SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 13*
Fauzeeya tana fitowa daga wanka ta shafa lotions d'inta ajiki masu k'amshi sannan ta ciro doguwarta bak'a mai adon flowers red ajikinta ta sanya, ta fesa turare mai k'amshi ta murza d'aurin d'an kwali mai ma'ana jawo k'ofar d'akinta tayi ta koma parlour ta zauna jugum ita kad'ai.
Bata jima da zama ba saiga sallamarsu Sameer sun fito daga gidan iyayen Nazifa driver akasa ya kawosu, jin motsinsu yasa ta d'ago kanta idanunta suka fad'a cikin nasu ai kuwa nan da nan ta sakar musu murmushi su kuma suka rugo da gudu sukayo wurinta, suna isowa suka fad'a jikinta ta k'ank'amesu cikin farin ciki tace"iyeehhh yaran hajiya sannunku da zuwa ya kuka barosu?"
Sameer dayake ya fi Sameera wayo yace"lafiya k'alau suke Aunty sunce agaisheku".
"muna amsawa mi aka ciyo acan da ba'a kawo mana tsaraba ba?".
Sameera ta shagwab'e fuskarta cikin b'atanci tace"munzo miki da tsaraba Aunty ga jikkar can abakin k'ofar parlour".
Fauzeeya ta kalli bakin k'ofar parlourn ta hango babbar jikka alokacin ne ta jaye jikinta anasu tace"bari in d'auko jikkar to".
Sukace"to Aunty".
Tashi tsaye tayi ta d'auko jikkar ta aje agabansu sannan ta zauna tana k'are musu kallo cikin so da k'aunarsu tace"kuna jin yunwa ne?".
Sameer yace"saida muka ci abinci gidan hajiya sannan muka tafo nan".
"lallai 'yan gatan hajiya kuke shiyasa idan kukaje can kuke k'ara k'yawo da k'iba"..
Sameera ta shagwab'e fuskarta cikin sagarci yayinda Sameer ya kalli Fauzeeya yace"eh haka ne".
Yana rufe bakinsa saiga Yaseer ya shigo cikin parlourn ahanzarce saboda ya manta da wasu takardu masu muhimmanci, ganinsa yasa sukayi masa sannu da zuwa ya amsa musu cikin sakin fuska yace"a'aaaa jikokinsu hajiya ne yaushe kika dawo?".
Sameera tace"yanzun nan muka dawo dad ".
"yasu hajiya ina fatar suna cikin k'oshin lafiya?".
"k'alau suke sunce agaisheku".Inji Sameer.
"muna amsawa".
Ya juya ya kalli fuskar Fauzeeya da murmushi k'unshe afuskarsa yace"my Fauzee ba ko magana".
Cikin kunya tace"ba haka bane yah Yaseer naga kana magana da yara shiyasa nayi shiru har ku k'arasa maganarku".
"OK na fahimta bari in d'auko takardun dana manta".
"ba damuwa yaya".
Yaseer ya shige cikin d'akinsa yana shiga ya nufi wurin da yake aje takardu cikin drower ya d'auko ya fito, suna zaune Fauzeeya ta kallesu tace"ina zuwa bari in raka babanku".
"to Aunty".Sukace atare.
Yaseer yana gaba tana biye dashi abayansa har suka iso parking lot ya jingina jikinsa ga mota yayi tsaye, yayinda Fauzeeya ta duk'ar da kanta cikin kunya tana murmushin dake k'ayatar da fuskarta.
Yaseer sai tsurawa k'yak'k'yawar fuskarta idanu yakeyi yana murmushi yayinda wani irin sinadarin k'auna da soyayyarta yabi jini da magudanar jikinta, tabbas yasan soyayya gamon jini ce kuma samun abokiyar rayuwa ta gari dace ne jifanta kawai yakeyi da kallon so yace"my Fauzee iyayena sunje gidanku an bani ke saboda haka ki gayamin irin kayayyakin da kike buk'ata cikin lefenki".
Fauzeeya ta d'ago kanta ta kallesa cikin shauk'in k'auna tace"haba yaya har sai ka tambayeni irin kayayyakin da nake so duk abinda ya sawwak'a ka siyamin zanyi godiya da kasancewa cikin farin ciki, saboda haka kada ka takurawa rayuwarka yaya kayi abinda zakaji sauk'i ta b'angarena babu matsala wlh".
Hak'ik'a tun daga kalamanta Yaseer ya tabbatar yayi dace da mace ta gari wani irin shauk'i da guguwar sonta ne ke fisgarsa alokacin ne yaji aduniyar so bazai iya rayuwa idan babu ita ba, kallon cikin k'wayar idanunta yayi yana hango gaskiyar abinda ta fad'a cikin taushin murya yace"hmmm my Fauzee kenan bazaki fad'i abinda kike so ba?".
Langwab'e kanta tayi cikin marairaice fuska tace"ba haka nake nufi ba ka fahimceni yayana atsakaninmu babu cuta bale wahalarwa ka saka azuciyarka zan zamo maka farin cikin rayuwa zan baka ingantacciyar rayuwar dad'i na har abada".
