[7/31, 2:00 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Har soron qarshe na cikin gidan suka shiga kana ta sauke qaton bukitin pentin dake kanta wanda ke cike da ruwa, ta kalli qaninta mai kimanin shekaru 11 tace "Nura dauki ka shiga dashi, ai xaka iya ko?" ya fara kicin kicin daukan bokitin yana cewa "eh ya SAKEENA, ai qarasawa ne kawai" ta labe a bayan kyaure shi kuma ya shiga cikin gidan da ruwan kamar shi ya debo.
Haka suka dunga debowa tana kawo masa har cikin soro yana qarasawa dashi saboda fin qarfinsa da bokitin yayi. Sai da suka cika duk abunda ke gidan sannan matar gidan ta dakko kwanansa ta xuba masa dafaffiyar taliya da manja da yaji, yayi mata sallama inda tai masa umarnin ya dawo da yamma.
Ya fito soro inda sakeena ke rabe ya nuna mata taliyar yana washe baki da cewa "ya Sakeena yau taliya akai, kamar tasan ina san taliya, taho muje gida muci" taja hannunsa suna tafiya itama da murmushin daya xame mata dabi a indai tana tare da Nura, ita kan ta rasa irin son da takewa qaninta Nura tanajin kamar itace uwarsa da ubansa.
A tsakar gida suka tadda matar babansu mai suna Inna, da harara ta bisu har suka ci burki a gefen tsakar gidan inda nan aka ware musu gurin xaman a tsakar gidan wanda Inna bata gajiya da fada musu cewar ko raban gado aka tashi baxasu samu inda ya wuce nan ba.
Idon Inna akan kwanan hannun Nura, tai kwafa da cewa "sannunku barbadaddu daga makarantar sai kuka tafi yawon barbada ko? Memakon ku dawo ku cire uniform yanda kowane dan arxiqi yake cirewa" Nura da bai cika raga mata ba ya harareta yace "ba yawo mukaje ba neman abinci mukaje, ba a bamu ba ai dole mu fita mu nema" sakeena tai saurin toshe mai baki tana juya musu taliyar. Inna kuwa kamar mai jira tahau sababi "eh baxan baku ba, ubanku meya mutu yabarmun banda wannan kejin gidan? Ita kuwa ba a xancen matsiyaciyar uwarku domin haka taxo garinnan da sunan aure daga ita sai kayan jikinta, wlh bantaba ganin abun kunyar dana gani akan uwarku ba wai kaxo gidan aure ko cokali babu balle tabarma shiyasa baxan daina xargin a bariki ya samota ba."
Duk da maganganunta na yiwa sakeena ciwo bata nuna hakan ba, sun duqufa lomar taliya kuma dama andade ba a hadu ba 😄. Ana haka qaramin dan Inna ya shigo me suna umar shekarunsa 6, idonsa na kaiwa kan taliyar ya nufesu yana cewa "lah taliya? Xanci," suka matsa masa ya xauna zaisa hannu kenan Inna taxo ta janyeshi yana tirjewa tana cewa "wlh baxakaci taliyar nan ba, inkaci kaci hantar ubanka, babu abunda ya hadaka da wadannan tanbadaddun" sakeena ta dago idonta taf kwallah, bata jurar duk sanda inna ta rabasu da yayanta saitayi kuka itadai tanason yan uwanta yan uba duk da inna bata bari ko doguwar magana ta hadasu. Muryarta na rawa tace "Inna dan Allah ki bari yaci, umar dan uwanmu ne Allah ya hadamu dasu bamu da wadanda suka fisu ku... " ta tari numfashinta "yimun shiru uwar tsara xance anyo gadan dadin baki irin na yan bariki a gurin gyatuma, karki kuskura ki kuma hada yayana masu usuli da ku, domin su in aka fara xayyano nasabarsu sai an dangana har kan sarkin musulmi. Ku kuma in banda qedarar uwarku mai kama da bulalar dukan mahaukata da idanu kamar na mayu da aka kawo mana ko kare ba a kuma nunawa da sunan dangin uwarku ba. Ai wannan qedara ta cuceni ta batamun zuria ta haifamun wake cikin shinkafa" ta qarasa tana share hawaye.
Sakeena ma hawayen take, inda sabo yaci ace ta saba da wannan gorin na inna amma xuciyarta bata jura duk sanda inna ta kira uwarsu da qedara kuma karuwa sai tayi kuka. Ta cire hannunta a taliya duk kuwa da yunwar da takeji ta barwa Nura yanaci dake shi bai gama sanin abunda duniya take ciki ba.
Tana yawan tunanin mahaifiyarta, sassanya doguwa fara me dararan idanuwa, duk bata gama wayo ba uwar ta mutu ta barsu cikin wata irin bahaguwar rayuwa wacce tayi tsananin qazanta bayan mutuwar ubansu. SAKEENA ABBAKAR LIMAN kenan.
**** **** **** **** **** **
Tun matar gidan da Nura ke aikatau bata lura da cewar aikin da Nura keyi na debo ruwa yafi qarfinshi harta gane, saboda kama sakeena da tayi a soro a tsaye taje xubar da shara ta tuhumeta me takeyi anan ko taxo yimata sata ne? Tsoron ambatar sata da tayi yasa sakeena fada mata gaskiya qanin take tayawa debo ruwa abasu abinci. Matar ta yamutsa fuska tana tambayar sakeena "wai ku baku da iyayene?" a dan diririce sakeena ta bata amsa "a e ai sun mutune" jikinta yayi sanyi jin hakan ta gyara tsaiwa tace "to aikema sai kixo indunga baki wani aikin kinayi, sai inbaku abincin da zai isheku." sakeena ta sunkuya har qasa tana mata godia.
Tundaga wannan rana suka xama bayi a gidan wannan mata. Da asuba tayi suke tashi suyi sallah sutafi makatar allo wacce sukeyi anatashi zasu tafi gidan aikinsu wanda da farko aikin sakeena a gidan shara da wanke wanke kafin daga baya matar gidan ta fuskanci sakeena qaqqarfar yarinyace ta hada mata da wankinta da kuma na yaranta wani lokacin harda na mijinta dan tsabar zalunci. Suna gama aikin safe zata basu dumamen abincin dare wani sa in da ruwan koko ko shayi suci su tafi. Sukan koma gida sako uniform din makaranta wanda daganan komi makarar da sakayi se sunyiwa inna nata aikin ba tare data basu koda ruwan gidan ba sannan su tafi makarantar boko wacce suna tasowa gidan aikinsu xasu dura suyini cur suna mata bauta har laasar lokacin shiga makatar yamma sannan su tafi in sun dawo ma nan suke komawa sudanyi abunda yarage kafin magrib su tafi gida da kwanon abincinsu na ladan bautar da suka yini sunayi. Suna sa qafa a gidan gorin Inna zaice salama alaikum tasasu agaba da zagi da gori da ambato uwarsu dake qarqashin qasa, hakan kuma baya hana acinye abincin da nata yayan duk kuwa da qoqarin hanasu da take.
Yakasance aikin yabi jikinsu harma da qarin wankau da sakeena keyi dan samar musu sabulun wanka dana wanki dan su huta gorin Warin dauka da kyamar zama kusa dasu da akeyi. Ada idan matar gidan tasata wankin yayanta takan faki ido tasa kayansu a kumfar ta wanke, cikin akasi ta kamata tai mata tas harda barazar korarsu daga aiki tayi, acewarta ya xata hada kayansu me baqar qazanta dana yayanta? Tun daga ranar sakeena ta samarwa kanta mafitar yin aikin wankau dan samar musu abun wanki.
Cikin qanqanin lokaci ya zamana sakeena da Nura yayan margayi Mal Habu Liman kanyi kowane irin aikin qarfi domin abasu abinci. me nema na tare da samu, sun sami saukin rayuwa ta fannin samun abin kaiwa bakin salati amma suna bautuwa bautar data wuce abunda ake basu.
***** **** ***** ***** ****
ASALINSU
Mal Abbakar Liman su biyu ne suka taso a gurin mariqinsu shi da yayarsa Hafsatu. Iyayensu sun mutu tun suna yara, riqonsu ya dawo hannun qanin ubansu. Hafsatu tayi aure da wani malamin makarantar secondary a qauyen wanda daga qarshe ya samu canjin gurin aiki daga qauyen zuwa cikin garin kano.
Yayin da Abbakar yakai munzalin aure kawunsa ya dade da rasuwa, kasancewar basu samu illimin zamani ba yasa yake sanaar jan mota xuwa garuruwa. Dafarko da karan mota ya fara kafin daga baya ya koma driver. Acan qauyensu (BAGGADANO) cikin qaramar hukumar Dawakin tofa a jihar kano ya hadu da Lauratu wacce ta kasance matarsa ta fari auren saurayi da budurwa. Sun haifi yaya 4 da Lauratu wacce yayanta ke kira da Inna kafin ya auri mayafiyar su sakeena.
Ya hadu da itane a wani xuwa da sukai da motar Lakoja (kogi state) ita kuma takasance tana tallan kifi. Xuwansa na farko suka hadu a tasha suka fara soyayya suka rabu bayan lokacin tafiyarsa yayi hankalin ta ya tashi amma yayi mata alqawarin xai dawo.
Mahaifiyar su sakeena ta kasance yaren Igala kuma mabiyar addinin Christa, duk da tasan akwai hatsari sosai kasancewar Abbakar bahaushe kuma musulmi amma ita soyayya bata shawara balle ta fada inda ya dace. Adawowar Abbakar ta biyun garin zancen soyayyarsu ta fasu har takai kunan yayanta dake walder a tasha. Tana xuwa gida basu nemi jin baasiba suka hauta da duka a fadarsu ai zagi ne garesu ace yarsu xata auri bahaushe kuma musulmi. "me xakiyi da auren bahaushe wanda kullum se yayi aure kuma kullum saiyayi Saki? Kuma musulmi for dat matter" cewar mamanta.
Abbakar besan abunda ake ciki ba, yagaji da xaman jiranta har kwanaki 2 amma ko me kama da ita be ganiba balle wanda zai bashi labarinta. Haka ya koma cikin qunar zuci domin yana qaunarta.
Ko wata daya me rufa ba ya kuma dawowa kogi domin ya mato murus akanta, akayi sa a labarin xuwansa yazo mata ta hanyar qaninta da ta roqeshi ya samata ido atasha ya gano matashi. Wannan zance ya faranta ranta cikin dabara ta sudade ta gudu da sanyin safiya lokacin duk gidan suna baccin asara.
Abbakar kamar ya xuba ruwa a qasa yasha lokacin da yayi arba da ita. Ta fada masa yadda akai ta gudo, ba tare da ya cika motarsa ba ya sata a gaban mota tare da sai mata qosai da bread sika daga xuwa Baggadano saboda kar abiyo sahun Linda (sunanta Keenan). Daga yadda ya yini yana kula da ita a mota Linda tayi yaqiinin wannan bahaushen Ba irin bahaushen da ake gorantawa a gidansu bane, kuma tanasa ran baxaici amanarta ba. Shima a nasa bangaren Abbakar tsakaninsa da Allah yakesan Linda kuma yana kwadayin musuluntar da ita abunda tasha cemasa tana kwadayi, dama kuma bai taba soyayya ba dan Lauratu matar ladan noma ce
Yana isa qauyensu direct gidan megari ya kaita kuma ya masa bayanin yadda ya gudo da ita da kuma auranta da yakeson yi. Bayan dan fadace fadace irin na manya kan yadda ya gudo da mace da hatsarin auren mushurika limamin garin ya musuluntarta akace ta zabi suna tace Abbakar ya tsabar mata shi kuma ya sanya mata Aisha sunan mahaifiyarsa. Washegari aka daura musu aure da Aisha wacce batajin hausa sai abunda ba a rasa ba. Yarenta kawai takeji na Igala sai turanci broken wanda dashi suke magana da mijinta wanda ya koya adalilin tafiye tafiye da yake.
Tashin hankalin da Lauratu matarsa tayi ba qarami bane dan fada ma bata baki ne. bare dataga Aisha kyakykyawar mace fara sol doguwa mai dara daran idanu irin na yaran igala ai saita kuma raina kanta. ita a fadarta karuwarsace suka gama sheqewa sannan ya taho da ita.
anfara xama me dadi irin na masoyan da sukai auren soyayya a bangare guda kuma mara dadi ta bangaren Lauratu dan zagin Aisha take ta uwa ta uba kafin ta fuskanci aikin banxa take dan batajin hausa. Ta fara gwada dukan Aisha duk kuwa da kashedin da amqociyarta Adama ke mata na cewa karta yadda suyi kokawa dan qedarai qarfi garesu, amma ga mamakinta sai gashi ta yiwa Aisha liqis ta barta kwance.
Bata taba ganin bacin ran Abbakar ba sai aranar domin bayan ya gama masifa kamar xai daketa sannan ya korata gidansu dan yace Aisha ba baiwa ya siyo mata ba da zata kamata da duka kamar diyar cikinta. Dakyar manya suka dawo da ita bayan ta kwana uku a gida. Daga nan aka rufe dukan Aisha a gidan sai dai xagi da habaicin cewa ita karuwa ce ko kuma ace mata qedara Sannan a tasa ta da bauta inyayi tafiya ta yan kwanaki. Duk da ba mawadaci bane amma yana da wadatar zuci dan haka Aisha a wadace take kuma yakan bata kudi ta ajiye a gurinta inxaiyi tafiya saboda yasan halin Lauratu.
Ana haka tasamu ciki ta haifi ya mace dakanta ta zabawa diyarta suna SAKEENA. Ta taso cikin soyayyar uwa da uba, ta debo uwarta a xubin fuska da idanu amma kuma ajiki bata kasance doguwa kamar Aisha ba. Sakeena nada shekaru 5 ta kuma samun ciki, Abbakar yayi murna kwarai domin yana burin Aisha ta kuma haihuwa yakaita ga ahalinta watakila insukaga albarkar yaya su yafe mata. A lokacin da Aisha ta tashi haihuwa taxo da tangarda tasha wuya kafin a kaita asibitin cikin qauyen ta haihu da namiji amma lfy sai a hankali.
Aisha nada yara 2 sakeena da Nuraddeen sai Lauratu dake da 7 maza 5 mata 2. Kullum Aisha na cikin ciwo wanda Abbakar ke zaryar nemar mata magani gari gari da kuma na asibiti. A bangare guda kuma Inna wato Lauratu tayi aiki tuquru wajen raba kan yayanta da dasu Sakeena. Tayi sa a kuwa domin inkaga yayanta dasu sakeena baxaka taba cewa sun hada iri ba xaka dauka xaman gidan haya ne ya hadasu, gidan hayan ma irin wanda ake xaman uwaka ubanka.
Sakeena nada shekara 8 Nura nada 3 Allah ya karbi rayuwar Aisha, wanda kafin ta mutu sai da takai komai sai anmata hakan kuma yasa Abbakar ya dena tafiye tafiye kuma duk abunda yake dashi ya qare a kudin magani ta mutu da burin ganin ta koma ga iyayenta sannan ta yabawa Abbakar kwarai gurin yadda ya riqeta kuma ta jaddada masa ya kular mata da yayanta dan tasan Lauratu bazata riqe mata ba kuma inya kaiwa yan uwanta xasu kafirta mata su.
Tun mutuwar Aisha shima Abbakar ya zamana lfyar sai ahankali kullum yana riqe da qirji wanda yake complain yana ji kamar zai fado. A daddafe yayi Shekara daya da rabi ,mutu kwakwai rai kwakwai kafin shima Allah ya karbi ransa, ya mutu batare da ya cika burin Aisha ba na nunawa yan uwanta yayanta da kuma nema mata gafararsu.
Mutane kanyi sharshin cewa soyayyar Aisha da ciwon yadda Lauratu ta raba masa kan yaya ya kasheshi. To koma dai meye ya mutu yabar yan marayu a hannun Allah wanda basu da dangin uwa kona uba a kusa balle su tallafesu.
Hajia ☺
[7/31, 2:01 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
SHARHI Ina bawa makaranta littafina haquri akan kuskuren da aka samu, na rubuta sunan littafi MUQADDARI a ranar dana fara posting cikin akasi sai akasamu wata marubuciya itama sunan littafinta irin nawa, to saboda haka na dan canja wani abu a nawan memakon MUQADDARI ya koma MUQADDARI NE. Ina fata baza a samu rudewa ba wajen gane littafin Rahmatullah (AL' AMARIN MARYAM) nagode sosai MARYAM BAITA ana tare 🤝🏽
Ko sati daya Mal Abbakar beyi da rasuwa ba rayuwar su sakeena ta qazanta, domin Inna tunda aka share makoki bata kuma basu ko kwayar dawa ba. Acewarta ubansu be mutu yabar mata ba, duk da cewa Inna gaskiya ta fada domin bai mutu yabar mata komai ba sai dan qaramin gidan da suke ciki amma kuma inta dubi bautar dasu sakeena ke mata ai ko ladar bautarsu ta basu.
Amma inda gixo ke saqar shine, bayan hana musu abinci dan tsabar mugunta saita hanasu xuwa makarantar primary dake garin wacce da ita da babu bambamcin Kadanne, domin ko sakeena yar shekara 9 dake primary 6 bata fahimtar komai bare Nura dan aji 2. Babbar matsalar dake hana sakeena karatu dai itace matsalar ido wacce aka haifeta da ita wacce kana kallonta xata karanci hakan aciki manyan idanunta wadanda ke xama jajaye a lokacin sanyi (sanda matsalar tafi tashi kenan)
Lokacin da tura takai bango shine lokacin da Inna ta qullesu suka kwana suka yini a daki babu ci balle sha bata basu ba bata kuma barsu sun fita sun nema ba. Sunyi magiyar sunyi kukan har sun gaji, qaramin danta umar shiyaje maqota yana dariya yana fadamusu. Matar gidan dattijuwa sunyi xaman kwarai da Aisha ta rufe kai ta shiga gidan ta ganewa idonta, sai dai ta kada dambu taliya Lauratu ta bude marayun Allah amma taqi, a cewarta tana rama abunda Aisha tai matane akansu. A qarshe dai da taga shirin kissan kai takeyi saita fita ta bar mata gidan da wani quduri a zuciyarta, tana matse kwallar jin su sakeena na roqonta dan Allah kobata budesu ba ta basu abinci suci.
Bata jima da fita ba sai gata ta dawo da tawagar megari da kuma megarin kansa, suka dau salati a tare suka dire lokacin da aka bude su sakeena aka samesu a jigace kwarai.
Lauratu tayi tsamo tsamo cikin tsananin tsoron irin hukuncin da xai biyo baya, aranta take aiyana wannan mace kwai tsinanna da nasan hukuncin da xata dauka kenan ai dana budesu tun lokacin data shigo. Ba wata doguwar magana megari yace a tafi da ita office din yan sanda tare da fada musu yunqurin kisan kai tayi wa yayan mijinta. Ai dajin haka ta kwantsama ihu tana neman aimata afuwa baxata sake ko kallon su sakeena ba.
An zayyano mata sharuda wanda ta yadda cewa xatabi kuma inta saba a tafi da ita a daure, acikin sharudan haddacewar xata kyale su sakeena suyi rayuwarsu tunda tace ita baxata iya daukar nauyinsu ba.
Bayan wannan sun fara wata iriyar bahaguwar rayuwa wacce babu me sakasu babu me hanasu, dan iya tadau matakin babu ruwanta dasu inzasu kwana su yini a waje baxata nemesu ba kuma insun shigo baxata tambayesu daga inda sukeba, iyakacinta dasu sakeena tai mata duk ayukan gida wanda ya hada damn shara da wanke wanke sannan ita da Nura su cika mata komai na gidan da ruwa. In akai rashin sa a suka fita kafin ta tashi tofa in sun dawo duk daren da sukai sai sunmata, nata yayan kuma suna shelelensu tsakaninsu da su kuwa sai sunyi ba dai dai ba suyi ta dura musu zagi da aibatasu.
Da farko sun fara gararanba, basu tasha basu kasuwa suna neman abunda xasuci makarantar ma sun dena xuwa saboda neman abunda xasuci. Sakeena dai bata da qawa saboda qazantarta, koda ta shiga cikin sanni akanyi mata gorin warin baki da tsamin dauda, acikin ajinsu na makarantar da bazuwa take bama gurin xamanta daban wanda babu me xama sai ita. Dake tasan gaskiya ne bata damuba, ita kanta warin jikinta yana addabarta ga soshe soshe da takeyi. To mutumne bame cemasa ya gyara.
Acikin hakan akadau lokaci. Xuwa wannan lokaci su sakeena sunxama expert a harkar bara, kwararo kwararo sukebi dan neman abinci xancen karatu kuwa tunda tayi jarrabawar kammala primary ta ajeshi gefe guda duk kuwa da tsananin san karatun da take a burinta ta zama me karanta labarai a gidan TV amma rashin kafin kwakwalwarta da raunin idonta yana togaceta daga hangen cikar burinta. Sai take kallon Nura a matsayin wanda inta tsaya masa xai xama abunda take burin ita din ta xama. Ta tattara hankalinta da qoqarinta gaba daya akan Nura da ganin yayi karatu, ita kanta batasan irin soyayyar da takewa Nura ba, duk da batasan yadda akesan Da ba amma tana jin soyayyar Nura a ranta kamar itace uwarsa da ubansa.
****** ****** ****** *****
yar matashiyar budurwa me shekaru 14 a duniya, wacce qazanta ta hana ainihin kalar fatarta bayyana, amma a fuska wata irin kyakykyawa ce, kyau me sanyi komai nata matsakaici daga kan hancinta har bakinta inka dauke manyan idanunta. Haqoranta ma duk da qaxanta ta dafar dasu hakan be boye tsaruwarsu ba. Fuskar sakeena ta Aisha ce sak wato irin ta kyawawan yaran igala wacce Inna bata gajiya da fada mata Kamarta da karuwar uwarta. Da alama bata cika tsahoba duk da bata gama girma ba, kuma tanada murmuren jiki wanda ke nuna inta samu jin dadi xa ayi Mace sosai.
Yanxu haka sakeena da Nura kanyi duk wani aiki na bauta indai xasu samu abinci, kuma babu lefi qazantarsu ta ragu da kashi 40 cikin 100. Nura dai ya samu shiga qaramar secondary dake garin bisa qoqari da jajurcewar sakeena wacce tai aiki tuquru ta tara kudin saya masa littafai da uniform, duk wani qoqrinta yanxu yanakan karatun Nura shiyasa har yanxu jikinta be cika samun canjin qazanta ba. Shima a nasa bangaren Nura bashi da burin daya wuce faranta ran ya sakeena, duk kuwa da qarancin shekarunsa ya fuskanci fafutukar da take dan inganta future dinsa.
A wani dare suna kwance kan tabarmar dakin mamansu wanda bayan mutuwarta ya xama nasu Nura ya tsurawa sakeena ido ta hasken farin watan daya ratso ta window, ta miqe daga kwancen da take ta matso kusa dashi tana murmushi tace "ai tunda naga kana Kallona haka Nura nasan akwai lbr, tashi kabani insha yau me akai a makaranta?" ya dade yana kallonta sannan ya magantu "ya sakeena babu abunda akai, kawai dai inaso ne inta kallonki sai nakeji kamar mun kusa rabuwa" ta zaro ido 😳 kafin tace "Nura karka qara Kira mana kalmar rabuwa duk rintsi muna tare Nura, ko aure xanyi sai nasamu wanda zai yadda intafi dakai sannan xan aureshi" ta Dan nisa kadan tai tunanin wazai auri qazama irinta? Ganin har yanxu idon Nura yana kanta tai saurin kintse tunaninta. Ya riqe sannunta duk biyun yace "ya sakeena Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya baki miji nagari, Allah ya kawo miki matemaki in shaa Allahu burinki na xama me karanta labarai xai cika komai wuya." kalaman Nura kenan wanda suka hana sakeena bacci a wannan dare tana tunanin ta ina dan qanqanin yaro kamar Nura ya iya tsara wadannan kalamai?
Kusan kwana uku kenan yau da yin hakan, kuma tanajin kanta sukuku kuma ba rashin lfy take ba ita kanta batasan meke damunta ba duniyar tai mata wani irin rashin dadi. Sau uku wata maqociyarsu na aikowa taxo tai mata wanki amma ta kasa xuwa. ranar ta biyar bayan antaso makaranta Nura ya sami sakeena har daki a kwance bata da lfy tun jiya yace mata zai tafi tallan ruwa wanda ya sabayi a tasha inyataso daga Boko. Ta kyada masa kai ba tare da tace komai ba, ya juya ya tafi idonta a kansa har ya fice daga dakin.
acan tasha wajen qarfe ukun rana cinikin ruwa nata garawa Nura har yayi dauka ta uku ya ware kudin me ruwan ya ware ribarsa ya xuba a aljihu. Wata mota dake shirin tashi wata mata ta yafitoshi da hannu da cewa "me pure water bani guda 4" kafin ya debo mata har me motar yaja shi kuma da quruciya yabi motar da gudu ba tare daya kamota ba har suka fita daga tasha, bai dena bin motar ba cikin tsautsayi wata motar ta taho daga daya barin a lokacin da yake qoqarin miqawa matar ruwan ta bankeshi ya fadi gefen titi wata motar tabi ta kansa. Innalillahi wa inna ialaihi raju'un ko shurawa Nura beyi ba ya mutu kansa yayi raga raga.
sakeena na kwance tana wahalanlan bacci sallamar maza ta tasheta, tayo wajen dakin da gudu saboda ihun Inna data jiyo. Tayi mugun ganin abu nannade a tabarma tana digar jini, cikin azama ta qarasa ta bude tabarmar duk da raunin ganinta da kuma yadda gawar Nura tai kwatsa kwatsa Haman be hana sakeena sheda Nura ba. Ta sulale a qasa ta fadi a gurin.
Wani maqocin margayi mal Abbakar dake xuwa cikin garin kano duk sati wato ranar asabar shine da yaje ya nemi gidan Hafsatu wato yar uwa ga margayin bayan sun gaisa yake fada mata mutuwar Nura da kuma halin da sakeena ke ciki. Ta dunga kuka tana sallalmi, duk da muna zamani na wayar hannu amma a yaran gidan yan samari a rasa me kiranta ya sheda mata saboda basu dauketa wata abuba? megidan yana dawowa ta fada masa asubar fari tana cikin motar xuwa Baggadano.
Acan kuma bayan kwashe awanni 36 acikin coma sakeeena ta farko, amma fa cikin wani irin yanayi domin babuci, babusha, babu magana, babu sallah. Tanadai xaune tanabin tsirarin yan xaman makoki da kallo. Duk wani me imani ya tausayawa sakeena, aciki kuwa harda Inna wacce har kwallah take sharewa inta Kalli sakeena. Domin inda wanda xai bada lbrin soyayyar sakeena da Nura to itace no 1. Ita kanta taji mutuwar yaron kuma tayi nadamar abunda tai musu.
Babu yacce batai da sakeena ba tun jiya data farko akan taci abinci tai wanka amma sakeena saidai taita kallonta kamar bata santa ba. itadai sai takega kamar sakeena ta samu tabin hankali.
Ana cikin wannan yanayine Hafsatu tazo wacce suke kira da Iya. Ta shigo gidan da ragowar hantsi kasamcewar tayi tafiyar sammako, yan Samari da yanmatan yayan Inna suka dunga xuwa gaisheta babu wanda ta amsawa saida suka tattara gaba dayansu tas su 7 inka dauke sakeena dakecan daki bata fito ba sannan Iya ta fara magana cikin bacin rai "yanxu duk yawanku arasa wanda xaisa katin naira 10 a waya ya fadamun mutuwar Nura? Karku manta nidin yayar ubanku ce kuma duk duniya baku da dangin uban daya wuceni, kodan qasa ta rufe idon Habubakar kukemun haka? Ko kuma dan Allah be bani haihu ba?" ta fada tana share kwallah. Inna dakecan gaban murhu tana rura wutar ruwan dama koko tai gatsal ta shiga cikin maganar "kinga Hansatu karki dorawa yara lefin daba nasuba, sune suka hanaki haihuwar? Ko kuma tunda ubansu ya mutu kikazo xaman mutuwarsa kin kuma dawowa duba zuriar sa? Ko kin taba kawo gishiri kince a barbadawa marayu a abinci?" da wannan kalami Inna ta rufe bakin iya domin tasan itama gaskiya ta fada, kuma dama can babu jituwa tsakaninta da Lauratu xamane suke irin na doya da manja duk da sukan kwashe shekaru basu hadu ba.
Iya ta miqe ta shige dakin da Indo diyar Inna ta nuna mata sakeena na ciki, ita kuma Inna ta wuce da mitar cewar "haka kawai da sanyin safiya kixo ki tasamun yaya agaba da masifa wai basa kulaki yo ke kulasun kike?"
yadda takewa mutane haka taiwa iya ta xura mata ido tana kallonta, iya dai ta kasa magana sai kuka ta kama hannun sakeena tace "haka kika koma sakeena?" tafi awa daya tana aikin lallashi amma sakeena ko gizau. Ganin haka ta kamota suka fito tsakar gida ta dauki tukunya da nufin ta dora ruwa akan murhun da Inna ta gama amfani dashi Inna ta banko labule ta fito tare da cewa karki tabamun itace na girkin ranane, ke baki qullo kin kawo ba kixo nayi tanadi ki rusamin da iyayinki na banxa da wofi. Iya tace "to hakan ma yayi dai dai" taja hannun sakeena suka fita maqota can gidan mal Ado wanda yaje ya fada mata mutuwar. Bayan sun gaisa ta nemi alfarmar Dan Allah ruwan xafi take so xataiwa sakeena wankin kai, dake sunsan halin Inna basuyi mamaki ba suka tashi suka dora mata cikin tukunya. Suna dan taba hira dake matan gidan biyu ne tana tsefewa sakeena cukurkudaddan gashinta. Anan iya takejin irin gwagwarmayar dasu sakeena sukai har ixuwa mutuwar Nura, kuka tayishi yafi gaban a fada ta tattara lefin gaba daya ta dora akanta be kamata ta bari zuriar Aisha yarinya me girmamata ta qare a hakaba duk da ta nuna bataso aurenta da Habubakar ba amma hakan be hana Aisha girmamata ba a matsayin yayar mijinta.
A cikin awa guda saida iya taiwa sakeena ruwa 3 daga kanta xuwa jikinta sannan taga ta fita. Bayan ta surka ruwan kokon da aka bata a gidan da ruwa ta bata tasha dakyar, amai ya biyo baya kamar ta amayar da kayan cikinta. Ta koma ta xauna sharaf jikinta ya kuma laushi saboda yunqurin amai. Mal ado da kansa ya fita ya samowa sakeena madarar shanu sabuwar tatsa, ta kafa kai ta shanye tas sannan iya tace tasa kaya, amma abun takaicin kayan sakeena sun mata kadan bayan yayyagewa da sukayi rigar da tasa ta dame mata qirjinta daya fara tasawa. Iya tace ta ciresu ta dauki nata kayan da taxo dashi wanda takeso gobe inxata tafi ta canja ta bawa sakeena tace ta saka. Duk da kayan sun mata yawa sai taji tafi sakewa aciki.
yinin ranar iya ta yishine tana kula da sakeena, kuma Alhamdulillahi ansamu cigaba dan taci abinci kuma iya tayi mata kitson hannu a kanta wanda tana kitson tana yiwa sakeenan nasiha akan mutuwar Nura, ta dago kanta karo na farko tai magana da cewa "iya Nura ya mutu, ya tafi yabarni ni kadai, babu gwaggo babu baba yanxu kuma babu Nura ya mutu wajen neman halak bani da kowa." iya ta kwantarta kan cinyarta tana qara lallashinta tace "hakane sakeena baki da kowa amma kina da Allah, haka ya tsara miki rayuwa, indai kina buqata xan tafi dake can birni gurina. Amma sakeena nima ba a dadi nakeba mijina ba shine dashi ba sai dai rufin asiri ga kuma kishiyata karkiga a birni nake kiyi xaton cikin jin dadi nake wannan dalili shiyasa kukaga bana xuwa muku saboda banda abunda xan baku. Inkin yadda xakibini bani da kowa kamar yadda kema baki da kowa sai muje muyi gwagwarmayar rayuwa tare" sakeena ta miqe daga kwance ta qurawa iya ido tana kwallah tace "iya xan biki komai wuyar da xansha acan, babu irin wahalar rayuwar da ban saniba, tun ina yar shekara tara nake nemawa kaina abinci. Kuma dama natsani qauyen nan banga amfanin xamansa ba tunda babu Nura" iya tace 'yawwa sakeena, tsakaninki da Nura yanxu addua ce"
Washegari a maqota sukai wanka daga sakeena har iya domin iya tayi batun tafiya da sakeena birni wanda baqin ciki yasa Inna tace bazasu taba mata komai na gidanba in sunje birnin sayi wankan. A gidan mal Ado sika qarasa kintsawa, tsahare matar sa ta bawa sakeena doguwar rigar yarta ta atamfa Leda sabuwa jin cewa xasu tafi burni harda turare karon farko da sakeena tasa turare a rayuwarta, sai taji kanta a matsayin yar gayu lamba 1 ashe qamshi haka yake saka nishadi? Inama dai masu yimata gorin wari zasu ganta yau suji qamshin jikinta. Suka koma gida dan sallama wa yan gidansu, sukam yaran sun nuna ko a jikinsu sakeena taje gaban Inna tana kuka tana cewa "Inna xan tafi Allah ya qaddara saduwarmu da alkhairi ki yafemun" Inna tace "meye na kuka? Kinyiwa kanki dama da kin xauna aure xanyi miki amma kinxabi kibi wacce batasan ciwon haihuwa xataje birni ta nemi kudi dake, in gaskiya ne mana ta daukeku tun kuna qanana sai da taga kin isa moruwa dayan kuma ya mutu wahala ta ragu sannan taxo? Allah ya raka taki gona" ta taso jikinta a sanyaye suka nufi tasha bayan anrakata kabarin Nura tai masa addua.
Wannan shine mafarin barin sakeena Qauyen Baggadano xuwa garin kano cikin unguwar Gwale. Wanda daganan rayuwar sakeena ta fara.
Hajia ☺
[7/31, 2:01 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
3⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Mal Lawan mijin Iya tsohon malamin makarantar qaramar secondary (retired) wanda bayan ritaya albashinsa ya gagareshi riqe gidansa duk da yana iyakar qoqarinsa amma ya gaza fansho ne kafin yazo ancinye rabi a bashi rabin kuma baya kai masa koda rabin wani watan ya qare wanda shikesa tilasa masa cin bashi. Wannan shine babban dalilin matansa suke sana a domin tagizawa da rage masa wasu wahalhalun.
Matansa 2 iya itace matarsa ta farko wacce suka kwashe shekaru basu haihuba kafin ya auro Hajara wacce yayanta ke kira da Hajjo wacce ta haifa masa yaya guda 2 maxa 4 mata. Hajjo ta raina qoqarin mal lawan akanta da yayanta don kullum cikin mita take, dan haka ta kama sana a haiqan tana saida gasarar koko kuma sanaar ta karbeta sosai amma duk da haka bata godewa Allah. Babban danta namiji ne me suna Nura wanda suke cewa Deni, sai saddiq , matan kuma Zara wacce aka aurar sai Hadiza fiddausi da kuma Amina autarsu. Duk da Fiddausi da Amina sun iya kitso da qunshi amma basu dau sanaar da wani mahimmanci ba sunfi gane xaman banxa da yawan bin maqota. Iya kuma itama tana sanaar yan qulle qullen kayan miya wanda ba wani abun azo a gani take samu ba. Matsayinta a gidan kuma irin matsayin matar da bata ajiye koda kwai ba a gidan da tarbiyya bata wadata ba, don sau tarima intai musu magana kan wani abu naba dai daiba sukan yimata dariya inta nuna jin haushinta uwarsu tai mata gorin haihuwa, mal lawan yayi iya qoqarinsa ya yaqi wannan abin amma kuma abin lura shine duk yadda namiji yakai ta tsari da tarbiyya inbai samu mace ta gariba wannan tsari bazai taba tasiri ba.
Iya dattijuwar macece mai kirkin gaske duk da in antabata tana da fada amma sau tari xakasamu fadanta akan gaskiya takeyi, tana da kirki da maida dan wani nata dan yayan mijinta ma haka ta daukesu nata ne tunda ita Allah be bata ba kafin uwar yayan tai tsalle ta dire tace bazata sabuba me haihuwa da naquda daban me iko daban dan haka ta janye yayanta daga iya. Duk da haka batai fushi ba takan gyara duk abunda taga yana buqatar gyara a matsayinta na babba a gida kuma Haman ya qara mata qima a wajen mijinta. Tsakaninta da zara Deni dai girmamawa ce don sun dauketa uwa, amma ta bangaren ragowar bata wuce yar shishshigi ba da shiga sharri ba shanu.
A dabi ance yawanci duk mutumin da be haihuba xaka sameshi me tsananin ibada. To iya ma dai hakan take abidar macece wacce baka rabata da nafilfilu dare da kuma rana ga azumin alhamis da litinin wanda da wahala ya wuceta.
Wannan kenan
**************
Sakeena ta saka qafarta a gidan tare da sallama me cike da kura kurai irin ta wadanda ilimin addini be ratsasu ba, iya itama tayo tata sallamar. Babu amsa duk da suna jiyo shewar mutane daga dakin dake kallon kofar shigowa gidan. Iya ta qarasa har qofar dakin ta daga labule tare da qara wata sallamar, hajjo ta amsa tare da tambayar iya ya hanya da qarin haquri? Ragowar yaran suka gaida iya da wata irin gaisuwar raini samfurin me sufurin. Sakeena dake bayanta da durqusa har qasa ta dunga aikin gaishesu daya bayan daya duk saboda kar ace tayi ba dai dai ba, suka dunga kallonta suna amsawa cikin kwaikwayar maganar ta qauyenci cike da shaqiyanci suna qunshe dariya. Iya taja hannunta sukai daki.
Gidane ginin bulo na xamani irin na mai rufin asiri, soraye biyu soron farko dauke da shagon samarin gidan sai soro na biyu wanda zai sadaka da cikin gidan. Dan tsakar gidan ba cika girma ba dan filin rabin fuloti ne, wanda hajjo ta cike fiye da kashi 2 cikin 3 da robobin gasarar. dakuna biyu ciki da falo iri daya sak masu matsakaicin girma mallakar iya da Hajjo sai falle daya na mai gidan kicin dan qarami sai bandaki guda daya tal wanda duk ahalin gidan ke amfani dashi.
Bayan sunci taliyar da iya ta bararraka musu don hajjo tace batasan xata dawo ba batai girki da ita ba, sukan taba hira suka kwanta don huta gajiya.
Sakeena tanacin tuwon dare a dakin iya yayin da iya kecan dakin mal lawan tana fada masa yacce ta wakana a Baggadano da kuma hukuncin da tayi na dakko riqon sakeena saboda halin data ganta ciki. Mutum ne me tawakkali da miqa lamura ga Allah yace "kin kyauta Hafsatu, ai riqon maraya lada gareshi Allah ya bani wuyan dauka" tayi masa godiya bisa hadin kan daya bata yace ta kira masa sakeena.
Bayan xuwan sakeena ta gaisheshi har qar shi kuma ya amsa cikin dattako yayi mata nasiha tare da yimata gaisuwar Nura. Ya kirawo yayansa mata guda 3 da kuma uwarsu hajjo ya gabatar da sakeena amatsayin baquwar da tazo zama dundundun da kuma roqon hadin kansu na taya shi da iya riqon marainiyar da babu uwa babu uba. Sunyi tsit dan babu lefi ya isa da gidansa ko xa ai rashin mutunci sai a bayan idonsa.
Bayan ya sallamesu sun fito sun bar iya aciki Amina ta bangaje sakeena wanda hakan yayi dai dai shigowar saddiq da kawo wutar lantarki lokaci guda. Sakeena data kusa faduwa saboda bangaxar da Amina tai mata tai saurin daidaita tsayuwarta ta duqa tana gaida saddiq. Ya kalleta ya kwashe da dariya yana kallon Hadiza yace "wannan goat dinfa daga ina?" suka kwashe da dariyar shaqiyanci jin ya kira sakeena da akuya, fiddausi ta tsaida dariyarta tace "daga England me dorawa kifin gidannan ta taho mana da ita wai ta dakko riqonta" sakeena dai batasan abunda ake nufi da goat ba balle ta damu, dataga saddiq ya wuce be amsa gaisuwarta ta tashi ta koma daki.
Ranar dai tayi kwanan dadi ita kadai akan gadon iya na katako a daki ciki da falo mai dauke da ledar tsakar daki a mulmule ga iskar fanka na kadata.
Mal Lawan na barin gidan Hajjo ta dasa mita yayin da agefe guda kuma take saida gasararta wa mutanen dake shigowa siya jifa jifa inda take cewa "haka kawai dan tsabar kyashi da mugunta yanda gidan nan yake har sai anje an dakkowa malam riqon wata dangin dangaro nasa iyalan ma da Allah ya dora masa dakyar yake iya dawainiyyarsu bare ankawo wata, dan kawai baki haihuba shine xakije dan mugunta ki dakko wata daga qauye dan a tauye nawa yayan" tafi qarfin minti 40 tana sakin maganganu makamantan wadannan, yayin da duk Wanda ya shigo siyan gasara idan meson jin tsegumine yakan tambayeta me akayi take wadannan kalamai ita kuma xata fada masa iya ce ta dakko riqon wata qazamar yarinya daga qauye.
Iya dai na daki tana lazimi kuma tanajinta yayin da sakeena ke baccin da iya ta tilasa mata bayan sallar asuba data tashi xatai aikin share share tace ta koma bacci in anjima tayi.
Har Hajjo ta gama saida gasararta tare da mitar zuwan sakeena Iya bata tanka mata ba. Ta karkade zaninta ta debe kudin cinikinta ta koma daki tabar tsakar gida kaca kaca da ruwan gasara wanda ya bushe ya xama fari da bokitan gasarar a tsakiyar tsakar gidan kuma dama haka takeyi kullum yayin da yayanta kecan daki na bacci sai sungama baccinsu tsaf wacce bata xuwa makaranta wato (Hadixa tayi candy) xata fito ta gyara gurin tana mitar Hajjo ta barta da aiki.
Iya ta tashi sakeena bayan shigar Hajjo daki, ta tashi da sauri dan dama baccin bawani dadi yake mata ba saboda rashin sabo. Ta fara shara tunda daga uwar dakin iya har tsakar gida ta share tas ta wanke tsakar gidan da ruwan famfon dake xuba kamar ya tsaga famfon tsakar gidan, ta wanke bandaki ta wanke qazaman bokitan gasarar Hajjo tas ta jeresu sannan ta wanke randa ta cikata da ruwa wanda kuma dai dai lokacin Hajjo ta fito. Ta kalli yanda gidan yayi tas a arabin awa, tasan ko ba a fadaba sakeena ce ta gyara dan nata yayan basayin ko shara ta dadin rai. Sai kuma tadanji kunya, sakeena ta sunkuya tana gaisheta ta amsa tana cewa sannu da aiki tare da cewa ga kokonki can da dumamenki a kicin. Sakeena tace 'to Allah anfana' ta dauka ta koma daki da nufin karyawa. Iya dake kallon sakeena tare da nazari tana godewa Allah da sakeena bata da San jiki kotanan ta samu saukin xama da Hajjo dan Hajjo macece meson ai mata bauta. Sai dai abu daya da Iya ta lura dashi sakeena nada qarancin tsaftar jiki don ko baki bata wanke ba balle tayi tunanin wanka gashi tana shirin cin abinci ahaka.
Ta kalleta a tausashe tace "sakeena baki wanke baki ba zakici abinci?" Ta dan diririce tace "ai banga gawayi ba" Ta dakko sabon brush ta matsa mata maclean tace tashi kije kiyi wanka ki wanke baki sai kixo kici abincin.
A bandaki ta dunga durzar jikinta da ruwan famfo da sabulu, ita kanta tanajin dadin yanda jikinta ke santsi ta gama ta fito ta tsuguna a bakin famfon tsakar gida tayi brush, ta miqe ta bude randa ta debo ruwa xatasha saboda kishirwar da takeji. Ya shigo cikin gidan riqe da nasa brush din a hannu daga shi sai singlet da dogon wando, kurbar ruwan sakeena da shigowar lokaci guda dan haka idonsu cikin na juna gabanta yayi wata irin muguwar faduwa ta fara tari babu qaqqautawa. Yana tsaye yana kallonta cike da kyamata, tarin yadan tsagaita ta ajiye kofin akan randar ta sunkuya tana washe yalayen haqoranta wanda take ganin wankensu da tayi yanxu ya isa yasa yellow din fita. Bai amsaba sai runtse ido da yayi ya qarewa qafarta me farce tsaqoqo da faso kallo kana jikinta xuwa qazaman haqoranta. Ya kwallah kiran "Hadixa" ta fito a gigice Hajjo na biye da ita dan ganin abunda ya sashi wannan ihun tace "gani yaya Deni" ba tare daya kuma kallon sashin da sakeena ke tsugune ba ya nunata da yatsa yace "meye wannan? Ina kuka samo wannan dirty girl din?" jin haka Iya ta fito tana bashi amsa da cewa "Nura yatace, diyar qaninace da yarasu shekarun baya na taho da ita jiya daga qauye" jin an ambaci suna Nura sakeeena ta qura masa ido cikin zuciyarta kuma tana maimaita sunansa Nura, suna mafi soyuwa gareta.
Ya kalli Iya yace "OH! Ai bansan ke kika kawota ba iya" ya juya ya kalli sakeena dake kallonsa kamar ta cinyeshi yace "ke karki kuma taba kofin gidannan daga nan har xuwa lokacin da wannan dirty mouth din naki zai samu tsafta" ya kai kallonsa ga Hadixa yace "wancan kofin na randa ta kafa baki ajiki a yardashi, sannan ki ware mata kwano da cokali nata da kofi karta kuma taba duk abunda akasan ina tabawa, ki kiyaye abunda nace" Hajjo ta fara sababi "a bar mata kofin dai ai baza a yarba, kuma ke sakeena kinajin abunda yace ko? To ki kiyaye domin saboda ke baza a takura dan masu gida ba, dan inbaki daina taba kayan gidanba yana iya dena cin abincin gidan lamarin da baxan yarda dashi ba" Iya ta bada amsa da "to Nura xata kiyaye" taja sakeena sukai daki cikin takaicin abunda Nura yayi duk da tasanshi da shegiyar tsafta da kyama amma abunda yayi ai be dace ba kuma a gaban sakeenar dan cin fuska kamar wata kuturwa?
***** **** ***** **** *****
Acikin sati dayan da sakeena tayi a gidan ya xamana itace me aiki, domin itace keyin duk wata ta hidima ta gidan tunda kan shara har wanke wanke har i xuwa wanke kayan gasarar Hajjo kuma safe da yamma take wannan aiki. Yayan Hajjo da daman basan aiki suke ba sai suka kuma sangarcewa suka qara gyara xama da miqe qafa xuwa yawan bin maqota. Kuma wannan hidima da take a gidansu bawai ta tsira daga iskancinsu bane, a a iskanci nanan daram daqam. Domin bata isa ta xauna ko kusansu ba duk da kasancewarta meson shiga mutane kuma sai tayi rashin sa a bata da farin jinin mutane sam tun a qauye bare kuma a birni. Duk kuwa da kasancewar Amina saar tace a haihuwa amma ko giftasu tayi sai sunyi mata dariya, ta rasa abunda sukewa dariya a tare da ita tunda yanxu dai ai tana wanka kullum tana wanke baki. Iya bata taba kyashin sakeena ke hidimar gidanba don tasan hidima a gida kamar xubin dashi ne gaba xaka dauka.
Wani abu da yayi ya mutuqar faranta ran Iya da sakeena shine: ranar da sakeena ta cika 13 dayz a gidan ya kawo mata takardar dauka a makarantar qaramar secondry da uniform da littatfai kayan makaranta dai rankatakaf. Sakeena ta dunga kuka tana masa godiya dan ta fidda ran xata kuma shiga aji. Iya ma bakinta yaqi rufuwa duk da tayi zaton haka, domin mal Lawan yayan wasu ma ya sakasu a makaranta balle sakeena domin shi mutum ne dayasan zaqin ilimi. Hajjo kuwa sai ta kasa shiru tace in sakeena ta fara makaranta waye xai dunga aikin gidan? Mal lawan ya bata amsa da cewa "sai ki dauki wata mai aikin"
Ranar Monday Sakeena anhade cikin uniform din makaranta, bakinta yaqi rufuwa, qafarta cikin safa da takalmi sandal. Jiya Iya tasata ta goge kaushin qafarta ta yanke farce, kanta kuwa ta wanke mata gashinta da bai cika yawa ba ta kitse matashi. Ta riqe littatafanta a hannu.
Tafe suke ita da Mal Lawan har office din principal, bayan anwa sakeena interview dan sanin ajin daya dace da ita aka fuskanci Sakeena kanta dai empty ne domin dakyar ta iya rubuta tarihin rayuwarta a qauye da harshen hausa me cike da kura kurai. Fisa alfarmar mal lawan kasancewarsa tsohon malamin makaranta ta samu aka sakata Aji 3 (j s s 3) dan tafi qarfin aji daya da biyu tare da yimata gargadin ta dage da karatu.
Amina Lawan ta saki baki lokacin da taga babanta da principal sun rako sakeena ajinsu. Home master ya shigar da sunanta a register mal lawan yace Amina fito ga yar uwarki. Ta fito saboda ganin idon Baba ta kama sakeena ta zauna a bencin su ya qara da cewa "ki koya mata abunda akai batanan kuma ki bata littafanki tayi aikin da akai batanan"
Amina baqin ciki kamar ya kasheta sakeena bama a makarantarsu kawai ba har a ajinsu? Meyasa Baba yake haka? Mal lawan har yakai qofar ajinsu sakeena tabi bayansa da gudu ta tsuguna ta riqe qafarsa tace 'Baba nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi." yana dariyar farinciki yace "amin sakeenatu ki dage da karatu sosai kinji shine gatanki"
Malamin daya shigo ajin ya buqaci ta tashi ta gabatar da kanta. Yayi mamakin ganin duk da kasancewarta baquwar yar qauye acikin aji amma ta bude baki tai bayanin kanta da sunanta kamar me fada a gidan radio.
Malamin na fita Amina ta hankadota daga kan desk din ta fadi qasa harta bata sabon farin hijabinta. Amina ta qara da cewa "ke har kin isa ki xauna guri daya dani? Banxa jaka yar qauye" yan ajin sika xagayesu suna kallo saboda sun dauka da gaske yar uwar Amina ce kamar yadda babansu ya fada. Monitor din ajin tace "ke Amina da alla ya xaki turota qasa ba gidanku daya ba?" ta yatsune fuska tare da riqe qugu tace "Allah ya sawaqe ta zama yar gidanmu, ni sunana Amina Lawan ita kuwa inaga ko sunan uba bata dashi yar aikin gidanmu ce babanmu ya sata a makaranta." monitor tace "indai kuwa hakane Babanku mutumin kirki ne, ke Sakeena koma desk din baya ki xauna tunda yar aikice ke ai bakya xauna kusa da yar masu gida ba. Wannan shine mafarin xaman sakeena a desk din qarshen aji, kuma shine dalilin daya qara dakusar da kwakwalwarta dan matsalar idonta bata bari ta iya hango rubutun da malami keyi harta kwafa.
Koda aka tashi daga skul Amina ta bawa Sakeena jakarta ta hada da tata tayi musu dakonta har gida wanda hakan shiya qara tabbatarwa yan ajin Sakeena yar aikice kamar yadda Amina tace.
A satin Sakeena na uku a gidan haduwarsu da Nura batafi sau 3 ba, dan lokacin da yake shigowa tayi bacci da safe kuma baya tashi da wuri har sai sun fita makaranta.
Nuran dai yana karatun HND ne a kano poly kamar yadda taji qannansa na yawan fada, dan gayu ne lamba daya duk da talakane liqis wanda ubansa ke hidimar karatunsa dan inganta gobensa. Kayan Nura na sakawa basufi set 6 ba amma kullum xaka sameshi tsaf dashi cikin wanki da guga ga kuma qanshin turaren da baya rabuwa dashi. A yanda sakeena ta fuskanta qannan Nura mata sunyi mutuqar dogara da wannan karatu nasa dan duk sanda ake xancen rayuwar jin dadi sakiji suna cewa ai in yaya Deni ya samu aiki yayi kudi zamuyi kaza, zamuyi kaza. Duk da duk sanda sukeyin irin wannan xancen Hajjo na yawan kwabarsu da cewa "ai ba sai lallai ya samu aiki zaiyi kudi ba, aikin gwamnati ai baya kawo kudi sai wahala. Banda abunku in Allah yasa ya auro yar gidan hamshaqin mai kudi ubanta ya buda masa harkar samun kudi ai sai mu warke" wannan shine maaunin da sakeena ta auna taga gaba daya Hajjo da yayanta sun dauki Nura a matsayin kadara wanda suka alaqanta jin dadin gobensu gareshi.
Karo na hudu da sakeena taga yaya Deni lokacin suna xaune ita da iya a kofar daki da safiyar lahadi ta bishi da kallo babu ko qiftawa kamar yadda ta saba. Baiji kunyar idon iya ba ya juyo ya doka mata tsawa tare da cewa "wai ke cutar kallo ce da kene? da alama inkina kallon mutum har manta kanki kike, to daga yau karki kuma sakewa inkamaki kina kallona" har yayi gaba kan Sakeena na sunkuye.
Iya taji haushi ta rufe Sakeena da fada, "inbanda abunki sakeena meye abun kallo a gurin mutumin da ya hanaki taba kayan gidansu? Canake saboda shi yanxu komai naki a gidannan daban yake kamar kuturwa" sakeena dai shiru tana sauraren fada iya a bangare guda kuma tana kallon Nura asace.
Adan satittikan da sakeena tayi a gidan ta fuskanci matsalolin gidan, abu na farko dai shine mal Lawan a halin yanxu driver ne a wani gidan me kudi wanda yake jigilar kai yayansa da dakkosu daga makaranta, saboda haka kudin da ake bashi dasu yake tagixawa yayi hidimar iyalansa kafin xuwan fansho a qarshen wata. Duk da abincin gidansa babu dadi amma kuma gidansa babu yunwa sam. Yawanci kudinsa kan tafi akan karatun Nura, saboda haka baya iya bawa yayansa kudin makaranta na kashe kuma shiyasa yake sakasu makarantar kusa da gida inda babu xancen kudin mota dan bashi da wannan halin. Amma kuma yana biyan school fees da sauran hidindimun littafai Hajjo ita ke bawa yayanta kudin makaranta (kudin break) wanda a duk sanda xata bayar sai tayi mita.
Wannan itace matsalar sakeena ta farko, domin iya bata da qarfin da xata dunga bawa sakeena naira 50 kullum domin cin abinci a makaranta. Dan jarin kayan miyan da take saidawa ba taka kara yayi ya karya ba. Sakeena dake gwanar hankali ce saita fuskanci matsalar kuma ta nemi shawarar Iya da ko xasu fara wata sanaar sai ta dunga fita tallah ko kuma ta dunga karbo wankau? Iya ta balbale sakeena da fada da cewa "Sakeena ki shiga hankalinki kisan inda yake miki ciwo, nan birnine ba qauyeba da xaki dunga yawan tallah da girmanki, kuma sanaar wanki ba Sana'a bace sanyi kan iya shigarki da quruciyar, ke macece baki da qarfin da xakiyi aiki dan biya kanki dukkan buqatun rayuwa ilimi shine kawai hanyar da xai kwaceki kuma shine gatanki dan haka ki dage da karatu" bayan hakan Sakeena batai zuciya ba taitabin iya da nacin su fara koda yajin siyarwa to da haka dai iya ta yadda sakeena ta daka yajin daddawa dana barkono suke siyarwa kuma ana ciniki babu laifi.
A bangaren makaranta kuwa abun babu dadi, domin sakeena ko tari bata isa tayi ba saboda Amina, ta takura mata sosai, in anfita break ita ke siyowa Amina da qawayenta abincin break ta kawo musu har aji sannam taje nata break din. Ga wani suna da suke fada mata a ajin wai me 40 (wato me shekaru 40 kafin ta waye tunda daga qauye tazo) tun bata gane abunda sunan ke nufi ba harta gane. Babu wanda ke kulata a ajin saboda qazantar dake danqare a bakinta ragowar masu tausaya mata kuma tsoron Amina ya hanasu kulata. Wata qawar Amina me suna Alawiyya ta taba fada mata cewa indai tanaso su daina takura mata to saita wanke wannan yellow din daudar dake bakinta. In antashi daga makaranta kuma a qa ida jakar data Amina ita ke dakonsu xuwa gida.
A bangaren sakeena dai ta rasa dalilin da yasa wannan dattin na haqoranta yaqi fita duk da kullum tana brush amma yaqi barinta wanda ta gane saboda shi mutane da yawa suke kyamarta. Gadai qafarta ta rabu da faso da kaushi, sannan kuma kanta ma duk sati iya na sake mata sabon kitso. Da abun ya isheta saita tambayi Iya dan Allah me xata saka a bakinta dattin ya fita? Iya ta kalleta da tausayawa tasan akwai abunda akaiwa sakeena ya sosa ranta tace "Sakeena kiyi haquri da inada yadda xanyi da munje asibiti anwanke miki haqoranki bazai wuce 2000 ba dattin dake bakinki ya farune saboda rashin wanke baki da bakyayi tun abaya sai ansa inji an kankare miki amma yanxu ta abunda xan baki kici a makaranta nake" wannan magana itace ta zaunawa Sakeena daram aranta ta quduri aniyar duk randa ta samu 2000 tata ta kanta xataje a wanke mata bakinta ta huta kyamatar da ake mata duk da tana ganin 2000 garinsu da nisa.
suna xuwa islamiyya kullum da yamma 4-6 kuma tana gane karatun sosai kodan iya tana mata bita ne a gida oho.
Bata cika wata 2 ba a makaranta akai jarrabawar qare zangon karatu na biyu (end of second term exam) wanda sakeena ta dauki ta qarshen aji kamar yadda take a bencin qarshe. Bata wani samu maki ba ko kadan har gwanda a hausa ta samu 30/100 a ragowar darussan kuma yawan kan jaki ta samu. Amina ta kwace result din sakeena da aka raba musu ta bude kowa yagani a ajin suka dunga yimata dariya suna mata ihun jakar ajin lamarin daya saka sakeena kuka haiqan. Kuma wannan yasa sakeena ta xama ware a ajin bata da qawa to a fadar Amina wazai qawa da daqiqiya?
Hajia ☺
[7/31, 2:01 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
4⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Mal Lawan ma dai baiji dadin ganin result din sakeena ba ko kadan duk da yasan bazatai abun arxiqi ba kasancewar anmata tsallaken aji har biyu sannan gashi bata da background na karatu amma kuma be zaton mata faduwa haka wanwar ba, ya bata rai sosai yace "sakeena ya haka? Ya kike nema ki bani kunya? Ana yawan fadan yayan qauye sunfi na birni kaifin basira ke ya aka samu haka daga gurunki?" ta qara qarfin kukan da takeyi tun daxu tace "Baba kayi haquri wlh duk bayanin da ake mana da turanci akeyi ni kuma banajin turanci shiyasa" dake malami ne saiya gane matsalar sakeena wato ba rashin basira bane matsalarta turanci ne matsalarta da xa ai mata da yaranta xata fahimta. Yace "to dakko littattafanki inga abunda ke ciki" ta tashi ta kawo masa, ya dunga budawa yana gani kansa a daure rubutun dake ciki tsilla tsilla wani shafunma head line ne kawai. Da mamaki yake dubanta kanta a qasa yace "yaya haka kuma? Rubutun ma baki iya kwafa?" tace "Baba a baya nake xama kuma idona yayi ta ruwa bana iya ganin rubutun dake kan allo" daya matsata saita fada masa yadda akai ta koma xaman baya. Ransa ya baci sosai, yayi mata nasiha me ratsa jiki na ta dage da neman ilimi dan ita din bata da gata saina ilimi. Daga ranar ya saka xaman karatu da xasu dungayi da sakeena duk bayan isha inta dawo daga islamiyya da suke xuwa tsakanin magrib da isha.
Hutun yayiwa sakeena dadi sosai, da safe bayan ta gama aiyukan gida takan xauna karatun da iya ke koya mata na addini. Da rana kuma suyi hidindimun gida in iyace take girki. Da yamma kuma suje islamiyya xuwa shida, da anyi magrib su kuma xuwa wata islamiyyar sai bayan isha su dawo daganan xatai sallah taci abinci lokacin mal lawan ya dawo suyi xaman karatun boko xuwa 9:30 pm. Yayi amfani da hikima da kwarewa irinta tsohon malamin makaranta yana koyawa sakeena karatu da irin method da yasan xata gane. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu da yake tasa ranta xata iya da kuma ciwon wulaqancin da amina tai mata. Sai dai Baba (mal lawan) kamar yadda suke kiransa ya fuskanci matsalar ido na mutuqar addabar sakeena dan insuna karatun yadda take qura ido dan ganin abunda yake koya mata ko kuma idon yayi ta ruwa, ya tausaya mata kuma yasan matsalar idon tana buqatar asibiti amma kuma shi bashi da yadda zaiyi ya temaketa. Sakeena ta dage dan so take ta fita kunyar Baba kuma tanaso akanta itama taji tana turanci.Da asuba inta idar da sallar asuba bata komawa bacci kamar yadda yan gidan keyi, takanyi bitar karatunta ne na boko dana arabi abunda taga bata ganeba takan tambayi iya ko Baba.
Iya ta fuskanci sakeena nada nasibi domin kasuwar saida kayan miya ta bude sosai. Sakeena ke mata dakan yaji, kuka kubewa da kalkashi da sauransu su quqqula su siyar kuma sanaar na rufa musu asiri babu lefi tunda har tana saiwa sakeena yan kayan gwanjo ta saka.
Yammacin lahdi suna xaune kowa a tsakar gida yayin da iya kewa sakeena kitson komawa makarantar da zasuyi gobe Monday gefe guda kuma sunajin labaran yamma a freedom "mu leqa mugano" sakeena tace "Iya, a rayuwata inaso inji ina karanta labarai a radio ko a TV" iya tana dariya tace "Allah sakeenatu? 😄 kice wata rana dai muryarki xanji a gidan radio?" tace "in shaa Allahu Iya bama muryata kadaiba har ganina sai kinyi a gidan TV" kafin Iya ta bata amsa Amina tayi caraf tace "dake cewa akai miki da irin kwakwalwarki ta kifi ake xama me karanta labarai ko?" Hadixa dake danna waya ta sheqe da dariya tace "au kice diskindarine ce" Amina tana tata dariyar tace "diskindarine lamba 1 ma kuwa" suka hadu suka dunga dariya da izgili. Hajjo na jinsu tana ganinsu amma tai bakam kamar bata gurin, Iya ma tai musu shiru hakama sakeena amma a ranta tasa cewa in shaa Allah xata dage da karatu kodan ta wuce gori.
