar uncle lesh sama da komai da kowa a rayuwata.
Banda iyayena da y'an uwana way'anda k'aunarsu dabam ce a zuciyata".
K'aunar shi daga Allah ne,wata jarabawa ce da ubangijina yamun domin ya jarraba imani na.
Ya jarabceni da tsananin son wanda bai ma san inayi ba. Ya kuma k'i fahimtata, zurfin cikina ne ya janyomun daga k'arshe ya jarabtu da son aminiyata d'aya daga cikin mutanen da nake matuk'ar so kuma zan iya komai akansu.
Wannan dalilin ne yasa nayi babbar sadaukarwa a rayuwata, na sadaukar da farincikina da rayuwata gabaki d'aya wa farincikin masoyina na zab'i na mutu indai hakan zaisa ya rayu acikin farinciki.
Lokuta da yawa da suka shud'e na nishad'antu da kallon kyakkyawar fuskar masoyina a lokacin da yake murmushi.
Naso ace nice zan rayu dashi har abada amma ina! Wannan itace kaddarata. Nasan ana d'aura aurennan zan mutu bazan iya kallonsa yana rayuwa da wata a matsayin mata baniba, kuma bazan iya auren mijin aminiyata ba bare nacigaba da sa rai.
Saidai nawa baya iya canza k'addararsa,zan mutu da k'aunarsa da soyayyarsa acikin zuciyata. Da fatar Allah ya gama fuskokinmu a aljanna.....
***********
Jin shirun yayi yawa har yanzu farida bata fito ba yasa adil ya biyota d'akin Dan ganin meke faruwa.
Nan ya tadda ita rike da wannan diaryn tana hawaye.
Saurin k'arasowa yayi tare da tambayar lafiya my princess? Bata samu cewa wani abu ba. Sai mik'a masa diaryn dake hannunta da tayi.
Cikin alamun rashin gane manufarta da hakan,ya k'arbi diaryn tare da cewa menene wannan?
Farida ta daga kai ta dubi agogon dake manne a bangon d'akin taga har 9:40 tayi.
Cikin sark'ewar murya tace bamuda lokaci yaya dole mu dakatar da wannan auren.
Banganeba auren meenah like nufi? Ya tambaya.
Daga mishi kai tayi alamar eh.
Saboda me to? Ya kuma tambaya a mamakince.
Tace amsarka tana cikin wannan diaryn na hannunka.
Nan take ya bud'a diaryn yana karantawa da sauri-sauri dan yaji farida tace basuda lokaci.
Abunda yagani ya matuk'ar saga masa hankali. "Meerah batada hankali ne zata kashe kanta akan soyayya? Akan kuma abunda zata iya samu?" Aransa yay wannan tambayar.
Kodai na kira malesh d'inne? Yay mgnr a zuciyarshi,har ya Ciro wayarsa a aljihu zai kirashi,can komai ya tuna? Kawai sai ya mayar da wayar.
Muje shine kad'ai abunda adil yace da farida ya juya cikin sauri rik'e da diaryn a hannunsa.
Itama bin bayansa tayi cikin sauri,ya rufe gidan suka tafi a hanzarce bai ma tsaya d'aukar babur dinshi ba napep suka hau.
Suna cikin tafiya a napep d'inne adil ya sake wata nannauyar ajiyar zuciya yace amma kina ganin munyiwa meenah adalci kuwa,idan muka dakatar da aurenta saboda son zuciyarmu?
Son zuciya kuma? Farida ta tambaya tana kallonsa. Yace eh son zuciya manah,banda son zuciya ya za'ayi muda yakamata ace munje gurin dan tayata murna. Shine zamuje mu rusa mata farincikinta dana iyalanta dan kawai munaso meerah ta rayu?
Wannan ba adalci bane.
Aganina mu nemi wata mafitar kawai kafin mu isa gidan kar muje garin ceto rai muje fa wani ran a hatsari.
Dogon numfashi farida ta sauke cikin kwancewar tunani tace yaya bafa muda wata mafita wacca tafi wannan,saura dak'ik'u kadan ad'aura auren, hakan na faruwa kuwa nasan mun rasa meerah kenan....
Tana kai nan a zancenta ta fara hawaye ta d'an dakata da zancen kafin ta cigaba da cewa nasan meenah zata fahimce mu.
Itama bazata so mu rasa aminiya kamar meerah ba, kuma zata iya hak'ura.
Dan meerah tafita sonshi itama ta hak'ura bare meenah da banajin son da take mai yakai rabin wanda meerar ke masa.
Adil dai bai kuma cewa komai ba,zuciyarshi a cunkushe take da tunani iri-iri har suka isa kofar gidansu meenah.
********************
K'ofar gidan cike take tam da jama'a manya da yara kowa yasha ado, duk fuskar kalla a wajen zama tabbatar da mai wannan fuskar,zuciyarshi cike da farinciki.
Sai hada-hadar d'aurin auren ake k'arasowar tawagar ango kawai ake jira.
Zuciyar adil da farida ta tsinke ganin wannan taron da kuma sanin abunda ya kawosu gun wato dakatar da auren.
Ya fuskokin wad'annan jama'ar zasu koma,bayan jin abunda suka zo dashi.
A sanyaye suka fito daga napep d'in ya biya kud'in sukayi gaba farida ta sunne kai k'asa ta shige cikin gidan, Adil ya tsaya a waje cikin mutane.
Hmmmm! Shin za'a d'aura auren meenah da malesh kuwa?? Ya meenah zataji bayan Isar farida da labarin?malesh fa ya zai kasance bayan jin wannan labarin.
Muje zuwa..
______________________________
❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤
Story & written by Rukayya Ibrahim lawal (ummu-inteesar)✨✨
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa Ginshiƙin Al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/109559843864286/?app=fbl
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Wannan page din nakune fans din MEERAH,saiyadda kukayi dawannan page din. Musanman babbar kawar meerah aisha ridwan dahir yar mutan jos
🏤🏤 P26 🏤🏤
Cikin gidan ma ya soma cika da mutane,Y'an uwan maman aiman wadanda suka zo daga nesa sai y'an uwa makusanta da k'awayen amarya na kusa da ita. Sune a gidan.
Sai hidimar shirya abincin buki ake.
Farida ce ta sako Kai cikin gidan tareda sallama,aka amsa mata.
Da anty aysher(yayar Meenah kenan) ta fara cin Karo,wacca ke rik'e da ludayin Miya a hannunta. Farida ta k'arasa gun tana gaidata"ina kwana anty" murmushi aysher tayi tace"lafiya qlau k'anwata" har k'in k'araso? Eh farida tace asanyaye.
Aysher ta Kuma cewa Yana ganki haka jiki asanyaye lafiya dai ko?
Farida tayi murmushin yak'e tace qlau anty,ina amaryar take ne? Ta tambaya a k'ok'arinta na dakatar da aysher daga tambayar tuhumar da take mata.
Aysher tace tana d'akinta ita da k'awayenta,bari naje anty,farida ta fad'a tareda juyawa ta nufi d'akin meenah jiki ba k'wari.
Shiga d'akin tayi tare da yin sallama suka amsa,Farhana ce ta zo da sauri ta rungume Farida "oyoyo k'awar amarya" nan ma yak'e kawai tayi,tace ina amaryar ne?
Turo kofar band'akin da akayi ne yasa ta mayar da dubanta gun. Meenah ce ta fito daga ciki tazo da sauri ta rungume Farida" oyoyo k'awata sai yanzu? Nida naso ki kwana Anan Amma kika k'i. Murmushin k'arfin hali tayi batace komai ba sai tunani da take aranta tanajin tausayin meenah na ratsata,gashi tazo ta tarad da ita acikin farin ciki amma zata rusa mata" kodai zata fasa fad'a ne? Meerah kuma fa?ta mutu kenan? Wani bangare na zuciyarta ya tambaya.
Duban farida meenah tayi cikin damuwa tace k'awata lafiya dai,na ganki a hakan? Jiya fa qlau muka rabu dake,nan ma shiru farida tayi.
Kawai sai meenah taji gabanta na tsananta fad'uwa,lallai ba lafiya ba.
Acikin yanayin damuwa meenah ta k'urawa Farida ido tace ki fad'amun, ina meerah? Kota mutu ne? Shine bakya son sanar dani? Ta karashe zancen tana hawaye .
Dak'yar Farida ta had'o kalmomi"bata mutu ba sai dai muna daf da rasata. Ta fad'a tana share k'wallar da ta taru a idonta.
Hankalin meenah ya tashi sosai tace meke damunta ne? Farida ta shaida mata meerah na asibiti rai a hannun Allah,andauka ma ta mutu ashe dogon suma ne tayi tun bakwai na safe har yanzu bata farfad'o ba.
Kome Farida ta tuna?oho saurin duba agogon dake d'aure a hannunta tayi,karfe goma da mintuna goma tagani,saura mintuna ashirin kenan ad'aura auren kenan.