Tabbas kalamanta sunyi matuk'ar tasiri azuciyarsa domin yaji farin ciki har cikin jijiyoyin jikinsa da k'wak'walwarsa cikin murna yace"na fahimceki masoyiyata nima da yardar Allah zan rik'eki amana da zuciya d'aya zan baki tsantsar kulawa da soyayyar gaskiya nizan wuce office".
"saika dawo ubangiji ya kaika lafiya ya dawo dakai cikin k'oshin lafiya".
"Amin amin my Fauzee".Yana k'arasa maganarsa ya shige cikin motarsa ya danna horn maigadi ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan da gudu, Fauzeeya tana tsaye tana kallo har maigadi ya rufe get d'in ta juya ta koma cikin gidan ta iskosu Sameer sai wasa sukeyi suna dariye dariye suna ganin Fauzeeya suka natsu, saboda fad'a takeyi musu idan suna yin muguwar wasa isowa wurinsu tayi ta zauna suka bud'e sabon shafi na fira.
**********************
Rai ab'ace Nazifa ta iso cikin shagonsu tana kumbura fuskarta kamar kumurci kallo d'aya zakayi mata ka gano tana cikin b'acin rai zuciyarta cunkushe da bak'in ciki, Safiya tana lura da chanjin yanayin Nazifa damuwa da takaici ne ta hango k'arara cikin k'wayar idanunta asanadiyyar haka ne yasa ta iso wurinta ta zauna gab da gab tace"k'awata lafiya mi yake damunki naga rayuwarki ab'ace?".
Nazifa tayi rau rau da idanu kwallar zallar takaici ne ya cicciko cikin k'wayar idanunta wani irin abu ta had'iye mai matuk'ar d'aci azuciyarta tace"kedai bari Safiya ina cikin damuwa saboda jiya naga abinda ya bani mamaki! ".
Safiya tayi wuru wuru da idanunta mamaki ne kwance afuskarta tace"ke kuwa Nazifa mi nene ya baki mamaki haka har ya zamo silar sanyaki cikin damuwa?".
Nazifa ta musk'uta cikin yanayin damuwa da rashin dad'in zuciya tace"jiya ina zaune cikin parlour kinsan ban shigo shago ba saboda banida lafiya alokacin ne Fauzeeya take mopping d'in floor aparlour, saiga sallamar Yaseer ya shigo cikin parlourn ahanzarce idanunsa baiyi tozali dani ba sai Fauzeeya! Kawai ganin nayi sunata fira suna kallon fuskar juna ni kuma alokacin bansan lokacin dana kwasheta da mari biyu........................ ".Labarin duk abinda ya faru ta kwashe ta gayawa Safiya tana kai k'arshen maganarta taja bakinta tayi shiru cikin d'acin rai.
Shiru ne ya biyo baya sannan Safiya ta saukar da numfashi tace"agaskiya wannan maganar taki abar lura da tunani ce Nazifa anyah mijinki bai fad'a tarkon soyayyar Fauzeeya ba anya babu wata a k'asa!?".
Rassssss! Gaban Nazifa ya fad'i hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne suka bayyana k'arara afuskarta tabbas maganar Safiya ta soki k'ahon zuciyarta cikin damuwa tace"haba Safiya ya zakiyimin wannan muguwar fata bayan kinsan babu abinda na tsana aduniya daya wuce kishiya! Agaskiya Yaseer bazai tab'a iya soyayya da Fauzeeya kidai sake wani tunani ".Safiya ta yamutsa fuskarta tace"bana miki fatar sharri arayuwarki Nazifa ya kamata kije kiyi tunani da nazari idan kika kad'aice".
"wane irin tunani zanyi Safiya? Bayan nasan babu wata soyayya atsakaninsu".
Safiya ta bintsire baki tace"kedai har yanzu baki fahimci wa nene namiji ba? Bakisan cewa namiji mugu ne duk yadda kike ganinsa shiru shiru yasan inda zai soka miki kibiya azuciya kedai kije ki tuntub'esa kiji daga bakinsa idan soyayya yakeyi da ita! "..
Nazifa ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarta tace"to ba matsala zan tambayesa inji ko sonta yakeyi inyaso daga baya in sanardake duk abinda ake ciki".
"hakan ya kamata kice tun farko k'awata saboda haka ki natsu kinsan yadda zaki tunkaresa da maganar kinji ".
"zanyi iyakar bakin k'ok'arina Safiya".
"ba komai ubangiji yasa mu dace baki d'ayanmu".
"Amin amin Aminiyata".
____________________
Da tsakar dare Yaseer yana k'unshe cikin d'akinsa yana aiki cikin laptop d'insa cikin natsuwa, saiga sallamar Nazifa ta shigo cikin tsakiyar room d'in yah Yaseer ya amsa mata batare daya d'ago kansa ba, Nazifa ta k'araso wurinsa ta zauna gefen gado tace"daddyn Sameer inason mu tattauna muhimmiyar magana dakai".
Yaseer ya mayarda kallonsa kacokam wurin Nazifa yace"ina saurarenki".
Huci ta sauke mai tattare da bak'in ciki da takaicin rayuwa tace"mike tsakaninka da Fauzeeya? ".
