SANADIN BOKO cmplt

 Sanadin Boko 1 01

Posted by ANaM Dorayi on 09:25 AM, 10-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

Na

Maryam Abdullah K.Mashi

Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta

kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu

kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma

suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce

poly wasu Jami'a, wasu Nursing school.

Sa'adatu da ke kusa da ni ta ce, "Hafsy don Allah kema

ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana." Nayi dan

murmushin takaici.

"Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda

in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni."

Ta zaro ido. "Kada kice min kina cikin wadanda za'a

dakile a kai gidan miji?

Na sake ajiyar zuciya.

"Ke dai Sa'a taya ni da addu'a, Allah Yasa ina da rabo,

dan kuwa ina son in ga karshen boko." Jamila ta dube ni,

"Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki

ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen

ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne?

Na ce, "To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke

ba kince aure ba?" Jamila ta ce, "Aure kuwa insha Allahu

ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna.

Sa'a ta ce, "Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki

za ki watsar da batun karatu. Na ce, "Dubu nawa akayi?

Ai ni boko yanzu muka sa dan ba."

Ta ce, "Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta

aikhairi". Na ce, "Ga magana da za ki yi kawai, Amin".

Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam

fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba,

da wuya naje wata Makarantar.

An sauke *yan zariya, sannan mu *yan Kaduna muka

nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita

ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana

da makarantar wato mun kammala.

Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna "Ga Hafsat

ga Hafsat". Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta

dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na

ce, "Innarmu ba su hamsin". Ta kwance habar zani ta

mika musu.

Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan

gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa.

Inna ta aje min kwano tare da cewa, "Alalar har ta

huce". Ta dire min kofin ruwa na ce, "Har yanzu bata

kare ba ne?" Ta ce, "Ta kare mana, ai tun kwanaki da

Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku

kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga

magariba tayi ne sannan in ba yara.

Nayi dariya tare da cewa, "Innarmu kenan! Ina Yaya

Ummar?" Ta ce, "Tun safe bai dawo ba, kin san nasai

mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako

na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan

yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan

ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina

fama da shi.

Na ce, "Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa

asiri". Ta ce "Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da

ni, na ce "Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna

ta ce, "Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?"

Na rungumota a jikina ina cewa, "Gani na dawo". Ta rufe

fuskarta, ita dole taji kunya.

Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce "Kin

zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa". Na rike

baki, "Inna har da Sakina?"

Ta ce, "Eh! Na ce, "Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da

karatuna ma". Innarmu ta ce, "Malam ne matsala, amma

ko Nas din nan da 'ya'yan Kawunki suke yi ai zan so

kiyi." Na ce, "Wane Nurse? Ni fa Jami'a nake so, burina

in zama 'yar Media".

Ta ce, "Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka,

sannan na ajiye tare da cewa, " 'yar jarida mana! Sai dai

matsalar kudi ne". Kai lomar alala da nayi baki, ta zo

daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar

na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa,

tare da shimfida mishi tabarma.

Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau

fuskar shi sake ya amsa, har da ce min "An dawo lafiya?"

Na ce, "Lafiya lau". Innarmu ta ce, "Allah cikin ikonSa

Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya

kammala."

Ya ce, "To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa

magana ya fito in hada su da Sakina in huta". Inna ta ce,

"Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi

makarantar gaba da..."

Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike

tsaye ransa a bace.

"Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya

ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya

shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata

tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon

zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin

wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun

gidan duniya ne?"

Inna ta kufulo itama, ta ce, "To dama ka saba ka min

tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu

sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, "To zan ga

wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke". Ya fita.

Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena

basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce

masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin

nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina

ba.

Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai

mita take, na ce "Innarmu ki bar batun haka, kinsan

gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana

sauraro". Ta ce, "Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka

dai mace tayi da ni naji mu kwashi 'yan kallo ni da ita".

Na idar da sallar isha'i, ina zaune a gurin ina istigfari,

wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce

"Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje". Ta ce, "To".

Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter

cewa na dawo.

Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan

na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo

kamshin turarensa.

Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka

wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin

farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da

kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa.

"Babyna". Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na'am".

Ya diro "Zo muje cikin mota." Na ce, "A'a mu zauna

can". Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu.

Ya dan gyara tsaiwa, "Kin ce fa baki son Baba ya dinga

ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai

ganni dole ko?"

Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa

Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga

suturar da yake sakawa.

Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba

jikina.. Ya katsemin tunani da cewa.

"Zo muje, na zo da muhimmiyar magana". Na ce masa,

"Nima ina da nawa muhimmin zancen". Baya ya bude ya

shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya

ce "Rufo kofar mana". Na ce, "Ka barshi haka ma ya yi.

Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka

kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin

wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina.

Ya ce, "Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki

ba." Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya

na ce, "Don Allah Munnir ka daina son taba jikina,

haramunne fa". Ya ce, "Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne

fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki

yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta

ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki

ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki

ba.

Na bata rai, ya shafi kumatuna.

"Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin

daure fuska". Shikenan, ban san lokacin da murmushin

ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya

ce, "To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in

kinji saikin bani goron albishir.

Na ce, "To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace

yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na

gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka

dai sani". Ya ce, "Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin

manta alkawarin da muka yi ni da ke?"

Na ce, "Ban manta ba". Ya ce, "To ki kyale fadan Baba

kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on

aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne

saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je

kasuwa musai kayan sawa?

Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake

matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai

rungume ni. Da sauri na ce, "Duk lokacin da ka shirya".

Ya ce, "Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din."

Na ce, "Um". Ya ce, "Wai ba ki murna ne angel dina?

Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin

zama *yar media insha Allah.

Na dube shi, "Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?" Ya

ce, "Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada

master dina, before time din kin zama *yar media ko?

Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin

juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, "Kin san ina son

aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki.

Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya

ce duk sai sunyi master sun fara aiki balle ni.

Na ce, "To sai yanda Innarmu ta ce". Ya ce, "Bana jin

Inna, zata yarda". Ya sake yin kasa da murya "In dan yi

kissing din kunnenki?" Naja baya tare da cwa, "A'a". Ya

ce, "To bari na tafi". Yana magana yana kallon agogon

hannunshi, "Zan kalli wasan Arsenal yau." Na ce, "Kai

kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan."

Ya ce, "Kema za ki koya in kinzo gidanmu". Nayi dan

murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi,

amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin

mata masu bukata.... Ya katse tunanina da cewa, "Ko

kada in tafi ne?" na ce, "A'a kaje sai gobe". Ya ce,

"Shikenan." Ya miko min wata farar leda.

""Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk." Na ce na

gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan

dawainiyar.

Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har

da kayan tea. Ta ce, "Kai yaron nan baya gajiya da

dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon

karatun kyayi can a dakin shi.

"Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara

hakuri." Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe,

sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana

son abinda nike so.

Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar

Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata

mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu

shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa

nake son in ganni a dakin kaina.

Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da

Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana

cewa, "Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira

ki ba, nasan gurin ki ya zo.

Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na

atamfar (Java), gyale na sura na ce "Inna Munnir na

kirana."

Ta ce, "To." Na nufi waje kai tsaye.

Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa

ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya

shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na

ce, "Muyi sauri ban ce zamu fita ba." Ya ce, "To".

Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a

gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga

wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai

tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To zabi wanda

ki ke so."

Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da

*yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar

zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi.

"Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi muje".

Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana". Cikin daga

sauti na ce, "To, to naji zan amsa, amma ni na gane

kamar zasu yimin kadan." Ya dan sassauto "Muje

gidanmu ki gwada." Da sauri nace, "A'a zasu yi min."

Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga

motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice cream". Na ce,

"A'a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma

nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min". Ya ce,

"To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada

na cinye ki."

Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a

dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana,

ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi

yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura

mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da

muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last

kudin shi don muyi karatu.

Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba,

amma ka fito ku gaisa.

Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi

cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce,

"Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga

lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um asibiti muka je

dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba za ki fada ba? Kin

san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja

min surutu sanadin bokon nan."

Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu yana

shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana

cewa.

"Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min

manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan

wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to

ban laminci wannan ba."

Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni,

ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta

ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya zaburo tamkar

zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji wa? Wa ya fada

miki?"

Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi

abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk

ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?" Inna

ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?" Nace, "Kuyi hakuri,

ba zan kara zuwa ba." Tayi kwafa tare da ci gaba da

yin aikinta. Baba ya ce "To wallahi ba zan yarda da

gantali ba, wai ku *yan boko."

Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni

na jajirce ki samu karatun boko." Na ce, "Don Allah

Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba". Ta ce, "To

me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min

karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?" Na ce,

"Na sani.

Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta

sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi

saurayi wani guri.

Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane

ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na

ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi

shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore

shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin

wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure

shi. Shi kadai nake jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi

ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina

cikin damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce,

"Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira goma

a amsomin panadol."

Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar

makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, "Kar ki

zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?" Na ce, "Ai

dazun ciwon kai ke damuna." Ban yi wata kwalliya ba,

kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari

mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu

saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su

kuma suna Makarfi Road.

Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga

motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri.

Daidai ya bude motar zai shiga na ce, "Munnir" Ya juyo

da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana

ciki, ya ce, "Beby lafiya?" Na jingina da motar, sannan

na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma

lokacin ne naga rashin hankalina.

Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo

biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na ce, "Ai ba

ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce "Dama nazo ne

na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko

zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba."

Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya

rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni"

Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka motar

yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki kiji." Na ce,

"A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan gaddamar nan, ki

daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala.

Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, "Ba

za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate

din gidan, muka shiga.

Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga

haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa fita

dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita.

Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin

gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau kin zo

gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su

Nana.

Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni

cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce,

"Shikenan.

Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai

kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna.

Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin,

jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi

ya zauna hannun kujerar da nike



Zaharaddeen Shomar

whatsapp 08168575100





Sanadin Boko 1 02

Posted by ANaM Dorayi on 09:42 AM, 10-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

Na

Maryam Abdullahi K/Mashi

Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai

kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina

kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim

kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya

zauna hannun kujerar da nike.

Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya mika

min, na girgiza kai tare da cewa, "Na gode. Ya ce, "Wasa

ki ke yarinya, rike nan ko na dura miki.

Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai iya.

Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na kwace tare da

mikewa.

"Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, "Dama ni banyi fushi

ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya kashemin

idonshi daya, nayi saurin kauda idona saboda yarr din da

tsigar jikina tayi.

Na ce, "Yaushe zaka zo? Ya ce, "Zauna to mu tsara in da

zamu dinga haduwa, don Babanku ya ce in manyana ba

su zo ba kada ya sake ganina.

Na ce, "Fada min daidai ina ne zamu dinga tsayawa? Ya

dan yi shiru, "To ni bansan yaya zamu yi ba, na ce zan

hada miki phone kin ce a gida ba za a barki ba, wai ke

ba ki da irin 'yar dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a

silent.

Na ce, "Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na

marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na lura

yana son su. Mu bar maganar party din nan, wallahi ba

Babana ba har Innarmu in ta sani zan bani, ka ji.

Ya tsare ni da manyan idanunsa.

"Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba "Ban san me yasa

gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena su Nana da

Suhaila Mom din mu da Dad din mu sune suka shirya

musu party din su last week. Amma ku sai ana hana ku.

Wannan duhun kai ne, yanzu fa an waye.

Na ce "Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da yake

son ya yi ma 'ya'yanshi. Ya ce "Shikenan dai, mu bar

maganar, naji nayi asarar kudina, kuma ba wani gida ke

ce dai ba ki ga dama ba.

Wani friend dina yarinyarshi itama 'yar Geto ce, amma ta

jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo muka yi shagali,

amma ke kin kasa.

Na ce, "Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido, sai kin

yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki hanyar fita, sai

kawai naji ya rungume ni ta baya, jikina ya dauki rawa.

Cikin rawar murya na ce, "Munnir la..la....lafiyarka? Don

Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi sun canza,

da sassarfa na fito na dau hanya. Ya biyo ni da mota shi

da abokinshi, wai na shiga su kaini gida, na ce, "A'a don

na tsorata, dole suka bar ni.

Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya min,

dama an ce mace da namiji in suka kebe na ukun

shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir ba, da tuni

na bar shi.

Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake tsayawa. Na

fada ma Innarmu ta ce saboda me? Na ce, Baba ya hana

shi zuwa nan.

Inna ta ce, "Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da

Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace wani

abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama kanki.

Na ce, "To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da Munir

ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba.

Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba bai sani

ba, Munir ne ya sai min form, sai dai tsorona daya randa

Baba zai sani.

Na zama cikin sa'a kamar ko yaushe, Munir ya tsaya

tsayin daka har na samu gurbin karatu a (B.U.K) Kano,

sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na ce ma Innarmu, ta

ce yau na yanke shawarar sanar da shi komai, tunda

gobe za ku je yin rijista.

Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar Innarmu

nake ji tar daga dakin Baba, domin bangonsu daya. Tana

sanar da Babanmu komai.

Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, "To bokon nan

ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na hakura

tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take so ko

duniya?

Inna ta ce, "Duka. Ya ce, "Karya ne, duniya ku ke nema,

kuma ga ku gata nan. Jami'ar da aka ce 'ya'ya suna

lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki sama da shekaru

amma baki damu ba. To magana ta ni uku ce, bata kai

hudu ba.

Na farko duk abin da ya faru da ita SANADIN BOKO ba

ruwana, zai shafe ki ne da ita.

Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba,

matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin da

Allah Ya dora min.

Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi mijinki,

duk ranar da wata ashsha ta samu SANADIN BOKO.

Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba

kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo kusa

dani ta zauna.

Tasa hannu ta dan dake ni, "Tashi Hafsatu.

Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce "Nasan kin ji

duk zancen da Malam yake yi ko?

Na ce, "Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce, "Insha

Allahu Malam karatun Hafsa zai zama alkhairi garemu da

kai gaba daya.

Ya ce "Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake magana.

Babah ta ce, " Hafsatu ki bar Babanki yayi iko da ke, ki

ce ma Innarku kin fasa karatu. Kalamanshi ba baki yayi

miki ba, amma ina ji miki tsoron alhakinshi kada ya kama

ki.

Na ce, "Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba yanzu

zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su yarda ya auri

mara ilimi ba.

Babah ta ce, "Sai shi? Akwai masu sonki da yawa, kuma

sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina nazari, nasan

Babah gaskiya ta fada min, amma ya zan yi da son

Munnir?

Na dube ta, "Babah ki duba irin hidimar da Munnir yake

yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba zan jirashi ba.

Ta ce, "To yanda ki ka gani, amma karatun nan tunda ba

na Muhammadiyya ba ne, banga dalilin naci ba.

Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki yake yi.

Anya auranki zai yi? Na ce, "Allah Babah aurena zai yi, ki

dubi dadewar mu da hidimar da yake min.

Ta ce, "Ba ta a nan, amma fa shawara ce." Na koma na

kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin dakinta.

Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya da

ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni ba. Nayi

guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta dawainiya da ni

ba zai aure ni ba?

Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata

Mahaifana biyu ma haka ne, duk SANADIN BOKO. Da

safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi na kasa

sha, Innarmu ma sukuku take.

Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan

alalarta manja, na ce "Inna ko dai zamu hakura da batun

bokon nan ne?

Ta dube ni, "Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce, "Naji

duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru, can ta ce,

"Abu daya zuwa biyu nike so ki min.

Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da

mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu kiyi abin

da ya kai ki makaranta, wato karatunki wanda nike fata

ya zama sanadin alkhairi.

Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da ya yi

wa boko, har kannanki suma su samu dama suyi cikin

kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu damar ci gaba

ba yana jin haushi.

Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na hada ki

da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu ya cika ni,

na ce, "Insha Allahu zan kula sosai, kuma zan fidda ki

kunya, SANADIN

BOKOn nan kowa zai huta, Baba zai yi alfahari da ni.

Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a jami'ar

Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi Innarmu bata

daina rokona in rufa mata asiri in lura da kaina ba.

Nan na tafi na barta da surutun 'yan gidanmu, da 'yan

unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri mai kudi, shi

yasa muka nace boko, wasu su ce dan kyan nawa bai fi

cikin cokali ba, amma mun kuke sai nayi boko.

Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta toshe

kunne watan kwaram daya ne. Baba har fushi yayi da ita,

sun jima kafin ya soma amsa gaisuwarta.

Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon su

bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba shi

hakuri suka ce wai karatun yana da amfani.

Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a'a tayi shi can

gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta, sai suka

ce ya yi hakuri 'yan kwanaki ne zata gama, don haka sai

ya dawo ya zura mana ido

******* ********** ********** *********** *********

Jami'a wata rayuwa ce da ta sha bamban da

secondary, banga laifin Baba ba yanzun don ya

kyamaci boko, sai dai na sha alwashin kula da kaina,

don haka na tsare gida bani da kawa ko aboki. Duk da

Munnir na shirin tafiya Dubai karatu don kammala

Masters dinshi, haka bai hana shi zuwa duk bayan sati

biyu ba. Tafiyar tashi bata yuwu ba har muka samu

hutun first semester, sati biyu dai za mu yi amma naji

dadi, sai dai wannan hutun ne hutun da ba zan taba

mantawa dashi ba a rayuwata. (Kuma shi ne dalilin

rubuta labari na "SANADIN BOKO" .

Sauran kwana biyar na koma Makaranta duk da inata

dokin zuwa gida amma zaman gidan bai mun dadi ba,

ko gaisuwata Baba baya amsawa har ta kai da naji

muryarshi zan boye.

Bello Abokin Munnir shi yayi sallama da ni, na sha

mamaki don bai taba zuwa shi daya ba. Ya ce, Munnir

ya aiko shi muje tare bashi da lafiya. A rude na je na

fadawa Inna, ta ce, "Yana asibiti ne?" Duk da ban sani

ba sai na ce mata, "Eh." A zatona yana asibiti ne, sai

da yaja mota sannan nace, "Wane asibiti ne." Sai ya

ce, "Ai yana gida." Har gefen su Munnir Bello ya raka

ni, ina shiga sai yace mun, "Toh yana ciki ni na wuce ki

fada masa don ya dameni in kawo ki har ciki. Na ce,

"Toh!" Na nufi ciki da tafiya cikin dari-dari. Tsakiyar

falon na tsaya na zabga Sallama, ga mamakina sai ga

Munnir ya fito daga kitchen sanye da gajeren wando da

vest duka farare tas, hannunshi dauke da ruwa (C way)

yana sha. Na ce, "Ah! Ka samu sauki ne?" Ya ce, "Eh,

A'a." Ya nuna min kujera, "Zauna." Na zauna ina kallon

shi tare da son jin karin bayani, "Ban gane eh, a'a ba?"

Ya tsugunna a gabana, "Ciwon ya dade yana ci na, ga

shi zan iya tafiya Makaranta cikin kowane lokaci ba

tare da na samu maganin ba." Na ce, "Wane irin ciwo

ne?" Ba tare da shakka ki tunani ba ya ce, "Ciwon

sha'awarki....."

Gabana ya fadi, na mike tsaye da sauri. Shima ya mike,

"Hafsat kin san ina son ki, wallahi na gaji da

sha'awarki. Ki so ni kamar yanda nike son ki." Na ce,

"Munnir ka san ina son ka." Ya ce, "To ki nuna min."

Na ce, "Ban gane ba? Sau nawa nake cwa ina son ka?

Ka sani." Ya ja tsaki, "Kin dai gane nufi na, ina son yau

daya ki taimaka ki nuna kaunarki gare ni." Na ce, "A'a

ba zan iya ba, domin haramun ne." Ya ce, "Ni fa zan

aure ki!" Na soma tafiya don fita ina cewa, "Sai ka jira

sai ka....." Maganata ta tsaya sakamakon murda kofar

da naji nayi ta a rufe gam. Na dube shi yana murmushi

ya ce, "Ki bani hadin kai don yau ta karfin tsiya ma zan

iya biyan bukata ta." Jikina ya soma bari na ce,

"Wallahi Munnir zan maka ihu, ka bude min kofa." Ya

zauna, "Ko kin yi ihu ba wanda za ya ji ki. Mom bata

nan tana gurin aiki, Dad ma haka, su Nana da Suhaila

suna Makaranta." Na zube gwiwoyina biyu a rude ina

cewa, "Ka min rai kada ka sa ni cikin matsala, don

Allah." Na soma kuka. Ya ce, "Nima ki taimake ni na

gaji, wanene za ya gane me muka yi?" Na ce, "Allah ya

sani, na tabbata zai kama mu." Amma da yake Shaidan

ya hura ma Munnir kaho sam ya ki karban uzirina.

Muka yi ta zaga falon har na fada wani daki, sai dai

kafin na rufo tuni ya banko, mun yi damben bala'i dashi

kafin ya samu nasarar aikata mummunan nufinshi a

kaina, bayan ya bi duk wata gaba ta jikina ya bugeta,

fuskata kuwa ta sha mari sai na ga kamar ba Munnir

dina ba.

Kuka iya kuka na yi shi, na mike ina gyara daurin

zanina, da kyar nake tafiya na fito falon, ya ce, "Duk kin

sa mun wahala, a yanzu wa zau sani in ba kin fada

ba?" Na ce, "Bude min kofa kawai ni dai na tafi." Ya

nufo ni, "Come on kiyi wanka sai na kai ki." Ban san

lokacin dana daka mishi tsawa ba, "Budeni mana"

Sabon kuka ya kwace min na ce, "Allah ya isa tsakani

na da kai, Insha Allahu sai Allah ya saka min." Ya tashi

ya bude tare da cewa, "Sai na zo." Ban kulashi ba na

fita, dole na share hawayena saboda Maigadinsu, na

fita ko ina a jikina ciwo ya ke. A haka na kai gida, kallo

daya Inna ta min tace, "Lafiya?" Jikina ya soma bari, ta

ce, "Ba dai jikin nashi ba? Na ga duk kin rude fuska a

kumbure." Na ce, "Umm jikin ne." Ta ce, "To shine na

kuka? ki masa addu'a." Na ce, "To." Na nufi ciki. Ta ce,

"Hafsa zo nan, menene wannan a zaninki?"mummunar

faduwar gaba ta ziyarce ni, zufa kuma ta shiga keto

min, amma sai na yi saurin cewa, "Fashin Sallah ne."

Duk da ban juyo ba kuma ban san mai ta gani jikin

zanin ba. A gani na in muka hada ido zata gane, ta ce,

"Haka kika ratso titi? Ga ruwa da na daura chan kan

wuta na tuwo ki diba ki maida min sai ki dauraye

jikinki."

Cikin bayi ina wanka ina kuka tausayin Innarmu ya cika

zuciyata, na karya alkawarin da na daukar mata, Allah

ya isa Munnir.

Cikin kwanakin da suka biyo baya ko Munnir ya zo

bana fita, ranar da zan koma Makaranta har goman

safe ina kwance a tsakar daki, Innarmu ta ce, "Ke da

naji kina cewa sammako zaki yi? Har yanzun kin kasa

tashi?" Na ja tsaki, yanzun na soma tsanar boko bani da

daman in tona asirina...

Yaron gidanmu ya shigo ya ce, "Hafsa wai in kin shirya

wani mai mota ya ce ki fito yana can saman layi." Na

ja tsaki, "Ka ce masa ya tafi na san hanya." Innarmu ta

ce ma yaron, "Kai zo, je kace tana zuwa." Yana fita ta

fara min fada wai bani da hankali, ta lura kullum zai

kirani in 'ki fita, haka ake yi? In ma sabani kuka samu

ba sai kiyi hakuri ba tunda shi har ya zo? Na kalli

Innarmu a zuciya na ce, "Da kin san abinda ya min sai

kin fini tsanar shi." Ban ce komai ba na ci gaba da

shiri. Inna ta kwance habar zaninta kudine 'yan hamsin

hamsin dubu uku na adashena na kwasa, sannan cikin

robar can tumatir ne na tafasa shi ga sabulu can inji

Baabarki..... Na ce, "Ki bar kudinki." Ta ce, "A'a na dai

baki ne, amma badan zasu ishe ki wani abu ba ne.

Yaron nan dake dawainiya da ke Allah ya gwada min

aurenku." Yana zaune yana latse-latsen waya ya diro,

"Gimbiyata, amaryata har yau fushi kike da ni? Gashi

doguwar tafiya za muyi? Don Kano zan kaiki." Ban

tanka shi ba ya amshi robar hannuna da leda ya daga

but ya sa. Ni dai tamkar na haushi da duka nake ji, ya

bude mun gaba na shiga don bani da yadda zan yi.

Tunda muka dau hanya yake mun magana amma ban

tanka shi ba. Ya ciro waya daga gefen shi ya ce, "Ga

wayarki." Sai lokacin na yi magana, "Bana so." Ya

daurata kan cinyarshi, "Dole ki so ta Hafsat don in na

tafi karatu ta yaya zan dinga jin muryarki? Ki saki ranki,

abun da ya faru ba wata matsala bace saboda ni zan

aureki..." Na zabga mishi harara tare da cewa, "A

ganinka kenan, amma ni addinina bai yadda don zaka

aure ni kayi ZINA dani ba." Ya katseni, "Ki daina cewa

Zina." Na daga murya na ce, "Ka biya sadaki na ne?

Iyayenka sun nemi aurena gun iyayena ne an basu? Ko

jama'a sun shaida." Ya ce, "Ba daya." Na ja tsaki ban

kara tanka shi ba har muka kai.

A dakinmu ba yadda bai yi ba na'ki tankashi, ya aje

mun kudi da waya ya tafi. Na saka kuka nayi ma ishi

na, tunanina in Allah bai yi aurena da Munnir ba fa? Ya

sakani cikin matsala kenan don ban san mai zance ma

mijina ba yayin da yace ina nakai budurcina? Dole in

dauki hakuri in lallaba Munnir ya aureni.