Ranar Monday Baba har makaranta ya raka sakeena ya fadawa principal din matsalar Sakeena ta raunin ido. Suka tashi har ajin shida home master din ajin ya zabarwa sakeena gurin zama a desk din gaba inda indai akai rubutu xata gani kuma yace dokarsa ce duk wacce ta canja mata gurin xama zai koreta.
Suna bada baya cikin sakeena ya qulle dan tasan yau xataci gidansu gurin Amina gashi ita kuma Allah ya dora mata tsoron Amina kamar mala'ikan daukar rai. Aikuwa xatonta ya xama gaskiya suna fita Amina ta taso ta dungure mata kai tana cewa "sai dai azabar miki kujerar gaba amma kwakwalwa dai ta kifi ce kuma ba xaman gaba ne qoqari ba. Kiyi karatun mugani" sauran daliban dake sit din gaban suka tashi suka barwa sakeenan gun dayar tana cewa "wlh gara in haqura da xaman gaba da inxauna da wannan qazamar intai magana kota bude bakinta kamar inyi amai nake ji" daga haka sit ya zama na sakeena ita kadai dan ta rasa me xama kusa da ita, ta sakata sosai hakan ya mata dadi kuma duk aikin da akai tana qura ido ta kwafa tana kuma ganewa babu laifi.
A duk sanda Nura ya shigo gidan kuwa danyin wani abu takan sunkuyar da kanta cikin faduwar gaban data rasa dalilinta domin tun sanda yayi mata warning bata qara yadda sun hada ido ba, kuma duk sanda ya shigo jikinta zaita karkarwa ta kasa koda motsi har sai yagama abunda yakeyi ya fita.
Suna cigaba da karatu da Baba kullum wanda hakan ke tagixa mata sosai.
Wata ranar asabar da safe ta ta gama aikinta da wuri dan bata koma bacci ba, bayan tayi karatun asuba saita zarce da aikinta ta gama komai har wankinsu ita da iya, Hajjo kawai take jira ta gama saida gasara ta gyara gurin. Tai wanka taje ta shirya cikin t shirt din da iya ta sai mata da zani ta fito domin daukar dumamenta a kitchen ta tarar Amina ta kwaso uniform dinta data gama wankewa yanxu ta shanya ta watsar a qasan tsakar gidan cikin ruwan gasara acewar Aminan wai kayan sun tare mata hanyar shiga bandaki inxata wuce saita sunkuya. Hajjo na kallonta tai wannan abu amma batai magana ba.
Sakeena ta qulle sosai tace"haba Amina yanxu fa na gama wankewa kika xubamun a qasa ai da saikiyimun magana inkwashe ko" Amina daman da tayi hakan ne dan Sakeena ta tanka mata dan wani irin tsanar sakeena takeji kamar ta kasheta. Ta hayayyaqo tace "an xubar din dan ubanki, nida gidanmu har kin isa ki takurani banxa jaka akuya me kwakwalwar kifi sai aikin wankin uniform kwakwalwa bata ja" Sakeena jin anxagar mata uba batasan sanda tayi kan Amina ba, ita kuma daman Aminan abunda take jira kenan dan tafi sakeeena girma tana ganin xata daketa.
Suka fara kokawa sosai, da Hajjo taga sakeena ke jibgar Amina sai tai kururuwa wai azo sakeena xata kashe Amina wanda ihunta ne ya fito da Iya wacce ke sallar walaha da kuma Hadixa da Fiddausi wadanda ke baccin asara. Su Hadixa sukai kam sakeena da duka babu xancen raba fadan, Iya ta fara hawaye tana basu haquri amma ko gixau, ga mamakin Hajjo sai taga duk da sun rufarwa sakeenar su ukun amma basufi qarfinta ba dan fada take daga zuciyarta Amina ta qure haqurinta. Dukanta suke itama dukansu take tun qarfinta. Saddiq hayaniyarsu ta tasheshi daga bacci ya shigo cikin gidan babu bin baasin abunda ya faru ko kuma lura da cewa yan uwansa sun rufarwa sakeena ita kadai, kawai ya samu sakeenan ya kai mata wani mugun duka da qafa tai gefe guda ta fadi. Ya kuma tunkararta yayin da Hajjo ke cewa "yawwa dakarmun abar banxa inkinfi qarfin mace ai bakifi qarfin namiji ba" iya tai saurin shan gabansa da bokitin qarfe a hannunta idanta jawur taci kuka ta daga boiktin tace "wlh inka kuma dukar ya saina kwala maka wannan bokitin, kai mahaukaci ne baka gani yan uwanka sun tarar mata? Kun hadu kuna dukan marainiya"
Deni ya shigo gidan jikinsa sanye da jc ya dawo daga motsa jiki. Ya tambayi baasin meya faru yaga gidan haka a ya mutse? Iya tana kuka ta fada masa duk yadda akai, ya qara tambayar fiddausi tace suma kawai sunga sakeena da Amina na dambe suka shiga. Ya matsa ya sharewa Iya hawaye ya kama kafadarta da hannun sakeena yakaisu daki yace "Iya kiyi haquri xanyi hukunci in shaa Allah hakan baxata kuma faruwa ba kedin uwa ce a garemu sakeena kuma qanwarmu ce" ya tashi ya fita.
Sakeena dai tunda Nura ya kama hannunta, taji wani irin baqon lamari tattare da ita jikinta yayi wani irin sanyi lakwas kamar bata da laka. Haryagama maganganunsa ya fita bata tsinci ko kalma daya ba, saida saki sannan ta maida idonta kan inda ya riqe a hannunta ta dunga kallon gurin kamar Nuranne maqale a gurin.
Yana fita ya ciro USB a dakin Hajjo yayiwa su fiddausi Amina da Hadixa dukan kan me uwa da wabi, Hajjo na bashi haquri da fada masa Amina ce da lefi bai kulata ba saida yaga sun daku sosai sannan ya kyalesu tare da yi musu kashedi da jan kunnen su guji yin hayaniya a gida nan gaba ko cin zarafin sakeena take musu bautar gidansu da suka kasayi. Sannan su guji xubar hawayen Iya. Ya juya ga saddiq yace "kai kuma kana namiji maimakon ka raba dake kai wawa ne saika biye musu ko? Kaiwa kanka kuma kanka kake xubarwa da girma dan inbananan kaine babba" ya juya ya koma dakinsa dake soro.
Tun daga haka Nura ya kwatarwa Sakeena yanci a gidan suka dawo xaman lfyar dole da ita tunda itama sunji da qarfinta, sannan kuma ta dena yiwa Amina dakon jakarta. Lokacin da Aminan ta bata jakarta don ta kai mata gida ta tsaya sheqeqe ta kalli aminan tace "wannan lokaci nayi miki dakon jaka ya wuce dan nagane ke bakisan mutunci ba kuma na dena tsoronki dan kedin xakin roba ce damisar takarda" Amina tayi qus don tasan karansu da sakeena bazaiyi dadiba. Mu amalar sakeena da yan aji kuma tanan kamar da babu me kulata.
Ranar wata alhamis suna xaune babu islamiyya, Fiddausi na yiwa wata mata da tazo gurin kitso. Yaron matar dan kimanin wata 9 sai rigima yake, sakeena ta daukeshi sai jijjigashi take tana zarya ta kyar yayi shiru ta goyashi yayi bacci.
Bahijja tana lura da sakeena tun daxu tunda ta shigo gidan bata xauna ta huta ba sai kaiwa da kawowa take cikin kuzari tana aikin gidan, ta qudure wani abu a ranta. Koda aka gama mata kitson sai tace sakeena ta biyota da Waleed (sunan dan nata) ta rakata gida, gidanta babu nisa sosai layi dayane tsiransu dasu sakeena.
Gidan dan flat me kyau sosai, sai dai da alama matar gidan tana da son jiki dan kaca kaca gidan yake tiles din har ya dafe saboda qazanta. Sakeena ta sauke dan ta juya xata fita, tace "Dan dakata mana sakeena xo ki xauna magana xamuyi" sakeena ta xauna a darare gabanta na faduwa kome ya hadata da wannan yar gayun? Bahijja ta katse shirun ta fara magana "sakeena dama ba wani abu bane na lura da nutsuwarki ne shine nace indai kinaso sai kixo in daukeki aiki, duk wata in dunga biyanki." Sakeena cikin xumudi tace "to Anty xanyi amma wane irin aiki?" Bahijja cikin jin dadin ta samu baiwa a ruwan sanyi ta gyara xama tace "xaki dunga yimin shara da wanke wanke duk wata xan dunga baki 3000" sakeena tai saurin cafe xancen tace "wlh xanyi Anty, amma ina xuwa makaranta kuma xanje in fadawa Iya inta yarda sai inyi" Bahijja tace "karki damu nima ina xuwa aiki, in kin dawo makaranta nima na dawo aiki sai kixo, yanxu sai kije ki fadawa maman naki abunda tace kixo ki fadamun"
Sakeena tana rawar jiki ta zayyanawa Iya yacce sukai da Bahijja, Iya tai shiru bata tanka ba har akai sallar magrib sannan ta kira sakeena cikin nutsuwa tace "Sakeena ba hanaki neman halak xanyi ba, amma ina gudun abunda xaije ya dawo kuma kedin marainiyace wacce na dakko amanarki, xan fadawa malam abunda yace sai muji amma ki kula ban cika san harkar masu kudi ba saboda munajin yadda mazansu da yayansu ke bata yara yan aiki, ki kula ki kare mutuncinki"
Bayan dogon dauki ba dadi mal Lawan ya amince da aikin sakeena a gidan Bahijja da mai gidanta Barrister Adam, duk da yasan Barrister mutumin kirki ne amma Saida yaje da kansa ya kuma danqa musu amanar sakeena ya fada musu kuma marainiyace.
Sakeena ta fara aiki a gidan Anty kamar yadda yake kiran Bahjja tana da yaya Hudu duk maxa 3 na makaranta sai wanda take goyo. Sakeena ta fuskanci Anty irin matannanne masu kafirin lalaci wanda hakan yasa ta xama qazamar qarfi da yaji. Randa sakeena ta fara aiki a gidan babu inda bata wanke ta goge ba a gidan ta yini tana aiki gidan yayi qal.
Jadawalin aikin sakeena shine, a ranakun makaranta sai antaso daga boko take tafiya gidan Anty wato da azahar taje tayi aikinta harta taya Anty girkin rana, sai 3:30 ta dawo gida tai sallah ta tafi islamiyya tana dawowa qarfe shida xata koma gidan har xuwa lokacin tafiya islamiyya kafin lokacin xatai qoqari ta qarasa duk wani aiki da bataiba sannan ta dawo gida, in sunje islamiyya sun dawo kuma tai sallah taje karatu gurin Baba har xuwa 9:30 ta nemi makwanci wanda a lokacin ta gaji tiqis, da asuba bata komawa bacci xatai bitar karatukanta kafin tai aikin gida tai shirin makaranta. A rana kun weekend kuma takan tafi gidan Anty ne tun safe da zarar ta gama aikin gidansu wanda har yanxu ba a dauke mata ba. Hakan yasa Sakeena bata cika xaman gidan ba.
Ranar da wata ya cika kwana 30 aka bawa sakeena kudinta na aiki dubu 3000 tare da sabulai da kuma kwancen kaya da anty ta bata. Murna gurin sakeena ba a magana ta bawa Iya kudin. Iya tace 'sakeena ai kudinki ne kiyi yadda kikeso dashi' tace "Iya so nake dama ki kaini asibiti a wankemun haqurina da kudin" Iya tace "to sakeena ai haqqin kine ranar litinin sai muje inkin dawo daga makaranta"
Ranar litinin sukaje asibitin murtala, bangaren dental suka biya 2800 huka hau layi. Akaxo kan sakeena ta shiga, mutumin ya haska bakinta ya saka safa yace "ki daure sosai bakinki yayi datti da yawa sai an kankare dakyau amma fa da xafi" sakeena tace "duk zafi xan daure, inaso a dena kyankyamina" yace "yawwa yata ki daure in wanke miki tas" ya fara kankare mata bakin yana jini ta daure kamar yadda tace, ita kanta da aka nuna mata dattin da aka wanko a bakinta saida taji kyama. A qarshe dai sakeena baki yayi tas haqora har daukan ido suke, aka nuna mata mudubi tai dariya sai taji ta burge kanta lokacin da taga jerarrun qananun haqoranta a mirror. Aka saka mata dokar wanke baki da daddare inxata kwanta da kuma da safe.
a ranar dai sakeena duk inda ta shiga sai dariya kamar anmata kyautar miji.
A wannan term din babu lefi sakeena ta tabuka dan taxo ta 36 acikin su 54. Baba yayi murna kuma ya qara qarfafawa sakeena gwiwa. Da aka koma hutu aka canja aji su Sakeena an shiga SS 1.
**** **** **** **** *******
A hankali Bahijja ta maida sakeena baiwarta kamar yadda ta qudure a zuciyarta, da farko aikin sakeena a gidan shara ne da wanke wanke sai kuma taya ta girki. Amma daga baya saita qara mata da rainon Waleed da kuma wankin uniform din yaranta na makaranta kullum. Abu yacigaba a watan sakeena na 5 tare da ita taga sakeenan ta fara wayewa ga kuma tsafta ta fara kankama a jikinta tana kuma kwalliya da kayan data bata saita kori almajirin dake musu wanki duk kuwa da ba ita ke biyansa ba, sannan wankin ya dawo kan sakeena kullum xata wanke kayan da yaranta 4 suka cire sannan ta qara mata da girkin gidan wanda ta koyawa sakeenan tun farkon xuwanta kuma ta iya. Ya kasance kullum tana cikin aiki koda tayo kwalliyarta daga gida intaxo ta fara bauta xaka nemi kwalliyar ka rasa kuma duk a 3000 duk wannnan tarin aikin. Bahijja kuma tayi hakane saboda kar mijinta yaga sakeena da canjin abincin yasa ta xama mace sosai ya kyasa shiyasa kullum tana cikin ruwa tana aiki. Tsakanin Sakeena da Barrister kuwa girmamawa ce irinta bawa da uban gida, dan in yana gidan iyakarta tsakar gida da kitchen a dokar anty Bahijja sai ya fita take da hurumin shiga falo. A bangaren yaran Anty kuwa sakeena bata da matsala ta jasu a jikinta kuma suma basa kyamarta sukan yi mata magana da turanci kamar yadda sakeenan tace su dunga yimata dan ta iya, inbata ganeba su fassara mata. Wani lokacin Alhaji babban dan anty har karatu yake koya mata.
A bangare guda kuma Iya ta tsani wannan aiki na sakeena dan bata da lokacin kanta kullum cikin bautar Bahijja take da danta Iya ne da sakeena ta dade da barin aikin nan duk kuwa da irin temakon da aikin kewa musu amma Iya dake babbace me hankali ta fuskanci yadda Bahijja cikin hikima take dakushe sakeena dan karta samu miji ta bar bauta mata.
Bata taba gajiyawa da aikin da take ba duk kuwa da tasan tana yini akan qafafunta cur, hakan na nufin rashin wayonta ko rashin sanin ciwon Kai ne? Kudin aikinta suna toshe mata abubuwa da dama duk kuwa da qanqantarsu, aciki take temakon Baba da rage masa nauyin siyan sabulun wanka ko man shafawa duk wata dan tana tausayin dattijon me qoqarin ganin ya sauke nauyin iyalansa amma kuma hakan nafi qarfinsa saboda tsadar da kayan masarufi suke shiyasa kullum al amarin gidan qara damewa yake. Acikin kudin dai takan dora jarin Iya na kayan miya Inya nemi karyewa, A gefe guda kuma takan dan ajiye wani abu a banki domin tunkarar matsalarta ta ido don abun na damunta sosai. Bata da matsalar abinci don ta samu cima me kyau a gidan Anty dan ita Bahijja sam abun hannunta be dameta ba duk abunda akaci xata ajiyewa sakeena nata, saboda haka safe, rana, dare sakeena nada kwano a gidan kuma abinci be kyau intaga dama taci acan intaga dama ta taho dashi suci da iya wani lokacin har su Hajjo kan samu dan sakeena ke xubawa kanta abinci inta gama kuma koxata kwashe duka Anty bazatai magana ba tawannan bangaren bata da matsala. A duk sanda Iya tayi mitar bautar da Sakeena kewa Bahijja tayi yawa sakeena kanyi dariya tace "iya aini ma ina morarta, ta bani abinci sau uku a rana babu geji, ta bani kwancen kayanta harda su turare inta rage duk tabani ta bani sabulu in wanke kayana da naki sannan ta koyamin girki wanda ke kanki kinji dadin hakan, sannan yayanta su koyamun karatu qarshen wata a bani 3000 kuma da sallah suyumin dinkin sallah. Nikam kome xan mata ban fadi ba kuma ban taba daukan bautar da nake mata mugunta ba, a dalilin haduwata da Anty wadanda suke kyamata sun xama qawayena Iya kiyi haquri wataran sai labari, aikin nan yana rufa mana asiri" A bangare guda kuma ba tun yauba Sakeena ta gane ta fada soyayyar yaya Deni irin makauniyar soyayyar nan wacce ake yinta babu ji babu gani, ada bata fuskanta ba amma tun randa ya raba fadansu dasu Amina ya riqe mata hannu ta gane tana sonsa kamar ta cinyeshi duk kuwa da qaracin shekaru irin nata. Abun na damunta duk kuwa tana mutuqar qoqarin dannewa amma hakan kan faskara a duk sanda taga yaya Deni jikinta kan kama rawa babu ji babu gani kamar mazari ga faduwar gaba a duk sanda taji muryarsa ko aka ambaci sunansa. Amma kash! Ta fuskanci Deni yana mantawa ma akwai wata halitta me sunan sakeena a gidan. A waje guda kuma tana ganin wani gagarumin yaqi a gabanta a duk sanda asirinta ya taunu tanasan Deni. Mutumin da uwarsa da yawansa suke burin ya auri yar hamshaqin me kudi dan su huta sukaji SAKEENA ABBAKAR LIMAN na azabar sonsa wacce a gurinsu take wulaqantacciyar yar qauye kuma baiwar Bahijja kamar yacce suke kiranta yanxu.
Duk sakeena na wannan tunani ne yayin da take kan hanyarta ta dawowa gida daga gidan Anty don xuwa makarantar islamiyya ta yamma. A fili tai magana bayan gama tunaninta a inda take cewa "To inma nidin baiwar Anty Bahijja ce kamar yadda yawan mutane ke fada sai me? Nidin ai ba wata tsiya bace da xan damu dan na xama baiwar wacce ta fini ku..., " maganarta ta katse yayindata kwabxa karo a dai dai qofar dakin su saddiq, ya riqeta yayin datake shirin kaiwa qasa ya girgaxa kafadunta yace "ke mahaukaciya ce? Kina tafe kina magana ke daya ba dole ki buge mutane.... " shima tasa maganar ta katse lokacin da ya tsinci manyan idanun sakeena cikin nasa xuciyarsa tai wata irin bugawa, ita dai sakeena batasan sanda ta washe masa fararen jerarrun haqoranta ba. Yayi gaggawar runtse idansa tare da sakinta ta fadi qasa shi kuma yayi waje. Ita dai sakeena tun daga lokacin har ixuwa kwanciyar baccinta ta jita cikin wani irin nishadi wanda tunda Allah ya halicceta bata taba jin irinsa ba, lokaci xuwa lokaci takan yiwa kanta murmushi ta shafa kafadarta gurin da hannun Deni ya taba tai dariya. Iya dake lura da ita tun daxu tai tsaki tace "sakeenatu! Anya kuwa lfyarki yau? Tun daxu kike dariya ke kadai sai magana nake miki kin share ni" tai saurin dawowa hayyacinta tana sunne kai tace "Yi haquri Iya banji ki bane, dama mafarki nayi naci jarrabawar qualerfiying"
A wata na gaba Deni ya tafi kwara state (illori) bautar qasa, ranar daya tafi sakeena ta labe a bandaki taci kukanta kuma tundaga ranar ta samu kanta cikin kunci, bata magana sai ta xama dole in antambayeta tace bata da lfy a lokacin ta lura soyayyar Deni itace qaddararta kuma akwai qalubale a gabanta babba.
Kamar yacce yake ga al adar mace me irin shekarunta itama tayi samari, duk da in akaxo sallama da ita ba fita take ba sai Iya ta tilasa mata amma itama iya daga baya ta daina tilasawa sakeena fitar tun bayan da sakeena ta xauna tai mata bayanin yawancin masu xuwa gurinta ba santa suke ba da yawa daga ciki in sunxo suna amfani da talaucinta da suka fuskanci sakeenan na cikine suna tallata mata soyayyar watsewa wanda hakan yasa ta tsani wani ya bude baki yace yana sonta.
Ana haka jarrabawarsu ta qualafyn ta fito cikin rashin sa a sakeena dai bataci ba, yayin da Amina kuma taci wanda hakan ke nuna sai anbiyawa sakeena kudin jarrabawar NECO da WAEC daga aljihun babanta taci kukanta dan tasan bata da gatan da xa a biya mata yayin da Amina dadi kamar ya kasheta dan tana ganin qarewar karatun sakeenan yaxo.
Baba ya rasa inda xaisa kansa akan matsalar kudin jarrabawar sakeena dan yanajin kunya ace ya kasa biya mata wannan kudin yarinyar da tasan ta dauke masa wata wahala amma shi tata tazo ya kasa tabuka wani abun kirki? Dan haka yaje gurin Alhajin da yakewa aikin driving ya roqe ya ranta masa kudi wanda yace ya dunga diba duk wata a albashinsa na har yagama biya. Dake yaji harkar karatu ce ya bashi babu musu.
A gefe guda kuma Iya da sakeena na nasu kokarin inda aka fasa bankin sakeena amma abunda yake ciki bekai ko rabin kudin jarrabawa daya ba kamar yadda suka xata. Sakeena yau a gidan aikinta jikinta a sanyaye qalau lokaci xuwa lokaci tana share hawayen yankewar karatunta ko kuma maimaita ajin SS 2. Alhaji babban dan Anty ya ganta tana kuka yaje ya fadawa Anty. Bayan dogon lallashi da ban baki dakyar anty tasha kan sakeena ta fada mata matsalarta.
Sai data gama aikinta tsaf ta dauki kwanon abincinta wanda damuwa ta hanata ci xata tafi gida Anty tai kiranta ta amsa kiran anty ta bata qunshin kudin da batasan ko nawa bane tace "gashi sakeena kyauta na baki kije ki biya kudin jarrabawa, duk sanda kike buqatar temako a kan karatu ki fadamun xan temaka miki ki dage da neman ilimi dan muma dashi muke taqama" godiyar da Sakeena tayi har saida anty tace ya isa ta taho gida cikin wani irin farin ciki da kwarin gwiwa da farin ciki take fadawa Iya. Itama Iyan taji dadi wannan abu da Bahijja tai ya faranta ranta kwarai. Da Baba ya xauna cin abinci suka sameshi da wannan xancen shima yayi murna kwarai kuma ya ciro kudin daya karbo ya bawa sakeena yace shima ga nasa temakon sakenna ta dunga kuka tana masa adduar gamawa da duniya lfy, suka hada kudi 30k wanda hakan ke nuna sakeena ta samu kudin jarrabawa guda 2 wato waec da neco a memakon su Amina da gwamnati ta biya musu kudin jarrabawar WAEC kawai. Amina dai murna ta koma ciki Sakeenan datake rainawa ta fita, dama haka lamarin ubangiji yake.
Baba da kansa yaje biyawa sakeena kudaden jarrabawar ya kawo mata receipt. Suka kuma durfafa karatun jarrabawar kammala secondary.
Wannan alheri da Bahijja taiwa sakeena ya kuma saka sakeena tsunduma cikin bautar Bahijja ka in da na in yayin da Bahijjan ta kuma sakankancewa ta miqe qafa ya xama ita da gidanta kofi sai taga dama take daukewa komai Sakeena keyi mata. Yayin da gefe guda kuma Barrister mijin Anty yake saka ido a duk lamuran sakeena da irin bautar da takewa gidansa da yayansa ba tare daya bari shashar matarsa ta gane yana da alaqa da wanzuwar sakeena a gidan ba, dan ita a ganinta tana da wayo yayin da ya raina wayonta kuma yake amfani da nasa wayon da kwarewar aiki cikin nata wayon.
Hajia ☺
[7/31, 2:01 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
5⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Yau sun tashi da baquncin Deni zai dawo bayan kammala Bautar qasarsa a kwara, yayin da su Sakeena suke dab da fara fara xana jarrabawar kammala secondary.
Dake wata yayi 20 ya xamana babu kudi a hannun Baba, tun safe ya fita da nufin samo dan abunda ya sawwaqa asamu a dafa kodan dawowar Deni bai dawo ba sai bayan laasar ya shigo jikinsa a sanyaye dan haka ya gama gararinsa bai samo komai ba. Hajjo naganinsa hannun babu komai tai kicin kicin da rai tace "Tun dazu nake jiranka ga magruba ta kawo kai ko karfanfana babu a gidan balle abunda yarannan xaici inya dawo" jikinsa a sanyaye yace "wlh Hajjo tun daxu nake yawon neman abunda xan kawo muku bansamu ba, Dan Allah ki ranta kudi ayi duk abunda xa ai inasamun fansho na xan baki" tai saurin katseshi da cewa "bani da ko sisi kudina tun jiya nasai geron gasara dashi, kuma ai muguntarka akan yayana yake tashi canike kwanaki haka kawai dan san gwaninta ka dauki kudi ka biyawa sakeena kudin jarrabawa amma ni yanxu nawa dan ya tafi shekara guda yau xai dawo amma ko ruwan naira 5 baka siyo da sunan inyaxo yasha ba" ta qarasa tana hawaye. Jikinsa ya qara sanyi domin shi ba a son ransa dansa xai dawo amma babu ko kwayar hatsi da xa a dafa a gidansa. Iya dakejinsu tana cikin daki ta tattaro duk cinikinta ta fito ta miqawa Baba tace "gashi malam iyakacin abunda yake hannuna kenan kayi haquri" ya karba yace "Allah yayi miki albarka Hansatu" ya miqawa Hajjo yace "gashi asamu ko shi kadai a dafawa taliya yaci, mu kuma bari inkuma fita inga abunda hali xaiyi" ta harari kudin tare da cewa "ni kuma Allah ya tsine min ko? wlh bazan karbi kudin kishiya ba taji dadin yimin gori" ya ajiye kudin yafita lokacin ana kiran sallar magrib.
Sakeena dai dake yau alhamis tana gidan Anty tundaga tasowarta daga makaranta har yanxu da ake sallar magrib, da kyar ta yakice aikin taje tai sallah ta dawo tana lazuminta na HASBUNALLAHU da Iya tace ta dungayi kullum da magriba 313 da asuba ma 313. A gefe guda kuma tana duba girkinta yayin da Anty da yaranta kecan falo suna kallo. Abun na Anty babu ko shaawa keda gidanki ace kin koma kamar baquwa sannan mutum tun qarfe daya yake tsaye yana miki bauta kamar inji. Sakeena na gama girki ta juyeshi a kula takai kan center carpet din falo ta ajiye tare da kawo ragowar kayan cin abinci ta jera taje ta tsuguna tana wanke kayan da tai amfani dasu. Tun dazu ya shigo yake tsaye yana kallonta duk da alamar gajiya a tare da ita dan ta yini tana aiki amma hakan be nuna ba a yanayin kazar kazar dinta. Ya lura yarinyar kyakykyawace irin kyan da saika nutsu xaka ganshi ba tafar daya ba, kuma yanaga shine dalilin Bahijja na takura mata da bauta dan ta dakusar da kyan nata. Ta dago bayan ta gama wanke wanken gabanta ya yanke ya fadi ganin Barrister a tsaye yana kallonta, ta tsuguna tana yimasa barka da dawowa. Bai amsa ba sai qara kafeta da idonsa da yayi, sakeena taji duk ta takura duk da doguwar riga ce a jikinta burmemiya wacce Anty ta bata kuma ta hana a rage mata ita acewarta maje gaba ce. Ya miqo mata tulin ledojin dake hannunsa masu dauke da tambarin gidan abincin JALSA tasa hannu xata karba ya hada hannunsa da nata hannun ya riqe tare da ambatar "SAKEENATU" tai saurin sakin ledojin tai kicin tana haki ta dafe kirjinta. Batasan iya lokacin data shafe a gurinba sai ji tai Anty na kwala mata kira. Ganinsa a xaune a kusa da matarsa kamar bashi ya riqe mata hannu yanxu ba yasa gabanta faduwa kodai ya fada mata abunda ya faru yanxu? "sakeena dauki kular abincin nan ki tafi da ita gida, kinga dear yayo mana take away" maganar Anty ta katse mata tunanin ta, ta janyo ledar kayan daya siyo ta dibawa sakeena kayan kwalam dangin su burger da shawarma sai gasashshiyar kaza ta hada mata da kwalin chivita tace "ga naki, sai da safe ki gaida Iya gobe ki tahomun da bushashshiyar kubewa tuwo xaki mana gobe" da sauri tabar dakin bayan ta dauki ledar da kular abincin saboda kallon da Barrister ke binta dashi.
Baba dai har aka kira sallar isha yana neman abunda xai kai a dafa a gidansa amma bai samu ba, sai bayan ya idar da sallah ne ya yanke shawarar xuwa wurin wani mai kanti domin karbar bashin garin rogo da suga duk kuwa da tsanar karbar bashi da yayi amma kuma inya duba iyalansa nacan na shirin kwana da yunwa sai yaga gara ya karya billensa ya karbi bashin. Yana rabe a gefen kantin yana jira mutanen dake siyan abu su ragu don yana jin kunyar fadar abunda ya kawoshi a gabansu kuma be xama lallai mai kantin ya bashi ba saboda tun wata yana da 10 yake cin bashinsa kamar yadda aka saba wanda xuwa yanxu kudinsa sun taru akansa sosai.
Sakeena na tafe tana tunaninta, me abunda Barrister yayi mata yake nufi? Shima dan iska ne kamar sauran maxan da ke neman yan aikin gidansu ko me? Amma bataiwa Barrister zargin hakan dan anata tunanin in akace ta fadi maza masu halin kirki yaya Deni shine no 1 a gurinta bayan shi kuma Barrister ne na 2. Harta gota Baba tana tunani bata ganeshi ba, har tayi gaba sai kuma ta dawo ta matsa kusa dan ta duba ko shidinne kuma meyake a dai dai wannan lokaci da akasari anfi samunsa a gida cikin iyalansa. Babu wutar lantarki shiyasa saida taje dab dashi ta shedashi, ta rage tsawo tace "sannu Baba, baka tafi gida ba?" yace "yawwa sannu sakeenatu andawo daga aikin ne?" tace "eh har na wuce na ganka nace bari injiraka mutafi gida tare" ya danyi shiru kafin yace "kayya sakeena da kin tafi tunda nasan a gajiye kike, ni ina jira aragune in karbo mana abunda xamuci" wani irin tausayin dattijon ya dirarwa sakeena, lallai Baba mutumin arziqi ne a wannan zamanin masu hali ma ba duk suka damu da sauke nauyin iyalansu ba bare mara hali. Tai qasa da murya tace "Baba kaga taho mu tafi taja hannunsa," babu musu ya bita dan shi dinma ya gama yarda da halin kirkin sakeena. Suna tafiya a hankali tace "ai Baba basai ka karbo komai ba, kaga abinci na taho dashi daga gidan aikina bayan nagama me gidan yaxo musu da abincin otel shine sukace intaho da wanda na dafa ka ganshi?" ta fada tana nuna masa kular. Yace "to Alhamdulillahi kuma zai ishemu sakeena?" tace "sosai kuwa Baba ai cikin kular ne riqe kaji" yana dariya ya daga kular cikin yabawa da quruciyar sakeena mai cike da nutsuwa. Ta nuna masa ledar tace "wannan kuma kaza ce a ciki da wasu kayan yan gayu" yayi dariya suka rankaya gida. Kamar tare suke da Deni yana shigowa suma suka shigo, aka kacame da murnar dawowarsa. A taqaice dai a wannan dare dai fried rice din da sakeena taxo da ita daga gidan Anty akaci aka qoshi harda kazar da aka bata Iya ta rarraba.
Sakeena kuwa sai satar kallon Deni take wanda a wata 11 da tai bata ganshi ba babu abunda ya ragu daga soyayyarsa dan yana daya daga cikin dalilinta na qin kula mane aurenta dan ta rasa da wane ido xata fara kallon wani namiji daba Deni ba, ta rasa da wace zuciyar xata fara son wanin Deni, bata da wannan qarfin halin ko kadan. Tana cikin azabar soyayyar me matuqar wahala wacce batasan ta inda ta shiga ba balle tasan hanyar da xata fiddata. Ta lumshe ido dai dai lokacin daya gifta ta kofar dakin Iya ta shaqi qamshin turarensa mai qarancin kudi cikin sanyin murya ta furta "Nuraddeen" wannan furuci karaf a kunnansa yayin da yake shirin fita. Ya juyo ya kalleta idonta a lumshe batasan ma yana gurin ba, tabbas xatonsa ya xama gaskiya wannan yarinya ta dade da fadawa tarkonsa. Yayi shuumin murmushi ya fita yana cije lips dinsa a ransa yana cewa "tsuntsu daga sama gasashshe"
A washegarin dawowarsa suna xaune da safe suna shan hantsi saboda yanayin sanyi da aka fara, Amina kewa Fiddausi qunshi saboda bikin qawarta da akeyi kuma yau da yammaci xasuje luncheon. Fiddausi ta kalli Amina tace "Amina yanaga kinamun wani abu kaman bishiyar dogon yaro? So nake aimin dan banxan qunshi kinsan mijin nata me masifar kudine kuma abokansa xasuxo luncheon din inasone nima insamo nawa mijin a cikinsu mu warke" Amina ta harareta tace "da Allah malama ke gajen haquri ne dake ki bari mana kiga nagama inbe kyauba sai kiyi qorafi" ta qarasa tana murguda baki kamar ba fiddausi ce gaba da ita ba. Hajjo dake uwar banxa ce sai tace "ke Amina kiyi mata me kyau kinji ko? Kema intasamo me kudin ai a dadinki, dama nagaji da wannan xaman naku rida rida babu miji kema gashi kina shirin gama makaranta" Amina ta zunburo baki tace "to Hajjo wazai ganmu yace yana so bamu da kaya? Ai yanxu samari basa kula macen da bata da kaya" Hajjo tace "amma ina iya qoqarina akanku ko? Duk jarina ina yake tafiya? Ko kun taba kawo anko banyi muku ba?" Hadixa dake gefe guda tana danna waya tayi kwafa tasaka baki cikin xancen tace "ai de yaya Deni ya gama karatu, in shaa Allahu ya kusa samun aiki mu huta wannan talaucin, Hajjo da kike cewa munqi aure ai yanxu ba a auren diyan talakawa" Fiddausi ta dora da cewa "ai wlh in talaka ma ya haifeka ya cuceka, da ana bada xabi yaushe xaka xabi gidan talaka a matsayin gidan ubanka?" Sakeena dake yankewa Iya farce ta shiga cikin hirar da cewa "ku godewa Allah, haka Allah yaso ya ganku kuma banda abunku ina lefin Baba? Yana iyakar qoqarinsa akanku. Ni ina fatan inama na girma da nawa uban koda gyartai ne inkirashi da BABA in nunashi a ko ina ina alfari da ubanane" Amina ta katseta da cewa "to monitan dawanau uwar yan tsari munji rufe mana baki munafuka wai ita me hankali, bazaki burgeni ba sai kin auri gyartai tunda naki uban be xama gyartai ba sai ki xama matar gyartai" Sakeena da yanxu bata cika ragawa Amina ba tace "wlh wanda nakeso ko yafi gyartai qasqanci ina sonsa a haka kuma indai shima yana sona kamar yadda nake sonshi to a shirye nake da in zauna dashi koda xan kwan da yunwa nidai kawai abunda nasani ina sonsa qarshen soyayya" a tare da fiddausi da Hadixa suka hada baki wajen cewa "wanene wanda kike so din? 😳" Sakeena tai fiki fiki da ido kardai ta saki layi har sun harbo jirginta tanason Deni? Dariyar Amina ta katse mata tunani a inda tana dariyar tace "kuma dai in banda abunku wannan kucakar ce tasan wata soyayya? Itafa wannan babu abunda tasani sai bautar gidan Bahijja, kun tsaya kuna kula shirmenta. Ai kawai Allah ya kawo mana me kudi lokaci daya mu tashi mubarta dan wannan kan asamu me kwasa za a dade kullum tana yawo burum burum cikin kwancen kayan Bahijja" da wannan magana ta Amina aka rufe hirar.
A hankali Deni daya koma xaman gida yanxu yake lura da duk wani taku na Sakeena, kuma ya tabbatar da Sakeena tayi zurfi cikin soyayyarsa. Yana yawan qarewa haluttun jikinta kallo a sace. A wani dare yana kwance yake qissima yanayinta. Sakeenan a yanda ya lura bata cika tsahoba duk da baxa a kirata gajeriya ba. Tana da dan murjajjen jiki babu rama kuma qiba bata samu maxauni ba ko kadan, a kalar fatar jikinta fara ce duk kuwa da wahala tana dusasar da farar fatar tata amma ga alama intasamu jin dadi farin xai qaru sosai. A fuskarta kyakykyawa ce irin kyan dabai cika gari ba, ma'ana kyawun nata sassanyane komai na fuskarta kamar jikinta matsakaici ne inka dauke idanunta da suke manya sosai wadanda su suke bayyana hadinta da wata qabilar bayan qabilar Fulani. Abunda yafi jan hankalin Deni gareta kuwa shine xubin halittar jikinta duk da qoqarin boye baiwar halittarta da Bahijja keyi hakan be hana Deni da Barrister gano body structure din Sakeena ba. A cike qirjinta yake taf duk kuwa da yarintarta kuma abunda yafi jan hankalin Deni kenan, wannan dalili yasa da wuya ka ganta babu mayafi ko hijabi koda a tsakar gidane. Yanda qirjinta yake haka qugunta yake shima Masha Allah kasancewar tana da zafin nama shiyasa da wuya tayi tafiya qugunta be kada ba. Wannan itace sakeena Abbakar Liman yar shekaru 17.
A gefe guda kuma Barrister ya matsawa Sakeena kwarai da yawan kallo, ko kuma tana aiki ta tsinceshi kawai a kanta yana kallonta. Ita bata iya rashin kunya ba balle tayi masa kuma tasan koda wasa bata isa ta tunkari matarsa ta fada mata ba saboda azabar kishin Anty, bayan hakan kuma Barrister ai ya kusa haifarta a haife domin first born dinsa Alhaji xaikai 15 years. Tagaji kwarai da wannan takura ita a rayuwarta tanason qimarta da mutuncinta ta yarda tasa kowace irin wahala amma ta tsira da mutuncinta bataso ko kallonta namiji yayi balle kai hannu jikinta don iya ta riga ta gama tsoratar da ita akan halayyar maxan wannan xamani da kuma qalubalen da macen data xubar da mutuncinta take fuskanta.
Kamar yadda ya saba sai ganinsa tayi a qofar kicin din a tsaye yana aikin kallonta tana yanka salad, wata irin fargaba ta shigeta cikinta ya kada. Ta nemi hanyar guduwa yasa hannu ya tare, ya kamo habarta ya sunkuyo dai dai fuskarta ya matse mata baki ya daure fuska tamau yace "ke ki kiyayeni, ki kalleni ki fadan abunda ke zuciyarki kina sona?" sun dade a haka idonta a runtse shi kuma yana riqe da fuskarta yana kallonta, daga baya ya saketa ya fice a kicin din. Yana fita ta fito ta nufi gida ba tare da taiwa Anty sallama ba, bata kuma kammala aikinta ba, tana tafiya tana share hawaye dan tasan ta rabu da aikin gidan kenan gara ta haqura tunda abun na Barrister yakai ga haka tunkan abunda takeji a radio na bata yan aiki ta afku a kanta.
Babu kalar tambayar da Iya batai mataba meya dawo da ita yanxu, tace bata da lfy ne. Bacci a daran kam sai dai barawo tana fara baccin xataji muryar Barrister yana tambayarta "kina sona?" washegari ta shirya ta tafi makaranta inda suke practical din jarrabawar WAEC, bayan dawowarta taci abinci ta miqe ta kwanta Iya ta tambayeta baxata gidan aiki bane tace "banajin dadi" ala dole Iya ta kyaleta bayan ta tilasa mata shan paracetamol.
Yan aiken Anty suka dunga zaryar kiran Sakeena amma taqi ko motsi yayin da Iya ke basu amsar sakeena babu lfy fa. Daga baya Anty taxo da kanta dan ta kasa koda dora abinci balle gyaran gida yaran ma sai indomie Alhaji ya dafa musu. Ta tasa sakeena a gaba sukaje asibiti aka aunata aka samu malaria wacce ba a rasa yan Nigeria da ita aka hadota da magani sukai gida. Washegari dole sakeena ta koma aiki bisa tilasawar Iya da nacin Anty.
Da wuri ta tafi saboda basu da jarrabawa, ta dunga aiki cikin sauri a planing dinta ta gama kafin lokacin dawowar Barrister kamar yadda ta dau matakin guje masa. Tayi sa a biyar da rabi ta gama aikinta kaf har girkin dare tayi ta wanke kwanikan ta bawa Anty uxurin cewa xataje gida tayi karatun exam ne.
Wannan matakin shi ta dauka kuma daga lokacin basu kuma haduwa da Barrister ba. Da wannan ta Saki jikinta a ganinta ta tsira.
**** **** ****** **** ****
Nuraddeen Lawan ya kasance dogo namiji irin tsawon maxan hausawa wato ba wani tsahon kuxo ku ganiba. Wankan tarwada, ba wani kyakykyawa bane amma gayun yasa ake ganinsa a matsayin wani handsome. Ya tara saje a fuskarsa wanda shine sirrin kyansa, dan kimanin shekaru 31 da haihuwa. Nura yayi karatu sosai dan ya tallafawa talakan ubansa ya karanta public administration ya samu shedar kammala HND me daraja ta farko wato first calss, amma ga dukkan alamu samun aiki xai masa wahala kamar yadda yakewa diyan takwarorin irinsa talakawa.
Yawanci saurayi me shekaru kamar nasa koban fadaba kunsan yana buqatar abokiyar rayuwa (matar aure). Nura a raayinsa yafison mace yar gayu ma'ana me kyale kyale, be damu da auren diyar me kudi ba kamar yadda uwarsa ke yawan kwadaita masa shidai kawai falleliyar mace kyakykyawa kuma yar gayu wacce ta iya daukan wanka wayayya kamarsa wacce xata iya bayyana masa soyayyarta a ko in kuma a gaban kowa. Wannan kalar mace itace xabin Nura. Amma kuma yana hasashen mafarkinsa baxai xama gaskiya ba duba da cewa shi ba kowa bane sai talaka dan talaka wanda be ajiye ba kuma bai bawa wani ajiya ba, wanda ake bashi abinci sau uku a gidansu. Wace yar gayun macece xata soshi a haka?
Tunda ya lura sakeena na sonsa sai ya shedan ya qissima masa tunda bai samu abunda yakeso ba kuma baya tunanin zai samu anan kusa me xai hana tunda ga me sonshi a gida ya dunga rage xafi a gurinta? Xai yaudareta da soyayyar bugi saita fada saiya bijiro mata da buqatarsa, ya yadda da wannan saqa da shedan yayi masa duk kuwa daba halinsa bane yin hakan. Amma sai wata zuciyar ta raya masa ai babu komai daga baya ka tuba ,ai a masu shekaru irin naka kadanne suke tsallake zina. Da wannan tunani ya kwanta yana shafa fuskarsa yana ayyana qirar sakeena da take boyewa, a wani bangaren kuma yana ganin game din bazai nisa ba sakeena xata sakar masa komai duba da yadda ta mace a kansa.
Sanyi ya kankama, yau antashi dashi sosai kamar snow xata xubo daga sama, sakeena ta kasance mejin sanyi a yanayin halittarta batason sanyi ko Kadan amma ya xama dole ta fita neman halak. Ta dakko robarsu ta man shafawa Habiba da nufin yin daqale ta lakace ragowar man ciki Wanda ko fuskarta be isheta shafawa ba bare jikinta. Ta rufe robar ta xura hijabinta tana murxa idonta daya kwana yana mata qaiqayi har ixuwa yanxu gashi wani dishi dishi take gani ko ta dunga ganin shudi a cikin idon, ta nemi fita daga dakin aranta tana qissima itama da san samune ta qudundune a gado yadda kowane dan gata yakeyi a lokaci irin wannan amma ina! Ita Allah be qaddara mata rayuwa irinta yayan gata ba. Iya tace "ungo" ta waiwaya ganin me iyan ke bata, gwangwanin man gyada Iya ta miqo mata tare da cewa "karbi wannan man gyadan ki dan mutstsuka a hannaye da qafafunki ko wannan waskanan ya ragu tunda man shafawar ya qare" ta karba ta tsiyaya ta shafa kamar yadda Iya ta umarceta sannan ta fita.
A tsakar gida ta tarar da Amina tana brush, Aminan ta kalleta sheqeqe tace "Baiwa xa'a tafi ne?" Sakeena ta bata amsa da cewa "Eh xantafi me xaman banxa" kafin Amina ta qara wata magana Baba dake daki yake jinsu yace "Yawwa da kyau sakeena, yi tafiyarki neman halak tunda baki dorawa kanki girman kaiba duk tsiya kinfi mai xaman banxa" Amina tai qus, sakeena kuwa ta tafi cikin jin kunyar shigar mata fadan da Baba yayi duk kuwa da yarsa takeyi.
Anty da yayanta harda mijinta na qudundune a daki, kasancewar weekend ne. Yayin da sakeena take xaune cikin muku mukun sanyi tana wanke wanke, haqoranta na hadewa saboda sanyi lokaci xuwa lokaci takan sosa idanunta da suka kada sukai jajur hancinta ya toshe saboda iska kanta kuwa kamar xai fashe saboda ciwo.
kamar yadda ya saba yana tsaye a jikin window din dakinsa yana kallonta, ko bata fada ba yasan sanyi takeji. Ya duba uban wanke wanken gabanta ga tulin wanki a gefe wanda ke jiranta intagama wanke wanken, ga wankin bandakuna ga girki. Yayin da Bahijja kecan cikin blanket tana qudundune. Ya qara qurawa sakeena ido ta cikin net din window yaga yadda fatar jikinta ta yamushe ta bushe kamar ta tsohuwar data shekara bataga mai ba, inbe qarya ba sai yace hannayen sakeena har baqi sukai da fashewa saboda tsabar aikin ruwa, kyakykywar fuskarta kuwa duk waskane ya fito babu kyan gani kamar fuskar almajiri bata mace ba, yana iya gano yadda jikinta ke rawar sanyi yayi tsaki tare dajin wani abu a ransa. Ya saki labule ya nufi dakin Bahijja. Ya furta "this is too much" afili.
Kamar yadda ya xata tana cikin bargo tana bacci ga room heater ta dumama dakin. Ya yaye bargon tare da bugun cinyarta yace "ke Bahijja tashi xamuyi magana" ta mutstsuke idonta jin ya ambaci sunanta tace "magana kuma dear? Maganar me kenan?" direct ya dauko topic din "Abunda kike sam bai dace ba Bahijja kiji tsoron Allah, ki Kalli sakeena a matsayin qanwarki ba wai be aikinki ba. Bautar da yarinyar nan take miki tayi yawa, ki tuna marainiyace aka bamu amana, ki dubi Allah ki rangwanta mata ayyukan gidannan ki tuna Bahijja muna da haula kodan haka ya kamata mu gyara dan bamu da tabbacin xamu rayu da namu yayan" kallonsa take ido a qanqance cikin tsabar masifa tace "dakata Adam, da xakaxo ka tasheni ka dirarmun da masifa sakeenar ce takai qararka gurina?" yace "a a kawai na duba yanayinta ne na tausaya mata tulin aikin da kike sakata" ta katseshi da cewa "to malam ka shiga taitayinka, babu ruwanka dani da kuma sakeena, kudi nake biyanta take mun bauta ba kyauta takemun ba, kuma ai bakaine kake nemar mun kudinba ko kuma biyanta. Ka dauke idonka daga sakamun ido kadai burinka kaga gidanka fes da naga baxan iyaba nasamu wacce xatai inbiyata, to kuma meye naka na saka ido???" yace "haka kikace ko? Ke wato bakyason gaskiya? To wlh xan dau mataki, kuma ko wane lokaci daga yanxu xan iya yanta sakeena ta kowacce hanya" ya juya xai fita, ta daka tsalle ta dira gabansa tana haki tace "Adam meye dalilin wannan hayaniya da sanyi safiya? Meye dalilin lullubeni da fada akan wata banxa sakeena yar qauye? Meye dalilinka na cewa tausayinta kakeji?" ya qurawa fuskar matar tasa ido kamar anan xai karanto amsar. Bahijja tai murmushi da tafa hannu tace "son sakeena kake ko Barrister Adam?" ya xaro ido cikin wata irin faduwar gaba ya maimaita "son sakeena kuma???" ya juya yabar dakin har yana tuntube Bahijja tana cewa "Ba fita xakaiba tsayawa xakai kaban amsa munafuki, itama daya munafukar bari infita in taddata"
Hajia ☺
[7/31, 2:02 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
6⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Tayi zarya yafi sau shurin masaqi da nufin fita ta katsawa sakeena rashin mutunci amma xuciyarta na kwabarta da cewa dakyar ne in sakeena nada masaniyar abunda Barrister yayi don, kuma inta yadda ta bata rawarta da tsalle ta hanyar yiwa sakeena rashin mutunci wazai cigaba da yi mata wannan bautar da sakeena ke mata? Da wannan shawara ta danni zuciyarta amma ta qudure xata kafawa sakeena tsatstsauran mataki domin daqile baraxanar cin amanarta da Barrister ke shirin yi.
Koda sakeena ta kammala duk aikinta taje yiwa Anty sallama ta fuskanci canjin fuska a gurin Anty ta dade a duqe a gabanta tana maimaita kalmar "Anty nagama aikin xan iya tafiya ko xa ayi miki wani abun?" amma Bahijja tai mata banxa tayi kicin kicin da rai tanawa sakeena wani irin kallon qasqanci. In banda namiji dan iskane kuma kwadayayye meya gani a jikin wannan kucakar yarinyar sakeena da bata rabo da tsamin dauda har yake sha'awa? Wannan shine tunanin da Bahijja keyi lokacin da sakeena ke gabanta tsamo tsamo a jiqe kamar yadda take yini aikin ruwa.
Anty ta karkada qafa ta murxa yatsunta biyu suka bada sautin "das" abunda yasa sakeena dago kanta xuwa kallon Anty tana nuna sakeena cikin tsoratar ta fara magana "Sakeena na daukeki a matsayin qanwata uwa daya uba daya shiyasa ban miki shamaki da ko ina a cikin gidana ba, to ina mai jan kunnanki karki sake inkamaki da lefin cin amanata, inma kin qudure wani abun ko xa a hada kai dake a shatalemun qafa gara tun wuri ki fadamun dan wlh duk randa na kamaki da lefin cin amanata sai qona wannan farar fuskar taki da ruwan batir "
Tunda ta fara magana cikin sakeena ke bada sautin qulululu, tana tunanin kardai Anty ta gano mijinta na binta kicin ko yana kallonta? Kodai ta fadawa Anty gaskiyar Barrister yana tare ta har yana riqe mata hannu? A a bazata fada mata ba dan xancen ruwan batir din da Anty tace xata qona mata fuska dashi ya tsoratata kwarai. Tsawar Anty ta katseta inda tace mata "tashi ki ban guri" ta miqe tayi waje da azama tana hardewa.
Yana ganin fitowarta shima ya fito daga cikin mota ya rufa mata baya, yana bayanta yayin da ita kuma take xabga sauri kamar yadda ta saba. Saida suka shiga layinsu sakeena inda ba mutane sosai sannan ya matsa gefenta tare da cewa "wannan sauri haka Sakeenatu kamar xaki tashi sama? Ke ko irin yangarnan ta mata baki iya ba?" ta juyo a razane jin kamar muryar Barrister, tayi mugun gani domin shidinne mutumin da yanxu aka gama yimata warning a kansa. Da qarfi ta furta "Innalillahi Wa'inna ilaihi raju'un" ta xura da gudu bata tsaya ba Saida ta shiga soron gidansu.
Barrister ya saki baki yanabin sahun sakeena da kallo bayan ta gudu, ya juya ya koma cikin motarsa ya xauna tare da dora kansa akan sitiyari yana tunanin sakeena. Ada can ya dauka tausayin sakeena yakeji har yake tunanin zai aureta ya bata ingantacciyar rayuwa duk da sunan tausayi. Amma kuma abunda ya faru daxu da safe tsakaninsa da Bahijja akan sakeena maganar Bahijja ta haska masa abunda ya manta wato kalmar so, Bahijja ta tunasar dashi tausayi fa saida soyayya yake samun gurbi, kuma shima daya nutsu bayan taqaddamar saiya tsinci sassanyar soyayyar sakeena a qasan zuciyarsa. Ya shafa sumar kansa ya furta "tanxz thank u vry much Bahijja domin haukan kishinki ayau yayimun rana tunda ya fassaramun karatun zuciyata"
Sakeena xaune a dakin Iya a tsorace, kimanin mintina 17 kenan da shigowarta. Iya ta dubeta cikin tausayawa tace "Sakeenatu" tai firgigit ta dubi Iya da cewa "mexan miqo miki Iya?" tai tsaki tace "ba cewa nai ki miqon komai ba kawai kiranki nayi, kinzo kinsamau guri kin takure ki tashi mana ki cire wannan jiqaqqun kayan jikinki." Iya taci gaba da mitar cewa "ni wannan aiki naki wlh bana sonsa dandai ba yadda xanyi ne, yarinya qarama dake kullum kina cikin ruwa kullum jikinki da danshi Allah ya kawo miki miji kije dakinki ki huta sakeenatu"
Bayan gama tuwon dare Iya ta dora mata ruwa cikin tukunya akan garwashin yayi xafi rau, Iya tace "sakeenatu fito kixo ki wanke jikinki ko kya daina jin sanyin, tunda da safe ba samu kike kiyi ba" sakeena da har yanxu take a tsorace ta sabe kayanta ta fito da daurin qirji ba tare data rufo komai a kafadunta ba kamar yadda ta saba saboda da taga magrib tayi duhu ya fara xuwa. Deni dake tsugune a bakin famfo yana alwala ya bita da wani mayataccen kallo, kamar yadda ya xata idanunta shi suke kallo ya sakar mata murmushi. Tayi mamaki karo na farko Deni ya sake mata fuska harda murmushi, tai saurin janye nata idon cikin kunya saboda ganin kallon da Nura ke mata babu ko qiftawa, ta dauki ruwan xafin ta shige bandaki tana bitar murmushin da Nura yayi mata.
Washegari haka sakeena tayi aikinta gidan Anty cikin kyara da hantara ga qarin wasu ayukan da Anty ta qirqira kamar xubar da yawu akan tiles din daki ko yin amai a dalilin qaramin cikin da take dashi. Duk wannan bai damu sakeena ba don hantara da tsawa tafi damunta dan ita a rayuwarta taqi jinin hantara ko tsawa hakan na tsikar da xuciyarta sosai. Wajen kwana 3 kenan anayin hakan, Barrister kuma rabonta dashi tun randa ya biyota hanya ta gudu.
A ranar kwana na 4 ne bayan gama aikinta tayi gida da kwanon abincinta tuwon shinkafa miyar zogale, tasa kanta a soron gidan sukai kacibiz da Deni yana rufe kofar dakinsa. Yayi mata murmushi kamar yadda ya tsira a yan kwankin nan, itama ta mayar masa ya matso gefenta yana leqen kwanan hannunta yace "haj sakeena me aka samo manane?" tai saurin miqa masa kwanon tana cewa "tuwon shinkafa ne yaya Deni karbi kaci" yayi dariya yace "a a ni na qoshi jeki kici abinki. Yanxu xanje kallon ball ne inna dawo da wuri xakixo dakina tayani hira?" tayi murmushi cike da jin kunya ta shige cikin gida. Shima muemushin yayi amma na samun nasara ya furta "first stage" ya fita yana tunani, inbanda hauka da shirme irin na baqauyiya sakeena inashi ina ita? Shi dan gayu wanda duk talaucinsa be taba yarda kudin turare ya gagareshi ba, meyin wanka 3 ko 2 arana. Yayin da ita takan yini a tsaye tana bauta wankan ma ba kullum take samuba, yanxu haka data shigo saida yaji tsamin gumi a tare da ita, fatar jikinsa a matsayinsa na namiji tafi tata kyau nesa ba kusa, amma wai danta rainawa kanta hankali shi take tunanin xai dating dinta koma ya aureta dan tsabar yaudarar kai.
Iya tana gama tuwo sakeena bata bari ta dora mata ruwan wanka ba kamar yadda ta saba, ta fito ta dora da kanta. Yanayin dumi ba tare da yayi zafi ba tayo shirin wanka ta fito hannunta dauke da brush. Iya ta bita da kallo saroro tace "sakeena yau kene haka da axamar wanka harda wanke baki?" ta danyi turus ganin Iya na shirin ramfo jirginta tace "um ai sanyi nakeji ne shiyasa nakeson yin wankan ko sanyin zai ragu" Tace "ai saiki bari ruwan yayi xafi sosai ki gasa jikinki amma yanxu kam ai dumi yayi."
A daddafe Sakeena ta bari ruwan yayi xafi dan ta matsu tayi wanka dan kar Nura ya dawo ya kirata hira kamar yadda yace ya sameta kaca kaca, ta fiso ya ganta tsaf. Ta salle jikinta tsaf tayi brush, tana idar da sallar magrib ta shafe kaf jikinta da mai har bayanta da cinyoyinta da Iya ke yawan shan fama ta shafa mai tanaqi yau dai albarkacin Deni ta shafa. Ta saka kwalli duk kuwa da bata sakawa saboda idonta ruwa yake ta saka jan janbaki ta dakko humrar da Anty ta bata ragowarta tun watan jiya amma bata taba sakawa ba yau ta saka a jikinta da hammata atamfarta ta sallah nouvo riga da zani da Baba yayi musu sallar data gabata ita ta saka wacce rabonta da sakawa tun a lokacin bikin sallar. Tayi daurinta me acuci ta qame guri guda ta kasa kunne kwarai tana jiran dawowar Deni ta hanyar bude kofar dakinsa.
Iya da tunda sakeena ta fara kwalliya take binta da kallo har ta gama ta magantu da cewa "tubarkallah diyata kinyi kyau, da halama dai xanyi baqon siriki kuma naga kina yidashi tunda aka dandasa masa irin wannan kwalliya. Yanxu da kina irin wannan kwalliya ai da yan matan gidannan basu miki gori ba dan basu fiki kyau ba gyara kawai suka fiki" Sakeena tayi murmushi taji kunyar maganar iya na cewa xatai baqo tace "to Iya ni ina naga lokacin kwalliya kullum ina gidan aiki inna dawo kuma dare yayi?" Iya tace "Eh to kema kina da gaskiya Allah dai ya baki miji nagari kije ki huta a dakinki"
Acan gidan Anty kuma Barrister yana dawowa daga sallar isha ya fesa wanka yasaka qananan kaya don ya boye tsufansa yana fesa turare Anty ta shigo ta toshe hanci tace "Barrister wannan turare naka bashi da dadi ko kadan" yace "yanxu ba, amma ai shi nake sakawa kike qanqameni kina shinshinata kedai kawai cikin ki yaxo da tsirfa" tace naji ina xaka haka kaci qananan kaya harda turare?" yaci gaba da taje sumarsa saida ya gama yana saka takalmi yace "inda kika aikeni" yasa kai ya fice. Ya shiga mota duk da ba wata tafiya bace ya nufi gidan su Sakeena.
Har 8:15pm tana xaman jiran dawowar Deni ko ina ya shiga haka? Ko ba a tashi ball dinbane? Yaro ya kwada sallama yace "wai ana kiran Sakeena a kofar gida" maganar taxo mata baxata hade da wata irin faduwar gaba, Iya tace da dan aiken "jekace gatanan" Sakeena tai saurin tarar Iya tace "Iya banfa san ko wanene ba, nikam babu inda xanje waya sanima ko shima dan iska ne?" Iya tayo mata daquwa tace "gidanku, canake tun magribar fari kiketa kwalliya kina xaman jiransa amma yanxu dan iya shege yaxo xakice baxaki fita ba" Sakeena tahau rantse rantsen cewar itafa bashi take jira ba. Iya ta dakko mafici ta radawa qafufan sakeena dake miqe tace "to inbashi kike jira ba ubanwa ki kaiwa wannan kwalliyar? Tashi ki fita yar qaniya" ta fito yafe da mayafi tana xunbura baki. Su fiddausi dake kallonsu ta labulen dakin Hajjo suka kwashe da dariya Amina tace "yaufa su o o andau wanka" suka kuma saka dariya.
Ta leqa dan shedawa baqon nata ya qaraso daga soro, amma bataga kowa ba sai mota dan haka ta koma soro ta tsaya da nufin ta danyi mintuna ta koma tace baqon ya tafi tunda bata ga kowa ba, a gefe guda kuma tana gudun Deni ya dawo yaganta tsaye da wani ransa ya baci.
Da sallama ya shigo soron, gabanta ya bada sautin "Dam" in kunnanta be mata qarya ba muryar Barrister taji. Ya qara tabbatar mata da hakan ta hanyar kunna hasken wayarsa ya haska fuskarsa sannan ya haska tata fuskar yace "Masha Allah sakeena wannan kwalliyar duk ni aka yiwa?" ta sunkuya ta gaisheshi amma yaqi amsawa yace "tashi ki gaisheni a tsaye, ni yanxu ba oganki bane saurayinki ne da yaxo neman aurenki" Ta ware masa manyan idanunta a fuskarta cikin kaduwa tace "Dan Allah kayi haquri ka tafi kar wani ya ganka yaje ya fadawa Anty wlh xata qonamun fuska da ruwan batir" ya qurawa sakeena ido yana mata kallon mamaki yace "well done, da abunda Bahijja ta tsorataki kenan ko? Shiyasa kike guduna?" tai shiru tana sharce kwallah, yayi qasa da murya yace "sakeenatu ko kiyi shiru ko in rungumeki in lallasheki, tun kafin ya rufe baki tayi tsit. Yayi murmushi ya qara haska fuskarta yace "in shaa Allahu haihuwarki ta farko ya mace xaki haifamun me kama dake" ta kwabe fuska xata kuma kuka ya dora yatsansa a bakinsa yace "shiiii kimun shiru, duk wani tsoro da kikeji nasanshi, Bahijja ce matsalar ko? To ba guri daya xan hadaku" Deni ya sawo kai cikin soron gidan, gaban sakeena ya yanke ya fadi tai tsam ko numfashi ta kasayi fargabarta daya kar ran Deni ya baci yayi fushi da ita ya janye son da yake mata.