Subhanallah Farida ta fad'a ta d'ora da cewa meenah bamuda lokaci dak'ik'u kad'an suka rage wad'anda zamu iya rasa aminiyarmu acikinsu.
Meenah tace bangane ba farida fahimtar dani, akid'ime tai zancen. Diaryn dake jakarta ta d'auko ta mik'awa meenah had'e da fad'ar kiyi hanzari ki duba bamuda ishashshen lokaci.
Cikin azama meenah ta fincike diaryn a hannun farida ta fara karantawa.
Tashin hankali Wanda ba'a sakawa rana. Innalillahi, inalillahi, inalillahi wa'inna ilaihir'raji'un shine k'ad'ai abunda Meenah taketa maimaitawa bayan ta gama ganin abunda zata iyagani kafin diaryn ya subuce a hannunta ya fad'i kasa.
Fad'uwar yan bori Meenah tayi ak'asa tana kuka mai cin Rai, "why? Why?? Why meerah??? Meyasa zaki mun haka. Ta fad'a acikin kukan.
Sam hankalinsu baya tare dasu ita da farida sai kuka suke sunma manta cewa da mutane a d'akin.
Sun d'auki lokaci a haka suna zaune suna kuka har basusan lokacin da Farhana ta fice daga d'akin ba,sai dawowarta tare da maman aiman suka gani.
Nan ma saida maman aiman ta Kira sunan Meenah da k'arfi sannan suka waigo suka ganta a tsaye.
Meke faruwa?ta tambaya a gurguje farida tayi k'arfin halin yi mata bayani. Itama hankalinta ya dungunzuma. Salmah! ta saka baki ta Kira yar k'anwarta da k'arfi aguje salmah ta shigo. kafin tai magana maman aiman tace k'ira mun abbunku da sauri.
************
A can asibitin kuwa a d'akin da aka kwantar da meerah Abba ne ya kalli ammi yace to Karima mu zamu tafi gun d'aurin auren nida arif, shi kuma adil din idan yadawo sai ku zauna tare anan. Kinga bazai yiwu ace dan Ameerah batada lafiya ba Wanda yaje d'aurin auren aminatu ba daga gidannan.
Hakane malam ammi ta fad'a tare da cewa adil din ma har yanzu bai dawo ba daga aikensa ya d'auko kaya tun takwas da arba'in har yanzu bai dawo ba,Allah sa dai lafiya. Ameen Abba yace had'e da duban arif dake tsaye agun yace muje koh?
Suka fice a d'akin har izuwa lokacin meerah bata farfad'o ba.
**********"
A gidansu Meenah kuwa Abbu ne tsaye a gaban y'arsa yana Bata hakuri tare dayi mata tuni dacewa rungumar k'addara ta alkhairi ko sab'anin haka yana d'aya daga cikin rukunnan imani.
A haka ya cigaba da lallashinta,dak'yar ta dakatar da kukan da take tace abbu, inason meerah ta rayu ni na hak'ura na yarda amayar da auren kanta. Abu d'aya ke damuna shine wannan mutane da aka Tara mezaku gaya masu anfasa auren?.ko.....
Kuka ne yaci k'arfinta ta kasa k'arasa zancen.
Abbu ya fice daga gidan hankali tashe.
************
A k'ofar gidan kuwa tawagar ango ce ta k'araso. Ango ya had'u cikin shadda sky blue yasha babbar riga da hula rantsattsiya,yayi kyau sosai, abokan ango ma kowa yasha wanka sunzo taya abokinsu murna,adil na ganinsu yaje suka gaisa ya shige cikinsu.yanaso yayi magana da malesh Amma yana fargabar mezai faru.
************
Kai tsaye gurinsu abbu ya nufo yana k'arasowa yace da malesh ina son ganinka tare da iyayenka yanzu a parlour na. Yana gama fad'a ya juya ya koma ciki, haka kawai sai malesh yaji gabanshi na tsananta fad'uwa.
Adai_dai lokacin Abba da arif suka k'araso,suka dunguma su duka har iyayen malesh din zuwa parlourn.
Abbu,baba muktar k'anin abbu,maman aiman ,farida,amarya meenah sune zaune a tsakiyar parlourn lokacin da su malesh suka k'araso.
Zama sukayi kowa na tunanin meza'a fad'amasu ne da aka tarasu,banda adil wanda yariga yasan meza'a fad'a shiyasa ya janyo su Abba suka zo.
Abbu ne ya mik'awa malesh diaryn yace duba wannan. Cikin fad'uwar gaba malesh ya k'arba,ya duba hankalinshi ya dugunzuma sosai. Shiyasa meerah ke masa abubuwan da take masa Ashe sonsa take?, meyasa ta cutar da kanta? Meyasa ba tasanar dashi ba,har ta bari ya kamu da son k'awarta?.....Abbu ne ya katse masa tunani da cewa dama na Tara ku anan ne dan na sanar daku halin da ake ciki, auren Amina da malesh bazai yiwu ba. A razane malesh ya d'ago kansa ya kalli Abbu tare da fiddo ido waje, saboda me? Abbu ina sonta fa,ya fad'a batare da yasani ba.
A gurguje Abbu ya basu labarin komai.... Sa'annan ya d'ora da cewa shiyasa muka yanke shawarar fasa wannan auren domin munaso mu ceto rayuwar Ameerah. Manish da tuni ya dask'are a wajen tsabar mamaki da kad'uwa wai Meerah amininsa takeso bashi ba,ashe shiyasa baya samun cikakkiyar k'auna da kulawa daa gareta?... muryar malesh ce ta dawo dashi hayyacinsa inda malesh d'in ke cewa,Haba! Abbu wannan wane irin hukunci ne ka yanke ba tare da kaji ta bakinmu ba? Wallahi inason Meenah sosai,bazanji d'ad'in rayuwa in Bata ba, itama haka tana k'aunata sosai.
Abbu karka cutar da rayuwarmu Dan ceto rayuwar Meerah. Cikin zubar da hawaye yake zancen....(tabdi yau anga hawayen yan maza,soyayya kenan manya)
Abban malesh yace mezai hana a had'a masa su biyu tunda waccan tana sonshi shi Kuma yana son Amina?. Ka duba zancennan Alhaji.
Abbu yace bakaji ita yarinyar tace bazata iya auren mijin aminiyarta ba?. Ai kawai a hak'ura.
Abban meerah yace to Alhaji mutane da ka Tara fa kayi ya dasu?...ba ma wannan ba itama Ameerar ka manta tanada miji ne,aurenta fa saura sati biyu.
Abbu Yace ba damuwa sai a d'aura da Ameerah yanzu,tunda gaka anan ga Y'an uwanta biyu dama kune waliyanta. Ga kuma Manish anan inaji ai shine angon Ameerar ko?ya kuma ji komai sai mu k'ara bashi hakuri.
Ya juya ya dubi gefen da malesh yake yace d'ana bawai bana sonka bane ko bana tausayinka,a'a so nake mu had'u mu ceto Rai mumina daga salwanta. Da kake maganar na yanke hukunci Kai tsaye kuwa,ga aminan nan ka tambayeta kaji ita da kanta ta yanke wannan hukuncin.
Saurin kallon side din da take ango malesh yayi cikin neman k'arin bayani, cikin kukan da ta kasa dainawa tun d'azu take magana"k'warai kuwa uncle ni na fad'i haka ka taimake mu ka ceto mana rayuwar aminiyarmu,kasani meerah ta fini sonka,dan itace ma ta mun nasiha akan na amince da aurenka lokacin da na k'i. Kuma dana tabbatar da hasashena ba abunda zaisa na yarda da aurenka. Zai magana ta katseshi da cewa uncle malesh idan har da gaske kake sona to ka aureta .Da gudu tabar wajen tana kuka mai tsuma zuciya. kowa ya mik'e za'a bar wajen kenan arif yace ita kuma Meenah wazai aureta yanzu. Karaf Manish ya karb'e zancen da cewa ni zan aureta.
Kowa ya kalleshi cikin mamaki da neman k'arin bayani.
Tabbas ni zan aureta tana son abar k'aunata sosai,harta barmata abunda takeso. saboda haka na amince Ameerah ta auri malesh,ni kuwa zan sadaukar da farin cikina wa na masoyiyata kamar yadda tayi wa masoyinta.
A yau na d'auki darasi daga labarin Ameerah na fahimci soyayyar gaskiya wacca ake Dan Allah kawai,wacca zaka iya barin farin cikinka Danna masoyinka. A haka taron ya watse dukda kowa zuciyarsa ba dad'i Amma sunji sanyi_sanyi yanzu, tunda Allah ya rufa asiri ansamu mai auren Meenah.
*******""""
A can kofar gidan kuwa dubunnan mutane ne suka shaida d'aurin auren Ameerah Usman lema da angonta malesh Adam sai kuma Amina Abbakar da angonta Manish aliyu. Kasancewar iyayen Manish maza suma suna gurin Kuma anmasu bayanin komai.
