Sara da sassaka hausa novels cmplt

 SARA DA SASSAKA baya hana gamji toho[11/4, 10:09 AM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏


      SARA DA SASSAKA

          (Baya hana gamji)

                       toho 


🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳                   



   Story 

       And

   Writing

            Rasheedat Usman

 

       ( Ummu Nasmah)



🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻


{United we stand and succeed ; Our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's}


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation



Godiya ga Allah subahanahu wata'ala daya sake dawo dani domin na nishadantar daku na kuma fadakar da mai saurarona.


   Shimfida


    Kirkirarran labari ne banyi shi dan cin mutuncin kowa ba, duk wacce taga yayi kama da halin ta, to labarin ne kawai yaxo a haka, ina son duk wacce taga yayi kama da halin ta, da tayiwa Allah ta gyara.

   Wannan lbrn yana tattare da ilimantarwa fadakarwa tare da zalinci cin Amana  da kuma soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu.



Masoyana ina alfahari daku a duk inda kuke mussaman friends dina dake cikin group din NASMAH KO NASIRAH

Ina yinku irin sosai dinnan ❣👌🏻



   Deducted

        To

My lovely momy ina alfahari dake, domin kedin uwace da kowacce ya, zatayi alfahari dake, ina rokon ubangiji daya karawa rayuwar ki albarka tare da nisan kwana.

    I love you so much momy nah.


Godiya Ta Mussaman


  Ga kungiyar KAINUWA✍🏻 WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 ina alfahari daku a koda yaushe  KAINUWA dashen Allah ba dashen mutum ba, makiyan ki fadawan ki, Allah ya bar kauna da zumunci kungiya mai hadin Kai.



P•••••••••••1️⃣ to 2️⃣



Rugar Ardo Boyi



" Dan Allah mama kiyi hkr na tuba wlh baxan sake ba, kimin rai dan Allah na rokeki kibar dukana haka.


  " Naki na bar dukan naki, shegiya mayya, yau zanga uban da zaizo ya kwace ki, a hanuna, wai ke ga mai uba koh, ba wanda ya isa ya miki ko fada ne sai ya hau mutum da masifa, to ai yanxu sai yaxo ya kwace ki, a hanuna.


  " Ihu yarinyar take tana bawa Wannan dattijuwar matar wacce baxa ta wuce shekaru 48 ba a duniya, hkr, ita kuma yarinyar da akewa wannan mungun duka baxata wuce shekaru 19 ba a duniya.

   Kimin rai mama na tuba !! na tuba nace baxan sake ba.


 " Innalillahi wa'inna' ilaihirraji'un haba salame yanxu da hankalin ki kike yiwa wannan yarinyar, irin wannan duka, ki duba fa kiga yadda jikin ta ke tsatsaffo da jini.


   " Wlh inna mero baxan kyale yarinyar nan ba, na tsaneta !! Na tsaneta !! Na tsaneta, kamar yadda na tsani uwar ta, kuma insha Allah sai nayi SANADIN SHIGAR KI DUNIYA, kamar yadda na kawo Karshen zaman uwarki a wannan rugar in kuma saka kiyayyar ki a zuciyar shi uban naki.


  " Ashsha !! ashsha keko salame meyayi zafi haka wanda har zuciyar ki, take cike da kiyayyar NASREEN.


 " Da sauri wacce aka kira da Nasreen din ta dago manyan idon ta da sukayi jajur tana kallon fiskar Mama salame.


 " Mari mama salame ta zabga mata sannan ta hankade ta gefe guda ji kake gum ta bige goshin ta akan wani dutsen da suke xaman alwala  a kai, take kuwa goshin nata ya tashi ya kumbura sosai, tace shegiya mayya kin dago wadannan idonun naki kamar na mujiya kina kallo na dasu, tashi ki dauki tulo maxa ki debo min ruwa a rafi kuma sau hudu zaki min, ko baxaki tashi bane dan ubanki.


    " Inna  mero ne tace haba salame kina ganin yanda jikin yarinyar nan  yake tsatsaffo da jini, kuma a hakan kice ta tafi rafi dibo ruwa, ina yar gwal take, taje ta debo ruwan mana ita, in yaso ita Nasreen zuwa yamma, idan ta dan ji dama dama sai taje dibo Miki ruwan.


" Mero kema fah kinji sunan da kika kira, cewa kikayi yar gwal ai kuma kinga yar gwal tafi karfin zuwa Rafi, tunda Allah ya kaddara muna da bayi a cikin gidan Nan, ai kinga sune zasu debo Ruwa, Amma banda dai yata.


" Kada kanta tayi wacce aka kira da yar gwal din, tace yawwa fada mata dai, ina da jaka a cikin gidan Nan, ai kuma saidai naci Nasha na kwanta nayi bacci, dan jikina baiyi kama dana wahalallu ba, ita dai Nasreen din mai zubin wahalan taje tata fama.


"  Dundu mama ta saukewa Nasreen a bayan ta, tace baxaki tashi bane, dan ubanki sai na kara miki kacakaca da jiki.



 " Shuru Nasreen tayi tana murxa goshin ta da hanun ta, yayin da take jin jiri na diban ta, gaba daya gidan juya mata yake, bibbiyu take ganin su, da kyar ta tashi ta nufi inda ake ajiye tulun, ta dauka tana hada hanya a haka ta fice daga cikin gidan.


    A rakube ta same sa a zauren gidan sai faman risgar kuka yake, tare da ajiyar zuciya, " NURUDDEEN lafiya kake wannan kukan dan Allah ka daina, kar nima ka sani kuka.


Yaron da ta kira da Nuruddeen din baxai wuce shekara 8 ba aduniya.

  Kamo hanun ta yayi yace " adda Nasreen mama bata tsoron Allah, muguwa ce azzaluma kuma malamin mu na islamiyya yace duk mutumin da yake zalinci baxai shiga aljanna ba. 

Adda Nasreen ki kalli yanda jikin ki yake fitar da jini, Allah ya isan ki, 


 " Murmushi Nasreen tayi, ta shafa kansa, tace karka kara kiran Mama da sunan muguwa ko kuma azzaluma, itama uwace a wajen mu, bamu da wacce ta fita a Yanxu haka, nasan dukan da Mama tamin yasa ka kira ta da azzaluma koh, to kayi hkr komai zai wuce, mu kalar tamu kaddarar kenan, ta Rashin samun gatan Mahaifiya, wannan wahalar da mama take samu, na lokaci kadan ne, daga zarar BABA ya dawo daga binni, zata daina, sai dai kuma inya kara komawa ta daura daga inda ta tsaya.


" Adda Nasreen, yunwa nake ji rabona da Abinci tun kokon safe, ciki na sai kugi yake min, naje karbar abinci rana Mama tace baxa ta bani ba, sai dai na jira sanwar Dare.


   " Murmushi Nasreen tayi dake ita Allah yayi ta mace ce mai yawan fara' a duk damuwar da take ciki baxai hana kaga murmushi dauke a fiskar taba " kayi hkr Nuruddeen yanxu inna fita zan biya lanbun malam sale na roke sa da ya taimaka min da yayan iccen sa ko ayaba ne, zan dawo maka dashi ka dan taba zuwa Daren muga abunda Allah zaiyi, 



  " Adda Nasreen Nabiya tun safe da ta fita tallen da Mama ta daura mata har yanxu bata dawo ba, ko lfy sai Allah.


  " Dariya Nasreen tayi har sai da dumple dinta ya lotsa, tace Nuruddeen ai kasan duk randa Mama ta daurawa Nabiya talle bata dawowa sai sakaliyar la'asar, dan haka karka damu ta kusa dawowa.


 Kadan kansa yayi alamun gamsuwa da maganar ta, adawo lfy ya mata, kafin nan ta fice zuwa Rafi.


   A cikin gidan kuwa, innah mero ne take cewa, Mama Niko salame har yaushe ne zaki bar kishi da Maimuna matar da kika riga kika batar da ita, ta shiga duniya, ko labarin ta  ba'a ji, ya kamata ace kin bar yaranta sun sami sukuni Koh.


  " Hmm Mero kenan, baki ga yanda soyayyar da Malam ke yiwa Maimuna ya koma kan yaranta ba, dani da yarana fah a cikin gidan nan, kirikiri yake nunawa yafi son yaran Maimuna, mussaman ma wannan shegiyar mai idanun mujiya, yafi kaunar ta fiye da kowa a cikin gidan nan, aiko kinga kyara da tsangwama yanxu ma na fara nunawa yaran Maimuna, har sai sun gaji da kansu sun bi uwar su DUNIYA.


  " Kiji tsoron Allah salame ki rage munanan abubuwa, ki gyale yaran nan suyi rayuwar yanci a gidan uban su, salame ki duba fah kiga irin zalincin da kika yiwa Maimuna, bata taba miki mugunta ba, saima biyayyar da take miki,  wlh tunda nake a Rayuwata ban taba ganin mace mai hkrn Maimuna ba.


  " Ikon Allah yau kuma mero wa'axi kika fara, to ai kamata yayi kice, muji tsoron Allah, ba naji tsoron Allah ba, tunda dani dake din, duk kwaryar sama ne da ta kasa.


   " A'a wlh salame ban kaiki mugunta ba, domin kuwa ni ban shigar da kishiya ta, duniya ba, sannan kuma ban taba zina da boka ba, ( wa iyazubillah) bana kuma kyarar yayan kishiya ta kamar yanda kike kyarar yayan Maimuna, kinga kuwa ai Halin mu ya babanta.


 " Hada fiska Mama tace ke mero, fice min daga cikin gida, tunda ba arziki bane ya kawo ki, aikin banxa harni zaki sa a gaba kina gaya min magana, kamar wacce kika samu yarki, to wlh ki rufe idon ki, akan lamarin cikin gidan nan, domin kuwa kinfi kowa sanin Salame ba kanwar lasa bace, domin  ba'a shiga gona ta, a fita lafiya, dan haka, ki kiyaye, in kunne yaji jiki ya tsira.


   " Tashin innah mero tayi, tace Allah ya Baki hkr daman hayaniya ce naji shi yasa na shigo naga meke faruwa, dan haka kinga tafiya ta.


  " Jeki munafuka Allah ya tura keya, mai yawan gulma zuwa gidan mutane.


  " Ita dai innah maro bata tanka mata ba tayi tafiyar ta.


   Lanbun mlm sule, Nasreen ta shiga, yana zaune a cikin duhuwar lanbun, mlm sule abokine ga mahaifin Nasreen aboki tun na yarinta.

   Karasa wa tayi har inda yake  ta sunkuya, ta gaishe shi


" Amsawa mlm sule yayi, yace, yata Nasreen yau kece a lanbun nawa.

  

" Ehh nice mlm daman naxo ne, ka taimaka min da wani abu daga cikin ya'yan itacen da Allah ya hore maka acikin lanbun Nan, Nuruddeen ne yake jin yunwa baici komai ba tun safe, shine nace fana xo gunka ko zan dan samu ko ayaba ne, na kaimasa ya samu ya rage yunwar da take damun sa.


   " Cikin tausayin halin da yaran suke ciki mlm sule ya girgixa kansa, yace yata ai kinfi karfin abunda yake cikin lanbun nan, ki shiga ki debi duk abunda kike so, sannan daga yau karki kara tunanin zuwa kice zaki roke ni, wani abu dake cikin wannan lanbun, ko yaushe kika zo ki shiga kawai ki deba duk abunda kike bukata, domin kedin yace a gare ni, baki da wani bambanci da ya'yan dana haifa..


  " Godiya Nasreen tayi wa mlm sule sannan tace, fa taje Rafi ta debo ruwa sai ta dawo ta dauki kayan lanbun.


" Nasreen !! Nasreen !! Nasreen.


" kawar Nasreen ce Indo ita daya ce kawarta a duk cikin rugar bata da wata kawar da ta wuce indo.

    Juyawa Nasreen tayi tare da cewa haba Indo wannan kira haka, ai kya bari ki iso, tunda naga tsakanin mu babu wani tazara.


 " Nayi zaton kafin na iso ki zaki dan tsere minne banyi tunanin kin ganni ba ma.


  " Na ganki naso ma dana fito na biya miki, to kuma nabi lanbun mlm sule ne, shiyasa ban biya miki ba.


" Lanbun mlm sale kuma, me kika jeki yi acan?


  " Wlh kekam Nuruddeen ne naje karbawa yayan iccen yunwa yake ji rabon mu da Abinci tun kokon safe.


  " Ai Kuma naga da safe MAMA takai murjin taliya gidan mu, ke nan bata baku abincin ba.


  " Bata bamu ba, ni ciki na bai dameni ba, nafi tausayin Nuruddeen da Nabiya, mussaman Nuruddeen bayi da hkrn yunwa, idon ta ne ya ciko da hawaye tace ina tausayin Nuruddeen, mussaman idan na tuno da yanda ya tashi Babu mahaifiya Nuruddeen a tsakar gida ya tashi, baida wata uwar da ta wuce ni, cikin zubar hawaye tace Ayya AMMI ki taimaka ki dawo gare mu, na tabbata idan kina kusa damu zamu samu saukin wasu abubuwan.


" Dafa kafadar ta Indo tayi tace, kiyi hkr Nasreen tabbas kina cikin halin kunci, insha Allah komai zai wuce, baxan gaji da cemiki wata Rana sai labari ba.

     Idan mun dawo daga rafin ki turo Nuruddeen gidan mu, akwai sauran abinci.


  " A'a Indo mlm sale ma yace idan na dawo na biyu na karbi yayan iccen.


" Shikenan ya naga jikin ki, ya na tsatsaffo da jini, goshin ki kuma, ya tashi.


 " Ke dai bari kawai Indo yawan maganar ma babu dadi.


 " Shikenan mu karasa rafin.

  

   *************************

Kwance take akan kirjin sa yayin da hanun ta, ke Wasa da gashin kirjin nasa, 

    " Sweet heart yaushe ne zaka barni naje gida tun jiya nake, tambayan ka, kaki bani amsa.


   " Murmushi yayi, tare da shafa gashin kanta,yace Baby kin cika yawan zuwa, gida ki bari sai, next week.


  " Tura bakin ta tayi, tace Gaskiya sweet heart ban yadda ba, kaga nayi kewar junior, ina son ganin dana.


  " Janyo ta yayi jikin sa, tare da manna bakin sa, akan nata, yafi 10 minute yana kissing dinta, yayin da hanun sa yake, murxa kan nipples dinta, ta cikin rigar ta, yace oh Baby ki bar zancen zuwa gidan nan fah, sai next week.


  " Ranta ne ya baci, ta  kwace jikin ta, daga nasa, gyara zaman rigar ta tayi, ta fice daga cikin dakin nasa.


  "  Zuhyra !! Zuhura zuhura !!


" Tana jin kiran da yake mata, tayi banxa dashi kamar wacce bata jinsa ba.


 Oh my God, ZUHURA kina da matsala, wlh, wai ace mace bata da lokacin kawo matsalar ta sai taga ina cikin kishin ruwar ta, sannan zata zomin da abunda zata guje min, why !! Why ZUHURA sai kinga na kawo gejin da baxan iya sarrafa sha'awa ta, sai ki tashi, na Rasa menene matsalar ki zuhura.

   Tsaki yayi tare da tashi ya bude fridge din dake dakin lemon tsami ya dauko, da abun matse shi, matse lemon tsamin yayi a cikin wani karamin cup, tare da zuba masa suger, kafa kansa yayi, ya shanye lemon tsami tas, san ya koma saman gadon sa yayi rigingine,tare da kafawa slim din dakin Ido, yana tunanin matsalar matar sa.



 khabeer kenan babban jami'in hukumar yan sanda na kasa da kasa, IPS jami'in Sirri


Tsaki ZUHURA taja sannan tace Aikin banxa kawai mutum baida aiki sai jarabar tsiya duk Randa ya dawo Kasar Nan banda sukuni rai da rai yana manne da mace, ni ina zan iya wannan jarabar tsiyar, ina ga da bana planning da Yanzu na Tara yara uku ko Hudu, dan irin su Abban junior sune masu saka mace yawan kunika,

  Kuma wlh babu abunda zai hanani zuwa gida anjuma duk abunda zai faru ya dade bai faru ba.

   " Ke Asabe kixo Nan.


" Da sauri Asabe ta Fito daga kitchen har tana bigewa da hanun kujera, tasan Halin ummin junior, sam bata da mutunci, ta maka Rashin mutunci hakan ba wani abubane a wajen ta.


" Barka da hutawa ummin junior naji kinyi kirana.


" Kallon shekeke Zuhura tayiwa asabe tace, kin gama lunch dinne.


" A'a ban gama ba tukkuna saura dakan doya ne.


" Haba Asabe tun yaushe kika daura abincin nan, ace har yanxu baki gama ba, ki fah daina mini horon yunwa, ai kin san ina da ulcer bana iya jure yunwa, Gaskiya baxan iya zama da keba kina min horon yunwa gwara na sanja ki, kawai, ki koma chan kauye, kije kita fama da dawa da masara.


" Kiyi hakuri ummin junior zan gyara insha Allah bari naje na karasa.


" Kije dakin Abban junior ki gyara masa ki wanke tollet dinsa ya fita sosai akwai turaren wuta a bedside drowern sa. Sai ki kunna Masa.

     Amma kije ki kira karima taxo ta karbi dakan doyan ina jin yunwa baxan iya jira har sai kin gama aiki Nan ba.


" Da to Asabe ta amsa sannan ta shige part din su na Yan aiki.

   Tare suka dawo da karima tayi dakin Abban junior ita Kuma karima tayi kitchen.


" Asabe tayi sallama wajen sau uku a dakin Abban junior shuru ba'a amsa mata ba.

    Shiga kawai tayi dakin, kai tsaye.


" Tsawa ya daka mata yace ke baki da hankali ne, zaki shigo dakin mutum babu ixini, ko haka akeyi a garin ku.


  Cikin girmamawa Asabe tace nayi sallama har sau uku ba'a amsa min ba, nayi zaton babu kowa ne a dakin shiyasa na shigo.


" Me kike nema a dakin nan.


   "Ummin junior ne tace naxo na gyara dakin.


   " Zaro idon sa Abban junior yayi, yace, ita zuhura ne tace kixo ki gyara min daki, yaushe yan Aiki suka fara mini gyaran daki ban sani ba.

    Kinga, jeki abunki, bana bukatar gyaran.

   

" Bayan fitar asabe ne Abban junior ya zauna tare da dafe kansa yace wato ita Zuhura tafi karfin ta gyara min daki sai dai Yar Aiki ta gyara,.

   Tabbas Lamarin Zuhura akwai gyara.


 " Zuwa Asabe tayi gun Zuhura tace Abban junior yace baya bukatar gyaran.


 " Tabe bakin ta tayi, tace okay shiya sani kije ki taya karima ku samu ku karasa aikin da wuri, in kun gama kimin magana ina bedroom Dina.


  "Shigar Asabe kitchen din ta samu har karima ta kusa gama dakan doyan.


  " Asabe har kin gama aikin da wannan uwar masifaffun ta saki.


  " Zama Asabe tayi tace ai bamma yiba, daman dakin Abban junior tace naje na gyara.


   " Nidai Asabe ummin junior tana bani mamaki, ban taba ganin macen da take yiwa mijin ta Abunda taga dama ba sai it's, ga shegiyar kazanta wai ace dakin mijin ki ma baxaki gyara ba, har sai kinsa wata ta gyara miki dakin mijin ki, inta dauro ma ta gama gane Miki sirrin miji.


  " Aini karima wlh tausayi Abban junior yake bani dan wlh duk sanda akace namiji baiyi dace mata ta gari ba, to Gaskiya yana cikin bakin ciki, ita fa ummin junior ko yan uwansa bata dagawa kafa ba.


   " Kema dai Asabe akwai ki da shirme, matar da bata dagawa mijin ta kafa ba, uban waye zata dagawa kafa, nifa wlh kullum nayi sallah saina roki Allah yasa Abban junior ya kara Aure sannan kuma ya samu mata ta gari, wacce zata share masa hawayen sa.


  " Ameen karima nima wlh ina masa wannan Addu'ar, kinga mu samu mu gama aikin nan kafin ta dawo kanmu.



   " Da karfi ya tura kofar dakin nata.

    Tana kwance rike da waya tana faman chart.

  Fisge wayar yayi daga hanun ta.


 

   " Lfy Mlm zaka wani shigo min daki a hargitse, wani abune kuma ya faru.


   " Murmushi mai ciwo yayi yace, tambaya ta ma kike  mai ya faru,.

   Wai Zuhura mai yake damun rayuwar kine yanxu zuhura abun naki har ya Kai da ki turo min yar Aiki dakina ta gyara min, wato ke kinfi karfin ki gyara min daki sai dai kisa yar aiki, wai Zuhura yaushe zakiyi hankali ne.

    Na fara gajiya fa da wannan Halin naki, wai ace kina mace ma baki iya girki ba, ke komai sai dai a miki.

     Abun kunya wai ina da mata amma duk sanda  nake kasar nan sai na je gidan mu naci abinci.



   " Hanu ta daga masa tace dakata Malam, wadannan abubuwan da kake jero min su, bafa yau aka fara su ba acikin gidan Nan, maganar tura yar aiki kuma ta gyara maka daki, na gaji ne da gyara kullum shiyasa nace, itama Asabe ta gyara yau.



    " Asabe Mata tace da zaki turo min ita dakin.


  " Na gaya maka gajiya nayi, dan koda jarabar ka kawai aka barni ya isheni ba sai an kara min da bautar cikin gidan nan ba.  

    Da kake maganar ka fara gajiya da Hali na, ai sai ka rabu dani kaje ka nemo wacce zata iya dakai.


   " Okay haka kika cemin kenan.


  " Kwarai kuwa haka nace.


  " Hanun sa ya daga ya wanke ta da mari.


  " Dafe fiskar ta tayi, tace ni ka mara Abban junior.


  " Na mareki ko zaki Rama ne, kuma bari kiji na gaya miki this is the last time da zaki kara turo min wata dakina,

Idan kuma kika kara Abunda zan miki gaba sai yafi wannan.


  Zanci gaba da typing idan naga ruwan comments dinku in kuma banga comments ba zan dakatar da rubutun

  Domin comments dinku shike nuna min karbuwar littafin a gare ku




Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


  (Ummu Nasmah)

[11/5, 2:04 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

          ⛏⛏⛏⛏

    SARA DA SASSAKA                                     

       (Baya hana gamji)

                   Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


  Story

        And

   Writing

            Rasheedat Usman


          ( Ummu Nasmah )


🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻


{ United we stand and succeed ; Our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's}


htpps://www.facebook.com/kainuwawritersassociation


    

 بسم الله الرحمن الرحيم



Dedicated

     To

    All fans of SARA DA SASSAKA baya hana gamji toho.

   Na gode sosai da karban littafin nan hanu biyu da kuka yi.

  Wannan page din naku ne SARA DA SASSAKA groups, kuyi yadda kuke so dashi.


   Ina jin dadin comment dinku, mussaman yanda kuke min sharhi, ina mungun jin dadi sosai,

   Ji nake kamar na sunkuya dukan ku, ku hau bayana na goya ku.

   I love you so much fans Dina.



P•••••••••••••3️⃣ to 4️⃣


Bayan ficewar Khabeer (Abban junior)  daga falon nasa, parking space ya nufa, motar sa ya hau, da nufin zuwa  gidan su.

  Jami'an tsaron dake tsaron gidan ne, suke ta gaishe da ogan nasu, Cikin mutuntawa yake amsa gaisuwar tasu, sagern Daniel ya kira.

 

   " Har bakin motar tasa Daniel ya biyo sa,.


  " Kallon sa Khabeer yayi yace, Daniel Aiken ka, nake son zanyi idan baka da wani abunda zakayi.


 " Oga ai ko ina da abunda zanyi zan bari naje Aiken ka bare ma babu wani abunda nake yi.


   " A'a Daniel bana son Abunda zan takura ku, Amma tunda kace babu, Fine.

   Ka dauki motar kaje gidan su Zuhura ka dauko min junior.


   " Shikenan oga an gama Yanxun nan zanje na dauko sa.

  Har Daniel ya juya, Khabeer yace.


  " Amm kaga Daniel idan ka daukosa ka biyo ta family Hause din mu, ka kawo min shi.


  " Shikenan oga zan kawo sa yanxun Nan.


  " Murmushi Khabeer Yayi yace, banda yanxu kam, cewa zakayi zan kawosa zuwa anjuma, yanxu nan kam, ai yana nufin kafin ma na bude idona kenan.


  " Dariya Daniel yayi kasancewar yasan Halin ogan nasu,  duk sanda yayi magana sai ya masa gyara.

      Shikenan oga sai na kawo San.


  " Jan motar Khabeer yayi tare da cewa Allah ya kawo ki lfy.

     unguwar fedaral low-cost dake cikin jihar Gombe, ya nufa hon yayi kafin Baba mai gadi ya bude masa kofar,

    Bayan yayi paking ne ya dawo wajen Baba mai gadi, Hanu ya mika masa sukayi musabaha,


   " Khabiru yaushe ka dawo kasar, bamu da lbr, dan ko Alhaji banji yana maganar dawowan naka ba.


   " Dawowar nawa ai Babu shiri Baba, Abunda mukaje neman mun samu cikin sauki, kaga kuwa ai dole mu nema gida da wuri.

   Mu kyalewa yan Indonesia kasar su.


   " Gaskiya ne khabiru kuna shan yawo Kam a jirgi, muma dai Allah yasa mu hau jirgin Nan, rike habar sa Baba yayi yace chap waya ga Iro a jirgi, ina hango kaina a cikin gajimare, aradu Ranar baxanyi bacci ba tsabar Dadi.


 " Dariya sosai Khabeer yayi, kana yace zaka hau jirgi kaima Baba insha Allah, 

   Daddy yana ciki kuwa,.


  " Ehh yana nan khabiru yanxun Nan ya rako, Malam Sadi.


  " Okay mlm Sadi yaxo gidan nan kenan.


  " Ehhhh yaxo, dan yanxun nan suka fita.


  Daxun nan dai ya fita ba yanxun Nan ba, da yanxun nan ne, aida  na samesa, Nima kaina na yi 20 minute anan.

    Bari na shiga ciki.


    " a fito lfy. Oh Khabiru sarkin gyaran zance,.

  Allah kasa wannan dan albarkan yayi silar hawana jirgi.

   Na ganni nayi fiffike a saman gajimare, aradu sai mun lula sama sai na sako kaina na leko naga tazarar dake tsakanin mu da kasa, ina ma na hango, Malam zakari ya'u ai ko da saina masa gwalo.



   Da sallama ya karasa falon nasu Momy Sarah ya samu hakince a falon ta daura kafa daya kan  daya tana tauna cingum.

   Momy Sarah kishiyar mahaifiyar Khabeer ce, wacce bata kaunar ganin ci gaban sa, mussaman ma, yanda taga Khabeer yafi danta KHALID tashen kudi.

  Yayin da su kuma yaran suke da matukar hadin kai, babu ruwan su, da cewa uwar su ba daya bace.


   " Ka rasawa khabeer yayi kusa da ita cikin girmamawa yace, barka da gida Momy Sarah, na same ku lfy.


  " Lfy lau Khabeer yaushe ka shigo kasar,.


   " Jiya da daddare na shigo kasar momy, naso zuwa da safe, sai kuma gajiya ta hanani fitowa.


  " Allah sarki to sannu da dawowa.


   " Tambayar ta mahaifiyar sa yayi, yace Momy Sarah momma fah, tana ciki ne ban ganta a falo ba.


   " Tana dakin Daddyn ku, ka shiga, daxun nan kuwa daman shima Daddyn naku yake maganar ka.


   Shikenan fana karasa.


   " Sanda Momy Sarah taga shigewar Khabeer.

   Sannan ta tabe bakin ta, tace kullum cigaba yake kara samu, abunda na tsana na ga kana samu kenan.


      " Da sallama ya karasa dakin Daddyn nasa sanda suka masa ixini sannan ya shiga, su uku ya samu da bakuwar da Daddy ya tsinta, a hanyar sa ta dawowa daga Bauchi bayan ya shigo cikin garin Gombe,  wacce tun sanda ya kawo ta gidan nasa bata magana sai dai Ido da kuma idan taga abu tana so sai tayi alamu da hanu a bata, yau kimanin shekara Hudu kenan da tsinto ta,  sosai Daddy yake mata magani Amma har yanxu babu wani sanji, suna Kiran ta da Mamy, har ta fahimci sunan da suke kiran ta dashi, suna cewa mamy zata dago Ido ta kalle su, amma magana kam babu.



  " Daddy ne yace khabiru yaushe ka dawo, jiya fa da safe na Kira ka, kace min kana Indonesia, yaushe kuma ka taso bamu da lbr.


  " Daddy kasan daman John mukaje kamawa shugaban masu safarar kwayoyi daga Nigeria zuwa Indonesia, so yaji lbrn ana neman sa ruwa a jallo, shine ya gudu Indonesia,.

    kafin muje munyi waya da jami'ain IPS dake can kasar sun taimaka mana sosai dan mun kamasa cikin sauki. shiyasa ma muka dawo da wuri.


  " Sannu da dawowa to, daxu Khalid yake cemin idan ya dawo daga Aiki zai biya gidan su Matar ka, ya dauko Mai sunana.


  " Ban sani ba ai Daddy har na aika Daniel ya dauko sa, amma Bari na kira wayan Daniel din nace ya bari kawai.


   " Hanu momma ta daga masa tace karka fara, ka bari Daniel din ya dauko sa, shima ai Khalid din ba daukosa zaiyi ba, Raina min Hankali kawai kuke yi, akan me jikokina zasu tashi a gidan, Alhaji Tanimu suma yaushe tarbiyar ta ishesu bare su bawa wani, tun farko sanda na hana ka Auren wannan yarinyar Zuhura. 

  Amma dake ku yaran yanxu idan kuna son abu idanun ku rufewa yake ku kafe kuki sauraron kowa, abinci ma wai sai kazo gidan Nan, kaci,.

   kai wannan ba abun kunya bane ma ace ka ajiye iyali amma baka da kwarya a gidan ka, daga yanxu na gaji da ciyar da Kato kamar ka, kaje kaima kaci abunda take ci, na kuma gayawa Momy sarahn naku, domin naga alamar itace mai daure maka gindi.


   " Shidai Khabeer hkr kawai yake bawa momma domin yasan duk abunda ta fada Gaskiya ne, babu za'ida a cikin zancen ta, shima kansa yanxu hkrn zama yake da Zuhura, ba wai dan yana jin dadin ta, ba.

    Kamo rigar sa yaji anyi ta baya, juyawa yayi, yaga ashe Mamy ce.

   Sunkuyawa  yayi yace, Mamy menene, kina son wani abune.


  " Alamu ta masa da hanu na ina junior.


  " Murmushi ya mata yace, yana zuwa yanxu Mamy, kina son ganin sane.


  " Da kayi ta masa alamun ehhh.


  " Yana zuwa yanxu to, kallon sa Khabeer ya mayar kan mahaifin sa, yace daddy, na fada maka, a dauki mamy a kaita India, domin su duba kwakwalwar ta, dan Gaskiya bana tunanin wannan abun sihiri ne, kamar yanda malaman nan suke fada maka, nafi dangata ciwon ta da matsalar kwakwalwa.


   " Kaga Khabeer babu wani matsalar kwakwalwa da yake damun wannan baiwar Allah, daxun nan zuwan mlm Sadi, yake cemin tabbas sihiri aka mata, kuma sirihin na karfa ne da garin su, kwai taji bata son zaman garin, kuma bayan haka sun dan hadata da rashin tuna abu da Kuma magana, a yanda mlm Sadi yake fada min, da za'a San garin nasu, acan ya kamata aje ayi bincike, domin gano abunda suka binne Mata, ko kuma a samu wanda ya sanda, hakan zai taimaka sosai.

  To kaga ni kuma ban san garin su ba Gaskiya, ina tunanin ma kamar daga wata rugar fulani, take,.


   " Ajiyar zuciya Khabeer ya sauke, yace to Daddy, yanxu meye solution, bai kamata ace taci gaba da zama a haka ba.


  " Babu wani solution Gaskiya sai dai muyi ta addu'a har Allah ya kawo mana mafita.


   " Momma ce tace Allah ya kawo mana mafita cikin sauki dan Gaskiya, baiwar Allah nan tana bani tausayi, duk yanda akayi tana da miji harda yara.


  " Hakan zai iya faruwa momma, Allah dai ya sauwaka mata wannan ciwon, bari naje gurin Momy Sarah ko zan samu Abunda zanci.


  " Harara momma ta aika masa, tace ai kaji kunya wlh, Matar ka tafi karfin ka,.


   " Murmushi Khabeer Yayi yace, tafi karfina kuma, Ni din.


   " Kaga shige ka bani waje, lusarin namiji.


  " Haba momma ki daina fadan...........


  " Bai karasa maganar ba momma ta tare sa tace karka kara min wata magana anan, 

   Idan ka tashi fita ka biya part din Hajiya ka dubata, bata jin Dadi.


  " Shikenan zan shiga, bari naje wajen Momy Sarah na.



   " Waya momy Sarah take da wata Abokiyar harkallata, kina jina Hajiya Binta, munyi waya da Alhaji Abbas, yace min wannan karon yara biyar suke bukata kuma Yan Mata, ya za'ayi mu samesu.


  " Daga can bangaren Hajiya Binta tace, Hajiya saratu wannan ai mai sauki ne, ko a kauye zamu samosu,.


  " Ajiyar zuciya Momy Sarah ta sauke tace, Alhamdulillah sai dai ba yanxu muke da bukatar yaran ba, kinsan wannan dan iskan yaron Khabeer sunje har Indonesia sun kamo mai gidan Alhaji Abbas wato John, yanxu haka shi kanshi Alhaji Abbas din baya Kasar Nan, bazai dawo ba sai komai ya lafa, but dole mu iya takun mu, Dan yaron nan shegene.

    Ki bari idan komai ya lafa zan miki magana.


   " Okay shikenan Hajiya Saratu sai na jiki din.


  " Maganar Khabeer taji a bayan ta yana cewa Momy Sarah.


   " A firgice ta juya, cikin inda inda tace, Khabeer yaushe ka kashigo dakin nan.


  " Kallon yanda Momy Sarah take hada zufa yayi yace, yanxu na shigo, lfy Momy Sarah kike hada zufa.


  " Saurin saita kanta tayi tace, lfy, zafine kawai yayi yawa.


   " Duk Airsing dake cikin dakin nan ga kuma fanka, tana aikin.


   " Fiskanta da Momy Sarah tayi Khabeer baiji zancen da sukeyi da Hajiya Binta bane ya sata kawar da zancen ta hanyar cewa, kaci abinci kuwa.


   " Abunda naxo nema kenan.


  " Okay muje daining table, sai kaci abincin Koh.

     Tare suka jera da Momy Sarah har daining suna Zama junior na shigowa falon da gudu.


   " Jikin Abban sa ya makale yace Abba yaushe ka dawo.


   " Shafa kansa yayi yace,jiya na dawo my son waya dauko ka Papa Khalid ne ko Uncle Daniel.


    " Uncle Daniel, Abba ina oyoyo Dina.


   " Kama kunnen sa yayi, yace junior Babu sannu da dawowa, sai oyoyo dinka kawai ka sani.


   " Dariya Momy Sarah tayi tace wama ya kalle tunda ya shigo idan ba kai dinba.


   " Juyowa junior yayi yace na ganki mana Sarah. Ke baxaki ban oyoyo ba shi Kuma Abba zai bani.


  Kama kunnen sa Khabeer yayi yace, kai junior ban hanaka cewa Momy Sarah, ba Sarah, bana ce kake kiran ta yanda kaji muna kiran ta, ba.



  " A'a Khabeer barshi yaro ne fah idan ya girma baxai fada ba,.




    ************************

      

  Rugar Ardo Boyi


  A hanyar Su NASREEN ne na dawowa daga Rafi suka hadu, jungudo, shida abokansa, kowa Yana tsoron jungudo a wannan Rugar, domin kuwa yaron ta caccan dan iska ne, baya ganin kowa da kima da mutunci, gashi kuma Allah ya daurawa jungudo soyayyar Naseen.


   " Cikin muryar Yan iskan mashaya, jungudo yace, kai Indo kuxo nan keda kawar ki.


   " Da sauri Indo ta kamo Hanun NASREEN tace, yau kuma mun shiga uku, NASREEN, jungudo ya tare Mana hanya.


  " Bamu shiga uku ba Indo, baxan sauraresa ba, mu tafi kawai,.


  Mu tafi fah, kikace NASREEN kin manta Rashin imani irin na jungudo ne, kixo muje muji mai zaice.


   " Kinga wlh Babu inda zanje Ni, bazan tsaya na saurari zancen mutum marar kima irin jungudo ba, tunda kina tsoron sa, kije ke ni kinga tafiya ta.

    Gaba tayi tabar indo cikin tsoro.

   

    " tare gaban NASREEN su jungudo sukayi, cikin izza yake cewa, haba Nasreen meyasa kike min haka ne, ko dan kinga ina sonki, kixo muje wajen bishiyar mainar chan mudanyi zance, inyaso sai ki shige gidan.


    " Babu wani zance da zanyi dakai jungudo kaga ka bani hanya na shige  naje nakai Aiken da aka min.


   " Acikin abokan nasu ne daya yace Oga idan bazata jeba ka bari kawai na dauketa na kaima ka ita.


   " Karka kuskura Hanun ka ya taba masoyiya ta, idan kuma kayi wannan kuskuren to wlh zakayi asarar Hanun ka, mu basu waje su shige,.


  Tahowa indo tayi, suka wuce, lanbun mlm sale suka biya ta karbo ayaba da lemo, sannan suka karaso gida.

   A kofar gidan ta samu Nuruddeen yana kwance a kasa har bacci ya fara diban sa, tashin sa tayi, ta basa ledar Hanun ta, tace gashi Nuruddeen kaje gidan Goggo kici, kaga idan ka shiga dashi cikin gidan Nan MAMA zata kwace ta bawa su, Buba.


    " To Adda Nasreen ke din baxaki ci bane,.


  Karka damu dani Nuruddeen kaje dai kaci ni zan jira abincin dare, ka ragewa Nabiya idan ta dawo zata zo gun goggon ta karba, maxa kayi sauri kafin wani ya fito ya gani.


   " Da sauri Nuruddeen ya karfi ledar yayi wajen goggo kakar su mahaifiyar Baban su.


   " Shiga cikin gidan su Nasreen tayi, a randar kasar dake tsakar gida taje ta juye ruwan.


   A wunin Ranar sanda Nasreen tayiwa Mama sau hudun Nan.


  " Da la'asar mama ta bawa Nasreen wankin kayan ta dana yaranta, babu musu kuwa ta karba ta hau wankin.


  " Da sallama Nabiya ta shigo gidan dauke da kayan talle, zuwa tayi ta mikawa Mama kudin tallen dubu da biyar ta bata, tace Mama ina abinci na,


   Bata kulata ba sanda ta kirga kudin sannan ta juyo tace, jakar uba, ke Nabiya wannan ne kudin wake da shinkafar tawa, to wlh baki isa ba, barauniyar banxa, kayana zai kai na dubu biyu, dan haka wlh baxan yi asara ba, dole ki nemo min kudina, ko kunya bakiji ba wai na baki abinci, bayan shinkafa ta da kikaje kika cinye, to baxan bayar ba.



      " Wlh Mama banci abincin kiba a haka mafa mama shinkafar nan tsadar ta nayi, ni naga ma ai tayi kudi.


  " A gidan uban waye tayi kudi to wlh sai kin nemomin cikon dari biyar Dita, ko kuma wlh yau na lahira sai ya fiki jin Dadi.


   " To yanxu Mama a ina nasan zanje na nemo Miki dari biyar.


   " A ko ina ma danni kudina na sani idan kinga dama kiyi sata ki kawo min kudi na, idanma iskanci zakiyi, kije kiyi ki kawo min kudina nidai kudina na sani,.




   More

        Comment


More 

       Typing



Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


      (Ummu Nasmah)

[11/6, 5:56 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

          ⛏⛏⛏⛏

    SARA DA SASSAKA                                     

       (Baya hana gamji)

                   Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


  Story

        And

   Writing

            Rasheedat Usman


          ( Ummu Nasmah )


🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻


{ United we stand and succeed ; Our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's}


htpps://www.facebook.com/kainuwawritersassociation


    

 بسم الله الرحمن الرحيم


  Deducted

         To

My kawalliya kawar Arziki, momyn Ahlan Allah dai ya kawo kudi na hau dake katuwar waya. 

   Ko fans dinki na GUDU AJEJI zasu samu su huce takaici.

  

  Amma tunda ban samu na saya miki wayar ba, to ga kyautar page guda kiyi yadda kike so dashi, 😄



P•••••••••••••5️⃣ to 6️⃣


   " Ni fah Mama babu inda zanje, na samo miki, kudi, ban saba sata da iskanci ba, dan haka kuma yau baxan fara, ba Na gaji !! Na gaji !! Na gaji da abunda kike min acikin gidan nan, Mama komai aka miki aduniya babu gwanin ta sai kyara da tsangwama, tun safe na fita tallen nan, ban dawo ba, sai yanxu, babu abunda nasa a ciki na tun kokon safe, shine har yanxu a ciki na, na dawo kuma yanxu Mama tsabar rashin tausayi kice baxaki bani abinci ba, sai dare, Kuma kice na koma naje na nemo miki, wata dari biyar wacce bansan da ita ba.

  Babu inda zanje Ni.


    " Zaro ido😳 Mama tayi tace ni kike gayawa magana Nabiya, yaushe kikayi wannan girman da zan fada ki fada, eh lallai kam kin gada a wajen uwa, baki dauko a kasa ba, da kike cewa baxaki yi iskanci ba, uwar ki kam ai ta tafi yin iskanci, wama ya sani ko wani katon ya kama mata daki, ta zama dadiron sa.


  " Nasreen dake wanki tana jin duk abunda Mama take fada, ne ta runtse idon ta, a duniya ta tsani Mama take danganta mahaifiyar su, da kalmar karuwa, ta gwammace gara ace ruwan zafi ta watsa mata a jikin ta, Akan ta aibata mata, mahaifiyar su.

  Tana cikin wannan yanayin ne taji muryar Nabiya na cewa.


    " Kinga Mama nifa duk abunda zaki fada akan AMMI ki fada bai dameni ba, saboda idan ma yawon karuncin da kike fada taje, ai bamu muka turata ba, da kullum idan kin tashi kike mana gori, kuma wlh yau ko kashe ni zakiyi, ba inda zanje, na nemo miki dari biyar sai dai ki kashe ni,.


   " Saukar mari taji a fiskar ta, nuna ta Nasreen tayi da yatsa 👉🏻 tace Ammi ba karuwanci ta tafi ba, babu wanda yasan abunda ya fitar da AMMI daga cikin Rugar nan sai Allahn da ya halicce mu, cikin zubar da hawaye tace, koda kowa a cikin rugar nan ya zargi AMMI ke bai kamata ki zarge ta ba, AMMI baxata bar kauyen Nan haka kawai ba, tasan tana da yara kuma tana sonsu sosai, tana da miji Kuma tana sonsa, tana da yan uwa, shin ki gaya min tayaya wannan baiwar Allahn zata tsallake wadannan dangin nata, ta tafi wata uwa duniya bana tunanin haka, tabbas ba a Halin lfy tabar rugar nan ba.


  " Kada kanta Nabiya tayi tace, kar soyayyar AMMI ta rufe miki ido Adda Nasreen har ki kasa gane laifin ta, idan har AMMI tana sanmu meyasa ta tafi ta barmu, kodan Nuruddeen bai kamata Ammi ta tsallake mu ta tafi ba, ni ban Zargi AMMI ba, amma tabbas ina da tabon yasar damu da tayi, ta shiga duniya, ki gaya min Adda Nasreen idan har AMMI tana nan, wani abun Mama bazata mana Shiba,.......


   " Ruwa mama ta debo mai sanyin gaske, ta sheka musu a jikin su.


   " Da sauri suka juyo suna kallon MAMA,.


  " Kinsan Allah yau Nabiya babu mai hanani cin ubanki a gidan nan, iccen maina Ta dauko ta hau zubawa Nabiya a jikin ta, tana cewa wlh idan har baxi fita ki kawo min cikon dari biyar dina ba, sai na miki dukan da baxaki iya tashi ba.


   " Duk dukan da Mama take yiwa Nabiya, hakan baisa bakin ta ya mutu ba, sai ma cewa take, sai dai kuma ki kashe ni wlh Amma babu inda zani na nemo miki kudin ki.


  " Haushi ne ya ishi mama na irin yanda, Nabiya ta Raina ta har take samun damar mayar mata da zance, hada Nabiya da kango Mama tayi tace bari na kashe ki, na huta, Dan ubanki.


   " Idon Nabiya sun firfito waje, domin ba shakar wasa Mama ta mata ba.


  " Da gudu Nasreen ta karaso wajen Mama tace, kiyi hkr Mama ki saketa zan biya ki dari biyar din.


   " Kallon baki da Hankali MAMA tayiwa Nasreen tace, a gidan uban waye zaki samo kudin da zaki biya Ni.


   " Kunce bakin zanin ta Nasreen tayi, ta dauko wata dunkulalliyar dubu daya, ta mikawa Mama gashi ki sake ta Dan Allah.


   " Tan kade Nabiya gefe tayi tace, ke kuma munafuka na dawo kanki, A ina kika samo kudi har dubu daya.


 " Kudin makarantar Nuruddeen ne Ranar da Baba zai tafi binni ya bani, yace naje na biya masa Ranar litinin.


   " Tabe bakin ta Mama tayi tace munafukan banxa daga ku har uban naku, wato tsabar munafurci, shine da na tambaye sa kudin makarantar Buba yace min baida shi, zai dawo ya same Ni.


   " Nabiya ce tace, sai ki bamu sanjin mu ai.


   " Baxan bayar ba kixo ki kwata marar kunyar karya.


   " Kamo Hanun Nabiya Nasreen tayi suka shige dakin mahaifiyar su wanda ya zama nasu a Yanxu, a bakin katifa suka zauna, Nasreen ce ta fara magana cikin sanyin murya.


   " Banji dadin Abunda kikayi akan AMMI ba Nabiya yau koda ace da gaske Ammi karuwancin ta tafi, a tunanina ai ke mai rufa mata Asiri ne.


   " Adda Nasreen yau kimanin shekara Hudu ina cikin rudani, shin Abunda ake fada akan AMMI Gaskiya, idan kuma har ba haka bane ina Ammi taje, har tsawon wannan shekarun, na tabbata da AMMI tana gidan nan wani cin mutuncin Mama baxata Mana Shiba, amma ke kullum kina boye laifin AMMI bakya so a fada, kuma dole a fadi laifin ta, tunda ta tafi ta bar Mana abun kunya.


    " Nabiya baki san AMMI ba kamar yadda ni nasan ta, na fiki sanin waye AMMI, Nabiya bakya jin furucin da mama take Akan AMMI, takan yawan cewa sai tayi sanadiyar shigar mu duniya kamar yanda tayi sanadin shigar uwar mu duniya, hakan yana nuna min cewa tabbas akwai Hanun MAMA a barin AMMI gidan nan.


  " Hmm Bana tunanin haka Adda Nasreen, mu bar maganar kawai,.


 " Shikenan yanxu ki tashi kije gidan Goggo akwai kayan iccen dana karbo a gun mlm sale kije ki karba Nuruddeen yana chan.


   " To na Gode Adda kece kika maye Mana gurbin mahaifiyar mu, kina iya shiga ko wani irin wahala a kanmu, yanxu Adda Nasreen kudin makarantar Nuruddeen da kika bawa Mama, a ina zamu samu mu biya, kinsan dai baxa su barshi Yayi jarabawa ba, muddun bamu biya kudin nan ba.

  Kuma kinsan ba lallai bane Baba ya dawo nan kusa.


  " Shuru Nasreen tayi, kafin ta dago idon ta ta kalli Nabiya, tace karki damu yar uwata, Allah zai mana mafita, insha Allah Nuruddeen zaiyi jarabawar Nan.


  " Muryar yar gwal sukaji tana cewa, lallai kam kun iya munafurci yanxu MAMAn kuke zagi, har da wani cemata muguwa chap kwalawa Mama kira tayi tace Mama kixo ana zagin ki.


   " Bude bakin ta Nasreen tayi tana kallon ikon Allah, a zuciyar ta take cewa ko yaushe muka zagi Mama kuma oho.


   " Ko kafin Nasreen ta dawo daga cikin tunanin ta, Nabiya tayi charap tace, " mun zageta Idan tazo ta kashe mu,.


   " Nasreen ce tayi saurin rufewa Nabiya baki, tace meye kiyi shuru mana,.


  " Bige hanun ta Nabiya tayi tace, baxan yi shurun ba, baxan iya hakurin kiba, domin ke hakurin ki yayi yawa, gidan nan zan bari, zan koma wajen goggo da zama, baxan iya bakin cikin gidan nan ba.


   " Kinga Nabiya ki tafi kafin mama taxo wajen Nan, gara ni tamin duk abunda zata min, amma bana so ta tabaki.


  " Juyawa Nabiya tayi sai gidan Goggo da hucin ta ta shiga cikin gidan, goggo tana zaune tana watsawa kajin ta hatsi yayin da Nuruddeen yake gefen ta, yana cin tuwon da goggo ta basa, zama kusa da goggo tayi ta fashe da kuka.


    " Kallon ta goggo tayi tace, ke kukan me kike haka, ya zaki shigo min cikin gida kina kuka, meya faru.


   " Cikin kuka Nabiya tace goggo zamu mutu yunwa zata kashe mu goggo, ba'a bamu abinci, gashi Mama tace muddun yau na kwana a cikin gidan ta, sai ta kashe ni.


   " Mikewa tsaye goggo tayi tace ba'a baku abinci, a gidan uban naku, sannan kuma zata kashe ki, ehh lallai dan zaki ya girma, Dole, Salame ne take muku wannan tsiyar, haba shiyasa Mana, naga yaron nan Nura ya shigo min gidan nan da ayaba yana cinta da sauri har hanun sa na rawa, ashe duk sharrin Salame ce tsinanniya zata kashe min jikoki da yunwa, kinga Nabiya share hawayen ki dauko min mayafi na maxa muje chan gidan naku, zanci uban Salame yau.


   " Da sauri Nabiya ta dauko wa goggo mayafin ta, dan tasan yau Mama ta banu a hanun goggo.


  " Kallon Nuruddeen goggo tayi tace kai Nura ka zauna kayi jirana, ina dawowa yanxu.


    " A hanyar su goggo ta tafiya ne, taci karo dasu jungudo suna ta hura sigari.


  " Nabiya ce ta taba goggo tace goggo kalli dan gidan mai gari jungudo yana hura miki karar sugari a kofar gida.


   " Ina yake dan kan uwar sa Hajara, kofar gidan nawa ne ya zama gun shan sigari.


    "  Ganin goggo da jungudo yayi ne, yayi saurin take sigarin a kasa.


   " Harara goggo ta balla masa, taxo har gaban sa, tace, dakko kayan ka kasha, dan banxa tacaccen marar kunya, kai dai kayi Asara wlh, dan Albasa batayi halin ruwa ba, wlh, iyayen ka kam dai mutanen kirki ne,.


   " Sunkuyar da kansa yayi yace, haba goggo meyasa kike haka, wannan yawa ne wlh, kina dizgani a gaban Abokaina.


   " Allah tacaccen dan iska, to tashi ka dake ni tunda ka girma, dan banxa yaushe ma aka maka kaciya, kuma wlh kafin na dawo ku bace daga wajen nan, idan kuma na dawo na same ku, kasan da wanda zan hada ka.

     Ke kuma Nabiya shige muje.


  " Hararar Nabiya jungudo yayi, yace munafuka, zamu hadu, sai na karya ki.


    " Juyowa goggo tayi tace, me kake cewa.


   " Bada ke nake ba.


   " da masifa Goggo ta shiga cikin gidan, Mama tana tsaye tana zagin Nasreen ita da yarta yar gwal,. Muryar goggo suka ji tana cewa.


   " Akwai babbar munafukar da ta wuce kine Salame,..


    " Da sauri Mama ta juyo tace, Sannu da xuwa goggo.


   " Cikin fada goggo tace sannu da zuwan gidan ku, ina ruwan ki da zuwa na, da har zaki min sannu, to bana bukatar sannu da zuwan ki.


   " Shuru Mama tayi domin kuwa tana tsoron Goggo kamar yunwar cikin ta.


    " Cigaba da magana goggo tayi tace, naxo naji dalilin daya sa bakya bawa yaran nan abinci, fada min meyasa.


  " Inda inda Mama ta fara, amm amm daman daman.


   " Katse ta goggo tayi tace yimin shuru munafuka daga jin maganar ki babu alamun Gaskiya a tare dake, kallon Nasreen tayi tace shiga madafin nan ki duba ko wani irin Abinci kika samu ki fito min dashi,.


   " Cikin tsoro Nasreen tace, goggo babu abinci a madafin, kuma Mama bata hana mu abinci ba, yau ba'a samu ruwa bane shiyasa batayi abinci ba,..


   " Salati Nabiya ta deba tace Adda Nasreen yaushe kika fara karya, Aradun Allah Goggo Mama tayi Abinci, daxu da safe kafin na fita talle har zabin Baba naga tasa an kama an yanka Mata.


   " Allah ya miki Albarka Nabiya, shiga kinji kije ki debo min duk abunda kika gani a madafin.


   " Kada kanta tayi tace an gama Goggo yanxu kuwa zan kawo miki.


  " Ita ko Nasreen tana gefe jikin ta sai rawa yake, tasan yau duk abunda goggo tayi wa mama sai ta rama a kansu, kuma duk abunda ya faru Nabiya ce taja musu.


   " Rankwashin Nasreen goggo tayi tace, shegiya farar kura uwar tsoro, watk kina tsoron zakin naki karta kashe ki koh, bayan na tafi.


    " Shuru Nasreen tayi bata kula Goggo ba, domin haushin Goggo take ji, tunda ta jawo Mata bala'i yau agun mama..


  Fitowa Nabiya tayi dauke da kwanon zabin da mama ta soya tace gashi Goggo Naman zabin danki ne da aka yanka.


   " Karba Goggo tayi tace, yawwa sannu yar albarka, kallon ta ta mayar kan Nasreen tace, ke kuma uwar yan tsoro. Sai kizo mu tafi gida na, ku kwana acan, baxama ku dawo ba har sai uban naku ya dawo daga binni.

   Ke kuma Salame ga gidan sun bar Miki, kiyi kwadon sa ki cinye, sannan taja su Nasreen tayi gidan ta dasu.


   " Ita ko mama babu abunda jikin ta yake sai tsuma, yau dai a ranta ta dauki aniyar maganin goggo a cikin rugar nan domin kuwa ita kadaice matsalar ta, a fili mama tace ina dawowa gare BOKA RABGAS yanda kamin maganin MAIMUNA nasan wannan tsohuwar ma baxata gagare ka ba.



   *************************


   Khabeer bai shigo gidan sa ba, sai wajen karfe goma na dare, dakin Zuhura ya wuce darect, ya sameta ta hada kanta da gwiwwa tayi shuru, zama Khabeer yayi kusa da ita tare da dago kanta, yace.


    " Zuhura wai abunda ya faru da safe ne bai shige ba har yanxu.


  " Kin kulasa Zuhura tayi.


   " Janyota jikin sa yayi yace please Zuhura kimin magana bana son ganin bacin ranki.


   " Kifa kanta tayi a kirjin sa tace kana son bacin raina Abban junior tunda har ka iya marina akan dan karamin kuskure, na fahimci yanxu baka Sona ka daina Sona shiyasa har kake min ihu a kayi na, ta karasa maganar ne cikin kuka.


    " Tayaya zan daina sonki Zuhura bayan kece farin cikin Rayuwata, ina sonki fiye da yanda nake son kaina, baxan kuma daina sonki ba har Karshen rayuwata, zan zauna dake a kowani Hali kike ciki, bana son kina furta kalmar cewa bana sonki.

    Ko fadan da na miki daxu da kuma Marin da na Miki na miki shine a cikin bacin rai, kiyi hkr ki sake ranki, idan kuma Marin da na miki ne ya bata miki rai, to ga fiska ta ki Rama.


   " Dago idanun ta dake tsiyayar hawaye tayi tace, promise baxaka kara min ihu ba.


  " Murmushi Khabeer Yayi yace promise Habibty na baxan sake ba, shikenan kukan ya kare haka.


   " Dariya tayi, tare da kokarin sa Hanun ta akan fiskar ta da niyan goge hawayenta.

       Rike hanun nata Khabeer yayi yasa harshen sa ya lashe hawayen nata tass, sannan yace ina nan Hanun ki bazaiyi aiki ba, 

  Kinci Abinci kuwa.


   " Taya zanci Abinci bayan Babu zuciyata a tare Dani.


   " Murmushi Khabeer Yayi yace, tashi muje ko ruwan tea kisha tunda zuciyar ki ya dawo kuma har ya nemi afuwar ki, ai sai kuma a taimakawa ciki a basa hakinsa.


   " Tsakanin mata da miji sai Allah, gadai Khabeer da Zuhura kamar basuyi fada ba.

   Bayan Zuhura tasha tea ne, sukayi dakin Khabeer, sanda ta tabbatar da Khabeer ya shiga wanka sannan itama tayi nata dakin domin shirin bacci.


  " Daure ya fito da towel a kugun sa yayin da yake rike da daya a hanun sa yana tsane ruwan jikin sa, dressing merro ya nufa mai ya shafawa jikin sa, tare da daukar turare ya shiga fesawa, ya fesa sunyi kala biyar a fatar sa, want irin kamshi ne mai dadin shaka yake fita daga jikin sa,.

     Drower ya bude da niyan dauko rigar bacci, sai yaji kwanciyar mutum a jikin sa, yasan baxai wuce Zuhura ba, juyo da ita yayi ta fiskance shi, 

  Tsayawa yayi yana kare mata kallo, tayi kyau sosai cikin shigar wata yar karamar sleeping dress, mai kalar yelow, rigar da ita da babu daya suke, domin kuwa komai na jikin mutum a bayyane yake, rigar irin mai botton din nan ne, Kuma ya karta gwiwwa, sai dan karamin pant da ta saka, ga wani tashin kamshin hunra da takeyi, lashe lips dinsa Khabeer yayi yanajin wani irin feeling na taso masa, 


  " Janye towel din dake kugun sa, tayi, cikin kissa ta shafo 🍌 sa dawo da hanun ta tayi kasan marar sa, tana shafawa a hankali, wani irin mika Khabeer yakeyi, ganin hakan da Zuhura tayi ne yasa ta tankada sa saman bed, ita da kanta ta balle button din rigar ta wurgar da ita gefe a hankali shima pant din tayi jifa dashi, fadowa jikin sa tayi cikin kissa ta ke magana a cikin kunnen sa, Habibina, wannan Daren naka ne gaba ki daya sai yacce kaga dama ka kyale ni.


  " Kasa magana Khabeer yayi sai ma birkito ta da yayi tayi kasa ya dawo saman ta, a hankali yasa bakin sa a nata, cikin kwarewa yake sarrafa harshen ta, yayin da hanun sa yake saman girjin ta yana shafo su a hankali, sanda yaxo dai dai saman nipple dinta sannan ya murxa shi, sake bakin nata yayi ya dawo dashi saman kirjin ta.




   Nima Rasheedat Ganin hakan da Nayi yasa nace nima bari na ajiye alkalami na nayi gaba sai kuma da safe.



More

    Comment


More

    Typing




Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻



  (Ummu Nasmah)

[11/7, 5:30 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story

    And

Writing

      Rasheedat Usman

     (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم



  Deducted

       To

   Khadija musa isah ina mungun jin dadin yanda kike sharhi Akan wannan book din, dan haka ga kyautar page.




P••••••••••••7️⃣ to 8️⃣


Basu tsagaitawa kansu ba sai wajen karfe biyu na dare, tare sukayi wankan tsarki, sannan ne Zuhura ta dauki kayan ta, ta mayar jikin ta, kwanciya tayi a gajiye tare da jawo bargo.


   " Shiko Khabeer alwala yayi ya tayar da sallah, domin wannan Al'adarsa ne, yawan yin sallar dare, bai kwanta ba sai karfe uku da Rabi, itako Zuhura a lokacin baccin ta ya dade da yin nisa.


  Karfe 4:50 na asubar fari Khabeer ya tashi alwala ya fara daurowa, kafin yaxo ya fara kokarin tayar da Zuhura, dakyar ta tashi.

    Sanda yaga shigar ta tollet kafin ya fice zuwa massalaci yasan Halin Zuhura sarai ba karamin Aikin ta bane yana ficewa ta koma tayi kwanciyar ta, dan sallar ba wani damun ta yayi ba.


   Bayan an idar da sallah ne Khabeer ya dauki Alkur'ani a massalacin Sanda gari yayi haske sannan ya dawo gida, a dakin nasa ya sameta tayi sallah har ta mayar da baccin ta, tollet dinsa ya nufa, ya wanke kayan sa tas, sannan ya dawo cikin dakin da kansa Khabeer ya gyara dakin sa, bed din da take kwance ne kawai bai gyara ba, sanda ya tabbatar da ya kintsa dakin nasa, sannan ya bita gadon tare da janyo ta jikin sa, A haka bacci ya daukesa yana Rungume da Zuhura a jikin sa.


  " Zuhura ta riga Khabeer tashi, dakin ta ta nufa Domin kintsa jikin ta, a falo taci Karo da Asabe tana gyaran falon.


   " Risinawa Asabe tayi tace barka da fitowa ummin junior, da fatan kin tashi lfy.


   " A takaice Zuhura tace lfy, ina fatan kun gama hada breakfast.


  " Ehh mun gama hadawa tun daxu, harma mun kai daining.


  " Okay kira min karima taxo, ta gyara min daki,.

  Idan kin gama gyaran falon ki tabbatar da kinje kinyi wanka, dan naji kamar kina tashin tsami.


  " Ran Asabe yayi bala'in sosuwa, amma haka ta daure tace to ummin junior, zanyi insha Allah.


  Zuhura bata fi 30 minute ba ta fito sanye da wasu riga teshart da wondon jeans rigar  red color ne an rubuta pretty da manyan bakake a jikin rigar, daining ta nufa, bude food plast din tayi, chiefs ta gani, kwalawa Asabe kira tayi.


   " Da sauri Asabe taxo tace gani ummin junior.


 " Kallon wulakanci tayiwa asabe sannan tace, akan wani dalilin Zaki soya min chiefs bayan shi naci jiya,.


   " Kiyi hkr cewar Asabe, naga kina sonsa ne, duk randa ba'ayi shiba sai kinyi fada, ban san yau bakya soba da baxan yiba.


  " Tsaki Zuhura taja, tace nidai na shiga uku da wannan bagidajiyar kauyen, kullum sai kin mini kuskure, sannan zaki zo kina sunkuyar min da kayi kina bani hkr,.


   " Ita dai Asabe hkr taci gaba da bawa Zuhura duk da tasan ba wani laifi da take mata, kawai dai cin mutunci ne irin na Zuhura.


   " A haka Khabeer ya fito ya same su, sanye yake da kananan kaya ash din wandon jeans da kuma yellow Riga, sai tashin kanshi yake, karasawa yayi, wajen nasu.


  " Da sauri Asabe ta rusuna tace barka da tashi Abban junior an tashi lfy.


  " murmushi dauke a fiskar sa yace lfy lau Asabe, meya hada ku da Aunty naki.


  " Cikin girmamawa Asabe take mayar wa Abban junior Abunda yake faruwa.


  " Murmushi yayi tare da cewa kiyi hakuri Asabe, kije ki Abunki kema kiyi breakfast din.


  " Godiya Asabe tayiwa Abban junior sannan ta wuce.


  " Zama yayi a kujerar daining din yana kallon yanda Zuhura take ta faman hada fiska.


  " Cikin sigar zolaya yace Hajiya Zuhura, hada fiskar me kuma ake, bayan ga farin cikin zuciyar ki, zaune a gaban ki.


  " Magana ta fara cikin fada fada tace, yanxu Abban junior Abunda kayi ka kyauta kenan.


  " Zaro Ido 😳 Khabeer yayi yace me kuma nayi.


  " Akan me zaka bawa yar aiki hkr, bayan ita baiwa ce, a garemu.


   " Dariya Khabeer Yayi yace daman har yanxu akwai bayi ne, ai banyi tunanin ana samun bayi ba, har yanxu, kada ma akwai bayin, to ita dai wannan ba siyan ta mukayi ba, ya kamata ki fahimci cewa ita ma fah Asabe mutum ce kamar ke, Babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda ya fi tsoron sa, maganar aiki da kike cewa tana miki kuskure, ai daman shi dan Adam Ajizi ne, 

   Duk abunda akace sai ka jira wani ya maka, to fah dole sai kayi hkr, kinga kamar ke, hkr ya kamaki dole, tunda komai sai an miki,.


  " Hmm Abban junior kenan yanxu dai ka gaya min magana cikin magana koh, tunda baxan yi aiki ba, na gamu da wulakanci, haka kake nufi kenan.


  " 🤷🏻‍♂ Nifa bance miki haka ba, maganar Gaskiya na fada miki, sai dai hausawa sunce, kurma shike gane karatun Bebe, kici abincin ki, nima fana shige gidan mu, naje nayi breakfast.


  " Yanxu Abban junior baxaka koyi cin abincin yan Aiki ba, sai dai kullum kake zuwa gidan ku kana cin abinci.


  " A gogon sa Khabeer ya kalla yace, ki bari idan na dawo zamuyi magana yanxu banda times, zan shige Office ta chan.


  " A dawo lfy ta masa, daga zaune,.


  " Tafiyan sa yayi daman shi bai saba da Zuhura ta rakasa ba duk sanda zai fita.