Shima Denin dayaga mutane a soro saiya fasa bude dakin nasa yayi cikin gida, ya leqa dakin Hajjo yayi mamakin ganin su Hadixa gaba dayansu a xaune su 3. To wacece a soro ke xance? Kardai sakeena ce? Ya tambayi kansa, kai! Bayajin sakeena ce domin yaga da alama babban mutum ne yaga mota a qofar gida kuma ga qamshin turare ya cika soron gidan. Ya leqa dakin Iya dan tabbatarwa ya taddata ita kadai tabbas sakeena ke xance,, to waye wannan yaxo gurinta? Tab koma waye dole ya kau dashi koda xatai aure saiya cika burinsa akanta inyaso duk wanda zai aureta ya auri ragowarsa.
Acan zaure kuma Barrister ya tsare sakeena da tambayar wai tana sonsa? Ta rasa amsar da xata bashi ga fargabar Deni ya ganta a tsaye da Barrister Allah Allah take ya tafi ta rau rau da ido tace "Dan Allah katafi dare yayi xa aimun fada" ya qara matsarta yace "xan tafi amma sai kin bani amsa kina sona?" tace "Dan Allah ka tafi inka dawo xan baka amsa" yace "to sakeenatu yaushe xan dawo din" tace "to rana ita yau" yace "a a yamun nisa xan dawo dai jibi" tace "to saida safe" ta juya xata shiga gida yace mata "dakata mana" ya fita yaje mota ya dakko mata wata leda ya miqa mata yace "ki gaida Iya" ta karba tayi godiya ta juya ta koma jikinta a sanyaye.
Tana shiga soro na biyu taci karo da Deni, tana shirin yimasa magana ya daure fuska ya wuceta. Ta shiga dakin Iya jikinta a sanyaye ta ajiye ledar a gaban Iya tace "gashi ya bani" Iya tace "Masha Allah sakeena da alama dai miji yaxo wannan abun arxiqi haka?" ta fada tana bude ledar ta fito da tarkacen mayukan shafawa na Nevea da sabulai dasu sure.
Sakeena da baqin cikin abunda Deni yayi mata yawa ga fargabar karya dena santa saita fashe da kuka tace "Iya da kike fadar haka to kinsan wanda yaxo ne? To Barrister ne mijin Anty Bahijja kuma ta tabbatar mun da cewa duk randa naci amanarta sai ta qonani da ruwan batir" ta qara qarfin kukanta. Iya jikinta yayi sanyi kwarai da kukan sakeena tace "to kuma kukan na miye sakeena? ai ba cewa nai dole ki aureshi ba addu a nake miki kullum Allah ya baki miji nagari wanda xai rukeqi tsakani da Allah ya tallafi maraicinki" Sakeena bata qara tofa komai ba ta tafi gadon Iya ta kwanta tana kuka. A wannan dare dai haka ta kwana babu dadi.
washegari da safe xata fita aiki ta tsaya a kofar dakin Deni ta kwada sallama yana ciki yace "shigo sakeena" da rawar jiki ta kunna kai dakin, ta sameshi kwance dagashi sai gajeren wando akan katifar dakin. Ta sunkuyar da kanta ganin yanda ta sameshi ta gaisheshi tare da "ya Deni kayi haquri wlh bani nace yaxo ba jiya" ya tashi ya xauna ya jingina da bango yace mata "zauna sosai" ta xauna ya matso kusa da ita kafadunsu na gugar juna ta dan matsa, ya kuma matsowa tare da cemata "relax" yace "yanxu dai bani lbr?" haka ya dunga hirarsa shi kadai ba tare da tasa masa baki ba domin a matse take da xama kusa da ita yayi da taga abun ya isheta ta miqe tace "bari na tafi gurin aiki" ya kasheta da murmushi yana shafe sumar qirjinsa yace "da daddare inna dawo xan kiraki hira saura ki kuma kirawo wani xance" ta fita tana wani irin murmushi najin dadi sun shirya da Deni.
A darare sakeena ke aikin gidan yau gani take kamar Anty xata gane mijinta yaje xance wajenta, da Anty ta kirata saita amsa a firgice har Anty taso ta gane akwai abunda yake going.
Yauma kamar jiya tasha wankanta da magrib ta xauna jiran Deni har sallar isha tana idar cikin sa'a aka aiko kiranta tun kafin dan aiken ya gama fada harta dauki mayafi ta fita. Kamar yadda ta xata Deni ke kiranta, wani farin ciki ya lullubeta amma memakon su tsaya kofar gida sai yace su tafi wata unguwar daban, dake idonta ya rufe saita bishi har unguwar dake gaban tasu suka sami dakali suka zauna ya matseta sosai amma data nemi ya matsa sai yayi fushi yace tunda bata yarda dashi ba shikenan. A dimauce tahau bashi haquri kuma ta yarda suka xauna a hakan.
Washegari ma haka akai ya kirata taci kwalliyarta ta shafa turaren da Barrister ya kawo mata a cikin kaya ranar. Iya ta hau fada tana tambayarta waye ne ke kiranta take rawar jiki haka? Itafa batason shashanci ace kullum sai saurayi yaxo xance. Sakeena dai tai qus batace Deni bane kamar yadda ya nemi ta boye, Iya ta gama fadanta ta fita ta bishi.
A rana ta 3 ne Barrister ya dawo kamar yadda yayi alqawari, sakeena ranta ya baci tun dagajin qamshin turarensa a soro. Itafa a ra'ayinta batason auren babban mutum tafiso ta auri matashi kamar Deni wanda zai nuna mata soyayya in sunyi aure ya dunga daukanta kamar a film din india. A wannan dare dai dakyar Iya ta lallabata ta fita bayan tace taje inta dawo xasu xauna suyi magana akan wanda takeso abashi dama ya fito.
Yau hirar batai wani armashi ba don sakeena ta hade rai saboda Deni ya fara tsikar da zuciyarta da soyayyar bogi, Barrister shiketa hirarsa tana amsa masa da "eh ko a a" suna cikin haka Deni ya shigo kamar wancan Karon. Haka kawai ransa ya baci da ganin sakeena da wani. Ya shige cikin gida yabar sakeena cikin tashin hankali.
Ya tsaya a kofar daki yace da Amina "Amina wai waye yake xuwa xance gurin sakeena a mota?" jin ance mota duk hankalinsu ya dawo kansa Hajjo ta maimaita kalmar "mota kuma?" sai kuma ta Kalli Deni tace "kai kuma meye hadinka da ita kake tambaya? Ina ruwanka da harkarta?" ta tsareshi da kallon tuhuma. Ya hade rai kamar abunda zai fada gaskene yace "tsoro nake azo gurinta a yaudareta da kudi, tai abun kunya ta bata sunan gidannan" ta sauke ajiyar xuciya tace "ta bata sunanta dai, abun kunya kam ai ta gajeshi tunda uwarta ai a dadiro suka hadu da uban" Amina ta katse musu hirar da cewa bari in fita inyi mana C I D.
Ta shigesu a soro tai waje ta gama qarewa motar kallo sannan ta dawo ta kunna fitilar wayarta ta haskesu babu ko kunya, ai kuwa tayo gida da gudu tana haki taja hannun Deni daki dan kar Iya taji abunda xata fada tace "wlh yaya Deni Barrister ne mijin Bahijja suke xance da sakeena" yana kallon Amina yace "Barrister fa kikace?" taci laya tace "wlh shine" daga haka ya tashi ya fita.
Hadixa ta malmalo ashar tace "in sun isa Allah ya tsinemun, duk muna zaune rida rida babu aure mu bece yana sanmu ba sai wannan jakar? Ai dole saita bare kowa ya rasa" uwarsu ta tasasu gaba suka gama shawarar gobe Amina xataje ta fadawa Bahijja cin amanar da Iya da Sakeena suke shirya mata.
Acan soro kuwa sakeena tai masa qaryar kanta na ciwo xata shiga gida. Yayi mata sannu ya ciro kudi ya bata amma taqi karba ya gyara tsaiwa yace "ki karba Sakeena domin xasuyi miki amfani dan kina iya rasa aikinki a kowane lokaci daga yanxu dan nasan wannan yarinyar data haskamu rahoto taxo dauka, ni aurenki nakesonyi don haka baxan rabaki da aikinki ba kuma in barki haka" saboda firgicin jin Amina rahoto taxoyi yasa batasan sanda ya danqa mata kudinba harya fita.
Ta xauna ragaf a gaban Iya tace "Iya na shiga uku na lalace Amina ta ganmu da Barrister dakyar inbata fadawa Anty ba" Iya tai tsaki tace "sakeena banaji yanda kike tsoron Bahijja ko Allah kina tsoro haka, to saime inta fada mata? Ai shiyace yana sonki sannan kuma ai ba aurensa kikai ba ko? Kuma banda shirmenki ina ruwan Amina da Bahijja harda xata fada mata ni banason shashanci" ta miqawa Iya kudin a salube tace "gashi ya bani" Iya ta karbi kudin cikin kidima ta irga 10k ta Kalli sakeena tace "fadamun gaskiya sakeena, badai wani abun ya nema kika bashi ba ya baki wannan kudin ko?" sakeena ta xaro ido cike da kwallah tace "Iya xargina kike? Inke baki yarda daniba keda kikasan halina waye xai yarda dani? Wlh iya ban taba iskanci ba" jikin Iya yayi sanyi tace "to meye na kuka kuma aini ma ba xarginki nake ba yawan kudinne suka tsoratani." Iya ta saka kudi a gefenta Baba yana shigowa ta tashi ta kai masa kudin tai masa bayanin komai, yayi adduar fatan alkhairi yace Iya ta ajiyewa sakeena kudin a gurinta.
Duk da bata da jarrabawa washegari amma bataje gidan Anty da wuri ba tana fargaba. Iyace ta qarfafa mata gwiwar taje bakomi da xai faru sannan ta tafi. Sai dai abunda sakeena bata sani ba tun sassafe Amina taje gidan ta fadawa Anty xuwan Barrister xance gurin Sakeena harma da qarin gishiri a miya.
Lokacin da sakeena ta shiga gidan Anty bata nuna mata komai ba tun tana dari dari harta saki jikinta tayi aikinta tsaf har girkin rana har xuwa dawowar yaran Anty daga makaranta suka cire uniform ta wanke ta shanya.
Anty ta kirata har bedroom dinta ta sameta ta xaci wani aikin xatai mata, kawai sai saukar wayar wuta taji a jikinta. Ta dunga ihu tana sosa duk inda Anty ta shimfida mata wayar, yayin da Anty ke dukanta babu qauqautawa saida ta gaji ta tsaya tana haki ta fara magana"ni xakici amana dan ubanki? Ke waye har da xakiyi dating mijina? Duk abunda nai miki a rayuwa baki godeba? Inbakici inbaki sha, inbaki kwancen kayana, ke har bra saina cire nake baki kisaka shine dake talaka tsinanne ne har xakici amanata? Wlh daga yau ko mijin wata akace ki kalla baxaki kuma kallonsa ba balle mijina ya sunkuya ya dakko wata kwalba tana shirin budeta tace "wannan fuskar da kike taqama da ita yau xan canjata" sakeena ta bude iyakacin muryarta ta dunga qara yayin da ta nutsar da kanta cikin cinyoyinta.
Alhaji babban dan Anty da yake wanka ya jiyo ihun sakeena kuma yaji ihun yaqi qarewa yayi saurin dauraye jikinsa ya fito daure da towel ya nufi dakin mamansa inda dagananne yake jiyo ihun sakeena a xatonsa wutar Nepa ce ta jata.
Yayi mamaki lokacin da yaga mamansa da sakeena ke kokawa mamansa na qoqarin xubawa Sakeenar wani abu a fuska. Yayi saurin qarasawa yace "mama miye haka? Meke faruwa?" ido rufe tace "Alhaji babu ruwanka acikin wannan abun, amanata taci shine xan mata hukunci" ya riqe hannun mamansa yace meye wannan?" direct tace "Acid ne xan qona fuskar macuciya" a raxane yace "what? Mama kinsan abunda kike shirin yi kuwa wlh xaki jawowa kanki life in prison wat wrongs wit u? Ta addanci a gidan lauya?"
Sakeena dai tunda ta samu Alhaji ya riqe hannun Anty tai waje da gudu ta nufi gida a tsananin firgice. Daidai qofar shiga gidan sukai Karo da Deni be lura da yanayin da take ciki ba yace "indai kina qaunata to karqi qara kula wannan tsohon wanda ya haifi kamarki inkuma na kuma ganinki dashi daga ranar mun rabu" bata kulashi ba ta shige ciki da gudu tana kuka a firgice.
Su Amina da sunfi awa guda suna dakon dawowarta tana shiga suka kwashe da dariya ta tsaya sororo tana musu kallon mamaki. Amina ta fara xagayeta tana cewa "sannu sakeena, kin xaqe da yawa daga xuwa aikatau sai ki fara son megida? Wannan shine sakamakon maicin amana namaga qoqarin Bahijja da bata karyaki ba" Hajjo tai tsaki tace "ai bata da lefi dan ita quruciya ke dibanta bata gane cewa karo da aljan sai an shirya ba, kinga babbar muguwa can wadda ta shirya mata gadar xare ita kuma tahau" ta fada tana nuna Iya wacce ke yanka kubewa.
Iya ta taso ta riqe sakeena tana bin jikinta da kallo inda shatar dukan Bahijja ya fito rudu rudu tace "sakeena yanxu Bahijja ce tai miki wannan dukan? Duk bautar da kike mata?" sakeena dai ba magana kuka take sosai, iya ta share nata hawayen tace da Amina "ke kuma Amina kin cika munafuka lallai gaskiyane da hausawa suke cewa munafuki ko a dakin uwarka ya rigaka sai dai ka kwana a waje. To amma ki sani baki cuci sakeena ba domin sara da sassaqa baya hana gamji tofo inkinyi munafurci kin rabata da Adamu Allah yana iya bata wanda ya fishi kuma baki isa ki hanaba" kafin Amina ko Hajjo suyi magana Baba ya shigo shiyasa sukai tsit. Ya tamvayi ba asi, Iya ta mayar masa yadda akai tana kuka ta nuna masa jikin sakeena. Shima hankalinsa ya tashi sosai ya Kalli Amina datai tsamo tsamo yace "nasan wannan ba idea dinki bace ke kadai harda uwarki da yan uwanki a ciki saboda haka baxance muku komai ba xubar hawayen wannan marainiya ya isheku kuda azzalumar data daketa." sukai qus, ya juya yaja hannun sakeena dake kuka suka fita yace da Iya "dora mata ruwan dumi xan kaita chemist in mun dawo saiki gasa mata jikin"
xuwa magrib sakeena jikinta yayi xafi sosai, sai rawar dari take Iya sai shafa mata rubb take a gurin daya fashe tana kuka da cewa "Allah ya isa baxan yafewa wannan yarinya ba ta daki marainyar Allah" saita share hawaye.
Sakeena bacci ya fara daukarta taji Iya taxo taja hannunta tace tashi kije malam na kiranki. ta saka hijabi ta samu Baba a soro tare da Barrister, Baba ya kama sakeena cikin zafin rai duk kuwa da haqurinsa ya yaye hijabin sakeena yana nunawa Barrister inda shatar dukan Bahijja ta batawa sakeena jiki yana cewa "kishi haukane da xata kama marainiya tai mata wannan dukan? Ko cemata akai sakeenar bata da gata." Barrister ya runtse ido ganin shatar waya a jikin sakeena karo na barkatai yace "Baba kayi haquri wlh bananan lokaci da Bahijja tai wannan aiki, amma hakan baxaisa infasa auren sakeena ba kuma indai har kanaso xanyi qararta abiwa sakeena haqqinta." sakeena ta katse musu xancen da cewa "ni ban manta alherinta ba a gareni kuma na yafe mata. Xancen aure kuma bana sonka dan haka karka qara xuwa gurina nagode da kulawarka Allah ya saka maka da alkhairi" ta juya ta koma cikin gida. Baba ya kalleshi yace "to kaji bata sonka saboda haka saika sama mana lfy. ita kuma matarka a sannu Allah zai hadata da dai dai ita." Baba ya wuce yabarshi a tsaye.
Ya kifa kansa a bangon soron zuciyarsa na wani irin tuquqin rabuwa da sakeena da kuma kunyar xubar masa da mutunci da matarsa tayi. Kuma wai dan Bahijja ta rainashi dakanta bayan dawowarsa ta fada masa ta xane sakeena sakamakon cin amanarta da tayi ta kuma haushi da masifa be tsaya sauraranta ba yayo nan gidan dan bawa sakeena da su Iya haquri kuma besan abunda tai yakai girman haka ba tunda har yarinya me kunya irin sakeena ta dubeshi cikin ido tace bata sonsa Allah ne kadai yasan me Bahijja ta fada mata bayan ta daketa. Cikin hanzari yayi waje ya nufi gida da nufin xuwa ya tayarwa da Bahijja hankali dan wlh ransa baxai baci shi kadaiba itama a darennan saiya nuna mata shi namiji wanda ya isa da gidansa.
Hajia ☺
[7/31, 2:05 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
7⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Sakeena sai data kwana uku tana jinya kafin ta wartsake, taji dadin kwanakinta datai sosai daga kan gado sai falon Iya ko tsakar gida sai xata shiga bandaki take fitowa. A gefe guda kuma tana kewar Deni wanda rabonta dashi tun ranar da Anty ta daketa. Kullum ta kanyi wanka ta mulmule jikinta da mai tasa turare da roll on duk dan ta xama yar gayu dan ta burge tauraronta Deni. A yan kwanakin da tayi babu wahalar aikin Anty sai ta gane dadin xaman guri daya, lallai xaman guri guda dadi gareshi wanda in mutum be wasa ba sai xuciyarsa ta mutu. Hmm Allah ya bamu hutu da jin dadi me dorewa.
A ranar kwana ta biyar ta warke sosai har ta fito ta taya Iya aikace aikacen gida da kuma dakan yajin siyarwa.
Da daddare tana xaune kewar Deni ta addabeta, tun daxu da tana daka take leqen ta inda xai bullo amma har ta gama xaman tsakar gida bai shigo ba.
Wajen qarfe taran dare tai shirin bacci, ta fita tsakar gida domin yin alwalar kwanciyar bacci. Tana duqe tana alwala yayin da kowa ke daki gidan yayi tsit Iya ma tanacan dakin Baba yau ita ke girki. Taji kamar ana kiranta cikin rada ta juya dan ganin waye ke kiranta, tayi arba da Deni ya yafitota da hannu, ba tare da tunanin komai ba ko qarasa alwalar ta bishi soron. Ya bude dakinsa suka shiga ya kunna fitila kasancewar akwai wuta, ya xauna itama ta nemi guri ta xauna a darare ya fara magana da tambayarta "ya jikin naki?" ta bishi da kallon mamaki dama duk wannan kwanakin yasan bata da lfy? Ta bashi amsa "da sauki ashe kasan bani da lfy?" yayi fuskar tausayi yace "nasan zaluncin da matar saurayinki tai miki, kema meya kaiki sakeena? Meya kaiki kula wannan dattijon mijin nata har ta kamaki ta dakarmun ke?" taji dadin kalaminsa, idonta ya cika da kwallah tace "wlh bani ke sonsa ba shine ya nacemun kuma sai da nace ni ya kyaleni inada wanda nakeso amma yaqi" ganin hawaye a fuskarta ya taso ya fuskanceta yasa hannu yana share mata hawayen yana cewa "ki daina kuka Allah xai saka miki" tai saurin dena kukan domin a tunaninta saboda kukan ya matseta in kuma ta daina xai koma maxauninsa.
Shi kuwa dan duniya Deni yayi amfani da wannan damar ya cirewa sakeena hijabin dake jikinta, ta firgita ta matsa gefe tana rawar baki tace "yaya Deni meye haka?" yayi shu'umin murmushi ya kamo sangalalen hannunta yace "bakomi sakeena kawai inason ganin inda wannan azzalumar matar ta dakane a jikinki" jin haka hankalinta yadan kwanta amma duk da haka bata sakeba.
Yacigaba da duba guraren da shatin bulalar ya rage, a wayence kuma yana kallon qirjin sakeena ta cikin yar yalolowar shimin jikinta me roba wacce ta kamata tsam har nipple dinta yana iya gani, ya hadiye yawu shedan ya qara qawata masa sakeena dake qamshin turaren nevea.
Yakai bayan hannunsa a hankali ya shafi dogon wuyanta, tai xunbur ta miqe tsaye shima cikin sauri ya tashi tsayen ya matseta a bango yace "ina xakije?" ta rarumi hijabinta tace "ciki xan koma kar Iya ta neme ni" yasa hannayensa akan kafadunta ya marairaice yace "ke yanxu in akace ki tafi ki barni acikin wannan halin sai ki barni?" Sakeena dai ta gama tsorata ko numfashi ta kasa yi saboda matsar da Deni yayi mata. Ya kamota gaba daya ya mannata a qirjinsa yana sakin wani irin nishi. Ta taga abun bana qare bane saita tureshi ta nufi qofar fita yayi saurin shan gabanta cikin rufewar ido yace "wai shin bakya sonane? Anya son da kikemun gaskiya ne? Indai da gaske kina sona ai duk abunda na nema xaki bani" ya tunkareta yana cire rigarsa yace "sakeena tunda kin tabbatar da kina sona to ki bani jikinki don shi nake buqata a yanxu" ya fada yana kiciniyar kwantar da ita a kan katifarsa.
Sakeena da kalaman Deni suka daskarar da ita ta lula duniyar al'ajabi har ya kaita qasa, ta farga lokacin da tajishi yana shirin hayewa kan ruwan cikinta. Cikin wani irin bacin rai da tsananin xafin nama ta miqe tsaye ta dauke Deni da wani irin gitattaccen mari ji kake "kau" ya dafe kunci yana kallonta a razane.
Ta nunashi da hannu ta fara magana cikin kakkausar murya "ka bani mamaki Nuraddeen, kuma ka bata wayonka, dama wannan itace kalar soyayyar da kakemun? Ko kakeso ka koyamun? Anya kuwa Baba ne ya haifeka? Baba mutumin arxiqi ace wai tsatsonsa yaso yin haka kuma a cikin gidansa? Ban xaci haka daga gareka domin da bakinka ka fadawa Iya cewar ita din uwace a gareka ni kuma qanwarka ce, ashe wannan kalaman naka duk yaudara ce. Nagode kwarai wannan abu dakai nufin yimun Allah ya kawo me irin halinka ya kwatantashi akan qannenka. Indai wannan ce kalar daka soyayyar to hell wit u nd ur fake luv" ta juya ta bude sakatar dakin da batasan sanda ya saka ba ta fice ta barshi da kunci a dafe kamar drawing yana kallonta😄
A wannan dare bacci a gurin sakeena sai dai in barawo, ta kwana da abunda Deni yayi mata a ranta cikin wani irin yanayi na fidda tsammani. Abun yayi mata ciwo fiye da abunda Anty tayi mata, ta fidda tsammanin jin dadin rayuwar duniya, to wanda take ganin yafi kowane namiji halin kwarai kuma take ganinsa a matsayin wanda xai xama uban yayanta shine yake shirin watsa mata rayuwarta, shine yayi qoqarin rabata da mutuncin da takeso fiye da komai da kowa. Ashe dama haka abun yake da ciwo ka yarda da mutum ya ha'inceka ko kuma ya karya yaddar da kai masa?
Sakeena tayi juyi ta qara zurfafa tunaninta, to bude zuciyarta da kwakwalwarta tayi tunani na tsanaki sai tagano Deni fa bashi da laifi duk laifin natane. Eh laifinta mana nakai kanta inda Allah be kaita ba, inbanda ita jakace me kwakwalwar kifi kamar yadda Amina ke yawan fada ina ita ina Deni? Ai mutum dai dai shi yake aura, ita kuma saita hangi wanda ya fita nesa ba kusa ba. Deni ya fita ilimi, asali, gata tsafta kwalliya da kuma wayewa. To taya xa ai ya sota? Ai dama dole sai dai da wata manufa kuma manufarce ya nuna mata ita yau. Lallai ta cika mayaudariya me yaudarar kanta, ita da take daga qauye taxo gidansu cin arxiqi tana yawan aikatau da kaya burum burum tayaya xatai soyayya da wayayyen namiji wanda yayi karatun gaba da secondary kuma ya rayu a birni cikin kyawawan yan mata masu kyale kyale wanda uwarsa da yan uwansa ke burin ya dakko musu qasaitaccitar mace ta kece raini?
Ta kuma juyi lokacin dare ya tsala sosai ta dakko batun Barrister duk da babu hadin kanta a xuwan da yayi amma akwai kuskure kwatankwacin wanda tayi akan Deni domin shima data jajurce ta nuna masa bata so daga xuwan farko da bai kuma dawowa ba har Amina ta ganshi taje ta fadawa Anty ta koreta. Data qara zurfafa tunani sai taga ai da Deni da Barrister kusan jirgi daya ya kwasosu duk da barrister be taba attempting bata mata rayuwa ba duk kuwa da yafi Deni samun damar yin hakan. Amma both Deni nd Barrister sunyi amfani da salo daya ta hanyar tambayarta "kina sona?" shima wataqil Barrister data amsa tana sonsa yayi yunqurin raping dinta. Wato ita bata da quality din da xa a ce ana sonta sai dai ita taso? Kuma ai dukkansu babu wanda ya taba cewa yana sonta. Lallai ta tafka uban kuskure, da wannan tunani ta tsinewa kalmar "so" dama soyayyar gaba daya tunda anso amfani da kalmar a illata rayuwarta. Lalli ta cika me kwakwalwar kifi da duk da bata gane wannan ba sai yanxu. Amma kuma ta godewa Allah da yasa ta farga tun yanxu basai da mai afkuwa ta afku ba taxo tayi fargar jaji.
Ta yanke shawarar tattara duk wani abu daya danganci soyayya ta watsar tunda bata karbeta ba, ita da bata da farin jinin mata ma ba balle maxa? Soyayyar qaninta Nura dake kwance a kabari ma kawai inta riqe ta isa cika mata xuciyarta har ixuwa lokacin da Allah xai kawo mata dan qauye kasashshe wahallale irinta ya aureta suje suyi rayuwarsu ta yadda indai xaiga mutuncinta da qimarta ya fiye mata maxan birni masu kyale kyale. Tana wannan tunani bacci ya kwasheta.
Saida Iya ta tasheta sannan ta tashi tayi sallah, idonta jajur tana xaune akan sallaya kanta yana sara mata. Duk yadda taso kawar da abunda Deni yayi mata amma abun ya gagara, gani take kamar a mafarki wai wanda takeso ta yadda dashi shine yayi mata haka. Ta fashe da kuka Karo na farko tunda abun ya faru, Iya ta katse lazimin da take tace "sakeenatu lfy?" bata kula Iya ba tacigaba da kuka domin tasan baxata taba iya sanar da wani abunda ke tsakaninta da Deni ba balle Iya. Sai da tayi kukanta ma'ishi kana tace da Iya Nura na tuna ya tafi ya barni ni kadai a wannan duniyar mara dadin xama. Iya ma ta share nata hawaye ta dunga aikin lallashin sakeena har tayi shiru.
***** ****** ******* ****
Satittikan da suka biyo bayan wannan lamari sakeena tayisune cikin wata irin nutsuwa, duk da kasancewaarta nutsatstsiya wannan abu daya faru ya koya mata hankali da tarin darasi saboda haka ta kame kanta ta kuma wata nutsuwa akan tata nutsuwar.
Inka ganta a tsakar gida to aiki take ko kuma tana taya Iya girki tana gamawa kuwa xata koma daki, ta tsani koda jin sunan Deni balle ganinsa kuma ta taki sa'a tunda abun ya faru befi sau 2 ko 3 suka hadu ba saboda tana tsananin gujewa hakan.
A tsammanin Iya da sauran ahalin gidan abunda Anty tai mata da kuma rabuwa da Barrister shine yake damunta wanda Iya kan yawan yi mata nasiha akan hakan. Yayin da koya suka hada ido da Amina sai tayi mata gwalo ko dariya, itadai sakeena ita tasan abunda yake nuqurqusarta.
A bangare guda kuma Deni tun sanda Sakeena ta kifeshi da mari ta fita daga dakin shima nadama ta aureshi. Yadda sakeena bata rintsa ba shima a daren haka ya kwana, ya la'anci shedan da son xuciya yafi cikin carbi. Wai shin meyasa ma yayi haka? Meye lefin sakeena don ta nuna tana sonsa? Meya hanashi nuna mata bai gane nufinta ba daga haka harta haqura ta kyaleshi wane tsautsayin ne ya kaishi yunqurin bata mata rayuwa? Gashi yanxu yayi biyu babu uku babu ko daya. Shi baisamu abunda ya nema ba a gurinta sannan kuma ya xubar da mutuncinsa a idon yarinyar abu na qarshe mafi muni shine marin da sakeena tayi masa yarinya qarama saar autarsu tai masa marin da rabonda ko iyayensa suyi masa irinsa shekaru ashirin baya. Amma fa duk munin marin da sakeena tai masa be masa ciwo ba kamar baqar adduar datayi masa na Allah ya kawo mai irin halinsa ya kwatanta abunda yayi mata akan qannensa. Wannan addua ta baqanta masa kwarai da gaske, daya auna saiya kwatanta yadda sakeena taji da kuma yadda yakeji a halin yanxu. Shifa kawai addua tai masa amma abun ya tsaye masa arai ina ga ita da yayi yunqurin batawa? Ya rasa yadda zaisa kansa a wannan dare, tausayin sakeena ya shigeshi karo na farko a rayuwarsa. Ya dunga juyi yana lalubar hanyar da xai gyara kuskurensa da kuma wanke kansa a gurin sakeena, da kyar daga qarshe ya yanke shawarar bin hanyar da yabi wajen nuna mata soyayyar qarya ita xai kuma bi ya gyara kuskurensa amma fa sai yayi amfani da hikima da kuma iliminsa. Wannan shine tunanin Nuraddeen a wannan dare.
A memakon ta bari damuwar abunda Nura yayi mata ta dameta saita maida hankali akan karatun jarrabawar da suke kain da nain domin ta gane kamar yadda Baba yake yawan fada mata bata da gatan da yafi na ilimi. Ta dauki tsafta ta riqeta hannu bibbiyu don ta gane tana daga cikin dalilan da suke sa a raina ajinta kuma dama can ita ba qaxama bace aikin gidan Anty ne ya maidata qaxamar qarfi da yaji. 10k din da Barrister ya bata da ita tai amfani gurin siyan kayan candy, taisai ankon material din da sukai ta bada kudin photo album tasai mayafi da sauran tarkacen inner wears. Baba ya basu 2k kowa ita da Amina yace suyi haquri bashi da kudi. Taji dadin kudin Baba taje ta siyo turaren da take masifar so "lailatus sahara" ta sai yan kayan kwalliya masu sauqin kudi ta ajiye yan canjin a gurinta.
Kasancewar wasu jarrabawa daya zasuyi wato WAEC kawai baxasu dawo NECO ba kamar su Amina, shiyasa suka shirya fatin candy ranar da xa ayi jarrabawar qarshe ta WAEC don wasu daga ranar anrabu kenan.
Ana gobe jarrabawar taje qunshinta, aka rangada mata baqi da ja aka kuma yimata kitsonta qanana ta fito shar. Ta nufo gida ana daf da magrib tana tafe tana kuma kallon qunshin hannunta wanda ita kanta ya burgeta. Tana shigowa soron sukai kacibis da Deni wanda da yana xaune a kofar gida amma hangota da yayi yasa ya tashi ya koma soro don tararta. Kuma dama ya dade yanaso yayi magana da ita tun bayan faruwar abun amma ta toshe duk wata dama ta yin hakan.
Ya tare gabanta yace "Sakeena dan Allah ki saurarani," ya miqo mata leda yana duban qunshin hannunta yace "gashi nima tawa gudummawar ce ta candy ayi haquri kyautar talaka babu yawa" ta galla masa wata uwar harara kamar idonta xai fado tace "OH! Daka nemi amfani da son da nake maka ka batamun rayuwa bakai nasara ba shine ka biyo ta hanyar yimin kyauta? To ai kafi kowa sanin bani da buqata domin ni bamai matacciyar xuciya bace irinka da xan xauna sai anbani, kafi kowa sanin Sakeena macece me xafin nema" yayi saurin magantuwa da cewa "Sakeena ya kike daga murya haka? Kar ajiyomu aciki" ta qara volume tace "sai me in aji? Nace sai me in anji ka nemeni da zina naqi yarda" yayi saurin barin soron kafin ajisu a gida afito. Tayi tsaki ta shige ciki.
Iya ta dunga koda lallen sakeena da cewa "Masha Allah diyata dagayin kitso da lalle kinyi kyau balle kinyi kwalliya? Ai nasan babu ta biyunki, yau gaba daya sai kika komamun mahaifiyarki Aisha sak. Allah sarki Allah ya kyauta makwanci." Hajjo dake tatar gasara ta doka tsaki, Amina kuwa da baqin cikin kyan qunshin sakeena ya hanata magana ta kasa daurewa tace "to ke sakeena da xaki tafi wani gurin ayi miki cewa nai baxan miki ba? Ko inda kikaje fina iyawa akayi? Ga abu anayi a gida kintafi anmiki a wani gurin dan mugun hali, ai da kinbari na miki da kudinki sun huta" sakeena ta juya ta Kalli Amina a sheqe tace "ai nasan kinayi na tafi wani gurin domin bana buqatar da kyautar, mutum da kudinsa ai kinga sai abunda yakeso." Kafin Amina tai magana sakeena ta shige daki tabar Amina da bin sahunta da kallo kuma dama taso sakeena ta kawo kanta gurinra qunshi tai mata na wulaqanci ta bata mata kwalliyar candy. Iya kuwa dariya tayi duk da sakeena bata da magana amma akwai iya maida martani.
A ranar kwana tayi karatun jarrabawar gobe, sassafe ta tashi tayi wanka suka nufi makaranta. Dake ta karantu bata wani jima ba a jarrabawar ta gama ta fito, suna zaune da qawayensu aka gama paper din gaba daya na kusa suka tafi gida domin yin sallah da sako anko, na nesa kuma suka shiga maqotan makarantar.
Sakeena dai saida tayi bacci bayan dawowarta gida saboda jiya bata samu jiba. Lokacin data tashi harsu Amina sun tafi, tai wanka ta shirya tayi kwalliyarta simple daga foundation sai jamvaki da eye liner dan bata da qarfin idon xana jagira duk kuwa da tana da burin taga ta iya kwalliya. Tasa material din dinkin riga da skirt yayi mata das dai dai jikinta tai acuci ta kafa dauri Iya ta miqo mata sabbin dan kunne da sarqa da agogo tace "ungo saka" ta washe bakinta tace "Iya yaushe kika saimun?" iya tana tata dariyar tace "me ya mace ai a hankali yake tanadi kedai kawai saka saurauniyar kyau yau kam ni kaina uwarki kin burgeni" ta gama saka komai tahau takalminta me tudu sabo ta yafa sabon mayafi da jakarta swaga ta dubi kanta a madubi, gaskiya gyara yana da dadi kamar ba itaba fatar jikinta tayi kyau tun bayan rabuwa da aikin Anty fuskarta tayi qal haskenta ya qaru saboda amfani da man nevea, jan bakin data saka dark purple (anti daba) ya qara haska fuskarta, idonta kuwa yasa eyeliner da mascara ya qara fitowa. Ta fesa turarenta taiwa Iya sallama ta fito, Su Hajjo sukayo waje don ganin kalar kwalliyar sakeena. Suka sameta yadda basu taba xata ba. Hadixa tace "kai sakeena kinyi kyau wlh kamar ba keba" ta dakko wayarta a daki tace "bari inmiki photo" duk da basu cika dasawa ba bata kwale Hadixa ba ta tsaya ta dauketa photo wajen guda 10 a wayarta sannan tace "to jeki kar a gama raba take away bakyanan" taiwa Hadixa godiya ta fita.
Deni dake daki ya daga labule dan yaga wucewarta, dan yanxu sakeena tsoro take bashi. Ya shaqi qamshinta tunkan ta qaraso, ya qura mata ido har ta wuce tai waje, bai gaji da kallonta ba ya bita kofar gida yana kallonta harta bacewa ganinsa. Ya sauke ajiyar xuciya haka kawai saiya samu kansa cikin farin ciki wanda besan dalili ba. Ya koma daki yana naxarin maganar sakeena ta daxu inda ta kirashi da mai "matacciyar xuciya" duk da ransa ya baci da maganar amma kuma in anduba maganarta gaskiyace tsantsa. Tunda ya gama service yaxo ya xaune a gida yana jiran aiki kuma aikin yaqi samuwa sai dai ya xauna abashi abinci yaci kuma hajjo ta bashi kudin kashewa kamar mace? Ga dattijon ubansa da kullum qarfinsa qarewa yake yana buqatar temako shi da yake babba a gida ya xaune wai shi graduate yafi qarfin Sana'a sai aikin gwamnatin da babu ranar samu (kuskuren da matasa ke tafkawa yanxu) ba dole suma qannansa su koyi xaman banxa ba xaman mutuwar xuciya? Tabbas ya xama dole ya tashi ya yaqi xaman mutuwar xuciyar da yake ya nemi Sana'a kowace irice koya samu ya daina amsa sunan me matacciyar zuciyar da sakeena ta kirashi.
Acan makaranta partyn candy ya kankama kafin sakeena taje, Amina tayi mamakin ganin sakeena aka dunga yaba kyan da tayi gurin qawayensu suka dunga photuna da ita a ciki kuwa harda qawayen Amina da Aminan wadanda basa kulata ada, yaudai sungane ashe sakeenar itama ba baya bace wajen kyau da kwalliya. Su Amina anje gidan kwalliya sunsha make up, anyi kitson gashin kanti anyi dinkin bayyana tsaraici ga kuma bleaching da akayi duk dan qarawa kwalliyar candy armashi. Amma sai sukaga sakeena da batai irin wannan haukan da sukaiba da kuma bayyana tsaraici sai ta fisu kyau, da kuma burgewa. Ashe dai kwalliyar hauka da baiyana tsaraici ba shine kyan kwalliya ba.
Sunyi party lafiya anraba snacks da lemo an gama an watse lfy ansha hutuna anrabu ana neman yafiyar juna dan wasu sai dai ku hadu a qiyama. Allahu Akbar dama rayuwar kenan (Allah ya jiqan ummana, Allah ya haska kabarinta ya saka kabarinta ya xama raudhul jannah ita da sauran Al ummar musulmi Aminnnn 😥)
***** **** ****** *****
Xaman gida ya biyo baya bayan kammala jarrabawar WAEC kafin NECO kuma duk abunda ke hannunsu dashi sukayi amfani wajen kammala makaranta. A dan tsakanin sakeena ta fahimci mahimmancin aikin Anty a wajenta domin koba komai tanaci ta qoshi harma wani ya samu yanxu ma tanaci ta koshi kuma tsafta ta xauna mata amma fa dole ba kamar a gidan Anty ba wacce sakeena kejin su Hadixa na gulmarta wai Barrister yayi mata kishiya yarinya qarama irinsu Amina yan gigin candy kuma ya hadasu ya gwamuxasu a gida daya kullum Anty tana yawan kai qarar Barrister da amaryarsa gurin uwar mijinsu. Sakeena tai mamaki wato Barrister matakin daya dauka akan Anty kenan? Iya kuwa hamdala ta dungayi tana cewa haqqin sakeena ne ya fara tambayar Anty.
Da xaman gida ya ishi sakeena ga kuma babu saita shawarci Iya ko xata bata dama taje wata private skul da aka bude a unguwar neman koyarwa koda ta yan nursery ce? Iya tayi nazari kafin ta kalli sakeena tace "sakeenatu kuma xaki iya koyawa yaran abunda ake buqata?" sakeena tayi dariya tace "in shaa Allahu xan iya koda yan primary aka bani, ai yanxu da da ba daya bane Iya na sami ilimi dai dai gwargwado babu abunda xance muku sai dai ince Allah ya saka muku da alkhairi" Iya tace "to Masha Allah, ai baxan hanaki nema ba tunda Allah yayiki haziqa me xuciyar neman nakai, yau xan miki adduar sa a gobe kuma in Allah ya tashemu saiki je" Sakeena tace "yawwa Iya Allah ya barmu tare"
washegari sakeena ta nufi makarantar da qarfin gwiwar Iya bayan ta sambada mata adduoi. Taje ta samu shugabar makarantar mace me kirkin gaske a haife xata haifi fiye da sakeena, ta karbeta hannu bibbiyu sakeena ta sheda mata abunda ya kawota cikin kwantar da kai. Matar ta nemi sanin matakin karatunta ta fada mata tayi jarrabawar kammala secondary. Matar ta bata haquri cikin tausasawa ta fada mata sunfi buqatar masu shedar karatun NCE da kuma Degree. Sakeena gwiwarta tai sanyi kwarai tayi godiya ta tashi xata tafi. Matar ta kuma kallonta ta karanta yanayin sakeena a fuskarta a matsayinta na uwa baxataso tata yar taje neman aiki aqi bata ba, amma gurbin aikin da suke dashi dakyar in sakeena taso shi amma bari ta fada mata da hannau gara mannau.
Har sakeena taxo fita ta tsaidata tace "zo diyata" sakeena ta dawo ta tsuguna ta sunkuyar da kanta. Tace "inkinason wani aikin saina baki, amma fa na lura da yara in zasu shiga bandaki ki rakasu in sunyi tsuguno kiyi musu tsarki." sakeena ta washe baki tace "wlh xanyi Hajiya aini dinma banfi qarfin hakan ba nagode Allah yasaka da alkhairi in shaa Allahu gobe xan fara xuwa aiki" tana dariya tace "ai baki tambayi nawa xan dunga baki ba, amma tunda baki raina aikin dana baki ba xan dunga biyanki 5000 duk wata" sakeena ta washe baki ta dunga godiya ta tafi bisa alqawarin gobe qarfe 8 xata fito aiki.
Koda taje gida bata bayyanawa Iya kalar aikin data samu ba kawai tace mata andauketa aikin gobe xata fara xuwa da albashi dubu biyar duk wata domin tasan Iya bazataji dadin cewa aikin tsarki xata dunga yiba duba da yadda ta tsani aikin gidan Bahijja. Ta qudure a ranta xata qoqarta matuqa ta tattala abunda xa a bata domin ta tunkari matsalarta ta ido wacce tana samun sauqi in shaa Allahu xata dora akan karatunta xuwa jami a.
Kamar yadda ta alqawaranta washegari ta fara xuwa aiki kuma Hajiya taji dadin ganinta sosai yarinyar ta burgeta bata raina neman nakanta ba. Data fara aikin ma sai taga aikin ma ba wani bane domin mafi yawan yaran fitsari kawai take rakasu in sun gama tai musu tsarki ta rakasu aji, sai ta koma tai xamanta dai dai kune sukeyin tsuguno. Shikenan aikin nata sai tajita kamar mai xaman banxa bame aiki ba kodan ta saba da wahalar gidan Anty ne? 12:30 pm ake tashi daganan tai gida sai kuma gobe.
A kwananta na hudu da fara aiki ne tana shigowa gida daga gurin aikin su Fiddausi suka kwashe da dariya kuma abin takaici har Hajjo. Sakeena ta waiwaya fuskarta na alamar tambayar me sukewa dariya? Amina tsagera ta fara magana "waini me ilimi na tafi makaranta neman aikin koyarwa, memakon aikin koyarwa sai na samu aikin tsarkin kashin yara" ta fada cike da izgili su Hadixa suka kuma saka dariya. Iya dake karya taliya a ruwan dake kan murhu ta tsaya kamar ansaka mata pause ta dunga bin sakeena da kallon tuhuma. Sakeena ta qanqance ido cike da bacin rai ta kallesu tayi tsaki tace "Alhamdulillah amma dai nafi mai xaman banxa xuciya a mace an jibge ana xaman jiran me kudi" ta juya ta shige daki. Hajjo ta kalli yayanta tace "ga dukkan alamu yarinyarnan ta riqa ta goge kaushi anci jar miya, wato harku takewa gorin aure" fiddausi tayi kwafa tace "hmm kedai bari Hajjo ni kaina abun ya ban mamaki ni banxaci ta iya rashin kunyq haka ba" Hadixa kuma tace "wai harmu takewa gorin aure shegiya sekace ita tayi auren?"
Acan dakin Iya kuma sakeena tunani take a ina sukaji labarin ta samu aikin makaranta har bata samu koyarwa ba sai tsarki wa yara? A iya saninta dai Baba ne kadai Iya ta fadawa dan bata boye masa komai to a ina su Amina suka sani?
Iya ta shigo dakin ta fallarawa sakeena harara kafin ta rufeta da fadan cewa batasan bata dauketa uwa ba sai yau tunda har ta boye mata kalar aikin data samu sai a tsakar gida taji. Sakeena a rude tahau bawa Iya haqura tace " Iya inkinyi fushi dani gurinwa xanje kenan? Ki tuna bani da uwa bani da uba bani da dan uwa ke daya kika ragemun wlh saboda karki hanani aikin shiyasa na boye miki naga bakyason inyi aikin wahala" Iya daga fada ta koma lallashi suka shirya da yar diyarta sakeena 😄 Daga haka sakeena tacigaba da aikinta sannan kuma tana tafiya da littafanta tana bitar karatun jarrabawar NECO.
A bangaren Deni kuwa tun washegarin ranar da Sakeena tai candy ya samu Baba da neman shawararsa xai fara Sana'a tunda aiki be samu ba. Baba yayi murna da wannan shawara ta Deni, ya kalleshi yana murmushi yace "Nuraddeen kodai wata kakeso tace sai ka nemi Sana'a xata aure ka?" Deni ya kalleshi cikin mamaki yace "Baba in mutum nasan mace sai yayi duk abunda take buqata?" Baba yana dariya yace "kwarai kuwa da alama wannan suruka tawa jajirtacciya ce tunda ta zaburar dakai ixuwa neman nakai" Baba yacigaba da magana "tunda da kanka ka nemi hakan naji dadi kwarai kuma xan kaika gurin alhajin da nakewa aikin driving yana da shaguna akwari ya baka jiran shago kafin Allah ya baka naka jarin ko ya baka aiki" Da haka Deni ya samu jiran shago a gurin Alhaji wanda in sunyi ciniki ake sallamarsa da 500 kullum in kuma babu ciniki a bashi 300 kullum amma aciki Deni kanyi kudin motar xuwa kwari daga gwale da kuma kudin motar komawa dan haka abunda yake samu ya riqe bashi da yawa amma duk da haka yana jin dadin aikinsa kuma yana alfahari da hakan. Ranar da aka fara bashi 500 a matsayin abunda ya nema da guminsa har kuka yayi saboda farin ciki kuma ya jinjinawa sakeena bisa tsayawarta akan nema da guminta tun tana qaramarta. Amma a bangare guda yayi iya qoqarinsa su kebe da sakeena ya bata haquri ya wanke kansa amma taqi kuma ga mamakinsa abun ya tsaye masa arai wanda ya rasa dalilin hakan. Su Amina da Hajjo kuwa duk inda suka xauna sai kaji suna ai Deni yana kasuwanci a kwari kai kace shagon nasane. Alhajin da Deni yakewa aiki wanda ada baiso aikin Deni ba don bashi da yadda amma a hankali saiya lura yaron yana da amana sannan gashi da ilimi wanda hakan tasa idan Alhaji yayi baqin yan china zai sai kaya sai Deni yayi masa tafinta saboda shi bai iya turanci ba. Duk sanda akai irin wannan baqi yakan sallami Deni da kudi mai tsoka kamar 2000 shi kuma ana bashi xai kashesu yasai abunda xa a amfana a gida Baba najin dadin hakan dan Deni ya fara nuna yasan ciwon kansa. A gefe guda kuma duk sanda Deni yayi irin wannan bajinta xakaji Hajjo na mitar cewa ya dunga tanadi domin duk wanda yaga ya xama me kudi saida ya tattala dan abunda yake samu amma shi daya samu kudi saiya hau gwaninta dasu ga wadanda basusan yadda yayi ya samu ba. shi kuma kan yawan fada mata na neman albarka yakeyi dukiyar da ake arxiqi da ita daban Allah yake kawota baisan cewa ita Hajjo kyashin Iya da sakeena suna na morar duk abunda ya kawo take ba.
Hajia ☺
[7/31, 2:08 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
8⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Koda sakeena ta fara jarrabawa sai ya xamana ba kullum take xuwa gurin aiki ba, amma dai kafin hakan ta fadawa Hajiya inda tace bakomi duk randa xatai exam ta dauke mata aikin ranar. Jarrabawar taxo mata da sauki saboda tayi karatun waec.
A wata ranar laraba ta dawo daga skul kimanin 6:00 na yamma ta shigo soron gidan ta gaji liqis don English sukai tun safe take makaranta sai yanxu suka kammala ga uwar yunwa na sakadarta sannan ga idonta dishi dishi take gani saboda tsabar kallon farar takadda da tayinin yi.
Deni shima da dawowarsa kenan daga kasuwa ya tari gabanta cikin harzuqa yace "wlh babu inda zakije yau sakeena sai kin tsaya kin saurareni domin nagaji da halin ko in kula da kike gwadamun." ta nemi hanyar wucewa ta gefensa ya tare, ta kalleshi ranta a bace tace "rufa maka asirin da nayi shine ya baka damar kuma attempting dina?" ya marairaice yace "Sakeena dan Allah kiyi haquri ki saurareni, abunda nayi miki bawai da gaske nayi shine har cikin xuciyata ba kawai gwadaki nakeyi amma a lokacin da kin bani dama da kinga qarshen film din"
Sakeena ta saki baki tana sauraran wani kalar rainin hankali daga Deni, sai da yagama qarairayinsa tas tana sauraransa sannan tayi tafi tana dariyar rainin hankali ta kalleshi ido cikin ido ta fara magana"Da kyau! A nace da kyau Nuraddeen Lawan👌🏾. Kayi qoqarin kwarai wajen shirya wannan wasan kwaikwayon amma sai dai kayi kuskuren samun masu sauraro domin sakeenar da ka dauka ada can baya har kuke kiranta da akuya yanxu ba itace a gabanka ba. Ka rasa da abunda xaka gwadani sai da zina? Meyasa baka gwadani da sata ba? Meyasa baka gwadani da addini ba? Meyasa baka gwadani da tsafta ba? Ko tsoron Allah? OH! Sai da zina? Saboda inna baka kaina shikenan sai kai amfani da hakan daganan kuma kaga sai na wakilci ragowar mata duk inda ka xauna hira sai kace ai duk mata yan iskane ko? Ko kuma inkaje gurin wata itama saika kuma gwada ta? Wannan kalma ta GWAJI da ita samari irinka masu tsatsar xuciya suke amfani suna bata rayuwar yayan mutane. OK na yadda ka gwadani, kaima Allah ya kawo wanda xaiwa yar cikinka abunda kaimun da sunan gwaji" tana gama fadar haka ta kewayeshi ta wuce ta barshi cikin wani irin Al ajabi.
A wannan dare kamar wancan rana Deni be rintsa ba, lallai ya yadda da ake cewa yayan qauye hikima ce dasu da basira yau sakeena da ya raina wayonta da iliminta ta shayar dashi mamaki, domin tayi abunda ko wadanda aka haifa a birni suka rayu aciki ba lallaine su iya ba. Wannan ma ai tafi su Hadixa da fiddausi wayo bare wata banxa Amina. Ya tattara hikima da xantukan qarya dan ya wanke kansa a gurinta amma kuma reshe ya juye da mujiya domin tayi masa wankin babban bargo cikin hikima da azanci, wannan yarinya duk randa ta samu ilimi wadatacce ba qaramar fasihiyar mace xa aiba. Tayi masa bulala da kalamanta kuma ya daku sosai. Yayi wata nadamar akan wacce yayi a baya wato haka zina ke zubar da qima da haifar da raini tun kafin a aikatata? To inaga an aikata? Ya dunga juyi cikin wani irin yanayi wanda yayi Kama dana farin shigan soyayya.
Ita kuwa Sakeena tunda ta barshi a soro bata qara tunashi ba, taje tai wanka taci abincinta dare nayi ta miqe tai baccinta harda munshari.
***** ***** ***** ***** ***
Rayuwa taci gaba a haka sai dai wata damuwa daya itace Deni ya kafawa sakeena takura, yawan kallo, tare mata hanya, binta duk inda xataje da daddare kamar wani bodyguard. Tun abun baya damunta har ya soma damunta don bataso wani a gida ko a waje ya fahimci halin da suke ciki.
Tuni ta kammala jarrabawarta tayi candy ta kuma cigaba da xuwa aikinta cikin kame kanta da nisantar duk wani abunda xai hadata da wani namiji. Yayin da su Amina suka dora daga inda suka tsaya na yawon bin maqota ita kuwa Hadixa tafi gane danna waya da hirar masari masu kudi, duk da basu rasa manema ba amma fa su da uwarsu sun tsaya tsayin daka wajen ganin sai mai kudi duk kuwa da fadan da Baba ke musu na suyi amfani da dama su fidda miji.
A yauma kamar kullum ta fito xata tafi aiki Deni ya fito daga dakinsa ya tareta ta kewayeshi xata wuce yayi ajiyar xuciya yace "I LUV U SAKEENA" wannan kalma ta daketa sosai kuma itace ta hanata fitar datayi niyya ta tsaya tsam tana nazarin kalmar karon farko a rayuwarta da aka furta ana sonta. Tayi matuqar qoqari wajen yakice kalmar daga ranta, ba tare data juya ta kalleshi ba tace "u'r too late" ta sa kai ta fita daga soron. Ya tsaya idonsa cike da kwallah dan ya rasa abunda yakeji game da Sakeena, ya kasa tantancewa soyayya ce? tausayine? Ko Kuma ganin qimarta yake? Kawai dai ta tsaya a ransa tayi kyam duk kuwa da yasan ba itace kalar matar da yakeson aura ba. Saddiq dake bacci a daki ya fito ya tadda Deni a soro ido cike da kwallah ya dafashi yana tambayar meye? Amma bai bashi amsa ba sai komawa yayi daki ya kwanta yana mai tausayin kansa.
Acan makaranta itama haka ta yini kalmar Deni na yimata amsa kuwwwa a kunnenta kamar a lokacin ya fada. To me hakan ke nufi? Wata salon yaudarace ko kuma gaskiya? Kai! Inma gaskiya ce itadai anshata ta warke bazata qara yadda dashi ba.
Kafin a tashi ta amsa kiran Hajiya ta amshi albashinta dan yau wata ya qare, tai godiya taje gida ta saka 2k a banki kamar yadda takeyi duk wata 3k kuma ta bawa Iya wacce ita sakeena ke bawa duk sanda ta dauki albashi tace ta kasafta musu har Baba idan Iya taqi karba tace haqqinta ne tayi yadda taso dashi sakeena kan marairaice tace baki daukeni ya ba kamar yadda na daukeki uwa. Dan haka Iya ta daina musu take karba ta raba musu tare da tarin adduoin nasara a rayuwar sakeena.
Iya ta warewa sakeena 1500 ta bata, ita kuma ta dauki 500, sannan ta ware 1000 tace "wannan kije ki siyo taliya ko macaroni ki bawa Baba dan ba a dau bansho ba kuma inaga aljihunsa babu komai gashi ko kwaya bamu da ita a gidan. Kuma shima Deni inaga kwana biyu kasuwar sai a hankali "Sakeena tace "to iya ta dauki 500 a cikin nata kudin ta qarawa Iya tace kema ki dau 1000 kinga anraba kenan, ni turare kawai xan siya da always, kema kisai turare ki fesa Baba yaji qamshin" Iya takai mata bugu tana dariya tace "yar banxa kin maidani kakarki dai, to nagode Allah yayi albarka" sakeena itama tana tata dariyar tace "Amin" ta fita da kanta taje kanti ta siyo taliya leda 2 macaroni ma leda 2 ta nunawa Iya tace "ka kayan Baba sai ki kaimasa" Iya tace "a a jeki da kanki ki kai masa ya saka miki albarka." tai sallama qofar dakinsa ya amsa yana xaune yana tunanin inda xashi ciyo bashin abunda xa a ci gashi har biyar ta kawo kai ba a dora abincin dare ba da rana ma dumamen tuwon jiya akaci.
Sakeena ta gaisheshi ya amsa da tambayarta aikinta tace "Alhamdulillahi Baba munyi salary ne shine na kawo wannan gashi babu yawa ta fada tana tura masa ledar gabansa wacce har canjin ta hada masa 280" ya dauka ya bude, ya dungawa shiwa Sakeena albarka da adduar Allah yajiqan iyayenta. Ya kwallah kiran Hafsatu, Iya ta shigo tana gyara dankwali tace "gani malam ya bata ledar da kudin yace "gashi sakeena ta kawo mana abunda xamuci saiku dauka ki dafa mana ga kudinan ayi cefane." Iya tace "a a malam sa kudinka a aljihu xanyi cefanen a nawa kason data bani" yace "To Allah yayi muku albarka keda diyar taki Allah ya qara cika hannunku da arxiqi na halak" suka amsa da amin suka fito tare, Baba ma ya dauke yan canjin da sakeena ta bashi ya rufe dakinsa ya fita.
Hajjo na xaune kan tabarma Hadixa na gefenta tana danna waya, ta dokawa su Iya harara tai tsaki tace "ni kuma nawa yayan Allah ya tsine musu ko? Tunda kin qullah makirci an sakawa yar riqo albarka? To itama wayasan abunda take kafin kudin suxo? Ai wlh gara intaxa da yayana da su dunga yawan bin maxa da sunan aikatau"
Daga Iya har sakeena babu wanda ya kulata harta gama, Iya ta aiki Sakeena ta siyo mata kayan miya suka dora girkin dare.
Da daddare an taru akan babbar tabarma a tsakar gida saboda zafin da ake gashi babu wuta, kowa da kwanon taliya da miya harda salad a gabansa yanaci yayin da suke ta hira hade da santi, Deni dai yanaci yana kallon sakeena babu ko qiftawa yayin da take a takure abincinma ta kasaci saboda kallon da yake mata har saddiq yaso ya fahimci akwai wani abu tsakaninsu.
Abun kunya Hajjo nacin taliya tana sakin santi da cewa "yanxu fa da ace a gidan arxiqi muke da abincin nan kowa nasa da rabin kaza akai"😂 Baba ya dubeta yana murmushi yace "hakan ma a godewa Allah Hajjo wani ko wanda be kaishi va nema yake, ai babban arxiqi shine wannan gamu guri guda munacin halak cikin kwanciyar hankali" saddiq kuwa cewa yayi "kyaleta Baba wlh hakanma abincin yayi dadi yanxu wa xaice babu nama aciki?" haka dai aka dunga hira har suka gama aka tashi sallar Isha.
Bayan sallar Isha sakeena ta gyara fuskarta da powder tace da iya xataje wani store a qasan layinsu siyo turare. Tace "to sai kin dawo karki dade banason fitar dare"
Ta fita tana tafiyarta a nutse har taje store din tasai turarenta "lailatus sahara" da kuma always (pad) ta juyo xata fito daga Deni a bayanta wanda tun daga gida yake binta bata sani ba.
Ta hade rai sosai taji kunyar ganinta da yayi tana siyan always, ta biya kudin suka fito ya jera da ita ya karbi ledar hannunta harta hanashi taga yana shirin fuzga ta sakar masa. Ya leqa ledar ya ciro always din, ta qara daure fuska tamau dan karyayi mata xancen iskanci. 😂😂😂
Yace "Hmmm Sakeenatu yan matan Iya da Baba, banda abunki ai bai dace kije siyan wannan abun da kanki ba, dan in anga kin siya ansan kene xakiyi amfani dashi, da kin aikeni ai sai insiyo miki da kaina inkawo miki basai kin fito da daddare ba kina qamshin turare harda saka powder. Haka ya dunga xantukansa kamar motsatstse, ita dai ko tari batai ba balle bashi amsa. Sai sukaxo soron gida sannan ya miqa mata ledar yace "gashi ki kiyaye abunda na fada miki dan inada kishi kan abunda nikeso" ta karbi ledarta tare da tabe baki, ta watsar da xantukansa anan inda yayisu ta shige gida. Shima sai dayaga shigarta sannan ya juya ya koma majalisa.
Ranar alhamis suna zaune da Iya aka aiko yaro ana sallama da sakeena, tun kafin Iya ta lallabeta akan ta fita ta miqe ta gyara fuskarta ta qara fesa turare tasa hijab ta fita.
Suna tsaye da saurayin nata da yace sunansa yunusa yanata xuba tana binsa da kallo ba tare data tanka ba, ta matsu ya tafi don taje ta kwanta. Deni ya sawo kai soron, idonsa tas akansu albarkacin hasken wutar nepa. Ya doka tsaki ya shige cikin gida.
Bata wani jima ba ta shige gida. Deni kuwa ya kwana cikin wani irin bahagon yanayi ya rasa ina zaisa kansa yaji sanyi, ji yake kamar yaje ya samu sakeena ya nada mata dukan tsiya saboda tsaiwar da tayi da wannan yaron. Ya juya ya kuma juyawa ya rasa mafita kawai saiya fashe da kuka yanayi yana toshe bakinsa saboda kar saddiq yajishi da haka bacci ya daukeshi cike da mafarkan sakeena.
Wayewar garin juma a tun daga sallar asuba yana daki bai fito ba breakfast dinsa ma sai daki Hajjo tasa aka kai masa. Bashi da niyyar fita kasuwa domin zuciyarsa babu dadi sam.
Sakeena ma yau babu aiki a makarantarsu saboda rasuwar wata malama da aka tashi da ita har taje ta dawo, dan haka tana zaune tana taya Iya qullin kayan miya.
Qarfe goma da rabi na safe 10:30 AM Deni ya shigo cikin gidan a lokacin duk ahalin gidan suna tsakar gida kowa yana harkarsa. Direct gurin da Baba ke alwala Deni ya nufa, ya tsuguna gefen Baba yace "Baba aure nakeso, ka dubi Allah kayimun."