Cikin firgici da matuk'ar mamakin maganarta yace"kamar ya kenan ban fahimci inda kika dosa ba?".
Nazifa ta musk'uta cikin yanayin damuwa tace"ina nufin miye alak'arka da Fauzeeya nace!? ".
Yaseer ya kalli cikin k'wayar idanunta ya hango kishinsa da tsantsar tashin hankali ne kwance afuskarta cikin mutuwar jiki yace"to tunda kin fahimci akwai alak'a mai k'arfi atsakaninmu to aurenta zanyi nan da watanni uku masu zuwa insha Allahu! ".
Afirgice Nazifa ta d'ago kanta idanunta suka fad'a cikin na Yaseer jikinta yana mazari da k'yarrrma! Wani irin d'aci da zogi zuciyarta keyi bak'in ciki da tsantsar kishinsa ne shimfid'e afuskarta cikin takaici tace"mi!Aurenta fa kace zakayi anya kasan abinda kake fad'a!? ".
"tabbas aurenta zanyi nasan abinda nake fad'a ina cikin hayyacina".
Kwallar zallar takaici ne suka gangaro afuskarta yayinda jijiyoyin kanta suka tashi tsaye rud'u rud'u cikin zafin rai tace"wannan auren bazai tab'a yiyuwa ba muddin muna tareda juna yanzu Yaseer ka rasa abinda zaka sakamin dashi sai kishiya! Aganinka wannan shine adalci da soyayyar gaskiya!? ".
"kina ji kina gani za'a d'aure aurena da Fauzeeya babu abinda zaki iyayi ai kin riga kinyi *SAKACI* arayuwarki Nazifa! ".
Nazifa ta kallesa cikin tsantsar tsana da zafin kishi tace"hmmmm tabbas zan nuna maka ainahin kalata ina tabbatar maka idan ka auri Fauzeeya ka haddasawa kanka masifa da fitinar rayuwa ka rungumi tashin hankali da bak'in cikin rayuwa! Babu kai babu kwanciyar hankali har abada za kaga mummunan abinda zai biyo baya! ".
"babu abinda zai biyo baya sai Alkhairi Nazifa duk abinda zakiyi kije kiyi ubangiji yafi ki".
"lallai kanada ja kenan ".
"Eh mana inada ja aure ne babu fashi sainayi ko zaki mutu saina aureta! ".
Hawaye suna sintiri afuskarta cikin zafin rai da tafasar zuciya tace"mu zuba mu gani nida ku acikin gidan nan shege ya fasa! ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta ta shek'a da gudu cikin d'akinta ta fad'a saman gado ta saki rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, bak'in ciki da tsantsar takaici ne kwance cikin k'wayar idanunta wani irin abu ke yawo cikin jikinta da magudanar jijiyoyinta, ji takeyi duniyar gaba d'ayanta tayi mata bak'ik'irin ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya gwamma mutuwarta akan irin wannan halin data tsinci kanta, hawaye ne yab'e yab'e saman fuskarta alokacin ne tururin zafi da k'una zuciyarta keyi risgar kukanta takeyi jikinta sai k'yarrrma da kad'uwa yakeyi, zafin kishi ne ke yawo cikin jini da gangar jikinta hak'ik'a ta k'ara tabbatarwa ayau namiji k'anin ajali ne ............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 14*
Kwance Nazifa tayi tanata rusar kukan bak'in ciki da tsantsar takaicin kishiya saida taci kukanta ta k'oshi sannan ta jawo blanket ta rufe jikinta, yadda taga safe haka taga rana saboda barci yak'i zuwar mata akan tsantsar damuwa da bak'in cikin rayuwa juye juye ta kamayi saman gadon akan tsantsar takaici da k'unar zuciya, dak'yar da sud'in goshi ta samu barci yayi awon gaba da ita wurin goshin sallar asuba.
Saida gari ya waye tayi sallar asuba sannan ta fad'a cikin bathroom tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar lace d'inta, idanunta duk sun kumbura akan kuka da matsananciyar damuwa kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin matsanancin hali da tafasar zuciya, wayarta ta jawo ta danna nombar mahaifiyarta ta shiga d'id'id'id'id'i hajiya Ramlat ganin ana kiranta yasa tayi receiving call tace"hello baby Nazifa ya kike?".
Jin muryar mahaifiyarta yasa Nazifa ta rushe da kuka tace"ina fa lafiya Ummu!".
Jin Nazifa tana kuka yasa hankalin mahaifiyarta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke cikin mutuwar jiki tace"kiyi hak'uri ki daina kuka miyake faruwa!? ".
Nazifa shasshekar kukanta kawai kakeji yana tashi cikin sark'ewar halshe tace"na shiga uku na lalace Ummu Yaseer ya cuceni ya gama da rayuwata! ".
Gaban hajiya Ramlat ya buga da k'arfi rasssss tsantsar fargaba da tsagwaron tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarta yayinda bak'in ciki yake kwaranya cikin jini da gangar jikinta dak'yar ta bud'i baki tace"ki daure ki daina kuka Nazifa yanzu dai abinda za'ayi kizo gida ki sameni domin insan abinda Yaseer d'in yayi miki! ".