A haka d'aurin auren ya watse kowa na farinciki da yake ba kowa ne ya fahimci wannan canjin da aka samu ba,sai dai mutane sunyi mamakin d'aurin aure biyun da akayi sabani yadda aka gayyacesu.
**************
Bayan kammala d'aurin auren da kamar awa d'aya,angwaye sun gama sallamar abokanansu saboda haka suka dunguma su hud'u zuwa asibitin da k'ara duba lafiyar Amarya meerah.
********
Ammi da Abba suna zaune a d'akin Abba na bawa ammi labarin abunda ya faru agurin d'aurin auren Meenah da kuma auren da aka daurawa y'arsu wacca ke kwance Rai a hannun Allah.
Aka turo kofar had'e dayin sallama, suka amsa.
Farida,Amarya Meenah, Ango malesh da Ango Manish sune suka shigo d'akin tare da adil da suka had'u akofar shigowa.
Bayan sun gaiggaisa da su Ammi, suka tambayi lafiyar Amarya Meerah. Da sauk'i za'a ce Dan har yanzu Bata farfad'o ba Amma likita yace daga yanzu zata farfad'owa ko wane lokaci.
Allah k'aro sauki ya bata lafiya suka fad'a atare.
Adai_dai lokacin ne Meerah ta bud'e idonta a hankali tana k'arewa d'akin da mutane cikinsa kallo..
Adil ne kad'ai ya lura da hakan,da sauri ya matsa kusa da ita yana cewa sannu k'anwata Allah k'ara afuwa.
Kalaman adil ne yasa suka fahimci ta farka daga dogon suman da tayi. Su duka suka matsa kusa da ita suna jera mata sannu.
Sauke idonta tayi akan malesh ta dak'yar ta iya daga d'aya hannun da ba'a jonawa drip ba ta yafito shi,da sauri ya k'arasa gun.
A hankali ta furta uncle and'aura auren? Yace eh Amma.....
Ina! Kafin Meerah ta k'arasa jin zancensa ta kuma suma akaro na biyu...danta d'auka da Meenah aka d'aura auren.
Ya Salam!!! malesh ya furta.....
Hmmm! Fans din Meerah ga page dinku kun k'agara kuji wa Meerah zata aura? To ga amsarku...
Sai dai wannan suman da taku mayi fa yaya zata kasance??.
Muje zuwa
Taku har kullum (ummu-inteesar)
*_❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤_*
*Story&written by Rukayya Ibrahim Lawal (ummu-inteesar)✨✨*
*Wannan page din sadauk'arwa ne a gareku yan biyu kyautar Allah wato HASSAN ATK&hUSSAIN 80K,godiya Mai tarin yawa a gareku da bazar ku muke rawa.*
____________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
🏤🏤 P27 🏤🏤
Ya Salam!!! Malesh ya furta a hankali had'e da duban adil yace ka Kira likita pls inaga fa ta Kuma suma ne.
Likita ne ya shigo d'akin tare da adil da yaje kiranshi. Bayan sun gaisa da likitan Kai tsaye ya wuce gurin da Meerah ke kwance,ya shiga aikinshi,yayi yan gwaje_gwajensa da zaiyi. Sa'annan ya dubi ammi yace mama wannan suman da tayi ba Mai tsayi bane, zata farfad'o nanda mintuna ashirin insha'allah.
Ya fad'a alokacin da yak'e k'ok'arinta cire mata drip din dake hannunta.
Ya fice daga d'akin bayan ya kammala aikinsa.
Shi kuwa adil sai ya janye angwaye sukayi waje suna firarsu. Dan kuwa angonta yace bazasu tafi ba sai ta farka,Yana so yaga yadda zata k'arbi wannan al'amarin ne.
A gidansu malesh kuwa bayan abbanshi ya dawo daga gurin d'aurin auren yake sanarwa da umman malesh yanda akayi da yadda lamarin ya sauya. A fusace umman malesh tace haba Alhaji me kukaje kukayi kenan? Yaya ga wacca yaro yace yanaso sai Kuma ku aura masa wata dabam,wacca ni ban ma santa ba. Ba wannan ba ma meyasa baku had'a masa biyu ba,inhar dole saita aure shin.
Abban yace haba hajia meye haka ne wai? Bakiji Mai na fad'a Miki ba ne? Yarinyar nan rayuwarta tana cikin hatsari zata iya rasa rayuwarta a ko wanne irin lokaci adalilin sonsa. Kuma tace bazata iya aurar mijin aminiyarta ba. Meye laifi Dan mun ceto rai.? Bakida tausayi ne ke?
A hasale umman tace koma dai menene ni ban yarda da wannan auren ba,ba zan k'arbi yarinyar da bansan wace ita ba.
Wannan karon abban malesh ya fusata sosai cikin daga murya yake magana, to bari kiji tun wuri ki ajiye wannan maganar. wannan itace kaddarar danki kuma yasa hannu biyu ya runguma dan me ke bazaki k'arba ba,naga ai shine Mai zaman auren bake ba.
Yana gama fad'a bai jira cewarta ba ya juya fuu ya bar d'akin a fusace.
********
A gidansu ango Manish ma irin haka ce ta faru sai dai shi tashi umman ta k'arbi abun hannu biyu ta masu fatan zaman lafia Mai d'orewa.
Maman Manish tace to Alhaji yanzu ya za'ayi kenan kaga shi wannan yaron bai kammala aikin gidansa ba Kuma lokacin da aka saka na bikinsa da saura. Ga Kuma d'aurin auren yazo adai_dai lokacin da ba'a tsammace shi ba ya za'ayi da tarewar Amarya?.
Alhajin Manish yace wannan inaga ba wata matsala anjima zamuje gidansu yarinyar sai mu zauna da magabatanta muji yadda abun zai kasance.
Allah ya Sanya Alkhairi yasa wanna n canjin ya zama Alkhairi a rayuwar yaran baki d'aya. Maman ta fad'a.
Ameen Alhaji yace had'e da mikewa ya shige uwar dakansa.
***************
A hankali meerah ta bud'e idonta bayan mintuna ashirin da biyar da tayi a sume, adai_dai lokacin Kuma su malesh suka shigo d'akin kamar an fad'a masu. Saurin runtse ido meerah tayi kamar Mai bacci. Ango malesh ya matso kusa da ita yace bud'e idonki Amaryata, k'ara runtse ido Meerah tayi dan a tunanin ta ba'a kawai yakeyi mata.
Farida ta k'araso gun tana cewa haba Amarya Meerah bud'e idonki ki kalli angonki mana,Yana Miki magana bazaki amsa masa bane? Bud'e idonta tayi ta saukesu akan farida cikin mamaki tana ganin kamar itama faridar zolayarta take,idan bahaka ba meyasa zata kirata da amaryar uncle malesh bayan Ayau za'a d'aura aurenshi da Meenah.
Malesh ne ya katse mata tunani da cewa haba my besty kitashi Mana muyi magana.
Ba musu Meerah ta tashi daga kwancen, ta zauna dan taji jikin nata yayi k'wari yanzu da ta farka.
Malesh yace yawwa d'azu kin tambaye ni ko and'aura auren koh? Bai jira cewarta ba ya cigaba da cewa amsar itace eh and'auramin aure Amma bada Meenah ba. Ware manyan idanuwanta tayi ta zuba mishi su, to uncle dawa aka d'aura? Ta fad'a batare da ta sani ba.
Da ke aka d'auramin aure? Taji saukar muryarshi kamar a mafarki.
Wayyo dad'i! Dama ace da gaske ne da zanfi kowa farinciki ta fad'a a ranta.
Naga bakya farinciki ko bakya sona ne besty? ya tambaya a k'ok'arinsa na gano shin dagaske ne tana mashi irin son da ta fad'a .
Mafarki nake ko gaske ne? Ta tambaya, ta d'ora da cewa da a gaske ne da zanfi kowa farinciki, in kuwa har mafarki ne to ba zanso na farka daga wannan daddad'an mafarkin ba. Duk wannan abun batasan afili take fad'arsu ba ta d'auka aranta take zancen.
Sai ji tayi Manish yace ba mafarki bane my Meerah da gaske ne.
Farida pls ciji kunne na Kona farka,Ta fad'a.
Murmushin k'arfin hali Meenah tayi tace dagaske ne k'awata ayanzu ke matar uncle lesh ce.
Meerah tace in har gaske ne to ke wazaki aura yanzu?
Waye mijin ta zakice Manish ya k'arb'e zancen had'e da cewa nine mijinta.
Fiddo ido waje meerah tayi cikin alamun matuk'ar mamaki da faruwar wannan lamari.
Tsantsar farin ciki ne ya lullub'e zuciyar Meerah har ya kasa b'oyuwa saida fuskarta ta nuna.