Duk wata halitta dake gidan hankalinsa ya dawo kan Deni da Baba, suka kasa kunne kwarai dan jin amsar da Baba xai bashi. Baba ya gama nazarta Deni kuma ya lura yana cikin hayyacinsa ya kada kai yace "To Nuraddeen wacece xata aureka baka da halin riqe ta?" yayi murmushin takaici yace "Baba wacce nakeso take sona babu ruwanta da xan iya riqeta ko baxan iya ba, soyayya takemun tsakani da Allah babu abunda muka sani sai san junanmu." Hajjo ta xaburo xatayi magana Baba ya daga mata hannu ta dakata. Ya kuma kallon Deni yace "wacece kake so din Nura?" Baiyi magana ba sai tashi da yayi yaje ya riqo hannun sakeena da gabanta ke masifar faduwa. yana janta tana turjewa mutan gidan na binsu da kallon mamaki, bai barta ba saida ya kaita gaban Baba ya duqar da ita yace "Baba sakeena ce wacce nakeso kuma take sona mun yarda xamu rayu tare duk wuya duk dadi" Baba ya dubi sakeena da take a mutuqar tsorace gumi sai yanko mata yake ta ko ina yace "Sakeenatu da gaske ne kuna san juna keda Nuraddeen?" Ta girgiza kai da sauri ta qara da cewa "wlh qarya yake yau na farajin wannan maganar daga bakinsa" Bata ankara ba taji mari "Tas" a fuskarta ta juya taga Deni na huci, maganar da ya farayi cikin qunar xuciyace yasa ta gane shine ya mareta "Ni xaki rainawa hankali? Soyayyarmu xaki qaryata Sakeena? Banxaci haka daga gareki ba, na dauka soyayyar gaskiya kikemun" yana gama fadar haka ya fashe da kuka. Sakeena kuwa kanta a qasa taji duk ta muxanta.
Baba ya kwantar da kan Deni a kafadarsa yana buga bayansa cikin lallashi. Yayin da sakeena ke duqe gabansa cikinta wata iriyar fargaba da debe tsammani.
Hajjo kamar an kunnata ta zaburo ta fara magana cikin daga murya tana girgaixa Deni "Deni yarona dan albarka meya sameka haka yau? Me abokai suka baka kasha? Nasan dana baya shaye shaye, waya bata maka tarbiyya da shan ganye? Nasan Kana cikin hayyacinka baxaka taba zabomin sakeena a matsayin suruka ba" Yana cigaba da kukansa yace "Hajjo acikin hayyacina nake, babu abunda nasha kuma ina qara tabbatar miki ni Sakeena nakeso indai kina qaunata kuma kunason xaman lfy a auramun ita"
Su fiddausi suka fashe da kuka duk su ukun, Hajjo kuwa ta rufeshi da duka iya qarfinta tanayi tana kukan cewa "wlh baka isa ba duk wani burina da tanadina akanka dan ka xama mutum ka samomin matar kwarai amma rana tsaka ka dakko min yar talaka jikar talakawa wacce aka haqiqance uwarta ma a bariki suka hadu da uwarta" Baba dayaga abun nata bana hankali bane ya janye Deni ya dakawa Hajjo tsawa. Ya tasa Deni a gaba yayi alwala ya canja kaya suka fita tare.
Suna saka qafa waje gidan ya hargitse, bayan Iya taja sakeena daki su Fiddausi da Hajjo suka dunga kuka kamar wadanda saqon mutuwa ya ruskesu yayin da Saddiq uban marasa mutunci yace da Hajjo kiyi shiru Hajjo in an isa ki xubar da hawayenki saboda wata tsinanniya Allah ya tsinemun, ita din banxa ta auri dan bakyaso itace ta haifar miki shi? Dama ni tun ranar da mukecin taliya naga sai kallonsa take shegiya me idon mayu. Amina ta karbe maganar da cewa "ai dama ta taba cewa akwai wanda takeso muna daukanta mahaukaciya ashe yaya Deni ta hango, me xaiyi dake? Wlh asiri sukayi masa tsinannu irin tsiya" Haka suka dunga xagin sakeena da Iya cikin tsabar rashin tarbiyya in wannan ta gama wancan ta karba. Ita dai Hajjo bata tanka musu ba kukanta takeyi, daga qarshe Saddiq ya rufe xancen da cewa " Allah ya tsinewa duk bokayen Baggadano domin sune sukai asiri dan uwansu ya haukace sannan uwarsu ta xubar da hawaye yayi kwafa da qarin cewa Ayi auran mugani" ya tashi ya fita.
Acan daki kuma xaman jugum jugum ya shiga tsakanin Iya da sakeena kafin Iya tayi qarfin halin fara magana "Sakeena dama Deni shine wanda kikeso din?" Bata bawa Iya amsa ba sai fashewa datai da wani irin kuka mecin rai tace "Iya dan Allah kiyi haquri ki yafemun na janyo miki xagi da cin mutunci bakiji ba baki ganiba har iyayena ma dake qarqashin qasa basu tsira ba." Iya tai shiru na dan lokaci kafin ta fara magana "Sakeena bawai san aurenki da Deni ne banayi ba Deni yaron kirki ne kawai qiyayyar uwarsa da yan uwansa nake hange miki don nasan abune mawuyaci su soki saboda baki da gata su kuma diyar masu hannu da shuni kuma yar gata suke buqata ya aura. Amma ki fadamun gaskiya akwai soyayya tsakaninku ko babu?" Sakeena bata da mafita illah fadar gaskiya dan haka ta fadawa Iya komai tsakaninta da Deni sai dai ta boye mata yunqurin bata mata rayuwa da yayi domin tayi alqawari baxata tauna masa asiri ba.
Iya ta kwantar da sakeena kan cinyarta tace "to har yanxu kina sonsa ko kuma bakya sonsa ki fadamun gaskiya dan baki da wacce xaki fadawa bayan ni" ta qara gyara kwanciyarta a cinyar Iya tace "wallahil azim Iya na haqura da Deni tun watannin baya, abunda ya fada yau kawai raayinsa ne ba nawa ba dan bamu taba tsaya munyi musayar kalmar soyayya dashi ba, ni burina yanxu be wuce insamu lfyar ido ba inyi karatu" Iya tace "To naji dadin jin hakan da sannu Allah xai kawo miki dai dai ke wanda yan uwansa xasu mutuntaki" a haka maganar ta qare, amma kuma Iya dake babbace saita fahimci Sakeena dai nasan Deni kawai ta haqura ne saboda qalubalen da take ganin xata iya fuskanta inta amince da soyayyarsa don a kalaman sakeena ma na yanxu batace bata sonsa ba cewa tai ta haqura dashi.
A wannan rana dai aka raba tukunya a gidan Mal Lawan don koda Hajjo wacce keda girki ta gama girkin rana bata bawa Iya da sakeena ba. Suma ganin haka basu tambaya ba suka dora nasu daban.
Da daddare ma haka aka kwatanta, kuma Baba ya gani amma baiwa Hajjo magana ba wadda ya lura qiris take jira tayi rashin mutunci.
Ya gama cin tuwo ya kunna radio yana saurare yayin da Deni ke gefensa wanda yau babu inda yaje suna tare da Baba tun sanda abun ya faru. Hajjo ta matsu kwarai su kebe da Danta ta kwabeshi ta fada masa abunda take hange masa na auran diyar mekudi amma kash! Daga Baban har Deni sunqi bata damar hakan.
Duk suna kan tabarma ita da mijinta da yayanta inka dauke bare (sakeena da Iya) dake can daki a qunshe sunacin ragowar abincin rana a matsayin dinner. Hajjo ta fara magana kamar yadda yayanta suka shirya mata "malam dama akan maganar daxu ne ta Deni, wato shirmen da yayi na cewar sakeena yakeso. To nifa gaskiya ban yadda ba a matsayina na wacce tai naqudar haihuwar da rainonsa kuma ni banaso ma dana yayi aure yanxu na fiso ya fara samun aiki ya ramamun wahalar da nayi akansa kafin yaje ya auro wata. Saboda haka wannan shine tsarina maganar aure ga Deni a jingineta dan baxata yiwuba wata can ta qulla makirci tayo masa shunen yar riqo dagani ya fara xuwa kasuwa ehe 😏" ta qarasa tana murguda baki kamar yarinya.
Baba ya kashingida fuskarsa bata nuna komai ba yace da Hajjo "innaqi bin umarnin naki fa uwata?" a harxuqe tace "sai nayi babban rashin mutunci ayi wacce xa ai don baxan xauna wacce batasan ciwon haihuwa ba ta kassaramun rayuwar Da" Hadixa dake saitin Hajjo tayiwa Hajjon alamar jinjina 👍🏼 yadda Baba da Deni baxasu lura ba.
Deni dai yana xaune kusa da Baba yana jinsu baice komai ba.
Iya ta riqo hannun sakeena suka fito daga daki suka nemi guri kan tabarmar suka zauna. Deni yana ganin sakeena ya gyara xama ya kafeta da ido kamar yadda sauran yan uwansa suma suka kafeshi da ido saboda ganin kallon da yakewa sakeena wasu ma harda tsaki.
Bayan gaisuwa da sannu da xuwa da sukai masa iya tace "Dama na kawo sakeena ne ta fada maka abunda ta fadamun da bakinta don waqa a bakin me ita tafi dadi."
Baba ya dubi sakeena yace "Ina sauraranki sakeenatu" babu wani shayi ko shakkar Deni yana kusa sakeena ta fara magana "Baba, kayi haquri da abunda xakaji, abunda ya faru daxu babu yawu na a ciki, ni da Ya Deni bamu taba tsayawa munyi musayar kalmar soyayya ba balle fahimtar juna duk abunda ya fada ya fadane don muradin kansa amma wlh babu wannan tsakaninmu na daukeshi kamar yayana uwa daya uba daya wanda babu aure tsakanimu har abada. Ni a tsarina babu aure anan kwana kusa na fiso insamu lafiyar ido incigaba da karatuna dan Allah Baba kayi haquri" Baba ya gama sauraran sakeena tsaf kana ya juya ga Deni da shima yake kallonta baki bude yace "Nuraddeen kaji abunda Sakeenatu ta fada, saboda haka kayi haquri ka nemi wata kasan baxan mata dole ba kamar yadda banwa yayana ba, inaso daganan maganar ta mutu Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi"
Hajjo ta saki ajiyar xuciya afili duk suka juyo suna kallonta, sannan ta dora da cewa "Alhamdulillah yanxu naji batu, kunnemi xaman lfy kenan? Allah ya kiyaye gaba haka kawai da xa a tsiro mana da jafa 'I muna xaman lfy" Babu wanda ya kulata, Baba ya tashi yayi waje Deni ya bishi, sakeena da Iya kuwa suka shiga daki.
Su fuddausi suka Saki tafi tare da shewa, Amina tace "gaskiya Hajjo aikinki yayi kyau acikin 15 minutes kin rusa qulunboton da akaiwa yaya Deni kinsa mutum yayi amai ya lashe." Hajjo tayi dariya ta bawa Amina amsa da cewa "Amina ai bar uwa akan danta, ai ita uwa babu abunda baxata iyaba dan ganin rayuwar danta tayi kyau" saddiq yace "shegiya wuya babu dadi ai fitar da nayi gidan wani malami naje yace asiri akaiwa Deni da kawukan mage shiyasa ya rikice atake a gurin ya karya asirin sannan nasa yayi turaren barkono dan ramako ga wanda yayi asirin" Hadixa tace "da Allah malam yimana shiru sarkin kwai, a fitarka har akai aikin karya asirin kuma aikin yaci? Ba dama kaji sanyin guri sai kahau sakin kwan jimina" ya taso yana durawa Hadixa xagi da cewa xai tumurmusata wlh dan shi ba saanta bane ko Zarah dake gidan miji ya girmeta bare ita. Hajjo ta shiga tsakaninsu da taga abun xai xama dambe.
Kwana biyu bayan wannan wato Lahdi da safe Iya ta aiki Sakeena kanti siyo sabulun wanki lokacin wajen qarfe taran safe, taje ta siyo ta shigo soron taji an danqi hannunta anjata har cikin daki. Ta firgita kwarai da tayi arba da Deni ido jawur yana kallonta, ta qanqame jikinta dan a tsorace take dashi rabon data ganshi tun shekaran jiya da daddare. Ya rutsata a bango yayi mata katanga da hannunsa yadda bata da damar guduwa.
Ya gama qarewa fuskarta kallo yayin da idonta yake a rufe ruf tana jiran abunda xai mata, yayi murmushin takaici kafin ya toshe mata baki ya fara magana. "shiiii, kimun shiru, ba kin qaryatani ba? Kince bama soyayya? Ni xaki watsawa rayuwa? Rayuwar dana wahala nida iyaye na wajen ginata shine a yan kwanaki zaki rushemun ita? To ai shikenan kinyi dai dai Sakeena Abbakar Liman, amma tunda kinqi a auramun ke ai saimu muyi rayuwar dadiro ko? Kinga hakan ma yafi muyi ta sheqe ayarmu muna haifawa iyayennu yaya shegu tunda sunqi subi maganata sunbi taki, kinga ma mun huta mu kwana muna sheqe ayarmu da safe ki tafi aiki intafi kasuwa su kuma suyi mana rainon yayan rariya su dau dawainiyarsu kamar yadda suka dau tamu su basu abinci kamar yadda suke bamu tunda son xuciyarsu ya hanasu su gane kina qaunata kamar yadda nake qaunarki, son zuciya ya hanasu su bamu dama mu kafa namu gidan mu xama iyalai, in sunqi ji ai baxasuqi gani ba. Ya dago fuskarta ya matse mata baki yace ai hakan yayi ko?"
Ta fara kici kicin kwacewa, ya fada hannunta duk biyun ya murde mata sannan ya qara matse bakinta yace "ai wlh babu inda xaki sai kin amince kuma kin furta cewa shawarata tayi" Sakeena dataji matsa kuma taga alama yaufa Deni ba a hankalinsa yake ba sai tace "Eh shawararka tayi" yayi dariya ya kuma kafeta da jajayen idanunsa kana ya saketa, ta dunga maida numfashin wahala tana xare ido. Ya sunkuya ya dakko sabulunta daya fadi lokacin daya murde mata hannu ya miqa mata. Ta karba jikinta na rawa ta nemi hanyar fita.
Yayi saurin dakatar da ita yace "tsaya saurin me kike nanfa dakin nan da dare xai xama namu ni da ke, don yau xamu fara soyewa, yanxu xanje kasuwa in shaa Allahu xan samo kudi xan fadawa Alhaji yau ango nake ya bani aron kudi in siyo miki kaza da fresh yo, kafin na dawo ki wanka kimun kwalliya kisa turare sosai inadason qamshi." cikin rawar baki tace "To" har ta kusa kaiwa kofa ya kuma tsaidata yace "dakata! Karki xaci xakimun irin wancan rainin hankalin da kikaimun na qaryata soyayyarmu ki kwana lfy. Wlh in kikaqi xuwa har dakin uwar taki xanxo in daukeki muxo muyi soyayyarmu. Ya kuke da itama? Ya fada da alamar tambaya, Babarkice ko kakarki?" Sakeena mararta ta kuma qullewa, lallai Deni ya zare tunda har ya manta matsayin Iya a gurinta, to ko wiwi yasha ne? Ita dai ta qara mai ta cire sakatar dakin xata fita ta kuma tsinkayan muryarsa yana cewa "ke! Ki daina wannan saurin haka don banason munafurci duk wanda ya ganki kice masa daga dakin dadironki kike kuma in anjima inxakixomun karki xomun kina wannan saurin, yanga xakiyimun yanda zansan mace ce ke ba namiji ba"
Babu shiri ta canja salon tafiyarta a hankali don ta samu su rabu lfy.
Baba, Iya da kuma Hajjo sukai baya da sauri jin ana shirin fitowa daga dakin, bayan sun gama jin komai. Suna kaucewa sakeena na fitowa tai cikin gida da sauri a tsorace take sosai. Ta shige uwar dakin Iya ta qudundune a gadon gabanta na faduwa. Iya ta dubeta tace "sakeena naga kin kwanta kin fasa mana wankin ne?" cikin qinqina tace "Iya bani da lfy ne sanyi nakeji har cikin bargona baxan iya ko fita tsakar gida ba balle wanki"
Iya ta dunga kallon sakeena da tausayi ta fuskanci a mutuqar tsorace take, to ita kanta uwar sakeenar a tsorace take da kalaman Deni balle sakeena.
Lallai wannan yarinya sakeena da xurfin ciki take, wato badan Baba da yake shirin fita yaji tashin magana daga dakin Deni yaxo ya kirasu ita da Hajjo dan jin abunda suke fada ba da ita kadai xata shanye wannan tashin hankalin?
Iya na xaune ta rasa mafita? Sai aikin tunani daga taji anshigo gidan ta furgita don tana zaton Deni ne zai shigo daukan sakeena a gabanta kamar yadda yayi alqawari. 😂😂😂
Hajjo na can daki tana ta zarya cikin rashin gane takameme wane abu xatai, kuka ko dariya baqin ciki ko farin ciki. yayanta sai tambayarta suke tai musu shiru.
Baba kuma gaba daya yafisu tashin hankali a matsayinsa na namiji kuma shugaba a gida wanda in abu mai kyau ya faru xai xama nasararsa in mara kyau ya faru xai masa laifinsa. Ya tufka ya ware, ya kuma tufkawa ya warware kafin ya yanke abunda yake ganin zai zama masalaha da kuma yiwa duk bangarorin biyu adalci wato Iya da Hajjo dan haka ya qulle daki ya fita.
Iya tai saurin fitowa jin qulle qofarsa tace "Malam yanxu inka fita Deni yaxo daukan Sakeena kamar yadda yayi alqawari ya xanyi dashi? Gida babu namiji kuma kasan yafi qarfinmu, ka rufamun asiri ka dubi girman amanar dana dakko ka xauna a gida karka fita Deni ya batawa sakeena rayuwa" kafin ya bata amsa Hajjo ta fito cikin masifa tace "ban haifi dan iska ba Hafsatu, kowa yasan Deni natsatstsan yarone kafin xuwan sakeena gidan nan dan haka inma iskancin ne sakeena ta fara sakashi a hanya." Iya cikin nata masifan itama ta tasowa Hajjo "Hajara ai kinji da kunnanki yanda lalataccen danki kewa sakeena tayin xuwa dakinsa dan aikata masha'a saboda haka saiki fadan waye dan iska a cikinsu?"
Baba ya tsaya yana nazarinsu duk su biyun, Allah yasa gidan babu kowa, su Amina anfita office (yawan bin maqota) yayin da sakeena ke qulle a uwar dakin Iya. Baba ya daka musu tsawa da cewa "Duk wacce ta kuma magana be yafe mata ba" sukai shiru a tare. Yasa kansa ya fita.
sai ranar asabar xan kuma posting in shaa Allah.
Hajia ☺
[7/31, 2:09 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
9⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Har dare sakeena bata yadda ta fito tsakar gidaba ita kadai, ko bandaki zata shiga sai tace iya ta rakata, yayin da iya ke rakata ta tsaya a kofar daki har sakeenar ta gama abunda xatai ta fito sannan su tafi. Iya kuma bata tambayi sakeena meye dalilin hakan ba kuma bata nuna mata tasan komai ba. Baba ya dawo gida be nemi kowa ba kuma bece da kowa komai ba.
Koda dare yayi abun dariya Iya ta saka sakata a daki duk kuwa da xafin da ake ita keda girki amma ko dakin Baba bata kallaba ita kawai ta tsare sakeena kar Deni yaxo ya jata kamar yadda ya fada. Shima Baban Iya haushinsa takeji saboda da taga hankalinsa a kwance yake be damu da furucin Deni ba ko daukan mataki akansa kodan ba diyarsa Deni ke yunqurin batawa? Wannan shine tunanin Iya.
Haka sukai bacci ita da sakeena cikin zafi amma duk da haka iya tana baccin tana farkawa dan sai takejin kamar ana buga kofar dakin, daga qarshema saita tashi ta dauro alwala tahau nafila da roqawa sakeena miji nagari.
Wayewar gari Monday gidan ya dade kamar yadda aka saba, Sakeena ta nufi aiki Deni kasuwa, Saddiq makaranta yayin da yayan gata su Amina ke gado ana bacci Baba ma ya fita sai Iya da Hajjo a tsakar gida kowacce na harkokinta.
Sha biyu da rabi Sakeena ta shigo gidan jikinta a sanyaye qalau, tun jiya da abun ya faru xuwa yanxu jikinta a sanyaye yake ga wata irin faduwar gaba data sakata a gaba amma duk tana danganta hakan da tsoratarwar da Deni yayi akanta. Ta xauna ragaf a gaban Iya dake kwance. Iya tai mata sannu dan a zatonta gajiya ce ta sata wannan sanyin jikin. Tace "sannu Sakeenatu ta miqa mata kwanon awara tace maxa ci kafin a qare abincin rana" taja kwanon gabanta tanaci tace "Iya ina kika samu awara haka?" Iya ta bata amsa da cewa "Zahra ce taxo ta kawo mana ita fall samira shine aka kasa aka bamu" Sakeena tace "Allah sarki shiyasa naga dakin naki kaca kaca ashe anxo da qawayenki" Iya ma tana dariya tace "eh yan qaniya suncimun gyada ba sun barmin dakin kaca kaca"
Tana gama cin abincin ta share dakin Iya da yayan Zahra suka bata sannan ta fita alwala. Ta leqa dakin Hajjo suka gaisa da Zahra a mutunce har tana tambayar sakeena aiki, Zahra da Deni a yayan Hajjo kam sune basu da matsala dan sun dauki Iya a matsayin uwarsu. Ta tambayi zahra ina yaran tace "su Amina sun fita dasu maqota" Sakeena ta qarasa bakin famfo tana alwala yayin da tabar Zahra da Hajjo sunata qus qus dinsu a hankali badan zargi babu kyauba da saitace xancensu da Deni ake fadawa zahran.
Kafin La'asar Baba ya dawo, ya kira Zahra suka dade a daki sannan suka fito yana yiwa yan jikokinsa yayan Zahran wasa. Koda xata tafi har daki ta tarda Sakeena wacce tunda taga 5:30 tayi ta qule uwar daka saboda da tasan koda yaushe Deni kan iya dawowa ita kuwa yanxu tsoronsa take fiye da komai a duniya. Tana dariya tace "Anty Sakeena kece haka a uwar daka a dai dai wannan lokacin? Ai da kin fito tsakar gida kinsha iska" Sakeena ta maimaita kalmar da zahra ta fada "Anty Sakeena" a zuciyarta, kafin ta bata amsa da cewa sanyi nakeji shiyasa na shigo uwar daki Anty Zahra" tace "to shikenan dama tafiya xanyi nace bari naxo nai miki sallama" Sakeena kanta ya kuma daurewa amma dai sai tai tunanin ai zahra karamci gareta ba wani abu bane dan taxo mata sallama kuma ta kirata da Anty. Tace "to nagode Anty zahra da qalau nake dana rakaki titi" tai saurin cewa "a a bakomi keda bakijin dadi yi xamanki su Amina sa rakani. Allah ya qara sauqi kinji" tasa kai ta fice
Kiran sallar magrib da sallamar Deni cikin gidan lokaci daya suka shiga kunnen Sakeena, qirjinta yayi wata irin bugawa har saidata dafeshi. Sai data tabbatar Deni yabar gidan ta fito a gurguje tai alwala ta koma daki.
Ga al'adar gidan bayan sallar magrib ake haduwa a babbar tabarma a tsakar gida aci abinci, in kuma lokacin sanyi ne ko damina sai a shiga dakin Baba. Wannan shine abunda Baba ya kafawa gidansa. To yau dai da jiya Sakeena duk bata halarci xaman cin dinner tare da su ba acan daki Iya ke kai mata.
Kowa ya tasa kwanon tuwonsa a gaba yanaci yayin da Sakeena ke uwar daka a xaune cikin wata irin fargabar da batasan kota mece ba. Baba ya kalli Iya yace "ina Sakeenatu?" ta bashi amsa da cewa "tana daki" ya kalli Amina yace "jeki ki rawon ita" Iya tayi Hamdala a zuciyarta dan bata raba daya biyu Baba tsakani xai yiwa Sakeena nan da Deni saboda in xaiyi magana me mahimmanci a wannan lokacin yakeyi saboda kowa na gurin. Wanda ita tun jiya take dakon ganin Baban yayi haka. Ta qara gyara xama ta fallarawa Deni harara wanda ya tasa tuwo a gaba ko hannu besa ba.
Acan daki kuma Amina tana fadawa sakeena kiran Baba ta juyo tana mitar cewa kinyi abu ya dameki ko xama cikin mutane kin kasa, waya fada miki xakici ribar soyayya da dan masu gida?
Ta gaishe da Baba sannan ta koma jikin Iya ta rabe saboda ganin Deni a gurin wanda yake kallonta ko kunyar idon mutane bayaji. Iya ma ta qara janyo sakeena jikinta saboda tsaro 😄
Baba yayi gyaran murya ya fara magana bayan ya wanke hannunsa da ruwan da Hajjo ta miqo masa. "Sakeenatu kiyi haquri, saboda wasu fitintunu danaga suna shirin tasowa wanda ba lallai na bayyana miki suba da kuma gujewa fadawa halaka a jiya nayi miki karanbani, bayan na fita da rana na halarci daurin auren yar abokina bayan ansallaci azahar kenan, NA DAURA MIKI AURE" sakeena tayi matuqar qoqari wajen danne firgitar da tayi, aure kuma? Saboda me? Akan me? Ko Baba ya gaji da xamanta a gidansa ne? Ko kuma biyan bashi yayi da ita don yasan xatai masa biyayya sabanin yayansa wanda ta haqiqance baxasu yarda ba? To inko hakanne baxata karya yardar da Baba yayi akanta ba. Mutan gidan kuwa gaba daya kallon Baba suke a firgice ta bangaren Iya da Deni kenan wadanda suke kallonsa kamar sun warke daga cutar makanta da alama maganar ta dokesu. Ta bangaren Hajjo da ragowar yayanta kuwa fuskarsu wasai suna murnar cewa fa anrabu da qaya duk da suna baqin cikin sakeena ta rigasu aure amma suna da yaqinin Baba ba wani mijin kwarai (me kudi) ya samowa Sakeena ba. Saddiq kuwa cikin farin ciki ya furta "game over"
Muryar Sakeena ta katsewa kowa nasa tunanin inda tace "To Baba nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biyaka Allah ya bani ikon bin wanda ka auramun." tana gama fadar haka ta miqe xata shiga daki. Tana tunanin shiyasa tun jiya take a sanyaye tana jin faduwar gaba ashe aure ne ya hau kanta.
Muryar Baba ta katseta yace "Dawo Sakeena ban gama maganata ba, ban kuma fada miki wane na aura miki ba" ta dawo kamar yadda ya umarceta ta tsuguna tana murnushin qarfin hali tace "Baba basai ka fadamun ba, wlh kowanene ka bani xan soshi xan masa biyayya dan nasa baxanka cuceni ba kuma baxan biyaka dawainiyar dakai a kaina ba. Ka ciyar dani, ka shayar dani, ka tufatar dani, ka tsare mutuncina da lafiyata sannan ka bani ilimi da tarbiyya, to ni kuwa in ban maka biyayya ba ai nasan baxan gama lafiya ba" Baba ya jinjina kai cikin yabawa da fasahar harsher da hikima ta sakeena sannan yace.
"Kamar yadda na fadamiki, bayan idar da sallar azahar a jiya lahadi na xama waliyinki a inda limamin masallacin unguwar nan ya xama wakilinsa na daura auranki da Nuraddeen bisa sadaki naira dubu ashirin ajalan ma'ana bashi wanda xan biya nan da qarshen wata innasamu kudina kamar yadda addini ya umarceni inwa dana aure."
Wannan karon sakeena kam bata iya danne razanarta ba, a firgice ta dago tana kallon Baba. Yayin da Iya da sauran yaran gidan suka hada baki wajen tambayar Baba "wane Nuran?" Baba yana murmushi yace "Ai acikin bayanina nace muku dana Nura ko? In bashi ba wa Allah ya doramun nauyin yiwa aure?" sukai dubansu ga Hajjo dan ganin wane yanayi take ciki. Suka sameta fuska jiqe da hawaye wani na korar wani. A tare suka kuma kai dubansu ga Deni dan ganin shi kuma ya yadauki lamarin, suka tarar dashi ya duqa yana sujudu shukur (sujjadar godiya)
Baba ya kuma dorawa da maganarsa "Nuraddeen ga amanar Sakeenatu nan na baka, ka dubi Allah ka riqe da kyau ka tuna itafin marainiyace marashiyar uwa da uba bata da kowa yanxu sai kai duk nauyinta yanxu Allah ya dora maka, nasan baka dashi amma ka xage dantse ka kare mutuncinta da martabarta. Na sanya tare warku xuwa qarshen watan nan kafin nan na hada abunda Allah ya horemun xan kama muku inda xaku xauna da sauran hidimomi. Nura ka karbi amanar dana baka?"
Deni ya matso ya riqe hannun Baba duk biyun yace "na karba Baba in shaa Allah xan riqe sakeena da mutunci da amana baxan ci amanar da kabani ba. Allah ya saka maka da alkhairi, kuma nima kafin qarshen wata xan adana abunda nake samu inyi nawa shirin." Baba yace "to Masha Allah naji dadin jin hakan" ya juya gurin sakeena yace "sakeenatu kinji zabin da nayi miki, ina fata kin karba kamar yadda kika alqawaranta tun kafin kiji waye mijin" Ta kuma qasa da kanta tace "Na karba Baba, koda wani ka auramun xan maka biyayya bare kuma tsatsonka Allah ya xaunar damu lafiya kuma ya hada tsakaninmu da alkhairi" Baba farin ciki ya kuma bayyana a fuskarsa, ya dubi su Iya da Hajjo yace "kunji ra'ayin ma'auratan yayanku, mexakuce?"
Shirun mintuna biyu ya biyo baya kafin Iya ta fara magana "Allah ya sanya alkhairi Allah yasa abokan arxiqin junane" Hajjo ma a sanyaye ta fara magana "Allah yasa albarka Allah ya kade fitina" Baba ya amsa da Aminnn kuma Allah yayi muku albarka.
Deni ya matsa gaban Hajjo yace "Hajjo ga matata nan sakeena, itama yanxu yarkice kamar yadda nake danki kisa mana albarka" tayi murmushin yaqe ta shafa fuskarsa tace "Allah yayi muku albarka Deni" Qannansa suka hau harararsa kamar idanunsu xasuyo waje, shi kuwa besan sunayi ba sai washe baki yake.
Deni shiya fara tashi daga gurin, ya nufi bakin famfo, Hajjo da Iya kowacce ta nufi dakinta xuciya babu dadi, Baba ma ya shige nasa dakin akabar sa idawan qannan miji da ganin yanayin da sakeena da Deni zasu kasance.
Sakeena ma ta miqe ta nufi dakin Iya, Deni dake tsaye a gurin famfo ya kafeta da Ido itama akai sa a ta kalleshi. Ya ware mata hannayensa yana mata murmushi yana nufin taxo, kallonsa take babu ko qiftawa yayi mata kyau sosai cikin polo shirt da Blue Jeans haka kawai taji baxata iya watsa masa qasa a idoba, a hankali ta nufeshi cikin slow motion ta fada jikinsa suka qanqame juna suka saki ajiyar tare. Ai su Fiddausi daganin haka duk suka baje kowa ya nemi hanya 😄 Saddiq kuwa cewa yayi a fili gayan nan fa zaija kaya shege.
Deni dai ya tafi wata duniya tunda yaji sakeena jikinsa, ido lumshe yanata yawo da hannayensa a tsakiyar bayanta. Yayin da ita kuma tayi luf a jikinsa tana shaqar qamshinsa. A hankali ta janye daga jikinsa cikin jin kunya tai qasa da kanta, yasa hannu ya dago habarta yana qarewa kyakykyawar fuskarta kallo. Yace "Sakeena kinga hukuncin Allah ko? Cikin ikonsa ya nufemu da xama abu daya. Ki yafemun abunda nai miki abaya dan Allah" tai murmushi batace komai ba ta juya ta shige dakin Iya.
Abincin da bataciba kenan a daren tahau gado ta kwanta, ta rasa takameme me takeji akan wannan aure, farin ciki ko baqin ciki? Amma dai ta tabbatar da soyayyar Deni tananan a ranta daram babu abunda ya ragu. Iya tanata yimata magana bataji ba har saida Iyan ta burkitota sannan ta farga.
Iya ta fara magana cikin bacin rai "nifa sakeena sam wannan aure naki bai kwantan ba, tayaya malam xai daukeki ya danqaki hannun mutanen da basa qaunarki? Ai yasan Hajjo da yayanta bazasu taba sanki ba. Kuma dan ni be daukeni wata abuba bai nemi shawarata ba balle in fadawa yayyenki da kuka hada uba, wannan hadin sam beba" Sakeena ta waro ido tace "Iya kece babba dan Allah tunda ita Hajjo bata nuna komai ba ke karki fara nunawa, karku batawa Baba rai aikin gama ya gama tunda an daura aure" Iya takai mata bugu tace "dan ubanki keda nazo ki goyamun baya mu yaqi abun shine xaki gwale ni? Kinason Deni ko? Soyayyarsa ta hanaki hango abunda na hango miki" Sakeena tace "Iya kiyi haquri duk abunda kikace inyi xanyi amma ki tuna ya Deni yanxu mijinane ko ina sonsa ko bana sonsa hakan baxai amfaneni ba" Iya ta kuma harxuqa ta kama kunnen sakeena ta murde tace "To dan ubanki wannan rawar kan da yake akanki inkika bashi hadin kai ya gama dake tun a gida wlh xai wulaqantaki saboda haka ki kiyayeni ko doguwar gaisuwa ban yarda kuyi ba ke dashi" Sakeena ta runtse ido saboda xafin murdar kunnen da Iya tai mata tace To Iya naji xan kiyaye" ta saki Kunnan sakeena ta nemi gurin kwanciya tana mitar wannan aure.
Deni kuwa yayi ficewarsa waje cikin nishadi ya nufi majalisarsu baki har kunne duk inda ya xauna saiya fada musu yayi aure jiya. Abokai suka dunga tayashi murna tare da yimasa iya shege irin na abokai. A cikin daran dai yayi bacci me dadi cike da mafarkan sakeena, ya dunga dariya shi kadai wato dai aure lokacine in lokacinka yayi koda shiri ko babu shiri sai kayi. Duk da sakeena ba irin kalar matar da yake mafarkin aura bace amma yayi mutuqar farin ciki da aurenta kuma da xuciya daya ya dauki aniyar riqeta.
Acan daki kuma Hajjo ta xauna ta zabga tagumi yayinda yan majalisarta wato yayanta suketa aikin xugata tare da tsinewa auran Deni da Sakeena. Ita kuwa Hajjo duk da bata qaunar auren ko kadan amma kuma batayi wani baqin ciki sosai ba, dalili kuwa shine : danta ya isa aure amma kuma bashi da aikin yi balle ya riqe iyali kuma baxata taba so ace Deni ya lalace ba ma'ana yafara bin matan banxa saboda rashin halin yin auran to tunda ga Sakeena bashikenan ba sai yayi auran kare kansa daga zina da ita inyaso duk randa yayi arxiqi saita uxxura masa ya qara aure irin wacce takeso kuma tayi duk yadda xatai ya sallami sakeena. Ta dakko maganar Zahra ta dazu bayan ta fada mata yadda sukaji Deni na yiwa sakeena tayin xuwa dakinsa, zahra ta bata shawarar cewa bataga amfanin hana Deni auren sakeena ba tunda yana sonta inda tace "Hajjo tunda saurayi kamar yaya Deni beji kunyar idionku ba ku iyayensa beji kunyar idon qannensa ba furta cewar ai masa aure ai kinsan tura takai bango shiyasan illar da rashin auren yake masa kuma in kukaqi yi masa duk abunda yaje ya aikata kuna da xunubi, kuma Hajjo da ace yau ga yayan Deni shegu na yawo ba gara ace ga yayansa na halak ba amma uwarsu bata da asali? Nikam banga illar auren sakeena ba koda bata da asalin tunda tana da halin kirki kuma ai Deni talakane wanda bashi da kudin aure kamar yadda sakeena take yar talakawa wacce ba a da kudin yimata kayan aure to basai ku barsu su rufawa juna asiri ba?" wannan shine shawarar da Zahra ta bawa Hajjo daxu da rana.
Maganar Amina ta katsewa Hajjo tunani inda take cewa "ai wlh karyar sakeena ta auri miji handsome kamar yaya Deni wannan aure sai mun batashi kafin qarshen watan tayi." Fiddausi ta karbe da cewa "tabbas kwancekwance xamuyi mu hada mata tuggu yanda ba yaya Deni ba har Baba sai yaji ya tsaneta" Hajjo ta katsesu ta hanyar daga musu hannu da cewa "bansaku ba" Hadixa ta matso tana leqa fuskar Hajjo tace "Hajjo? Me hakan yake nufi? Kina nufin kin karbi sakeena a matsayin surakarki kenan?"
Hajjo ta fashe da kuka jin an kira sakeena da surukarta da kuma tunawa da tayi yanxu fa duk mutan unguwa suna kallon sakeena a matsayin surukartane. Kuma duk yadda taso ta danne ta karbi hakan amma abun ya faskara. Ta qara sautin kukanta tace dasu fiddausi "bance ku kashe masa aure ba, ya kikeso inyi? Dame xanji? Da baqin cikin ya auri yar talaka mara asali kuma yare xanji koda maganganunku? Ku kun jibge kunqi aure muna hada kafada daku shi kuma talauci ya hanashi auren duk kuwa da yanaso, ko so kuke ace yayana baqin jini garesu?" ta qarasa tana gursheqen kuka. Su Hadixa jikinsu yayi sanyi ganin kukan Hajjo cikin kukan tacigaba da cewa "Allah ya tsinewa talauci domin talauci ne yasanya Dana auren yare wacce qedara ta haifa kuma nima haka xata haifamun yare, wai ni Hajjo nice xan xama kakar yare?" Ta share hawayenta ta kuma cewa "Sakeena kinyi nasarar auren Dana amma kuma baxan taba bari ki haihu dashi ba wallahil azim xaki qaraci xamanki xuwa lokacin dana diba miki kiyi gaba" Haka dai suka dunga qulle qulle ita da yayanta har xuwa lokacin kwanciya bacci.
Washegari Deni ya shigo har dakin Iya ya gaisheta ta amsa tana basarwa ya sosa kai yace "Iya ya sakeena ta kwana?" tace "lfy lau tana wanka xata tafi aiki" yadan hade rai yace "Iya ban yadda ta fita ba, na soke aikin nan daga yau ban bata izinin fita ba" Iya ta saki baki tana kallonsa daga baya ta fara magana "Deni ka dubi Allah ka barta ta qarasa xuwa qarshen watan nan tunda yau 3 ga wata kaga in anbata kudinta sai ta daina xuwa kudin xasuyi mana amfani auren yaxo mana baxata bamu shirya komai ba" yadan kau dakai yace "to shikenan Iya na yadda amma ni yanxu xan fitane ina sauri yau xamuyi baqi a shago dan Allah ko ke ko Baba wani ya rakata makarantar ya sheda musu tana da aure yanxu a kulamun da ita don Sakeena yarinya ce batasan haqqin aure ba" Iya ta bishi ta to tana masa kallon mamaki daga aure jiya har yafara saka doka? Dai dai fita daga dakin Iya sukai kacibiz da sakeena ta fito wanka daga ita sai daurin qirji don bata xaci ganinsa yanxu ba. Ya kalleta yace "inxaki fita ki saka hijab kuma ki kiyaye magana da kowane namiji kinji ko?" ta gyada kai yayi waje ita kuma ta qarasa ciki.
Iya ta harareta tace "wai meya hanaki saka hijabi da xaki shiga wanka kamar yadda kikeyi da?" sakeena tace "Yi saquri iya banxaci ganinsa yanxu ba shiyasa na fita haka" tayi tsaki tace "to daga yau inxaki shiga wanka ki dunga rufe jikinki domin ko babu mijinki a gidan akwai surukanki da kuma qannansa saboda haka karki kuma fita wanka haka gantsar gantsar ke dama ga jiki masha Allah" sakeena cikin kunya ta amsa to Iya.
Kamar yadda Deni ya umarta haka akai Baba ya saka Iya ta raka sakeena makaranta ta fada musu tayi aure shekaranjiya lahadi abunne yaxo baxata shiyasa basu jiba sai yanxu. Malaman suka dunga taya sakeena murna iya na amsawa da amin sunaiwa sakeena tsiya ashe tana da mr right dinta shiyasa bata shiga sabgar kowa.
Data dawo hardasu Hajjo ayi mata sannu da xuwa ta amsa a darare dan tsoron Hajjo take a matsayin surukarta. Iya ma dai wannan sabuwar fuskar da Hajjo ta saka ta yiwa sakeena kirki bata gamsheta ba don tafi kowa sanin halin Hajjo unguluce bata jelar banxa dole tasan akwai wata qulalliya a qasa.
A daki ta yini sur dan sai taji ta kasa sakewa duk kuwa da babu wanda ya caja mata fuska.
xuwa magrib Iya ta gama girkin dare yayin da kowa yana daki yana shirin sallah ita kuma tana bakin famfo tana wanke muciyar datai amfani da ita. Taji andafata, ta dan juya a raxane dan bataji taku ba, tayi arba da Deni a tsaye xatai magana yayi mata alamar tayi shiru, ya miqa mata ledar wani store a hankali cikin rada yace "ki bawa sakeena" ya juya ya fita da alama bayason uwarsa da yan uwansa susan da wannan abun daya bayar.
Ta gama abunda xatai ta koma daki ta bawa sakeena saqon Deni, a gaban Iya sakeena ta zazzage ledar taci karo da turare da man shafawa cocoa butter da tarkacen chocolate. Iya sai taji xuciyarta tayi sanyi tausayin Deni ya kamata da alama yan kudi ya samu yau shine yaje ya kasowa sakeena su, kuma bayason uwarsa tasani saboda gudun magana. Ta yabawa qoqarinsa kuma taga alamar zai riqe sakeena da mutunci kamar yadda ya fada. Tayi godiya tace da sakeena "debesu ai nakine mijinki ya baki amma ki kula karki yadda yan uwansa susan yana baki abu a boye." tace "to" ta raba ta ajiyewa iya nata alawar ita kuma ta debe mai da turaren tayi cikin daki.
Ta tasa kayan a gaba tana kallon kyautar Deni karo na farko a rayuwarta, lallai yanason qamshi shiyasa yayi mata kyautar turare kuma in shaa Allah xata kiyaye baxata yadda yajita bata qamshi ba.
Tun daga ranar Sakeena ta kuma kamewa sosai ko xaman tsakar gida bata cika yiba indai ba suna aiki da Iya ba kuma daga Hajjo har yayanta babu wanda ya canja mata fuska sai dai ma shishshige mata da su keyi ,Saddiq ne kawai duk sanda suka hada ido saiya doka mata harara ko kuma yayi tsaki inya ganta.
Iya ta saka mata mugun tsaro da yadda saita kwana ta yini bataga Deni ba, koda ya nemeta a tsakar gida takanji Iya na bashi amsa da cewa bacci take ko kuma tanamun aikine aciki. Hakan na mutuqar takura Deni shi da matarsa sai dai ya hangi giftawarta. Itakam sakeena hakan be dameta ba sam, saima wata dama data samu ta karatun novels tunda Iya ta hanata aiki. Takanyi wankanta kullum sau biyu safe da dare ta lallai laye cikinta da mai ta saka turare.
A irin haka ta samu wani novel me suna ZUCIYA DA KWANJI na maimuna idris sani Beli ta karanceshi 1-4 ta kuma maimaitawa littafin ya mata dadi sosai soyayyar Fatima da Abu turab tayi matuqar burgeta sai take fatan Ya Deni ya kasance me sadaukarwa a gareta kamar yadda Abu turab yakewa Fatima. A ciki kuma ta dauki darasin yadda xata xauna da mutane kamar yadda Fatima ta xauna da kishiyoyinta sadiya da Hindu sannan ta dauki aniyar tsafta da kwalliya kamar Fatima.
A rana ta shida da daura aurensu da Deni tayi wankanta tsaf da magrib kamar yadda ta saba ta shafa mai lotion saboda xafi ta saka turare, bakinta ma tsaf yake ta wankeshi da taje wanka. Duk abunda take Hajjo na kula da ita, ta qudure yau shirinta zai fara aiki. A kayi xaman cin abinci babu sakeena kamar yadda Iya ta hanata, kuma Deni ma yau be dawo ba. Baba ya tashi yaje sallar ishsha ya dawo ya kashin gida ya kunna radio.
Dai dai lokacin Deni ya dawo ya shiga yayi wanka ya koma daki. Hajjo ta dakko miya ta kuma dorata akan wuta tayi xafi ta xubawa Deni abincin sa ta rufe ta kwallah kiran Sakeena, kina inane Sakeenatu?
Sakeena ta sako hijabi ta fito ta tsuguna a gefen Hajjo tace "gani Hajjo" tana murmushin qeta tace "Maxa dauki abincin mijinki ki kai masa, yanxu ya dawo" sakeena tai wuqi wuqi cike da tsoro takai dubanta ga Iya wacce ke xaune itama akan tabarmar.
Iya dake macece itama saita gane nufin Hajjo dan haka ta magantu "ke Amina tashi ki miqawa Deni abinci ke kuma sakeena koma ki qarasamun gugar dana sakaki" Hajjo cikin kwantar da murya da makirci tace "Haba Hafsatu, sakeena fa surukatace amma nema kike ki nuna mata bani da iko akanta,, yanxu dan Allah lefine dan nasata kaiwa mijinta abinci? Ai haqqintane ta kai masa amma duk kin takura yarinya tun daga daura aure ko mijinta bata gaisarwa wannan abun da kike mata wlh ba gata bane in yanxu bata koya ta iya ba in suntafi gidansu wane irin xama kike tsammanin xasuyi? Ai haqqin aure ba sai an tare a dakin miji yake farawa ba, haqqin aure na farawa ne tun daga daura aure." Iya ta jinjinawa makircin Hajjo kwarai da gaske ta bude baki tace "sannu Hajara uwar kinibibi shi haqqin auren da kike magana akai naki Dan ya sauke haqqin sakeena dake kansa?" Baba ya tashi daga kashingidar da yayi ya dagawa Iya sannu da cewa "dakatamun Hafsatu, keda kike babba amma daga gunki baraka xata bullo? Abunda Hajara ta fada ai gaskiyane ni kaina na lura kin takure sakeena kin hanata koda fitowa tsakar gida to me kike nufi? Yanxu yaron ya dawo ya fito daga wanka kice Amina taje takai masa abinci ga matarsa a gida? Kikasan wane hali xata taddashi? In kuwa matarsa ba shikenan ba? To wlh Hafsatu ki shiga hankalinki baxan yarda ki batamun gida ba, ita da take qarama ta kwantar da kai kuma ta rungumi wannan aure amma ke shine xaki tsiro da fitina?" ya juya ya Kalli sakeena dake tsugune tayi fiki fiki yace "ke sakeena meye matsayina a gurinki?" cikin sanyin murya tace "Babana" yace "To indai kin daukeni uba daga yau kicigaba da mu'amalarki yadda kikeyi ada kafin aurenki da Deni. Ni ubanki ne ba uban miji ba, Hajjo ma uwarki ce ba uwar miji ba daga yau ki dunga xuwa kullum kina gaida mijinki da safe kuma inya dawo ki dauki abincisa ki kai masa kiyi masa hannu da xuwa. Ki nemi aljannarki a gurinsa kinji sakeenatu?" tace "to Baba" Sakeena ta dauki abincin Deni ta nufi dakinsa dake soro.
Iya kuwa tayi tsumu jin makircin da Hajjo ta shirya mata ita da sakeena, dake kuma Baba namijine be fuskanta abunda Hajjo ke nufi ba. Cikin kwantar da murya Iya tace "kayi haquri malam in shaa Allah baxan kuma ba" yana dariya yace "Yawwa Hafsatu Allah yayi miki albarka, dadina dake saurin karbar lefinki"
Hajjo tayi murmushin cin nasarar ganin plan dinta ya tafi successful, kamar yadda ta tsara so take Deni ya kusanci sakeena tun a gida inma ta kama maganar tariyarsu ta sha ruwa. Inma Deni ya maida kwalamarsa akanta ya sawwaqe mata tun a gida hakan xaifi mata domin tasan halin namiji sarai ba qaramin aikin namiji bane inyasan mace a gida ya sallameta, wanda in hakan ta faru burinta ya gama cika.
Da sallama Sakeena ta shiga dakin Deni, ya gama shirinsa tsaf cikin wando 3 quarter da riga armless. Yace "shigo mana sakeena keda dakin mijinki kika tsaya daga waje?" Ta qarasa gabansa ta ajiye masa kwanunkan abincin sannan ta koma gefe ta gaisheshi. Bai amsa ba sai hannunta daya riqo yace "zo in koya miki gaisuwar ma'aurata" ta qaraso gabanta yana wata irin faduwa ya dorata a gefen cinyarsa.
ta xauna a darare, yanayin xaman da tayi yasa dole ta saqala hannunta a kafadarsa shi kuma ya riqo qugunta yana kallon fuskarta. tayi qasa da kanta saboda kallon da yake mata yakai fuskarsa qasan wuyanta yana shinshinar qamshin turaren humrar da yajiyo a gurin, ta tsinci kanta cikin baqon yanayi, ta dan fara ture kansa saboda tuno kashedin da Iya ke mata. Tace "ya Deni bari inshiga gida kar Iya ta nemeni" ya dago kansa yana kallon kwayar idonta yakai hancinsa kan nata hancin bakinsu ma ya hadu guri guda. A hankali kamar me rada yace "wazai nemeki bayan gurin mijinki kika taho?" sakeena ma dai tunda taji lebensa akan nata ta tafi wani duniyan ga mamakinta sai taji dadin hakan sannan kuma tayi fatan Allah yasa Deni ya sumbaceta irin sumbar da take gani anayi a finafinan turawa lokacin da take aikin gidan Anty. Yadan sumbaci lebenta kadan, ta lumshe ido tana shafar wuyansa ta baya amma taso ace kiss yayi mata sosai.
Shima kuma qanqameta yayi ya kuma qasa da murya yace "kinsan fassarar sunanki kuwa Sakeena?" ta danyi shiru saboda ta kasa magana, ya shimfideta akan katifarsa ya bita ya danneta sosai ya hada qirjinsa da nata ya sake mata nauyinsa, ta tsorata ta fara tureshi ya danne hannyenta a jikin katifar da nasa hannyen.yace "relax my dear just fassarar sunanki xan fada miki. Da sauri ta fara magana "eh nasan fassarar wlh sakeenatu yana nufin nutsuwa. Kuma inxaka fassaramun sunana ai basai ka hau kaina haka ba" Yadanyi dariya ya qara tusa kansa cikin wuyanta ta fara mutsu mutsu, yasa qafafunsa dan ya danne nata qafafun da take wutsul wutsul dasu cikin rashin sani suka barar da miyar busashshiyar kobewar dake kwanon da sakeena ta shigowa da Deni shi.
Ya dagata dan dole yace "kash kinga kinmun bari ko?" itama ta tashi tace "kayi bari dai" ta dakko hijabinta ta mayar ta dauki kwanon miyar tace "bari in karbo maka wata" bata jira amsarsa ba tai waje. Lokacin data shiga gida Iya ta koma daki sai Baba dake jin kowanne gauta. Hajjo kuma na gefe xaman jiran shigowar sakeena don taga wace irin tafiya take.
Sakeena ta tsuguna gefen Hajjo tace "Hajjo a qara xubawa yaya Deni miya wancan ta xube" Hajjo ta bita da kallon mamaki tace "miyarce ta xube garin yaya kuka xubur? kokawa kuke har kuka xubar da miyar bakusani ba?" Baba dake gefe yayi gyaran murya tun kafin Hajjo tai baran barama. Tai shiru ta karbi kwanon ta xubowa sakeena miyar tana mitar cewa yanxu kunja saina kuma kada wata miyar saboda ya dumamen gobe.
Itadai sum sum ta fice taje kofar dakin ta ajiye miyar tace "yaya Deni ga miyar nan Saida safe" shima yana tsugune yana gyara gurin da sukai barin miya, yayi murmushi yace xamu kuma haduwane Baby na.
Ta salallaba dan a xatonta Iya tayi bacci ta shige uwar daka ta kwanta tana murmushin jin qamshin turaren Deni a jikinta ta shafo lips dinta inda ya sumbata daxu wani irin farin ciki ya rufeta. lallai ta yadda babu abunda yafi soyayya dadi rabon datajita cikin farin ciki haka tun Nura qaninta na raye. Dukan da Iya ta dada mata a cinya shiya dawo da ita hayyacinta.
Iya ta xauna gefen gadon ta tsare ta da kallon tuhuma tace "Dadewar me kikai a dakin Deni?" ta diririce ta fara qinqina kafin tace "wlh Iya babu abunda yayimun hira kawai mukai." ta gyada kai tace "akwai abunda Hajara ke shirya miki wanda qarancin shekarunki baxaisa ki ganeba kuma tayi sa a malam ya yarda da abunda take shirin yi ba tare da sanin bada kyakykyawar niyya takeyi ba. Kece kadai wadda xaki hana hakan faruwa. Bana saba umarnin mijina xaki dunga gaida Deni kullum da safe da kuma xuwa kaimai abincin dare kamar yadda malam yace amma dan Allah sakeena karki yadda Deni yasanki ya mace tun a gidan nan, inkikai min haka kin temakeni domin Hajjo so take ta watsamin rayuwarki" Sakeena jikinta yayi mugun sanyi duk da bata gama gane ainihin abunda Iya ke nufi ba amma tasan abune mai mahimmanci tunda taga Iya na roqonta.
Ta kwantar da kanta a kafadar Iya tace "Iya ki bar roqona kin yarda dani ni kuma in shaa Allahu baxan baki kunya ba"
Daga wannan rana kulkum sakeena xataje dakin Deni ta gaisheshi da safe, haka kuma da daddare itace me kai masa abinci. Kuma tana iya qoqarinta wajen tsare kanta domin bata barin ya taba abunda ya wuce hannu a jikinta, iyakacinta dashi ya ruqe mata hannu tunda yayi yunqurin sa mata hannu a riga ta bata rai tare da ce masa ai dama tasan dalilin da yasa ya aureta kenan saboda taqi amincewa ya lalatata shine ya biyo ta hanyar aure gashi tun kan aje ko ina ya fito da xulamarsa. a lokacin data fadi haka ya gigita kwarai ya dunga bata haquri tare da roqonta ta manta abunda yayi mata a baya sharrin shedan ne shi da kyakykyawar niyya ya aureta.
Tacigaba da fitowa tsakar gida tana harkokinta, ita sau tari ma tana mantawa wai ita suruka ce a gidan yanxu. Baba yaji dadin hakan sosai da yaga gidansa ya dawo normal, shima Deni baya wani abu da yake nuna sakeena matarsa ce sai dai in anhadu a hirar dare yakan sakota a ciki jifa jifa. wannan canji bewa Hajjo dadi ba sam dan ita ba haka taso ba, amma kuma tana gani ai bata makara ba xata kuma jarraba wani abun, yayin da Iya kuma hankalinta ya kwanta ganin daga Deni har sakeena abunda take xargi baya gabansu.
Sati na biyu acikin watan Deni ya karbi slip din Amina da Sakeena na waec ta fito online xeje ya duba musu. Tunda ya fita sakeena ke xaryar bandaki tana gudawa, fargabarta daya kar jarrabawarta batai kyau ba Deni ya rainata yayi mata kallon daqiqiya sannan ga abokan adawarrata wadanda yanxu suka rikide suka xama qannan miji, tasan indai bataciba ta shiga uku a wajensu. Baiwar Allah ko abinci ta kasa ci, har Iya ta lura ta tambayeta ta fadawa Iya abunda take fargaba Iya ta kwantar mata da hankali da qarfafa mata gwiwa da cewa ai tayi karatu kuma tayi addua itama tai mata in shaa Allahu xataci.
Deni dai be shigo gidan ba sai bayan sallar magrib lokacin anyi xaman cin abincin dare, yana shigowa cikin sakeena dake a tsure ya kuma qullewa. Yaxo ya xauna ya gaida su Baba ya miqawa Amina takarsa yace "ga result dinki, kinyi qoqari sosai auta" ta bude tana dubawa ita dasu Hadixa ta tashi tana nunawa Baba shima ya dunga dariyar farin ciki yanasa albarka.
Tun daga nan sakeena ta sare ganin ko inda take Deni be kallaba, idonta ya ciko da kwallah cikin qarfin hali tace "yaya Deni ni ina nawa" ya kalleta yayi shiru sannan yace "miqomin abincina" ta miqe a salube su saddiq na qunshe dariyarsu taje ta dakko masa ta kawo. Ya bude ta faraci ita kuma tana gefe tana sharar kwallah Iya da Baba nayi mata kallon tausayi.
sai da ya gama tas yaje ya wanke hannunsa yazo ya tsaya akanta ya zaro takarda daga aljihunsa yace "ga taki" ta miqe da hanxari xata karba, yayi sama da takardar yana dariya. Ta dunga hadashi da Allah ya bata yaqi yana dariya yace "Haba mana sakeena, kiyi dage mana ki karba kardai kicemun ke wadace." ta dunga tsalle dan kamo takardar yana kuma dagata sama su fiddausi na yimata dariya, can dai taga ta kasa tai masa cakulkuli ai kuwa babu shiri ya saki takardar yana dariya. Ta cafe ta hau dubawa, shima ita yake kallo yana murmushin jin dadi. Ta dago tana kallonsa ta fada jikinsa cikin tsananin farin ciki suka qanqame juna.
Su Hajjo suka bisu da kallon mamaki dan kamar sun manta da mutane a gurin ta dago kanta tace "yaya Deni wlh ka razanani da na dauka result dina be kyau bane" yana dariya yace "ai nasan baxaki bani tukwuici bane shiyasa nayi miki haka a matsayin tukwuici." ta harareshi yana kashe mata ido yace "yan mata sai Jami a ko?" tace "in Allah ya yarda" ya sumbaci goshinta yace "Allah ya horemun sakeena ilimi har sai kince ya isheki"
Ta juya ta kaiwa Baba ya karba ya duba yana murmushi ta dunga yaba kyan result din yana yiwa su Iya bayani, ya dafa kanta yace "Allah ya sanya alkhairi" ta miqawa su Hadixa da sukai jugum jugum ganin abunda sakeena da Deni sukai a gabansu. Suka karba suna gani ransu ya kuma baci dan ganin result din sakeena har yafi na Amina kyau dan ita B dinta har tafi C yawa.
Baba kuma wani irin farin ciki yake ciki, lallai yayi dogon tunanin aurawa Deni Sakeena ya lura yaran suna san juna kuma tunda akai auren kullum cikin farin ciki yake ganinsu duba da abunda sukai yanxu a gaban kowa yayi nuni da hakan wanda daga Sakeena har Deni babu wanda ya nuna alamar cewa sunyi wani abun daban su kawai hakan a gurinsu ba wani abu bane. To Iya ma dai tunaninta irin na Baba ne ganin su Deni haka hankalinta ya kuma kwanciya da auren kuma ta tabbatar da Deni nason diyarta sakeena. Hajjo da yayanta ne kawai abun baiwa dadi ba, inda aranta ta dunga tsinewa auren yare, kuma yau sakeena ta nuna mata ita ba zallar jinin hausa Fulani bace. in banda rashin kunya irinta yare wacece tsinanniyar macece xata rungumi mijinta a gaban mutane haka? (amma fa inji Hajjo ba injini ba😄) su kuwa su Fiddausi kishin soyayyar da sukaga dan uwansu nawa Sakeena itace damuwarsu.
Hajia ☺
[7/31, 2:10 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣0⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
#team Sakeena nd ya Deni#
Yan kwanaki sun wuce kowa nata shirinsa na tariyar auren Deni da sakeena, Iya ta tashi da kanta tatafi Baggadano domin fadawa yan uwan sakeena kuma yayan dan uwanta maganar auren sakeena. Ranar data tafi ta kasancewar asabarce tana tafiya dake da sassafe ta tafi kuma ta fadawa sakeena baxata kwana ba ba komai dare xata dawo. Hajjo ta leqo dakin ta samu sakeena na bacci, ta duma mata dundu tace "ke wai wace irin matar aure ce? Kinxo daki kin nade kina bacci yayin da mijinki kecan yana wankin kayansa na sakawa, ai dake matar arxiqi ce da yanxu yafi qarfin wanki" Sakeena ta miqe ta fita bayan gama sauraren fadan Hajjo. Ta samu Deni yanata aikin wanke yan tsirarun kayansa, ta qarasa tasa hannu a cikin kumfar tana cewa "ya Deni barshi in maka" baiyi magana ba sai hannunta daya kama ta cikin ruwan yana murxa mata. Ta dan janye hannunta takai dubanta ga sama hadari ya hado sosai koda yaushe ruwa kan iya sakkowa yayin da Hajjo tasa yayanta a gaba suna bacci a daki. Cikin rada Deni yace "barshi Baby xanyi da kaina inkinada kaya masu dauda jeki kawo mun in hada in wanke mana" itama tayi qasa da murya tace "basu da yawa kayan ban dade da yimana wanki ba ni da Iya" yace "maxa jeki kwaso ragowar kixo muyi" ta shiga daki ta debo wankin ta kawo tasa hannu a kumfar, ya rada mata a kunne "kawai kisa hannu aciki kamar kinayi, saboda Hajjo" tace "to" tayi kamar yadda yace amma fa yana wankin yana riqe mata hannu. Duk sanda yayi hakan saita dago ta dubeshi shi kuma ya kashe mata ido. Da haka har ya gama wankin, lokacin har anfara yayyafi yayi wanka a gurguje ya fita daurin aure daganan xai wuce kasuwa.
Haka sakeena ta wuni daki yayin da saddiq daya fuskanci Iya bata nan ya dunga dura mata ashar tare da yimata alqawarin xaman uquba a gidan Deni sai kace shine Denin duk da Hajjo na kwabarsa be dena ba cewa yake "kyaleni in fadi abunda ke xuciyata Hajjo danni ban iya munafurci ba, tunda yarinyar nan tai sanadin zubar hawayenki naji na kuma tsanarta" Hajjo kuwa yana fadar haka dadi ya lullubeta cewa take "Allah sarki saddiqu da alama duk kafi qaunata cikin yaya na, haihuwa mai rana ko kana gudu haifi kayar." haka dai aka yini abu daya kamar ibada, sakeena ta yadda idon Iya ba qaramin kariya yake bata ba a gidan tunda duk tsiya da tananan bai isa yayi mata wannan xagin tsamar naman ba.