"to.. to.. Ummu ganinan tafe".K'it ta katse wayar bak'in ciki shimfid'e afuskarta sake gyara fuskarta tayi da powder sannan ta jawo mayafi da handbag d'inta ta rataya a kafad'arta, jawo k'ofar room d'in tayi ta sanya key ta kulle zuciyarta sai zogi da rad'ad'i takeyi mata.
Aparlour ta hango Fauzeeya tana kai da kawo tsaye tayi wuri d'aya ta katsa mata tsawa cikin hargowa tace"keeee!Don ubanki zo nan! ".
Daga sama Fauzeeya taji maganarta ai kuwa cikin fargaba da tsantsar tsoro jikinta yana k'yarrrma ta iso wurin Nazifa ta gurfana cikin sanyin jiki tace"gani Aunt........ ".
Kafin ta k'arasa maganarta Nazifa ta d'auketa da gigitattun maruka hud'u masu zafi da rad'ad'i wanda asanadiyyar haka saida ta wuntsila k'asa ta fad'i d'immmmm hankalinta da natsuwarta suka fice na wucin gadi, hawaye masu zafi suka wanke mata fuska.
Nazifa ta kalleta cikin tsana da tafasar zuciya tsantsar kishin mijinta da takaici ne kwance cikin k'wayar idanunta wani irin abu mai d'aci sai yawo yakeyi mata cikin jini cikin tsagwaron k'iyayya ta nunata da yatsa tace"'yar iska butulu yanzu ki rasa sakayyar da zakiyimin saina auren mijina! In raineki tun kina 'yar shekara goma har zuwa girmanki yanzu kinga kinyi nono kin isa ci shine zakizo ki lik'ewa Yaseer yaji babu wadda yakeso sai ke,alal hak'ik'a kin d'auko ruwan dafa kanki kin jawa shegiyar kakarki da ubanki Labaran masifa arayuwa! Hmmmmmm na fahimci shegen kwad'ayi da buri ne zaisa ki auri mijina ".
Fauzeeya tana dafe da kuncinta yayinda take zubar da hawayen takaici da b'acin rai cikin matuk'ar tsoron Nazifa tace"Aunty kiyi hak'uri wallahi ba laifina bane laifin zuciya ne da batada k'ashi sai tsoka".
Nazifa ta girgiza jikinta tareda karkad'a kanta tace"zakiyi nadamar soyayya da mijina arayuwarki saina haddasa miki k'unci da fitina arayuwa! Bazan rok'eki akan kada ki auresa ba ki auresa d'in zakiga abinda zai biyo baya! ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta fuuuuu ahasale ta nufi parking lot.
Fauzeeya ta mik'e tsaye tana hawayen takaici wani irin abu ke mata yawo cikin jikinta zuciyarta cunkushe da bak'in ciki da tsantsar tashin hankali tace"tafd'ijam inada aiki babba agabana ni Fauzeeya ji yadda take ta marina adalilin zan auri mijinta! Duk abinda zatayi taje tayi aure kam kamar gobe ne saina auri Yaseer ko mutuwa zatayi! ".K'arasa maganarta keda wuya ta fad'a cikin kitchen ta k'arasa girka jallof rice taji kayan had'i.
*********************
Nazifa ce ta parker motarta aparking lot na gidan iyayenta ta sanya key ta kulle motar sannan ta juya ta shiga cikin gidan ba kowa aparlour sai k'arar TV, direct room d'in mahaifiyarta ta nufa ta iskota zaune saman gado Nazifa ta isa wurinta da sauri ta fad'a ajikinta ta rungumeta tana rusar kukan bak'in ciki da kishin mijinta, hajiya Ramlat ta k'ara k'ank'ameta ajikinta tana bubbuga bayanta alamar lallashinta ta dad'e tana kuka mahaifiyarta tana lallashinta dak'yar ta tsagaita dayin kukanta tace"ki daure 'yata ki gayamin dalilin dayasa kike zubar da kwalla haka kamar wadda akace iyayenta sun mutu?".
Nazifa tasa hannu ta share hawayenta tsab cikin zafi da zogin zuciya tace"Ummu Yaseer ne zaiyimin kishiya kuma ya rasa wacce zai aura sai Fauzeeya yarinyar da kika d'aukomin domin ta dingayimin ayyukan gida! ".
Hajiya Ramlat ta d'ago kanta da sauri cikin firgici tace"what!Anyah da gaske kike fad'a kuwa?".
"wallahi Ummu gaskiya nake gaya miki Yaseer aure zai k'ara kuma da Fauzeeya! ".
Hankalin mahaifiyarta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke gabanta ya bada dummmmm cikin kad'uwa da razana tace"lallai Yaseer ya cika butulu wato ya rasa sakayyar dazai miki sai kishiya shiyasa akwanakin baya ya mareki ya koroki gida! To bazata sab'u ba wannan auren bazai tab'a yiyuwa ba saboda haka kishakuruminki zanje in samu tsohuwar munafukar kakar Fauzeeya inci mata mutunci, sannan yanzu ne ya kamata kina komawa gida ki koreta tabar miki gidan mijinki tunda ba gidan ubanta bane! ".