-Yana kiran wayata sosai, tun ina sharewa har na

hakura don ban san yadda zan yi ba, sai dai bashi da

wata daraja ko kima a ido ba, ko na aureshi gani nake

ba zan girmama shi ba, tunda na ga irin nashi rashin

Imani.

Sai mene? Tun jiya sha hudu ga wata ya dace in ga

al'adata amma har yau sha biyar shiru. Wannan ya

tilastamin shiga rudani.

Dora John dakinmu daya har ta gane ina da matsala ta

ce, "Hafsy yaya ne?" Na ce, "Ciwon kai ne." Ta bani

panadol da sauri na sha don kuwa kan nawa na ciwo.

Kwanaki uku suka biyo baya gashi banji daga Munnir ba

cikin 'yan kwanakin, naje na sai kati na kira shi, yana

dagawa na soma kuka, ya ce, "Mai ya faru?" Na ce,

"Banga period dina ba yau kwana uku." Ga mamaki na

sai na ji bai damu ba ya ce, "Zan shigo wannan ba

wani abun damuwa ba ne."

Washegari sai gashi da wani abokin shi, yana shigowa

na soma kuka nan take ya bata rai, "Kukan nan ya

soma isata, zan barki ki karata in dai ba zaki daina mun

kuka ba." Abokin shi Bello ba karamin tsanarshi nayi ba

har da cewa, "Daga sau daya sai ciki?" Munnir ya ce,

"Nima dai nayi mamaki bata fa tsaya ba ma, gaskiya in

anyi bikin mu juya Mahaifarta za'ayi don bana son yara

su wuce biyu tsanani uku." Tsabar bakin ciki ya hana ni

tankasu, ni dai burina ya san yadda zai yi dani. Bello ya

kira wani abokin shi anan Kano wai shi Nasir, ya zo

suka tafi suka yi magana sannan suka ce inzo mu je

asibiti.

Mun shiga office din Likita mace 'yar kimanin shekara

arba'in tana tsaye da farin gilashi, ta tsareni da ido

bayan duk mun zauna ta kalli Nasir, "Me ke tafe da

ku?" Duk muka yi shiru, Munnir ne mara kunya shine ya

ce, "Mun kawota ne bata ga period dinta ba, so muna

so a gwada ta." Ta tsareshi da ido, "Kanwarka ce?" Ya

ce, "Budurwa ta ce." Bakin ciki ya cika ni, na sunkuyar

da kai ina hawaye, "To ku dan bamu wuri." Suka fita.

Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a

sarke na ce, "Wallahi...



Zaharaddeen  Shomar

what's app 08168575100



Sanadin Boko 1-03

Posted by ANaM Dorayi on 09:47 AM, 10-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

NA

Maryam Abdullahi K/Mashi

To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara,

"Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi

Anty fyade yayi mun." Ta ce, "Tun yaushe?" Na ce,

"Za'a kai wata daya." Ta bani wata 'yar roba ta nuna

min wata kofa, "Shiga toilet ki bani fitsarinki." Ina

fitowa naga wata nurse tsaye ta ce, "Don Allah sister

ina son result yanzun nan." Ba jimawa ta shigo, Likitar

tayi ta juya takardar sannan ta dube ni ta ce, "Kina da

cikin wata daya da kwanaki." Nan da nan na soma

zufa, zuciyata na kwadayin ina ma mafarki ne? Cikin

tsananin kuka da kunan rai na ce, "Ya cuce ni. Mai

zance da Innarmu? Abun da Baba yake tsoro ya faru.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Kuka na ya shigo da

su, ta mika mishi result ya duba sannan ya kalle ta, "To

yanzu doctor ya za'a yi tunda gaskiya ni da ita karatu

muke yi, bamu shirya taron Baby yanzun ba." Na dube

shi yana magana hankalinshi kwance kamar wanda ya

aikata abin arziki. Ta ce, "Baka shirya tarban Baby ba

mai ya kaiku aikata haka?" Ya ce, "Tsautsayi ne." Ta

ce, "A'a ku ji tsoron Allah, aure shine ya fi dacewa da

ku, karatun boko ba zai hanaku aure ba. Amma sai

kaga ana wasa da Sunnag kun zabi boko sama da raya

sunnar Manzo (S.A.W), to ku sani Manzon Tsira

(S.A.W) ya ce aure Sunnar shi ne, duk wanda ya ki

sunnarshi baya tare da shi. Kun fi yadda kuyi ZINA fiye

da aure." Ta nuna shi da biron hannunta, "Musamman

irinku 'ya'yan 'yan boko, Iyayenku sun rike wuta sai

kunyi karatu mai zurfi basu damu da halin da zaku

shiga ba kasancewarku balagaggu, burin su ku iya

turanci tare da kawo musu kyawawan sakamako

lokutan jarabawar ku. Ba su damu ku san addininku ba

bare kusan illar ZINA."munir yace to doctor, yanzu

menene mafita? Don matsala ne cikin nan don Allah a

cire shi tayi suru tana tunani. Bello yace in bazaki

iyaba muje wani asibiti doctor hindu tayi shuru tana

nazari, tace to zan tai makeku sai a lokacin naji sanyi

ya ratsa zuciya ta. Ta bani wasu kwayoyi wai kafin nan

da sati daya zai fita, suka ce nawa? Tace dubu goma

nan take suka biya. Sun saukeni makaranta sanan suka

wuce, da alkawarin zaya rinka kira yaji abinda ke tafiya.

Yau kwana tara shuru sai laulayin da nasoma gadan-

gadan, ga sheka amai nan ga zazzabi na kwasa na

koma wajen doctor hindu ana kai mata kati na tace a

turo ni duk da yarinyar da naga ta shiga bata fito ba,

itama yarinyar duk a firgice take, taci kuka ta gode

Allah nace sannu doctor. Tace yauwa ya jiki? Cikin

saurin baki nace da sauki amma fa har yanzu bai fita

ba. Ta mikye tare da diban wayoyin ta ce ku biyo ni.

Muka biyo ta cikin harabar asibitin muka nufi wani gida

kirar zamani dan madaidai ci. Ta umurce mu mu zauna

kan kujerum da ke kayatacen falon,ta shiga wani daki

daga cikin dakunan biyu dake cikin falon. Jim kadan ta

fito ta canja shigarta zuwa doguwar riga ta atanfa. Ta

shiga kicin yafito da doguwar gorar ruwa (swan) da

kofuna guda biyu. Ina takure cikin hijabi na, zazzabi ne

ya rufe ni ta tsiyaya ruwan ta miko min, sha ruwa nace

a a sanyi nake ji ta koma takawo min paracetamol na

sha. Ta zauna ta zuba mana ido, ta dubi dayar tace

asabe ko? Yarinyar tace eh, menene labarinki?

Yarinyar ta ce, Sunana Zainabu,amma an fi kirana da

Asabe.Mu 'yan asalin nan kano ne, a karamar hukumar

kunci can wani kauye ana ce masa kurje. Wata mata

mai suna Gambo tana zuwa kayaunkan garinmu tana

diban yara 'yan aiki, wata rana taxo gidanmu ta ce da

Babata su bada ni ana samun kudi sosai, wai can zan

samu kudin kayan daki. Sai na ce ni ba zani ba, nafi

son nan don ina talla kuma ina zuwa karatun allo. Sai

Babata ta ce to abar shi, don Babanmu in ya ji ba zai

yarda ba, ta ce can ma ana karatun Muhammadiyya,

kuma za su saki ga cima mai kyau za ki canza. Haka

dai ta zuga Babata hr ta yarda, sai da suka yi rigima da

Babana sannan ya yarda. Gidn Hjy Mairo aka kai ni, ba

wani aiki sosai kuma bata da tukara. Ba ta da Matsala

in kaga damuwarta to ran danta ya 6aci, don shi ne

dan ta kwallin tal. Yawancin aikin nawa duk nashi ne

don tana zuwa aiki shi ma yana zuwa makaranta,

amma ya fi ta zama gida.Ba mu cika shiri da Yasir ba,

don shi yana da fada. Watana 3,ranar wata Litinin ina

kicin, ya shigo wai in dafa masa Idomie, nan na bar

komi na shiga dafa masa, don Hjy ta ce kome nake yi

in yazo da nasa in bari in masa don a zauna lfy. Ba ta

so ta ga yana zagina, na ce to. Da na gama na nufi

dakinsa, na aje zan fita ya ce in dawo, cikin sauri na

dawo don ina matukar tsoronsa, kawai sai ya ce in cire

kayana. Na soma zare ido, ya ciro wuka da sauri na

cire ya kwantar dani ya aikata alfasha da ni, sannan ya

hana ni kuka. Ya kuma ce idan wani ya ji sai ya kashe

ni. Naja baki nayi shiru, duk uwar wuyar da na sha tun

daga nan muka daina fada, Yasir ya maida ni tamkar

matarsa. In Hjy bata nan sai ya kira ni dakinsa, akwai

lkcn ma da Hjyn taje Umra ta barmu tare da wata 'yar

uwarta don ta lura da mu, da kuma gidan,amma Yasir

cikin dare zai zo ya buga in kofa, dakinshi nake kwana.

Nan da nan nayi wani girma, kirjina ya cika. Daku abn

da ya gani zai sai min,wata rana na tashi ba lafiya,sai

amai nake shekawa,Hjy ta kira Likitansu tun kafin ya

gwada Ni ya ce yana zaton ina da ciki,ya ce amma bari

dai ya gwada. Gwajin Farko ya nuna ina da ciki, nan ta

shiga salati da sallallami, ta tsare ni wai in fada mata

wanda ya min, na ce Yasir ne.

Nan ta hau ni da duka wai na masa sharri, dan shekara

ashirin da biyar dinne yaya iya yi min ciki? Da ya dawo

ta tambaye shi da har ya musa sai yaga ta watso min

kayana, wai na tafi zan yi ma danta sharri, sai ya ce

mata shi ne,amma tsautsayi ne. Ga mamakina, bata yi

masa wani fada ba, sai dai ce masa tayi kada ya kara,

kuma Babanshi zai dawo. Ta kai ni wani asibitu aka

cire min shi ta dinga min fada wai ko ya kira ni kada

naje. A cewarta, wai bashi da laifi ni ce mai laifi. Sati

biyu ina jinya, Sannan na gyagije, ganin ta sa mana ido,

sai ya ce in dinga barin dakina a bude zai ringa zuwa.

Na ce Hjy ta ce mu daina. Ya sake zare min ido, dole

na bi yanda yake so, wai baya so Hjynshi ta sani, don

ta ce mishi in ya sake sai ta aura masa ni, shi yasa duk

ya tashi hankalinsa yanzun. Doctor ta ce, To shi baya

son ya aure ki ne? Asabe ta ce, tab ita ma nasan tana

tsorata shi ne, domin ba ta da burin yayi aure yanzun.

Burinta shi ne ya yi karatun boko mai zurfi,kuma ya

zama wani abu a kasar nan SANADIN BOKO." Na jinjina

kai, tuni zazza6ina ya sauka. Labarin Asabe ya ta6a ni,

kallo na dinga bn ta da shi, Yarinya ce ba zata wuce

Shekara sha uku zuwa sha hudu ba. Wanna ma ai child

abuse ne, ya kamata a hukunta su shi da Hajiyar shi.

Doctor ta katse min tunani da cewa Hafsat me ya faru

da ke kuma, menene labarinki?? Na zuba mata ido,

hawaye suna zubowa, ta ce fada min ina so ne in

taimake ku, na ce zaki cire min cikin? Ta ce Eh, zan

cire miki in har naji labarinka, kin cancanta a cire

miki.Ina nufin in ban da son ranki hakan ta faru ba. Na

share hawaye,sannan na ce da ita. "Sunana Hafsatu,

Mahaifina dan asalin jihar Borno ne, ya fito daga gida

tun zamanin yana saurayi, a kano ya yada zango, nan

yake 'yar sana"arshi.Sun hadu da Mahaifiyata a can

lkcn tazo gidn yarta a Na'ibawa. Babana Shi ne ta

tambaya ya yi mata kwantancan gidan Malam Ma'aru

me Almajirai mijin yarta kenan.Daga lkcn ya nuna yana

sonta, ta amince hr yaje Maliunfashi jihar Katsina,

unguwar Fayamasa. Ya samu kar6uwa cikin dangi, don

yana da nutsuwa da ilimin addini aka ce ya turo

magabatansa.Mahaifanshi sun rasu sai babban wansu

Babagana, shi ne ya zo suka hadu da wani uban

dakinsa. A nan kano suka zo, sune suka amsar masa

auran Innarmu.Ba su jima a kano ba ya soma zuwa

kaduna, ya fara sana'ar saida lemo da Ayaba,daga

bisani ya nemi gida a hayin rigasa ya dawo da

Innarmu,lkcn tayi haihuwar farko wato Yayana Ummar.

Gidanmu gidan haya ne, Mai girma gaske a layinmu kaf

ba gidan da ya kai namu yawa don gidan yawa ake ce

mana. Mata goma sha ne, kowace da 'ya'yanta wasu

hudu wasu shida,wasu goma sha. Babana ya sake auro

wata matar daga kano, itama nan gidan ya samu daki

kusa da na Innarmu., Babah tana da kirki da nutsuwa,

shi yasa duk yanda Innarmu taso suyi rigima bata

biyewa, dole itama ta saki suka zauna lfy. Yanzun

Babah 'ya'yanta 6, Innarmu 8. Ni ce 'ya ta 2, masu bina

3 duk maza ne, sannan mata. Innarmu gidan su 'yan

boko ne, ko na ce kowa yasan Katsinawa da boko. Don

haka tana da burin mu 'ya'yanta muyi boko, shi ko

Baba ba ya da burin mace ta wuce primary. A nashi

ra'ayin nayi saukar Alkur'ani mai girma ya min aure.

Tun muna kanana Innarmu ta kwadaita mana boko, don

haka ni da yayana mun taso muna son karatun

boko,Primary 5 Umar yake lkcn da ni ma aka sani.

Babanmu bai cika biya mana kudi Makarnta ba, don bai

cika samu ba.Amma in yana da shi yana ba mu,ganin

haka ne yasa Innarmu ta kama sana'a. Gyada take

soya mana ni da Yayana in lkcn dafaffiya ne kuma ta

dafa mana da wannan muke samun rufin asiri. Cikin

haka Yayana ya gama Primary aka kukata ya shiga

Junior. Kwanci tashi nima na gama primary, sai dai

lkcn ne Baba ya ce Bokona ya isa haka, izifina ishirin a

Islamiya ya ce da na sauke za a min aure. Innarmu ta

ce ina, yanzun kai ya waye ko ita tayi makarantar gaba

da primary balle 'yarta. Sun yi hatsaniya hr abokinsa

makocinmu Baba Garba, ya saka baki kan cewa Baba

yayi hakur ko aji 3 in yi wato karamar Sakandire. Baba

ya ce, shi kenan,amma fa ba ruwan shi, ko yana taka

kudi ba zaya ba ni ko na fensir ba. Abubuwa suka kara

yi wa Innarmu yawa, ga Yayana Umar kudin jarabawa

yasa makarantar tsaya. Sai dai karen mota ya koma

yana yi wa wani mu2m a layinmu,kasuwa-kasuwa.Inna

ta zaunar da ni ta ce Hafsatu,kin san yanda zamu yi?

Na ce A'a na me? Ta ce, na karatunki, kina so ko? Na

ce "Tab so kai ba ki ga su Saliman ajinmu na su suna

ta zuwa, ta ce to dagewa za ki yi zan dinga alala da

safe ki dan zaga. Sai kuma ki zo ki dauki gyada, na ce

Innarmu ni wlh Na gaji da talla,wata rana mu2m ya yi

ta yawo a ki sayar ta ce sakarya kin zaga tas za a

saye. Asusu zan yi riba ko nawa aka ci sai mu zuba

kafin gama zangon farko mun tara kudin da za ki shiga,

na ceto,gwangwanayen gyada muka fafe wasu tayi

alala.Nan da nan ya kare, Ta dafa min gyada na dauka

ta ce maza Hafsatu, Allah ya bada sa'a kin ji, kan lkcn

Ismaiyya ki saida. Na ce to, Ta ce bn da wasa fa, don

na san ki, na ce to.Wasa kam inadashi,kowa ya sani

har na gama primary duk report card dina ba wanda ba

a rubuta min na cika wasa ba, a haka kuma nake

karatuna.

a haka kuma nake karatuna haka kuma na dage da talla

na wata ranar litinin ina tafiya nice har baban titi na

tsallaka, sai ga wata yarinya tana tallan kwakumeti,

tace ke ina kike zuwa? Na ba ko ina yawon talla nake.

Tace zomuje (governmeet college) ana cinikin gyada in

yan makaranta suka tashi nace, to muje tafiya ce sosai

har gidan gwamna ta nuna min. Muna isa agajiye muka

zauna gin din bishiyoyi ga yan talla nan kala-kala har

da masu gyada babu abin da yafi mun dadi irin yanda

naga yara nata wasa saboda yan makaranta basu tashi

ba. Masu carafke masu yar gala gala nayi, wasu na

tayin ziro-ziro duwatsu na tsinta nima nashiga yin yar

carafke, batare da na huta ba koda dalibai suka taso

nan kowa yasaki wasa suka shiga saida kayansu, ni ko

ban damu ba na cigaba da wasa na sai da takowa ta

kare sanan aka shiga siyan nawa. Washe gari nacewa

innarmu a kara mai makon mudu hudu a dafa biyar.

Yau ma wasa na dora haka nan sai da ta kowa ta kare

don su suna zaune, a gaban kayan su niko ina can ina

wasa na. Zuwa yanzu na saba da dabar hanya zuwa

(government college) wata rana ina zaune kan duntsen

da na dasa a matsayin abin zama na, gaban tirena

hannuna zarene ina ta wasa dashi na hada injin nikan

barira inata yar waka ta. Sai naji magana kusa dani

ance ke gyadarki ba ta saida wa bace? Ba tare da na

dubeshi ba nace ta saidawa ce mana,ya ce, "Sa min

daya a leda sarkin wasa." Na ce, "Zaba." Ya ce, "Zabar

min." Sai lokacin na kalle shi na dan kara zare ido

saboda kyawun shi. Haka nan ba Uniform a jikin shi,

kenan ba dan Makaranta ba ne. Na mika mishi ya ciro

wani farin kyalle ya shinfida akan jijiyar bishiya ya

zauna ya soma cin gyadar. Ni kam kallonshi nike a

raina ina cewa, "Dama 'yan gayu suna cin gyada?" Ya

dube ni, "Ki yi wasanki mana kada ki sa na kware." Na

dauke idona daga bisani na tashi, na soma 'yar gala-

gala ta. Yana lura da yadda kowa ke tsaye kan kayansa

banda ni, da ya mi'ke zaya tafi ya ce, "To sarkin wasa

ga kudinki." Sabuwar naira biyar ya bani a mike, a

rayuwa ta babu abinda ke burgeni irin sabon kudi, na

ce, "Amma na gode, kalleta kar-kar bazan kashe ta ba."

Ya ce, "Mai zaki yi da ita?" Na ce, "Ajiyewa zanyi ba

zan sashi cikin asusu ba bare har na lankwasa ta."

Murmushi yayi sannan ya ce na bashi daya. Ba bashi

ya ci rabi ya bar saura, na ce, "Ji fa baka cinye ba." Ya

ce, "Na koshi." Da zai tafi ya kuma bani sabuwar naira

goma wai in bashi canji na ce, "Wai don Allah kai kuwa

a ina kake samun sababbin kudi?" Bai amsa ba yana ta

kallona. Na ciro tsohuwar biyar na mika mishi. Ya

girgiza kai, "Ba na amfani da Tsohon kudi." Na ce,

"Saboda mene?" Bai amsa ba ya ce, "Gobe zan amshi

gyada." Na ce, "Toh"Ku san kwana 2 ban ga mu2min

ba, sai ranar 3. Yau ma shigar shi ta 'yan gayu kamar

kullum. Ya amshi gyada zai tafi ya kuma bani sabuwar

10. Na ce a, ka manta ne kana bi na canji? Ya ce haka

ne, to rike wannan don ni in na ciro kudi bana maida

su. Na ce ko? Tab, amma dai sun maka yawa ne ko?

Ya dube ni ba alamar wasa, ya ce "Mu ne ai muke kera

su. Na zaro ido ina kallon shi, cikin matukar mmk

"Kana nufin ku ke buga kudi? Ya sake dubana, kwarai

kuwa, na Maida hankalina duk a gare shi. Ka ce kana

da su lodi? Ya saka hannu cikin aljihu shi ya ciro

sabababn dal 'yan naira ashirin da goma-goma na zaro

idanu. Tabbas yanzun na yarda na ce kai ko kaji

dadinka, ina ma ni ce. Ya ce da me za ki siya? Na ce

na farko zan biya kudin makarantana, kuma na dinga

sai mana kayan dadi da su nama da mota, su

mashin.Kai komai sai na sai mana. Ban lura ba, ashe

shi kam dariya na ba shi, ya ce to ai ni kin ga duk na

siya abubuwan da ki ka ce, na yarda kam, shi yasa

gaka nan dan gayu da kai, ka ta6a zuwa kasar waje?

Ya sake darawa, sannan ya ce eh, da yawa ma. Ya tafi

ina ta kallon shi. Sa'a da Zaituna wadanda muke tafiya

tare dasu, da na basu labarin dan gayun nan na ce

ashe sune suka buga kudi kin yarda suka yi. Suka ce to

in shi ne me zai kawo shi nan yana karyawa? Na ce shi

ne ya fadamuku karyawa yake yi? Suka ce min tun

yaushe suka san shi a nan Makarantar. Na ce ko dai

yana koyarwa ni na yarda su ke buga kudi, Ga sabbin

kudi nan dami a gunsa, Lura da su Sa'a suka yu cewa

ba zan yarda da su ba sai suka bar ni. Sau dai suka ce

min ni wawiya ce, sai ka ce bn yi zaman aji ba, sunan

na gama aji 6 bn san komai ba, na ce naji din. Su

Innarmu a da Baba na kuke ina ba su labarin dan gayu

mai buga kudi, amma wai sai suka ce zolayata yake yi,

nayi duk wani kokari na wai don su yarda da ni cewa

gaske ne,amma sun ki. Sai dai na dauki alwashin zan

masa tambayoyin da zai gamsar da su.

washegari jumma‘a ba mu cika jimawa ba, saboda ana

sallah juma‘a a masallacin da ke kallon makarantar

amma kin bin su Sa‘a nayi na fake da cewa sai gyada

ta ta kare. In tashi yan makaranta tuni sun watse ina

ina zaune gaban gyada yar ragowa ce ma, sai kalke

kakle nake. Can na hangoshi zai shiga makarantar, ya

sanye da wani ubansun yadi fari kar hatta takalminshi

da hular kanshi. Duk da yau ce na soma ganin shi da

manyan kaya ban kasa ganeshi ba. Da gudu na bishi

ina cewa tsaya tsaya ban san sunan shi ba bare na

kira. Shiko bai san dashi nake ba a haka mukayi nisa

cikin makaran tar sai dai wani ya lura shi nake bi sai

ya tai maka ya tsai da mun shi. Na lura yaji mama kin

ganina yace, sarkin wasa ina zaki haka? Na tsaya ina

haki saboda gudun da nasha yace sannu na ce yauwa,

dama kai nake ta jira zan tam bayeka ne. Yace na me?

Nace wai dan Allah da takarda kuke yin kudi? Yayi

dariya har hakoranshi farare suka fito yace eh, da

takarda ne to in na baka zaka iya yi min saboda

mutane sun kiyarda ne dani in nace naga masu buga

kudi sai ace karya ne zolayata kake yi. Yace zanyi

maki in kina so nace innaso kai, to da wace irin takarda

kuke yi? Yace ta rubutu nace gobe zan duba jaka ta da

in dauko. Yace ba ayi fa da tsohon littafi ko kina son

tsohon kudi ne? Nace a a taf na fison sabo yace to

shike nan ki kawo sabo nawa za abuga maki yawan

kudin? Nace zaka iya min dubu malala gashin tunkiya?

Ga mamaki na sai naga yana dariya har da rike ciki

nima na soma dariyar ya numfasa ya ce,in ban da abin

ki sarkin wasa wane ne ya san yawan malala gashin

tinkiya, Na ce to ko dai nawa ne ina so yanda dai ishe

ni na gama karatuna. Ya ce,wai dama nan kin yi

karatu? Na dube shi, ba na fada maka ba cewa na

gama primary? ya ce ban ji ba lokacin da ki ka

fada,yanzun JS1 za ki shiga? "Eh tallar da nake ai kudin

rijista muke nema, kaga in ka bugo min kudin na daina

talla, ina gama secondry har ta gaba in je in fara aiki.

Ya ce "Wane aiki ki ke son yi,? Ina nufin me ki ke son

ki zama? na daga kaina sama ina nazarin ya ma ake ce

musu? Ya ce ba ki san me ki ke so ki zama ba? Na ce,

"Ya ma mutanen da ke yin labarai a Talabijin ko

Rediyo? Ya ce, " Media ki ke so? na ce yawwa, haka

zan zama 'yar media,yayi murmushi, to ni zan wuce, ina

kayanki? Sai lokacn na tuna da tirena da kudina cikin

ledar gwangwani, na ce to sai gobe. Na tafi ina

waiwayanshi, ina cewa kai,wannan mu2min dan gayu

ne,ga kamshin turare yana yi. Ranar Litinin tsawo naga

ta min,yau kam d murna na iso,na nutsu ban yi wasa

ba,saboda wata zuciyar da ke ce min in ya ki zuwa fa,

ga shi na zo da sabon littafina, ba karamin damuwa

nayi ba da na ga lkcn tafiyarmu yayi ban gan shi ba.