Juyowa tayi ta fuskanci malesh dake zaune kusa da ita. Tsabar murna batasan sanda ta Rungumeshi ba tana cewa ina matukar k'aunarka lesh dina, I love u to the extend that I can't explain. Sai hawayen farinciki suka Fara bin kumatunta.
Sam ta manta da mutane a d'akin, Ammi da Abba da yashigo yanzu da suka ga abun yafi k'arfinsu sai suka bar d'akin.
*******
Wani kishi ne ya tasowa Meenah hartaji kamar takaiwa Meerah duka saboda rungume hubbynta da tayi.. dak'yar ta iya jurewa da ta tuna cewa yanzu fa duk mafarkinta ya tashi a banza kenan tunda ba shine mijinta ba. Jin kuka na k'ok'arin zuwa mata yasa
Tace am inaga yakamata mutafi ai ko? Tunda naga ai ta warke dama ga maganin cutar ya samu ta k'arashe zancen tana yar dariya wadda ta iya fatar bakice kawai.
Malesh yayi dabarar zame jikinshi daga na Meerah data k'ankameshi dan ya lura Meenah bataji dad'in hakan ba.
Suka saka dariya dukkansu had'e dacewa
Hakane suka amsa mata tare da mik'ewa su dukan zasu tafi, Farida ce tace to Amarya Ameelesh mu zamu tafi.
Ameelesh Kuma? wow! Farida kin iya saka suna kuwa yadace dasu sosai Kuma yay dad'i. Manish ya fad'a cikin matuk'ar k'arfin hali Yana murmushi.
Farida tace ai bani na saka mata ba ga tanan ka tambayeta kaji hakan naganshi rubuce a diarynta.
Sai a yanzu Meerah ta fahimce dalilin wannan sauyin da aka samu wato anbankad'o sirrinta kenan shiyasa.
Manish yace to sarauniyar masoya mu zamu tafi, Amma kafinnan zanso kisan dalilin da yasa na hak'ura da aurenki. Na k'aru sosai a dalilin labarin soyayyarki na fahimce minene son gaskiya,saboda haka na sadaukar da farincikina wa naki kamar yadda kikayi wa abun k'aunarki. Dan ki tabbatar cewa ni Mai k'aunarki ne har abada.
Ita kuwa Meenah na aureta ne adalilin k'aunar da take maki da sadaukarwar data maki, bazan taba bari masoyinki ya koka ba.
Bayan sun fice saida Meerah ta sakko dakanta tayi alwala tayi sujudus_shukur tana k'ara godewa Allah da ya dawo mata da farinciki alokacin data yanke k'auna da duniya ma baki daya.
*********
Meerah dai sauk'i ya samu sosai dan Aranar Bata kwana a asibiti ba saida aka sallamesu suka koma gida.
*************
Iyayen Manish sunje gidansu Meenah sunyi magana akan tarewarta.
Baba karami(k'anin Alhajin Manish) yace suna neman Alfarma a k'ara masu sati d'aya dan yaro ya samu ya kammala aikinsa sai Amarya ta tare.
Baba muktar yace wannan ba matsala kaga muma anan zamu samu dama aje akwaso kayan d'akinta daga gidan malesh tunda anriga an mata jere.
Allah ya nuna Mana, baba k'arami ya fad'a suka yi masu sallama suka tafi.
***********
A gidan su Meerah ma irin haka ce ta faru, Abban malesh yazo tare da mutanensa akan maganar tarewar Amarya.
Abban Meerah yace to gaskiya muna buk'atar ku d'an k'ara Mana lokaci Koda sati d'aya ne mu dai_dai ta al'amuran. Domin bamu gama shiryawa ba kasancewar ada da sauran sati biyu kafin auren.
Yan uwana da zasu zo daga kano ma akwai buk'atar a sanar masu.
Abban malesh yace badamuwa zamu saurareku nan da sati d'ayan, bari mutashi sai anjima Alhaji Usman. Suka fice daga gidan.
Ammi kuwa shiryawa tayi taje gidan iyayenta dake cikin gari (k'ofar rini)
Ta sanar masu da yadda lamarin ya sauya,yanzu andawo da bikin wannan sati.
Saboda haka suka fara Shirin wanke Amarya.
Anty hafsa k'anwar Ammi itace ta k'arbi aikin gyara yar tata saboda haka tasa aka turo mata Meerah gidanta tun ranar monday.
Sosai tashiga gyarata da d'irka mata abinci dan Asamu ta tada komad'a tunda shekaran jiyan nan ta taso daga gadon asibiti duk ta rame.
Abba ma ya kira yan uwansa a kano ya sanar dasu saboda haka suka fara Shirin zuwa sokoto kwanannan.
Acikin kwana biyun da Meerah tayi agidan Anty hafsa ta canja sosai tayi kyau ta cicciko duk Raman nan babu yanzu.
Sai k'yalli da d'aukar ido take.
********
A ranar laraba da misalin karfe goma tsoffi mata suka taru agidansu Meerah,harda tsoffin gidansu ango. suka wuce KOFAR RINI dan jik'on lallen Amarya( Wanda za'a wanketa dashi)
Kamar dai yadda Al'adan garin take.
Dan a gidan kakannin nata za'a wanketa.
Kai tsaye daga gidan anty hafsa Aka wuce da Amarya gidan kakanninta da yamma.
Acan ta tarar da wasu yan matanta Dan su farida manyan k'awaye suna tare da ita agidan antyn.
K'arfe takwas na dare aka fara shagalin wankin Amarya.......
Muje zuwa(ummu-inteesar) ce.
*❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤*
*Story & written by Rukayya Ibrahim Lawal(ummu-inteesar)✨✨*
________________________________
*Wannan page d'in naki ne AUNTY HAUWA* *Shugabar Arewa writers association*
*muna Alfahari dake.*
*Wannan page d'in* *sadaukarwa ne agareki sai yanda kikaso yi dashi.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
🏤🏤 28 🏤🏤
Gidan ya cika da jama'a sosai sai kid'an k'orai dake tashi, wata dattijuwa aka samu ta raka Meerah toilet ta mata wankan lallen.
Amarya ta fito shirye tsaf acikin atamfa ja Mai ratsin fari an mata riga da Zani biyu dayan ta d'aura shi a k'ugunta sai d'ayan da aka mata mayafi dashi aka rufe mata fuskarta.
Tana zaune kan gado ita da k'awayenta,mutane sai shigowa suke ganin amarya dangin Ango ma sun zo sun ganta.
A haka taron ya watse ya rage saura Amarya kawai da k'awayenta da zasu tayata kwana agidan.
kamar dai yanda Al'adar garin ta tanada (duk gidan da aka wanke Amarya anan zata kwana).
Can zuwa shabiyu da rabi na dare Meerah ta tashi zaune ta duba taga k'awayen nata su uku da suke tare duk sunyi barci.
Sai kawai ta d'auko wayarta ta rik'e tana jujjuyawa tana tunanin Kiran malesh, sai kuma taga dare yayi .
Kawai sai ta canja shawara ta rubuta mishi text guda biyu ajere ga abunda take cewa:
Zuciyar da ta karaya,rayuwar data shiga zullumi sakamakon rud'ani da rikicewar tunanin rasa muradina, Wanda zuciyata ta cika da so da k'aunarsa.
Ayanzu wannan zuciyar ta samu nutsuwa sakamakon samun Wanda zuciya ke tsananin bege.
Sako na biyu kuwa cewa tayi:
I feel relax and comfortable whenever I remember that you are my husband.
Ta tura mishi ta koma ta kwanta tanajin wani nishad'i a ranta.
**********
Acikin barcin da baiyi nisa ba malesh yaji k'arar shigowar sak'o a wayarsa,ya lalubota ya duba.
Abunda yagani ne yasaka shi tashi zaune cikin hanzari yana mai k'ara karanta texts d'in da aka turo masa da bak'uwar lambar da bai santa ba.
Mamaki ne ya k'ara cikashi lokacin da ya karanta sak'o na biyu.
Yanzu Kam ko ba'a gaya mishi ba yasan Meerah ce ta turo masa wadannan texts din.
Dan A yanzu itakad'ai ce da ikon da zata iya kiranshi da mijinta.
Cigaba yayi da rik'e wayar a hannunsa Yana ta mamakin wad'annan kalaman da Amaryar tasa ta turo masa.
" Ashe dama dagaske ne tana matuk'ar sonsa kamar haka?". Shiyasa kenan take basa irin waccan kulawar data bashi a baya.
Sai kawai ya shiga tunano abubuwan da suka faru A school lokacin baya. Ya Kuma tuna sanda ta bashi labarin soyayyar wata yarinya Mai cike da tausayi Ashe a fakaice sak'on zuciyarta take isarwa Amma ya kasa fahimta.
A haka ya wanzu yanata tuna baya batare da ya mata reply ba.