  

   ~~~~~~~~~~~~~~~


  Momy Sarah dake zaune a dakin ta ne ta dannawa Hajiya Hindatu Kira ringing biyu Hajiya Hindatu ta daga.


  Daga can Hajiya Hindatu tace Hello, Hajiya Saratu, lfy kira da wannan safiyar.


  " Sha daya fah yanxu, ai kinga gari ya waye, ya kk.


  " Normal meke happening, nasan idan munga kiran ki cikin biyu ne, ko an samu ko kuma ta baci, yanxu dai wannene daya.


  " Allah ya shirye ki, Hajiya Hindatu, wato har kun canfa ni ko.


  " Babu wani canfi abunda yake yawan faruwa ne.


  " To yanxu Alhaji Abbas ya kirani, yake shaida min, ya aiko da waddan nan kaya yana bukatar yanxu aje airport a karfa,.


   " Wasu kaya kenan Hajiya Saratu.


   " Cocaine mana maxa kije yanxu sai dai nasan muna da matsalar jami'an tsaro, dan Gaskiya yanda cocaine dinnan zai fita a cikin airport din nan akwai matsala Gaskiya, na kira layin wayan Hajiya Binta switch off.


   " Shuru Hajiya Hindatu tayi tana tunani, sai can tace, akwai matsala kam, amma mai zai hana mu nemi sagern Umar yaje ya fito mana dashi nasan shi babu wanda zai bincike sa, mussaman ma idan yana sanye da uniform.


  " Duk abunda kika ga zamu samu mafita kije kiyi kawai nidai burina kayan nan su fito daga airport din, kar dai a samu matsala, idan kin dauko ki ajiye a gidan ki, zanzo  zuwa dare.


   " Okay babu damuwa insha Allah zasu fito.


  Katse kiran Momy Sarah tayi sannan ta fice zuwa folon.


   " Momma da junior ta samu suna zaune yayin da Nana da fa'iza suke kokarin jera breakfast a saman daining,

  Fa'iza da Nana ya'yan momma ne da kuma najeeb.


 Itama Momy Sarah tana da  Khalid faty da Kuma Hasina.


   " Kusa da momma Momy Sarah ta zauna tace Maman Khabeer kasance war haka take Kiran Mama dashi.

   Keda wannan uban yan surutun kike zaune.


   " Dariya momma tayi tace, gashi nan kuwa ya cika min kunne da surutu kamar parrot.


   " Turo bakin sa junior yayi yace, momma nine kike kira like parrot, Koh.


   " Momy Sarah ce tace ehh kai akace like parrot ko karya akayi.


  " Cikin tsami tsamin muryar sa yace, ai dan Abba ya hanani cewa babba yayi karya ne, dana ce momma da SARAH sunyi karya.


   " Kamo kunnen sa momma tayi tace ja'iri marar kunya ai yanxun ma ka karya ta mu.


   " Kwace kunnen sa yayi daga hanun momma yace, kuma wlh idan Abba na yaxo sai ya rama min dukan kunnen na d kikayi, kema ya daki kunnen ki.


  " Dukan su dariya sukayi, Momy Sarah tace kuruci dangin Hauka,.


  Nana ce tace momma breakfast is ready.


  " Okay junior jeka kira Daddy kace an gama breakfast.


   " Da gudu junior yayi part din Daddy.


   Da sallama Khabeer ya shigo cikin gidan.

      Kusa da Momy Sarah ya zauna, gaishe dasu yayi cikin girmamawa.


   " Kannen nasa ne suka gaishe shi, kallon Nana yayi yace ina su Khadija


 " Nana ce tace suna daki wanka suke, amma Yanxu zasu fito, muyi breakfast.


  " Momy Sarah ce tace ya iyalin naka,


   " Tana lfy Momy Sarah, ina mamy bangan taba.


  " Tana cikin dakin ta cewar Momy Sarah.


  " Tashi Khabeer yayi ya nufi dakin da Mamy take kwana a ciki,.


  " Tana zaune Rike da wani photo wanda ya zama mata abun kallo a koda yaushe, hawaye ne kwance a saman fiskar ta, tun barowar ta gida da photon ta fito.

     Bata ji motsin mutum ba sai ji kawai tayi an dafa ta.


  " A raxane ta juyo yayin da ta sake photon a kasa, ganin Khabeer ne yasa tayi ajiyar zuciya.


   Idon Khabeer ne yakai kan photon da mamy ta yasar, hanun sa yasa ya dauko photon.


  Ni kaina Rasheedat da nake dauko muku wannan labarin sanda na yasar da biro na, dan ganin wadanda suke jikin photon Nan NASREEN ce tare da NABIYA sun Rungume juna suna dariya, da kayan fulani a jikin su.


  " Karewa photon kallo Khabeer yayi, alamun yayiwa mamy da hanu yace waye wadannan din.


  " Kallon sa kawai takeyi tana son ta masa magana Amma bakin ta yayi nauyi baxata iya maganar ba.


  " Fiskantar hakan da yayi ne, ya mata alamun ya'yan kine.


  " Kai ta daga masa, alamun ehh.


   " Ajiyar zuciya yayi yace kina son ki gansu ne.


  " Nan ma dai kan ta daga masa.


  " Yace to ki daina kukan zan nemo miki su insha Allah, na kawo miki su har cikin gidan Nan.


   " Nan ma dai kada masa kan tayi.


  " Da kansa yasa Hanun sa ya share mata hawayen nata.





Tir kashi tofa ko tayaya Khabeer zai iya ciki alkawarin da ya dauka wa mamy, a ina zaiga Su NASREEN.


 Kuci gaba da biyo ni domin jin yanda zata kasance.





  Yau nayi muku typing kadan kuyi hkr, abubuwa ne suka min yawa.



More

    Comment


More

   Typing



Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


(Ummu Nasmah)

[11/8, 3:48 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story

    And

Writing

      Rasheedat Usman

     (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم



  Deducted

       To

 Aunty Jamila wannan page din naki ne Aunty na sai yanda kikayi dashi.



  SANARWA

Idan ban manta ba kafin na fara typing na fada muku cewa baxan ke typing Ranar Asabar ba, saboda ina da school a wannan Ranar,.

     Ranar Lahadi ma, sai zuwa dare zanke turo muku.


  Akwai masu biyoni ta privete suna cewa na turo musu SARA DA SASSAKA ina roko gare ku dan Allah ku daina tambaya ta book ta private ku nema a group domin baxan iya turo muku ba, ina da abubuwa da yawa, ban hana cewa a biyo ni ta private mu gaisa ba, gaisuwa kam zamu gaisa amma dan Allah a daina tambaya ta book ta private.

   Wanda na batawa yaji haushi na yayi hakuri🙏🏻



P••••••••••••9️⃣ to 1️⃣0️⃣


" Mamy zan tafi da pic dinnan zanje nayi copy nasa gobe zan dawo miki da wannan din.


 " Kada kanta Mamy tayi alamun ta yadda.


 " Yace tashin mamy muje yi breakfast kinji.


  " Mikewa mamy tayi suka jera tare da Khabeer har falo, isar su falon sun tarar kowa ya hallara a daining din,.


   " Sanda Khabeer yajawa mamy kujera ta zauna tukkuna sannan ne shima ya samu wajen Zama.


  " Good morning Daddy, cewar Khabeer.


  " Morning, khabiru ya Aiki naku, ina fatan komai normal.


  " Alhamdulillah Daddy tunda na dawo ma, ban leka office din ba, yau nake son zuwa idan na tashi daga Nan.


  " Allah ya taimaka ya kare ku daga sharrin makiya, domin Aikin nan naku yana da hatsari,


  " Ameen Daddy, kullum muna ganin Alkairin Adu'ar ku gare mu babu abunda zamuce a gare sai Allah ya saka muku da alkairi.


  " Momma ce ta umurci Nana da tayi seving din kowa.


   " Dumamen Tuwon shinkafa miyar yakuwa Nana ta sawa Daddy dasu momma, kular soyayyen dankali yasha kwai, Nana ta bude da niyar sawa Khabeer, dakatar da ita yayi ta hanyar cewa ta samasa tuwo, shi yake bukata.


  " Tuwon ta samasa ta tura masa gaban sa tare da tea mai kauri.


   " Suna tsaka da breakfast din ne, Khalid ya shigo cikin gidan da sallamar sa,.


   " Nesa dasu ya zauna Yana jiran su gama breakfast din.


   " Daga daining momma tace, Khalid bazaka zo kayi breakfast din bane.


  " Dariya Khalid yayi yace, momma yaushe Rabona da nayi breakfast a cikin gidan nan, ai sai su wa'ie wadanda ba'a girka musu a cikin gidan su,.


  " Harara Khabeer ya aikawa Khalid, sannan ya kawar da kansa gefe, yasan magana Khalid yake nema dashi, kuma baxai samu ba.


  Momma ce tace, fada masa dai dan uwan tuzuru, mutum yana da mata amma kullum sai yaxo gida yaci abinci Abun kunya.


   " Dariya Khalid ya kara shekewa da ita, yace momma, nace ya kara Aure yaki, ya zauna da lusarar Mac.........


  " Daddy ne ya katse masa maganar tasa yace ya isa haka khalidu, bana son yawan gutsiri tsome, ina ruwan ku da sha'anin gidan sa,.


   " Shuru khalid yayi yaci gaba da danna wayar sa,


   " Bayan sun gama breakfast din ne Khabeer ya dawo kusa da dan uwansa, yace wai meyasa jiya nata kiran layin wayan ka baya tafiya,.


   " Ina ga matsalar network ne, dan jiya wayana a kunne yake, true out ban kashe ta ba,

   Ya hanya, Ranar da ka kiran kace min yanxu jaku jirgin ku zai tashe, wlh naso naxo na tare ka a Airport, sai kuma wasu sabgogin suka dauke ni.


  " Babu damuwa, jiya Hashim ya kira ni mun fara magana dashi, Akan kayan super market din nan, yana gaya min wata maganar da hankali bazai dauka ba, wai kaya sunyi low, sannan kudin da suke kasa baxasu Isa a zuba wasu kayan ba, dana bincike sa, sai yake fada min cewa kazo ka karfi kudi kimanin 4 millions.


   " Ehh Bros naje na karbi 4 millions a hanun Hashim, saboda ina bukatar shi.


   " Amma Khalid me kayi da wadannan kudade bayan super market din ma baka zama, na rasa yaushe zakayi hankali khalid, ka fada min me kayi da wadannan kudade.


   " Haba Bros 4 millions ne fa kawai na karba, kake ta min binciken.


   " 4 millions ba kudi bane da baxan bincike ka ba, arzikin wani kenan, wani su din ma baida su, ka fada min ina ka kaimin kudi.


    " Motar da ka siya min na sayar da ita, shine na karbi wasu kudin a Hanun Hashim na cikata na sanja wata.


  " Hmm duka duka yaushe na saya maka waccar motar da har zaka sanja ta, khalid ka taimaki rayuwar ka, ka dinga zaman super market din nan, saboda rayuwar ka, ta inganta fa na bude, babu wata ribar da nake dauka a cikin super market din nan, nace ma duk ribar naka ne, Amma wai bai isheka ba, sai ka shiga cikin kudina, ka zauna kana bawa matan banxa, kudina kana shaye shaye da wasu, Gaskiya baxan iya ba, tura ta fara kaini zuwa bango, tunda kace baxaka yi karatu ba, zaman super market din ma kace baxa kayi ba, to zan rufe super market din, kowa ma ya huta.


   " Amma Bros..........


  " Katse sa yayi yace enough khalid, bana son jin wata magana daga bakin ka, Allah ya gani, ba irin gatan da ban maka ba, ganin yawan rikicin da kuke da Daddy akan daukar masa kudi da kake yi, yasa na bude maka wannan super market din, amma duk da haka ka kasa yin hankali.


  " Momy Sarah da suke zaune a wajen ne, ita da momma da su Nana tana jin zafin Abunda Khabeer yake yiwa danta, a zuciyar  ta tsinewa Khabeer yafi sau hamsin,.


   " Momma ce tace, ya isa haka Khabeer, ba dan uwan ka bane, meye laifi dan ya karfi kudin ka yana gadara dana yayan sane, ya sanja mota, yaje ya dauki na wani Mana, kar na sake jin maganar nan, kaje ka bawa Hashim din, wasu kudin ya kawo kayan.


  " But amma momma a haka zamu zubawa khalid ido yana abunda yaga dama, momma karki manta da cewa khalid yana da mata fah kuma ciki gare ta, a hakan za'a barshi ya tara iyalai ba tare da yasan zafin nema ba.........

 Ringing din wayar sane ta katse masa maganar da yake, 


  Daga wayar yayi CP yagani rubuce a screen din wayar.

    Da sauri ya danna wayar tare da karata a kunnen sa, kamewa yayi kamar wanda yake gaban CP.


   " Daga can bangaren CP yace wa Khabeer maxa yanxu kasa jami'an tsaro su kewaye Airport, an kawo mana rohoton cewa, akwai wani dauke da cocaine a cikin Airport din.


   " Da karfi Khabeer yace, cocaine sir a cikin Airport na garin nan, jirgin wacce kasa ce sukayi wannan gangancin da har za'a shiga da cocaine basu yi checking ba.


   " Da sauri momy Sarah ta zabura ta miki tace What.



*************************


 Rugar Ardo Boyi


  Tsugunne na hango Mama gaban wani Katon mutum baki wuluk mummuna. Idanun sa jajaye yayin da bakin sa kuma idan ya bude sai kayi Amai.


  " Kaji matsala ta boka RABGAS bani da matsalar da ta wuce ta wannan tsohuwar da wannan shegiyar yarinyar mai kama da tsitaka, wato Nabiya, so nake dukan su a kashe min bakin su, yanda duk abunda nace Babu mai iya minimum musu,.


  " Wata irin dariya marar dadin sauraro BOKA RABGAS yayi, yace kinzo inda za'a miki maganin matsalar ki, wannan karon ba jikin ki muke bukata ba, Bakin kadangare muke so, tare da bakar hawainiya, idan kin kawo su, bukatar ki ta biya.


    " Boka bansan inda zan samo bakin kadangare da bakar hawainiya ba, sai dai ko zaka taimaka min, sai na bada kudi ko Nawa ne, aljanu su samo.


   Dariya BOKA RABGAS ya sake yace sai ni boka rabgas mai rundunar shaidanun Aljanu, sai kuma ya murtuke fiskar sa marar kyan gani yace, saboda kene kawai Aljanu na zasu miki wannan Aikin, kije ki kawo kudi dubu 30 da kuma Bakin bunsuru wanda za'a yankawa aljani Sharshar yasha domin shine wanda zai miki wannan Aikin.


  " Kirari Mama tayiwa bokan tace zata je tasa gonar ta na gado a kasuwa zata kawo kudin sannan ta tashi ta fita da baya da baya.


    " Da Rana bayan su Nasreen sun gama cin abincin Ne , ta tashi Nuruddeen yaje yayi wanka Shirin makarantar boko wacce ba'a dade da bude musu ita ba a rugar tayiwa, Nuruddeen.


    " Nuruddeen ne yace da kin bar zancen zuwa na makarantar Nan, kinga babu kudin makarantar kince kin bawa Mama kudin, kuma ko naje korata zasuyi.


   " Cikin Sanyin murya Nasreen tace, kayi hkr kaje ka Nuruddeen, idan sun koreka kace suyi hkr, Baban kane yayi tafiya, idan ya dawo za'a kawo musu.


   " Nabiya dake shanyan kayan Goggo ne tace, Adda Nasreen Sanda nace Miki karda ki bawa Mama kudin makarantar Nan kika Bata, gashi yanxu Babu inda zamu samu dubu mu biya Masa, Baba kuma Allah ne kadai yasan Ranar dawowar sa daga binni.


    " Kallon Nabiya tayi tace, Baba yace bazai dade ba, kwana goma kawai zaiyi, kuma kinga Yanxu kwanan sa 7 da tafiya, kaje Nuruddeen ka gwada idan sun koreka sai ka dawo.


   " Goggo ne ta karaso wajen nasu tace kuskus din me kuke Allah dai yasa ba gulma ta ake ba.


   " Nabiya ce tace ke har kin kai ayi gulman kine mu damuwar mu muke kokawa, ba take muke ba.


   " Allah sarki jama'a kuji min yarinya wai ban kai ayi gulma ta ba, lallai akuyar daure ta samu sake, tunda na taimake ki daga Hanun wannan azzalumar Uwar goyon taku ba, dole kice min bata ni kuke ba, ke kam shegiya da yau kin wuni a tasha wajen yan talle.


   " Dariya ce ta kwacewa Nasreen tace kai goggo kina da matsala wato yau kuma gori ne ya tashi kenan.


   " Yo to Nasranatu ai wannan shegiyar Nabiyanatu idan ba'a mata gorin baza'a shirya da ita ba.


 " Hada fiska Nabiya tayi tace, ni goggo ki daina cemin Nabiyanatu, suna na Nabiya ehe da haka Ubana ya yanka min rago.


    " Sandar dake hanun goggo ta daga zata saukewa Nabiya,.

  Ko kafin sandar goggo yayi kasa Nabiya ta zille ta gudu.


   " Kallon Nasreen goggo tayi tace Nasranatu naji duk abunda kuke kokawa, kunce bakin zanin ta Goggo tayi ta hado kudaden ta, dari takwas da hamsin ne bawa Nuruddeen tayi tace gashi Nura ka kai musu wannan kace gobe zaka ciko musu dari da hamsin.


   " Karba yayi da murnar sa ya tafi makaranta.


  " Kallon Goggo Nasreen tayi tace goggo kin bashi kudin duka baki rage wanda zaki kashe ba.


    " Me nake siya Nasranatu, komai nayiwa yaran Maimuna ban fadi ba, domin kuwa Babu abunda Maimuna bata min, ba dan haka karki damu, anjuma ki kama kaxa daya kije ki sayar inyaso gobe sai a basa cikon dari da hamsin din ya kai musu





More

     Comment


More

    Typing




Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


(Ummu Nasmah)

[11/10, 5:49 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story

    And

Writing

      Rasheedat Usman

     (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم



  Deducted

       To

     All members of Hausa novel 2 Gaskiya babu abunda zance muku, domin kuna nunawa wannan book din kauna, jiya kawai da ban turo muku ba, naga kun damu sosai, na gode sosai da kulawar ku gareni.



P•••••••••••1️⃣1️⃣ to 1️⃣2️⃣


Kowa dake cikin falon juyowa yayi ya kalli momy Sarah, 


  " Khalid ne yace Momy ya naga kin birkice daga cewa an ji lbrn wasu sun shigo da cocaine airport.


  " Saita kanta momy Sarah tayi, tace ai abunne abun tsoro yanda rayuwa ta lalace, matasan mu sun lalace da shan miyagun kwayoyi, yanxu dan Allah kuji fah wai har daga wata kasa aka shigo da wannan hodar ta iblis.


  " Shuru Khabeer yayi Yana karewa Momy Sarah kallon yanda rashin Gaskiya ya fito a fiskar ta, yasan ko ina mutum marar Gaskiya yake yakan ganesa daga kalaman sa zuwa yanayin sa, sai dai har ga Allah bai kawo a zuciyar sa cewa  Momy Sarah tana da alaka da wadannan yan ta'adda ba.

   

  " Momma ce tace, ke dai bari momyn yara, rayuwa ta lalace, matasan mu masu jini a jika wadanda zasu taimaki kasar mu, wasu yahudawa sun lalata musu rayuwa, Allah dai ya kawo mana sauyi.


  " Gyaran murya Daddy yayi yace, Allah dai ya kyauta, kai khabiru tsayuwar me kake kuma da baxa shige kaje ba.


  " Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dannawa inspector Siraj kira, bayan ya daga ne yace, inspector dan Allah yanxu ku tura jami'an ku zuwa airport, ina son su kewaye Airport din gaba dayan ta, a rufe kar kowa ya shiga kar kuma kowa ya fita, sannan zan turo jami'an mu na sirri, zasu shiga cikin airport, ka kira sagern Saleem kace masa ya kira all network na layukan da ake amfani dashi su rufe na tsawon 3 hours yanxu Nan bana son ko wani layin waya ya kara amfani nan da 15 minute, zamu hadu da ku yanxun nan.

   Katse kiran yayi tare da kashe wayan, kallon Daddy yayi yace, a Mana addu'a zamu fita.


  " Fatan alkairi daddy ya masa, sannan Khabeer ya yasa kai ya fice daga cikin gidan.


  " Momy Sarah kuwa babu abunda cikin ta yake sai kugi, a kidime ta shiga bedroom dinta, junior ta gani kwance a saman bed dinta, yana sharar baccin sa, harara ta wurga masa, tace dan tsiya, wannan uban naka da yake neman shiga min hanci da kudunduno sai nayi maganin sa,

  Da sauri ta dannawa Hajiya Hindatu Kira, Domin dakatar da ita daga zuwa airport din, amma ina kaddara ta riga fata domin shi kanshi layin nata an kulle sa bare kuma ta samu damar kiran wani layin.

   Na shiga uku ni Saratu Allah kasa Hindatu bata je airport din nan ba, muddun aka kama Hindatu kashina ya bushe, wayo Allah na, Allah ka rufa min Asiri na.


   " Haka Momy Sarah tayi ta zagaye dakin, ta kasa zaune ta kasa tsaye, tollet kuma taje yafi sau 6 .


  Shiko Khabeer darect office din su ya nufa, jami'ai 7 ya dauka amintattun sa, yaran da ya basu horo da Hanun sa,.

  Tare suka fice cikin shigar normal Kaya, baxaki taba cewa police bane su, a motar Khabeer suka nufi Airport din.


  " Hajiya Hindatu kuwa ta dade da tsufa a Airport din, yayin da suka gama tsadance kudin da zata bawa  sargent Umar.

  Tana tsaya bakin Airport din, tana jiran sa ya karbo Mata.

    Bata ankara ba sai ji kawai tayi police sun kada su cikin airport din.

  Wani irin kugi cikin ta yayi tace mun shiga uku yau kuma asirin mu zai tonu.


   " Shigar su khabeer airport din sun tarar har su inspector Siraj sun fara aikin su, cikin kwarewa da taka tsantsan Khabeer yake aikin sa, 

   checking din, kowa ake yayin da aka saka camerar tsaro, wacce zatana nuna shige da ficen kowa.


  " Allah sarki hausawa suka ce duk wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a tashar walakanci, Sargent Umar daya karbi cocaine din ne ya rasa yaya zaiyi da shi, babu abunda Sargent Umar yake hadawa sai gumi, yasan muddun ya shiga Hanun IPS ya shiga uku, wani daki ya shiga tare da Ajiye jakar cocaine din, a hankali ya fice daga dakin.


  " Khabeer dake tsaye a wajen computers din yana kallon duk abunda yake faruwa ne, yayi murmushi, kallon Kamal yayi, yace Kamal kuje kuyi Arresting din Sargent UMAR.


   " Da sauri Kamal yace, yes sir.


  " Fita shima Khabeer yayi yabi bayan Kamal, 

   Yana tsaye ya zuba hannayen sa a cikin Aljihun sa suka kawo masa Sargent Umar har gaban sa.

   Kallon sa Khabeer yayi yace, agun waye ka karbi cocaine din.


   " Kansa yana kasa yace sir ni kuma cocaine, a wajena.


  " Tsawa Khabeer ya daka masa yace, ina tambayan ka kana tambayata, idan ba so kake kayi Asarar Aikin ka ba, ka nuna min waye ya baka wannan cocaine din, sannan waya baka kongilar karbo ta, ka fada min nace.


   " Tunanin rasa aikin sa da Sargent Umar yayi, yasa yace sir zan nuna maka, 


  Sashi a gaba security sukayi yana bi yana kare mutanen wajen kallo, mutumin da ya basa cocaine din daya ga Sargent Umar yana kokarin tona masa Asiri ne yasa shi daurawa wata mata bindinga a kayi, yana bara zanar muddun ba'a basa hanya ya wuce ba, zai dauke kan wannan matar.


  " Nuni Khabeer yayi da a basa hanya, da sauri Kamal ya kalli Khabeer yace " sir kasan me kake shirin yi kuwa, mai laifi fa kake kokarin bawa hanyar tsira.


  " Tsuke fiska Khabeer yayi yace Kamal, yaushe ka fara koya min Aiki, ita wannan matar da ya daura mata bindinga shin bata da iyalai ne, ko kuma zamu bari ne ya aikata abunda yayi Niya, karfa ka manta da cewa shifa dan kwaya ne, kasan duk inda dan kwaya yake kuma bayi da cikakken hankali, dan haka ku basa hanya ya shige.


   " Basa hanyar sukayi, ya shiga, yayi nisa da nufar kofar da zai fitar dashi daga Airport din Khabeer ya dauko bindigar sa ya harbe kafar mutumin, 

 Kara mutumin ya sake tare da wurgi da bindigar gefe,.

  

  Umarni Khabeer yayiwa matar da ta dauki bindingar ta taho wajen sa,


   " Tare da Sargent Umar da mutumin aka hada aka sawa Sarka, umarni Khabeer yayi da cewa a tafi dasu office zaizo daga baya.


   " Ajiyar zuciya Hajiya Hindatu ta sauke, tace Alhamdulillah na haye wannan hadarin, 


  Hanya aka bawa kowa ya fice daga airport din.


   " Shiko Khabeer gidan sa ya shige darect, a falo ya samu Zuhura tana zaune ta daura kafa daya akan daya tana taunar chingum, a gefen ta ya zauna tare da daura kansa a kafadar ta, " yace Habibty na gaji da yawa.


   " Itako Zuhura tsabar rashin hankali babu sannu da zuwa bare kuma ta kawo masa ko ruwa ne mai sanyi yasha.

  Sai cewa tayi, to me zan maka da kake cemin ka gaji, ko chan inda kaje din basu baka abinci bane.


   " Murmushi Khabeer Yayi idan da sabo ya saba da halin Zuhura na rashin nuna kulawa a garesa, yasan duk sanda Zuhura take rarrashin sa, ko take masa abunda yake so, yasan akwai abunda take nema a garesa, da zarar ta samu Kuma, zasu koma gidan jiya.

   Bai cemata komai ba ya tashi ya shige bedroom dinshi, da takaicin Zuhura, har ga Allah yanxu kam ya fara tunanin Karin Aure, dan baxai iya rayuwa da Zuhura a haka ba.


  " Momy Sarah dake zaune ta hada tagumi ne, taji ringing din wayar ta, Hajiya Hindatu, da sauri momy Sarah ta daga wayar bata jira me Hajiya Hindatu zata ceba, tace, sun kama ku ko.


  " Daga can Hajiya Hindatu tace, da sun kama ni ai baxaki ga wannan kiran nawa ba, lbrn abunda ya faru a Airport din ta bawa Momy Sarah, ta karashe maganar da cewa, Ai alhamdulillah na samu na sha da kyar.


   " Tsaki Momy Sarah tayi tace, kinsha a gidan uban waye, Sargent Umar yana hanu ne zaki ce kin Sha, baki shaba, domin kuwa dole ne Sargent Umar ya fadi cewa kece kika tura sa, kuma muddun aka kama ki, nima nasan baxan tsira, ba, 


   " Cikin kidima Hajiya Hindatu tace mun shiga uku yanxu menene mafita,.


  " Shuru Momy Sarah tayi, sai can tace, dole ne mu sanja miki kama, ta hanyar miki zane a fiskar ki, domin kuwa na tabbata ko kasar nan kika bari wannan dan shegiyar baxai kyale ki ba sai ya kamo ki,.


 " Ajiyar zuciya Hajiya Hindatu ta sauke tace, indai hakan ne zaisa na fita daga cikin tarkon IPS na yadda, domin wannan dan mijin naki cinnaka ne, baisan sabo ba,.


  " Momy Sarah ce tace ki jiran ina zuwa da daddare, sannan ta katse kiran.


  Zama tayiTare da daura Hanun ta a kayi tace na shiga uku ni jikar Abubakar.


  

************************


Wasa wasa Satin su Nasreen biyu a gidan Goggo, yayin da Nasreen har wani yar kiba tayi, farin ta ya kara fitowa kasancewar tana samun tayi wanka kullum a gidan Goggo, sabanin gidan su da, dakyar mama take barin ta tayi wanka Ranar Juma'an ma.

 

  " Sai a lokacin na kare mata kallo,doguwa ce tana da dan kiba daidai gwargwado kirjin ta a cike suke, a kuma tsaye kyam tana fadin kugu,  farace sosai ba farin wasa ba, tana da cikar fiska mai dauke da manyan idanu gashi idanun nata Zara zara suke a tsaye kamar ta shafa Ailener, girar ta kuwa har ta kusa hadewa da yar uwarta, sai kace wanda aka zana mata shi, kanta dauke yake da dogon gashi, baki wuluk, hancin ta dogo ne kuma yana da dan kauri kadan, Gaskiya Nasreen ba karamar kyakkyawa bace.


   " Suna zaune a tsakar gidan Goggo dukan su hudu  Goggo Nasreen Nabiya Nuruddeen, suna cin gyada, Baban su Nasreen ya shigo cikin fada, 


  " Allah sarki yaro shiko Nuruddeen ganin Baban sa yasa ya ruga da gudu yana oyoyo Baba yaushe ka dawo daga binni.


  " Bigesa Baba yayi yace ban sani ba dan Uwar ku, 


   " Rike haba goggo tayi tana kallon ikon Allah.


  " Nuna Nasreen Baba yayi yace dake zan fara babbar munafuka, wato shine tsabar rashin imani zaku tafi ku bar Salame da aiki koh, ina sa kafata ina fita kuma kuka saka taku kafar kuka fice ko, wato aikin idan zai kasheta ya kashe ta ko.


  " Zaro ido Nasreen tayi tana kallon bakon al'amari Baba da bai taba musu ko tsawa ba, yau shine harda zagin su.




Comments

  And

  Share



Alkalamin Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)

[11/12, 4:38 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story 


     And


        Writing


            Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم


Dedicated 

      To

Maman Usman tsohuwa mai ran karfe kisha zaman ki, ki huta Kakus wannan page din naki ne.

  Sai kinga dama ki bawa su mmn Aiman da su sis mener, su karanta


SANARWA


Dan Allah friends dina ku isar min da sakon nan akwai wani wanda ya kirani Namiji ne yake cemin wai dan Allah na sayar masa da littafin SARA DA SASSAKA akan farashin dubu biyar  5000 wai zai turo min number na whatsapp dinsa Ni kuma na tura masa Account number na, shi kadai zankewa typing ina tura masa, yace min ya sami number nane a sanda na fara tallen littafin, kuma yaga dana fara typing din littafin ya karbu sosai dan haka yake bukatar na sayar masa shima zai sayar da book, din, sai dai Abunda nake son ka sani cewa, koda ace zan sayar da littafina baxan sayar maka ba, domin kuwa nafi karfin 5 k dinka bare kuma book dina bana sayar wa bane, nayi shine saboda masoyana masu kauna ta, duk mutumin daya ce SARA DA SASSAKA na kudine karya ne danfarar ku zaiyi littafina FREE ne.



 Taya murna Dijan Birni

       

💃💃💃💃💃💃💃💃

Ayya raye Ayye Ayye Ayya raye Ayye Dije ba'a kanki ne aka fara ba ba'a kanki ne za'a kare ba zaman gidan wani tilas, Amarsu ta Ango Dijan Birni kinsha kamshi yaude an tare a gidan Ahmed Allah ya sanyawa Rayuwar Auren ki albarka, yasa daga first night, jirgin ku ya harbo yan biyu✌🏻 congratulation Dijan Birni💃💃💃💃💃💃💃💃



P•••••••••••1️⃣3️⃣ to 1️⃣4️⃣


 " Tsawa Goggo ta daka wa Baba, tace Nice Babbar munafukar MUSA tunda nice naje na dauko su, ni zaka kira da haka ba suba, yanxu Ashe musa da hadin bakin ka, matar ka take wahalar da yaran ka, ka bani mamaki musa, yaran da basu sami ishashen gatan Mahaifiya ba, Ashe gatan Uban ma zasu Rasa, Ashe musa ni ban isa na dauki ya'yan ka su zauna a hanuna ba, tabbas yau ka nuna min matsayina akan yaran ka.


  " Sunkuyar da kansa Baba yayi yace, ba haka ne nufina ba Goggo gani nayi bai kamata ace sun tafi sun bar Salame da Wahalar gida ba, kuma ai Goggo kema mai rike sune,. Kiyi hkr idan ranki ya baci.


  " Cikin fada Goggo tace karya kake Musa, da ka dauke ni a matsayin wacce zata iya rike ya'yan ka, da yanxu baka zo nan ba, ka tsaya kana zagin su, idan Salame ta shanye ka, to ni wlh bata isa ba, domin kuwa nafi karfin bokan ta, ni da kake gani na, kishiya ma sunyi sun barni bare kuma wata suruka, sanda uwata ta haife ni sanda aka gewaye ni kur'ani, kaga kuwa babu abunda yar iskar matar ka zata min,.


  " Nasreen dake zaune hawaye na tsiyaya a idanun ta, azuciyar ta ji take duniyar ma ta isheta, ina ma da ba'a haifeni ba, da yanxun bana shan wannan wahalar da nake sha, 

  Tashi tayi taje ta tsugunna a gaban Baba, tace kayi hkr Baba, bansan ranka zai baci ba, da tun sanda goggo tace mu biyo ta, wlh da bamu bita ba, kayi hkr Baba karka juya mana baya domin kai kadai ne gatan mu, bamu da wani gatan daya wuce naka, kai kadai muke........


  " Katse ta Nabiya tayi, Baba bashi kadai bane gatan mu, muna da Allah da kuma Goggo, laifin me muka yiwa baba, da har zaki basa hkr, shi Baban yasan wahalar da muke Shane, ina kam kullum tafiyar sa yake ya barmu da Mama tana Azaftar da mu, hatta wannan dan yaron ba'a saurara masa ba, ta nuna Nuruddeen da yatsa kuma kai kanka Baba kasan da wannan, kana bamu hkr, a duk sanda Mama ta kuntata Mana, amma wai yanxu  Baba kaine kake zagin mu Akan Mama, 

  Nikam Baba baxan koma wajen Mama ba, ka barni nayi zamana a hanun Goggo.


  " Cikin tsawa Baba yace naki na barki a wajen goggon yar banxa marar kunya, wato rashin kunyar taki da mutane suke fada har takai, kaina, bari kiji na gaya miki, koda ace yau idan kin koma Hanun Salame zaki mutu, sai kin koma, domin kuwa dole ne na cikawa Salame Alkawarin dana daukar mata, na zan dawo mata daku, ku shige ku dauko kayan ku mu tafi.


  " Idon Nabiya ya kada yayi yaji jajur, bata son ace tayi musayan yawu da mahaifin ta, amma shi baba ya kasa gane hakan, ita kuma wlh tayi rantsuwar cewa tabar Hanun Mama, baza ta sake komawa cikin wannan Bakin gidan ba.

  Matsowa tayi gaban Baba, tace wlh Baba ko zaka kasheni baxan koma wajen Mama ba, sai dai Idan gawata zaka kai gidan, kuma koda ace Goggo tace baxan zauna a gidan ta ba, na gwammaci na shiga Duniya, inyaso nabi bayan Ammi, idan ma karuwancin da ake cewa taje ne, nima zan bita na daura a inda ta tsaya.......


  " Saukar Marin da taji a kuncin tane, ya hanata karasa maganar, rike kumatun ta tayi tana kallon Baba.


  " Kara mata marin Baba yayi yace, wannan ya zama Rana ta karshe da zaki, kara siffanta Maimuna da karuwa domin kuwa ita din mutumiyar kirki ce, Maimuna baxa ta taba karuwanci ba, har yanxu na kasa gano abunda ya fitar da Maimuna daga cikin wannan Rugar,

  Duk inda Maimuna take na tabbata bata cikin halin lfy, idon sane ya ciko da Hawaye kasa karasa maganar yayi, sakamakon taso masa da ciwon dake cikin zuciyar sa da Nabiya tayi, kasa daure hakan da yayi ne yasa shi ficewa daga gidan.


  " A jiyar zuciya Goggo ta sauke tace, ku kyale ni dashi, zanyi maganin sa, Babu inda zakuje kun dawo gidan nan kenan,

Juyo da kallon ta tayi ga Nabiya tace ke kuma na dawo kanki, Dan Ubanki, shine zaki saka mahaifin ki, a gaba kina mayar masa da magana kamar wanda kika samu sa'an ki, karki sake wannan kuskuren, domin hakan babbar musiba ce ga yaro, mayarwa iyaye magana, duk abunda yake miki shuru zakiyi ki danni zuciyar ki, ki masa biyayya koda ranki baya so, sanadin wannan biyayyar da kika masa sai Allah ya duba lamarin ki, ya sauya miki da Abu mafi alkairi a rayuwar ki.


  " Goggo raina ne ya baci da yawa, shiyasa, ki duba fa Goggo yanda BABA ya dawo bin bayan MAMA lokaci daya, duk wahalan da muke sha, ya kasa gani,.


  " Duk da haka hkrn nan dai shi zakiyi, domin shine mafi alkairi a gare ki.


  Nasreen dake gefe tana jin duk Abunda suke fada, bata samusu baki a zancen su ba, domin gani take duk Rashin damuwa yasa su magana, tashi tayi tare da kama Hanun Nuruddeen, suka nufi hanyar fita daga cikin gidan, 


   " Sunan ta goggo ta Kira, tace Nasranatu ina zaki je kika nufi hanyar fita.


   " Bata son yawan magana Hakanne yasa a takaice tace wa goggo Zan fara aiki ne da abunda kika fadawa Nabiya na cewa ta dinga biyayya da maganar mahaifin ta.


  " Shuru goggo tayi domin tasan hausawa sunce baki shike yanka wuya, bata da ja tunda tasan ta fada, 

   Kinga Nasranatu komawa Hanun Salame matsala ce ga rayuwar ku dan haka, ki dawo ki barni da mahaifin ku, dole zai bar min ku.


   " Cikin zubar da hawaye tace kiyi hakuri goggo baxan iya tsallake umarnin mahaifi na ba, nasan kina san mu bakya son Abunda zai samu cikin wahala, kiyi hkr ki barni na cika umarnin mahaifin mu, ita Nabiya tunda tace baxa ta koma ba, sai tayi zaman ta. tana gama fadin haka ta fice daga gidan.


  " Masifa Goggo ta hau yi, oh ni Hadiza, ina nema muku mafita amma ja'irar yarinyar nan tana neman samin tsakuwa a ido, to shikan  Nura kam zanje har gidan na dauko sa, dan baxan barshi ya wahala ba, ke kuma kije ki can ki karata tunda wahalar kike so.


   " Tashi Nabiya tayi ta dauki buta tana kokarin shiga bayan gida tace rabu da ita Goggo, taje ta din, tasan Halin Mama ai, jiki magayi.


  

  Itako Nasreen da sallama ta shiga cikin gidan shuru taji kamar Babu kowa a cikin gidan, dakin mahaifiyar su ta bude suka shiga.


 Yayin da ita kuwa MAMA tasa yarta yar gwal, a daki tana bata sako.


  " Kinga yar gwal, kudin nan dubu Talatin,ne ki rike su da kyau kinga dai gona ta na gado na sayar na samu wannan kudin, kije wajen BOKA RABGAS ki Kai masa, kice gashi injini ya kuma baki sakon ki kawo min, kice masa na gode sosai, aikin da yamin Akan Mlm Musa yayi kyau sosai,

 Kije maxa ki dawo yar albarka.


  " Karba yar gwal tayi ta nufi wajen BOKA RABGAS.

  

   

*************************

 

Wasa Wasa kwanan su Sargent Umar uku a rufe Khabeer bai waiwaye suba.

   Bawai kuma baya zuwa division din bane, yana zuwa, haka kawai baiga daman ganin su ba.


  " Da misalin karfe 10 na dare, Khabeer yana kwance a dakin sa, yana aiki da laptop din sa, Zuhura tayi sallama dakin dauke da cup din coffee, a gefe ta ajiye masa tare da juyawa.


   " Zuhura Khabeer ya kirata.


   " Tsayawa tayi tana jiran mai zaice Mata.


    " Ina jiran ki 10:30.

    

    " Allah ya kaimu tace a takaice tayi ficewar ta.


  Baya gama aikin nasa ne ya shiga tollet yayi wanka tare da shirin kwanciya, 11:30 yama fitar da ran Zuhura zata dawo, bai jima da kwanciya ba, sai kuma ga Zuhura ta shigo dakin, gefen sa ta kwanta, tare da daura kanta a kirjin sa, 


   " Abban junior, kayi hkr na dan makara,.


  " Babu komai yace a takaice tare jawo ta jikin sa, hanun sa yasa yana shafa bayan ta, tare da manna bakin sa a cikin nasa, chafkar harshen sa, tana tsotsa kamar wacce ta samu sweet, a hankali ya zame bakin sa daga nata yasa kansa a wuyan ta yana shinshina, a haka har ya gangaro, saman Nonon ta, bakin sa ya daura yana tsotson daya yayin da hanun sa yake murxa nipple dinta, 


Ganin danayi suna kokarin Afkawa junan su yasa nace, safiya mai Albarka gwara na tafi wajen Momy Sarah naga Halin da take Ciki.


  " Kwance Momy Sarah take a makeken gadon ta, tana tunanin Halin da zata shiga idan Asirin ta ya tonu, gashi har yanxu shuru babu, wani lbr akan maganar case din, duk da sawa da tayi aka tsaga fiskar Hajiya Hindatu tare da sauya mata wajen Zama, amma hankalin ta baya kwance bacci ma kansa gagarar ta yake, ta rasa nutsuwar ta da kwanciyar hankalin ta.




08147537180




Share 

     And

      Comment



Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


(Ummu Nasmah)

[11/13, 6:17 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story 


     And


        Writing


            Rasheedat Usmau


 (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم



🤳🏻

     08147537180 



Friends dan Allah ku taya ni da Addu'a akwai abunda nake nema jiya naje nayi interview, za'ayi posting din sakamako Ranar Juma'a please ku taya ni da Addu'a Allah yasa ina daga cikin wadanda zasu sami wannan Aikin 🙏🏻



SADAUKARWA

  

Sadaukarwa gare ki, 

REAL NANA A''ICHA.




P•••••••••••1️⃣5️⃣ to 1️⃣6️⃣


Haka Momy Sarah ta kwana cikin rashin kwanciyar hankali, bacci ma dan barawo ne shiyasa ya sace ta, 


 Washe gari da safe Momy Sarah itace da girki, tasan kuma ko tasa faty da Hasina ba lallai bane su mata, shiyasa ma bata tsaya batawa kanta lokaci ba, ta shiga cikin kitchen din da kanta,


  " Kafin kowa ya tashi Momy Sarah ta gama breakfast din, daki ta koma tayi wanka, kafin zuwa sha daya ta fito.


  Sanda Momy Sarah ta fito, falon Babu wanda idon ta ya fara gani sai Khabeer sanye yake da uniform din police, wonderful kunga yanda Khabeer yayi wani irin kyau uniform din yayi matukar karbar sa, ya kuma dace da kalar fatar jikin sa kasancewar sa farin mutum, da a lama dai yau yana da wani serious Aiki ne dan sai hakan ta kasance suke sanya uniform, wani tsinkewa zuciyar momy Sarah tayi, gani take kamar a lokacin Khabeer zai gane cewa itace aka aikowa cocaine din.


  " Murmushi Khabeer ya mata tare da cewa good morning momyn mu,.


  " Morning tace masa cikin dariyar yake wacce tafi ta kuka ciwo, ya Zuhura ta kwana biyu bata leko muba.


 " Kafin Khabeer ya bawa Momy Sarah amsa sukaji muryar momma tana cewa ta shekara biyu dai ba kwana biyu ba, daman ita zuhura tana zuwa gidan nan ne, yar iko, da kuma samun goyon bayan miji na kyale ta da yayi ta Raina iyayen sa,.


  " Dariya Khabeer yayi, amsar da zai bawa Momy Sarahn ma fasawa yayi, dakin mamy ya shige, bai tankawa Momma ba, 


  " Tabe bakin ta Momy Sarah tayi  a zuciyar ta, tace Allah ya hada ka da mungun tsautsayin da zaisa wannan kafar taka ta karye, muga da wacce kafar zakayi binciken, wani tunani ne ya fado mata a ranta, dariya tayi a zuciyar ta tace, yess good dole nasa a sunce min notting na tayar motar ka yanda zakayi mummunan Accident,

 Nima na huta da fargabar ka.

  Dan iska gashi kuwa yanda yake kula da wannan yar kauyen tsintacciyar magen ko uwar sa baya kula da ita haka.


  " Taba ta da momma Tayi ne ya sata dawowa cikin hayyacin ta, 

   Tunanin me kike haka momyn yara, Alhaji sai magana yake baki jiba.


  " Babu komai muje daining din, kafin yaran su fito,


   " Kusa da kujerar Daddy Momy Sarah ta zauna, tare da gaishe da Daddy, amsawa yayi, yace danki baixo bane, ina son ganin sa yau,.


  " Yaxo yayi dakin mamyn su, kasan dabi'ar sane indai yaxo gidan nan sai ya fara shiga dakin ta kafin ya zauna.


  " Allah sarki dan albarka hakan yana da kyau sosai tausayawa wanda yake cikin damuwa mu fara breakfast din kafin ya fito Koh.


  " Da to Momy Sarah ta amsa sannan tayi serving dinsu.


  " Mamy na zaune tayi tagumi tare da kafawa saman daki Ido, da alamu dai tunani take, kuma tayi nisa sosai a cikin tunanin, zama yayi kusa da ita yace mamy, shuru Babu amsa, kara kiran sunan ta yayi a karo na biyu nan ma shuru, babu amsa.

   Taba ta Khabeer yayi.


   " Da sauri ta juyo ta kalle sa, murmushi tayi tare da shafa kansa.


  " Tunanin me kike haka mamy, kina tunanin yaran ki Koh, gashi ban dawo miki da pic dinsu ba, kiyi hakuri ban samu nayi coping su bane, Amma insha Allah yau idan na dawo daga Aiki zanyi kokari naga nayi coping din.


  " Kada kanta tayi tare da sakar masa murmushi.


  " Kama Hanun ta yayi yace, tashin muje kiyi breakfast ni yau ina axumi.


  " Tashi tayi suka fito tare, zama sukayi Khabeer ya jawo flet ya zubawa Mamy Abinci ya tura Mata gaban ta, sannan ne ya dago yace good morning Daddy.


  " Murmushi Daddy yayi yace morning my son, sai yanxu aka ganni,.


  " Murmushi yayi yace, sorry Daddy, hankali na yafi kwanciya, idan naga Mamy tayi breakfast.


  " Hakan yana da kyau, kaci abincin zamuyi magana.


  " Ina axumi Daddy, fitama da zanyi, zuwa office yau nake son fara bincike akan case din nan.


  " Dam !! dam !! Dam gaban Momy Sarah ya buga ji tayi Abincin ma ya ishe ta, ajiye sporm din tayi, tare da daura tagumi.


  " Daddy ne yace to daman ina sone, zakaje garin su mlm Iro mai gadin gidan nan, akwai wanda ya hada mu dashi, mai suna musa, shine zaiyiwa mahaifiyar ka kiwon shanun ta, kwanan nan mutumin yaxo harma mun gana dashi kwanan sa goma, ya tafi da shanun, so ina son zakaje chan Rugar tasu ka duba mana wajen zaman sa, da kuma yanayin yanda yake kiwon shanun.


  " Ai bansan garin su mlm Iro ba daddy,


  " Yamin kwatance yace min idan kaje dukku ka tambayi, Rugar ARDO BOYI ba'a rasa wanda zai nuna maka hanyar ba, idan kaje garin sai ka tambaya inane gidan jauro jatau, za'a kaika har gidan, nan ne gidan su mlm iro.


  " Shikenan to zanje amma sai zuwa jibi saboda ina son a cikin kwana biyun Nan, na gama bincike akan case din cocaine din nan.


  " Babu damuwa Allah ya kaimu jibin.


  " Ameen Daddy sallama ya musu, sannan suka masa addu'a, Momy Sarah ce kawai bata masa addu'ar samun nasara ba.


  


  " A hanyar sa ta zuwa division din nasu ne, yaga kiran abokin sa, daga kiran yayi tare da cewa Abokina ya akayi.


  " Daga can yace normal Officer, na fa dawo yanxu haka ina cikin garin Gombe,


  " Kai SADIQ wasa kake min koko da gaske kake please serious, da gaske kana Gombe.


  " Kwarai kuwa yanxu ma haka ina nan jeka da fari family Hause din mu, kana ina ne kai.


  " Ina hanyar zuwa office, yaushe zamu hadu.


  " Idan na tashi daga family Hause zan biyo ta office din naka.


  " Okay sai kaxo ina tsumayar ka, 


  " Okay bye.


 " Bye Khabeer yace tare da katse wayan.


  Sadiq aminin Khabeer ne na hakika, tare suka taso tun nursery School har zuwa University, shi sadiq yana Aikin Zane wato Art a cikin garin Abuja, yakan zuwa Gombe sa'i da lokaci yayi hutun sa, ya koma har yanxu Sadiq baiyi Aure ba, a cewar sa, shi har yanxu baiga matar Aure ba.


 " Isar Khabeer division din, darect cell ya nufa, dama ya riga da yasa kamal ya fara hura masa , markel da Sargent Umar kafin ya iso.


  " Duk police din da suke wajen sanda suka Sara Masa, dakatar da Kamal yayi daga dukan da yakewa su Sargent Umar, tsugunnawa yayi a gaban su, ya tamke fiska, ya fara magana,.


  " Markel sange sunan ka Koh.


  " Da gyar wanda aka kira da markel din yace yes,my name cikin karfin Hali.

    Domin kuwa sunsha azaba a hanun kamal ba ta wasa ba.


  " Okay, ina so ka sanar dani waye ya turo ka da cocaine cikin kasar mu, kuma jihar mu, daga wacce kasa kuma.


  " Shuru yayi yaki magana,


   " Murmushi Khabeer Yayi yace, ka tausayawa kanka ka fada min cikin sauki tun kafin ka fada min cikin wahala,.


  " Nan ma dai shurun yayi yaki cewa komai domin kuwa ya kudurce a ransa cewa ko wacce irin wahala zaisha baxai tonawa uban gidan sa asiri ba,.


  " Okay dauke shi Kamal, wahalar da kuka basa bata shiga jikin sa ba, kuje kuta gana masa azaba daga nan har zuwa, gobe, zan kara waiwayo sa.


  " Kallon sa ya mayar kan Sargent Umar yace, kai kuma munafikin Hukuma zaka fada min waye ya turo ka cikin Airport ka karbi cocaine din ne, koko sai nasa an sanja min kamannin Fiskar ka,


  " Cikin in ina da sanin Halin waye Khabeer yasa Sargent Umar cewa zan fada muku, 


  " Okay ina sauraron ka. Tell me.


  " Hajiya Binta itace ta turo ni, nasan baxaka santa ba, tana zaune ne a unguwar byfass. Nasan gidan ta, zan iya kaiku.


  " Murmushi Khabeer Yayi yace good information nawa take biyan ka, idan ka kai mata,. Sannan menene alakar ka da shi markel.


  " Tana biyana dubu dari biyar ne, amma shi markel ban sanshi ba, nidai aiki na shine na je na karbo sakon kawai,.


 " Okay babu damuwa zamuje gidan ta cikin dare.

  Kamal ku shirya yanda lamarin zai kasance, zan neme ka karfe daya na dare.


  " Ita kuwa Zuhura ta shirya taci ado tare da daura wani dan karamin gyale, zata gidan su, dan ta gaji da jiran Khabeer, yau kusan sati biyu tana tambayar sa yana mata kwana kwana, yanxu kam ta gaji tafiya zatayi ba tare da ixinin sa ba, inya so duk abunda zai faru ma ya faru, 




🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Kuyi hkr da wannan wlh kwana biyun nan bana jin dadin jikina ga shi kuma bana samun zama sosai, da cewa nayi zan bari sai na samu time, sai kuma naga da Babu gara ace babu yawa ne, kumin uxiri. 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻



Share

     And

      Comment


Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


     (Ummu Nasmah)

[11/15, 10:37 AM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story 


     And


        Writing


            Rasheedat Usmau


 (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم

🤳🏻


08147537180



 Sadaukarwa


 Gareki my little sister, Autan mu maijidda Usman Happy birthday sisi nah Allah ya karawa rayuwa Albarka, 🎂🎂🎂🎂🎂 I love you sisi nah 😘




P•••••••••••1️⃣7️⃣ to 1️⃣8️⃣


Karfe shadaya a gidan su Zuhura ta mata da sallama ta shiga falon nasu, babu kowa sai sistern ta Saleemat dake zaune ta daura kafa daya kan daya, amsa sallamar Saleemat tayi, tace Aunty yau kece a cikin gidan nan, gsky rabonki da zuwa kin juma.


  " Wlh kuwa Leemat, ina umma na ganki ke daya a cikin falon.


 " Tana cikin bedroom din ta yanxun nan ta shiga, ina junior na ganki ke daya.


  " Kallon mamaki ta mata tace junior kuma Leemat, junior da yake cikin gidan Nan zaki tambaye ni, lafiyan ki kuwa.


  " Itama Saleemat kallon mamaki ta mata, tace bangane, lafiya ta ba, kina nufin kice baki san yaya Khabeer ya aiko Daniel ya dauki junior ba.


  " Da karfi Zuhura tace WHAT Khabeer din, yaushe ni banda wannan labarin.


  " Tun Ranar da mukayi waya dake, kike cemin ya dawo daga Indonesia, da yamma ya aiko aka dauke sa.


  " Huturun danja, cap.

 Lallai Khabeer ya Raina min wayo, tun randa ya dawo nake tambayan sa zanje gida, naga junior yake min kame kame, Ashe munafikin ya san abunda ya shirya, wato wadannan yan iskan iya'yen nasa ne suka sashi yaxo ya daukar min dana ya Kai musu, to wlh baxata yiwuba, domin kuwa babu yar iskar matar da ta Haifa da ko ta taya ni nakudar sa, daga nan can zan biya, naje na dauke Dana.


  " Daga bayan su suka ji Umma na cewa yawwa aini nasan biri yayi kama da mutum, nasan dai Zuhura baxata aiko a bata junior ba, wato ni banda kimar da Khabeer zai barmin dansa,  tsabar ma ya Raina ni, tunda ya dawo baixo ya gaishe niba bare kuma naga tsarabar sa, kuma duk kece shegiyar da kika sake masa har ya samu damar raina mu.


  " Haba Umma meyasa kike haka ne, kinsan dai duk abunda kike sani nayiwa Khabeer ina iya bakin kokari na, taya zan sakewa Khabeer har ya raina ku, maganar tsaraba kuma da kike yi, Umma nafa aiko muku tsarabar nan.


  " Dan ubanki wannan ba tsarabar sa bane domin kuwa kece kika aiko min ba Shiba, yanxu dai ina kudin da nace ki bani.


  " Tura bakin ta Zuhura tayi tare da bude bag dinta, dubu hamsin ta mikawa Umma tace gashi dubu hamsin ne ba'a samu darin ba.


  " Kallon shek`ek`e Umma tayiwa kudin tace, dubu hamsin, me dubu hamsin zata mini, yanxu ke, Zuhura duk abunda nake fada miki, bakya ganewa, yanxu ke kudin ma sai kin tsaya miji ya Baki, to ba'a yiwa namiji haka, idan har kinsan ma'ajiyar sa, jeki kawai ki dauka ba tare da sanin sa, ba idan kuma har kika tsaya, sai miji ya Baki, kina tare da wahala domin kuwa bazai baki wanda zai ishe kiba, duk macen da kika ga tana cikin wadata, to harda wannan dabarar take.


  " Shuru Zuhura tayi sai chan tace, kuma fah haka ne Umma, kin kawo shawara mai kyau, shiyasa nake sonki Umma akwai bada good shawari, kinga yanxu Umma rike hamsin din, daga yau zan fara amfani da shawarar ki, gobe ki Aiko Leemat ta karba miki cikon hamsin din, shi kuma Khabeer nida shine yau zamu gamu, zai fada min dalilin sa na zuwa ya dauke min dana, daga gaban uwata zuwa gaban wata katuwar banxa, da kuma abunda ya hana sa zuwa ya gaishe ki.


  " Dariya Umma tayi good, sai yanxu kika dawo hanya domin shi namiji da kike gani Zuma ne sai da wuta, domin kuwa basu da granti kamar service din waya, yanxun nan, zaka kira kaji ta shiga, anjuma kuma ka kira ace maka, unable to connection.


  " Na gane Umma kuma insha Allah zan tashi daga inda kika daura Ni, nida Khabeer a cikin gidan sa, shege ka fasa.


  Kusan wuni Zuhura tayi a gidan su, sai misalin biyu da rabi na Azahar tayi nufin komawa gidan ta, har ta dauki gyalen ta, ta fito suka hadu da mahaifin ta Alhaji Tanimu ya dawo daga kasuwa, komawa Zuhura tayi ta zauna tare da gaishe da mahaifin ta.


 " Cikin sakin fuska ya Amsa, yace ya mai gidan naki.


  " Yana lfy Baba.


 " Yayi kyau, kici gaba da hkr domin shi zaman Aure Dole sai da hkr, wata rana za'a saba wata rana kuma za'a zauna daidai, kullum ina gaya Miki kiyiwa mijin ki biyayya, i nayi Bari na Bari, ki kyautatawa yan uwan sa, ki yiwa iyayen sa biyayyah kamar yanda zaki Mana, ki bawa mijin ki hakkinsa dake kanki.

 Wannan shi ake kira zaman Aure, kuma baxan taba gajiya da tunatar dake suba.


  " Harara Umma ta 

Dokawa Alhaji Tanimu, cikin tsawa tace haba Alhaji ya kullum yarinyar Nan taxo gidan nan sai kayi ta cemata kibi mijin ki kibi iya'yen sa, aiko hadda ne ya kamata ace ta haddace, ke Zuhura tashi kiyi tafiyan ki dallah.


  " Girgixa kansa Alhaji Tanimu yayi, yace Halin kine bana so ta dauka, domin Sam ke baki da kyawun hali, ni kaina ina zaune dake ne, albarkacin ya'ya'n  dake tsakanin mu, da badan haka ba, wlh da mun dade da rabuwa, sannan su mazan yanxu mazan zamani ne, bazasu iya hkrn da mu mazan da muke yiba.

    Mamana kije kici gaba da yiwa mijin ki Biyayya Allah ya miki Albarka.


  " Sunkuyar da kanta Zuhura tayi kamar mutumiyar kirki, tace Amen baba, kullum ina kwatanta abunda kake fada min, babu wata matsala dake tsakanina da mijina ko yan uwansa suna sona ina sonsu.

 

" Tsaki Umma taja, tare da tashi ta bar wajen.


 " Masha Allah Allah ya Miki albarka, hanun sa yasa a cikin Aljihun sa, ya dauko, wata tsohuwar dari biyar yace ungo karbi wannan, ko adaidata sahu kya hau.


  " Kallon Baba tayi, tace a'a Baba, da mota ta nazo Ni, bana bukatar kudi, bag dinta itama ta bude, ta dauko dubu goma tace, ga wannan Baba.


 " Zuhura baki gajiya da hidima da mu, jiya ma naga kayan Abincin da mijin ki ya aiko Mana, ki mana godiya kafin Allah yasa mu hadu dashi.


 Da to Zuhura ta amsa tare da musu sallama ta fice.


  " Darect gidan su khabeer Zuhura ta wuce da sallama ta shiga falon nasu, Nana da Hasina ta samu zaune, suna kallo, dago kanta Nana tayi tace sannu da zuwa Aunty Zuhura, ki zauna ga waje.


  " Yawwa sannu, amma ba zama bane ya kawo ni, naxo ne daukar junior, na mayar dashi inda aka dauko sa.


  " Tsuka Hasina taja tace aikin Banxa kawai, kema dai Nana aikin yine da bai ishe ki ba har kika tsaya, nunawa wannan Abun karanci, nidai ina da aikin yi, kinga tafiya ta.


  " Itama Zuhura tsuka taja sannan tace, karamar marar kunya, da ki tsaya mana kiga yanda zanci ubanki.


  " Momma da tun daxu take tsaye, a bakin kitchen tana jin dibar Albarkan da Zuhura takeyi, ne yasa ta karasowa, ta dauke Zuhura da kyawawan Mari har Uku.


  " sanda zuhura taga star dafe fiskar ta tayi tare da dagowa ta kalli momma.


  "  nuna ta da yatsa momma tayi tace, Alhaji kike zagi a cikin gidan Nan, har kina da bakin da zaki shigo cikin gidan nan, kice zaki ci ubanta, idan kina da kunya a idon ki, ko meye Hasina ta miki baxaki zagi uban ta ba, domin kuwa komai tsiya surukin kine uban mijin ki, kinzo karbar junior ko dake sanda aka Auro ki da junior kika taho daga gidan ku, to bari kiji na gaya Miki, ko shi uban junior bai isa ya karbe sa a hanuna ba, bare kuma ke, idan baki sani ba ki sani ba bana kaunar ki a bisa dole da kuma kaddara yasa Khabeer ya Aure ki, domin nasan Babu ta inda za'ace ya'yan Hauwa suna da tarbiya, na fiki sanin wacece Uwar ki, a tafin hanuna take, junior baxai kara kwana a wannan lalacaccen gidan ubannaki ba, gidan da babu tarbiya a cikin sa, kije ki sa mijin naki yaxo ya daukar miki shi.


  " Momy Sarah da tun daxu take jiyo hayaniya yasa ta fitowa da sauri, kusan tare suka fito da mamy tana rike da Hanun junior,


   " Maman Khabeer lfy nake jin hayaniya cewar Momy Sarah, Zuhura yaushe kika zo gidan nan.


  " Momma ce tace, tun dazu taxo tana mana diban Albarka wai taxo tafiya da junior harda cewa zata ci uban Hasina.


  " Zaro ido Momy Sarah tayi, tare da jin dadi a cikin zuciyar ta, ta dai ci uban naku, tunda danki ya Hanan zaman lfy, kema ai ga matar sa ta hana ki, zama kalau, kema kiji yanda nake ji a Raina.

    Amma a fili cewa tayi haba ke kuwa Zuhura, wannan fah surukar kice, kike yiwa rashin kunya, ki gyara Halin ki zuhura, bakya abu mai kyau, ai nan ma gidan uban junior ne.

 

  " Juyawa Zuhura tayi da niyar ficewa daga gidan sai taji muryar junior yana cewa.


   " Ummi, ki cewa daddy ya kawo min keken da yace idan naxo na daya a ajin mu zai saya min.

   Ki ce masa nine first class.


  " Tsuka Zuhura taja, ita duk a tunanin ta, junior cewa zaiyi zai biyo ta, ficewa tayi ba tare da ta tanka masa ba.


  " Itama momma komawa kitchen tayi taci gaba da aikin ta.


  " Yayin da Momy Sarah ta koma daki tana dariyar mugunta.


  

   Misalin karfe goma da rabi Khabeer ya shigo cikin gidan bai tsaya neman Zuhura ba domin bayi da Time yanxu, fita zai kara yi, zasu je gidan Hajiya Hindatu bincike.

  Wanka yayi tare da shiryawa cikin kananan kaya, takalmin sau ciki ya tsugunna ya daura tare da soka karamar bindigar sa a cikin takalmin, yayin da ya rike daya a Hanun sa, sha daya daidai yabar gidan.


  " Itakuwa ZUHURA tana chan bedroom din ta tana zaman jiran sa, domin kuwa ya zata nuna masa iyakar sa a gareta, kamar yanda iyayen sa, suka zagi nata iya'yen a gaban ta haka itama zata zagi nasa iya'yen a gaban sa.


  " Babu kowa a kofar gidan Hajiya Hindatu, da alama ma dai kamar gidan a rufe yake, sanda suka taba ne suka tabbatar da a rufen yake, kallon Nazeer da Ibrahim da kuma gedion yayi, yace daya ya tsaya a Nan daya kuma yayi gefen can ya tsaya, daya ma yayi ta gefen can, kai kuma kamal da kai da mustapha da Dalladi zamu haura mu shiga cikin gidan, fara haurawa kamal sai wannan munafikin Hukuman ya biyo ka, wato Sargent Umar, ka tabbatar ka yi setting dinsa da bindiga kafin ya hauro idan yayi kokarin guduwa, na baka ixinin ka dauke sa da bindiga.



  Bayan sun gama haurawa ne, suka nufi dakin nata, shima dai still a rufe, dafe kansa Khabeer yayi, yace ina zamu sami ko kusa ne mu bude dakin nan dashi.


  " Mustapha ne yace, akwai a wajena oga.


  " Karba Khabeer yayi tare da kokarin bude dakin, cikin ikon Allah kuma dakin ya budu,


  " Bincike suke a dakin domin suna bukatar ko basu sameta ba su sami wani shaidar da zasu iya gane ta dashi.


  " Bedroom din ta Khabeer ya shiga, babu inda bai bincika ba, baiga komai ba, wanda zai taimaka musu a bincike su, hankalin Khabeer ne yakai kan wani dan karamin photon Hajiya Hindatu da Momy Sarah dake kife, wajen hoton ya nufa, har ya sunkuya zai dago hoton yaji muryar Kamal na kwala masa kira a falo, fasa daukar pic din yayi, ya nufi falon, wani karamin photo na Hajiya Hindatu ita kadai tana murmushi kamal ya mikawa Khabeer, karba Khabeer yayi tare da karewa pic din kallo, kara zurawa pic din ido yayi sakamakon hango dantsen hanun Hajiya Hindatu da yayi Anyi zanen Ant (wato cinnaka) a gefe kuma anyi wani dan karamin Rubutu wanda sai ka nutsu sosai ka gane mai ka rubuta, group shine a rubuce jiki.

   Murmushi Khabeer Yayi yace mun samu shaida, mai wahalar ganewa, wato mutanen nan ba iya miyagun kwayoyi suke safara ba, da akwai wani abunda suke bayan wannan, idan har tunani na yazo dai, harda yara da yan mata suke safara, domin kuwa kungiya ce da su, mai Alamar 🐜 ant .

   Mu koma office tabbas akwai a hanun wannan markel din, muje mu gani.


  

  " Akwai kuwa zanen 🐜 a hanun sa , rike kansa Khabeer yayi yace wannan babban case, ne dole mu nemi jami'ai na mussaman domin kuwa baxamu saurarawa duk wanda muka samu yana da hanu a cikin wannan kungiyar ba, koda kuwa waye ne shi.



************************* 

Washe gari da safe na hango Nasreen dauke da tulu ita da indo sun dauko ruwa suna dawowa, tadin su suke gwanin sha'awa domin shakuwar indo da Nasreen ta wuce a kirata da Abota sai dai ace Aminta.


  " Jungudo dake biye dasu ne a baya, wanda su basu san da hakan ba,


  " Yar gwal ne ta taho ta gaban su zata wuce, hanyar Nasreen ta yiwo saboda neman magana, ita dai burin ta, taga tayiwa Nasreen asarar tulun ta, ganin haka da Nasreen tayi ne yasa ta kauce daga hanyar, ta koma gefe.


  " Kara biyo ta yar gwal tayi, da karfi ta bige Nasreen kafin indo ta ankara Nasreen da tulun ta sunje kasa, shikam ma tulu ba'a maganar sa domin kuwa yayi raga raga ya fashe.


  " Cikowa idon Nasreen yayi da hawaye, ta kasa magana sai kallon yar gwal dake sheka mata dariya.


  " Indo ce tace haba yar gwal ki duba fa abunda kika Mata, duk hanyar da take wajen nan bai isheki ba sai kin biyo ta wajen ta.


  " Ko kafin yar gwal tayi magana, taji an hada ta da kango shake mata wuya jungudo yayi, sanda idon ta ya firfito, kafofin ta ya kwasa yayi kasa da ita ji kake gum yar gwal tasha kasa, da karfi ya taka kafofin nata, k'as k'as k'as kafofin yar gwal sun karye, Cikin magana ta mashaya yace, wannan kadan na miki, idan baki fita harkar Nasreen ba, sassara ki zanyi.


  " Cikin bacin rai Nasreen ta wankawa jungudo mari.


  " Zaro idon ta indo tayi tare da rike bakin ta.


  " Ina runka da abunda ta min yar uwata ce, koma me tamin munfi kusa.


  Shafa inda Nasreen ta maresa yayi tare da yiwa Hanun sa kiss yace naji dadin wannan marin da kika min ko ba komai zanyi farin ciki Hanun masoyiya ta ya taba fiska ta.




Share

     And

         Comment



Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


     (Ummu Nasmah)[11/17, 5:50 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳

Story 


     And


        Writing


            Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)



___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم

🤳🏻 


08147537180



  Godiya


Na gode sosai masoyana yan uwana masu kaunar book dina, na gode sosai Ubangiji ya karfi addu'ar ku, Aikin da nake nema na samu, nasan Allah ne ya amshi addu'ar ku da ta iya'yena Babu abunda zance muku, sai godiya.

    Da wadanda suka kira ni ta waya suka min sannu da jiki, alhamdulillah jikina yayi sauki sosai na gode Allah ya bar kauna.



  Sadaukarwa

  

Ga duk wani masoyina dana littafi na da wanda na sani dama wanda ban sansu ba, wannan page din naku ne kuyi yanda kuke so dashi. Domin ina jin dadin comment dinku.

  


P•••••••••••1️⃣9️⃣ to 2️⃣0️⃣


Jijjiga yar gwal Nasreen take Cikin tashin hankali, take cewa " kiyi kokari ki mike dan Allah muje gida.


  Sunkuyawa Indo tayi tace, " bafa zata iya tashi ba, domin kuwa ta karye, Abunda yafi kawai ki tsaya a nan naje na kira Mama.


  Dago idanun ta da suka rine suka koma kalar red tayi, tace " na shiga uku Indo, jungudo ya jawo min masifa, Nima Mama karya ni zatayi, wlh yau Babu mai kwatata a hanun Mama sai Allah.


  " Kin gama magana tunda kika ce Allah, bari naje na kira Maman na dawo, ina ga zaifi tsayawa bata lokacin da mukeyi.


  Bayan tafiyan Indo ne kiran Mama, Nasreen ta dago kan yar gwal ta daura a saman cinyar ta, sai sannu take mata, tana cigaba da kuka mai tsuma zuciya.


  Itako yar gwal azaba ma ya hanata kuka ita kadai tasan mai take ji a kafarta.


   Suna cikin wannan Halin ne Mama ta taho a guje ta sunkuya akan yar gwal tana cewa, " meya same ki Amina, dake haka ne Asalin sunan yar gwal, waya karya ki, ki fada min mana kinyi shuru.