"haka za'ayi Ummu ina komawa gidan zanyi mata korar kare sannan kuma idan zakije gidan munafukar kakarta nima zamuje nida Safiya muyi mata cin mutunci fiyeda tunaninta, saita gwammaci da bata d'auki jikanyarta taba Yaseer ba zata gane shayi ma ruwa ne".
"haka ya dace kiyi karki kuskura ki ragawa duk wani danginta saboda laifinta ya shafi kowa babu sani babu sabo! ".Cewar hajiya Ramlat cikeda son fitina da tsananin bak'in ciki arayuwa.
Nazifa ta musk'uta cikin yanayin d'acin rai tace"ai babu ragowa tsakanina da ita har abada tunda har ta shigo cikin gonata ta gama yawo! ".
Hajiya Ramlat tace"tashi kije shagonki ki cigaba da harakokin gabanki har hajiya Sadiyan sainaje na gaya mata bak'ak'en maganganu saboda nasan duk ita ke d'aurewa Yaseer gindi ya k'ara aure! ".
Nazifa ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tace"wallahi duk itace saboda na fahimci matar nan ba sona take ba".
"karki damu zan d'auki kwakkwaran mataki akansu! ".Inji hajiya Ramlat.
"to Ummu nina wuce sai munyi waya".Cewar Nazifa alokacin ne ta mik'e tsaye rataye da handbag d'inta a kafad'arta cikin matsananciyar damuwa da tarin takaici.
"OK ba matsala ubangiji ya kiyaye hanya".
"Amin ya rabbi Ummuna".Ta sanya kai tayi ficewarta daga cikin gidan direct parking lot ta nufa tana isa ta shige cikin motarta ta danna horn maigadi ya wangale mata get d'in ta fice daga cikin gidan da sauri ta nufi hanyar zuwa shagonsu..
_Hmmmm nidai Mugirat ina gefe ina mamakin k'arfin hali irin nasu hajiya Ramlat, miyasa tun farko ta b'ata tarbiyar Nazifa ya zamana bata ganin mutunci da kimar mijinta bayan tasan cewa aljannarta tana k'ark'ashin tafin k'afafunsa idan bai k'ara aure ba zina takeson yayi ohon mata._🤔
____________________
Nazifa tana isa tsakiyar filin shagon ta hango Safiya zaune tana lissafa kud'in da sukayi ciniki yau da sauri ta isa wurinta ta zauna, batace mata komai ba saida ta bari ta k'arasa lissafin da takeyi sannan Safiya ta d'ago idanunta ta kalleta tace"Nazifa sai yanzu kika shigo yau fa kinyi late ashago".
Nazifa ta saukar da numfashin d'aci da tafasar zuciya bak'in ciki da tsantsar takaici ne cunkushe cikin zuciyarta tace"kedai bari ina cikin tsaka mai wuya da matsanancin hali wlh yanzu ma saida na biya gidanmu na sanar mata halin da nake ciki!".
Safiya tayi tagumi da ajiyar zuciya tace"kardai kicemin hasashena ya zama gaske Nazifa".
Nazifa ta gyara zamanta cikin suyar zuciya k'asan zuciyarta sai ciwo da k'una yakeyi mata cikin takaici Tace"hasashenki ya zama gaske Safiya Yaseer aure zai k'ara kuma da Fauzeeya !".
Maganar ta razana jikin Safiya sosai cikin rawa da mazarin jiki tace"wace Fauzeeyar zai aura!? ".
Nazifa tayi mata wani irin kallo mai tattare da bak'in ciki tace"wace Fauzeeyar kika sani bayan wadda takeyimin ayyukan gida da kula da yarana! ".
Hak'ik'a maganar ta soki k'ahon zuciyar Safiya cikin fargaba da tsantsar tashin hankali dayake kwance k'arara afuskarta tace"ina lillahi wa inna ilaihirraji'una! Lallai na tabbata ayau namiji bayada tabbas yanzu Yaseer ya rasa wacce yakeso kaf garin nan sai Fauzeeya yarinyar da kika raineta ahannunki tun kina amarya tanada shekara goma ko sha d'aya, ya kamata ki tashi tsaye mu d'auki mummunan mataki akanta saboda ta gane cewa ba'a tab'a cin amanarki azauna lafiya! ".
"kema kenan kina goyon bayana akowane lokaci ".
"ina goyon bayanki d'ari bisa d'ari k'awata ai mun riga mun zama d'aya abokin kuka shi ake gayawa mutuwa! ".
"zansa mana ranar da zamuje gidan kakarta da ubanta muci musu mutunci har sai sunyi matuk'ar nadamar bada Fauzeeya ga mijina ".
"OK duk ranar da kika sanya ki gayamin muje muyi musu wankin babban bargo ".
"zan sanardake Safiya".
Cigaba da firarsu sukayi cikin natsuwa da damuwa cunkushe cikin zuciyarsu, maganar auren Yaseer kawai suke maimaitawa suna zagin Fauzeeya da iyayenta yafi gaban misali.