Ina kulle gwangwanaye sai gashi, na ce hr na cire rai,

ya ce ai zan zo, na ciro littafi na ba shi, tare da cewa

wannan takardar ta isa? Ya ce eh, na ce na gode, na

mika mishi gyada tare da cewa na rage mishi ne. Ya ce

ya gode ya tafi. kai, kuruci dangin hauka, nifa

tsakanina da Allah na yarda suke buga kudi. Daga

ranar ban kuma ganin shi ba, Kusan sati 2 hr na soma

tunanin ya gudune da kudina kun ji shirme. Wata ranar

Jumma'a ranar za a yi wa dalibai hutu hr cikin

Makaranta muka shiga muna ta ciniki,mun saida mun

fito sai na hango shi tsaye gurin zaman mu. Da sauri

na isa gurin shi, me bugakudi......


Zaharaddeen shomar

whatsapp 08168575100



Sanadin Boko 1-04

Posted by ANaM Dorayi on 09:56 AM, 10-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

@* NA

Maryam Abdullahi K/Mashi

"Da sauri na isa gurin shi, me buga kudi ina ka tafi na

daina ganinka? Ya ce aikin kudin ki ne ya 6oye ni, na ce

Allahu! Har ina cewa ka gudu. Ya yi dry, na gudu da

kudin ki ki ke zato Na ce eh, nima ina dry. Ya ce kai kina

da bn dry, to ga kudinki,amma muje gidan ku na bawa

iyayenki kada wani ya bi ki ya kwace. Cikin murna na ce

to daga nan ma in sun gan ka sun fi yarda. Na kama

hanya a kafa ya ce ga mota can zo muje, in kin san

hanya direbn mu sai ya kai mu, ba tare da wata shakka

ba na ce to. Sam na manta da su Sa'a, sai da zamu

shiga motar naji muryarsu,suna cewa ke Hafsatu ki ka

sani ko dan yankan kai ne? Na dube shi, shima ya ji

amma sai yayi tamkar bai ji ba, na ce ba wani dan

yankan kai na shiga motar da dan tirena, shima ya shiga

ya ce kawarki fa,shawara suka baki nace tame? Yace

kin san ni ko dan yankan kai ne? Duk da gabana ya fadi

amma sai na dake nace, bakayi kama dasu ba yace suna

da kama ne? Nace oho amma kai bashi bane yace, dama

sunanki hafsatu? Nace eh abakin su sa‘a kaji ko da suka

kirani dazu ko? Yace eh nace yan bakin ciki ne, dan fa

nace masu kana buga kudi sai suka ce mun karya ne, kai

malamin makaran tane. Yace gaske ne ni malamin

makaranta ne, amma daga yau na gama nace, duk da

kudin da kuke bugawa basu ishe ka ba sai kayi koyarwa?

Yayi dariya yace bautar kasa aka turoni daga jahar mu.

Nace bautar kasa kuma? Yace kema watarana zakiyi in

dai kikayi karatun da kike fadi, gwamnati zakiyi wa aiki

na wata tara ko shekara.

Ban gane nufinshi ba amma nace Allah yasa naga

lokacin.

Da gudu na shiga cikin gidan mu ina cewa inna fito kiga

mai buga kudi ya bugo min inna ta saka hijab ta fito tana

cewa ni ban gane wanan shirmen naki ba, ina mai buga

kudin? Wannan yarinya da wautar tsiya kike inna tayi

turus lokacin da tayi arba da rantsatsiyar motar tace

hafsatu aina kika jajibo wadan nan...? Cak! Maganar ta

tsaya lokacin da saurayin ya bude motar ya fito

kyawunshi yasa inna tunain ko aljani na janyo, ta soma

karanta (ayatul kursiyu) zata juya gida na rike mata

hannu. Inna dan Allah ki tsaya mana zo muje gurin su

tace a a hafsatu muje ciki bana tsamanin wadannan

bil‘adama ne nifa nasan banda aljan ke ina kika isa kiga

mai buga kudi, sai dai in jabun kudi. Saurayin yatako har

gaban inna ya dan rusuna ya gaishe ta, ta amsa tana

dan dari dari, nace to wanan ce inna ta sai ka bata

kudina inna tayi ta maza tace samari daga ina? Ni fa ban

fahimci surkulen da yarinyar nan take yi min ba? Yayi

mur mushi ya dube ni jeki kawo min ruwa nasha, da gudu

nayi ciki ban saurari inna ba da takecewa in dibi na baba

yafi sanyi

ina tafiya ya dubi inna yace mama zolayarta nake yi, ni

dan bautar kasa ne an turo ni daga Adamawa state, ina

koyarwa a makaranantar da take zuwa talla. Yawan

wasanta ke burgeni har na shiga sabagarta, sai kuma na

fiskanci cewa tana son karatu amma rashin hali ya hana

hakan. Dan ta fada mun tana talla ne dan kawai ta tara

kudin makaranta. To ni nazo ne in ba damuwa zan

taimaka mata don ni daga yau in sha Allahu na bar

kaduna kenan, don na gama abin da ya kawo ni, dai dai

nan na taho da ruwa na ce masa gashi. Inna tace mika

mashi yace a a dama basha zanyi ba bakiga na sha ruwa

a mota ba? Nace eh yace to maida. Yaci gaba da cewa

dama nawa ne kudin nata? Tace ni ban tambayi nata ba

amma lokacin na wanta inaga dubu uku muka kashe? Ina

ga ba zai wuce hakan ba. Ya ciro yan daurin nera goma

gama guda uku sababbi fil ya mika mata ga wanan

mama dan Allah ku biya mata kudin makaranta, ku cika

burinta har tazama abin alfahari nan gaba. Allah ne kadai

ya san al‘ummar da zasu anfaneta. Innarmu jiki yana bari

ta amshi kudi tana ta zubo mashi godiya ma, sai daka

tsale nake tamkar yarinya karama, ina cewa shi kenan na

huta talla. Innarmu ta harareni tana cewa to kiyi mashi

godiya mana, nace na gode yayi murmushi ya tafi yana

daga mun hannu nima haka. Sai dai kash nayi mantuwa

ban tambayi sunan shi ba, a lokacin ban damu in san

sunan shi ba muka nufi cikin gida da murna innarmu bata

da rufi, don haka a tsakar gida ta fada musu cewa wani

bawan Allah ya taimaka min da kudin makaranta. Wasu

suka taya mu murna ciki harda babarmu, wasu kuwa sun

nuna bakin cikinsu a fili don Ade ina bayi naji tana cewa,

maman abba yau kinji matar nan mu zata rainamawa

hankali ta dai tura yarinyar ta maula. Maman abba tace

ai shegen son kudi irin na maman hafsatu ya isa, ace

mata sai rashin godiya Allah duk fa kokarin mujinta ta

raina. Daga can asabe ta sako baki shi wannan mujin

nata ai tuni ta gama dashi katsinawa kuma da shegen

asiri? Dubi fa fada irin na mutumin nan sai da tasha

karfin shi ga kishiya kuma sai yan da akayi da ita Ade ta

ce, ayi dai mu gani, kina nan yarinyar zata janyo mata

abin kunya, Maman Abba ta ce ta dage sai yarinya tayi

boko, za su ga boko ai. Na fito cikin takaici ina kallon su,

sai nan da nan suka canza mgn. Asabe ce suna ta zagin

ki,wai kina asiri ke Bakatsina,wai zan ja miki abin kunya.

Inna tana da fada, balle in an ta6o ta, ta fita da sauri

Yayana Umar ya hau ni da fada,wai don ubana ni

mahaukaciya ce da zan fada mata, na ce ka ji gulmar da

suke yi ne? Hayaniyarsu ce ta fito da mu, Umar ya je

yana cewa, Inna ta bari ta dawo daki, nan dai haka gidan

kan rikice wani lkcn. Musamman in ana fada kan yara, ko

gulma. Innarmu tana da fada kowa a gidan yana shakkar

ta6o ta. Bayan komai ya lafa, muna daki ta ce "Hafsatu

kin dai ji da kunanki, ina so ki baiwa mara da kunya, ki

kare min mutuncinki, kiyi karatunki ki zama abn sha'awa

da kwatance na ce to Inna. Cikin kwazo na soma

karatuna, kudin dan gayu mai buha kudi ya bugo min sun

taimaka min kwarai. Inna tayi musu kyakykyawan

adani,sun ishe ni har zuwa lkcn da na gama JS 3, lkcn

shekaruna 14 girma ya soma zuwa min 'yan alamu sun

bayyana. Na kan ji mutane suna cewa, wai ban cika kyau

a fuska ba, sai dai jiki. Yawan fadin ina da diri shi ne ya

sani jin cewa ni mace ce musamman in nayi kwalliya.

Wata safiyar Jumma' naje fitsari sai naga jini, cikin

fargaba nazo har da hawaye nake fada wa Inna. Ta ce,

Hafsatu girma ne ya kama ki yau nawa ga watan bature?

Na ce 7. Ta ce to duk 7 ga wata za ki ga wannan jinin.

Ta iya yiwuwa yazo kafin 7, ko bayan 7, amma duk wata

dai za ki gan shi. In kuma ba ki gan shi ba hakan na

nufin kina da ciki. "Na zaro ido ta ce ai ba a samun ciki

haka sai in kin kasance me wasan banza da MazaNa

sauke ajiyan zuciya,don nasan bana yi. Na ce ni dama

ba ruwana da maza, ta ce na sani, amma ki kara.sannan

ki kara sa tsoron Allahn ki cikin zcyrki. Daga yau din nan

an bude miki fayil dinki, duk aikin alkairi ki ko akasin

haka za a rubuta miki, don haka sai ki kula, ki kuma san

me ki ke ciki. Tun daga wannan lkcn nasa ma raina

tsoron maza, nake kuma duba duk wani aiki da zan yi

zunubi zai ja min ko lada.

Marubuciyar tace'Yan uwa mata zan dan mana wani tuni

nan gurin, mu nutsur da 'ya'yanmu muyi musu bayani

mai kyau tare da nutsa tsoron Allah cikn zukatansu, lkcn

da suka samy kan su a irin wannan yanayin na

balaga.....Allah yayimana jagora

Ba zan manta da Jumma'ar ba, misalin 4 da mintina na

yamma gari yayi sanyi La'asar, nayi kwalliyata da riga

da wandon pakistan da Inna ta sai min a gurin wata

mai gwanjo. Kore ne kalar lemun tsami da gyalanshi,

Sakina kanwata yarinyar Baba kishiyar Innarmu ta ce "

Yaya Hafsatu zan biki." Na ce, zo muje gidan kanwar

Innarmu zan je Hayin Malam Bello na kai mata kudin

dashin sabulu da suke yi. Ko can gidan matan gidan

suna ta yaba yanda kayan suka yi min kyau.Dai-dai kan

layin Biliya wasu matasan samari suna tsaye jikin

mashin, kallo daya na musu na dauke kaina ban kuma

kawo komai a raina game da su ba. Sai naji takun

tafiya, ana cewa 'yanmata ji mana,maza sun sha yi min

haka bana tsayawa, don Innarmu ta fada min karatu

basa haduwa da soyayya, kada na sake na kula kowa.

Ya zagayo ta gabana Beby saurare ni mana. Na' kalli

fuskarshi,sai zcyta ta buga, ina son mu2m mai kyau,

daga ganin shi dan gidan 'yan gayu ne. Na harde

hannuwana a kirjina, ya sake dubana daga sama kuwa

gsa kasa, "Wow! Ya sunanki?" na ce "Hafsatu." Ya ce

"Nice name, Hafsy ina ne gidanku?" Kawai sai na samu

kaina da yi masa kwantance, can kasa muke Abuja

Road, layi na shida marar kwalta, kana zuwa layin ka

ce ina ne gidan yawa za a nuna maka. Ya dan yi shiru

don ya fahamice a geto take amma sai yace zan zo

anjima ko gobe zan samu ganinki? Nace eh yace to sai

kin ganni na tafi ina wai wayanshi sakina tace yaya

hafsat mijinki ne? Cikin yar dariya nace eh mijinane

wasa ne ya ruda ni na kasa sukuni, tare da boyiwa

innarmu don kada ta hanani fita, sai dai har tara banji

ance ana kiran hafsa ba,har fita nayi gurin bakin titi ina

tunanin wai ko yazo bai gane layin ba na dawo daf da

zan shiga gida na ganshi tsaye kofar gidan mu. Wani

sanyi naji acikin zuciyata, sai na soma tunanin zan jene

na ce mashi gani ko ko ce mashi zanyi ni kake nema?

Sai na yanke shawarar na bi ta gabanshi, har na daga

labulen buhun da yake kofar gidadanmu zan shiga, sai

naji yace hafsy sai na tsaya tare da sauke a jiyar

zuciya, sannan na wai wayo na tako cikin irin tafiyar da

ban taba sanin na iyata ba. Duk da yake dare ne a kwai

kwan lantarki a kofar gidan, yace nafi minti 5 ina jiranki

nace ina yini? Yace lfy da farko dai sunana munnir jafar

dalibi ne a (A B U) zariya ina shekara ta 2. Sanan

muna zaune ne a nan makarfi road son munnir ya kara

shiga ta, don a rayuwa ta inaso in auri miji dan boko

nace ni kuma na gama js3, yace me ya hanaki cigaba?

yanayin garin ne. Haka muka ta fira sam bansan dare

yayi ba har 10 ta gota ba sai da naji karan raidiyon

baban mu ya nufo gida. Ya tsaya tare da cewa wacece

nan? Ke hafsatu me kikeyi haryanzu? Na dubi munir

nace ga baba na. Ya cire hular kansa hana sallah yace

ina yini baba? Ya dubeshi lfy lau zo ki shige muje, nace

to sai anjuma yace zan zo gobe nace to. Tun kafin

mushiga daki baba yake min fada tare da tambayata

wanene wannan yaron ya dame kugu? Nace dazum ne

muka hadu dashi. Hayaniyar shi ne ta tashi inna daga

dan baccin da ta soma, tana tam bayarshi lfy malam

kake fada da tsohon daran? Yace amma dai ke

sakaryar uwace, 10 ta wuce yarinyarki tana can tana

zance da wani kato ke kuma kin hamgame baki kina

bacci Inna tace hafstu na can tayi baci tuni dakin

babarsu, ba ita kagani ba ita da bata fita zance ma

yace to ga tanan ma bare ki karyata ni. Inna tace hafsa

zance kika fita? Ya mukayi da ke? Baba yace ni dai

tashi ya turo mun iyayensa dama ni burina in aurar da

ita. Inma shi bayi zaiyi ba akwai mutane da dama sun

min magana. Inna tace je ki kwanta itama ta maida kai

ta kwanta alamun zancen baba bai shigeta ba. Da safe

ta tsareni da son jin wajen wa na fita? Nace inna wlh

jiya ne fa da kika aikeni ya ganni shine yazo. Tace

amma nace maki ki fita hanyar samari ko? Kin san

babanki matsawar zaki rinka tsayawa zance kina son

karatun nan zaki barshi ko nace inna naga shi wannan

yana son karatun, don su gidansu yan boko ne. Maman

shi da baban shi duka aikin gwamnati sukeyi yace min

jami‘a yake yi (A B U) zariya tace to ni dai banaso

kurinka tsayawa nace yama ce zai bani kudi nacigaba

da karatu na. Inna tace to indai ko haka ne sai dai

kitafi makarantar kwana, saboda kin san babanku sarai.

Koda munnir yazo washegari, haka na zauna na fada

mashi komai dangane da ma haifina game da kin boko.

Yace taf kice cutarki zaiyi? Tun kina karama zai

kasheki da aure ai gaskiyar innarki ne kada ki yarda.

Nace kudine matsalar mu sai dai in shiga ta kwana

yace haka ne, yace zan baki kudi bari dad dinmu zai

bani kudi in yadawo tafiya. Nayi ta masa godiya yace a

a shidai abinda zanyi mishi kada in saurari kowa kuma

na saki jikina dashi, nace kada yaji komai cikin sati 1

na gama yarda munir na sona, nima kara sonsa nake

duk zuwa yakan zo min da wani abu, turare ko dan

zobe ko dan wani abun kwalama. Bana manta ranar

lahadin da yazo min sallama zai koma makaranta ya

kuma bani kudi naira dubu 20 har kuka nayi mashi dan

bana so rabuwa dashi. Ranar shida abokin sa sukazo

wai shi faisal, kawai sai naji munnir ya rumgume ni,

wani abu naji tun daga tafin kafata har tsakiyar

kaina,shiko sai cewa yake inyi shuru in daina kuka

hannun shi kuma na zaga sassan jiki na, fadan inna ya

fado min cikin rai inda take cewa. In kula da kaina

wasan banza da namiji zai iya sawa in sami ciki, nayi

sauri na janye jiki na daga gareshi, yasa hannu yana

share min hawaye muka yi ban kwana na shiga gida.

Suna tafiya faisal yace munir dagaske kana son

yarinyar an? Munir yace da dai nazo na dan kwashi rabo

nane, sai kuma na gane yariyar ba yar hannu bace.

Sannan kuma nasamu kaina da sonta na gaske faisal

yace ka dai san dadinka ba zai barka ka auri yar geto

ba ko? Yace kai nif zan zaba da kaina ba zan yarda ace

min naje ga yar wani ba. Nikam ina shiga gida muka

soma murna da inna, nan muka shiga tsara yanda

zamuyi wa baba bayanin munir. Washegari inajin inna

tana cewa baba wai kananta da yayansu sunce ta kaini

zasu nemmar min makarantar kwana. Baba yace a a

shifa bai yarda ba, tace yayi hakuri kwana nawane zan

gama? Baba yace nifa ba kin karatun nake ba, nafiso

tayishi a can dakinta inaso kisani har in yarinya ta

soma tsayawa da saurayi mafi kyawu shine ayi mata

aure. Inna tace za ayimata malam, wannan yaro da ka

ganta dashi shene yake son auranta na lura itama tana

sonshi yace to ba sai ya turo magabatan shi ba muyi

zancen manya! Inna tace yo shima ai karatun yake sai

ya gama itama ta gama kafin nan. Shuru yayi bai sake

tankawa ba shurun ba yana nufin ya yarda bane,

shurunsa yana nufin mukarata can shi ba ruwansa.

Kwana 2 tsakani muka shirya ni da inna muka nufi

manunfashi kananta kawu sha‘iabu da kawu bashir

harda wanta kawu kabiru sun sunji dadi sun kuma tsaya

har saida nasamu shiga ss1. Haka baba ya hakura ya

zuba muna ido, na cigaba da karatu cikin nasara da

kwazo, yan gidanmu kam da makota sai gulma da

tsegumi, ba mu damu ba. Fatan inna shine inzama abin

kwatance nan gaba.

A duk lokacin da nazo hutu munnir nazuwa, haka duk

lokacin ziyarar dalibai in yana da sarari yakan zo.

Hidimar karatuna shi yake yinta haka nan duk wani

kaya na yan mata shi ne yake siyan min, wanan shine

yasa na kara sake wa dashi. Matsalata dashi son taba

jiki na, kawai lokacin da wani hawaye yayi min wai in

bishi muje dakin wani abokin shi, niko nace a a muji

tsoron Allah ba don son da nake yiwa munnir ba a tuni

na hakura dashi. Cikin haka na gama karatuna na

secondary. Na dubi likitar idanuna suna zubar da

hawaye nace, anty ko lokacin da na gama karatu na

baba ko gai suwa nayi baya amsawa, kannena yaran

kishiyar mama na guda 2 ya musu aure. Sannan

karatuna kafin na tahoshi sai da ta kai yace in har wani

abu ya biyo baya abakin auran innata, sannan in nemi

uba..... Kuka ya kwace min mai karfi, ina fadin na shiga

ukuna zan kashe auran iyaye da kaina. Munir ya cuceni

fyade yayi min anty ki taimaka ki cere cikin nan. Yan

gidanmu da yan unguwarmu duk dariya zasuyi mana.

Kalo kawai likitar keyi cikin tausayi har nayi kukana mai

isata na gama ba wanda ya bani hakuri. Daga ita har

asabe tace to, ke hafsat ki koma makaranta gobe kizo,

keko asabe ki kwana nan nace anty don Allah nima zan

kwana nan din, ko naje makarantar ba zan iya komai

ba, tace shikenan. Ta mike sannan ta nuna mana wani

daki, ku shiga nan kuyi sallah da komai a ciki. Ba tare

da ta jira amsa ba ta nufi dakin ta, kaiwa da kawowa

kurum take yi. Ta ina zata bullowa wayanan yara? Sam

bazata cire cikin ba, bazata kuma bari suje su cire su

zubar ba. Ta lura Asabe tafi saukin kai don haka da ita

zata fara. Yanda naga rana haka na ga dare, alwaula

kawai nayi na yi nafila. Daga bisani na koma istigifari,

washegari bayan ta lalabemu mun karya, sai ta bamu

wasu magun guna tace kada in damu in koma

makaranta insha, suna da karfi na sati 3 ne, ta tabata

cikin zai fita nayita godiya na komo. Sai da daktar

hindu ta sami shugabar kungiyar kare hakkin bil adama.

Tayi mata bayanin komai game da halin da asabe ke

ciki, Shugabar Hjy Adama ta ce, to za su samu Hjyr

Yasir su fara neman sulhu, in ta ki kuma to za a maka

Yasir a kotu. Doctor Hindu taji dadin haka, don haka ta

tambayi Asabe yaushe aka fi samun Hjy Mairo a gida?

Asabe ta ce Lahadi da rana, sauran ranakun sai dare

ake samunta. Sun same ta cikin Kasaitaccen falonta

tana shan kayan Marmari, suka sanar da ita dalilin

zuwansu. Ta ce, sam ita dai ba danta ba, ai ta ja mata

kunne, nan suka nuna mata cewa zata amsa kira a kotu

gobe Litinin. Yasir na dawowa ta hau shi da fada, ya ce

tayi hakuri sharrin shaidan ne, ta daka mishi tsawa ta

ce, yi min shiru,wawa kawai. Ta tausasa murya a bin

da nake so da kai, za su shigar da mu kara, saura in

mun je ka saki baki ka nuna kai ne, ina so ka bata rai

ka hade fuska ka nuna sam ba ka sam ba ka san

zancen ba. Ni kuma zan tsaya maka, Babanka zai tsaya

maka, domin duk Alkalin garin nan ba wanda zai ketare

bukata mahaifinka. Yasir cikin murna ya ce, "To Hjyta.

A daran ranar ta kira mahaifin Yasir ta shaida mishi

abn da ya faru, wai me aikinta tayo ciki tazo ta ce

Yasir ne, yanzun haka kungiyar kare hakkin dan adam

ta shigo cikin lamarin sun ce za su shigar da kara,Ni

kuma na ce su shigar, ya ce amma ba ki da hankali,

kina fa da masaniyar ina da burin tsayawa takara a

siyasa mai zuwa, ko kin manta? Kin san cewa abokan

gaba za su iya fakewa da wannan su ci zarafina har

suyi nasarar kada ni? Ta ce to yanzun yaya za'ayi? Ya

ce bani Yasir din a waya, ko ba ya kusa? ta ce ba ya

kusa, ka kira layinsa. Yasir ya daga kiran wayar

Mahaifinsa, ko gaisawa ba su yi ba ya jeho masa

tambaya, gaya min gaskiya kai ne kayi cikin? Yayi shiru,

fada min na ce kai ne ka min shiru? Uban ya fada cikin

daga murya. Yasir ya ce "Dad ba zan kara ba,

Mahaifina ya ce, Ok kai ne kenan? Ya ce Tsautsayi ne.

Alhjn yayi shiru yana nazarin abn yi. Can yaja tsaki, in

ka kuma ranka zai 6aci fiye da zatonka. Abn da zan

maka sha mmki, kila ma kayi zaton ko ba ni ne na haife

ka ba. Ya ci gaba da fada. In ma ba iskanci ba duk

nawa ka ke 25 years amma ka iya jarabar mata? Yasir

ya dinga ba wa Mahaifin shi hakuri, Alhjn ya ce shi

kenan, ya kira Hjy Mairo ya ce, kada su shiga kotu, su

nemi sulhu duk yanda aka yi su fada mishi. Washegari

da kanta taje ofishin shugabar kungiyar don neman

sulhu. An kira Dakta Hindu sun zo tare da Asabe,

sharadin 2 suka gindaya wa Hjy Mairo, aka c ta za6i

daya.Na farko ko dai dan nata ya auri yarinyar bayan ta

haihu, na 2 kuma in ba zai aure ta ba, to zai dauki

nauyin cikin tun daga yanzu hr zuwa lkcn da za a haife

shi a yaye shi. Daga bisani su dauke shi. Hjy Mairo ta

nemi saukin Asabe ta rike danta za su ci gaba da mishi

komai,amma shugaba ta ce a'a ba za su yarda ba,

domin Asabe in ta samu miji aure zata yi. Ba zai yiwu

ta tafi da dan wani gidn wani ba. Nan ta take ta kira

mijinta ta mishi bayanin komai, ya ce su dauki za6i na

biyun in yaso zasu yi shawara in ya dawo. Ta ce to.

Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa

hannu Daga nan ta tafi........


Zaharaddeen SHOMAR

WHAT'S APP 08168575100


SANADIN BOKO 1-5

Posted by ANaM Dorayi on 11:57 AM, 12-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu

Daga nan ta tafi. Likita ta dubi shugaba ta ce, " Amma

ko da Asaben zata ba su dan su sai an sake zama, don

kada suje su halaka shi, kin san mutane ba imani.