  Hawaye ne kawai suke zuba a idon yar gwal, Domin kuwa bata da bakin magana.


  Sunkuyawa MAMA tayi ta goyi yarta, sukayi gida, a kofar gida suka samu Baba yana zaune rike da carbi yana tasbihi, da sauri ya tashi yace Lfy Salame meya sami Aminatu.


  " Mlm kawai kaje ka kira mana mlm Iro mai daurin karaya, naji ance ya dawo daga binni, kuma daurin sa yafi kyau.


 " Subahanallah Bari naje na kira sa yanxun nan ki shiga bari naje.


  Baba da mlm Iro tare suka shigo cikin gidan,

  Cikin kwarewa mlm Iro ya daura kafan yar gwal, yayin da taci bakar Azaba a wajen daurin.


 kudi dubu Hudu Baba ya basa, amma mlm iro yaki karba, yace Ai mlm Musa kafi karfin na karbi kudin ka, ka barshi kawai nidai fatana daurin Yayi kyau.


  " Na gode sosai mlm iro, mutanen da ka hada ni dasu, gidan da kake Aiki acan binni kafin na dawo sunce min zasu turo dansu yaxo yaga wajen zamana da kuma yanayin kiwon nawa, kuma har yanxu naji shuru babu labarin sa.


       Dariya mlm Iro yayi " yace, oh Khabiru ne, karka damu zaizo, kasan yaron jami'in tsaro ne babba bai cika zama a cikin wannan kasar tamu ta Nigeria ba, kullum yana sama kamar tsuntsu, yana hanyar kasashen waje, yanxu haka idan ta dauro baya kasar nan, amma tunda sukace zaizo to zaizo din.


  " Shikenan mlm Iro Allah ya kawo sa lfy, nima hankali na zaifi kwanciya yaxo yaga inda nake zaune.


  " Mutanen basu da matsala fah tunda sukace zaizo to zaizo Nima da kake ganina baxan koma binni ba sai yaxo mu koma tare.


 " Shikenan muje nima wajen goggo nake son zuwa, rabona da ita tun jiya, ina son ma na biya lanbun mlm sale, tunda na dawo shima bamu samu mun hada ba.


  " Tare suka fice inda Baba ya fara biyawa lanbun mlm sale.


  Sati daya da daurin karayar yar gwal, amma kullum babu wani sauki saima wani karin zogin azabar da take sha, wuni take tana kuka tare da kiran mutuwa, hankali Mama yanxu sam baya kwance, neman lafiyar yarta take, duk inda taji mai magani sai taje ta, Amma hakan bai hana mama gallazawa Nasreen Azaba ba, saima karin wani da ta samu.


  Nasreen na hango zaune da tarin wanki a gaban ta, gama diban ruwan ta kenan mama ta kawo mata su, ga kuma wanke wanke da shara shima yana jiran ta.

   Tayi baki ta lalace, Idan kasan Nasreen a baya, to yanxu idan ka ganta baxaka gane ta ba, domin kuwa duk wahala ta kodar da ita, Baban ma da suke samun sauki a wajen sa yanxu ya watsar dasu, shima kullum yana cikin hantarar su.

   Ta fara wankin kenan taji shigowar Nuruddeen da gudu yana kuka.


  Kiran sa tayi, ya taho wajen ta.


  " Meya same ka Nuruddeen?


  Cikin kuka " yace Adda Nasreen, yanxu naje gidan Goggo na samu ta watsarwa da Nabiya kayan ta waje tace mata wai tabar mata gidan ta, wai mune shegu wanda aka barwa abin kunya, tace nima idan na sake zuwa gidan ta, sai ta yanka Ni.


  Dafe kirjin ta Nasreen tayi tace " Goggon ce tayi haka, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un la'ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minazzalimin allahumma ajirni fil musibati.

   Yanxu ina Nabiya take?


  Ta dauki kayan tayi hanyar barin rugar nan, tace nace Miki kiyi hkr, ki yafe mata, idan akwai laifin da ta miki, wai baxata kara dawowa rugar nan ba, tace min wai sai wata Rana.


  " Na shiga uku Na shiga uku wani irin masifa ce take damun rayuwa ta, kullum ina cikin bakin ciki, sam babu farin ciki, a cikin Rayuwata, shin yaushe ne zan samu SAUYIN RAYUWA? Yaushe zanyi rayuwa kamar ta kowacce d'a ? Yaushe zan samu farin ciki? Da karfi tace sai yaushe?


    Da gudu MAMA ta fito, cikin fada tace meya haka kike min ihu a cikin gida dan ubanki.

  Daman kina da farin cikin rayuwa ne, a baiwa kika zo duniya kuma a haka zaki koma, ni kimin wanki na, ko kuma naci ubanki.


   Nasreen Bata  tsaya sauraron Mama ba ta fita da gudu, domin taje ta tare Nabiya daga barin rugar, bayan ta Nuruddeen yabi da gudu shima.


  " Gudu Nasreen take tana kwala kiran sunan Nabiya amma shuru Babu amsa, bata san Nuruddeen yana binta a bayan ta ba, sanda taxo har Karshen wajen fita daga rugar, babu Nabiya, Babu Alamun ta, waje ta samu ta zauna, tare da fashewa da kuka mai cin rai, kukan ta take Babu mai rarrashin ta, kamar wanda akace ta dago idon ta, mota ta hango daf da Nuruddeen yayin da shi kuma yake tafiyan sa baima san da wata mota a bayan sa ba.


  " Nuruddeen ta kira sunan sa da karfi, sai dai kash bai jita ba, ganin hakan da tayi ne ya sata tashi da gudu ta nufe sa, amma sai dai ina kaddara ta riga fata, domin kuwa motar nan ta taka Nuruddeen.

   Ihu Nasreen tasa tare da daura hanun ta a kanta, da gudu ta karasa wajen, ko kafin ta isa mutane har sun taru a kansa.

   Jini ne malale a wajen, domin kuwa kan Nuruddeen ya tsage, Kullu Nafsin za'ikatul maut. A take Nuruddeen ya koma ga mahaliccin sa, ko shurawa baiyi ba.


 Kasa kuka Nasreen tayi, saima dago sa da tayi ta manna sa a kirjin ta, tafi 30 minute tana shuru kafin da karfi tace " Mama Baba Goggo kune sanadiyar Rasa yan'uwana a lokaci guda, daga farko na Rasa AMMI na gashi yanxu ma na rasa Nabiya kaima Nuruddeen ka tafi ka barni ya kuke so nayi da Rayuwata, ku kadai nake kallo naji dadi kune masu debe min kewa, kune Yan uwana kuma kawaye na, daku nake shawara kune kadai nake iya gayawa damuwata, gashi kun tafi kun barni, ni kadai, mama goggo Baba, baxan taba yafe muku ba, daga yau nayiwa kaina alkawarin tashi na nemi ilimin, shari'a zanyi ko wacce irin bauta ne  idan har zan samu kudin da zan biyawa kaina kudin makaranta, domin kuwa dole na dauki fansar jinin dan uwa na da kukayi sanadin barin sa duniya, Dole zan bar kauyen nan bayan Anyi sadakar bakwai dinka Nuruddeen domin zamana a cikin wannan rugar bata da Amfani, tunda babu ku a Cikin ta.

  Na dauki kaddara Nuruddeen zanci gaba da maka addu'a har Karshen numfashi na.


 Mazan wajen ne suka daukesa sukayi gidan su dashi.


  Shi kansa Baba yayi jimamin Rashin Nuruddeen, yayi kuka sosai, kwanar keso Nuruddeen yayi washe gari da safe misalin goma akayi sallar jana'izar sa.


  " Nasreen bin kowa dake wajen take da kallo, domin kuka ma ta kasa yinsa ita kadai tasan mai take ji a cikin zuciyar ta, 

 Har akayi sadakar ukun Nuruddeen Nasreen bata kula kowa, iya kacin ta amsa gaisuwa, indo dawowa tayi gidan su Nasreen da kwana, kullum tana cikin rarrashin ta da bata baki.


  " Itako Nabiya daman akwai yan kudi a hanun ta, cikin dukku ta nufa darect anan ta kwana washe garin ta je tasha motar da zai kaita  cikin garin Gombe ta hau.


  Karfe shadaya ta isa cikin garin Gombe, bayan sun sauka ne, Nabiya ta nemi waje cikin tashar ta zauna tare da rafka Uban tagumi tana tunanin yan uwan ta, ga wata bakar yunwar da ta dameta kuma bata da ko naira biyar din da zata siyi pure water bare kuma ace abinci.

    Wuni tayi kas acikin tashar yayin kowa yake harkar gaban sa, Babu wanda ya kalle ta.

  

Hajiya Hindatu da yanxu kamannun ta suka sauya sakamakon tsaga fiskar ta da Momy Sarah tayi ne, ta hango Nabiya, ta dade zaune cikin motar ta tana karewa yanayin Nabiya kallo, a zuciyar ta, ta ayyana cewa wannan yarinyar tayi daidai da irin yan matan da Momy Sarah tace ta samo mata, koma daga ganin Alamun ta, tana cikin Halin damuwa, bari naje kawai ta hanyar taimakon ta, na bata wajen Zama a gida na, kafin daga baya musan abun yi. 

  Bude murfin  motar tayi ta fito.

  Amma sai dai Kash kafin Hajiya Hindatu ta samu damar karasawa wajen, Nabiya, taga wata farar mota, mai tintak glass ta tsaya a gaban ta, ta bude mata motar ta shiga, sannan ne mamallakin motar yaja suka bar wajen.


  " Oh cewar Hajiya Hindatu, waye wannan yamin shigar tsaye, yamin asarar makudan kudade.



*************************


 Kwanan Zuhura biyar tana gaba da Khabeer wanda shi baisan gabar me take dashi, ba, tunda yasan Basuyi fada ba, sai dai ya kudurce a ransa cewa shima bazai kulata ba har sai ta sauko da kanta ta neme sa.


  Yau da sassafe ya shirya ya fito da niyan zuwa RUGAR ARDO BOYI Aiken Daddy, kiran Kamal yayi a waya bayan Kamal ya daga ne, Khabeer yace " zanyi tafiya yau zanje wani kauye, kuma ina ga zan kwana biyu acan, na nemo excuse agun oga,  ina so kuci gaba da binciken nan karku tsaya  jirana, duk abunda yake faruwa ka Kira ni nasan ka da kokari na kuma yarda dakai 💯 shiyasa na jagorance ka a wannan Aikin, karka bari a samu matsala.

   

  " Insha Allah oga zamuyi iya kokarin mu, kafin Allah ya dawo dakai, dan mun fara samun good information agun shi markel din.


  " Okay aikin ku yana kyau,  sai na dawo Koh.


  Adawo lfy Kamal yayiwa ogan nasu sannan ya katse kiran.


Ita ko Momy Sarah hankalin ta ya fara tashi, domin kuwa tana da labarin zuwan su khabeer tsohon gidan Hajiya Hindatu tasan kuma tunda Khabeer ya gane tsohon gidan Hajiya Hindatu, tofa Dole saiya nemo ta, zai kuma iya gane ta domin kuwa wayon bala'i ke gareshi.

  Gara ta nemi hanyar da zata kawar da hankalin sa, daga wannan bincike, ba kuma ta kowacce hanya bace sai ta hanyar batar da junior.


 Wayar ta ta dauka ta dannawa, Ajabo kira.


  Ringing daya Ajabo ya daga, kirari yayiwa Momy Sarah kafin yace Hajiya Saratu, me kike bukata a gareni.


  " Ka saurare ni da kyau Ajabo, aiki zan saka, zan kuma biyaka dubu dari biyar 500,000  sai dai Aikin yana da matukar hatsarin gaske.


  " Dariya Ajabo ya bushe dashi sanda yayi mai isar sa kafin yace babu aikin da zai bani wahala indai ta fannin kidnapping ne ko kuma kisa, fadi kawai daya a ciki, wannan kike bukata daga gare Ni.


 Ajiyar zuciya Momy Sarah ta sauke sannan tace " junior nake son ka sace min shi na turo maka photon yaron ta WhatsApp dinka, yana karatu a makarantar matrix academy, Ranar Monday nake so ka dauke sa, jibi kenan, ka ajiye shi a wajen ka, kafin nasan abunda zanyi akansa.


 " Wannan karamin Aiki ne Hajiya Saratu, kisa a ranki nama dauko sa yana hanuna




 Tirkashi tofa ana wata ga wata, shin ya rayuwar Nasreen zata kasance, bayan Rasa yan uwan ta?


 Shin waye ne ya dauki Nabiya a mota?


Shin Khabeer zai hadu da Nasreen kuwa domin gashi munga yana shirin tafiya rugar su?


Shin Momy Sarah zatayi nasarar sace junior kuwa?

Idan kuma har tayi nasarar sace sa, shin Khabeer zai dakatar da binciken kuwa?


Kuci gaba da biyo ni domin warware muku amsar tambayar ku



Abunda yasa na muku typing kadan waccan page din comment dinku yayi kadan shiyasa nima na muku typing kadan, domin kuwa More comment more typing.




 Share

    And

      Comment


Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


    (Ummu Nasmah)

[11/20, 10:24 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

           ⛏⛏⛏⛏

   SARA DA SASSAKA

       (Baya hana gamji)          

                  Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

           🌳🌳🌳🌳


Story   And  Writing 


               By


 Rasheedat Usman

 (Ummu Nasmah)



بسم الله الرحمن الرحيم



P•••••••••••2️⃣1️⃣ to 2️⃣2️⃣


🤳🏻

08147537180

___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________


 بسم الله الرحمن الرحيم

       


Sadaukarwa gareku kungiyar KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻 kungiya mai hadin Kai babu wanda ya isa yaji tsakanin mu.

   Muna posting fans suna jin Dadi muna bari suna jin haushi Allah ya kara mana tunani tare da basira.


Aunty fauza yar Amana uwar mu gatan mu, Allah ya kare mana ke daga sharrin mahassada.


Real Nana Aisha

Marubuciyar 

(Rayuwar muce haka)


Ummu Fatuma marubuciyar

(Dija kaya)


Aunty Hauwa

Maman Uswan

Marubuciyar

(Makauniyar Rayuwa)


Ummu Hafeez

Marubuciyar

(Komai muk'addarine)


Real Maryam

Marubuciyar

(Iyayen mu a yau)


Hauwa'u Salisu

Marubuciyar 

(Mamana ce)


Zarahn Abdul Momy Ahlan

Marubuciyar 

(Gudu ajeji)


Surayyah B Abdul

Shuryn Khan

Marubuciyar 

 (Soyayyar fari)


Fauziya sale madaki

Marubuciyar

(Rayuwar Amatullah)


Aunty mamie

Marubuciyar

(Matar Fari)


Smart Feenat

Marubuciyar

(Wahala da gata)


Fatuma sardauna

Marubuciyar

(Shu'umin Namiji)


Sadaukarwar page din nan gaba daya naku ne kuyi yanda kuke so dashi. 



📝🖊️


Daga ido Nabiya tayi domin sake kallon matar da ta dauke ta, hada ido sukayi, Nabiya tayi saurin saukar da idon ta kasa.

  Murmushi matar tayi tace" yan mata, meyasa ina bude miki mota kika shiga ba tare da tunanin ko zan cutar dake ba?


  Cikin sanyin murya tace saboda ina bukatar taimako, a Halin da nake ciki tun fitowa ta daga gida babu abunda naci, yunwa tana damuna sosai, kuma ina tunanin ke ba matar da zaki cutar da wani dan Adam ba ne.


 " Haka ne, ni sunana Aishatu ina da zama a cikin unguwar New GRA ina da yara Hudu, IBRAHIM shine Baban dana yana da mata harda yara biyu, sai sajida itama tayi Aure tana da yaron ta daya Hafeez, sai Sadiq, sannan Kuma auta Khadija wacce za kuyi sa'a da ita, suna Kira na da Hajiya.

  Dawowa ta daga Aiki kenan yanxu, sai na hango ki, kuma naga alamu  kamar kina cikin damuwa, shiyasa na tsaya domin taimakon ki.

  Da fatan banyi laifi ba.


 Murmushi Nabiya tayi tace " Babu wani laifi, saima godiya daya kamata ace na Miki.


  " Okay Bari mu karasa gida kiyi wanka kici abinci, Idan kin huta zaki bani labarin ki.

  Zaki iya kira na da Hajiya kamar yanda yarana suke kira na dashi.


  To Hajiya na gode Allah ya saka da alkairi.


Da ameen Hajiya Aisha ta amsa, 

Babu wanda ya kara magana a cikin su har suka karasa gidan Hajiya Aishatu dake unguwar New GRA.

 

Sun sami Sadiq da Khadija wacce suke kira da khady zaune a falon Hajiya suna kallon series film da MBC Bollywood sukeyi mai suna لكنه لي

Da gudu Khady ta tashi ta rungume Hajiya, 


 " Oyoyo Hajiyar mu, yau kin dawo da wuri, nayi zaton zaki kai 1:30 sai kuma naga kin dawo da safen Nan.


  " Kudai Bari Auta na, kinsan Aikin Night dinnan wahala garesa, sai mutum ya kwana Babu bacci, shiyasa gari yana wayewa na nemi excuse na dawo na samu nadan samawa idona hutu.


  " Kinyi dai dai Hajiya ni dama kinbi maganar Abba ki ajiye aikin nan kawai, ki samu ki hutawa Rayuwar ki.


Sadiq ne yayi caraf yace " Hajiyar ce zata ajiye wannan Aikin kima daina Bata yawun bakin ki,

 Koda yake watakil zata ji maganar Abban tunda sweet heart dinta ne.


  " Dankwalon 🖐 sa Hajiya tayi tace kaci gidan ku, Naki nabi maganar Abban naku, Babu wani hutu da zanyi domin kuwa nasan muhimmancin aiki na, bawai ina aikin nan dan na samu kudi bane, ina yine kawai domin na tallafawa mata yan uwa na, mussaman a Yanxu da likitoci basa kula da mace wajen haihuwa da kyau, ya kamata ace zuwa Yanzu kun gane manufar Aiki na.


 " khady ce tace Hakane Hajiyar mu, na fahimce ki, kuma baxan kara miki maganar ki ajiye Aiki ba.

   Kallon ta ta mayar kan Nabiya tace sannu da zuwa.


 " Yawwa sannu cewar Nabiya, na sameku lfy.


" Lfy lau and you


 Shuru Nabiya tayi kasancewar bata iya yaren turanci ba.


 Sadiq ne yace " Hajiya a ina Kika samo beautiful baby, haka.


" Hararar sa Hajiya tayi t tace ban sani ba sarkin yan iyayi.


 " Allah ya baki hkr ni ba bakon zafi bane, kinga ma wucewa ta school.


 " Allah ya kiyaye a dawo lfy manga na, idan ka dawo zan fada maka wacece ita.


  " Okay bye.


Hajiya Aisha ne tace " kinga Auta kaita dakin ku, tayi wanka idan ta fito ki bata kayan ki ta saka, akwai abinci ne?


 " Ehh Hajiyar mu Akwai sauran breakfast.


" Okay to idan ta shirya sai ki bata Abincin taci, zan shiga ciki, sai Azahar zan fito, idan na fito zamuyi magana.


 "A Fito lfy Khady tace, tare da kama Hanun Nabiya sukayi dakin ta,

 Toilet ta kaita darect tare da nuna mata yanda zatayi Amfani da abubuwan cikin toilet din, sabon brush teeth ta bata, shima dai sanda ta taimakawa Nabiya sannan ta gane yanda zatayi amfani dashi, kasancewar tafi gane tayi brush da gawayi da lallai da kuma alumun.

Da kanta Khady ta wankewa Nabiya gashin kanta towel ta nuna mata tace idan kin gama  karki mayar da kayan jikin ki, ki daura wannan  sannan ne ta fita ta barta a toilet din domin tayi wanka.

  Tayi wajen Awa 1 a toilet din tana gurzar jikin ta sannan ne ta fito daure da towel din.


 Murmushi Khady tayi, Ganin yanda Nabiya tayi wanka fes da ita, tashi tayi tace " sister kinji bakin ki, ya Miki dadi ko, dan Gaskiya brush yafi gawayi wanke baki da kyau.


 " Gaskiya ne Khadija nima naji bakin nawa ya min dadi, sai dai abun ya cika zak'i da yawa.


 " Kardai kin shanye baki zubar da kunfan ba.


  " A'a ban sha kunfan ba, amma dai gsky da na gama na dan totsi kadan.


 " Murmushi Khady tayi tare da kada kanta, tace to karki kara sha, ba na sha bane baki kawai ake wankewa dashi.


 " Shikenan Khadija baxan sake ba.


 " Ki kirani da Khady sister nayi gane hakan, yanxu dai ganan mai ki shafa, sai nazo na miki make up din ko, kafin nan bari na dauko Miki kayan da zaki saka ko.


  ************************

Karfe shadaya dai dai a cikin Rugar Ardo tayiwa Khabeer da kyar da kwatance ya gane rugar, bayan shigar sa rugar ne ya rasa ta ina zai fara neman gidan jauro jatau, yayin da yara suka zo suka bi motar da kallo,  indo ya hango tana tafe rike da sanda a Hanun ta, tana kora shahanu.

  Bude murfin motar yayi tare da nufa wajen ta, " salamu alaikum yan mata.


  " Dago idanun ta Indo tayi, tace Ameen wa'alaiku mussalam kwod'o. (In ance kwado ana nufin bako da harshen fillanci).


 " Murmushi yayi kasancewar shima bafulatanin ne, yana ji kuma ya iya, shima cikin Fillancin yace mata, sannu da Aiki, ina dan neman taimako ne daga gareki, ko zan samu?


 " Taimako Kuma a waje na kwod'o amma fada min naji ko zan iya maka.


  " Gidan jauro jatau nake nema ko zaki nuna min?

 

" Gaskiya kwod'o kayi hkr bansan kaba, kaga baxan nuna maka gidan mutane ba, kalli moton ka da kaxo da ita mai kyau irin na masu yankan Kai.


  " Zaro ido 😳 Khabeer yayi yace masu yankan Kai ne suke da mota mai kyau.


 " Ehh mana ai ance sune masu kudin binni, kaga kar rana tamin zan tafi kiwo na, kaga nagge na har sun fara jin kishin ruwa.


  " Yanxu kina so kice baxaki nuna min ba kenan kin san dai dani dan yankan Kaine da tun daxu na sace ki.


 " Ka sani ko baffah na ya min kariya da irin ku.


 " Dariya Khabeer yayi yace Baffahn ki bai isa ya miki kariya ba, sai dai Allah ya kareki, please tell me dan Allah.


 Hakane kuma fah, to amma naji kamar kamin yaren turanshi kasan ban iya jin turanshi ba, Da mun shiga makarantar bokon har munje aji Uku Aradun Allah na daina, saboda mlm zakariyya mugune kullum sai ya zana mufa duka ajin idan mutum daya yayi laifi Aminiyata ce, Nasreen taci gaba da zuwa har taje aji biyar, Maman ta, ta hanata. 

  Meye ne plash toll mo din ka gayan da fillanci dan Allah.


 Dariya ce ta kwacewa Khabeer, sanda yayi mai isar sa sannan cikin harshen fillanci yace " cewa nayi kiyi hkr ki gaya min gidan.


 " Amma sai ka fada min gurin wa kaxo a cikin gidan jauro jatau din.


" Har yanxu dai baki yadda dani ba kenan, to shikenan, wajen mlm Iro naxo, wanda yake aiki a birni.


 " Washe bakin ta Indo tayi tace oho sai yanxu ma na tuna da cewa kawu Iro yana zuwa binni, muje to na kaika gidan kasan kawu nane shi wan Inna na.


 "  Masha Allah kice igiya ta cinke a gidin kaba kenan to Su naggen naki fah Yaya zakiyi dasu.


 " Karka damu dasu Babu abunda zai same su anan, kaga chan kanwata ce zata kular min dasu kafin na dawo.


 " Shikenan muje to ki hau mota ta mu karasa gidan ko.


  " Kada kanta tayi tace a'a bazan hau moton kaba kaxo kawai muje da kafa babu mai daukar maka moto, idan yaso daga baya sai ka dawo ka dauki abun ka.


  " Muje to baxan miki musu ba bare kice baxaki raka niba, dan nasan hanyar da kike nema kenan. 


  " Dariya Indo tayi tace kwod'o ka cika zolaya.


 " Karki kara cemin bako, sunana Khabeer.


 " Nikam baxan kira sunan kaba kwod'o zance maka, kaga muna surutu har mun iso gidan bari na shiga na maka magana da shi.


 Da to Khabeer ya Amsa mata sannan ya samu dakalin kofar gidan ya zauna.

 Ita kuma ta shiga.


 Tare suka fito da mlm Iro, cikin farin ciki, yace khabiru yau kaine a garin namu,.


 " Nine Baba, hanu ya mika masa sukayi musabaha.


 " Lale !! lale !! Lale marhaban, sannu da zuwa ya su Alhajin da sauran iyalan.

 

 " Suna lfy Baba Daddy ne ya aiko ni maganar shanun momma da aka bayar da kiwon su, anan rugar taku.


 " Kwarai kuwa khabiru nasan zancen, yanxu dai tashi mu shiga cikin gidan ku gaisa da iyalai na, sai kaci abinci ka huta ko, idan munyi Azahar sai muje can wajen mlm musan da Naggen Hajiyan suke wajen sa.

  Acan ma zaka sauka zuwa kwana biyun da zakayi, zaka fi ganewa idonun ka abunda yake tafiya.


 " Shikenan Babu damuwa, hakan ma yayi.


************************

Saude !! Saude !! Saude wai ina kika shiga ne kam.

  Shurun da taji ne yasa ta nufar boss cutter wajen Zaman su Saude.

     da karime ta fara haduwa, tana wankin kayan ta, cikin fada tace ke karima ina wannan Bagidajiyar kauyen take, ta barni  ina ta faman kunfar baki wajen kiran ta.


  " Cikin ladabi karime tace barka da fitowa ummin junior.


  " ✋ Bashi na tambaye ki ba cewa nayi ina wannan Bagidajiyar kauyen take Saude, ko sai na kara maimata miki ne.


  " Tana cikin daki tana bacci daxun nan bayan ta gama miki Aiki ta shiga ta kwanta.


  " duba agogon wayan ta tayi, 12:00 am kada kanta tayi tace, bacci yanxu, uban wa ya bawa baiwa lokacin baci yanxu, to maxa kije ki tasan mini ita yanxun nan ku same ni a falo na, sannan ta juya ba tare da taji amsar da karime zata bata ba.


  " Kada kanta karime tayi a fili tace Allah ya kyauta, sannan ta shige kiran Saude.


  " Da sallamar su kuwa suka shigo falon.

  Bata amsa musu ba, sai ma tabe baki da take faman yi.


  " Zaman dirshan sukayi saude tace Gani ummin junior.


  " Tsawa ta daka mata tace, yaushe Khabeer ya bar gidan nan, kece kawai kike shigowa part din nan da asubar, dan haka gaya min yaushe ya fita.


  " Ajiyar zuciya saude ta sauke, tare da hamdala ganin ba laifi tayiwa uwar gijin nata, magana ta fara a cikin nutsuwa tace ummin junior, ina ga 9:15 yabar gidan nan naji kuma kamar yana waya da wani yana cewa zaiyi tafiya ne, kuma zaiyi kwana biyu acan.


  " Cikin bacin rai Zuhura tace ku tashi ku bace min da Gani anan.


 Tashi sukayi suka fice abunsu, dama kiris suke jira.


 Cije yatsan ta Zuhura tayi tace lallai kam wato shi mutumin fita yayi a harka ta saboda nayi fushin da shi, tabbas kuwa tashi tayi taje dakin sa, drowarn mirror taja inda yake ajiye kudina sa, 

  Kudine a shirye cikin drowarn, rafar yan dubu dubu ta dauko guda biyu wanda idan aka lissafa, rafa biyun da ta dauka zasu kai kimanin dubu dari biyar, juya su tayi a hanun ta, tace yanxu na fara diban kudin ka Khabeer har sai ka fara tunanin Aljanu ne suke debe maka, tunda har ka fara nuna min nida banza daya muke a wajen ka, Namiji Allurar Kaya, na miji ba dan goyo ba.

 Zamu zuba mu gani Khabeer, ina dai dai daku da wadannan yan iskan iya'yen naku.


  Haka take ta maganganun ta kamar wacce Khabeer din ke tsaye a gaban ta.



Kumin hkr dan Allah, bana jin dadin jikina ne shiyasa bakwa ganina akai akai yanxun ma daurewa kawai Nayi na muku wannan dan guntun page din.


Please ku sani cikin Addu'ar ku yan uwa, Allah ya bani lfy.



Share

   And

    Comment



Alkalamin Rasheedat Usman 📝

  


    (Ummu Nasmah)

[11/23, 6:26 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya Hana Gamji)

              Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


Story And Writing

           

           By


            Rasheedat Usman


(Ummu Nasmah)


    🤳🏻

                    08147537180



                 *﷽*


Godiya

Ina godiya gareku masoyana da addu'ar ku gareni da yawanku kun kirani kummin sannu da jiki na gode sosai Allah ya bar zumunci kuma alhamdullilah jikina da sauki sosai. 

  

Maryam Adamu ibrahim na gode sosai da katin da kika turo min allah yabar zumunci.

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



P••••••••2️⃣2️⃣ to 2️⃣3️⃣


Kira ta dannawa umma ringing daya umma ta daga wayan.


  " Ya akayi Zuhura har yanxu banga sakona ba, kinsan dai Hajiya rukayya ta dame ni akan kudin ta ko.


 " Kiyi hkr Umma yanxu haka akwai kudin dana diba a dakin Abban junior, zai kai kimanin dubu dari biyar, ki turo min Saleemat tazo yanxu ta amshe su, kafin ya dawo, zaki dauki dubu dari a cikin su, sauran kuma kisa dan liti ya saya min fili da su, ya kamata nima yanxu na fara ajiye abun kaina.


" Alhamdulillah yar albarka sai yanxu nasan kin fara gane hanya, idan kina haka kwanan nan za'a fara lissafa ki acikin matan da suke ji da kansu a cikin wannan jihar, Yanzu Leemat ta fita bata nan, ki jiran yanxu zanzo na amshe su da kaina, kinsan hausawa sunce zuwa da kai yafi sako.


 " Hakane Umma, sai kin zoki din.


  " Ki tana da min nama mai dan Romo Romo, da sauran abun Dadi, kinsan bakin uwar taki son dadi gareshi.


  " Dariya Zuhura tayi tace zanko tana da Miki Umma, sai kinci nama har sai kince kin koshi.


 Itama Umman dariya tayi tace " kona koshi zanyi guzirin anjuma ke dai kiyi da yawa.


 " Shikenan sai kinxon ki gaishe da Baba.


 " Zaiji wannan lalacaccen uban naki wanda baya tsinanawa iyalan sa komai, sai aukin Allah yace Annabi yace.


  " Tabe bakin ta Zuhura tayi, tace Umma wannan tsakanin ku ne, nikam sai anjuma.


   Katse kiran tayi, ta jingina kanta jikin kujera, 

A zuciyar ta tace, Allah dai yasa kar Abban junior ya dawo yanxu har sai Umma tazo ta tafi.


 💫💫💫💫💫💫💫💫

Yau ta kama Monday, da sassafe momma ta shirya junior, cikin uniform din sa, breakfast dinsa ta saka masa a lunchbox dinsa, daman Already Daniel dake kaisa school ya riga da yazo shi, dakin Daddy ya shiga da gudu ya fada jikin sa, 


  " Daddy Daddy ka tashi muyi sallama zan tafi school.


  " Bude idon sa Daddy yayi, yace kai mai suna baxaka bari Sai ka dawo daga school din ba mu gaisa, saika tashe ni daga bacci dan kaniyar ka.


  " Sorry Daddy ban sani bane ai ko zan dawo ko baxan dawo ba shiyasa gara na tashe ka mu gaisa, kuma kaga yanxu zaka kira min Abba na da Papa khalid, da kuma ummi na.


  " Ka cika yawan magana junior, waya ce maka idan ka fita baxaka dawo ba?


 " Malamar islamiyyan mune tace, idan mutum ya fita sai anga dawowar sa, tace idan zamu fita mu gaisa da kowa kuma mu nemi yafiyar sa, saboda ba lallai ne ka dawo ba.


 " Dariya Daddy yayi yace, malamar ku tayi Gaskiya, bari na kira maka Abban naka ku gaisa.


  " Yawwa Daddy kayi sauri, nasan yanxu momma zata Kira ni tace time yayi.


  " Kiran wayan Khabeer Daddy yayi, switch off

Kallon junior yayi yace kaji layin Abban naka Yana kashe.


 Hada fiska junior yayi yace " yanxu kenan Daddy baxan gana da Abba na ba.


  Yawan maganar nan ya isa haka, ya kana magana kamar wanda idan ka fita zaka mutu maxa tashi ka tafi school.


  " Tura baki yayi yace to ai Daddy baka kira min Papa khalid din ba.


 " Baxan kira shiba, maxa tashi ka tafi kaban waje,  bana son yawan magana.


 " Please Daddy.......


" Shut up mai suna maxa tashi ka tafi school sai ka dawo nasa a kaika wajen khalid din.


  Ransa bai so ba ya fice daga dakin Daddy yana daga masa hanu.

  Dakin Momy Sarah ya nufa, tana zaune a Bakin gadon ta.

   Gefen ta ya zauna yace good morning Sarah.


  " Morning junior, an tashi lfy.


 " Lfy lau Sarah dan Allah kira min ummi na a wayan ki, nace daddy ya kira min su yaki.


  " Shafa kansa momy Sarah tayi tace, karka damu bari na kira maka ita yanxun nan, hanun ta tasa ta dauko wayan a gefen ta, sanda tayi 3 miss call kafin Zuhura ta daga.

   Sallama Momy Sarah ta Mata.


  " Zuhura dake zaune a kujerar falon ta,  da kyar ta amsa sallamar, babu yabo babu fallasa ta gaishe da Momy Sarah, domin haka kawai ta tsani Momy Sarah, tafiya kaunar momma fiye da Momy Sarah.

   Shuru tayi tana jiran taji mai Momy Sarah zata ce, sai taji muryar junior yana cewa.


 " Hello ummi na.


  " Cikin farin cikin jin muryar danta da tayi, ta gyara zaman ta, tace my son, kaine.


  " Nine ummi, ina Abba  na jiya baizo gurin mu ba.


  " Bata ranta Zuhura tayi, tace junior daman bani ka kira ka gaishe ba, daman Abban ka kake nema.


  " Sorry ummi good morning.


  " Baxan Amsa ba, baka son zuwa waje na, koh junior, meyasa kake gudu na ne Kam.


 " ummi bafa bana son zuwa gunki bane, kece kullum sai kike min fada kina min ihu ko kuma ki kaini gidan su Aunty Leemat, kuma kullum Umman ki sai ta zagi Abba na da momma har ma da Daddy, ni kuma bana so, Ranar dana fadawa momma tace min karna yadda na kara zama a gidan Umman ki, wai babu tarbiya a gidan.


  " Rintse idon ta Zuhura tayi cikin jin zafin Abunda dannata yake fada mata,

 Cikin bacin rai tace kacewa momman naji sakon ta da ta turo min na gode, arashin tarbiiyar tamu, danta ya ganni ya Aura.


  Shiko yaro babu hankali yace to Ummi zan fada Mata, ina Abban yake.

 

 " Cikin tsawa tace ban sani ba dan ubanka kaje wajen momma daka mayar da ita uwarta ka sai ta nemo maka shi uban naka.

  Katse kiran tayi cikin jin zafin yanda aka raba ta da danta. (A cewar ta Amma)


 ( Hattara iyaye mata yana da kyau ace uwa tasa danta a jikin ta, ya kasance indai yana gida to yana kusa da ke ki zaman to mai tausayi ga danki, ya kamata ace shine abokin shawarar ki, hakan ne zaisa yaro shima ya kauna ceki ya soki yaji tausayin ki.)


 ( Ya kamata ace kina  kyautatawa dangin mijin ki, mussaman ma ace iyayen sa, hakan na karawa mace mutunci da kima a wajen miji, su maxa suna son suga matan su suna kyautatawa dangin sa.

   Amma duk sanda aka ce yau kina wulakanta dangin mijin ki, shima kansa mijin baki kyale ba, to wlh sunan ki sorry, don kuwa duk soyyayar da yake miki wata rana saiya tsane ki, kuma wlh kisa a ranki sai ya karo miki wata bima'ana kishiya, idan kuma taxo ta rungume sa hanu biyyu ta kyautatawa dangin sa, to wlh sai yafi sonta fiye dake sai dai ki zama yar kallo a cikin gidan ki da kuma dangin mijin ki, dan haka dan Allah mata mu kiyaye)


 Tsaki taja tace Aikin banxa dannaka ma an rabaka dashi, kuma duk laifin Khabeer ne daya kaimin dana gidan, zaka dawo wlh dole ka dawo min da dana, dan babu wata katuwar da ta taya ni nakudar Dana.


  Shi kuwa junior kuka yasaka ya fice daga dakin Momy Sarah da gudu.


  Dariya momy Sarah tayi kasancewar a handsfree tasa wayar tana jin duk abunda Zuhura take Fadi,

 " Yau dinnan zan raba muku gardama akan wannan yaron domin kuwa daga yau kunyi bankwana dashi.

  Text ta turawa Ajabo kamar haka.


  " Yau nake son ka dauke yaron nan yanxu nan za'a kawo sa mkrnt kasan yanda zakayi ka dauke sa. 

   Daga Hajiya Saratu.


  " Fadawa jikin momma yayi yana kuka.


  Zaunar dashi momma tayi tace, junior meya sameka kake kuka.


 " Cikin kuka yace momma Ummi ce.


  " Ummi kuma a ina kaga ummin naka.


 "Sarah ce ta kira min ita, yanda sukayi da Mahaifiyar tasa yake ta jero wa momma, sai da ya gama yace ba ruwana da Ummi baxan kara kulata ba, kuma sai na fadawa Abba na.


 " Numfashi momma ta sauke tace Allah ya kyauta, tashi ka dauki lunchbox dinka maza uncle Daniel yana jiran ka, karka makara, idan ka dawo zan kira maka Abban naka, harda papa khalid din ma.


 " To momma, lunchbox din ya dauka, tare da dagawa momma hanu.


 " Itama Hanun ta daga masa, tace ayi karatu da kyau.


 ⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


Sosai Khady ta shirya Nabiya cikin wani tsadadden material orange color, mai ratsin baki a jiki tayi matukar kyawu, dan bazaka taba kallon ta kace yar kauye bace, daining suka fito tare da Khady ta zuba mata abinci,

 Sosai Nabiya taci abincin kasancewar yunwar dake damunta.

Bayan ta gama ne ta dawo kusa da Khady ta zauna sukaci gaba da kallo.

  Janta da zance Khady take yi.

 Yayin da Nabiya take amsa mata jefi jefi.

Ba'a juma ba kuwa Nabiya ta sake da Khady sosai.


 Karfe biyu na Rana Hajiya ta fito daga bedroom dinta, a falon ta samesu suna ta zance tamkar wadanda sukayi shekara da sabawa.

 Kusa da su ta zauna tace to" nima gani na fito ayi zancen Dani.


 Dariya sukayi dukan su cikin hadin baki sukace " Sannu da fitowa Hajiya.


 " Yawwa kuma sannun ku da shan fira, ina Sadiq bai dawo bane.


 " Khady ce tace " ehh Hajiya yaya Sadiq bai dawo ba Gaskiya.


  " Okay yace assignment zaiyi summit ya dawo baida lectures yau,.


  " Wata kil yabiya wani wajen kinsan ya Sadiq da kafar yawo.

  Dan daxun nan ma yake cemin yana son zuwa gidan su yellow.


  " Daga bakin kofa yace ya take da taki uwar yan gulma daga ce miki zanje gidan su yellow shikenan Kuma sai kika zo zaki min munafurci a wajen Hajiya koh.


  Dariya Hajiya tayi, tace to kaji iyayen fada, kullum idan Bakuyi ba bakwa jin dadi, sai ka samu damar karasowa Koh.


  Karasowar yayi tare da zama kusa da Hajiya, kallon Nabiya yayi yanda yaga ta sunkuyar da kanta kasa, shi sam bai gane ita bane yayi zaton kawar Khady ce. Maida kallon sa  kan hajiya yayi yace har kin tashi kenan.


  " Na tashi my son.

Kallon Nabiya tayi, tace menene sunan ki yan Mata?


  " Kanta a kasa tace Sunana Nabiya.


  " Menene ya fito dake daga cikin kauyen ku, ya kawo ki nan, ina son ki bani lbrn ki.


  " Idon Nabiya ne ya ciko da hawaye, cikin rawar murya ta fara bawa Hajiya Aisha lbrn Rayuwar ta, tun barin mahaifiyar su garin su har zuwa itama barin ta kauyen, cikin kuka ta karasa maganar da cewa bansan Halin da Adda Nasreen take Ciki ba, nasan hankalin ta zai tashi da rashina, sai dai kuma ni a nawa tunanin hakan da nayi shine daidai,.


  Babu wanda bai tausayawa Nabiya ba Khady har kuka tayi tsabar tausayin Halin da suka cintsi kansu a ciki.

 Shima Sadiq ya tausaya mata ainun domin kuwa sunga jarabawar Rayuwa.


  " Hajiya ce tace, kiyi hkr Nabiya daman ko wani dan Adam da irin tasa kaddarar, ku kaddarar kuce taxo da haka,.

  Na tabbata mahaifiyar ku bazata aikata zina ba, tabbas itama da akwai abunda ya fitar da ita daga Rugar ku, kamar yanda kema dalili ya fitar dake, na tausayawa Yar uwarki sosai, kuma insha Allah duk sanda Alhaji ya dawo kasar nan, zan rokesa muje mu Rugar taku domin na dauko ita yar uwar taki,.

  Sunan Nabiya Hajiya ta Kira.


 " Dago kanta Nabiya tayi tare da Amsawa.


  " Magana Hajiya taci gaba dayi,

  " Ina son ki dauke ni tamkar uwar da ta haife ki, ki dauki yarana tamkar yan uwan da kuka fito ciki daya, zan baki jin dadin da kika rasa a baya kuma ina da tabbacin ya'yana zasu rike ki yar uwa, abu daya nake so gareki shine ki rike mu Amana.

   Ina fatan zaki zauna tare dani a matsayin uwa.


  Sadiq ne yace Hajiya tabbas wadannan mutanen sun cancanci a taimake su, kuma insha Allah zan dauki Nabiya tamkar yanda na dauki Khady Allah ya hada kanmu.


  " Rungume Nabiya Khady tayi tace Hajiya yau Nima na Sami yar uwata mace wacce zan koka damuwa ta da ita.

  Kallon Nabiya tayi tace dafatan zamu rike juna bisa Amana tare da yarda.


  " Hawayen Nabiya kasa tsayuwa sukayi tsabar dadi, wai yau itace ta samu wata uwar wacce zata bata kulawar da ta rasa agun tata mahaifiyar yau itace ta samu Karin wasu yan uwan bayan Nasreen da Nuruddeen babu abunda zata ce ga ubangiji sai godiya.

   Cikin muryar kuka tace Hajiya bani da bakin da zan iya muku godiya dashi, sai dai nace Allah ya biya ku da gidan Aljanna, zan miki biyayya Hajiya kamar yanda ko wacce ya take yiwa uwar ta, zanso yaran ki tamkar yanda nake son Adda Nasreen da Nuruddeen, fatana Allah ya bani ikon kyautata Muku.


  Ameen Hajiya tace tare da mikewa zuwa kitchen.



🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 


Tana zaune ta hada uban tagumi tana tunanin yan uwan ta, hawaye ne suke zirara a idanun ta, a duk sanda ta tuna da Nuruddeen, mussaman idan taxo ficewa ta zauren gidan su sai tayi kuka idan taga wajen zaman sa, ita Kuma Nabiya ko wanne Hali take Ciki sai Allah, ko tana raye ko tana mace sai Allah ne ya sani.


 Tana cikin wannan tunanin taji ana doka sallama a kofar gidan nasu.

  Tashin tayi ta fito cikin nutsuwa, tace wa'alaikumussalam. 

   Kawu Iro kaine sannu da zuwa.


Yawwa Nasranatu mlm musan yana ciki ne.


" Ehhh yana ciki bari na masa magana.

  Kallon Khabeer tayi tace sannun ka daxuwa.


 Kusan suman tsaye Khabeer Yayi, kasa amsa mata sannun ta yayi, gani yake kamar idanun sane suke masa gixo, wannan kamar wacce Mamy tabani photon ta, tabbas itace yar mamy ce A fili yace Alhamdulillah kukan Mamy ya kusa karewa.






Share

    And

     Comment



Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


 (Ummu Nasmah)[11/25, 9:33 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

             ⛏⛏⛏⛏

Şคrค ໓ค ŞคŞŞคkค 

 (๖คฯค hคຖค ງค๓วi)

             t໐h໐

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


Story And Writing

           

           By


 Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)



🤳🏻


0814753718

 


                 ﷽



Wannan page din sadaukarwa ne gare ku, Hausa novels Zallah group, ina jin dadin sharhin da kuke yiwa wannan book din, yana sani nishadi sosai, domin kuwa yin muhawara akan book, yana saka WRITERS nishadi sosai da kuma kara musu himma wajen typing, Gaskiya Babu abunda zance daku sai dai nace Allah yabar kauna, acikin ku akwai mutum Uku da sukace suna bukatar idan na gama rubuta SARA DA SASSAKA na rubuta musu tarihin Rayuwa ta, Maryam I Umar da mai suna Rashida Bello funtuwa, kuyi hkr a gaskiya banda Ra'ayin Rubutun novel akan tarihin rayuwata,  amma kuyi hkr idan tarihina kuke son ji, zan samu lokaci na mussaman na ware domin group din ku,  insha Allah zan baku tarihin Rayuwata koda a takaice ne.

 Na gode sosai da kaunar ku gare ni🙏🏻 


___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



 P•••••••2️⃣4️⃣ to 2️⃣5️⃣


" Khabiru bakaji ana gaishe ka ba ne cewar mlm Iro.


  " Dawowa tunanin sa yayi, sannan yace sorry hankali na yayi wani waje.

 Kina lfy.


 " Lfy lau cewar Nasreen, kawu Iro bara naje na kira muku Baban.


  " Ya jikin yar uwar taki da fatan dai babu wata matsala yanxu ko.

  

 " Da sauki sosai Baba, sai dai wani sa'in takan kwana tana kukan kafar tana mata zogi, sannan gefe kadan da wajen karayar yana fitar da ruwa.


 " Subhanallah indai haka ne to Gaskiya dauri baiyi kyau ba, amma kira min amahaifin naku.


  " Shikenan kawu Iro fana kira San.


 " Sanda Nasreen ta shige cikin gidan, sannan ne Khabeer ya mayar da kallon sa kan mlm Iro, yace Baba wannan yarinyar tana da Mahaifiya kuwa yanxu A raye?


  " Cikin mamakin tambayan da Khabeer yayi mlm Iro yake kallon sa, yace meyasa kamin wannan tambayan khabiru?


  " Murmushi Khabeer yayi, cikin hikima da dabara irin ta jami'in tsaro, yace Naga Alamun hakan ne tun daga yanayin ta.


  " Wani irin yanayin Kenan ka gani a tattare da ita.?


  " Wannan tambaya haka Baba sai kace wani dan jarida, to amsar ka ta farko itace, naga yanayin suturar jikin ta duk wacce take da uwa a kusa, bazata barta da shiba, domin kuwa daud'ar jikin sa yayi yawa, da alamu dai Rabon ta da wanka ta kwan biyu, wannan shine dalilin da yasa na maka tambaya, Amma fa kayi hkr Baba karka ce na cika shishigi.


  " Ajiyar zuciya mlm Iro ya sauke yace, ko daya khabiru, bakayi shishigi ba, kawai dai nayi mamakin yanda a lokaci kankanin ka gano cewa Nasranatu bata da uwa, 

Ba kuma mareniya bace.


 " Kallon mamaki Khabeer yayiwa mlm Iro, yace ban gane me kake nufi ba Baba, ba mareniya bace ita, to ina mahaifiyar ta?


  " Ta bace khabiru ta shiga duniya an rasa gane menene ya fitar da ita daga cikin Rugar nan, wasu mutanen daga cikin Rugar nan suna rade radin cewa Maimuna mahaifiyar Nasreen yawon karuwanci ta tafi, kamar dai yanda kishiyar ta take fada, har wasu daga cikin mutanen gari suka yadda.


  " Runtse idon sa Khabeer yayi, saboda jin zafin kiran Mamy da kalmar karuwa da mlm Iro yayi, cigaba da tambayan mlm Iro yayi, Amma yanxu kai Baba ka yadda da cewa mahaifiyar ita Nasreen din zata Aikata Abunda kuke zargin ta dashi?


 " Ehh to gsky bana tunanin zata Aikata hakan, amma dake dan Adam Ajizi ne, zata iya sauyawa, daga mutumiyar kirki zuwa ta banxa, amma a yanda na santa kam, Gaskiya mutumiyar kirki ce, dan Babu na biyun ta a cikin kauyen nan gsky, jin haushin ta daya da nayi, na yadda ta watsar da rayuwar yaranta, mussaman shi marigayi Nuruddeen, kullum sai ya tambayi yaushe mahaifiyar sa zata dawo, ya mutu yana kewar mahaifiyar sa, a Gaskiya khabiru yaran nan suna shan bakar wahala a cikin gidan mahaifin su, yanxu haka maganar da nake maka ita dayar yar tata Nabiya, ta shiga duniya itama Babu labarin ta, tabi sahun mahaifiyar ta, ta basu mummunan gado na shiga duniya.


  " a Gaskiya Baba Iro ka bani mamaki, bai kamata ace a matsayin ka, na mutum mai hankali kake zargin wannan baiwar Allah ba, domin kai da kanka kace babu na biyun ta a cikin wannan kauyen naku, kaga kuwa hakan ya nuna cewa baxata aikata abunda kuke zargin ta dashi ba, dan haka zato zunubi koda ya kasance Gaskiya, ba kusan mai ya fitar da ita ba, Allah da ya halicce mu shine kadai yasan abunda ya fitar da ita.


  " Baba dake tsaye a bayan su tun fara zancen su ne yace Kwarai kuwa yaro Allah ne kadai yasan mai ya fitadda Maimuna daga cikin Rugar nan, nine mijin ta, kuma ina da tabbacin cewa baxata Aikata Abunda ake zargin ta dashi ba, kuma ina ji a jikina Maimuna zata dawo gareni.

   Zata dawo a lokacin da idona baxai iya kallon ta ba, domin nasan sanadin Rashin kulawata da juya musu baya da Nayi shine babban dalilin daya fitar da Nabiya daga cikin garin nan, ga mutuwar Nuruddeen da har yanxu yaki fita daga cikin raina, Nasranatu bata kulani, har yanxu taki saurarana, a nufin ta nine wanda nayi SANADIN RABUWAR ta da yan uwan ta, ni kaina na rasa menene yasa nake jin rashin kaunar su a zuciyata a cikin wadannan yan kwanakin, na kasa takawa Salame burgi akan cutar dasu da take, duk da nasan da hakan.


 " Khabeer yaji dadi sosai a cikin ransa yanda yaga Baba bai yadda cewa Mamy karuwa bace, acikin ransa yake cewa, lallai barin Mamy wannan garin akwai lauje cikin Nadi, tabbas akwai munafurci acikin barin ta garin su, kuma koma Mainene, zai fito tunda har Allah yasa an gano garin su, maganar Daddy ya tuno, mlm Sadi yace ciwon mamyn ku, maganin sa Dole sai ansan garin su, domin kuwa sammu ne, wanda aka binne dole sai an tone kafin ta dawo cikin hankalin ta.

   Alhamdulillah tabbas Mamy duk wanda baisan ganin ki a wannan garin, ya shiryawa, dawowar ki, domin kuwa ke din ciwon Ido ne gare su, Zasu san cewa zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ruwa ana iska sai yayi, Makiyin ki yayi hkr Mamy Dole zai ganki, Domin kuwa SARA DA SASSAKA baya hana gamji toho danki Khabeer zai zamo gatan ki, zai tsaya domin ganin kin samu lfy da kwanciyar Hankali, baxan dagawa duk mutumin dake shirin ganin bayan ki kafa ba.

   Kallon Baba Khabeer yayi yace, Allah ya kyauta ya jikan Nuruddeen, ita kuma mahaifiyar Nasreen Allah yasa tana Halin lfy.


  " Ameen yaro na gode, kaxo lfy.


  " Lfy lau Baba.


  "Alhamdulillah hanu ya mikawa mlm Iro sukayi musabaha sannan ne mlm Iro yake jajanta masa kafar yar gwal, yace mlm musa ashe kafar yarinyar nan Amina ta fara Ruwa, baku zo kun min bayani ba.


 " Wlh kuwa mlm Iro, nayi niyan zuwa na gaya maka, uwar yarinyar taki, wai sun karbi maganin suna sawa a wajen tana ganin kamar zai bushe wajen.


 " Allah sarki to Allah ya bata lfy, ganan khabiru Alhaji ya aiko sa, yaxo yaga wajen ka, da kuma yanayin kiwon ka, yace min zaiyi kwana biyu ne, ya koma, amma dai gashi nan kasan hausawa sunce waka a bakin mai ita tafi Dadi.

  Khabiru ga mlm Musa.


  " Hanu Khabeer ya Kara mikawa mlm musa, yace kamar yanda Baba Iro ya gaya maka, hakane.


  " Baba ne yace Hakan yana da kyau, tun Ranar Laraba muke tsammanin zuwan sai yau Allah ya kawo ka.


  " Ehh wlh Aiki ne ya rikeni, yanxun ma da karfi na ajiye Aikin a gefe na taho.


  " Allah sarki Allah ya taimaka to yanxu zan baka dakin zauren nan, kake kwana, sai dai zakayi hkr da wajen namu kasan yanayin kauye dana binni ba daya bane, sai dai kayi hkr da Abincin mu da kuma wajen kwana.

   Maganar kiwo kuma daman na yanke shawarar cewa Nasranatu itace zatayi kiwon shanun, duk dama ban fada mata ba, amma idan na shiga ciki zan fada mata, idan yaso zaku na tafiya tare kana Ganin yanayin kiwon namun.


 " Hakan yayi Baba Allah ya kaimu goben, maganar Abinci da wajen kwana kuma, karka damu dashi.


 " Mlm Iro ne yace, to  khabiru ni Bari na wuce koh, tunda ka samu masaukin ka, hanu ya mikawa mlm musa sukayi musabaha, shima Khabeer ya mika masa, sannan ya wuce.


 Baba da Khabeer sun dan juma suna hira, yayin da mlm musa yasa aka kawo masa abinci, Tuwon dawa ne miyar lami ko wake Babu a cikin ta, sai kuma zabuwar daya sa aka yanka domin Khabeer din.

  Allah sarki Khabeer shida baya cin abincin kowa idan ba na momma ba ko Momy Sarah sai kuma yau gashi an hadosa da tuwon dawa miyar lami, wacce baisan wacce ta dafa sa ba.

   A Dole yasa Khabeer dan tsakurar tuwon sbd kar Baba yaga kamar ya Raina abincin su, shi bawai tuwon dawa da miyar lamin bane damuwar sa, shi damuwar sa waye ce ta girka kazama ce ko mai tsafta, Allah dai yasa ba wannan Nasreen din bane ta dafa, domin kuwa kayan jikin ta ma kadai ya isa ya sawa mutum virous, dakyar ya samu yaci kadan, naman ma kadan yaci.

 Sai misalin karfe Tara Baba yayiwa Khabeer sallama ya shige cikin gida domin kwanciya.

  Shima Khabeer din tashi yayi ya debi ruwa a dakin da aka masa masauki, ya fito ya zaga tolet din dake waje domin yin wanka da brush.


 Bayan shigar Baba ne ya je Bakin kofar da Nasreen ke kwana yace Nasranatu.

   Shuru Nasreen tayi taki amsawa kuma tana jin sa, sanda yayi baki wajen hudu sannan ne ta amsa tare da fitowa.


  " Kallon ta baba yayi yace Nasranatu kardai har kinyi bacci na tashe ki.

  

 Shuru tayi bata basa ansa ba saima kada masa kai tayi Alamar a'a.


 " Murmushi mai ciwo Baba yayi yace har yanxu baki huce ba Nasranatu kina fushi dani ko.


  " Sunkuyar da kanta tayi tace, a'a Baba ni bana fushi dakai.


 Kina fushi dani mana, tunda bakya son magana dani.


  " Nifa Baba bana fushi dakai.


  " Shikenan tunda haka kika ce daman ina son na sanar dake cewa, kece zakiyi kiwon Nagen dana taho dasu daga binni, gobe da safe zaki fara fita, shi wannan kwadon daya zo, tare zaku ke fita dashi, kinji ko.


  " Ehh naji Allah kaimu goben.


  " Ni zan shige na kwanta sai Jango Koh.


 " Allah yari Aim Baba.


 Dakin ta, ta koma ta zauna tare da jawo kayan ta, daman yau tayi niyar barin wannan Rugar, jira daman take kowa ya kwanta yayi baci ita kuma ta fice.

  Misalin wajen sha daya Nasreen ta fito, saida ta tabbatar kowa yayi bacci, sannan ta fito da dan dangwalin ta, tayi hanyar waje.

    

  💫💫💫💫💫💫💫

 Tun safe Hankalin  su momma yake tashe, sakamakon neman junior da akayi aka rasa, sosai hankalin su ya tashi Daniel da khalid Babu irin neman da basuyi ba, amma Babu junior bare labarin sa, sun tambayi mai gadin makarantar yace yaga fitar yaron shida wani yaro, sunyi wajen mai sayar da sweet, yace daga nan bai kara ganin sa ba.


 Ita ko Momy Sarah uwar munafukai nunawa tayi tafi kowa tashin hankali, domin kuwa kuka take curcur da hawayen ta.

 Duban khalid dake zaune yayi tagumi tayi, tace kunje kun kai report police station ne.


 "Daniel yakai yanxu haka suna bincike, Momy ni damuwata ma idan na kira numbern yaya Khabeer bata shiga na rasa yaya zanyi, kodai na kira Aunty Zuhura ne na sanar Mata.


 Momma ce tace" a'a khalid, karka daga mata hankalin ta da Daren Nan, ka bari sai da safe.


 " Daddy da yayi shuru tun daxu ya kasa magana ne, yace khalidu kara naiman numbern khabirun muji ko zai shiga




Share

     And

   Comment


Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻



    (Ummu Nasmah)

[11/26, 10:00 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya hana gamji)

             Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

         🌳🌳🌳🌳



 Story and Writing


             By


 Rasheedat Usman

       

      (Ummu Nasmah)


         

                *﷽*



Wannan page din sadaukarwa ne gareki Mom Affan dake cikin group din KAINUWA fan 11 ina jin dadin sharhin ki, kiyi yadda kike so da page dinnan domin kuwa naki ne.

   Allah ya bar zumunci.


___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________



P••••••••2️⃣6️⃣ to 2️⃣7️⃣


 Kara kiran wayan Khabeer khalid yayi, amma still cewa suke unable to connection, a takaice dai inda yake babu service.

  Dafe kansa khalid yayi, yana tunanin Halin da junior yake ciki.

 

 Mamy da babu bakin magana hawaye ne kawai yake fita daga idanun ta, domin tayiwa muguwar sabo da junior, kusan ma shine abokin hiran ta, wata rana kam ma tare suke kwana.


 Dakyar Daddy yasa kowa ya koma dakin sa ya kwanta, shima khalid a Ranar dakin gaurancin sa ya tuna, Domin kuwa anan ya kwana.


  Kasa kwonciya Mamy tayi, tana tunanin junior.


 Bayan shigar momma daki alwala tayi ta tada sallah, tare da addu'oin Allah yasa junior yana hanun na gari, 

Shima daddy ba'a barsa a baya ba wajen tsayuwar dare.


  Tollet Momy Sarah ta shiga ta dannawa Ajabo kira, ringing daya kuwa ya daga, tun kafin tayi magana yace.


  " Hajiya Saratu, nafa cika Aiki na, yanxu haka yaron nan yana cikin gida na.


  " aikin ka yayi kyau sosai Ajabo insha Allah gobe zakaji alert, ka kula sosai da yaron, karka bari a samu wata matsala, har sai na samu hanyar da zan fitadda shi daga gombe zuwa kano, daga nan zamu hada shi da sauran yaran a fita dasu kasar waje, nasan yanxu dole hankalin Khabeer zai bar kan binciken mu, ya koma na dansa, dan haka ka kula sosai.


 " Karki samu damuwa Hajiya domin kuwa ni bana samin kuskure a Aiki na.


 " Okay sai kaji ni bye.


 " Murmushi momy Sarah tayi bayan ta katse kiran, tace dani kake zancen Khabeer, badai kace sai kaga bayana ba, to ni zan fara ganin naka, kafin kai kaga nawa.


 Washe gari da asubar fara Daniel da kamal suka shigo cikin gidan, a falo suka sami Daddy da khalid, bayan sun gaisa ne Kamal yake cewa Daddy.


  " Munyi duk wani bincike da zamuyi, Babu wani good information da muka samu akan bacewar junior, amma har yanxu muna kan binciken kuma insha Allah zamu samesa kafin zuwa dare, sannan kuma, tun jiya nake kiran numbern oga bata tafiya, ina ga kamar inda yake Babu service.


 " Khalid ne yace, muma tun jiyan muke neman numbern sa, yaki tafiya, Amma inga nan da zuwa dare idan Babu labarin junior dole gobe zamuje can garin da yaje domin yasan Halin da ake ciki.


  " Insha Allah zamu samesa, domin gsky a matsayin mu na Hukuma bazamu so har yaji maganar bamu samo sa insha Allah zamu gansa, kafin ma Oga yaji lbrn.


 " Daddy ne yace to Allah yasa a samesa Daniel, ina fatan baka sanar da Mahaifiyar yaron ba Koh.


 " Ban sanar da ita ba, Daddy asali ma, ban koma gidan ba tun jiya a station na kwana.


☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️


 Junior da tun sanda aka shigo dashi cikin gidan, yake fama da warin sigari, dana giya.


  " Kallon Ajabo junior yayi cikin taurin zuciya irin na ubansa yace, mena muku kuka dauke ni daga school, kuka kawo ni nan, kuma sai damuna kuke da wari.


  " Dauke sa da mari Ajabo yayi yace dan ubanka mu muke warin, kaji dan iskan yaro.


 " Fashewa da kuka junior yayi sannan yace ka daki Allah ya isa kuma wlh idan Abbana yazo nan kun shiga uku.


 " Bushewa da dariya Ajabo yayi tare da kallon s man yace S man tambaya mana shi ta ina uban nasa zaizo nan.


 " Kai kake kula wannan shashashan yaron, kaga tashi mu bar masa wajen muje can falo muci gaba da  cacar mu,

 Tashin kuwa sukayi tare da dannawa dakin da suka bar junior a ciki key.


  Shuru yayi tare da jin gina kansa a kangon dakin, tunanin zancen da suka taba yine da mahaifin sa ya fado masa a ransa,

 " Wani dan karamin warwaro ya basa mai kamar agogo tsakiyar sa kuma anyi Alamun agogo, yace ka rike wannan a Hanun ka junior, karka ke ciresa domin kuwa yana da matukar amfani a Hanun ka, koda ka fada zan iya gano inda kake ta hanyar wannan, koda kuwa kasar nan ka bari, kaga nawa nima a hanuna, connection dinsa daya ne dana Hanun ka, ka adana shi sosai, karka yadda kuma kowa yasan amfanin sa.


 " Murmushi junior yayi cikin murna ya dago tsintsiyar hanun sa tare da shafa agogon yace Abba na zaizo, ya tafi Dani.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


Karar bude kofar da Khabeer yaji ne, yasa shi fitowa daga cikin masaukin sa domin ganin waye zai fita da Daren nan haka kusan 12:00pm, haska ta yayi da wayar hanun sa, cikin mamakin yace " yan Mata, ina zuwa da wannan Daren haka.


 " Cikin Razana Nasreen ta juyo, domin ita duk a tunanin ta kowa yayi baci,zata iya ficewa ba tare da kowa ya ganta ba.

    Cikin gatsali da tsiwa wanda bansan Nasreen tana da shiba naji tace, 

" Inda ka aike ni zanje, ko akwai wani sakone, da zaka kara min.


 " Murmushi Khabeer Yayi yace Allah sarki idai har inda na aike kine to ki dawo na fasa Aikan.


 " To fah tunda ka fasa naka aikan, ni bari naje nawa aikan.

   Tare da sa hanu zata bude kofar gidan.


 Ko kafin tasa nata hanun tuni Khabeer ya rigata saka nasa, yace karkiyi haka mana, ina kallon ki mace mai mutunci, amma Yanxu naga kina fitar dare, wani kallon kike tunanin zan Miki, da kuma wani suna zan kira ki.


 A Yanxu kam Nasreen ta fara hasala, domin kuwa bata kaunar ta kara kwana cikin wannan gidan, da sukayi sanadin RABUWAR ta da AHALIN ta, cikin fushi tace.


 " Kamin duk kallon da yaxo ranka, sannan ka kiran da ko wani irin suna na batanci domin kafin ka kiran dashi an kira mahaifiya ta dashi, kaga kuwa baxai min ciwo sosai ba, dan haka dan Allah ka bude min kofa, na samu na bar cikin wannan Bakin garin kafin gari ya waye min.


 " Bafa zan barki ki tafi ba, har sai kin fada min dalilin da zaisa ki gudu ki bar garin ku, a cikin kuma wannan tsohon Daren, da zaki iya haduwa da Abunda zai iya cutar da ke.


 " Hmm labari na bayi da dadin ji, kuma bana bukatar tuna su.


 " Ni bari na fara tuna Miki, dan uwan ki ya mutu, yar uwar ki ta gudu, mahaifiyar ki ta bace, shine kema da kika saura kike kokarin guduwa ki shafe tarihin ahalin ku acikin wannan rugar taku, wanda kuma shine, abunda makiyan ku, suke bukata, tabbas kina barin wannan Rugar, to burin su ya cika, na son ganin bayan ku.


  " Tabbas maganar Khabeer tayi tasiri a zuciyar Nasreen, sai dai baxata iya hkrn jure wani sabon cin mutuncin ba, tasan kwanan nan za'a fara yada cewa itama Nabiya ta tafi yawon karuwanci.

  Juyowa tayi ta kalli Khabeer, tace har an baka lbr na kenan, ance maka mahaifiyar mu ta tafi yawon karuwanci koh.


  " Ko daya Babu Wanda ya fada min, sai dai ina son ke ki sani cewa nasan inda mahaifiyar ku take.


  " Murmushi Nasreen tayi, tace haba kwado, idan kana son ka hanani tafiya ne ai basai ka fake da cewa kasan inda AMMI na take ba.

 Domin kuwa yau ka shigo garin, baka da wata masaniya akan mahaifiyar mu, dan haka kabar wannan tatsuniyar.


 " Murmushi shima Khabeer Yayi yace ba tatsuniya nake miki tabbas mahaifiyar ku tana gidan mu, jirani inada hujjar da zata tabbatar miki da hakan.


 " Ina jiran ka, je ka kawo hujjar.


 Wayar sa ya bude tare da binciko mata hotonsa wanda suka dauka su Uku dashi da Mamy da junior ya mika Mata.


 " Karba tayi tana karewa pic din kallo, cikin Al'ajabi da mamaki, tace wannan Ai AMMI ce !! Ammi ce !! AMMI ce !! Tana ina dan Allah ka taimaka ka kaini wajen ta.


  " Murmushi Khabeer Yayi yace kiyi hkr ki kwantar da hankalin ki zan kaiki wajen mahaifiyar ki, amma Dole ki koma cikin gida, sai gobe da safe zamuyi magana.


 " Da to ta amsa tare da mika masa wayan sa ta koma cikin gidan.


 Girgixa kansa Khabeer Yayi cikin tausayin halin da ya ga yarinyar tana ciki, sannan shima ya koma cikin dakin nasa.


Cikin farin ciki da murna Nasreen ta koma.


Mama da fitowar ta kenan daga bandaki taga fitowar Nasreen daga zauren kofar gida, ne tasa salati tare da salallami, tace Nasreen yanxu yawon bin maxan naki har yakai, kike fita cikin tsakiyar dare, da karfi ta kwalawa Baba kira, tace mlm ka fito kaga ikon.


  Nasreen  tsayawa tayi tana kallon ikon Allah wai itace ta dawo daga wajen maxa.


  Da sauri Baba ya fito daga dakin sa, yace " lfy kuwa Salamatu kike min wannan kiran cikin wannan tsohon Daren haka.


  " Gashi nan dai idon ka ya gane maka, cikin tsohon Daren da kake gani yarka ta fita yawo iskancin ta, ta girma an gansame a gida Babu miji ai dole a fita neman inda za'a rage zafi.


  " Haba Salamatu yanxu dan Nasranatu tayi ba daidai ba, bazaki hukunta ta ba har sai kin Kira ni, ai kema uwace gare ta, kinga ni na koma gata Nan a gaban ki ki mata hukuncin daya dace.


  " Ai daman ko ka fada ko karka fada, yau saina mata dan iskan duka, na kira kane domin idon ka ya gane maka, karka ce nayiwa yarka sharri.

 Kaje ka jajibo wani bako dan binni wayayye ai dole ya rinjayi yarinya ya kwakuleta.


  Shidai baba baice komai ba ya juya zuwa cikin dakin sa.


  " Sanda mama ta dauko tahau dokawa Nasreen, tace yau dan ubanki sai na karya ki, kamar yanda kika saka wannan dan iskan yaron jungudo ya karya min yarinya, ai asirin ki ya tonu yau zata gaya min, kuma wlh kema saina karya ki.


  Tsabar takaici da haushin Baba yasa Nasreen bata jin zafin dukan da mama take Mata, domin kuwa a yau tsanar Baba da haushin sa ya darsu a zuciyar ta, tunda har a gaban sa MAMA zata kirata da mai bin maxa, ya kasa daukar mata ki.

   Jin saukar sanda a tsakar kanta ne yasa ta kurma uban Kara.


 " Khabeer dake zaune saman sallaya yana lazimi yaji ihun Nasreen, da sauri ya fito tare da shigewa cikin gidan.


 Itako Mama dukan Nasreen take kamar wacce ta samu jaka.


  Tsawa Khabeer ya dakawa Mama yace, ke baiwar Allah, wani irin duka kike mata cikin wannan tsohon dare kamar wacce ta kashe miki Rai.


  Kyale dukan Nasreen mama tayi, tace " kai kuma a waye, oh ashe dai dole kaxo ka karbe ta, tunda ka samu abun morewa daga nan har kabar Rugar nan, kallon Nasreen din tayi tace to ga kwarton naki yaxo, karbar ki.

   Kuma wlh yau baxan barki ba saina karya ki. 

Taci gaba da doka mata sanda.


  Runtse idon sa Khabeer yayi cikin zafin rai ya murde Hanun Mama tare da kwace sandar nuna ta yayi da sandar yace, ke wacce irin mata ce, wacce babu imani da tausayi a cikin ranki, anya kuwa ke musulma ce, dan duk macen da take daura goshin ta, a kasa ta kalli gabar, baxata Aikata Abunda kika Aikata ba, kince nine dan iskan ta, kuma kwarton ta koh, na yadda da hakan, Amma ba anan ya kamata ki fada ba, wajen gari ya kamata ki fita ki fada kowa ya sani, in yaso axo a tsire mu.

