SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 4*
Fauzeeya tana fitowa daga cikin d'akin Yaseer ta nufi d'akin dayake mallakinta ta jawo mayafi ta yafa a kafad'arta, fitowa tayi ta wuce ta gabansu Sameer ta nufi hanyar fita daga cikin gidan tana isa waje ta tari mai keke napep tareda biyansa kud'insa inda zai kaita tayi masa kwatance,har suka iso unguwar da kakar Fauzeeya ta wurin uba suna isa bakin k'ofar gidan mai keke napep ya tsaya, Fauzeeya ta fito daga cikin napep d'in ta shige cikin gidan mai keke napep ya tadda napep d'insa ya k'ara gaba.
Fauzeeya tana isa tsakiyar gidan ta hango Iya Kulu zaune saman tabarma tana dama fura taji nono sai girgiza kanta takeyi,Fauzeeya ta iso wurinta da sallama abakinta ta zauna gab da kakarta Iya Kulu ta dubeta cikin mamakin dawowarta gida yanzu tace"Fauzeeya 'yar kaka ya akayi ne kika dawo gida yanzu ko wani abu ne yake faruwa?".
Fauzeeya ta shagwab'e fuskarta tareda bintsire baki tace"babu komai Iya kawai dai nazo ne domin in gana da k'awata Adama".
Iya Kulu ta rik'e baki tace"hmmm iyayin banza gareki Fauzeeya yanzu akan kinason ganin Adama ne shiyasa kikazo ganinta".
Fauzeeya ta zumb'ura baki tace"eh mana ke Iya kin cika ganin nisan da unguwar da muke zaune".
Iya Kulu ta harareta da wasa tace"unguwar da kike akwai nisa mana yanzu dai ya mutanen gidanku?".
Fauzeeya tace"lafiya k'alau suke".
Iya Kulu tana kammala dama furar ta d'ibawa Fauzeeya nata akofi tace"gashinan kisha idan kika gama shan furar sai kije gidansu".
Fauzeeya ta d'auki kofin furar ta kafa kai ta shanye furar sannan ta ciro kud'i abakin gefen zanenta ta mik'awa Iya Kulu dubu uku tace"Iya ga kud'i nan ki samu na cin goro".
Iya Kulu ta amshi kud'in cikin tsantsar farin ciki tace"kayyyy nagode sosai Allah ubangiji yayi miki albarka ya jik'an mahaifiyarki".
Fauzeeya taji dad'in addu'arta sosai har cikin zuciyarta da sassan jikinta tace"amin ya rabbi Iya nizan wuce zuwa gidansu Adama".
Iya Kulu tace"to..to.. d'iyar albarka idan kin koma gida ki gaida ubangidanki Yaseer".
Fauzeeya tayi murmushin dake tattare da bak'in ciki tace"zaiji da yardar Allah".Tana k'arasa maganarta taja k'afafunta ta nufi hanyar zuwa gidansu Adama.
**********************
Tana isa tsakiyar gidan ta hango Inna Amo mahaifiyar Adama da Adama zaune saman tabarma suna fisgar sure suna sanyawa cikin roba, Fauzeeya ta isowa wurinsu ta duk'a har k'asa ta gaida Inna Amo Inna ta amsa mata fuskarta asake tace"ya Iyarki Fauzeeya?".
Cikin kunya tace"lafiya k'alau take Inna".
Fauzeeya ta mik'e tsaye yayinda Adama ta tashi tsaye tana kallon fuskar Fauzeeya tace"mu shiga cikin d'aki Fauzeeya zaman gidan Yaseer ya amsheki fa".
Fauzeeya tabi bayanta suka shige cikin d'aki suka zazzauna saman gadon Inna Amo, alokacin ne Fauzeeya ta kalleta cikin fara'a tace"ban gane zama gidan Yaseer ba ya amsheni bayan kinsan ina cikin matsananciyar soyayyarsa?".
Adama ta saukar da numfashi tace"ina nufin kinyi k'iba kin k'ara k'yawo kina bani mamaki Fauzeeya taya kina zaune gidansa amma kin kasa jawo ra'ayinsa ya soki wannan ai rashin dabara ne?".
"bazaki gane ba Adama Yaseer yanada tsattsauran ra'ayi ba kowace mace bace ke burgesa kedai ki bani shawarar yadda zanyi in sace zuciyarsa ya soni".
Adama ta saukar da numfashi tace"kina abu kamar ba wayayya ba kinsan matarsa bata yawan zama gidan mijinta, kamata yayi ki dinga yawan kwalliya da shisshige masa ajiki ta haka ne zai soki Fauzeeya,amma idan kikasa wasa har abada bazai tab'a sonki ba kindaiji na gaya miki!".
Fauzeeya ta rausayar da kanta cikin sanyin jiki tace"naji zan gwada shawarar da kika bani Adama".
Adama tace"ya kamata kam ki tashi tsaye idan ba haka kina ji kina gani ki rasa Yaseer har abada!".