Shugaba ta ce, wannan ka'ida ne, yanzun ki dauki

yarinyar nan ki koma da ita gidanku,gobe zamu je mu

samu iyayenta. "Doctor ta ce, Insha Allahu." Washigare

suka nufi kauyen kurje, iyayen Asabe sunyi murna da

zuwanta, amma da suka ji dalilin zuwan nan suka soma

kuka tare da yiwa Asabe Allah ya isa. Asabe na ta kuka,

Doctor suka yi ta bai wa iyayen baki tana rokon su yafe

ma Asabe. Da kyar suka shawo kan su, sannan suka yi

musu bayanin komai game da yanda suka yi da Yasir.

Mamanta ta ce, to ni dai ba za ta zauna min a nan va,

kauyen nan suyi ta zagina suna yada ni 'yata tayo ciki.

Ta sake rushewa da kuka, Likita Hinda ta ce zan tafi da

ita in zauna da ita hr ta haihu, in ta yaye sun dauki

dansu sai ta samu miji tayi aurenta, ko a nan ne.

Maman Asabe tana ta gdy, shi ko Babn tunda yayi waje

hr suka tafi bai dawo ba, suka dauko hanya bayan sun ba

uwar Asabe sha tara ta arziki.

***** ***** *****

Sati 3 daidai babu alamun cewa cikin jikina zai zube,duk

da cewa kusan kullum sai na je gun Likitar, ita kuma sai

tayi ta kwantar min da hnkl, wai in jira sati 3n su

cika,don ba za ta iya bani wani magani ba tunda aikin

wannan bai kare ba. Sam lkcn bn san yaya Asabe take

ciki ba, don nima ina cikin nawa tashin hankalin, gara ma

Asabe. Bana iya cin abnci,yunwar ma ba jin ta nake

ba,karatu kuma ina mantawa cewar shi na zo yi, don ko

na shiga aji ba na fahimtar komai, ga laulayi mai tsanani.

Munir kuma bai kuma zuwa ba,wayar ma sau 2 ya kira ni,

cikin sati 3 da likita ta bani yau kam ko sisin mashin bani

da shi, a kafa na sabi hanyar zuwa gidan Doctor. Asabe

tare da me yiwa Likita aiki wata gyatuma ana kiranta

Yalwa, su na samu. Asabe ta ce min Likita tana cikin

asibiti zama nayi don jiranta. Sai uku da rabi muna sallar

La'asar ta shigo, da fara'ar ta tare ni tana cewa? na dai

san bukata ta biya tunda ban gan ki ofishina ba. Kamar

ko yaushe,sai hawaye suka soma zuraro min, na ce wlh

Likita ya ki fita, ni dai a kwakule min shi. Ganin tashin

hankalin da na shiga, sai ta lallashe ni da cewa, nayi

hakuri bari ta dan huta. Na koma na zauna ina

kuka,wanda ya zama abn yina koda yaushe, tun da

Asabe ta bani lbrn yanda aka kwashe da tata rigima

hankalina ya kara tashi. Addu'ata Allah yasa nima kada

Likitar ta ce haka za a yi, domin zancen cikin ne sam

bana kaunar Innarmu taji bare Babana. Sai shida saura

ta fito, na dora sabon kuka Nan ta hau ni da fada,wai in

tashi ni tafi kukana ya min magani. Na share hawayena,

tare da bata hakuri,ta ce "Hafsatu! Ina son ki bani aron

hankalinki, ki saurare ni, na ce to. Ta ci gaba da magana.

Cikin nan naki ba zaya fita ba, domin na baki duk wani

magani mai karfi,amma a banza. In ko ki ka ce a

kwakule shi akwai yiwuwar ki rasa ranki. Da sauri na ce

gwara na mutu zan fi son akai gawata ga iyayena fiye a

kai ni gaban su da ciki. Ta ce, To naji amma kin shirya

abn da za ki fada wa Mahalccinki? Kin mutu gurin kisan

kai ko in ce ma kin kashe kanki? Kin fi son kunyar lahira

fiye da ta duniya? kada ki manta, kin ce fyade ya miki

ko? Na daga kai cikin kuka, ta ce to ki dauki wannan abn

a matsayin kaddara. Kada ki manta, Ubangiji ya kan

jarabci bayinsa don ya gwada Imaninsu, ke me zai hana

ki rungumi kaddara? Allah ba ya dora ma wata rai abn da

ba zata iya ba, Zufa ta rufe ni, na ce Likita ba za ki gane

ba ne.Innata da Babana auran zai mutu SANADIN

BOKONA. Alhakin Babana ne kash! Hakika da na san

haka zata faru gare ni da na yarda Babana ya aurar dani,

in yaso sai in ci gaba da karatun acan gidan mijina.

Likita ta ce, Yanzun dai shawar da zan baki ita ce, kije ki

samu shi saurayin ki tunda yana sonki, ku sulhunta, in

kin haihu a daura muku aure. In kuma kina son sako

hukuma kamar na Asabe to in sako, za su tsaya miki a

kwatar miki 'yanci. In ta kama hr kotu kuma ko su waye

iyayenshi. Na ce A'a zan fi son in same shi muyi magana

don bana son asirina ya tonu a unguwarmu. Likita ta ce,

yauwa, in kun sasanta ni kuma zan fahimtar da iyayenki,

na rike kai, Boko! Boko!! Na jajirce sai nayi boko,yanzun

kuma gashi tun ban je ko ina ba bokon na tsane ta.

Likita ta ce, "Hafsaty duk wanda ya dauki boko sama da

aure a karshe sai yayi nadama, saboda halin da ki ka

shiga ina son ki kwana a gidannan anjima zan baku lbrna,

don ki san kinyi kuskure kema." Tara na dare da 'yan

mintina Likitar ta shigo sanye da kayan bacci masu kauri

riga da wando, tire ne a hannunta dan karami mai dauke

da kayan marmari, lemo da ayaba da abarba. Ina zaune

zugum kan sallaya Asabe na kwance a tsakar daki ta

dubi Asaben "Tashi! "Tashi!! Tun yanzy kin soma bin

sanyin kasa? kada na kuma ganinki.Asabe ta tashi,

Likitar ta ce In bacci ne ki hau gado mana. Ta zauna

bakin gado ta turo mana plate din kayan marmarin bayan

ta dauki abarba guda daya dama ina jin bakina babu dadi

sai shiga bayi nake ina zubar da miyau Na dauki lemu

guda daya ina dan lasa, Asabe ma ta dauka. Likitar ta

dube ni Tun ranar da naji lbrnki naji ina son in fada miki

nawa. lbrn. Amma kafin na fada miki ina son ki sanar da

ni daga ranar da ki ka fara ganina zuwa yau me ya birge

ki a tare da ni? Na gyara zama, Na farko iliminki,sai kyan

halinki,ga shi kina da kyau,ke ba kya tare da matsala

kina da kudi. Tayi guntun murmushi,sannanta dubi Asabe

ta ce, Asabe ban yi kama da mai matsala ba ko? Asabe

tayi murmushi. Anty ai ke ba ki hada hanya da damuwa

ba, bare matsala. ke kam kin ji dadinki. Likita tayi shiru

na dan lkc sannan ta ce. "Sunana Hindu, mahaifiyata

Bafullatana ce, mahaifina yana da kudi sosai,don lkcn da

aka haife ni ma yana matsayin Sakataren Gwamnati.

Mun taso cikin daula da gata, haka nan muna da kyau

'yan gidanmu tamkar mu ne muka hallice kanmu.

Yayyena 2 maza,sai kuma kannena guda 5. Mu 8 ne

gurin mahaifinmu, amma a gurin Mamanmu mu 5 ne,

Kishiyar ta ke da 3. Tun da na taso nake da tsananin son

BOKO burina kullum in zama Likita,wannan yasa

mahaifina ke matukar sona,don shima dan bokon rikau

ne. Shi irin matanan nan ne wadanda za su iya hana

cikinsu su ba ma boko,takarda komai tsadarta in dai ta

boko ce zai siya. Wannan tasa nake zaton dama an

halicce ni don nayi Boko. Lokacin da na gama secondary

ina da shekara 18, kyawuna ya kara fitowa Nan fa

samari suka min ca 'ya'yan manyan mutane,masu kudi

da sarakuna.Ni kam lkcn wani faifai na bude na

walakanta samari, don in fito in zage saurayi ko dan

wanenr baya damuwata.Bana manta wani saurayi

Nasir,Babanshi shi ne Gwamnan jiharmu wancan lkcn

tamkar zai yi hauka don sona, kullum sai ya zo gidanmu

ya min kuka,amma na ce ni fa sai na zama Doctor.

Babana ya daure min gindi, ina ta tsulawa samari tsiya.

Yayuna maza sukan suna son aure,mma Babanmu ya ce

suma ba yanzu ba. Amma shi a wannan lkcn ya sake

dallo wata amaryar wadda bata wuce sa'a ta ba.Sam ban

damu ba, Su Hjy kam ransu ya 6aci,haka yayuna. Babban

sai ya shiga dibn mata yana kawo su wai don Babanmu

ya gani ko zaya mishi aure,amma sai Baba ya kira shi

yana zagin shi. Abn da in na tuna yake bani mmk lkcn

Baba hr d cewa in zya nemi matan shi yaje can ya

nema,amma ya daina kawo masa gida. Na ce Alhj fada

zaka masa ya daina,ya ce kyale shi Hindu, yaje yayi ta

yi,wata rana kan shi zaya bari. Ni dai har na tafi Jami'ar

Ahamadu Bello,ba suyi auran ba.Karatu gurina ba

sauki,sam bana wasa da BOKO. Shekarata 3 a Jami'a

sannan aka yi wa yayuna aure, shima da kyar suna ta

hada Babanmu da mutanen da yake jin kunya. Kwanci

tashi na kammala karatuna,tsawonshekara 7. Lokacin ina

da shekara 25. Saboda kwazona, na samu damar zuwa

wani kwas kasar Germany na tsawon shekara 2. Hjyta hr

d kuka,don bata son tafiyar burinta in yi aure,amma na

kekasa kasa na ce ko na gama karatu sai na fara aiki.

Haka kuwa, ina gamawa ban jimaba na soma aiki a

babban asibitinmu a matsayin babbar Likita. A lokacin

Shekarata 30 babu kadan,sai a wannan lkcn ne hankalina

ya dawo jikina. Nayi boko na zama Likita,yau gani inna

aiki. Nan fa maza suka sake min ca! amma duk wanda

na ta6a babu na aure,sai dai in zan yarda a lalace,daga

wanda zai ce in zo in raka shi Abuja,sai me cewa in zo in

raka shi Dubai. Da na nuna ba haka nake ba, sai na dinga

nemansu daya-bayan-dayaina rasawa,daga karshe duk

suka gudu. Lokacin ne kuma idona ya raina fata,wasu

suka dan soma zuwa amma fa ba yaro,don ko wani ma

zaya girmi Babana, na ce tab, ni kan ai saurayi sabon

jini. Kafin shekara na nemi suma tsofaffin na rasa.Bana

manta wani dattijo da ya soni na ki, sai gashi ya kawo

min wata 'yar yarinya ba za ta fi sha takwas ba, ba ta da

lfy tana laulayin ciki. Ya ce min, Matarsa ce. Sai na

soma tunanin cewa in nemo samarina na da mana,duk

wanda na bncika sai in samu lbrn cewa yayi aure.

Hankalina ya tashi matuka, yanzun gurin mu2m daya

nake sa rai,wato Nasir wanda ya soni tamkar ransa, duk

in da zan samu lbrn Nasir naje amma bn samu lbrnshi

ba. Wata safiyar Asabar, misalin karfe goma na safe,na

nufi supre markte don siyan kayan shafa, domin nawa

sun kare. Ina sa kafa daya kan na dago dayar,wata 'yar

kyakkyawan yarinya 'yar kimanin shekara sha biyo ko sha

daya ta rugo da gudu daga ciki sai ko ta rungume kafata

tana cewa . Anty 6oye ni Fadil za ya kwace min

(Teddy)na. Na daga ta sama,daidai lokacn da yaron ya

iso, daga gani kaninta ne yana da kiba. Ya ce, Anty nima

ki ce ta bani boll dina. Na dube ta, ina boll dinsa? Tana

dry ta ce, Anty boll dinsa fa tana mota. Na ce to dauko

masa, zan sauke ta ta sake kankame ni. Anty Fadil yana

da karfi zaya ture ni ya kwace (Teddy) na. Dry na ke t

musu, ga shi sai naga sun shiga raina, na ce to muje in

sai maka wata boll a ciki. Muna isa daidai gurin kwallaye

na ce za6i wadda ka ke so, yarinyar ta ce Anty nima zan

kara (Teddy) daya. Muryar Babnsu naji ya ce, sannu da

kokari sun dame ki ko? Ina daga ido na sauke kan Nasir,

da sauri na ce Nasir! Da alama sai lkcn ya gane ni, ya ce

a'a Hjy Hindu BOKO uwaka ubanka ya karatu? Sai naji

tankar ya min habaici ne, na ce Alhmdulillah, mun gama

hr na soma aiki,ya ce lallai kam buri ya cika, na ce

yaranka ne wadandan? Ya ce, eh Fadil da Fadila,sai

kanwarsu Yasmeen. Na karkata kai tare da cewa, Allah

ya raya su. Ya ce Amin. Na ce, yanzun kana ina ne?

yace muna Abuja ne mun zo hutu ne, ke fa? kafin nayi

magana wata mata kyakkyawa ina ga zan girmeta ta iso

tana sanye da after dress me shegen kyau. Ta ce Beby

ka gan su? Ya ce ga su nan sweet heart, ta dube ni ta

yatsina baki tare da cewa, wannab fa? Ga mmkina sai na

ji ya ce,Ina tsohuwar budurwata Hindu,? To ita ce

wannan. Nan take ta watso min wani mummunan kallo,

sannan ta figi yaranta gami da cewa, mijin mace daya zo

muje. Yayi murmushi tare da daga min yatsu 2 gami da

cewa bye. Ban iya tsayawa siyan komai ba na fita. A

gida ma ina shiga kai tsaye dakina na nufa,na fada kan

gadona ina kuka. Tambayar kaina nake, wai dama gaske

ne da Bature ya ce dama sau daya take zuwa ma mu2m

a rayuwa? In ko haka ne na cuci kaina na bar damata ta

wuce. A ranar ne na soma tsanar BOKO akida, tun daga

nan na koma ga Allah, ko yaushe nayi sallah addu'ata ita

ce Allah ya ban miji. Kawayena, sa'annina duk sunyi aure

da yaransu,kuma bn tsere musu a karatu ba,tunda aina

aiki suma suna aiki. Amma sun tsere min don suna da

aure ga kuma 'ya'yansu. Doctor Hindu ta dube ni,

Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma

sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga

don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya

aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin

kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci

gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da

nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka

wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi

asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu

duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba.

Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti

da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su

hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke

tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi

kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau

wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba

da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai

saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika

kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta

jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma

halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI,

nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban

wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge

maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da

nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada

kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki

daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan

kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure

ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace.

Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi

ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani

da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don

Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma

baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk

kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje.

Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu

ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk

kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle

kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko

bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na

fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na

shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi

amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari

biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na

koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi

kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a

cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan

wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir

inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko

unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min

sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na

zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada

cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi

hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na

rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango

kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba

dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai

naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta

waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi.

Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai

me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi

magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala

mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom....

ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai

yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako

zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu

kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da

sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya

nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina

nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki

koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a

fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A

gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani

kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma

fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa

raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me

kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce,

"To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah

ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can

gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai

muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato

na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi.

Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban

taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure

na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza

kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire

wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban

danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake

fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa

ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba

amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni

magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo

cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani

ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne

ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci

na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani

na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika

zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da

kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min,

shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne

tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina

takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani."

Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama

yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar

mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi

Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke

da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi

kukan kura na shako wuyanshi ba ina kuka ina cewa,

"Allah ya isa." Shi kanshi yayi mamakin yadda ya so

kwacewa daga jikinshi ya kasa.Muryar Mom dinsu muka

ji tana cewa, "Lafiya? Ke, ke sake shi mana me ya faru?"

Na kasa magana sai wani irin kuka nake yi ina fadin, "Ya

cuce ni." Ta dubi Munnir, "Me kayi mata?" Ya ce, "Ban fa

ko sanya ba daga aiko ta gurina ta shakeni wai na mata

ciki." Wani kallo Mahaifiyarsa ta watso min sannan ta

nuna ni da yatsa gami da cewa, "Ke! Shiga taitayinki, tafi

can ki nemi wanda ya miki ciki." Cikin tsananin kuka na

ce, "Wallahi shine ya min fyade. Kuma da shi muka je

asibiti Likita ya ce ina da ciki." "Ke!" Ta kara daka min

tsawa, "Fita a nan." Na ce, "Nifa ba inda zani sai dai ya

san yanda zayayi da ni......." Saukar mari na ji, sannan ta

ce, "Fita ko in kirama Iyayenki 'yan sanda." Ta fita da

sauri tana kiran Baba megadi, ya iso ta nuna mishi ni,

"Baba fita da wannan bana son in kuma jin ko labarin an

ganta a layin nan, in haka ta faru har da kai zan

hukunta." Ya dubeni ya cem "Mu je." Na tsaya ya ce,

"Shige mu je mana ina magana kina kallona." Na dago

jajayen idanuna na kalli Munnir, wani murmushi ya saki

na mugunta sannan na ce, "Akwai Allah." Na fita

megadin yana biye da ni sai da muka fito ya ce, "Yarinya

kin yi kuskure, koda ban san abinda ya faru ba, amma na

san yana da nasaba da abinda yayi ta faruwa da wasu

'yan mata a gidan nan." Na dube shi, "Baba me ya faru

da wasu 'yan matan?" Ya ce, "Samarin gidan nan da

abokansu suna kawo 'yan mata ta hanyar yaudararsu da

kudi, su yi lalata da su." Na dube shi bayan mun fito

wajen gidan, "Baba ni nawa salon yaudarar ya bambanta

da na sauraNan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa

yasa hannu Daga nan ta tafi. Likita ta dubi shugaba ta

ce, " Amma ko da Asaben zata ba su dan su sai an sake

zama, don kada suje su halaka shi, kin san mutane ba

imani. Shugaba ta ce, wannan ka'ida ne, yanzun ki dauki

yarinyar nan ki koma da ita gidanku,gobe zamu je mu

samu iyayenta. "Doctor ta ce, Insha Allahu." Washigare

suka nufi kauyen kurje, iyayen Asabe sunyi murna da

zuwanta, amma da suka ji dalilin zuwan nan suka soma

kuka tare da yiwa Asabe Allah ya isa. Asabe na ta kuka,

Doctor suka yi ta bai wa iyayen baki tana rokon su yafe

ma Asabe. Da kyar suka shawo kan su, sannan suka yi

musu bayanin komai game da yanda suka yi da Yasir.

Mamanta ta ce, to ni dai ba za ta zauna min a nan va,

kauyen nan suyi ta zagina suna yada ni 'yata tayo ciki.

Ta sake rushewa da kuka, Likita Hinda ta ce zan tafi da

ita in zauna da ita hr ta haihu, in ta yaye sun dauki

dansu sai ta samu miji tayi aurenta, ko a nan ne.

Maman Asabe tana ta gdy, shi ko Babn tunda yayi waje

hr suka tafi bai dawo ba, suka dauko hanya bayan sun ba

uwar Asabe sha tara ta arziki.

***** ***** *****

Sati 3 daidai babu alamun cewa cikin jikina zai zube,duk

da cewa kusan kullum sai na je gun Likitar, ita kuma sai

tayi ta kwantar min da hnkl, wai in jira sati 3n su

cika,don ba za ta iya bani wani magani ba tunda aikin

wannan bai kare ba. Sam lkcn bn san yaya Asabe take

ciki ba, don nima ina cikin nawa tashin hankalin, gara ma

Asabe. Bana iya cin abnci,yunwar ma ba jin ta nake

ba,karatu kuma ina mantawa cewar shi na zo yi, don ko

na shiga aji ba na fahimtar komai, ga laulayi mai tsanani.

Munir kuma bai kuma zuwa ba,wayar ma sau 2 ya kira ni,

cikin sati 3 da likita ta bani yau kam ko sisin mashin bani

da shi, a kafa na sabi hanyar zuwa gidan Doctor. Asabe

tare da me yiwa Likita aiki wata gyatuma ana kiranta

Yalwa, su na samu. Asabe ta ce min Likita tana cikin

asibiti zama nayi don jiranta. Sai uku da rabi muna sallar

La'asar ta shigo, da fara'ar ta tare ni tana cewa? na dai

san bukata ta biya tunda ban gan ki ofishina ba. Kamar

ko yaushe,sai hawaye suka soma zuraro min, na ce wlh

Likita ya ki fita, ni dai a kwakule min shi. Ganin tashin

hankalin da na shiga, sai ta lallashe ni da cewa, nayi

hakuri bari ta dan huta. Na koma na zauna ina

kuka,wanda ya zama abn yina koda yaushe, tun da

Asabe ta bani lbrn yanda aka kwashe da tata rigima

hankalina ya kara tashi. Addu'ata Allah yasa nima kada

Likitar ta ce haka za a yi, domin zancen cikin ne sam

bana kaunar Innarmu taji bare Babana. Sai shida saura

ta fito, na dora sabon kuka Nan ta hau ni da fada,wai in

tashi ni tafi kukana ya min magani. Na share hawayena,

tare da bata hakuri,ta ce "Hafsatu! Ina son ki bani aron

hankalinki, ki saurare ni, na ce to. Ta ci gaba da magana.

Cikin nan naki ba zaya fita ba, domin na baki duk wani

magani mai karfi,amma a banza. In ko ki ka ce a

kwakule shi akwai yiwuwar ki rasa ranki. Da sauri na ce

gwara na mutu zan fi son akai gawata ga iyayena fiye a

kai ni gaban su da ciki. Ta ce, To naji amma kin shirya

abn da za ki fada wa Mahalccinki? Kin mutu gurin kisan

kai ko in ce ma kin kashe kanki? Kin fi son kunyar lahira

fiye da ta duniya? kada ki manta, kin ce fyade ya miki

ko? Na daga kai cikin kuka, ta ce to ki dauki wannan abn

a matsayin kaddara. Kada ki manta, Ubangiji ya kan

jarabci bayinsa don ya gwada Imaninsu, ke me zai hana

ki rungumi kaddara? Allah ba ya dora ma wata rai abn da

ba zata iya ba, Zufa ta rufe ni, na ce Likita ba za ki gane

ba ne.Innata da Babana auran zai mutu SANADIN

BOKONA. Alhakin Babana ne kash! Hakika da na san

haka zata faru gare ni da na yarda Babana ya aurar dani,

in yaso sai in ci gaba da karatun acan gidan mijina.

Likita ta ce, Yanzun dai shawar da zan baki ita ce, kije ki

samu shi saurayin ki tunda yana sonki, ku sulhunta, in

kin haihu a daura muku aure. In kuma kina son sako

hukuma kamar na Asabe to in sako, za su tsaya miki a

kwatar miki 'yanci. In ta kama hr kotu kuma ko su waye

iyayenshi. Na ce A'a zan fi son in same shi muyi magana

don bana son asirina ya tonu a unguwarmu. Likita ta ce,

yauwa, in kun sasanta ni kuma zan fahimtar da iyayenki,

na rike kai, Boko! Boko!! Na jajirce sai nayi boko,yanzun

kuma gashi tun ban je ko ina ba bokon na tsane ta.

Likita ta ce, "Hafsaty duk wanda ya dauki boko sama da

aure a karshe sai yayi nadama, saboda halin da ki ka

shiga ina son ki kwana a gidannan anjima zan baku lbrna,

don ki san kinyi kuskure kema." Tara na dare da 'yan

mintina Likitar ta shigo sanye da kayan bacci masu kauri

riga da wando, tire ne a hannunta dan karami mai dauke

da kayan marmari, lemo da ayaba da abarba. Ina zaune

zugum kan sallaya Asabe na kwance a tsakar daki ta

dubi Asaben "Tashi! "Tashi!! Tun yanzy kin soma bin

sanyin kasa? kada na kuma ganinki.Asabe ta tashi,

Likitar ta ce In bacci ne ki hau gado mana. Ta zauna

bakin gado ta turo mana plate din kayan marmarin bayan

ta dauki abarba guda daya dama ina jin bakina babu dadi

sai shiga bayi nake ina zubar da miyau Na dauki lemu

guda daya ina dan lasa, Asabe ma ta dauka. Likitar ta

dube ni Tun ranar da naji lbrnki naji ina son in fada miki

nawa. lbrn. Amma kafin na fada miki ina son ki sanar da

ni daga ranar da ki ka fara ganina zuwa yau me ya birge

ki a tare da ni? Na gyara zama, Na farko iliminki,sai kyan

halinki,ga shi kina da kyau,ke ba kya tare da matsala

kina da kudi. Tayi guntun murmushi,sannanta dubi Asabe

ta ce, Asabe ban yi kama da mai matsala ba ko? Asabe

tayi murmushi. Anty ai ke ba ki hada hanya da damuwa

ba, bare matsala. ke kam kin ji dadinki. Likita tayi shiru

na dan lkc sannan ta ce. "Sunana Hindu, mahaifiyata

Bafullatana ce, mahaifina yana da kudi sosai,don lkcn da

aka haife ni ma yana matsayin Sakataren Gwamnati.

Mun taso cikin daula da gata, haka nan muna da kyau

'yan gidanmu tamkar mu ne muka hallice kanmu.