*BAYAN KWANA BIYU*
Aranar aka tura Yaseer a ma'aikatarsu cikin wad'anda zasuje wani aiki ajahar Kataina har na tsawon sati guda, aranar dak'yar suka rabu shida Fauzeeya saboda yarinyar tana matuk'ar sonsa da nuna masa tsantsar soyayyar gaskiya, ab'angaren Nazifa bata wani damu ba akan zaiyi tafiya saboda dama tun farko akwai abinda ta k'ulla azuciyarta, tana ganin ya fice daga cikin gidan ta fashe da dariyar mugunta saida tayi dariyar mai isarta sannan ta tsagaita dayin dariyar ta tunkari room d'in Fauzeeya gadan gadan babu annuri afuskarta cikin zafin rai da k'unar zuciya .
Fauzeeya tana zaune saman gado itadasu Sameer su suna wasa ita tana karatun novel cikin phone d'inta mai suna *JINKIRIN ALKHAIRI* kwatsam! Taji motsin tafiyar mutum ya shigo cikin d'akinta ta d'ago kanta da sauri sai taga Nazifa ce cikin tsinkewar zuciya tace"Aunty kece wani aiki zanyi miki ne!? ".Gabanta yana dukan uku uku saboda kallo d'aya tayi mata ta gane ba alkhairi bane ya kawota d'akinta.
Nazifa ta girgiza kanta alamar a'a sannan ta mayar da kallon gefensu Sameer tace"ku tashi ku fita ku bamu wuri zamuyi magana da ita! ".Sameer ya langwab'e kansa yace"mom wasa fa mukeyi ".
Daka musu rikitacciyar tsawa da hargowa tayi tace"nace ku fice daga cikin d'akin nan! ".Kafin ta rufe bakinta suka mimmik'e tsaye suka shek'a da gudu saboda sun matuk'ar firgita da razana akan tsawar da tayi musu.
Suna ficewa ta mayar da kallonta ga Fauzeeya wadda ta gama firgita da lamarin Nazifa cikinta sai k'ugin tsoro yakeyi k'ululululu zad tsoro! Nazifa tayi mata walak'antaccen kallo tace"keeee don kutumar uwarki kina jin dad'in zaki auri mijina ya ciki kamar yadda yake cina kin matsu ayi aure ya zura miki jijiyarsa cikin k'ugunki! To ayau zaki gane ke k'aramar shed'aniya ce saina babance miki tsakanin aya da tsakuwa! "..............😢
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 15*
Fauzeeya ta razana da firgicewa akan kalamanta tun anan ta fara zubar hawaye tana rok'on Nazifa cikin tsananin tsoro domin tasan ayau babu mai k'watarta ahannunta sai Allah, tana kuka cikin tsinkewar zuciya tace"dan girman Allah Aunty Nazifa kiyi hak'uri karki cutardani wallahi indai yah Yaseer ne na hak'ura da aurensa! ".Nazifa ta banka mata harara kamar idanunta zasu fad'o a k'asa tace"k'arya kikeyi bak'ar munafuka dama daga gani ya saba cinki idan bana nan shiyasa kika lik'e masa saboda kinsan dad'in maza".Sharri da k'azafin da tayi mata yayi matuk'ar cin mata rai da sanya bak'in ciki da tsantsar rad'ad'i azuciyarta amma saita daure tace"duk abinda zaki fad'a ki fad'a idan har zaisa kiji sanyi azuciyarki amma dan girman Allah kiyi hak'uri Aunty".
"yimin shiru idan kika k'ara kirana da Aunty saina tsinka miki mari! Da kin d'aukeni yayarki da bazakiyi gigin auren mijina amma dayake shaggun iyayenki kwad'ayayyu ne shiyasa zasu had'a aurenki da Yaseer domin ku samu abin duniya! ".
Fauzeeya ta girgiza kanta cikin yanayin fargaba tace"ba haka bane Aunt...........".Kasa hak'uri Nazifa tayi ta k'arasa maganarta ta rufe da shegen duka ko'ina ajikinta ji kakeyi dim dim dim dim, ai kuwa nan take Fauzeeya ta saki kuwwa da kururuwar neman agaji amma ina babu kowa cikin gidan daga ita sai Nazifa da yaranta!.
Cigaba da dukanta takeyi kamar ta samu jaka saida tayi mata lik'is da d'an banzan duka sannan ta tsaya tana mayarda numfashi da haki wuk'ar data b'oye cikin zanenta ta d'auko tace"yau cikin gidan nan saina nakkasaki inga ta yadda auren zai yiyu! Saina yanke miki nonuwa in tura wuk'a akasanki inga ta yadda zai aureki!".
Duk dayake Fauzeeya tana cikin matsanancin hali hakan baisa hankalinta yak'i tashi ba zuciyarta ta girgiza jikinta duk tsami da ciwo yakeyi mata, saboda ba k'arya ta daku sosai cikin kad'uwa ta gurfana ak'asa saman gwiyoyinta hawaye masu zafi sai shatata sukeyi saman fuskarta tace"karki nakkasani Aunty na tuba na bar miki mijinki bazan auresa ba!".