  Kallon Nasreen yayi yace, shige kije dakin ki, ki kwanta.


Sake baki mama tayi tana kallon Khabeer, tana son ta dakatar da Nasreen Amma tana shakkar Khabeer, rike hanun ta da Khabeer ya murde tayi yanda yake mata azabar zafi.



💫💫💫💫💫💫💫💫


Acikin kwana bakwai shakuwa mai tsanani ya shiga tsakanin Nabiya da Khady, da Sadiq, mussaman ma Sadiq idan yana gida bayi da Abokiyar hira sai Nabiya, 


Ita kanta Hajiya tana jin dadin yanda yaran suke zaune lfy.


  Yaya Hashim ma ya dawo kuma Hajiya ta gabatar masa da NABIYA ya karbe ta Hanun biyyu,


Mussaman Aunty Hauwa matar Yaya Hashim har nema tayi Hajiya ta bata Nabiya, ta koma wajen ta da zama ko zata samu Abokiyar hira, tunda shi yaya Hashim yana yawan tafiye tafiye,

   Amma Hajiya fir taki tace babu wanda zai raba mata kan ya'yan ta.

 Dole yasa aunty Hauwa ta hakura ta kyale sa.


 Ya da sassafe Khady da Nabiya suka tashi Domin daura breakfast, tare sukayi komai suka gama suka jera a daining.


  Shadaya dai dai kowa Yayi fito daining, bayan sun gama breakfast ne, Hajiya take tambayan Nabiya tayi primary ne, domin tana son zata biya mata Neco tayi, idan sakamakon ya fito ina son ZANYI miki joining din makarantar su Khady

Kuci gaba da tafiya tare duk dama ita ta kusa gamawa.


 Godiya Nabiya tayiwa Hajiya sannan tace ta gama primary, harma ta fara secondary school ajinta biyu ta daina zuwa sakamakon yawan talle da Mama take daura Mata.


  Hajiya ce tace hakan ma ai kinyi kokari Nabiya ba kowani dan kauye bane yake karatu, zansan abun yi zaki koma makaranta insha Allah



Share 

     And

  Comment



 Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


(Ummu Nasmah)[11/29, 9:15 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya hana gamji)

             Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

         🌳🌳🌳🌳



 Story and Writing


             By


 Rasheedat Usman

       

      (Ummu Nasmah)


               

                  ﷽



Sadaukarwa


Gareki sister AMINA ina jin dadin yanda kike min sharhi Allah ya bar kauna na gode sosai.


Da kuma masoyana a duk inda kuke ina alfahari daku.

  Koda ban kira sunan ku ba nasan kun san kanku domin kuwa kuna da yawan da Alkalamin Rasheedat Usman bazai iya rubuto sunan kuba.



 ALBISHIRIN KU MASOYANA


Ina kuke masoyan littatafan Rasheedat Usman, to albishirin ku.

 Rasheedat taxo muku da wani sabon salon labari mai rikitarwa da kuma sark'ak'iya Ga kuma Abun ban tausayi, tare da yaudarar kauna cin Amana tare da ha'inci.

  

 ta yarda da ita taci amanar ta, taba shi Amanar ta ya ha'ince ta, ta shiga  Cikin mawuya cin hali har takai ga sun haddasa mata ciwon zuciya, ku biyo Alkalamin Rasheedat Usman duk Ranar litinin da Laraba domin jin wannan labarin mai Ban tausayi tare da zazzafar soyayyah mai ratsa zuciyar mai sauraro.


Ga nan sunan littafin


💑💑💑💑

          AKAN Y'AR UWATA

(Hawaye na ya zuba)

                 💑💑💑💑

 _____________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



___________________________________



P•••••••2️⃣8️⃣ to 2️⃣9️⃣


 Yun kurawa Nabiya tayi, tace kinga sister Khady tashi muje mu karasa Aikin mu, kinsan dai munyi akan yau zamu fita shopping Koh.


  " Kuma fa haka ne sis Nabiya, kallon Ya Sadiq tayi, please Yaya dan Allah ka taimaka ka kaimu shopping din nan.


 " Hararar ta ya Sadiq yayi yace waye drivern ku, tunda kema kin iya driving din, ai sai ki tuka ku, kuje ni Babu inda zan fita yau domin kuwa ina da kallon kwallo yau About  12:00 to 2:00,

Dan haka kuyi tafiyan ku, kawai.


 Kusa dashi Nabiya taxo ta zauna tace haba yayana please dan Allah ka taimaka ka kaimu bafa jumawa zamuyi ba, a mun dade muyi 1 hours 

Please dan Allah yayana.


 " Tabe bakin sa yayi yace babu fah inda zanje ehe, domin na gama gane ku a gidan Nan, idan kuna son abu a waje na, zaku na lallaba ni, Amma daga zarar na muku abunda kuke so to babu wani dan iska baya na.


  " Sorry ya Sadiq idan baka kaimu ba waye muke dashi wanda zai kaimu, please dan Allah kayi hkr. Kayi dropping din mu cewar Nabiya.


 " Duk fah magiyar ki Naby baxanje ba, kuje idi driver ya kaiku.


  " Kamo Hanun Nabiya Khady tayi, tace tashi muje mu karasa Aikin mu sister wannan baxai kaimu ba, gara muje mu kama Idi driver zaifi mana sauki.


  " Tashi Nabiya tayi tace, muje sis, kai kuma wlh zaka gani sai mun rama.


 " Dariya Sadiq yayi yace sai dai ku rame, yara.


 " Juyowa khady tayi tace  ai yanxu mun wuce munzalin da za'a kira mu da Yara sai dai ace y'an mata.


 " Dariya Hajiya tayi tace oh kudai idan kun hadu waje daya sai kun taba Hali, kinga khady idan kun tashi tafiya ku dauki key na mota na, kija ku.

 Sai karki kuskura kike wannan uban gudun a titi , 

   Kai kuma Sadiq idan ka samu times koda Ranar da baka da lectures ne, kake koyawa Nabiya driving.


  Tsalle Khady da Naby sukayi, cikin farin ciki suka rungume Hajiya.

 Thank Hajiyar mu Allah dai yabar kauna.

  Gwaliyo sukayi wa Sadiq Naby ce tace, kaki kaimu gashi kuma an bamu motar zamu tuka da kanmu.


  " Za dai ta tuka ke kuma ina Kika iya driving yar kauye kawai.


  " Oho dai Amma dai yanxu gani nan cikin birnin a zaune daram.

 Gashi har mota zaka koya min, Kuma dole ka koya min😜.


  Ko kafin ya Sadiq yayi magana Khady taja Hanun Naby sunyi kitchen.


  " Kwafa yayi sannan ya tashi tare da cewa Hajiya ni nayi ciki zanje na dan kwanta zuwa 12:00 ki tashe Ni.


 " Da toh Hajiya ta Amsa sannan ta tashi itama tayi nata dakin.


  " Misalin 11:00am Naby da Khady suka fito cikin wani had'ad'd'en boyal less green color dakin Hajiya suka nufa.

  Sun tarar da ita tana ninke kayan da aka wanke mata, Khady ce tace Hajiya ina key din yake.

 

 Nuni ta musu da saman Wadrop  dinta.


 Bayan sun dauka ne suka mata sallama, adawo lfy ta musu tare da gargadin su akan su dawo da wuri kar su dad'e.


  Annur plaza suka nufa, 

 Fannin turaruka suka yi, inda suka jidi sosai Khady kadai ta d'ebi set 8 yayin da Naby ta d'ebi set 10.

   Juyawan da Naby zatayi taji taci karo da mutum, kusan a tare wayoyin Hanun su suka zube kasa, dukan su sunkuyawa sukayi da niyar daukowa Naby ta riga kai Hanun ta kasa, yayin da bisa kuskure shima ya daura Hanun sa, akan nata, wani irin shakin gaba ki d'ayan su sukaji, yayin da kirjin su ya buga a lokaci daya.

 Dago idon ta Nabiya tayi domin Ganin waye ne wannan.


 " Sark'ewa idon su yayi da na juna yayin da yaji wani bakon lamari ya ziyarci zuciyar sa,  ya kuma kasa dauke idanun sa akan ta, a zuciyar sa yake cewa, wow beautiful Baby.


  " Daniel dake bayan sane yace Oga KAMAL mun gama kai muke jira, da sauri Kamal ya kauda idon sa daga cikin nata, yace okay ina zuwa.

 Kallon Naby Yayi yace sorry Yan Mata.


  Kauda kanta gefe tayi ba tare da ta tanka masa ba ta mike tace, sis Khady muje.


  Murmushi KAMAL yayi yace Yan Mata na bata Miki rai da yawa Koh, shiyasa baxa ki min Afuwa ba.


  Nan ma shuru Naby tayi ba tare da ta kulasa ba, 

 Khady ce tace, yar uwata mai yafiya ce, ina da tabbacin yanxu ma haka ta yafe maka, kawai dai ina ga yanxu Babu Ra'ayin magana ne, a tare da ita.


  " Sis Khady kamar haka naji ta Kira ki dashi Koh.


 " Ehh Amma Ainihin suna na Khadija in ka Kira ni da Khady ma babu laifi.


 " Na gode sis Khady, ko zaki iya fada min sunan yar uwar taki.


  " Kallon Nabiya tayi yayin da suna hada ido ta doka mata harara, dariya Khady tayi tace


" Sunan ta Nabiya Amma ni ina Kiran ta da sister Naby.


  " Nice name wayar sa ya mika mata yace samin phone number naki da Kuma na yar uwar ki Naby.


 " Karba tayi tasa mishi numbern ta ta miko masa, tace ita sister Naby babu waya yanxu a hanun ta, Amma ina ga wannan ta isa muyi sharing da ita.


  " Zaro😳 ido kamal yayi cikin Al'ajabi yace Sister Khady ya zaki cemin wannan Beautiful Babyn bata da handset, Gaskiya in possible.


 " Kufula Nabiya tayi, cikin fada tace kinga sister Khady idan baxa ki zo mu tafi ba, ni kinga tafiya ta ya zaki tsaya kina bata mana lokaci Akan Abunda baida Amfani.


  " Sake baki Khady tayi tana kallon Naby domin ita dai bata san Naby da fada ba amma gashi ta dage sai yi take yi.

 

 " Dariya ma ta bawa KAMAL yace Naby niko nake.......


 Da katar dashi tayi tace ya isa haka bani da time dinka, sannan ta wuce ta barsu tsaye a wajen.


 " Hkr Khady ta bawa KAMAL sannan tace zasuyi waya ko zuwa anjuma.


💫💫💫💫💫💫💫💫


Washe gari da safe Baba ya fito suka gaisa da Khabeer sun dan taba hira sannan ya koma cikin gida yasa MAMA ta bada abun Karin kumallo a kaiwa Khabeer.


 " Koko da kosai ta bawa Nasreen tace hingo kije ki kaiwa kwarton naki shegiya ta maxa an gado Halin uwa.


  Ita dai Nasreen Bata ce mata komai ba ta dauki abun Karin kumallo ta nufi wajen Khabeer.

Yana zaune a zauren gidan Akan wata karamar taburman kaba.

Ajiye masa tayi sannan ta gaishe sa.


 " Cikin fara'a ya Amsa tare da bude kwanon Abincin.

   Shidai harga Allah baxai iya cin abincin da ya fito daga hanun Mama ba, domin a iya jiya kadai ya kyamace ta.

  Gefe ya matsar da Abincin sannan yace Nasreen.


 " Dago kanta tayi tace na'am.


  " Ko kinsan dalilin daya fitar da Mahaifiyar ki daga kauyen Nan.


 " A'a kwad'o ban sani ba wlh.


 " Okay mahaifiyar ki bata Halin lfy, dan tun barin ta garin nan bata magana sai dai ido kawai. Munyi 

Magani Babu wani nasara, a karshe ma dai ance dole sai an dawo da ita gida sannan asan ta inda za'a fara mata magani dan haka tunda Allah yasa na gane garin su, na yanke shawarar yau din nan zan koma gida, domin mu dawo da Mamy wannan kauyen domin sama mata magani.


" Cikin farin cikin nasreen ta dago kanta tace ...........



Kuyi hkr da wannan wlh ban samu time ne kwana biyun Nan ina zuwa Aiki ga kuma aikin cikin gida,

 

Kumin afuwa sisters🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻





Share

    And 

   Comment



Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


    (Ummu Nasmah)

[12/1, 12:53 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya Hana Gamji)

              Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳



Story And Writing

           

           By


 Rasheedat Usman


             (Ummu Nasmah)



🤳🏻

08147537180


               

               *﷽*


Deducted to


Zara'u musa.


 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



 P•••••••3️⃣0️⃣ to 3️⃣1️⃣


" Dan Allah k'wado ka tafi dani naje naga Ammi na, ina tsoron kar kak'i dawowa Idan ka tafi, idan yaso sai mu dawo tare.


 " Murmushi Khabeer Yayi yace a'a Nasreen baxan tafi dake ba, domin kuwa koda nace zan tafi dake mahaifin ki baxai yadda ba.

  Bare ma zan dawo, nan da zuwa sati d'aya kiyi hkr, zaki ga mahaifiyar ki insha Allah.

 Na Miki wannan Alkawarin.

   Sannan karki kuskura ki sanar da kowa kinji labarin inda mahaifiyar ki take, kinji Koh.


 " Shikenan kwod'o baxan fadawa kowa ba, Allah ya maida ka gida lfy, yasa ka cika min Alkawari na.

  To yanxu kwod'o ya maganar zuwa kiwon da Baba yace zamu na zuwa tare.


 " Gaskiya Babu ita, dan banga wani Alamun Rashin kula a tattare da su ba, kawai yanxu ki tashi kije ki kira min Baban naki.


  Da to ta amsa tare da mikewa ta shiga cikin gidan, a bakin kofar dakin MAMA ta tsaya gefe kadan da inda yar gwal take kwance.


 " Sannu Adda dake haka take kiran yar gwal dashi, ya jikin naki.


 Ya mutsa fiska yar gwal tayi cikin gatsali tace, dallah malama kauce daga kaina jikar mayu, kinxo ki k'arasa min k'afar ne, gashin Yanzu ma samin ido da kikayi a cikin gidan Nan, yasa kafar tana min Ruwa.


  Mama dake cikin madafi ne tace " yar gwal keda waye nake jin muryar kine, kodai baki ne.


  " A'a Mama wannan jikar mayun ce yar karuwa taxo ta tsaya a kaina, yiwa wacce zata bani magani.


  " Daga cikin madafin MAMA tace, ke Nasreen ki kauce daga kanta kafin na fito na same ki, ranki ya b`aci.

   Shegiya mai bin maxa, suna kwakuleta, to dan ubanki wannan kwad'on kam yafi karfin ki.

 Sai dai irin su yar gwal, kuma bari kiji na fada miki, idan ma sonsa kike to ki cire sa, a ranki, domin wannan mijin yar gwal ce, dole sai ya Aure ta ko ta Halin Yaya.


 Barin wajen Nasreen tayi, ba tare da ta tankawa musu ba, domin kuwa ita ko a ranta Bata taba kawo soyayyar wannan kwad'on ba, bare har ace na cire sa a Raina, to wai ma idan banda mama, ina ni ina wannan mai kyawun mutum, kamar balarabe, me zaiyi Dani, yar kauye marar gata.


Tsuka yar gwal taja shegiya tsinanniya akan ki wannan tsinanannen jungudo ya karya min k'afa.

     Daga murya tayi yanda Mama zata juyo ta tace, wlh ina sonsa Mama, ki taimaka nima na shiga binnin Nan. 


 Ai kamar ma yaso ki an gama, indai bokaye basu kare ba a duniya, dole ya Aure ka.


 (To fah bari muga kota wani Hali Khabeer zai so yar gwal 😄 )


      Nasreen  dakin mahaifin su, ta shige risinawa tayi tace, " inbali jam Baba.


 " Sai jam, ya baku fita kiwon ba, har yanxu Nasranatu.


  "Na mishi magana shi kwad`on  yace min na masa magana dakai tukunna, yana zauren kofar gida.


 " Shikenan zanje na samesa, kiran sunan ta Baba yayi yace Nasranatu.


  " Na'am Baba.


  " Baxan gaji da baki hkr ba akan abunda ake Miki Acikin gidan Nan, nasan kina hkr, Amma dan Allah ki kara hkr akan hkr, tabbas ana cutar dake, a cikin gidan nan, mussaman Salame, Babu yanda na iya da ita, ban isa na mata magana ba, yanxu sai ta hauni da zagi, har mak'wafta  sai sun jiyo mu, ata magana ta, a gari ana cewa matata tafi karfi na.

  Nasan kina jin zafin rabuwa da y'an uwan ki mussaman ma Nuruddeen da yabar duniyar ma gabaki daya gwara ita Nabiya muna sa ran zamu k'ara Ganin ta, amma shikam Nuruddeen ya tafiya kenan har Abada baxai dawo ba, idon sane ya ciko da hawaye, ya ci gaba da cewa, akwai bakin ciki sosai a cikin zuciyata, mussaman na rasa AHALIN Maimuna da nayi, ina jin ciwo sosai a zuciyata, ke kadai ce wacce kika rage min nake kallon ki tamkar MAIMUNA.

  Kuka ne yaci k'arfin sa ya kasa k'arasa maganar.


 Itama dai Nasreen kukan take, sosai na rashin y'an uwan ta, ga wani irin haushin mahaifin nata da take ji, mussaman idan ta tuno cewa, bakin cikin sune yayi sanadin y'an uwan ta. 

   Tashi tayi ba tare da tacewa Baba komai ba, domin kuwa kallon tsana take masa.

  Har taje bakin kofa taji muryar Baba yana cemata, kije ki gidan Goggo tana neman ki.


 To kawai tace sannan ta fice, taje dakin su dauko hijab, gidan su Indo tayi niyan zuwa ta rakata.


  " A zauren gidan Baba ya fito ya sami Khabeer yana zaune.

   zama shima Yayi, tare da yiwa Khabeer sannu da hutawa.

  "Yace Nayi zaton ai kun jima da tafiya wajen kiwon, sai yanxu Nasranatu take cemin Ai baku tafi ba, kace amin magana.


 " Ehh Baba ni nace ta maka magana, daman ina bukatar naje gida ne yau dinnan, saboda ina da uzururruka da yawa a gaba na, kuma naga su shanun babu wata Alamar yunwa a tattare da su, kuma Baba Gaskiya tunda na shigo garin nan service din waya na ya dauke, Babu Halin nayi waya gashi kuma ban sanar da iyalina nayi tafiya ba, nayi tunanin idan na karaso na Kira ta, na sanar da ita, kaga kuma hakan bai yiwu ba, gara na koma ko zuwa wani sati na dawo.


 (🤔 To fah ko meye dalilin da yasa Khabeer yaki sanar da Baba mamy tana wajen su, zai koma ne ya dauko ta?  kudai biyo ni muji menene dalilin sa na yin hakan)


  " baba ne yace, Babu damuwa khabiru tunda hakan kace, yanxu idan ka shirya zaka biya ta gidan mlm Iro ne dan yace tare zaku koma.


  " Baba ai a shirye nake jakata kawai zan dauka na shige zanbi wajen Baba iron naji, idan ya shiryawa tafiyan to sai mu tafi.


 ' to shikenan dauko jakar naka na maka rakiya, zuwa gidan mlm Iron Koh.


  To yace tare da mikewa, hakikanin Gaskiya Khabeer yaso sake haduwa da Nasreen Amma ina hakan bai samu ba, sakamakon kasawa da tsarewa da Baba yayi.


  " Isar su gidan Baba iro sun samu baya nan yayi lanbun mlm sale,

  Can din suka nufa, bayan sun gaisa ne, da mlm Iro da mlm sale

 Baba yake sanar dashi cewa khabiru fa zai koma gida yau yau.


 " Cikin mamaki mlm Iro yace lfy kuwa khabiru zaka koma gida yanxu, kodai baxaka iya cimar kauyen namu ba, kasan cimar mu da taku ba daya bane.


 " Murmushi Khabeer Yayi yace, a'a wlh Baba Iro ai abincin ku bashi da wani, kowa ma zai iya cinsa, akwai uzurin da zai maida nine,  Baba iro kaifa kasan yanayin Aiki na, yakan iya taso min koda yaushe, kuma nayiwa shi Baba baya nin abunda zai maida ni gida.


 " Hakane kam khabiru ku ba zaunannu bane, shikenan kaje kawai ni ko jibi na dawo.


 " Hanu Khabeer ya mika musu sukayi musabaha tare da dauko rafar kudi na dubu dari 100,000 ya ajiye musu, yace su raba Babu yawa.


Godiya suka masa sosai, har Bakin motar sa suka rakasa, sanda yaja sannan suma suka koma.


 Iya daf da ficewa daga cikin Rugar ya hango Indo zaune nesa kadan da shanun ta,

  Paking yayi a gefe sannan ya fito daga cikin motar, wajen indo ya karasa, 


  " Sannu yan Mata.


 " Dago kanta tayi suka hada Ido murmushi ta masa, tace kwod'o daman kana kauyen nan har yanxu baka koma binnin ku ba.


 " Ina nan yanxun Nan da kika ganni zan koma, sai dai kuma ban samu kai ko daya ba a garin na ku.

 Shine na tsaya ko zaki bani naki.


Murmushi  ta masa, tace " baka da mantawa kwod'o wai daman tun sanda na raka ka gidan kawu Iro, kana Nan.


 " A'a ba gidan sa na zauna ba gidan Malam Musa makiyayi.


  " Da gaske kwad'o gidan su subajo nane fah, koda yake rabona da gidan tun sanda akayi sadakar Arba'in din Nuruddeen.

 Yan uwan kune a gidan.


 Murmushi Khabeer Yayi ba tare da ya bata Amsar tambayan ta ba, yace kinga yar jarida ni na tafi kar nayi rana a hanya.


 Allah ya kiyaye hanya ta masa, sannan yaja motar sa sai cikin garin Gombe.



  💫💫💫💫💫💫💫

Sha biyu daidai Khabeer ya isa cikin Unguwar New GRA Hom ya dannawa mai gadi, kafin ya wangale makeken get din.


  Daniel dake zaune gefen  mai gadi ne ya tashi a firgice, cikin tsoron Abunda zai faru dashi, idan aka sanar da ogan nasa b'atar dansa junior.


  Paking space yaje yayi paking sannan ya fito, a motar, da sauri jami'ain dake tsaron gidan suka nufa sa domin gaisuwa,

 Bayan sun gaisa ne Khabeer ya maida kallon sa kan Daniel, yace 


 " Lfy kuwa Daniel, nagan ka so silent haka.


 " Lfy lau oga cewar Daniel.


 " Yanayi ne ya sanja kenan, to ga key din motar nan, kaje station din mu, wajen Kamal, kace yayi arranging case din cocaine din nan da na bar masa, ya ajiye duk wani bayanai daya samu a kusa ina zuwa Around 6:00pm station din.

   Idan ka dawo ka bayar a wanke motar ni zan shiga ciki na samu na huta.


 Karban keyn yayi yace yes sir, 


  " Da sallama ya karasa cikin falon nasa, Babu kowa sai Zuhura tana zaune saman daining tana cin abinci, amsa sallamar tayi tare da kawar da kanta gefe 


 Murmushi Khabeer yayi domin kuwa yasan dole haka zata faru, ana fushi dashi, yayi kwana biyu baya gida, ba kuma tare da ya sanar da ita ba.

 Karasawa Bakin daining din yayi tare da daura kansa a kafadar ta, yace Habibty na, baxa'a min sannu da dawowa ba ne.


 " Cewa tayi sanda ka tafi ai kace min, nayi tafiya, kaga kuwa ai Dole yanxu nace maka sannu da dawowa.


 " Amin Afuwa Habibty nayi laifi🙏🏻.


  " Shikenan ya wuce sannu da dawowa.


  " Yawwa Habibty na ko kefa, yanxu bari na karasa daki na samu na watsa Ruwa ko zanji Dadi, 

   Ki samu ki hada min tea mai kauri kafin na fito, dan wlh ina jin yunwa sosai.


  " Kiss ta manna masa a fiskar sa tace angama Habibina.

    

  Shigewa dakin nasa yayi, abun Haushi abun takaici yanda ya tafiya yabar dakin sa, haka ya dawo ya sameta.

  Duk k'ura, kansa ya kada sannan ya hau gyaran dakin tun kafin ya shiga wankan.


  Ita Koh Zuhura dakin ta, ta nufa, ta sake wasu kananan kaya, tare da kara bude jikin ta da turaruka, domin kuwa a hanu take, tana bukatar mijin ta, 


  Kitchen ta nufa ta hada masa tea sannan ta yi dakin nasa.


 Fitowar wasa daga wanka kenan ta shigo d'akin towel ne a jikin sa, zama yayi gefen ta tare da karbar kafin tea din.


 A hankali yake kurbar tean sosai yasha sannan ya mika mata cup din yace ta mayar kitchen, 

Dressing merro ya nufa ya mulke jikin sa da mai Mass kamshin da Dadi, turare ya fesawa jikin sa.

 Gajeren wando kawai yasa sannan ya fada saman gadon sa.


  A kwance Zuhura ta shigo ta samesa, tsayawa tayi tare da rike k'ugu.


 Murmushi Khabeer ya mata, tare da Miko mata Hanu Alamun taxo.

  Fad'awa jikin sa tayi, cikin kissa da kwantar da murya tace I miss you Habibina.


 "  Miss you too baby na.

   Mai zan samu ne a wajen ki yau, wacce zan huce gajiya ta.


  " Duk abunda kake bukata zan baka shi yau.


  " Ke nake bukatar ki mallaka min kanki😉 tare da kashe masa ido daya.


   " Murmushin itama tayi tare da manna bakin ta a nasa.


  " Sanda sukayi wasa da junan su sosai sannan ne suka Lula duniyar ma'aurata.


 Bayan komai ba ya lafa ne sun dawo cikin nutsuwar su, Zuhura na kwance saman kirjin Khabeer ta fara magana kamar wacce take rada.


 " Please Abban junior, dan Allah ka dauko min junior, ina bukatar ganin dana a kusa dani, shekarar junior fa guda kenan baya tare Dani.


Shafa kanta Khabeer yayi yace, Babu damuwa zan daukosa nima kaina ina bukatar naga junior yana tsakanin mu.





Share

   And

 Comment


Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻



(Ummu Nasmah)

[12/3, 9:17 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya Hana Gamji)

              Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


Story And Writing

           

           By


 Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)



🤳🏻

08147537180


*بسم الله الرحمن الرحيم*



 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


 Deducated

               To 

AKAN Y'AR UWATA fans Gaskiya naji dadin yanda kuka karb'i book din Hanu biyu.

  Na gode sosai Allah ya bar zumunci.




P••••••••3️⃣2️⃣ to 3️⃣3️⃣


  "Amma gsky Zuhura ina son ki rage yawan tsangwaman junior da kike yi, kinga abunda yake sawa, yaron nan baya son zama A wajen ki kenan, Sam baki da hkr akan yaro, yanxu ko na daukosa ma,ba zaku shirya ba, indai ba rage saurin Hanun ki, kikayi ba, Abu kad'an duka.


 " Abban junior, bawai ina tsangwaman junior bane

Baya jin magana ne, shi ga rigima ya masa yawa, duk hkrn ka, junior sai ya k'ure ka Amma ba damuwa zan gyara, insha Allah.


  Murmushi Khabeer Yayi, "yace yawwa ko ke fah, kinga idan kina lallab'in sa zaku zauna lfy, kinsan shi Yaro yana son mai Rarrashin sa, sannan Zuhura akwai abunda yake damuna a zuciyata game dake.


  'Dago kanta Zuhura tayi ta kalli Khabeer tace " Abban junior wani Abune kuma yake damun ka game dani.?

 

  " shuru Khabeer yayi sai can yace, Anya kuwa Zuhura bakya family planning kuwa? Ki duba fah kiga yanxu haka shekarar junior 6 Amma har yanxu shuru ko b'atan wata baki K'ara yiba.

  Gaskiya Zuhura ina da Alamar tambaya a gareki, domin kuwa nasan yanda kike da k'iyayyar Haihuwa, junior ma kansa da yaya Kika yadda kika haife sa.


  " Sanja fiska Zuhura tayi, cikin kissa da munafurci, tace Haba Abban junior yanxu dan Allah zargi na kake, Gaskiya banji dad'in hakan ba, domin kuwa ni kaina a Yanxu ina buk'atar haihuwa, Akan wani dalili zanyi family planning kenan?


 " Dole na zarge ki Zuhura domin kuwa shi kansa Cikin junior kinyi kok'arin zubar shi, da yaya Kika yadda junior yaxo duniya, karki manta da cewa fah ke da bakin ki  kince min daga junior kin rufe haihuwa, sannan yanxu kice ina zargin ki, Ai dole na zarge ki kuwa.


 " Cikin hasala Zuhura ta tashi tace, oh Ashe baka manta ba kenan, okay tunda ka tuna shikenan, ina tunanin Ai shi junior ma kad'ai ya ishe mu rayuwa, to akan me zaka damu da cewa sai na k'ara haihuwa?


  " Saboda ina buk'atar haihuwa, sannan Kuma ki sani baxan zauna da d'a daya ba, domin kuwa Allah baiyi ni acikin sahun wad'anda suke da k'oyi daya a duniya ba.


  " Okay sai kaje ka nemi matar da zata haihu maka, Amma ba Zuhura ba, domin kuwa baxan ta haihuwa ba kamar Akuya, naxo na tsufa da wuri, ka cuceni kai ka zauna kana yaron ka, 

 Kana ganin na lalace halittu na, sun fara sauyawa kaje ka Auro yarinya ni ka cuceni, dan haka Babu wani haihuwar da zanyi, junior ma kad'ai ya ishe mu.


 " Ya ishe ki dai Amma ba ni ba, ina buk'atar wani bayan shi dan haka zan nemi wata Matar da zata haifa min yara a cikin gidan Nan, domin kuwa Allah ya Halatta min na Auri Mata d'ai d'ai har 4 kinga kuwa ai baxan ga bak'in Cikin yara ba, tunda Allah ya bani wannan damar, ke kije ki zauna da guda d'ayan Amma ni ko guda goma 10 Allah ya bani alhamdulillah Ina buk'atar su kuma zan gode masa domin kuwa ni'ma ya bani.


 " Wlh k'arya kake Khabeer, Babu wata Y'AR ISKAR matar da ta isa ta shigo gidan Nan, da sunan cewa matar ka, domin kuwa ni kad'ai ce matar ka daga nan duniya har lahira, Banda dai kishiya a cikin gidan Nan, sai kuma idan mutuwa nayi, kayi Aure Amma banda ina raye Kam.


  " Murmushi Khabeer Yayi yace " saboda tare aka Halicce mu dake, dole na k'arasa Rayuwata dake, tunda na Riga da na zama wahalalle, Zuhura ya kamata kisan cewa ina mungun d'aga Miki k'afa a cikin gidan Nan bawai fa k'arfi na kika fiba, yasa nake kyale ki, kawai ganin damata ne yasa nake kyale ki, Amma ki sani cewa kin fara kaini bango, ki kiyayi Ranar da zaki k'ure ni, domin kuwa Ranar baxata Miki kyau ba.


 Cikin huci Zuhura tace " ba'a halicce mu tare ba, Amma ka sani cewa an Halicce kane domin ni d'aya, zan iya Aikata komai a kanka, koda kuwa kisan kai ne, indai akan kane zanyi shi.


  Zuwa yanxu Zuhura ta fara k'ure Khabeer, domin kuwa yasan idan ya kara wasu lokuta yana sauraron ta, komai zai iya faruwa, hakan ne ya sashi tashi ya bud'e drowarn sa, kayan sa ya dauka yasa ka, ya fice ya barta tsaye tana k'ananan maganganun ta.


  Huci kawai Zuhura take yi, domin kuwa ta dauki Aniyar cewa idan har Khabeer yayi kuskuren neman Aure to wlh sai ta kafa masa mummunan tarihi.

   Cikin Bala'i take cewa, Aikin Banxa aikin wofi, baxan haihun ba, kuma baka isa k'ara Aure ba, Idan ma wad'annan shashashun iyayen naka ne suke zugo ka.

  Bude drowarn mirrorn sa tayi, ta dauki rafar yan dubu dubu sannan ta fice.


  Shiko junior yau kwanan sa 3 a hanun Ajabo, wahala da Azaba babu irin wanda Ajabo baya ganawa junior, gaba ki daya yaron ya rame Yayi bak'i hatta bakin nasa ma ya mutu.

  Rabon da su basa Abinci tun jiya da dare.

Wani irin Azabebben yunwa yake ji,

 Kuka yake curcur da hawayen sa, yana kiran sunan Abban sa.


  Ajabo dake zaune, a gefen junior ne, yaji kukan yaron ya isheshe, cikin hasala ya tashi ya figesa tare da wurga sa, cikin wani Bakin d'akin da Babu koda haske a cikin sa.


  " Kara sautin kukan sa junior yayi Yana, zasu kashe ni Abba basa bani Abinci, Daddy kaxo ka dauke ni a wajen, momma kema kixo ki dauke ni, SARAH kixo karsu kashe ni, Babu abunda na musu, suka kawo ni, Nan Mamy kinga kina sona kixo ki dauke ni daga wannan gidan, Papa khalid uncle Daniel, Yunwa nake ji.

  Sanda yayi kukan sa, mai isar sa, Babu mai ceton sa, a haka bacci b'arawo ya sace sa.


  Mamy tana zaune a falo tayi tagumi, rike da photon junior a Hanun ta, hawaye ne suka zuba a fiskar ta, na rashin junior,


 Momma dake zaune a kusa da Mamy ita ma tayi, shuru, Domin kuwa ita yanxu ta fitar da tsammanin za'a Sami junior , tabar komai a Hanun ubangiji domin kuwa yafi ta sanin Halin da junior yake ciki.

  

  Fitowa Momy Sarah tayi, taci Uban kwalliya da jaka a Hanun ta, ta zuba hijabin munafurci, 

Kallon momma da Mamy tayi, ta tabe bakin ta, " Tace maman Yara ni zan fita unguwa.


  Ajiyar zuciya momma ta sauke tace a dawo lfy, 


  " Yawwa Momy Sarah tace a dak'ile kamar baxa ta Amsa ba.

  Sannan ta fice.


   Darect sabon gidan Hajiya Hindatu Wanda suka sauyawa Mata, ta wuce, hom ta danna, mai gadin ya wangale mata get din.

   Paking tayi sannan ta k'arasa Cikin gidan.

A falo ta tarar da Hajiya Hindatu zaune.


  Kusa da ita Momy Sarah ta zauna, tace " shegiyar gari, kawai sai kika buya.


   " Kedai Hajiya Saratu bari Abun ne sai da b'oye kamanni, kinsan nine next mission din, d'an ku, dole kuwa na iya taku na.


  " D'an masu d'a dai, domin kuwa ni ba dana bane.


  " Wai Hajiya Saratu wani irin mataki zamu dauka akan yaron nan ne Khabeer, kinsan idan har ya gane daya daga cikin Yan kungiyar mu akwai matsala, babba fah.


  " Dariya Momy Sarah tayi tace to kura Uwar tsoro, wani mataki zan dauka ko wani mataki na dauka, karki manta da cewa Saratu ne fah na sa an dauke min d'an sa, junior, neman hanyar fitar dashi nake daga gombe, xuwa Kano, A hada dashi a cikin yaran da zamu fita dasu domin sayar da kidney nasu, aje can a hallaka sa.

   Kinga yanxu hankalin sa zai bar kanmu ya koma na neman d'an sa.


  "Kai k'awata dadi na dake akwai Kai, kanki na mungun kawo wuta, yanxu har kin Dan samin nutsuwa a Raina.


 " yanxu dai ba wannan ba, ya maganar yara ya'n matan da nace Miki ana bukatar su, guda biyar, kinsan fah John ya kirani jiya yace min a cikin satin Nan ake son yaran.


  " Na samu guda hudu kuma irin wadanda ake buk'ata saura daya ne, kwanakin baya akwai yarinyar dana gani a tashar mota, ta cika 💯, amma Abun takaicin kafin na karasa gare ta, wata ta dauke ta,

  Sai dai na bibiyi matar na kuma san inda yarinyar take, Dan haka bani 2 days zansa a dauko min ita.


   " Good aikin ki yana kyau Hindatu, Ni yanxu zan wuce sai naji ki.


Shiko Khabeer daga gidan sa, office din su ya wuce darect.

  Office din KAMAL ya shiga, tare ya same su da Daniel suna zaune, suna binciken files.

 Tashi dukan su sukayi kame tare da sara Masa, waje Khabeer ya Samu ya zauna. Yace

  " Kana Nan kenan Daniel har yanxu.


 " Ehh wlh Sir nazo kuma oga KAMAL yadan bani Aiki.


 " Yayi kyau, KAMAL.


  " Yes sir cewar KAMAL.

  Barka da dawowa.


  " yawwa Ya maganar case din dana bar maka, me ake ciki yanxu.


  " Sir case din nan fah har yanxu Babu wani change, shi markel Sange daya kamata mu sami good information a wajen sa, yaki bamu hadin kai, mun masa Azabar mun masa Rarrashin amma yaki, bamu hadin kai, da alamun dai ko kashe sa zamuyi baxai bada sirrin kungiyar su ba.

  Ita kuma Hindatu har yanxu mun kasa gano inda take.


  " Murmushi Khabeer Yayi, yace okay shi markel yaki bada information dinsu kenan.

 Ba k'in fad'a yayi ba kune baku masa yanda zai fada ba, Amma nasan yanda zanyi dashi, ita kuma Hindatu, gobe zamu koma gidan ta, zamu sake bincike sosai.

Dole ne sai mun binciko wannan kungiyar domin kawo k'arshen ta.


  " Shikenan sir Allah ya kaimu, goben, Sir.


  " Umhum menene?


 " Sir daman so nake na tambaye ka, ko kaje gida yau.


 " Wani gida kenan? cewar Khabeer.


  " Gidan ku, nake nufi sir.


 " A'a banje ba, yanxu nake da niyar zuwa idan na tashi daga nan.

 Amma lfy kuwa kamin wannan tambayan?


 " Ehh to Sir daman so nake na sanar dakai cewar, yau kimanin kwana Uku, an nemi junior an rasa shi, munyi bincike Amma Babu wani nasara.


  " A zabure Khabeer ya mike yace, what? Me kake son cemin, d'ana junior ya b'ata, a garin yaya hakan ta faru?


 " Sir Nima ina Nan office zaune, brothern ka khalid ya k'ira ni, yake cemin, tunda junior yaje school, times din tashin sa yayi, da akaje daukar sa, sai ba'a gansa ba, munje school din munyi bincike, a yanda mai gadin school din yake sanar damu cewa, yaga yaron ya fita, da ya tare sa sai ce masa Yayi wajen mai sayar da sweet din Bakin get din zaije ya saya.

 Yace to tun sanda ya fita sai kuma wata sabga ta debesa, yama manta cewa da yaron ya fita.


  Lokaci d'aya idonun Khabeer sukayi Red color, Cikin bacin rai ya kalli Daniel, yace " ina jami'ain tsoron dana bayar suke lura da junior a cikin school din, sannan kai Kuma meya hana ka zuwa da wuri ka dauke sa, nuna Daniel yayi da yatsa👉🏻 duk abunda ya sami d'ana kai da IB ne sanadi Domin kuwa kune wanda na baku tsaron sa, har kukayi sukaci aka d'auke min.

   Tabbas Babu shakka wad'annan Yan kungiyar da muke bincike, sune suka dauki junior Domin kauda Hankali na a kansu.

    Sai dai daukar junior ba ita bace nasarar su.


💫💫💫💫💫💫💫💫


Tun jiya Nabiya take fushi da Khady, Akan tsayawa sauraron KAMAL da tayi,

  Ita dai Khady Babu abunda take sai rarrashin ta.

 A haka Sadiq ya fito ya samesu.


  " Kai ina Hajiya ne?


  " Naby ne tace Hajiya bata nan ta fita Aiki tun safe.


   " Okay wai da, yau ina son zuwa Abuja ne, kinsan Ambassador UMAR ya bani zane, yana son za'a fara ginin a cikin satin Nan, 

  So ina son tfy yau, Idan yaso gobe na dawo.


 " Khady ne tace to amma ya Sadiq kassan dai muna da kai A class Koh, kuma 2:00 zaka mana lectures, sannan kuma kace zaka tafi Abuja yanxu.


  " Mtss Ni harma na manta da ina da lectures daku, amma dai kinsan cewa, wannan kwangilar zanen yafi min lectures dinku muhimmanci Koh.

 


  " Amma dai yaya idan ka mana haka baka kyauta mana ba, kuma Allah sai na kai karar ka wajen Yaya Khabeer.


  Dariya Sadiq yayi, yace ni ai kin tuno min ma, ina son kiran sa, naci kaniyar sa, tun sanda na dawo, garin nan, na kirasa amma har yau mun kasa haduwa.




Share

  And

Comment




Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻


           (Ummu Nasmah)

[12/9, 2:24 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya Hana Gamji)

              Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


Story And Writing

           

           By


 Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)



🤳🏻

08147537180


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


Deducated

   To

KHADIJA TAHIR Mamyn Ajmal Allah dai ya bar kauna, Gaskiya ina jin dad'in yanda kike son book din SARA DA SASSAKA.


Murna


  Barka da dawowa Mamyn Ahlan.


Ina masoyan Gudu ajeji, to ku shirya ganan Zarahn Abdul ta dawo da Shirin ta domin cigaba da nishadantar ku.




P••••••• 3️⃣4️⃣ to 3️⃣5️⃣


Kusan 3 miss call SADIQ yayiwa Khabeer,  bai d'aga ba.

   Ajiye wayar Yayi yace


" wata k'ila baya kusa da wayar ne.


  Khady ce tace,

" ya SADIQ daman fah, yaya Khabeer yanxu ya daina zuwa gidan Nan, dan Ranar ma Hajiya take tambayan ko dai kun samu matsala dashi ne.


  "Matsala kuma Khady, wani matsala ni kuma zan samu da Khabeer, ba tare muke kullum ba, kinsan zaman waje d'aya shike kawo fad'a Ni nafi tunanin sabgogin sane sukayi yawa, yaushe ma ya cika Zaman k'asar na.


 " Hakane kuma ya SADIQ, Amma ina ga gobe zan d'auki Khady muje gidan sa, muji dalilin dayasa yake mana yaji yanxu.


 " Allah Ya kaiku lfy, daman kekam kun saba hawa sama ku rikito k'asa, watakil ma kafin kuje mayi waya dashi, bani da time ne ishashen da na d'auke ku munje gidan nasa.


  Ita dai Nabiya duk zancen nan da suke hankalin ta baya garesu yau kuma tunanin y'an uwan ta, takeyi,  Nasreen da Nuruddeen, ko wani Hali suke ciki yanxu, nasan suna nan suna shan wahala wajen Mama, Allah Sarki Adda Nasreen, ki yafe Ni ba'a son raina yasa na tafi na barku ba nasan kuna cikin k'unci da wahala. hawaye ne ya ziraro daga idanun ta.

  Maganar zuci take wanda bata san ya fito fili ba.


  Kallon su suka mayar gare ta cikin jin tausayin Halin da take Ciki, SADIQ ya tashi ya dawo kujerar da take, yace


  " Nabiya, meyasa baxaki dinga hkr akan jarabawar Rayuwar kiba, tabbas rashin d'an uwa akwai ciwo, Amma idan kinyi tunani ai ba mutuwa bace ta rabaku, insha Allah zaku had'u wata Rana, bare ma kuma Hajiya tace Miki, Idan Allah yayi dawowar Alhaji lfy, zata nemi ixinin sa, muje har kauyen naku, kinga idan tasan inda kike zaku na ziyartar juna.

   Dan Allah ki cire damuwar nan a ranki.


  Numfashi Nabiya taja sannan tace, Ya SADIQ Dole ne nasa damuwa a Raina mussaman idan na tuno Halin da ya'n Uwana suke Ciki, Suna Hanun Azzalumar Uwar rik'o, wacce kullum take Cikin k'untatawa rayuwar mu, bamu da wani yanci a cikin fad'in kauyen mu, agun mutum biyu kawai muke samun sauk'i Goggo da Baba, kuma suma sun juya mana baya, cikin kauyen nan kuma muna fama da gorin cewar mahaifiyar mu ta tafi yawon karuwanci, ina jin zafin AMMI a Raina, yanda ta watsar da rayuwar mu domin wani burin ta na duniya, na tabbata AMMI koda hak'k'in Nuruddeen kawai aka barta ya isheta, ganin ishara.

  Adda Nasreen kullum burin ta shine tayi karatun Boko, mai zurfi ta zama lawyer Amma tsabar rashin gata yasa daga primary muka tsaya, yau ni kuma da ban wani sa burin karatun a Raina ba gashi na samu damar ina ma Ace Adda Nasreen ce ta samu wannan damar ba niba.

   Bana son Rayuwar Adda Nasreen ya k'are a cikin wannan kauyen zanso Ace itama ta fito cikin birni, tayi karatu domin samun cikar burin ta, sai dai hakan baxai yiwu ba, saboda bata da wannan gatan.

  Share hawayen ta tayi sannan ta daga Hanun ta sama tace

  🙏🏻 Ya Allah ina rok'o gare ka daka inganta Rayuwar yan uwana, ya Allah ka k'addara saduwar mu, ya Allah ka kawo haske Acikin Rayuwar wad'annan bayin naka masu neman taimakon ka.


  Khady da hawaye ya gama wanke mata fiska na tausayin Halin da k'awar ta wacce ta zama mata y'ar uwa yanxu, tace Amin, tabbas sis Naby dole ki damu, ni kaina A yanxu haka na tausayawa y'an uwan ki, bare kuma ke da suke jinin ki, sai dai Abunda nake so dake shine ki sassauta fushin ki akan mahaifiyar ki, ki mata uziri domin kuwa baki san Halin da take Ciki ba

Watak'ila bata cikin hayyacin ta tabar kauyen naku, mussaman idan kikayi la'akari da Halin Uwar goyon ku, Sam bata da imani zata iya Aikata komai, dan mutum mungun Icce ne.


  Ya SADIQ ne ya nisa yace tabbas maganar Khady haka ne, Babu abunda d'an Adam baxai iya aikatawa ba, kuma ko wani Hali Uwar ki take ciki uwar kice, baxa kiyi fushi da ita ba, kisani cewa akwai Ayoyi da Hadith wad'anda suke nuna muhimmanci iyaye.

 Dan haka koda wasa karna k'ara jin kina Aibata mahaifiyar ki, gara ki fad'i Alkairi akan ta.


  Nabiya taji dad'in yanda su Khady suka nuna kulawar su a gare ta, har suke mata nasiha.

Ringing d'in wayar Khady ne ya katse musu zancen nasu, kallon screen d'in wayar SADIQ yayi KAMAL ya gani a rubuce, cikin tuhuma yake kallon ta, zaiyi magana kenan ta rigasa.


  " Bani yake nema ba to saurayin Nabiya ne, ita yake nema ba niba nasan yanxu zaka fara masifar cewa Akwai Alk'awarin SUDES a kaina.


  Dam !! Dam !! Dam gaban SADIQ ya buga, cikin zuciyar sa yake cewa, *TARKON DANA D'ANA AKE NEMAN KAWAR MIN DASHi.*

 Kallon sa ya mayar kan Nabiya, cikin tuhuma yace


*" Waye wannan Kamal din*?


 

 🤔🤔🤔 Ko wacce Amsa Nabiya zata bawa SADIQ.

   Nima dai Rasheedar ban sani ba.


💫💫💫💫💫💫💫💫


Khabeer office din ya bari, ya doshi hanyar gidan su, cikin tashin hankali.

 Isar sa k'ofar gidan nasu bai tsaya jiran a bud'e masa get ba, a wajen kawai Yayi paking ya doshi cikin gidan

 Tun a kam ya shiga cikin gidan yake kwalawa mutanen gidan Kira.

 *"Momma Momy Sarah mamy*


  Momy Sarah dake cikin kitchen ne ta fito da sauri jin muryar Khabeer dandai Babu Wanda yasan ya dawo daga kauyen. 


  Itama momma fitowa tayi, cikin sauri, illah Mamy dake kwance tana bacci bata ji kiran Khabeer ba.


  " Lfy khabiru cewar Momy Sarah? Kake mana irin wannan kiran.


  Momma kam jikin ta ne ya mutu data ga Khabeer ko bata tambaye sa ba tasan yaji lbrn b'atan d'ansa.


  Cikin kunar Rai yace 

  *"Momy Sarah garin yaya junior ya b'ata garin Yaya Akayi Wannan sakacin, ki fad'a min ina d'ana yake*


  " Cikin bugawar zuciya da tsoron ko Khabeer yasan cewa ita ta d'auke junior ne yake mata wannan tambayan.

 Da kyar ta had'iye yawu mai d'acin gaske, tace

  " Ni Kuma Khabeer ina zan sani yaron da aka turasa school.


  Ajiyar zuciya momma ta sauk'e  sannan taxo ta Kama Hanun Khabeer ta zaunar dashi tace kaga khabiru ka kwantar da Hankalin ka, komai ya samu bawa jarabawa ce daga ubangiji.

   Junior dai ya b'ata Babu inda ba'ayi nema ba Babu shi Babu lbrn sa, su kansu jami'ain naku sun yi k'ok'ari Allah dai shine kad'ai yasan inda junior yake.


  *" Momma ni zan Nemo junior a cikin Awa Ashirin da Hud'u idan har ban samo junior a cikin wadannan awannin ba, to zan cire uniform dina na ajiye wannan Aikin domin baida Amfani a wajena idan har na kasa ceto Rayuwar D'ANA guda d'aya a duniya, sai dai momma ina Miki rantsuwa da ubangiji na, wlh !! wlh !! wlh duk wanda na samu da Hanu cikin d'aukar junior, Wlh baxan tab'a d'aga masa k'afa ba, sai yayi munguwar dana sanin tab'a AHALI NA koda kuwa dan'uwa nane na jini agogon Hanun sa ya duba yace Yanxu k'arfe Hudu da Rabi na yamma, Nan da karfe Hudu da Rabi na washe garin gobe junior kana cikin gidan nan, murmushi Yayi azuciyar yace koma waye ne ya d'auki junior ya rage min yawan Aiki domin kuwa ina da tabbacin cewa wad'anda muke bincike akan su sune suka dauki junior*



    Momma ce tace, *"Ina bayan ka d'ari bisa d'ari Allah ya baka sa'a Muhammad Khabeer*



Itama Momy Sarah cewa tayi Allah ya bada sa'an, Amma fah a zuciyar ta Adu'ar rashin nasara take masa.


  Tashi yayi ya fice daga cikin gidan.


  *D'akin ta Momy Sarah ta shige cikin tashin hankali, 

wayar ta ta dauka ta dannawa Ajabo Kira, Switch Up aka cemata, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un cewar Momy Sarah, 

please Ajabo ka bud'e layin ka

  *Ina cikin tashin hankali yau, dole komai dare a bar garin nan da junior*

  


Tirkashi koya zata kaya, waye da nasara Momy Sarah ce ko Khabeer.


*Kudai kuci gaba da suburbud'o min ruwan comments nima zanci gaba da muku ruwan typing*




*Share*

     *And*

      *Comment*



*Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah)*[12/10, 2:49 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya Hana Gamji)

              Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


Story And Writing

           

           By


 Rasheedat Usman


 (Ummu Nasmah)



🤳🏻

08147537180


*بسم الله الرحمن الرحيم*


 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


Gaskiya Fans Babu abunda zance muku sai Godiya, yanda kuke Ruwan comment, Abun ba'a cewa komai.


  *SARA DA SASSAKA FANS*


  Comment dinku yana bada wuta 🔥🔥🔥.


Harma da sauran group din da ba nawa ba, na gode sosai Allah ya bar zumunci mai d'aurewa.


Kuci gaba da Ruwan comment ni Kuma zanci gaba da Ruwan Typing


*I love you so much fans* 😘




P•••••••••3️⃣ 6️⃣ to 3️⃣7️⃣


Zuciyar momy Sarah babu abunda take sai bugawa, har ta d'auki hijabin ta, zata fita taje gidan Ajabo, sai Kuma tayi tunanin idan ta fita yanxu kar a zarge ta, fasawa tayi ta cire  hijab d'in, falon ta fito momma kawai ta samu, Zama tayi itama, tare da kwalawa Nana kira.


Fitowa Nana tayi daga d'akin su, tace " gani Momy Sarah.


  " Ki shiga cikin kitchen ki k'arasa girkin nan zan shiga ciki na kwanta kaina ke ciwo.


  " Da to ta amsa sannan ta shige cikin kitchen din.


 Momma ce ta maida kallon ta kan momy Sarah, tace " Allah ya k'ara sauki, Alhaji ma ce ki had'a masa fruit salad, kafin ya dawo.


  " Okay bari Nana ta gama girkin sai ta had'a masa, ni bari na shiga ciki.


  " A fito lfy momma ta mata, ta mayar da hankalin ta kan tibi.


  Harar gefe Momy Sarah tayiwa momma, a zuciyar ta tace, " gayyar tsiya, kin haifi d'a ya addabe mu, insha Allah badai kuga k'arshe na ba, sai dai ni naga naku.


  Khabeer kuwa darect gidan sa ya wuce.

 A falo ya tarar da Zuhura tana zaune, rike da Novel na turanci a Hanun ta mai suna Heart beat.

Bai kulata ba yayi wucewar sa d'akin sa kasancewar haushin ta itama yake ji.

  Itama bata damu da shigowar sa ba, illah ma tab'e bakin ta da tayi, irin wannan damuwar kace.


  Uniform d'in sa Khabeer yasa tare da d'auko agogon sa sak da wanda ya sawa junior ya Hanun sa, yasa a aljihun sa, saboda tsaro ba dan tsoro ba, domin kuwa a yanayin Aikin su babu yarda tsakanin su da kowa, harma matar tasa Zuhura.

 Fitowa yayi ya sake fita zuwa office din nasu.


Darect d'akin bincike ya nufa yayin da ya Kira Kamal a waya yace ya tattaro masa jami'ain tsoro kwararru, Yanzu su samesa d'akin bincike, sai a lokacin yaga kiran abokin nasa SADIQ.

 

  " Wayyo Allah Sorry Sadiq wlh na Manta da cewa ka shigo garin nan, Amma insha Allah zuwa dare zan neme ka.

 Maida wayan sa Aljihu yayi sannan ya maida kallon sa ga jami'ain tsoron dake d'akin.


 Cike d'akin yake da computer kota ina, ba'a fi 15 minute ba sai gasu SADIQ sun karaso.


 " Idris Khabeer ya kira tare da d'auko agogon a aljihun sa, Location number na Agogon ya d'auko wanda dai dai da location number na Agogon Hanun junior.

 Yace

  

  " Idris kaine wanda kafi kowa kwarewa Akan harkar computer, ga wannan location numbern ka duba mana wacce unguwa take ko kuma wani gari yake, yanxu nan.


  Karb'a Idris yayi tare da zama ya fara aikin sa cikin kwarewa, yayin da su khabeer ke tsaye suna kallon yanda wannan location din ke wuce Anguwan nin dake cikin Gombe Local government, sanda yaxo Anguwar madaki sannan ya tsaya cak a wajen.


  D'ago idon sa Idris yayi ya kalli ogan nasu, yace

" Sir wannan location din ya tsaya a unguwar madaki, duk yanda Akayi Abun harin mu yana unguwar Idan dai ba kuma yasar da agogon akayi a unguwar ba.


  Murmushi Khabeer Yayi, yace bazasu yasar dashi Domin kuwa basu san Amfanin sa ba, zasu d'auka cewa normal Agogo ne marar daraja da tsada, saboda bai shigo kasar Nigeria ba, nima kaina a Kasar Cairo ya saya, yanxu Abunda za'ayi shine ka duba mana a wani layin yake mu zamu tafi unguwar inyaso zamu ke waya da kai.

  Kallon sa ya mayar kan su Kamal yace zamu tafi daku yanxu.


  

   Ya hada kansa da gwiwwa yayi shuru, domin kuwa gani yake yanxu kukan sa baida Amfani.


  Ajabo ne ya shigo d'akin rik'e da take away a hanun sa, ya ajiye masa yace d'auki kaci.


 Girgixa kansa junior yayi Alamun baxai ciba.


  Cikin muryar yan daba Ajabo yace kana son sanin waye Ne yasa ni na kawo ka nan, domin kuwa yaune last day d'in ka na kwana a gidan nan, gobe za'a shige dakai Kano, yaro daga nan sai mu fita da kai k'asar waje. 


  " A hankali junior yace waye yace ku d'auke ni

To kuna Duka na.


  " Kasan Saratu?


  " Girgixa kansa junior yayi yace a'a kasancewar baisan sunan Momy Sarah da Saratu ba.


  " To kasan Momy Sarah tunda kinfi gane ta da hakan.


  " Ehh na santa SARAH ce a gidan mu take.


  " To itace ta sani na d'auko ka, bari ma kaga na kira maka ita video call.

  Kira ya dannawa Momy Sarah ta video call, sai kuma akayi sa'a tana Online, 


 Ganin kiran Ajabo yasa Momy Sarah d'aga wa da sauri, bata yi tunanin komai ba.

   Fiskar junior ta fara cin karo dashi, harara ta zabga masa.


  Da sauri junior " yace Sarah ina momma da Daddy da Abbah na, da Papa khalid, kixo ki mayar dani gida Sarah dukana suke kullum basa....


 Tsawa Momy Sarah ta daka masa tace " shut up sun dake din Babu uban da zaizo ya mayar da kai gida, kaida gida kam har Abada, 


 Dauke wayan Ajabo yayi daga wajen junior, sannan yace


  " Hajiya Saratu nafa fara gajiya da ajiyar yaron nan, idan baxa ki d'auke sa ba, to zan mayar dashi inda na d'auke sa.


  " Ka cika gaggawa Ajabo, to ka kwantar da hankalin ka, mun gama magana da Sadam zaizo yau misalin, 11:00pm ya tafi dashi zuwa KANO.

Amma fah ka kula sosai domin kuwa Uban sa neman sa yake ido rufe.


 " Shikenan Hajiya Saratu karki damu Babu mai kama mu.



  Su Koh su khabeer suna tafiya Idris na kwatanta musu layin da zasu bi , a haka har suka shigo layin gidan Ajabo, sun d'an wuce gidan kad'an, Idris yace " su dawo baya, kadan.

 Dawowa sukayi, " yace ku tsaya a nan, yace akwai gida ta gefen daman ku.


  Kallon wajen Khabeer yayi yace " akwai.


  " Ku shiga gidan to, a gidan junior yake, ko kuma a samu agogon a ciki idan ma ba'a Sami junior ba.


  Fitowa sukayi Khabeer yace wa Kamal da kai da Saleem zamu shiga tare, ku kuma d'aya ya tsaya a nan sauran kuma duk ku zagaye gidan nan.


  A hankali suka shiga gidan shuru Babu kowa, har suka shigo mashigar falon Ajabo, an rufe da key ta ciki, dauko safiyon key sukayi wanda yake bud'e  ko wani irin kofa.

  Suka bud'e a hankali suka shiga, suna bin bango, 

   Daki uku suka gani a cikin falon, Kamal ya shiga d'aya Khabeer ma ya shiga d'aya, shima Saleem ya shiga d'aya, d'akin da Khabeer ya shiga a nan junior yake da Ajabo, 


Junior Zaune yake baiyi bacci ba Ajabo ya daure masa hannayen sa da kafofin sa, yayin da shi kuma Ajabo sai baccin sa yake tare da gwarti.


  Jin karar bude k'ofa yasa junior saurin d'ago kansa, yacce Abbah Sarah ce tace kaxo ka dauke ni koh.


  Shidai Khabeer bai tsaya sauraron junior ba, ya saita kan Ajabo da bindiga wata ya k'ara cirowa ya harbi bango, a zabure Ajabo ya farka, kokarin gudu yake.

Khabeer yace kana motsi zan dauke ka da wannan bindigar.


  Komawa yayi, yayi Zaman dirshan, yana faman had'a gumi, jin karar harbi yasa su Kamal karasowa da sauri, Saleem ne yayi kan junior ya since mass Hanun sa da kafofin sa, tusa keyar Ajabo sukayi zuwa waje yayin da Khabeer ya sab'i junior a kafad'ar sa.

  Rabuwa sukayi da su Kamal yace suyi station da Ajabo zai maida junior gida yana dawowa yanxu.


 Khabeer har yayi hanyar gidan su da junior sai Kuma ya fasa, yace gara kawai ya kaisa gidan su SADIQ zuwa ya gama binciken sa.


  A k'ofar gidan su SADIQ ya tsaya ya kira layin wayan SADIQ, Amma switch Off, bincika layin wayan Khady yayi, 1 Miss call ya mata ta d'aga, yace ki fito kofar gidan ku ina jiran ki.


  Kallon Naby tayi tace sis, Abokin ya SADIQ da muke tad'i d'axu shine yaxo yanxu, zo muje mu mana yana waje.


  " Sis Khady jeki kawai ni ina nan sai kin dawo, 


  Khady batace komai ba ta tashi ta d'auki gyalen ta ta fita.


  A k'ofar gidan ta samesa tace "  ya Khabeer wata sabon gani yau kaine a unguwar mu.


 " Wlh kuwa, SADIQ ya koma ne, na kira wayan sa switch Off.


  " Ehh d'axu ya tafi Amma ai ya kira ka daxu baka daga ba.


 " Ehh wlh ina busy ne, shiyasa, ga junior ki shiga dashi cikin gidan, zuwa gobe zanzo, kicewa Hajiya Amin Afuwa, zan shigo gobe.

Kallon junior yayi yace jeka Aunty sai gobe zanzo na kaika wajen momma koh, kaga karsu zo su k'ara dauke ka a gun momma, gara ka zauna a nan sai gobe ko.


Kad'a kansa junior yayi sannan ya taho wajen Khady


  " Shikenan to ya Khabeer sai kaxo Kan,          kama Hanun junior tayi suka shiga cikin gidan.


 Office din Khabeer ya koma ya samu su KAMAL suna cin uban Ajabo da Azaba.

  Amma tsabar taurin kai yak'i basu Amsa,


 Shaking Khabeer ya d'auko ya jona tare da fara yiwa Ajabo Azaba dashi, ganin Khabeer na neman ransa ne yasa shi cewa  " zan fad'i Gaskiya.


  Dakatawa Khabeer yayi daga masa shaking din yace ina jinka.


  "Hajiya Saratu ne  Kishiyar mahaifiyar  ka tace na dauke sa na Ajiye mata shi, a gida na,.

 Zuwa Ranar da zata samu damar tafiya dashi Zuwa jihar KANO.


 Dariya Khabeer yayi yace wannan k'aryar bata karb'u ba, ka Nemo wata kaga bana son rainin hankali, ka fad'a min gsky tun kafin na nakasa ka, ka kasa amfani.


 Rantsuwa Ajabo yake Akan cewa Momy Sarah ce tasa shi Amma Khabeer yaki yadda sai da yace a d'auko wayar sa a Duba akwai text's din da turo masa tare da kuma chart din da sukayi ta WhatsApp.


 Wayar Khabeer yasa aka d'auko masa Yayi bincike sosai, Cikin Rud'ani da Razana tare da Al'ajabi yasa Khabeer sake wayan ta bad'i kasa, saurin jingina da bango yayi yace *Momy Sarah*.






*Kuyi hkr da wannan naso ace ya na dubo yanda Nasreen take Amma Hakan bai samu ba kasancewar ina da Uxiri mu tara daku next page*





*Share*

   *And*

 *Comment*




*Alkalamin Rasheedat Usman✍🏻*




*(Ummu Nasmah)*

[12/14, 3:14 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


  *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

08147537180


*بسم الله الرحمن الرحيم*



 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



*Sadaukarwa*


*Sadaukarwan wannan littafin naku ne*


Zainab M Bello

Hauwa'u Sani

Sadiya Bello

Karima muh'd

Bilkisu Umar

Firdausi Usman

Maimuna Rayyan

Alawiyya Usman

Hafsat mus'af

Maryam m Usman.


*A Gaskiya bani da bakin da zan muku godiya, domin kuwa na tabbatar da ku masoyan SARA DA SASSAKA ne na hak'ik'a kwana biyu da banyi typing ba, kunji ni shuru, kuka Kira ni a waya domin jin ko lfy, to a Gaskiya naji dad'i hakan sosai domin kuwa masoyin kane zai damu da kai na gode sosai Allah yabar kauna*




P••••••3️⃣8️⃣ to 3️⃣9️⃣


Idon Khabeer ya kad'a yayi jajur, shidai ko a mafar ki bai tab'a zaton momy Sarah zata iya cutar dashi ba bare kuma gudan jinin sa, a fili yace " to wai ma me nayiwa Momy Sarah ne me zafi haka wanda har ya kaita da kidnapping d'in d'ana, 

Lallai mutum mungun Icce ne.


  Muryar Ajabo yaji yana cewa" Saboda kana bincike Akan Hajiya Hindatu.


  Khabeer baice komai ba saima takowa da yayi har gaban Ajabo ya dank'i wuyan sa, yace " k'arya kake dan Momy Sarah tasa An d'auki junior, bashi zaisa Ace tana da Hanu acikin k'ungiyar wand'annan Yan ta Addan ba, masu ta'ammali da miyagun kwayoyi, nasan waye *MOMY SARAH* nasan Abunda zata Aikata nasan wanda baxa ta Aikata ba, dan ka rufe min Bakin ka, karka K'ara dangan tamin Matar Uba da wannan mummunan sunan.

   Sannan ya sake sa tare da hankad'e sa ya bugu da bango.


  " Dariya sosai Ajabo yayi sannan yace " Ni nafi ka sanin waye Hajiya Saratu domin kuwa kai ka zauna da ita ne kawai gida d'aya, Amma baka San Ainihin true colors din Hajiya Saratu ba, ita wannan kungiyar da kake bincike a cikin ta, ina d'aya daga cikin members d'in ta domin kuwa kungiya ce da ta tara, mutane iri iri, k'abila daban daban, kiristan and Muslims, wannan kungiyar tamu bata tsaya a iya safarar miyagun kwayoyi ba, harda safarar y'an mata da kuma k'ananan Yara, 

 Muna kai y'an matan Kasar waje, Ana lalata dasu, suma K'ananan yaran waje muke fitar dasu, muna cire kidney nasu, muna sayarwa.

Wasu yaran su rayu wasu kuma su Rasa Rayuwar su sanadin hakan.

  Hajiya Saratu itace mataimakiyar shugaban mu wato oga John.

 Zan k'ara baka shaidata a karo na biyu hanun rigar sa ya zame sai ga zanen 🐜 ya fito b'aro b'aro a dantsen hanun sa, 

Yaci gaba da cewa, akwai Itama a nata Hanun, kaje ka duba, Idan har Babu ka dawo ka harbe ni, Raina ya Zama hukuncin k'aryar da na maka.


  Dafe kansa dake barazanar fashewa Yayi, zuciyar sa tafasa yake, duk da bawai ya yadda da maganar da Ajabo yake fad'a masa ba.

  Amma dai akwai k'amshin Gaskiya a tattare da wannan lamarin, zaije yayi Arresting din Momy Sarah, zaiyi bincike mai tsanani idan har Maganar Ajabo ya tabbata, baxai tab'a d'agawa momy Sarah k'afa ba, duk da uwa na d'auke ta, Amma Dole ta fiskanci Hukunci, Momy Sarah kin b'atawa gidan mu Suna, why !! why !! why !! why.

   Juyowa yayi yace " KAMAL kuxo muje, muyi Arresting d'in Momy Sarah.


  Zaro ido KAMAL Yayi cikin firgici yace " sir karkayi gaggawan yanke hukunci, ka bari a k'ara bincike tukkuna, kuma Sir koda Hakan ta kasance da gaske, ni a gani na, Sir, a rufe Case d'in nan kawai, idan yaso kai ka san yanda zaka yi Momy Sarah tabar wannan Harkar ina ga hakan zaifi amma ace..................


 Bai k'arasa maganar ba Khabeer ya daka masa tsawa, " yace shut up KAMAL, yaushe ka fara Ha'inci a aikin ka, to bari kaji na fad'a maka *wlh ko Momma ce na kamata da Hanu cikin case d'in nan sai ta fiskanci Hukunci daga Hanun Hukuma dan haka Babu ruwan ka da sami Baki cikin wannan Case d'in tunda na fiskanci Babu Gaskiya Cikin lamarin ka idan kaga dama ka tashi muje idan kuma baka ga dama ba, ka zauna*.


  Ficewa yayi, cikin sauri suka biyo bayan sa, yayin da Sargent Umar ya tsaya jiran Ajabo.



 Momma da Momy Sarah sai Daddy da Mami suna cin abincin dare, a daining, su Nana sun tafi makarantar dare.


  KAMAL ne yayi sallama cikin falon.

   Daddy ne ya Amsa, ya kalli KAMAL yace.

  " Kamalu lfy kuwa, naga ka shigo jikin ka a sanyaye, har yanxu ba'a samu mai suna na ba Koh?


 Daga bakin k'ofar falon suka ji muryar Khabeer na cewa " An samu junior Daddy, abunda ya kawo mu gidan nan yanxu kenan.


  Sake cup d'in glass d'in dake Hanun ta Momy Sarah tayi, cikin Razana tace *WHAT*.

  

   Cikin kallon Tuhuma Khabeer yace mata *Yes*.


 _________________________

   _______________________

________________________

 

   " Ki fad'a min, Uban wa ya baki damar shiga min cikin d'aki har da zaki d'ebi Ruwan dana b'oye, dan ubanki da uwar ki Maimuna, zaki fad'a min ne, ko sai na k'ara maka miki wannan sandar shegiya, matsanaciyar yarinya, yar tsiya.


  Cikin kuka Nasreen ke cewa " kiyi hkr MAMA wlh fitsari ne ya matseni kuma na Duba Randar waje Babu Ruwa shiyasa na shigo na d'ebi nakin kiyi hkr dan Allah baxan sake ba.


  " Fice ki bani waje shegiya mayya.


  Fita daga d'akin Nasreen tayi, a tsakar gida ta had'u da yar gwal, dake koyan tafiya, Amma har yanxu k'afar tana d'an mata Ruwa kad'an .

  Kallon banxa tayiwa Nasreen tare da tsirtar mata da miyau, Y'AR JARABA, wanda Y'AR UWAR KI da ita Uwar taki suka bi duniya.

 Haka dai za'a k'are cikin bak'in ciki da takaicin Rayuwa.


   Ci kanki Nasreen bata cewa, Yar gwal ba, saima ficewa daga gidan da tayi, ta nufi hanyar gidan Goggo, a k'ofar gidan su, Indo taci karo da ita, cikin dariya Indo tace.


  " K'awata kina nan kuwa kwana biyu kin b'ace b'at a cikin Rugar nan.


  Hararar ta Nasreen tayi, " tace ban Sani ba, ai kin bani mamaki wlh, Rabon ki d gidan mu tun sadakar bakwai d'in Nuruddeen, kin kyauta ai.


 " Ayye k'awata kiyi hkr dan Allah wlh bana son zuwa gidan kune, Mama take gaya min magana bana jin dad'in yanda take Aibata mahaifiyar ku, wlh Abunda yake hanani Zuwa gidan ku kenan.


  " Shikenan ai, yanxu muje ki raka ni gidan Goggo.


  " Muje to.


  Sun d'an yi nisa da tafiya ne, Indo tace, 

 " Yawwa K'awata nikam kwanakin baya akwai wani kwd'on daya zo gidan ku, mai wata k'atuwar mota, d'an gaye d'an Binni.


  Aikuwa Indo ta tab'owa Nasreen inda yake mata k'aik'ayi cikin Ranta take cewa Anya kuwa zai dawo, koma dai d'an yankan Kaine, Allah sarki AMMI na, Allah yasa, ba sayar dake yayi ba dan d'an Adam Abun tsoro ne.


  Tab'ata Indo tayi, tace

 " Tunanin me kike haka ina magana, kinyi shuru.


  " Babu komai Indo, yaxo, kwanan sa d'aya ya tafi.


 " Gaskiya Nasreen ina son wannan kwad'on naso kafin ya tafi yace yana sona, cap k'awata, dana ji dad'i wlh zan shiga binni.


  Murmushi kawai Nasreen tayi bata ce mata komai ba, har suka shiga gidan Goggo.


 Tana Zaune Akan taburman kaban ta, suka same ta, gefen ta Nasreen ta samu zata zauna kenan Goggo ta daka mata tsawa, tace

  " Karki Kuskura ki zauna min saman taburma ja'ira marar kunya.