Yayyena 2 maza,sai kuma kannena guda 5. Mu 8 ne

gurin mahaifinmu, amma a gurin Mamanmu mu 5 ne,

Kishiyar ta ke da 3. Tun da na taso nake da tsananin son

BOKO burina kullum in zama Likita,wannan yasa

mahaifina ke matukar sona,don shima dan bokon rikau

ne. Shi irin matanan nan ne wadanda za su iya hana

cikinsu su ba ma boko,takarda komai tsadarta in dai ta

boko ce zai siya. Wannan tasa nake zaton dama an

halicce ni don nayi Boko. Lokacin da na gama secondary

ina da shekara 18, kyawuna ya kara fitowa Nan fa

samari suka min ca 'ya'yan manyan mutane,masu kudi

da sarakuna.Ni kam lkcn wani faifai na bude na

walakanta samari, don in fito in zage saurayi ko dan

wanenr baya damuwata.Bana manta wani saurayi

Nasir,Babanshi shi ne Gwamnan jiharmu wancan lkcn

tamkar zai yi hauka don sona, kullum sai ya zo gidanmu

ya min kuka,amma na ce ni fa sai na zama Doctor.

Babana ya daure min gindi, ina ta tsulawa samari tsiya.

Yayuna maza sukan suna son aure,mma Babanmu ya ce

suma ba yanzu ba. Amma shi a wannan lkcn ya sake

dallo wata amaryar wadda bata wuce sa'a ta ba.Sam ban

damu ba, Su Hjy kam ransu ya 6aci,haka yayuna. Babban

sai ya shiga dibn mata yana kawo su wai don Babanmu

ya gani ko zaya mishi aure,amma sai Baba ya kira shi

yana zagin shi. Abn da in na tuna yake bani mmk lkcn

Baba hr d cewa in zya nemi matan shi yaje can ya

nema,amma ya daina kawo masa gida. Na ce Alhj fada

zaka masa ya daina,ya ce kyale shi Hindu, yaje yayi ta

yi,wata rana kan shi zaya bari. Ni dai har na tafi Jami'ar

Ahamadu Bello,ba suyi auran ba.Karatu gurina ba

sauki,sam bana wasa da BOKO. Shekarata 3 a Jami'a

sannan aka yi wa yayuna aure, shima da kyar suna ta

hada Babanmu da mutanen da yake jin kunya. Kwanci

tashi na kammala karatuna,tsawonshekara 7. Lokacin ina

da shekara 25. Saboda kwazona, na samu damar zuwa

wani kwas kasar Germany na tsawon shekara 2. Hjyta hr

d kuka,don bata son tafiyar burinta in yi aure,amma na

kekasa kasa na ce ko na gama karatu sai na fara aiki.

Haka kuwa, ina gamawa ban jimaba na soma aiki a

babban asibitinmu a matsayin babbar Likita. A lokacin

Shekarata 30 babu kadan,sai a wannan lkcn ne hankalina

ya dawo jikina. Nayi boko na zama Likita,yau gani inna

aiki. Nan fa maza suka sake min ca! amma duk wanda

na ta6a babu na aure,sai dai in zan yarda a lalace,daga

wanda zai ce in zo in raka shi Abuja,sai me cewa in zo in

raka shi Dubai. Da na nuna ba haka nake ba, sai na dinga

nemansu daya-bayan-dayaina rasawa,daga karshe duk

suka gudu. Lokacin ne kuma idona ya raina fata,wasu

suka dan soma zuwa amma fa ba yaro,don ko wani ma

zaya girmi Babana, na ce tab, ni kan ai saurayi sabon

jini. Kafin shekara na nemi suma tsofaffin na rasa.Bana

manta wani dattijo da ya soni na ki, sai gashi ya kawo

min wata 'yar yarinya ba za ta fi sha takwas ba, ba ta da

lfy tana laulayin ciki. Ya ce min, Matarsa ce. Sai na

soma tunanin cewa in nemo samarina na da mana,duk

wanda na bncika sai in samu lbrn cewa yayi aure.

Hankalina ya tashi matuka, yanzun gurin mu2m daya

nake sa rai,wato Nasir wanda ya soni tamkar ransa, duk

in da zan samu lbrn Nasir naje amma bn samu lbrnshi

ba. Wata safiyar Asabar, misalin karfe goma na safe,na

nufi supre markte don siyan kayan shafa, domin nawa

sun kare. Ina sa kafa daya kan na dago dayar,wata 'yar

kyakkyawan yarinya 'yar kimanin shekara sha biyo ko sha

daya ta rugo da gudu daga ciki sai ko ta rungume kafata

tana cewa . Anty 6oye ni Fadil za ya kwace min

(Teddy)na. Na daga ta sama,daidai lokacn da yaron ya

iso, daga gani kaninta ne yana da kiba. Ya ce, Anty nima

ki ce ta bani boll dina. Na dube ta, ina boll dinsa? Tana

dry ta ce, Anty boll dinsa fa tana mota. Na ce to dauko

masa, zan sauke ta ta sake kankame ni. Anty Fadil yana

da karfi zaya ture ni ya kwace (Teddy) na. Dry na ke t

musu, ga shi sai naga sun shiga raina, na ce to muje in

sai maka wata boll a ciki. Muna isa daidai gurin kwallaye

na ce za6i wadda ka ke so, yarinyar ta ce Anty nima zan

kara (Teddy) daya. Muryar Babnsu naji ya ce, sannu da

kokari sun dame ki ko? Ina daga ido na sauke kan Nasir,

da sauri na ce Nasir! Da alama sai lkcn ya gane ni, ya ce

a'a Hjy Hindu BOKO uwaka ubanka ya karatu? Sai naji

tankar ya min habaici ne, na ce Alhmdulillah, mun gama

hr na soma aiki,ya ce lallai kam buri ya cika, na ce

yaranka ne wadandan? Ya ce, eh Fadil da Fadila,sai

kanwarsu Yasmeen. Na karkata kai tare da cewa, Allah

ya raya su. Ya ce Amin. Na ce, yanzun kana ina ne?

yace muna Abuja ne mun zo hutu ne, ke fa? kafin nayi

magana wata mata kyakkyawa ina ga zan girmeta ta iso

tana sanye da after dress me shegen kyau. Ta ce Beby

ka gan su? Ya ce ga su nan sweet heart, ta dube ni ta

yatsina baki tare da cewa, wannab fa? Ga mmkina sai na

ji ya ce,Ina tsohuwar budurwata Hindu,? To ita ce

wannan. Nan take ta watso min wani mummunan kallo,

sannan ta figi yaranta gami da cewa, mijin mace daya zo

muje. Yayi murmushi tare da daga min yatsu 2 gami da

cewa bye. Ban iya tsayawa siyan komai ba na fita. A

gida ma ina shiga kai tsaye dakina na nufa,na fada kan

gadona ina kuka. Tambayar kaina nake, wai dama gaske

ne da Bature ya ce dama sau daya take zuwa ma mu2m

a rayuwa? In ko haka ne na cuci kaina na bar damata ta

wuce. A ranar ne na soma tsanar BOKO akida, tun daga

nan na koma ga Allah, ko yaushe nayi sallah addu'ata ita

ce Allah ya ban miji. Kawayena, sa'annina duk sunyi aure

da yaransu,kuma bn tsere musu a karatu ba,tunda aina

aiki suma suna aiki. Amma sun tsere min don suna da

aure ga kuma 'ya'yansu. Doctor Hindu ta dube ni,

Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma

sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga

don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya

aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin

kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci

gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da

nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka

wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi

asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu

duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba.

Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti

da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su

hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke

tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi

kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau

wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba

da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai

saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika

kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta

jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma

halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI,

nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban

wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge

maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da

nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada

kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki

daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan

kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure

ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace.

Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi

ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani

da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don

Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma

baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk

kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje.

Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu

ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk

kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle

kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko

bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na

fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na

shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi

amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari

biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na

koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi

kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a

cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan

wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir

inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko

unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min

sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na

zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada

cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi

hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na

rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango

kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba

dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai

naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta

waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi.

Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai

me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi

magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala

mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom....

ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai

yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako

zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu

kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da

sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya

nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina

nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki

koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a

fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A

gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani

kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma

fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa

raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me

kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce,

"To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah

ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can

gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai

muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato

na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi.

Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban

taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure

na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza

kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire

wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban

danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake

fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa

ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba

amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni

magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo

cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani

ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne

ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci

na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani

na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika

zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da

kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min,

shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne

tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina

takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani."

Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama

yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar

mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi

Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke

da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi

kukan kura na shako wuyanshi ba ina kuka ina cewa,

"Allah ya isa." Shi kanshi yayi mamakin yadda ya so

kwacewa daga jikinshi ya kasa.Muryar Mom dinsu muka

ji tana cewa, "Lafiya? Ke, ke sake shi mana me ya faru?"

Na kasa magana sai wani irin kuka nake yi ina fadin, "Ya

cuce ni." Ta dubi Munnir, "Me kayi mata?" Ya ce, "Ban fa

ko sanya ba daga aiko ta gurina ta shakeni wai na mata

ciki." Wani kallo Mahaifiyarsa ta watso min sannan ta

nuna ni da yatsa gami da cewa, "Ke! Shiga taitayinki, tafi

can ki nemi wanda ya miki ciki." Cikin tsananin kuka na

ce, "Wallahi shine ya min fyade. Kuma da shi muka je

asibiti Likita ya ce ina da ciki." "Ke!" Ta kara daka min

tsawa, "Fita a nan." Na ce, "Nifa ba inda zani sai dai ya

san yanda zayayi da ni......." Saukar mari na ji, sannan ta

ce, "Fita ko in kirama Iyayenki 'yan sanda." Ta fita da

sauri tana kiran Baba megadi, ya iso ta nuna mishi ni,

"Baba fita da wannan bana son in kuma jin ko labarin an

ganta a layin nan, in haka ta faru har da kai zan

hukunta." Ya dubeni ya cem "Mu je." Na tsaya ya ce,

"Shige mu je mana ina magana kina kallona." Na dago

jajayen idanuna na kalli Munnir, wani murmushi ya saki

na mugunta sannan na ce, "Akwai Allah." Na fita

megadin yana biye da ni sai da muka fito ya ce, "Yarinya

kin yi kuskure, koda ban san abinda ya faru ba, amma na

san yana da nasaba da abinda yayi ta faruwa da wasu

'yan mata a gidan nan." Na dube shi, "Baba me ya faru

da wasu 'yan matan?" Ya ce, "Samarin gidan nan da

abokansu suna kawo 'yan mata ta hanyar yaudararsu da

kudi, su yi lalata da su." Na dube shi bayan mun fito

wajen gidan, "Baba ni nawa salon yaudarar ya bambanta

da na saura


Zaharaddeen Shomar

whatsapp. 08168575100



Sanadin Boko 1-6

Posted by ANaM Dorayi on 12:26 PM, 12-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

." Kuka ya sake sarkeni, na ci gaba da cewa, "Shekara 3

da doriya yana min dawainiya da sunan zai aureni, kuma

Wallahi Baba fyade ya min." Megadi ya ce, "Kuskurenki

shine zuwan da kika yi gidan nan, ki kiyaye zuwa gidan

samari ko dakin samari. Yanzun kije ki yi hakuri, in ba

haka ba zaki jawa Iyayenki matsala. Kin san masu kudin

nan ba duka bane suke da tsoron Allah, 'ya'yansu su ne

'ya'ya na wasu tamkar dabba suka dauke su. Shi Munnir

sau nawa yana samuna yana rokona shi da abokansa wai

in kai musu kudin gaisuwa gidajen 'yan matansu a

matsayin nine Ubansu." Na ce, "Baba ka je?" Ya ce, "A'a

ni nasiha na musu dan nima inada yara da jikoki. Tunda

haka samarin yanzu suke yi, su kai kudin gaisuwa don su

bata yarinya. In ta'ki su ce aurenta zasu yi. Na san koda

ban kai musu ba sun je sun samu wani, kuma ya kai

musu, kila ma sun cimma burinsu, don haka ki je kiyi

hakuri ki kuma kiyaye gaba." Na ce, "Na gode." Ko da

wasa ba zan ce maigadin nan ina da ciki ba.

Tahowa na yi ina mamakin kalaman Munnir, wai ya

taimakeni ne don bukatarshi, dama haka halin maza ya

ke? Dama Munnir mayaudarin 'yan mata ne? Tafiya nake

amma sam ban dauki hanyar gida ba ko cikin mafarki ai

ba zanje gida ba. Zuciyata ta bushe na share hawaye na

na nufi Babban titi. Kwatsam! Sai ga Yayana Umar ya

sauke wani a mashin, cak na tsaya don mun riga mun

hada ido. Cikin mamaki ya ce, "Hafsa daga ina haka?"

Gabana ya fadi matuka, amma sai na kanne banda wata

damuwa na ce, "Na zo ne yau ko gidama ban karasa ba,

gidan su wata na zo." Ya ce, "Wacce watan?" Na 'kirkiro

'yar dariya, "Yar ajinmu ce ta yo mana gaba da kaya to

na zo kuma bata karaso ba." A take karyar tazo min, ya

ce, "Hau na kaiki gida." Muna cikin tafiya ina tunanin ban

so na hadu da Yaya Umar ba, sai ya jeho min tambaya,

"Hafsa sai na ganki duk a hargitse, fuska a kumbure

kamar kin sha kuka." Gabana ya yi mummunar faduwa

amma don kada ya ganoni na ce, "Kukan lafiya? Ka sam

zaman mota, kuma baccina na sha har na gaji." Ya ce,

"Irinku ne ake sace wa, nan da Kano kin hangame baki

kina bacci,." Na ce, "Cikin kwanakin nan ne bamu samu

bacci ba saboda karatu."

Ko Inna abinda ta soma tambaya ta shine lafiya? Cikin

dariyar da bata kai zuci ba na ce, "Lafiya Innarmu." Na

shige daki na kwanta kan gado.Jim kadan Ummi kanwata

ta shigo da kwanon alala ta ce, "Anty gashi." Na amsa

na aje. Ummi ta tsaya tana kallona, ina zaton dan wasan

da na saba yi mata ne taga ban mata ba. Inna ta shigo,

"Wai Hafsa lafiya na ganki kwatsam! Kuma kina zuwa kin

zube a gado?" Ban san yadda aka yi maganar ta zo min

ba, sai dai kawai naji ina bata amsa, "Innarmu gajiyar

mota ce, kuma dama bani da lafiya ne. Can ma muna ta

sintirin asibiti shine aka ce in zo gida in nemi na hausa."

Cikin fargaba da Tausayi ta ce, "Ashsha, me ke

damunki?" Sai kurum na ji bakina ya ce, "Shawara da

Basiri." Ta jinjina kai, "Sannu, Allah ya sauwake, jiki da

jini haka ne. Ta ce ci alalar." Ta daga murya, "Ummi!

Ummi!!" Yarinyar ta shigo da gudu. Inna ta ce, "Kira min

Baban gida in aike sh dattawa ya hadowa Hafsa

maganin basir da shawara." Ta kwance habar zaninta ta

ciro kudi naira dari 3 da ashirin ta ce, "Ungo ka hau

mota ka je layin dattawa gurin masu magungunan

gargajiya ka siyo mata maganin shawara da na basir."

Ya ce, "To." Ya amsa ya fita.

Bani da damar in ki sha domin Inna tsareni take, a

cewarta tun ina karama bana son magani. Duk lokacin da

zan sha ina sha da niyyar cewar Allah ya sa cikin nan ya

fita amma shiru, sai ma tsananin amai da ya karu gareni

da kuma kasala. Tausayin Inna yana sani kuka, in naga

irin fadi-tashin da take yi gurin neman min magani.Wata

rana ina kwance dakin Baabah amai ya sarkeni na tashi

da sauri kafin na bude kofa na soma sheka shi. Baabah

ita ce ta taimaka min na gyara jikina ta kuma kwashe

aman. Har na kwanta ta ce, "Hafsa!" Na ce, "Na'am." Na

tashi zaune, ta ce, "Zo nan." Na mike na bita can kuryar

daki ta ce, "Hafsa ki fada min tsakaninki da Allah me ke

damunku?" Gabana ya yi mummunar faduwa, zufa ta

keto min na ce, "Me,,,,,me kika gani?" Ta ce, "Hafsa na

ga wasu alamu da suke nuna kina da ciki, menene

gaskiyar hasashena?" "A'a bani da komai." Tayi-tayi da ni

in fada mata gaskiya amma na dage kan cewa bani da

komai, don haka ta kyaleni tare da cewa, "Shike nan.

Dama ke nake tunanin zaki bani hadin kai domin Innarku

ba zata fahimce ni ba na sani shi yasa na miki magana."

Na ce, "Ni fa kalau na nake." Don haka sai ta rabu da ni.

Kafin sati 2 duk 'yan gidanmu sun gane halin da ake ciki,

amma banda Innarmu sam bata lura ba bata zata ba, ba

kuma ta tsammanin haka zata faru ba, 'yan tsegumi har

cewa suke mata, "Yaya 'yar boko da jiki?" Haka ta ce,

"Da sauki." Tana washe baki ita a dole an gaishe ni.

Sannu a hankali zance ya soma fita makota sai gashi ana

shigowa dubani, niko ko yaushe ina cikin Hijabi. Baabah

Maimuna ita ce ta shigo dubani yau kawar Innarmu ce

kut da kut ta kalli Innarmu, "Kin san zancen da yake

yawo unguwar nan?" Ta ce, "A'a." "To 'yan gidanku sun

fita suna yada cewa Hafsa ciki ta yo." Inna ta mike cikin

tsananin tashin hankali, "Wane dan sharrin ne? Wallahi

zan iya maka mutum a kotu." Maimuna ta ce, "Saurara

kiji, kafin ki fita kiyi wata magana soma tuhumar ta

tukunna." Innarmu ta ce, "Haba Maimuna, sanin kanki ne

Hafsa bata da rawar kai irin na 'yan iska, sharrine kawai

za'a mata. Kin san bani da hakuril dole sai ba ni ba'asni

wanda ya mata wannan sharrin." Maimuna ta ce, "Don

Allah ki bar zancen nan." Amma Inna bata saurareta ba

ta fita tana fada, wai yaya za'a yi ta bar wannan zancen

ana kallon 'yarta a matsayin 'yar iska!

Kai tsaye sashen su Asabe ta nufa tana fadin, "To

munafukai magulmata masu zuwa lahira da kokon

dambu! Za kuce 'yata cikine da ita, to aniyarku ta biku.

Kuma Insha Allahu 'ya'yanku ne zasu yi ba tawa ba.

Kanta aka fara ciwo da za'a mata sharri?"Kuma in sha

Allahu yayanku ne zasuyi ba tawa ba kanta aka fara ciwo

za a mata shairi? Asabe tace aina kika ji? Mu nan dai ba

wanda ya san haka inna tace rufe min baki munafukai, to

nazone in muku gar gadi zan maka mutun a kotu, sai ta

fito mun da wanda ya fada mata. Ade tace maganar

gaskiya ki bin ciki yarki dan muma a makota mukaji. Inna

tace ahaf na san duk inda aka zaga aka zago kune zaku

fadi wanan maganar, kuma zaku amsa kiran alkali,gida

ya hautsine baba ya shugo yana tambayan ba asi, babah

tace a a yar rigimar yara ce ba sai kaji ba. Nufinta kada

yaji don tasan in yaji sai yabi duddugi amma jin zantukan

sun cika gidan har makota sun soma zagayowa, ya fito

dan jin ba‘asin tun bai karasaba ya soma jin muryarsu

Ade na cewa an dai fada maki kije ki tuhimi yarki, ba kizo

ki tasamu kina zagi ba. Ki dau mataki tun kafin lokaci ya

kure miki, in shairi a ka mata sai kiji dadin kaiwa kotun.

Asabe ta kara da cewa, inko kin tafi yanzun kya iya zuwa

kiji kunya. Ya iso gurin yace zo, babah ta malam na

kiranki don Allah kiyi hakuri ki bar zancen nan, wanda ya

fada ba don kansa ba. Ta nufo daki inda baba ke kiranta,

ina kuryar gado tare da fatan Allah ya dauki raina

yanzunnan. Baba ya dubeta, to in kin gama fadan kira

min yar bokon yar taki inna tace saboda Allah malam

daga ciwo sai ayi mata sharri? Ca wa fa sukayi tana da

ciki yace ai ba abin mamaki bane kira min ita. Hafsa

zonan, na fito kishirya mutafi asibiti inna tace malam

asibiti suna bada maganin basir ne? Acan makarantarsu

fa sunyi na asibitin sun gaji shinefa sukace ta taho gida

ayi na hausa. Yace to ai ba matsala bace wanan,

matsalata in tabatar da zargin da ake yi mata inna tace

ai! Malam kaima ka yarda za ta iya? Yace kwarai kuwa,

yace ita ba mutum bace? Ya ba kanshi amsa yacemutum

ce kuma baliga mai lafiya, don haka yanzu da bayanin

likita zan yarda da duk abinda zakuce. Nan take tsoro ya

kamani hankalina yafi da tashi. Inna tace je kushirya

kutafi asibitin inma har har danine sai muje. Yafita tare

da cewa ina jiranku waje. Nace inna kice masa don Allah

mu bar zuwa asibitin nan kinji? Tace a a ki shirya kindai

san halin babanki, in ba‘aje likita ya wankekiba bamu da

zaman lafiya, nace inna mudai mu hakura ba sai mu

barsu da Allah ba, masu cewa inada cikin? Tace shin

hafsat kodai kina da cikin ne?nazaro ido nace a a ni bani

da komai tace to shirya muje, garuwa ki daureye jiki

nace to a ban daki tamkar in haure yar gajeruwar

katangar mu in gudu, domin na san yau idan mukaje

asibiti asiri na yagama tonuwa. Yau auren iyayena zai

rabu na shiga 3! Nan wata zuciyar ta fada mun ba laifina

bane, in bisu inje asibitin inyaso duk yanda Allah yaga

daman zai faru dani shikenan, sai in rungimi kaddara.

Afili nace Allah ya isa munnir asibitin dutse muka je,

baba shine ya yankar min kati suka tura mu gurin da

zamu ga likitan mata. Duk da halin da nake ceki sai da

nayi Allah wadai da shugabannin da muke dasu. Asibiti

ka mar wannan ace likitoci mata basufi uku ba, ga mata

nan sun kusa 100, wata mata dake kusa dani tace min

tun asubahi suka zo nan tayi sallah. Amma har yanzu

ba‘a zo kanta ba. Ina ganin rashin kula da ba ayi da

likitocin shine dalili da yasa basu zuwa aiki. Haka muka

yini a gurin, amma baba ya dage sai munga likita. Muna

shiga ya bashi kati likita ya tambayi meke damuna?Kafin

nayi magana baba yace yata ce, munzo ne ayi mata

gwaji kotana da juna biyu. Likita yace bari yaji ta bakina,

ya tambayeni meke damuna? Nace basir da shawara,

yace yaya kikeji a jikinki? Nace amai da zazzabi. Kama

hannuna yayi ya duba, nan take ya bamu wata takarda

wai muje amin gwaji nayi fitsari na kawo. Nan take

sakamako ya fito baro baro ina da ciki nurse bata fada

muna ba, ta dai bamu sakamakon mu kaiwa likita.

Lokacin zuciyata ta gama bushewa, na mekawa Allah

komai. Mun shiga yana rubuta muna wani magani, sai da

ya gama sanan ya duba. Ya kali baba, tana da miji? Baba

yace a a likita yasake kalona, amma ke kinsan kina da

ciki? Wata muguwar faduwar gaba naji, tamkar yau

nasoma jin cewa inada cikin. Baba yace tanada ciki ko?

Yacigaba da rubuta wata ta karda yana cigaba da cewa

tana dauke da ciki. Abinda sakamako ya nuna kenan.

Amma kuje ayimata (scan) don kusan ko wata nawa ne

inna kawai na kallah wada ta kafa min idanu sun kada

sunyi jajajir,Baba ya ce a"a bama bukatar sai tayi

hoto,dama tabbacin cewa akwai cikin muke son sani,

tunda akwai shi kenan. Ya kalli Innarmu,bana bukatar sai

na sake tuna miki komai daga ke har ita. Ya fita abinshi.

Inna cikin kuka ta ce, Hafsa haka zaki min? Hafsa na

dace da wannan sakamakon? kin min adalci kenan? cikin

kuka nima na ce kiyi hakuri Inna, wlh fyade Munnir ya

min. Ta ce, karya ne, ki min shiru. Ta dubi Likitan da ya

zuba musu ido,don Allah Likita ka taimake ni ka cire

mata cikin nan. Da saurin Likitan ya mike tsaye cikin

murya mai karfi, fita anan domin nan ba asibitin zubar da

ciki ba ne. Muka fito muka nufo gida, Inna na fadin

Hafsa kin cuce ni kin kuma cuci kanki. kafin mu isa gida

tuni Baba yaje yayi fadan shi a tsakar gida kamar yanda

ya saba, muna isowa kowa sai kallonmu yake yi. Muna

shiga yazo ya ce ya va mu zuwa da safe mu fice,

yanzun ma don dare ne. Mutane na ta bashi hakuri,amma

ya ce to wane hakuri zai yi? Dan ya ce mata in haka ta

faru a bakin aurenta, kuma ta yarda. Ranar inna kasa

fadan nata tayi, duk da matan gidan da suka cika a kofar

dakinmu. Ni kaina kasa min fada tayi sai kuka da take

shara6awa. Mun kule can daki, can cikin sulusun dare

na tashi dan bacci taya dauki Inna na fice. Bayan na

kwashe duk wani abuna mai mahimmanci,

Baban titi na mika ina tafiya ba tare da tsoro ba. Daf! da

Asubahi naji wata mota suna cewa kano ne? na tsaida su

na shiga duk da cewa ba ni da ko sisi,saboda ragowar

kudina na mikawa Inna tun zuwa na, wato kudin wayata.