"bayan kinga mutuwa k'iri k'iri ba shiyasa kike cewa kin fasa aurensa to bazan tab'a yarda da maganarki ba, ayau saina cire miki nonuwa inga iyakar iskanci k'asanki kuma saina sa wuk'a na hudeshi ya zamo kamar na wadda maza suka cita! ".
Ganin tana rok'onta tana botsarewa yasa Fauzeeya ta tabbatar zata iya aikata abinda take fad'a tunanin yadda zata gudu takeyi, can taji Nazifa ta chapki nonuwanta wuk'a rik'e ahannunta Fauzeeya ta k'ara gigicewa da d'imaucewa tana kuka kokuwa ne ya kaure atsakaninsu ita Fauzeeya tana ceton ranta ita kuma Nazifa tana son yanke mata boob's!.
Cigaba da kokuwa sukayi kowaccesu tana son cimma burinta akan 'yar uwarta dayake k'arfinsu ba d'aya ba Nazifa ta sake jujuyata ta fyad'a atiles kaji gwammmm!Wani irin rikitaccen zafi da rad'ad'i ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta ai batasan lokacin da tayi k'ara tace"wayyo ni Allah Fauzeeya na shiga uku jama'a kuzo ku taimakeni zata kasheni akan toshewar basira da *KISHIN JAHILCI*!".
Shurinta ta dingayi da k'afafunta har saida ta fashe mata baki da jini fuskar Fauzeeya duk ta kumbura taji jajir saboda ta galabaita da shan matuk'ar wuya ahannun Nazifa, akwancen ma ta tunkarota da wuk'a tsirara ahannunta gadan gadan zata yanke mata boob's, Fauzeeya tana hankalceta da ita tana isowa zata aitawar da mugun nufinta Fauzeeya tasa k'afarta d'aya ta shureta ta fad'i k'asa kafi gwaffff! Wani irin zafi ya ziyarci sassan jikinta Fauzeeya tayi wuf cikin matuk'ar zafin nama ta fito daga cikin d'akin ta ranci na kare kamar zautatta, su Sameer suna zaune parlour tazo ta wuce ta gabansu suna cewa Aunty Aunty lafiya amma ina Fauzeeya tayi nisa batajin kira.
Haka ta isa wurin maigadi daga ita sai kayan jikinta babu takalmi bale d'an kwali baba maigadi yana ganin ta fito afirgice ya kalleta cikin razana yace"lafiya Fauzeeya mi akayi ne!?".
Fauzeeya sai numfashin wuya da haki takeyi dak'yar ta bud'i bakinta tace"ka taimakeni baba Aunty Nazifa zata kasheni! ".
Cikin kad'uwa da razana afuskar baba maigadi yace"mi kikayi mata ne da zata kasheki!? ".
"babu lokacin baka amsa kadai taimakeni wata rana zan gaya maka".
"to babu damuwa ".Baba maigadi ya shiga cikin d'akinsa ya d'auko wani zane mai kamada mayafi ya bata sannan ya ciro kud'i cikin aljihunsa d'ari biyar ya bata yace"ki rufe jikinki da wannan zane sannan kud'in ki tari mai keke napep ya kaiki gida"."To nagode sosai baba ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairi".Tana rufe bakinta ta fice daga cikin gidan da sauri domin kada Nazifa ta iskota ta halakata abanza akan bak'in kishi!.
Tana ficewarta baba maigadi ya zauna saman teburin da yake zaune cikin tausayin Fauzeeya, bada jimawa saiga Nazifa ta fito ayamutse tana neman Fauzeeya kanta ya kumbura a inda ya bugi k'asa k'arasowa tayi wurin maigadi tace"baba ina Fauzeeya? ".
"ke kuwa miyasa kike nemanta!? ".
Babu kunya bale tsoron Allah tace"sata tayimin! ".
Baba maigadi yayi saurin kallonta arazane domin ya gano gaskiyar abinda take fad'a k'wayar idanunta ya tsurawa kallo na tsawon lokaci yana karantar abinda yake cikinsu, hango rashin gaskiya yayi cikinsu sannan yaja numfashi yace"yanzun nan ta fice da gudu da farko inace ma ko maciji ta gani ta shek'o ashe sata tayi miki".Yace kamar ya yarda da zancenta.
Nazifa tayi k'yafci cikin tsananin takaici da rashin nasarar cika mugun nufinta akan Fauzeeya Tace"shikenan ta tsira yanzu amma gamona da nata wani karon ba k'yau saboda wallahi saita biyani kud'ina data sata! ".
"hak'uri zakiyi hajiya saboda Fauzeeya k'aramar yarinya ce bisa gareki".Inji baba maigadi.
Wani irin matsiyacin kallo tayi masa mai nuni da walak'anci tace"ba zanyi hak'uri ba ko zaka biyani kud'ina data sace ne sannan yanzu Fauzeeya data gama lalacewa atiti ita kake kira da yarinya, shin in tambayeka ko tare kuka had'a baki kaida ita kuka sacemin kud'i ko tana baka jikinta kana kwasar dad'inta ne shiyasa kakeson kareta?".