"ki daina yimin mugun fata Adama domin idan na rasa Yaseer rayuwata zata iya tarwatsewa in lalace! Bakisan yadda nakeji ba azuciyata ba soyayyarsa tayimin mugun kamu cikin rayuwata".
Adama ta dafa kafad'arta cikin tausayawa k'awarta tace"kibi komai asannu Fauzeeya sannan ki rage sakawa zuciyarki damuwa duk abinda ubangiji ya k'addaro ga bawa babu makawa saiya sameshi".
Cikin mutuwar jiki da tsantsar damuwa dayake shimfid'e afuskarta Fauzeeya tace"haka ne Adama nizan wuce gida yanzu na baro yaransa su kad'ai".
Adama yace"to yayi ki gaida uwargidanki Nazifa".
"hmmmmmm naji amma bazan iya gaya mata ba saboda matar nan sai ahankali".
"to Fauzeeya ki cigaba da hak'uri ubangiji yana tareda masu hak'uri".
"a'a babu damuwa sai wata rana".
"sai wata rana d'in".
Adama ta rakata har bakin k'ofar gida sukayi tsaye suna firarsu cikin jin dad'i,bada jimawa ba saiga mai keke napep ya gifto ta gabansu Adama tayi saurin tsayar dashi ya parker napep d'insa, Fauzeeya tayiwa Adama sallama ta shige cikin napep d'in ta zauna mai keke napep ya tambayeta inda zai kaita tayi masa kwatance unguwar da gidan Yaseer yake, tadda napep d'in yayi suka fice daga cikin unguwar yayinda Adama ta juya ta koma cikin gidansu.
Sunyi tafiya mai nisa har suka iso bakin get d'in gidan Yaseer ya ajeta kud'i ta ciro daga cikin k'aramar handbag d'inta ta biyasa, ya amshi kud'insa ya k'ara gaba Fauzeeya ta shige cikin gidan murmushi k'unshe afuskarta.
Tana isa tsakiyar parlourn ta iskosu Sameer kwance saman carpet suna minshari Fauzeeya ta k'araso wurinsu ta zauna tareda gyara musu kwanciya,can dai ta mike tsaye ta fad'a cikin d'akinta domin ta watsa ruwa taji sanyi ajikinta ta dad'e tana wanka sannan ta fito daga cikin bathroom d'in tana goge jikinta da k'aramin towel, direct wurin mirror ta nufa ta shafa mayuka masu k'amshi atamfarta ta ciro ta sanya d'inkin doguwar riga ta sanya ajikinta yayi mata d'ass kamar tare aka haliccesu, turare ta fesa sannan ta dawo wurin gadonta ta fara barci tana lumshe idanu cikin sanyin jiki.
**********************
Yaseer ya tashi tsaye ya shiga cikin bathroom yayi wanka tareda d'auro alwala, yana fitowa daga cikin toilet ya shafa manshafi mai k'amshi shaddarsa ya ciro light blue taji aiki ya sanya ajikinsa, turarensa masu shegen k'amshi ya feshe jikinsa dashi ya saka hula da agogo ya jawo k'ofar d'akinsa ya fito.
Yaseer ya iso tsakiyar parlourn zai wuce kenan idanunsa suka hango 'ya'yansa kwance saman carpet suna barci, wani irin d'aci da zogi zuciyarsa keyi ga bak'in ciki k'unshe cikin ransa asanadiyyar rashin dace da mace ta gari, wani irin abu ke yawan taso masa a k'irji yana damunsa, dak'yar ya kauda kansa daga barin kallon fuskar 'ya'yansa ya juya ya fice daga cikin gidan direct parking lot ya nufa, isarsa parking lot keda wuya ya bud'e k'ofar motarsa ya shiga ya zauna danna horn yayi da k'arfi maigadi y wangale masa get ya fice daga cikin gidan da sauri.
**********************
Nazifa bata dawo cikin gidan ba sai kusan sallar magarib alokacin har Fauzeeya ta kammala girka abincin dare tuntuni,Nazifa ta shige cikin d'akinta ta watsa ruwa tareda d'auro alwala tana fitowa daga cikin toilet d'in, ta shimfid'a sallaya ta fara ramakon sallolin da ake binta harta kammala.
Tana zaune saman sallaya tana addu'o'i saiga Yaseer ya shigo cikin d'akinta sanye da jalabiya black colour, wurinta ya k'araso ya zauna yana jiran ta shafa addu'ar afuskarta tana shafawa ta juyo ta kallesa batare data ce uffan ba, Yaseer ya dubeta cikin rashin walwala yace"Nazifa".
"na'am"Ta fad'a batare data dubeshi ba.
Yaseer yayi huci mai k'unshe da takaici da bak'in cikin rayuwa kallo d'aya zakayi masa ka gano baya cikin kwanciyar hankali yace"yanzu irin wannan rayuwar da kika d'aurawa kanki kina ganin haka yafi dacewa awurinki miyasa bazaki bani dama ba mu shimfid'a tsabtatacciyar rayuwar aurenmu? ".