 Gefe suka koma kad'an da ita, sannan Indo ta gaishe ta.

  Amsawa tayi cikin sakin fuska.


  " Ina wuni Goggo cewar Nasreen.


  " Banga wunin ba, nace banga wunin ba Yar marar sa mutunci, dan ubanki naji duk Abunda kike Aikatawa wato ke kinga Yaro d'an Binni koh, shine zaki dinga binsa cikin dare Yana Lalata dake, ke ga jarababbiya ko.

 

  Hawaye ne ya ziraro daga idon Nasreen, " yau Kuma sharrin da Mama tamin kenan, na shiga uku ni Nasreen.


  " Yanxu ma Kika fara shiga uku dan ubanki, naji Labarin wannan lalacaccen yaron jungud'o yana sonki, to zanje wajen ubansa, suxo su kawo kud'in Aure, Nan da sati biyu mu Aurar dake mu huta.


 "Jungudo Kuma mutumin da baida Tarbiya d'an kwaya, Haba Goggo. Cewar Indo.


Ita dai Nasreen tayi shuru Domin kuwa tasan tunda Goggo ta Kira Auren nan to sai Anyi, domin kuwa magana d'aya take.

  Kuma dole abi umarnin ta.

 A cikin ranta tace

  " Na shiga Uku banda gata a duniya Banda mai kauna ta.



Kuyi manage da wannan bana typing Ranar Asabar yanxu ma nayi ne saboda kiran da y'an uwa ke min.


*Share*

     *And*

  *Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻


  *(Ummu Nasmah)*

[12/15, 4:14 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

08147537180


*بسم الله الرحمن الرحيم*



 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


      *Sadaukarwa*

Sadaukarwan wannan page d'in naku ne domin kuwa kunfi, kowa yiwa book d'ina *SHARHI DUK WACCE BATA GA SUNAN TABA TO GASKIYA BATA SHARHI*


Ummy Ahmad

Senorita

Daga group din kundin Arewa Writers, ina jin dad'in sharhin ku.


SADIYA

Daga Aunty Fauza Hausa novels group.

  Ina jin dad'in sharhin ki sosai.


أحلام فاطمة 

Daga group d'in GUDU AJEJI kema bani da bakin da zan iya Miki godiya, domin kuwa kina kaunar book d'in SARA DA SASSAKA, Allah yabar kauna.


Gare ku *SARA DA SASSAKA* fans group,


Maman Usman

KHADIJA TAHIR momyn Ajmal.

Asma'u Aliero

Maman khairat

Fateema Abdullahi

Pretty

Maman Aiman

Asiya yabo

Lawiza Idris Yahya

Maman futu'atul khair

Rimat A


Wad'annan sunfi kowa yin Sharhi ga Book D'ina, Ina matuk'ar yi muku godiya bisa kaunar book d'ina da kuke, Allah ya barmin tare, Domin sharhin ku yana🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


Duk wacce bata ga sunan ta ba, sai ta dage da sharhi Akwai Page d'in gaba.


*I love you so much my Fans*



*P*••••••4️⃣0️⃣ to 4️⃣1️⃣


 Ga baki d'ayan su mai da kallon su sukayi wajen Momy Sarah, Daddy ne yace.


 " Lafiya Saratu Kika Razana haka sai kace wacce bata da Gaskiya.


 Murmushin takaici Khabeer Yayi yace

" Daddy .............


Bai k'arasa maganar ba, Zuhura ta shigo a kidime cikin tashin hankali, tana cewa.


  " Khabeer !! Khabeer Khabeer !! Khabeer.


 Cikin tsawa Khabeer yace, *ke* wani irin Rashin hankali ne wannan, waya baki ixinin fitowa daga gidan ki, kixo Nan.


  " Bana bukatar izinin Khabeer, domin kuwa da kai da y'an uwan ka, maha'inta ne, d'ana junior ya b'ata yau kwana 5 ku kasa gaya min sai yanxu aka kirani ake fad'a min, saboda ni bani da iko da d'ana.

  Cikin matsanacin Kuka ta Tsakomo wuyan rigar Khabeer tace, ka nemo min d'ana, duk inda yake

Ka Nemo min d'ana Khabeer, domin baxan iya Rayuwa babu shiba.


  Cikin b'acin rai da k'unar zuciya Khabeer ya hankad'a Zuhura gefe, ya fara magana cikin fasata.


  " Baxaki iya Rayuwa babu junior ba? Kad'a kansa yayi yace hmm

Yaron da baki damu da Rayuwar sa, ba yaron da Kika figesa daga jikin ki, tun kafin yakai yaye, ki wurga sa gidan ku, yake yawo tsakanin gida biyu, gidan su mahaifiyar sa dana mahaifin sa, shine kike Kira da baxaki iya Rayuwa babu shiba, hmm k'arya kike Babu soyayyar junior a zuciyar ki Zuhura.


  Itama cikin fushi tace,

 " Fad'a min Khabeer wacce uwa ce zata haifi d'a tace bata sonsa, kasan wannan zance ne, ina son d'ana fiye da yanda nake son kaina, dan haka Dole ku nemo min d'ana duk inda yake.


  A Yanxu Zuciyar Khabeer ta fara tafasa domin kuwa Idan ya k'ara five minute yana sauraron Zuhura zai iya sauk'e fushin sa akan ta.

 " Zuhura Fita kibar gidan Nan kafin na juyo da fushi na gareki, cikin tsawa yace *ki fice daga gidan nan nace Miki*.


  Juyawa tayi tace zan fita sai dai ina son ka sani cewa, muddun baka nemo min d'ana ba, na gama Rayuwar Aure a gidan ka.


  Daddy ne yace " Zuhura kinsan Abunda kike Aikatawa kuwa, harshen ki fah kike d'agawa Sama Dana MIJIN KI kina da Hankali kuwa, daman haka kike Ashe.


  Bata kalli Daddy ba, tace " Nama wuce haka Daddy.

  Sannan tasa kanta da niyan ficewa daga falon.


Ko kafin ta fice Khabeer ya kira sunan ta.

  "'Zuhura.


   Tsayawa tayi cak ba tare da ta Amsa ba ko kuma ta juyo.


  " Daga Nan wajen kiyi gidan ku, karki kuskura ki koma min gida, sai sanda na neme ki, idan kuma kika kuskura na dawo na same ki a gida na, wlh sai kinyi nadamar Aure na a rayuwar ki.


  Sai a lokacin Zuhura ta juyo tace

  " So what dan nabar gidan ka, wacce tsiyar nake d'auka a cikin gidan naka, mtss taja tsaki tare da ficewa.


   Momma ce tace.

 " Kaga Abunda nake fad'a maka koh, nak'i Auren ka da yarinyar nan, Amma kace sai kayi, to ga irin Abunda nake guje maka, nasan zuri'ar su bata da kyau, Amma kace kaji ka gani.


  Dakatar da ita Daddy yayi yace.

 " Ya isa haka ya kamata ki daina tuno Abunda ya wuce.

    Kai kuma kabiru meya kawo ku, dukan ku cikin gidan nan.


  Daga idon sa yayi ya kalli Momy Sarah dake tsaye tsamo a gefe cikin tsoro ta sunkuyar da kanta k'asa.

  Cikin bacin rai da takaici yace.

 

  " Daddy munxo tafiya da Momy Sarah ne saboda muna zargin dasa Hanun ta a b'atan junior.


 Cikin pretending Momy Sarah tace what Khabeer kasan me kake cewa kuwa, ni kake Zargi da b'atan d'anka, Nice zan sace junior, menene Ribata idan na sace junior.


  Takowa Khabeer yayi har gaban Momy Sarah yace.

 " Ba zargin ki nake ba, na tabbatar da hakan, Hanun sa yasa da k'arfi ya yaga Hanun rigar Momy Sarah na dama.

 

  Sauk'ar maruka Khabeer yaji a fiskar sa.

  D'ago idon sa yayi ya Kalli Momma, data maresa, sannan ya maida kallon sa zuwa dantsen Hanun Momy Sarah, zaro idon sa yayi, cikin matsanacin firgici, domin kuwa zanen tambarin K'ungiyar da yake bincike akai ya fito b'aro b'aro a hanun *MOMY SARAH* ja da baya yayi cikin tsoro da Al'ajabi yace momma kina ganin Abunda nake Gani kuwa, ki taya ni dubawa meye a Hanun Momy Sarah zanen k'ungiyar wand'annan Yan ta'addan ne fah, *innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un la'ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minazzalimin allahumma ajirni fil musibati*.

Mai da kallon sa Zuwa ga Daddy yayi yace, *Daddy Momy Sarah yar ta'adda ce mai safarar miyagun kwayoyi tare da k'ananan Yara tana fitar dasu k'asar waje, ana cire kidney nasu suna sayarwa, daddy Momy Sarah bata tsaya iya Nan ba, har y'an mata take fitarwa waje ana Lalata da su Daddy...................*


 Shak'o wuyan sa momma tayi cikin fad'a take cewa

  *" Ka haukace ne Khabeer, nace ka haukace ne, Hajiya Saratu kake dangan tawa da wannan mummunan Aikin, tabbas Babu hankali yau a jikin ka, Khabeer.*

 

  

    Daddy ne ya k'waci Khabeer dak'yar a Hanun momma, cikin taushin murya da Sanyin jiki yace, Ba'a Haka Hajiya Zainab, kamata yayi mini komai a hankali cikin Salama bada tashin hankali ba, ta hakan ne kawai zamu gano Gaskiyan Abunda ke faruwa.

   Kowa ya samu waje ya zauna.


  Zaman kuwa kowa yayi Amma Banda Momy Sarah dake tsaye cikin tashin hankali da kunyar Abunda ta Aikata, sai yanxu tayi nadamar sace junior, gashi yanxu wankin Hula ya kaita dare.


  " Ki zauna mana Hajiya Saratu cewar Daddy.


  Cikin kunya ta zauna, sannan ne Daddy yace, SARATU Abunda kabiru yake fad'i a kanki Gaskiya ne?


  Shuru Momy Sarah tayi tak'i magana.


  " Kiyi magana SARATU kinyi shuru kodai Gaskiya ne Abunda kabiru yake fad'a.


  D'ago kanta Momy Sarah tayi tace

":A'a bansan Abunda Khabeer yake magana akai ba, sai dai ni Khabeer ya bani mamaki, wai ni kake Zargi da sace junior, harma da sharrin Safarar miyagun kwayoyi, mena tare maka a rayuwa haka Khabeer, kodai saboda Bani na haife kaba, ban taba rik'e ka da wata manufa, na dauke ka tamkar d'an da na haifa a ciki na,  Ashe kai a wajen ka Abu ba haka yake ba.

  Tana maganar ne cikin kukan munafurci.


  " Khabeer kaji Abunda Uwar ka Saratu ta fad'a.


  " A'a ni ba UWATA bace domin kuwa mahaifiya ta bazata Aikata wannan mummunan Aikin ba, dan Allah Daddy karka K'ara dangan tani da SARATU a matsayin uwa ta.



 😳😳😳😳😳😳 Gabaki dayan su zaro ido sukayi jin yanda Khabeer ya Kira SUNAN MOMY SARAH darect ba tare da saya mata ba.


   Momma ce zatayi magana Daddy ya d'aga mata Hanu Alamun tayi shuru.

 shurun tayi ba tare da tayi magana ba, Amma dai Khabeer yana shan mugun Kallo a wajen ta.


  Magana Daddy yaci gaba dayi yace menene shaidar ka, da kake DASHi na zargin Hajiya Saratu.


  Wayar Ajabo ya mik'awa Daddy tare da mik'o masa photon Hajiya Hindatu wacce take d'auke da wannan zanen itama a Hanun ta.

 Karb'a Daddy yayi, ya Duba da kyau.


  " Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un la'ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minazzalimin allahumma ajirni fil musibati

 Cire hular kansa Daddy yayi tare da goge zufan daya tsatsaffo masa, cikin firgici ya Kalli Momy Sarah, yace SARATU wannan Hindatu ce, Aminiyar ki gata kuma d'auke da wannan zanen 🐜 wannan wayar Kuma ga numbern ki da duk wani shaidar cewar kece Kika d'auke junior, TIR da Halin ki Saratu bansan Haka kike ba, kin b'oye min munanan Halin ki, ki bayyana min kyawawa naki, yaushe Kika fara wannan muguwar sana'ar? mena rage ki dashi? Ci ko Sha ko kuma sutura, ko bana iya biya Miki buk'atun kine?.


  Shuru Momy Sarah tayi tare da tashi cikin sauri ta warce bindigar Hanun KAMAL ta d'aura Akan momma, tace, Baku da lokacin mini wannan tambayan, ku bani hanya na wuce ko kuma na harbe wannan UWAR TAKA.


  Zaro Ido Mamy tayi dake zaune tun d'azu tana kallon su ta kasa magana.


  Shima Daddy Kallon Khabeer Yayi, yaga wani irin Action zai d'auka.


  Takowa Khabeer yake yana nufar Momy Sarah cikin rashin tsoro yayin da ita kuma take gargad'in sa da cewa ya dakata ko ta harbe momma, k'in dakatawa Khabeer yayi yaci gaba da nufo ta, sauk'ar Harbin bindiga momma taji a k'ofar ta wanda yasa ta danna k'ara.


  Runtse idon sa Khabeer Yayi cikin tsanar Momy Sarah da jin haushin ta, ya saita Hanun ta dake rik'e da bindigar da tasa bindigar ya d'auke Hanun, itama Momy Sarah k'ara tasa, tare da sake bindigar a k'asa, cikin zafin nama Kamal ya k'arasa ya d'auke bindigar ya d'aura ta akan Momy Sarah.


  Karasowa Khabeer Yayi gaban momma dake rik'e da kafarta cikin Azaba ta rintse idon ta, Khabeer ya kama Hanun ta, ya d'aura mata bindinga yace

" Rama Harbin ki momma, ki harbe ta, a inda ta harbe ki.


  Girgixa kanta momma tayi Alamun bazata iya ba.

  Kama Hanun nata Khabeer Yayi ya saita k'afar Momy Sarah, itama ya harbe ta.

Wani irin k'ara Momy Sarah tasa tare da zubewa a k'asa.


 Daddy ko juyawa Yayi ya koma d'akin sa cikin takaicin Momy Sarah da DANASANIN AUREN ta.


  Kallon Kamal Khabeer yayi yace ku d'auke ta ku kaita cell, ni zanje nakai momma Hospital.


 KAMAL ne yace Sir bullet d'in dake Hanun ta da k'afar ta fah, Abdullahi zai iya cire Mata.


  " Ban bada wannan izinin ba, abarta dashi ya kwana tukunna a jikin ta, idan yayi tsami sai a cire mata gobe.


  " Kallon Khabeer tayi cikin huci tace sai kayi DANASANI Arayuwar ka na kamani da kayi.



*************************


Itako Zuhura darect gidan su ta wuce da kuka ta k'arasa Cikin Falon nasu, Umma dake zaune ne ta mik'e tace.

  " Lfy Zuhura kika shiga min gida cikin kuka

Waye ya  mutu.





*Share*

     *And*

*Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻


        *(Ummu Nasmah)*

[12/18, 1:57 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*




🤳🏻

*08147537180*




*بسم الله الرحمن الرحيم*


 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



   *Sadaukarwa*


  Gare ku sister's.


Maman Abdul

Group din kainuwa fan 11.


Momyn Asas

Rimat A

Maman Asfar

Ummu Nasmah group.


Shalam

Meenat


Group d'in Nasmah ko Nasirah.


Ramlat Abdulkarim

Maman Usman

KHADIJA TAHIR

Lawiza Idris

Sadiya

Zee byby

Asma'u Aliero

Maman Aiman

Meener

S

Aunty 3949


*SARA DA SASSAKA fans group*


Wad'annan kune kad'ai Naga sharhin ku.

Wannan shafin naku ne kuyi yadda kuke so dashi, mallakin kune.


Domin sharhin ku Yana.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥



*Kuci gaba da suburbud'o Ruwan sharhi ni kuma zanci gaba da suburbud'o muku Ruwan Typing*


*Love you so much fans*




P•••••••4️⃣ 2️⃣ to 4️⃣3️⃣


" Ba mutuwa akayi ba Umma, Amma Kuma da wannan Abunda ya faru gara ace mutuwar ce.


  " To fah yau kuma wani irin masifa zanji wacce tafi mutuwa, to Allah dai yasa ba Khabeer d'in bane ya gane kina masa d'auki d'ai d'ai ya sasako ki gida.


  " Ko d'aya Umma junior ne ya b'ata, an nemasa sama da k'asa Babu shi, kuma Abun takaicin ma Umma, Babu Wanda ya sanar dani, b'atan junior, sai d'azu k'awata farida ta kira ni, take sanar dani, wai itama a cikin gari taji tace bari ta kira tamin jaje kafin taxo.

    Umma shine fah na d'auki gyale na, naje gidan su naji shin da gaske ne, Amma Umma tsabar wulakanci da cin mutunci, iya'yen Khabeer suka zage ni, tas har Daddy yana gaya min bak'ar magana, dan na mayar masa da Amsa, shine Khabeer yace karna kuskura na koma masa gida, na dawo gidan mu sai Randa ya neme ni.


  Tsuka mai k'arfi Umma taja cikin jin Haushin Zuhura tace.


  " Mtsss Amma dai Zuhura ke shashasha ce, marar tunani, yanxu ke dan Khabeer yace karki koma masa gidan sa, shine Kika biye sa kika dawo gida, to na tambaye ki Mana.


     "  Ina jinki cewar Zuhura.


  " Gaya min Me Zaki d'auka a gidan uban naki, me Uban naki yaci, me naci, me Leemat taci, me sagir yaci, me Kuma zaki ci, ni kaina Zaman hak'uri nake a cikin gidan Uban ku, bare kuma ke da kika Saba da jar Miya kici kaza Kici kwai, harma ki d'aura shayi mai kauri akai, nan kuma gidan uban naku, daga shinkafa garau garau, sai kuma tuwo, Randa akayi dace ne, za'a daura shinkafar da Miya, Amma    kuma  Kinga Abincin da kike aiko min da d'an kud'in nan, ba k'aramin   taimaka min  suke  ba.

Shine kike son kimin bak'in ciki, saboda d'an da baya k'aunar ki, yafi k'aunar uwar ubansa fiye dake da kikayi nak'udar sa, to Wlh k'arya kike tashi zakiyi yanxu nan ki Koma gidan ki.


  Zaro ido waje Zuhura tayi tace.

  " Na koma gidan sa fah kikace Umma, korata fah Yayi, yace Idan na yadda na dawo sai nayi mamakin sa, shine zaki ce na Koma Umma.


  " Kwarai kuwa komawa zakiyi ko kashe ki zaiyi sai kin Koma Wlh.

Hkr zaki sawa zuciyar ki, dan junior ya b'ata sai meye, cewa Akayi baxaki k'ara haihuwa ba bare hankalin ki ya tashi, idan kin so nan da jibi Yayi yawa kin samu wani cikin, yanxu ki tashi kije hospital a cire Miki wannan robar da kika sa, na Planning d'in, shi kuma junior Allah ya fito dashi, Idan ma ya hallaka, Allah zai baki wani, tashi maxa ki tafi.


  Baban Zuhura dake shigo ne ya tsinci zancen da Umma ke yiwa Zuhura yace.


  " Amma dai ke kam Jummai sam halin ki bayi da kyau wlh, yanxu yar taki kika zaunar kike yiwa wannan hud'ubar ta tsiya, tsawa ya dakawa Zuhura yace, ke kuma munafuka, daman tsiyar da kike shukawa kenan a gidan Auren naki kullum ina Miki kallon mutumiyar kirki ashe mutumiyar banxa ce, nemi guri ki zauna, ina magana kina kallo na.


  Waje Zuhura ta samu ta zauna tana tura baki.


  Umma da ta cika ta batse, saura k'iris ta fashe ne tace wa Baba.


  " Ta zauna a ina Alhaji, a wannan bak'in gidan naka, to baxata zauna ba, gidan mijin ta zata koma, inda take samun walwala har muma muke rab'ar danshin ta, cikin tsawa Umma tace wa Zuhura, *ke tashi ki koma gidan ki, nama fasa ki koma ke d'aya muje na rakaki har sai naga kin shiga gidan ki na juyo, Babu wanda ya isa ya jamin Asara*.


  Tashi Zuhura tayi, Mahaifin nata ya k'ara daka mata tsawa yace.


  " Ki zauna nace koh baki ji bane, Ita Uwar taki kaunar ki take yi, da miji zai koroki, tace ki koma ba tare da ta kirashi ta zaunar daku ba, taji ba'asin abunda ya had'a ku, kafin ta mayar dake, Amma tsabar son Abun duniya shine zata Saki sai kin koma dole, to baxaki koma ba sai na kira khabirun naji mai ya had'a ku.


  Magana Umma zatayi Baba ya tare ta hanyar cewa.

  " Karki kuskura naji muryar ki, idan kuma kikayi magana, to wlh kema zaki bar gidan Nan, kuma kin barshi kenan har Abada, Tunda ke wawuya ce marar hankali kin girma harda jikoki Amma har Yanzu kin kasa yin hankali, ke kam baxaki tab'a hankali ba, tunda har Yanxu baki dashi.


   Juyawa Umma tayi cikin fushi tabar falon zuwa d'akin ta.


 Shi Kuma Baba kiran layin wayan, Khabeer yayi.


  Khabeer dake tsaye harabar Asibiti ne yana jiran likitoci su fito da Momma daga cire Mata bullet. Yaji kiran waya, d'ago wayar yayi, yaga Baba rubuce Akan screen d'in wayar, cikin girmamawa Khabeer ya daga wayan tare da gaishe da Baban.

Daga can Baban Zuhura yace.


  " Khabiru idan ka gama Aikin da kake ina son kaxo gida ka same ni, zuwa dare.


  Da to Khabeer ya amsa tare da cewa " insha Allah, Zanxo Baba, Amma Inaga zankai zuwa k'arfe tara.


  " Babu damuwa khabiru Allah ya kaimu lokacin.


Sallama sukayi sannan kowa ya kashe wayan sa, juyawa Baba yayi yace wa Zuhura.

  " Ki kuskura ki fita daga gidan nan kiga Abunda zan miki dake da Uwar taki marar Hankali.


  Tura bakin ta Zuhura tayi tare da cewa, 

  " Ni Babu inda zanje Ni 


  Wajen awan Momma d'aya da shigar da Momma Emergency, aka fito da ita a keke ana turata, sanadin bullet d'in daya shiga k'afar ta, yasa baxata iya takawa ba.

   D'akin hutu suka shigar da ita yayin da Khabeer yabi bayan su, shida Daddy.


  Kallon su Momma tayi cikin dashewar murya, idon ta na zubar da hawaye, tace.


  " Alhaji kayiwa d'anka nasiha ya rage zafin Zuciya, meyasa zai harbi Hajiya Saratu, gani Nayi komi tsiyar Saratu, tana mazaunin Uwa ce a garesa, tunda komin yaya dai, matar Ubanka ne, kuma tana da yara tare dashi, jinin ku d'aya da y'ay'an ta, baka kyauta ba, kamata Yayi kabi komai a hankali, shawara d'aya zan baka, shine karka kuskura ka yanke hukunci Akan Saratu ba tare da kayi bincike ka tabbatar da Gaskiya ba.


   Magana Khabeer zaiyi Daddy ya d'aga masa Hanu, yace karka ce komai Khabeer, ita mahaifiyar ka, bata fahimce ka bane, Amma ni na fahimce ka ba kuma zan hanaka yin aikin ka ba Akan Saratu, nasan baxaka tab'a yiwa Saratu sharri ba, domin kuwa baku taso da nuna y'an Ubanci ba tsakanin ku, koda nine dana haife ka, na Aikata wannan banfi k'arfin ka hukunta Ni, ba a matsayin ka na Hukuma, kaje kayi Aikin ka, Ubangi Allah ya baka sa'a, ita kuma Saratu ina mata fatan Samun shiriya a rayuwar ta.


  Murmushi Khabeer Yayi cikin jin dad'in yanda mahaifin sa ya fahimce sa, yace.

  " Na gode sosai Baba da fahimta ta da kayi tabbas ke ubane da ko wani d'a zaiyi alfahari da samun ka a matsayin Uba, na gode sosai Daddy daka fahimce ni Allah yasa itama momma ta fahimce ni kamar yanda ka fahimce ni.


   Yanxu Daddy Bari naje na kira Nana sai ta zauna a wajen momma, kafin na dawo Zuwa Dare, gashi Anbar Mamy cikin tashin hankali.


  " shikenan sai ka dawo, Nanan ta taho Yanxu.


  Ko kafin Khabeer ya Amsa sukaji an turo k'ofar d'akin da k'arfi, da sauri Khabeer ya juya yaga wani marar Hankali ne, ya shigo musu haka.

Khalid ne, cikin zafin nama ya cakomo wuyan Khabeer, yace.


  " Wani irin laifi mahaifiya ta ta maka da zaka mata wannan mungun cin mutuncin, Ashe daman Khabeer zaka iya wulakanta mahaifiya ta, wlh yau koni ko kai a cikin Asibitin Nan, Dole a d'auki gawar d'aya.


 Wuk'a khalid ya ciro cikin Aljihun sa, ya daga ta sama yayin da Hanun sa d'aya ke danke da wuyan Khabeer.


  Zaro ido momma tayi tare da yunkurin tasowa, Daddy ya kamata ya mayar da ita ya kwantar.


Sannan Yayi wajen su khabeer, Hanun sa Daddy ya mik'a yace wa khalid.


  " Bani wuk'ar nan.


 " K'in mik'a masa wuk'ar yayi, cikin zafin nawa ya daga Hanun sa zai sokawa Khabeer a Cikin sa..............



  *************************


Sammako goggo tayi sassafe zuwa gidan mai gari, d'akin Uwar gidan sa, talatuwa mahaifiyar jungudo ta nufa, cikin sakewar fuska, Talatuwa wacce suke kira da Inna, ta gashe da Goggo tare da mata kiran mai gari.

Bayan mai gari ya shigo ne yace,


  " Yau kuma Goggo dija ce a cikin gidan nan, lale maraba da dake.


  Washe hak'ori Goggo tayi, tace

  " ran mai gari ya dad'e, nice nazo tafe da k'ok'on bara ta, a hanu, Allah yasa zan samu Abunda ya kawo ni.


  Cikin mutuntawa mai gari yace, 

  " Goggo me zaki nema a waje na ki rasa, ki fad'i damuwar ki, ni Kuma insha Allah indai baifi k'arfi naba zan Miki shi.


  Dad'a washe hak'ori Goggo tayi tace

  " To alhamdulillah, daman ba wani abu bane naxo ne, neman iri, ina sone, mu had'a zuri'a tsakanin mu, ma'ana ina son mu had'a jungud'o  da Nasranatu Y'ar wajen d'ana Musa Aure.


  Dariya mai gari yayi sannan yace goggo ai wannan Abun farin ciki ne, kuma Nasranatu yarinyar kirki ce, kowa na yabon kyawun halinta a cikin k'auyen Nan, nayi farin ciki sosai Amma bari nasa a kira shi jungud'o muji ta Bakin sa, kinsan yaran yanxu ba'a tilasta su akan Abu.

 


  Matarsa talatuwa ya kira yasa ta Kira masa jungud'o, tare suka dawo dashi ya zauna ya gaishe da, goggo, sannan Mai gari yake mayar masa da bayanin da goggo taxo masa.


  Wayyo hoho, kuxo kuji dad'i a wajen jungud'o, cikin zumud'i da murna yace, ai Baffah daman na dad'e ina son Nasreen, dan haka, ina maraba da wannan Auren.


  A tare goggo da Mai gari suka furta alhamdulillah, cewa goggo mai gari yayi, anjuma zasu je wajen mlm Musa asa shartin Auren.


  Godiya goggo tayiwa mai gari sannan ta fice daga gidan mai garin, gidan su Nasreen ta wuce darect.


 A tsakar gida ta samu Nasreen nayiwa Mama wanke wanke, yayin da ita Kuma da yar gwal suke Zaune suna cin wake da k'uli.


  Yunwa ce a cikin Nasreen dan rabon ta da tasa wani abu a cikin ta, tun jiya da Rana sai uban ruwan da take Sha, Amma k'ememe Mama ta hana ta abinci, yanxu haka Ranta na k'aunar wake da k'uli nan, Mama ta haranta Mata shi.


  Sallamar Goggo sukaji yayin da Mama cikin kirsa ta amsa tare da kawowa goggo kujera yar tsugunno, Zama Goggo tayi tare da tambayan Mama mlm Musa.


  Yana ciki cewar Mama, tare da kawo mata wake da k'ulin da Kuma Ruwa.


  "A'a Salame na gode abincin nan ya ishe Ni, kidai Kira min Musan kuxo dukan ku muyi magana.


  D'akin mlm Musa Mama ta shiga ta kira sa, tare suka fito, rik'e da taburma a hanun Mama ta shimfid'a, kallon Nasreen goggo tayi tace


 " Kema Nasranatu kixo Nan, harda ke cikin maganar.


  Tasowa Nasreen tayi tare da Samun waje gefe kad'an dasu ta zauna, goggo ta fara koro musu bayanin yanda sukayi da mai gari.


   Wayyo Allah dad'i cewar Mama a cikin Ranta, Alhamdulillah ko banxa naga k'arshen Zuri'ar Maimuna indai har Auren jungud'o da Nasreen ya tabbata.


  Ita ko Nasreen zuciyar ta ne ya tsinke cikin takaici da Bak'in ciki, sunkuyar da kanta tayi tana jiran taji mai Baba zaice Amma Abun takaici da Bak'in ciki sai taji Baba yana cewa Allah ya kawo su lfy.


  Alhamdulillah Mama ta k'ara cewa cikin Ranta, dan batayi tunanin Baba zai yadda da Auren da wuri haka ba, lallai Boka RABGAS aikin ka yana kyau.

  A fili tace Amma Gaskiya naji dad'i sosai, Allah ya sanya Alkairi.


  Ameen goggo tace, tace gashi kuma Yaro gidan su gidan mutunci gidan manyan mutane, kedai Nasranatu kinyi dacen dangin miji.

  To Musa ni na wuce Idan sunxo duk yanda kuka ajiye shartin Auren kaxo ka sanar dani.


  Da to ya amsa mata sannan ya tashi ya mata rakiya har waje, daga nan shima Baba wajen mlm sale yaje da mlm Iro ya sanar dasu suxo su karb'i Neman Auren NASREEN.



  Misalin k'arfe Hudu na yamma kuwa sai gasu mai gari da jama'ar sa sunxo neman Auren Nasreen, yayin shi mlm Iro sam ransa baiso a bayar da Auren Nasreen ga jungud'o ba, sai dai Babu yanda ya iya tunda har sun basu lokacin zuwa neman Aure.


 Cikin mutunci da karanci suka tarbi juna, yayin da Mlm Musa ya yadda da ya bawa jungud'o Auren Nasreen, sunsa shartin Aure sati d'aya Tak 1 week.

  Alhaji Salisu shine ya bada sadakin Nasreen inda mlm sule shi ya Amsa naira dubu Goma cip, cikin mutunci suka watse, yayin da shima mlm Musa ya shiga cikin gidan sa.


  Ya sanar wa MAMA cewa ansa shartin Auren Nasreen sati d'aya,


  Guda Mama tasa ka tare da cewa, alhamdulillah mlm kace mu fara shiri Nima bana zan Aurar da y'ata Nasreen, sai Kuma tasa kukan munafurci, Allah sarki Maimuna, Allah ya k'addara bazaki ga Auren y'arki ba.


  " Babu komai haka Allah ya k'addara cewar Mlm Musa.



 Nasreen dake tsaye tana jin duk abunda suke fad'a ne, ta ruga d'akin su da gudu, gefen katifar AMMIn ta ta kwanta tare da sakin wani Kuka mai tsuma ZUCIYA........


"Dan shaye shaye shine zan Aura wanda bai ganin darajar mutane.




*More comment more typing*



*Share*

    *And*

*Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻



     *(Ummu Nasmah)*

[12/19, 8:18 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*




*بسم الله الرحمن الرحيم*


 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



*Sadaukarwa*


Gare ki my lovely friend

*HAUWA'U MUHAMMAD TUKUR*

  *Momyn D'ayyib*


Wannan page din

 sadaukarwa ne gare ki Allah ya Raya miki Zuri'ar ki Rayuwa mai Albarka🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻




 *P*•••••••4️⃣4️⃣ to 4️⃣5️⃣


Kuka Nasreen take sosai Babu mai bata hkr, haka taci kukan ta, tayi shuru dan kanta, Hanun ta ta d'aga sama ta fara jero Addu'a.


  " Ya Allah Gani gare ka bani da gatan daya wuce Naka, ya Allah kamin zab'in abunda yafi Alkairi a gare Ni, Idan Auren Jungud'o shine Alkairi na, ya Allah ka shirya shi, ya daina wad'annan munanan halayan nasa, idan kuma bamai shiryuwa bane ya Allah ka kawo min agaji, shima wannan kwad'on daya min Alk'awarin dawo min da AMMI na, ya gudu ya manta Dani, Allah kasa AMMI da Nabiya suna Halin lfy a Hanu na gari, ya Allah ka inganta Rayuwar Nabiya da ni'imar ka, Allah ka raba ta da k'ara Shan wahala a cikin Rayuwarta.

  

Tana gama Addu'ar ta share hawayen ta, ta mik'e ta fito waje, kayan wankin Mama dana yar gwal ta had'a ta hau wankewa, tana wankin ne Mama tayo kanta da zagi cikin isgilanci take cewa.


  " Ke matar d'an shaye shaye Matar dan giya da wiwwi, dan Ubanki da d'an sauran ruwan nawa zakiyi wanki ni ki barni haka, to maxa d'auki tulu ki tafi Rafi, ki d'ebo ko sau biyar ne, in yaso kixo kiyi wankin, kinji Amaryar d'an giya.


   Duk da Nasreen taji zafin maganganun Mama, Amma hakan baisa ta nuna mata jin zafin a zuciyar ta ba, sai ma tashin da tayi, ta d'auki tulun, da gangan Mama tasa Mata,wanda ita Nasreen bata lura ba, sai kawai jinta tayi, ta fadi kasa warwas, cije leben ta tayi cikin Azaba tare da rik'e kunkumin ta daya bugu.


  Dariya Mama da yar gwal suka shek'e mata dashi, yar gwal ne tace

 " Madalla Allah shi K'ara,

A haka dai za'a k'are daga wahalar gidan uba sai ta gidan miji, rana ita yau dai iyanxu kina can kin fara shan bugu Hanun d'an giya.


  Ficewa daga gidan Nasreen tayi ba tare da ta d'aga ko Ido ta Kalle suba.


 

  Zaune Baba yake a gaban Goggo yana cewa.


    " Goggo na fidda Nagge na guda d'aya na bawa Mlm Iro yaje ya sayar min ita, in yaso na kawo kud'in ayiwa Nasreen kayan d'aki dasu, tunda ansa Auren yayi wuri naso ace ansa Auren ya kai ko zuwa tsakiyar watan gaba, to sai shi mai gari ya nuna min cewa kece kike so asa Auren da wuri.


  Numfasawa Goggo tayi tace.

 " Ehh nice nake so a saka Auren da wuri, sai dai kuma baxaka sayar da shanun ka, ko d'aya ba, tunda Allah yasa akwai kayan d'akin Uwar ta da ta shiga duniya tabar su, a d'ebe su akai ta dasu, Maganar Abinci kuma wanda za'a ci Ranar wuni, ka aiko axo a bud'e Rumbun nan a D'iba.


   " Haba Goggo kayan d'akin Maimuna za'a D'iba akai y'arta dasu gidan miji, Gaskiya Goggo bana tunanin wannan tsarin Yayi, nikam ki barni naje na saidar da Kaya na, nayiwa yata kayan d'aki, har gobe bana fitar da rai cewar Maimuna zata dawo, Idan ta dawo Babu kayan d'akin ta fah me zance mata Goggo?


  Cikin b'acin Rai Goggo tace.

  " Kace mata ankai Y'ar ta dasu gidan miji dasu, bare ma ba dawowa zata yi ba,  tana can yawon tsiyar ta, ne zata dawo.


 Tashi Baba yayi cikin b'acin rai, baxai iya tsayuwa yaji ana fad'in munanan kalamai akan Maimuna ba, 


  " Na barki lfy Goggo cewar Baba.


  Tabe bakin ta goggo tayi tace, Oh saboda na fad'i Gaskiya akan Maimuna shine zaka tafi, to kaje ka, sai dai ka sani Idan har ka d'auki saniya ko guda d'aya ne ka siyar da sunan zaka yiwa Nasranatu kayan d'aki, to wlh ban yafe maka ba.


  Baice mata komai ba Baba yasa kansa ya fice cikin takaici da b'acin rai.


  Ita ko Nasreen bayan ta fita ne suka had'u da INDO a hanya, koma wa gidan su Indo tayi itama ta d'auki tulu suka tafi Rafi tare ita Indo a niyar ta Nasreen zata taya d'iban Ruwan.

   Sau biyyu biyyu sukayi, wankin ma Indo ta taya Nasreen har suka gama tare, suna yi Mama na zagin su, babu wanda ya kulata cikin su.


  Indo ce takai duban ta ga Nasreen tace.

   " Ban gane ba naji kamar MAMA na Kiran ki da matar d'an giya, waye kuma d'an giya.?


  Murmushi mai cin rai Nasreen tayi sannan ta fara bawa Indo labarin Abunda ke faruwa game da Auren ta da jungud'o.


  Salati mai k'arfi Indo tasa cikin zubar da hawaye tace.

 " Yanxu ke Nasreen kika yadda za'a cuci Rayuwar ki, jungud'o, tantirin d'an Iska, kwanakin can fa, yayiwa wata yarinya yar RUGAR BUBU fyad'e aka b'oye maganar saboda yana da gata, shine ke saboda baki da gata za'a cuce ki.


  " Ya na iya Indo, Baba shi kad'ai ne wanda ya kamata Ace ya dakatar da Auren nan, Amma shima ya goyi baya, to ya ZANYI INDO na mik'awa Ubangiji lamari na shi yasan yanda zaiyi Dani.


  " Tabbas kuwa ubangiji maji rokon bawan sane, na tabbata yanda Kika sha wahala baxai bar Rayuwar ki ta wulak'anta ba, Ina da yak'inin cewar *AKWAI HASKE ACIKIN RAYUWAR KI* insha Allah Al'ummar RUGAR NAN Sai sunyi Alfahari dake.


  " Allah ya Amshi Addu'ar ki INDO shiyasa a kullum nake Alfahari da Samun ki a matsayin Aminiya, na gode sosai.


  Wankin suka ci gaba dayi, sai waje magrib suka gama, sannan Nasreen ta rako INDO har k'ofar gidan su, ta koma.



*************************


Ko kafin khalid yakai wuk'ar jikin Khabeer, tuni Khabeer yasa k'afa ya jidesa, taka !! taka khalid yayi zaije k'asa, ko kafin ya k'arasa Khabeer yasa Hanun sa d'aya ya rik'o Khalid tare da murd'e Hanun sa mai rik'e da wuk'ar , karb'e wuk'ar Daddy yayi sai lokacin Khabeer ya sake khalid tare da d'auke sa da tagwayen maruka har guda Uku, magana ya fara cikin Izza wanda shi kansa Daddy baisan Khabeer dashi ba,


  " Hmm yanxu khalid kaine kake tunanin zaka iya gwabzawa dani, ko irin ka Hud'u aka Had'a zan iya dasu, bare kuma kai da shaye shaye ya gama da Kai, kasani cewa, Ban tab'a d'aukar Momy Sarah A matsayin kishiyar uwa ba, Ko yaushe kallon uwa nake mata, haka zalika Kuma ban tab'a d'aukar ku a matsayin y'an Uba ba, ina d'aukar kune a matsayin Wanda muka fito ciki d'aya, bai tab'a rike mahaifiyar ku da mugunta ba, *Amma sai dai Kash, Ashe ita Uwar ku mugunwa ce, mai yad'a fasadi a bayan k'asa, mai cutar da Rayuwar y'ay'an mutane Ciki harda k'ananan Yara wad'anda zasuji ba basu gani ba, take shigo da miyagun kwayoyi cikin Kasar ta ta haihuwa, sai yanxu na fahimci cewar Shaye shayen da kake yi, har da d'aurin gindin SHASHASHAR UWAR KA, ina mai shawartar ka da cewa koda wasan wasa karka kuskura ka k'ara Zuwa da niyan kwatanta makamancin wannan Haukar taka ta saka Hanu a jikina, duk kuwa Ranar da tsautsayi yasa, ka k'ara Aikatawa tabbas a Ranar zan Sanja maka kamanni wacce mummunan dabbar jeji sai tafi ka kyan gani*.


Yana gama fad'ar haka yasa kai ya fice yabar

  Khalid da hucin Zuciya.


  Kallon Daddy khalid yayi, cikin huci yace,

  " Daddy...............


  Saurin dakatar dashi Daddy yayi ta hanyar d'aga masa Hanu, yace fice ka bani wuri, shashashan Banxa, marar Hankali.


  K'in ficewa khalid yayi ya tsaya yana huci Akan Daddy.


  " Baxaka fice bane ka tsaya kana kallo na, ko zaka zo ka dakeni ne, da ka tsaya kana huci.


  Kad'a kansa yayi sannan ya fice yana kwafa tare da hararar Mama.


  Yana Fita Daddy ya dafe kansa dake Sara Masa, tun jiya da abunnan ya faru yake jin jiri k'arfin hali kawai yake yi, saboda Idan ya nuna gazawar sa, yasan Al'amuran sai sunfi haka tab'arb'arewa.

  Waje yasa mu gefen momma ya zauna tare da daura kansa a kafad'ar momma ya runtse idon sa yana neman sauk'i a wajen ubangiji, 

  " Mena ragi Saratu dashi, wacce har sai ta nemi kud'i ta mummunan hanya, kin cuceni Saratu.....


Jin da yayi an rufe masa Bakin sane yashi bud'e idon sa, momma ce.


 Cikin sanyin murya tace

" Alhaji karka yiwa Hajiya Saratu, baki domin kuwa kai mijin tane Addu'ar ka zai iya kamata, ka mata yayi ka nema mata shiriya wajen Ubangiji, Hadith ne guda da yake cewa, *fal yakun khairan Auli yas mut*.

  Ka nema mata shiriya ina ga hakan zaifi.


   Murmushi Daddy yayi cikin k'aunar tsohuwar matar tasa, wacce Allah yayi ta da kyakkyawar Zuciya, yanxu duk Abunda Momy Sarah tayi mata, harma kwance take a asibiti ta dalilin SARATU Amma wai itace take nemawa Saratu Sauk'i.

   Maida kansa yayi ya kwantar tare da cewa to Allah ya shirye ta.


  Shiko Khabeer fitar sa station d'in su ya nufa, d'aki na mussaman wanda aka Ajiye Momy Sarah ya shiga, tana Zaune, yayin da kamal keta famar bincikar ta, tak'i magana.


  Runtse idon sa Khabeer Yayi sanadin ganin Momy Sarah zaune a d'aki na mussaman wanda ake tsare tantiran masu laifi,yau kuma Matar Uban sa ne zaune a cikin sa ana binciken ta, takowa har gaban ta tare da dafa teburin dake gaban ta, ya kira sunan ta darect yace

" *SARATU* 


wanda Hakan Yayi bala'in girgixa Momy Sarah Abunda bata tab'a jiba kenan Khabeer ya Kira SUNAN TA darect, hatta su Kamal ma sanda Hakan ya girgixa su, zuciyar Momy Sarah kuwa ba karamar tsinkewa yayi ba.


   Ki taimaki Rayuwar ki ki sauk'ak'awa Hukuma bincike, ki fad'a mana inda shugaban naku yake, tun kafin ki fad'a dan dole domin Azaba.


  Kallon Khabeer Momy Sarah tayi tace lallai d'an Zaki ya girma, yanxu Khabeer kaida aka haife ka a hanuna naci kashin ka naci fitsarin ka, kaine yau a gabana kake tsaye kake musayar yawu dani, kai Khabeer.....


Dakatar da ita Khabeer yayi ta hanyar cewa.

" Uwata ce ke da baxan bincike ki ba, kinga Saratu, waye yasaki kici fitsari na da Kashi na, da kike zancen su, ni yanxu takaici nake da kike kiran cewa kin raineni, domin kuwa na Rainu a Hanun munguwar mace wacce bata d'auki Rayuwar d'an Adam a baki komai ba, juyawa yayi ya kalli KAMAL yace, bama bukatar jin komai ma daga Bakin ta, zanje gida zan d'auko wayar ta, ta isheni duk wani bincike na, Kara maida kallon sa wajen Momy Sarah yayi yace password d'in wayar kuma, Nasan shi tun ba yauba, *JUNIOR*

Dariya yayi yace koba shi bane.


  Ta kaici da haushin sanin possword d'inta da Khabeer yayi shine ya hanata magana.


  Ficewa Khabeer Yayi tare da cewa Kamal kar a yadda a cirewa Momy Sarah bullet d'in jikin ta sai gobe.



  A k'ofar gidan su khabeer ya tsaya yayi sallah sannan ya k'arasa Cikin gidan nasu, dukan su k'annen nasa tare da Mamy a falo ya samesu suna Zaune sunyi shuru, tare da tagumi, y'ay'an Momy Sarah ya kalla take suka basa tausayi, yasan yanxu haka suna jin ciwo a cikin zuciyar su na abunda mahaifiyar su ta Aikata.

  Kiran sunan Fatuma yayi.


  Cikin sanyin murya tace.

 " Na'am yaya Khabeer.


  " Jeki Kira min NANA sannan ki shiga d'akin Momy Sarah ki d'auko min wayar ta.


  Da to Fatuma ta amsa sannan ta tashi  tayi ciki.


  Gaban Mami Khabeer yaje ya sunkuya, Hanun ta ya kama yace.

 " Mami ki daina tunanin nan jikin momma fah da sauk'i sosai ina tunanin ma zuwa gobe za'a iya bamu sallama.


  Daga masa kai Mami tayi alamun ta gamsu sai kuma ta masa alama da Hanu na ina yakai Momy Sarah Kuma.


   Murmushi yayi yace Mamy Momy Sarah tana Hanun Hukuma. 


  Nan ma d'aga kanta tayi. Cikin b'acin rai.


  " Yawwa Mami ni daman ke yar *DUKKU CE RUGAR ARDO* 


  A Razane Mamy ta daga kanta, cikin mamakin inda Khabeer ya san sunan RUGAR Su, d'aga masa kanta tayi cikin sauri Alamun ehh.


  Murmushi Khabeer yace         "  to Mamy naje Rugar ku.


   Murmushin itama tayi, sannan ta masa Alama da Hanu, yaga yaranta.


  Shuru Khabeer Yayi ya rasa mai zaice Mata, baya son tasan cewa Nasreen ce kawai ta rage a cikin y'ay'an ta.

 Nisawa Yayi yace.

  " Dukan su suna lfy harma na sanar dasu cewa kina gidan mu, zan dawo musu dake.

To yanxu kuma wannan case d'in ya rik'e Ni, baxan samu komawa ba, har sai na gama wannan Case d'in.


   Murmushi tayi tare da masa Alamun nasara cikin jin dad'in samun labarin yaranta suna lfy.


  Komawa kujera yayi ya zauna tare da tunanin Halin da Nasreen take ciki a hanun munguwar yadikkon ta, jin shuru da yayi yasa shi kwalawa Nana da Fatuma Kira, kusan tare suka fito.


  Mik'o masa wayar Fatuma tayi, tana son tambayan sa labarin mahaifiyar ta Amma tana tsoro haka Dole yasa tayi shuru da Bakin ta.


 Karb'an wayar Yayi tare da cewa Nana d'auko hijab d'in ki, muje hospital, Zaki kwana tare da momma ke kuma Fatuma anjuma zan turo Daniel yaxo ya kaiki ki kai musu abinci.


  To Fatuma tace, sannan su kuma suka fice da Nana ya sauk'e ta a asibiti shi Kuma ya wuce gidan su Zuhura domin Amsa kiran mahaifin ta.


 A harabar gidan ya tsaya tare da kiran Baban Zuhura,yace masa yana cikin gidan.

   Fitowa mahaifin Zuhura Yayi suka isa falon su Zuhuran tare, 


  A k'asa Khabeer ya zauna yak'i hawa kujerar Babu yanda mahaifin Zuhura baiyi dashi ba Akan ya zauna akan kujerar Amma Khabeer yak'i.

   Dole ya hkr ya kyale sa.

Zuhura ya kira tare da Umma.

  Gaishe da Umma Khabeer yayi, ta Amsa cikin mutunci kamar mutumiyar kirki.


Ita ko Zuhura d'ago kanta tayi ta Kalli Khabeer sannan ta mayar da kanta gefe tana tura baki.


  Mahaifin Zuhura ne ya fara magana ta hanyar cewa.


  " Khabiru daman ba wani abu yasa na Kira ka ba, daxu ne Zuhura taxo min da cewar kace ta dawo gida sai ka neme ta.

  Shine nace Bari na Kira ka naji meke faruwa?


  Kan Khabeer na k'asa yace

   " ehh Baba nine nace ta dawo sai na neme ta, ba Kuma haka kawai yasa nace ta tafi ba, Na gaji da Halin Zuhura ne Baba.


  " To Alhamdulillah Khabiru ina son ka sanar dani menene Zuhura take maka wanda har ka fara gajiya da Halin ta.


  "D'ago kansa Yayi ya kalli inda Zuhura ke zaune, sai kuwa akayi sa'a itama ta d'ago nata kan, Ido suka had'a, yayin da Khabeer ya kawar da nasa Kan yace.


  "Baba Zuhura ta raina iyaye na bata ganin girman su bare kuma darajar su, Baba tsabar Bak'in Halin Zuhura yasa y'an uwa na basa kaunar zuwa gida na, domin kuwa ko sunxo Zuhura bata sauraron su, K'arshen ta da masifa zasu Rabu, duk wannan abunda yake Faruwa nasan su wasu tana yinsu a gabana wasu kuma gaya min ake Amma duk da haka na shanye su, na kyale Zuhura, Amma Baba yau a gabana Zuhura take kiran iyaye na da maha'inta har mahaifi na yana fad'a Zuhura na mayar Masa, wannan dalilin yasa nace ta dawo gida sai na neme ta.


  Numfasawa mahaifin Zuhura Yayi tare da hawa kan Zuhura da fad'a, fad'a yake mata kamar zai dake ta, sannan ya dawo kan Khabeer yace..............





Naso ace na tab'o Nabiya yau sai dai Kuma Babu time kuyi hkr mu had'u a next page, naso ace page din yau yafi haka yawa.



*More comment more typing*


*Share*

     *And*

*Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻



     *(Ummu Nasmah)*

[12/20, 6:03 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳



*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*




*بسم الله الرحمن الرحيم*



 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________




Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un

  Allahu Akbar.😫😫😫😫😫😫😫

Ubangijin daya bamu ke yafi mu sanki, kuma shine ya k'arbe ki, tabbas munyi babban Rashi, Ubangiji Allah ya jik'an ki da Rahama *NAYI* yasa mutuwa hutuce a gareki.


Ya ubangiji ka mata masauk'i da gidan Aljannar ka mad'aukakiya wato Jannatul Firdausi. 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 



 *Sadaukarwa*


 Gare ku sister's wannan page d'in mallakin kune


 احلام فطمة

And


Maman khairat.


Na gode sosai da k'unar ku gare Ni.


 Allah dai yabar k'auna nata suburbud'o muku Ruwan Typing.




*P*••••••••4️⃣6️⃣ to 4️⃣7️⃣


 " Kayi hkr khabiru bansan irin wannan zaman kuke da Zuhura ba, da tuni na saita mata Zama, kayi hkr ka d'auki matar ka ku koma.

Juyowa yayi wajen Zuhura yace ke Kuma wlh Zuhura kiji tsoron Allah ki gyara zaman takewar Auren ki, ki Sani cewa iyaye ba Abun wulak'antawa bane, yanda bazaki so a wulak'anta Miki naki iyayen ba, to kema karki wulak'anta iyayen wani, wlh Zuhura koda wasa nak'ara jin labarin kin yiwa mijin ki wata tsiyar koko y'an uwan sa, to wlh karki kuskura ki dawo min gida ki nemi wajen shiga, badai Nan gidan ba.


 Cikin k'unk'uni Da tura baki Zuhura tace, shikenan Baba shi kad'ai zaka bawa ikon magana ni baxa'a Bani ba.......


  Bige Bakin nata Umma tayi tace.

  " Kinci gidan ku, ba'a baki ikon magana ba, maxa tashi kije ki d'auko jakar ki, kibi mijin ki.


  Tashi tayi tana tura baki tayi bedroom d'in Leemat.


  Hak'uri mahaifin Zuhura ya k'ara bawa Khabeer.


  " Babu komai Baba ya wuce, ni zanje mota na jira ta, kud'i ya cire dubu hamsin ya ajiye musu, tare da cewa ayi hkr Baba Babu yawa.


  Carap Umma tayi ta d'auke kud'in tace

" Mai yawan kenan mun gode Allah ya saka da Alkairi.


  " Ameen cewar Khabeer tare da ficewa.


 Kallon Baba yayi yace.

" Andai ji kunya da son Abun duniya, ko kunya Babu, Suriki yana Ajiye kud'i kina d'ebewa har Hanun ki na neman had'uwa da nasa.


  Tsuka Umma taja tare da tashi rik'e da kud'in a Hanun ta, tace

" Taka akeji ni kaga shigewa ta, ni gara ma da ya koro ta, ko banxa na samu 25k.


  Kad'a kansa Baba yayi tare da cewa Allah dai ya kyauta, ya Kuma ganar dake.


  " Ya ganar damu dai.


  Fitowa Zuhura tayi ta wuce su ba tare da tacewa kowa K'ala ba .


  A mota ta samesa yana zaune yana jiran fitowar ta, da k'arfi ta bud'e murfin motar, ta shiga tare da bugo murfin motar, shidai Khabeer ci kanki baice mata ba, yaja motar sa, sukayi gaba, ko kafin su isa Zuhura tayi tsuka yafi sau goma.


 Wani Irin wawan burki Khabeer yaja, wanda sanda ita kanta Zuhura ta tsorata, cikin fushi yace.


  " Malama karki k'ara min tsuka a mota Idan zagina zakiyi ki Fito fili ki zageni sai nasan dani kike.

     Ko kuma ki fice min daga mota.


  Tab'e bakin ta tayi tace

" Kaga Malam ina Ruwan ka da tsuka ta, koko kaji nace dakai nake, sai wani tsarguwa kake.


  " Nadai gaya Miki wlh na k'ara jin tsukar nan sai kin fita min daga mota ta.

  

 Haka suka k'arasa gidan suna fad'a.


  Kowa d'akin sa yayi, yayin da su Asabe da karima kuma suke ta aikin su.


  Misalin k'arfe goma na dare, Khabeer na zaune yana ta aikin bincike a wayar ta, tanan ne ya gano Hajiya Hindatu ta hanyar, chart d'insu.

Bud'e Datar Khabeer yayi, sako suka ta shigowa, anan ne yaga sak'on Hajiya Hindatu kamar haka👇🏻


  " Hajiya Saratu yarinyar nan fah yau nake son zuwa gidan su, ina so sai na jawo ta jikina ne kafin mu d'auke ta.


  Murmushi Khabeer Yayi ganin tana Online tare da tura Mata 👇🏻


  " Karki jeki tukunna, gobe ina son mu had'u dake, a Ammar hotel.


 Turo masa tayi 👇🏻


 " Ammar hotel kuma Hajiya Hindatu meyasa baxamu had'u a cikin gida naba, har sai munje Ammar hotel, naga bamu tab'a had'uwa a wani wajen ba, idan ba gida na ba.



 Murmushi yayi tare da tura mata👇🏻


  " Saboda tsaro kinsan yanxu hankalin Hukuma a kanmu yake Amma can zamu samu tsaro sosai, Babu wanda zaiyi tsammanin muna wajen.


      " Shikenan to misalin k'arfe nawa zamu had'u.


  Dariya sosai Khabeer Yayi ganin har ya shawo kanta lokaci k'ank'ani, kafin ya tura mata👇🏻


   " Misalin k'arfe 6:30pm kafin nan k'afa yad'an d'auke, saboda muna buk'atar Sirri.


  " Shikenan Hakan ma yayi, dan wannan d'an mijin naki ba k'arami shegen Naci garesa sa ba ni bari na sauk'a, dare ya fara shiga.


      Murmushi Khabeer yayi yace.

   " Oh wato haka nake shan zagi wajen Momy Sarah duk ban Sani ba.

  Tura Mata yayi 👇🏻


" Okay bye


 Itama bye d'in ta turo masa tare da sauka daga Online d'in.


  Sai dai kuma duk iya binciken Khabeer ya gagara gane wani Alama na shugaban k'ungiyar su Momy Sarah, contact d'inta ya shiga yahau bincike, nan ma dai Babu sa'a sai wata number da ya gani wacce ya kasa gane ma'anar ta, saboda Alphabet ne kawai             *(J H N A T)* duk iya lissafin sa ya kasa gane ma'anar alphabet d'in.

 Gajiya ne tare da bacci suka sashi Ajiye wayar ya kwanta.


Cikin dare Khabeer na kwance yana baccin sa hankali kwance Zuhura ta shigo d'akin, dressing merron sa taje ta d'ebe duka key d'in dake wajen, sannan ta fice tana cewa zaka san ka had'ani da mahaifi na.


  Washe gari da safe, misalin Sha d'aya Khabeer ya fito cikin Shirin fita Office, gashi yana son yabi gida ya duba Mami, bai damu da shiga bedroom d'in Zuhura ya duba ta ba, yayi hanyar ficewa daga falon, sai dai bisa mamaki da Al'ajabi, Khabeer yanasa Hanun sa da niyan bud'e kofar falon, yaji shi rufe gam an sa key, komawa.

 

  " To fah Yau kuma Zuhura key tasawa kofar nan kenan.

 Juyawa yayi zuwa d'akin sa, da niyar d'auko key d'in, sai dai kuma wayam Babu key ko d'aya a wajen, duk inda yake tsammanin zai samu key ya duba a d'akin Babu koda Alamar key.

  Bedroom d'in Zuhura dai daya k'i shiga, saboda gudun masifar ta, nan d'in ya nufa.


  Tsayawa turus Khabeer yayi sakamakon ganin Zuhura tana kwance cikin kayan bacci sai baccin ta take hankali kwance, yayin da duk surar jikin ta suka bayyana, wani zubawa tsikar jikin Khabeer yayi, yayin wani irin kasala ya shiga jikin sa, sha'awa ce mai k'arfi, ta bijiro masa sakamakon, kwana biyu da sukayi basu jone gado d'aya ba.

  Kauda kansa gefe Khabeer yayi, tare da kiran sunan ta.


 Cikin bacci Zuhura taji Ana kiran ta, Kuma kiran yak'i ya kare hakan ne yasa ta bud'e idanun ta a hankali ta sauke su Akan Khabeer, mik'a tayi wanda sai da tasa Khabeer ya kusa sumewa a wajen tace.

 " Lfy Malam kake tashi na yanxu.


  Bai ce mata komai ba ya mik'a mata Hanun sa yace.


  " Bani key d'in da Kika d'auka a d'akina.


  " Yaushe na shiga d'akin ka kuma na d'auki key.


  " Bansan jan zance Zuhura waye zai shigo d'akina ya d'auki abu Idan bake ba, ko kina tunanin duk abunda kike a d'akin bana kallon kine, to Bani key d'in gidan nan.


  " Baxan bayar ba, Babu inda zakaje yau a gidan nan zama zakayi mu wuni tare.


  Kallon ta Khabeer Yayi cikin zaro ido😳 na wuni a gida, to fah a wani dalilin kenan.?


   " A dalilin ganin damana ta fad'a masa cikin gadara.


   Dariya sosai Khabeer yayi, yace

  " Anya kuwa Zuhura yau kina da Hankali, a jikin ki, 

Saboda Banda Abun yi sai na zauna tare dake Koh.

  Kinga Zuhura, d'auko min key d'innan ki bani sauri nake zanbi hospital.


  " Wlh ko ina zakaje baxan bada key d'in nan ba.


  Kyale ta yayi ya doshi dressing mirror ta, itama bata kulasa ba kasancewar tasan bata ajiye a nan ba, sai ma shigewa tollet da tayi, ba inda Khabeer bai duba ba a d'akin Zuhura, Amma bai samu key d'in ba, har ya juya zai fita, sai kuma wata zuciyar tace baka duka karkashin Bed d'in ta ba, komawa kuwa yayi tare da sunkuyawa, hango key's d'in yayi suna zube a k'asa, dariya Yayi mai sauti yace

" Wai ita a haka tayi ajiya, d'auka Yayi tare da zuwa Bakin tollet d'in yace, Hajiya Gaskiya kin iya Ajiya, to nikam na tafi mu wuni lfy, ficewa yayi yana dariya.


  Sauri Sauri Zuhura take ta gama wankan nan ta fito, Amma ko kafin ta fito Khabeer ya har yaja motar sa yabar gidan, k'wafa tayi tare da komawa bedroom d'inta tana cije yatsa.


 Gidan su khabeer ya fara shigewa darect, ya samu k'annen nasa duk sun tafi school Nana kuma tana Asibiti, bedroom d'in Mamy ya shiga ya samu tana zaune rik'e da carbi a Hanun ta, sunan ta ya Kira yace.


  " Mamy yau ke d'aya ce a gidan.


  " Nice tace Masa.


 " Wani Irin zabura Khabeer yayi yana nuna Mamy da Hanu yana cewa.

 " Mamy ke ... Ke kece kikayi magana yanxu, ki amsa min Mami.


  Murmushi Mamy tayi tace, nine khabiru, nine Nayi magana.


  " Daman kina magana Mami, kika nuna mana bakya magana.


  Kama Hanun Khabeer tayi tace, khabiru, nima Kaina haka na tashi yau naji harshe na ya sake min, har na Samu damar magana.

    Khabeer ina son komawa garin mu, Bansan Halin da Yara na suke ciki ba, Nasan Nasreen mai hkr ce, zata iya jure duk wata wahala, Amma banda Nabiya.


  Alhamdulillah Khabeer ya furta tare da cewa, baxaki koma garin ku yanxu ba, Mamy, nace Miki yaran ki suna Halin lfy, Babu abunda ya samesu, ki bari na gama da wannan Case d'in tukunna, momma ta Samu lfy, Idan hankalin kowa ya kwanta Sai ki koma Rugar taku Mamy, tare ma zamuje, kiyi hkr.


  Shikenan khabiru, bari na d'auki hijabi na sai muje asibitin tare koh.


  " A'a Mamy ki zauna a gida kawai anjuma za'a sallamo su suma.


   "Shikenan to ALLAH ya bata lfy.


 Daddy fah yana nan kuwa.


" Gsky tunda ya fice sallar Asuba bai dawo ba.


  " Okay ina ga ya shige hospital ne.

   Khabeer yace Mamy na zan shige.


 A dawo lfy ta masa tare fatan nasara.



 Asibitin ya wuce darect Nana ya samu tana zaune ita kam momma bacci take.

Gaishe shi Nana tayi, bayan ya amsa ne yake tambayan ta Daddy yaxo kuwa.

  Ehh yana wajen doctor.


 " Okay an kawo muku breakfast ne ya tambayi Nana.


  " Ehh Fatuma ta kawo kafin ta wuce school.


  " Okay bari naje wajen doctor na samu Daddy.


  Office d'in doctor ya shiga, bayan sunyi musabaha ne daddy yake masa bayanin ai an basu sallama, momma kawai suke jira ta tashi daga bacci su wuce gida.


  Bill d'in abubuwan da Akayi momma Khabeer ya tambayi doctor ya rubuta masa sannan ya biya sa kud'in sa, yacewa Daddy ya shige Office.


  Fatan alkairi Daddy ya masa sannan yace idan da hali anjuma yana son zuwa zasu gana da Momy Sarah.


 Shuru Khabeer yayi sai zuwa can yace Babu damuwa Daddy sai kaxo, sannan yasa kansa yabar asibitin.


  Acan Office d'in ma Khabeer ya samu ana cirewa Momy Sarah bullet sai zabga Uban ihu take, tun daga waje ana iya jiyo sautin kukan Momy Sarah.



*************************

Junior kuwa Ay'an kwanakin da yayi a gidan su, Khady shak'uwa mai mai tsanani ya shiga tsakanin su, mussaman ma da Nabiya, itace mai masa komai, kullum kuwa Yana cikin bata lbrn momma da Mamy, mussaman ma Mamy yafi bayar da lbrn ta.


Gabaki dayan su suna zaune a falo, Hajiya ce ta fito Hanun ta rik'e da takadda, zama tayi gefen su, tare da shafo kan junior tace.


  " Junior ka fara kewar Abban ka koh.


  Dariya junior Yayi, yace

" Ba Abbana kad'ai ba harda Mamy da momma da Daddy, 


  Dariya dukan su sukayi Hajiya tace.


  " Baka ce kayi kewar Momy Sarah ba.


  Had'a ransa junior Yayi yace, Babu Ruwa na da ita, munguwa ce.


   Zaro ido Hajiya tayi tace Momy Sarah ce munguwa, kul na k'ara jin ka fad'a mata haka.


  Nabiya ce tace, 

" Ka cika yawan magana junior, tashi kaje d'aki ka d'auko min, fruit din dana ajiye saman frish.


  Tashi yayi da gudu ya shige bedroom din nasu.


   Hajiya ce tayi magana tace 

   " Nabiya munyi magana da Mlm isma'il, Akan zancen Neco da Zaki zana, so na biya kud'in yace Idan an kusa farawa zai mana magana, sannan kuma ta mik'o mata waya a kwali sabuwa dal tace ga wannan kuma wayace na siya Miki k'irar Infinix hot 8, kije kisa a caji, idan ta caju sai Khady ta nuna Miki yanda ake amfani da ita.


  Tsalle Nabiya tayi ta k'ank'a Hajiya tana murna, 

   " Wow Hajiya na gode sosai Allah yasa ka da alkairi yabar zumunci, tabbas kin nuna mini gata wanda ko wacce uwa take nunawa d'anta, baxan tab'a mantawa dake ba a Rayuwata.




************************


Mama na hango tana bincike cikin D'akin ta sakamakon jin warin da tayi, tana tunanin ko b'era ne ya mace mata cikin D'akin, wani K'ara Mama tasa.


 Tare da d'aura Hanun ta a kayi, tace

 " Na shiga Uku, waye ya fasa min kwalban Nan, Nasan dai Nabiya yau bata wuni gidan nan ba, tana gidan Goggo zata mata wanki, kwalawa yar gwal kira tayi.



  Shigowa d'akin yar gwal tayi tace gani mama.


  Nuni ta mata da hanu tace.

  " Waye ya fasa kwalban Nan.


 " Nice cewar yar gwal, kud'i nane ya fad'a lungun, naxo d'aukowa bisa kuskure hanuna ya bigesa ya fad'i.



   " Shikenan kin cuceni kin kashe ni, tunda kwalban Nan ta fashe tabbas duk inda Maimuna take ta dawo hankalin ta, yanxu Babu asirin da zan mata ya kamata, wannan d'in ma da yaya nasamu ya cita, kin cuceni yar gwal, rufe ta da duka Mama tayi, Babu ji Babu Gani




*Karku manta da cewa bana typing Ranar Asabar.*




*Share*

    *And*

*Comment*



   *Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻[12/23, 5:37 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

SARA DA SASSAKA

  (Baya Hana Gamji)

              Toho

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


Story And Writing

           

           By


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



                     *MAKAMAR KAINUWA* 👸🏻



📱

*08147537180*



*بسم الله الرحمن الرحيم*


 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



  *ZARAHN ABDUL MOMYN AHLAN* 

      *SAHIBAR KAINUWA*

*(My k'awalliya k'awar Arziki Allah dai yabar k'auna ta waje na)*


Ina taya ki murnar kammala shahararran novel d'inki mai suna

*GUDU AJEJI* Abunda kika fad'akar Allah ya baki ladan sa wanda kika yi kuskure kuma Allah ya yafe Miki, 

   

    Tallah Tallah Tallah.


Ina kuke makaranta littafan hausa, to ku matso kusa, domin kuwa nesa taxo kusa, shaharrun marubutan nan naku wad'anda suka saba nishadantar daku, sun shirya tsaf sun baje muku basirar su, domin nishad'antar daku da tsarabar sabuwar shekara.


  *Rasheedat Usman*

      *(Ummu Nasmah)*

Ta Zauna tayi muku Nazarin kyakkyawan labari mai k'ayatarwa, tare da ilmantarwa, zaku ci dariya  sannan zaku ilmantu, labari ne wanda na tsarashi a nutse, domin ku masoyana kudai ku biyo ni cikin littafin. *(INDO A BIRNI)*

     1 -- 1 -- 2020  idan mai kowa mai komai ya kaimu.


Gata nan fah ta taho da shirin ta tsaf, ta saka tunanin ta tare da basirar ta Rubutu ne zata muku shi mai ma'ana, wanda zai nishad'antar daku, ya baku mamaki tare da tausayi, kudai ku biyo Alk'alamin *ZARAHN ABDUL MOMYN AHLAN* 

A cikin book d'inta mai suna *(K'ANNEN MIJI NA)*

   Domin taya ku murnar Sabuwar shekara 1---1---2020 da yardar Allah.


Idan Ana dara uwa aka fidda, ina kuke masoyan Book d'in *DIJA K'HAYA*

Ku matso kusa a yauma *UMMU FATUMA* ta dawo muku da wani sabon labari wanda zai saku cikin Shauk'i mai suna, *(ABINCIN ZUCIYATA)*

Karku sake a baku labari.


 Kudai ku biyo fitattu sha biyar 15 Kainuwa Writers, domin kuwa mun shirya tsaf domin ganin farin cikin ku masoyan mu.

   Muna Alfahari daku a duk inda kuke.


 *P*••••••4️⃣8️⃣ to 4️⃣9️⃣


Cigaba Mama tayi da dukan y'ar gwal, tana zagin ta.

   Ita ko y'ar gwal ta cika tayi fal, cikin zafin Zuciya da haushin dukan da Mama ta mata ya sata ture Mama gefe da k'arfi, tana huci.

  Taga !! taga Mama tayi zata fad'i sai kuma Allah ya bata sa'a ta cafke murfin k'ofar d'akin nata da k'arfi, salallami Mama ta d'auka tana cewa.

   

   " Y'ar gwal nine kike niyar wurgarwa k'asa, ni y'ar gwal, Ni Uwar ki, Anya kuwa kina neman Albarka ni ta k'arasa maganar tana nuna kanta da hanu tare da firfito da idanun ta waje.


  Cikin tsawa Y'ar Gwal tace.


  " Ya kike so na Miki to Mama, kin sani a Gaba kina duka kamar wacce kika Samu jaka, sai na barki ki jimin ciwo kenan, Akan wannan y'ar kwalbar mai warin tsiya, nidai wlh Mama daga yau karki k'ara duka na, tana turo baki ta k'arasa maganar.


  Cikin tsoro da Al'ajabi Mama tace, 

 

  " Oh ikon Allah ni Salamatu yau naga y'ar zamani, to Uwata Baxan K'ara dukan ki ba, bare ki tsine min na shiga duniya.

  Tana k'arasa fad'ar haka ta dauki hijab d'inta, sai gidan BOKA RABGAS, ta fice ba tare da ta k'ara tankawa y'ar gwal ba.


  Tabe bakin ta y'ar gwal tayi, tana k'ananan magana ita a dole taji haushi an dake ta.


  Cikin Sa'a Mama ta Samu wajen bokan Nata yau Babu, kowa, Babu sallama, ta shiga kuma ta Baya !! Baya


  Wata Irin Dariya marar dad'in Sauraro, bokan Yayi, take kuwa, Jajayen hak'waren nasa suka bayyana, wanda idan nace muku zai iya fin shekara baiga Aswaki ba, karkuyi mamaki, shi kanshi gun zaman bokan zan iya cewa bola ne,

Gefe kad'an dashi Mama ta zauna tare da jero masa kirari.


  " Kaga bokan da yaga jiya yaga yau boka mai ran karfe, wanda ke gani har hanji, kunji boka mai manya Aljanu boka........


  D'aga mata hanu bokan Yayi Alamun ya isa haka  kirarin, cikin wata Irin murya marar dad'in Sauraro yake magana.


  ' Salame ta k'are miki nasan Kinxo ne Akan fashewar kwalbar da Mukayi wa Kishiyar ki Asiri, dashi tabbas Salame masifa tana tin Karo Rayuwar ki, Domin kuwa Maimuna zata dawo garin nan Hhhhhhhh ya bushe da wata Irin Dariya, sai kuma ya had'a fuska.


  Zaro ido mama tayi, tare da dafe k'irji tace


 " Na shiga Uku boka ka taimaka min, Bana k'aunar dawowar Maimuna cikin garin, kasan nasha bak'ar wahala kafin na Samu nasara akan Maimuna.


  Dariya bokan ya k'ara bushewa dashi sannan yace, karki damu za'ayi Aiki akan ta, muna son zaki kawo mana Bak'in bunsuru, wanda zamu yanka, mu bawa Aljanu, Ziyad, yasha jinin sa, saboda dashi zamu yi wannan Aikin  za kuma ki kawo mana koren k'adangare, wanda wannan k'adangaren shine zamu aika zuwa duk inda MAIMUNA take, a wannan karon kam, ba k'ara shigar da Maimuna duniya zamuyi ba, *KASHETA* zamuyi sannan zaki kawo kud'in da za'ayiwa Aljanu sadaka dashi.


  Numfasawa Mama tayi, cikin tunanin inda zata samo koren k'adangare, gara ma Bak'in bunsuru za'a iya samun sa, kallon ta mayar wajen boka, tace.

   

  " Boka a Gaskiya Babu inda zan samu koren k'adangare shima Bak'in bunsurun bansan inda zan samesa ba Gaskiya, sai dai Idan zan bayar da kud'in, ko za'a samu a wajen ka.


   Cikin d'aga murya boka yace


  " Kin samu ma Amma idan har zaki biya mu dubu d'ari buk'atar ki ta biya an riga angama.


  Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace.