Dummmmm gaban baba maigadi ya buga da k'arfi kalamanta sun soki k'ahon zuciyarsa cikin jikinsa sai zafi yakeyi masa tun ranar da ubangiji ya haliccesa ba'a tab'a k'aga masa k'azafin da yayi masa ciwo irin wannan ba ,cikin matuk'ar b'acin rai da tafasar zuciya yace "dakata yarinya! Daga kawai na baki hak'uri kike neman ki k'agamin sharri da k'azafi ke wace irin zuciya ne dake da bakida tausayi bakisan darajar d'an Adam, ki kalleni da k'yau ahaife na haifeki da kike neman yimin rashin kunya! ".
Nazifa ta rik'e k'ugunta tana karkad'a jikinta cikin rashin tarbiya ta tofawa baba maigadi miyau afuskarsa tace"munafikin banza na k'aga maka sharri duk abinda zakayi kaje kayi kuma ubangiji yayimin tsari da matsiyaci kamarka ya haifeni wanda bayada komai sai tulin talauci da tsiya! "..
Baba maigadi ya shafi miyan data shafa masa afuskarsa yace cikin tsanar walak'anci "keee yanzu ni kike tofawa miyau afuskata saboda bakida albarka!? ".
Nazifa tayi clapping d'in hannunta 👏 tayi dariyar rainin hankali tace"an tofa maka miyau Barau kaine d'ebabben albarka wanda uwarsa ta mutu da takaicinsa".
Jin ta ambaci sunansa yasa baba maigadi yayi murmushin takaici ya dubeta yace"hmmmm hak'ik'a mahaifiyarki bata baki tarbiyar k'warai ubangiji ya tsine miki albarka yarinya! ".Nazifa tayi charap tace"yadai tsine maka albarka halan kai mahaifina ne da zaka tsine mini albarka dan kutumar ubanka idan Yaseer ya dawo saina sa ya sallameka kabar gidan nan tunda ba gidan ubanka bane! ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta fuuuuu ta nufi cikin parlourn akumbure.
Kallon bayanta baba maigadi ya dingayi yana cewa "hmmmmmm wannan yarinyar iyayenta sunyi matuk'ar hasara domin basu bata tarbiyar kirki ba ".Yana k'arasa maganarsa yaja bakinsa ya tsuke yana jinjinawa rashin mutuncin Nazifa da rashin kunyarta, sak'e sak'e ya dingayi azuciyarsa cikin matuk'ar b'acin rai da zafin cin mutunci. ...
____________________
Fauzeeya tana fita daga cikin gidan Yaseer ta samu mai keke napep ya kaita har cikin unguwarsu a k'ofar gidan kakarta Iya Kulu mai tsamiya ya sauketa ta biyasa kud'insa ta juya ta shige cikin gidan yayinda mai keke napep d'in ya tadda napep d'insa ya k'ara gaba.
Fauzeeya tana isa tsakiyar filin gidan ta hango Iya Kulu zaune saman tabarma tana tsintar k'asa cikin shinkafa sallamar Fauzeeya ne yasa ta d'ago kanta tareda amsa mata sallamar, ganin jikanyarta ayamutse yasa hankalin Iya Kulu ya tashi zuciyarta ta girgiza cikin matuk'ar fad'uwar gaba tace"Fauzeeya lafiya kika zo haka kamar wadda aka koro? Ji yadda kika shigo tamkar mahaukaciya! ".Fauzeeya ta isowa wurinta cikin firgici da d'imuwa tace"Iya Aunty Nazifa ce ta koroni da wuk'a ahannunta tsirara! ".
Iya Kulu ta firfito da idanunta waje cikin matuk'ar tsoro da d'imaucewa akan kalamanta tace" wuk'a ta koroki da ita halan ta haukace ne!?".
Fauzeeya tayi murmushin takaici tace"bata duk haukace ba Iya tsabar hauka ne da bak'in kishi harda cewa takeyi saita yanke mini boob's taga yadda Yaseer zai aureni ahaka ".Iya Kulu tayi wuru wuru da idanunta mamaki da Al'ajabi ne kwance afuskarta k'arara cikin tsoro tace"amma agaskiya Nazifa ta haukace batada hankali! Wato so tayi ta kashemin ke tun kafin lokacinki yayi hmmmm ta Allah ba tata ba muguwar aniyarta ta bita !".
"Iya taji labarin aurena da za'ayi da Yaseer shine tace saita nakkasani! ".
Iya Kulu tayi tagumi cikin zullumi tace"afff ai wannan zancen banza halan saboda ita kad'ai aka halacci Yaseer ai namiji mijin mace hud'u ne saboda haka saidai tayi hak'uri ta rungumi k'addara aure kam babu fashi sai an d'aurashi! ".Fauzeeya ta jaye mayafin da baba maigadi ya bata ta nunnunawa Iya Kulu jikinta tace "duba ki gani Iya mugun kashi ta bani harda shurina kamar ta samu jaka ".Iya Kulu ta gyad'a kanta cikin matuk'ar b'acin rai tace"eh tabbas so tayi ta kashemin ke hak'ik'a Nazifa ta fifita daga cikin hayyacinta! "."Idan kinma ga yadda mukayi kokuwa da ita saina baki tausayi saboda nasha matuk'ar wuya ahannunta jikina duk tsami da ciwo yakeyi............
0 Comments