RASHIN GATA cmplt

 *RASHIN GATA*

🤦🏻‍♀️🙇🏻‍♂️🤦🏻‍♂️


Gajeren labari don nusar da iyaye.


*RUBUTAWA: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL*



*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*

*Y'AR GANTALI*

*RIKICIN MASOYA*

*A SANADIN KAMA*


          *AND NOW*


*RASHIN GATA*



*GARGAƊI: Wannan ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi don wani ko wata ba, idan hakan ya yi daidai da halayyarki/ka to arashi ne, na rubuta ne domin faɗakarwa ga iyaye masu irin wannan halin.



SADAUKARWA: WANNAN LABARIN GA BA ƊAYAN SA SAUKAR NE GA IYAYE MAZA DA MATA A DUK INDA SUKE, ALLAH YA JIKAN IYAYENMU WAƊANDA KE RAYE ALLAH YA MASU KYAKKYAWAN ƘARSHE.

________________________________



*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

_________________________________

*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*

_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts

arewawritersassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


Page 1 to end🔚🔚🔚🔚




Wata malama ce tsaye gaban allo a cikin aji, ta na famar koyar da ƙananun yara da ba za su haura shekaru shida zuwa bakwai ba.


Kamar an ce tada kanki, a kujerar baya ta hango wani tsamurmurin yaro, ya kifa kansa a desk da alama hankalinsa baya ajin, saurin zuwa gun shi ta yi ta ɗago kansa, hawaye ta gani kwance a fuskarsa, da alamar damuwa take tambayarsa "Me a ka yi maka kake kuka?" 


"Bakomai." Yaron ya faɗa.


Hannunsa ta ja zuwa gaban aji ta ɗora shi kan kujerar gaba ta ce "Zauna a nan." Ba musu ya zauna.


Tsayawa ta yi ta na nazarin yaron sosai, da dukkan alamu damuwa ta samu matsugunni a zuciyar yaron, gashi nan a yamutse duk sauran yaran za ka gansu a tsaftace, amma shi kayan jikinsa duk datti ga shi ya gama tsamurewa kamar kamun yunwa.


Tambaya ta jefa masa, shiru ba amsa, ta kuma tambayarsa nan ma shiru.


Ganin hakan ya saka ta yi amfani da  ƙwarewarta na zaman ta cikakkiyar(care giver) Mai bada kulawa ta musamman, domin gano matsalar yaron.


"Kowa ya fiddo fensirinsa da takarda ya zana mun duk abinda yake so." Ta faɗa.


A take yaran suka shiga jagwalgwala zane a kan takardunsu kowa ya na abunda ya iya.


Bayan sun kammala ta fara dubawa ɗaya bayan ɗaya.


Wani yaron ya zana mota,wani mashin, wani gida da dai sauransu.


Amma ga mamakinta wannan tsamurmurin yaron duk ya fi su ɗan ƙwarewa a zane, sai dai shi ta kasa fahimtar ina zanensa ya dosa.


Wani mutum ya zana riƙe da ƙatuwar dorina, gashin kansa a hargitse fuskarsa a murtuƙe, a gabansa wani yaro ne tsugune a kan gwuiwowinsa ya ɗaga hannu sama, a can nesa wata mata ce ya zana ta na zaune ta na ciyar da wani ƙaramin yaro abinci, amma gun wadancan biyun na farko take kallo baki a buɗe da alamar ta na faɗa ne.


Bayan Malama Fatima ta gama nazarin zanen, sai ta dubi yaron ta ce "Ya sunanka?"

"Hafiz." Ya amsa.


Dubansa ta yi cikin kulawa ta ce "Yawwa Hafiz me ye wannan ka zana?"


Nuna mata ya shiga yi ya nuna babban ya ce "Wannan Babana ne." Ƙaramin kuma ya ce "Wannan ni ne."


Ya nuna matar ya ce  "Wannan Mamata kenan."

Sai ya nuna jinjirin cikin zanen ya ce "Wannan ƙanina ne Abbas, Su baba sun fi son shi."


Daga nan Malamar ta fahimci cewa damuwar da yaron ke ciki ta samo asali ne daga gida, domin yara sukan bayyanar da damuwarsu ko shauƙinsu ta hanyar zane.


Girgiza kai kawai ta yi ta fice daga primary 2 ɗin ta na tunanin mafita.