***********
Ita kuwa Meerah da ta ji shiru har bayan shud'ewar sa'a d'aya ba reply d'insa, sai zuciyarta ta sosu "yanzu Kam ta tabbatar baya k'aunarta kawarta yakeso" nan danan taji zuciyarta na mata zogi "Amma ba komai kaddarata kenan,Kuma tunda ina sonka insha'allah kaima zaka soni watarana uncle" ta fad'a a ranta tare da gyara kwanciyarta.
*********
Meenah fa??
Ita kuwa Meenah saida dare yayi ta kwanta ita kad'ai a d'akinta a dai-dai lokacin da take mafarki tare da fatar kasancewa tare da "Uncle malesh" a matsayin mata da miji.
A sannan ne abun yadawo mata sabo fil.
Wani bangare na zuciyarta najin zafin Meerah.
Meyasa Zaki mun haka Ameerah? Meyasa tun farko kika zo mun da shawarar k'arbar soyayyar "uncle" bayan kinsan kina sonsa??
Da baki zomun da wannan shawarar ba da watakil ina cikin farin ciki ayanzu, gashi kin rusa min why? Why Meerah?? Tana fad'a a hankali hawaye na bin kuncinta.
A takaice dai a ranar tsakanin Meenah da Malesh da Manish ba Wanda yayi barcin dad'i kowannensu ya kwana ne da damuwa a ransa.
Ita kuwa Meerah haka ta kwana ba yabo ba fallasa.
********
Kanawan dabo sun zo sokoto a ranar da akayi kamun Meerah Wanda Adil da arif suka d'auki nauyin Yinsa saboda taya k'anwarsu daya tilo a duniya farincikin RANAR AURENTA.
Saidai wannan kamun na Amare biyu akayi domin Adil ya sanarwa Meenah da Manish cewar su shirya Dan dasu za'a had'a ayiwa kamun a tare.
Amare da angwaye sun had'e sosai sun kuwa dace da juna sosai.
Inda Amarya Ameerah da Ango malesh suka saka Kaya kala d'aya:
Purple &pink.
Anyi wa Amarya Meerah doguwar gown purple sai ta d'aura head pink,jakarta da takalmi suma kalar pink ne.
Tasha make up ta had'u sosai.
Shima malesh kayansa kalar purple sai akayi masa aiki da zare pink,hularsa da takalminsa suma pink. Ya had'u sosai abun ba'a cewa komai.
Amarya Meenah da Angonta Manish (da aka sakaya😜)kuwa ba laifi suma sun had'e cikin shigarsu iri d'aya. Su kuwa red colour sukayi.
Ko wacce Amarya tana zaune kusa da Angonta a mazauninsu, sai dai me? Angon Meerah Yana satar kallon abar sonsa Meenah, Maimakon ya kalli Amaryarsa.
Shima Ango manish Yana satar kallon Matar amininsa Kuma Abar k'aunarsa Meerah.
Su farida da faheemah manyan k'awaye agurin Meerah sun sha kyau ranar,Adil ma a ranar ya wanku sunsha pics shida Adridar shi (farida kenan)
Anyi shagali an watse lafiya kowacce Amarya aka maidata gidan iyayenta.
Ranar jumma'a akayi WALIMA. Ranar assabar itace ranar tarewar Amaren a d'akunansu.
************
8:00 na dare motocin d'aukar Amarya sukai parking a kofar gidansu Meerah.
Meerah tasha kuka sosai a lokacin da aka zo fita da ita daga gidan taga dai dagaskene za'a rabata da ammin ta.
Gashi Bata San suwa zata riska a matsayin dangin Ango ba Ko zasu karb'eta ko yaya? Shine abunda ya Sanya ta k'ara kuka.
A haka aka fito da ita daga gidan aka sanyata a mota.
Gidansu malesh aka fara kaita,Anty hafsa da wasu biyu daga cikin iyayenta mata sai farida Aminiyarta sune suka shiga motar AMARYA.
Dan su damk'a amanarta a hannun surukanta.
Tun daga kan tarbar da aka masu zaka fahimci cewa tabbas Meerah bata samu k'arbuwa ba a gurin mahaifiyar Ango.
A haka su Anty hafsa suka k'araci surutunsu na bada amanar y'arsu,suka tashi suka fice batare da hajiya ta tamkasu ba sai Yan uwanta ne suka amsa masu da cewa: insha'allah zamu rik'e maku ita amana ai yanzu ta zama y'a a gurinmu Allah dai ya basu zaman lafiya da zuri'a tagari.
Jiki ba k'wari suka fito daga gidan suka Kuma hawan mota,
Aka ja sauran motocin Yan rakiyar Amarya Aka wuce da ita gidanta.
*************
Kai tsaye bedroom d'inta aka shiga da ita aka zaunar da ita akan gado.
Iyaye suka fice suka barta da ita da k'awayenta suna jiran isowar ango da abokananshi.
Bayan sun iso anyi (SAYEN BAKIN AMARYA) Yan mata sun k'arb'i kud'insu a hannun abokan ango(kamar yanda Al'adar garin take)sai kowa ya watse aka barsu su biyu kad'ai.
Guri ya samu ya zauna kusa da amaryarshi batare da yace komai ba.
A yanayin da yake ciki bazaka iya fahimtar cewa Yana cikin farinciki ko akasin haka ba.
Shidai gashinan kawai Wannan ranar bai ma San da wanne suna zai kirata ba. RANAR FARIN CIKI KO AKASIN HAKA?.
Tabbas baya bakin cikin aurenta saboda tana sonshi saidai Kuma ya rasa meyasa baya Jin tsananin farinciki kamar yanda yaji a lokacin da aka fara bikin aurensa da MEENAH.
***********
Meenah ma aranar ta tare agidan Manish bayan an kwaso kayanta daga gidan malesh an mayar mata gidan Angonta.
Ango Manish ma kusan haka ce ta faru dashi, ga Amaryarshi zaune a kusa dashi Amma ya kasa Koda kallonta bare ya tamkata.
Itama sai kuka take kasa-kasa acikin mayafi shikenan zata rayu da Wanda Bata taba mafarkin rayuwa dashi ba.
***********
A can dakin Amarya Meerah kuwa angon nata ne ya katse masu shirun da ya gifta na tsawon mintuna goma sha biyar da cewa Am.. kitashi kiyi alwala kizo muyi nafila Dan godewa Allah da ni'imar da yamana na zama ma'aurata.
Tsananin farinciki ne ya cika zuciyar Meerah ta godewa Allah da ya nuna mata Wannan ranar.
Alhamdulillah,Allah nagode maka daka nunamun Wannan ranar da nakasance mata agurin uncle lesh,ka had'amu a inuwar aure.
Bayan sunyi sallar nafila raka'a biyu sun kammala ya ya masu addu'ar Allah yasanya alkhairi a aurensu, ya Sanya Wannan canjin ya ya zama alkhairi a rayuwarsu su duka,kuma Allah ya basu zaman lafiya Mai d'orewa ya kad'ai fitina a tsakaninsu.
Mik'ewa yayi bayan yagama addu'ar dak'yar kamar Wanda akayiwa dole ta d'auko plate da ledojin kazar amarcin da yashigo da ita...........
Muje zuwa🤔🤔🤔😍 (ummu-inteesar ce)✨✨
_____"
❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤
Story & written by Rukayya Ibrahim Lawal (ummu-inteesar)✨✨✨
11 jan. 2020 ________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
🏤🏤 P29🏤🏤
Suna kammala cin kazar ya tashi ya wanke plate d'in ya mayar inda ya dauk'oshi.
Sa'annan ya tashi yaje yayi brush ya haye gado yayi kwanciyarsa tare da ce mata goodnight.
Hakannan itama ta tashi jiki a sab'ule tayi brush ta sauya kayan jikinta zuwa sleeping dress ta d'ora hijab akai sa'annan ta rab'a gefen gadon d'aya ta kwanta cike da zullumi da tunanin makomar wannan auren nata.
Har bacci b'arawo ya d'aukesu su duka.
Asuba ta gari.
*********
Bayan kwana biyu dakai Amare d'akunansu kowacce aka Kai gararta gidan iyayen mijinta.
Ba laifi su Abba sunyi k'ok'ari sosai Dan kuwa buhu biyar sukayi na shinkafa y'ar gwamnati sai buhun gero biyu da k'aramin buhun gishiri d'aya. Sai jarkar manja d'aya da ta mangyad'a d'aya sai golum din manshanu d'aya da kayan Maggi da katoon din taliya biyar.
A haka aka d'auka garar Meerah aka Kai gidan iyayen malesh.
Nan ma dai umman malesh bata yaba ba, Dan taji labarin cewa garar Meenah ta lunka ta Meerah sau biyu.
Shiyasa take k'ara jin tsanar Meerah a ranta domin ita ta rabata da yar gidan arziki da yanzu ita za'a kawowa wannan garar. Ko can da ma tana son Meenah ne saboda arzikin gidansu, tasan idan yaronta ya auri Meenah zata more.