" Zan biya boka inhar buk'ata ta zata biya, bani da damuwar kud'i ko nawa ne zan iya kashewa, dubu Goma ta ajiye masa tare da cewa zata je tasa sauran gonan gadon ta kwalli d'aya tak a duniya a kasuwa, zuwa jibi zata aiko yar gwal da kud'in.


  Dariya Boka ya bushewa dashi sannan yace.


   " Sai kin kawo tashi ki b'ace min da gani, la'ananniya, ki tashi nace b'acacciya cikin tsawa yayi mata magana.


  Tashi mama tayi ta fice da baya baya tana yiwa bokan kirari.


  Itako Nasreen tana zaune ta gama yiwa Goggo wanki ta gaji, sai dai kuma Alhamdulillah goggo ta bata Abinci taci ta k'oshi tagumi ta Zabga tana tunanin yanayin rayuwar ta, a lissafin ta, Auren ta da jungud'o yau saura kwana Uku, ita damuwar ta ma da taji goggo na Kiran cewa da kayan d'akin Ammin ta za'a kaita, gidan miji, goge guntun hawayen ta tayi, ita da goggo zata yadda da an kaita haka koda taburma ne, yafi mata kwanciyar hankali, Akan a kaita da kayan da aka kawo mahaifiyar ta gidan miji.

   Kiran da goggo ta mata ne yasa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta Lula, Amsawa tayi tare da Tashi ta nufi d'akin goggo, jungud'o ta hango Zaune tsakar d'akin goggo, had'a fiska Nasreen tayi tare da juyawa tabar wajen, hanyar k'ofar gida tayi, da nufin komawa gidan su, goggo ta biyo ta, cikin fad'a tana cewa.


  " Ficewa zakiyi kina jina ina kiran ki, dan Uwar ki.


  Bata tankawa goggo ba, kuma bata da niyar dawowa, Domin kuwa ta tsani Ganin fiskar jungud'o, dan ta gwammace gara taga Maciji kububuwa, Akan taga, fiskar jungud'o, tafiyan ta tayi tana cewa wlh baxan dawo ba, idan yaso yau ku kashe ni, dake da Baban.


 Komawa goggo tayi tana mita har ta shige d'akin nata, hakuri ta hau bawa jungud'o tana cewa.


  " Ja'irar yarinya marar kunya, zanxo ne har gidan naku na same ki.


  Babu komai jungud'o yacewa Goggo, karki wani je ki same ta, *Ai AKWAI ZAMA MA NA HAR ABADA* yana jiran mu, tunda yau saura kwana Uku Auren.




*************************

Nabiya ansa waya a chaji ya cika, daman Already da sim card Mai rijista Hajiya ta kawo mata wayan, sai faman ture ture suke ita da Khady, junior kuwa yasha pictures a cikin wayan nan Babu adadi.

  Bayan sun gama ture turen ne suka bud'e WhatsApp, dariya Khady tayi tare da cewa.


  " Alhamdulillah waya ta ta huta, na kuma huta da nacin kiran wayan da kamal ke min kinga yanxu zan tura mishi number ki.


  Had'a fiska, Nabiya tayi tare da bankawa Khady harara tace, 


  " Wlh karki fara koda wasa domin kuwa ni bana son yawan naci, sai kace ana soyayyar dole nace bana so ai sai yayi hkr ya kyale ni nasha iska koh, ko ana soyayyar dole ce.?



  Dariya Khady tayi har tana rik'e cikin ta, cikin dariyar tace,

   " nidai baxaki ji mutuwar sarki a Baki na ba, naje na tofa nawa, wata Rana na ganku kuna zuba Love, shikenan kuma kun barni da kunya.


   Tsuka Nabiya taja, tace

" Allah ya sauwak'a Ni Babu wani soyayya a gabana, karatu na shine yake gaba na ba wani soyayya ba, yawwa ke munyi Tuya mun manta da Albasa, kinsan bamu Kira ya *SADIQ* ba yamin tubuli yasan nima na faso gari.


  Dariya Khady tayi tace

" Kuma fah Hakane ni wlh na manta dashi ma kwatakwata yau.


  " Nikam ban manta dashi ba, Domin kuwa yana Raina, cewar Nabiya.


  Dariya Khady tayi tare da kiran layin ya SADIQ, ta mik'awa Nabiya wayar, Ringing biyu ya d'aga tare da sallama, kasancewar baisan numbern ba.


  "Aslm d'an k'auye cewar Nabiya.


  Dariya SADIQ yayi kasancewar gane Nabiya ce ta kira sa, cikin jin dad'in kiran ta, domin kuwa yau yana k'ishir ruwan jin muryar ta.


 " Y'ar K'auye ya Akayi ne.


  Had'a fiskar ta tayi kamar wanda Sadiq d'in ke kallon ta, tace.


  " Munyi fushi  ya Sadiq, Rabon da ka kira mu yau kwana biyu kenan.


 Wani Irin dad'i SADIQ yaji, ganin yanda Naby ta damu dashi har rashin kiran sa ya dameta.


  " Sorry Sweet sister na, wlh kwana biyun nan ina busy ne, Amma dai Amin Afuwa.


  "Amma ka Ya SADIQ ALBISHIR.


  

  " Goro fari tas sweet sister nah.


  " Ka bani goron kafin na fad'i maka.



  " Oh sister Naby to shikenan na Miki Alk'awarin komai kike so idan na dawo zan Baki.


" Okay, Hajiya ta siyan min waya sabuwa dal da ita ma nayi kiran ka.



 " Wow sweet sisi na, lallai Hajiya ta kyauta kice *Y'AR K'AUYE* ta faso gari Gaskiya na Miki murna, Hajiya ta fanshe ni Gaskiya.


  Naby da Sadiq sunsha hira sosai kafin su Ajiye wayar.


  Junior kuwa yau Babu d'uriyar sa, sun tafi hospital da Hajiya.




  ***********************

  

Tsayawa Khabeer yayi yana ganin yanda Momy Sarah taci uwar wahala wajen cire bullet d'in, har ga Allah Momy Sarah ta basa tausayi, sosai domin kuwa tayi munguwar wahala, tun tana kuka har kukan yaxo ya gagareta, kiran sunan Kamal yayi tare da basa umarnin cewa ayiwa Momy Sarah Allurar bacci ta 24 haurs ta samu hutu sosai, tare da ce masa ya shirya jami'ai suna da fita 6:30pm.

  Office d'in sa ya shige domin gabatar da aikace aikacen sa.



   Agurguje


Alhamdulillah cikin sa'a su khabeer suka kama Hajiya Hindatu, basu wani sha wahalan binciken Hajiya Hindatu ba domin kuwa bata wahalar dasu ba wajen gaya musu Gaskiya, anan ne Khabeer ya gane wad'annan Alphabet d'in daya kasa gane Number waye ne, ashe number Ogan su MOMY SARAH ne wato John.

  Yanxu binciken Khabeer ya koma kan John, yana iya Bakin k'ok'arin sa na ganin ya gane inda John yake Zaune, kasancewar Momy Sarah ce kawai tasan inda yake ita kuma taurin kai ya hanata magana.

  Har yau manyan Khabeer basu san yana gudanar da wannan bincike ba Domin kuwa yasan muddun suka sani idan k'ungiyar tana da k'arfin za'a it's dakatar dashi, kasancewar lalacewar k'asar mu ta Nigeria.

   Cp ne kawai yasani ya Kuma goyawa Khabeer baya tare da masa fatan alkairi.


 Momma Alhamdulillah jiki yayi sauk'i sosai, domin kuwa babu inda bata takawa suna zaune lfy da Mamy dan sanda momma da daddy sukaji Mamy tana magana sunyi farin ciki sosai, Amma har yanxu Babu wanda ya tambaye ta, abunda ya fito da ita daga garin su, duk da dai shi Daddy yana da niyar hakan a ransa Amma yafi so, sai hankali ya kwanta, an gama Case d'in Momy Sarah tukunna.


Zuhura Kam Rashin hankali sai ma abunda ya k'aru domin tsiya iri iri take nunawa Khabeer, duk da dai shi baya biye Mata, a cewar sa tana cin darajar mahaifin sa.



 Gudu take sosai cikin wani Bak'in jeji bayan ta kuma Damusa ne ke binta, Gudu take sosai tana kiran suna Ubangijin, tayi nisa cikin jejin ne, kawai sai taga Zaki, tsaye gaban ta, ihu tasa da k'arfi tace KHABEER.......



  A matuk'ar Razane Khabeer ya tashi daga baccin shima da k'arfi ya kira sunan ta NASREEN.







*Share*

 *And*

*Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻



       *(Ummu Nasmah)*

[12/24, 4:08 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


  *Sadaukarwa*

Ga dukkan *MASOYANA*

A duk inda kuke, ina Alfahari daku, harma wad'anda suke biyo ni private, wanda bana group d'in ku, ban kuma san group dinku ba, Gaskiya ina Godiya sosai da k'aunar ku gareni na gode sosai Allah yabar zumunci.


  Dan Allah duk wacce ta min magana ta private ban Amsa mata da wuri ba, tayi hkr, wlh sak'onni summin yawa bana gani wani sak'on da wuri, wani kuma ko na gani, a waiting yake zuwa min,

So kuyi hkr karku ce na muku wulak'anci.



*P*•••••••5️⃣0️⃣ to 5️⃣1️⃣


Sai kuma ya Fara kiran innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un la'ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minazzalimin.

   Sharce gumin daya tsatsaffo masa Yayi, tare da jingina kansa jikin gadon.


  Zuhura dake gefen sa ne ta tashi itama a Razane sakamakon jin k'arar Khabeer.


  " Lafiya Abban junior ka Tashi a Razane da ihu, kaida kake tashi cikin nutsuwa tare da Ambaton Ubangiji, yau kuma ka tashi a Razane, wai ma tukunna waye wannan *NASREEN* d'in da kake kiran sunan ta a Razane.


  Shidai Khabeer bai cewa Zuhura komai ba saima daura kansa da yayi a kafad'ar ta, yayi shuru sai kuma ya tafi maganar zuciya.

  " Anya kuwa Nasreen tana cikin Halin lafiya, ban tab'a mafarki mummuna Irin wannan ba, akan wani d'an Adam, sai ita duk yanda Akayi yarinyar nan tana cikin matsala, dole gobe naje garin su.

  Ajiyar zuciya ya sauke tare da d'aukar wayar sa ya dannawa SADIQ Kira.


 SADIQ dake zaune yana nafilar dare ne yaji k'arar wayar sa, Hanun sa ya mik'a ya d'auko wayan, KHABEER ya gani Rubuce a screen d'in wayar, Khabeer cikin wannan daren ya furta to fah lafiya kuwa? Dagawa yayi ko sallama baiyiwa Khabeer ba, yace " lfy kuwa Khabeer kake kira da tsohon daren nan., K'arfe 3 fah Yanxu.


  Daga can Khabeer yace, to lfy ba lfy ba, labari ne mai tsawo Sadiq, zaifi kyau sai mun had'u mu tattauna, yanxu dai Na Kira kane naji ka dawo gari ne?


   " A'a ban dawo ba, please Khabeer ka fad'a min meke faruwa karka barni cikin damuwa.

   Please tell me what happening?


  " Bafa wani abu bane na tashin hankali SADIQ, so nake gobe misalin k'arfe 12 zaka min rakiya zuwa Dukku, kuma kace baka dawo ba.


  Ajiyar zuciya SADIQ ya sauk'e yace sai yanxu hankali na ya kwanta, yaci gaba da cewa Amma dai Khabeer kai ba k'aramin d'an Iska bane, Ranar da zan bar cikin Gombe kasan nayi Kiran wayar ka baka d'aga ba, ba kuma ka neme ni ba daga baya, kuma Nasan kaga kiran. Sai yanxu dake damuwar kace, ka neme ni ai, koda yake daman ai nasan nafi damuwa da kai fiye da yanda ka damu dani.


  Dariya Khabeer yayi, yace.


  " Kai dai SADIQ ka cika k'orafi wlh, kamata Yayi ka tambaye ni menene yake faruwa, bawai ka hau k'orafi ba.


  " To naji lawyer Uban y'an kare kai, yanxu na tambayi dalili sai a gaya min.


  Dariya Khabeer yayi yace

  

  " Labari ne mai tsawo fah Sadiq baxai yiwu muyi shi a waya ba, dole sai mun had'u.


  Okay gobe zan biyo jirgin k'arfe tara insha Allah zuwa 10 na iso Gombe, idan ka shirya ka biyo gidan mu kawai mu wuce.


  Dariya Khabeer Yayi sosai kana yace.


  " Shege Uban y'an san jin gulma daga jin akwai zance shine har zakayi samakkon dawowa gida to Allah ya dawo da kai lfy.


  Dariya shima SADIQ Yayi kana yace.


  " Ehh na yadda aje a hakan, gulma ne dai sai naji.


  Wafce wayar Zuhura tayi cikin k'ula tace.


  " Ya haka ne kam Malam, ya ni ina maka magana kak'i sauraro na, sannan kuma ka kira Sadiq kana zance zakuje Dukku bayan yanxu ka gama kwalawa wata Gardiyar mace kira, kaga Malam ka fad'i min waye ce Nasreen?


   Tsuka Khabeer yaja cikin haushin Zuhura yace.


  " Duk yanda Akayi da jaki sai yaci Kara wlh kuma duk randa akace bakayi dace da Mace ta gari ba, wlh bakaji dad'in Aure ba, ke dai Zuhura har Abada baxaki tab'a hankali ba, ina Ruwan ki da koma waye ce Nasreen meye Case d'in ki.


  " Wlh Abban junior idan kana soma ka kirani da Abunda yafi jaka amma dai sai ka fad'a min waye Nasreen.


  Dariya Khabeer yayi cikin zuciyar sa yace bari nayi maganin ki, yau kema sai kin kwana cikin bak'in ciki tunda ke mahaukaciya ce.

  Kallon ta yayi yace


 " Okay So kike kisan waye Nasreen ko, ita d'in Zuciyata ce, itace farin ciki na, agunta nake tunanin samun kwanciyar hankalin Aure wanda na Rasa daga gare ki, *ITACE MATAR DA ZAN AURA*


  Zaro ido waje Zuhura tayi, cikin d'aga murya sama tace.


   " Kasan me kake kira kuwa, Khabeer, Wata Jaka shegiya tsinanniya kake kira fah a matsayin matar da zaka Aura, wlh k'arya kake Khab..............


  Bata k'arasa ba Khabeer ya dauke ta da tagwayen maruka har guda Uku masu lfy yace.


  " ke har akwai wata jaka ce wacce ta wuce ki, koko uwata ce ke da idan nayi niyan Aure zaki hanani, ballagaza cikon lissafi ma Irin ki, wacce sam baki da culities na mata, me ake da macen da bata iya girki Bata san mutunci miji ba, bare tasan na iyayen sa, macen da bata iya d'aukar buk'atar miji, Idan Ana kiran sunan matan da suka isa, ki cire kanki a ciki domin kuwa ke lusarar mace ce.

  Ina zaune dake ne albarkacin mahaifin ki, da kuma d'anki, idan ba haka ba da tuni na dad'e da shafe ki a tarihin Rayuwata.


  Takaici Bak'in Ciki, haushi ga kuma Bak'in cikin marukan daya mata da kuma bak'ar maganar daya gaya mata, duka suka taruwa Zuhura a k'irjin ta, kasa tankawa Khabeer tayi sai ma ficewa daga d'akin da tayi da gudu tana kuka.

   

 Tsuka Khabeer yaja sannan ya shige tollet ya dauro Alwala, jallabiyar sa ya zura a jikin sa sannan ya tada sallah, Khabeer shine bai maida bacci ba har saida yayi sallar asuba, sannan ya dawo yabi lafiyar gado.




  *************************


  Misalin k'arfe goma da rabi na safe, *SADIQ* ya shigo gidan nasu, da junior ya fara cin karo a tsakar gidan yana buga Ball, sake Ball d'in junior yayi ya ruga da gudu wajen SADIQ yana oyoyo Uncle.


  Dariya SADIQ yayi ya d'aga junior sama yace.


  " Oyoyo my son, yaushe kaxo gidan nan bani da labari.


  Ya tsunsa biyar junior ya d'agawa SADIQ yace


  " Kwana na haka uncle.


 " Eyye my son kace ka Dad'e banda labari.

 Karasawa sukayi cikin gidan junior yana yiwa Sadiq gwarancin sa.

  Da Nabiya suka fara cin karo tana guga a falon, wani irin sanyi Sadiq d'in yaji a zuciyar sa, sakamakon ganin fiskar masoyiyar tasa wacce ya kasa furta mata kalmar ina sonki.


  Murza idon ta Naby tayi tace


  " Wa nake gani kamar ya SADIQ kodai idonuna ne suke min gixo, 


  Dariya Sadiq yayi yace


   " dake idanun naki na k'auye ne ba, dole ai su Miki kokonto, to ni d'in ne dai *Y'AR K'AUYE*

  

   Dariya tayi tace


 " Y'an K'auye dai ba y'ar K'auye ba, kowa ma Asalin sa k'auyen ne ehhe.

  Tana tura masa baki.


  Dariya sosai Sadiq yayi kana yace to naji Allah ya huci zuciyar ki.


  "Ameen kam ya SADIQ, to tunda ka bani hkr bari nima na maka ya hanya.

Sannu da dawowa ya hanya duk da dai ba'a ce mana ana hanya ba.


  " Ke dai bari kawai sweet sister, wani uxiri ne ya dawo dani yanxu ma haka wanka zan shiga naxo na fice.

  Sauk'e junior yayi yana cewa ina sauran mutanen gidan suke na ganki ke d'aya.


    " sun fita ita da Hajiya sunje unguwa Uku barkatu, wai Hajara yar gidan Aunty Salma ce ta haihu.


  " Ayya hajara ta haihu kenan, to Allah ya Raya, kinga sweet sister dan Allah yiwa junior wanka zamu fita dashi ne yanxu.



  " Okay Babu damuwa tashi tayi tare da kashe dutsin gugan ta kama Hanun junior suka wuce bedroom d'in su.


 Shima Sadiq nashi bedroom d'in ya shige.


Shabiyu dai dai Khabeer ya shigo cikin gidan su SADIQ kansa tsaye kasancewar shi ba bak'o bane cikin gidan, shuru yaji falon Babu kowa, zama yayi a d'aya dake cikin kujerun falon tare da ciro wayan sa ya dannawa Daddy Kira.

Bayan daddy ya d'aga ne suka gaisa sannan ne Khabeer yake sanar da Daddy cewa yau baxai samu shigowa gida ba, zaiyi tafiya shida SADIQ yanxu haka yana gidan su SADIQ sai zuwa yamma idan ya dawo zai shigo.

 A dawo lfy Daddy ya masa tare da fatan Allah ya tsare hanya.


 SADIQ da NABIYA kusan tare suka fito da SADIQ, kallon mamaki Khabeer yabi su dashi, yana tunanin wannan kuma waye san Khabeer bai gane Nabiya ba, kasancewar waye da Kuma hutun da jikin ta ya samu, gashi kuma tasha makeup, tayi mungun banbanci da nabiyan daya sani a picturen da Mamy ta basa.

Junior ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula ta hanyar fad'awa jikin sa yana oyoyo Abba.

   Dago sa Khabeer yayi yace  

  

   " My lovely son, shine ko ka nemi Abba koh, ka Samu Hajiya ka manta damu koh.


  " A'a Abbah Sarah ce munguwa bana son na koma ta k'ara taikeni.


  Dariya Khabeer Yayi yace bakin kane ai taikewan, har yanxu harshen ka bai gama Zama ba.


  Nabiya ce ta katse su ta hanyar cewa, Ina wuni.


 Khabeer bai kalleta ba ya Amsa

" Lafiya.


  Junior ne yace


  " Abbah Aunty Naby tana da kirki, itace take min komai a cikin gidan nan, tare ma muke kwana da ita, Abbah.


   Murmushi Khabeer yace.


  " Kace ka samu Sabuwar Aunty ban sani ba.


  SADIQ ne ya duba agogon Hanun sa, 11:00 yace 

   "kaga Officer tashi mu tafi 11 rana ta fara, tashi yayi tare da kama Hanun junior suka fice.


  A hanyar su ta tafiya ne SADIQ ke tambayan Khabeer mai zaije yi dukku.


  Numfashi Khabeer yaja yace 

   

  Abokina Abubuwa ne suka cab'e a Kaina, kasan Mamy wacce Daddy ya tsinto a hanyar sa ta dawowa daga Kano 

  To ALLAH yasa na gane k'auyen su sakamakon kiwon shanu da momma take yi, Ashe mijin tane Wanda aka bawa kiwon shanun momma, Sanda naje garin ne na fahimci Hakan sakamakon picture dana samu Hanun Mamy na y'ay'an ta, da y'ar tata na gane, sai dai abun tausayin, yarinyar tana cikin wahalar Rayuwar Gaskiya, labarin abubuwan da suka faru Khabeer ya bawa SADIQ.


 Numfashi SADIQ yaja yace.


     " Tabbas tana cikin k'uncin rayuwa Gaskiya Amma Gaskiya Khabeer baka tunanin ka karya mata Alk'awarin daka d'auka mata na cewa zaka dawo Mata da Mahaifiyar ta.


  " Babu maganar karya Alk'awari anan SADIQ kasan wannan zuwan da zanyi bawai na shirya masa bane, kawai kamawa tayi, kuma  Gaskiya bana son mamy ta dawo Rugar nan har sai naji *LABARIN* ta nasan Abunda ya fitar da ita daga garin su, kasan bana cikin kwanciyar hankali Akan Case d'in Momy Sarah.


   "Case d'in Momy Sarah Kuma Sadiq ya tambaya cikin mamaki.


  Murmushi Khabeer Yayi yace


    " Abunda ya hanani neman ka kenan 2days Momy Sarah dai Y'AR ta Adda ce cikakkiya, har junior ta sa aka sace.


  Zaro ido SADIQ yayi yace


  " *Khabeer kasan me kake fad'i kuwa*


  Dariya Khabeer yayi yace.


  " Kowa haka yake mamaki Idan yaji zancen nan.



 *************************


Acan kuwa Rugar Ard'o B'oyi yau juma'a ake ribibin D'aurin Auren *NASREEN da JUNGUD'O*  Mama da Goggo har sun sa an d'ebe kayan d'akin Ammi an Kai gidan mai gari inda za'ayiwa NASREEN jeren d'akin ta.


  Gayya sosai Mama tayi harda gogaggun k'awayen ta, Nasreen kuwa tana shan bak'ar magana da zagi wajen su, matar d'an giya kuwa an kirata dashi yafi sau dubu, dangin mahaifiyar Nasreen kuwa sunxo suma, a wulak'ance Mama ta karb'e su, sunji takaicin yanda aka kasa yiwa Nasreen kayan d'aki, sai dana mahaifiyar ta za'a kaita d'akin miji.


Nasreen kuwa tana can d'akin Ammin ta tana rusgar kuka, ko a mafarki bata tab'a tsammanin cewa da gaske zata auri jungud'o ba, sai gashi yanxu ta tabbatar da hakan tunda saura  3 haurs a daura mata Aure dashi.

  Kuka take sosai tamkar ranta zai fita daga jikin ta, a Yanxu ji take mutuwar ta yafi mata Rayuwar ta, ta tsani rayuwar ta, ta Kuma tsani *MAHAIFIN TA DA GOGGO TARE KUMA DA MAMA* acewar ta sune sanadin wannan Aure da zatayi na Rashin Gata.




Tirkashi wannan shi ake Kira, Tashin hankali wacce ba'a samata rana, koya zata kasance gadai Nasreen ana Shirin d'aurin Auren ta da jungud'o.

   Ga kuma Khabeer da Sadiq suna nufo wannan K'auye.



Kudai kuci gaba da biyo

 *Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻

 

Domin jin yanda zata kasance.




    *Share*

       *And*

   *Comment*



  *Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻




       *(Ummu Nasmah)*




     *(Ummu Nasmah)*[12/25/2019, 9:15 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



    *Sadaukarwa*


Gareku kungiyar KAINUWA WRITERS ASSOCIATION, Kainuwa dashen Allah ba dashen mutum ba mak'iyan ki fadawan ki, k'ungiya mai had'in kai.




*P*••••••5️⃣2️⃣ to 5️⃣3️⃣

 

Dafa kafad'ar Nasreen INDO tayi cikin tausayin halin da take ciki tace.


  " Ki daina kukan Nan haka Nasreen, zaki cutar da kanki, Babu makawa wannan Auren sai anyi shi, to meye Amfanin kukan naki, dan Allah ki daina.


  Ai kuwa kamar wacce Indo ta k'ara tunzura Nasreen, ta k'ara sautin kukan nata, cikin kukan ne tace.


  " Kuka ya Zama Dole a gareni Indo, ko banyi kuka dan takaicin Auren Jungud'o ba, zanyi kuka domin Bak'in cikin da aka k'ulla min na kaini gidan miji da kayan d'akin mahaifiya ta, meyafi wannan bak'in ciki Indo? Ki fad'a min idan banyi kuka ba, me zanyi banda gata a duniya banda mai bin kaduma, ki duba fah kiga Indo, duk cikin dangin mu, aka rasa mai hana Baba kaini gidan miji da kayan d'akin Ammi na, cikin matsanacin kuka ta k'arasa maganar.


  Tashi Indo tayi itama cikin hawaye, tace bari naje wajen *NAYI NA* na manta tace naxo na karb'a Miki sako.


  Nasreen bata tanka Indo ba har indon ta fice daga d'akin.



  Inna Asabe ce yar AMMI take ta faman Rarrashin Nasreen, amma ita Nasreen kamar k'ara zugata suke.



MAMA kuwa yau Zuciyar ta fari tas take jin sa, ko banxa tasan Nasreen gidan wahala zataje koda masifar mahaifiyar jungud'o aka barta ya isheta, bare kuma shi jungud'o tantirin d'an Iska kuma mashayin giya.

Itama yar gwal ba'a barta a baya ba, wajen, jin dad'in abunda ya samu Nasreen, sosai take yiwa Nasreen habaici da isgilanci, ita dai Nasreen saidai ta d'aga ido ta kalle ta, ta sunkuyar.


  *JUNGUD'O* kuwa baki yak'i rufuwa, yau Ansha wankan manyan kaya harda, gare, an kifa Hula Zanna bukar, biyu kawai yake jira ta cika su nufi masallaci wajen d'aurin Auren shida abokansa.



  Karfe d'aya saura Khabeer da Sadiq suka iso cikin k'auyen, darect k'ofar gidan su Nasreen Khabeer suka nufa, yara Khabeer ya hango suna wasa k'ofar gidan yayin da mutane ke shige da fice cikin gidan, kallon Sadiq Khabeer Yayi yace.


 " Ya za'ayi muga yarinyar nan ne kam, naga ma kamar ma biki suke Cikin gidan.


  Kallon Khabeer d'in shima Khabeer yayi yace.


  " Ka aika yaran nan mana suyi ma kiran ta, kawai tunda ita ba baya gare ta ba bare a kirata.


  Juyawa Khabeer yayi da niyan kiran yarinya d'aya a wajen ta musu kiran Nasreen, sai kawai suka had'a Ido da INDO tana k'ok'arin shiga cikin gidan.


  Dariya INDO tayi tare da nufo Khabeer cikin jin dad'in ganin sa, sanda taxo daf da motar nasu ta tsaya tare da cewa.


  " Kwad'o Kaine a garin namu yau, Lale marhaban.


  "Murmushi Khabeer Yayi yace.


  " Nice Indo, yau ba kiwo kenan, nagan ki ke d'aya ba tare da shanun ba.


  " Eh wlh kwad'o ana bikin k'awata ce, Yau.


  " Ayya kice yau Amare kuke, daman kuwa Kinga ina neman wanda zai min sallama da Nasreen d'in gidan nan sai kuma gaki Allah ya kawo ki, ko zaki min kiran ta.


  Cikin mamaki Indo tace


  " Wacce Nasreen d'in, ai itace ake Auren ta yau.


  What Khabeer ya ambata da k'arfi, " kina so kice an d'aura Auren Nasreen yau.


  " A'a ba'a d'aura ba sai k'arfe biyu za'a d'aura, kuma Abun haushin ma, bata son Auren, Auren dole zasu Mata.


  " Auren Dole kuma cewar SADIQ, Akan me za'a mata Auren dole?


  " Akan son Ra'ayin Iyayen ta, ita bama Auren Dolen bane, damuwar ta, wanda za'a Aura matan ne, d'an giya.


  Tsawa Khabeer ya dakawa Indo sai da ta tsorata yace


  " Kinsan me kike Fad'i kuwa, su iyayen nata mahaukata ne da zasu Aura mata d'an giya, haba ki dinga fad'in Abunda hankali zai d'auka Mana.


  Kallon Khabeer tayi cikin jin haushin tsawar da Khabeer ya Mata tace.


  " To kwad'o k'arya zan maka, tana fad'in haka ta juya da niyar barin wajen cikin fushi.


  Da sauri Khabeer ya dakatar da ita domin kuwa shi ya fahimci Gaskiya Indo ke fad'i,


" Yi hkr y'an mata dan Allah ki tsaya.


 Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba.


  Kallon Khabeer SADIQ yayi tare da banka masa harara yace.


  " Sai ka samu damar fitowa ai Uban y'an zafin Zuciya wanda baka cin ribar Zance.

  Fitowa sukayi tare suka bar junior a cikin motar yana shan baccin sa.


  Fiskantar indo SADIQ yayi tare da cewa.


  " Baiwar Allah dan Allah gaya mana meke faruwa da yarinyar nan ne, wani irin Hali ne da ita marar kyau da za'a dauke ta a bawa d'an giya Auren ta.


  " Bata da wani mungun Hali ko kad'an sai ma makircin kishiyar mahaifiyar ta wacce itace sanadiyar wannan Auren da Kakar ta, Saboda tsabagen Rashin k'aunar da suke Mata, sunyi wannan abunne dan ganin sun lalata Rayuwar Nasreen, na Rasa me Nasreen ta tsare musu ita da mahaifiyar ta, tsanar da suke Mata Yayi yawa, cikin kuka Indo ta k'arasa zance.


  K'wafa Khabeer Yayi yace tabbas biri yayi Kama da mutum, Nasan wannan mafarkin da nayi dama dole akwai abunda ke faruwa.

  Ko kafin SADIQ yayi magana Khabeer ya rigasa ta hanyar cewa, 


 " A ina zan Samu shi MIJIN da za'a AURA matan.


  Shuru Indo tayi, sannan tace 


  "baxai wuce yana gidan su ba.


  " Ko zaki iya kaimu gidan nasu Khabeer ya tambaya Indo.


   " Me zaku masa idan na kaiku d'an mai gari ne fah.


  Murmushi Khabeer Yayi yace.


  " Babu abunda zamu masa kedai ki Mana rakiya.


  " Shikenan muje Amma da k'afa zamuje mu.


  "Ba damuwa muje da k'afar cewar SADIQ.


  Security Khabeer yasa a motar yabar junior a ciki suka d'auki hanyar gidan mai gari.


  Isar su k'ofar gidan sun

Tarar da k'ofar gidan mai garin cike da mutane sai kad'e kad'e da raye raye ake, tsayawa sukayi a gefe yayin da ita Kuma INDO ta kutsa kanta zuwa cikin gidan, da k'yar da taimakon Buba k'anin jungud'o Indo ta sami ganin jungud'o, bayanin yana da baki a waje ta masa, duk da yad'an yi mamakin su waye suka zo neman sa, bayan shi yasan baida wasu bak'i da zasu zo neman sa, binta yayi suka fito k'ofar gidan da Indo.

  Har inda su khabeer suke tsaye Indo takai jungud'o sannan ne tace.


 " To kwad'o ga jungud'o ni zan koma gida kar a neme ni.


  Murmushi Khabeer yayiwa Indo tare da ciro kud'i a aljihun sa, dubu biyar ya bawa Indo.


  K'in karb'a Indo tayi, acewar ta bata buk'atar su, Khabeer yayi yayi da indo ta karb'i kud'in Amma tak'i, haka sai hakura Khabeer yayi ya kyale ta tare da Mata godiya.

  Har ta fara tafiya Khabeer ya tsayar da ita ta hanyar ce mata,


 " kar tacewa Nasreen sunxo k'auyen nan.


  Amsawa tayi da to sannan ta shige.


  Kallon Sama da k'asa Khabeer ya k'arewa jungud'o tare dayin tir da Allah wadaran wad'anda suka had'a wannan Auren idan ba Rashin hankali da kuma cuta ba, ina Nasreen ina Auren wannan d'an iskan k'auyen.


  Hanu jungud'o ya mik'o musu suyi musabaha, SADIQ ne ya mik'a masa hanun, Amma shikam Khabeer, nad'e Hanun sa yayi cikin Aljihun sa yak'i basa, yana Ganin hararar da Sadiq ke aika masa ya kawar da kansa gefe, kansa na kallon gefen ne ya fara magana cikin nutsuwa, tare da gadara.


  " Kaine jungud'o Koh? Ya jefa masa tambaya.


  " Eh nine cewar jungud'o cikin tunanin waye wad'annan d'in.


  " Kasan da cewa Wacce zaka Aura bata sonka, Koh?


  Cikin k'osawa da maganar sa, jungud'o yace.


  " Na sani sai Akayi Yaya, iyayen tane suka gaji da ita, suka kawo min tallen ta da kansu kaga kuwa, bani ne nasa aka mata Auren dole ba, wannan iyayen ta ya kamata ka koma ka tuhuma.


  Murmushi Khabeer Yayi har saida fararen hak'oran sa suka bayyana, cikin yabawa izza irin ta jungud'o.

SADIQ ne zaiyi magana Khabeer ya d'aga masa Hanu, yace.


  " So nake ka fasa Auren ta, ka maida Auren kan yar uwar ta, mema take da suna 🤔 yawwa yar gwal take ko yar zinare, koma menene sunan ta ban damu ba, nidai kawai buk'ata ta ka fasa Auren Nasreen ka Aure ta, idan har ka min haka zan baka millions 5 idan kuma kak'i Amsa buk'ata ta, zakayi *biyu babu*  zaka rasa Nasreen tare kuma da rayuwar ka, tare da ciro bindiga ta gefe yanda mutane baxasu gani ba ya nuna Masa *Dan haka zab'i ya rage Naka*,  Ka zab'i *Rayuwa ko mutuwa*.


  Jungud'o da tun Sanda Khabeer ya nuna masa bindiga ya fara rawar d'ari tare da k'ara ja da baya, cikin in iyna na yace.


  Nafi k'aunar rayuwa ta fiye da Nasreen, na yadda na zab'i Rayuwa ta, sai dai buk'atar ka na na Auri yar gwal baxai yiwu ba har sai ka Bani kud'in Hanu da Hanu, Niko na maka Alk'awarin Auren yar gwal a yau d'in nan.


 Dariya SADIQ yayi cikin Jin dad'in yanda basu wani sha wahalan samo kan jungud'o ba, tare da d'agawa Abokin nasa yatsa alamun jin jina👍🏻.


Murmushi Khabeer Yayi tare da cewa muje mu baka da matsalar kud'i, sai dai ina k'ara tabbatar maka cewa, sab'awa umarni na, dai dai yake da Rasa Rayuwar ka.


  " Na yadda muje cewar jungud'o.


  Jerawa sukayi da jungud'o har k'ofar gidan su Nasreen inda sukayi parking d'in motar tasu, wata k'aramar jaka Khabeer ya bud'e motar ya ciro, tare da kallon junior da har yanxu baccin sa yake bai farka ba, bud'e jakar yayi sai ga rafas rafas na dubu dubu, mik'awa jungud'o yayi yace, 4 millions a nan, zan cikata maka sauran kud'in daga baya, ko kuma mu juya dakai, cikin gari na cire kud'i a Bank na baka, kaga yanxu bamu da times muje Koh saura 1 hours ne, a shiga sallah ya kamata kaje kasan yanda zaka wargaza wannan Auren.


  Juyawa jungud'o yayi tare da cewa yanxu ma kuwa.


 Bayan tafiyan jungud'o ne Khabeer ya jin gina kansa jikin motar sa tare da sauk'e ajiyar zuciya, a fili yace.


  " Alhamdulillah na taimaki Rayuwar y'ar ki mamy, domin kuwa bana son ki dawo k'auyen nan cikin bak'in Ciki, har Uku, na rashin Nuruddeen da Kuma b'atar y'arki.


  Muryar SADIQ yaji yana cewa, 


  "baka gama taimakon ta ba Khabeer muddun ka tafi ka barta a haka, to tabbas ka kara jefa cikin wani tashin hankali da masifar ne.


 Kallon SADIQ Khabeer Yayi yace


  " ban gane me kake nufi ba? Kamin magana yanda zan gane.


  Ajiyar zuciya shima SADIQ yayi tare da cewa.


  " Ka raba Nasreen da Auren Jungud'o, sannan Kuma ka had'a y'ar Uwar ta da Auren shi, baka tunanin Idan har ka tafi ka barta cikin wannan K'auye, bazasu k'ara neman wani wanda ma yafi jungud'o munanan halayya su had'a ta dashi Aure ba.

  

  Shuru Khabeer yayi zuwa can yace.


  " Tabbas maganar ka zata iya kasancewa Gaskiya, domin kuwa, a d'an zaman da nayi dasu na kwana biyu na fahimci irin k'iyayyar da wannan Matar take yiwa yarinyar nan, shiyasa ma yanxu na mata *k'aik'ayi koma kan mashek'iya*.

  Menene solution yanxu SADIQ?


  " Solution d'aya ne kawai Khabeer, shine kafin mubar K'auyen nan, a d'aura maka Aure da yarinyar nan.


  Kallon baka da hankali Khabeer Yayi SADIQ, sannan yace.


  " Kasan me kake cewa kuwa, ko ka manta da cewa ina da Mata ne, sannan Kuma Babu niyar mata biyu cikin Rayuwata, na tsara Rayuwata ne da mace d'aya kawai.

  Kai mai zai hana kayi wannan taimakon tunda kaga kai baka da Mata single kake, sai mu sami ladan tare.





*************************


Tun fitar Khabeer Zuhura ke Hauka ita d'aya cikin gidan, kuka take tana surutu ita d'aya.


  " Wlh baxaka tab'a K'ara Aure ba, domin kuwa ni kad'ai ce matar ka danni kad'ai aka Halicce ka, Babu wacce ta isa shigowa cikin gida na, muyi sharing d'in miji da ita ba, wallahi bazai yiwu ba, ina sonka Khabeer bana son ko wacce Mace ta rab'eka koda kuwa Y'AR UWAR KA ce ta jini.

 Khabeer Idan har kace zaka *K'ara Aure sai na kashe duk wacce ka Auro*


  Zuhura fah yau ta haukace Akan kishi domin kuwa, gabaki d'aya ta hargitsa kayan d'akin ta, harta zanin gadon ta bai tsira ba, shima sai da ta yaye shi ta wurgar gefe.




  Sorry sister's wlh yau ina busy ne, shiyasa na muku typing kad'an, kuyi hkr dashi Babu yawa.




*Share*

    *And*

*Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻



     *(Ummu Nasmah)*

[12/29/2019, 1:47 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


  *Sadaukarwa*


Na sadaukar da wannan page d'in gare ku.


*Amina Abubakar*

    *And*

*Mu'az*


Wannan page d'in naku ne kuyi yadda kuke so dashi, domin kuwa Gaskiya ina Jin dad'in yanda kuke min shares na book D'ina, Allah ya bar k'auna na gode sosai.



P••••••••5️⃣4️⃣ to 5️⃣5️⃣


 " Ni ina da wacce nake so, Kuma ka ganta yau a cikin gidan mu, duk da ban sanar da ita soyayya ta ba har yanxu, amma ina da tabbacin zata Soni, please Abokina duk da bansan yarinyar nan Nasreen ba, Amma na fahimci Halin k'uncin rayuwa da take ciki, ka taimaki Rayuwar ta Khabeer.


 Wani Irin kallo mai wuyar fassarawa Khabeer ke yiwa SADIQ, kafin cikin Halin ko inkula yake cewa.


  " Idan shikenan abunda zaka fad'a  kana iya shiga mota mu tafi Koh.


  SADIQ dai bai daddara ba, yaci gaba da cewa.


  " Khabeer kayi tunani kafin mubar Nan, kar kaxo kana danasani daga baya, a lokacin Kuma time's ya k'ure maka.


  " Na gaji dajin wad'annan tatsuniyar taka, SADIQ, gani nayi kaima fah a Yanxu kana da Halin da zaka Auri Mata sama da Hud'u ma idan anayi, ka Aure su mana dukan su, dole sai ni zaka tursasa Nayi abunda banyi niyya ba, ko kuma zanyi Aure ba tare da sanin iyaye na bane, please SADIQ na rok'eka ka shiga mota mu tafi.


  SADIQ bai k'ara cewa komai ba ya shiga motar Khabeer yaja suka bar k'ofar gidan su Nasreen.


  Ita kuwa Mama Y'AR GWAL ta kira gefe tare da bata kud'i dubu Arba'in tace.


  " Ki rik'e su da kyau, ki kaiwa Malam kice masa iya Abunda ya samu kenan, ya baki sak'on ki kawo min, saura kuma Idan ya baki, shima ki fasa, kiga yanda zanyi dake a cikin gidan nan.


  Karb'a y'ar gwal tayi, tana tura baki tare da k'unk'uni, ta fita.


  " Sai yanxu kika dawo ne INDO, naga kin juma.


  " Ehh wlh Nasreen, Nayi ce ta aikeni, shiyasa na juma, sak'on naki ma tace sai ta shigo anjuma.


 " Ayya Babu damuwa, bari na zaga bayan gida,



 Jungud'o kuwa ya tada bori a wajen d'aurin Aure, shifa Baya son Auren sa da Nasreen, saboda suna da Abun kunya cikin zuri'ar su, Uwar ta ta shiga duniya yawon karuwanci, haka ma y'ar Uwarta, dan haka shi da y'ar gwal yake son a d'aura musu Aure.


  Mari mai gari ya d'auke jungud'o dashi, tare da cewa.


  " Baka isa ba wlh, baxaka mai Dani tsohon banxa ba, wani Irin rashin hankali ne wannan, za'a d'aura maka Aure da yarinya ka dawo kace baka sonta Y'AR UWAR TA kake so, ba zai yiwu ba to.


  Baba ne yace Babu damuwa, ranka shi dad'e, nine mahaifin Nasreen da Amina, dan haka na amince a d'aurawa Jungud'o Aure da AMINA.



  Har gitsewa gidan yayi da hayaniya, kowa yana mamakin Baba, wannan wani Irin Uba ne, yak'i y'ar ka, kuma ka basa wata Y'ar taka.


  Shiko Baba ba komai yasa yayi hakan ba, sai dan ya nunawa Mama kuskuren ta, saboda yana sane tsaf da itace ta had'a Auren Nasreen da jungud'o, ta hanyar tunzura Goggo, baya k'aunar Auren Nasreen da jungud'o, Babu yanda ya iya ne, yasa ya amince, yasan Halin Goggo zata iya daina magana dashi kan wannan Auren, kuma fushin Uwa akan d'anta masifa ce babba.


 Mai gari ne yace


 "  Mlm Musa kasan Abunda kake cewa kuwa.


 " Na sani ranka ya dad'e, a d'aura Auren kawai.


 " Shikenan tunda Kaine kace haka da kanka.


 Sun kusa ficewa daga cikin Rugar wani tunani yaxo zuciyar Khabeer.


 " Karfa nabar garin nan, su d'aura Mata Aure da wani Irin jungud'o, ya Mamy zataji a zuciyar ta idan ta dawo ta samu, duka rayuwar yaranta ya lalace, ya kamata koda Nasreen d'in ce ta tsira, ciwon zaizo Mata da sauk'i fiye da ace duka Babu Ingantacciyar Rayuwa.


  Reba's yayi tare da juyawa cikin Rugar da bala'in gudu yana cewa SADIQ zanje na taimaki Rayuwar ta, kodan Saboda mutuncin mahaifiyar ta, da kuma k'aunar da take yiwa d'ana junior, sai ina son ka zama shaidata, bawai zan Auri Nasreen da niyar zama da ita na har Abada bane, zan Aure tane domin na inganta mata Rayuwar ta, ta hanyar fitar da ita cikin gari, tare da bata ilimin da zata dogara da Rayuwar ta, ina mata wad'annan abubuwa zan sauwak'e mata,  taje ta nemi miji tayi Auren ta.


  Murmushi SADIQ yayi, cikin jin dad'in zancen Khabeer yace hakan ma Yayi, Amma muyi sauri mu k'arasa karsu watse daga wajen d'aurin Auren.


  Cikin 15 minute suka k'arasa masallacin Juma'a na Rugar, sun Samu har an d'aura Auren Jungud'o da y'ar gwal ana raba goro, k'arasawa sukayi wajen, tare da mik'a musu Hanu, mlm Iro da Mlm Musa sunyi mamakin ganin Khabeer a wannan lokaci, bayan sun gaisa ne, Khabeer ke cewa mlm Musa, yanxu shigowar su garin, sake jin abunda ke faruwa na fasa Auren Nasreen da Jungud'o yayi, Gaskiya Baba banji dad'in Abunda ya faru ba, shine na yanke shawarar cewa Zan Auri Nasreen Idan har ka amince mini.


  Kallon kallo aka hau yi a wajen tare da sauraron Amsar da Mlm Musa zai bawa Khabeer.


Yayin da jungud'o kuma ya sake baki yana kallon Khabeer, 

 "wato so yake ya Aure ta, shine yasa zai had'ani da kud'i da bindiga, yace na fasa Auren Nasreen, Allah ya isa to tsakanina da kai.


  Nisawa Baba yayi tare da cewa.


  " Khabiru ka tab'a ganin inda aka d'aura Aure ba tare da sanin iyaye ba, kaje ka nemo yardar iyayen ka, ka dawo ni kuma zan baka Auren Nasreen.


  SADIQ ne ya nisa tare da cewa.


  " Mahaifin Khabeer ya Amince Mana, asali ma bamu xomu nan ba saida muka nemi yardar sa, yace mucewa mlm Iro ya karb'awa Khabeer Auren idan har ka yadda zaka had'a zuri'a dashi.


  Saurin kallon SADIQ Khabeer yayi, Jin k'aryar daya tsula take ko tsoro baya ji.


  Washe Baki shi kuma mlm Iro yayi jin ance Uban gidan sa yace ya karb'a masa Auren d'ansa.

  " An gama ai mlm Musa tabbas y'arka ta Samu miji na gari da kuma surukai na gari muddun ka bawa khabiru Auren y'arka.


 Mai gari ne yace.

" Kunsa wad'annan d'in ne da suke maganar a basu Aure.


 " Mun sansu Ranka shi dad'e, nuna Khabeer yayi yace, a gidan mahaifin sa nake Aiki, shi kuma mlm Musa, shi yake kiwon shanun mahaifiyar sa.


  " Alhamdulillah cewar mai gari, Mlm Musa shawarin da zan baka itace ka d'auki yarinyar nan ka basa, kaga dai cikin garin nan zaiyi wuya ta samu mai Auren ta, kasancewar Abun kunya da Uwarta da y'ar Uwarta suka bar Mata.


  " Babu damuwa mlm Musa yace, na yadda a d'aura Auren Allah yasa hakan shine Alkairin ta.


  SADIQ ne ya ciro kud'i dubu d'ari ya dank'awa mlm Iro sadakin Nasreen, amsa mlm Iro Yayi shima ya dank'awa mlm Musa, k'in karb'a mlm Musa yayi yace, a rage kud'in sunyi yawa.

 

  SADIQ ne yace,

" A'a Baba karka damu, sadaki baya yawa, mudai buk'atar mu, Allah ya sanyawa Auren Albarka.


 Babu yanda mlm Musa ya iya haka ya k'arbi sadakin inda aka d'aura *AUREN  MUHAMMAD KHABEER ISAH BABA DA NASREEN MUSA TUKUR AKAN SADAKI NAIRA DUBU D'ARI*.


 Inda mutanen gari suka watse suna gulmar cewa mlm Musa ya sayar da y'arsa domin kuwa babu wacce aka tab'a bada sadakin ta sama da dubu 15 a K'auyen sai Nasreen mai dubu dari.



  Da gudu shehu mak'ocin su MAMA ya shiga cikin gidan yana k'walawa  MAMA kira.


  Da sauri MAMA ta fito daga cikin d'akin ta, tana cewa.


  " Lafiya Shehu har an d'aura Auren Nasreen d'in ne.


  Tab'e bakin sa Shehu yayi cikin gulma da tsegumi yake cewa Mama.


  " Cewa zakiyi har an d'aura Auren nasu ne, ai Aure biyu aka d'aura, k'asa yayi da muryar sa yace, Mama Salame, ashe daman Auren nan cutar ki za'ayi to bari kiji, Nasreen ba jungud'o ta Aura ba, wani Attajiri d'an Binni, kinma sanshi wanda yaxo kwanakin nan.


  " Ehhh na ganesa k'arasa min zancen da sauri.


 " To shi Nasreen ta AURA ba jungud'o ba, sadakin ta ma dubu d'ari ne, sai kuma aka Aurawa y'ar gwal jungud'o.


" Kasan me kake cewa kuwa, kaga bana Irin wannan wasan da kai meye had'in y'ar gwal kuma da Dan giya, ai sai dai Nasreen d'in marar Gata.


 " Wallahi da gaske nake Mama Salame, wlh y'ar gwal ce ta Auri jungud'o Nasreen ce ta Auri wannan d'an Binnin.



 *DAM !! DAM !! DAM DAM !! DAM* kike jin k'irjin Mama ya bugae, dafe k'irjin tayi tare da yanke jiki ta fad'i.



*************************


MOMY SARAH da Hajiya Hindatu, suna zaune waje d'aya cikin cell d'in, duk wanda yasan Momy Sarah da, ya ganta Yanxu baxai gane ta ba tayi bak'i ta rame,  duk ta fata hayyacin ta, a Yanxu Momy Sarah ta fara Nadamar abunda ta Aikata tun kafin ma a yanke mata hukunci, tana kuma shirye da ta fad'awa Khabeer gaskiyar inda John yake, ko a Mafarki bata tab'a tsammanin cewa Asirin ta zai tonu ba, duk da ta kawana biyu bata ga Khabeer ba, Amma tana shirye a duk lokacin da yaxo ta bashi good information Akan k'ungiyar su.


  A yau daddy ya kawo mata ziyara cell d'in, inda aka fiddota domin su gana.


  Sunkuyar da kanta k'asa Momy Sarah tayi domin kuwa tana kunyar hada Ido da Daddy, bata da Idon da zata kalle sa dashi, kanta a sunkuye ta gaishe da Daddy.


  Amsawa Daddy yayi tare da ce Mata.


  " Saratu dubi yanda kika maida Rayuwar ki Abun tausayi, da gatan ki da mutuncin ki, duk kika manta dasu kika ta Aikata b'arna, a yau an wayi gari Saratu kin zubar da mutuncin ki dana yaran ki, gashi Sanadin wannan Abun kunya da kikayi, Kinsa Khalid yabar garin nan, ya wurgar da matar sa da ciki ya tafi yabar ta, duk ta dalilin ki, yaran ki mata kullum suna cikin k'unci, ina zaki kai wannan zunubin Saratu.


  Shuru Momy Sarah tayi ba tare da tacewa Daddy komai ba, har time d'in da aka basu ya cika, Momy Sarah taki tankawa Daddy bayan gaisuwar da ta shiga tsakanin su.


 Sai da daddy ya tafi ne Momy Sarah ta fashe da wani Irin kuka mai cin rai, a Yanxu ta tsani kanta, ta tsani HAJIYA BARA'ATU domin kuwa duk itace tasa ta cikin wannan mummunan Halin da take ci, sai yanxu ta yarda da sharrin k'awa da kuma Zuciya duk sune suka sata wannan Halin da take ciki a Yanxu. " Kaicona ni Saratu na cuci rayuwata, gashi yanxu inda son Abun duniya da son zuciya ya kaini.


 Momma da Mamy kuwa zama suke na lafiya da Amana, komai tare sukeyi hatta ga girki.


Suna zaune a falo ne momma take cewa Mamy ya kamata ta bata labarin Rayuwar ta, tunda an zama daya ai yanxu.


  Murmushi Mamy tayi tare da cewa yanxu kuwa.


  Daddy dake shigawa ne yace. 


  " Kuce nayi sa'ar shigowa da wuri da ansha labari banda ni.


 Dariya sukayi dukan su, sannan Mamy ta fara cewa.





Nan zan dakata sai kuma gobe, saboda ina busy, kuyi hkr idan kun sami, kuskure cikin Rubutun yau Saboda banyi editing ba Gaskiya.




*Share*

   *And*

*Comment*



*Alk'alamin Rasheedat Usman✍🏻*



  *(Ummu Nasmah)*

[1/1, 12:39 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


 Deducated to


All fan's of SARA DA SASSAKA baya hana gamji toho.


  Ina sonku kamar yanda kuke Sona.


  Sannan ina neman Addu'ar ku, zan fara Exam Ranar Alhamis.




P•••••••5️⃣6️⃣ to 5️⃣7️⃣


 " Suna na Maimuna, ni y'ar Asalin cikin garin Dukku ne, a wata K'aramar Rugar fulani, wacce ake kira da Rugar Buba, mahaifina Mlm Nura yana da matar sa d'aya mai suna Aishatu, Mutanen gari na kiran ta da Sogiji amma mu muna ce Mata Innah, yaranta Uku ne kacal a duniya, Sani shine babba muna kiran sa da suna Bandirawo, sai Zainabu Wacce muke kira da Yaya Asabe, tayi Aure harda yaran ta Hud'u, sannan ni Auta cuna cemin, Bod'd'o, na taso cikin gata da kulawar iyayena da y'an Uwana, tsabar soyayyar da suke min yasa mahaifina da Bandirawo, sanda na cika shekara 12 a duniya, suke tafiya dani wajen kiwon shanun su acewar su basa son suyi nisa dani, kasancewar mahaifina makiyayi ne, niko nakan jin dad'in tafiya dasu kiwon, domin suna kula dani fiye da yanda ya dace, sab'anin mahaifiya ta, da bata min Abunda suke min acewar ta zan sangarce, shiyasa bana yadda na zauna kusa da Innah indai Baffa na yana nan.


  Wata Rana a can wajen kiwon namu, na gamu da wani matashin saurayi mai suna Musa, d'an gefen Rugar mu, ana Kiran Rugar tasu da Rugar Ard'o B'oyi, da farko da wasa muka Fara dashi yakan yawan zolaya ta, a haka sabo mai tsanani ya shiga tsakanin mu, har soyayya ta fad'a Mana, wata Irin soyyayah muke, mai Tsananin Gaske, wacce muke jin baxamu iya Rayuwa ba, idan Babu d'aya, Amma duk soyyayar da muke bamu tab'a yadda iyayen mu sun Sani, muna soyyayar mune a b'oye, kwatsan Rana tsaka sai Baffah ya gane akwai soyyayah tsakanin mu, Hakan ce ta sashi kiran Musa ya ajiye sa, tare da tambayan sa gaskiyar abunda ke tsakanin mu, Musa bai b'oyewa Baffah komai ba, yayin da Baffah yaji dad'in jin zancen Musa, ya Kuma yi masa na'am akan yaje ya turo mahaifin sa idan da Gaske yana sona.

  Sai a Ranar nake jin cewa Musa yana da Mata, Amma baida yara ko d'aya, kasancewar Allah baya bar masa yaran ana Haifan su suke komawa.

 Duk da jin da nayi Musa Yana da mata, hakan baisa naji wani Abun a Raina ba, kuma na shiryawa Auren sa, koda kuwa matan sa Uku ni zanje ta Hud'u.

  Dangina dana Musa sunyi na'am da Auren mu, sai labarin matar sa, da mukaji tace, badai na shigo gidan ba, sai dai idan mutuwa tayi.


 Nida iyayena hakan sam bai d'aga mana hankali ba, acewar mu, haukar kishi ke damun ta, mahaifiya ta kullum cikin fad'a da nasiha take min da kuma yanda zan zauna da kishiya, alhamdulillah kuma ina d'aukar duk abunda ta fad'a min kamar hadda.


 Wata Rana ana saura sati bikin mu, Musa yaxo Rugar mu, naga rigar sa, kamar Alamun manja, naso nayi shuru ban tambaye sa, ba, sai na kasa hkr, har saida na tambaye sa.

  Bud'ar bakin Musa cemin yayi Uwar gidan kine, ta watsa min manja jikin kayana wai dan kar naxo Hira.

  Zaro ido waje Nayi tare da cewa " Daman da gaske ne Abunda ake fad'a Akan Matar ka.


 Kallo na Musa Yayi tare da cewa, Kinga Maimuna mubar zancen nan, kinsan fah mutan gari da gulma tare da yad'a k'arya, kawai mubar zancen nan.

  Shuru nayi ba tare da na k'ara d'ago masa zancen ba har ya koma.


  Bana mantawa A Ranar Alhamis ana gobe za'a d'aura Aure na, a ranar kwana nayi banyi bacci ba, ina mugayen mafarkai, kasancewar Allah Yayi mai yawan ibada, hakan yasa na d'an samu sassauci, Amma fah na kwana cikin wahala, tun daga Ranar na dage da Addu'a,  Azkar safiya da maraice baya wuce ni,.


  Washe gari Juma'a aka d'aura Aure na, da Musa, iyayena sun min fad'a sosai kafin a kaini d'akin mijina.

  Bayan an kaini ne, da yamma lis, goggo Addaji k'anwar mahaifiya ta, da Yaya Asabe suka d'auke ni zuwa d'akin Uwar gida domin kai Amanata, tun daga kallon da Uwar gidan Musa ta Mana, Wacce suke Kira da mama Salame, zaki san Babu mutunci gunta, Amma hakan bai kashewa yan uwana gwiwwa ba, goggo Addaji ne ta fara magana.


  " To Uwar gida, ganan k'anwa na kawo miki Amanar ta,. Da fatan zaki Amshe ta, Hanu biyu, idan tayi ba daidai ba, a gyara Mata, ita kuma Maimuna, baxata sab'a miki ba insha Allah.


  Tabe bakin ta, Mama Salame tayi cikin isa da iko take magana.


  " Ban d'auki wannan Amanar ba, ina son ku tashi ku fice min daga d'aki tunda babu kud'in wani tsoho cikin ginin d'akin nan, kin Aure min Miji sannan kuxo kuce ga Amana an kawo min, ai Babu Amana tsakanina da kishiya.


  Tashi Goggo Addaji tayi tana Allah wadarai da Halin Mama Salame, muka bar d'akin ta Zuwa nawa d'akin.


  Sanda su Goggo Addaji zasu tafi nasiha suka min sosai tare da cewa na rik'e Azkar domin kuwa wannan Uwar gidan nawa Babu Imani cikin lamarin ta.

  Godiya na musa, ina kuka suka fice suka barni.


  Da farko zamana a gidan mlm Musa, MAMA Salame bata, shiga lamarina, ganin da tayi ina mata biyayya yanda ya dace, hatta ga girki, nice meyi har Ranar girkin ta, Mlm Musa yana jin dad'in yanda nake wa Salame biyayya, A idona Salame ta haifi yara wajen Uku Babu rai, kasancewar ni ban samu haihuwa da wuri ba, kwatsan rana tsaka sai Allah ya bani Ciki, wohoho kuxo kuga Bak'in Ciki wajen Salame, tun daga Ranar da akace ina da ciki Salame ta fara min mugunta da nemana da masifa, sai dai ban tab'a nuna mata ya dameni ba, kuma bawai bana jin zafin Abunda take min bane, ina ji hakuri ne kawai nake da Salame duk dan a zauna lfy, tsabar wahalan da Salame take bani shine yasa ciki na zubewa, Salame taji dad'in hakan sosai, tun daga yanayin ta zaki gane farin cikin da take ciki baya misaltuwa, Niko Nayi hkr na rungumi k'addara, wata takwas da zubewar ciki na, sai Kuma Allah ya K'ara bani wani cikin, wanda shi Kuma duk muguntar Salame baisa ya zube ba, hakan ne yasa Salame, fara shiga malamai dan Azabar da cikin a cewar ta, ita bata haihu ba nima baxan haihu ba,  tasha barbad'a min magani cikin Abinci, zan kuma yi Bismillah tare da Addu'a naci, duk yanda Salame zatayi cikina ya zube tayi amma yaki zubuwa, hakan yasa Salame, fara zagina da gaya min bak'ar magana, bana kulata, watan Ciki na tare da kwana goma na haihu, inda na samu yarinya mace, Salame Ranar Hauka ce kawai batayi tsabar Bak'in ciki, dan ko ruwa ma k'in daura min tayi, sai da Mahaifiyar mlm Musa Goggo taxo ta d'aura min, kasancewar goggo tana sona fiye da Salame, Ranar Suna y'ata taci suna Nasreen, tun Nasreen bata san kanta ba Salame take mata mugunta, har duka tana mata, amma ban tab'a nuna mata ina jin haushin Abunda take yiwa Nasreen ba, shekarar Nasreen d'aya ita ma Salame Allah ya bata Ciki, murna wajen Salame ba'a magana.

  Nasreen nada shekara d'aya da wata tara Salame ta haifi y'arta mace itama, aka rad'a mata Suna Amina inda Salame take kiran ta da y'ar gwal, sosai Salame take nunawa Y'ar Gwal soyayya, ko kusa da y'ar gwal Nasreen taxo Salame sai ta maketa, ta ta hantarar ta, muna cikin wannan Halin ne Allah ya K'ara bani Ciki, kuxo kuga murna wajen mlm musa, a cewar sa Allah ya Azurta shi da zuri'a, a wannan karon Salame, har guba ta samin a cikin Abinci, Allah ya kiyaye banci ba.


  Salame fah ta rasa Yaya zatayi dani cikin gidan mlm musa, duk wani muguntar ta, baya tasiri a kaina, haka Kuma asirin ta baya cina, na K'ara haihuwar y'ata Mace, taci suna Nabiya, Nabiya tun tana zama na fara gane tana da fad'a, Sanda Nabiya tayi shekara, Uku a duniya Salame ko hararar ta tayi saita rama, duk fad'an da dukan da Salame zata mata sai tace mata Allah ya isa, Amma duk Salame tafi tsanar Nasreen na rasa me Nasreen taci Mata a duniya ana haka fa na K'ara Samun Ciki, Ranar cikin dare Salame ta kama ni da kokuwa tana k'ok'arin dukan  Ciki na, Mlm Musa ne ya kwace ni da k'yar Hanun ta, a Ranar kuwa ya yiwa Salame Saki d'aya, Har na haifi d'ana Nuruddeen mai sunan mahaifina, mlm Musa bai dawo da Salame ba saida Nuruddeen, yayi shekara Uku kafin mlm Musa ya yadda nan ma dakyar ya yadda ya dawo da Salame, tun dawowar Salame nake fama da ciwon kai mai Tsananin Gaske, kullum mlm Musa cikin karb'o min magani yake, wata Rana bana mantawa muna Zaune tsakar gida dukan mu har da yara, bud'ar bakin Salame sai take cewa insha Allah Maimuna kin kusa barin garin nan, yanda kikayi sanadiyar igiyar Aure na d'aya haka kema sai kin bar garin nan, d'ago Kaina Nayi na kalleta ba tare dana tanka ta ba, bayan Salame tayi wannan maganar baifi da sati d'aya ba, na shiga ban d'aki, tunda na shiga naji Kaina ya juya min daga lokacin naji bana k'aunar garin burina kawai naga nabar garin, hakan ne kuma ta kasance, na fice nabar garin mu, Amma duk abunda nake hankali nah yana jikina magana ne kawai baxan iya yiba, har had'uwa ta da Alhaji, zuwa yanxu danake baku labarin nan hankali na bai tab'a barin jiki na ba.


  Kallon momma tayi tace wannan shine labari nah.




 A nan zan dakata sai gobe zamu dawo cikin labari, masu zuwa gidan mai gari kai Aure Kuyi hakuri sai gobe kuje kuci tuwon dawar ku miyar kuka🤪




*Share*

    *And*

*Comment*



   *Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻


  *(Ummu Nasmah)*

[1/3, 10:11 AM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


 *Deducated to* 


  Amina Abubakar.


Ina yinki irin overn nan, kamar yadda yanda kike son book ɗina.



5️⃣8️⃣ To 5️⃣9️⃣


Ko kafin mamy ta gama bada Labarin tuni Hawaye na tausayin Baƙar wahalar da mamy tasha wajen Mama, ya wanke fuskar momma, kallon mamy mommo tayi, tace.


  " Lallai maimuna kinsha wahala a hanun Salame, wannan matar zaiyi wuya tayi ƙarshe mai, domin kuwa ta Aikata munanan Ayyuka a rayuwarta, kiyi hkr maimuna insha Allah zaki ci ribar hkr.


  Daddy ne ya nisa yace, 


  " Alhamdulillah mun godewa Allah, tunda gashi yanxu kin samu lafiyar jikin ki, saura kuma idan An gama case ɗin Saratu, muje garin naku tare dukan mu harda shi khabirun, Ubangiji ya ƙara miki hkr sai kuma ki dage da Azkar, bari naje na watsa Ruwa.


 Tare daddy da momma suka tashi, tayi ɗakin nasa domin haɗa masa Ruwan wankan.



  *************************


 Jijjiga Mama suke suna ƙiran sunan ta Amma ko gezau Mama bata yi ba, Gabaki ɗaya ƴan Aure sun taru tsakar gida cikin, al'ajabin mai ya samu Mama, mero ce ta kasa hkr ta dubi Shehu tace


   " Kai Shehu mai ya sami Salame, gani nayi kuna magana ta yanki jiki ta faɗi, me kace mata?


  Cikin tsoro, Shehu yace.


 " Nifa wlh Innah mero ba wani Abu nace mata ba, cewa fah kawai nayi bada junguɗo aka ɗaurawa Nasreen Aure ba, da ƴar gwal ne.



  Salati kowa ya ɗauka tare da cewa, 


  " Shehu kasan me kake cewa kuwa bada Nasreen aka ɗaura Aure ba, da ƴar gwal, chap *wannan shi ake kira Dara taci gida* cewar Asabe ƙanwar mamy.


  Ita ko Nasreen wani irin sanyi taji a ranta, *Lallai Allah maji Roƙon Bawan sa ne, gashi Allah ya rabani da Auren junguɗo Alhamdulillah* Nasreen ce ke maganar zuci.


  Juyawa tayi ita da innah Asabe, suna mai godiya ga Allah, suka shige ɗakin Ammi, ba tare da damuwa da Halin da Mama take ciki ba.


 Da ƙyar suka samu Mama ta dawo hayyacinta, Amma dai tun farfaɗowar ta, bata kula kowa ba, sai hawayen dake gudu samar fuskar ta, ita kuwa ƴar gwal har yanxu bata dawo daga gidan boka da Mama ta aike ta ba.


  Tare Baba da su khabeer suka jero har ƙofar gidan, khabeer ne yace.


  To mufa Baba zamu koma, saboda dare ya fara kawo kai, naga yanzu har 3:30. 


  Kallon khabeer Baba yayi yace.


  " Khabiru ka tsaya na shiga na fito maka da matar ka, ku tafi tare, zaman Nasreen cikin wannan ƙauye da Auren ta, zai zama abun magana, gara ka tafi da ita, babu kuma wanda zai bika Saboda ina tsoron kar wani Abu ya faru kasan mutanen karkarar nan namu sai a hankali, sihiri ba komai bane a wajen su, ka tafi da ita daga baya koni zan Kawo goggo da Halima suxo suga wajen zaman ta, itama goggo baxan sanar da ita ba sai bayan kun tafi.


  Shiru khabeer yayi kasancewar baiso haka ba yaso sai yaje ya sami iyayen sa, sun tattauna tukunna, sai dai baxai yiwa Baba musu ba, dole yasa shi amsawa Baba da to.


  Iso Baba ya musu zuwa ɗakin dake cikin zauren gidan. Sannan ya shiga ciki.

    Ɗakin mamy ya shiga ya sami Innah Asabe da Nasreen suna zaune, sannu da shigowa Innah Asabe ta masa sannan ya sami gefe guda ya zauna, ya mata bayanin yanda ɗaurin Aure ya kasance, tare da ce mata.


  " Yaron kirki ne na sansa nasan gidan su, asali ma shanun da nake kiwon su na mahaifiyar sa ne, zasu tafi da mijinta, kuma bana son kowa ya bisu, yanda yayiwa Khabeer bayani haka itama ya mata.


  Hamdala Innah Asabe tayi tace.


  " Alhamdulillah tunda ka yadda da Asalin sa ai shikenan, Allah yasa hakan shiyafi Alkairi, tashi Baba yayi yace, Innah Asabe ta haɗawa Nasreen kayan ta zata bi mijinta su tafi,  yanzu.


  Nasiha sosai Innah Asabe tayiwa Nasreen, sannan ta haɗata da  kayan ta, ta rakota har ɗakin zauren.


 Shiko Mlm Musa fitowar sa daga ɗakin Ammi, Innah mero ke cemasa Salame bata da lfy.


  Allah ya ƙara sauƙi yace, sannan ya shige ba tare da ya leka ɗakin nata ba.


 Kusan tare su Nasreen suka shiga ɗakin da Mlm Musa, Nasreen kanta a ƙasa ta gaishe su, yayin da sadiq ya tashi a firgice yana nuna Nasreen da hanu.


   " Na Na Nabiya, Kardai ace kene Nasreen yar nabiya.


  Saurin ɗago Ido Nasreen tayi tace.


  " Ina kaga Nabiya, ina take dan Allah.


  Zama sadiq, tare da kallon Baba dake zaune shima, sannan ya gaishe da innah Asabe, shima khabeer cikin mutunci ya gaishe ta.


  Mlm Musa ne ya jefowa sadiq tambaya, ina kasan Nabiya.



  Amsa masa Sadiq yayi da cewa, mahaifiya tace ta tsince ta, yanxu haka tana gidan mu hanun mahaifiya ta.


  "Alhamdulillah cewar Baba, Allah kaine abun godiya daka tsare min ƴata.

  Gaskiya naji daɗi sosai, kuma insha Allah zan samu lokaci naxo khabiru ya kaini gidan ku, domin na godewa mahaifiyar ku.


  Kamo hanun Nasreen yayi ya haɗa dana khabeer yace.


  " Khabiru ganan ƴata Nasreen na baka Amanar ta, khabeer ka riƙe min Nasreen kamar yanda Uba yake riƙe ƴarsa, karka cutar min da ita, idan ta maka laifi ka mata hukunci kamar yanda Addini ya tana da mana.


  Itama Nasreen kallon ta yayi yace.


  " Nasan ke mai biyayya ce da hkr, ina son ki ƙara akan wanda kike dashi, Nasreen ki Sani zaman Aure ba zaman wasa bane, kibi mijin ki domin aljannar ki tana tafin ƙafar sa, ki sani cewa mijin da kika Aure yana da iyalinsa, bake ƙadai bace, karki Raina matarsa koda wasa, kibi iyayen mijin ki da ƴan uwansa, ki kasance mai kyauta, da sakin fuskar cikin mutane, ki zama mai hkr a duk inda kike Allah ya muku Albarka.



 Da ameen suka Amsa Nasreen tana kuka ta shiga mota suka tafi.


  Ita kuwa ƴar gwal, da gudu ta shigo gidan, Innah mero ta samu a tsakar gida, cikin haki take cewa Innah mero da gaske waini ce aka Aurawa junguɗo.


  " Ehhh dai dai kika ji, kece kika Auri junguɗo.


 Wani irin ƙara ƴar gwal tasa tare da sakin kwalbar da boka ya bata ta kawowa Mama, kwalbar na isa ƙasa ta tarwatse, fashewar ta keda wuya Mama ta fito a guje tana dariya tare da tsire ɗankwalin ta tayi jifa dashi gefe, sai kuma ta fara soshe soshe tana tonawa kanta asiri,


  " Nice na yiwa maimuna asiri ta shiga duniya, nice nayi asiri goggo ta tsani ƴaƴan maimuna, haka tata tonawa kanta asiri, zurawa tayi da gudu tayi waje, binta Mlm Musa sukayi tare da wasu manzan dake waje amma duk da haka sun kasa kama Mama ta shige jeji.



  Dawowa Mlm Musa yayi, ita kuwa ƴar gwal Babu abunda take sai kaku, da daddare Mlm musa yasa aka ɗauki ƴar gwal aka kaita gidan mai gari, ɗaki ɗaya ne aka saka ƴar gwal nanma ko siminti Babu Babu wata tarba da aka bawa ƴan kawo amarya ko arzikin ruwa basu samu ba, bare abinci, haka suka juyo suka dawo suka bar ƴar gwal cikin ɗakin ta.


  A bige junguɗo ya shigo cikin gidan yana warin giya, haka ya faɗawa Ƴar gwal ba tare da cika sunnar Manzo ba.





  Kuyi khr da wannan ina jarabawa ne.



*Share*

   *And*

*Comments*


 *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


  *(Ummu Nasmah)*

[1/6, 8:13 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


 *Deducated to*


Mu'az

Amina Abubakar

Momyn Ajmal

Munaya


 Wannan Page ɗin naku ne kuyi yanda kuke so dashi.



 *P* 6️⃣0️⃣ to 6️⃣1️⃣


Ƙarfe huɗu da rabi khabeer suka iso cikin Gombe, SADIQ ya fara sauƙewa, tare da Cewa SADIQ gobe ya kawo masa Nabiya misalin ƙarfe goma na safe, inyaso kayiwa Hajiya bayanin komai, idan yaso ko da hajiyar sai kuxo tunda Daddyn ku baya nan.


  " Ba damuwa khabeer insha Allah zamu xo kallon Nasreen da kanta ke ƙasa yayi, yace.

  Amarya me maganar suger, sai gobe, a ajiye min sauran kaxar amarcin zanzo, na ƙarasa miki Ita.


  Murmurshi Nasreen tayi A hankali tace Allah ya kaimu goben, ka gaishe min da Nabiya.


   " Zataji insha Allah, khabeer sai ka ganni, junior kam yana bacci ya buɗe Ido ya gansa, kusa da Uwar sa.


  Dariya khabeer yayi tare da cewa Allah ya kaimu, ka gaida min da Hajiya.


  " Zataji SADIQ yace sannan ya shige cikin gidan nasu.


  Jan motar khabeer yayi ba tare daya ɗaga kanka Ido ya kalli Nasreen ba, khabeer yaso bin gidan su, amma gara kawai ya shige gidan sa, idan yaso gobe yaje gidan nasu, da safe, da wannan tunanin khabeer ya nufi hanyar gidan sa.

   Daniel Khabeer ya samu zaune bakin get ɗin gidan shida Isma'il, Bayan yayi parking ne, suka zo tare da miƙa masa gaisuwa, kallon rashin sani suke bin Nasreen dashi, lura da hakan da khabeer yayi ne yasa shi ce musu kowa ya koma bakin Aikin sa.