Koda magriba tayi Aka hadu gurin cin abinci ma haka saddiq ya dunga hararar sakeena a bayan idon Baba da Deni. Yayin da ana idar da sallar ishsha hadarin dake kwance ya taso garin ya hadu yayi baqiqirin. Sakeena cikinta ya qulle, gata da tsoron ruwa ga Iya bata dawo ba, yanxu in Iya acan xata kwan itakam yau sai dai ta kwana dakin Hajjo dan baxata iya kwana daki ita kadai ba. Maganar Hajjo ta katseta a tunanin da take inda tajiyota na tambayar Deni ina zashi a wannan hadarin? Bataji amsar daya bata ba tadaiji tana cewa "ai sai Sakeena taxo tayaka hira, inaga ma a dakin naka xata kwan tunda uwarta har yanxu bata dawo ba" ai Sakeena najin aikin da Hajjo ta baro na kwana da Deni tai tsalle tayo waje tace "Hajjo ai sai inkwana a dakinki wajensu Amina" Hajjo ta bita da kallo tace "lallai Hafsatu ta qoqarta wajen nuna miki ki rainani, in badan raini ba har infadi abu ki musa? Mu xamaninmu ai uwar miji ko wuta tace kafada sai kafada wlh" Deni ya katse Hajjo dan kar maganar tai nisa yace "shikenan Hajjo yadda kikace haka xa ai kiyi haquri, ke kuma sakeena koma dakin Iya xan shigo saimu kwana anan" wani farinciki ya ziyarci Hajjo, wato dai inji masu hikima kance komai wayon amarya sai ansha manta, tasan dole yau Deni xai maida sakeena mace duk kuwa da tsaron da Iya ke sakawa tasan babu yadda xa ai a hada saurayi matashi kamar Deni da qaramar yarinya me tashen balaga kamar sakeena kwana guri daya ace basu aikata komai ba bare ma ace a matsayin ma aurata. Ta shige dakinta ta rufo qofa harda sakin asabari saboda anfara ruwa, shima Baba ta sakar masa nasa saboda karya jiyo ihun sakeena.
Sakeena kuwa tana komawa daki ta qara saka turare ajikinta ta saka hijab gabanta na wata irin faduwa wai yau da Deni xata kwana a matsayin mijinta kuma a dakin Iya. Tanaji anfara ruwa ta nemi guri a gado ta qundundune ta kunna yar qaramar fitilar caja saboda dauke wutar nefa da akai.
Bataji shigowarsa ba sai kwanciyarsa taji a kan gadon kusa da ita, tayi wata irin xabura ta xauna ta jingina da allon gado tace "ya Deni meye haka babu sallama?" ya dariya yace "xan shigo gurin matana sai nayi sallama?" ta harareshi tace "da alama a yan kwanakin nan babu kalmar dake maka dadi kamar matarka" ya lumshe ido yace "eh wlh Baby ko abokaina haka suke cewa ni kullum bani da hira sai matana" ya kwanta ya qafafunta ya balle botiran shirt dinsa yace "sakeena dan dannamin qirjina mana" ya fada yana kama hannunta yana mannawa a gashin dake qirjinsa. Tai saurin janye hannun tace "xo muje falo inbaka lbr" ya riqo hannunta yace "haba sakeena ga gado mu tafi kan leda ga sanyin leda mu xauna? Ki bari mana mu xauna anan muyi hira kinga na samo mana wani film ma a wayata me kyau sai mugani" sakeena mayyar kallo tanaji ance film tace "Allah ya Deni? To kunna mana" ya jingina shima da allon gadon kafadarsu na gugar juna ya dakko waya ya saka ear pc ya kunna musu wani indian film "AkashVaani" suka fara kallo, can ya katse kallon ya lumshe ido ta dubeshi tace "lfy ya Deni?" idonsa lumshe yace "sakeena bakisan yadda yanayin damuna ke tada tsumin soyayya ba? Inama muna gidanmu ne yanxu da munyi soyayyarmu babu fargaba, Allah yasa ranar da xa a kaiki ana ruwa, a kwana ana ruwa muma mu kwana muna soyayya" bugun kofar gida da ake ya katse musu hirar, jin babu wanda ya fita budewa yasa Deni ya tashi ya fita dan ganin waye a wannan dare.
Sakeena ta jiyo muryar Iya tana shigowa cikin gidan, inda takewa Deni bayanin mota ce ta lalace musu a hanya shiyasa sukai dare. Da sauri sakeena ta fito falo ta xauna, tana cewa Iya sannu da xuwa dama inata fargabar kwana ni kadai. Iya ta shigo daki tana cire kayan da suka jiqe, Deni dai bai dawo dakin ba ya koma nasu dakin.
Da asuba Hajjo tai arba da Iya ta fito alwala, ta cije yatsa ta fallarawa Iya harara tace "ke kuma yaushe kika dawo?" Iya ta bata amsa da cewa "jiya cikin dare"
Iya ta zaunar da sakeena ta fada mata yadda sukai da Inna da kuma yayanta inda sukace tunda sakeena batazo da kanta kawo musu goron bikin ba da kanta har saida aka daura aure to baxasu xoba kuma duk yadda iya taso yimusu bayanin auren yaxo baxata ne sunqi sauraranta kuma bayan haka ma a fadarsu tunda sakeena tabar qauye bata taba xuwa gaishesu ba ko aika musu da wani abun duk kuwa da tana burni dan haka taje suma sun rabu da ita yadda ta rabu dasu. Iya ta basu amsa da cewa dama dai bakuyi niyyar xuwa ba saboda kunji talaka ta aura, amma inbadan haka ba ta yaya xa a ce ku kuna manya kuma kuna da yawa amma babu wanda ya taba ko tambayar sakeena ta waya? Saboda haka Iya tace su raba gadon gidan da Abbakar ya bari su fidda Sakeena da Nura. Anan ma suka turje duk kuwa da suna da halin fitar dasu sakeena amma sai sukace basu da kudi amma in sun samu xasu turo mata da kudin.
sakeena ta share hawaye tace "yanxu Iya haka xa ai bikina ko kare baixo ba daga dangin ubana? Na uwa kuwa bani da kowa. Iya Dan Allah ba dole aimun gorin asali ba, ni wlh xuwansu yafi duk abunda xasu bani"
Iya ta dubeta tace "sakeena share hawayenki ki daina kuka akan wadanda basu damu da ki mutu ko ki rayu ba, na tabbata da Lauratu da yayanta sunga me kudi xaki aura wlh da ko ba a gayyacesu ba xasuxo amma yanxu tunda ke talakace kuma matar talaka basu da buqatarki" sakeena ta yadda da maganar iya ta share hawayenta tana fatan Allah yayi mata arziqi ko sayi xumunci da yan uwanta.
Ana saura kwana 6 wata ya qare Deni ya kirawo Iya har dakinsa ya bata atamfofi guda 5 wadanda kudinsu basu wuce 3k ba kowacce yace "Iya gashi uban gida nane ya bani in xuba a lefe, kuma gashi bani da halin yiwa sakeena lefen amma ga wannan ki bata dan Allah iya ayi mata dinki me kyau irin wanda ake yayi banaso kowa ya sani. Ya dorawa Iya 3k akai yace wannan kudin dinki ne. Tayi malejinsu. Ya dakko wata leda yace wannan ma abata abokainane suka hadamun yan kudi shine na sai mata babu yawa ragowar kudin xan siya mana kayan abinci ne dan kar wahala taiwa Baba yawa" Iya ta karba jikinta a sanyaye tana kallon Deni da tausayi ta fuskanci yana qaunar sakeena amma yana mutuqar tsoron uwarsa. Maganarsa ta katse mata tunani "Iya boye kayan kiyi kamar daga unguwa kike, kice da sakeena inna kuma samun wasu kudin xan bata kudin qunshi da retouching" Iya ta share kwallar tausayinsa ta boye kayan a mayafin jikinta kamar yadda ya buqata tace "kabar kudinka Deni kaima kai naka shirin, ni xan bawa sakeena kudin qunshin da shamfo" ta juya ta fita yanata yimata godiya.
Tayi sa a babu kowa a tsakar gida tayi wuf ta fada daki, ta samu sakeena tana guga ta zazzage atamfofin a gabanta. tace "gashi inji Deni yace inbaki a boye ga kudin dinki ma ya bayar saboda haka sai muje anjima akai gidan dinkin a gwadaki yace ai miki me kyau amma bayaso yan uwansa da uwarsa su sani" sakeena ta dunga daga kayan tana binsu da kallo tana yaba kyan atamfofin. Iya ta miqa mata daya ledar, sakeena ta zazzage ta undis suka biyu baya, pant 6, bra 6, sai skirt 2, shimi me roba 2, sai takalmi guda 2, da mayafai 2, sai turare kwali 2. Duk masu sauqin kudi. Iya da sakeena suka kalli juna a tare, iya ta fara cewa "Allah sarki Deni ya sakemun abunda nake shirin yi, wlh jira nake aban dashi na gobe muje insiya miki yan kayan sakawa kinga yaro kamar ya shiga xuciyata ya gani. Allah ya saka masa da alkhairi adduar da nake miki ta samun miji nagari ashe Deni ne nagarin ada kam banason aurenki da yaron nan amma yanxu na fuskanci yana qaunarki kuma komai talaucinsa baxai bari ki tagayyara ba, kinga yan kudin ai na sai miki yan kayan kicin ko?" Sakeena dai tayi shiru tana tausayin mijinta wato kamar yasan bata da undis nata duk sun saki ko ina yasamu kudi haka? Soyayyarsa ta qara ninkuwa a xuciyarta ta quduri aniyar biyayya a gareshi. Ta tattara kayan ta boye atamfofin kuma sukai dinki da Iya aka gwadata duk riga da skirt. Koda iya tadau dashinta ajiyewa sukai da xummar sai qarshen wata sakeena ta samu albashi sai suyi siyayyar gaba daya.
****** ****** ******* ****
Komai aka saka masa lokaci tofa angama dashi, kamar yadda aka tsara qarshen wata taxo amma ta kama ranar talata dan haka aka saka ranar tariyar su sakeena ranar asabar xa a yini da kai amarya gaba daya. Baba ya bata sadakinta naira dubu ashirin kamar yadda ya fada, ta karba ta kaiwa Iya a inda ta saiwa sakeena drawer me biyu ta hannu me kyau tunda basu da halin yin kayan daki kuma basa dunga xuba kaya a leda ba ko a buhu. Washegarin ranar Baba yaxo da labarin ya kama musu gida amma basu samu a kusa ba saboda babu na irin kudin da suke buqata. Kamar yadda taji Iya na fada mayan sunje sunga gidan dake Sani mai nagge dakuna uku ne a gidan ciki da falo kowane daki, akwai mace daya a gidan yar dattijuwa xata haifi sakeena a haife da yayanta 4, wacce ke a daki daya. To Su sakeena ma daki dayan aka kama musu cike da falo yayin da daya dakin ma akwai mace aciki amma tayi tafiya sunje garinsu ganin gida ita da mijinta. Bandaki dayane a tsakar gida babu famfo sai rijiya a gidan babu kicin kowa a qofar dakinsa yake girki. Sai tsakar gida lailaye da siminti kamar yadda iya tace gidan dai bashi da laifi kuma matar gidanma iya tace tana da kirki ga dukkan alamu.
Sakeena tai sallama da malaman makaranta da kuma Hajiya, suma suka hada mata gudummawar 10k ga albashinta ta hada 15k ta nufo gida tana murna a wani bangaren kuma tana jimamin rabuwa da mutanen kirki da suka xauna da ita da mutunci.
Ta nunawa Iya kudin ta dunga godiya, aka fasa bankin sakeena wanda take tarin kudin aikin ido da takeso ayi mata suma kudin sun taru babu lefi aka hada da dashin Iya. Iya tai dariya bayan ta gama irga kudin tace "masha Allah wato dai su kudi wawaye ne taruwarsu bata da wuya, yanxu wannan kam ai sun isa rufa mana asiri a matsayinmu na talakawa" Iya tace maxa tashi shirya sakeena mu tafi kasuwa kafin wani abun ya shigo ya kassara kudin" sakeena ta marairaice tace "Iya ai ban tambayi ya Deni ba" Iya gwalo ido tana kallon sakeena tace "ke dan qaniyarki tashi mu tafi in mun dawo ni da kaina xan fada masa" sakeena ta qara marairaicewa tace "Iya infa na fita bada izininsa ba malaiku tsinemun xasuyi tayi har in dawo" Iya tace "to shikenan gobe ma fita da wurwuri inya dawo yau Kya tambayeshi yar dadi miji" sakeena tana dariya tace "Iya aike na gada, dan bantaba ganin kin fita bada ixinin Baba ba" Iya dariya kawai tai dan tasan sakeena gaskiya ta fada
Da dare Sakeena da taje kaiwa Deni abinci ta fada masa Xancen fitarsu da Iya gobe, yana kallonta yace "To Sakeena amma dan Allah inxaki fita kisaka hijabi kinga cikin maxa xaki shiga, inada kishi akanki sakeena" tana murmushi tace "to ya Deni xan kiyaye in shaa Allah" ta miqe xata tafi Shima ya miqe ya riqo hannunta ya mairaice ta dubeshi tana kallon hannunsa dake cikin nata tace "xan tafi ya Deni" ya qara marairaice mata yace "sakeena wlh so kawai nake injiki jikina, dan Allah in rungumeki?" bai jira amsarta ya jawota ya matseta tsam a qirjinsa, sun dade a haka kafin ya saketa ya koma ya kwanta ba tare da yace komai ba itama sakeena ta fice a dakin.
Washegari suka nufi kasuwa da Iya basu kasuwar rimi basu kofar wambai haka suka kusa yini a kasuwa sukayo siyayya ta rufin asiri, andan siyo mata kayan kicin na amfani harda risho Iya ta siyo mata Suka xubo kayan a qatuwar robar tara ruwa suka taho. Suna sauka yara suka shige da kayan dakin Iya su Hadixa nata baxa ido suga abunda aka siyo. Iya bata xauna ba ta tafi gurin wanda aka bawa fentin drawer din sakeena ta kai masa cikon kudinsa, ya fente tas tayi kyau kamar sabuwa.
Da daddare saiga Baba da katifar gado no 1 sabuwa qal a leda, ya kira iya da sakeena ya basu da cewa "gashi sakeena kiyi haquri naso inmiki kayan daki amma Allah be nufa saboda abun ya hademun gaki ga Deni amma ga katifa da ledar tsakar daki kiyi haquri kinji diyata Allah ya baku xaman lfy." ta duqa suka hada baki da Iya suka dunga godiya da fatan raya zuria.
Suka koma daki Iya ta dunga hamdala dama tana tunanin inda xata samu kudin saiwa Sakeena takifa tunda gado bai samu ba sai gashi Allah da iko ya kawo yanxu kam abunda ya rage kadanne wanda take fatan in shaa Allahu kafin ranar asabar din xata samu ayi.
Ranar juma a da safe ta tsefe kanta taje saloon akayi shampoo, yayi shar gashin ya miqe saboda bata taba shampoo ba. Tana dawowa ta wuce qunshi akai mata ja da baqi hannu da qafa tai shar tayi kyau. Dare yanayi aka taru akayi kamu aka feshe sakina da turaren kamu.
Aka watse bayan gama kamu, akabar sakeena da sanyin jiki don taga fa auren da gaske ne. Denin ma duk sai taji ya fita a aranta tunda zai rabata da Iya matar da tasota ta qaunaceta a lokacin data rasa kowa a duniya. Denin ma rabonta dashi tun shekaran jiya daya shigo tambayarta ankawo mata dinkin ta tace masa eh. Tun farar safiya akaje aka gyara inda xasu xauna aka kai mata yan kayan dakinta aka shirya risho ne kawai ba a kaiba Iya tace saita xuba kalanzir. Sakeena ta fashe da kuka bayan ta gama tunaninta. Iya dake saka lagwani a risho ta Kalli Sakeena tace "me kuma akai sakeenatu?" bata cewa iya komai ba sai sautin kukanta data qara. Iya ta matso bayan ta ajiye aikin da take ta kwantar da Sakeena a jikinta tace "nasan abunda kikewa kuka, kowa da haka ya girma sakeena, mu lokacin da akai mana aure ma bamu kaiku wayo ba, kuma nima ina jin ba dadi xan rabu dake amma kuma ya muka iya tunda haka rayuwar ya mace ta gada? Kiyi haquri kinji kibi mijinki ki xame masa matar rufin asiri" Sakeena cikin murya kuka tace "Iya Dan Allah ki yafemun haqiqa kinyi qoqari tun daga kan bani taribiyya har ixuwa kan ilimina da aurar dani ga mutum nagari nagode Iya ki yafemun" iya tana nata kukan tace "na yafe miki sakeenatu Allah ya baku xaman lfy da xuria ta gari ku kawomin yan yayanku inyi rainonsu kamar yadda nayi naku 😄" Sakeena da iya sukai dariya lokaci daya.
Sallamar Alhaji dan gidan Anty ta katse musu sallama, Iya ta hade rai dan bata manta dukan da uwarsa taiwa sakeena ba. suka gaisa da sakeena cikin raha har tana tambayar ragowar yan uwansa. Ya miqa mata envelop yace "wai gashi inji Abbanmu yace baisamu lbr kinyi aure ba sai yau, wai yana miki fatan alheri" ta karba tayi godia duk da batasan meye ciki ba. Suka bude envelop din bayan tafiyarsa tai karo da kudi yan 1000 guda 10 sabbi gal. Iya tai hamdala ta karbi kudin tasa hijabi ta nufi dakin Baba daganan tai waje da alama unguwa ta tambaya. Sakeena ta miqe ta tana tunanin ina Iya xata a wannan daren? Taci gaba da tunanin yan uwanta bazasu ba kenan kamar yadda suka fada? Da haka bacci ya kwasheta. Batasan ko qarfe nawa ba lokacin da taji Iya na tashinta a barci, ta miqe tana mutstsuke ido, Iya ta miqo mata samira tace "maxa ci dahuwar kaza nasa ai miki ban bada kudinba to yanxu Allah ya kawo shine naje na karbo. Ta miqo mata zanin gado tace dama shima ba a siya ba shine yanxu naje na siyo." ragowar kayan kuma Iya bata nuna mata ba kuma itama bata damu ba tayiwa Iya godiya taja kwanon kazar taci fiye da rabi taji ta qoshi amma fa badan dadi ba. Taje ta kuskure bakinta Iya ta miqo mata jarka tace "sha iya shanki kiban ragowar" ta kafa kai tasha da yawa ta bawa Iya ragowar.
Gari ya waye gida ya cika da dangin Hajjo wadanda suka bugo sammakon xuwa. Aka fara dora girki irin na bikin gidan talaka, yayin da suketa xarya dakin Iya dan ganin sakeena amarya, tayi tas cikin daya daga cikin atamfar da Deni ya bata riga da skirt kowa yaxo kuwa sai ya yaba da cewa a yayi iya xaben kyakykyawar mace ga kunya.
Ta barin sakeena kuwa tana tashi Iya ta bata ragowar kaxar jiya ta cinye ta dama mata wani gari da nono ta shanye sannan tayi wanka ta shirya cikin atamfar Deni.
wajen azahar aka kawo motar haya wacce Baba ya dakko haya aka cikata da dangin Hajjo suka nufi Sani mai nagge ganin gidan Deni. Sukaje suka dawo a salube, marasa hankali a cikinsu suka dunga sakin maganganu da cewa "a amaryar dai gatanan fara qal babu lefi amma daki fayau babu komai, da alama dangin amarya dai basu da xuciya. ko dan gadon bono babu? Yo wannan da a qauye ne wlh baza a aureta ba, amarya kam anyi kyan banxa" wata qanwar Hajjo ta karbe maganar da cewa "Yo ina dangin suke balle ace sunyi rashin zuciya? ai Nura me gajeran asali ya dakko mana ko kunga wani wanda xa a kira da dan uwanta a a taron nan?"
Duk wannan magana da suke a kunnan Iya da Sakeena da kuma abokan arxiqi da suka cika dakin Iya dan taya murna. Sakeena ta fashe da kuka jin ana mata gorin asali abunda tafi tsana a rayuwarta. Iya ta dubi Sakeena xuciyar na ciwon kukan da akasa sakeena a ranar bikinta, ta miqe ta fita tsakar gidan cikin bacin rai. Ta kalli masu yiwa sakeena cin fuska tace "Wai shin da kukewa sakeena gorin ba ai mata kayan daki ba shi Nuran meya yiwa sakeena a matsayin kayan aure? Ko ya baku lbr ya kawo wani abune in banda sadaki da ubansa ya biya masa? Saboda haka da sakeena da Nura kwaryar sama ke dukan ta qasa, sannan maganar cewa sakeena bata da asali wai shin daga ina wannan lbr ya samo asali? Wlh babu kaffara sakeena tafi Nura asali domin ita danginta babu jikokin tsinburbura da barbushe kuma inkunasan sanin asalinta ku tafi Dawakin Tofa (Baggadano) ku tambayi zuriar Malam Liman. Saboda haka inbakusan inyi muku tone tone ku samawa yara xaman lfy tunda sunasan junansu inba haka ba wlh xan farke muku laya domin nasanku yadda bakwa xato ko kun dauka bansan cewa uban wata boka bane babarta kuma yar bori?" Ai dajin haka uwar Hajjo dake cikin daki ta fito tana hada hanya ta bawa Iya haquri ta kada yayanta wadanda suka tsiro da fitinar tayi daki dasu.
Ta koma daki ta lallaba sakeena tai shiru, ta tasata a gaba taje ta kaimata ruwa tayi wanka ta fito ta sakata ta shirya lokacin har qawayenta sun fara xuwa wata yar ajinsu a boko da sukai aji daya tai mata makeup ,tayi kyau sosai, Iya ta miqo mata lace wanda kudinsa xai kai 5k tace "maxa saka kinji yar albarka" sakeena ta karba tana kallon Iya a ranta tace to inaji iya wannan kayan jiya ta anso daga dinki shiyasa take boyewa. Ta Kalli lace honey colour me kyau dinki riga da skirt me net anmata high neck yayi kyau kwarai ya dace da xamani, ta dunga godiya, ta saka akai mata dauri me kamar gwaggoro iya ta kuma miqo mata sarqa da su agogo da sabon takalmi da mayafi duk ruwan madara wanda suka dace da lace din. Sakeena ta washe baki tace "Iya duk ni kadai? Haka kika iya hada too much?" Iya tana dariyar ganin sakeena cikin farin ciki tace "yar banxa kin dauka nima ban iya gayu ba irin naku?"
Ta fito amaryarta tas ta fito tsakar gida qawayenta masu waya suna daukarta a photo. Kamar abun shiri saiga Deni ya shigo cikin milk din shadda dinkin tazarce ya kafa hula. Abokan wasansa suka saki shewa tare da yimasa gudar ango kasha qamshi. Ya Kalli sakeena kamar ba itaba kwalliyar ta mata kyau sosai ya dakko wayarsa ya miqawa Zahra yace "Dauke mu hoto zahra" ta karba ta qunshe dariya tana cewa ya Deni anty sakeena ta rudaka, yace eh wlh Zara kamar ba itaba tayi kyau. Tace anty sakeena cire mayafin mana, kafin tayi wani motsi Deni ya fusge mayafin ya miqawa Amina da suke gefe suna tabe baki da surutai irin na baqin ciki wai biki a gida kamar a qauye? Wata qawarsu tace "ai kuwa Amina sakeena dai tayi kyau kuma ni banga illar biki a gida ba, da can ba haka akeba kafin mu saki al adarmu mu aro ta wasu? Kuma gashi mijinta kyakykyawa dan gayu dashi daga ni yana sonta Allah ya bamu e tata" Amina cikin fusata tace "Allah ya baki dai don ni nafi qarfin candy aure wlh" tace "to xauna kiga qarshen biro da takadda wlh ni inasamun wanda yayimun aure xanyi domin aure baya hana karatu"
Sakeena dai da Deni sai hoto ake musu yayin da Deni beji kunyar mutanen gurinba ya riqe matarsa ana ta yi musu ita kuwa kanta yana qasa cikin jin kunya. Haka aka qarasa yinin biki aka watse
Dayin magriba Iya tasata kuma wanka lokacin sakeena kamar xata shide saboda kuka, ta kuma bata tsumi tasha. Ta bata atamfar da Deni ya kawo ta saka da komai sabo harda mayafi da takalmi ta bata 1k ta saka a Jakarta qarama pos. Ta dunga fesawa sakeena turare kafin ta rakata dakin Baba ta tarar da Deni shima a xaune ta nemi guri ta xauna ita kuma Iya ta fice. Baba yayi musu doguwar nasiha ya tunasar dasu haqqin miji akan matarsa da kuma haqqin mace akan mijinta ya rufe da addua bayan ya jaddawa Deni amanar sakeena da cemasa yarinya ce yayi haquri da ita kuma yayi tarbiyyarta.
Ya tashi ya fito dasu tsakar gida, yan tsirku suna nan ana jiran ace a taho kai amarya suje suga daki. Baba yace "kowacce mace ta tafi gidanta na soke kai amarya ni xan rakasu gidansu kamar yadda addini ya tanada" aka fara yan qananan maganganun cewa wane irin biki ne wannan babu kai amarya? Shi kuwa Baba yayi hakanne saboda gudun kuma faruwar rigimar da akai daxu.
Suna shirin fita daga gidan sakeena ta coge cikin kuka tace "Baba banga Iya ba, ban mata sallama ba" Baba yace "yi haquri kinji sakeena muje ai ba kun rabu bane har abada" suka fita tana kuka. Iya uwar dakinta ta qule itama tana kukan rabuwa da sakeena.
Suka shiga motar da Baba ya aro gurin uban gidansa, babu abunda kakeji sai tashin kukan sakeena. Ya kaisu har qofar gida ya fadawa sakeena adduar da xatai tayi tasa qafar dama ta shiga gidan. Baba ya rakasu har dakinsu a gurguje ya fito ya tafi saboda rugugin hadarin da garin yake.
Deni ya kunna fitilar wayarsa ya dakko caja a kunna ya lalubo tabarma ya shimfida musu a falon da abubu komai sai tarkacen robobin ruwa da yan tsirarun kayan kicin. ya kamo hannun Sakeena wacce ke tsaye ya xaunar da ita akan tabarmar daya shimfida. A daidai lokacin aka fara ruwa kamar da bakin kwarya, yayi murmushi ya yayewa sakeena lullubin kanta wanda ta rufe har fuska yace "Sakeena lallai soyayyarmu gaskiya ce, kinga adduar da nayi Allah yasa a kawoki ana ruwa Allah ya karba" tai shiru babu amsa tana cigaba da kukanta. Yasa hannu ya dago kanta dake duke ya kalli yadda idonta yayi ja saboda kuka yace "Haba mana sakeena, kukan namiye kamar ba dani xaki xauna ba? Kuma fa auren soyayya mukai" ita dai batace komai ba. Ya jata suka miqe tsaye yace "xo muyi alwala muyi sallar godewa Allah." suka tsaya nan qofar daki sukai alwala saboda ruwan da ake tsakar gidan babu kowa ga alamu an rufe kofar gidan kowa yana daki. Deni ya dakko qatuwar robar ruwan sakeena sabuwa da bokitai ya tara musu ruwan sama anan kofar dakinsu.
Ya jasu sallah raka'a biyu sukai suka idar, ya tamabayeta abunda ta sani akan adddini ta fada masa, yayi murmushi yace "madallah" ya dafa kanta yayi mata addua. Ya dakko qulin kazarsa wadda sakeena bataga lokacin daya shigo da itaba, ya baje musu, amma qiri qiri sakeena taqi ci domin ta rasa abunda ke mata dadi gashi yau wata irin kunyar Deni takeji. Da kyar da dadin baki ya lallabeta ya bata abaki sukashanye kwalin hollandia guda daya. Ya dakko sabbin brush guda biyu ya matsa musu oral B suka wanke baki a inda sukai alwala. Suka koma dakin jikinta sai karkarwa yake. Deni ya cire rigar shaddar jikinsa, ya xama daga shi sai dogon wando da singlet yace da sakeena "shiga ciki kisa kayan bacci Baby" da sauri ta shiga uwar dakin, shima kamar falo babu komai sai sif da kuma katifa daga jikin bango wacce tasha sabon xanin gado da filo biyu. Ta nemi gefen katifar ta xauna cikinta yana bada sautin qululu. Kimanin mintina 5 taji tahowarsa cikin dakin tai saurin kwanciya ta bawa qofa baya, yaxo ya kwanta gefenta ya kashe fitilar hannunsa ya ajiye, yasa hasken waya yana haska fuskar ta runtse ido. Yace "ya baki canja kayan ba sakeena?" cikin tsananin firgita tace "haka nake kwana bana canja kaya" ya ajiye wayar a gefe yace "to bari in rage miki su kisha sassanyar iskar da ake" ta tashi xaune tace "ni ka kyaleni sanyi nakeji" yayi murmushi ya maidata ya kwantar a kan jikinsa yace "to Baby xo inbaki dumin jikina ki rage jin sanyin." ta dan dade akansa a kwance tun gabanta na faduwa harya dena saboda ta xaci yayi bacci.
Can taji ya yunqura ya kwantar da ita kan katifar ya fara rabata da kayan jikinta a hankali. Hawaye ya wanke mata fuska lokacin da taji yana balle mata bra dinta, ta riqo hannunsa cikin rawar murya tace "ya Deni ban shirya ba" shima cikin tasa rawar muryar yace "kiyi haquri sakeena babu wanda ya taba shiryawa hakan" yacigaba da abunda yake, shinshinata yake yana sumbatar duk wata gaba ta jikinta ta labbansa yana sakin nishi ahankali daga baya ya dire kan abunda yake matuqar daukan hankalinsa a jikin sakeena. Ya taba, ya murxa ya kafa baki yana sucking nipple dinta kamar babu gobe, tun sakeena tana daurewa har ta fara shirin raba kansa da qirjinta domin nipple din ya fara yimata xafi. Ya dago kansa idonsa jajur yace "kina qaunata sakeena?" tai shiru babu amsa, duk da bata fada ba yasan amsar ta Eh ce. Ya qara cewa "indai har kina qaunata kuma soyayyar da kikemun gaskiya ce to karki qara yunqurin hanani wannan abun da nake miki, domin shine qarshen matakin soyayya sannan indai kika bari nayi miki to nima qara sanki xanyi fiye da yadda kike sona" cikin kuka tace "to" shikuma yaci gaba da abunda yake, yayin da sakeena tayi matuqa wajen gayyato dauriya danta nunawa Deni tana sonsa.
Wasan yacigaba Deni ya luguiguita sakeena matuqa kafin daga baya ya nemi maidata cikakkiyar mace, anan labari yasha banban domin sakeena taji wuyar data xarce tunaninta ai saita saki murya ta dunga kunxuma ihu iya qarfinta fadi take "ni ka kyaleni, bana sonka wlh na dena sonka, wayyo Iya yaya Nura xai kasheni" shima Deni xuwa wannan lokaci baya hayyacinsa domin shima nasa surutan yake cikin sambatu da gushewar hankali irin na novice. Inbadan ruwan saman da yaketa kwararawa ba da har maqota sai sun hana bacci da ihunsu bama mutan gidan ba.
Lokacin nutsuwa taxo masa sakeena ta gamayin laushi tiqis, ya kwanta a gefenta yana sharce gumin daya tsatstsafo masa a goshi duk kuwa da sanyin da garin ya dauka. ya dakko fitila ya kunna ya haska fuskarta, ya tarar da ita ido bude jajur dashi tana kallon silin. ganin ya kunna fitila ta lalubi dankwalin kayanta da Deni ya watsar kan katifa ta rufe jikinta. Ya kai bakinsa kan kunnenta yana shafa gashin kanta daya hargitse yace "me kuma xaki rufemun Baby? Ai mun xama abu guda yanxu, babu kunya tsakaninmu" batai masa magana ba shima bai kuma cewa komai ba ya kwantarta qirjinsa yana shafa bayanta tare da kalaman lallashi da godia. Tayi bacci a haka shi kuwa tunani yake, yasamu sakeena yadda yayi zato a matsayin macen data kare mutuncinta har xuwa gidan mijinta kuma dama shi be taba zaton mata shashanci ba. Ya kuma fadawa tunanin abokansa wadanda suke yawan fada masa cewar in mutum nason more dadin aure to ya auri matashiya wato yar shekaru 20 xuwa sama domin a fadarsu auren yar shekaru qasa da ashirin duk bata lokaci ne don basa iyawa namiji komai sai rakin tsiya amma matashiya duk abunda kakeso xata maka a harkar soyayya. To shikam yau ya karyata duk kuwa da cewa shima a nasa raayin yafison matashiiyar ba yarinya ba kamar sakeena, yau dai sakeena qanqanuwar yarinyar yar 17-18 wacce ya kusa ninka shekarunta ta shayar dashi wata irin xuma kuma ta kawar masa da kwayinsa akan ya mace na tsawon shekaru. Ya katse tunaninsa ya tashi daya tuna a gidan haya suke dole ya temakawa sakeena tun a cikin dare basai da safe ba komai a idon mutane. A hankali ya kwantarta kan filo ya xira wando ya fita falo, yana kici kicin kunna risho abun Allah aka kawo wuta saboda ruwan ya tsagaita yayi hamdala ya dakko heater ya dakko bokitin ruwan saman daya tara ya juna, ya koma ya kwanta kusa da sakeena. Kimanin baccin awa daya ya sureshi kafin ya farka a firgice yaje ya duba ruwan harya tafasa. ya fita yakai bandaki yaji dadi daya samu bandakin fes kamar bana hadaka ba, saida ya gama hada komai yakai toilet sannan yaxo ya tashi sakeena ta farka tana kuka ya daura mata xani amma ta kasa tafiya dan haka ya dauketa.
Ta tsuguna domin yin fitsari amma ta kasa sai wani azabar radadi cikin kuka tace "ya Deni na kasa fitsari kuma inaji" ya dafata yace "daure kiyi Baby kinji Allah yayi miki albarka" dakyar sakeena tai wani fitsari me azabar xafi hade da jini bayan Deni ya temaka mata ya riqeta kafin tayi. Haka ya dunga saka sakeena cikin ruwan dumi da gishiri kafin daga baya suyi wankan tsarki su fito, lokacin xaxxabi ya rufeta sosai ya bata paracetamol tasha ya gyara gurin da suka kwanta sannan suka kuma komawa suka kwanta yana rungume da ita.
Yau kam zaqin amarci yasa Deni makara, basuyi sallah ba sai da gari ya waye sosai suka tashi. ya shigo da ruwan katuwar jarkar daya tara musu cikin daki, ya debi wani a bokiti ya jona musu ruwan wanka. sakeena nakan sallaya tana kallonsa. ya tashi ya share dakin fes lokacin ruwan wankan ya dahu ya kaimata toilet yazo ya tsuguna yace "ranki ya dade nakai miki ruwan wanka taso kije kiyi kinji Baby" tai dauriya kwarai ta cije ta daura xani ta saka hijab ta fita tsakar gida. Ta tarar da matar gidan tana aikin sharce tsakar gidan ta sunkuya ta gaisheta, itama ta amsa da fara a tana tambayarta kwanon baqunta. Ta shige tayi wankanta tsaf ta fito tana tafe tana ware qafa saboda azaba. Ta samu ya fito mata da kaya ta shirya shi kuma ya tafi nasa wankan. yaji dadi lokacin daya fito ya samu tayi kwalliya tasha jambaki tana juye ruwan xafin daya jona cikin tea flask. yayi saurin karbarta yace "koma ki xauna sarauniyata ki jira na ida hada mana abincin" ta koma ta xauna kamar yadda yace, ya shige daki few minutes ya fito shima ya shirya yana qamshi. ya hado musu kayan breakfast tea da bread sai yan kayan shayi na sachet, ta duqar dakai ta gaisheshi ya amsa yana cire mayafin data lulluba yace "daga yau na haramta miki xama da mayafi a daki sai inxaki fita tsakar gida. Ya hada musu tea suka sha yaje ya wanke cups din ya dawo.
Yaxo ya dora sakeena akan cinyarsa suka qule uwar daki, tun tana dari dari harta sake suna hira yana qara fada mata yadda yake qaunarta. Bai fita ba ko kofar gida yace mata anbashi hutun 7 days a kasuwa. Da lokacin dora abincin rana yayi da kansa ya siyo kayan miya ya gyara xai fita kai markade matar gidan tace ya bawa danta Amir yakai masa duk aiken da yake buqata ma ya aiki Amir din. Yayi godiya ya bashi
Da kansa ya shirya musu miya da ragowar kazar jiya da sukaci ya dafa musu taliya ita sukaci kuma tayi dadi kamar ba girkin namiji ba koda yake ai yayi bautar qasa a wata jahar dan ya iya girki ba abun mamaki bane.
Da dadadre ya kuma sakata wanka shima yayi suka kwanta gabanta na faduwa kar akuma irin ta jiya amma kuma saiya rungumeta yana mata hira har ta Saki jiki yayi wasanninsa da ita sukai bacci.
**** ***** ***** ***** ****
A iya kwanakin hutun Deni 1 wk sunyi wata rayuwa me dadi shida sakeena, baya xuwa ko ina sai masallaci yayin da suke yini tare suyi wasanninsu suyi hirar soyayya ko kuma ya sa musu kallo a wayarsa. Tuntana dari dari dashi harta sake ganin be kuma neman komai a gurinta ba. Bata aikin komai sai wanka da sallah komai shike mata har girki. Ranar daya koma kasuwa ranar ta fara girki, sun rabu cikin shauqin juna ta yini a salube cikin kewa gashi yace karta fito tsakar gida indai ba aiki xatai ba. Ta gama girkinta kafin ya dawo tayi wanka tayi kwalliya, yaji dadi sosai lokacin daya dawo yaga har ruwan wanka takai masa. Yayi wnka yaje sallah suka xauna sukaci cous cous din data dafa musu sukasha lemon xaqin daya shigo dashi. suka kwanta bayan sallar isha suna hira a lokacin Deni ya kuma neman haqqinsa na aure a karo na biyu amma kash ya tarar da sakeena bata da tsarki, yana dubanta yace "yaushe yaxo kenan?" cikin kunya tace "daxu da azahar" ya koma ya kwanta yana cixon lebe. Ya dakko wayarsa ya kunna musu film din Dadin kowa yace "so nake insamu yan kudi ayiwa su Baba girki muje mu gaishesu Hajjo kullum saita kirani tana tambayar lfy muke wai so take ta ganmu. sakeena tanaji anyi xancen gida cikin sauri tace "ya Deni inada 1000 da Iya ta bani naxo da ita basai ayi girkin da itaba muje" yana kallonta yace "Allah ya sawaqe ban bakiba in karba sakeena ki riqe abarki ki dunga kashewa tunda bani da halin baki kudin kashewa akwai shirin da nake ina gamawa xamuje"
Kamar yadda ya fada ranar da suka cika kwana 14 wato 2 wks kenan saigashi da kaxarsa da kayan miya da safe. Sakeena ta karba cikin murna da axama ya tayata sukai stew ta debi taliya biyu cikin kayan abincinsu ta dafa suka cika sabbin food warmers din Sakeena da taliya da miya suka shirya sunyi kyau sosai ya riqe daya ta riqe daya suka hau napep suka nufi gwale gida.
Sunyi saar tarar da Baba a gida domin ga kekensa nan a soro. Sakeena ta rigashi shiga saboda shi ya tsaya biyan dan sahu. Amina ce ta fara ganin sakeena tayi shar ta kuma haske a 2wks kawai baqin ciki ya kamata tace "kinacan shar dake kinajin dadi Baba ya kwashe kudinsa yayi miki aure mu kuma an barmu da yunwa." sakeena bata kulata ba ta nufi dakin Iya ta kwada sallama kuma lokacinne Deni ya shigo Iya ta qanqame sakeena tana farin cikin ganinta yayin da acan tsakar gida Hajjo ta rungume Deni anata murnar ganinsa aka hadu duk a dakin Baba anata murna da gaisawa Baba bakinsa yaqi rufuwa ganinsu kuma da gani lfy suke xaune dan daga sakeenar har Denin sun canja. Sakeena ta ajiye flasks din a gaban Baba tace "Gashi Baba ya Deni yasa akai muku" Baba ya dunga godiya suka fito sakeena tabi Hajjo har dakinta ta kuma gaisheta, Hajjo tana kallon sakeena a sace a xuciyarta tana fata Allah yasa Deni bai dirkawa sakeena cikiba ganin irin wannan kyau da tayi, inko hakane ta makara domin shiyasa ta dunga zabgawa Deni waya dan suxo ta aiwatar da plan dinta kan sakeena.
Sakeena ta miqe xata koma dakin Iya Hajjo tabita da kallo tace "ina xaki sakeena? Aini yanxu na xama uwa a gareki ya wuce kixo dakina ki tafi, kiyi sakewarki da nan dakin da dakin Iya duk daya ne." Sakeena dai ta xauna a takure saboda kallon qurullar da Hajjo ke mata ta miqe qafa Hajjo ta qurawa qafar ido ganin tayi fari tas tayi luwai luwai, can dai dataga ta kasa gane komai saita kira sakeena uwar dakinta ta xaunar da sakeena cikin hikima da nuna kulawa tace "Sakeena dama a matsayina na uwa a gareku ke da Deni naga ya kamata in tunasar daku abunda quruciya ta hanaku tunawa. Ni a ganina be kamata yanxu ku xauna haka ba babu tsarin iyali duba da yadda akai aurenku kuma ga halin rashi da kuke ciki ga Deni babu halin riqe mata ma balle kuma Da shine nace mai xai hana kiyi tsarin iyali koda na shekara daya ne mugani xuwa lokacin ko abubuwa sun warware saiku fara haihuwar" Sakeena tai dan gajeren tunani irin nata na quruciya taga tabbas maganar Hajjo gaskiyace yanxu in sun haihu ya xasuyi da Dan? Ta kalli Hajjo tace "Eh gaskiya ne Hajjo xan fadawa ya Deni inyaso ya kaini asibiti aimun" Hajjo tayi mata daquwa tace "gidanku da inaso Deni yaji ai da shi xan fadawa bakeba, bakomi ake fadawa namiji ba ni yanxu uwa nake gareki tunda kin amince xan tura Hadixa gurin malamar asibitin qawarta ce tai mata bayani inyaso in anjima saita rakaki kuma sannan wannan maganar ta tsaya dagani saike karki fadawa waccan uwartaki kinji ko yata" sakeena tace "to Hajjo babu wanda xan fadawa" ta kuma kallon sakeena tace "anya ma kuwa sakeena wannan kyau da kikai babu ciki jikinki? yaushe rabonki da al ada?" cikin kunya tace "yau nagama daxu nai wanka" Hajjo ta sauke boyayyar ajiyar xuciya. Tana fita Hajjo ta kira Hadixa sukai qulle qullansu suka gama.
Iya ta dubi sakeena bayan ta dawo dakin tace "xaman me kikai a dakin Hajjo harda qulewa uwar daka? cikin basarwa sakeena tace "bakomi Iya" Iya ta kuma kallonta tace "kidaiyi hankali da ita dan wlh bata qaunarki aurenku da danta ma dan anfi qarfinta ne" ta amsa da "to"
Suka dunga hira da iya cikin farin ciki har Iya ta yi mata kitso a tsefaffan kanta. Iya ta kuma duban sakeena a karo na barkatai tace "sakeena yace ko ba shafe shafen nan naku na yaran xamani kika fara ba naga kinyi wani fau dake" sakeena tana dariya tace "wlh Iya cocoa butter muke shafawa ni da ya Deni kawai xaman guri daya ne." Iya tace "lallai kuwa xaman ya amsheki kinyi tas dake" Haka sakeena ta yini dakin iya suna hira yayin da Deni ya wuni gurin abokansa na unguwa suna hira, Baba kuwa duk abunda ya fita ya gani saiya siyo ya kawowa sakeena duk saida ya qarar da yan kudin aljihunsa. Su Hadixa kamar su suke sakeena.
Can bayan laasar Hajjo ta kwallah kiran "sakeena fito kuje Hadixa ta rakaki gaida qawata sabuwa tanata zancenku nace inkunxo na turaki ku gaisa" sakeena ta gyara fuskarta ta fito suka tafi da Hadixa Hajjo ta bisu soro tace cikin rada "ke bafa gidan sabuwa xaku ba gurin malamar asibitin xaku" sakeena cikin rashin damuwa tace "to Hajjo" ita harta manta xancen ma.
Sukaje gidan matar ta dubi Hadixa bayan sun gama gaisawa tace "duk ukun xa ayi at the same time? Hakan fa yana bada matsala" Hadixa tace "to wai ba angama magana dake ba? Kuma inba ai ba yanxu ina xa a dunga ganinta duk wata 3 ana mata kawai ki mata" matar ta cika sirinji da allurai 3 dam ta dannawa sakeena. Ita kuma xuciyarta daya bata kawo komai ba, allurar da akeyinta duk bayan wata uku 1 Hajjo tasa anwa yar mutane ta wata 9 lokaci daya dan tsabar rashin imani da dalili mara maana.
Suka dawo gida sakeena ta koma dakin iya bayan Hajjo ta jaddada mata inta fadawa wani wannan maganar wlh saitasa Deni ya saketa.
Haka suka gama yininsu bayan sallar isha sukaci tuwo sukai wanka, Iya ta hada musu kayan miya irin wanda take siyarwa Hajjo kuma ta basu garin tuwo da gasara cikin jug. Su Amina suka rakasu har bakin titi sukahau napep suka tafi.
Suna xuwa gida sukai shirin bacci, a ranar dai Deni ya
[7/31, 2:13 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣1⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Wayewar garin lahadi suka tashi da baquntar matar daya dakin gidan dake rufe sundawo daga tafiyar da sukayi me suna Mariya. Da fitar Deni sakeena ta hado yan kwanikan da suka karya ta fito tsakar gida sanye da hijabi kamar yadda Deni yayi mata umarni. Tana aikinta suna hira da umman amir wato daya matar kamar yadda suke kiranta. Mariya tai but ta fito daga dakinta tana mutstsuke ido alama daga bacci ta tashi ta dubi sakeena kallo na qurullah sannan ta maida kallon ga umman Amir tace "wannan itace amaryar gidan namu?" Umman amir ta bata amsa da "eh itace sunanta sakeena mijinta kuma Nura" ta dubi sakeena tace "sannu sakeena, amma kuma meye na fitowa da hijabi ai duk mazajenmu sun fita" sakeena tayi dariya tace "eh nasani umarnin mijinane hakan" Mariya ta tabe baki, ta koma ta debo nata aikin ta fara tanayi tanawa sakeena hira don ta shige mata amma saitaga sakeena bata damu da ita ba.
Tana gama aikinta ta tashi ta koma daki. Inda ta manta cokali a gurin, da sauri mariya ta dauka ta nufi dakin sakeena don taga meye aciki, tayi sa a sakeena na uwar daki a kwance dan haka babu neman izini ta banka uwar dakin tana qarewa komai kallo tace "sakeena ga cokali kin manta" ta karba tace "nagode amma inkinxo ki dunga sallama ko ki tsaya iya falo" ta tabe baki tace "kinji yarinya daga gwaninta?" ta fice fuu bayan ta gama ganin abunda takeson gani.
Yauma kamar ragowar kwanakin kafin ya dawo ta gama girkinta tuwon masarar da Hajjo ta basu jiya da miyar kuka tayi wanka tayi kwalliya ras. Ta kintaci lokacin dawowarsa taje ta wanke toilet wanda dawowar Mariya yasa ya fara daukan qazanta. Tana fitowa daga bandakin dauke da tsintsiya a hannu saiga sallamarsa. Ta cillar da tsintsiyar ta tafi da gudu ta daneshi, shima ya rungumeta yasa hannu ya dauketa sukai daki yayin da Mariya ke leqensu ta tagar dakinta.
Ya direta a tsakar dakin yana kallon kwalliyarta yace "kinyi kyau sosai Baby, amma meyasa bakisa hijabi na sameki a tsakar gida haka gashi kinyi kwalliya?" Ta dan marairaice tace "kayi haquri naga xan shiga bandaki ne kuma ba kowane namiji a gidan amma kayi haquri daga yau xan kiyaye" ya rungumeta yace "na haqura Baby, ki dunga kiyayewa kinji, inada tsananin kishi akanki" sukai murmushi tare yayi shirin wanka takai masa ruwa ya fito dan shiga, Mariya tai saurin fitowa qofar daki ta kafeshi da kallo. Ya shiga ya gama ya fito tana xaune dandamalin kofar daki, sakeena ta miqo masa ruwan alwala yanayi. Ya gama ya miqe ya farga da kallon da Mariya ke masa yayi saurin shigewa daki yana tsaki.
Bayan sallar isha sunci tuwonsu a kwano daya cikin soyayyar juna suka wanke baki bayan sun gama Deni ya dora sakeena kan cinyarsa suna kallon shirin dadin kowa sabon salo a wayarsa wanda aka haska jiya kuma dama duk sanda xasuyi kallo haka yake dora a cinyarsa sunayi yana mata wasannin soyayya. Bayan sun gama suka kwanta kamar jiya yauma haqqinsa ya nema ta kamo hannunsa tace "wai ya Deni dadin wannan abun kakeji ne?" yana lumshe ido yace "dadin baxai fadu da baki ba Baby" ta kada kai tace "to nikam banaso wlh da xafi kuma sam ni banjin dadinsa" ya toshe mata baki yace "shiiii ki daina fadar haka, malaiku xasu tsine miki kuma bana ce miki in kina bani qara sonki xanyi ba? To kawai ki dunga haquri xafin na dan lokaci ne xaki daina ji" tace "to" haka yayi amfani da wayonsa da kuma qarancin shekarun sakeena yasha budurinsa san ransa, ya kwantar da ita a qirjinsa bayan komai ya lafa yace "Sakeena" ta dago ta kalleshi dan a yan kwanakin nan be cika fadar sunanta ba sai dai yace Baby idonta taf bacci ga gajiyar daya saukar mata yanxu tace "naam ya Deni" ya sumbaci goshinta yace "tanxz, thank u very, kin inganta rayuwata kin temakeni kin kareni daga fadawa halaka kin rufamun asiri, inason aure sosai ina buqatarsa saboda shekaruna sun kai amma ina hango aure a matsayin wani babban lamari gareni wanda baxan yishi kwana kusa ba duba da yadda auren yayi tsada, sanin hakan yasa shedan ya kitsamun fadawa halaka Allah yasa kika bijirewa hakan sannnan kika rufan asiri a qarshe kikaiwa mahaifina biyayya ta hanyar karbar aurena hannu bibbiyu, duk da bani da komai kuma ban miki komai ba Nagode sakeena Allah ya bani ikon riqeki da gaskiya" ta amsa da "Amin ya Deni, amma ni da kai duk mun rufawa juna asiri ne, yanda kake talaka mara kudin aure haka nake yar talakawa wacce ba a da kudin aurar da ita kaga mun hadu munyiwa juna rufin asiri" yana shafa kanta yace "a a Baby ke xaki iya samun Mai kudi yace bai buqatar komai sai ke kodan kyanki da farar fata" ta toshe bakinsa tace "ni kuma kai nakeso bakomi ba" haka dai sukai bacci cikin sambatun soyayyar juna. Da safe ta dama musu koko da gasarar da Hajjo ta basu, ta dumama musu tuwon jiya suka karya dashi Deni yana ta santin cewa wai sakeena waya tsiro da yin dumame? Tace tana dariya gama ci na baka lbr 😄 shima yana dariya yace to gaskiya yayi basira, ta qara sautin dariyarta tace na fika sanin haka, ya kintse tasa dariyar yace ke bafa santi nike ba 😄
"Amma dai mijinki a bazawara ya aureki ko?" itace tambayar da Mariya ta fara taryar sakeena da ita lokacin data fito wanke wanke. Sakeena tai sakato tanabin Mariya da kallon mamaki, tayi murmushi tace "abunda yasa na tambayeki naga ba aimiki kayan daki bane, mu kuma a garinmu auren baxawara ne kawai akeyinsa babu gado" ran sakeena ya baci da wannan cin fuska na Mariya daga haduwa jiya ta watsawa mata harara tace "A bariki ya auroni ba a baxawara ba" Mariya taja baya tace "a a yi haquri daga tambaya? Kuma ma ai naga baku fito wankan tsarki ba da asuba shiyasa na kuma tabbatarwa baxawara ce ke, ai da budurwa ce kullum sai yayi saboda doki kinga ni lokacin da nake amarya salisu har da rana dawowa yake daga aiki yayi" kafin sakeena ta bata amsa umman Amir ta fito ta tsawatar musu saboda taji duk abunda suke.
Koda Amir ya dawo daga makaranta ummansa tace duk me aike ta kawo zai tafi cefane Mariya ta bayar sakeena kuwa batai niyyar girki ba sabida tana da ragowar dumame xataci da rana da daddare kuma xatai musu jellof din shinkafa da daddawa da barkono wadanda Iya ta bata kuma tayi hakanne don nemawa Deni sauqi. Mariya taxo har qofar dakinta tace "amarya naga baki bada kudin cefane ba?"sakeena cikin hargagi tace "ke ni inada komai na girki" ta kada kai ta fita, sakeena tai tsaki daga jiya xuwa yau kawai ta fara gundura da halin shishshigi da bin kwakwkwafi na Mariya. Abun mamaki tana gama girki wajen azahar sai gata da kwano shaqe da abinci ta kawowa sakeena har daki, a lokacin ita sakeena ma har ta gama cin tuwonta tana karatun novel. Ta ajiye kwanon tare da cewa "amarya gashi naga baki girki ba shine na kawo miki" ta miqe daga kwance ta dauki kwanon tare da danqar hannun Mariya duk kuwa da cewa xata bata ratar wajen shekaru 7. Ta kaita waje ta damgwarar mata da kwanon tace "gashi ni naci abinci bani da buqata kuma daga yau karki kuma shigarmun daki tunda nima bana shiga naki" bata jira amsar da xata bata ba ta koma daki.
Da daddare sunacin abinci da Deni take fada masa yadda sukai da Mariya, yace "da kyau Baby, kamar yadda kikai yau ban yarda ki karbi abincin kowa ba kuma kema ban yarda ki bawa kowa ba, su riqe nasu na arxiqi muma mu riqe namu na takauci"
**** ****** ***** ****** *
Watanni biyu sun shude da bikinsu kuma a lokacin ne rayuwa ta fara garasu, domin dan kayan abincin da suke dasu sun qare, gashi abunda Deni ke samowa a kasuwa be wani taka Kara ya karya ba a times kudin kan tafi ne a transport dinsa daga gida xuwa kasuwa. Sauqin abun ma Iya kan mata aiken dan kayan abinci da kayan miya a duk sanda Deni yaje amma duk da hakan suna dandana kudarsu kuma suna rayuwa irinta hannu baka hannu kwarya. Bata qara xuwa gida ba kamar yadda duk cikin yan uwan Deni babu wanda yazo inka dauke zahra kuma duk sanda sukai waya da Iya ta wayar Deni intai mata korafin rashin xuwanta Iya kance "to sakeena ai bamayi ta xuwa gidan yara ba da girmanmu tunda kuna xaune lfy shikenan" sau tari sukan kwana da yunwa ita da Deni in akai rashin dace ba ai ciniki a kasuwa ba wanda hakan kesa 300 din da aka bashi su tafi a mota ya dawo da 100 gida wacce ke tilasta musu cin awarar naira 100 ko garin kwaki su kwana haka ya tafi yabar sakeena da safe da neman abunda xataci kota yini da yunwa kafin ya dawo ya samo dan abunda xasuyi maleji.
A gefe guda kuma Mariya yar hayar gidan ta bude wuta kwarai wajen takura rayuwar sakeena,
A dan xaman watanni biyu sakeena ta fuskanci wacece Mariya ciki da bai, mijin Mariya salisu ya kasance kurtun dan sanda ne wanda yake mutuqar tsoron bacin ranta dan haka tai mugun rainashi tare da maidashi mijin tace. Duk albashinsa yana tafiye akanta abunda taga dama shi take dafawa taci ta bawa yan korarta wato yan matan maqota da suke shigowa inma taga dama taqi girki kuma tilas inxai shigo ya taho musu da abunda xasuci. Tana da saka ido da shishigi da bin kwakwkwafi ga kafirin munafurci, a kullum Mariya ke tara yan mata ayi xaman majalisa tun safe har xuwa yamma dai dai lokacin dawowar Deni saboda shi kadai ke dawowa da yamma. A duk kuma lokacin daya dawo kuma xasu bishi da kallo yayin da shi kuma xaiyi wankan da ya saba yi da kuma alwala a takure saboda kallon da suke masa. Inda a washegari xakaji sun kafa hirar kyau da iya gayu irin nasa harda ma sajen dake fuskarsa, a inda sakeena ke daki tana jinsu. In wata a ciki ta kwabesu da cewa matarsa fa xata iya jiyosu Mariya kance saime intaji? Ai mijin mace hudu ne kuma duk wacce ta auri me kyau ai tasan sauran, kuma inma sakeenar ta tanka wlh sai tasa salisu ya kaita station. A duk sanda ta fadi haka sukan saka shewa da cewa sai matar officer.
Halin Mariya bai tsaya nan ba takan qiyin wankan tsarki harsai rana ta fito su sakeena sun fito yin aiki sannan taje tayo ta fito tana yarfe gashi tare da yiwa sakeena habaici kamar kishiyarta. Akwai sanda ta fito tana yarfawa sakeena ruwan dake kanta tana cewa "ai wlh duk macen da mijinta bai kusantarta wlh baya qaunarta domin mudai a gurinmu kwanciyar aure itace soyayya" umman Amir dake tana gurin ta fara yiwa Mariya fada da cewa "ke asirin shimfidar mijinki kike taunawa dan baki da hankali?" ta tasowa mata cikin fitsara tace "ai badake nake ba, wacce nake da ita tasan kanta"
Ire iren wadannan abubuwa sune matsalar sakeena a gidan aure, domin kullum da kalar takalar rashin mutuncin da Mariya xatai mata, yayin da Deni ya hanata fita tsakar gidan kwata kwata sai da kwakwkwaran dalili kuma yayi mata kashedin duk sanda ta kula mariya sukai fada saiya saba mata.
Umman Amir kam bata da matsala macece me kirki wacce bata iya shiga sharri ba shanu ba, taja girmanta kwarai kuma ta tarbiyyantar da yayanta. mijinta ya kasance yanajan motar haya ne kuma ya tsayawa iyalansa basu nemi komai sun rasa ba, shine na qarshen shigowa gidan kullum kuma shike rufe kofa kuma yana riga kowa fita saboda yanayin sanaarsa. Sai sakeena tai sati bataji muryarsa ba a gidan. Umman Amir ta dauki sakeena da Mariya a matsayin yaya inda in suka fara fada takan tsawatar a matsayinta na babba amma daga baya dole ta dena saboda Mariya da yan majalisarta sukan yimata rashin kunya intai irin wannan gyaran dan haka taji dadin hana sakeena fitowa da Deni yayi. A inda Mariya kecewa umman amir munafuka wai ta hada kai da sakeena. Umman amir kan yawan temakawa sakeena da abunda xataci a bayan idon Mariya, inda sakeena ke karba dakyar saboda hanata karbar abinci da Deni yayi, duk sanda taqi karba takance karbi kici sakeena har ga Allah baki lefiba, ni Dan Allah na baki kuma nayi kwatan kwacin irin wannan rayuwar da kikai kafin Allah ya hore abawa baban amir mota. To wannan shine dan saukin da sakeena ke samu. Takanyi fatan inama ta iya kitso ko qunshi data taimakesu ita da mijinta wanda yunwa da wahala tasa duk sunyi baqi sun qare.
Tsakaninta da Deni babu matsala don be fasa lallaminta ba da nuna mata soyayya, a kullum kan ya fita yakan jawo mata ruwa a rijiya ya cika mata komai, wanda hakan kewa Mariya ciwo dan ita bata samu hakan ba daga nata mijin. Yan majalisarta na fara xuwa xakaji tana xancen "sai aukin ja mata ruwa a jiye ko kuma ai mata wanki weekend amma anbarta da yunwa" su Saki dariyar iskanci suce "badai ta auri kyau ba, yo ina amfanin kyau babu kudi?"
Abu daya ke damun sakeena da Deni shine dena nuna xulamarsa da yayi akanta, wato a shimfidarsu tun bayan fadawarsu cikin rayuwar qunci shima saita fuskanci buqatarsa akanta ta ragu da kashi 50 cikin 100. Bawai baya kusantarta ba, no yanayi amma sai suyi 10 dayz hakan bata afkuba kuma dama shi duk sanda hakan ta faru baya bari sukwan da janaba saboda kunyar mutan gidan a daren yake tasata suyi wanka kafin su kwanta. Wanda hakan kesawa Mariya taga basa komai sabida basa wankan safe. Ita bawai tana damuwa bane ya kusanceta ko kuma tana buqata, a a ita kawai a haukanta sai takega kamar yadda Mariya ta fada baya sonta duk da be wani abu da xai nuna hakan ba. Amma dai abun na matuqar damunta, kuma gashi baxata iya fada masa ba. Sannan abu na gaba tun randa Hajjo tasa akai mata allura bata kuma period ba.
Wannan kenaan.
****** ***** **** ****** **
Yauma dai kamar yadda aka saba ta tashi tanajin yunwa saboda jiya Deni 100 ya shigo da ita gida, suka siyo garin rogo na 50 sukasha babu sugar suka kwanta da safe kuma ya siyo musu qosai na 50 sukaci wanda babu inda yaje musu. Wajen 2::00 na rana taji umman Amir tana ta fama da Amir yaxo yakai musu gugar kayansu, sakeena tayi xunbur da miqe ta nufi tsakar gida, tana fitowa su Mariya sukai shiru suka fara binta da kallo kamar yadda suka saba. Tayi sallama dakin umman Amir tace "shigo mana sakeena" ta shiga a kunyace tace "umman Amir naji kina cewa xaki kai guga mexe hana ki bani inyi miki ki ban kudin" cikin mutuntawa tace "to sakeena ba komi rufo dakinki kixo nan kiyi saboda karki fita da kaya wadannan suka gani" taje ta rufo taxo. Ta juna iron ta fara gugar, suna dan taba hira da ita. Ta dakko ragowar breadin safe ta miqawa sakeena tace "ungo ci kafin ki gama kinga yau sun cinye abincin tas" ta karba babu musu dan yunwa takeji, ta cinye gayan breadi tasha ruwa ai kuwa taji ta samu qarfi. Nan da nan ta gama gugar kuma umman Amir ta bata 200 duk kuwa da cewa gugar batakai haka ba, ta kuma kallon sakeena a karo na barkatai ta tausaya mata yarinyar duk ta mokade ta rame saboda yunwa tace "sakeena xaman nan haka bazai miki ba ki nemi sana a kinji? Ni badan kishi irin na Nura ba wlh dana samo miki aiki gidan Alh Dalha can inda nake xuwa yiwa matarsa da yayansa kitso, tun kwanaki mai musu girki tayi aure suke neman me girki kuma girkin kadai xakiyi suna da masu aikin komai. Sannan wlh suna da mutunci basu da Matsala ga girmama mutane" sakeena tace "to umma xan fada masa in shaa Allahu xai amince, inkinje kice ansamo in sunaso" tace "a a fara fada masa dai inya amince na fada musu yadda Deni baison ko naminjn kuda ya kalleki" sukai dariya a tare suka fito. Mariya ta doka tsaki tace "angama gulmarmu Allah ya isa kuma duk baqin cikin mutum na gaba yayi gaba." babu wanda ya kulata.