Amma wannan tsinanniyar yarinyar tazo tashiga tsakaninta da wannan burin nata.
Tabbas sai ta Sanya wannan yarinyar tayi nadamar lik'ewa auren yaronta da tayi.
**********
Bayan wata uku da bikin su Meerah aka yi auren Yaya Adil da Farida.
Murna agun Meerah ba'a magana, dan saida tayi kwana hud'u a gida lokacin bikin. Acewarta yawon zai mata yawa ne,tunda kullum saita je gida gwara tayi zamanta har a kammala bikin sai takoma.
Mijin nata bai hanata ba dan yasan ko wacece farida da matsayinta a gurin matarshi, Koma bada farida akayi auren ba bazai hanaba domin kuwa Adil yayanta ne Wanda take bi.
shak'uwar dake tsakaninsu Bata misaltuwa. Ta ko ina bikin ya zame Mata dole.
Biki yayi biki ansha shagali an gama lafiya Amarya ta tare d'akinta saidai fatar Allah ya Basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba.
***********
Kwanci tashi asarar Mai rai a yau Meerah ta cika wata biyar a gidan uncle malesh saidai bawani cigaba da aka samu ta bangaren ummansa dan har zuwa wannan lokacin Bata k'aunarta. ko da sunje gidan umman Bata kulata ko gaisuwarta Bata karb'awa, banda bak'ak'en maganganu ba abunda umman ke fad'a mata.
"Natacciya" shine sunan da umman ke fad'a mata,Wai yaro baya sonta Amma ta nanik'e Masa kamar chin-gum.
Hakanne yasa Meerah Bata son zuwa gidan iyayen mijin nata Dan Koda yaushe suka je da b'acin rai take dawowa. Abbansa ne kad'ai ke nuna Mata k'auna.
Sai shine ke rarrashinta, Duk da cewar shi kanshi ta bangarensa ba wani haske dan har lokacin akwai k'aunar meenah a zuciyarsa.
Lokuta da dama yasha kiranta da sunan Meenah sai yaji tai masa banza kamar Bata ji ba sa'annan zai gano ya kwafsa.
Sai kawai ya nemo wata dabarar da zai fidda kansa, dan har ga Allah Yana tausayawa Meerah halin da take ciki da Wanda tashiga a baya a sanadin soyayyarsa.
Shiyasa ya guduri niyyar kyautata mata da k'ok'arin nuna mata so. Dan yasani abu ne Mai matuk'ar wuya yakuma samun soyayyar gaskiya kamar wannan.
*********
Manish fa?
Shima ya kasa mantawa da SOYAYYAR MEERAH k'auna ce wacca tayi tasiri ajikinsa da yake jin cewar har abada bazai daina Son MEERAH ba.
"SOYAYYAR MEERAH" ita ce jigon rayuwarshi Kuma abarda bazai taba mantawa ba a rayuwarshi har abada.
Sai-dai zuwa wannan lokacin ya k'arb'i k'addararshi hannu biyu Kuma Yana k'ok'arin kyautatawa Meenah da Bata kulawa da sauke mata duk wani hakkinta dake kansa.
A bangaren meenar ma hakane zuwa yanzu ta hak'ura da malesh Bata ganin kowa a zuciyarta sai mijinta tana kyautata Masa da yimasa biyayya.
Dukda itama akwai abu d'aya dake damunta shine yadda Manish ya kasa mantawa da Meerah har wasu lokutan yake kiranta da sunan Meerah batare da yasani ba.
Tana jin kishin Meerah sosai a ranta bayan ta kwace Mata miji a farko ta hak'ura, wannan ma tana k'ok'arin kwace Mata tunaninsa.
*************
A cikin wannan lokacin ne Kuma umman malesh ta kunnowa Meerah wuta ta hanyar turo Mata k'anwarta Maryam Dan ta dawo gidan da Zama.
Malesh baiso ba Dan yasan ko wacece Anty Maryam saboda rigimarta aurenta biyu duk sun mutu, tana da yara biyu yanzu haka tana zaune ne agidansu auren ya gagara.
Amma ba yanda ya iya tunda umurnin mahaifiyarsa ne, Amma aganinsa baidace ba ace ta koma gidansa da Zama alhali tana bazawara Kuma matsayin k'anwar mahaifiyarsa,duka-duka auren watansa nawa?, wannan ai zubar da girma ne.
A haka Yana ji Yana gani Anty Maryam ta tattaro kayanta da yaranta ta tare agidansa A wata ranar assabar.
**********""
Meenah Kam yanzu alhamdulillah ta samu kwanciyar hankali, suna zaune lafiya ita da mijinta.
Yanzu haka tanada ciki wata hud'u,sai nan-nan manish yake da ita ko k'waro bayaso ya tabata.
***********
Zaune take akan kujerar palour ta d'ora kafa d'aya akan d'aya sai hura hanci take, Anty Maryam kenan.
Fitowa Meerah tayi d'auke da plate d'in sakwara da miyar agushi taji naman Kan rago, ta nufo inda Anty Maryam take zaune durk'usawa tayi har k'asa tana mik'awa Anty Maryam plate d'in.
Karb'a tayi tana dad'a hura hanci, hannu tasaka ta d'ebo Loma takai baki, tun kafin ta had'iye ta fara yamutsa fuska tana k'ok'arin maido da lomar bakinta tana kakarin amai a lokaci d'aya.
Ba dan abincin baiyi dad'i ba, a'a tanaso ne kawai ta wahalar da Meerah tare da cimata mutunci dama dalili take nema.....
D'agowa Anty Maryam tayi a fusace tare da daka Mata tsawa, tace "ke haka ake girki a gidanku?" Ta tambaya had'e da cewa "wace jakar ce ta koya maki wannan girkin?"
Yi hak'uri Anty ba.....
Bata jira ta k'arasa zancen ba ta katse ta ta hanyar daka Mata tsawa a karo na biyu tana cewa maza ki b'acemin daga gani mutuniyar kawai.
Sum-sum Meerah ta mik'e tana b'oye hawayen da suke k'ok'arin zuwa Mata.. har ta kusan shigewa d'akinta Antyn ta Kuma kiranta ta dawo tace da ita wa kika barwa wannan kayan anan? Kizo ki kwasheshi Kuma ki tabbatar kin girkamin wani,
Tuwon shinkafa da miyar taushe Zaki mun kinji ni???.
Daga Mata Kai Meerah tayi alamar eh, tace dakyau saura Kuma ki kumayin Wanda bazai ciwu ba kigani.. qatt...
Juyawa tayi ta shige kitchen tana kuka tana d'ora sabon girkin da aka umurceta..
Ak'asan ranta tana tausayin kanta da irin wannan k'addarar da ta sameta. Ita kam soyayyar uncle Bata k'areta da komai ba sai rashin kwanciyar hankali.
Ita kanta Bata gane tayi wauta ba sai a yanzu data shiga matsala "Rashin soyayyar dangin miji mussanman mahaifiyarsa" ba karamar masifa bace a rayuwa.
Bare ita da zafin ya had'ewa biyu ba soyayyar miji, Bata uwarsa da Yan uwansa.
Ada ta d'auka data mallakeshi tayi bankwana da damuwa da bak'in ciki Ashe a yanzu ne ma ta bud'e KOFAR wadannan abubuwan.
Tabbas tayi wauta data kasa mayar da al'amarinta gurin ubangiji a lokacin da ya jarabceta da sonshi, ta Sanya son zuciya ta Manta da neman zab'in ubangiji yayin da wata matsala irin wannan ta kunno a rayuwarka.
Ta Manta da istikharar da manzo (s.a.w) ya bawa sahabbansa. Tabbas tayi kuskure dole ta koma ga Allah tayi istigfari tare da neman mafita....
😭😭😭😭Allah sarki Meerah..
Gsky kina cikin matsala babba..
#Ummu-inteesar.
_____"
❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤
Story &written by Rukayya Ibrahim Lawal(ummu-inteesar)✨✨
January 14,2020.
________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
🏤🏤 p30🏤🏤
Bayan shigewarta kitchen anty maryam ta dinga lasar hannu aranta tana cewa shegiyar yarinya Kuma fa ta iya girki, sakwarar Nan tai dad'i da badan ina son na rabata da gidan d'ana ba ai da na cinye duka..
"Nayi wauta ma da nasaka ta d'auke ragowar da na d'an ci kad'an bayan ta fita...
*******"**
Haka dai Meerah ta cigaba da tunani had'e da nadama har ta kammala tuwo da miyar ta Kuma d'auko wa ta kawowa anty maryam.
Wannan karon anty Bata k'i ba k'arba tayi tana had'e rai sai-dai Bata ce komai ba gudun karta yiwa kanta asarar daddad'an abinci a karo na biyu.