Cikin haushin kalamansa Nazifa ta b'ata fuskarta tace"yanzu kuma mi nayi maka Yaseer waikai har yanzu ka kasa fahimtata?".
"kece kika kasa fahimtata Nazifa saboda bak'ya son gaskiya duk abinda nake nufi kinfi kowa sani!".Yace ahasale.
Nazifa ta daga masa hannu cikin rashin girmamawa tace"ya isa Yaseer! Yawan complain d'inka ya fara isata saikace gareka aka fara auren mace 'yar business, idan banyi business ba kallonka kakeson in zauna inyi bafa zaka tab'a samun yadda kakeso ba har abada kaji dai na gaya maka gaskiyar zance! ".
Yaseer yaji matuk'ar zafin kalamanta har cikin jini da tsoka cikin zugi da tafasar zuciya yace"lallai na tabbatar da bakida tarbiya Nazifa hmmm hak'ik'a nayi nadamar aurenki arayuwata saboda kwata kwata wannan rayuwar da kika sawa gaba bamai b'ullewa bace ".Nazifa tayi masa kallo mai tattare da raini tace"nima nayi nadamar aurenka Yaseer domin ka cika yawan damuwa! ".
Yaseer ya jijjiga kansa cikin dacin rai yace"zaki gane bakida wayo da sannu zaki fahimci abinda kikeyi bayada k'yawo sannan duk abinda kikeyi ki cigaba duniya ce ta ishi kowa riga da wando! ".Yana rufe bakinsa yaja k'afafunsa yabar d'akin Nazifa zuciyarsa sai tururin zafi da k'una takeyi.
Yana ficewa daga cikin d'akin Nazifa tayi tagumi cikin zafin rai da rad'ad'i azuciya can ta nisa tace ohhh ni Nazifa naga ta kaina wannan auren ya fara isata rayuwar Yaseer tanada matsala mutum sai kace mai zuciyar kafirai ".
Tana rufe bakinta ta d'auko wayarta tayi dialling nombar Safiya ta shiga tana ringing d'id'id'id'i, tana shiga Safiya tayi receiving call d'inta tace"hello Nazifa lafiya zaki kirani cikin dare ?".
"hmmm ina fa lafiya Safiya Yaseer duk ya takurawa rayuwata ya hanamin rawa gaban hantsi nifa na fara gajiya da halayyarsa! ".
Safiya tayi doguwar ajiyar zuciya cikin lallashi da tattausan lafazi tace"ki daina cewa kin gaji da halinsa Nazifa rayuwar aure da kike ganinta sai hak'uri nima fa Haidar yana yimin irin abubuwan da mijinki yakeyi miki, hak'uri kawai nakeyi ina b'oye wasu abubuwa cikin zuciyata saboda haka ki share da maganarsa ki cigaba da sha'anin gabanki".
"to shikenan zan sharesa d'in".
"hakan ya kamata sai da safe".
"OK good night ".Tana k'arasa maganarta ta katse phone d'in tareda ajeta saman kan gado blanket ta jawo ta lullub'e jikinta dashi ta lumshe idanunta saboda tayi saurin tashi da safe zuwa wurin business.
B'angaren Yaseer yana komawa cikin room d'insa zazzafan hawaye suka dinga sintiri saman fuskarsa yayinda zuciyarsa sai zogi da k'una takeyi masa akan yalwataccen gadonsa yayi masauki ya kwanta, alal hak'ik'a da yasan haka Nazifa zatayi masa dabai aureta ba tabbas baiyi dace da mace ta gari ba.............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 5*
Dak'yar Yaseer ya samu b'arawon barci yayi awon gaba dashi zuciyarsa cunkushe da tarin damuwa da bak'in ciki mara misaltuwa, harda mafarkin ya auri Fauzeeya yayi yana auratayya da ita ta haifa masa k'yak'k'yawan yara, cikin tsakar dare ya farka afirgice jikinsa sai tsiyayar zufa yakeyi yana karanto addu'o'i cikin ransa domin ya kad'u da firgita akan mafarkin da yayi! Ya jima zaune yana kwararo addu'o'in neman tsari daga shaid'an, sannan ya shafe addu'ar ajikinsa ya kwanta cikeda damuwa da rashin dad'in zuciya, haka ya dinga juye juye ya kasa barci har aka sallar asuba ya mik'e zumbur ya fad'a cikin bathroom ya watsa ruwa ajikinsa tareda d'auro alwala, yana fitowa ya zura jalabiyarsa ya nufi hanyar zuwa masallacin dake cikin unguwar.