Sakeena tasa Amir ya siyo mata yan kayan miya da taliyar Hausa (ta fulawa) ta 100. Ta tashi girki wajen qarfe hudu lokacin. Su Mariya sukass shewa da cewa "yau fa ba sabonba tawaire andora tukunya" itadai bata kulasu ba farin cikinta daya yau bazasuyi kwanan yunwa ba ita da mijinta, burinta kawai ta gama tai wanka kan ya dawo shima yayi su hadu suci abinci.
Burinta ya cika wajen qarfe biyar ta gama dafadukan taliya wanda yaji daddawa da albasa takai daki ta juye a flask tai wanka tai kwalliya ta dau novel tana karantawa. Duk da cewa tanajin yunwa kuma tun tana girkin yawunta ke tsinkewa amma bataciba tafiso Deni ya dawo suci tare yadda suka saba.
Wajen biyar da rabi Saddiq yayi sallama ya shigo gidan, sakeena ta taryeshi da girmamawa don batai tsammanin zaizo gidanta ba duba da yadda yaqi jininta. Suka gaisa yake cemata yaxo gidansu wani abokinsa ne kusa da nan shiyasa ya biyo. Ta dakko masa ruwa a jug ta dakko masa flask din taliyar data gama dafawa yanxu da faranti da cokali da kuma service spoon ta ajiye masa ta koma daki don ta bashi guri yaci. Saddiq yayi dariya ya dauki cokali ya cinye taliyar tas cikin mugunta duk kuwa da cewa tafi qarfin cikinsa yana cewa aransa shegiya kya kuma neman wani abincin dan daganinki keda Deni today ta tabaku shegu waiku masoya kwayi soyayyar da yunwa ai.
Sukai sallama ta rakashi har soro ya tafi, ta dawo ta bude kwanon ta tarar duk ya cinye. Tace "Ashe dai taliyar nan babu rabona duk da raina ya biya babu komai Allah ya kawo wani abun baqonka ai annabinka ina lailfin wanda ya tuna dakai yaxo?" taje ta wanke kwanikan ta kife tana jiran tsammanin wa rabbuka.
Acan gida kuwa saddiq ya fadawa Hajjo da su Amina yadda suka kwashe da sakeena suka dunga dariyar mugunta ya qara cewa "ni wlh daga Deni har ita duk sun wani mokade kamar yan gudun hijira" Hajjo ta cije lebe tace "hmm ai sunajin garin, bakaga kullum sai yaxo ba ko xan bashi wani abun ni kuma na hanashi dan da inbashi suci da wannan tsinanniyar yaren gara ya xauna da yunwa, dan banxa gashi da xurfin ciki kowa ya ganshi yasan a wahale yake rayuwa amma yaqi saduda. Ai yanxu kam ya gane hangen da nake masa na auren diyar masu akwai dan da itace iyayenta ai bazasubar yarsu da yunwa ba" Fiddausi tace "yaushe rabon da kijishi yana qamshi ko ya hau online? Yo babu kudin turare babu na Data" Saddiq ya saki dariiya yace "haka suke soyayyar da tsamin gumi kenan, hahaha kowa ya tuba dan wuya ba lada"
Su kuwa bayin Allah masoya suna can kwance bayan an idar da sallar isha saboda andauke wuta anfara iska ga hadari , babu abunda sukaci dan yau Deni aljihun nasa naira 100 ce suka ajiyeta xuwa da safe. Yayi zurfi cikin tunani na neman mafita shi kansa yunwa yakeji duk kuwa da yasamu rogo da gyada yaci a kasuwa, bare sakeena da bai bar mata komai ba sai ruwan rijiya. Kunyar sakeena yakeji ya kasa sauke nauyinta duk kuwa da yana iya qoqarinsa amma abun yaci tura. Ya shafa bayanta yace "Sakeena" yaji shiru alamar tayi bacci. Ya kuma shafata yace "sakeena kiyi haquri na bakki da yunwa ba a son raina hakan ke faruwa ba yanxu bama ciniki a kasuwa yawanci naira 100 Alh ke sallamarmu da ita, wannan dalili shiyasa bana xo miki da buqatata ta aure duk kuwa da inason hakan amma ya xanyi inba haquri ba, ban baki abinci kinci ba inxo miki da buqata ai sai zaluncin yayi yawa" Sakeena ta kuma luf bayan ta gama saurarensa. Allah sarki Deni shiyasa zargi ba dadi ashe duk abunda yake mata har takejin haushi ba rashin soyayya bane yanada dalilin yin hakan.
.Da wannan tunani bacci ya kwasheta, can wata masifaffiyar yunwa ta saukar mata da ciwon kai wanda yasa dole ta tashi don ta gaza dauriya duk da tana kwance ji take uwa xata fadi. Ta daki cinyar Deni dake kwance ya tashi yana dubanta tace "ya Deni yunwa nakeji baxan iya kwana haka ba" Ya mutstsike idonsa ya qura mata ido tunda suka shiga wannan halin yaune rana ta farko da sakeena tace masa tanajin yunwa. Lallai tura takai bango tunda har sakeena ta fada masa tanajin yunwa duk da kawaici irin nata. Ya tashi yasa Shirt akan dogon wandon jikinsa bece mata komai ba ya fice tana binsa da kallo.
Tana xaune tana dakonsa har 10:30 tana tunanin ina ya tafi gashi anfara ruwa.
Acan Deni kuwa nufinsa yaje gida can gwale ya karbo musu tuwo suci. Ya fara tafiya aqafa cikin gwarin gwiwa. Har ya wuce wani gurin me shayi ya dawo jin ana musun ball wacce aka gama daxu. Ya matsa kusa domin jin yadda aka kaya tsakanin Nig da Iceland. Yana tsaiwa a gurin me shayin dake fifita shayi a cups yace "Alh me xa a baka?" Deni yayi murmushi yace "a a kawai na tsaya ne naji yadda wasan ya tashi" wani matashi a gurin yace da Deni "ai abokina Nig ta lallasa Iceland" Deni yayi dariya yace "to Masha Allah, Allah ya temakemu a wasa na gaba" ya juya xai tafi, me shayin yace "ai baxaka tafi haka ba abokina saboda murnar musulmi kuma Dan arewa (Ahmad Musa) wani Alhaji da yaxo yanxu ya bani kudin komai na nan gurin yace in raba komai free murnar cin kwallayen. Kawai fadi abunda kakeso abaka" Deni yayi dariya tare da hamdala a xuciyarsa yace da me shayin "a dafamun indomie da kwai muci da me dakina shi kuma Alh Allah ya qara arxiqi ya temaki qasarmu 9ja" matasan gurin suka amsa da amin sukaci gaba da shewa kamar rana yayin da me shayin keta aikin soya musu kwai yana miqo musu. Deni ya xauna, yana sauraren hirarsu har me shayi ya gama dafa masa ya juye masa a baqar leda babba ya dora masa wainar kwai biyu, ya miqa masa yace "gashi me gida angama maka" Deni ya riqe ledar ya jita dam yace "wannan duk ni kadai?" yana dariya yace "ko taima kadan a qara maka?" Deni yace "a a naji da yawa ne" me shayin yace "ai kace da madam xakuci shiyasa aka dafa maka 3" Deni ya miqe ya riqe ledar yana godiya xai tafi, me shayi yace "tsaya mana abaka ruwan shayi ku dumama cikinku bakaji garin ya dau sanyi ba?" ya tsaya kuwa ya qulla masa shay a ledoji biyu yasha madara da milo murtuk. Ya karba yana godiya ya tafi.
Lokaci daya shiga gida har 11 tayi. Ya samo tea flask ya juye musu ruwan shayin aciki ya cika dam harda ragowa ya juye musu ragowar a cup. Ya ajiye ya dakko tray ya juye musu abincin sai turiri yake. Ya ajiye flask din shayin yace gobe da safe munsami abinci. Ya cire jiqaqqun kayansa yasa gajeren wando da singlet ya shiga dakin dauke da Cup din shayi da farantin abinci. Ya bubbuga kafadar sakeena wacce ta gaji da jiransa bacci ya dauketa.
Ta tashi tana matse jiki saboda sanyi da kuma xaxxabin da yunwa ta haifar mata tace "ya Deni ina kaje ina kaje hankali ya tashi" yace "jeki wanko bakinki muci abinci" ta tashi ta fita tana layi taje ta wanko taxo. Suka sha tea din a cup daya yana kurba yana bata, suka gasa ciki. ta Kalli indomie din gabansa tace "ya Deni ina kasamo wannan?" ya bata amsa da cewa "eat don't talk" Tasa hannu sukacinye ta tas. Suka sauke hamdala tare bayan gamacin abinci, lallai sun yinwata sun tashi da super pack 3 da soyayyan kwai hudu. Sukaje suka wanke baki suka dawo ga mamakin sakeena ta dainajin xaxxabin da ciwon kai, lallai yinwa ba dadi. Suka xauna hira yake fada mata yadda ya samo. Ta fara tunanin abunda taji Deni na fada daxu, rabonda su kadaice harta manta. A hankali ta haye cinyarsa ya ajiye wayarsa da yake dannawa ya riqe qugunta yace "ya akai Baby?" tana shafa sajensa tace "ya Deni baka taba yimun kiss ba" yayi murmushi ya sumbaci lebenta yace "nayi miki sakeena ta" tana qara shafarsa tace "ba haka ba ya Deni, irin wanda nike gani in muna kallon film a wayarka" ya waro ido yana mata kallon mamaki, kafin yayi magana yaji ta hada bakinsa da nata tana tsotsa cikin shauqi a karo na farko a rayuwarsu, tun suna xaune sai gasu kwance kan katifa suna mutsutstsuke juna. Sakeena dai itace ta jagoranci wasan yayin da Deni ya xama dan kallo sai yadda tayi dashi, ta dunga yimasa abunda be xaci ta iyaba suka shude mintina a haka kafin komai ya lafa ta kwantar da Deni kan qirjinta tana shafar kwarin bayansa shi kuma yana qara qanqameta cikin gushewar hankali.
Sai da ya gama dawowa hankalinsa ya qura mata ido, ta kauda kanta cikin kunya. yaja hancinta yace "ke, kinsa sai ihu nake gida da mutane ko?" tana dariya tace "ai suma suna nasu ihun wani tym din ma harsu hanamu bacci" ya dorata a qirjinsa yace "Gara da Allah Baba ya farga ya aurar dake da wuri, dake dinnan? Hmm" tayi dariya tana kuma shige masa. Yace "tashi muje muyi wanka" tace "ya Deni dan Allah mu bari da safe mayi wankan nima Mariya taga munyi ta dainamun gori. Ya hade rai yace "ke banason shashanci da qauyanci, kowa sai yasan abunda mukai? In ta kuma miki gorin kice mata ke saboda soyayya tare kuke wankan da mijinki"
Washegari sukai baccinsu na safe har xuwa qarfe tara kodama yunwa ke hanasu baccin safe. ya tashi bayan sun farka ya siyo musu bread da 100 din jikinsa suka sha da tea din jiya. Suna karyawa sakeena ta kawo masa xancen aikin da sukai da umman Amir, ya hade rai sosai har sai da sakeena ta tsorota. Ya dunga zazzaga mata masifa a qarshe ya kalleta yace "dole ki nemi aikatau sakeena saboda kin auri talaka wanda ya kasa daukar dawainiyar ko? Baki duba darajar aure ba kike neman tafiya yawan aiki ko?" ta saka kuka jin abunda yace ,kukanta yasashi yayi shiru ya janyota jikinsa yana lallashi yace "dena kuka kinji kiyi haquri, amma karki kuma yimun irin wannan maganar inada kishi sosai" itama bataja fushin ba ta haqura suka shirya. Taga baya shirin fita tace "ya Nura yau baxaka fita bane" yana danna waya yace "Baby banga amfanin xuwa kasuwar ba tunda xuwana be hanamu kwana da yunwa ba, saboda haka na daina xuwa xanyi tunanin yin wani abun" ta kalleshi da tausayi ta kwantar da halshe tace "ya Deni ko baxaka samu komai ba xuwan yana da amfani at least xaka samu wani experience din, kuma ai xaman haka baxai maka dadi ba inkuwa ka fita ka shiga cikin mutane sai kaji sauqin damuwa, Allah yace tashi in temakeka baxaka xauna a gida ba kace Allah xai axurtaka dole saika motsa kwanji ka nema, karka raina abunda kake samu wata rana sai lbr bayan wuya kuma sai dadi" ya qurawa sakeena ido cikin burgewa yana mamakin fusaharta kamar ba qaramar yarinya ba. yace "to Baby na yadda kikace haka xa ai bari na shirya in fita"
Ya tashi ya shirya suka fito maqale da juna, yan majalissar Mariya suka bisu da kallo har suka fice ta rakashi soro ta dawo suka Saki tsaki cikin tsabar hassada.
***** ***** ************
A cikin kwanaki 3 suka kuma wayar gari cikin babu, gashi jiya sunyi kwanan yunwa wanda hakan shiyasa Deni tashi ya nufi Gwale da safe dan ya karbo musu gasara gurin Hajjo. Sai wajen 9 ya isa gidan saboda a qafa yaje, ya tarar Hajjo ta gama sai da gasara. Ya shiga har daki ya sameta, ta kalleshi dake uwa ce nan take ta gane yana tare da yunwa, tun kafin yayi magana ta tashi taje ta kawo masa koko a jug me xafi da dumamen tuwo. Yaja abincin gabansa xaisa hannu Iya ta dago labulen dakin ta kallesu kana tace "Nura daka nan uwarka tasaka a gaba ta baka abinci xakaci ita marainiyar daka barota acan meka bata taci?" jikinsa yayi sanyi ya ajiye jug din da yayi niyyar kaiwa bakinsa ya kasa dagowa ya kalli Iya saboda kunya. Hajjo kuwa tsaki ta doka. Iya bata qara cewa komai ba tayi gaba.
Ya tashi jikinsa a sanyaye ya tsallake abincin ya fito waje yana nadamar abunda yayi, yasan da sakeena ce ta samu wani abun baxataci bata bashi ba. Hajjo na kwallah masa kira amma bai juya ba yayi soro. yana dab da fita Iya ta kirashi ya juyo kansa a qasa yace Iya kiyi haquri baxan qara hakan ba. tace "Nura ka kula kuma duk sanda kasami wani abun ka tuna cewa ka karbi amanar sakeena ne a gurin mahaifinka kuma kayi alqawarin xaka riqe, Sakeena tana sonka karkayi amfani da son datake maka ka wahalar da ita. sakeena bata juriyar yunwa ko kadan shiyaasa take aikin qarfi don samun abinda xataci, amma saboda soyayyarka ta jure yunwa to Dan Allah ka kula da ita, yarinya ce me xafin nema kayi haquri ka bata dama ta nemi sana a kodan ta temaki kanta baxata yuwu ku xauna haka ba kayi haquri ba shishshigi na maka ba amma wannan itace gaskiya" ta miqa masa food flask cike da dumamen tuwon shinkafa miyan xogale da jug din koko ta dora masa 200 tace "gashi kaje kuci da matarka" ya karba ya tsuguna ya qara bawa Iya haquri da godiya kana ya tafi.
Ya shiga mota ya koma gida, ya tarar da sakeena a kwance da gani yunwa ke damunta ya qara nadamar abunda yayi ya Kuma tausaya mata. Ya tasota suka sha kokon suka cinye tuwon duk yawansa, duk abunda yake cikin sanyi jiki. Ya bata ragowar canjin Iya yace ta sai abinci taci. Har ya fita ya dawo ya kamota ya rungumeta yace "ina sonki sakeena" ya juya ya fita tana mamakin wannan canjin da tagani.
Haka ya yini tunani a kasuwa, yana kuma nanata maganar Iya a xuciyarsa. tabbas tayi gaskiya in baibawa sakeena abinci ba ai bai kamata ya daureta ba maana ya hanata nema dole yasan abunyi.
Da azahar acan gida Iya taiwa gidan sakeena tsinke, murna a gurin sakeena kamar me, ta rasa inda xatasa Iya. Ta dauki naira 100 da Nura ya bata tasa Amir ya siyowa Iya alala a maqota. Iya binta take da kallo cikin tausayi sakeena dirarriyar mace amma duk ta xuge lallai suna cikin wani hali. Ta fito da abincin data taho dashi dama shiyasa bata fito da wuri ba saida taa gama girki ta debo musu. Tasa abincin a gaba sukaci sakeena ta debarwa Deni. Iya ta dunga fito mata da abubuwan amfani dataxo mata dashi harda yan kayan abinci ta siya mata da taliya yar awo. Sakeena ta dunga murna tana godiya. Iya ta mata nasiha tare da umartar ta da fara sana a don ragewa mijinta wahala. Sakeena ta kwantar da kai ta fadawa Iya duk yadda sukai da Deni akan aikin da umman Amir ta samo mata. Haka suka yini da Iya suna hirarsu har sakeena ta gama girkin dare, lokacin da Deni ya dawo. Iya ta kuma hadasu ta musu nasiha, shima ya fito da ledar daya shigo da ita ya ciro hijabi ya miqawa sakeena ta wareshi taga xungureren hijab ne har qasa na yadin toyobo me hannu.
Yace "gashinan sakeena, Iya ki shaida na yarje mata taje aikin girkin da umman Amir ta samo mata, amma ta kiyaye aurena dake kanta kuma ta kama kanta, inxata tafi tasaka wannan hijabin. Yau munyi baqi ne a kasuwa na samu kudi na siyo mata inna kuma samu xan sai mata wani ta hada. Gashinan na baki amanar kanki, ina qara jaddada miki ki kiyaye inada kishi sakeena Dan Allah ki kula da kanki. Kuma sai na fita xaki fita naki aikin Sannan kuma kafin na dawo ki tabbatar kin dawo." Iya farin ciki ya kamata ta dunga yimasa godiya ta kuma hadasu ta musu nasiha tai sallar magrib sukaci abinci sannan ta shiga dakin umman Amir ta fada mata Deni yabar sakeena aiki kuma ta mata godiya. Umman Amir ta tabbatarwa da Iya gobe xata raka sakeena gidan aikin. Deni da sakeena suka raka Iya har bakin titi ta tafi.
Wannan shine mafarin fara aikin sakeena gidan Alh Dalhatu inda take musu aikin girki rana da dare, tana xuwa qarfe goman safe in Deni ya fita ta dawo qarfe shidan yamma Karin ya dawo. Da alqawarin xa a dunga biyanta 5k duk wata.
Hajia☺
[7/31, 2:15 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣2⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Ranarta ta farko a gidan aiki ta kasance kamar ranar da kowane irin ma aikaci kan tsinci kansa a gurin aiki. Bata fita da wuri ba domin ranar Saturday ne sai da Deni yayi musu wankin kayansu tas ya shanya sannan ya fita itama suka fita da umman amir wacce xata rakata.
Gidan babu nisa sosai tsakaninsu dan haka a qafa suka isa, tun daga gate sakeena ta gane ba qaramin hamshaqin mai kudi bane me gidan. Da suka shiga ciki kam har xuwa falo sai ta tsinke da ganin irin kayan alatun da aka qawata gidan dasu. Ita ada can ta dauka gidan anty Bahijja shine aljannar duniya domin shine qarshen gida me kyau a tunaninta amma kuma data shigo nan sai taga ai ko boy quarters din gidan data hango ta kere gidan Bahijja a tsaruwa.
Suka tadda matar gidan a falo tana danna waya. Umman Amir ta gabatar da sakeena bayan sun gaisa ta kuma fada mata kamar yadda sukai a baya aikinta iya kacinsa rana da dare saboda tana da aure. Matar wadda taji suna kira Mama ta kalli sakeena a tausashe tace "diyata sakeena ina miki fatan akkhairi da fara aiki a qarqashina, xan daukeki ya kema ki kalleni matsayin uwa. Inada yara guda 3 Babban namiji ne sunansa Ahlan sai qannansa Hassana da Usaina yan biyu ne. Yawanci basa tashi breakfast sai 11 nasan lokacin kinxo saboda haka kowanne xai fada miki abunda yakeso ki masa, banason qazanta kuma banason lattin gama abinci saboda mijina kullum cikin baqi yake duk da bai cika xama a gari ba sai qarshen wata amma yana yawan samun baqi wanda suke xuwa domin duba wani abun ko kawo Ahlan kudin ciniki da sukai da Alh. Karkimun rashin gaskiya karki dau abunda ban baki ba duk qanqantarsa, inkikai hakan xakiji dadin xama dani ni kuma xanyi iya yina inga na kare mutuncinki baxan bari a wulaqantaki ba. Kin yarda?" Sakeena ta sunkwui da kai tace "in shaa Allahu Mama xan kiyaye baxaki kamani da lefin cin amana ba nayi alqawari" Mama ta washe baki jin sakeena ta anbaceta da mama tace "Barka da xuwa gidan Alh Dalhatu" ta kwallah kiran Habiba. Taxo ta durqusa tace "gani mama" ta nuna sakeena tace "ga yar uwa na samo muku, itane xatana girki yanxu saboda haka aje a nuna mata komai xata fara aiki yanxu a kuma samar mata da time table na girki a gwada mata yawan abincin da ake" Habiba ta amsa taja hannun sakeena suka tafi tabar umman amir suna hira da mama.
Sakeena sai da ta kuma tsinkewa ganin girman kitchen din da kuma injinan da aka shaqare kicin din dasu kamar baxa a mutu ba, Habiba ta dunga nuna mata komai dallah dallah, da alama itace me wanke wanke. Sakeena batai girman kaiba yawanci bata san amfanin injinan ba ta dunga tambayar Habiba yacce ake amfani dasu ita kuma tana nuna mata dake ta jima a gidan.
Ta fara aikin girkin rana a tsorace dan kartayi ba dai dai ba ko kuma tayi be dadi ba a koreta. Tana cikin aikin taji an danno qararrawa wacce qararta har tasa sakeena firgita. Habiba dake jera kayan data wanke tace "sakeena duk sanda kikaji andanna wannan to ana kiranki ne a falo" sakeena tace "to rakani falon dan na manta hanyar" ta rakata kamar yadda ta buqata. Ta tarar da mama da wasu yan mata biyu kamar daya sak a falon suna xaune kowacce ta harde dayar taci kwalliya dayar kuma tana sanye da kayan bacci, da alama sune yan biyun. Ta duqa gaban mama tace "gani mama" ta kalli sakeena da murmushi da alama tafiyarsu xata wiyu dan tanason girmamawa tace "kinyi breakfast ko? Da akwai ragowar breakfast a kicin din kici" sakeena tace "ai nayi a gida kan na fito" tace "to dama yan biyu ke kiranki xaki hada musu abinci" ta juya garesu tace "to ga sabuwar me girkin tamu" me sanye da kayan baccin ta kalli sakeena a sheqe tace "ke sandwich xakimun sai Lipton kiyi sauri" cikinta ya qulle meye kuma sandwich? Ita a makaranta batai Food nd nutrition ba economics tayi. Tace "ke! Xaman me kike kije kiyi abunda na saki da sauri xan tafi lectures ne" cikin sanyi tace "meye sandwich? wlh ban iya ba" dayar ta sheqe da dariya tace "in kinsan baki iya girki ba kam meya kawoki nan? Sandwich dinne baki iya ba? Common sandwich?" mama ta shiga maganar da cewa "Ke usaina banason iya shege, kuyi mata a hankali mana dama wani sain kuke koremun yan aiki da iskancinku". Ta dubi sakeena tace "jeki kicin Habiba ta nuna miki littafin girke girke akwai aciki ki duba yacce akeyi ki je gida ma dashi ki dunga dubawa" tace "to"
Ta koma kicin ta fadawa Habiba saqon mama ta dakko mata tullin littafan girke girke ta bata ta kuma dakko mata sandwich bread dake qaton fridge din kicin din. Da taimakon Habiba da kuma littafin girkin wanda suke da harshen turanci sakeena ta hada dan guntun turancinta ta yiwa Hassana sandwich din ta hada a tray ta nufi falo gurin Hassana ta durqusa har qasa tace "gashi Anty" kan Hassana ya fashe jin ankirata da Anty. Ta dubi usaina tace "kinji yanda ake girmama na gaba ko? Kinqi kirana anty yau Allah ya kawo me kirana da Anty har gida" Usaina tace da sakeena ke nima ki dunga cemun Anty dan tare mukaxo duniya da ita ko da secon 1 bata girmeni ba" mama tana jinsu tana dariya. Hassana ta dubi sakeena tace "kaimun bedroom dinmu yanxu xan shiga inyi brush" ta fada tana nunawa sakeena up stairs. Usaina tai sauri tace da Hassana "Da Allah malama ya xaki turata sama dakinmu? Ko kin mata abunda Hindu ta mana, tadaukemun xobe na na English gold ban taba sawa ba? Ta cije lebe ta qara da cewa Abba yace 280k ya saya mana amma ta dauke ta barni da takaici, ita wannan din kinsan halinta ne? To wlh duk abunda naga babu sai kin biyani" mama ta harareta tace "bansan cin fuska Usaina, sakeena hau ki ajiye mata" tahau jikinta a salube, daki dayane tal a saman wanda ke nuna sukadai ne a benen. Ta buda ta shiga, a gurguje ta ajiye ta fito tana jinjina wannan uban daki da uwar dukiya duk na yara biyu kacal? Tab.
Qarfe daya da rabi ta gama girkin rana ta lodoshi a wata kura da ake turawa ta silver ta kawo falo, Habiba ta koya mata yadda ake shirya dinning, yadda ake ajiyewa kowa farantinsa a saitinss da cup. Mama taxo ta yaba kwarai da girkin bayan taci tace "da kyau sakeena diyata ashe expert ce akan girki duk da baki da shekaru" wannan yabo na mama yadan bawa sakeena kwarin gwuiwa. Ta koma kicin ta dora girkin dare duk da kwabarta da Habiba keyi na cewa ta bari sai anjima lokacin dora girki beba taxo suje dakinsu suyi kallo. Tace "barni inyi ingama Habiba inkoma gida da wuri" ta maida girkin dare, tana ta aikinta cikin gwarewa da hijabinta xurmeme. Wajen qarfe biyar mama ta shigo kicin din tace "sakeena me ake dafa manane gidan ya cika da qamshi haka." tayi dan murmushi tana wanke kifin data ciro a freezer a sink tace "Fatan erish potato ne da fresh fish nayi, sai jellof din cous cous sai kifi da xan gasa yanxu" mama ta bude food warmers din tace "um yummy" sukai dariya a tare da sakeena tace "kamar kuwa kinsan bamason tafarnuwa da yawa yar kadan ake sakawa. Yanxu dai kiyi haquri xan qara miki aiki duk da kin kusa gamawa, dan Allah zobo drink xakiwa Ahlan bayasahan lemon kwali. Kuma in akwai abunda kike buqata na girki saiki rubuta a qaro" sakeena tace "to bakomi mama yanxu xan hada zobon"
Ta dafa xobonta da pineapple da kuma cocumba tasa danyar citta ya dahu ta narka sugar ta xuba. wanda hakan shiya xama aikinta na qarshe, ta hada komai takai dinning ta shirya kamar daxu, lokacin 5:30 a gurguje ta gyara kicin din ta maida kayan datai amfani dasu, na wanke wanke ta waresu Allah Allah take ta tafi gida kar Deni ya rigata dawowa.
Mama ta sakko bayan ta gama kallon sakeena ta CCTV camera din dake dakinta wacce ita da yayanta kawai sukasan da ita a gidan. Ta yaba kwarai da tsaftar sakeena da salon aikinta yau daya kawai.
Sakko warta tai dai dai da shigowar sakeena falon ta tsuguna tace "mama na gama inbabu abunda xa ai xan tafi" Mama tace "To sakeena sannu da aiki amma beyasa bakici abinci ba daga na rana harna dare, ke banaji ko ruwan gidannnan kinsha" sakeena tai shiru tana tunani, ita wlh tama manta da abinci dan tunda taci tuwo a gida rabonta da kai wani abu bakinta kuma batajin yunwa kodan ta saba yini da yunwar ne ko kuma dan aiki yasha kanta?
Tadan motsa tace "naci abinci mama, ina gamawa na xuba naci" tayi dariya tace "banason qarya sakeena wlh ko ruwa bakisha ba" tai xukudi tana mamakin ya akai mama tasan bataci komai ba? Ta kwantar da kai tace "yanxu innaje gida xanyi mana girki shiyasa nake sauri in koma"
Mama tace "kinga inkinaso mu shirya dake in kinyi abincin rana ki dunga ci, na dare kuma ki dunga diba kina tafiya dashi gida in kinje kwaci da mijinki kin huta girki, inba baki da raayin cin abunda kika dafa xaki iya dafa duk abunda kikeso. Qin cin abunda kika dafa kan iya janyo miki xargin kin xuba wani abun aciki saboda haka cin abincin wajibine a gareki" sakeena ta bude baki cikin tsoron jin intaqi cin abincin xa ace tasa wani abun. Mama tace maxa dakko warmer a kicin ki dibi abinci ki tafi kar mijinki ya dawo ya taddaki kina qaurin girki baki wanka ba.
Taje ta dakko tana dariyar jin abunda mama tace. "maxa xuba duk abunda kikeso" ta fara diban abincin kamar na wasan yara.
Mama ta taso taxo gurin ta karbi cokalin hannunta ta fara xuba mata abincin tana cewa "kawo in diba miki, haka kawai yarinya xaki janyomin Allah ya isan Abba tahau kaina. Shidin yasha fadamun cewa in akabar koda mutum daya dake qarqashinsa da yunwa be yafe ba, saboda shima da dan aikin gida ya soma rayuwa kafin yayi nasa arxiqin dan haka be yarda a wulaqanta me aiki a qarqashinsa yana cewa mutum daraja gareshi bakasan wazai xama ba a future. Sannan banda abinki sakeena mu 4 ya xamuyi da wannan abincin daga ni sai Ahlan sai yan biyu Alh baya gari su kuma masu aiki suna nasu girkin a kicin dinsu daban. Saboda haka ki dunga sakin jiki kina diban abinci yadda zai isheku dan inba baki diba bayarwa xa ai indai mun gama ci, ni banason kwauro da dan hannu ki kiyaye kinji diyata" ta qarasa maganar tana miqawa sakeena warmer din data shaqe taf da kalolin abinci. Sakeena ta karba tana godiya ta juya ta tafi tana jinjina karammaci irin na mama kamar ba matar me kudi ba.
Cikin sauri take tafiya burinta ta isa gida kafin Deni ya dawo. tai farin ciki data isa be dawo ba, Mariya na xaune da daurin qirji tana girki a kofar daki, tabi qayattaccen flask din hannun sakeena da kallo.
Da sauri ta jona ruwan wanka, dakin fes yake baya buqatar gyara dan ta gyara kanta fita. ta dakko flask din ta shiga dakin umman Amir ta nuna mata abincin tare da yimata bayanin duk yadda ta kaya yau a gidan. umman Amir tayi dariyar farin ciki tace "ai dama na fada miki indai kika riqe gaskiya xakiji dadin xama dasu. Suna da mutunci" sakeena tace "tabbas naga hakan" ta xubawa umman Amir abincin duk kuwa da tana kwabarta ta barshi amma bata fasaba sai data xuba mata.
Har tai wanka tayi kwalliya ta shinfida musu tabarmar cin abinci ta shirya kwanikan Deni be dawo ba. sai da ta fito tana kwashe kayan shanyar da yayi musu da safe saiga sallamarsa, suka kalli juna cikin farin ciki yayi murnar ganin tabi umarninsa ta dawo kafin ya dawo.
Ta cire ruwan data jona masa takai masa yayi wanka, a gida yayi sallar magrib saboda an idar a masallaci kuma yana idarwa ya xauna gurin cin abinci alama yunwa yakeji. Itama taxo ta xauna, shiya bude flask din yayi dum ganin abunda yake ciki ya dubeta ya qara duban abincin wanda qamshinsa ya cika dakin daga budeshi sai a lokacin ya kula da food warmer din bata sakeena bace. Ya qura mata ido, ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
Ya fara magana cikin bacin rai "Sakeena wannan abincin da kwanon daga ina" Cikin sanyin jiki tace "kaso nane na gidan aiki na taho dashi muci tare" ya daka mata tsawa da cewa "ke! rufemun baki" taja bakinta ta tsuke ta fasa yimasa bayanin da yasa ta taho da abincin.
Ya fara fada kamar xai daketa "dan kin rainamun hankali kuma na barki aiki shine xaki tahomun da abinci? Wato ga talaka dan iska wanda bazai iya daukar nauyinki ba ko? Shiyasa kika yanke shawarar fara kawomun abincin gidan masu kudi daga haka kuma saiki rainani ki daina yimun biyayya ko kifi qarfina tunda kina ciyar dani wlh baki isaba sakeena, nace baki isa ki maidani sakarai ba" ta fashe da kuka jin yadda yake magana da daga murya wanda ta tabbata ana jiyosu a tsakar gida, amma ga mamakinta kukanta bai hana Deni hargagin masifar da yake ba. Da sauri ta nufeshi ta rungumeshi ta qara sautin kukanta, sai a lokacin yayi shiru. Tana cigaba da kukanta tace "ya Deni ka tsaya ka saurareni kaji yadda akai, wlh ina sonka baxan tabayin abunda kake fada ba koya kake ina sonka kuma xan maka biyayya Dan Allah ka saurare ni" Ya qara matseta jikinsa tsam yana shafar bayanta yace "to yi haquri yimun bayani kinji, ina sonki sakeena ina tsoron kar idonki ya bude da rayuwar gidan masu kudi da cima me dadi ki gujeni" tace "ya Deni soyayyar gaskiya bata qarewa, baxan taba iya gudunka ba kamar yadda nasan baxan daina sonka ba" yayi murmushin jin dadi, tana jikinsa ta fada masa duk yadda akai.
Ya fahimceta kuma ya yadda dan bai taba samunta da yimasa qarya ba, ya sauketa sukaci abincin tare yanata santi da mamakin wai sakeena ce tai wannan girkin, ita dai yaqe kawai take, sam bataji dadin abunda ya faru ba tsakaninsu yanxu. Abincin ma tsakura kawai tayi.
Bayan sallar isha suna falo yana gugar kayansu daya wanke ita kuma tana duba littafan girkin da Mama ta bata daxu, tanayi tana hamma bacci takeji dan yau batai baccin data saba yiba na safe.
Ya gama gugar yaxo ya tada ita daga baccin data fara yace "sakeena xo muga wani film dana samo mana" tace "to" suka shiga uwar daki sukai shirin bacci ya kunna musu film din "KI&KA" na kareena kapor da arjun kapor suka fara kalla, itakam basuyi nisa ba tayi masa sai da safe ta kwanta. Shima ya kashe wayar ya kwanta a bayanta yace cikin rada "sakeena har yanxu fushin kikeyi dani?" tace "a a just inajin bacci ne" ya matseta sosai yace "ni kuma da sonake kimun irin kiss din da muka gani yanxu a film" tayi dan murmushi tace "kayi haquri sai gobe" bai qara cewa komai ba ya haye jikinta dan yau baijin xai iya haqura, batare da wani hadin kan sakeena ba ya samu biyan buqata.
Washegari ta isa da wuri da Deni suka fita tare sai da yaga shigarta gidan sannan ya tafi kasuwa bayan ya qara bata haquri dan ya lura tun jiya bata ware ba.
Dake Sunday ce duk yaran suna gida, ta shiga falo domin gaida mama da kuma jin abunda xa a dafawa su Hassana na breakfast. Ta rar da mama da wani saurayi yanata game a system yana ta ihu da tabara kamar yaro qarami abun babu ko tsari. Saurayin da xaiyi saan mijinta koma ya girmeshi wai shine ke wannan ihun dan kawai yanayin game 😏 Allah sarki ajebo.
Ta gaida mama yayin da ihun saurayin ya hana taji abunda mama ke fada. Mama ta dubeshi tace "Ahlan kaxo ka cikamun falo da ihu ka hana inji kunne, tashi ta tafi sashinka ina dalili xakaxo har gurina ka takuramun?" ya juyo yace "Haba Mom cinyeni fa akai, memakon kimun jaje." ya juyo sai a lokacin ya lura da sakeena, ya qura mata ido kana ya Kalli mama yayi mata alamar wacece da hannu? Mama ta bashi amsa da cewa "sabuwar me girkinmu ce saika fada mata abunda xatai maka na karyawa" ya juya ya qara kafawa sakeena ido yace "Duk abunda hannunki ya dafa xanci, amma anya ke a shekarunki har kin wani iya girki?" Batace komai ba sai tashi datai ta tafi domin sai takega inta tsaya bashi amsa kamar tozarta aurenta ne.
Taje kicin ta samar masa da abun breakfast ta dama masa oat ta kai masa falo kan dinning lokacin ta tarar su Hassana ma sun sakko, tana ajiyewa ya tashi ya haye table din tare da cewa "kewai bakijin xafi ne kike yawo da wannan xurmemen jalbab din? Muda muke falo cikin AC ma munajin xafi bareke a kicin gashi kin yaba wannan abun." wannan Karon ma batace komai ba ta nufi hanyar sauka daga dinning area din. Yayi caraf ya riqo hannunta yace "ke! Wanene ke ina miki magana kinmun shiru? Ki tsaya kiyi serving dina" ta fara kici kicin kwace hannunta ya kuma riqeta gam, su Hassana da suka hau dinning din yanxu suka fara dariya. Mama tanacan kan kujera tana danna waya ta hangesu ya riqe sakeena tana yunqurin kwacewa.
Tace "kai Ahlan, cikata karka qara riqeta matar aure ce, banason wannan dabia taka ta turawa" a tare Ahlan dasu Hassana suka maimaita kalmar "matar aure???" suka jiyo suna kallon mama dan tabbatar da abunda ta fada, ta qara tabbatar musu tace "wlh matar aure ce, a gidan su umman Amir suke haya da mijinta" Ahlan ya saki baki yana qarewa sakeena kallo kafin ya maida kallonsa ga mama yace "wai dama har yanxu qasar nan ba a daina Child Abuse ba? Wannan yarinyar ina ta isa aure inba xalunci ba, aiko su Hassana basu isa aure ba bare wannan yarinyar da na tabbata batafi 15yrs ba"
Sakeena dai tunda ta samu ya saketa ta gudu dan haka bataji qarshen film dinba.
A ranar haka tai aikinta a kicin yayin da Ahlan ya yini a falo duk sanda ta shigo saiya bita da kallon qurullah duk kuwa da uban hijabin dake jikinta.
***** **** **** ***** ****
A kwanaki 7 da sakeena tayi tana aiki a gidan ta fuskanci mutan gidan Kam basu da matsala tun daga kan mama har yayanta. Matsalarta daya Ahlan wanda duk da anfada masa tana da aure be fasa yimata kallon qurullah ko janta da hira inta shigo falon yin wani abun. Wannan dalili yasa bata shiga falo indai yananan kuma tana qoqarin gama aikinta kafin qarfe shida ta tafi gida kafin ya dawo office. Ita dasu Hassana babu matsala dan tasamu karbuwa gurinsu a dalilin girmamasu da take. Sau tari insuna musun kayan da xasu saka ita ke bin bayan Hassana mama kuma ta bi bayan Usaina aita muhawarar kayan da xa a saka kafin daga baya sakeena ta sasantasu cikin hikima.
A wannan kwanaki datai tana aiki a gidan yasa daga ita har Deni sun dawo hayyacinsu ma'ana sun daina kwanan yunwa sunyi kyan gani kullum xataxo musu da abinci isashshe suci har su rage, inxai kwana su ajiye inbaxai kwana ba su bayar. Abunda Deni ke samu a kasuwa kuwa sun barshi a breakfast, in aljihunsa da nauyi suyi tare inbabu nauyi kuma ya siyo abunda xaici shikadai ita intaje gidan aiki saita karya.
A ranar kwana na 8 Iya taxo musu da magriba. Ta kallesu sunyi kyan gani akan kwanakin baya tace "kai wannan mutane Allah ya saka musu da alkhairi har kunyi kyan gani. Nima yanxu hankali ya kwanta kullum ina cikin tunanin kun kwana da yunwa, dama xuwa nayi inganku ai kuwa nayi farin xuwa naji dadin ganin canji" qarshe dai da Iya suka hadu sukaci abincin da sakeena taxo dashi a kwano daya. Deni ya qara girmama Iya a xuciyarsa tunda har ta damu da halin da suke ciki shida sakeena, sabanin tasa uwar da yan uwansa da basa nemansa saboda bashi da shi kuma basasan matarsa. Suka raka Iya har titi tahau napep ta tafi.
Ita da Deni kam basu da matsala gishiri kan kaxa suna xaman lfy da soyayyarsu mai shiga rai. Inta dawo tana bitar littattafan girkin da aka bata, turancin da bata gane ba ta nunawa Deni ya fassara mata.
Tana tsaye a kicin tana aikin abincin rana, yayin da Ahlan ke tsaye yana kallonta ta tagar kicin din ta waje jikin net. Kallonta yake kamar yadda ya saba a kwanakin weekend inyana gida, ya furta "Gold a kwata" ma'ana kyakykyawar mace a gidan talauci. Sakeena ta juyo a firgice jin muryarsa da kuma abunda yace ta qara gyara hijabin jikinta tace "kana buqatar wani abune in miqo maka?" yace "no pretty kawai ke naxo kallo" ta qara daure fuska tacigaba da aikinta, wannan hali na Ahlan yana mutaqar bata tsoro duk da anfada masa tana da aure amma bai fasa kallon ta ba kamar ba musulmi ba ko kuma kamar besan abunda kalmar aure take nufi ba. Kuma tasan ko giyar wake tasha baxata iya fadawa Deni wannan batunba, saboda tanason aikinta kuma fadawa Deni yana dai dai da Third World War (yaqin duniya na uku) Ahlan yakai 18 minutes yana kallonta kafin ya juya ya tafi, ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah kasan temakon da aikin nan ke mana ni da mijina kamar yadda kasan abunda bawannan naka yake nufi dani, Allah ka shiga tsakanimu."
Ranar laraba da wuri ta gama girkin rana wajen 11 saboda Habiba tace xatai mata qunshi da kitso ta iya. Tana gamawa suka tafi can dakinsu Habiba aka fara saka mata lallen a qafa da hannu wanda Habiba tace 2 hrs yakeyi nan da 1:30 xa a cire. Inna wata dattijuwa dake dakin itama tana aiki ne a gidan sai yaba kyan qunshin take, sakeena kuwa bakinta yaqi rufuwa yau xata burge Deni rabonta da qunshi tun na bikinsu. Ana gama qunshin aka fara kitso duk da Habiba tana cewa bata iya sosai ba amma dai yayi kyau sosai akan sakeena dake bashi da cika. Daya da rabi tanayi aka cire qunshin dan sakeena ta damu acire xatai sallah.
Masha Allah qunshin yayi jajur a farar qafarta, tana idar da sallah ta nufi kicin ta dora abincin dare taje falo dan debo abincin da xataci, Hassana ta kalleta tace "Wow sakeena gaskiya qunshin nan yayi kyau" tana murmushi tace "nagode anty Hassana" suka gama xuxuta kyan qunshin ta koma kicin tana aikin girki cikin sauri tanacin abinci. Burinta ta gama kafin dawowar Ahlan. Wajen qarfe 3 ta xaga bayan gidan inda su Habiba ke taruwa suyi hira inbasu da aiki. Ta xauna babu kowa a gurin sai Habiba dake wanke wanke, ta zauna suka fara hira Habiba na bata labarin qaunyensu tana dariya, har Habiba ta gama wanke wanke ta tashi domin kai kwanikan kicin tabar sakeena ita kadai tana jiran dawowar Habiban.
Yana ganin Habiba ta kauce ya qaraso gurin, yau beje aiki ba yatashi bayajin dadi, kuma tun safe yake san ganin sakeena ya tambayi mama tace ta gama aikinta tana can tana hutawa.
Ya tsaya a gabanta yayin da kanta ke duqe tana qara kallon qunshin qafarta, yayi gyaran murya ta dago a firgice xata gudu yace "wlh inkika tafi saina yimiki abunda xaki gwammace kin tsaya gara kawai ki tsaya ki saurareni. Ta dawo ta xauna tana neman hirji gurin Allah, ya fara kewayeta tana xaune kanta a qasa yace "hmm kedai kinji dadi komai naki me kyau da shiga rai, amma kin tafka kuskure da kika bata rayuwarki ta hanyar aure, aurenma na talaka. Meyasa xakiyi aure yanxu pretty? Meyasa baki bari sai kin girma ba ki auri right person? Wannan mijin naki mugu ne ba sanki yake ba kawai yayi amfani da talaucinki ne ya aureki kuma dake shege ne mugu har ya turoki neman masa kudi ko? Kinga da nine nayi nasarar aurenki kota yaya xan nema miki jin dadin rayuwa baxan taba bari ki wahala ba" sakeena ta tashi ta katseshi domin jin ya taba abunda tafi qauna Deni, tace "karka kuma wulaqantani ta hanyar xagarmin miji, bakasan komai akan rayuwarmu ba saboda haka babu ruwanka, ina sonsa fiye da komai a rayuwata" ta juya tayi hanyar kicin, Ahlan yace cikin sanyin murya "ikon Allah komai naki me kyau masifar ma kyau take miki, qunshinki yayi kyau sosai ki dunga yimun inaso"
Fadin irin farincikin da Deni yayi da ganin wannan qunshi bata bakine yayi murna kwarai. Ya sumbaci hannunta da tafin qafarta yafi sau shurin masaqi yanayi yana cewa "sakeena Allah yayimun arziqi in maidake yar hutu ki xama baki da aiki sai dai kiyimun kwalliya ki kame a falo kina latsa remote." tana dariya ta qura masa ido tana tunanin maganar da Ahlan ya fada mata daxu akan Deni, a xuciyarta tace "Ahlan besan soyayyar da Deni keyimun ba da bai fadi haka ba" Deni yaja mata hanci yace "tunanin me kike Baby?" ta dawo hayyacinta take riqo fuskarsa tace "ya Deni kaimun alqawari .." tun kafin ta qarasa ya tareta da fadin "nayi miki kowane irin alqawari ne sakeena wlh nayi, ina sonki" tayi dariya ta sumbaceshi tace "to tunda kayi alqawarin bari na fada maka abunda nakeso. Dan Allah ina neman alfarma Duk randa Allah yayi maka arxiqi abu na farko da nakeso kaimun shine ka samamun lafiyar ido, na biyu kuma Dan Allah ka maidani makaranta in cika burina. Ya Deni kamun alqawari?" ya mannata a jikinsa yace "nayi sakeenatu ki rubuta ki ajiye duk randa Allah ya horemun aikin idonki shine farkon abunda xan fara aiwatarwa." a wannan dare haka suka raba dare suna hirar yadda rayuwarsu xata kasance in Deni yayi arxiqi.
Washegari ma dai a gidan aiki sakeena ta kuma fuskantar takura daga Ahlan, duk da cewa kafin ta tafi sai data saka baqar safa a qafarta ta rufe qunshin saboda a tunaninta qunshin ne yaja mata iskancin Ahlan jiya.
Ta tsinceshi akanta lokacin da take shirya table, gashi babu kowa a falon. ya kalleta tun daga sama har qasa yayi murmushi yace "Wannan gayen mugun dan iskane, wato saboda yasan shi ba a ajinki bane shiyasa bayan ya zalunceki ya aureki ya kuma tilasa miki saka bukka ko?" Ya fada yana nuna hijab din jikinta, ya kuma dariya yace "sai dai yayi kuskure kuma ya makara domin abu me kyau fa me kyau ne komai kwaskwarimar da xa ai masa baxa a maidashi mummuna ba, inkinje kice masa Ahlan Dalhatu yace ya yaba kwarai da muguntarsa kuma bashi kadai yake da wankin idon ganin mace me kyauba da kuma tarin ni'imomi" ya juya ya fita yabar sakeena da qirji a dafe.
Wannan ita kadaice matsalar sakeena, domin ko Mariya yanxu basu cika haduwa ba tunda bata yini a gidan. kuma saita gwammace takurar Mariya sau dubu akan wacce Ahlan ke mata yanxu.
Bata qara tabbatarwa mutan gidan sunada kirki ba saida qarshen wata tayi, ranar ta kasance asabar kuma tayi dai dai da cikar sakeena 15 dayx da fara aiki a gidan. Tana xuwa taga manyan motoci sun cika harabar gidan ta aza baqi akai. Saida ta shiga ciki Habiba ke fada mata Abba ne ya dawo wato Alh Dalhatu, koda taje falo babu kowa matar da yayan duk suna part dinsa.
Tabi shawarar Habiba ta gama girki da wuri domin ta fada mata inyananan qarfe 1 suke lunch da family dinsa. Tayi abinci na alfarma ta qure basirarta, kafin qarfe daya ta shirya table ta kuma gyara falon ta saka turaren wuta wanda ya dace da qamshin girkin tayi sallah ta kwanta a dakin su Habiba.
Can wajen qarfe biyu taji Habiba na tashinta, ta tashi a fuirgice tana tambayar lokacin girkin dare ya qure ko? Habiba tai dariya tace "a a kixo Alh ne yace a kirawo kowa xa a biya albashi" a ranta tace ni kam yaushe naxo ai babu ni aciki amma dai ta tashi tabi Habiban xuwa falon mama.
Ta tarar falon cike da ma aikatan gidan yayin da Alh da yayansa duk da mama suke kan kujeru, ta nemi gefe kusa da Habiba ta rabe. Ahlan ya fara kallonta kamar yadda ya saba.
Bayan dan jawabi da nasihar ruqe gaskiya da kuma godiya, Alh ya bawa kowa albashinsa yadda ya saba tare da umartar sarkin gida da abawa kowa kayan abinci dai dai da buqatarsa wato na maxa yafi na mata yawa tunda su akwai nauyin iyali akansu.
Sakeena jin angama jawabi kowa ya tashi itama ta tashi don dama batasa ran da ita a salary ba tunda bata cika ko 20dayx ba. Mama ta tsaida ita, ta dawo ta xauna tace "Alh itace sabuwar me girkin da nake fada maka" yace "to Masha Allah," yace "nawa kukai xaki dunga bata?" mama ta amsa da "5k sai dai in cikin alfarmarka kaga xaka qara mata tunda matar aure ce"ta fada tana dariya. Shima dariyar yayi yace "to shikenan abata kayan abinci itama kamar na magidanci abunda xai kawo matar aure aikatau ai babban abune" ya irga 5k ya bata, tasa hannu biyu ta karba tana godiya. Tsakin Ahlan ya katse mata godiyar, shi dai jin ankira sakeena da matar aure ne ya sashi tsaki dan yatsani jin hakan, sannan ga daya abun haushin godiyar da sakeena keta xabgawa dan kawai anbata 5k da kayan abinci. suka kalleshi a tare dan jin dalilin tsakinsa, ya kuma doka wani tsakin ya xarowa sakeena qananan idonsa yace "ke da Allah kin ishemu da godiya sai kace maroqiya dan kawai anvaki 5k" sannan ya juya ga mama yace "nd plz mom ki daina anbaton wannan mummunar sentence din na cewar "matar aure ce" dis is totally Child abuse yarinyar da bata wuce a kama hannunta a rakata skull ba itane akewa kirarin aure? Dan Allah banason ji mom" Duk suka bishi da kallon mamaki.
Alh ya katse musu mamakin ta hannyar yi masa daquwa yace "Dan uwaka lokacin dana auri taka uwar shekarunta 14 nima kenan child abuse din nayi?" bece komai ba sai tashi da yayi ya fita suka bishi da kallo. Alh ya dawo da kallonsa kan sakeena yace "rabu dashi kinji bature ne, a qasar daya tashi ba a aure haka shiyasa yake fadin haka. Kin iya dashishin alkama?" cikin kunya tace "eh Abba na iya" yace "yawwa diyata shi nakeso kiyimun a dinner da miyar taushe asaka gyada da tantakwashi sosai" tace "to" mama da su Hassana kuma suka dariyar jin abunda yace.
Dake tasamu tsakin alkama dan kanti a store shiyasa aikin ya mata sauri, tanayi tana farin cikin abunda Abba ya bata lallai sun san darajar dan Adam ita bata xaci a masu kudi akwai irin Abba da mama ba, tana aiki cikin sauri da nishadi tana sambatun kirkinsu. Habiba tana mata dariya tace "sakeena ai kirkin Abba ya wuce nan Allah ya kaimu sallah kiga yadda yakewa masu aiki a qarqashinsa kuma dama ya saba raba mana kayan abinci kuma duk da yasan wasu siyarwa suke be fasa ba, ai babu makawa Abba da mama yan aljannah ne don sun samu shedar duniya indai ka riqe gaskiya xakaci ribar xama dasu" sunata hira da Habiba tana tayata aiki acewarta koya take, 4:30 ta kammala abincin harda kunun aya wanda yasa kayan qamshi da dabino da kwakwa babu flavour ko daya. Wata yar aiki ta shigo ta fada mata saqon Hassana wai ta hada mata salad ta kai mata up stairs.
Suka gama aikin duk Habiba ta shirya mata table ita kuma ta hada salad din Hassana ta nufi sama kai mata, da nufin tana sakkowa sai gida.
Ta samesu kwance a kan gado suna kallo a system. Hassana tace "yawwa sakeena sannu nagode" ta karba sakeena tai hanyar fita, Hassana ta katseta tanakai salad din data debo bakinta tace "saurin meye kike haka sakeena kamar xakici da baka?" Sakeena tana murmushi tace "inasone in koma gida inyi wanka kan mijina ya dawo" Usaina miskila sai lokacin ta kalleta tace "wai da gaske kina da aure?" Hassana ta galla mata harara tace "mama xatai mana qaryane?" tace "no, just naji bata taba fada da bakinta bane tana da aure" Hassana ta kalli sakeena tace "to kiyi wankan anan mana sai miki make up wlh na iya ban dade da gama makarantar kwalliya ba" sakeena ta danyi yaqe, tace "Anty Hassana gara in tafi gida banxo da komai na wanka ba da kuma kaya" Hassana ta kamo hannunta tace "ke inada komi sabo sai invaki, plz ki yarda kinji kar Usaina taje ta fadawa mama suyi mana dariya" sakeena tai dariya, itadai a son ranta tafiso taje gida amma baxata iya gwale Hassana ba ina lefin me sonka? Tace to.
Hassana ta miqo mata towel ta cire kaya a kunyace ta daura, tace "Wow sakeena haka kike da sturucture? Shiyasa kike saka hijab? Koda yake gara da kike sakawa dan in ana ganin irinku maxa baxasu Kalli irinmu ba" sakeena tai dariya ta shiga bathroom din. Hassana ta bita ta cika mata baho da ruwan kumfa wanda yasha wasu liquid soap sai qamshi yake, ta matsa mata toothpaste a sabon brush ta fita ta barta.
Sakeena tai wanka cikin wani irin yanayi na mamakin masu kudi komai nasu daban. taji jikinta kamar leda saboda santsi, ta wanke bakinta qal ta fito. Hassana ta qara qarfin AC din dakin tace xo mufara kwalliyar sakeena tace "ai ban shafa mai ba" Hassana ta riqo kafadarta ta xaunarta gefen gado ta fara goge mata fuska ta wani abu tace "ai a cikin sabulan da kikai wanka dasu akwai me sinadarin man shafawa ciki wanda inkinyi wanka dashi baki buqatar shafa mai duba jikinki xakiga kina maiqo. Ta duba ta tarar kamar yadda Hassana ta fada.
Cikin qanqanin lokaci saiga sakeena tayi tar cikin simple makeup, Hassana tace "Wow dubi Usaina" tace kai sakeena kina da sansanyan kyau. Bayan gama kwalliyar ta tashi ta cirowa sakeena wata yar qaramar top da wando pencil tace "saka wannan muga" tana shirin maida undis dinta Usaina tace "no bari abaki sabbi" ta tashi ta ciro mata bra da pant ta bata ta karba ta saka ta saka kayan da Hassana ta bata. suka kalli juna a tare suka furta "hot Baby" Hassana tace "ashe kayanmu xasuyi miki? Ai bansani ba muka hada aka bayar, amma akwai wasu dana kuma warewa an bata manasu a wanki." ta dunga ciro kaya tana lodasu a qatuwar ledar store ta hada kaf da wanda sakeena ta cire tace "to gashi kije kita yiwa megida kwalliya in mun kuma hadawa xamu baki" ta dakko turare ta fara fesawa sakeena ta lumshe ido tana shaqar qamshin. Hassana tace "ya miki dadi ne?" sakeena tai murmushi kawai. Ta ajiye mata kwallabar tace "gashinan dauki. Usaina tace "ki bata ragowar tunda Abba ya dawo ai xamuje shopping din qarshen wata." ta miqe tana cewa "hakane fa ni nama manta" ta dunga jidowa sakeena ragowar turare da mai harda sabulai da toothpaste. Sukai mata leda guda.
Ta tsuguna har qasa tana godiya kamar xatai kuka su abunma dariya ya basu. Hassana tace "bakomi aike qanwarmu ne ba Anty ne kinace mana ba? to kuma tunda mu aunties dinki ne ai babu godiya."
Mama ta murda dakin ta shigo, ta Kalli sakeena ta waro ido tace "Masha Allah haka kike sakeena? Yau yan biyu na sun fito dake" sukai dariya, ta nunawa mama kayan da suka bata, mama tace "to angode yan biyu ina taya diyata godiya, Allah yayi albarka. Nima ina da wasu yan kaya nawa xan baki ki kaiwa mamanki" ta qara yin godiya ta xura qatan hijabinta suka fito. Mama ta kuma bata nata kayan suma leda guda. Ta hada kaya da yawa ga kayan abincin da Baba ya bayar abata, mama tace a kirawo yara a waje su rakata gida da kayan. Ita dai Allah Allah take ta tafi karsu hadu da Ahlan ko yaya Deni ya rigata dawowa.
Burinta ya cika har aka samo yaran suka debi kayan Ahlan be fito ba kuma harta koma gida Deni be dawo ba.
Ta cire Hijabinta ta jona masa ruwan wanka ta xauna tasa kayan a gaba tana kallo, wato dai duk mai kudin da kaga yana wulaqanci taka haye yayi ba dan nagada bane? Yau kam Alh Dalhatu da iyalansa sun nuna mata hakan. Ta qara kallon kayan abincin, buhun shinkafa babba, kwalin taliya, macaroni, cous cous da indomie.
Harta idar da sallar magrib be shigo ba ta cire ruwan wankansa daya tasafa. Tace a fili "ya Deni yau lfy kuwa?" tana maganarsa sai gashi ya shigo. Wani irin baqon qamshi yayi masa maraba. Ya dubeta ya Kuma waro ido dan tabbatarwa itace. Tayi murmushi, baice komai ba ya dauki ruwansa ya nufi wanka.
A gurguje yayi wankan ya shirya yaxo gabanta ya qura mata ido yace Sakeena natace ko kuma watane daban?" ta hure masa ido sukai dariya tare. Ta miqe ta dakko musu abinci, ya bita da kallo bai taba ganinta cikin qananan kaya ba sai yau, lallai Allah yayi halitta a jikin sakeena. Ta ajiye abincin, ya kau da abincin yace "ba wannnan ba bani lbr wannan canjin da kika samu? Ta nuna masa kayan dake jibge a falon wanda be gansu ba sai lokacin. Ta fada masa duk yadda akai ta kuma dora masa 5k din a hannunsa tace ga albashin. Ya kalleta cikin tausayinta da girmama soyayyar da take masa tabbas Iya ta fadi gaskiya sakeena tana sonsa over.
Ya katse tunaninsa yace "sakeena da kudi da kayan duk nakine kiyi yadda kikaga dama dasu" ta shige jikinsa ta kwantar da kanta a haqarqarinsa tace "ya Deni ni da abunda na mallaka da kuma abunda xan mallaka anan gaba duk nakane indai har kana qaunata kayi duk yadda kaso dasu" ya qara kwantarta sosai yana shafa kanta yace "ina qaunarki sakeena xanyi duk yadda ya dace amma fa sai kin taayani" tace "to" yace "kudin a siyo kero a ajiye galan daya, mu siyi toothpaste da turare tunda duk bamu dasu, a sayi sugar saboda breakfast sai ki riqe ragowar. Yana murmushi ya qarasa cewa na raba kudi saiki raba kayan abincin" tace "to, muna da turare da toothpaste sai dai kaika siyo turaren da kake sakawa na maxa. A raba kayan biyu komai mukaiwa Baba rabi shima a rage masa nauyi, a cikin namu kuma xan dibarwa umman Amir, nasan ragowar xasu kaimu qarshen wata tunda bamu cika cin abinci ba saina safe" ya qura mata ido yana qimarta ta qaru sosai a gurinsa tunda har tasan taiwa Babansa hidima" ta tabashi tace "hakan yayi?" yace "ni na isa ince beyi ba sakeetun Baba?" sukai dariya lokaci daya.
Ta miqe ta raba kayan yana tayata, suka raba komai, ta fita ta kaiwa umman Amir nata. Ta dawo tana nuna masa kayan dasu Hassana suka hada mata, ya dunga yaba kayan yana sakawa tana gwadawa tana tafiya a gabansa, kasancewar ta danfi su Hassana qiba kayan sukai mata tsam. Daga masallacin isha ya wuce ya siyo duk abunda suka lissafa, ya dawo da kaya tace "ya Deni memakon kaxo muje tare" yace sakeena kinyi irin wannan kwalliyar kike xaton xan fita dake? kishin nawa na kaishi ina? kedai Allah yaban kudi in maidake irin matar da nake mafarkin mallaka" da sauri tace "au yanxu ni ba irin xabinka bace ko?" shima cikin sauri yace "karkimun mummunar fassara plz" kasancewar abunda suka siyo babu yawa yasa 3k tai ragowa a kudin, ya bata ta dauki 1k ta bashi 2k tace to ga naka" xaiyi magana ta manna masa bakinta suka xube a qasa.
A wannan dare dai sakeena ta gurxu a hannunsa tun tana jurewa buqatarsa harta gaxa ta fara tureshi. Yana qara qanqameta yace "meye haka sakeena? Da kinfi jarumta saida kika sabamun da jarumtarki sannan ki xama raguwa?" Haka dai suka kwan tana kan qirjinsa ya kwakwumeta badan ya gaji ba sai sunsunar turarenta yake.
Da sassafe suka karya da ruwan tea da indomi, sukai wanka suka chada ado shiyasa kayansa na angwanci ita kuma wani lace ta cada ado dashi cikin kayan da Hassana suka bata, ta yafa mayafin daya shiga da kayan tasa takalmi. Suna ta qamshi suka fito saboda kishi saida ya rakata har gidan aikin ya tsaya a kofar gidan ita kuma ta shiga ciki tambayo izinin yau baxata samu xuwa girkin rana ba xata gidansu kamar yadda suka tsara ita da Deni. Mama kadaice ta tashi dake Sunday ne tace "bakomi sakeena dandai yau daya kiyi yininki a gidanku gobe kyaxo ki gaida mamanki kinga amfanin waya kenan da kinada waya ai saiki bugo ki fading uxurinki basai kinxo ba" suka rabu ta fito kofar gida suka tafi da Deni Wanda ya kama hannunta ya riqe dan nunawa wadanda ke kallonta matarsace.