Muje ya cewa Nasreen.


 Binsa a baya Nasreen tayi, har cikin falon nasa, da sallama suka ƙarasa falon, Zuhura dake zaune, a cikin falon ne ta ɗago kanta, ta sauke sa kanna khabeer, da junior dake maƙale a kafaɗar mahaifin nasa.

 Tashi tayi da sauri ta nufo Khabeer tana ƙoƙarin karɓar junior cikin dariya da murnar ganin ɗan nata data fara cire rai dashi, sai kuma idon sa, ya sauƙa a kan Nasreen dake tsaye bayan khabeer, ta sunkuyar da kanta ƙasa, kallon mamaki da wulaƙanci tayi mata, sannan tace.


   " Abban junior waye wannan? Tana nuna Nasreen da hanu.


  Kallon Nasreen yayi, cikin halin ko inkula yace.


  " Nasreen ce wacce take Mazaunin matata a halin yanzu, yau ɗinnan aka ɗaura mana Aure da Ita.


  " Na shiga Uku, Aure khabeer, sai Kuma tayi dariya tace, kaga ka daina min irin wannan wasan, banso yana tsinka min Zuciyata.


  " Babu wasa tsakanina dake a halin yanzu maganar gaskiya nake gaya miki, kinga karɓi junior ki kwantar dashi.


  " Dallah dakata min malam✋ kasan me kake faɗi kuwa Aure da wannan kazamar bafulatanar, hmm Idan ma mafarki kake to ka farka, domin kuwa Babu kai Babu ƙara Aure a rayuwar ka, har Abada, dani kaɗai zaka ƙarasa rayuwar ka.

  Kallon Nasreen tayi, cikin tsawa tace, ke kuma malama fice min daga gida kafin na miki mungun dukan da baxaki Amfanu ba.


  Cikin tsoro da rawar jiki Nasreen take ƙoƙarin juyawa tabar cikin gidan.

 A Zuciyar ta kuwa cewa take na shiga Uku, nabar wahala na dawo cikin wahala.


 Kamo hanun Nasreen khabeer yayi tare da kwantar da junior kan kujera, bai Kuma tankawa Zuhura ba, yaja hanun Nasreen yana ƙoƙarin shiga da ita ɗakin sa.

  Tare gaban sa Zuhura tayi,tace.

 

  " Wlh yarinyar nan bazata zauna cikin gidan nan ba idan ba so kake yau ayi kisan kai cikin gidan nan ba.


  Murmurshi khabeer yayi mai sauti, kafin yace.


  " Idan kin tashi kisan kai ɗin, akwai bindiga cikin dressing merro na, zaki iya Amfani da ita, kinga daga nan zaki ƙarasa rayuwar ki a gidan kaso.


  " Sai dai kuwa na ƙarasa rayuwar tawa a gidan kason amma muddun kabar yarinyar nan cikin gidan nan tabbas sai na kashe ta.


 " Mahaukaciya sai kuma kitayi, yana faɗi mata haka yayi cikin ɗakin sa da Nasreen, tare da ture Zuhura gefe, ya sawa ƙofar key.


  Hauka Zuhura take tsakanin ta da Allah tana zagin khabeer, tare da masa fashe fashe cikin falon, khabeer yana jin haukar da Zuhura take, yayi banxa da ita.

  Kallon Nasreen yayi, tare da miƙo mata take away ɗin da suka saya a hanya tare da abun sha, yace.


  " Gashi, ganan banɗaki ki tashi mu shiga na nuna miki yanda ake amfani da kayan ciki, sannan ki tabbatar kinyi brush, ma'ana kin wanke bakin ki kafin kixo kici abinci ni zanje office sai Anjuma zan dawo, cikin tsoron kar khabeer ya fice ya barta da Zuhura ta tashi suka shiga tollet ɗin, ya nuna mata komai kafin ya fito ya barta, Bayan ya fito ne yasawa kofar key yanda duk haukar Zuhura baxata iya buɗewa ba.


 Tana zaune tayi kaca kaca da falon yayin da duk ta fasa hanun ta da kwalaben turaren wuta, jini ne kawai ke zuba a hanun nata, sunkuyawa khabeer yayi tare da ƙoƙarin kamo hanun nata dake zubar da jinin, saurin kwace hanun ta Zuhura tayi tana cewa,.


  " Na tsaneka khabeer bana son ganin ka, ka matsa daga kusa dani, mungu azzalumi, macuci ka cuceni, ka faɗa min dame na rageka dashi da zaka ƙara Aure meye bana maka, Allah ya isa tsakanina dakai baxan taɓa yafe maka ba ka cuceni.


  Tashi khabeer yayi tare da ficewa daga gidan ma gabaki ɗaya, dan ya lura Zuhura neman masifa take dashi.


 Ganin ficewar khabeer yasa Zuhura tashi tayi kitchen ɗinta wuƙa ta ɗauko tare da nufo ɗakin khabeer, sai dai Kash ɗakin rufe yake gam da key Babu halin ta buɗe, duk iya dabarar ta, ta kasa buɗewa, zagin Nasreen take daga bakin ƙofar tana cewa, ki buɗe ƙofar nan, idan kika bari na buɗe, wlh sai nayi ajalin ki, cikin gidan nan, zaki san kin Auri mijina, nice ajalin ki.


Ganin da Zuhura tayi Nasreen bazata buɗe bane, yasata komawa saman kujera, tare da sakin wani marayan kuka, mai ban tausayi.


  Nasreen dake cikin ɗakin tama kasa cin abincin tsabar masifar tsoron Zuhura daya tsarga mata, gani take kamar Zuhura zata ɓalla ƙofar ta shigo, addu'a ta shiga yi cikin Zuciyar ta, tare da neman tsarin Ubangiji daga sharrin Zuhura.

   Oh ni kuma tawa ƙaddarar kenan ta shan wahala, ya Allah ka duba wahalar dana sha a baya ka, kareni daga sharrin wannan matar, ka rabani da ƙara shan wani wahalar.



  Shi kuma khabeer darect office ɗin su ya shige, office ɗin Kamal ya shiga tare da zama, bayan sun gaisa ne khabeer, ya fara yiwa kamal tambaya game da yanda case ɗin su Momy Sarah ke tafiya.


  " Ranka ya daɗe yau kwana biyu kenan Momy Sarah take cewa tana son ganin ka.


  " Momy Sarah Kuma? Okey bari naje naji abunda ke faruwa.


  Tana zaune ta haɗa kanta da gwiwwa, Gaba ɗaya ta rame ta fice hayyacinta idan ka ganta baza kace Momy sarah da ka sani bace.


  " Momy Sarah khabeer ya kira sunan ta 


 Ɗago kanta tayi, tare da kama hanun khabeer, tace


  " Khabeer nayi dana sanin abunda na aikata cikin rayuwata, gashi yanxu ba'aje ko ina ba, na fara girban Abunda na shuka kaicona khabeer gashi mungun Aikin da nayi yasa, ɗana ya shige duniya yabar matar sa, na cuci rayuwar ƙananan yara  da basu san komai ba, a duniya, nayi sanadiyyar lalacewar yaran mutane da yawa, kaicona khabeer, daga kai har mahaifiyar ka, kun riƙeni da zuciya ɗaya ni kuma na cuce ku, maganar take tana kuka sosai har tana ajiyar zuciya.

  Oga John da kake nema, yana India, cikin birnin mumbai, a unguwar kwalkwata, ka kawo wayana zan  tura masa text ɗin cewa ina zuwa jibi cikin India ya faɗa min inda zamu haɗu, zai kira ni a waya domin ya tabbatar da cewa nice na turo text ɗin, kai kuma kayi ƙoƙari zuwa jibi ku haɗu, idan kuma ka sake baku haɗu ba, to tabbas ka rasa John kenan.


  Khabeer yaji tsusayin Momy sarah sosai, har takai ga idon sa ya ciko da kwalla.


  " Na gode Momy da bani wannan information da kikayi, sannan kici gaba da tubawa Ubangijin ki, shine kikayiwa laifi, zai kuma yafe Miki.

 Sawa khabeer yayi aka kawo wa Momy sarah wayar, ta turawa John text, ba'a juma da tura text ɗin ba, john ya kira, inda Momy sarah tace masa zasu haɗu, duk abunda suke khabeer ya danna recording.


 Bayan sun gama ne khabeer ya fice daga office ɗin cikin tsusayin Momy sarah.




*Share*

   *And*

*Comments*



  *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


   *(Ummu Nasmah)*

[1/10, 4:19 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah*


*Godiya ta tabbata ga Ubangijin taliƙai wanda cikin ikonsa da ƙarfin addu'ar ku fan's ya bayyana mana fareesa cikin ƙoshin lfy, ALLAH mun gode maka.*


*Mu'az muna miƙa sakon godiyar mu gare ku tare da abokan aikin ka, wato* 


*Husaini 80k*


*Hassan ATK*


*Prince Abdul*

 

*Abdul Nakowa*


*Its b y Ibrahim*


*Farst Class*


*Abu Sameer*


*Ibrahim Bros*


*+218921127536*


*Mun gode sosai Allah ya saka da Alkairi*


*Fan's bazamu manta da ƙaunar ku gare mu ba, a gaskiya munji daɗin Addu'ar ku garemu Allah ya saka da Alkairi*



*P*•••••••6️⃣2️⃣ to 6️⃣3️⃣


  Bai tsaya, cikin station ɗin ba, gidan sa ya shige kasancewar dare yayi, har wajen tara na dare, shigar sa cikin gidan Zuhura tana zaune cikin falon kamar yanda ya fita ya barta sai hawaye dake gudu saman fuskar ta da alamu dai sallar ma, batayi ba, Zama khabeer yayi kusa da ita cikin tausayin baƙin kishin ta, yace.


  " Zuhura, meyasa kike ɗaga hankalin ki, akan abunda bai kai ya kawo ba, meye acikin kishiya, a tunani na, kina da wayewar da baxaki damu ba, dan na ƙara Aure, kuma wannan Auren bawai nayi shi bane dan son rain........


  Hanu Zuhura ta ɗaga masa, cikin dashewar murya tace,


  " Bana son jin komai daga bakin ka, ka tashi daga kusa dani Kafin na illata Rayuwar ka.


  " Please ki share hawayen nan, bana son na ganki cikin damuw.......



  " *KATASHI KUSA DANI NACE* bana ƙaunar jin kalaman bakin ka.


  Dole tasa khabeer tashi ya ƙyale Zuhura badan yaso ba, ya shiga ɗakin sa.


  Zuhura tana ganin khabeer ya shiga ɗakin sa, kuma da wata mace ciki ba ita ba, sai ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana magana ita ɗaya kamar zaucacciya.


  " Wlh baxan haƙura na ganka da wata mace ba, sai na kashe ka, na kashe ta, sannan nima na kashe kaina, dole yau dukan mu baxamu kwana cikin gidan nan ba, tunda kai munafiki ne, zakayi Aure a ɓoye ba tare dana sani ba.


  Shigar sa ɗakin ya samu Nasreen na zaune, saman sallaya tana rera karatun ƙur'ani cikin ƙwarewa da bawa, ko wacce kalma haƙƙinta.

  Cikin sha'awar karatun nata, da kuma zaƙin Muryar ta, shine ya basa mamaki, har ta kaisa ga maganar zuci.


  " Daman ƴan ƙauye suna karatun Addini ne, haka, ikon Allah kuji yanda yarinyar nan take karatu tartilan tajweedan, ikon Allah lallai mutum duk yanda yake ba abun rainawa bane.

 Zama yayi saman kujerarsa dake cikin ɗakin yana cigaba da sauraron ta.


  Ita koh Nasreen kanta na kallon gabar bata ma san ya shigo ɗakin ta, ba tsabar ta maida hankalin ta da tunanin ta kan karatun ta.

Bayan ta gama karatun Suratul Ahƙaf ne, tayi Addu'a, ta shafa, sannan ta juya da fuskar ta, yamma sai a lokacin taga khabeer Zaune, domin kuwa ita bata ji shigowar sa ba.


  " Sannu da dawowa kwaɗo, ta furta a hankali kamar mai tsoron magana.


  " Yawwa sannu, ki daina kira na, da kwaɗo sunana khabeer.


  Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tace.


  " Baxan iya kiran sunan ka ba, sai dai idan ka amince min, na kiraka da *BANDIRAWO*, amma sunan ka yamin nauyi a baki na.


  Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


  " Ban Amince miki ba, sai dai ki kira ni da, Abban junior kamar yanda Auntyn ki Zuhura ke kira na dashi.


 Dam gaban Nasreen ya buga jin ambatan sunan Zuhura da yayi, domin kuwa tana mungun tsoron matar.


  " Shikenan zan kira ka da hakan.


  Nuni khabeer ya mata da gadon sa, yace.


  " Ki hau gadon nan ki kwanta, ni zan kwana saman wannan kujerar, sannan ki tabbatar kin shiga tollet kinyi wanka kafin ki kwanta, sannan wannan kayan jikin naki ma, ki sauya su, gobe idan Allah ya kaimu zan barwa SADIQ kuɗi ya ɗauke ki, kuje ku sayo kaya, Saboda ni bana nan, zan bar ƙasar nan, by 1:00 da tare zamuje, mu sayi kayan.


  Da to Nasreen ta amsa sannan ta ɗauki kayan ta, wanda idan tayi wanka zata sanja a tollet, dan gaskiya bazata iya sauya kaya a gaban sa ba.


  Bayan ta fito daga wankan ne, rike da kayan data cire su, gana masgo dinta take ƙoƙarin mayar da kayan, taji Muryar khabeer na cewa.


  " Karki mayar da kayan nan cikin kayan ki, masu wanki, ga can dosbin kije ki saka ciki, sannan kuma ki cire hijab ɗinnan, ke bakya gajiya ne, tun safe hijab ke jikin ki, kinƙi cire sa.


  Wucewa dosbin ɗin tayi ba tare data Amsawa khabeer ba, ba kuma ta da niyar cire hijab, ɗinta, koda take gidan su ma bata cire hijab bare kuma yanxu da take Zaune ɗaki ɗaya da ƙaton namiji.


  Tollet ɗin shima khabeer ya tashi ya nufa, wanka yayi tare da fitowa ɗaure da towel a ƙugunsa ko a jikin sa.

 


  Nasreen data ɗago kanta ne, sai sukayi ido huɗu da khabeer ɗaure da towel a ƙugunsa, saurin rufe idon ta, tayi tare da furta innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un na shiga Uku.


  Dariya ce, taso kwacewa khabeer, ganin yarintar Nasreen a fili, wai na shiga Uku, kaɗa kansa yayi tare da nufar dressing merro, yana goge ruwan jikin sa, da ƙaramin towel dake riƙe a hanun sa.

Ita dai Nasreen tana rufe da idon ta gam taƙi buɗe su, acewar ta, bata taɓa ganin namiji a tuɓe haka ba.


  Shiryawa khabeer yayi chap cikin pyjamas ɗinsa na bacci, sannan ya ɗauki filo da system ɗinsa, yayi kan kujera, tare da cewa Nasreen.


  " Sai ki samu damar buɗe idon naki tunda na gama shiryawa koh.


 Buɗe idon nata tayi ba tare da ta ɗago ta kalle saba, shima bai kalleta ba yaci gaba da danna system ɗinsa.


  A hankali Nasreen ta kwanta akan gadon, wanda tunda take bata taɓa kwanciya kan gado mai laushin sa ba, ji take kamar kan auduga ta kwanta tsabar laushi, duƙunƙunewa tayi cikin hijab ɗinta.


  Shiko khabeer bai kwanta ba sai wajen 12 na dare, cikin Bacci yaji an shaƙe masa wuya, a firgice ya buɗe idon sa, Zuhura ce sunkuye a kansa ta shaƙe wuyan sa, tsakanin ta da Allah, ita a dole tana neman rayuwar sa, hanun sa khabeer yasa ya fincike nata hanun daga wuyan sa, yana tari cikin azaba, idon sa kuma yayi jajujur.

Cikin ɓatsin rai yace.


  " Zuhura kin haukace ne, kashe ni kike sonyi.


Cikin huci Zuhura take cewa.


  " Kashe ka zanyi khabeer na kashe wannan tsinanniyar daka Auro sannan nima na kashe kaina dade na zauna ina kallon ka, da wata Mace cikin gidan nan, na gwammace naga gawarka kwance, domin soyayyar ka, bazata barni nayi tarayya dakai tare da wata ba.


 Nasreen koh da tun shigowar Zuhura ta koma ƙarshen gado ta maƙale, tana jiran sarautar Allah, idon ta kuwa ya ciko da ƙwalla, Babu abunda take sai shashashsheƙar kuka.


Ran maza fah ya ɓaci.

 Tashi khabeer yayi ya miƙe tsaye tare da ɗauke Zuhura da wasu tagwayen maruka, wanda sai da yasa Zuhura ganin wasu taurari sun wulga ta gabanta, kama Hanun ta yayi ya murɗe ya kuma ƙi sake su, murza hanun yake cikin salon na mugunta runtse idon ta tayi cikin Azaba, faɗa khabeer ya fara cikin ɓacin rai tunda yake bai taɓa jin haushin mace ba irin Zuhura domin yau Zuhura ta kaisa bango tunda har abun nata ya kai ga tana neman rayuwar sa tabbas yau tura ta kaisa bango.


  " Zuhura kinyi ƙarya ki iya kasheni muddun dai da wannan Hanun naki ne, sai dai idan Bacci nake ki soke ni da wuƙa, koko ki harbe ni da bindiga ban ankara ba, amma banda wannan Hanun naki, wannan itace soyayyar da kike iƙirarin cewa kina mini, ƙarya kike Zuhura da kina sona baxaki nemi Rayuwata ba, komai munin Abunda na miki, bare kuma Babu muni cikin Abunda na Aikata, wacce Irin macece ke Zuhura, wacce bata fahimtar mijinta, tun jiya nake ƙoƙarin na fahimtar dake dalilina na wannan Auren amma kinƙi Saurarona, ya kike so nayi dake, shine yanxu zaki zo ki nemi Rayuwata, tabbas yau na tabbatar da Rashin hankalin ki Zuhura, ke wacce Irin ballagazar macece.


  " Ya isheka khabeer, ya isheka, domin kuwa idan baka kirani matar rufin Asiri ba, bazaka kirani ballagaza ba, Kuma Wlh yau na rantse saina kashe wannan matar har kai ɗin ma.


 Murmurshi mai ciwo khabeer yayi, Yace.


 " Zuhura bakya daga cikin matan rufin Asiri, domin kuwa matar rufin Asiri itace mai karɓar duk abunda mijinta ya kawo Mata, mai Adana masa kayan sa, ta tsaftace masa ɗakin sa, ta masa girki wanda koda yazo da baƙin sa, ba zaiji Kunya ba, ba Irin ki ba wacce kullum take cikin ɗagawa mijinta hankali wacce bata damu da abincin mijinta ba, wacce bata damu da shimfiɗar mijinta ba, wacce bata damu da gyaran gidanta ba, wacce kullum take cikin ɗauke kuɗin mijinta ma'ana sata,. Ko kina tunanin cewa bansan kina min ɗauke ɗauke bane cikin gidan nan, duk abunda kike yi tar nake kallon ki, domin kuwa ni ba mahaukaci bane nasan Abunda na ajiye cikin ɗaki na, komai kuwa yawan sa, domin Babu wanda yasan inda nake ajiye kuɗina cikin ɗakin nan sai ke, a Hakan kike kiran kanki matar rufin Asiri?


  Shuru Zuhura tayi cikin sanyin jiki domin kuwa bata taɓa tunanin cewa khabeer yasan tana ɗaukar masa kuɗi ba, cikin kurari Zuhura tayi kan Nasreen gadan gadan tana cewa.


  " Koma me zaka faɗa ka faɗa amma Wlh yau sai nayi Ajalin wannan tsinanniyar daka Auro.


 Dakatar da ita khabeer yayi ta hanyar cewa.


  " Dakata Zuhura, badai akaina kike wannan haukar ba, to kije na Sakeki saki ɗaya.


  Turus Zuhura ta tsaya waje ɗaya ta gagara gaba ta gagara baya, wani irin tsinkewa Zuciyarta tayi, sai Kuma tasa kuka, tana cewa.


  " Ka sake ni fah kace khabeer, nice fah Zuhuran ka, wacce *MUKAYI AUREN SOYAYYAH* .


 " Kwarai kuwa Zuhura na sake ki, ba ƙarya kunnen ki ya miki ba keɗin da mantawa kikayi da Auren soyayyar mukayi kike neman Rayuwata, adalci ɗaya zan miki shine na barki har gari ya waye cikin gidan nan Kafin ki tafi gidan ku.


 " Bazan jira wayewar gari cikin gidan kaba khabeer, zan tafi cikin daren nan, kallon Nasreen tayi tace.

 Ke kuma tunda har akanki aurena ya mutu, to Wlh kema sai nayi Ajalin ki, Bama na Auren kiba, ki rubuta ki ajiye nice ajalin ki.


  Tsawa khabeer ya dakawa Zuhura, 


  " Get out, ki fice min daga ɗaki nace miki.


  " Ko baka faɗa khabeer, yanxu ma kuwa, juyawa tayi tabar ɗakin nasa a fusace.


  Kiran security na gidan khabeer yayi ya basu umarnin cewa karsu bar Zuhura ta fita cikin gidan da wannan daren.

  Juyo da kallon sa yayi kan Nasreen dake ta faman shashashsheƙar kuka, yace


  " Ya isa haka kaina ciwo yake, min dan Allah karki ƙara min da naki, Zuhura ta isa ta miki Abunda Ubangijin ki, bai hukunta miki bane, ki daina jin tsoron ɗan Adam, domin duk sanda kika kasance matsoraciya, tabbas sai kowa yaci kashi a kanki, ki kasance jaruma a duk inda kike, hakan ne zaisa duk wani maƙiyin ki, zaike jin shakkar ki.

Yana gama faɗa mata haka ya koma ya kwanta.


  Washe gari da safe Zuhura sammako tayi tabar gidan khabeer, junior kuwa ko kallon sa batayi ba, tana jin yana kukan zai bita Amma taƙi kula Yaron.


 Khabeer ne ta fito ya ɗauke sa, yayi cikin ɗakin sa dashi, Nasreen ya miƙawa shi ta karɓe sa tare da cewa taje ta masa wanka, wankan Nasreen ta masa, ta shirya shi cikin kayan da khabeer ya ajiye masa, sannan itama tayi nata wankan, bayan sun gama shiryawa ne, suka fito falo, shi kuma khabeer ya shiga wanka.

  Asabe suka samu cikin falon tana shirya abinci a daining area, kallon mamaki Asabe ke bin Nasreen dashi ganin sun fito ita da junior cikin ɗakin khabeer, a Zuciyarta take cewa, ko sabuwar ƴar aiki ummin junior tayi ne, Asabe bata kula Nasreen ba, saima Nasreen data gaishe ta cikin girmamawa, fitowar khabeer, daining ya nufa tare da cewa Nasreen taxo suyi breakfast su samu su isa gidan nasu karsu SADIQ su rigasu isa.





*Share*

     *And*

*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻



      *(Ummu Nasmah)*[1/12, 5:37 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*P*••••••6️⃣4️⃣ to 6️⃣5️⃣


Ruwan tea da breed kawai khabeer yasha, kasancewar baya cin abincin ƴan aiki, itama dai Nasreen abincin ba wani mai yawa taci ba, duk da yayi banbanci dana ƙauyen su, amma hakan baisa ta nuna ƙauyancin ta ba, bayan sun gama breakfast ɗin ne, khabeer yace su tafi, kama Hanun junior Nasreen tayi suka fito har harabar gidan, motar sa, khabeer ya hau itama Nasreen ta shiga tare da junior, Hon yayi bakin get ɗin gidan nasu, wani matashin saurayi ne, ya buɗe get ɗin wanda ya karɓi Baba iro, shigowa khabeer yayi tare da yin parking, suna fitowa daga cikin motar su SADIQ na shigowa, da tasu motar, da katawa khabeer sukayi, da shiga cikin gidan suka tsaya jiran su SADIQ, Nabiya dake hango Nasreen ta cikin motar ji take kamar ta buɗe ta fito kafin ma suyi parking domin gani take kamar idon ta, gizo take mata ba Nasreen bace.


  Bayan sunyi parking Nabiya ta rigasu fita daga cikin motar da gudu ta nufi Nasreen, itama Nasreen hango Nabiya yasata, tahowa da gudu, Rungume juna sukayi, tare da sakin wani ajiyar Zuciya, Nabiya ce tace.


   " Adda Nasreen kece nake gani kodai idona kemin gizo.


  " Nice Nabiya, shine kika tafi kika barni cikin ƙunci da wahala, banyi tunanin zan ƙara ganin ki, a duniya ba.


  " Sharewa Nasreen hawaye Nabiya tayi, tace, a'a Adda ba guduwa nayi na barki ba, na gaji ne, da wahalar Mama da Goggo shine yasa nabar cikin garin, ina Nuruddeen yake Adda ban ganshi tare dake ba.


  Sunkuyar da kanta Nasreen tayi cikin rasa wacce irin amsa zata bawa Nabiya, Muryar khabeer taji yana cewa


  " Mu shiga ciki tukunna ma ƙarasa maganar a ciki.

  Khady da Hajiya da suka tsaya kallon su Nasreen ne, suma suka rufa musu baya zuwa cikin gidan.


  Da Sallama suka shiga cikin gidan, momma da su Nana suna Zaune a falon har Daddy kasancewar yau Asabar Daddy baida aiki yana gida, Amsa Sallamar Daddy yayi, momma ce tace.


   " Hajiya yau kece cikin gidan namu, lallai yau mun tashi da Sa'a.


  Murmurshi Hajiya tayi tare da cewa.


  " Mune tafe, Allah dai yasa anyi breakfast damu.


  Dariya Daddy yace,


  " Ai Hajiya Zainab ba'a rasa nono a ruga, tunda mun samu baƙoncin ku, ai dole mu nema muku breakfast.

    Ku dai bismillah ku zauna.


  Cikin dariya Hajiya ta zauna, Khadijah ce ta tashi, ta kawo musu Ruwa.

  Bayan gaishe gaishe da wasa da dariya da akayi sannan Hajiya ta gyara zama kasancewar SADIQ ya sanar da ita komai, magana ta fara.


  " To Alhaji duka wannan taron namu da ka gani wajen ka mukaxo da muhimmiyar magana, Allah yasa zaka fahimce mu.


  Murmurshi daddy yayi, yace.


   " Hajiya me zaki zomin dashi na kasa fahimtar ki, ina sauraron ki, duk dama na ganki da baƙin fuska.


   Kallon khabeer da Nasreen tayi da kansu ke sunkuye ƙasa, tace wa daddy.


  " Akwai baƙuwa cikin gidan nan naku, wacce a yanda khabeer ya bani labarin cewa ka tsince ta ne cikin wani hali na rashin lafiya, to muna buƙatar ganin wannan baiwar Allah domin kuwa tafe muke da yaranta, gasu nan, sune baƙuwar fuskar da kake cewa ka gani.


   " Ikon Allah cewar daddy Allah Abin godiya, yanxu wannan yaran maimuna ne.


  Momma ce tace.


  " Ai kuma sai yanxu nake ganin tsantsar kama tsakanin su da mamin nasu, ikon Allah, a ina kuka samesu?


  Daddy ne yace,


   " A'a ki bari a kira maimuna tukunna ko wani irin bayani ne, sai ayi a gaban ta.


   Kinga Nana maza tashi kije ki kira mamyn ku, ku taho tare.

   Tashi Nana tayi, tare da shigewa ɗakin Mamy, tana kwance, amma ba bacci take ba, Sallama Nana tayi, ta amsa tare da cewa, mamy kixo inji daddy yana cikin falo, Amsawa mamy tayi da to , sannan ta tashi tayi suka fito tare tun daga nesa, Nasreen suka hango Ammin su na tahowa, kusan a tare suka mike tare da rugawa a guje, Mamy data hango yaran nata gani take idonta ƙarya take mata, sanda taji sun faɗa jikin ta, tare da sakin wani marayan kuka.

  Ga baki ɗaya wajen tsayawa sukayi suna kallon su, cikin tausayi.


  " Kece Ammi kece yau muke gani da idanun mu, meyasa kika tafi kika barmu cikin wahala Ammi, munsha wahala bayan bakya nan Ammi munsha wahala.

  Nasreen ke magana cikin kuka.


  Ɗago kanta Mamy tayi tare da cewa.


  " Ban tafi na barku dan son raina ba, hasali ma, bansan dalilin daya fitar dani daga cikin rugar ba, sai dai cikin ikon Allah yanxu gani cikin hankali na, lokaci kawai nake jira na koma gare ku, kullum daku nake kwana nake tashi, bani da wani burin daya wuce na saku cikin ido na.

  Shafa kan Nabiya tayi tace.

  Nabiya da alamu bakya cikin wahala domin kuwa yanayin jikin ki ya nuna cewa bakya tare da wahala.


  Gyaran murya Daddy yayi tare da cewa su nemi waje su zauna.

  Zaman sukayi, sannan daddy  ya kara godiya ga Ubangiji, ya kalli Hajiya Zainab, yace Hajiya bismillah, zaki iya bamu labarin yanda kika samu yaran nan.


  " Kwarai kuwa Alhaji, labarin yanda ta hadu da Nabiya ta basu, har kuma zuwa jiya dawowar SADIQ cikin gidan sannan ta dubi khabeer tace khabeer bismillah, sai ka ƙarasa labarin.


   " Sunkuyar da kansa ƙasa khabeer yayi sannan ya fara basu Labarin farkon zuwan sa ƙauyen su Nasreen ɗin har zuwa Ranar juma'a daya je ya samu za'a ɗaurawa Nasreen Aure da junguɗo, duban Daddy khabeer yayi yace.

   Ku gafarce ni daddy, ganin da nayi ana shirin cutar da rayuwar Nasreen ta hanyar aura mata mashayi, yasa nayi amfani da damar da Ubangiji ya bani, na dakatar da Auren ta da junguɗo, na mayar kaina, ma'ana na Auri Nasreen ba tare da sanin ka ba, mun kuma yi ƙarya da sunan ka, kan cewa, Mlm iro ya karɓa min Aure da izinin ka.


  Shuru falon ya ɗauka, yayin da kowa ke jiran wacce irin amsa Daddy da momma zasu bayar.


  Nisawa Daddy yayi tare da cewa.


  " Baka min laifi ba khabiru dan kayi Auren taimako ba tare da izini na ba, ai yanxu an riga da an zamo ɗaya da maimuna, domin kuwa ƴaƴan maimuna ƴaƴa nane, Ina roƙon Ubangiji da yasa wannan Aure ya Zamo Alkairi gare ku, ya rabaku da sharrin shaiɗan cikin lamarin Auren ku, yasa wannan Aure ya kullu kenan har Abada, Babu rabuwa a cikin sa, tabbas ina tayaka murna, domin ka samu mata ta gari na tabbata Abunda ya fito daga jikin maimuna, abune mai kyau, Allah ya muku Albarka gabaki ɗaya.

   Sai dai kuma idan mahaifiyar ka tana da Abunda zata ce.


  Cikin jin daɗi SADIQ da khabeer suka amsa da Ameen.


  Murmurshi momma tayi cikin farin ciki tace.


  " Ai alhamdulillah babu abinda zance nida nake soma ka ƙara Aure, gashi kuma cikin sauƙi ka samo ƴar mutunci abu ɗaya kawai zance shine baxaka koma da Nasreen gidan kaba, zan riƙeta a hanuna nan da ɗan wani lokaci, kafin na baka Ita.


  Murmurshi khabeer yayi tare da cewa


  " Shikenan Momy Babu damuwa.


  Hajiya ce tace


  " Ai Hajiya momma na rigaki cewa zan tafi da Nasreen gidan na, domin mata shiri na musamman, dan haka dole ki bani ƴata na koma da ita.


  Dariya sukayi duka momma tace ai shikenan tunda kin min fin ƙarfi, yana iya.


Cikin jin daɗin yanda suka damu da ƴaƴan ta, mamy tace.


  " Babu Abunda zance muku sai Allah ya saka da Alkairi, kun soni kunso ƴaƴa na, na gode sosai Allah ya saka da Alkairi.

  Nasreen ina Nuruddeen yake.?


  Sunkuyar da kanta Nasreen tayi cikin zubar da hawaye tace.


  " Ammi Nuruddeen ya koma ga Ubangijin sa, babu Nuruddeen cikin duniyar nan, Ranar da Nabiya tabar rugar mu, Nuruddeen ya rasu sakamakon bigesa da mota tayi.


  Kuka sosai Nabiya keyi, tana tuno rayuwar su da Nuruddeen, Allah sarki rayuwa, ashe rabuwar mu, kenan da shi tunda gidan Goggo, yana kuka yana cewa, dan Allah Adda Nabiya karki tafi ki barmu.


  Mamy kuwa hawaye ta zubar tare da bin Nuruddeen da addu'a tasan Ubangijin daya karɓe ta yafi ta sonsa Allah ya jiƙanka da rahama Nuruddeen, Abunda Mamy tace kenan tayi shiru.


 

Nisawa khabeer yayi Yace.


  " Daddy Na sake Zuhura yau, yanxu haka bata gida na, ta koma gidan su.


  " Khabiru me yayi zafi haka harda saki, ko dan ka ƙara Aure ne, ka saki matar ka, uwar gidan ka.


  " Ko ɗaya daddy sakin Zuhura baya daga cikin Auren dana ƙara, Abunda ta masa ya sanar dasu.


 Allah ya kyauta daddy yace, tare da cewa Allah ya sasanta tsakaninsu ku, domin kuwa akwai ɗa a tsakanin ku, dole zaka dawo da matar ka.


  Momma kam bata ce komai ba, saima cewa da take cikin zuciyarta Allah yasa Zuhura karta dawo.


Agogon hannun sa khabeer ya duba tare da ce musu shi zai wuce yana so zaije London yanxu akwai Aikin da zai kaisa.


  Fatan Alkairi Daddy ya masa, suma su Mamy Addu'a suka mass sannan Sadiq ya tashi ya masa Rakiya.


  Hajiya sun ɗan juma suna hira kafin suma su tashi tafiya tare da barin Nasreen da Nabiya tare da mahaifiyar su, suyi kwana biyu kafin daga baya su dawo wajen Hajiya.



  Wannan kenan.


Cikin nasara da Sa'a khabeer ya samu damar chapke john inda ya gama haɗa duk wani information akansu, inda ya miƙa su zuwa ga kotu, za'a shiga shari'a ranar 10 ga watan 1 Nasreen kuwa Hajiya bata barin khabeer ya ganta, duk sanda yaxo gidan, ɓoye Nasreen Hajiya keyi, tuni yanxu soyayya tayi ƙarfi tsakanin Nabiya da SADIQ.



  Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, a yaune aka shiga kotu dasu Momy sarah........




  Mu haɗu daku next page domin jin yanda zata kasance a kotu.




*Share*

     *And*

*Comments*



   *Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻



    *(Ummu Nasmah)*

[1/15, 3:51 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*P*••••••6️⃣6️⃣ to 6️⃣7️⃣


          *KིOིTིUི*


 Cike kotun yake da jama'a, yayin da ake zaman jiran Alƙali, ba'a juma ba, Alƙalin ya samu isowa, bayan zaman alƙali ne, aka shigo dasu Momy sarah, hanun su ɗaure da ankwa, kanta sunkuye Momy sarah yake ta kasa ɗagowa ta kalli jama'ar wajen, su daddy da momma harma da Mamy sunxo court ɗin, harda yaran Momy sarah, hatta Khalid da ba'ayi tsammanin yana garin ba, yaxo, wajen khabeer yaxo tare da mika masa hanu sukayi musabaha, Mai gabatar da ƙara, shine ya tashi ya gabatar da ƙaran, sannan Alƙali ya nemi ganin lawyern wanda ake ƙara, 

Akace basu da lawyer, neman lawyern wanda yayi ƙaran alƙali yayi, nan ma sukace basu da lawyer sai dai suna da cikakken shaida a Hanun hukumar ƴan Sanda, Alƙali nema yayi da a gabatar masa da shaidar, khabeer ne ya haɗa duk wasu Files na case ɗin da duk wani shaida da yasan suna dashi, ya miƙawa maga takarda, shi kuma ya miƙata ga alƙali, bayan dube dube da alƙali yayi, ne ya ɗago kansa tare da fara yiwa su Momy sarah tambaya ɗaya bayan ɗaya, Alhamdulillah basu wani bawa alƙali, wahala ba, suka amsa laifin su, kaurewa kotun tayi da hayaniya, tare dayin Allah wadarai da halin su Momy sarah, bayan rubuce rubuce da alƙali yayi ne, ya ɗago tare da buga teburin gaban sa, nutsuwa kotun yayi, sannan alƙali ya fara magana kamar haka.


   " A ƙarƙashin doka ta 112 kotu ta yankewa John hukuncin rai da rai tare da aiki mai tsanani. a gidan yari, sakamakon kamasa da kotu tayi da hanu dumu dumu cikin hallakar da rayuwar ƙananan yara, ta hanyar sawa a cire musu kidney tare da safarar yara, ƙasashen waje ana lalata da su, wasu yaran da aka cirewa sun rayu da kidney ɗaya wasu kuma sun mutu ta wannan hanyar.

 Hayaniya kotun ta ɗauka kowa na murnar hukunci da kotu ta ɗauka akan John, ƙara buga teburin alƙali yayi kafin akayi shuru, magana yaci gaba dayi. 


Sai Gedyoung da Hajiya Zainab, kotu ta yanke musu hukuncin rai da rai suma a gidan yari, a ƙarƙashin doka ta 112 sakamakon kama su da kotu tayi da hanu cikin taimakawa John wajen safarar yara ana cire kidney nasu.


   " Sai kuma Hajiya saratu da sauran abokan harkar ta wato Hajiya Hindatu, A ƙarƙashin doka ta 102 kotu ta yanke musu hukuncin shekara Goma 10 a gidan kaso tare da aiki mai tsanani, sakamakon kama su da kotu tayi da hanu cikin taimakawa John wajen safarar miyagun kwayoyi cikin wannan ƙasar tamu, tare da safaran yara ƴan mata, suna fitar dasu waje, ana lalata dasu, buga teburin gaban sa alƙali yayi alamun Shari'a ta ƙare.


  Kama kansa khabeer yayi cikin matsanancin tausayin Momy sarah da yaranta, wani irin ciwon kai, yaji ya taso masa, jajur idonsa yayi, jin yanda Momy sarah zatayi shekara Goma gidan yari, Khalid kuwa kuka yake harda shashashsheƙa, Haka momma itama kukan take, Daddy kam Babu Abunda yake cikin Zuciyarsa, sai innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, da yake furtawa, wajen Momy sarah dukan su suka nufa har khabeer.


  Daddy ne yayi ƙarfin halin cewa.


  " Saratu kinga Abunda halin ki, yaja miki koh, gashi yanxu kece, kika kwana ciki, kin yiwa kanki mungun ɗauri, harna shekara Goma a gidan kaso.


  Sai a lokacin Momy sarah ta daga kanta cikin kuka da danasani, tace.


  " Tabbas nayiwa kaina mungun ƙulli, gashi ƙwadayi na da son zuciyata ya kaini ya baro Ni, na kasa haƙuri da Abunda mijina ke wadatar dani, na raina arzikin sa, nasa son duniya da ƙwaɗayi cikin raina, yanxu gashi inda son duniya ya kaini, na ɓatawa yarana suna, nasa ahalina kuka, ka yafe min Alhaji, domin kuwa yanxu naga rayuwa, illar rashin haƙuri da Abunda nake dashi, gashi yanxu son kuɗi ya kaini ga hallaka.


  " Na yafe miki saratu ki cigaba da istigifari a wajen Ubangijin ki, domin neman Afuwar sa.

  Daddy na gama faɗar haka ya juya ya bar wajen da sauri sakamakon hawaye dake neman, zuwa masa.


  Kamo hanun momma da khabeer Momy sarah tayi, cikin hawaye tace 


  " Ku yafe Ni, kun ruƙeni da zuciya ɗaya, wanda ni sam bada haka na rike kuba, Momma ki riƙe min yara na, Amana, na baki su amana ki kula da rayuwar su, domin nasan shekara Goma ba kusa take ba, khabeer ka yafen a bisa wahalar da ɗanka da nayi, nayi maka munguta kala-kala domin ganin kafi ɗana komai, hatta lalata, dukiyar ka, naso yi, amma hakan ya gagara sai ƙara cigaba da kullum kake daɗa yi, tabbas wannan shi ake kira da *SARA DA SASSAƘA BAYA HANA GAMJI TOHO* gashi duk sassaqa da nake maka, sai ƙara yabanya kake tare da baza Inuwa mai sanyi kuyi hkr wataƙil na mutu gidan yari ku yafe min ko zan samu sassauci cikin zuciyata.


  Share hawayen ta momma tayi tace.


  " Mun yafe miki duniya da lahira momyn yara, Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawa da kika faɗa, insha Allah yaranki bazasu yi kukan rashin uwa ba, za kuma ki fito kiga yaranki insha Allah.


  Khabeer kasa magana yayi, da ƙyar yace Momy, kiyi hakuri, insha Allah zaki fito ki same mu cikin ƙoshin lfy, zan kuma dinga ziyartar ki Lokaci zuwa lokaci, yana gama fadin haka shima bar wajen da sauri.


Kamo Khalid Momy sarah tayi tare da masa nasiha, akan ya kintsu ya zama na kirki, tana son halin data faɗa ciki ya zama *DARASI GA RAYUWAR SA, DOMIN HAUSAWA SUNCE GANI GA WANE YA ISHI WANE TSORON ALLAH*

  Momy sarah tana ji tana gani aka sata a gaba zuwa gidan yari, KUKA sosai Khalid keyi yana gani aka wuce da mahaifiyar sa.


  Motar sa khabeer ya buɗe, yana dafe kansa yaga an miƙo masa hanu, ɗaga kansa yayi ido suka haɗa dana SADIQ, cikin tausayin halin da khabeer ke ciki, SADIQ yace.


    " Bari naja motar nasan a halin da kake yanxu jan mota ba naka bane, kallon Khalid SADIQ yayi yace, bismillah shiga baya mu tafi.


  Khabeer shiga motar yayi ba tare da yacewa Sadiq komai ba.



  Rayuwa kenan yau gare ka gobe ga wanin, wai yau Momy sarah ce zatayi shekara goma gidan kaso, tabbas duniya ba komai bace, duk yanda ka ɗauke ta, haka zata tafi da kai yau gadai ƙarshen Momy sarah.



     *Rugar ARƊO*


  Mama na hango tafe cikin bola tana tsince tsince, kanta babu ɗankwali haka ma ƙafarta Babu takalmi, tafiya take tana surutu tare da tonawa kanta asiri akan abunda tayiwa Mamy, hauka sosai Mama tayi gashi Haukar tata mai dariya ce.


   cikin rugar kuwa, ko ina lungu da saƙo ansa cewa mamace tayiwa Mamy asiri ta shigar da ita duniya, kowa Allah wadarai yake da halin Mama, tare da ƙara binta da baƙar Addu'a.


   Allah sarki rayuwa, ƴar gwal tayi baƙi ta rame, tsabar baƙar wahalar da take sha a gidan junguɗo, duk randa yasha ya bugu, to ranar kuwa ƴar gwal zata ci ɗan banxan duka wajen junguɗo, bayan ya gama dukan nata, ya kela amansa a tsakar ɗakin koko kan gadon ta, kuma dole ta kwashe. 

   Ga tsangwaman Uwar miji da take fama da ita, duk wani aiki mai wahala na cikin gidan ƴar gwal ake haɗawa, tsabar wahalar da take sha yasa cikin jikinta zubewa, gashi bata isa tace baza tayi ba, idan junguɗo ya dawo a sanar dashi, yaci ubanta la'ada waje, gorin Abunda uwarta tayi kuwa kullum sai an mata, shi cikin gidan manya da yara.

  Gaskiya ƴar gwal tana cin baƙar azaba a cikin wannan gidan Auren nata.


rayuwa kenan, Abunda kake yiwa wani yau gashi ya dawo kanka, ada Yar gwal itace ke taka Nasreen yau gashi itama wasu na taka ta, son ransu, shiyasa ita rayuwa, ka bita a sannu, domin kuwa *DUK ABUNDA KA SHUKA SHI ZAKA GIRBA IN KAIRAN KAIRAN IN SHARRAN SHARRAN ALLAH KASA MUFI ƘARFIN ZUCIYAR MU.*


       *GOMBE STATE*


 Yau Watan Zuhura biyu a gidan su babu khabeer babu labarin sa, mahaifin Zuhura kuwa ya kira NUMBER khabeer, bata tafiya, har office yaje, sai ace masa khabeer baya nan, haka ma gidan sa, idan yaje nan ma cemasa ake khabeer baya nan.


  Khabeer kuwa shine yasa NUMBER mahaifin Zuhura a Black list ya kuma umurci ma'aikatan sa, daga na gida har office da cewa idan mahaifin Zuhura yaxo suce masa baya nan, Saboda baya son ya kirasa maganar Zuhura, bazai iya ce masa bazai dawo da Zuhura gidan sa ba, saboda yana mungun kunyar tsohon, Saboda Dattakon sa.


  Yanxu umma mahaifiyar Zuhura ta juya mata baya, a cikin sati biyu kacal, kullum cikin mita take yiwa Zuhura, ga kuma sake mata aiki da Umma tayi, itace wanke wanke shara wanki, Abunda bata yinsa kenan, cikin gidan Auren ta, komai mata ake tana daga zaune, Naira biyar da Zuhura zata kashe yafi ƙarfin ta, domin kuwa duk zamanta gidan khabeer bata tara kuɗi ba koda ta ɗebo mahaifiyar ta take bawa, sai yanxu Zuhura ta *banbance tsakanin aya da tsakuwa tabbas yanzu ta gane cewa komai kashin gidan mijin ka, yafi maka gidan ubanka, gashi tun yanxu ta fara gani, mahaifiyar ta da ada take sonta gashi yanxu ta juya mata baya, saboda yanxu bata dashi, batama damu da al'amarin taba ma, bare taji tausayin ta, Hatta Leemat ƙanwar ta, ma rashin mutunci take Mata, a yanxu Zuhura tana son komawa gidan mijinta, koda kuwa da mata biyu ne, ita ta Uku ta shiryawa komawa, tabbas ta gane cewa, Rayuwa sai kana dashi ake yi dakai*.


  Sai dai Abunda Zuhura bata sani ba, shine bata gaban khabeer kwatakwata, kuma bawai baya sonta bane a'a yana son matar sa, kawai halinta ne, ya tsana.



  Hajiya kuwa ta gyara Nasreen daga ciki har waje, Nasreen tayi wani mungun kyau bazaka ganta kace daga cikin Ruga ta fito ba, acikin wannan wata biyun, Hajiya babu kalan gurkin da bata koyawa Nasreen ba, har asibiti suka je aka yiwa Nasreen wankin haƙori, sosai Nasreen tayi kyau, har yau Hajiya taƙi bari khabeer yaga Nasreen.


  Yau tun safe khabeer ke gidan Hajiya a cewar sa yana son ganin Nasreen, zasuyi magana kan karatun ta, daƙyar Hajiya ta yadda tabar khabeer yaga Nasreen.


  A hankali take takowa cikin nutsuwa, da tafiya mai tafiya da Zuciyar wanda ke kallon ta, tana sanye da doguwar riga ta material mai Adon pink color, ta yane fuskar ta, da Pink ɗin gyale, tun sanda take tahowa khabeer yake kallon ta, ko'a Zuciyar sa, baiyi zaton Nasreen ɗinsa bane, kallon Ƴan India yake mata, domin kuwa Nasreen ba ƙaramar dirarriyar mace bace, doguwa ce, mai matsagaicin jiki, tana da hips masu ɗaukar hankali, idan tana tafiya suma kansu juyawa suke, ƙirjinta a cike suke da boobs kuma tsaye suke ƙyam tana da ɗan faɗin fuska kaɗan tare da ɗan ƙaramin baki, tana da manyan idon farare tas gashin idon ta zarara tsayayyu, gashin girar ta kuwa kamar wanda aka zana mata, tana da tsayin gashin kayi, tare da ɗan yawa kadan.


  Sanda ta iso gaban sa tayi sallama sannan khabeer ya gane Zuhura da Muryar ta, kusan suman tsaye khabeer yayi, yanda yaga Nasreen ta zama big girl cikin ƙanƙanin lokaci, harma ta zarce Nabiya kyau nesa ba kusa ba, dariya SADIQ yayi tare da dukan kafaɗar khabeer, yace.


  " Kai malam dawo cikin hankalin mana, naga kamar kayi nisa da yawa.


  Hararar SADIQ khabeer yayi tare da amsawa Nasreen sallamar ta, Gefen kujerar da khabeer ke zaune Nasreen ta zauna, tashi SADIQ yayi yana cewa, bari na bawa ma'aurata waje, na tafi wajen tawa matar.

 Murmurshi khabeer yayi tare da girgiza kansa.

 Gaishe da khabeer Nasreen tayi cikin girmamawa, amsawa yayi tare da cewa jiya yaje rugar su, wajen Baba, ya karɓo takaddun, makarantar ta, harda na Nabiya, yace.


  " Nayi zaton bakiyi Secondary school ba, sai Baba yake sanar dani cewa kinyi, yanxu ga Admission na karbo miki, harma nayi registration, yanxu Abunda ya rage kawai ki fara zuwa ne.

Sai dai na miki rigima ta wajen zaɓa miki couse, Low na cika miki Allah yasa dai ban miki rigima ba.


  Murmurshi Nasreen tayi cikin farin ciki da murna, a rayuwar ta, bata san dame zata sakawa khabeer ba, domin kuwa yayiwa Rayuwar ta hallaci, ya rabata da Auren mashayi, ya gwammace ya Aure ta, duk da tana ƴar ƙauye, baiji ƙyankyamin Auren ta ba, haka kuma iyayen sa, suka yiwa nata mahaifiyar Hallaci, ta hanyar riƙeta bisa Amana, tun bata san inda hankalin ta yake ba, har ya dawo jikin ta, tabbas tayiwa Rayuwar Alƙawarin riƙe Auren khabeer bisa Amana, tare da masa biyayya iya ƙarfin ta.

 Muryar khabeer da taji yana cewa. 


  " Kinyi shuru ko couse ɗin bai miki ba ne.


  Murmurshi Nasreen tayi tace.


  ' yamin sosai na gode Allah ya saka da Alkairi.


" Ameen khabeer yace, yana mai ƙarewa Nasreen kallo kamar wanda zai haɗiye ta, sun ɗan juma suna taɗi jifa jifa kasancewar Nasreen ta kasa sakin jiki dashi.



 Daddy kuwa ya saka ranar da Mamy zata koma rugar su, cikin satin da za'a shiga, wanda aka yanke shawarar cewa zasuje harda nemawa SADIQ Auren Nabiya, domin kuwa daman mahaifin SADIQ suke jira kuma gobe zai dawo.

 

  

      *RUGAR ARƊO*


  Alhamdulillah yau su Mamy suka sauƙa a cikin rugar su lfy wanda harda su Nasreen, cikin tafiyar, mota Uku sukayi, khabeer da Nasreen da SADIQ motar su ɗaya, sai Daddy da momma tare da mamy da Khalid suma motar su ɗaya, sai Hajiya da Alhaji mahaifin SADIQ, da kuma khady suma tasu motar ɗaya. 

  Daddy sun yiwa Mamy tara ta arziki sosai dan abinci ma mota guda suka cika mata shi, parking sukayi ƙofar gidan su Nasreen ɗin, su Nasreen ne suka fara sauƙa sannan sauran ma suka sauƙa kallon, rugar Mamy take, cikin ganin ta sauya mata, har cikin gidan suka shiga tare da Sallama, Goggo dake zaune tasa, Baba gaba da zagin cewa ya sayar da Nasreen gashi yanxu ko labarin ta, babu, taji Sallama.


  Amsa Sallamar Goggo tayi tana ƙare musu kallo domin kuwa babu wanda ta shaida cikin su, sanda suka ƙaraso ne, Baba ya tashi a firgice yana nuna Mamy da yatsa yana cewa.


  " Maimuna kece nake gani, koko idona ke min gixo?


  " Itama goggo a razane take kiran sunan Mamy, gani take Kamar ƙarya idonta ke mata.


 Murmurshi Mamy tayi tare da shimfiɗa musu taburma data gani jingine jikin bango, suka zaune sannan tace.


 " Nice Mlm Allah yayi dawowata.


  Zama Mlm Musa yayi tare da ɗaga hunun sa sama yana mai godewa Ubangijin sa, daya dawo masa da matarsa gida lfy.


  Mamy ce tace akwai baƙi maza a waje, take sanar da Mlm Musa.

Tashi yayi tare da zuwa ya shigo dasu.


 Bayan an gaisa ne, aka fara yaushe gamo, tare da bada labarin Abunda ya faru a baya, sosai suka fahimci juna, haka Goggo ta nemi tafiyar su, Nasreen, sannan ne suke sanar dasu Mamy Abunda ya samu mama da kuma wahalar Auren da ƴar gwal take sha wajen junguɗo, sosai su Mamy suka tausayawa Mama, tare da fatan Allah ya bata sauƙi.

  

 Cikin lokaci ƙankani labarin dawowar Mamy ya cika rugar, kowa ƙoƙari yake yaxo yaga Mamy.


  Alhamdulillah Mlm Musa ya bawa SADIQ Auren Nabiya inda suka sharti sati biyu rak, godiya sosai Daddy sukayi, shine ma ya cire dubu ɗari yace ga sadakin na biya ya biya, cikin mutunci da girmamawa, su momma suka dawo daga rugar su Nasreen tare da barin su acan, akan cewa, sai ranar Aure za'a dawo dasu, za'a haɗa shagalin bikin Nabiya dana Nasreen.



  Zuhura kuwa kullum tana kiran NUMBER na khabeer baya ɗauka, ta mishi text ba iyaka amma Babu ko reply, duk da haka Zuhura bata haƙura, tana neman khabeer.


 Domin kuwa rayuwa ta mata ƙunci wahala take sha cikin gidan nasu, harta abinci bata samun wanda ranta yake so, ita yanxu burin ta, ta ganta ta dawo gidan mijinta.



  Hausawa sukace Rana bata ƙarya sai dai uwar gijiya taji kunya, yau dai Allah cikin ikon sa, ake ɗaura Auren SADIQ da Nabiya, sosai Mamy tayiwa yaran nata nasiha, akan zaman Aure, tare da jaddada musu Halaccin gidan da zasu zauna na auren su.


    gagarumin shagali, SADIQ da khabeer suka shirya wanda za'ayi a Ammar Hole.


  bayan ɗaurin Auren ne  da yamma,  ƴan uwan su Nabiya dake cikin rugar harma da abokan arziki suka rankayo zuwa birni.


  Kasuwa biyu sukayi waɗanda suka hau motar su SADIQ akayi gidan Hajiya dasu, waɗanda suka hau tasu khabeer kuma akayi gidan su khabeer dasu.


  Karɓar mutunci aka musu, yayin da ƴan rugar su Nasreen suke ta faman nuna ƙauyancin su, Indo kuwa ƙawar Nasreen tana maƙale a gefen Nasreen.


Aunty Sadiya ƴar ƙanwar momma itace ta yiwa Nasreen shirin zuwa dinear wanda zasuyi ƙarfe tara na dare, cikin wani baƙin boyel mai ratsin ja, Aunty Sadiya ta shirya, Nasreen yayin da tasha makeup na gani a faɗa, gaskiya Nasreen tayi kyau sosai, jan mayafi aunty sadiya ta yafawa Nasreen, suka zauna jiran zuwan Ango.


  Khabeer kuwa suna zaune dasu sadiq a main falon sa, yayin da junior ke maƙale a gefen sa, yaji shigowar text, da kamar bazai duba ba, yana dubawa kuma sai ga text ɗin Leemat ne ƙanwar Zuhura tana ce masa 



   " Zuhura tana kwance tun safe bata da lafiya sai suma take, sun kaita asibiti, yanxu haka tana asibitin nasarawa, rai a hanun Allah,.

  Allah sarki tsakanin Mace da miji sai Allah, take khabeer ya gigice ya tashi a firgice yana ƙoƙarin fita


 SADIQ ne yace bawan Allah ina zaka kana ganin times ɗin dinear yayi.


  " Bashi bane a gabana yanxu, Zuhura tana can asibiti Babu lafiya, wajen ta zanje, ni na fasa nawa dinear, kai kayi kawai.


  Kallon shi SADIQ keyi baki buɗe, haka khabeer ya fice yayi wajen Zuhura.



  Tana kwance kuma a gadon asibiti, sai famar rawar ɗari take, da alamu zazzaɓi ke damunta, amma likitoci sunce harda damuwa yake damunta, khabeer yayi mamakin yanda yaga Zuhura ta rame tayi baƙi lokaci kaɗan, buɗe idon ta, Zuhura tayi da kyar tana cewa ina son zanyi magana da khabeer.


  Ficewa su Leemat sukayi, da Umma suka barsu su biyu cikin ɗakin, a hankali Zuhura ke riƙon khabeer akan ya yafe mata ya maida ita gidan ta.


  Sosai khabeer ya tausaya mata, sai dai koda zai maida Zuhura gidan ta, ba yanxu ba, sai ta ƙara hankali tukunna, kallon ta yayi tare da cewa.


   " Naji zanyi tunani tukunna, kafin na yanke shawara,.

  Khabeer shine ya biya komai na maganin Zuhura, bai bar asibitin ba, sai wajen sha ɗaya na dare.



  Wajen dinear kuwa, SADIQ, ne ya ajiye Khalid a madadin khabeer, tare da bawa waɗanda suka zo dinear haƙuri na rashin ganin khabeer, sakamakon kira gaggawa da aka masa wajen aikin sa, ya musu ƙarya da haka, ita kanta Nasreen a haka ta ɗauka, domin bata san wajen matarsa yaje ba, haka akayi dinear aka watse ba tare daya musu daɗi ba.



  Shiko khabeer tun komawar sa, gida yake ji a ransa, baiyiwa Nasreen daidai ba, yasan bazata ji daɗi ba, na rashin ganin sa wajen dinear, kiran SADIQ yayi a waya, bayan SADIQ ya ɗaga ne khabeer ke tambayar da, ya sukayi dinear.


  Wanke sa SADIQ yayi tas tare da sanar dashi ƙaryar daya sashi yiwa mutane.


 Dariya khabeer yayi tare da cewa.


  " Ka kyauta ai, Wlh ji nake kamar ban kyauta mata ba.



   Dariya SADIQ yayi yace.



  " Akan zakaji haka, bayan kace, baka aureta dan ka zauna da ita ba, tunda kace sakin ta zakayi.



  Dariya khabeer yayi tare da cewa.


  " Haba SADIQ wani mai hankali ne zaiyi gangancin rabuwa da Nasreen a matsayin matar da zai zauna da ita.

   A gaskiya yanda bake ji yanxu a cikin zuciyata Aure na da Nasreen mutu ka rabane...............




*Share*

     *And*

*Comments*



  *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


  *(Ummu Nasmah)*

[1/16, 8:41 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻



  *KUYI HAƘURI*


 *Indo a birni fan's, bawai naƙi muku typing ɗin Indo a birni bane, a'a bani da times ɗin da zanyi typing book biyu a rana ɗaya ne, aiki yamin yawa, idan ban manta ba, saida na jera kwana Uku ina typing ɗin INDO A BIRNI banyi typing ɗin Sara da sassaqa ba, shine naga suma ya kamata nayi musu typing kuyi hkr zakuji ni gobe da 10 Read more na Indo a birni insha Allah*🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪



*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



*P*•••••••6️⃣8️⃣ to 6️⃣9️⃣


Dariya sosai SADIQ yayi sannan yace.


  " Daman ai kallon ka kawai nake, nasan duk sanda yarinyar nan ta shigo gari, bazaka iya rabuwa da ita ba.


  Dariya shima SADIQ yayi tare da cewa.


  " Yau naji rashin kunya wajen SADIQ surukar taka kake kira da yarinya, lalle SADIQ baka da kunya, to wlh daga yau ka fara girmama mu, domin yanxu mu yayunka ne, ya ƙarasa maganar cikin zolaya.


  Dariya SADIQ yayi tare da cewa.


  Lallai ashe baza'a girmama kuba, yawwa sorry ban tambaye ka jikin matar ka, Zuhura ba.


 " Hmm SADIQ Zuhura bata da lafiya sosai gaskiya, duk ta fita hayyacinta, tana cikin damuwar rashi na, kusa da Ita, ni kaina banji daɗin yanda naga Zuhura ta koma ba.


  Ajiyar Zuciya SADIQ yayi tare da cewa.


  " To sai ka maida ita kawai, tunda kana son matar ka, amma sai dai gaskiya ina tunanin zaman Zuhura da Nasreen gida ɗaya, akwai matsala gaskiya domin kuwa Zuhura bata da mutunci.


  " A'a Sadiq ba waje ɗaya zasu zauna ba, ai kowa da part ɗinta, d'azu ma suka gama shirya part ɗin nata, duk da ban shiga na duba ba, amma dai gaskiya koda zan dawo da Zuhura ba yanxu ba, dole sai tayi hankali tasan meye rayuwa, ya kuma zaman cikin ta, yake, yanda koda ta dawo baxata, ɗaga min hankalin gida ba.


  " Hakan ma daidai ne, dan gaskiya Zuhura sai a hankali, Allah dai ya ganar da ita gaskiya ya shurye ta.


  " Ameen SADIQ ina Amarya Nabiya, yau naso ganin rawar kanka, wajen dinear ai sabon shiga, ɓarawo da Sallama.


  " Dariya SADIQ yayi sannan yace, ina kuwa zaka gani tunda ka gudu wajen uwar gida, sarautar Mata, ni kaga bari na gudu sai da safe.



  Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


  " Allah ya tashe mu lfy ango na Nabiya.



  Nasreen kuwa suna zaune da indo suna hira kowa yayi bacci ya barsu, kallon Nasreen Indo tayi tare da cewa.



  " Kinga abunda nake gaya miki koh, cewa Allah bazai barki cikin ƙunci ba, wata rana sai labari, to gashi yanxu wahalar da Mama ke baki ta zamo tarihi, Nasreen ki riƙe kwaɗo bisa Amana, domin ya taimaki rayuwar ki, ki yiwa iyayen sa, biyayya kamar sune suka haife ki, kiso ɗansa tamkar ɗanda zaki haifa, ki girmama Uwar gidan sa, dai-dai Misali, karki raina ta, sai idan kinga, itace ta raina kanta, nasan ke mai haƙuri ce, ki ƙara a kan wanda kike dashi, tabbas zaki zama abun alfahari, a idon kowa.



  Cikowa idon Nasreen yayi da hawaye, ta kamo hanun Indo tace.


  " Ke ƙawace ta gari Indo, tabbas da duka ƙawaye haka suke, da rayuwar Auren mu bazata samu tangarɗa ba, ƙawaye da yawa sune suke, taimakawa wajen tarwatsa Auren ƙawayen su, sai gashi yanxu Indo kece kike bani shawara yanda zan zauna cikin gidan aurena cikin, farin ciki, tabbas ke ƙawace ta gari, wacce zanyi alfahari dake, a cikin rayuwata, tabbas kin bada gudunmawa a cikin rayuwata, bazan taɓa mantawa dake ba, na gode sosai Allah ya saka da Alkairi.


  Murmurshi Indo tayi tare da cewa.


  " Ameen ya kamata mu kwanta kinga dare yayi fah.


  Kwanciya sukayi Amma ita dai Nasreen bacci bai ɗauketa da wuri ba.


  Washe gari da safe momma da kanta ta shigo ɗakin ɗauke da ƙaramin Kula a hunun ta, da kuma wani ƙaramin, jug, kusa da Nasreen ta zauna, Yayin da Nasreen ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin kunyar momma ta gaishe ta, su Indo ma gaishe ta sukayi, ɗago kanta momma tayi tare da cewa.


  " Nasreen ya kamata fah ki daina jin kunyata domin ni uwace a wajen ki, ba suruka ba, ki ɗago kanki ki kalleni.


   ɗago kanta Nasreen tayi, cikin jin kunyar momma.


  Murmurshi momma tayi tare da miƙa mata kulan tare da cewa maza cinye yanxu ki bani kwanon karki tauna ƙashi naman kawai zaki ci, ina Zaune a nan.

 Karɓa Nasreen tayi tare da ƙarewa naman barun kallo wanda yasha garin magani, a hankali Nasreen kecin naman duk da bata san maganin meye bane, sanda ta ci ya kusa rabi sannan ta ajiye, miƙa mata jug ɗin momma tayi tace, shanye shi shima maza.

 Daƙyar Nasreen ke iya haɗiye ruwan cikin jug ɗin mai shegen baurin tsiya, sannan ta muƙowa momma jug ɗin karɓa momma tayi tana Cewa yawwa ƴar albarka, bari a turo muku, breakfast naku koh.


 Kallon Innah Asabe tayi tace 


  " Innah Asabe ko zaki taimaka muje ki karya cikin ɗaki nah.


  Dariya Innah Asabe tayi, Cikin jinjinawa karanci irin na momma, tare da tashi tace, muje mu to.


  Da misalin ƙarfe 1 na azhar, momma tasa idi drever ya ɗauki su Innah Asabe ya kaisu suga ɗakin Nasreen, kasancewar da la'asar zasu koma ƙauyen su, ita kuma Nasreen sai dare khabeer zaizo ya tafi da ita, sai sun jira Daddy.

 Tace daga nan ya shige dasu gidan Hajiyar su SADIQ suga ɗakin Nabiya, za kuma ta ƙara hadasu da wasu yan garin su, Nasreen ɗin suje suga ɗakin Nasreen d'in.


  Haka kuwa akayi idi drever har gidan ya kaisu tare da ƙarbar key wajen John suka yi part ɗin Nasreen wanda yake jere dana Zuhura.


  Wow tabarakallah masha Allah, ɗakin Nasreen yayi mungun haɗuwa, komai na falon, black and white ne, hatta labulen ɗakin, Babu Abunda Babu na more rayuwa cikin ɗakin, sai kuma cikin uwar ɗakan ta, shi kuma, Pink and white, yayi kyau sosai cikin ɗakin nata, haka ma kitchen ɗin ta, shi Kuma komai green ne, gaskiya gidan Nasreen ya haɗu Babu laifi, ƴan ƙauye sunsha ƙauyanci tare da shafe+ da kalle+ kafin akayi gidan Hajiya dasu.


  Cikin mutunci da girmamawa Hajiya ta karɓe su, tare da musu iso zuwa ɗakin da Nabiya take, tana zaune tsakiyar fado, ita dasu khady da ƙawayen khadyn sai shashewar su, suke, kasancewar Nabiya Babu baƙonta cikin gidan kowa kallon ɗan uwa take masa, sun ɗan juma cikin gidan kafin Hajiya tasa aka kaisu, Federal Lowcourst inda Sadiq yayi ginin sa, inda kuma Hajiya ta mata setting ta, itama Nabiya nata ɗakin yayi kyau Babu laifi, duk da bai kai ɗakin Nasreen tsaruwa ba, ita komai nata na ɗakin, Ash color ne har cikin uwar ɗaka zuwa kitchen ɗinta, komai ash.

  Daga nan gidan su khabeer aka dawo dasu.


  Karfe huɗu dai dai khabeer yaxo cikin gidan nasu tare da motacin abokansa, wanda dasu za'a kai jama'ar Ƙauyen, har cikin falon su, ya shiga, yayin da abokanan wasa keta famar tsokanar sa, ɗakin momma ya shiga ya samu suna zaune ita da Aunty Kubra ƙanwar momma, gaishe da su yayi, Aunty Kubra ne tace, xoka samu waje ka zauna anan daman neman ka nake.

  Zama gefen ta khabeer yayi yana dariya.


 " Kaga khabeer, faɗa nake so to maka, akan Auren ka, na farko da kuma auren da kayi yanxu.



  " Ina jinki Aunty na.


  " Khabeer ka dawo da matar ka, Zuhura kodan albarkacin ɗanta, duk da nasan halin Zuhura bata da kirki, amma kayi hkr, ka dawo da ita, kodan albarkacin Dattakon  mahaifin ta, kwanakin baya taxo har gida na, a yanda ta nuna min tayi nadama sosai.

 Ita kuma wannan Amaryar taka, karka sake ta biyo bayan Zuhura, ka nuna mata muhimmancin iyayen ka, saboda kar ta raina maka su kamar yanda Zuhura ta raina su, Abunda nake son sanar dakai kenan.


Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


  " Insha Allah Aunty, Nasreen bata daga cikin matan da zata raina na gaba da itama bare kuma iyayen mijinta ina da wannan tabbacin a raina.


  Momma ce tace.


  " Tabbas nima ina da wannan tabbacin akan Nasreen, Allah dai ya baku zaman lafiya, Daddyn ku, yace kaxo ƙarfe takwas na dare ka tafi da matar ka, amma yace ko bai samu dawowa da wuri ba ka jirasa.


  Da to khabeer ya amsa sannan yace.


  " Momma idan muna waje muna jiran su, saboda na karbi motar su, Abbas ne.


 " Okay ina ga summa shirya bari a musu magana.


  Nasreen tana kuka, ƴan uwan ta suka tafiya suka barta, khabeer kuɗi ya basu cash dubu ɗari biyu yace suyi tsaraba.

  Sunji daɗi sosai yanda khabeer da iyayensa suka musu mutunci, haka suka tafi suna son barka.


  Da daddare misalin ƙarfe 8 khabeer ya shigo cikin gidan, nasu a falo ya zauna, kasancewar ya samu Momma da Aunty Kubra a falon, tashi momma tayi, taje kiran Daddy yayin da Aunty Kubra ta shiga fito da Nasreen.


  Kanta a ƙasa ta shigo cikin falon tare da zama a kasa, gaishe da daddy tayi kanta sunkuye ya amsa, sannan ne Daddy yayi gyaran murya, ya fara magana kamar haka.


  Alhamdulillah khabeer yau dai gashi Allah ya ƙara ɗaura maka wani kiwon a kanka, ya azurta ka, da kara aure a karo na biyu, to ina son na sanar dakai cewa Hadith ne guda da yake cewa dukan ku masu kiwo ne, kuma kowa za'a tambaye sa, akan kiwon da aka basa, matar ka ƴaƴan ka, suma kiwo ne a wajen ka, dan haka sai kayi da gaske wajen kula da iyalan ka, khabeer ka zamo mai adalci tsakanin matan ka, kar soyayyar ɗaya daga cikin su ya rinjaye ka, ka cuci ɗaya, idan har ka kasance daga cikin masu rashin adalci tsakanin matan ka, to tabbas zaka tashi ranar gobe ƙiyama da ɓarin jiki ɗaya a shanye, sannan ina mai umurtar ka, da acikin watan nan ka dawo da matar ka, Zuhura domin darajar mahaifin ta, yazo har gida ya same ni, kan maganar, na kuma amsa masa da cewa, zaka dawo da ita.


  " Insha Allah Daddy zan dawo da ita, duk da bana jin daɗin zama da Zuhura amma zan dawo da ita, saboda albarkacin ku, amma Wlh daddy banyi niyan dawo da Zuhura nan kusa ba, naso sai ta shekara biyu a gidan su, amma tunda kunyi magana zan dawo da ita.

  Kuma insha Allah zan zamo mai adalci tsakanin su, insha Allah.


  "Yawwa Allah ya maka albarka, kallon Nasreen Daddy yayi tare da cewa.

  Ƴata, na dawo gare ki, ina son ki kasance mai biyayya ga mijin ki, karki yadda wani ƙaramin Abu ya shiga tsakanin farin cikin ku, ki zure ko wani irin abu domin farin cikin ku, ki zamo mai riƙe sirrin mijin ki, ki kasance mace mai tsafta tare da iya girki, kiso ƴan uwan sa, kamar yanda zaki so naki, ki kasance mai hakuri da duk wanda kike zaune waje ɗaya dashi idan kikayi haka tabbas kin dace a cikin rayuwar ki, za kuma ki zamo mafi soyuwa a Zuciyar mijinki, ban miki wannan nasiha a matsayin suruki ba, na miki shine a matsayin Uba.


  Godiya sosai Nasreen tayiwa daddy, kuma nasihar sa, ta shiga jikin ta, sosai.


  Itama momma sosai ta musu nasiha ita da Hajiya Kubra, sannan khabeer ya ɗauki matar sa suka tafi, a hanya khabeer ya tsaya ya sayi kazar sa, da ɗan drinks.





  Wayyo Allah Wlh banso na tsaya a nan ba, naso nayi typing mai yawa sai dai Wlh yau bana jin daɗin jiki na, kuyi hkr da wannan.

 Ban samu nayi editing ba, idan kunci karo da typing error kuyi hkr.



*Share*

*And*

   *Comment*



  *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


  *(Ummu Nasmah)*

[1/21, 5:07 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*



*Tallah Tallah Tallah*


Ina kuke makaranta littattafan Hausa to ku matso kusa ga dama ta samu shahararriyar marubuciyar nan taku *ZARAHN ABDUL MOMYN AHLAN*

 wacce ta saba nishadantar daku, cikin daɗaɗan litattafan ta, irin su, *GUDU A JEJI SHUHUDA NIDA ƘANNAN MIJI NA* a yauma ta sake dawo muku da wani sabon salon labari wanda zai nishad'antar daku, mai taken *WAYA KASHE ZAHRA'U* acikin farashi ƙalilan, Naira 200 kacal zaki bayar kisha karatun ki, cikin nishaɗi, karku bari a baku labari, duk sanda zata sake Free page, zata ajiye muku Account Number, tare da Number waya.

  Sai mun jiku.

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*P*•••••••7️⃣0️⃣ to 7️⃣1️⃣