A room d'in Nazifa itama ta tashi daga barci ta d'auro alwala tareda kabbarta sallah, haka room d'in dasu Fauzeeya suke barci itama ta falka daga barci ta d'auro alwala ta fito daga cikin toilet, shimfid'a sallaya ta kabbarta sallah raka'a biyu tana sallame sallah ta zauna tana kwararo addu'o'i, bayan ta shafa addu'ar afuskarta ta mike tsaye tareda linke sallaya ta adanata saman drower, cire hijabinta tayi ta aza saman gadon direct ta nufi cikin kitchen ta had'a musu breakfast ruwan zafi ta juye aplask ta rufe, sannan ta kwashi kayayyakin ta nufi wurin dinning table ta jajjerasu samansa zad sha'awa da tsari.
Tana gama jerawa ta koma cikin d'akinta domin tayiwasu Sameer wanka tana wurinsu ta sungumi baby Sameera tayi cikin toilet da ita, ta jima tana wanke mata jiki lungu da sak'o sannan ta d'auraye mata jiki da ruwan k'warai ta rungumota ajikinta tayo cikin d'aki da ita, tana isowa cikin d'akin ta kwantar da ita saman gado tareda rufe mata jiki da bargo, Sameer taja hannunsa ta shiga cikin toilet dashi tayi masa wanka fess ta fito dashi daga cikin toilet.
Suna isa tsakiyar room d'in ta zauna gefen gado tareda shafawa Sameer manshafi sai b'ata fuska yakeyi, Fauzeeya dai bata ce masa k'ala ba ta cigaba da abinda takeyi tana kammala shafe masa jiki ta ciro tufafinsa 'yan kanti masu k'yau ta sanya masa, sannan ta d'auko Sameera ta rungumeta saman k'afafunta tana shafa mata manshafi ita kuma sai shagwab'a takeyi mata Fauzeeya tana biye mata, kayan kwalliya ta jawo tayi mata had'ad'd'iyar kwalliya mai masifar k'yawo sannan ta ciro mata riga da sicket masu shegen k'yawo da tsada ta sanya mata.
K'aramin madubi Fauzeeya ta d'auko ta saita adaidai saitin fuskar Sameera tana murmushinta mai k'yawo tace"kin gani ko kinyi k'yawo babyna".
Sameera ta kalli fuskarta dake cikin madubi ta fashe da dariyar murna tace"gaskiya Aunty Fauzee kin iya kwalliya na gani nayi k'yawo sosai"..
Fauzeeya tayi dariyar dake bayyana hak'ora tace"da gaske na iya kwalliya babyna?".
Sameera ta sake washe k'ananan hak'oranta masu haske da k'yawo tace"eh mana kin iya sosai Aunty".Tana rufe bakinta sukaji Sameer yaja tsoki mtssss ya zumb'ura baki yace"Aunty ji yadda kike wani kod'ata kina k'arawa kanta zama k'atoto ina Sameera taga wani k'yawo idan ma ba fari dasai bola!".
Fauzeeya ta k'yalk'yale da dariyar mugunta domin zancen Sameer ya matuk'ar sanyata dariya can ta tsagaita tace"kai Sameer miye abin kishi saboda nace baby Sameera tayi k'yawo?".
Sameera tayi charap tace"dallah rabudashi Aunty duk bak'in ciki ne da jiyewa".
Sameer ya hasala yana huci kamar zaki yace"rufemin bakinki ko yanzu inyi miki shegen duka mara jin magana kawai ".
Fauzeeya ta jawo hannunsa alamar lallashinsa tace"a'a kada ka kuskura ka dukarmin yarinya idan ba haka ba zamuyi fad'a ni dakai".
Sameera ta lahe ajikin Fauzeeya kamar mage tace"barshi Aunty saina had'ashi da mom in gaya mata zai dukeni".
"ya isa dai yanzu dai na shiryaku muje parlour muyi breakfast kowa ya tsaya ga kansa".
"to Auntynmu".Suka fad'a kusan atare da juna.
Jan hannunsu tayi suka nufi cikin parlourn.
Yayinda acan dinning table tun d'azu Yaseer ya fito shida Nazeefa suna breakfast babu wanda yayiwa wani magana, kowanensu zuciyarsa k'unshe take da haushin abokin zamansa musamman Yaseer dayake ganin tana tauye masa hak'k'insa,ita kuma anata wautar so yake ya takurawa rayuwarta ya hana mata neman na kanta, sun jima zaune suna kintsa cikinsu suna sak'e sak'e cikin zuciyarsu daga k'arshe Yaseer ne ya fara tashi saboda idan ya cigaba da kallonta zai iya haifar masa da babbar matsala domin ba k'aramin haushinta yakeji ba, direct parking lot ya nufa ya shiga cikin motarsa maigadi ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan.