Ya samo musu napep suka loda kayan aciki suka nufi Gwale cikin farin ciki.
Hajia ☺
[7/31, 2:17 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣3⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Lokacin da suka isa ko taran safe batai ba, suka samu kowa a gida sun sami tarya me kyau a gurin Iya da Baba yayin da Hajjo da yayanta kebin Sakeena da kallo jin qamshin da take da kuma ganin lace din jikinta wanda yadda yake rawa kawai xai bayyana maka tsadarsa. Suka qara mamaki ganin kayan da almajirai ke shigowa dasu suna jibgewa yayin da sakeena takai ledar hannunta dakin Iya. Suka gaisa dasu Baba wanda kecewa Iya a xubo musu abin karyawa suma. Deni yace ai sunci abinci kafin su fito.
Hajjo dai sai yaqe takeyi tana qara qurawa kayan da suke gabansu ido kamar ta fada ciki. Deni yace "Baba ga kayanan injimu ni da sakeena" Baba yayi godiya tare dasa albarka yasa Saddiq ya bubbuda aka gani ya dunga godiya da tarin adduoi Iya na tayashi ita kuwa Hajjo suna kallon kallo da yayanta.
Baba ya tashi ya fita, kowa yayi dakin uwarsa, da sauri Hajjo ta riqe hannun Deni xuwa cikin uwar daki ta fara magana da bacin rai "Deni wato kudi ka samu ka manta dani ko? Kakewa matarka bushasha kalli suturar jikinta da yadda tayi kyau, tana shigowa ta fara yimun kallon raini ni da yayana, kuma inxaka bawa ubanka abu saika hada da sunanta? Sannnan ai naga takai wata leda qatuwa dakin uwarta meye ka bata ta kaiwa tata uwar Kai kuma taka ko oho?" Ya runtse ido jin yadda Hajjo ke xuba babu commer balle full stop.
Saidata gama tsaf kafin yace "Hajjo aida tun farko ko a gaban Baban kika tambayeni dana fada miki ta yadda kayan suka samu. Wadannan kaya da kike gani ko zarena babu a ciki gaba daya gumin sakeena ne" ya fada mata duk yadda akai ta samu aiki da kuma kyautar da akai mata ta raba biyu ta kawo musu rabi. Ta sauke ajiyar xuciya tayi tsaki tace "yo ai dama tun farko abunda ya kamata kayi kenan bakai ba, ta saba wahala irin ta qauye yayin da kai kake dan hutu, da tun farko ka turata aikatau din taje ta nemo ai dabaku wannan yunwar ba kwanaki, meye amfanin aurenta dama inba hakan ba?" Deni yayi tsit yana sauraren Hajjo, ya jinjinawa son xuciya da muguntarta wato tasan kwanaki a cikin yunwa suke amma batai wani yunqurin temakawa ba? Kuma ta yadda ya tura sakeena aikatau tunda ba diyarta bace, uwa uwace amma wata uwar kam sai a hankali.
Ya fito ya leqa dakin Iya suka kuma gaisawa yayiwa sakeena sallama yace ya tafi kasuwa saiya dawo da magrib xasu tafi.
Hajjo ta fito ta warwarewa yayanta duk abunda Deni ya fada mata, suma sai a lokacin suka dan samu kwanciyar hankali, dan suma a xatonsu daukaka Deni ya samu yakewa sakeena bushasha Amina tace "amma kam inaga a gidan mugun me kudi ta samu aikin irin wannan uban lace haka da qamshin turare?" Hajjo tana sakace da tsinke tace "eh mana tunda kikaji sunyi kyautar buhun shinkafa ai kinsan masu arxiqi ne sosai" Hadixa tana danna waya tace "shiyasa daxu na ganshi online ashe Haj sakeena kuku ce tasai masa Data" suka sheqe da dariya a tare.
Acan kuma dakin Iya hira suke me dadi ita da sakeena. Yayin da Iya keta yaba kirkin iyalan Alh Dalhatu da kuma kyan da sakeena tayi. Can Iya ta kuma kallon sakeena tace "anya kuwa sakeena baki harbuba? Yaushe rabonki da al ada?" gabanta ya yanke ya fadi data tuno qullaiyar da suka shirya ita da Hajjo. Cikin sanyi jiki ta shatawa iya qarya da cewa "jiya nayi wanka" Iya ta lura da canjawarta tayi zaton rashin samun cikin ke damunta tace "to kuma meye abun damuwa? Ai haihuwa ta Allah ce in lokaci yayi sai anyita kamar mutuwa ce"
Ta katse hirar ta janyo ledar kayan da Mama ta bata ta bawa Iya tace "kema ga naki kayan inji Mama" Iya tana godiya ta fito da kayan set biyar kuma duk da kyansu. Ta kalleta tace "to ai sai a fitarwa da uwar mijinki ko?" sakeena tace "a a cewa tai inkaiwa Mama na" Iya tai dariya tace "yaro man kaxa, uwar miji ma ai uwace sakeenatu kuma inkika bata xataji dadi sannnan kyauta na warware gaba, inkina musu kyauta wata rana sai ki nemi qiyayyar da suke miki ki rasa. Suma su Fiddausi ki dan tsinto musu a wadanda aka baki ko baxasu yimusu dai dai ba kindai basu" Tace "to" Iya ta tsinci set biyu wadanda sukafi kyau a cikin kayan tasa a leda tace "to maza jeki ki qara gaisheta ki kai mata" ta miqe ta nufi dakin Hajjo.
Ta shiga tayi sa a tasamu duk yan majalissarta a falo inka dauke saddiq da ya fita yanxu. Ta qara gaishe da Hajjo kana ta miqa mata ledar. Ta karba bayan Hadixa tai mata alama da hannu, ta bude ta fito da kayan, ta kalleta tace "sakeena wannan kayan daga ina?" cikin sanyin jiki tai mata bayanin anbata ne a gidan da take aiki shine ta raba musu ita da Iya. Amina tai caraf tace "kan uban can kayya sa, ke dan rainin hankali kwance xaki kawowa Hajjo? Ance miki kowa irinki ne daya saba rayuwar wulaqanci da bauta da qasqanci? To wlh Hajjo tafi qarfin wannan kwancen kamar yadda sukace ki kaiwa uwarki to ki kaiwa uwartaki ku qarata kune matsiyata." Fiddausi tai dariya ta fusge kayan a hannun Hajjo tana dubawa tace "kai rayuwar talauci batai ba, wato da ace yaya Deni diyar kwarai ya aura yar asali da dangi yar masu kudi da fa turame xa a kawowa Hajjo ba kwancen wasu ba" Amina tace "sosai ma kuwa ai wlh dole ma yaya Deni ya auro mana yar gaske ba gamin ganbixar igala da Fulani ba." tana fadar haka ta karbi kayan a hannun Fiddausi ta cillasu waje tace da sakeena "tashi kibi kayanki kafin in cillaki yadda na cillasu" sakeena ta miqe ta Kalli Amina tace "wannan kuma shine qarya, sai dai ki cilla kayan amma wacce ta kawo kayan kinyi tsarara kuma kinyi kadan ki cillata" Hajjo ta bude baki tace "iye! Lallai kin cika jinin qedara, yanxu a gabana kike fadin haka?" sakeena ba qara cewa komai ba ta fita ta dauki kayan da Amina ta wullar ta shige dakin Iya.
Iya taji duk abunda akai. tace da sakeena "share hawayenki babu komai nice na jawo miki amma sunwa kansu kinga kome kika samu baxan kuma saki kai musu ba"
Can dakin Hajjo kuwa sakeena na fita Hadixa tace "wlh Hajjo manyan kayane fa sakeena ta kawo miki ki kaiwa kanki kikaqi karba, daya a tamfar ma fa super exclusive ne wlh kuma itane karshe I mean ba ai ta wannan shekara ba" Hajjo ta dumawa Amina dundu tace "duk ga shegiyar data watsa kayan waje nan dama fa niyyata in karba inna gama ja mata rai saboda karta rainani intaga ina karbar kwance" Amina ta xunburo baki tace "aiku dama ba ai muku gwaninta, to wlh daga yau na dena saka baki acikin abunku"
Sakeena ta yini sukuku duk dauki da take na xuwa gida susha hira da Iya sai taji ya kau. Iya ta dunga lallabata a xatonta abunda su Amina sukai mata yake damunta, amma a xahiri sakeena tana cikin nadamar biyewa Hajjo da tayi aka durka mata allurar planning, tun kafin aje ko ina ta fara gane kuranta domin sai taji abunda su Amina sukai mata da kuma maganar iya ta daxu yasa tanason taga Danta domin koba komai inta haifawa Nura yaya dole Hajjo ta karbesu kuma ta hada jininta da Igala da take kyamata inyaso taga ya xatai dasu. Sannan in ada tana gudun haihuwa saboda talauci yanxu kam ai Allah ya kawo musu mafita xasu iya rainon dansu da abunda take samu na aiki. Kuma dole fa inda Da a rage nuna mata wata qiyayyar kodan Dan. Lallai ta tafka wauta kuma xata duqufa roqon Allah ya bata ciki. Gabanta ya fadi data tuno duk wannan abunda akai fa Deni be sani ba amma tasan duk randa ya sani xata dandana kudarta duk da tunda suke be taba yimata xancen haihuwa ba koda wasa amma tana ganin Deni baxaiqi son Da daga gareta ba. Cikin kuka tace "Allah ka rufamun asiri ka axurtani da dan kaina" Iya ta xauna kusa da ita tace "au sakeena xancen haihuwar da nai miki daxu shiya saki a wannan halin? Inbanda abunki sakeena ai duk abunda Allah be baka ba ba alkhairi bane gareka. Kuma wata nawane da auren naku gaba daya? Sannnan ko Allah be baki haihuwa ba baxai toxartaki ba, ni na isheki misali Allah be bani ba amma saiya a xurtani da ke, kika mayemun gurbin yaya bila adadin. Share hawayenki kinji Allah yana tare dake" tadan saki jikinta don kwantarwa da Iya hankali amma xuciyarta babu dadi.
Ana idar da sallah Deni na shigowa shi da Baba. Baba ya miqawa sakeena qunshin leda tasa hannu biyu ta karba ya qara da cewa "a dunga kula kinji yanayin da dana yanxu ba daya bane Allah ya rabaku lfy" ya juya yana jaddadawa Deni ya qara kula da ita, ta share hawayen tausayin Baba domin tasan a xatonsa ciki gareta. Yayin da Hajjo suka hada ido da Hadixa sukai dariya.
Duk da tilasawar da Iya kemata taci abinci dan da rana ma bataci wani abun kirki ba amma abun yaci tura, dole ta kyaleta yayin da Deni ya karanci akwai abunda ke damunta dan haka yace su tashi su tafi dan suje ta fada masa damuwarta. Iya ta hada mata kaya rankata kaf kamar yadda ta saba yayin da Hajjo ta xuba musu gasara, ta basu.
Suna tafe cikin napep yana mata hira amma tai masa banxa ita kadai tasan yadda takeji. Sun isa gida sukai shirin kwanciya sai a lokacin ta kunce ledar Baba. Ta tarar da kaza gasashshiya yar hausa irin gashin masu tsire, Allah sarki xatonsa ciki gareta shiyasa ya siyo mata. Deni dake bayanta yace" inye diyar Baba wannan ke kadai kenan keda jikansa dake cikinki" Ta fashe da kuka wanda yasa Deni yayi shiru yana dubanta da mamaki, ya juyo da ita yace "fadamun haihuwar ce bakyaso ko kuma da nine talaka bakyaso ki haihu? Ina lura dake tunda Baba yayi miki batun cikin da kike dauke dashi kika canja" batace komai ba sai kwanciya tai a cinyarsa tana kuka wurjanjan.
Ya dunga shafar bayanta da kanta har tayi shiru. Ya dagota yace "fadamun menene ya saki damuwa?" ta qura masa jajayen idanunta tace "kaima kanason haihuwar ne?" yayi murmushi me sauti yace "Haba sakeena wane tambayane wannan? Taya xa ai naqi haihuwa tunda nasan inayin abunda xai kawo min haihuwar, sannan kuma ai kinga gidanmu babu wasu jikoki sai yayan zahra wanda sai dai suxo da yawo su tafi tunda bamu da iko dasu kasancewarmu dangin uwa, amma in muka haihu ni da ke ai kinga dan ya xama na Baba da Iya halak malak tunda bashi da gidan kakannin uwa da na uba wanda ya wuce gidanmu. Bare ma yau da Baba yayi batun cikin jikinki sai naji na qagu mu haihu kinga Baba ma yana buqatar yaga jikokinsa na gudu a tsakar gida rabonsa da ganin yaro a gidansa tun daga kan Amina" sakeena ta kuma jin fargaba ta shigeta tace "to ni bani da ciki wlh kuma daxu ma Iya ta tambayeni na fada sai dai fatan Allah ya kawo" yace "amin ai babu komai xan qara kwaxo musamu" ya fada yana kashe mata ido.
Ta juya ta kwanta cikin wata irin nadama, ya biyota yace "amma fadamun meye dalilin kukanki da damuwar da kike ciki?" a taqaice tace "bakomi" shima ya barshi akan bakomi din ya miqe ya rufe kazar data bude bata ko sa hannu ba, amma a ransa yasan dole akwai abunda akaiwa sakeena wanda yayi imanin Mahaifiyarsa ce ko qannansa. Shima kwanciyar yaxo yayi kowa da abunda ke ransa.
Qarfe hudun dare ta tashi tayo alwala ta duqa sallah da kai kukanta gurin me duka (Allah) tasan shi kadaine xai yaye mata damuwar da take ciki don a wannan lokacin bacci be ganta ba.
Tana duqe har kiran asuba ta tada Deni yayi alwala ya tafi masallaci, ita kuma taci gaba da lazimi har gari ya danyi haske, ta jajjaga kayan miya ta dora musu kaxar jiya tayi pepe soup qamshinsa ne ya tada Deni a baccin daya koma. Ya tashi yace "sakeena qamshin meye haka ya cika gida?" tai masa murmushi kawai ta kaimasa ruwan wanka, ita kam har tayi nata.
Yayi ya fito ya shirya yaje ya samo musu bread suka karya da Lipton da romon kaxa, yanaci yana mata santi tana dariya. Lallai Allah gatan bawa tsaiwar daren da tayi taji damuwarta ta ragu sosai, suka gama ya dakko leda ya fito da hijab qato kamar wancan ya miqo mata yace "gashi tun jiya na siyo miki naga bakya cikin yanayi ban bakiba, gashi ki hada da wancan ki dunga sakawa" ta karba da farin ciki tace "to nagode wlh saina fara sawa yanxu ma" ta wareshi ta saka dake dark purple ne saiya haskata sosai. Ya kalleta yace "kai sakeena shima hijabin sai naga ya fito da kyanki gaba daya kodai insiyo miki niqab?" ta qura masa ido tana mamakin irin kishinsa. Ya sassauta murya yace "ina takura miki ko? Kiyi haquri ina sonki ne shiyasa nake protecting dinki" Batace komai ba, qarfe tara suka fito yayi kasuwa ita kuma tayi gidan aiki.
Tana shiga falo Hassana dake kan dinning tana breakfast ta taso da gudu ta rungumeta tana cewa "sakeena munyi missing dinki jiya bakixo ba" Usaina kuwa bata taso ba sai murmushi take wanda ke nuna taji dadin ganin sakeena. Ta tsunguna ta gaishesu, suna sauri sauri xasu tafi skull. Hassana ke fadawa sakeena tayi musu rice nd beans with salad shine favourite din Abba kuma suma 12 xasu dawo tare zasuyi lunch da Abban.
Ta dunga daga musu hannu har suka fita suma suna daga mata, itama tana qaunar yan biyu har cikin ranta. sune mutane na farko da basu nuna mata kyama ba duk da kasancewarsu yayan gata. Tayi fatan itama Allah ya kawo ranar da xa a wayi gari ta tafi makaranta ba aikatau ba ko xaman banxa.
****** ***** ***** ******
Aikinta yacigaba kamar yadda takurar Ahlan itama tacigaba, tsakaninta da iyalan gidan babu matsala ko kadan inka cire shegen kaya wato Ahlan wanda duk sanda suka hadu saiya xagi mijinta da jinjinawa muguntarsa. Yan biyu kam xata iya cewa sune qawayenta na farko a rayuwarta duk da sun girme mata amma sun jata ajiki sun maidata yar gida qarfi da yaji tun tana dari dari harta saki jiki dasu. A duk lokacin da bata da aiki dakinsu take xuwa ta kwanta, sau tari ita ke gyara musu kayansu kuma bata fasa girmamasu ba. Ita da Deni xamansu lfy lau. Ta maida tashin qarfe hudu wajibi, intashi bata komawa sai intagama aiki ta kwanta a dakin su Hassana. Koda wata ya qare aka kuma bata kayan abinci kamar wancan, da albashinta su Hassana suka hada mata ragowar turarensu dasu mayuka kamar wancan hardasu yan kudade.
Ranar ma haka suka raba kayan da Deni kamar wancan karon suka kaiwa su Baba nasu a washegari wanda ya tsira Deni saida ya fada masa inda kayan abincin suka fito. Ya fadawa Baba gaskiyar aikin da sakeena keyi da kuma wahalar da suka sha kafin samuwar aikin. Ya kira sakeena ya dunga xabga mata addua da godiya tunda gashi a dalilinta shima gidansa nauyi ya ragu sosai. Hajjo ta dunga tsaki ita bataga wani abun xuxutawa ba dan sakeena tayi wannan, ai dama itadin baiwa ce.
Nasu kayan abinci ma wancan basu qare ba dan haka sakeena yanxu tafi qarfin yunwa abinci kam sai dai ta bawa wani, kai bama abinci ba har sutura yanxu tafi qarfinta wanda hakan kewa su Amina ciwo mutuqa dan sunga tafi qarfinsu.Tana yawaita yin sadaka, ita da Deni sunyi tas kowa yagansu yasan wahala ta kau.
A yanxu kam bata da matsala saita rashin haihuwa sai kuma takurar Ahlan.
**** **** ***** **********
Yau asabar tana kicin tana aikin abincin rana tana Allah Allah ta gama ta gama taje sucigaba da kallon Korean series din da suke da yan biyu.
Tana suyar kajin da xata xuba a miya ta tsinci idanun Ahlan a kanta yana tsaye kofar kicin ya harde hannu yana kallonta. Tayi saurin janye nata idon tana ta'awizi, ya qaraso dab da ita tayi baya da sauri tana cewa "kaji tsoron Allah miye haka?" ya ware mata idanunsa yace "ke xancewa kiji tsoron Allah ki daina azabtar da xuciyata, kullum cikin mafarkinki nake duk da inason yakice ki da kuma warning mama amma abun yaci tura. Wlh pretty inkinason kanki da lfy ki rabu da mijinki ki aureni inba haka ba xansa a batar dashi" ta dafe qirji tana kallonsa a raxane tace "Allah yayi mana tsari dakai, ban taba san wani abu kamar ya Deni ba inaso inka tashi batar dashi ka hada dani" Ya sunkuya akan gwiwarsa yace "plz pretty leave ur husband be wit me, i beg u" tayi saurin yin hayar fita, yayi caraf ya riqe mata hannu yace "tunda kinqi ta lallami ya xama dole inyi amfani da daya tsarin don samunki, kowane lokaci daga yanxu xaki iya samun lbrin batansa" ya cikata yayi waje.
Kallon da bata qarasa ba kenan, ta xaune a kicin cikin fargaba da zullumi har xuwa yamma ta gama abincin dare ta tafi babu sallama.
Tana tafiya a hanya taga wata mota me baqin glass tana binta, kawai saita qaddara Ahlan yasa a biyota ne aga gidansu kafin dare yaturo satar Deni kamar yadda yace.
A firgice tai wanka ta qule uwar daki gabanta na faduwa, kana ganinta xakasan a tsorace take. Deni ya dawo ya taddata haka yayi wanka xai fita sallah ta saka ihu ta riqeshi tana cewa dan Allah ya rufa mata asiri karya fita. Ya riqeta yana kallonta cikin Al ajabi yace "sakeena fadamin meke faruwa kinji" ta qara qanqameshi tace "babu komai tsoro nakeji karka barni ni kadai" bai tsananta bincike ba ya haqura amma sam be yadda da itaba wane irin tsorone tun tana amarya bataji ba sai yanxu.
Sukai sallar isha tare, shi yayi musu girki saboda bata taho da abinci ba. Abincin da ya dafa ko spoon biyar bataiba tace ta koshi, shima yaji duk ya fita ransa saboda halin da take ciki.
Suka kwanta tana riqe dashi tamau, bayan tasa musu sakata a daki fargabarta kar axo sace Deni.
Baccin ma dai babu dadi saboda rashin kwanciyar hankali. A cikin baccin tai mafarkin wasu qattin maxa sunxo suna jan Deni ita kuma tana ihu tana riqeshi Ahlan itama yana riqeta yana dariya. Ta kwallah wata irin qara tace "Ahlan ka sakarmin hannu babu ruwanka da mijina" Deni ya girgixata da qarfi, ta farka a firgice tana kuma maimaita Ahlan ka sakarmun hannu. Ya kunna wutar dakin ya dubeta yace "waye naji kina kiran sunansa? Tayi wuqi wuqi cikin qinqina tace "bakowa" ya xaro mata ido yace "sakeena ki fadamun waye Ahlan da naji kina ambata?" ta kuma cewa "bakowa kawai nayi mafarki ne" ya ce a karo na 3 "daga daxu da yamma xuwa yanxu a tsorace kike wanda hakan yasa nagane akwai abunda ya faru just tell me" ta qara cewa babu komi fa mafarki nayi"
Ya tashi cikin mutuqar bacin rai ya ciro belt dinsa dake rataye yace "Sakeena inkinason kanki da lfy ki fadamun waye Ahlan inba haka ba wlh cikin daren saina kasheki da duka inyaso nima a kasheni" ta tsorata matuqa taga shima baya hayyacinsa cikin tsoro tace "Dan gidan Alh Dalhatu.. " kafin ta qarasa taji saukar belt jikinta ta tsala ihu, ya kuma xuba mata sai dayayi mata ciki 3 kafin ya cillarshi ya tsuguna ya damqota ya murdeta yace "shine yake riqe miki hannu? Shine kukecin amanata dashi? Yawwa ashe shiyasa ake baki abun duniya a gidan ashe ban gishiri invaka manda kukeyi, ni inanan sakarai na yadda dake ashe anacan ana loleki?" cikin tsoro tace "wlh ba haka bane, ka tsaya kaji" ya matse mata baki cikin fita hayyaci yace "to yayane? Bani lbr kinji maci amana" tana rawar baki ta bashi lbr tun farkon ganinta da Ahlan har xuwa abunda yace mata jiya, ta fada masa gaskiya dan taga gaskiyarce kawai xata kwaceta.
Ya sheqe da dariya cikin fita hayyaci taja baya don ya fara bata tsoro, ya kamota ya dagata ya makata akan katifar yasa qafafunsa ya danne nata yace "kina xaton xan yadda da wannan Kalama qaryar da kika shirya?" tai saurin cewa "wallahil azim, iya gaskiyar kenan innamaka qarya Allah karyasa ingama da duniya lfy" jikinsa ya danyi sanyi ya daga qafafunta daya danne, tayi saurin miqewa karya kuma danneta tana sakin nishin wahala. Ya qara juyowa ya cakumeta yace "to meyasa tun farko baki fadamun ba? Yanxu sakeena har wani namiji ya riqe miki hannu amma ki kasa fadamun?" cikin rawar murya tace "wlh tsoron yadda xaka dauki maganar ne ya hanani fada maka"
Ya koma ya kwanta, tabi bayansa da kallo, yayi xunbur ya miqe ya matse mata baki yace "Yanxu duk kariyar da nake miki duk hijabin dana saka miki saida wani ya hango kyanki? Ke wai duk gidan da kikaje aiki sai kin xabaro xuciyar namiji? Ke wace irin macece me hatsari?" tai quri tana qifta ido cikin tsoronsa.
A wannan dare dai sakeena bata rintsa ba saboda bala in Deni wanda kusan duk bayan rabin awa saiya maqureta tare da tambayar ta fada masa gaskiya. Wani irin zazzabi ya saukar mata da matsanancin ciwon kai.
Qarfe takwas din safe ya tusata gaba suka nufi gidan Alh Dalhatu dan tsabar bala i ko wanka be bari sunyi ba bare karyawa. Suna fitowa daki Mariya ta sheqe da dariya tace "yaufa munga qarshen soyayya, waya fada miki namiji dan goyo ne? Ai kawai ki mallake shege ku xauna lfy amma kinkaqi xakiga tasko, gaskiya jiya kin daku" sakeena ko kallonta batai ba domin bala'in da take ciki ya wuce ta kula Mariya.
Sakeena ce ta fara bude gate din gidan ta shiga Deni na biye da ita, a lokacin ko kallon gabanta bata iyawa tsabar ciwon kai.
Ahlan yana xaune a harabar gidan yana watsawa tattabaru abinci. Yana ganin shigowar sakeena ya taso ya nufota cikin shauqi, tsabar idonsa ya rufe ko lura da Deni dake bayanta beyi ba. Ya qura mata ido yace "pretty kece yanxu? Kamar kinsan da mafarkinki na wayi gari" Deni ya xage iya qarfinsa ya sauke masa naushi a fuska sai ga Ahlan a qasa kwance wanwar kamar matacce. Masu aikin gidan da suke gurin sukai saurin isowa suna riqe Deni da tambayar waye shi?
Yanqurin kwacewa yake yi ya qara caskala Ahlan amma sun riqeshi yayin da sakeena ta durqushe a gurin tana gursheqen kuka. Me bawa flowers ruwa yayi sauri yaje ya kirawo Mama dake falo. Ta biyoshi jin cewar wanine ke dukan Ahlan.
Tana kallon sakeena tadau hasken abunda yake shirin faruwa taqara bawa masu riqe da Deni umarnin su riqeshi sosai tana xuwa, ta koma taje ta taso Abba wanda ke bacci.
Gida dai ya hargitse cikin mintuna qililan, Abba yace su sakeshi ya kuma tada Ahlan suka shiga falonsa tare, sakeena da yan biyu sai kuka suke.
Abba ya kalli Deni ya tabbatar cikin bacin rai yake sosai, shi kuma saiya kwantar da nasa bacin ran yace "Dan samari fadamun meya hadaka da Ahlan kaxo har gidansu kana bugunsa?" Deni bece komai ba sai nuna sakeena yayi wacce har yanxu kuka take. Abba ya maida kallons ga sakeena yace "diyata gayamun meya faru" cikin rawar murya ta fara magana wacce daga baya kuka ya hanata qarasawa.
Ahlan ya katse musu xancen yace "duk abunda ta fada hakane anyi, harma wanda bata fada ba. Nifa Abba gaskiya ina sontane kuma na kasa haqura shiyasa ma jiya nai mata baraxanar inbata rabu da mijinta ba xansa a batar dashi" Su mama suka tsura masa ido cikin mamaki yayin da Deni kejin kamar ya tashi ya kuma lallasashi.
Abba ya nisa ya dunga bawa Deni haquri da kalamai kyawawa da kuma nuna masa shi besan hakan ba da tuni yadau mataki. Deni yaji xuciyarsa tayi sanyi ganin yadda wannan dattijon ke roqonsa yayi haquri kamar shiyayi lefin. Abba ya kuma juyawa ga Ahlan yayi masa xaxxafar tunatarwa da kuma fado masa illar abunda yayi na soyayya da matar aure sannan ya kafa Hujja da ayoyi da Hadisai ingantattu.
Qarshe dai ansamu maslaha Deni yayi godiya yace "kuma kuyi haquri daga jiya sakeena ta gama aiki nasa ta ajiye aikinta" Abba cikin jimami yace "karkayi haka kaji yaro baka haqura ba kenan? Ka barta da aikinta shi Ahlan xan maidashi can gurin harkokina na Lagos amma kabar sakeena sun shaqu da yarana suna santa." Deni yace "Alh kayi haquri be dace saboda sakeena Ahlan yabar gidansu ba" ya juya gurinta yace "ke taso mutafi" ta miqe yan biyu suka fashe da kuka Hassana ta rungumeta tace "sakeena Dan Allah karki tafi wlh muna sanki" sakeena ma kukan take, Usaina tana nata kukan ta dakko wayarta ta bawa sakeena tace "gashi ki riqe xamu dunga waya" Deni yayi saurin cewa "a a ta gode amma banason iyalina da waya."
Abba ya lura Deni irin mutanenne masu murdadden hali da raayin riqau. Ya dubeshi yace "to tunda ka hanata aikin ai bakwa xauna haka ba inkayi karatu xan hadaku da yaro yanxu ka bashi photocopy na credentials dinka sai a nema maka aiki, ke kuma sakeena bari a baki haqqinki na aikin wannan watan" ya fada hana irga kudi. Ya irgo ya miqawa mama ta miqo mata, itama maman nata hawayen take. Sakeena tayi godiya sosai dan daga yadda taji kudin a hannunta tasan ba qaramar kyauta Abba yayi mata ba.
Maganar Ahlan ta katse mata godiyar inda yake cewa "Abba to tunda xa a samar masa aiki nima ya barmun pretty yaje ya auri kalarsa wacce tai dai dai dashi wlh basu dace da pretty ba zaluntarta yake" Mama tasaki tsakin takaicin Ahlan. Abba kuma cewa yayi "yanxu duk ayoyin dana ja maka baka. nutsuba ko?"
Deni yaja hannun sakeena sukai wajen falon bayan ya tabbatar da Ahlan yana da matsalar tabin hankali, inba haka ba mai hankali ai baxaiyi abunda yayi ba. Sakeena tana jiyo sautin kukan Hassana wacce mama ta riqeta suna kukan tare. Suna gab da fita gidan taji muryar Usaina tana cewa "sakeena shikenan sai wata rana, amma duk sanda kike buqatar neman taimako ki nememu a shirye muke mu temaka muki ta kowace hanya ke qanwarmune. Cikin watannan xamu tafi Law school a Lagos in mun dawo kixo mu ganki plz" sakeena ta juyo tana share hawaye ta kasa magana. Deni ya jata suka fita.
Tafiya suke cikinsu a sanyaye ita kuka take sosai, shi kuma yana jinjina soyayyar da yan biyu kewa sakeena ne sai yaji be kyauta ba daya rabasu amma ya xaiyi da Ahlan. Yaron da aka saka ya karbo takaddun Deni yana bunsu har cikin gida ya tsaya a kofar daki. Sakeena ta shiga ciki ta binciko takaddun Deni (CV)wadanda basa rabo da photocopy saboda irin haka, ta fito Deni ya bita da kallo yace "baxaki iya xama dani ba in babu aiki ko? Tunda kinsaba rayuwar jin dadi yanxu, in gaskene kina sona ki bar wannan aikin bani da buqata ko dako xanyi inbaki duk abunda kikeso xan kare martabar aurena baxan kuma kuskuren turaki aikatau ba" batace masa komi ba, ta fita ta miqawa yaron takaddun.
Ta tsaya akansa bayan ta dawo tace "Nuraddeen inbaka manta ba abaya na xauna dakai bakada aikin yi wanda hakan yasa muka sha kwana da yunwa, to meyasa yanxu xan gujeka dan kawai nayi rayuwar yan wattanni a gidan Alh Dalhatu? Abunda nayi na bada takaddunka nayi ne saboda ka dade kana gararanbar neman aiki baka samu ba sai yanxu damar samun aikin taxo kana nema ka saqawa xuciyarka wani abu daban, kuma may be wannnan ita kadai ne damar samun aikinka" ta wuceshi taje ta kwanta a uwar daki ta lulluba saboda sanyin da takeji.
Shiyayi aikin kaf tundaga shara har wanke wanke girki da kuma dora ruwan wanka bayan yayi ya shirya yaje tada sakeena dan tayi nata wankan su karya, sai dai tun yana kiran sunanta ta tashi har ya fara tabata amma bata motsa ba, ya tsorata lokacin da yaji jikinta xafi rau ga kanta ma. Duk da a gigice yake bai hanashi gane sakeena a sume take ba.
Cikin sauri ya sabeta yayo waje da ita lokacin Mariya harta tara mutanenta, kuma yanajin lokacin da yake shirin fita tana fada musu cewa "ai inaga ciki tayo gidan da take aiki, dan jiya kwana yayi yana jibgarta yana tambayarta waye Ahlan kuma da sassafe ya tasa qeyarta gidan" yayi tsaki a fili, lallai gidan haya bala'i ne wato duk abunda kake ido nakai, Allah ya horewa kowa yayi nasa. Haka ya fita ba tare daya rufe dakinba. Ya tare napep ya shiga da ita kamar matacciya.
Qaramin asibitin local government ya kaita wato sha ka tafi, suka amsheta aka shinfideta suka debi jininta aka tafi kwaji. sai a lokacin ya tuna babu kudi jikinsa balle ya biya kudin test. yace suyi yanxu xai dawo. Da sauri ya koma ya tarar har umman Amir ta janyo musu dakin, ya bude ya dakko kudin da Abba ya bawa sakeena daxu ita kuma ta ajiye masa yana fushi be dauka ba, ya fito umman Amir ta fito tana tambayar lfy a gurguje ya fada mata sakeena babu lfy tana asibiti nan kusa.
Lokacin da ya dawo har result ya fito likitan dake duty ya rubuta mata treatment, ya biya kudin sukace dole asa mata ruwa saboda jikinta yayi laushi. Duk ya biya kudin akai mata allurai wasu kuma aka saka cikin drip din aka jona mata, har lokacin bata farko ba amma sunce akwai allurar baccin da sukai mata.
Yana gaban gadon a xaune a kujera riqe da hannunta me qarin ruwan, yayi nadamar dukan da yayi mata jiya dan ga shatin belt nan a kafadarta gurin yayi ruwa kamar quna. Koda wasa be nufin fadawa kowa a gidansu ba dan da kunya ace dukan da ta yayi harta suma. Yasan kuma zata rufa masa asiri babu mejin wannan maganar, waishin ma meya kaishi dukan mace kamar wani jahili? Besan meyasa jiya ya kasa controlling din fushinsa ba gashinan ya jawo musu abun fada a gidan haya.
Yana riqe da ita har xuwa yamma be matsa ba sallah ma anan yake, lokacin ruwan ya qare duka biyun. Likita yaxo, sakeena da tundaxu ta farka amma taqi bude ido jin muryar likita ta bude yayi mata sannu ya sallamesu bayan ya gargadeta da shiga gidan sauro dan akwai malaria sosai a jikinta ya rubuta mata yadda xatasha maganin suka tafi.
A gida ma dai haka ya dunga nan nan da ita har yakai mata ruwa ya rakata toilet ya tsaya a Kofar ya jira tayi wankan ta fito saboda tana jiri ya riqeta suka koma taji dadin wankan dan ruwan da xafi sosai. Umman Amir ta shigo suka gaisa tana mata jajen jiki tace "yanxu nake shirin inje dubaku na jira in qare girki ne kuma sai gaku" ta ajiye musu flask tace "ga abincin ma tunda kun dawo sai kuci, Allah ya qara sauki" Deni yayi godiya umman Amir ta burgeshi ta iya jan girmanta bata nuna taji abunda ya faru tsakar daren jiya ba duk da yasan tajin. wannan shine iya xama kabar abunda be shafeka ba.
Ana kiran sallah tayi sallolin dake kanta a xaune, ya hado mata shayi tasha don yunwa takeji, ya bude abincin umman Amir shinkafa da miya da salad. Dama nufinsa ya fita siyo musu abinci kuma sai gashi sun samu tare sukaci. Ana idar da isha tai brush tasha magani ta kwanta bata jira Deni ba kuma tunda suka taho bata tanka masa ba.
Kwana 3 cur yana jinyarta komai saiya mata baya fita ko ina, ta warke ras kuma ta huta sosai, amma fa batace masa komai domin tana cikin wani irin yanayi na masifar kewar su Hassana kamar yan uwanta na jini take jinsu batasan tana qaunarsu haka ba saida suka rabu.
Shi kuma a nasa bangaren ya xata rashin lfyar ce tasata haka dan ko gaisheshi batayi xaman kurame suke a dakin ko abu ya tambayeta sai dai ta nuna masa da hannu. Amma a rana ta 4 yaga ta karbi aikinta har ta bawa Amir kudi yayo mata renting din littafin hausa (novel) sai fuskanci sakeena fa fushi take dashi, ya fita kasuwarsa ita kuma ta yini kwance dan da rana ma awara tasa aka siyo mata taci tunda hannunta cike yake da kudin da Abba ya bata duk da aciki akai hidimar asibiti.
Da yamma tai girkinta harda nama tai wanka tasa English wears amma batai kwalliya ba yacce ta saba. Ya dawo da wuri dan shiri yake nema, amma ba fuska dole shima ya kama kansa ya debi ruwa yaje wanka. Bayan sallah sun xauna cin abinci yana kallonta amma taqi yadda su hada ido, ya gaji da wannan horo nata gara suyi duk wacce xasuyi a dawo dai dai. Ya ture abincin da sukeci ya kamota gaba daya ya dora akan cinyarsa yana kallon fuskarta tai qasa da kanta, yasa hannu yana shafar cinyarta data dame acikin wandon jeans. Cikin sanyin murya yace "I'm sorry baby, nayi lefi ki yafemun na kasa controlling kainane lokacin shiyasa na bugeki amma wlh ba halina bane kuma I promise you baxan kuma ba" tayi murmushin yaqe tace "bakomi ai duk laifinane dana dauka ka yarda dani amma abun takaici ashe xargina kake" Yayi saurin qanqameta yace "stop it plz, bana zarginki xargi fa yana haramta xama, kishine ya rufe mun ido lokacin shiyasa na yi duk abunda nayi" haka dai ya dunga ban baki tace masa ya wuce suka shirya. Da yaga bataci wani abincin Kirki ba yaje ya siyo mata maltina ya hada mata da peak masu sanyi ya bata sha tasha maganinta, ai kuwa taji dadin shansu. Suka kwanta yanata matseta tasan abunda yakeso amma ta share taqi bashi hadin kai dole ya haqura.
Dake yanxu rayuwa da harkar samun aiki ta xama wakasani waya sanka sai gashi ranar juma a wacce tai dai dai da kwana 5 da karbar takaddun Deni ya samu kiran waya cewa yaxo screening din daukar aiki ran Monday a Kaduna state yaxo da original credentials dinsa. Yana kasuwa kiran ya sameshi, ya dunga murna yana godiya ga Allah ya dunga Allah Allah a tashi kasuwa yaje ya fadawa sakeena, yayi sa a sunyi baqi yau akai masa kyakykyawar sallama. Ya dawo gida lokacin ko 5 batai ba, sakeena na kici kicin dora girki sai gashi yana shigowa ya kwallah mata kira, Mariya da mutanenta suka xura ido a xatonsu wani dukan xai kuma yimata. Ta fito cikin hanxari tana tunanin lfy Deni yanxu kuma yana kiranta tun daga tsakar gida? Tana fitowa yaxo da gudu sureta yana juyi da ita kamar ya manta akwai wasu a gidan bayansu. Suna dariya duka ya sauketa ya riqota ya jata daki suka bar sa idawa a tsaye qiqam kamar sun hadiyi rodi. 😆
Acan daki ya labarta mata yadda akai, ta tayashi murna ta miqe dan dora girki, ya hanata yace tayi xamanta kawai wanka xasuyi su fita cin abinci bayan isha a restaurant yau aljihunsa a cike yake.
Kamar yadda yace haka akai bayan sunyi sallah ta hade cikin after dress shi kuma yasa qananan kaya suka fita riqe da hannun juna sukaje sukaci abinci kamar yadda take gani a film, bayan nan sukaje store yayi mata shopping saida ya kusa qarar da kudin daya samo a kasuwa duk kuwa da yawansu, suka nufo gida tana ayyana cewa lallai in Deni yayi arxiqi xataji dadi domin ta fuskanci irin mutannenne masu kyautatawa iyali.
Dariyarsu tasanar da Mariya shigowarsu ta leqosu ta taga ta tarar Deni riqe da ledoji a hannunsa sakeena kuma rataye da Jakarta da wayarsa a nata hannun, suka bude daki suka shige.
A ranar dai sunyi soyayyar da suka dade basuyi ba, tana xaune kan cinyarsa suna kallo a wayarsa tana shan ice cream din da suka siyo shima tana bashi suna dariya.
Yayi yan shirye shiryensa a ranar asabar kuma yaje ya fadawa Abba kiran da akai masa kamar yadda sakeena ta bashi shawara sai dai yayi rashin dace Abban baya gari shi da mama yan biyu kuma suna skull ya dawo ya fada mata. Sun tsara xai tafi KD gobe Sunday da yamma ya kwanacan inda da sassafe xaije gurin screening din.
A daren ranar dai taji tausayinsa ta bashi abunda yaketa qulafuci ta hanashi, yayi murnar hakan dan dama a yunwace yake dashi dandai karya nuna ne tayi fushi. Sunsha soyayyarsu suka tashi da safe sukai shiri yasa kayansa kala 3 a jaka duk suka hada kudadensu guri daya har wanda Abba ya bata duk ta hada masa yayi guxuri inda suka tsaida shawarar baxai dawo ba sai komai na aikin ya kammala tunda ba kusa bane. Itama da nata kayan inda xata koma gida harsai ya dawo itama ta dawo. sunyiwa kowa sallama batare da fadar inda xasu ba, yan gidanma sun dauka tare xasuyi tafiyar.
Acan Gwale xuwansu da kuma lbrin da sukakai na xuwan Deni interview yasa gidan ya cika da sowa duk da basu fadi ainihin abunda ya faru ba kawai sunce me gidan da sakeena take aiki ne ya samar masa, ganin haka yasa shikuma yasa ta ajiye aiki. Baba ya dunga murna ya tattaro yan kudinsa ya qarawa Deni yaqi karba yace yana da isassun kudi Baba yace "karbi ka qara guxuri baya yawa tunda bakasan addin kwanakin da xakai ba" ya karba yayi godiya. Hajjo ta jashi daki tana masa fadan dan me xe raba sakeena da aikinta ai daya barta da abunta koda ya samu aiki saiya dunga tattala abunda yake samu yayi aure ita kuma abunda ake bata a gidan aikin ta dauki nauyin kanta. Shi dai baice komai ba dan mamakin kalamanta. Qarfe 4 ta yamma yayi sallama dasu da sakeena dake kuka Baba ya rakashi tasha yahau motor KD.
Ta kasance cikin kewa sosai bayan tafiyarsa ga takurar Hajjo a gefe wacce ta wajabta mata yi mata wanki da kuma yi mata girki duk ranar nata girkin. Baba bece komai ba haka Iya domin ba kowane abu xaka xauna ka dunga magana akaiba sai ka xama sakarai kuma a rainaka.
A kwana na hudu iya ta lura sakeena fa ko abinci bataci saboda kewar mijinta tasa mata katin 100 a waya ta bata ta kira Deni. Sunsha hirarsu ta soyayya yake fada mata sunyi interview din kuma Alhamdulillahi ya amsa fiye da rabi na tambayoyin da akai masa yanxu yana jiran fitowar result din ne wato jerin sunayen wadanda sukaci kwajin wato suka shiga tsarin daukan aikin, wanda yake daukan 1 wk kanya fito. Tayi masa fatan samun nasara suka dora hirarsu har xuwa qarewar kudin.
A yan kwanakin kullum tana cikin tsaiwar dare wacce ta karkata akalarta akan samun aikin Deni, yayin da Hajjo ta maida hankali gurin kwazawa mutane Deni ya tafi jarrabawar daukan aiki, kullum xancen kenan idan ta xauna cinkin gasara, ita da yayanta kuwa hirarsu ta xama inya Deni yasamu aiki xaiyi musu wannan xai musu wancan.
A kwanan Deni na 13 ne a KD ya dawo da yammaci liqis, kuma yaxo da kyakykyawan lbrin ya samu aiki har an bashi gida qarami cikin rukunin ma aikatan company din.
Qiriri Hajjo ta hanashi cin abincin da sakeena ta hada masa ta jashi dakinta ta xuba mata nata abincin datai masa, yana ta tsakura yana hangen sakeena dake wanke wanke a tsakar gida ya matsu kwarai su kebe da ita ya jita jikinsa dan yayi missing dinta sosai amma Hajjo data lura saita xuge labulen dakin ya dena gano matarsa.
A gurguje ya gama ana idar da sallah yace sakeena ta fito su tafi gida, Hajjo tai tsalle ta dire tace babu inda xasu yau ya dawo ya kwanta ya huta a gidansu batasan jaraba, ala dole yabi umarninta tunda uwa ce ya haqura da tafiyar.
Baba ya dawo aka dora murnar samun aikin Deni dashi amma jikinsa yayi sanyi jin aikin a kaduna ya samu shi a nasa tsarin yafison xamansu kusa dashi amma ya ya iya? Deni ya qara kwantar masa da hankali da cewa ai company din babban company ne kuma a Arewa a kaduna kadai suke da reshe saboda haka yana iya dawowa kano da xarar sun bude company din da suke ginawa yanxu.
Yayin da kowa ke murnar wannan aiki sakeena na daki na tunanin wani qalubale da take hangowa yana tunkarota a dalilin wannan aiki na Deni.
Sai dai kash abunda duk basu sani ba samun wannan aikin na Deni shine silar qaddarar Sakeena Abbakar Liman wanda xamu iya Kira da MUQADDARI NE.
Hajia ☺
[7/31, 2:18 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣5⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
A yan kwanakin da suka biyo baya sakeena ta fuskanci wasu irin canje canje daga mijinta Nura wadanda tun tana kawar da kai taga abunfa ya fara yawa.
Da farko ita da Deni sun fara wani irin xama kamar na sabbin ma'aurantan da aka hadasu aure basusan juna ba. Basa um basa um um, inya dawo yakan shige daki yayi xamansa har xuwa lokacin dayaga damar fitowa yaxo ya ci abinci intana kusa ta xuba masa inbata kusa kuma sai dai taxo ta tarar yaci abunsa.
Babu magana babu, hirar soyayya, babu yaganta acikin damuwa ya tambayeta rabon da Deni ya kebanta da ita a shimfida harta manta duk kuwa da cewa tasan be cika jurewa hakan ba, wayar Deni da take xama a hannunta bata da shamaki da ita a yanxu dai ko kiransa akai baya bari ta miqo masa xai tashi ya dauka yayi waje, ya dena amsa waya a gabanta. Gaba daya Deni dai ya janca mata. Tagaji da wannan hali nasa ta xaunar dashi tayi masa magana akan hakan ta roqeshi akan in tamasa lefi yayi haquri.
Cikin rashin kulawa yace mata "babu komi just aikine yamun yawa a office" ya shiga bedroom ya barta. Tabi bayansa da kallon mamaki ta share yar kwallarta. Ta fara tuno rayuwarsu a baya lokacin da Deni baya da komi amma yana sonta yana tattalinta, yayi mata wanke wanke yayi mata shara yayi mata girki wanki gugarta duk Deni kemata, kai sada bra Deni ke wanke mata a rayuwarta xata iya cewa pant ne kawai bai wanke mata ba kuma shidinma dan tana wankeshi a wanka da tasan inta ajiye xai wanke mata. Deni baison yaga ko fuska ta canja yayi mata tausa, ya tsefe mata kai ya yanke mata farce amma yanxu Deni duk ya manta wannan soyayyar.
To abun tambayar anan wai dama abaya yana mata hakane don bashi da kudi kuma bashi da aikinyi yanxu kuma ya samu bashi da wannan tym din ko kuma yaudararta yake a baya? Ko kuma yanxu yayi kudi yaga bata dace dashi ba a matsayinta na matar ladar noma kamar yadda taji ana yawan fadar cewa matar talauci daban matan arxiqi daban yawanci indai kaci talauci da namiji inyayi arxiqi saiya auro maka yar tayin cin arxiqi? Waxai amsa mata wadannan tambayoyi.
Ta qara sautin kukanta tana nadamar wannan samun aiki na Deni saita gwammace xamansau a cikin talauci suci garin rogo su kwanta amma suna soyyarsu me shiga rai. Wannan aiki na Nura ya rabata da farin cikinta kuma ya kawo mata tarin matsaltsalu gabas da yamma kudu da arewa. Sai dai fatan Allah ya mata magani.
Washegari xai fita dan ta gwadashi tace masa "Dan Allah ya Deni ka tahomun da ayaba ina so naci" bai amsa ba yayi gaba ita a xatonta ma beji ba. Sai da ya dawo tana masa sannu da xuwa a gajarce yace mata "yawwa" ya dire mata ayaba a gabanta ya wuce ciki. Ta dubi jikinta kwalliyar da intayi Deni ke gigicewa ko kuma ya dauketa ya shigar da ita daki yau itace a jikinta amma Deni ko a fuska be nuna yagani ba.
Ta qara xage dantse wajen kwalliya da tsafta da kuma roqon Allah amma fa abun babu sauki kamar ana qarawa wuta iskar gas. Ita ba qawaba ita ba waya ba ta rasa yadda xata kanta taji sanyi sai dai kullum ta yini ta TV a kunne.
A nasa bangaren shima Deni ya rasa abunda ke damunsa, tabbas yasan baya kyautawa amma ya xaiyi shima haka ya samu kansa, sakeenarce gaba daya ta fice masa arai kamar battery din waya yana sauke caji haka kullum yakejin sakeena na kuma fita a ransa.
Ra'ayinsa na baya daya dade da gogewa a ransa wato na aurar mace yar gayu lamba daya, yanxu kam ya dawo sabo fil. Dan haka ya fara qawance da irin fala falan yan matannan da suke cuno baki suyi selfie asaka a social media. Dake shima ba baya bane wajen kyau da iya daukar gayu ga kuma yan canji da suka qara fito dashi shiyasa yan mata sukai masa caaa.
Sau tari yakan tambayi kansa wai meya ja raayinsa ixuwa auren sakeena duk da cewa ba class dinsa bace? Allah ya tuba badan kar yayi butulci ba da saiyace yana regretting aurenta.
Amma kuma yasan ko giyar wake yasha ko wace irin saqa xuciyarsa tai masa baxai iya rabuwa da sakeena naba saboda wasu dalilai.
Matar daya aureta bashi, babu lefe, babu kudin aure, matar da mahaifinsa ya danqa masa amanarta sannan tasha kwana da yunwa saboda shi matar da take yini aiki a gidaan masu kudi domin samar musu abunda xasuci ita dashi. Sannan abu na qarshe a dalilinta nema ya samu wannan aiki to shi kuwa inyasaki sakeena yasan be cika dan halak ba kuma da wane ido xai dubi Baba da Iya da kuma ita kanta sakeenan? Kai! Baxaima iya ba dole sakeena tacigaba da xama a matsayin matar halacci kuma ladar noma duk rintsi duk wahala domin be manta haliccinta ba a gareshi. Wannan dalili shine yasa ya kasa yiwa sakeena wulaqanci kamar yadda xuciyarsa ke tunxurashi yayi mata.
Kuma shi kansa bayajin dadin yanayin da yake ciki kullum xuciyarsa babu dadi ya rasa inda xaisa kansa ya samu sauqin quncin dake addabarsa.
****** ******* *********
Haka wannan xama nasu yacigaba salam babu sauki wai ciwon arne. Hankalin sakeena be gama tashiba sai ranar da abokan Deni sukaxo gidan Karo na farko tun aurensu suka yada xango a falo yayin da sakeena ke bedroom, tana xaton wani aikine ya kawosu domin taji Deni na tayi musu bayani su kuma suna tambayarsa abunda basu ganeba.
Can wani ya nemi a kawo masa ruwa xaisha Deni ya kwallah mata Kira tare da umartatta ta kawowa baqo ruwa. Ta yafo mayafi akan riga da xanin dake cikinta ta fito ta shiga jikin ta fasa pure water ta cika jug na glass ta dora cups ta dora a tray ta kai musu. Ta tsuguna ta gaishesu, duk suka xubo mata ido. Dayan wanda taji suna Kira da Mani ya dubi Deni yace "kai mutumina wannan fa daga ina?" Deni ba tare daya dubesu ba ya bashi amsa da "qanwata ce taxo jarrabawa ne" sakeena ta dago a raxane tana dubansa amma hankalinsa yana kan computer din gabansa. Hankalinta ya dawo kan Mani inda ya dafa kafadarta yace "sannu yan mata, meye sunanki? Jiki sanyaye tace "sakeenatu" yace "yawwa sakeena ya jarrabawar? In kingama kijirani xanxo inmadaki kano inyiwa Baba gaisuwa da neman iri" Deni yayi saurin cire hannun Mani a kafadar sakeena yana cewa "kaifa dan iska ne meye haka" direct Mani yace "nifa Nura naga matar aure kawai intaqare jarrabawar ku auran ita tayi karatun a gidana" Deni ya daka mata tsawar data katse mata mafarkita yace "ke da Allah shiga ciki kinxo kinsamu a gaba"
Ta kifa kan gado ta fashe da kukan baqin ciki. Ashe abun na Deni yakai haka? Ashe abun nasa ya wuce duk yadda take xato? Shin wai me taiwa Deni yake mata wannan hukunci? Wai yau Deni ke kunyar nunata a matsayin matarsa wanda hakan yasa wani banxa wanda ba muharraminta ba ya tabata tare da furta yana sonta a gabansa.
Ta tuno a baya lokacin da Ahlan ya nuna hakan akanta ta tuno yaqin da akai da Deni akan hakan amma yanxu ko ajikinsa.
Tabbas yanxu Deni baya sonta baya buqatarta a rayuwarsa, a wancan lokacin Deni duk inda ya xauna sai yayi xancen matansa amma yau duniya me yayi itane yake kunyar nunawa a matsayin matar tasa. Lallai ya cika mayaudari wanda yayi amfani da damarsa ya yaudareta daga baya ya watsar da ita.
Koda lokacin bacci yayi haka suka kwanta ita tana kallon yammma shi kuma yana kallon gabas. Ranta cikin quna yayin dashi kuma yaketa chatting da yan matansa.
Da safe ta tashi ido jajur saboda tayi kwanan kuka da kuma ciwon ido. Tana falo ya fito cikin shirin office yasha dark blue suit yayi kyau sajen fuskarsa ya kwanta luf ya kuma haske ya cika sosai ya xama namiji cikakke giant wanda yan mata masu budadden ido ke nema ruwa a jallo. Ta qura masa ido cikin yaba kyau da tsari iri na Deni. Tana sonsa tana qaunarsa har yanxu babu abunda ya ragu na soyayyarsa a ranta saima qaruwa da yayi. Ya shigeta ya fice ya bar mata qamshinsa, da so samu ne da kwanciya takeso tayi a jikinsa ta fada masa damuwarta don bata da aminin da yakaishi a duk fadin duniya.
Tayi kwalliyarta me kyau (amma fa a ganinta 😆) ta cakare ta xauna a falo tana jiran dawowar Deni. Tayi sa a ko rabin awa batai da xama ba ya shigo, ta tashi da gudu ta rungumeshi tana sinsinar jikinsa. Yadan bubbuga bayanta kafin ya cireta jikinsa ya shige uwar daki.
Bayan sallar isha ma daya dawo masjid haka tayi qarfin halin haye masa cinyarsa ta kwantar da kai a qirjinsa abunda ta dade bata samu ba. Yana ta danna waya be kulata ba har ta fara bacci, can taji ankirashi ya xameta a qasa ya fita can waje amsa wayar. Tana xaune gurin tana jiran dawowarsa, sai dai me? Tun tana irga mintuna ya gama wayar ya dawo har aka shude awa yana waje yana waya.
Jiki a salube ta shige bedroom ta kwanta, tayi xunbur ta tashi tana kallon kanta a madubi. Tayi duba na tsanaki sai ta ganta tayi wani muxu muxu ta xube sosai ta fita hayyacinta babu komi jikinta sai farar fata fuskarta kuwa daga dogon hanci sai manyan idanuwa. Kwalliyar datai ma sai taga sam batai masa kyau ba. Tabbas dole Deni ya gujeta yanxu don babu yadda xa ai ahadashi da ita a bangaren gayu da kuma aji. Bama wannan kawai ba komai na rayuwa Deni ya fita ko acan baya bare kuma yanxu don haka bashi da lefi dan yaqi nunata a matsayin matarsa. Anci moriyar ganga inji hausawa.
Ashe dama da gaskene da ake cewa in mutum ya sake ya auri wanda ya fishi komi na rayuwa rainashi yakeyi? To ita dai yau taga tabbas a gurin Deni, amma meyasa tun abaya batai wannan tunanin ba sai yanxu da lokaci ya qure mata?
Ta laluba xuciyarta ta samu soyayyar Deni danqam aciki ko gixau bataiba balle tayi tunanin xata raba kanta da ita. Meyasa Deni yayi mata haka? Meyasa ya yaudareta sai data gama aminta dashi sannan ya barta da soyayyarsa ya juya mata baya? Kodan bata da gata ne? Kodan ya aureta a arha ne bai wahala kafin auren ba? Wannan dare a haka sakeena tai bacci cike da kewa da kuma soyayyar mijinta Deni wanda yayi mata nisa yanxu.
***** ***** *************
Sun dauki yan satittika a haka cikin wannan xama marar fasali, babu duka, babu zagi, babu cin mutunci ko wulaqanci babu rashin abinci ko wahala amma fa akwai dan karen halin ko inkula qiri qiri Deni yace mata Dan Allah ta rage damunsa inda hali yafiso tayi rayuwarta yayi tasa. Hakan kuwa akai ta tattarashi ta ajiye ta rungumi tashi tsakiyar dare tayi adduointa ta kaiwa Allah kukanta.
Daga qarshe ma dai saiya koma kwanan falo ya bar mata bedroom din, wannan abu yayi mutuqar daga mata hankali duniya kenan wai yau Deni da kansa ya raba musu makwanci? Ya samu chance sosai a kasancewarsa shi kadai inda yake raba dare yana hira da yan matan da basusan ciwon kansu ba ko kuma ince wadanda kamun kai yayi musu qaranci, domin duk macen daxata xauna tana chatting da mijin daba nata ba har tsakiyar dare tofa wlh tayiwa kanta illah kuma tabbas ba kamun kai a gurinta don daga raba daren nan hirar batsa xata fara shiga tsakaninku wanda daga haka kin barar da mutuncinki a gurinsa ko aure xaiyi tofa baxai aureki ba ko jiyayi wani xai aureki shine xai fara bada shedar cewa baki da kamun kai. Kuma in kinada hankali ai xakiga kin shiga rayuwar auren wata kina cuxguna mata domin shi dare Allah ya kebanceshi ga iyalai. Dadin da dawa kemafa watarana matar aure ne sai ki auna inke wata tasamu mijinki a waje tana masa haka ta hanashi lokacinki xakiji dadi? Tofa kisani abunda kayi wlh sai anyi maka duk wayonka duk dabararka. (qalubalenku yan mata masu irin haka, domin yanxu ta wannan hanya kuna bada muguwar gudummawar tarwatsa gidajen aure. Allah ya shiryemu amin)
To shima dai Nura yabi sahun takwarorinsa maxa masu irin wannan dabia, ya fara hirar banxa da yan matan banxa duk kuwa da cewa ba halinsa bane hakan a wasu lokutan yan matan da suka fishi wayewa a wannan fanni har pics suke dauka na nuna tsaraici kona shigar banxa su tura masa. Yayin da ya hana tasa matar riqe waya saboda yana gudun kar tayi abunda yake. Ita dai baiwar Allah ta miqa lamarinta ga Allah kuma tayi imanin xai mata magani tunda yace "ku roqeni xan amsa muku"
Ranar Sunday yana xaune falo yana sanaar wato chatting ta fito ta tsuguna gefe tai masa sannu da gida. Ya dubeta a gajarce ya amsa kafin ya maida dubansa kan wayarsa. Ta qara qasa da murya tace "ya Deni Dan Allah waya xaka aramun xan kira Iya kwana biyu bata nemeni ba" a kaikaice ya dubeta yace "tunda bata nemeki ba ke meye naki na nemanta, qarata xaki kai kenan?" hankali kwance ta dubeshi tace "kwanayin wani abune wanda ba dai dai ba har kake ganin xankai qararka saboda shi?" yadan diririce jin ta yarfa masa magana cikin sauri yace "ke! xaki fara wannan xancen naki na xarwance ungo nakira miki ita tsaya anan ku gama wayar ki bani wayata" ya fada yana miqa mata wayar.
Sallamar Iya cikin kunnuwanta ya hanata bashi amsa tace "Wls Iya kin manta dani wajen sati biyu baki nemeni ba" tace "wayyo sakeena yi haquri kinji yar albarka kina raina wlh nadanyi jinya ne saboda kar indaga miki hankali shiyasa ban fada muku ba amma yanxu na warke" sakeena tace "Allah sarki Iya ta Allah ya qara sauki ai na kusa xuwa Kano in shaa Allah, wajen wata 5 ban ganki ba ai nayi kokari ko?" tace "kinyi diyata Allah ya kawoki nima inaso in kangi, ga Baba a kusa ku gaisa" ya karba sukai hira cikin farin ciki. Ta samu kanta cikin nishadi sosai wajen 19 minutes suna hira sai da taji Deni ya fara tsaki sannan ta katse hirar da tambayar Iya da cewa me takeso ta siyo mata inxataxo? Iya ta bata amsa dacewa "Duk abunda kikawomun sakeena inaso amma fa ganinki ya fiyemun duk abunda xaki kawo" tace "to ki fara share hanya inanan qarshen watannan in Allah ya yadda" sukai sallama ta miqa masa wayar ta koma kicin.
Tana girki tana tunani da kuma farin cikin jin muryar Iya da Baba. In banda abun Deni meye nasa na tunanin xatakai qararsa? Intakai qarar maganin me hakan xatai mata? Amsar itace babu sai dai ma ta dagawa Iya da Baba hankali, Hajjo kuma da tawagarta suyi murnar cinta da yaqi. Ta daura aniyar cigaba da ruqe sirrin aurenta da juriya da kuma addua har randa Allah xai yaye mata.
Ranar laraba ta tashi da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun ran Monday yake damunta tana daurewa amma yau yaci qarfinta, kasancewar bata taba ciwon mara ba a rayuwarta sai wannan karon yasa ta jigata dakyar tai wanka ta dawo ta kwanta da daurin qirji. Ya kamata ace Deni yasan bata da lfy tun jiya saboda ko girkin dare batai ba haka ma na safe amma dan tsabar rashin kulawa be gane ba ko kuma ya gane bashi da lokacin kulawa da itane oho.
da wuri ya dawo ana idar da sallah laasar. Yaga falon a yadda ya fita ya barshi tun jiya ba a share ba bare gogeshi. Ya shiga bedroom din da nufin tambayarta baasi ya taddata tana ta murqususu a kan gado cikin azabar ciwo. Tausayinta ya kamashi dan betaba gani tayi ciwon data jigata haka ba. Ya kamota yana tambayarta meke damunta cikin dauriya tace mararta ke ciwo tun jiya.