Part ɗin Nasreen khabeer ya wuce da ita darect, ɗakin daya kasance shine bedroom ɗinta suka shiga, Nasreen bin cikin ɗakin take da kallo, domin kuwa ɗakin ya mata kyau sosai, bayan sun zauna ne, khabeer ya umurci Nasreen da tayi Alwala suyi sallar nafila raka'a biyu, hakance kuwa ta kasance Alwala Nasreen ta ɗauro, sannan shima khabeer ya shiga ya ɗauro nasa Alwalar, bayan sunyi sallar ne, khabeer ya kama goshin Nasreen tare da jero addu'oi sosai yayi addu'a, sannan ya sake goshin nata, tambayoyi khabeer yayiwa Nasreen game da fiƙihu, alhamdulillah duka Nasreen ta amsa masa tambayoyin sa, shi kanshi khabeer yana mamakin sanin addini Irin na Nasreen wacce ta fito cikin ƙauye kuma ƙauyen ma rugar Fulani, ledar kazar ya jawo tare da ɗauko filet ya juye, Bismillah yacewa Nasreen, sunkuyar da kanta ƙasa Nasreen tayi tare da cewa.


  " Na ƙoshi.


 Murmurshi khabeer yayi, domin kuwa yasan, ba wani ƙoshin da tayi, kawai fulako ne irin na fullo, domin kuwa bazata sake taci abinci a cikin gidan nasu ba.


  " Kinga Nasreen kifa ci kazar nan karki kwana da yunwa, domin kuwa nasan baki wani ci abinci a gida ba.


 Ƙin ci Nasreen tayi, sai da khabeer ya matsa mata tukunna, taci kaɗan wacce bata wuce cinya ɗaya ba, drinks ɗin ma kurɓa tayi ta ture plate ɗin gefe alamun ya isheta.

  Murmurshi khabeer yayi ganin yanda Nasreen take takure dashi, tashi yayi tare da buɗe Wadrop ɗinta, ya ɗauko mata wasu Arnan sleeping dress, waɗanda su da Babu ɗaya suke ya ajiye mata, tare da cewa taje tayi wanka ta sasu a jikin ta, shi zai koma ɗakin sa.


 Bayan fitar khabeer ɗin ne, Nasreen ta ɗaga rigar baccin tare da juyasu tana tunanin yanda zata fara sakasu jikin ta, ita gani take, bazata iya sasu a jikin ta, ba domin kuwa da kunya tasa waɗannan kaya.

  Sai kuma tayi tunanin nasihar Ammin ta, da take Cewa.


  " Nasreen ki yiwa mijin ki biyayya duk abunda ya saki kiyi masa muddun bai saɓawa Shari'a ba, domin kuwa Aljanar ki, tana ƙarƙashin ƙafarsa, bijere masa masifa ne gareki.



  Jikin ta ne, yayi sanyi, sannan ta ɗauki kayan tayi tollet dasu.


 Brush Nasreen ta fara sannan ta ɗaura wanka, tsame jikin ta tayi da towel, sannan ta saka kayan tare da saka ƙatuwar hijab ɗinta, ta fito, mirror ta nufa ta mulke jikinta da mai, tare da ɗaukar humra wanda Hajiya ce tayi mata, ta mulke dukan lungu na jikin ta, dashi, wani ƙaramin turare ta ɗauko wanda shima Hajiya ce, ta bata na shafawa a matsi matsin jiki, mai bala'in ƙamshi, shima ta shafa, wani ƙamshi shi kanshi ɗakin ya ɗauka, barema kuma jikin ta, maida hijab ɗin tayi jikinta, sannan ta kwanta bisa gadon ta, tare da duƙunƙunewa cikin hijab ɗin, sai kuma ta tafi tunanin duniya, tare da tariyo rayuwar ta, ta baya, a haka bacci mai nauyi ya ɗauketa.


  Shi kuwa khabeer, bayan ya gama shirin Baccin sane, ya jawo system ɗinsa, ya buɗe ya jima sosai akan system ɗin kafin ya sauƙa, agogon bangon dake manne cikin ɗakin, ya ɗaga hansa ya duba, 11:05 Zuhura ce ta faɗo masa cikin ransa, haka kawai ya tsinci kansa dason kiranta yaji yanayin jikin ta, ringine ɗaya kuwa Zuhura ta ɗauka, kamar wacce take jira ya kira, tana ɗagawa kawai saita fashe masa da kuka.


  Runtse idonsa khabeer yayi, dan baya son jin kukan mace a rayuwarsa, mussaman ma ace macen da take da gurbi cikin Zuciyarsa.


  " Please Zuhura, dan Allah kibar kukan nan, kinsan dai bana son jin kukan ki, koh.


  Cikin kukan Zuhura tace.


  " Abban junior Dole nayi kuka, saboda baka sona yanxu, ka maida hankalin ka, akan matar da ka aura, ka mantani cikin rayuwar ka.


  Murmurshi khabeer yayi, gano kishi ne, cike fal yake damun Zuhura, Zuhura Sarkin kishi.


  " Kindai san cewa, maganar cewa bana sonki, bai taso ba Zuhura, ke kanki shaidace akan irin soyayyar da nake miki, sai dai Halinki ne bana so Zuhura, sam Halinki baida kyau, dalilin daya sani rabuwa dake kenan, koda zan maida ke gidana, Zuhura dole sai kin sauya Halinki, muddun baki gyara Halinki ba, Zuhura dole ne mu rabu rabuwa Kuma ta har Abada, *ZAƁI NA GAREKI ZUHURA, KO KI GYARA HALINKI KU ZAUNA LAFIYA DA ABOKIYAR ZAMAN KI, KO KUMA KIƘI SAUYA HALINKI MU RABU RABUWA TA HAR ABADA*. Wannan shine gaskiyar lamari, dan baxan iya zama dake ba Zuhura,  kina ɗaga min hankali kullum ba, iyayena basu tsira ba, haka kuma itama Nasreen dana aureta bata tsira wajen ki ba, baxan iya ɗaukar wannan ba, yanxu kam.


  " Abban junior, ko a yanzu naga darasin rayuwa, na gane kuskurena, na gane cewa idan baka dashi ko iyayen ka, ma sai kaga sauyi a tare dasu, Abban junior ada mahaifiyata tana marmarina Saboda ina dashi ina kawo mata, haka mijina yana bata, ayau da aka wayi gari banda komai, Umma na ta juya min baya, kullum tana cikin hantara ta, da kuma haɗani da dukkan ayyukan gidan, saboda kawai bandashi, Ada duk abunda nake aikatawa a gidan mijina itace take Sani, mahaifina shine kawai yake rarrashi na, ko dama can shine yake min faɗa na zauna lafiya a gidan Aure na, haka kuma yanxu shine yake min nasiha da rarrashina, khabeer na shuryawa zaman lafiya cikin gidan ka, koda kuwa da mata Uku zan zauna, Please Abban junior, ka dawo dani gidana.


  Murmurshi khabeer yayi, haƙiƙa yaji daɗin yanda Zuhura tayi sanyi lokaci ɗaya, *ALLAH DAI YASA BA TUBAN MUZURU TAYI BA*.


  " Shikenan Babu damuwa zanzo gidan naku, ko zuwa jibi, zamu tattauna yanxu dare yayi, kinga har 12:09pm zan kwanta.


 Cikin murna da farin ciki, Zuhura sukayi Sallama da khabeer, domin kuwa yanxu gidanta take son komawa, ta gaji da wahalar da Umma ke sata kullum cikin gidan nan.


  Tashi khabeer yayi, tare da nufar ɗakin Nasreen, duk da yasan yanxu tayi nisa, cikin bacci, sai dai zuciyar sa, bazata iya haƙura da Nasreen ba, yanda yake lissafo surar ta, haka yake jin wani irin felling na ɗaukar sa, tura ɗakin yayi, ya shiga sannan ya sawa ƙofar key, tana kwance duƙunƙune cikin hijab, ganan bargon kuma ta barshi gefe, murmurshi khabeer yayi tare da kwanciya gefen ta, yana ƙarewa fuskar ta, kallo, ita ko Baccin ta, takeyi Hankali kwance, ahankali khabeer ke yaye hijab ɗin Nasreen, har yayi nasarar kawo ta, wuyan ta, juyin da Nasreen tayi shine ya bawa khabeer nasarar cire hijab ɗin gaba ɗaya daga jikinta, wohoho kusan suma khabeer yayi ganin yanda halittar jikin Nasreen yake, tun daga yatsan ƙafarta yake ƙare mata kallo har yaxo kan Santala-Santalan cinyoyinta ƙugunta ya ƙarewa kallo da suke cike dam gwanin ban sha'awa, subhanallah, sanda khabeer yaga boobs ɗin Nasreen sanda yaji zubuwar abu ta ƙasansa, domin kuwa wata munguwar sha'awa ce, ta taso masa, barema kuma an daɗe ba'a gamu ba, joystick ɗinsa tashi tayi ta tsaya ƙyam, a hankali yasa hanun sa, yake ɓalle mata boturan rigar, har yayi nasarar cire rigar daga jikinta, a hankali yasa hannun sa, bisa boobs ɗinta yana shafawa a hankali, tare da murja nipple ɗin, ɗayan hanun nasa yasa bisa marar ta, yana shafawa a hankali, wani irin miƙa Nasreen tayi, tana jin wani irin daɗi na ratsata, cikin bacci, ƙara sakewa khabeer jikinta tayi, tana murmurshi cikin bacci, a hankali khabeer ya ɗaura bakinsa bisa na, Nasreen yana ƙoƙarin zura harshen sa, cikin bakin nata, sai a lokacin Nasreen ta buɗe idonta, daƙyar, fes ta sauƙesu bisa fuskar khabeer, saurin rufe idonta tayi ganin mutum kwance rabinsa a jikin ta, tana ƙoƙarin magana khabeer yayi saurin haɗe bakinsa da nata, mutsu-mutsu Nasreen keyi, ganin wani sabon abu wanda bata saba gani ba, cikin rayuwar ta, ganin da khabeer yayi Nasreen na ƙoƙarin sa ƙarfi ta ƙwaci kanta yasa shi sake mata nauyin sa, gabaki ɗaya a jikin ta, romace ɗinta yake sosai, Nasreen tun tana tsoro har ta sakewa khabeer jikinta, domin kuwa sosai jikinta ke amsar saƙon sa, sai lokacin na fahimci cewa itama Nasreen tana daga cikin mata masu ƙarfin sha'awa, khabeer kuwa yayi nisa baya jin ƙira, gani yake kamar bai taɓa kusantar wata mace ba, idan ba Nasreen ba, domin kuwa Nasreen tasha gyara wajen Hajiya ciki da waje,  ahankali khabeer ya zamewa Nasreen ɗan pant ɗin dake ƙugunta, ya cire nasa ma tare da wurgi dashi gefe, a hankali ya saita joystick ɗinsa yana ƙoƙarin shigar ta, a matse take gam, khabeer ya rasa hanyar shiga, ita kanta Nasreen saida ta fara jin zafi a ƙasanta sannan ta dawo hayyacinta, ƙoƙarin ture khabeer take amma ta kasa, jin zafin ya fara yawa yasata fara kuka tana yiwa khabeer magiya ya ƙyaleta, amma ina khabeer yayi nisa baya jin ƙira, kuka Nasreen keyi sosai tana kiran Ammin ta, da Goggo, da baba, wannan daren fah har Mama sanda Nasreen ta kira, kuka kuwa tasha shi har sanda Muryar ta, ta dashe, khabeer sanda ya kashe ƙishin ruwarsa kafin ya koma gefe yabar Nasreen na zubar da hawayen azaba.


  Runtse idonsa khabeer yayi yana jin wani irin sanyi mai daɗi na ratsa jikinsa, wani irin nishaɗi yake ji, tabbas sai yanxu ya samu mace dai-dai dashi wacce zata iya ɗaukar bukatar shi, yasan Zuhura cikakkiyar mace ce, sai dai har ga Allah yana jin Nasreen ta fita Zuma nesa ba kusa ba, haka kuma ta fita dirin jiki, buɗe idonsa yayi jin shashsheƙar kukan Nasreen yaƙi ƙarewa cikin tausayin ta, ya jawo ta, jikin sa, ya mannata da ƙirjinsa, yana dukan bayanta a hankali alamun rarrashi, daƙyar ya samu tayi shiru sannan ya tashi ya shiga tollet, ruwa mai zafi khabeer ya haɗawa Nasreen, tare da zuba gishiri kaɗan, dawowa yayi ya ɗaga Nasreen caɗak kamar ƴar baby yayi tollet da ita, a ruwan zafin ya ajiye ta, wani irin azaba Nasreen taji, ƙara tasa tare da ƙoƙarin tasowa daga cikin ruwan, riƙeta khabeer yayi tare da maidata cikin ruwan, yace.


  " Please Baby ki zauna cikin ruwan nan, muddun kina son ƙasanki ya daina miki zafi, idan kuma kinƙi zama to Wlh zan ƙara.


  Jin yace zai ƙara yasa Nasreen komawa cikin ruwan ta zauna tana cije bakin ta, idonta na rufe tacewa khabeer ya fita ya bata waje zatayi wanka.


 Murmurshi khabeer yayi tare da ficewa, daga tollet ɗin, zuwa yayi ya ɗauko mata wata ƙaramar doguwar riga marar nauyi, ya dawo yana ƙoƙarin shiga banɗakin, dan yasan ba lallai bane Nasreen ta iya fitowa ɗaure da towel, jin motsin shigowar khabeer yasa Nasreen saurin turo ƙofar, tana cewa.


  " Ni karka shigo, ka gane min jiki, dan Allah ka koma ɗakin ka, ni wanka zanyi.


 Dariya khabeer yayi cikin zolaya yace.


  " Haba Baby wani jemage ne kuma dare bai gani ba, waike yanxu jikin naki zaki ɓoye min, bayan na gama gane shi yanxu, tare da rataye mata rigar jikin mariƙin kofar, yana dariya yace to idan kin gama wankan ga rigarki jikin maƙalin ƙofar.



  " Ita dai Nasreen bata tanka masa ba, saima wankan ta da tayi, bayan ta gama wankan ne, ta taso da ƙyar, take takawa tana cije baki, a haka tasa hanun ta, ta ɗauko rigar da khabeer ya ajiye mata ta zura, a hankali take tafiya cikin dauriya, har ta isa kofar ɗakin nata, ta rufe tare da danna key, wai tana tsoron khabeer karya dawo ya karasata, juyawa tayi ta zaune a bakin gadon ta, a hankali tana wash, ji tayi an ɗaura mata hanu bisa cinyar ta, razana tayi, zata sa ihu, khabeer ya kunna wutar ɗakin zaro ido Nasreen tayi, ganin khabeer kwance, har yayi wanka ya sauya kayan jikin sa, tuno Abunda ya faru kuma da tayi tsakanin su, sai tayi saurin maida kanta ƙasa cikin jin kunyarsa.



 Murmurshi khabeer yayi tare da cewa...............




KUYI hkr da wannan, 


*Share*

    *And*

*Comments*


 *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


  *(Ummu Nasmah ce)*

[1/22, 3:43 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*P*•••••••7️⃣2️⃣ to 7️⃣3️⃣


" Waike kin rufe kofar ne, saboda karna dawo, to ai na daɗe da dawowa kin makare cikin tollet, jawota yayi ta faɗo jikinsa, mannata yayi da jikin sa tare da jawo bargo ya rufe su, cikin raɗa yake cemata.


  " kifa kwantar da hankalin ki, ni babu abinda zan miki, bacci kawai zamuyi.


shuru Nasreen tayi tare da laɓewa s jikinsa, hanun sa khabeer yasa ya zagaye ƙugunta, a haka bacci ya ɗauke su, suna jin bugun numfashin juna, da asuba khabeer shine ya fara buɗe idon sa, jin kiran Sallah, tashi yayi tare da ɗauro alwala, sannan ya dawo ya tashi Nasreen, buɗe idonta tayi da ƙyar tsabar baccin dake cikin idon nata, sallah khabeer yace ta tashi tayi sannan shima khabeer ya fice zuwa masallaci.


  Daƙyar Nasreen ta samu tayi Sallah idonta na rufewa, yau ko karatun da ta saba yi bata samu damar yiba ta koma ta kwanta, khabeer kuwa saida yayi karatu cikin masallacin, har alfijir ya keto kafin ya shigo cikin gidan, ɗakin Nasreen ya nufa, tana Bacci ya kwanta gefen ta tare da jawota jikinsa, ahaka shima Bacci ya ɗauke Sa.



  Ƙarfe goma da rabi dai-dai Nasreen ta buɗe idonta, ganin ta, tayi kwance bisa ƙirjin khabeer, yana Baccin sa Hankali kwance, haka kawai Nasreen ta tsinci kanta da ƙare masa, kallo sagensa dake kwance luf shiyafi ɗauke mata hankali, hanun ta, ta ɗaga da niyar shafo sajen sai kuma tayi saurin sauke hanun ta, tashi tayi da kyar jin har yanzu kasan ta, yana mata zafi duk da dai ba sosai bane, tollet ta shiga tayi wanka tare da brush, sannan ta fito ɗaure da towel ta rufe jikinta da hijab, mirror ta nufa, ta shafe jikinta da mayuka, batayi wani makeup ba, powder kawai ta shafa sai lipstick, sannan ta feshe jikinta da turare, kayan da suka sayo da SADIQ ne, Nasreen ta dauko Black ɗin doguwar riga, wanda tasha stone, yafa ɗankwalin tayi akanta sannan ta fice zuwa falo, da kanta Nasreen tayi mopping din falon, turaren wuta ta dauko ta saka cikin falon sannan ta shiga ɗakin khabeer nanma ta gyara shi, tasa turaren, tsaf Nasreen ta gyara part ɗin nata take kuwa ya ɗauki ƙamshi lungu da saƙo, ɗakin nata shima ta gyara shi, sai gadon da khabeer yake kwance a kaine kawai bata gyara ba.


 Kitchen ta shiga da niyar ɗaura musu breakfast, sai dai kuma duk iya dube duben ta, cikin kitchen ɗin bata samu wani Abunda ya danganci abinci ba, haka dole ta fito daga kitchen, tana ƙare masa kallon barnar kuɗin da akayi cikin kitchen ɗin.

Ɗakin khabeer ɗin ta koma tuno cewa bata sauya masa bedsheet ɗinsa, ba, ta shiga domin sauya masa.


  Shiko khabeer a hankali ya buɗe idonsa, wayan ya gani babu Nasreen, tunani yayi ko tollet ta shiga, wani irin ƙamshi ne, ya bugi hancinsa, wow wonderful, wannan wani irin turareni khabeer ya furta, dandai shi tunda yake cikin gidan bai taɓa jin irin wannan ƙamshi mai daɗin shaƙa ba, cikin gidan, sai dai ƙamshin airfresh da Zuhura ke amfani dashi, tashi yayi ya nufo nasa ɗakin da niyar yayi wanka, turus yayi ya tsaya a falon yana ganin ikon Allah, yanda aka gyara falon, sai tashin ƙamshin turaren wuta da yake yi, yasan dai su Asabe basa gidan, sun tafi ƙauyen su hutu, bare yace sune sukayi wannan aikin, to kodai Nasreen ce, ya ayyana cikin ransa, ɗakinsa ya shige bisa mamakin sa, sai yaga Nasreen tana ta famar kintsa masa ɗakin.

Sunan ta yaki, ta ɗago kanta ta kallesa, kafin ta maida kanta ƙasa, ƙara sowa yayi kusa da ita tare da cewa.


  " Meyasa zaki fito kiyi wannan aikin bayan kinsan ba jin daɗin jikin ki kike yiba, wannan aikin ai ya miki yawa, akwai ƴan aiki wanda zasu miki so ba sai kin wahalar min da kanki ba.


 Murmurshi Nasreen tayi tare da mayar masa amsa da cewa.


 " A'a bana bukatar ƴan aiki, domin kuwa ni aiki ba wani abu bane mai wahala a wajena, na saba dashi sosai, dan haka ni zanyi aikina da kaina bana bukatar taimakon Wani.


  Murmurshi khabeer yayi cikin jin daɗin yanda Allah ya masa sauyi da mace ta gari cikin kanƙanin lokaci, Allah shine abun godiya, shigewa tollet yayi ya barta tana faman shimfiɗa, bedsheet.

Ko kafin khabeer ya fito daga wanka Nasreen ta gama gyara ɗakin tayi ficewar ta, falo.


  Jin buga ƙofar da Nasreen taji ana yine yasata nufar wajen, buɗe kofar tayi, sai taga Nana da Khadijah, suna tsaye riƙe da basket a hanun su, murmurshi Nasreen tayi musu tare da musu sannu da zuwa, faram faram Nasreen ta karɓe su, suna wasa da dariya, basket ɗin suka ajiye sukace gashi inji momma breakfast ne, tace a kawo muku, godiya Nasreen ta musu, sun ɗan juma suna hira har khabeer ya fito ya samesu, sosai yaji daɗin yanda yaga ƴan uwan sa, sun sake a cikin gidan nasa, suna hira, saɓanin Zuhura da kullum take cikin ɗaure musu fuska.


  Da zasu tafi har compaunt ɗin gidan Nasreen ta rakasu, Daniel ya maida su, sannan Nasreen ta dawo cikin gidan.


  Alhamdulillah yanxu Rayuwa tayiwa Nasreen da khabeer daɗi, sosai khabeer yake jan Nasreen a jikin sa, tun tana ɗari-ɗari dashi, yanxu harta sake dashi, wani irin shaƙuwace ta shiga tsakanin su, wanda ko aiki ma daƙyar Nasreen take barin khabeer ya fita, yau ki manin watan Nasreen biyu cikin gidan khabeer, yayin da ta fara zuwa makarantar ta, inda take karantar Low, gidan khabeer fah ya samu sauyi hatta su Daniel sunsan Ogan su yayi sabuwar amarya, tsabar mutuntawa da Nasreen ke musu, su Asabe kuwa yanxu basa girki cikin gidan domin kuwa Nasreen itace take yin kayan ta, iya kacin su da aiki sharar tsakar gidan ne, shima kanshi khabeer tunda ya auri Nasreen bai ƙara zuwa gidan su yaci abinci ba, na matarsa yake ci, wata rana Nasreen da khabeer suna zaune a falo da daddare, suna hira, yayin da Nasreen tayi filo da kafar khabeer, khabeer ne ya nisa yace.


  " Baby ina son fah gobe zanje gidan su ABOKIYAR ZAMAN KI ZUHURA zamuyi magana maybe ta dawo jibi, tunda daman na daɗe da maida Auren mu, so ina son gobe zaki shirya da safe, tunda baki da lectures, zamuje gidan yari mu gaishe da Momy Sarah tunda kinga bata sanki ba, ya kamata kuga juna, daga nan kuma zan shige dake, gida wajen momma, so idan na dawo daga gidan su Zuhura zan biyo na ɗauke ki, sai mu dawo gida koh.


  Wani irin bugawa ƙirjin Nasreen yayi, jin khabeer ya ambaci sunan Zuhura, wani irin kishin Zuhura taji cikin ranta, amma tsabar iya duniyanci da Nasreen tayi da kuma ƙara samun cikakkiyar wayewa da itayi yasata nunawa khabeer tama fishi son dawowar Zuhura.


  " Shikenan Abban Allah ya kaimu goben, ya kuma dawo da ummin junior gidanta lfy, goben idan muje gidan momma, ina son zamu dawo da junior, gidan nan, ya kamata ace shima yanxu yana tare damu.


  " Murmurshi khabeer yayi tare da shafo fuskar Nasreen Yace.


  "An gama Baby na, duk abunda kikace haka za'ayi kinsan yanxu na zama mijin tace, sai yanda kikayi dani.


  Dariya Nasreen tayi tace.


  " Kardai ka zugani kasa kaina yata girma na manta cewa mu biyu ne, a wajen ka.


  Dariya shima khabeer yayi haka suka ta hiran su, gwanin ban sha'awa.


 

  Yau Nabiya tun safe take kwara amai ga hajijiya dake damunta, ta rasa inda zata saka Ranta, SADIQ duk ya fita hayyacinsa, ganin farin cikin sa kwance babu lafiya, gyalen ta, ya ɗauko mata, ya tallafe ta, har mota, asibitin Dr Abubakar bukar suka nufa, binciken doctor na farko ya gani cewa Nabiya nada shigar ciki, har tsawon wata ɗaya.

Murna wajen Sadiq ba'a magana, dubu hamsin ya ajiye doctor yace goron Albishir.

 

 Tun a mota SADIQ ya dannawa khabeer kira yana ɗauka ya fara ce masa.


  " To Uban ƴan gori yaudai gori ya kare, tunda an kusa fara kirana da Daddy.


 Dariya khabeer yayi, sosai kafin yace............


Kuyi hkr da wannan Wlh yau ina busy ne, shiyasa nace da babu gara ko kaɗan ne, na muku typing.



 *Share*

*And*

*Comments*



*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


  *(Ummu Nasmah ce)*

[1/24, 3:14 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم*



*d̸e̸d̸i̸c̸a̸t̸e̸d̸ t̸o̸*


*Aྂlྂlྂ wྂrྂiྂtྂeྂrྂsྂ oྂfྂ kྂaྂiྂnྂuྂwྂaྂ iྂnྂaྂ yྂiྂnྂkྂuྂ iྂrྂiྂnྂ sྂoྂsྂaྂiྂ dྂiྂnྂ nྂaྂnྂ aྂlྂlྂaྂhྂ yྂaྂ kྂaྂrྂaྂ mྂaྂnྂaྂ bྂaྂsྂiྂrྂaྂ tྂaྂrྂeྂ dྂaྂ hྂaྂzྂaྂkྂaྂ*


 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*P*•••••••7️⃣4️⃣ to 7️⃣5️⃣


 " Ehh lallai abu yayi kyau, shege na waje na, ashe daman haka ka iya aiki, kace bugu ɗaya ka yiwa ƙwallon ka, ta faɗa raga, kallon Nasreen yayi yace kinji ƙaninki, SADIQ har ƙwallon sa, ta faɗa raga, ya kusa zama Daddy.


  Murmurshi Nasreen tayi, tare da farin cikin samun ƙaruwa da ƴar uwarta tayi.

   

" Kwarai kuwa, kaga ai na fika ƙoƙari tunda gashi ni an gani a ƙasa, kaga daga yau ka fara kirana da Daddyn boy, ka kuma cewa matarka ni ba surikin ta, bane.


Dariya khabeer yayi

 Suka cigaba da magana da Sadiq cikin wasa da dariya, Kafin ya masa fatan Alkairi, tare da samun ƴan biyu, kashe wayar khabeer yayi ya shiga cikin ɗakinsa, tare da fitowa da key ɗin mota, tare da kwalin waya riƙe a hanun sa, zama yayi kusa da Nasreen tare da kama tafin hanun ta, ya ajiye mata, makullin motar tare da ajiye mata shima kwalin wayar bisa cinyarta, Yace.


  " Nasreen wannan key ɗin mota ne dana saya miki tare da waya, ina sane tun shigowar ki, gidana ban baki waya ba, har kika fara zuwa school, ba komai yasa nayi haka ba, illah kawai na gwada hakurin ki, naga zaki iya Zama Babu waya, duk da kina ganin mata da yawa cikin makaranta, waɗanda basu kaiki ko nace basu kai mijinki shiba, sai kuma naga haƙurin ki, domin kuwa hakan ya nuna min cewa ke bakya daga cikin matan da suke ganin abu hanun wani suce dole suma sai sunyi, ina fatan zaki gafarce ni, bisa hanaki waya da nayi da wuri.


  Wow Nasreen wani irin daɗi taji cikin ranta domin kuwa ta kwan biyu tana ƙaunar waya, buɗe kwalin wayar tayi tana dubata cikin xunuɗi, waya ce mai kyau ƙirar Iphone 11 mai shegen kyau wacce zatayi dubu ɗari Uku ko huɗu, kallon khabeer tayi tace.


  " Na gode sosai Abban junior Allah ya saka da Alkairi, ya ƙara buɗi, naji daɗin wannan kyautar sosai, sai dai ita wannan key ɗin motar ne, nake ganin kamar........


 Da katar da ita khabeer yayi ta hanyar cewa.


  " Kike ganin me zakiyi da ita tunda baki iya mota ba koh?


  Murmurshi Nasreen tayi ganin khabeer har ya gano Abunda take son cewa, girgiza masa kai tayi alamun ehh.


  " To karki damu nida kaina zan fara koya miki motar, idan bana nan kuma, daniel zai koya miki, so karki damu da wannan.


 Murmurshi Nasreen tayi ta rungume khabeer tana masa godiya cikin murna.


 Washe gari da safe Nasreen Bayan ta tashi tayi dukkan ayyukan ta, na cikin gidan, ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast, tare da yiwa Momy Sarah girki na musamman, ferfesun kaza ta mata, sannan ta mata sakwaran doya da miyar ƙwai, sai drink da ta mata, kunun Aya tare da zoɓo, sai kuma ta dama mata kunun shinkafa mai rai da lfy wanda yasha.


 Kusan goma da rabi Nasreen ta gama aikin girkin, sannan ta jera nasu breakfast ɗin bisa daining, na Momy Sarah kuwa, a Basket ta shirya shi, ɗakin ta taje ta shirya, ta fito cikin atampar ta, java Holand green color, ɗinki ya mata kyau sosai a jikin ta, feshe jikinta tayi da turare, sannan ta nufi ɗakin khabeer, yana kwance yana shan Baccin sa domin kuwa baida time ɗin tashi, gefen sa, ta Zauna cikin kwarewa wajen iya tashin miji a Bacci, a hankali take hura masa iska cikin kunnen sa, yayin da hanunta ke shafa kansa, a hankali ya buɗe idonsa, ƙamshin jikin Nasreen shine ya fara dukan hancinsa, lallausan murmurshi ya mata tare janyo ta, ta faɗo jikinsa, murmurshi itama Nasreen tayi tace.


  " Abban junior, kamata yayi ka tashi, fah ka shirya, kasan wajen zuwan mu, da yawa ina son muje har gidan su Nabiya, mu dubata.


  Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


  " Ba yauba zuwa gidan SADIQ, ki bari sai nan da kwana biyu, yanxu tashi ki haɗa min ruwan wanka.


  Tashi Nasreen tayi ba musu ko jayayyan cewa sai taje gidan Nabiya, tayi banɗaki, ta haɗa masa ruwan wankan, kusan karo sukaci khabeer zai shiga ita kuma Nasreen tana fitowa, jawo hanun ta khabeer yayi yace.


  " Muje ki taya ni wankan koh Baby na.


  Dariya Nasreen tayi tare da cewa muje to, sanda khabeer ya shiga cikin tollet ɗin, Nasreen ta kwace hanun ta fito da gudu tana cewa 


  " Naƙi wayon salon ka sani wani sabon wanka.


 Murmurshi khabeer yayi yace.


  " Zaki shigo hanuna, zan rama ai.


 A falo Nasreen ta zauna jiran fitowar khabeer.


 Bai wani juma ba, ya fito cikin shirin sa, daining suka zauna, bayan sun gama breakfast ɗin ne, khabeer yacewa Nasreen taje ta ɗauko hijab ɗinta su wuce, yana so zai shige office idan ya kaita gida, bayan sun dawo daga prissing.


 Nasreen bata wani juma ba, ta fito sanye da hijab har ƙasa, abun ya burge khabeer sosai, domin kuwa yana mungun takaicin ganin matar Aure sanye da gyale a jikinta, ta fita unguwa, basket ɗin Nasreen ta dauka suka shige gidan yarin.


  Khabeer bai wani sha wahala ba, wajen ganin Momy Sarah, a office ɗin shugaban gidan yarin suka zauna aka fito musu da Momy Sarah.

Allah sarki rayuwa, Momy Sarah tayi baƙi ta rame har wani tsufan wahala tayi, tana ganin khabeer saita fashe da kuka.


 Tausayin ta ya kama khabeer sosai ganin yanda rayuwar Momy Sarah ta koma, zama tayi ta fuskanci khabeer tace.


  " khabeer kaine tafe yau, gaskiya naji daɗin zuwan ka, ya mutanen gidan Kowa yana lafiya dai koh.


  " Kowa yana lafiya, Momy, Momy kin rame sosai, ki rage yawan damuwa, dan Allah damuwar dai bata da amfani, ki ɗauki ƙaddarar ki, Momy dan Allah.


 Murmurshi mai ciwo Momy Sarah tayi, kafin tace.


  " Khabeer ko bansa tunani a cikin zuciyata ba, dole nayi baki na rame, Babu abinci mai kyau, khabeer Babu walwala, haka kullum muna cikin bauta, khabeer taya bazan rame ba khabeer.


 Shuru khabeer yayi, domin maganar Momy Sarah gaskiya ce, tabbas rashin walwala na saka rama.

 Katse masa shurun sa, Momy Sarah tayi da cewa.


  " Wacece wannan khabeer, kodai itace amaryar taka da Daddyn ku yake sanar dani kayi ne?


  " Itace Momy, sunan ta Nasreen, Nasreen ga Momy Sarah, mahaifiyar Khadijah da Khalid.


  Sai a lokacin Nasreen ta gaishe da Momy Sarah, amsawa Momy Sarah tayi cikin sakin fuska, tare da sawa Rayuwar Auren su, albarka, nasiha sosai Momy Sarah tayiwa Nasreen, *(🤔 ikon Allah wai yau Momy Sarah ce da nasiha, lallai duniya tafi gabaruwa iya jima Allah yasa mu dace)*


 Basket ɗin da Nasreen ta taho dashi ta miƙawa Momy Sarah, khabeer sun juma sosai suna ganawa da Momy Sarah, domin kuwa shi kansa shugaban prissing ɗin bai isa bawa khabeer time ba, cikin prissing ɗin domin kuwa yana da right dinda zai iya zuwa ya gana da koma waye cikin wajen.


  " Momy mu zamu wuce, zamu bar miki basket ɗin, duk sanda Khalid ko daddy suka zo zasu taho dasu, dan Allah Momy karki saka damuwa cikin ranki.


 Cikowa idon Momy Sarah yayi da hawaye tace.


 " Zan rage insha Allah khabeer, na gode sosai da wannan ziyarar da kuka kawo min, khabeer idan kaje gida kacewa fatuma dan Allah ta kulamin da yara na, mussaman Khadijah itace ƙarama tana bukatar kulawa.


  " Momy karki damu, insha Allah su Khadijah baza suyi kukan rashin ki ba, momma zata kula dasu kamar yadda zata kula da Nana.


  " Shikenan khabeer na gode sosai, Nasreen na gode Allah ya baku zaman lafiya, yayiwa Rayuwar Auren ki, albarka.


  Da amin Nasreen ta amsa, sannan sukayi Sallama, suka tafi Momy Sarah na jin kamar ta bisu.


 Cikin mamaki da al'ajabi Nasreen taga khabeer yayi hanyar gidan Nabiya shida yace ba yanxu ba, kallon sa tayi cikin murmurshi tace.


  " Abban junior, naji daɗi sosai, gaskiya dan harna cire rai.


 Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


  " Lura da hakan da nayi yasa, nace bari na kawoki, Baby na, domin ina son ganin ki, cikin farin ciki koda yaushe, yana faɗin hakan ne ya danna hom a kofar gidan SADIQ ɗin.


 Da sauri mai gadin ya fito ya buɗe get, ɗin khabeer na ƙoƙarin shiga, mai gadi ya dakatar dashi da cewa, ai oga Sadiq basa nan sun fita shida Madam.


 " Oh shit khabeer yace tare da cewa okey ba damuwa, juyawa yayi yanaa cewa Nasreen.


  " Amma dai gaskiya wannan ɗan iskan surukin naki ya cika yawo, bari muje gida na kirasa naji inda yaje ɗan iskan gari.


Murmurshi Nasreen tayi tace.


     " Daman Allah ya ƙaddara bazamu haɗu ba, ina ga gobe muyi clear da ita cikin school.


 Allah ya kaimu khabeer yace, sannan suka cigaba da hiran su, har suka shigo cikin gidan nasu.

  A falo suka taradda momma zaune tana kallo, Babu kowa sai ita kaɗai, sallama sukayi momma ta amsa tana musu lale maraba, zama Khabeer yayi tare da cewa.


 " Momma ina yaran naki, naganki ke ɗaya cikin gidan.


 " Suna school, tun safe sai 5:00pm zasu dawo, Nasreen sannu da zuwa kece yau tafe cikin gidan namu.


 Murmurshi Nasreen tayi tace.


  " Ehhh nice momma, daga ƙasan da take zaune tace, na sameku lfy momma.


 " Lfy lau Nasreen, cewar momma, yau zamu wuni kenan.


 " Ehh momma, sai dare zan tafi.


  Tashi khabeer yayi yana cewa.


 " To momma bari na tashi na tafi tunda ni kin manta dani cikin gidan.


 Murmurshi Momma tayi tace.


 " Naga ƴata ne, ina zan tuna dakai, yawwa khabeer jiya Daddyn ku ke sanar dani cewa, gobe su Kubra zasuje maka kususun matar ka Zuhura.


  " Ehhh Momy haka ne, insha Allah gobe Zuhura zata dawo.


  " Gaskiya banso ka dawo da Zuhura cikin gidan kaba, domin kuwa Hankali zata ɗaga maka cikin gidan ka, kana zaune lfy.


  ' a'a Momy hakan bazata kasance ba insha Allah, komai normal zai tafi.



  " To Allah yasa, sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya.


  Da amin khabeer ya amsa yana kallon Nasreen ƙasa-ƙasa ganin yanayin ta, ya sauya jin an ambaci sunan Zuhura.

Kafin ya fice daga cikin gidan.



  Nasreen tun tana ɗari-ɗari da momma harta sake da ita, wunin Ranar Nasreen itace ta yiwa momma girki, har su Nana suka dawo daga school, Nasreen ta shiga cikin su, Babu nuna girman, suka cigaba da harkokinsu.



  Khabeer tun 4 na yamma yake gidan su, Zuhura suna shan hirar yaushe gamo, sosai khabeer ya jawa Zuhura kunne game da gidan sa, Zuhura dai ta amince da duk wani sharaɗin khabeer, sanda ya tashi tafiya, dubu ɗari biyu ya ajiye mata, yace koda wani hidimar da zatayi.


  Ƙarɓa Zuhura tayi tare da yiwa khabeer godiya, karo na farko kenan a wajen khabeer daya taɓa jin yayiwa Zuhura kyauta ta gode masa, har tsakar gidan nasu wajen motar sa, Zuhura ta rakasa, tana ɗaga masa hanu yaja motarsa ya fita.


 Gidan su ya koma ɗaukar Nasreen sosai yaji daɗin yanda ta sake cikin kannen sa, suna hira, ita kanta momma cewa take sai yanxu tasan tayi suruka, sanda Nasreen suka zo tafiya momma turaruka masu tsadar gaske ta bata guda uku, tare da mata albarka.


  " Godiya Nasreen tayiwa momma sosai, tare da alkawarin da su Nana suka mata kan cewa ranar monday suna, zuwa gidan nata, kafin suka nemi hanyar gidan su.


  A gajiye Nasreen ta shigo cikin falon tare da zubewa saman kujera alamun ta gaji.


 Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.

 Raguwa kawai kafin ya shige nasa ɗakin.


  Nasreen ta ɗan juma cikin falon kafin itama ta nufi nata bedroom ɗin, shirin bacci tayi tsaf kafin ta shige ɗakin Baccin nasu ita da oga khabeer, a daren Ranar Nasreen sun rayashi da Angon ta khabeer sosai.


  Washe gari da safe Nasreen tunda ta farka da asuba bata maida bacci ba, saboda tana da lectures by 9, part ɗinta ta gyara, har ɗakin mijin ta, sannan ta ɗaura breakfast, bata yi wani Abu mai nauyi ba, kasancewar bata da ishashen time, ruwan tea kawai ta dafa wanda yasha na'a-na'a da ɗanyar citta da kanan fari, sai kwai data soya, sai kuma ta tafasa Indomie, a gaggauce tayi breakfast ɗin sannan tayi shirin school, ɗakin khabeer ta koma ta samu yana bacci, peper da biro ta ɗauka ta masa rubutu tare da ɗaga wayarsa ta ajiye ƙasansa ta fice zuwa ɗakin junior.


 Yana zaune shi kam yana shirin school, kallon Nasreen yayi yace.



  " Good morning Momy.


  "Morning junior haw Are You.


  " Fine momy, harkin fito, wai da so nake mu fita tare idan an ajiye ni school sai a wace dake, tunda kuna gaba damu.


  " To kaga tunda Allah yasa ka shirya muje kayi breakfast sai mu wuce, da sauran time, kaine ma nake ganin kamar kayi let.


  Fita sukayi tare junior yayi breakfast, sannan suka wuce school, daniel shine ya sauke su.


Nasreen darect Class lectures ɗinsu ta shige, sai wajen 11  suka fito daga lectures ɗin.


  Department ɗin su Nabiya Nasreen ta shige, ta samesu ita da khady suna zaune, sai famar chart suke, Zama Nasreen tayi gefen su tare da cewa .


  ' Barka da hutawa Momy Nabiya ashe kuma mun sami karuwa, jiya muje gidan ku, nida Abban junior, mai gadin ku yace kun fita.


  " Ehh munje gidan Hajiya, kin kusa Zama Momy dai zakice yar rainin wayo, kinga mubar wannan maganar, kinga wannan yarinyar ta kusa dake ta nuna khady, faɗa zaki mata, wai khamal ne yake sonta, tana so tana kaiwa kasuwa, to Wlh kibar jan ajin hanka karya tsinke.


  Dariya Nasreen tayi tace, to Hajiya Khadijah kinji Abunda, ƙawar ki, take gaya miki kibar jan Ajin haka, to meye ma, aibun khamal, naga dai yana da nutsuwa da hankali.


 Mtss kema dai Aunty Nasreen kina kula iskancin Naby, yo to da ita maiya hanata son khamal ɗin tunda ita ya fara cewa yana so.


 Dariya sosai Nabiya tayi sannan tace.


  " Aini time ɗin akwai yayanki cikin zuciyata, shiyasa.


  Dariya itama khady tayi sannan tace.


  " Zanyi tunani akansa naga wani matsayi ya kamata na basa.


 " Dako ki Kyauta cewar Nasreen sun juma suna tadi kafin daniel yaxo ya ɗauki Nasreen, sanda suka biya ta makarantar su junior suka dauke sa, sannan sukayi gida.


  Yau dai Allah yayi dawowar Zuhura cikin gidan ta, tare da Aunty kubra suka shigo cikin gidan, sai ƙanwar mahaifiyar Zuhura, Ummu Kulsum, duk sun watse sunbar Aunty kubra, tace ita sai ta

Ta jira khabeer yazo Kafin ta koma.


 Ƙarfe takwas kuma dai-dai khabeer ya shigo, cikin gidan, part ɗin Nasreen ya shiga ya sameta Zaune ita da junior sai shiririta suke yi, murmurshi khabeer yayi tare da kaɗa kansa ya zauna gefen su, yana cewa.


  " Wato kudai hankalin ku ya tafi can wata uwa duniya bakwa jin sallamar mutum.


 Murmurshi Nasreen tayi tace.


  " Sannu da dawowa, muna game bamu ji shigowar kaba.


  Shima junior sannu da dawowa yayiwa mahaifin nasa.


  " Ina kuwa zaku jini hankalin ku ya tafi wata uwa duniya, am kina sane da cewa Zuhura ta dawo koh.


  Dam gaban Nasreen ya buga cikin ƙarfin hali da danne ƙishin ta, tace.


  " Ka dai cemin zata dawo yau, amma bansan har ta ƙaraso ba, tun ɗazu na gama girki aida na aika musu, amma yanxu ma, bata ɓaci ba, akwai sairan abincin bari na bawa junior saiya kaimusu.


  " Okey ba damuwa bari ni na shiga ciki na rage kayan jiki na.


 A fito lfy kawai Nasreen tace masa kafin ta tashi ta shige kitchen ɗin ta, fitowa tayi da abinci cikin basket tacewa junior gashi yakai part ɗin mamansa, ƙarba junior yayi yana murna, yayi part ɗin Zuhura.


 Zama Nasreen tayi ta kwantar da kanta bisa kujerar falon tana jin wani Abu mai ɗaci cikin ƙirjin ta, cikin ranta take cewa, shikenan fah yanxu mu biyu muke da khabeer.


  Fitowa khabeer yayi, ya zauna tare da kwantar da kansa bisa kafaɗar Nasreen, Yace.


  " Baby tunanin me kike haka.


  " Babu komai, kawai kaina ke ciwo, ya aikin.


 " Alhamdulillah yanxu kinga ƙarfe tara, ki tashi muje part ɗin Zuhura, ina son magana daku.


 Dato Nasreen ta amsa masa, sannan ta shiga ɗakin ta, ta ɗauko hijab ɗinta, suka shiga part ɗin Zuhura.


 A falo suka samesu har Aunty kubra, zama Nasreen tayi tare da gaishe da Aunty kubra,

Cikin sakin fuska, Aunty kubra ta amsa har tana zolayar Nasreen.


  Gaishe da Zuhura Nasreen tayi. 

Cikin mamaki da al'ajabi, fuskar Zuhura A sake ta amsawa Nasreen gaisuwar ta, Babu wani haɗa rai.


  Aunty kubra ce tacewa junior ya tashi ya tafi ɗaki ya kwanta dare yayi, sannan ta maida dubanta ga Zuhura tace.


  " To Zuhura gashi dai Allah ya dawo dake gidan ki, sai dai ina son na miki faɗa akan abu ɗaya zuwa biyu.

  Zuhura ki rage kishi cikin ranki, ki zauna lafiya da mijinki da *ABOKIYAR ZAMAN KI* domin kuwa babu Abunda yafi zaman lafiya daɗi, ki Rungumi mijinki da ɗanki, kishiya dai ba part ɗin ku ɗaya ba, bare kice zaki ke ganin ta hankalin ki yana tashi, idan har tayi wani Abu da bai dace ba, ki mata faɗa a matsayin ki na babba.

   Sai Abu na biyu, ki gyara zamantakewar ki da dangin mijinki, mussaman mahaifiyar mijinki, kiyi mata biyayya iya iyawar ki, ki dage da addu'a Allah ya rage miki kishi cikin ranki.

  Wannan shine abinda nake son tunatar dake.


 Nisawa Zuhura tayi tace.


" Aunty kubra insha Allah, zan gyara, ko a yanzu naga darasin rayuwa, insha Allah bazan ɗauki Nasreen a kishiya, a matsayin ƴar uwa zan ɗauketa, haka kuma dangin mijina, zan gyara zamantakewa ta, dasu, tabbas basuji daɗin zama dani ba, amma ina da tabbacin yanxu zan gyara.

 Kallon Nasreen tayi tace.

 Nasreen ki yafe min abunda na miki zuwan ki cikin gidan nan, kuma ina fatan zamu zauna lafiya.


 Murmurshi Nasreen tayi tace.


 " Insha Allah Aunty nikam ta wajena babu wata matsala, zamu zauna lafiya insha Allah.


   " Alhamdulillah Aunty kubra tace, tare da yiwa itama Nasreen ɗin faɗa, shima khabeer yayi musu nasu nasihar, kafin ya tashi ya raka Aunty kubra, daniel ya maida ta gida.


 Koda ya dawo har bakin part ɗin Nasreen ya rakata yana rarrashin ta, kiss ya mata a goshin ta sannan ya wuce part ɗin Zuhura.



  Nasreen tunda ta shiga ɗakin ta, take jin zuciyarta, Babu, Baccin ma kasawa tayi, domin kuwa ta saba kwana jikin khabeer, gashi ya tafi ɗakin matarsa ya barta cikin kewa.

 Daƙyar bacci ɓarawo yayi nasarar sace Nasreen.


 Da asuba kuwa da murɗa Nasreen ta tashi ga amai da take ta kwarawa, sai jiri, gagara fitowa tayi ta gyara ɗakinta, bare kuma girki.


  Tashin khabeer da safe yaga sauyi sosai, domin kuwa kamshin daya saba tashi yaji ya doki hancinsa yau babu shi, haka kuma ɗakin babu gyara, fitowar sa, ma falon su Asabe ya samu suna girki kamar yadda suka saba mata, tsuka khabeer yaja tare da shigewa yayi part ɗin Nasreen ko zai samu Abunda zaici.


  Shigar sa part ɗin Nasreen, yaga ko gyara part ɗin batayi ba, cikin mamaki ya dubi daining nanma wayam Babu komai, ɗakin Nasreen ya nufa da sauri, kwance ya sameta a ƙasa, sai kwara amai take, da sauri ya karasa ya rikota jikinsa tare da mata sannu, ɗagata yayi ya kaita tollet ya sake mata ruwan ɗumi, a kanta, ya wanketa tas sannan ya naɗoto a towel, ya ajiye ta saman gadon ta.

 Gyara wajen da tayi aman yayi sannan yaxo ya ɗauki doguwar riga ya zura mata tare da hijab, yana mata sannu, ya kamota suka fito waje da niyar zuwa asibiti.


 A motar ya ajiye ta, sannan ya shiga part ɗin Zuhura da sauri, tana zaune ya sanar da ita cewa Nasreen bata da lafiya zasu Hospital, Addu'ar samun lfy Zuhura ta mata, har bakin motar ta biyo khabeer tana yiwa Nasreen sannu da jiki.



  Gwajin farko doctor ya gane Nasreen na ɗauke da ciki na tsawon wata biyu, sosai khabeer yayi murna, koda suka dawo gida sun sami Zuhura zaune cikin part ɗin Nasreen tana jirar dawowarsu ita da junior, koda khabeer ya sanar da Zuhura Nasreen na ɗauke da ciki, bata nuna ɓacin ranta ba, saima farin ciki da tayi.



 Su SADIQ ma sunji labarin samun cikin Nasreen, sosai sukayi murna, har zuwa sukayi shida Nabiya suka wuni.



 Alhamdulillah rayuwa yanxu ta yiwa khabeer daɗi domin kuwa, matansa sun haɗa kansu, Zuhura ta ajiye komai ta Rungumi Nasreen hanu biyu, yanxu Nasreen ta fara gyarawa Zuhura abubuwan ta, yayin da ta ke koya mata girki, ko wani girki tare suke shiga kitchen suyi, cikin Nasreen dana wata huɗu khabeer ya biyawa Zuhura da momma da Umma mahaifiyar Zuhura, da kuma Ammi kujerar Hajji, ita kuma Nasreen yace sai Allah ya sauƙe ta, lfy zasuje tare dashi.


  Kowa yayi farin ciki da wannan abun Alkairi da khabeer yayi, haka kuma momma tayi murna sosai da hadewar kan Nasreen da Zuhura.


 Ranar asabar Nasreen da Nabiya suka shirya da niyar zasu ƙauyen su, zasuyi sallama da Ammi kafin su wuce Hajji, shirye shirye sosai khabeer yayiwa Nasreen na zuwa kauyen su, kayan abinci ma dasu zannuwa da shaddodi, wajen mota guda wanda zasu kai tsaraba.............



 Mu haɗu daku a next page wlh na gaji.



*Share*

    *And*

*Comments*



*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



      *(Ummu Nasmah ce)*

[1/27, 6:20 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏

            ⛏⛏⛏⛏

*SARA DA SASSAKA*

  *(Baya Hana Gamji)*

              *Toho*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

          🌳🌳🌳🌳


*Story And Writing*

           

           *By*


 *Rasheedat Usman*


 *(Ummu Nasmah)*



🤳🏻

*08147537180*



                *(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻



*بسم الله الرحمن الرحيم*



🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Deducated to All fan's of Sara da sassaqa.

 ___________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________


*P*••••••••7️⃣6️⃣ to 7️⃣7️⃣


Nabiya itace ta biyowa Nasreen ta gidan ta, cikin Nabiya ya fito sosai domin kuwa, yanxu cikin ta, wata bakwai, da SADIQ baiso Nabiya taje ba, yaso ace saita haihu, amma Nabiya tace ita ina, dole sai taje sunyi Sallama da Ammin ta, Da daniel suka tafi, ƙarfe huɗu na yamma suka shiga cikin RUGAR ARƊO,

Da sauri naji Nasreen na cewa daniel ya tsayar da motar, gefe daniel yayi parking, da fitowa Nasreen tayi domin gaskatar da Abunda idanunta suke gane mata, tabbas kuwa mamace, cikin bola sai tsince-tsince take, ta fice hayyacinta, idan ba kasanta farin sani ba, bazaka taɓa cewa ita bace, nufar wajen Maman Nasreen tayi cikin sanyin jiki, Nabiya da taga da gaske Nasreen fah wajen Mama zata nufa, ta fito itama da sauri tasha gabanta tana Cewa.


  " Ina kike ƙoƙarin zuwa haka, da sauri.


 Muni Nasreen tayiwa Nabiya da Bolar da mama ke ciki tace.


 " Kina nufin kice min baki gane Mama ba, mamace fah wacce take uwa a garemu, wacce mukayi rayuwa a hanun ta, Nabiya itace fah take rayuwar bola.


  Taɓe bakin ta Nabiya tayi tace.


  " Saime dan mamace, ni Wlh ba Uwata bace, domin kuwa da uwata ce, da bata azabtar da rayuwata, wacce rayuwa mukayi a hanun ta banda rayuwar wulaƙanci da tozarta, Rayuwar Bola Kuma yanzu ma ta farata, ki rufawa kanki asiri da Abunda yake cikin ki, ki raba kanki da zuwa wajen mahaukaciya, danko saita illata ki, ita ko a jikin ta.


 " Hmm Nabiya kenan, koma me Mama ta mana ya riga da yawuce, ya kamata kibar tunashi, kamata yayi ki ramawa duk wanda ya miki sharri da alƙairi, zanje wajen Mama koda kuwa zata kasheni, domin kuwa ni har gobe ina ɗaukar Mama a matsayin uwar da ta haifeni, dan haka ki bani hanya na wuce, tunda ke baki da zuciya mai kyau.


  Shuru Nabiya tayi, yayin da maganganun Nasreen suka ratsa jikinta, cikin sanyin jiki ta kaucewa Nasreen daga hanya, shi kanshi daniel da yake tsaye gefe baisan wacece Mama ba, ya tausayawa halin da take ciki.


 Ƙarasawa Nasreen tayi wajen Mama, ta sunkuya, cikin cikowar hawaye dake ƙoƙarin zubowa daga idanunta tace.


  " Sannu Mama.


 Bata kulata ba, saima kallon ta, da tayi tana dariya tare da miƙomata wani ƙwano mai tsatsar gaske, sai a lokacin hawayen dake idanun ta, sukayi nasarar zubowa, ta miƙa hanu ta karɓi kwanon ƙarasowa Nabiya tayi, ta dafa kafaɗar Nasreen tace.


  " Mama bata da hankali a jikin ta, wanda zata saurareki, ki tashi mu tafi.


 Tashi Nasreen tayi hawaye na zuba cikin idanunta, suka shiga cikin mota, a ƙofar wani gida mai kyau ginin zamani sukayi parking, kallon daniel Nabiya tayi tace.


  " Yaka tsaya anan kuma, mu ƙarasa mana.


 " Nan ne gidan naku Madam.


 Zaro ido sukayi Dukansu biyu, cikin haɗin baki sukace.


 " Gidan mu kuma, wani gidan namu, da yake kewaye da zana.


 " Shine dai, Madam ku shiga za kuji koma menene.


 Shiga sukayi, cikin gidan cikin al'ajabi da mamaki. Aikuwa Ammi suka tarar zaune tana tsinkar karkashi, Yayin da wata matashiyar budurwa, take mata shara, da sallama suka shiga cikin gidan, murmurshi ɗauke fuskar Ammi ta amsa.

Zama sukayi gefen Ammi Nasreen ce tace.


  " Barka da gida Ammi, da fatan mun sameki lafiya.


 " Lfy lau sai Alkairi, sannun ku da zuwa.


 Yawwa Ammi cewar Nabiya tare da gaida ta, itama wannan budurwa zuwa tayi ta gaishe dasu Nasreen.


 Cikin rashin hakuri Nabiya tace, 


 " Ammi ya naga gidan nan ya sauya ya koma ginin zamani, Baba ne yayi sabon gini.


 Murmurshi Ammi tayi, itama cikin mamaki tace.


 " Wai daman bakuji labarin wannan ginin ba?


 " Ehhh wlh Ammi ba muji ba, gaskiya.


 " Ikon Allah cewar Ammi, to mijin Nasreen dai shine yayi wannan ginin, Kuma ya kwana biyu dan zaikai wata huɗu, har wuta da Ruwa na soler yaja mana wajen guda shida cikin RUGAR Nan, sai ko albarka ake masa tare da Nasreen kunga harda mai mana wanke wanke da shara ya ɗauko, ni nayi tunanin ma, ya sanar daku.


 Zaro ido Nasreen tayi, tace.


 " Ko kaɗan wlh Ammi bai sanar dani ba, amma gaskiya ya kyauta, Allah ya saka masa da Alkairi, gashi ma ya biya miki Hajji.


  " Ehhh wlh, nidai gaskiya Babu Abunda zance da khabeer sai Allah ya saka masa da Alkairi, ya ƙara masa sabon buɗi, tabbas ya nuna min ƙauna, tun kafin ya Auri ƴata, ya kasance suruki gareni.


  Nabiya ce tace,


 " Ammi naji daɗi sosai, khabeer ya kyauta, gaskiya bamu da bakin da zamuyi masa godiya sai dai Addu'a.


 Nasreen ce tace.


  " Ammi Baba baya nan ne.


 " Yana nan yaje gidan Goggo, baima juma da fita ba.


 Ammi da yaranta sunsha taɗi wunin ranar kayan da suka taho dashi kuma daniel ya nemi yara aka jibgesu cikin, ɗaki ɗaya dake cikin gidan.

Baba kuwa bai shigo gidan ba sai sakaliyar la'asar, cikin murna da ganin mahaifin nasu suka gaisa, sai kuma Nasreen ta kawowa baba zancen Mama.


  " Baba yanxu dan Allah haka za'a bar mama cikin rayuwar Hauka, sai kace wacce bata da gata, gaskiya Baba ya kamata a nemawa Mama magani.


 Nisawa Baba yayi kafin yace.



 " Nasranatu, daman kinbar maganar salamatu, abunda ta shuka, shine take gurbewa, kinga kuwa kowa yaci ladar kuturu, saiya masa aski.


  ' a'a Baba bai kamata ake tuno Abunda ya wuce, gaba ya kamata mu kalla ka sakawa duk wanda ya maka sharri da alƙairi wannan shine ake kira jin ƙai, idan ban manta kaine kamin wannan huɗubar Baba.


" Hakane Nasreen tabbas nine, sai dai ina son ki sani cewa ni banida kuɗin da zan iya kashewa salamatu na magani, domin kuwa hanuna bai cuɗi bayana ba, su Kuma masu maganin yanxu kuɗi suke buƙata.


 " Tabbas kana da gaskiya Baba, ni zan biya duk wani kuɗin maganin da za'a yiwa Mama, karka damu da kuɗi Baba, neman lafiyar mama shine a gaban mu, jakarta Nasreen ta ɗauko, tare da fito da rafar kuɗi wajen dubu ɗari tace gashi Baba, wannan kuɗin Abban junior ne ya bamu shi nida Aunty Zuhura, a fara amfani dashi, a ɗauko mai maganin, kafin nan.


 Karɓa Baba yayi tare da yiwa Nasreen albarka cikin rayuwar ta, ita kanta Nabiya ta jinjinawa, Farar zuciya irin na Nasreen, wacce ta mata sharri ta saka mata da Alkairi, danko wlh ita ko kuɗi sun mata yawa gara ta, zubar dasu, akan tayiwa Mama magani.


 Washe gari da safe, su Nasreen suka shirya da niyar cewa zasu gidan Goggo daga nan zasu biya gidan mai gari, wajen ƴar gwal daga nan kuma zasu wuce gidan su Indo.


 Sun sami Goggo tana zaune, kan taburmar ta, cikin farin ciki Goggo ta tarbe su, bayan gaisuwa ne, Goggo, saita fara kuka, cikin tashin hankali Nasreen tace.


  " Goggo lafiya kike kuka.


 " Dole nayi kuka yaran nan, idan na tuna da cin mutuncin dana muku, gashi Allah ya muku sakayya, Kuma wlh duk sharrin salamatu yasa na muku haka, ku yafeni dan Allah, mussaman make Nabiya da mukayi sanadiyyar barinki rugar nan.


 Murmurshi Nasreen tayi tace.


 " Goggo ai komai ya wuce mun yafe ki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya.


 Godiya Goggo tayi musu, kafin suka ta taɗin yaushe gamo, sai da azahar suka bar gidan Goggo inda Nasreen ta ajiye Goggo dubu ashirin, itama Nabiya dubu goma ta bata, gidan mai gari suka yi.


  A sunkuye suka sameta, sai zabgar wanki take, ga kuma tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, dakyar ma take tafiya, gashi tayi baƙi ta rame, wankin ma da gani ba nata kaɗai bane zai kai na mutum Uku, sallama Nasreen sukayi, ɗago kanta Ƴar gwal tayi, sam bata gane su Nasreen ba, sai da sukayi magana.


 " Nasreen kune tafe, sannun ku da zuwa, tun jiya ai naji labarin zuwan ku, mu karasa ciki.


 Shiga sukayi cikin ɗakin nata, yayin da yaran gidan sukayi ca a kansu suna kallon su, gaisawa sukayi kafin Nabiya tace.


 " Ƴar gwal kece haka, kike wanki Abunda bakya yi, wani irin bauta kike haka, kinga kuwa yanda kika rame.


 Kuka ƴar gwal tasa cikin kukan take ce musu.


 " Haka nake fama kullum, nike wankin junguɗo dana mahaifiyar sa, duk wani aikin cikin gidan nan nice nake yinsa, ga duka da nake sha hanun junguɗo duk sanda yasha ya bugu, mutanen garin nan suna cewa alhakin kune yake binmu nida mahaifiyata, kuma tabbas haka ne muddun baku yafe mana ba, alhakin ku bazai barmu ba, cikin kuka ta ƙarasa maganar.


 Nasreen da tayi shiru, tana tausayawa halin da ƴar gwal take ci, kafin tace.


 " Mun yafe muku, Kuma insha Allah Mama zata samu Lafiya, ki cigaba da haƙuri, a gidan Auren ki, insha Allah komai zai wuce, jarabawa ce, kuma insha Allah zaki cinyeta.


" Na gode sosai Nasreen Allah ya saka da Alkairi, na gode.


 Sanda suka tashi tafiya, dubu goma Nasreen ta bawa ƴar gwal, sannan suka wuce gidan su Indo, abun haushi Nasreen bata samu Indo ba, wai taje rugar Abba tauɗo garin kakanun ta, Nasreen taji haushi sosai, sai sako ta bari tace a bawa Indo idan ta dawo, Atampopi ne, kala shida anyi ɗinki dai-dai jikin Indo, sai dogin riguna, sannan suka fito sukayi gidan su.

 


 Kwanan su Nasreen uku cikin rugar, Baba kaf ya rabar da kayan Abincin dasu Nasreen suka kawo, Mama ma, an kira mai magani, ya kamota tare da sa mata mari, aka adana ta, a wani ɗaki, ana mata magani, randa suka cika sati ranar suka dawo cikin Gombe, da tarin tsarabar ƙauye.


Nabiya suka fara sauƙewa kafin sukayo gidan, IPS khabeer, babu kowa cikin gidan, sai masu gadi, cikin mamaki Nasreen ta leƙa part ɗin Zuhura, shima ta gansa kulle, to ina sukaje ta ayyana cikin ranta, nata part ɗin ta nufa, tasa key ɗin dake hanun ta, ta buɗe, duhu baƙiƙƙirin dakin, ƙoƙarin nemo wajen wuta take ta kunna sai taga an kunna hasken ɗakin tare da cewa 


 " Happy birthday to you !! Happy birthday to you.


 Ware idanun ta, Nasreen tayi ganin khabeer da Zuhura sai junior tare dasu Asabe.

  falon nata kuwa an masa ado da boloon da wasu abubuwa masu sheƙi, dariya tayi cikin farin ciki ta tafi da gudu ta rungume khabeer, juyi khabeer yahau yi da Nasreen yana.


  " Happy birthday to you my angel.


 Dariya Nasreen keyi sosai, kafin khabeer ya sauƙeta taje ta rungume Zuhura.


  Itama Zuhura dariya tayi tace happy birthday to you, duk dama kin manta da auntyn ki, kikaje kika rungume miji, kega ƴar miji daɗi, ko Kunyar ɗanki junior bakyaji koh.


  Dariya Nasreen tayi, tace.


  " Kai Aunty duk fah murna ne ya cika min ciki.


  Dariya sukayi duka, kafin suka yanka cake, bayan su Asabe sun fita ne, suka zauna suka khabeer tsakiyar su, cikin alamun gajiya Nasreen tace wash nagaji Wlh.


  Dariya khabeer yayi cikin zolaya yace.


  " Oh Sarkin raki, wani gajiya kikayi, ba wani aiki kikayi ba, kinje a mota kin dawo a mota, tsabar raki kice kin gaji.


  Kafin Nasreen tayi magana Zuhura ta riga ta ta hanyar cewa.


  " Kaji Abban junior da wata magana, aidole momyn junior ta gaji, kasan masu juna biyu basu cika son zaman takura ba.


  Dariya Nasreen tayi tace.


  " Yawwa Aunty faɗa masa dai ko zaifi gane yaren ki.


 Magana khabeer zaiyi Zuhura tayi saurin rufe masa bakinsa da hanun ta, tace kinga momyn junior maza tashi kije na haɗa miki ruwan wanka, ki samu kiyi kixo kici abinci, sai ki samu ki huta.


 Haka kuwa akayi Nasreen wanka taje tayi sannan ta fito suka ci abinci, Bayan sun gama cin abincin ne, khabeer ya dubi matan nasa, cikin ƙaunar su, Yace.


  " Alhamdulillah da farko ina mai godiya ga Ubangiji daya haɗa min kan Matana, wanda basa zaman kishi, sai Zama na Amana da yarda da juna, gaskiya ina jin daɗin hakan sosai, sannan ina muku Albishir da cewa, insha daga ku babu wata, na rufe babin Aure cikin rayuwata, saidai kuma na gidan Aljanna wato hurul'aini, sai kuma Albishir na biyu da nake son na muku shine, na buɗewa Zuhura babban super market a nan cikin babbar kasuwa, mai suna *ZUHURA SUPER MARKET* ke kuma Nasreen na buɗe miki gidan man fetur da kuma Oil  zuwa gas  mai suna *mrs Khabeer Oil and gas* wanda na yanke shawarar cewa zan dawo dasu Baba cikin garin Gombe, yaxo ya shugabanci wannan gidan man.


  Rasa bakin magana su Nasreen sukayi cikin farin ciki da murna, sosai suka godewa mijin nasu tare da masa fatan Allah ya ƙara masa buɗi, miƙawa kowa takarda yayi mai ɗauke da shaidar ya mallaka musu.



  Ranar wata talata da daddare Nabiya ta tashi da naƙuda, SADIQ bai wani ɓata lokaci ba, yayi Hospital da ita kafin ya kira Hajiya a waya ya sanar da ita, sosai Nabiya tasha wahala wajen haihuwa, inda cikin ikon Allah da asubar ranar Laraba ta haifi ƙaton Yaron ta, na miji mai kama da ubansa sak, Nasreen da taji labari, sassafe suka tafi ita da Zuhura da khabeer, sai ɗaga Yaron Nasreen take tana juyashi, Hajiya ce tace.


  " Saura ke Nasreen, kema Allah ya sauƙe ki lfy, cikin kunya Nasreen ta amsa da Amin.


  Ammi ma taxo ta, kasancewar sun dawo cikin Gombe da zama, Baba na kula da gidan man Nasreen.


  SADIQ kuwa sai rawar kai ake an samu Yaro, karfe uku na yamma suka sallame su, suka dawo gida.


  Da Baba yaso ɗauko Goggo daga ƙauye taxo ta zaunawa Nabiya, sai dai Babu Halin hakan kasancewar tana kula da Mama wajen bata magani, kuma alhamdulillah yanxu Mama ta fara samun sauƙi.


 Ranar suna Yaro yaci sunan *NURUDDEEN* marigayi, sosai Nasreen da Ammi suka ji dadin karan da SADIQ ya musu, aiko Yaro yaga gata wajen Nasreen da khabeer, ita kanta akwati Uku tayi ɗaya cike yake da kayan baby ɗaya kuma da Atampopi da less, sai ɗaya kuma kayan shafe-shafe na jarirai, shima khabeer ba'a barsa a baya ba, wajen bajinta.

 Shiko SADIQ ba'a magana Abunda yayi, cikin farin ciki da annashuwa aka watse daga taron sunan.


 Rayuwa yanxu tayiwa kowa daɗi itama Mama ta samu lfy ta kuma roƙi gafarar su Nasreen, tare da Ammi, amma Baba yace shi sam bazai maida ta gidan saba, anyiwa baba roƙon duniya amma yaƙi, haka ya bawa, Mama takardar sakinta, taci gaba da rayuwar ƙauye.


 Ammi kuwa, da momma sunje sunyi aikin hajjin su, lfy sun dawo sai fatan Allah ya amshi ibada, ranar dasu momma suka dawo a ranar Nasreen ta tashi da nata naƙudan, cikin dare suna kwance da khabeer sai taji kamar ana mintsinin ta, a jikinta tun tana daurewa, har haƙurin ta, ya ƙare domin kuwa yanxu bayanta ke mata ciwo gadan-gadan tashin khabeer tayi cikin tashin hankali, kallon yanayin ta, da khabeer yayi ya gane cewa haihuwa ce, baiyi ƙasa a gwiwwa ba, ya ɗauke ta tare da kiran Zuhura a waya yace taxo Nasreen Babu lfy, bayan Zuhura taxo itace ta haɗa duk wani kayan da mai haihuwa take buƙatar su,, sai asibitin Baba didi, cikin ikon kuwa Nasreen bata wani juma ba, ta haifi yaranta biyu kyawawan gaske mace da namiji, Zuhura Itace ta fara riƙe yaran a hanun, sai kuma taji cewa itama tana sha'awar haihuwa, ƙarbar su khabeer yayi yayi musu kiran sallah a kunnen su, tare tauna dabino ya samusu a bakin su ya kuma basu ruwan zamzam, tare da musu addu'a, sanda aka gamawa Nasreen komai aka fito da ita ɗakin hutu sannan suka kira kowa suka sanar dasu, take kuwa asibitin ya cika da ƴan uwa da abokan arziki, kowa na murnar samun twins ɗin da akayi, Nabiya ma, da little Nuruddeen, ba'a barsu a baya sunxo sunga yara, daman shi Sadiq baya gari yana Abuja.

 Dawowar su, gida Hajiya mahaifiyar SADIQ da kanta ta zaunawa Nasreen.


 Ranar Lahadi da dare, ana gobe suna khabeer ya shigo ɗakin Nasreen yake sanar da ita cewa yayiwa Baba mai suna, sunan Yaron Musa, ita kuma macen Momy Sarah yayiwa takwara, taci sunan saratu, Nasreen taji daɗi sosai.


 Washe gari suna ba'ayi wani bidi'a kasancewar khabeer yace baya so, Nasreen ta samu kaya sosai domin kuwa kowa ya nuna bajintar sa.


  Khabeer komawa yayi part ɗin Zuhura gabaki ɗaya da zama kafin Nasreen tayi arba'in, aikuwa Nasreen bayan tayi arba'in tasha gyara sosai wajen Hajiya, ciki da waje, yaranta kuwa sunyi ƙiba, gwanin sha'awa, sai kace ƴan wata Uku, Ranar da khabeer ya dawo ɗakin Nasreen kusan zaucewa yayi, tsabar zumar da Nasreen ta masa.


Yanxu Nasreen ta koma makaranta inda take tafiya da nani yana kula mata da Aslan da Aslamy wanda da haka take yiwa yaran nata laƙabi.


  *A gurguje*


 Bayan shekara goma


Da gudu wani matashin yaro ya fito yana Cewa.



  " Abba !! Abba !! Abba.


 Khabeer dake zaune falo yana riƙe da waya a hanun sa, yace


  "Wai menene Aslan nake shan wannan kiran.


 " Abba wai inji bros junior bazaka je ɗauko Momy Sarah damu ba, nida Aslamy.


 Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


 " Inji waye, zuwa daku kai dashine dai baxan jeba, gashi ma har kun shirya momyn ku kawai muke jira, kinga Ahlan da shuhuda ma sun shirya, ya nuna mata wasu yara biyu dake zaune gefe suna wasa ba tare da sun kula suba, wanda Nasreen ta sake haihuwa bayan Aslan da Aslamy.


 Dariya yaran sukayi tare da koma part ɗin Zuhura da gudu suna murnar dasu za'aje.


 Tashi khabeer yayi tare da shigewa ɗakin Nasreen, yaga me take taƙi fitowa har yanzu, tana zaune gaban mirror tana ƙoƙarin ɗaura sarƙa a wuyan ta, karɓar sarƙan khabeer yayi ya ɗaura mata, tare da ɗaura kansa bisa kafaɗar Nasreen Yace.


 " Baby na kinga yanda kikayi kyau kuwa kin koma yarinya ƙarama, kamar bake bace kika ajiye yara huɗu.


 Dariya Nasreen tayi tace.


  " Ai dole na zama yarinya, yanda Abban junior ke shagwaba Ni.


 Dariya khabeer yayi tare da cewa.


 " Sai kika tuno min sanda kike ƴar ƙauye, amaryar junguɗo, wayaga Nasreen gidan junguɗo mashayi.


 Dariya Nasreen tayi sosai kafin tace.


   " Da kuwa ina can ina fama da wahalar surfe da bautar gida, gaskiya anso lalata rayuwata sai Allah ya dubi zuciyata ya turo min da hasken rayuwata Khabeer ya taimake ni, ya fiddani daga ƙangin bauta ya dawo dani Mutum ta hanyar inganta Rayuwata da hasken ilimi, gashi yanxu har na gama karatuna ina jiran aiki kuma naje har garin ma'aiki na sauke farali, shiyasa a kullum nake daɗa ƙaunar ka HABIBINA.



 Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.


 " Ki daina tuna Abunda ya wuce farin cikin zuciyata, nice ya kamata na miki godiya, sakamokon haska min gida da kikayi, ki daina tuno waɗanda suka miki mugunta, domin basu isa su tare miki hanyar samun kiba, ko kin manta karin maganar nan ne ta Hausawa da suke Cewa *SARA DA SASSAQA BAYA HANA GAMJI TOHO*





 ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN, INA ROƘAR UBANGIJI ABUNDA NAYI KUSKURE YA YAFE MIN, ABUNDA NA FAƊA DAI-DAI KUMA YA BANI LADANSA, ALLAH YA BAMU IKON AMFANI DA DARUSSAN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFIN.



  Anan nake ce muku bissalam sai mun sake haɗuwa daku cikin sabon Novel ɗina mai taken, *RUƊANIN ZUCIYA BIYU*



*SHARE*

   *AND*

*COMMENTS*


  *ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*


   *(UMMU NASMAH CE)*



Post a Comment

0 Comments