Nazifa tana jin k'arar motarsa alamar ya fice daga cikin gidan tayi k'yafci tace"aikin banza ji yadda yake wani d'auremin fuska yana b'ata rai ni ina ruwana idan ma domin nice ka tabbata cikin b'acin rai ".K'arasa maganarta keda wuya ta mik'e tsaye ta shige cikin d'akinta ta shirya sharp sharp cikin shaddarta ash colour, handbag d'inta ta rataya a kafad'arta hannunta rike da key d'in motarta ta nufi parking lot, kodasu Fauzeeya suka iso dinning table suka zazzauna basu isko kowa ba serving dinsu tayi itama ta d'ebi nata tana ci kad'an kad'an ayangace dayake Fauzeeya akwaita da son yanga da kuri,ci sukeyi cikin natsuwa har suka kammala ta kwashe kayayyakin da suka b'ata ta wankesu tasss ta adanasu awurin daya kamata.
Fitowa tayi daga kitchen d'in ta iskosu Sameer har sun dawo cikin parlourn suna buga game murmushi ta sakar musu ta samu wuri ta zauna saman cushion, su kuwa game d'insu suka cigaba da bugawa suna k'yalk'yalar dariyar farin ciki kallo d'aya zakayi musu ka gane suna cikin kwanciyar hankali da natsuwa itadai sai kallonsu takeyi tana murmushinta mai k'ayatar da fuskarta.
____________________
Yaseer ne na hango cikin wani irin katafaren office had'ad'd'e zaune saman kujera gabansa teburi ne babba cikeda takardu da computer, laptop, shiru yayi cikin matsananciyar damuwa tun d'azu daya shigo cikin office d'in ya kasa yin aikin k'warai, haushi da tsagwaron takaici ne shimfid'e saman fuskarsa kallo d'aya zakayi masa ka gane kwata kwata baya cikin hayyacinsa, tagumi yayi biro ne rik'e ahannunsa idanunsa sun kad'a sunyi jajir akan tsantsar damuwa, ya fad'a duniyar tunani saiga sallamar Abduljalal ya bud'e k'ofar ya shigo yana isowa wurinsa yaja kujera ya zauna, ya jima yana nazarin abokinsa sannan ya tab'ashi yayi firgigit ya dawo cikin hayyacinsa, kallon tausayawa Abduljalal yayi masa yace"haba Yaseer ka rage yawan sanyawa kanka damuwa idan ba haka ba wani ciwo zai iya kamaka akan mace zaka zauna kana neman kashe kanka abanza, ai wannan rashin tunani ne ya kamata kayi abinda ya dace!".
Yaseer ya d'ago fuskarsa ya kallesa cikin damuwa yace"bazaka tab'a gane irin yadda nakeji ba Abduljalal ina buk'atar mace wallahi nakai mak'ura wurin buk'atuwa saboda kwata kwata rabon da Nazifa ta bani hak'k'ina na auratayya harna manta kullum sai jamin rai takeyi".
Abduljalal yayi matuk'ar kad'uwa da razana akan maganarsa cikin matuk'ar mamaki yace"abinda ka fad'a gaskiya ne Yaseer?".
"kana mamakin maganata ne ka daina mamakin zancena domin Nazifa ta wuce tunaninka".
Abduljalal yayi shiru na tsawon lokaci can yace"lallai kana cikin tsaka mai wuya Yaseer amma gaskiya ya kamata ka d'auki kwakkwaran mataki akan Nazifa idan ba haka zata sakaka cikin wani irin mugun yanayi".
"nina rasa wani irin mataki ya kamata in d'auka akanta saboda ta riga tayi nisan kiwo batajin kira".
"kadaiyi tunanin irin matakin daya kamata ka d'auka abokina nizan koma office d'ina na barka lafiya".
"OK ba damuwa friend".
Abduljalal ya fice daga cikin office d'in ya nufi nasa yayinda yabar Yaseer zaune yana zullumi da tunanin mafitar daya kamata ya d'auka,dak'yar ya tattaro dauriya ya sanya azuciyarsa ya fara wasu ayyukan domin kada suyi masa yawa.
**********************
Nazifa da Safiya na hango zaune cikin hamshak'in shagonsu suna siye da sayarwa zaune suke saman kujerar roba, mutane sai sintirin zuwa sukeyi sayayya ashagon yayinda sunada yaro mai suna Anwar shike kula da duka shagon da abinda yake cikinsa.
Suna zaune suna firarsu cikin fara'a da kwanciyar hankali Nazifa ta dubi fuskar Safiya tace"hmmm lamarin Yaseer sai ahankali yanzu haka fushi yakeyi dani baya yimin magana ".Safiya ta yamutsa fuskarta tareda karkace baki tace"aikin banza yiwa karen mak'wabta wanka ki k'yaleshi kada ki kula dashi idan ya gaji dayin fushin da kansa zai sauko yayi miki magana".
Nazifa ta yamutsa fuskarta tace"ai bana kulasa Safiya saboda abin nasa yayi nisa nidai iyakata idanu dashi".
"gara da kika fita batunsa saboda bak'in ciki yakeson yayi miki domin kada ki samu kud'i ".
"ai tuni na harbo jirginsa besty na fahimci hassada da bak'in ciki yakeson yimin saboda bayason cigabana".