Sai da muka dau hanya suka ce dari biyar zan ba da, bn

yi mng ba, don haka sai suka zata na yarda ne. bakwai

da 'yan mintuna muka isa Gyadi-Gyadi, suka ce kudina,

na ce bani da kudi,don Allah su taimaka min. Nan

kwandastan ya hau ni da zagi, ni dai kallon shi nake yi.

Direbn ya ce, in je amma nan gaba in banda kudi in dinga

magana tun kafin na hau mota, don ba kowa zai iya

kyale ni ba. Na ce na gode.Sai lokacn kuma na soma

tunanin ina zan je? Wata zuciyar ta ce bakina karanta

littattafan su Anty Fauziya D. Sulaiman da su Anty

Sadiya ba? Ai suna fadin cewa in yara sun gudu su kan

je wani gidan a rike su a taimake su. To suma ai sa rike

ki in kin je ki zauna da sy za su fahimce matsalarki don

suna rubutu kan haka. Amma sai wata zuciyar tace, ki je

gurin Likita nan, ban san lkcn da na tsaida dan mashin

ba, na masa kwantace muka tafi. Ta fito kenan zata ofis

sai gani, ta ce a'a Hafsa ce .da safen nan? Na ce eh,

Anty ga shi ma bani da kudin da zan ba mai mashin din.

Ta zuge jakarta tana cewa, nawa ne? na ce,daga Gyadi-

Gyadu ne ba muyi ciniki ba, ta bashi dari biyu,naga dai

ya bata canji, amma bn san ko nawa ba ne, ta ce daga

ganin ki ba wata nasara amma shiga ciki. Sai da ta huta

bayan ta dawo sannan na fada mata komai, tace to ke

yanzun menene burinki? Na ce ni da zan samu wani dan

aiki in dauki nauyin kaina ba tare da na sake neman

taimakon kowane da naminji ba, zan so haka,amma da

wuya tunda takardun sakandire kawai gare ni, ta ce

amma bn san hikimar guje ma iyayenki da ki ka yi ba,

musamman mahaifiyarki wadda ta gwada miki kauna. Da

kin bita kun gudu tare ko kwa tsira tare. Na ce Aunty ina

tsananin jin kunyar mahaifiyata. Ba zan iya zama da ita

ba. A halin yanzun itama nasan ta dauki hanyar gidansu,

da wane ido zan kalle su? Ta ce to yanzu ina son ki

zauna nan mu ga yanda za"ayi. Ni da Asabe mun zama

'yan gidan Doctor Hindu, ita ke mana awo da komai,

magunguna duk ita ke ba mu. Cikin haka hr muka shiga

watan Haihuwarmu ko na ce haihuwar Asabe. Ta kawo

min kaya jarirai yayin da Asabe aka kawo mata daga

gidan su Yasir. Doctor ta ce, Kin gani kin hana mu dauki

mataki da kema yanzun dole su ringa yi miki komai. Na

ce, Bar su kawai Anty, Ni yanzun ba n da burin da ya

wuce in haihu lafiya, ina so in tsaya da kafafuna ko Allah

zai taimake ni in dawo da iyayena farin cikin su. Ina tuna

kannena, musamman Ummi, Nasan Baba kishiyar

Innarmu bata da mugunta, zata rike su amma nasan ba

za su yafe min ba, Matsawar suka ji cewa ni ce na

kashe auren uwarsu da ubansu. Doctor ta ce kada ki

damu, Insha Allahu za ki dawo musu da komai. Asabe ta

haihu'ya mace, kyakykyawa. Duk da 'yan gidan su Yasir

da shi kan shi ba su zo ba, amma sun aiko da komai

hatta ragon suna. Sannan suka ce ta sa ma 'yarta sunan

da take so. Doctor ce ta bada shawar a saka sunan

mahaifiya Yasir wato Maryam.A cewar Likitar, zai fi

girmama yarinyar duk lkcn data koma gare su. ...

A ganina matsalar Asabe mai sauki ce, don mahaifiyarta

har duba ta tazo sa6anin ni da ban san halin da nike ciki

ba? suma ba su san in da nike ba, Mai aikin Doctor ita

ce ke mata wanka., Kwanci tashi ni ma(E .D. D) na ya

cika har ya gota, amma shiru ba batun nakuda bare

haihuwa, Ranar Litinin tana min gwaji ko na ce awo, ta

ce yaran nan naki fa yayi girma da yawa ga shi kin kasa

kwantar da hankalinki jininki kullum kara hawa ya ke yi. ,

Yanzun ya wuce ka'ida ina miki tsoron afkawa cikin

matsala, kin kasa daukan kaddara. Kuka ya kwace min

Anty zan so in mutu a gurin haihuwa nan, shi ne kawai

burin zcyta. Likitar ta ce dama mun saba fada, duk lkcn

d zan miki awo,mugaye fatan d ki ke yiwa knki kuwa da

kina da kambun baka da yanzun kin lalace., Na ce Allah

isa tsakanina da Munnir Ta ce " Ameen. Amma yanzun

na fi so ki kwantar d hnklnk kin ji? Na ce to. Wasa- wasa

gani na kara sati 3 ta ce in na kara kwana 3 za a yi min

akin. Talata Doctor ta tafi wani taro a brnin Tarayya,

ranar ce kuma na soma nakudar Haihuwa. Haka na kwna

na yini, mai aiki tana kula dani, bayan magriba ta shigo

fada ta hau mu da shi me yasa b muje asibiti ba? Ni kam

na galabaita matuka,gado aka turo aka dauke ni, zuwa

cikin asibiti, amma haka na sake kwana dole ayi min aiki.

dn hk Likitar tasa a min shiri a sani a dakin tiyata.Tare

da taimakon wani Likitan suka yi nasarar ciro min katon

yaro namiji. Hakika na matukar shan wahala, kusan

kwana 3 ban sami kaina ba., Sai a rana na 4, din ranar

har na tashi an jingina min filo. Likitar ta kawo min

yaron. kai na kauda domin a ganina shi ne silan raba ni

da iyayena. Ban ta6a ganin fushin Likitar ba a iya

zamana a gidanta sai yau. Ta ce, Dauke shi ki ciro nono

ki bashi . Na fashe da kuka Anty ban yi aure ba kada ki

sa in ba shi nonona su fadi, ba zan ba shi ba. Ya ya

za'ayi ya raba ni da iyayena, na ci gaba da kuka, ta ce

ke rike shi kafin in zabga miki mari. Shi ina ruwan shi?

Shi ya samar da kan shi ko samar da shi ku ka yi? Don

me za ki ga laifin shi ? Da ba ku aikata abin da ku ka

aikta ba da Allah bai samar da shi cikin mahaifarki ba,

ganin irin kukan da nike yi yasa ta koma lallashina,

bayan na dauke shi. Babansa ya juya masa bya, kada

kema ki zama kin juya masa, Kina nufin ba za ki rungumi

kaddara ba? da lallashi ta shawo kaina na ciro nono yana

sha ina kuka. Satina daya na gargije, muka koma gida.,

Ba a yanka ragon suna ba, sai dai na ce ma Anty duk

sunan da ya dace ta sa mishi ta ce a sa mishi

SHADDAD. sunan wai yana mata dadi. Har ta kara da

cewa da Allah ya nufe ta da aure ya bata da sunan da

zata sa masa kenan, don haka yaro ya ci suna Shaddad.

A hankali na rinka jin kaunar yaron tana shigata, sai dai

kullum kamanninshi da Munnir kara bayyana take, ban

ta6a ganin da mai tsanabin kama da ubansa ba irin haka.

Zuwa yanzun zcyt ta dake,watanmun 3, Wata rana Doctor

Hindu ta zo mana da lbr mai dadi, wai ta samu miji,

tsohon ministan ilimi na kasa. Muka yi ta murna, ita kam

har da Azumi 2 don nuna godiya ga Ubangiji. Sati 4 aka

sa bikinta, mu ne har Katsina gidansu. 'Yan uwanta da

take bamu lbr duk mun gansu,ita ce ta dinka mana

ankon dinner. Ranar daurin aure da dare aka yu dinner.

Sam na kasa sakewa,saboda kallon da maza ke min, duk

da yaron da ke kafadata. Ni kuwa yanzu duk namiji da

zai kalle ni ko da bisa rashin sani ne ai bn da makiyi

kamar su. Mun sha biki,sannan muka dawo,mun samu

gidan yasha gyara,an zuba komai sabo,shi yana zaune a

Abuja da Iyalansa, amma ita zata zauna a gidanta

saboda aiki. Ada na cika wasa da tsokana ga son raha,

amma yanzu na koma miskila,masifaffiya, mara

fara'a.Bugu da kari yanzu ba ni da tsoro, musamman

akan namiji. Kwanci tashi hr Asabe ta yaye 'yarta, kuma

tuni an kaita gidan su Yasir. Bayan hukuma ta shiga

batun don kare lafiyar yarinyar. Sannan ta samu miji a

can kauyensu, mun je har can bikinta garin da aka kaita

ya dan fi kauyensu zama birni. Ni kam kullum cikin yiwa

Likita naci nake, ta samar min aiki ko na gida ne, ta ce

an gudu ba a tsira ba, dubi abin da ya faru da Asabe

sanadin aikin gida. Cikin satin da muka yi wannan

maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani

Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu.


Zaharaddeen Shomar


what's app 08168575100



Sanadin Boko 1-7

Posted by ANaM Dorayi on 12:29 PM, 12-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn

cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da

nisa tsakaninsu da unguwarmu.Na ce ba komai zan iya,

ba d jimawa ba na yaye Shadad, na ci gaba da zuwa

aikina, a wata dubu goma ake biyana. Shawara ta bani,

wai in bude (account) tunda bn rasa komau ba, hatta

sutura tana bani nata. Dan Adaidaita ta samo min duk

wata sai dai in biya shi, sauran na kai banki, Nayi-nayi ta

dinga cire wani abu a cikin albashina, amma sai ta ki ta

ce ita don Allah take zaune da ni,matsala daya a gurin

aikinmu ita ce manajanmu ba shi da mutunci.Farkon

zuwana ya yi ta shige min shi yana sona, ganin yanda na

birkice mishi sai ya sama min lfy, amma akwai zuga

rashin mutunci. In minti daya ka kara bisa karfe 8, to

zaya iya korarka, ban ta6a kai takwas ba tare da naje ba,

sbd ina matukar son aikina. Shadad yana da hkr yana

zaman shi gurin mai aiki. Cikin haka muka wayi gari cikin

farin ciki, Doctor ta samu juna biyu, Mijinta mu2m mai

mutunci da sanin ya kamata. Yayi murna, sai dai cikin

yazo mata da matsaloli masu dama, ko dn ta manyanta

ne? oho. Kwanci tashi ta shiga watan haihuwarta, mijin

ya ce ta shirya su tafi Abuja ta haihu a can, wani asibiti

na musamman. Sun tafi ko yaushe muna waya da ita,

maganarta daya kullum ita ce mu sa ta addu'a, sannan

ta ce min " Hafsa koda bn dawo ba kiyi kokari ke nemi

mahaifanki tare da neman yafiyarsu. Mummunan lbrn da

ba zamu ta6a mantawa da shi ba, musamman ni, shi ne

na rasuwar Doctor Hindu, nayi kuka tamkar raina zai fita.

Ta rasu bayan awa daya da haihuwarta, ta samu 'yan

tagwaye mace d namiji, Innalillahi wa inna ilaihin raji'un,

ko dangin Doctor basu kai ni jin mutuwarta ba, domin ni

ita ce dangina uwata kuma ubana. Can Abuja a kayi

jana'izarta, amma gidanmu ake zamn makoki, in da

dangin ta da na shi suka zo. Tun kafin bakwai na soma

tunanin gurin zuwa, don kan yanzun asirina ya tonu,

gatana ya fadi., A zaton danginta ni 'yar aiki ce, amma

dangin mijinta sun zaci ni 'yar uwarta ce, yaranta

tubarkalla, lafiyyu ana ta ji da su. Ranar 7 kuwa

subahanallah,tunda aka ce mu hada kayanmu za su rufe

gidan hankalina ya tashi, mai aiki kuwa dama daga

kauye take, bata samu matsala ba don ta riga ni tafiya.

Ga shi gobe zan koma aiki hutun da gurin aikina suka

bani a matsayin uwata ta rasu, kamar yanda na fada

musu. Rahma ce ta fado min a rai, yarinyar da muke aiki

shago daya da ita.Rahma tana da mutunci, bari in nemi

taimakonta. Na kira lmbrta t daga, na ce Rahma don

Allah ina nema wani agaji, ta ce na me? muryata ta

sarke, Rahma ina son dakin haya a unguwarku, zan

samu? Ta ce yau-yau din nan? Na ce eh, ta ce gskiya ba

za a samu ba, sai dai in an bincika a hnkl. Na ce na

shiga uku! Ta ce wai me yake faruwa? Na ce ba ni da

gurin kwana, ta ce, gidanku fa,? Na ce ba gidanmu ba

ne, kuma yau masu gidan zasu rufe gidansu, Ina da

matsala. Ta ce ok, yanzun kina ina? Na ce ina gidan ina

hada kayana, ta ce to za ki gane gidanmu? Na ce eh, ba

Tukuntawa ba? Ta ce eh, Mama tana nan sai kiyi mata

bayani kafin na dawo, na ce to na gode. Sun bani kayan

sawa nata da yawa, na nemo dan tasi ya dauke ni zuwa

Tukuntawa unguwar su Rahma, Mama da matar Yayan

Rahma ne kadai a gidan. Muka gaisa, Mama ta ce daga

ina? Sobada ganina da ta yi da kaya riki-riki na ce

sunana Hafsat gurin aikinmu daya Rahma. Ta ce oho,

yarinya da ku ka zo duba ni kwanaki ko? Na ce eh, ta ce

ba Rahma ta ce min Mamanki ta rasu ba? Na ce eh ba

Mamana ba ce, ta rike ni ne kuma yanzun 'yan uwanta

sun zo zasu rufe gidan saboda ya zama na 'ya'yanta. To

shi ne nake son ko zan samu dakin haya nan kusa da ku?

Ta ce to za a cigita, sauke yaron ki shiga da kayan ki

can dakin Rahma.

Ina jin dadin zama da su Rahma don ina yin biyayya gare

su, matar wan Rahma ce ka dai ke son min tambayar

kurilla,tana yawan cewa to wai ina iyayenki? Ban ta6a

amsamata ba, don ko Rahma bata san komai a kaina ba,

bata san Matsayin Shadad a gurina ba, duk da ta

cancanta in fada mata. Matsawar da nayi da son samun

dakin shi yasa su Mama suka sa ne man dakin, amma d

ta ce in yi zamana a nan gidan tun da ba ni da matsala,

haka dana. Na ce, a'a ni dai na fi sobn na samu daki

gidan mutunci gidan Hjy Iya aka samu dakin sai dai sun

ce min sai nayi hakur, don tana da fada. Na ce, ba

komai, in dai sai an tsokane ta ne zata yi to ba za ta

ta6a yin fada da ni ba. Matsalar in da zan dinga kai

yarona kafin ya isa shiga makaranta, ko da rainon kudi

ne. Ta ce, ki dinga kawo shi nan mana tunda shi ba mai

haya niya ba ne, Mun je naga dakin, karami ne ta ce

dubu shida shekara, dari biyar kenan dk wata, na ce ba

komai, zan biya. Naje banki na ciro dubu ashirin cikin

kudina nazo na bata shida, naje kasuwa na siyo kayan

abnci da yar tukunuya da dan risho na dawo.

Zaman mu da Hjy Iya ba matsala, don ina bn ta sau da

kafa,daga ni sai ita a gidan tun Asubahi in na tashi zan

wanke mana bandaki, in share tsakar gidan, komai na

dafa zan bata. In ko zan yi wanki na kan ce kawo naki

Hjy, kullum sai dai ka ji tana shi min albarka, Shadad

kuwa dama tuni ta ce in dinga bar mata shi tunda in

bana nan ba shi da matsala, musamman in ya gane cewa

gidan muke kwana. In ko unguwa na fita dashi kiwa ce

dashi, sannan ya yi ta 'yan rigime-rigime. Mun zauna

yanzu albashina da kyar nike kai dubu biyar banki a

wata, saboda hidimomin gida wanda a da ban san suba,

kai ko kan wannan ba zan manta da Doctor ba, domin ita

ce ke yi min komai. Burina na gaba shi ne, in koma

makaranta, amma yaya zan yi da aikina wanda shi na

dogara da shi? Wata rana da dare na shiga gurin Rahma

muna hira, na ce mata ina son na koma makaranta, ta ce

aikin fa? Na ce shi ne matsala, amma ina son in samu ko

'yar Diploma ba sai nayi jami'a ba, ta ce hakan ma yana

da kyau. Aikina daga karfe takwas din safe ne zuwa

hudu na yamma, sannan wasu su zo masu kaiwa dare,

na ce Rahma ko in koma aikin dare ne. Ta ce albashinsu

fa bai kai namu ba kuma yawan cinsu duk maza ne, na

ce to ya zanyi? Haka nan zan hakura in dai manaja zai

yarda ta ce matsayaci ba, sai shegen iko sai ka ce gurin

shi. Na ce ai dama ba shi ne da gurin ba? Ta ce ba shi

ba ne, na wata Hjy ce mai kudi, ina zaton ma ba a kano

din nan ta ke ba. Na ce to Allah dai yasa in dace zan

tare shi in masa mgn, Rahma ta ce to in ya ki fa? Na ce

ki taya ni addu'a ya yarda, Rahma ta ce to Allah yasa a

dace, in za ki masa magana sai muje tare .Haka ce kuwa

ta faru, domin washegari muna tashi daga aiki sai muka

nufi ofishin manaja, yana zaune gabn shi laptop ce.

Muka gaishe shi, cikin daurewa ya amsa, na ce "Yalla6ai

nazo neman uziri ne. Ya harare ni,wannan karon ko me

kika zo nema kuma kowa ya mutu ba zan ba ki wasu

kwanaki ba, sai dai in ki nemo wadda zata zauna

madadinki. Rahma ta ce, Sir, ba mutuwa akayi ba, tana

son koma mkrnt ne. ya ce, to sai ta bar aikin. " Ya ci

gaba da abn da yake yi. Muka kalli juna ni da Rahma, na

ce ko zan iya komwa akin dare? ko kuma in zo duk lkcn

d nike free hr dare? Ya ce wace makaranta? Na ce poly

zan shiga, ya kalle ni dama ba ki riga kin shiga ba? Na

ce eh, ya ce to in kin shiga sai muyi magana. Ni da

Rahma muka yi godiya, bai amsa mu ba, mu dai muka

fita muna mamakin yanda ya saurare mu. Ina jin an fara

saida form na garzaya na sayo. Rahma tana ta min

dariya wai na cika zumudi, Allah shi ne mai shirya ma ba

wa al'amuran shi. Yau gani na samu gurbin karatu a poly,

daga karfe daya zuwa biyu nake tashi, uku in zo shago,

bn damu da rage min dubu biyun da aka yi cikin

Albashina ba, saboda na samu shiga makaranta. Kuma

na samu irin course din da nake so, wato (Mass comm)

Rahma da murnarta take shaida min saurayinta Sagir zai

turo magabatan shi, na ta6a baki tare da cew. "Yau an

yo odar kaya a shop din nan, kin lura? Tace eh na lura

mana. Amma me yasa kullum na dauko batun Sagir sai

ki daure fuska? Haka nan ranar da na ce kuje ku gaisa

kikaki.Shi ko kullum sai ya ce in gaishe ki. Na ce, um, ki

dai yi hattara da samarin yanzun. Ta ce, Sagir yana da

kirki kuma aurena zaiyi, na kafa mata ido, kada ki ba wa

namiji amana fa, in kin yarda kenan. "Ta ce, to zan kula.

Wata rana ta ce min za su je gidan Yayar Sagir, zata

gaishe ta, wai tayi 6ari, na shirya muje na kalle ta

dabadan Rahma ba ce dana zabga mata ashar. Amma

Rahma ta wuce in zage ta, kema da zan fada miki ki ji

da sai na ce miki kada kije, ta ce ko zan san dalili? na ce

yaudarar mazanzamani.Tayi 'yar dariya, "Hafsat me yasa

kin matukar tsanar maza ne? Me suka miki har haka?"

Murmushin takaici ya subuce min na ce, "Sun min da

yawa." Ta ce, "Kada ki manta shekararmu 1 da Sagir

kuma kudin gaisuwarshi na gidanmu." Sam ban san

lokacin da maganar ta subuce min ba sai ji nayi ina

cewa, "Shekaru 3 da watanni muka yi ni da Munnir,

amma hakan bai hana shi yaudarata ba."Hawaye suka

soma zuba daga idona. "Rahama zan fada miki amanar

sirrina, in kin boye min kin kyauta, in kin tona min don

kanki ke da Allahn ki." Nan na kwashe komai na labarta

mata, ni kuka Rahma kuka, ta rungumeni babu mai ba

wani hakuri sai da muka gaji da kanmu. Na ce, "Rahma

zan koma boko ne kawai don faranta Ran Mahaifiyata,

Insha Allahu zan kawo haske cikin zukatan Iyayena

SANADIN BOKON nan." Rahma ta ce, "Ina bayanki, Allah

ya shige mana gaba. Lallai zan ja baya da Sagir kuma ba

zanje gidan Yar tasa ba." Na ce, "Na kula Sagir dinki

kamar bashi da matsala, duk daba anan take ba. Ki ci

gaba da mishi yadda kika saba amma ko da wasa kada ki

bishi wani guri. Amma ni a kan kaina na gama soyayya,

na kuma sha alwashin duk namijin da yayi gangancin

cewa yana sona zan ci zarafinsa matuka. Rahma ko

kinga laifina?" Ta ce, "A'a."Rahma 'yar amana ce, ko

Mahaifiyarta bata fadawa labari na ba, haka na ci gaba

da Karatuna tare da aikina, na tsare mutuncina ko a

makaranta nasha jin ana zagina wai na cika girman kai,

daga ganina ni ba 'yar kowa bace sai shegen Iyayi, ga

daure fuska. Sam ban damu ba, sai dai mutum in ya isa

ya zo gabana ya fada.

Kwanci tashi har na hada Diploma, kuma ina da burin ci

gaba da HND,shekara 2 kenan. Cikin shekara 2 har

Shadad ya isa shiga Makaranta, kuma na lura zaya dauki

Karatu sosai, shekarunshi 4 kenan da 'yan watanni. A

hanyar zuwa gurin aikina naga wata Makaranta Al-Iman,

boko ce da Islamiyya don haka na je Makarantar na

karbar masa form, sun ce yaro ya zo tun 8 na safe sai 6

na yamma. Duk da Islamiya da hadda, sati da lahadi sai

karfe 2 zai je. Alhamis da Juma'a karfe 2 zasu tashi.

Tsarin makarantar ya min daidai domin zan samu lokacin

daukan shi, sati na zagayowa ya soma zuwa, da dare

kuma inai masa bita.

Tambaya daya ya min wadda ta sa ni kwana kuka, tare

da tunanin me zai faru nan gaba? Ko ba komai nasan

nan gaba akwai kura, abin da ya faru ranar da ya fara

zuwa Makaranta ya dawo muna yin home work ya ce,

"Anty." Na dube shi, "Menene?" "Me yasa da kika kaina

Makaranta baki sa min sunan Babana ba? Duk 'yan

ajinmu ana kiransu da sunan Babansu, ni kuma ana

kirana da Shadad H." Gabana ya fadi, amma da yake shi

karami ne yanzun ba zai fahimta ba sai na ce, "H din nan

farkon sunana ne Hafsat na sa maka ko baka so?" Ya ce,

"Anty kowa sunan Babanshi yake sawa, wani yaro yace

min wai menene H? Wai Hamza sunan Babana?" Na ce

masa, "Ban sani ba, nace ba sunan Babanka ba ne,

sunana ne kaji ko?" Ya ce, "To." Can kuma sai naji ya ce,

"To shi Babana ya sunan shi?" Gabana ya sake faduwa

na daure na ce, "Na manta, amma in na tuna zan fada

maka." Na mike don kar ya sake yi min wata tambayar.

Shadad karamin yaro ne amma in ya maka magana sai

kayi zaton Babbane. Ina tsoron nan gaba kadan ya

tsareni don in fito masa da Ubansa, abu 1 na sa a raina,

shine zan zama uwarsa kuma ubansa, zan yi masa komai

da uba zai ma dansa.

Tun da na bar gida har yau ban daina kuka ba, ban daina

tunanin iyaye da 'yan uwana ba, kullum sai na zubar da

hawayena tare da yin Allah ya isa kwando dubu ga

Munnir, ba zan zagi Boko ba sai dai ba zan gaji da cewa

itace sanadin shigata matsala ba.

Haka kwanaki suka yi ta shurawa Allah ya taimake ni na

koma don samun HND sai dai manejin rayuwa nike,

albashina yayi karanci ya dauki nauyin karatuna da na

Shadad, don ma na tara kudi da farko lokacin Dr. tana

nan. Sai dai na dauki alkawarin ko zamu kwana ba mu ci

ba bazan taba neman taimakon abokin halitta ba, sai dai

in nema a gurin Mahalicci.