Jin shiru Antyn Bata ce komai ba yasanya Meerah ta mik'e tana yiwa Allah godiya da yasa ba'a Kuma ci Mata mutunci ba, tabar wajen.
A takaice dai Meerah ta Zama kamar baiwa a gidan mijinta saboda irin azabtar da ita da anty maryam keyi.
Itace wankin su sadeeq da fariha y'ay'an Antyn,ita ce wankansu, ita ke wa anty wanki da guga ga aikin gida gana mijinta.
Ga baki daya ta Zama abar tausayi, Dan ma Wai shi mijin Yana tausaya mata saboda yasan halin da take ciki a gidan shike ta lallashinta da Bata baki. Akan cewa tayi hak'uri komai nada lokaci insha'allah wata rana zata fita cikin wannan k'angin.
Yanzu Kam ta dage sosai da addu'a tare da neman mafita a gurin ubangijinta domin shine Mai rahma Mai jink'ai.
Nafilfili takeyi duk dare had'e da addu'ar Allah ya kawo Mata d'auki a cikin wannan lamari.
A tsakiyar dare zaune take akan sallaya bayan ta kammala nafilfilin da ta Saba yi addu'a take sosai akan matsalolin da suka shafi rayuwarta, musanman wannan matsalar ta gidan aurenta cewa take:
Ya halimu ya alimu ya hayyu ya k'ayyumu ya hannanu ya mannan ,
Allah ka kawomun d'auki a cikin rayuwar aurena,ya ubangiji na Kaine ka jarabceni da son wannan bawan naka. Nasha wahalar rayuwa akan soyayyarsa daga karshe k'iyayyar mahaifiyarsa da danginsa ta Zama masifa a rayuwata.
Allah na gode maka da wannan jarabawar Allah ka bani ikon cinyeta ka kawomun d'auki da agaji na gaggawa acikin rayuwata.
Allah ka zaba mun mafi alkhairi a rayuwata....
Tana addu'ar tana zubar da hawaye tare da k'ank'antar dakai ga ubangijinta.
Malesh ne ya farka ya ganta akan sallaya tana hawaye ta daga hannayenta sama Alamar tana addu'a ne.
Ko Bata fadamishi ba yasan tana cikin matsala Kuma yasan abunda ke damunta bai rasa nasaba da zaman anty maryam gidannan da a zabtar da ita da take tsawon wata uku.
Saukowa yayi daga Kan gadon yazo gabanta Yana lallashinta "habah bestyna Kuma wifey na Yaya zaki dinga kuka cikin dare haka?" Kiyi hak'uri manah bana gaya Miki cewar komai zai wuce wata rana ba?..
Ni kaina ba'a son Raina Anty maryam ke zaune a gidannan ba dan nasan halinta zata iya cutar dake abayan idona...
Ko dai ta kuma Miki wani abun ne bayan bana Nan?
Gayamun me ta Miki ne?
Sai a lokacin Meerah ta fashe da matsanancin kuka tare da kifa kanta akan cinyarsa tana rera kuka Mai tsuma zuciyar Mai sauraro.
Rarrashinta ya shiga yi akan tayi hak'uri ta gaya Mai meke damunta.
Cikin shesshekar kuka take cewa Ni Kam naga jarabawar rayuwa akan soyayyarka Ashe haka so yake? Ashe laifi ne Dan na soka? Zuciyata bata mun adalci ba ta rasa wazata so sai Wanda baya k'aunata a matsayina na matarsa. Baya mun kallon matarsa saidai k'awa agaresa Kuma danginsa basa k'aunata,komai nayi badai-dai bane agaresu... A gaskiya so bai........
Kuka ne yaci k'arfinta ta kasa k'arasa zancen.
Wani irin tausayinta yakeji Yana ratsa sassan jikinsa sai faman lallab'ata yake, kiyi hak'uri habibtie insha'allah zansan yanda nayi na lallab'a anty maryam tabar gidan Nan kinji kiyi hak'uri.
Waye Kuma ya gaya maki cewar bana sonki? ina sonki fa bestyna ko kin Manta a makaranta ba mai Jin kanmu Ni da ke? Ya tambaya cikin sigar lallashi.
Mik'ewa tayi tare da Zama ta kalleshi ido cikin ido tana share hawayen idonta " dagaske kana so na uncle?" Ta tambaya tare da kafeshi da ido tana so ta tabbatar da abunda taji.
Lallausan murmushi ya sakar mata tare da d'aga Mata Kai alamar tabbatarwa lokaci d'aya yace tabbas ina sonki matata ki Sanya a ranki Ni naki ne ke kad'ai.
Kidaina ganin laifin zuciyarki Dan ta zab'a maki Wanda ya dace dake Kuma Mai k'aunarki. Ina sonki abokina ne ya riga ni furtawa shiyasa na nemi soyayyar k'awarki a wancan lokacin, but I love you my wife. ya fad'a dukda cewa ya fad'i hakane kawai Dan ya faranta ranta.
Ai kuwa ba k'aramin Jin dad'i Meerah tayi ba ta fad'a jikinsa tare da k'ank'ameshi fad'a take Alhamdulillah Allah abun godiya.
I love u too my husband I really love you.
**********
Bayan wata biyar Meenah ta haifi yarta santaleliya fara sol Mai kama da ita.
Farinciki agun Manish ba'a magana, Ranar suna yarinya taci sunan Ameerah suna kiranta da little Meerah. Wato dai yayiwa ex dinshi takwara,
Meenah taji kishi akan hakan sai-dai Bata nuna hakan ba ko a fuska.
**************
Wata matashiya na hango zaune akan kujera 2 sitter tana cin alale dakin acike yake da jama'a alamar bikin suna ake, sai da na matso daf da ita sannan na gano Ashe Meerah ce Kuma tana d'auke da cikin wata biyar a jikinta Wanda daga nesa bazaka iya fahimtar hakan ba saboda kad'an cikinta ya turo zaka ma d'auka cewa tumbi ne ta ajiye.
Tana cin alalen suna Hira da k'awarta farida tayi kyau sosai.
Mai jego ce ta shigo d'auke da jinjirar a hannunta tazo gaban Meerah ta mik'a mata y'ar tare da cewa k'arb'i wannan takwarar taki Mai tsinannen nauyi, kowa shakkar d'aukarta yake saboda nauyinta.
Murmushi Meerah tayi sai a lokacin taji cewar jinjirar sunanta taci hakan na nufin kenan Manish bai Manta da ita ba.
K'arbar little tayi tare da fad'ar andaiji ai tunda ku ragwaye ne dole ku fad'i haka. Bani y'ata Ni banajin nauyinta ai saniya Bata gazawa da kahonta...
Dukkan mutanen dake d'akin suka bushe da dariya...
##ummu-inteesar✨✨
_____"
*❤❤SOYAYYAR MEERAH❤❤*
*Story &written by Rukayya Ibrahim Lawal* *(ummu-inteesar)*
*THE END*
✨____________________ _*wannan page din kacokan sadaukarwa ne gareki AUNTY HAUWA ADMIN ina yinki over.*_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
🏤🏤 p31🏤🏤
Yanzu Kam Alhamdulillah an samu sassaucin k'iyayyar da umman malesh da k'anwarta suke nunawa Meerah.
Anty ta rage takura mata saboda tsantsar biyayya da girmamatan da take da Kuma nunawa y'ay'anta soyayya da yarinyar take sai taji zuciyarta tayi sanyi k'iyayyar da takeyiwa Meerah ta ragu da kusan 50%
Abangaren umman ma hakane ada idan sunyi waya da k'anwar tata takan tambayeta ya shegiyar yarinyar nan kin dai sakata a k'unci Koh?
Amma ga mamakinta ayau suna waya da yayar tata take tambayarta "Wai Ni kuwa Maryam yaushe Zaki dawo?"
Dawowa Kuma Yaya? Bakece kika turoni Nan Dan na takura shegiyar yarinyar nan ba?
Kuma kike tambayar...
Dakata Maryam ki dawo gida kawai Ni na hak'ura da wannan abun haka, Nan da y'an wasu watanni zata haifamun jika miye ribata idan tashiga k'unci yaranta zasu taso suji labarin k'iyayyar dana nunawa mahaifiyarsu yakike ganin abun zai kasance?.
Mamaki ne ya cika Maryam tace kindai hak'ura kenan Yaya?
Ai dole na hak'ura kodan lafiyar jikana dake cikinta idan tana cikin k'unci zai iya shafar lafiyar d'an cikinta. Nikam ki dawo haka Maryam na hak'ura.
To Yaya ni kaina zuwa yanzun tausayi take bani wallahi kusan wata biyar kenan ina k'untata Mata zan nemi yafiyarta data d'ana malesh na dawo gida.
**********
Wannan sanyin da zuciyoyinsu sukayi bai rasa nasaba da addu'oin da Meerah ta dage dayi ba dare ba rana.