Safiya ta rik'e baki tace"mazan yanzu da kike gani sai abarsu saboda babu abinda suka iya sai yiwa matansu hassada da kushe saboda basuson matansu su zamo wani abu arayuwata, shiyasa kikaga ko Haidar yayimin fad'a da guna guni nake fita batunsa domin ni arayuwata na tsani namijin da bayason cigaban matarsa".
Nazifa tayi ajiyar zuciya cikin damuwa tace"Yaseer kam yana daga cikin irin wad'annan mazan shiyasa bana bashi fuska domin kada ya kawomin raini da ikon banza"."Ai yanzu mu mata saimun tashi tsaye mu k'waci 'yancin kanmu idan ba haka ba kina ji kina gani zaki zama baiwar k'aton banza! "."Abin dai ba'a cewa komai ubangiji ya karemu daga sharrin mazaje 'yan bak'in ciki"."Amin amin aminiyata mukam yin business yanzu muka fara saidai zuciyar mutum ta buga ya mutu bamuda hasara sai riba! "..............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 6*
Nazifa tayi murmushi tace"kayyy Safiya bakida sauk'i cikin lamarinki muddin zaki samu kud'i gaskiyar magana rayuwarki tana burgeni".Safiya ta musk'uta cikin yanayin murna tace"hmmmm bana wasa muddin haraka idan ta kud'i ce saboda yanzu zamani ya riga ya waye namiji da mace kowa na kansa yake nema"."Wannan maganar taki haka yake k'awata".
Cigaba firarsu sukeyi cikin kwanciyar hankali da natsuwa har zuwa wani lokaci mai tsawo, can da suka fara jin yunwa suka kira yaronsu Anwar suka bashi kud'i domin yayi musu take away na abinci, yana ficewa daga shagon yahau mashin d'insa ya nufi hanyar zuwa restaurant saboda ya siyo musu abincin, bai wani jima ba saigashi ya dawo rik'e da ledodi uku ahannunsa yana parker mashin d'in abakin shagon yadda zai iya hango mashin d'insa, ya iso wurinsu yaba kowaccesu leda d'ad'd'aya shi kuma ya d'auki d'aya ya kuma mazauninsa yana ba cikinsa hak'k'insa su Safiya ma tuni sun fara cin abincin atsanake.
____________________
Yaseer yana tashi daga office d'insa bai zarce ko'ina ba sai babban asibitin da abokinsa yake aiki wato doctor Zaharadden, office d'insa ya shiga kai tsaye da sallama abakinsa ya shiga doctor Zaharadden dake zaune yana rubuce rubuce atakardu idanunsa sanye da farin glass, jin muryar Yaseer ne yasa ya d'ago fararen idanunsa suka fad'a cikin na Yaseer murmushi k'unshe a k'yak'k'yawar fuskarsa yace"a'aaaa ashe inada babban bak'o ayau".
Yaseer ya iso wurinsa yaja kujera ya zauna murmushin da baikai zuci ba yayi yace"nine bak'o doctor baka rabo da zolaya wlh".
Doctor Zaharadden ya kallesa cikin so da shak'uwa yace"hmm haka dai kace abokina ya madam da iyalinka? ".
"duk lafiya k'alau suke doctor nine dai banajin dad'in jikina shiyasa nace bari inzo ka dubani ko mi yake damuna".
Doctor Zaharadden ya langwab'e kansa cikin tausayawa yace"ayyah Yaseer ubangiji ya baka lafiya amma nasan rashin lafiyarka baya rasa nasaba da son buk'atuwa da mace, saboda idan baka manta akwanakin baya da kazo na bincikeka na gano sperm ya taru cikin mararka saboda baka samun yin sex da matarka".
Yaseer ya huci mai tattare da d'acin rai da bak'in ciki yace"maganarka gaskiya ne doctor Zaharadden nina rasa yadda zan b'ullowa al'amarin Nazifa wlh kwata kwata bana gabanta itadai babban burinta bai wuce ace ta samu kud'i ba".
Doctor Zaharadden ya cire glass d'in dake sanye afuskarsa ya girgiza kansa yace"wannan ba magana bace kace ka rasa yadda zaka b'ullowa al'amarin matarka na gaya maka tuntuni kaje ka sameta kuyi magana ta fahimtar juna ta yadda zata fahimceka, idan kuma tak'i baka goyon baya mafita mafi sauk'i agareka shine ka k'ara aure saboda ina tsoron kada afka tarkon shaid'an, saboda kaga idan bakada mai biya maka buk'ata to gaskiyar zance akwai babbar matsala Yaseer saboda komi ma zai iya faruwa dakai".
Yaseer ya jijjiga kansa alamar gamsuwa da maganarsa cikin matuk'ar haushi yace"na gamsu da bayaninka doctor yanzu dai rubutamin maganin dazan sha in rage abinda nakeji cikin marata".