Cikin wannan halin yarinyar Hajiya Iya wadda ke zaune a

Saudi ta zo ta dauke ta tare da barin amanar gidan a

hannun Babban Yayan Rahma. Amma ni Hajiya Iya ta ce

in yi zamana kyauta har sai lokacin da Allah ya daga,

don ta ce ina lura da ita, kuma duk abinda na ci sai na

bata koda bata san da shi ba. Na ji dadin samun wannan

rangwame duk da cewa kudin ba wasu yawa bane dama,

amma sauki yana da dadi. Na dawo ni 1 a cikin gidan, in

zan fita na kulle, in sati ne ko lahadi ko dai wane lokacin

ne Shadad ba zai je Makaranta ba sai na kai shi gidan su

Rahma gurin mama, in ko ba nisa zanyi ba nakan yi

kasadar kulle shi ya taka kujera ta ciki ya sa sakata, in

na dawo sai na kwankwasa ya bude.

****** ******** *******

A garin Kaduna tun da aka wayi gari Hafsat ta gudu,

bakin ciki ya karu ga zuciyar Innarta, don haka ta tattara

yanata-yanata ta fice ta bar su Ummi suna ta kuka,

Baba tana lallashinsu. Har ta isa Malimfashi idanunta

basu kafe da hawaye ba, bata boyewa 'yan uwanta

komai ba,sunji bakin ciki suma saidai sun bata shawarar

tayi mata addu'a kada ta mata baki.Haka ta ci gaba da

zama har zuwa lokaci mai tsawo. Wani abokin wansu

Babba ya zo ziyara daga Huntuwa ya ganta ya ce yana

sonta, bata da zabi tunda duk yayyinta sunnuna sun

amince, kuma aurenta da uban 'ya'yanta ba kome.

Alhaji Danlami Matarshi ta rasu wurin haihuwa, amma

yana da yara kuma yana zaune tare da su ne,

shekarunsa 3 kenan rabonsa da aure, ta tare a gidansa

dake Nasarasa Funtuwa, dole ta koyi hakuri domin zama

da yara sai hakuri, in ta kalle su sai ta tuna da nata da

ke can wani gida. Sai ta kyautata musu ko don a

kyautata ma nata, yadda take kula da Yaran sai suma

suke son ta.

Cikin haka ta samu ciki ba don san ranta ba, amma ba

zata butulcewa kyautar Allah ba. Ta haifi danta namiji ya

ci sunan Rabi'u. Umar ya kan kawo mata ziyara da 'yan

kannanshi, mijinta yanada kara don in zasu tafi yanai

musu shatara ta arziki. Shi kuwa Babansu Hafsa har yau

yana bakin cikin tafiyar ta duk da shine ya koreta, yana

kuma addu'a Allah kada ya bashi mai irin halin Hafsa

cikin 'ya'yansa, ganin halinta ne da na Uwarta, ko wani

buri suka ci na son abin duniya shiyasa suka dage da

boko, boko har taje ta yi abinda taga dama.Ni kuma

lokacin rayuwa ta min tsanani, zuwa wannan lokacin

kudin da ke cikin account dina sun kare, albashina ya

min karanci, karatuna ga na Shadad, ga abinda za mu ci,

omon wanki, sabulun wanka har da suturar sawa, duk a

dubu 8. Don ma bana biyan haya. Yau na wayi gari ko na

karyawa bani da shi, ga shi wannan watan shine zan

bada kudin term na Shadad dubu 4, gashi zan yi

registration, gashi bamu da komai na abinca ga kudin

dan adaidaita sahu. Hakika komai ya tsananta gare ni,

kukana ya karu, nadamar barin gidan Iyayena ta sake

shigata sai dai ba zan iya komawa gidan yanzu ba, duk

da kuncin rayuwar da nake fuskanta. Lallai babu komai

cikin barin gida in ba takaici ba, danabi Mahaifiyata na

san danginta za su saurareni za kuma su fahimceni, zan

samu gata ni da dana kafin Allah ya min sakayya akan

Munnir. Bana ba duk wata 'ya mace shawarar barin

gaban iyayenta don gudun zubewar mutuncinta. Hawaye

na bin kumatuna ban damu da na share su ba, domin da

hawaye na karewa da yanzun nawa sun kare. Muryar

Shadad ce ta katseni, "Antyna menene yake damunki

kullum kike kuka?" Na share hawaye tare da kakaro

murmushi, "Babu komai." Ya dafa cinyata, "Kina tunanin

Iya ne?" Na ce, "Eh." Ya tambayeni ni don ya san kalmar

da zan fada mishi kenan, a duk lokacin da ya tambayeni

haka nake ce masa. Ya bata rai, "Anty to muje gurin Iya

din, ni bana so kina kuka." Na ce, "Da nisa jirgi ake hawa

kuma bani da kudi." Ya ce, "To ina girma zan saya mana

jirgi muje ko?" Na ce, "Allah ya sa." Kicin na shiga ina

dubawa, ko zan ga dan wani abin na baiwa Shadad, duk

da nasan cewa bani da komai. Shiru na yi tare da tunanin

abinda zan bashi. Rahma ta yi sallama, na amsa, ta

shigo kicin din tana cewa, "Ina Hajiyar gidan nan?" Na yi

guntun murmushi tare da cewa, "Rahma kenan, duk

tsokana kin santa." Ta ce, "Na zo shan tea din kin nan

mai kayan kamshi." Na ce, "Sai dai na baki kayan

kamshin ki je ki dafa." Ta zuba min ido cikin sanyin jiki,

sannan ta ce, "Hafsa kin 'ki daina kukanki ko?" Na ce,

"Ina kika ga ina kuka?" Ta ce, "Haba Malama, ga idonki

nan?" Ta shiga bude-bude, bata ce min kala ba ta fita.

Ina cewa, "Rahma zo ki ji." Bata juya ba ta wuce. A

zuciyata na ce Rahma kenan, ita dai ta tsani ta ganni

cikin damuwa, ina son zama da ita don ita kadai ce kan

sani murmushi. Jim kadan sai gata da kunshin kosai da

jug dauke da koko, bata min magana ba ta zuba ma

Shadad. Na ce, "Rahma koko kuka dama?" Ta zabga min

harara sannan ta ce, "Ai wallahi Hafsat kina bani haushi,

ina lura da ke duk matse-matsen da kike yi cikin satin

nan, har ta kai baki da abinda za ki ci amma ba zaki iya

tambaya ba? Ni kam ko yaushe gidan ki nake cin abinci,

saboda ina daukarki 'yar uwa ta jini." Na ce, "Rahma

dama ni dake ai babu wani bambanci duk daya ne." Tsaki

Rahma taja, sannan ta dora min dari 5 kan cinya, zan yi

magana ta ce, "In kin ce tak Allah ya isa." Da kallo na

bita har ta fita sannan na saka dariya, Rahma kenan.

Karatuna ya shiga wani hali, har ina ganin in ba wani

ikon Allah ba tsayawa zaiyi. Cikin wannan matsatsi aka

sa ranar auren Rahma da Sagir, kullum tunani na me

zanyi ma Rahma lokacin bikinta? Da dare Rahma tana

min kitso muna hira na ce, "Rahma kin san me nake

tunani?" Ta ce, "Kudin Registration?" Na ce, "A'a, so nake

ki fadi abin da zan miki lokacin biki." Cikin tsokana ta ce,

"Italian bed da leader sit." Muka sa dariya, na ce "Allah

ya hore, har kayan kicin sai na miki." Ta ce, "Ni dai

Hafsat nafi son ki bada hadin kai lokacin bikina kin ga

dai bani da wata aminiya sai ke, sauran duk kawaye ne."

Na ce, "Tabdijan! Rahma kada ki sani yin abinda ba zan

iya ba." Ta saki kaina, "Kin san Allah?" Ta nuna ni da

kibiya, "In bikina ya yi kyau ke ce in ya baci ke ce, kuma

yanzune zan san matsayina a gurinki." Na ce



Zaharaddeen Shomar

what's app 08168575100



Sanadin Boko 1-8

Posted by ANaM Dorayi on 12:13 PM, 18-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

, "Maida wukar, Allah ya kaimu. Yauwa dama ina son in

miki batun da ke raina. Ina son in samu manaja ya bani

koda rabin albashina ne in sai ma Shadad takardu." Ta

ce, "Kin san rashin mutuncin sa, abinda zai fi dai in

tambayar miki rance gurin matar Yayana." Na ce, "A'a ki

bari zan same shi in yaga dama zai yarda." Rahma ta ce,

"Hafsa kenan, ke bakya son bashi sam! Kuma ai naga

bashi hanji ne yana cikin kowa." Na yi 'yar dariya. Haka

kuwa na yi, na samu manaja da bukata sai ya ce, "Kin

cika daure fuska, da ace kina da fara'a har karin albashi

zan miki. Banda kyautukan da zaki yi ta samu a kai-a

kai." Na sake hade fuska, "Bana bukatar karin ko wata

kyauta. Hakkina kawai nake so." Ya ja tsaki, "To sai ki

jira lokacin baki hakkin ya yi, ke bazaki taba ganewa ba.

Wai me ma zakiyi da kudin?" Ban amsa shi ba har sai da

ya sake maimaita tambayar, Na ce, "Zan biya kudin

littafan makaranta ne na yaro."Ya yi tsaki, "To sai ki jira

lokacin don in kin ga na yiwa mace mutunci itama ta yi

min ne." Na mike ba tare da na sake magana, don

Manzon Allah ya ce ka fadi alkhairi ko kuma ka yi shiru,

amma na so in zabga masa ashar in ya so ya kore ni

gaba 1 daga aikin. Cikin kwanakin sai manaja ya soma

shige min, duk da dinke fuskar da nayi masa, ya zo ya

kawo min albashina wai gashi nayi bukatar da zan yi, na

ce ya barsu ai ni na ma hakura. Kwatsam! Rannan sai

naji ana buga min gida, lokacin 9 ta gota na dare, don

har na soma bacci. Na zo na bude, nayi mamakin ganin

manaja a gidanmu na ce, "Lafiya?" Ya ce, "Kalau, na zo

ne mu gaisa." Na ce, "Na gode da gaisuwa. Sai da safe."

Na juya ya ce, "Kina nufin har mun gaisa? Bai dace ki yi

min haka ba." Na ce, "Za a min fada an hanani fita." Na

fadi haka da nufin karema kaina mutunci. Ga mamakina

sai naji ya ce, "Haba yarinya, ni zaki yi wa karya? An ce

miki bansan cewa zaman kanki ki ke yi ba? Ni zaki saki

jiki ki ci arziki ki saki, in ba zaki saki ba talauci sai ya yi

ajalinki." Jikina ya yi sanyi lakwas, na maimaita kalmar

zaman kaina! Na ce, "Ni ce mai zaman kaina?" Ya ce,

"Sharri na miki? Kowa ya san ke kadai ce ba kuma a san

iyayenki ba." Ya ja tsaki tare da cewa, "Banza mara

rabo." Ya tafi.

Ranar na yi kukan da ya isheni, wato kowa ya san

zaman kaina nake? Wata zuciya ta ce, "To yanzun ai an

daina kiwon dabba mutum ake kiwo." Sai dai da mutane

zasu min adalci ya kamata su san cewa bana hulda da

maza, da ace ina da wani aikin lallai zan bar super

market din nan, sai dai bani da zabi.

Da safe duk da kirkiro fara'ar da nike yi sai da Rahma ta

gane cijewa nake yi saboda damuwar da ke raina. Ta

kafa min tambayar me ke damuna? Nanfa na fada mata,

na kara da cewa, "Dama duk mutanen unguwar nan

kallon da suke min kenan? Ina zaman kaina?" Rahma

cikin muryar lallashi ta ce, "Sam, shi dai yabi diddigi ya ji

cewa ke 1 ce anan. Amma ba maza kike tarawa ba,

kowa yana yabonki a unguwar nan don kin tsare kanki,

kuma shi ya fada hakane don takaicin bai samu abinda

yake so ba. Ki barshi da Allah." Nace, "To in ban barshi

da Allah ba yaya zan masa? Ai bani da yanda zan yi

dashi. Da ace ma ina da wani aikin barin musu wurinsu

zan yi." Rahma ta ce, "To ai ba gurinshi ba ne shima cin

arziki yake yi, don haka ba inda za ki je." Daga wannan

lokaci muka sa 'yar tsama da shi, ya bi duk ya tsane ni,

nima kuwa ya kara dasa min tsanar maza, yana son ya

ga nayi wani dan kuskure ya tozarta ni, niko duk wata

hanya da zata ja min cin mutuncin shi na 'ki sakaci da

ita, lokacin zuwa aikina baya cika nake isowa,

musamman in zuwan safe zan yi.

******** ******** *****

Munnir an kammala karatu an kuma dawo gida. Tuni ya

manta da wata Hafsa da labarinta. Ya iso gida cike da

soyayyar Mina, yarinyar wani kusa ce a gwamnati, sun

kulle ne tun a yanar gizo ta (Facebook), sun jima suna

soyayya kafin suga juna, bayan ya zo hutu itama ta dawo

daga inda take karatu, suka hadu. Sun yaba da juna, sai

dai sanin cewa ba za ayi musu aure da wuri ba suka

kazanta soyayyar su ta hanyar biyan bukatar zukatansu.

Sam! basu dauki hakan laifi ba, nasu ganin duk cikin

soyayya ne a nasarance suke koman su don boko suka

sani, shi suka iya, kuma shi suke yi. Sun dai kulla

alkawari ga junansu cewa za suyi aure in lokacin yinsa

ya zo, Allah ka shirye su shirin Addinin musulunci.

(Ameen).

¤¤¤¤¤¤¤¤¤

Bikin Rahma ya gabato don haka na ciro dubu goman da

na makale na ce mata na ba da rabin kudin Registration

naje nasai mata sestin kula da jug. Dubu bakwai na

kashe, nazo na kai mata gida, batan hakan ya min dadi.

Su Mama suna ta gdy, ta ce yanda garin nan babu kudi

shi ne zaki ta wannan dawainiya har haka? Na ce Mama

ta kama ne. Da dare ina krtn Alkqur'ani,sai gata ta ce,

Yayi kyau Hafsa, ina kika samu kudin sayan kayan ban

masu tsada?Na ce Daga Sarki Allah. Ta ce, ba dai kudin

Registration din ba ne? Na ce in sune fa? Don Allah zo ki

zauna muyi batun anko. Ta ce ba zama nazo ba ki zo in

ji Sagir da wani abokinshi, ki fada musu kudin abubuwan

da zamu yi. Da karfi na ce " What? hum........ hum.....

Rahma kada ki sani cikin hulda da maza. kije kawai ki

amsa, na yarda zamu je kasuwa siyayyar tare. Zata yi

mgn na rantse mata da girman Allah cewa ba zani ba, ta

juya ba tare da ta ce kala ba. Nasan tayi fushi, amma

sam fushinta bai dame ni ba, in dai akan abin da zai sa

nayi hulda da maza ne har nai musu dry. Don ni nasha

alwashin namiji ya gama ganin hakorina. Mun je kasuwa,

duk abn da zamu bukata gurin walima mun sayi, don

Walima kadai zamu yi kayatacciya, sai dai ta ce, Sagir za

suyi (Dinner) kuma za su yi (Pink & blue day). Kullum

rokona take in je har dai na amsa mata zani. hakan ya

tilasta min siyan shadda kamfala (pink) mai ratsin

bulu,yayin da Shadad na dinka masa(blue) din shadda,

atamfar walima kuwa Rahma da kanta ta sai min.,

Bikinmu yayi kyau, komai a gidana aka yi duk da cewa

ina zuwa gurin aiki da mkrnt, kin yi wa Manaja mgn nayi

don ba zan sake yi mishi wani zance ba, ko neman wani

abu. Ranar daurin aure kam ban je makarantaba, kuma

banje aikin ba, saboda aubuwan sun kwa6e min.

Malamai sun halarci walima, sun kuma yi nasiha akan

mahimmancin yin aure tare da falalar da ke tare dashi.

Sun ja hanklin iyayen yara masu cewa su dole sai

'ya'yansu sunyi boko mai zurfi, ko sai sun kama aikin

kafin suyi aure. da cewa wannan ba koyarwa addinin

Musulunci ba ce. Suka ce, ita mace babu abinda yafi

daraja da mutunci a gare ta irin aure. Sun ce boko ba ya

hana aure, kamar yanda aure baya hana boko. In

'ya'yanku suka lalace saboda kun hana su aure sai boko,

hakika laifin zai fi ta'allaqa a kanku iyaye., Nasihar da

suke yi ta sani shiga dogon tunanin, ni kaina misalice

SANADIN BOKO gani yau na zama 'yar kaina, domin da

ace ban ce bokoba nabi zancan mahaifina nayi auran da

yaso, da yanzun ina tare da dangina da ban kashe auran

iyayena ba, da ban haifi shege ba, da maxa ba su dinga

latsa ni suna son mu lalace ba. Ban san hawaye na

sauka daga idanuna ba, sai dai hannun Rahma naji a

kumatuna tana share min tare da yi min rada a kunne.

Haba Hafsa cikin fa taro ki ke, ya ya za ki ba mutane

damar yin tunanin ke wacece? Please ki share don Allah.

Walima ta tashi lfy, na ce da Rahma bari na leka shop,

kin san ban dauki uxiri ba, ta ce min ba damuwa. Naje na

samu su Ishak, ya ce nasan kuna biki shi yasa ban tashi

ba, na fada mawa manaja cewa zan zauna madadin ki

har ku gama biki, ya kuma san auran Rahma ne shi yasa

bai ce komai ba.Ya kara da cewa, ki koma har sai kun

gama ki mata fatan alheri, mun so muzo daurin aure

amma kin san Manaja. Na ce na gode, ya ce a'a ba

komai, wata rana irin haka zata iya faruwa da mu, na

dawo nake fada ma Rahma ta ce, Ishak da Musa suna da

kirki sosai, dn dai kin kasa Fahimtarsu ne. Na ce, Ba zai

sa don sun kar6ar min aiki in sakar musu fuska ba,

gaisuwa kawai ke hada mu ko da, kuma ita zan ci gaba

da yi kadai. Anje anyo ma Rahma danki(jere) an zo ana

ta lbrn kyan gidan an ce ango ma ya zuba labulaye da

kayan wuta, Sai an kai Amarya sannnan za'ayi sauran

shagalgulan da ango suka shirya, wai ba a son mutane

suyi yawa, sai ka nuna pass sannan zaka shiga. Da muka

kai amarya unguwar Sharada, gidan kam ko ni ya min

sosai, taso in kwana na ce mata ta min hakur sai gobe in

mun hadu gurin (pink & blue day' . Ta ce don

girman Allah kada ki ki zuwa, na ce kin sanni Rahma in

har na ce zan yi abu bana fasawa, ta ce shi kenan, ki

gaida min Shadad. Na tafi ina hawayen rabuwa da

Rahma, don ita wani bangare ne na farin cikina. Gidan

su Maman Rahma naje na dauko Shadad, jikinshi naji da

dumi, ina zuwa gida na bashi (paracetamol) Na kwantar

da shi. Sannan na shiga gyaran gida. Ina zuwa na samu

ma yayi bacci, nayi Shafa'i da wutiru nima na kwanta.

Cikin dare na farka don yin nafila kamar yanda na saba,

sai dai kawai naji jikin yaro sharkaf da zazzabi. Na cire

masa riga na dunga goge masa jiki da ruwa mai sanyi.

Sanna na kara bashi magani, kafin safe Allah ya

taimakeni jikin yayi sauki. Sai dai yan rigin gimun da

yake yi na shiga gidan su Rahama muka gaisa da su

mama, ina zama

Kiran Rahama na shugowa, ina ji dama nasan ita ce, dan

bani da number kowa a cikin zumu dina na daga ina

cewa hajiya kenan, amarsu ta ango. Ta katseni da cewa,

ba wata hajiyarki, shine ko ki kirani da safe ko? Nace shi

kenan sai na hau doka maki kira da safe kisa angonki ya

ji haushi na. Tace wane ango? Kin san Allah ba nan ya

kwana ba, tare da su hadiza kawaye na muka kwana, ba

ke kinki ba? Nace ai gara da na dawo, dan na sami

shadad da zazzabi haka muka kwana. Amma yanzu

Alhamdu lilahi. Tace to Allah ya kara sauki. Tace don

Allah ina sa ido gurin programme din nan, wlh in baki

zoba bikin zai baci, don kina da muhinmanci matuka a

gurin. Nace to zan kokarta duk da shadad nata yan

rigingimu, kin sanshi in baya jin dadi sai yayi ta rigima,

tace yaro kenan Allah dai ya kara sauki,nace amin, yace

kizo da wuri dai. Sai da na fara yima shadad wanka,

sannan na shiga na fito naga gari ya soma hadari, nayi

alawala dan yin sallar la‘asar, haka kawai yau naji ina

sha‘awar shafe shafe a fuskata. Na fito da kayan shafa

da rahama ta di bar min na lefenta, har da jaka da

takalmi da mayafi ta bani duk pink, tun asali ni mai son

yin kyale kyale ce, halin da na tsinci kaina ne yasa na

daina, nafi minti 30 ina kyalekyale a fiska ta. Na dinga

kalon kaina a madubi nasan nayi kyau sosai, har shadad

yana kallo na, nace nayi kyau? Ya daga kai ina kulle gida

rahama na kira na, na daga tace aminiyata ki tai makeni

kada kisa naji kunya, wlh guri yayi guri amma ke kadai

muke jira da wani abokin sagir da ya sauka daga

adamawa state, anje daukoshi daga filin jirgin don Allah

kiyi sauri. Nace to zubaina ganin zuwa amma fa garin

akwai hadari, Allah yasa in sami abin hawa da wuri.

Tsaye nake a bakin titi duk wani dan a daidaitan da yazo

yana dauke da mutane, masu son banza watan yan rage

ma mata hanya suna tsayawa Amma ni ko kallon su

bana yi. Wata jibgegiyar jeep ta zo ta gifta, sai kuma ta

dan dawo.sai tin inda nake ta tsaya, gilashin motar ya

sauka a hankali,naga mai tukin saurayine yana sanye da

shadda yar gaske blue mai duhu, hularshi itama blue ce,

amma kalar sararin samaniya. Ta gefen ido na kaleshi,

sannan na dauke kaina. Yace, yan mata ina zaton guri

daya zamuje in na lura da shigar da ke jikin ki ko? Na

kaleshi nace ba dole hakan ta kasance. Yace, yace ki

shugo muje kinga hadari. Nace kuje na gode. Glashin

baya ya sauka, naji saukar galas din ne da wani sauti da

yayi, amma ban waiga ba, saima na dan kara taku biyu

ta baya na. Muryar da naji ne tamkar in waiga, amma sai

na dake yace shugo mana ga hadari nason zubo da ruwa

gaki da yaro. Na dubeshi dan son in tuna inda na san

wanan muryar, kyawunshi yasa nayi saurin kauda kaina,

tare da cewa kuje ni ba zan shiga ba.daga cikin motar

naji wani yana cewa don Allah mutafi amma za a

taimaka mata tana yiwa mutane yanga,da sauri na

kallesu cikin bacin rai, idanuna har kan kancewa sukayi

don ta kaici, cikin kalon hadarin kaji nace taimako? Ce

muku nayi ina neman taimako? Na dan duka tare da leka

motar, kai me fadin taimakon nan kasani bana neman

taimakon wani abin halita sai ma halincci, ni ban tsai da

ku ba. Na kara rike hannun shadad da kyau, na soma

tafiya dai dai da ruwan ya kece, kamar da bakin kwarya,

ba tsanmani sai naga kofar ta wangale na bakin kofar ya

sauko kafa tare da sauko hannu ya dauki shadad zuwa

cikin motar, a gigice na dubesu yace ki shigo in kuma ba

zaki shigoba ki samemu a can. Amma shi kam ruwa ba

zai dake shi ba. Bani da zabi, tunda sun daukar min yaro

dole na shiga. Gashi bana son dukan ruwan, don haka sai

na shiga. Shadad na ciyar mutimin da muryarshi ke sani

faduwar gaba, kamar na taba jinta ada innaso in tuna

inda nasan muryar ko mai irinta. Muryar ta sake katseni

da tunanin da nake yi, yace ma shadad boy ya sunanka?

A zatona shadad ba zai yi masa magana ba, saboda shi

yaro ne mara son ma gana, musanman in bai san mutun

ba, sai naji yace shadad. Mutumin ya mai maita sunan

shadad, sunanka yayi dadi, to wanan fa? Ya nunani ya

sunanta? Shadad ya kalle ni, na zabga mashi harara,

amma ga al‘ajabi na sai yaron nan ya kauda kai yace

anty. Mutumin yace to kana zuwa makaranta? Yace eh

al‘iman sunan makarantar mu, kuma muna yin (A B C D)

har da(1234). Na rike baki inata al‘ajabin yaron nan,

tunda nake dashi ban taba jin yana rarata surutu haka ba,

harda kin kalona shida ko abu aka bashi da ya kali

fuskata zai gane, in ina nufin ya karba ko karya karba

amma sam ya ki kallona tunda ya gane ina hararan shi.

Mutumin yace gud, kana yin kokari? Yace eh mana, har

ma naci number one, aka min kyautar books. Anty na

kullun tana koya min karatu, da su home work harda ma

islamiyya, ban san sanda nace shut up stupit boy!