©©©©©©©©

Bayan Hafiz ya je gida Mamansa ya tarar a kitchen, ya gaida ta sannan ya ce "Mama yunwa na ke ji, a saka min abinci."


Wata uwar tsawa ta daka masa ta ce "Matsa daga nan, ba zan bayar ba tunda ka roƙa."


Sum-sum ya janye daga gun ya je ƙofar ɗaki ya zauna ya na kuka, ga yunwa ga faɗa kuma idan ya matsa ya san kan zancen, don zai sha duka ne a banza."


Koda Sadiya(Maman Hafiz) ta gama girkinta, kai tsaye ta wuce ɗaki ta ɗauko Abbas ta zauna ta na bashi a baki, ko kallon Hafiz bata yi bare ya saka ran za ta ba shi.


A taƙaice dai haka ta bar yaron na ta ya wuni da yunwa, kuma ba wanka bare ka yi tunanin za a cire masa uniform.


Da yunwa ta ci shi a gurin ya ɓingire ya na barcin wuya.


Babansa na shigowa gidan, ya tarar da shi a gun ya saka ƙafa, ya ɗauke yaron da shuri, firgigit ya farka a wahalce ya saka kuka.


Kullum haka rayuwar yaron take, baya samun nutsuwa da walwala a gidansu kullum ya na takure, sai dai ya ga a na ta ririta ɗan uwansa, idan ya yi magana Maman ta zage shi, baban kuma abu kaɗan yaron zai yi ya hau shi da duka.


Duk yaron ya tsamure, sai uban kai ƙungurum amma ba naman jiki, saboda (Malnutrition) rashin wadataccen abinci mai gina jiki.


Kullum idan ya je makaranta baya fahimtar komai, sai damuwa da tunani.


Tun ya na shiru-shiru har ya zama taƙadarin yaro a makarantar, kullum cikin kai ƙararsa a ke gun malamai har suka fara gajiya da shi.


Akan haka Malama Fatima ta shirya tsaf don zuwa gidan su Hafiz, tana so ta bawa iyayensa shawara.


Bayan ta gama darasinta a ajinsu Hafiz ta fice, da aka kusa tashi ma ita ce ta dawo ajin domin yin last period, ana tashi ta ja hannun Hafiz ta ce "Yau a tare zamu tafi gidanku, mu je."


Kasancewar dama babansa ke kawo shi makaranta idan kuma an tashi baban Abdul (wani makwafcinsu) shi ke maida su gida tare da ƴaƴansa, ranar bai jira baban Abdul ba suka wuce tare da Malama.


Bayan isar su gidan, suka gaisa sosai da Sadiya, anan take mata bayanin ko ita wace sannan ta ɗora da cewa "Yaronku ya na cikin damuwa sosai, wanda hakan ya haifar masa daƙushewar ƙwaƙwalwar, baya iya kama komai ko da an koyar da shi, kuma da dukkan alamu baya samun abinci mai gina jiki yana ci domin ga shi duk ya tsamure, kuma ana barin shi da datti."


Ran sadiya ne ya fara ɓaci har ta buɗi baki za ta ce wani abu kuma sai ta yi shiru.


Nan fa Malama Fatima ta ɗora da bata shawarwarin irin abincin da ya kamata ya dinga ci, da kuma yanda za ta kula da tsaftar jikinsa domin samar masa da ingantacciyar lafiya.


Amma Sadiya bata ɗauki ko ɗaya daga cikin shawarar nan ba, sai ma korar Malamar da ta yi daga gidan nata.


Malamar ta zo fita kenan ta haɗu da Baban Hafiz a zauren gidan, nan ta mai bayanin abinda ke tafe da ita, ta ɗora da cewa "Kuma don Allah ku daina dukansa domin duka ya kan fanɗarar da yaro, yanzu ga shi har ya fara zama yaro mara ji saboda *Rashin gata* da ya taso a ciki, training ɗin da kuka masa kenan, idan ba ku gyara ba a gaba zaku yi nadama."


Shima Habibu bai saurare ta ba, domin mugun haushi ta ba shi, taya za ta zo har gidansa tana gaya masa magana son ranta? A zafafe ya ce "Malama ɓace mun daga nan, ki riƙe banzar shawararki wataƙila za ta miki amfani anan gaba." Ya na gama faɗa ya shige ciki, yayinda ta juya cikin sanyin jiki ta bar gun, ta na ƙara tausayawa Hafiz.