Doctor Zaharadden yace"kaje kayi tunanin mafita abokina kada ka kashe kanka abanza ita mace babu ruwanta kana mutuwa zata sake sabon aure! ".Yana rufe bakinsa ya jawo wata farar takarda ya rubuta masa magungunan dazai siyo yasha wadanda ya tab'a rubuta masa, yana kammala rubutawa ya mik'a masa takardar ahannunsa.
Sannan ya k'ara da cewa"na rubuta maka magungunan da zaka siyo kasha amma dan girman Allah Yaseer ka nemi mafitar data dace banason kaje ka fad'a cikin wani irin mugun yanayi!".
"insha Allahu zanyi k'ok'arin ganin na kiyaye doctor nizan wuce zuwa gida".
"OK no problem ka gaidamin madam".
"zataji insha Allahu".Yana k'arasa maganarsa ya mik'e tsaye sukayi musabaha da juna sannan ya fice daga cikin office d'in doctor Zaharadden.
____________________
Yaseer yana fita daga office d'in doctor Zaharadden ya shiga cikin motarsa ya nufi hanyar komawa gida, yana tafiya ahankali cikin motarsa sai nazari da tunanin maganganun doctor Zaharadden yakeyi azuciyarsa ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa, ya rasa abinda yakeyi masa dad'i aduniya wani irin abu yakejin yana yawo cikin jini da sassan jikinsa, dak'yar ya kauda komai cikin zuciyarsa ya iso wurin mai saida kayan marmari irinsu lemu,ayaba,kankana,abarba,tuffa da dai sauran kayayyakin marmari yana zaune cikin motarsa ya kira mai saida kayan marmarin ya shek'o da gudu ya iso wurinsa yace"Alhaji mi kake buk'ata? ".
Yaseer ya sauke numfashin takaici yace"lemu,abarba,da kanka zaka bani na naira dubu".Ya zaro kud'i agaban aljihunsa yaba mai saida kayan marmarin.
Mai saida kayan marmari ya juya ya nufi wurin teburinsa ya sanya abubuwan da Yaseer ya lissafa masa cikin ledar ya kawo masa, godiya sosai Yaseer yayi masa ya bashi k'yautar dubu biyar ya amshe yanata godiya sannan ya koma bakin sana'arsa, kujerar da babu kowa Yaseer ya aje ledar anan sannan ya tadda motarsa ya nufi hanyar zuwa gidansa.
Acan gidan Yaseer kuwa tuni su Fauzeeya sun dawo daga school har tayiwasu Sameer wanka itama ta shirya cikin riga da sicket wad'anda suka bayyana surar jikinta, dayake Fauzeeya akwai surar jiki mai jan hankalin d'a namiji saboda duk dayake bata wuce shekara sha shidda ba amma akwaita da hives sannan gata da boob's manya manya, idan ta kasa k'ananan kaya har hangosu kakeyi tanada shape mai k'yau gaskiya domin duk inda ake bid'ar mace Fauzee ta wuce can, shiyasa alokutta da dama Yaseer yakeyi mata fad'an sanya k'ananan tufafi saboda ko manyan kaya ta saka sai anga tudun boob's d'inta.
Yanzu ma zaune suke saman cushion aparlour suna kallon tashar dad'in kowa saiga sallamar Yaseer ya shigo cikin tsakiyar parlourn Fauzeeya ta mik'e sannu ahankali ta amshi kayan dake hannunsa, tareda yi masa sannu fuskarsa ad'aure ya amsa mata bata wani damu da yadda ya murtuk'e fuskarsa ba ta juya ta nufi hanyar d'akinsa domin takai mishi briefcase d'insa, Yaseer ya zauna cikin parlourn yana jiran fitowarta domin bayason suna keb'ewa da ita gudun afkuwar mummunan k'addara, ya dad'e zaune baiga fitowarta ba gashi kuma ya gaji yana buk'atar wanka da hutu zumbur ya mik'e ahasale ya nufi hanyar d'akinsa.
Yana tura k'ofar d'akin ya shiga ya hango Fauzeeya tana k'ara gyara masa shimfid'a tareda fesa room freshner mai k'amshi, cikin matuk'ar takaici da b'acin rai ya kalleta yace"waike wace irin yarinya ce mai shegen taurin kunne! ".
Sai alokacin ne Fauzeeya taji muryar muradin zuciyarta juyo tayi ashagwab'e tana girgiza jikinta tareda karkad'a k'ugunta cikin kashe murya tace"haba yah Yaseer yanzu kuma mi nayi maka ne?Gyaran d'aki kawai nakeyi maka ba wani abu ba amma dan girman Allah kayi hak'uri".
Yaseer ya banka mata uwar harara cikin haushinta yace"ke dakata banason dogon surutu na gaya miki idan har ina buk'atar shiga d'akina ki daina shigowa tunda niba mijinki bane amma saboda taurin kunne irin naki kinyi biris da maganata, sannan kada ki k'ara saka k'ananan kaya acikin gidan nan ke ko manya ne ke dinga saka hijabi asamansu".