Mutumin ya kalle ni, shikuma shadad ya kwanta lakwas a

jikin mutumin. Ya tsorata dan bana mashi tsawa, ko

yawan zaginsa. Na daga can gefen yace. Ke! Wai wane

irin hayaki kanki ya keyi? Ko kuwa ance maki wani kyau

ne dake? Ko ance miki sonki ake yi? Ko kuwa burgewa

ce wannan masife masifen da kike yi. Nace kai saurareni

bana son shishshigi da katsalandan cikin lamari na, nayi

magana da kai? Ko nace ka kalle ni ne bare ka tan tance

kyauna?gani na kayi a filin gasar kyau? Balle kace nace

ina da kyau ne? Masifa kuma dole ku jita tunda ku ka

nace sai kun dauko ni, haka nan bana bukatar burge

kowa cikinku na fison in burge kaina. Don haka yi ta

kanka dan dukanku bakwa gaba na, zaiyi magana mai

dauke da shadad ya daga masa hannu alamun yayi

shuru. Shi kuma yaci gaba da shafa kan shadad wanda

yayi kwance a jikinsa. Wayata ta shiga ruri, ban ko kula

ba dan nasan rahama ce, sai yi take tana katsewa, ana 5

din na daga a kufule, don itama haushinta nakeji ba don

bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan.



zaharaddeen Shomar

what's app 08168575100



Sanadin Boko 1-09

Posted by ANaM Dorayi on 12:23 PM, 18-Sep-15

Under: SANADIN BOKO

Don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za

ya hadani da wayanan gardawan. Cikin fada nace wai

meye ne kika dame ni da kira, ina hanya in kuma zaki

matsa min sai na juya gida abina. Tace mai da wukar

Allah ya baki hakuri, da ma ruwan da ake shekawa ne

nace bari naji ko kin koma gida ne saboda ruwan sai

direban su sagir yazo ya daukeki. Nace na hutar dashi,

gani nan zuwa na kashe wayata tare da tsaki.Harabar

hotal dam yake da jama‘a, ko ince motoci jama‘a sun

cika holl din suna tsayawa na kama kofar zan buduwa.

Ashe daga gaba ne direbab zai bude mu. Yana budewa

na fita, sanan na nufi ciki mai surutun tsiya nan shadad

ba tare da na kalesu ba na nufi wata yar baranda ina ta

yi mashi fadan irin surutun da ya dinga tsugawa acikin

motar, sai ya bale mun da kuka yana fadin.uncle! Uncle!!

Nace yi min shuru ko in mareka, sarkin shishigi, bai daina

kukan ba, na na ciro wayata na kira rahama gani nan fa

ba zan iya shiga ba, mutane sunyi yawa. Ta ce mun

ganki kin tsaya ga Aisha nan tazo zata taho dakegurin

mu tare zamu shiga. Nice a gefen amarya sauran

kawaye suna bayan mu,haka nan ango da abokan shi

suna biye da mu, ina reke da hanum shadad, wanda har

lokacin bai daina gunjin kuka ba, muka shiga. Kidan da

ke tashi kamar zai fasa kwanya yasa naji tamkar in bar

gurin kai tsaye. Wani mai dauke da abin magana yace,

ango da amarya sun shigo, kowa da amininshi zai zauna,

sagir ya zauna gefen shi wanan mutumin, ni kuma ina

gefen Rahama tare da shadad

ta dube ni, mutuniyata wa ya taba ki ne, naga fuskarki ta

kasa boye fushinki, nace uhm! Ke dai bari, abokanan

muijinki ne wlh, sai kuma shadad yaron nan ya kular dani

yau. Tace to dan saki fuskar mana saboda guri ya

kayatu, kisan fushinki zaisa gurin ya dishe. Na harareta

tare da dan murmushi, tace ko kefa. Sagir yace ranki

yadade, ya gajiya? Na nace tana gurinku ya jama‘a?

Yace gasu muna tare nace Allah yasa alheri, da ganan

na maida hankalina gun mai abin magana, yace za mu

kira baban bako kuma baban abokin ango don yayi mana

jawabin maraba tare da dan fada mana wanene sagir.

Sai dai kafin nan babar kawar amarya hajiya hafsat sai

ta bude mana taro da adu‘a, na kali rahama tace please,

tashi kawai. Na mike cikin natsuwa na isa gurin na

amshi abin maganar. Shadad yazo ya rikeni yana kuka,

sai wai abokin ango ya taso ya daukeshi. Bayan n gama

adu‘a na dora da karanbanin nawa, ina bawa jama‘ar da

ke gurin nan shawar kada suyi liki, almubazaranci ne ga

duk mai sha‘awar ya burge ango da amarya su dan ka

musu a hanun su, amma ba dole bane kuyi yanda

nace,sha wara ce. Na koma na zauna, bayan sun bini da

tafi. Shiko da zaije yin jawabin maraba tare da shadad

yaje yana rike da hanunshi. Cikin jawabin ne naji yana

jaddada maganata cewa abinda na fada yayi kyau, don

haka ba‘a son liki, duk wanda zai lika yazo ya ba ango ko

amarya a hannusu. Wanan ma yasa aka kashe rawa da

za‘ayi, rahama ta dinga yi min dariya wai a gaisheni da

karfin hali har ta sanima na dinga dariyar. Sagir cewa

yayi nazo na hanasu rawa, to wane rawa zasuyi ba liki?

Nace tai makonku nayi ai rawa haramun ce ko? Haka

aka ta gabatar da abubuwan da za ayi har lokacin da

akayi sanarwar ango da amarya tare da da masu tayasu

zama dan dibar abinda suke son ci da kansu,

kasancewar dibi da kanka ne za ayi a gurin. Muka hadu

muka jeru amarya tana biye da ango yayinda ni kuma

nake biye da abokin nashi, shi kuma yana dauke da

shadad a kafada tamkar wani danshi. Ango yasa abida

yake so sai fruit ya ce ko zaki tai maka min? Inji abokin

ango tamkar ince a'a amma sai nace me zan sa maka?

Ganin yana sabe da shadad yace ki samin ko menene,

zan ci. A raina nace kaji dashi, ba tare da tsayawa tunani

ba ko mai hanu na yakai shi nake zuba masa, sai da na

shake plate din sannan na bi bayanshi da plate 2. A

gabanshi na dire tare da samashi cokali, na koma ma

zaunina. Sai kurum naji sarkin surutun nan wato mai rike

da abin magana yana cewa, kai gaskiya ango da amarya

kun burge ni, kun zauna da aminan ku kuma mata da miji

har da dansu, to yace ke amarya yaya bakiyi koyi da

kawarki ba kema ki zuba ma ango da kanki? Kai abokin

angon nafa yi maka murna, matar kada kayi mata

kishiya, dubi yanda ta cika maka plate da kaji da kifi kila

abinda ka fi so kenan, wanan ya nuna ko a gida ba a

barinka da yunwa. Sai kurum naji gurin ya dau tafi. Da

sauri na dubi plate din, lallai kam kaji ne da kifi, sai dan

cosilo a gefe, na dubi fuskarshi yana dan murmushi.

Rahama da sagir kuma dariya naga suna ta shekawa nan

take na hade rai tare da kin kai komai bakina. Shiko

shadad sai uban cin naman nan yake yi, shi da mutimin

tuni gurin ya rikice da ciye ciye kowa na diba da

kansaRahama tace to kici mana,nace mata ke ni nama

koshi, ba yan haka ma ni ba zan iya cin komai a taron

nan ba, kowa yana kallona. Haka nan bayan an tashi duk

na matsu naje gida domin magariba ta yi, ina so inyi

sallah sai dai tun da muka fito banga shadad ba, ban ga

mutumin nan ba. Nace rahama ina suke? Tace suna

cikin jama‘a in dan jira. Can nesa na hango wani shago

naje na siyo ruwan naira 10 nayi alwala, nasami gefe

dama da hijabina a jaka, nayi sallah ta. Rahama tazo

tana ce min sun dawo? Nace ke zan tam baya, ina

mijinki? Kune kuka sanshi ku zaku nemo shi. Takira sagir

tace sun ko dawo? Hafsat tana son zuwa gida. Yace a'a

na kira wayarshi kuma a kashe, tace a a to ina ya shiga?

Kai kana inane? Yace gani nan kusa da shago ina kallon

ku ai. Muka nufi girin ango, hankalina ya tashi da rahama

take fada min wai wayanshi a kashe.rahama ta dubi

angon ta tace, ba kace min bako ne ba? Yace eh amma

kano ba bakuwa bace a gurinshi. Ki kwantar da

hankalinki, yauwa gasu nan zuwa ma, duk muka kai

duban mu gurin shi. Yana rike da hanunshi, shi kuma

yana reke da leda. Suna tafe suna yan zan tukansu har

suka isko mu, nace kai ka cika shegen yawo, ina kaje?

Na finciko shi yace anty munje masalaci ne da uncle, ba

kin ce mun wai in dinga sallah a farkon lokacinta ba?

Nace naji ni dan Allah wuce muje na dubi rahama sai

watarana, tace dinner din fa, anjuma karfe 10 naja tsaki

ke kinsan ba zan iya wanan galafirin ba, gara ke sai dai

nazoo. Sagir yace ki bari a kaiki don Allah, gari yayi

sanyi ga duhu, nace nagode, sai anjima nayi gaba.Wani

daga cikin abokan da suke tsaye wanda har dashi muka

shigo motar nan da zamu zo, ya dubi rahama yace kai

wanan kawar taki ta cika masifa, ita ba kyau ba rahama

tace a a kada ka zagar mun kawa masa‘udu, hafsat bata

da masifa,tana da kirki sosai na jima banga mace mai

saukin kan hafsat ba, ita dai abu 3 ta tsana a rayuwarta,

inko mutun ya kiyaye ba mai jin su. Ni da ita bamu taba

yin fada ba koda munyi sai dai ni ni na ta sababi na

amma bata biye min. abubakar lamido yace yanzu kai

kaga masifarta? Ya dubi masa‘udu masa‘udu yace au

yanzu duk abinda take maka baka gani ba? Yace ni kam

me tamin? Bata min komai ba, duk abubuwan da takeyi

sun matukar burgeni. Ya dubi rahama, ni kam in tambaye

ki? Rahama tace ina jin ka, yace amma dai ba matar

aure bace ko? Rahma tace a a daga nan bai sake

magana ba. Duk abubuwan da Abubakar Lamido ke gani

daga hafsat bai taba ganin wani aibunta ba, tunani 1 ya

dameshi, ina ya santa? Shi dai yasan cewa koda a hanya

ne ya taba ganin ta. Anashi ganin Hafsat ta san

mutuncin kanta shiyasa take wanan dabi‘un. Acikin

masauki ya kasa zaune da tsaye, baisan meyasa ya

damu kanshi da dabi‘un hafsat ba, bai taba ganin mace

da ta burge shi irin ta. Yasan daga ganin halayenta za

asha wuya kafin a samu soyayyar ta, duk da bashi da

tabacin sonta yake ko burgeshi take. Ya dai san ko ma

dai menene ya damu da ita. Kafin kwana 3 ya damu da

son sanin wacece ita? Alwashi ya sha ma kansa ba zai

bar kano ba har sai yasamu cikaken labarinta, wanda

yasan gurin rahama ne kadai zai san haka, haka a rana

ta 4 ya kira sagir yace gashi nan zuwa, zaya ci dinner

tare dasu. Duk da tulin kayan da aka tara a gaban shi na

lashe-lashe da tande-tande, sam basu dameshi ba, ya

dubi sagir cikin hausarshi na fulanin yola ya ce, nikam ka

bani dama inyiwa amaryarka wasu tanbayoyi game da

kawarta nan sagir yace wace ba dai hafsatba? Bai san

da lilin fadiwar gaban da yaji ba, haka nan bai san

lokacin da kalma ta fito daga bakinshi ba, tana da miji

ko? Ya tsare sagir da idanun shi masu kama da na

mata.Sagir ya ce bata da miji, amma fandarrarun

halayenta ne zasu gundire ka, yace bana zaton haka,

yanzu dai nafi so ka min izinin zantawa da matarka,

yace to ya kirata tazo ta zauna tare da cewa ba dai har

ka gama cin abincin ba?Yace ai kafin abincin ya samu

shiga nikam sai naji batun kawarkinnan hafsa. Rahama

ta dubeshi da sauri tace me kake son sani game da ita?

Yace unguwarsu da kuma dan lbr ta haka rahama tace

unguwarmu daya, sannan ita daliba ce a Poly yanzu haka

tana HND dinta ne. Iyayanta fa mutanen kirki ne?

Rahama ta danyi din sanan tace eh yace ta taba aure

ne? Kuma shadad dan tane? Nan take zufa ta karyo

mata, amma bata da amsar da ta wuce eh ya jijiga kai,

dama nayi zaton danta ne duk da batayi kama dashi ba

sun rabu da mijinta ne ko ya rasu ne? Nanma tace eh,

yace Allah sarki inaga shiyasa bata son hulda da maza,

dama ance mace in mujinta ya rasu kafin ta manta da

wuya. Iyayan ta din sunan layinku? Rahama tace eh, a a

karatu tazo suna kaduna. Gurin aikinmu daya ne super

market ne, yace to zan iya samun number dinta?

Rahama tace wai gaskiya yallabai sai dai kayi hakuri, in

na baka number ta zai iya zama sanadin rabuwar mu

kwata-kwata. Ya dan yi shuru yana nazari, Rahama tace

duk yanda kake tunanin hafsat ta wuce nan. Yace amma

ina zaton bakinki naji yana fadin tana da saukin kai da

dadin zama, kuma bata da fada? Rahma tace gurinmu

mata ba, amma game da maza sam bata da sauki, ta

tsani namiji ta kijinin ace anason ta sanan bata son

taimako daga namiji, ko wannen abu 3nnan ba taso.

Yace to me tafi so? Rahama tace abinda tafi so shine

kada kashiga harkarta, in kuma kashiga kayi tsananin

dace ta kula ka to kada ka tam bayeta ko wace irin

tanbaya, sannan kada kace kana sonta, ban san me

zakayi ba ta saki jiki da kai ba, don naga maza da yawa

wanda suka sota amma dole suka hakura rashin sakin

fuskarta yasa maza suna tsoranta. Da zaka hakura da ya

fi maka lada don ko taji hau shin abinda MC yace mata a

gurin bikinmu inda yace ku miji da mata ne. Abubakar

yace niko sai naso ace gaske naji dadi maganarsa.

Rahama ba zan iya hakura da hafsat ba don ina jin wani

abu game da ita wanda ban taba jinshi a wata yarinya ba

ina zaton shine so. Su Rahma suka sa dariya sagir ya

nisa yace lalle sonka din nan ya iya jan rigima ya fada

inda zaku sha wahala Abubakar yace sona yayi daidai

don yasan bama ra‘ayin mata marasa aji wadanda ke bin

maza da kansu suce suna so zanje in gwada sa‘a ta

kafin na bar kano zanga yada zamuyi. Sukace Allah ya

taimaka yace kasan ban sami daurin aure ba so bansan

gidansu rahama ba bare insan nasu hafsa din. Yace bari

inje in nuna maka daga nesa suka fita suna dariya ba

tare da yace komai ba shi tuni ya manta da menene a

gabanshi ko da sagir ya nuna mashi sai yace ba yanzu

zanje ba sai gobe da safe.

Ni kam tuna ranar da muka dawo daga bikin rahama

kulin shadad bashi da magana sai ta uncle dinshi tun ina

jin haushin shi ina mai fada har na dawo lallashinsa,

saboda har lokacin yana fama da zazzabi nakan

lallabashi da cewa kayi hakuri zai zo ya daukeka

ranar cikin dare har da cewa to anty kirashi a waya nace

to ka bari sai da safe yanzu yayi bacci, cikin kwana ukun

nan da kyar na samu ya manta da maganar uncle sai

jifa-jifa. Da safe yana sanye da kayan makaranta ni kuma

nayi shirin gurin aiki. Yau bani da lecture da safe don

haka gurin aiki zanje dama ka‘idar da manaja ya bani

kenan dan a daidaitanmu yana jira, shadad ya fita da

gudu ni kuma na kule dakin na fita. Ina rufe gida naji

muryar shadad yana cewa anty ga unclena anty na wai

wayo baya na datse kwado, ilai kuwa yana tsaye jikin

wata yar kyakyawar motar blue kiran kanfanin (toyota)

sanye da t-shirt da wando jeans baki, riga baka da ratsin

ja. Ta kalmin kafarshi baki ne sauciki. Na dauke fuskata

daga kalonshi bacin nayi fuskar shanu shadad wanda

tuni ya daneshi, murna yake yana cewa unclue kazone?

Da ma anty tace indaina kuka zakazo, takaici ya kamani.

Shi kuma sai ya dubeni anty antashi lfy? Ba tare da na

kaleshi ba nace kalau na daga labuln dan a daidaita na

shige. Sai naji yana cema dan a dai daitan, ungo nan

malam kaje sai bayan kwana 2 ka dawo tun da nazo ni

zan rinka kaisu kafin in tafi. Ya mika mushi yan dubu

dubu sababi fil guda 3 ya amsa yana cewa na gode

yalabai to sai zuwa yau she zan dawo yace nan da

kwana hudu haka nace sannu da karfin hali menene

gamina da kai? Da har zakaso ka min iko? Bai ce kala ba

ya juya. Na cema dan a daidaita sahu muje na leka

nacewa shadad zo mutafi ko nayi tafiyata. Mutumin ya

kaleni shima fuska a kame ki fito muje ban san sanda

nace to ubana! Sai kazo ka jani ya kara matsowa saitin

dan a daidaita yace ka sauketa katafi abinka. Sai kawai

mai a daidaita yace kiyi hakuri yar uwata, ki sauka ban

tankashi ba bankuma sauka ba,gani nayi zamuyi latti

nace yanxu kai malam haka zamuyi da kai? Duk tsawon

lokacin da muka dauka yau kace bazaka kaini ba? Yace

to Alhaji ne yace ki sauka ai, kuma ni bansan

dangantakarku ba kada in shiga hurumin da banawa ba.

Nace to bawata dan gantaka a tsakanin mu, asalima ni

ban sanshi ba da muna da alaka da baka gan shi ba ko

sau daya? Yace ki sauka mana nasan duk yanda akayi

kunsan juna. Ganin zai bata min lokaci sai na sauka na

dauki jakata nace shadad ya wuce muje, a mota yasaka

shi amma ya tada mota sukayi gaba. Na tare mai mashi

muna ciniki yazo yace mai mashi tafi abinka, in ka

dauketa zaka gamu da hukunci... kafin ya rufe baki yaja

mashin ya kara gaba. Na kaleshi nace me kake nufi

dani? Yace gurin aiki zan kaiki kawai,nace banaso dan

Allah kai mayene? Yace a'a ni ba maye bane, to bin me

kake min? Nifa ba yar iska bace. Yace nasani ai, to dan

Allah kafita hanyata, in kanawa darajar mahaifinka. Yace

don girman Allah ki shiga motar nan mu tafi, kada

shadad yayi latti, sannan inaso ki bani lokaci nazo mu

dan tautauna, nace bani da lokacin da zan iya baka, ka

fita harkata please, nacigaba da tafiya. Ranar dai a kasa

na tafi gurin aiki, shikuma sukayi wani guri shida shadad,

nasan sai dai suyi tambaya amma shadad ba zai iya

gane makarantar ba, ganin nakusa bansha wahalar hawa

abin hawa ba na karasa, takwas ta gota ina shiga ishak

yace yau bamakaranta kenan? Nace eh, gashi ma nayi

latti, musa yace manaja kuwa yazo yananan ya zagaya

ciki nasan sai yayi maki surutu, nace uhum sai dai yayi

tunda dai latti na riga nayi shi.Ina zama yana isowa, ban

ko kalleshi ba na jawo takarda dake kan teburina zan

fara duba abubuwan da suka fita da safen nan, sai ya

ce, "Kin san zaki zo da safe me yasa zakiyi latti?" Na ce,

"Abin hawa ne ban samu ba." Ya ce, "Amma ai ba'a

wahalar mai ko?" Na ce, "Kamar yaya?" Ya ce,

"Ballantana ki ce ana wuyar abin hawa." Na ce, "Akwai

abin hawa mana." Ya ce, "Baki da kudi ne?" A kagare na

ce, "Ina da shi." Ya ce, "Ok kin soma gajiya da aikin

kenan?" Na san shi sarai zai iya cewa ya koreni, kuma

dai Allah ya sani da aikin na dogara, don haka nace,

"Tunda ba halina bane lattin amin uzuri." Ishak yace ayi

mata hakuri Sir. Ya ce, "Kune kuka iya bada hakuri ita

bata iya ba ko? To ba zan mata uzuri ba, sai dai in

taimaka mata." Cikin sauri na ce, "Bana son taimakon

kowa sai na Allah, nace dai amin azuri." Ya ce, "To ki je

gida ki huta na sati 2 don ki koyi yadda zaki dinga zuwa

aiki." Muryarshi muka ji ya ce, "Uzuri za'a yi mata

manaja." Ya dubeni har na mike, "Koma ki zauna.

Manaja akwai uzuri a rayuwa, ko tana latti?" Ya ce, "A'a

ranka ya dade bata dai da mutuncine, in banda rainin

hankali tana fada min akwai abin hawa kuma tana da

kudi amma ta zo latti?" Ya ce, "Duk da haka ka mata

azuri da tace baka san dalilin ta ba, so tayi zamanta." Na

dube shi ina mamakin karfin halinsa, sai naga ya nufi

Ofishin manaja na ce kila ya san shi ne. Ni dai na zauna

na ci gaba da aikina. Ina jin Musa da Ishak suna mitar

rashin mutuncin shi.Abubakar ya dubi Manaja ya ce, "Ka

daina yiwa mutane haka, musamman na kasa da kai, a

rayuwa dole ne mutum ya dinga hakuri, yanzun kasan

uzurin da ya tare ta?" Manaja ya ce, "Yallabai yarinyar

nan bata da mutunci sam!" Ya ce, "Ko zan iya sanin

halayen ta marasa kyau?" Ya ce, "Na 1 bata da fara'a ga

kallon banza, kuma ta fi karfin kace zaka taimaka mata

sai ta hau bala'i, ina ce sakin fuska ma abu ne?" "Ni

kuma hakan ya birgeni." Abubakar ya katseshi, "Ban ga

laifinta ba, don ta kare mutuncin ta. Shi kenan sai ya

zama zubar da mutunci don bata saki fuska ba?" Manaja

ya yi 'yar dariya, "Yallabai yarinyar nan fa in ma sonta

kake ka hakura don ba zata baka hadin kai ba, in mata

kake so 'yan gayu isassu na debe kewa sai in kawo

maka su. A ina ka sauka?" Abubakar ya ce, "Na fada

maka ina son ta ne? Ko na fada maka ina son mata ne?

Inma matan nake so ai baka fini saninsu inda zan same

su ba, ina maka nasiha ne ka daina wulakanta na kasa

da kai, in dai suna yin abinda ya dace." Ya ce, "To zan

kula Yallabai -ya ci gaba da cewa- Ya hajiya? Ai mun yi

waya da ita jiya tace matake fada min kana Kano zaka

shigo ka duba abubuwan dake tafiya." Abubakar ya ce,

"Kwarai kuwa, bari in duba takardun. Fito min da su." Ya

jima sannan ya kammala ya fito, Manaja yana biye da

shi ya tsaya kusa da ni, "Ki yi hakuri kin ji ko?" Sannan

ya fita.Ni kam ban ko kallesu ba. Tunanina 1 ina ya kai

min yarona?

Lokacin tashina nayi na nufi Makarantar su Shadad na

dauke shi muka nufi gida. Tun akan hanya ya isheni da

labarin Uncle, Anty Uncle ya sai min ice-cream ya kai

min da muka yi break da su sweat, kuma ya tambayi

Auntynmu wai ina karatu? Ta ce mishi inayi sosai,

kuma ana lura dani wurin yin home work, yana ta jin

dadi. Na yi tsaki tare da cewa, "Yi min shiru." Da dare

ina Sallar Isha'i naji bugun gida, sai da na idar sannan

na nufi zauren nace wanene? Ba'ayi magana ba har

zan juya aka sake bugawa nace wanene wai? Yace

Abubakar ne. Na gane muryarshi amma sai nace, "Wa

kake nema?" Ya ce, "Shadad." Na yi shiru ina nazari,

hausawa sunce mai Da wawa, inna bar wannan

mutumin zaya fake da dana ya cutar da ni, gara in

masa rashin mutunci ko ya fita daga harkata. Na bude

kofar sannan na dogare bakin kofar, "Kai Malam! Ka

fita idona, ina ganin kimarka bana son ta kaimu ga

rabuwa fata-fata ni da kai, ina nufin in zabga maks

rashin mutunci, ka ja tsumman rayuwarka ka yi gaba,

ka fita harkar yarona, anzo za'a fake da yaro a cuceni."

Na ja tsaki tare da maida kofar garam na barshi tsaye

da leda shake da kaya.

Daga ranar ban kuma ganinshi ba, hakan ya min dadi

don haka na godewa Allah. Sai dai damuna da Shadad

keyi na kiran Uncle har da kuka. Kwana 8 bayan haka

ina ta kici-kicin girkin rana, yau lahadi sai da yamma

zan fita aiki. Tuwon shinkafa miyar alayyahu nake son

mana na gama kwashe tuwon cikin leda na zuba a kula

na samu Shadad yana home-work na ce, "Yauwa ka

zauna zanje kasuwa in dawo." Daman nakan barshi. Ya

ce, "To Anty." Ya tashi ya dauko kujerar da yake

takawa yasa sakata ta ciki.

Na nufi kasuwar don ba nisa sosai. Ban fi minti 30 ba

na dawo, sai dai me? Kofar gidan a bude, haka na nufin

Shadad ya cire sakata, a hanzarce na shiga. Takardun

shi suna gurin, takalminshi suna gurin. Kaf babu inda

ban dyba ba cikin gidan amma ban ganshi ba, da

hanzari na nufi makota duk da na san baya zuwa,,,,,

Me ke shirin faruwa da nine?

End of 1


Zaharaddeen Shomar

whatsapp  08168575100



Post a Comment

0 Comments