Lokacin da ya kai primary 5 ya fara zama fanɗararren yaro, mara ji numba ɗaya.


Ciwuka ne suke ta kaiwa yaron farmaki, saboda rashin wadataccen abinci, sosai ya ke fama da rashin lafiyoyi iri-iri, amma a haka suke barinsa ba wata kyakkyawar kulawa.


Wata rana Mahaifin Habib ya zo gidan don duba yaron, shi ne ya ɗauki yaron zuwa asibiti, bayan an gama ba shi duk wata kulawa da ta dace, Likita ya basu shawara akan yanda za su kula da lafiyar yaron, Malam Sa'id kakansa ya je da shi gidansa don basa kyakkyawar kulawa.


Su ne suka samar masa da ingantacciyar lafiya, saboda su na ba shi abinci mai gina jiki, irinsu ƙwai,nama wake, kifi da dai sauransu, nan da nan sai ga yaro ya fara warwarewa har ya fara yin 'yar ƙiba.


Rashin jin yaron ya saka Malam Sa'id ya mayar da shi gidan ubansa.


Kullum cikin ɗebo masu rigima ya ke, domin zuciyarsa ta gama ƙeƙashewa, a da ya na da tausayi ga shi shiru-shiru, amma saboda mugayen halayen iyayensa da suke nuna masa ya saka ya zama taƙadari, shi a ganinsa hakan ɗabi'a ce mai kyau domin cikin irinta aka renar da shi.


Ganin cewa ba a son shi an fi son ɗan uwansa, hakan ya sa ya tsani ƙanen nasa kullum cikin dukansa ya ke, yaran unguwa ma haka ba su da shaket idan ya na unguwar.


Lamarin yaron ya fara damun Habibu(mahaifinsa), hakan ya saka ya kira shi wata rana ya na masa faɗa, faɗar ya ke "Hafiz me kake son zama ne? Wai kai wane irin shegen yaro ne mara jin magana? Kullum sai ka daki ƴaƴan mutane?, ga yawan ɗebo min rigima da kake."


"Haka na ga a na yi a gidanmu." Ya faɗa cike da rashin kunya, ya juya ya barin gidan.


A lokacin da Hafiz ya kai shekaru goma sha biyar a rayuwarsa, ya gama zama gagararre na ƙarshe.


A wata rana Litinin bayan an taso daga makaranta, a hanyarsu ta dawowa gida ya yi faɗa da wani yaro, nan zuciyarsa ta rufe, ya ɗauki wani murgujejen dutse ya jefi yaron da shi.

A take maɗigar yaron ta fashe sai jini.


Da gudu mutanen gun su ka zo su ka ɗauki yaron zuwa asibiti, tun kafin su isa asibiti yaron ya cika.


Iya tashin hankali Habibu da Sadiya sun shiga a lokacin da labarin ya riske su.


Iyayen Sadiq yaron da Hafiz ya kashe, suka ce basu yarda ba, nan fa suka maka Hafizu ƙara a kotun ƙanunun yara.

Da yake yaron bai kai munzalin Shari'a ba, sai aka tura shi gurin da a ke ajiye ƙananun yara masu laifi irin nasa, har zuwa lokacin da zai cika shekaru goma sha takwas sannan a yanke masa hukuncin.


Haƙiƙa Habibu da Sadiya sun ga illar *RASHIN GATA* DA rashin kulawa da suka yiwa yaron nasu a shekarun baya, da sun ba shi kyakkyawar kulawa, ko sun saka shi a jiki, tabbas da ba a zo wannan matakin ba.


Yanzu gashi su na ji su na gani an raba su da yaron nasu, wataƙila ma ya tafi kenan har abada, domin kisa ne akan duk wanda ya yi kisan kai, haƙiƙa sun zalunci ɗan nasu, kuma duk abinda ya aikata sune sila.


Sun yi kukan baƙin ciki har sun gode Allah, daga nan suka ɗaura ɗamarar gyara rayuwar sauran ƴaƴansu, don gudun kuma faɗawa matsala irin wannan.


Tabbat bi hamdillah

Anan na zo ƙarshen wannan taƙaitaccen labarin.


Taku har kullum Ruky i lawal.



RUKAYYA IBRAHIM LAWAL.



Post a Comment

0 Comments