Fauzeeya tayi masa wani irin kallo mai tattare da so da tsantsar k'auna tace"naji bazan sake kaji nifa banason b'acin ranka yanzu dai abinda za'ayi kazo kayi wanka idan ka gama in baka abinci kaci".
Yaseer yayi tsaye sakatoto yana matuk'ar mamakin kalaman da suke fitowa daga bakinta domin ya firgita da kad'uwa akan yanayin maganarta, b'oye komai yayi cikin zuciyarsa yace mata"hmmm lallai yarinyar nan bakida hankali to fita ki bani wuri in cire tufafina inyi wanka".
Fauzeeya ta zumb'ura baki tace"kadai shiga ka fito ina jiranka ni babu inda zanje! ".
Yaseer ya hasala da suk'uwa iya suk'uwa yayi mata mugun kallo ya d'auko belt d'insa saman drower yace"idan baki ficemin a d'aki ba wallahi zanyi miki shegen duka fa".
Fauzeeya ta k'ara gyara zamanta tana lumshe idanunta alamar barci tace"saidai ka kasheni ka kaiwa kakata gawata amma muna nan tare dakai bazanje ko nan da can ba".
Yaseer ya gyad'a kansa cikin takaicin maganarta yace zaki gane bakida wayo yanzun nan jikinki zai gaya miki".Yana rufe bakinsa ya nufi wurinta gadan gadan yaga ko alamar guduwa batayi ba, yana karasowa wurinta ya daga hannu zai zuba mata bulala ajiki tayi sauri ta fad'a cikin jikinsa ta k'ank'amesa kamar wani zai k'wace mata shi jin saukar lallausan fatar jikin mace da tudun boob's d'inta yasa Yaseer ya shiga cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara saboda ya dad'e rabon daya jishi ajikin mace, k'ok'arin b'an'bareta yakeyi ajikinsa domin kada ya afkawa d'iyar mutane amma ita sai k'ara mannewa takeyi ajikinsa saboda taji dad'in yadda suke rungume da juna..
Dak'yar ya fitar da nishin buk'ata ya dubeta yace"kiyi hak'uri Fauzeeya ki jaye jikinki anawa kada shaid'an yayi galaba akanmu kinji na rok'eki".
Fauzeeya ta yamutsa fuskarta tareda bintsire baki tace"bazan tab'a jaye jikina ba har sai kayimin alk'awarin kana sona zaka aureni nifa yah Yaseer tun lokacin da idanuna sukayi tozali dakai na afka cikin kogin soyayyarka, saboda haka ruwa ko iska basu isa su raba soyayyar dake tsakaninmu ba".
Rassss gaban Yaseer ya fad'i hankalinsa yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tashin hankali ne ya ziyarci sassan jikinsa da k'wak'walwarsa, tattaro dauriya yayi ya b'oye fargabansa yace"naji Fauzeeya aiba sai kinyi haka zan fahimci kina sona kamata yayi ki gayamin da bakinki saimu daidaita kanmu batare da sanin kowa ba"."Hmm kai d'in ne za'a ce ana sonka ka amince zama guda nifa da gaske nakeyi ina sonka Yaseer please ka amshi soyayyata ".Inji Fauzeeya kamar zatayi kuka.
"na amince nace miki ki sakemin jiki! ".Yace atsawace.
Fauzeeya tace"karka k'ara yimin kuwwa nifa banason fad'a kaji saboda haka ka kiyaye".Babu yadda ya iya da ita domin ya tabbatar idan bai bita ta lalama ba saidai su tabbata ahaka, hakan ne yasa ya sassauta murya cikin tattausan lafazi yace"kiyi hak'uri masoyiyata bazan sake ba kuma na amince da soyayyarki gareni "."Bani nombar wayarka yanzu ".Yaseer ya gaya mata da baki ta kwashe cikin k'wak'walwarta yana kammala gaya mata ta had'e bakinsu wuri d'aya tana tsutsa jikinsa duk ya mutu domin shi dama abuk'ace yake da mace, zazzafan sak'onni ta dinga aika masa shi kuma sai numfashi yakeyi ganin tsayuwar ta gagaresu yasa suka zazzauna saman gadon suna kissing d'in juna, sun jima suna romance kamar zasu cinye junansu Yaseer ya shiga cikin wani irin yanayi na daban ya mance dawa yake tare, kwantar da ita yayi yana shafar ko'ina ajikinta ita kuma sai wani langwab'ewa da numfashi take fitarwa tsotsar bakinta yakeyi kamar mahaukacin zaki, sun jima suna yamutsa junansu can Yaseer yasa hannu yana mammatsa boob's d'inta ita kuma sai k'ara narke masa takeyi ajiki, matsawa yakeyi yana cika hannunsa can ya ciro boob d'inta guda ya saka abakinsa yana tsotsa..........
0 Comments