Allah maji rok'on bawa ya k'arba addu'arta tunda har gashi Ayau anty Maryam tazo har gabanta tana bata hak'uri da neman yafiyarta akan abubuwan data d'inga yimata na cutarwa da cusa bak'in ciki a zuciyarta.
Bayan ta tabbatar mata da ta yafe anty Maryam ta tattare y'ay'anta da kayanta tabar gidan malesh bayan Shima ta bashi hak'uri akan cutar mai da mata da tayi.
Bak'aramin dad'i Meerah taji ba da Anty ta bar gidan a bayyane tace Alhamdulillah.
**************
Shi kanshi mijin nata yanzu Yana matuk'ar sonta da nuna Mata k'auna,
Yana tarairayarta kamar k'wai.
Sai A yanzu yakeji a ranshi cewar yayi dacen mace tagari wacca take mishi k'auna ta hak'ik'a tunda har ta iya jure cutarwa da wulak'ancin da danginsa sukeyi Mata.
Tabbas shi Mai sa'a ne a rayuwa da yayi sa'ar mallakar zuciyar tsaleliyar mace kamar Meerah Mai hak'uri da juriya gashi ta kasance Mata tagari a gareshi. Tunda duk abunda danginsa ke Mata Bata tab'a Kai k'ararsu ko tasa gurin iyayenta ba,ta boy'ewa kowa damuwarta dukda cewa yasan ita gwana ce a gurin b'oye sirri a zuciya,tanada wannan jarumtakar Amma ya jinjina Mata sosai.
Ya K'ara yiwa Allah godiya da yasa Bai yi fatali da damar da tazo masa sau d'aya a rayuwa ba.
A lokacin yaso yak'i wannan Auren da aka had'a Kai tsaye, tabbas da yayi haka har abada bazai daina nadama ba...
Allah ya mashi chanji mafi alkhairi agareshi,shiyasa duk abunda kaga Allah yayi maka to shine Alkhairi a gareka.
yasani "Meenah tana gidan mijinta hankali kwance harma ta Manta dashi, Wanda ya tabbatar da da ace Meerah ce a matsayin Meenah Koda tayi aure da wani dabam a yanda takesonshi bazata taba mantawa dashi ba"
Saboda haka yake K'ara godewa Allah da wannan baiwar da ya mashi a rayuwa ta mallakar mace Mai matuk'ar sonshi wacca yayi imani bazata iya cutar dashi ba.
*****************
Meerah kuwa yanzu tana cikin walwala da nishad'i farincikin da tajima tana mafarki yanzu ta sameshi a gidan aurenta.
Kyakkyawar rayuwar aure suka shimfid'a Mai cike da soyayyar juna,tausayi da kulawa.
A yanzu Jin ta take tamkar sarauniya gani take tafi kowacce mace sa'a a rayuwa data mallaki miji irin malesh.
******************
Bayan wata uku Meerah ta haifi kyawawan y'ay'anta Mata guda biyu masu matuk'ar kama wato dai tasamu identical twins. kamar yaran da mahaifiyarsu ta fito sak.
Fad'ar irin farincikin da malesh yayi Bata lokaci ne, hakama ummansa murna take sosai zan iya cewa tajima batayi farinciki irin na wannan ranar ba da take rik'e da wad'annan yaran a matsayin jikokinta abunda batada wato jikoki Kuma abunda bata taba samu ba, wato y'ay'a Mata har kukan farinciki saida tayi take a gurin taji duk wata tsana da takeyiwa sirikartata ta fita a ranta.
Kusan wuni umman malesh tayi a gidansu Meerah tana rungume da jikokinta Bata ma son bayar da babies din sai dole. Take agurin ta nemi yafiyar Meerah akan k'untata rayuwarta da tayi tabbas
Mijinta ya fad'i gaskiya dayake cewa ta sassauta k'iyayyarta ga sirikarta Dan wata rana zata iya Zama mafi soyuwa a ranta, gashi kuwa ta faru a yanzu ma ji take kamar tafison Meerah akan d'annata.
Ranar suna yara suka ci sunan MUBEENAH & MUNEEBAH saidai fatar Allah y Raya su.
A gidansu Meerah akayi taron sunan kasancewar haihuwar fari ce an mayar da ita gidansu acan ta haihu, acewar Ammi sai tayi Arba'in biyu zata Koma d'akin ta.
Inda malesh ya kasa jure haka a ranar da ta cika 50 days a gida malesh yaje gidan kamar kullum.
Yace da ita tazo suje mota suyi wata magana bazai iya fad'a anan ba kunya yakeji.
Kasancewar yanzu ya siyi mota dan tun bayan haihuwar yan biyu kofofin arziki suka bud'e Masa kasuwancinsa ya fara hab'aka.
Ta mik'e zata biyoshi yace to d'auko d'aya yarinyar kasancewar d'aya na hannunsa ne dama.
Har ta bud'i baki zatai magana ya dakatar da ita ta hanyar daga Mata hannu.
Hannu ta saka ta d'auki Mubee tabishi a baya, a mota ta sameshi ta bud'e dayan side d'in tashiga kafinma ta gama daidaita zamanta taji ya sakawa motar lock ya tad'a ta dasauri ya hau hanya.
Cino baki Meerah tayi kamar wata baby tana cewa" Ina Kuma zaka kaini kaida kace zamuyi magana?" cike da shagwab'a tayi zancen.
Siyar da ke zanyi amsar da ya Bata kenan batare da ya kalli side d'in da take ba.
Zaro ido waje tayi Alamar tsoro tace "nashiga uku kodai Dan kaga kaina yanada girma ne shine zaka siyar abaka kud'i?
Eh yace Mata, dariya sosai yadingayi ganin duk ta tsure.
Yana k'arasawa bakin gate din gidanshi ya fita motar ya bud'e gate din sa'annan ya dawo ya shige da motar ciki.
Kallonshi kawai take batare data iya cewa komai ba to miyake nufi ya gudo da ita Nan kodai Yana nufin ta dawo kenan? A ranta take zancen kamar ya karanci abunda ke ranta yace: kina mamaki ko? Ba dama na gayamaki bazan bari ki Kai 80days agida ba? Fito kawai malama mushiga ciki.
A'a uncle ka maidani gida kafin su Ammi su ankara da guduwar dakayi damu kasan fa ta nace akan sainayi 80 days zata maido Ni.
Bai tamkata ba yafito daga motar yasa Kai ya shige cikin gidansa da yarsa Munee a hannu bayan ya kulle gate din gidan da makulli.
Kamar ta fashe da kuka haka taji bayan da ta iya dole tabi bayanshi tunda ba damar fita ya rufe gidan....
Tana shiga parlourn ya tintsire da dariya au wifie baki Koma gidan ammin bane? Na d'auka ai kintafi tuni cike da k'eta yake zancen.
Kuka ta saka mashi tare da d'aukar filon dake Kan kujerar ta jefeshi dashi.....
Dariya yake sosai harda rik'e ciki.
Da haushin ya Mata yawa sai ta tashi ta nufi bedroom d'inta tana cewa Dan kaga ana sonka kakewa mutane mugunta to andaina sonkan....ta fad'a a lokacin datake shigewa d'akin.
************
Anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa Mai suna "SOYAYYAR MEERAH"
Mai d'auke da darussan rayuwa musanman abunda ya shafi soyayya.
Duba da irin halin da soyayya take ciki a wannan zamani, y'an Mata da samari basa Gina Soyayyarsu akan gaskiya da rik'on amana.
Da yawan matasanmu suna Gina Soyayyarsu akan k'arya da yaudara duk kuwa soyayyar da aka Ginata da tubalin k'arya tabbas zata roshe ne daga k'arshe Kuma bawani amfaninta da za'asamu.
Yan Mata nawa kuka sani a zamanin nan da sukeyin soyayya irin ta MEERAH?.
K'awaye nawa kuka sani da suke da aminci a tsakaninsu kamar MEENAH, MEERAH DA FARIDA?
Wacca k'awa ce zata iya sadaukar miki da farincikinta a wannan zamanin?
Kowane kawance na gaskiya ya kamata ya Zama irin k'awancen Meenah,Meerah da Farida ta yadda zaku dinga raba damuwar junanku a tsakaninku.
A wannan zamanin wacece zata iya Sadaukarwa ga masoyinta kamar yanda Meerah tayi?
Daga karshe Ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da yabani damar kammala wannan k'ayattacen littafi Mai suna SOYAYYAR MEERAH Kuma littafina na farko Dana fara wallafawa a media.
Dafatar wannan littafin ya fad'akar Kuma ya k'ayatar tare da bada nishad'i.
Allah yasa muyi amfani da fad'akarwar dake cikinsa. Ameen.
Amincin Allah da rahmarsa su tabbata a gareku readers na wannan book.
Sai kun jini a cikin sabon littafina Mai suna Y'AR GANTAL
I(MAI HANGEN NA WANI).
#UMMU-INTEESAR
❤❤❤
_____"
0 Comments