Da sauri ya debo mata kaya ya ajiye mata yace "daure kisa bari inje insamo napep muje asibiti" ya fice da sauri. Itama tai qarfin halin tashi ta xura kayan tasa hijab ta koma ta kwanta tana jiransa.
Wajen 5:00 pm sai gashi da sauri ya kamota ta miqe yana riqe da ita suka fito yana cewa "kinga ma bansamu napep dinba sunqi biyoni ciki sai motar abokin aikina na aro, Allah ya hore insai mota kodan irin wannan." tace "amin" taji tasamu sauki a dabiance saboda kulawar daya nuna mata, yaushe rabon da taga haka daga Deni? Yaushe rabon da hannunsa ya taba fatar jikinta?
Wani private hospital sukaje nawani consultant a fannin mata. Babu wani layi saboda yawanci yafi xama da daddare to sudai sun taki sa a xuwansa kenan sukaje kuma sune na 3 a layi. Yana riqe da ita har akaxo kansu suka shiga.
Yana xaune Dr din ya fara manyanta suka xauna kan kujerun da suke gaban table din guda biyu. Suka gaisa ya tambayeta meke damunta a taqaice tace masa ciwon mara. Ya kuma tambayanta yaushe rabonta da period tace anjima sosai. Ya qura mata ido yace "kina da aure?" Deni yace "eh matatace" likitan ya kuma kallon ta cikin xargi yace "inda wani abun ki fada bayan wannan saboda musan maganin da xamu baki da kuma shawara" cikin hardewar baki da tsoro tace babu.
Ya danna bell wata likita ta shigo sanye da lapcoat ya fada mata wasu kalmomi da tests ta yarensu na likitoci yace aje aiwa sakeena su. Ta amsa suka tafi da sakeena ya bawa Deni takaddar biyan kudi yace yaje ya biya charges din su jira a waje result ya fito.
Aka gama yiwa sakeena kwajin ta fito tanabin bango Deni ya tarota suka xauna jiran result yayin da gabanta ke wata faduwa, azabar ciwo bata hanata adduar Allah ya rufa mata asiri ba.
Kimanin rabin awa likitan taxo ta kirasu office din likitan farko. Suka xauna tai qasa da kanta gabanta na dukan tara tara.
Ya gama naxarin result din ya dubi sakeena kana yace "sakamakon yin allurar family planning da kikai ba bisa qa'ida ba hakan ya haifar miki da daukewar al ada na tsawon lokaci wanda hakan ya farune saboda rufe kofar mahaifarki da wannan sinadaran allura sukai. Dan haka yanxu xa ai miki allurai guda biyu da kuma wannan maganin wanda xaki shanyeshi duka inkinci kin qoshi sosai. In sun karbi jikinki xaki iya samun dawowar al adarki nan da dan lokaci kadan inkuma bata dawo ba xaki dawo muga abunyi" gumi ya shiga yankowa sakeena jin yaufa abunda ta boyewa Deni asiri ya tonu. Shi kuwa Deni kallon ta yake cikin matuqar kidima da gigita anya kuwa likitan nan result din sakeena yake karantawa? Sakeena ce tai allurar planning ba bisa qaida ba? Koda yake da qamshin gaskiya tunda bata musa ba kuma alamun rashin gaskiya ya bayyana qarara gareta.
Maganar likita ta katse masa tunani inda yake musu nasiha da jan kunne akan yin tsarin iyali ba bisa qaida ba ko neman shawarar masana. Deni ne yayi qarfin halin yi masa godiya suka tashi ya kira nurse taje da sakeena tai mata allurai biyu da wani magani guda daya tal a kwali.
Suna tafiya a hanya yanajan mota yana tunani yayin da sakeena tasa kuka don batasan irin hukuncin da Nura xai mata ba. Kukanta shi ya tabbatar masa da maganar likita gaskiya ce. Ya fada kogin tunani, to wai yaushe sakeena tayi wayewar da xata xage taje ai mata planning bada saninsa ba? Yaushe akai mata planning din kuma a ina waya bata shawarar? Lallai ta raina masa hankali ashe duk wannan abunda ake tasan abunda ta qullah shi ta maida sakarai. Ashe shine wawa sakarai ba sakeena ba tunda harta iya haintarsa yananan uwarsa tana mata gorin haihuwa yana tare mata ashe itace ta yaqi haihuwar da kanta. A fili ya furta "sannu sakeena kura da fatar akuya" ta qara fashe da kuka. Ya tsaki yace "ki adana hawayenki muje gida munafuka yau Allah ya toni asirinki maha inciya me haintar mijinta. Yau xaki fadamun wanda ya nuna miki inda ake xuwa yin planning dan wannan ba idea dinki bace saki akai a hanya"
Ya tsaya a hanya ya sayi gasashshan nama da L&Z milk suka nufi gida. Ta rigashi shiga gidan saboda ya tsaya maida motar daya aro.
Tasamu guri kan kujera ta xauna tana kukanta tuni ta daina jin ciwon saboda tashin hankali. Ya shigo ya ajiye ledar a gabanta yace "ci kisha magani" tasa gwiwarta qasa ta fara bashi haquri yayi saurin katseta yace "a a karki soma abinci kawai nace kici, badai har kinsan kiyi abu bansani ba? Yaushe kikai wannan wayewar" xata qara magana ya daka mata tsawa tayi shiru ta fara tusa naman tana kurbar madarar, shi kuma ya xauna kujerar dake kallon ta yayi tagumi yana mata kallon mamaki. Ta katse masa tunani da cewa "naqoshi" ya miqa mata kwalin maganin ta ballah ta hadiye.
Ya dawo kan center table ya xauna gwiwarsu na taba juna ya matseta sosai cikin nutsuwa yace "Sakeena waye ya sakaki kiyi planning?" tana hawaye tace "babu kowa" ya qara maimaita tambayar tai shirue
tana shashsheqa. Ya qura mata ido yace "Hassana da Usainane yayan Alh Dalhatu ko?" da sauri ta girgixa kai ya daka mata wata irin tsawa yace "to uban waye inba suba?" ta fara ja da baya dan taga ya xuciya.
Ya kamota ya qara dangwarar da ita a gabansa yace "wlh inkinason kanki da lfy ki fadamun gaskiya" cikin qinqina tace "Hajjo ce ranar xuwana gida na farko da aurenmu tasa Hadixa ta rakani gurin wata qawarta me aikin asibiti taimun, tace inna haihu a lokacin baka da halin daukar dawainiyar mu ni da Dan" cikin Al ajabi Deni ke kallon ta har tagama fada masa.
Ya riqe kansa da hannu biyu yana maimaita "Innaillahi wainna ilaihi rajuun" ya dade a haka kafin ya tashi ya fita waje lokacin har an idar da sallar magrib.
Itama ta dade a xaune kafin taje tai alwala tayi sallah tare da roqon sauki gurin Allah.
Tana gurin har akai isha tayi hadi da shafai wal wutir. wajen 8:30pm ya shigo kamar be ganta ba ya shige bedroom. Ta dan jima a xaune kafin xuciyarta ta bata shawarar taje ta bashi haquri. Ta miqe tana rabe rabe ta shiga bedroom din. Ta sameshi kwance kan gado ko takalmi be cireba yana kallon silin da alama yayi xurfi cikin tunani. Ta hau gadon a hankali ta kamo hannunsa daya dafe goshinsa dashi, ya tashi a xabure ya fusge hannunsa ya nunata yana cewa "a a sakeena karki kuskura ki qara kai hannunki jikina tunda kin isa da kanki har asakaki abu kiyi ba tare da kin fadamun ba duk da cewar abun ni da ke ya shafa." ta hade hannyenta biyu ta fara bashi haquri, ya katseta da cewa "a a bakimun komi ba kanki kikaiwa ni ko yanxu naga dama xan iya aure kuma in haihu da ikon Allah kefa? Kin bata mahaifarki"
Ta fashe da kuka mecin xuciya tace "wlh yaya Deni nace xan fada maka ka kaini asibiti da kanka tace ai bataso kasani shiyasa bata tareka da xancen ba kuma tace indai nabari wani yaji xancen bayanni da ita sai tasa ka sakeni" ya juyo da sauri yana kallon sakeena wacce ta kifa kai tana kuka bayan ta gama fadar haka.
Lallai Hajjo ta cika azzaluma mayaudariya meyin zamba cikin aminci. Tai amfani da qarancin shekarun sakeena da kuma makauniyar soyayyar da sakeena ke masa ta rabata da haihuwa da danta,(Deni)sannan ta tsoratar da ita ta hanyar hanata fada kana daga baya abu mafi ciwo itace wacce ta fara aibata sakeena da kiranta juya duk da kuwa itace ta maidata juyar qarfi da yaji. Wai meyasa Hajjo ke haka? Wai Hajjo wace irin uwace da take tarwartsa rayuwar auren danta? Baqin ciki yayi masa yawa ya rasa yadda xaisa kansa yaji sanyi ya miqe ya fita. Ko 5 minutes beba ya dawo da kwallin taba, ya xari guda daya ya kwanta ya kunnata ya fara xuqa.
Warin sigari yasa sakeena ta dago tai arba da Deni yana xuqa yana fesar da hayaqin. Tace "subhanallahi" ta dafe qirji tace "ya Deni sigari yau kai da kanka kakesha?" ta yunqura xata kwace yasa qafa ya hanbararta ta fada qasan gadon yace "ki kyaleni tunda anhada kai dake anaso aga bayana, kunsamun baqin ciki kun quntatamun rayuwa" ta riqe bayanta inda ya amsa sabida faduwar da tayi dashi. Shima ko rabi besha ba tari ya turniqeshi saboda be taba shaba dole ya kasheta ya juya ya kwanta rub da ciki cikin rashin sanin abunyi.
Suna wannan hali aka fara bugun qofa, ta dubi agogo kusan 9:30 to waye yake bugu yanxu? Ya tashi yana hada hanya yaje ya bude. Ya waro ido yana mata kallon mamaki, itace ko kuwa gixo tai masa? Yanxu a dai dai wannan lokaci to meya kawota? Da sakeena tana da waya da saiyace itace ta kirata. Hajjo ce da fagon kayanta a hannu a buhun bacco.
Ya tare hanya cikin fita hayyaci da matsanancin bacin rai yace "meya kawoki? Ko kinxone ki qarasa kashe rayuwata da hainci? Meyasa bakya qaunata bakya qaunar farinciki na?" ta waro ido tana masa duban mamaki tace "Deni ka ganeni kuwa? Ni kake fadawa haka? Ko kasha wani abun ne?"
Yayi dariya yace "naganeki mana Hajjo ce wacce ke amsa sunan mahaifiya a gurina. Kuma tabbas nasha wani abu, sigari ce nasha ba haka kikeso ba? Itama dayar data nemi hanani sha gata can nai mata qafa ta kasa tashi" ya juya ya koma bedroom yabar Hajjo da tafa hannu da salati tana cewa "Allah ya isa tsakanina dake sakeena kin cuceni kin koyawa dana shaye shaye." tana xaune tana ta hawayenta kafun ta ankara da qullin nama da madarar da sakeena ta rage daxu akan table ta janyo tahau ci dama yunwa takeji kuma taga alamar gidan babu lfy gara ta samarwa kanta abinci kafin kwayar da Deni yasha ta sakeshi ayi wacce xa ai don tagaji da kashe kudi babu biyan buqata gara ta fito fili ta fadawa Deni ya saki sakeena tunda bata haihuwa kota tsine masa. Ta qulle falon tayo alwala ta dungura sallolin da ake binta ta kashe fiilar falon ta kwanta tana cewa "ai sakeena yau ko aurenki ya kwana a raye shaa Allahu baxai yini a raye ba." da wannan tunani tayi bacci.
Acan kuma Deni ya koma bedroom ya kwanta, sakeena ta gama jinyar buguwar da tayi a baya ta lallaba haura kan gadon ta kwanta. Tana kwanciya ya juyo ya daka mata tsawa da cewa ta fita daga dakin. Ta saka kuka tana bashi haquri. Yasa hannunsa a baki yace "shiii yimun shiru tashi ki fita falo ga abokiyar burminki can taxo kuje ku ida qullah abunda kukai niyya tunda keta haifa ba niba shiyasa kikabi umarninta saboda itace ta biya sadakinki ko?" ta qara sautin kukanta.
Ya miqe tsaye ya ciro charger din laptop dinsa cikin hargagi yace "wlh sakeena inbaki bar dakin nan ba a daren nan saina miki walmukalafatu (sassabawar kamanni 😆)" tai saurin dirowa a gadon ta fito.
Hajjo da hargagin Deni ya tasheta daga Dan baccin data soma ta kasa kunne taji lokacin da yake cewa zai doketa inbata fita ba. Tai tsallen murna tace "Masha Allah haquri me tadda rabo ashe sunayin fadan gara da naxo naga dahir" ta koma ta kwanta.
Sakeena ta fito da gudu ya banko kofar yasa Key, taxo ta kwanta akan tiles ta takure. Sam bata lura da mutum akan kujera ba saboda duhun falon. Hajjo tana kallon ta ta cikin mayafi tana dariya.
Da asubar fari ta tashi tai wanka tasamu kanta cikin jini tayi hamdalar dawowar al adarta maganin ya karbeta kenan kamar yadda likita yace. Bata da pad ko guda daya sai dankwalin tsohon kayanta ta nada tayi qunxugu dashi. Ta shiga kicin ta dora breakfast ta fito suka gaisa da Hajjo ta amsa fuska sake dan ta lura ba xaman dadi suke ba ga tanan duk ta rame ta kade.
7:00 AM dai dai ya fito rataye da jaka cikin shirin fita. Sakeena tai saurin fitowa daga kicin tace "yaya ina kwana, nagama breakfast inkawo maka?" Ko kallonta baiyiba balle tasa rai zai amsa mata. Ta koma kicin da nufin ta hado masa a flask ya tafi dashi.
Hajjo tai murmushin cin nasara, gaisuwar Deni ta katseta ta amsa tana "tambayarsa me akai jiya tajiyoshi yana ihu?" bai bata amsa ba, sai damin kudi daya ciro a Jakarsa ya kamo hannunta ya dora mata yace "Hajjo gashi nasan abunda ya kawoki kenan, to gashi na baki. Amma ina roqon alfarma da ki daina xuwa gidana domin hakan na qara sani cikin qunci, ke mahaifiyatace ba yadda xanyi dake kuma banaso inyi abunda xaisa kiyi fushi dani. Kudi sune matsalarki to ki xauna a inda kike ko bakixo ba xan dunga aiko miki dasu. Amma plz kiyi nesa da rayuwarmu ni da matata" Hajjo tai sakato tana sauraran Deni yana fada abunda bata taba xato ba koda a mafarki. Ta farka lokacin da ya saki hannunta ya miqe xai fita. Ta dauki kururwa da sallami tare da cewa "shikenan sakeena ta raba ni da gudan jinina shikenan yau Nura ya koreni a gidansa kamar yadda ya kori yan uwansa uwa daya uba daya" yasa kai ya fita daga falon sakeena ta fito a kicin da gudu hannunta dauke da food flask ta bishi harabar gidan wanda yasa mata dokar karta fito saboda maxa. Ta miqa masa ya kauce xai wuceta, tai saurin tsugunawa ta kama kafarsa ta riqe tace" Yaya Nuraddeen kayi haquri nayi kuskuren boye maka abu biyu wato xancen Ahlan da na Hajjo amma in shaa Allah nayi alqawari baxanyi na uku ba, baxan qara boye maka komai ba. kayi haquri ka yafemun na tuba karka fita kana fushi dani bakasan abunda Allah xaiyi ba. fushinka bala ine gareni kayi haquri ka yafemun"
Kalaman sakeena sukaxowa Nura da wani irin yanayi da kuma sauyi. jikinsa yayi sanyi qalau kamar yadda yaji soyayyar ta ta xama sabuwa fil a xuciyarsa. wai meye lefin wannan yarinyar ne da suke wahalar da rayuwarta shi da uwarsa da yan uwansa? Meyasa suke wasa da rayuwar marainiyar yarinyar nan? Ya tuno tun farkon xuwan sakeena gidansu da irin yadda ta dunga aikin qarfi domin ragewa mahaifinsu wahala duk da bai haifeta ba. Amma duk cikin yayan da Baba ya haifa babu wanda ya temaka masa kamar sakeena. Ya tuno kalaman sakeena lokacin da Babansa ya aura masa ita, tunkan tasan shi aka aura mata ta miqa wuya taiwa Baba tausasan kalamai wanda yasan da ace qannansane wato yayan da Baba ya haifa yayiwa irin auren da yayiwa sakeena da abune mawuyaci suyi masa biyayya.
Yakai kallonsa gareta tana tsugune riqe da qafarsa tana hawaye. Ya tuno abunda yake mata a kwanakin nan, meyasa yayi mata haka? Yasa hannu ya dagota idonsa cike da soyayyarta ya share mata hawaye yace "ya isa dena kuka kinji, kema kiyi haquri nasaki kuka. Inna dawo xamuyi magana akan rayuwar aurenmu a nutse, kiyimun dan wake da zobo drink kinji baby" tana murmushi tace "to ya Deni nima ka siyomun pad jinin yaxo daxu da asuba" yaja hancinta yace "kice mun kusa samun Baby?" tana murmushin jin kunya tace "in shaa Allahu ya Deni" ta miqa masa flask din breakfast din ya karba ya sumbaci goshinta ya juya ya tafi suna dagawa juna hannu.
Ta nufi cikin gida cikin wani irin farin cikin dawowar Deni da soyayyarsa rayuwarta. Hajjo tai saurin komawa ta xauna daga leqensu da takeyi. Tabi sakeena da kallo harta shige bedroom. Ta jinjina kai lallai sakeena ta cita da yaqi, meta fadawa Deni haka harya hanata xuwa gidansa ita kuma ta bishi waje suka soye. Meyasa jiya taji suna fada amma yanxu har sun dinke? Wai meyasa duk wani tanadi da tayi kuma takeyi don rabasu har yanxu ta kasa cimma burinta? Ta saka kukan baqin ciki wai yau ita Deni ya kora yace tai nesa da rayuwar aurensa? Wai yau sakeenan data raina ta gagareta ta rabata da Deni qiri qiri. Ta share hawaye tace a xuciyarta "wlh sakeena kinyi kadan lokaci yayi da yakamata indaina kuka akanki, ya xama dole insan abunyi ayau kuma a yanxu inyaso duk abunda xai faru ya faru. Nayi makircin beyi ba, nabi ta qarqashin qasa beyiba. To yanxu da kwanjina xanyi inyaso duk abunda xai faru ya faru"
Sakeena ta fara gyaran daki cikin matsanancin farin ciki, ta gama taje kicin ta hadowa Hajjo breakfast a tray ta kai mata inda take xaune falo. Ita kam farin ciki yasa ko yunwar bataji, ta fara gyara kicin din.
Acan falo Hajjo ta duba agogo kimanin awa daya da rabi da fitar Deni ta tabbatar duk inda yake yanxu yana office. Ta shiga kicin tace dakko muciya ta rafkawa sakeena a gadon baya, ta gantsare tare da cewa "wash wayyo bayana" tayo falo da gudu tana kallon Hajjo a raxane tace "Hajjo menai miki?" xuciya a bushe Hajjo tace "ubanki kikaimun, inkinason kanki da lfy sakeena ki fice daga gidan dana kiyi naki guri inyaxo xansashi dole ya biyoki ta takaddar saki." sakeena ta xaro ido tace "Hajjo kiyi haquri baxan fita ba don bantaba fita bada ixinin mijina ba" ta qara daga muciya ta sauke mata a gwiwar hannu tace "To tsaya karki fita in kasheki da duka. Ni uwar mijinki nace ki fita ki tafi"
Ala dole sakeena ta miqe tai waje don taga Hajjo tabbas so take ta kasheta da duka kamar yadda tace. ta tsaya a waje Hajjo ta koma ciki ta dakko mata hijabi da silifas a kofar toilet ta watsa mata tace "maxa a tafi" Sakeena tasa hijab ta samu guri ta xauna Hajjo ta qara biyota da muciya ta kwasa da gudu har xuwa gate din gidan.
Megadin gurin ya tashi yana kallon su yace "ashsha yi haquri Hajiya yaran yanxu sai da haquri inka daka ta xuciya sai illatasu da duka" Hajjo tasa kukan munafurci tace "ba yata bace matar danace, na kamata tanasamun guba a abinci nai mata nasiha akan abunda tayi shine ta dakko wuqa xata kashe ni shiyasa na korota a gidan" ya bude baki yana duban sakeena kafin yace "ai saiki bari Dan naki yaxo yayi muku sharia har xuwa kotu dan wannan babban lamarine " ta qara fashe da kuka tace "ai ta mallakeshi ita xai goyi baya"
Megadi ya Kalli sakeena cikin kyama yace "fice daganan muguwa me fuskar salihai" xatai magana ya hanata ta kalli Hajjo tace "to Dan Allah ki bari in dauki kudin motar xuwa Kano in tafi" ko kallon ta Hajjo bata qarayiba ta juya ta koma ciki cike da farin cikin cimma buri. Shima megadi ya xauna yana sauraren radio, can dai ya dakko hamsin ya wullawa sakeena yace "ga sadakanan muguwa."
Tadau hamsin din ta tari napep ta roqi alfarma ya kaita tasha.
Acan tasha ta samu motar kano tayi lodi saura qiris ta cika tace da kandastan "Dan Allah malam inshiga ka kaini kano amma bani da kudi a hannu in munje xaka kaini har gida Babana ya baka kudinka" ya sheqe da dariya irin ta yan tasha yace "Allah ko? saboda ke kika saimun motar? Jira anan Allah ya kawo wanda xai kaiki Dan daganinki ma guduwa xakiyi daga gaban iyayenki."
Ta matsa a tsorace take sosai saboda wannan ne karon farko dataxo irin wannan gurin ita kadai. A taqaice dai sai data tare mota 4 tana musu bayani kamar na farkon amma babu wanda ya saurareta. Ta rasa yadda xatai ga rana ta farayi tana gudun kartayi dare ta kasa gane gida ko sunje kano.
Can wata mata dake lura da sakeena ta madubin motar datake ciki daga wajen tashar kadan ta fito taxo kusa da sakeena ta xauna, tai saurin gaisheta ta amsa. Fuskarta jajur taci bleaching ga kalangu a fuskartata kallo daya xaka mata kasan cewar shahararriyar yar duniya ce. Ta dafa kafadar sakeena tace "ya sunanki yan mata? ta bata amsa da "sakeena" tace "ina xaki diyata?" sakeena tace "kano amma bani da kudin mota Dan Allah ki temaka ki bani" tace "kwantar da hankalinki har kano xan kaiki nima can na nufa kinga motata can a waje taso muje aida na kowane" sakeena tai godiya ta miqe tace "amma hajiya inkina always ki bani ta jikina ta jiqe karna bata miki mota" tace "bani da always amma tsaya ina xuwa"
Sakeena na tsaye matar taje ta dawo ta miqawa sakeena pampers tace "sa wannan tunda tafiya xamuyi" tai godiya ta rakata bandakin cikin tasha ta biya mata kudi ta shiga ta canja ta fito taji dadin jikinta ta kuma yiwa Hajiya godia kuma ta aminta da ita saboda wannan temako.
Suka tsaya gurin abinci ta saiwa sakeena shinkafa da miya da hadin salad da maltina aka saka mata a leda suka nufi wajen tasha gurin da motar ke fake suka shiga da maxa biyu a gaba sai sakeena da Hajiya a baya. tace da mejan motar "to muje" ya kalleta ta madubi yace "can din ko?" tace "eh" ya kunnah motar suka dau hanya. Sakeena kuma ta bude abincinta ta faraci hankali kwance.
Hlo readers, xaku jini shiru kwana 7 muna bikine. Nagode
Masu bina inbox suna cewa in turo musu Dan Allah su bari kar mutum yaga na masa wulaqanci bani da lokacin turawa ta private innatura gprs shikenan in kinyi missing wata ta tura miki.
Hajia ☺
[7/31, 2:19 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣6⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Hajjo ta koma gida ta miqe a cikin kwanciyar hankali tayi karin kumallo, ta gama takai kayan kicin, Ta tsaya ta qarewa kicin din kallo tana adduar Allah ya bawa su Hadixa wanda yafi wannan. Ta fara bincike harta dire cikin fridge, ta zaqulo frozen chicken tana cewa "shegiya marowaciya ji kaji kamar suyi magana amma kota soya ta dunga aikamun, duk da bakusa bane aiko ta tasha ta turamun" ta narkasu ta yayyanka ta badesu da curry da kayan qamshi da Maggie tasa albasa ta dora, amma sai dai kunna gas ya gagareta babu yadda bataiba ta kasa ala dole ta haqura ta maidasu fridge ta dawo falo ta xauna tana kallon dole.
Har lokacin sallar azahar yayi ta tashi tayi wanka tayo alwala tayi sallah ta farajin yunwa amma dole ta haqura tasha lemon data gani a fridge da bread tunda bata iya kunna gas ba.
Ta dawo ta kwanta sam bata qoshi ba don tasaba dakin 😄
Can office kuma Deni ya yini aiki da tunanin sakeena yayi duba sosai na tsanaki ya dorawa kansa lefi duk abunda Hajjo taiwa sakeena shiya bada kofa tunda ya samu aikin nan ya lura sakeena tayi bankwana da jin dadin aure, ya tattara hankalinsa gaba daya ya koma kan waya yana daka ta sharrin social media yana quntatawa yarinyar da aka danqa masa a manarta kuma yayi alqawari xai riqe.
Ya dunga tsara kalaman da xaimata magana dasu inya koma na zallar soyayyar gaskiya da ban haquri. Ana tashi office ya wuce shopping mall ya saiwa sakeena pad din da tace da kuma turare masu dadi sai set din kayan wanka na lux, ya sayi wani kyakykyawan kati me dauke da kalaman ban haquri, katin yana hade da wata flower a tsakiya tanata qamshi. Ya nufi gida.
Yana sallama falo da Hajjo ya fara arba, duk da beji dadin ganinta ba domin a xatonsa ta tafi kano kamar yadda yace mata, ya tsuguna ya gaisheta ta amsa tana qurawa ledar hannunsa kallo. Ya tashi ya shige ciki dan yasan sakeena bataji shigowarsa ba da tuni ta fito taryarsa kuma yasan xuwan Hajjo ya takurata shiyasa be taddata a falo ba. Sai dai me? Yaje bedroom, kicin harda toilet ya duba babu sakeena. Hajjo na kallonsa ta wutsiyar ido tana cewa aranta "ka gama leqenta inkaga batanan ai dole kaban ledar hannunka nasan yanxu ai ta tsufa a Kano"
Yaxo ya tsaya hankali a tashe yace "Hajjo ina sakeena?" tai tsaki tace "Aida tun farko ka tambayeni da baka tsaya wannan xaryar banxar ba. To ta fita, kana fita itama tasa qafa ta fita" ya xauna ragwaf kusa da Hajjo yace "Ba gaskiya bane wannan, sakeena baxata taba fita bada ixinina ba, ko sanda muke kano da take da gurin xuwa bata fita babu ixinina ba bare anan da batasan kowa ba?" Hajjo ta dau salati da cewa "To nayi maka qarya Nura, karfa ka manta nifa uwace a gurinka" ya tashi ya fita da sauri a nufinsa ya shishshiga gidajen dake cikin quarters din kota shiga sai kuma yayi tunanin ai yawanci lokacin basanan wasu matansu suna aiki wasu makaranta kuma a yadda yasan sakeena baxata shiga gurinsu ba tunda bata sansu ba.
Ya dawo cikin gida xai dauki wayarsa, cikin xuciyarsa yana nadamar hana sakeena waya da yayi da yanxu abun bekai hakaba. Ya tarar da Hajjo ta dakko ledar daya tabbatar a bedroom ya batta ta bude dukta fito da kayan daya siyo ta dauki saitin mai tana cewa "wannan kam na daukarwa Amina, yar banxa kullum dama cikin sakani siyan mai take. Wannan audugar matan kuma da turare na bawa Hadixa ita fiddausi yanxu Musa yana semata nima ai anragemun wahala" takaici ya rufeshi ya shige uwar daki ya dakko wayarsa daya saka caji ya rasa waxai kira kuma kansa ya kulle.
Ya qara xama kujerar Hajjo yace "ki dubi Allah ki fadamun inda sakeena take" taja dogon tsaki kamar xata tsinke halshe tace "badai nace ma ta fita ba ka qaryatani? To ai sai kayi kuma" yace "wlhil azim Hajjo sakeena baxata fita bada ixinina ba na shedeta akan hakan, nafi kowa sanin halin sakeena a duniya, tabbas korarta kikayi shiyasa ta fita" ta bude baki jin ya ramfota. Ya tashi ya shiga toilet yayi alwala ya fita sallah. A sujjadar qarshe ya dunga roqon Allah ya saukaka masa hanyar ganin sakeena.
Harya nufo gida dabara ta fado masa ya koma bakin gate da sauri wurin gate man. Suka gaisa ya tambayeshi koyasan wannan? Ya nuna masa hoton sakeena a waya. Yace "Eh daxu dai da safe wata dattijuwar mata ta biyota har nan da muciya tana bugunta tace wai matar dantace tasa mata guba a abinci dan ta mata fada shine ta dauki wuqa xata kasheta shiyasa ta korota" Deni ya cukemeshi yace "To yanxu tana ina? Kai wane irin dabba ne daga fada maka haka xaka yadda?" wadan da suka fito daga masjid din cikin gurin
suka xo da sauri suka rabasu tare da bin baasin abunda ke faruwa.
Me gadi yana hakin shaqar da Deni ya masa ya fada musu komi tare da qarin bayanin cewa "Kuma sai da nace ta bari mijin yarinyar ya dawo ta fada masa tace a a wai bayan matarsa xaibi. Kuma ni banda haka banyi komi ba saima sadakar nera hamsin na bata ta tare napep ta hau" Cikin sauri Deni yace "ina kaji tace ya kaita?" yace "ni banjiba saboda na kunna radio amma dai tace da daya matar Dan Allah ta bata kudin motar xuwa kano ta hanata ta tafi ciki ta batta" aka hau bawa Deni haquri da shawarar ya tuntubi mutan kano yaji tunda ga dukan alamu can ta nufa.
Ya koma ciki ransa baqinqirin yau badan Hajjo uwarsa bace wlh da saiya karyata saboda duka. Ya shiga yayi wanka, yana fitowa hankalinta kwance ta tareshi tace "kai xoka kunnamun wannan gas din na kasa, na yini da yunwa gashi ina neman kwana da ita" ya dubeta yace "Hajjo kinwa sakeena duka da muciya kin koreta har bakin gate tare da hanata kudin motar xuwa kano amma hankalinki a kwance kamar bakiyi komi ba harkike xancen cin abinci? Yanxu in yar mutane ta bata fa?" ta daga masa hannu cikin masifa tace karkayimun mugun baki, tana kano bata bata ba, kuma na daketa nakoreta duk gaskiya ne nayi hakanne don na isa kuma inaso indai nina haifeka ka bita da takaddar saki gobe inyaso ko cikin satinnan ne sai ka nemi mace ka aura yar asali yar babban gida inma baka da kudin aure xan saida gonata inmaka" bece komi ba yayi hanyar bedroom, tace "kai Dan ubanka dawo ka kunnamun gas din, duk ka daga hankalinka akan wata banxa sakeena me rangwamen gata" ya koma ya kunna mata ya fito ya shige bedroom.
Taje ta dora tafashen kaji tana aikinta tana qulla irin abunda xatai in Baba ko Deni suka kawo mata matsala akan sakin sakeena.
Har tara da rabi yana kan pray mat ya tasa waya a gaba yana jiran kiran Baba ko Iya suyi masa fada akan xuwan sakeena ita kadai. Amma sai dai har xuwa goman dare babu wanda ya kirashi cikinsu. Ya dauki wayar ya danna kiran Iya, amma yayi saurin katse kiran kafin ta shiga saboda wani tunani da yayi. Yanxu inya kira mexece musu? Dacan be kirasu ba tun safe ko yamma sanda taje sai yanxu tsakiyar dare? No yasan sunyi fushine don sakeena xata fada musu Hajjo ce ta daketa ta korota, gara ya bari xuwa da safe sun huce ya kirasu ya basu haquri, inyaso tunda Friday ce goben yana dawowa aiki ya tattaki Hajjo su tafi kano yaje ya fadawa kowa abunda tayi na rufewa sakeena mahaifa ya kuma ci uban Hadixa akan hada baki da akai da ita sannan suyi weekend a Kano Sunday da yamma ya dakko his lovely wife su dawo su bude sabuwar rayuwa dashin sa dayake yi na kudaden allowances da ake basu xai nemi dauka ran Monday ana bashi zai kaita asibitin ido.
Da wannan tunani yaji fiye da rabin damuwarsa ta tafi yayi murmushin farin ciki. Ya tashi ya fito falo ya tarar da Hajjo a kwance tana bacci a kan center carpet ga faranti nan taci soyayyun kaji ta barsu da kwalin exotic. Ya kashe TV da fitila ya dakko bargo ya rufa mata a shiga kicin, ya dama out ya koma bedroom yasha ya kwanta.
Saboda yasa abun a ransa hakan yasa baccinsa be nauyi ba, yanayi yana farkawa duba wayarsa ko Baba ya kira har akai kiran farko ya miqe yaje yayo alawala ya fara nafilfili.
Har wajen shida da rabi yake jiran kiran Baba har xuwa bakwai lokacin da yayi wanka yayi shirin fita. Dauriyarsa ta qare ya dakko waya yayi shahadar quda ya danna kiran Baba gara duk fadan da xaiyi masa yayi a wuce gurin.
Ya amsa sallamar Baba ya tsuguna ya gaisheshi kamar yana gabansa. Shida Baban suka dan dau shiru na yan seconds shi yana jiran Baba yayi masa xancen sakeena yayin da Baba yake jira Deni ya fadi dalilin wannan kira nasa da sanyin safiya.
Baba ya gaji da shirun yace "kace da Hajara ta taho da wuri dan nasanta da tafiyar dare ni kuma banason wannan tafiyar ta tsakiyar dare." jiki a sanyaye Deni ya amsa ya kashe wayar.
Hannunsa na karkarwa ya kira Iya, maganar farko data fara yimasa bayan gaisawa itace "Tunda naji ka kira da sassafe sakeena ce ta takura ka ko? Ban ita mugaisa" Hankali a tashe yace "tana bandaki na kirane in gaisheki inta fito xan kuma Kira"
Da gudu ya fito falo bayan kashe wayar yana cewa "Hajjo kinji wai sakeena bataje Kano ba yanxu mukai waya da Baba da Iya" ta mutstsuke ido tayi tsaki tace "Haka kawai ina baccina me dadi ka tasheni da xancen wata banxa, ba wani nan tanacan sun hada baki ne sun boye maka dan a daga maka hankali" ta kwanta ta koma baccinta.
Duk da wani sashin na xuciyarsa ya yadda da maganar Hajjo amma haka kawai yaji hankalinsa be kwanta ba. Ya fita harabar gidan lokacin Mukhtar abokinsa wanda suke tafiya tare ya fito. A gurguje Deni yayi masa bayanin cewar fa sakeena bataje kano ba. Mukhtar ya kawo shawarar suje tasha su tambaya kota xo. Suka amince da shawararsa suka shiga motar mukhtar din su 4 suka yiwa tasha tsinke.
Da hoton sakeena na cikin wayarsa sukai amfani wajen cigiyarta wajen mutanen tashar. daga can qarshe bayan sun shafe awa daya suna tambaya wani dattijo yace tabbas ya ganta jiya ta xauna akan bencin dake kusa dashi kafin wata mata taxo ta mata magana ta tashi sukayi xagaye cikin tashar ta sai mata abinci daga baya kuma ta shiga motar matar dake waje qirar golf suka tafi.
Deni ya dafe kai ya xauna ragwaf a qasa, su mukhtar sune sukaje gurin sarkin tasha suka tambayeshi motar data dau sakeena. yace "ai mu muna da hurumi ne kawai acikin tasha babu ruwanmu da motar dake waje saboda haka bansan komi akai ba"
Hajjo na xaune tana breakfast taga anshigo da Deni ana rirriqeshi. Sukai mata bayanin da akai musu a tasha sukace sun tafi wajen aiki xasuje suyi bayanin halin da Deni ke ciki.
Itama sai lokacin taji faduwar gaba to ina yarinyar ta nufa? Kodai Baggadano ta tafi? Ta taba Deni dake xaune gabanta kamar gunki ya dago ya dubeta idonsa jajur jijiyoyin kansa sun tashi, cikin dakiya tace "karka daga hankalinka nasan tana Baggadano" bece komi ba.
A taqaice dai Deni sai da sukai kwana 2 a KD suna neman sakeena da kuma bin diddigin motar data shiga shida abokansa amma babu ko lbrn wanda yace yaga motar bare wata sakeena.
Ranar Sunday dole suka nufi Kano shi da Hajjo wacce itama xuwa yanxu jikinta qaura yayi laasar.
Wajen azahar suka shiga gida, Baba yana daki yanacin abinci yayin da Iya take wanke wanke itace ta fara ganinsu a razane tace "Deni baka da lfy ne na ganka haka a yamutse?" Be bata amsa ba sai kallon tausayi da yake binta dashi. Direct dakin Baba yawuce Hajjo kuma cikin rashin gaskiya ta nufi dakinta aka bar Iya da duban hanya tana jiran shigowar sakeena.
Ta kasa haquri ta katse wanke wanken ta nufi dakin Baba tace "Deni amma dai ba Kaduna ka baromin sakeena ita kadai ba ko? Inata kallon hanya banga shigowarta ba" Ya sunkuyar da kai ya dago ya fara magana.
Ihun da Iya ta kwantsama ya janyo hankalin duk wata halitta dake cikin gidan yayin da Hajjo ta kuma tsurewa dan tasan Deni ya fasa kwai.
Su Hadixa duk su ukun suka yo dakin Baba jin dalilin ihun Iya saddiq ma daya shigo cin abinci ya biyo bayansu da sauri. Magana Iya take cikin kuka hannunta duk biyun bisa kanta, Baba kuma na gefe yayi shiru yayin da Deni ke xubar da hawaye.
Saddiq ne yayi qarfin halin tambayar Baba meke faruwa dan yaga Baban ne kawai me dan saukin damuwa. Cikin sanyi jiki Baba ya fada masa kaf abunda Hajjo tai tun daga kan sawa ayiwa sakeena allurar planning, hana yimata aikin ido da kuma korarta a gidan Deni ranar alhamis wanda hakan yasa ba a ganta ba har yanxu kamar yadda Deni ya fada musu yanxu. Cikin tsanin bacin rai saddiq ya janyo Hadixa ya fara jibgarta yana cewa "Dan uwarki dake aka hada baki akai haka? Tabbas da hannunki ma acikin korarta da Hajjo tai shegiya me baqar zuciya." Babu wanda ya kwaci Hadixa duk ihun da take, Hajjo na jinta amma ta kasa fitowa kwatarta saboda itama yau fa a tsorace take.
Iya tana kuka tana cewa "shikenan Hajara burinki ya cika kin kada sakeena dawa. Allah sarki yarinyar nan ta dunga mitar bamuyi sallama ba lokacin tafiyarta kaduna ashe rabuwar kenan, ni Hafsatu na shiga uku yar mutane ta bata a hannuna ya xanyi." Baba ne ya tausheta ta daina kuka yace "Yi shiru Hafsatu in shaa Allahu sakeena tana Dawakin Tofa gobe da sassafe xamuje can mugani" Iya ta share hawayenta tace "mal banaji sakeena xataje Baggadano saboda abunda xai kaita can din qanintane Nura wanda baya raye yanxu amma Allah ya kaimu goben"
Saddiq ya shiga dakin Hajjo tai saurin tashi ta tareshi tace "shine dan rashin sanin ciwon kai kasamun ya a gaba kanata jibga ko? meyasa bakwa kishina ne? Shi wancan yaje ya taunamun asiri kamar bani na haife ba, ai da yana da hankali saiyace fita tayi tunda ba wanda yasani sai ni dashi" Saddiq cikin mamaki yace "Hajjo 😳 kinsan kuwa girman abunda kikayi? Silar bacewar dan mutum fa kikayi, kinsan kuwa hukuncinki a dokar qasa? To wlh akan wannan xa a iya yimiki daurin rai da rai. Kiyi fatan kawai aga yarinyar nan a Baggadano inba haka ba? Hmmmmm" ya juya ga ragowar qannansa yace "ku kuma wlh duk wacce keda hannu aciki ta kuka da kanta. Hajjo da kin fadamun abunda xai kikai Kaduna kenan wlh dana hanaki, babu yawuna cikin wannan abun Allah ya gani" Amina cikin rawar baki tace "wlh tallahi babu ruwana ita da Hadixa da Fiddausi suka qullah ni basa sani wai bani da kunya" ya nuna su Fiddausi yace "Tofa koda yaushe xaku iya tsintar kanku a gidan yari kuda Babarku bisa lefin hada baki da salwantar rai" yasa kai ya fice.
Gida dai yayi dib. Iya, Baba da Deni suna cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, yayin da Hajjo da su Hadixa ke xaune daki cikin matsanancin tsoro da fargaba.
Motar farko data tashi wacce xata Dawakin Tofa su Iya da Baba da Deni na ciki, sunyi xukudi sunata jimami hadi da adduar fatan Allah yasa sakeena tana can.
Karon farko Deni yaje mahaifar su matarsa. Iya ta shige cikin gida tabar Deni da Baba a tsaye waje, jimawa kadan ta leqo tace su shigo. Gidan babu lefi tsaf saboda Dahiru yayansu sakeena dan Inna yayi aure yana xaune a gidan to albarkacin haka an gyare gidan tsaf gashi da tsafta.
An gaisa da Inna yayin da ta tura aka kira yayanta dake kusa a xatonta xancen raba gado Iya ta kuma xuwa dashi.
Dahiru shine babba kuma shi ya fara magana bayan angama gaisawa yaji su Iya basuce komi ba yace "Iya mun ganki da sassafe wlh in maganar raba gidan nance ta kuma kawoki sai dai fa kiyi haquri kinsan damuna tayi nisa duk kudadenmu mun xubasu a gona kuma har yanxu ba a yi girbi ba" Baba yayi sauri ya riga Iya magana da cewa "A a ba wannan maganar ce ta kawomu ba, dama mijin sakeenatu ne yaxo gaisheku. Tunda akai auren yakeso yaxo amma Allah be nufa shiyasa yau mukai sammako muka rakoshi" ya qarasa fada yana nuna musu Deni. wanda yake bi masa me suna Labaran yace " Yo ita ina sakeenar hegiya? Wato tayi arxiqi ko tafi qarfin taxo qauye gurinmu hine ta turo mijinta" Baba ya basu haquri da cewa ai batajin dadine likita yace kartayi tafiya me nisa shiyasa amma tace tana gaishesu. Dahiru ya qara cewa "Ai yanxu kam bata ta tamu ta manta da cewa da uba ake ado duk duniya mune gatanta, aurenma da akai ba a fada mana saida aka daura dan an rainamu muma shiyasa muka kyaleta taje ta ruqe wadanda takega sun fimu"
Jikin su Deni yayi sanyi ganin babu alamar sakeena a gidan. Basu wani dade ba Deni ya basu kudin daya ware tun a gida domin yi musu alheri. Kudi qara magana nan da nan sai gashi suna bada saqon a gaida sakeena da jiki, Dahiru ya kamo zabi guda 2, Labaran kwan xabi, Inna kuma ta bada man quli sukace akaiwa sakeena kayan dubiya kuma ace suna gaisheta da jiki. Baba yayi qarfin halin qara basu haquri da karbar lambar wayarsu da alqawarin xa a dunga fadamusu duk abunda ya shafi sakeena. Aka rabu suna madallah.
Xaman jugum jugum ya kawosu kano tundaga Baggadano, Iya kuwa tun amota take kuka tana hango gagarumar rigimar da ka iya biyo baya a duk sanda yan uwan sakeena sukasan ta bata duk da kuwa basa ta tata amma jin hakan kansa su tada rigima ko suyi tijara.
Suna shigowa gida Baba ya samu kujera a tsakar gida ya xauna, Deni kuwa ya zame a bango yayi dabas a qar, yayin da Iya ta xauna kofar dakinta ido jajur. Hajjo nagani haka ta garxaya bandaki ta tsuga gudawar da tun safe da suka tafi take yinta. Basai sun fada ba daganin yadda suka shigo tasan sakeena bataje Baggadano ba. Su Fiddausi kuwa daki suka qule.
Baba ya kwallah kiran "Hajara" Hajjo tasaki butar hannunta wacce ta fito daga bandaki da ita. Taxo gefe ta rakuye, ya kalleta kallo irin na Allah wadai yace "Dake da duk wanda kuka hada hannu wajen batan sakeena ina washartarku daku gaggauta nemo yar mutane kafin qarshen satin nan inba haka ba xan bawa doka dama tayi aiki akanku" ta xube kan gwiwarta xatai magana ya katseta da hannu yace "wlh Hajara babu ruwana ko kiyi abunda nace ko in daukeki da kaina inmiqawa hukuma ke kuma infada musu duk abunda kikayi."
Deni yaxo ya kama hannun Baba ya fara magana xuciyarsa a bushe yace "Baba inka tashi miqa Hajjo gurin hukumar Dan Allah ka hada dani, nima naci amanar sakeena, naci amanar soyayyar da takemun. Tunda nasamu aiki sakeena tai bankwana da farin ciki, tasha kwana tana kukan baqin ciki dana ciwon idonta a dalilin wannan aikin, na daka ta waya da sharrin social media na batawa sakeena rai tare da quntata mata. Aikin dana samu ta dalilinta shiya rabata da farin cikinta." Iya ta matso ta cukumo Deni ta falla masa mari tace "Au dama kai da nake ganin a gurinka ne kadai sakeena ke samun sauki har da kai acikin wadan da akayi rubdugu kukaiwa yarinya taron dangi kuka saida ita? amma dake munafiki ne kai shine ka boye naka lefin?"
Ya kalleta yace "Iya ni butulu ne, haqiqa na mance alheri. sakeena ta aureni lokacin da nake tsananin buqatar aure kuma nake dab da fadawa halaka saboda rashin auren, amma kuma bani da ko taro nayin auren, tayi watsi da duk wani Kyale kyale na auren wannan xamanin ta aureni akan naira dubu ashirin kacal wanda bani da halin bata sai Baba nane ya bata, tayi aiki da kwanjinta ta hana kanta hutu ta samar mana abunda xamuci bayan mun shafe tsawon lokaci muna kwanan yunwa. Ai kinga da ni mutumin kirki ko wannan kadai ya isa in kalla inriqeta da Amana ko? To sakeena ba a nan kawai halinta ya tsaya ba tayimun biyayya sau da qafa tayimun soyayyar da harna mutu baxan samu macen da takemun irinta ba, kuma Hajjo tayi amfani da soyayyar da sakeena kemun wajen hanani haihuwa da sakeena" Iya tana kuka ta shaqeshi ta kuma kifeshi da wani marin tace "Dan ubanka biyani diyata, wlh sai kun fitomin da yata" ta rufeshi da duka. Su Hadixa tuni sunyo waje suma suna kuka, Saddiq ya shigo daga waje. Shima nasa kukan ya saki ya banbare kwalar Deni daga hannun Iya yace "Dan Allah Dan manxonsa ku rufa mana asiri, muji da bala in da muke ciki mu xauna mu nemi mafita kar yarinyarnan ta salwanta, bamusan kalar mutanen da suka dauketa ba" Deni ya dubeshi yace "saddiq dan me xaka hanata dukana? Iya Dan Allah ki dakeni koda itace ne ko xan samu hawaye su fita daga idona inji saukin abunda nikaji a xuciyata."
Ido jajur Saddiq ya dubi su Fiddausi yace "in kunsan wani abu akan batan sakeena ko kuma inda kuka turata gara ku fada tun anan kafin muje state C I D"
Suka kwalo ido a tare. Amina jikinta yana rawa ta matso gaban Baba take zaune kan kujera ya zabga tagumi tace "wlh Baba bansan sun shirya batar da sakeena ba. Ni dai kawai nasan Hajjo ta kaiwa yaya Deni rubutun rabasu shi da sakeena tace masa na tsari ne, sannan kuma tasani naje nakai musu laya nasaka a qasan katifar gadonsu tace indai ansaka a daren xai saketa wannan kadai nasani, amma ina yawan jinsu dasu Hadixa suna hirar xuwa gurin malami akan raba yaya da sakeena" Hajjo dake gefe tahau rantse rantsen karya Amina ke mata, shi kuwa Deni kallon Hajjo yake yana hawaye yana juya kai.
Saddiq ya matso jikin Hajjo yace "Dama kin wuce yacce nake daukanki? Dama saida kika aikata abunda na hanaki? Meyasa baki rabasu ba tun yana jobless dinsa sai da ya samu aiki a dalilinta? Wane irin kalar son xuciya ne wannan?" Baba ya dagawa saddiq hannu ya miqe xe fita, Hajjo taje ta tare masa hanya tana kukan nadama tace "malam ka dubi Allah ka rufamun asiri, wlh ban tura sakeena ko inaba ni dai kawai burina tabar gidan Deni amma bawai ta bata ba kuma danasan hakan xata faru da ita da ban koreta ba" Baba ya tureta ya wuce.
Saddiq ya tasa su Fiddausi da Hadixa a gaba yayi fadan, yayi dukan, yayi lallashin su fada masa abunda suka shirya da Hajjo akan batan sakeena amma sukaqi dansu da wayonsu baxasu taunawa uwarsu asiri ba kamar yadda Amina tayi.
******** ******* ********
Sakeena ta gama cin abincinta ta jingina baya ajikin kujerar mota tana kallon daxuxxukan da suke wucewa, tana murnar xuwa kano da ganin Iya duk da tafiyar bata dadi bace amma dai ai tasan Deni baxai yadda da maganar Hajjo ba nacewa ta xuba mata guba, dan haka hankalinta kwance ta daddake gwangwanin malt. Driver nata sharara gudu jefi jefi suna hira da wanda ke zaune daya sit din, Hajiya kuma tanata danna waya.
Sakeena ta fara gyangyadi Hajiya ta kwantar da ita kan cinyarta tace "yi baccinki yan mata" xuciya daya ta fara baccinta. Allah sarki ta dauka kowa kyakykyawar xuciya gareshi irin tata.
Sai da ta tabbatar baccinta yayi nisa sannan Hajiya ta ajiye wayar da take dannawa ta leqa fuskar sakeena tace "masha Allah kyakykyawa da ita" mejan motar yace "Haba Hajiya yaufa babu kasuwa naga bamuyo kamu sosai ba ni dana dauka xamu cika bayan motar da yan mata?" Hajiya tayi dariya cikin duniyanci tace "ai kuma munyo babban kamu, wannan ai babbar kadarace ga quruciya kuma danya ce shataf" ta qara kallon fuskar sakeena tace "wannan yan kudade kadan xan kashe mata infara girbar riba. Ga Manya fitulu kuwa (idanu) dama wani dan China yaban cigiyar a samo masa mace me ido xai biyani ko nawane" suka kwashe da dariya a tare. Hajiya ta kuma cewa "yanxu haka wani laqanin aka bashi da mace me ido kasansu da tsafi. Yar banxa dagani ma guduwa tayi daga gaban iyayenta dan wannan tafiyartata bata shiri bace tunda ba kudin mota. Inkun tara ma akan saurayi ta gudu, dan shashanci take xaton xan taimaketa haka ziqau, ai sai dai mu taimaki juna." suka kuma saka dariya. Ta fara yunqurin cirowa sakeena xoben hannunta da abun hannun dake dauke da sunanta tana cewa "wannan ai dole a cireshi dan ba a xuwa bariki da sunan gaskiya. Sabon suna xan xaba miki sabida tsaro daga yau kam kin tashi daga sakeena" Ganin sakeena na motsi xata farka yasa dole ta haqura da cirewar.
sun shafe tsawon yini suna tafiya yayin da tun kimanin awa hudu baya sakeena ta farka Hajiya ta kuma bata abincin da suka siya a hanya taci tasha lemon ta Hajiya ta xuba mata kwayar saka bacci ba tare da saninta ba. Suka tsaya tai fitsari ta canja wata diaper din suka dora a tafiya. Ta koma baccinta da temakon maganin baccin.
Sanyin asuba ne ya tada ta daga nannauyan baccin da take, dan tun tana jurewa sanyin harya gagareta dole ta farka. Ta dubi garin duhu dundum, Hajiya ma baccinta take.
Tadan fara tsorata wace irin tafiyace wannan tun safe har yanxu basuje Kano ba? Ita lokacin da sukaxo da Deni basuyi wannan dadewar a hanya ba. Ta taba Hajiya wacce ke bacci amma bata tashi ba. Tayi wa driver din magana shima ya shareta, dole tai shiru sukacigaba da tafiya tana duban hanya har gari ya fara wayewa.
Lokacin da gari ya gama wayewa hankalin sakeena ya fara tashi domin sun fara shigowa cikin mutane kuma suna wuce qauyuka tana ganin wasu murda murdan mutane masu yawo rabin tsirara daga maxa har mata. Duk da ba ko ina ta sani a Kano ba wannan gari da suke be mata kama da arewa ba balle wata Kano.
A tsorace ta juya ta kalli Hajiya tace "wai har yanxu bamuxo ba? Wai Dan Allah ina xaku kaini nifa Kano nace muku xanje" Hajiya ta muskuta taci gaba da danna wayarta wacce tasa caji ajikin powder bank ko kallon sakeena batai ba balle ta tanka ta.
Sakeena cikin kuka da tashin hankali tace da driver "kai ka saukeni wlh ni Kano xani nan inane?" suka hada baki shi da dayan sukace "Nan birnin ikko ne, ikko ikon Allah" suka sheqe da dariya bayan gama fadar haka.
Ta saki kururuwa jin cewa a Lagos take tace "wayyo Allah na, na shiga wayyo ya Deni" ta fara buga glass din motar ko motocin dake wucewa jefi jefi xasu temake ta. Hajiya tasa murgujejen hannunta ta murde hannayen sakeena suka fara kokawa. Sakeena ta samu ta gartsa mata cixo ta saketa babu shiri, taci gaba da buga glass din tana ihu tana neman temako, driver yayi amfani da madannan gaba ya xuge glass din motar ya qara gudu dan sun kusa isa inda xasu tsaya.
Tafiya suke shi da drivern sa tun daren jiya suka taso daga katsina inda yaje gaida Babarsa, ya dubi agogo ya qara bawa drivern umarnin ya qara gudun mota saboda yanaso yaje gida ya watsa ruwa yasa uniform xai wuce office suna da meeting. drivern ya dan dubeshi ta madubin gaba yace "oga tunda kana da kayan aikin a tare da kai a jikin jaka bexe hana mudan sami wani ko qaramin otel ne anan qauyen ka shiga kayi wanka kasa kayan aikin, kaga muna shiga cikin gari saika wuce office basai kaje gida ba" ya jinjina kai yace "gud idea in kasamu ka tsaya to"
Basu yi wata tafiya sosai ba suka tadda wani local hotel da sauri ya dau trolly dinsa ya shiga ciki. 15 minutes da shigarsa ya fito cikin shirinsa tsaf yana qamshi sanye da uniform ash clr wanda ke nuna shi Jami'in hukumar Costums ne. Gaban rigarsa maqale da da sunansa ajikin qarfe MOHD SAGEER A.
.
Drivern ya saluting dinshi ya bude masa qofar baya ya shiga shima ya shiga. A dai dai wannan lokacin ne motar su sakeena ta giftasu da gudu, kuma yaga yadda wata mace a cikin motar ke bubga glass. Cikin sauri yace "mal Ilu yi sauri bi bayan wancan golf din akwai matsala"
Wanda aka kira da mal Ilu yabi bayan su sakeena a million, ganin ana binsu nasu drivern ya qara gudu suka dunga tsere a titi. Da sauri Sageer ya ciro yar qaramar bindiga ya saita tayar motar ya harba, amma sai yayi rashin sa a be samu ba.
Daga cikin motar ya juyo yace Hajiya da matsala wlh inaga wanda yake binmu sojane ko jami in tsaro kisan abunyi da sauri ya fara harbi fa karmu shiga hannu. A gigice ta bude kofa ta hankado sakeena kan titi tace "na cillarta maxa samu wani gurin mu rabe karka sake su kamamu"
Acan kuma Sageer yace "mal Ilu wane irin driving kake ne kamar mace? Kayi sauri kasha gabansu ina tunanin mutum suka sato cikin motar" kafin ya qare maganar yaga an wullo mutum daga ciki wanda hakan yasa mal Ilu cin wani wawan birki, qiris ya rage be taka sakeena ba.
Suka fito cikin sauri ya tsuguna gabanta yace "tabbas sato ta sukai ganin xa a kamasu suka wullarta" ya hannu ya daga sakeena wacce ta sume garin wullowar da akai mata duk ta kukkuje
a hannu da fuska ya sata a mota yace mu tafi da sauri cikin gari mu kaita asibiti.
Da sauri suka shiga cikin gari suka qarasa wani private hospital wanda Sageer ke ganin likita. A gaggauce yayi masa bayanin yadda ya samo ta dake akwai sanayya tsakaninsu ya karbeta aka kwantar da ita yace in antashi office xai biyo yaganta.
Koda yaje office ya makara yayiwa ogansu bayanin abunda yasashi latti. Ana tashi asibiti ya koma duk da yagaji saboda sun yini aiki. Ya samu sakeena kamar yadda ya kawota a sume se dressing da akayi mata a ciwonka da taji. Likitan yana tsaye kanta yana qara daura mata wani drip din yakewa Sageer bayanin daya daga masa hankali. "na fada maka mr Sageer doguwar suma ta shiga wato coma, kuma akwai karaya a hannunta wanda sai xuwa safe in likitan qashi yaxo xa a gyara mata" ya dafe goshi yace "To yanxu Dr sani yaushene xata farfado kenan? don musan daga inda take" Dr ya dauki file din sakeena dake kan fridge ya bude yana cewa "ai kuwa banace ba, domin wasu kan iya daukan watanni a coma sai dai fatan Allah ya taqaita. Gashi anbude mata file babu suna wane suna xamusa kenan?" ya motsa kafada yace "To aini yadda ka ganta nima haka na ganta, ko muryarta banjiba bare sunanta, wadanda fa suka satota wurgota sukai dan rashin imani daga cikin motar" Dr ya fara dan duba jikin sakeena yana cewa "amma yakama ace akwai wata alama a jikinta daxaisa agane daga inda take, kuma da kamar da uniform ne ma abun xaixo mana da sauki." yana duba jikin sakeena yaci karo da abun hannunta yayi saurin sunkuyawa yace "yawwa ga sunanta nan ajikin wannan abun sakeena" ya fada bayan ya dago kansa daga kallon abun hannun.
Sageer ya gyara tsaiwa ya mamaita sunan "Sakeena" Dr sani yace "Eh SAKEENA MOHD SAGEER ba don haka na rubuta yanxu a jikin file dinta" suka fita daga dakin sukaje nurse station na cikin asibitin ya nemi nurse sukai magana da ita akan xata dunga kula da sakeena har xuwa farkowarta kamar yadda Dr sani ya bashi shawara. Ta fadi kudin ya biyata, ya biya kudin gado dana magani sannan yayi gida.
Washegari ma kafin yaje office saida ya biyo ganin jikin kuma yaji dadi daya samu sister a dakin da gyara sakeena angoge mata jiki har an canja mata kaya ana bata abinci ta hanci. Yayi mata godiya, tace asiyowa sakeena kayan sawa da undis harda always. Koda ya dawo office acan ya dira yakai kaya niqi niqi.
A kullum yana xuwa asibiti sau biyu safe da dare inya taso aiki, kuma ya gamsu da kulawar da ake bawa sakeena, tuni anmata gyaran karayar hannunta kuma harta soma warkewa tunda ba a motsa hannun. A kullum burinsa ta farka ta fadi ita wacece kuma daga ina take, ya maidata don yasan duk inda iyayenta suke suna cikin tashin hankali. A haka aka kwashe 2 weeks cur.
******* ****** ***** *****
Acan Kano kuma fadar tashin hankalin da iyalan mal Lawan ke ciki bata baki ne, Deni ya xama kamar wani xararre, ya daina kula Hajjo dasu Hadixa kwata kwata ko dakin Hajjo ya daina shiga Iya tun tanajin haushinsa har ta fara tausaya masa.
A cikin kwana na 5 da batan sakeena lbr yajewa Zahra sai gata da rana tsaka cikin tashin hankali a dakin Iya suka xauna da Deni kuma ya fada mata duk yacce akai. A lokacin dataxo Hajjo bata nan ta tafi yawan bin malamai akan batan sakeena. Saidata dawo zahra ta sameta dan jin inda aka haihu a ragaya. Tana kuka tana rantsewa zahra ita bata tura sakeena ko ina ba kuma duk gidan malamin da taje sai ace mata sakeena bata kusa tayi nesa da gida ta yiyu ma bata qasar. Zahra tayiwa Hajjo fadan cewa yanxu fa ba bin malamai ne abun yiba addua ce kawai mafita domin kuskure fa anriga anyi. Hajjo na kuka tace da zahra "Dan Allah zahra ki roqi malam yayi haquri karya kaini gurin yan sanda kamar yadda yace kuma ki fada masa wlh ban tura sakeena ko inaba ni dai kawai na koreta a gidan Deni. Kuma kiyiwa dan uwanki nasiha nasan na masa lefi yayi haquri baya kulani yanxu, sai dai na hangeshi daga nesa ko kallo na bayayi" Zahra ta share kwallah ta tausaya Hajjo, uwa uwa ce koda kuwa mahaukaciya ce. Tace "to xan musu magana bari xuwa yamma su dawo"
Bayan la'asar aka samu zama da Baba, zahra da kuma Deni. zahra ta fada musu duk saqon Hajjo kuma ta dunga bawa Baba da Deni haquri da kalamai masu dadi da kwantar da kai. Saddiq ya shigo suka hadu aka dora. Baba yace "shikenan zahra taci darajarki ita kuma sakeena mucigaba da nemanta da fatan Allah yasa tana hannu nagari" tace "nagode Baba, yaya Deni kai bakace komi ba kayi haquri ka yafewa Hajjo." Ya Kalli zahra yace "ai banyi fushi da itaba, ya xanyi da ita tunda uwatace, nima kice ta yafemun xan shiga in anjima in gaisheta." tace "yawwa yaya kokaifa Allah ya bayyana mana anty sakeena. Kuma dan Allah kayi haquri ka koma gurin aikinka mu durfafi addua a lamarin damuwa babu abunda xata qara" A qarshe dai zahra saidata tasa Deni har dakin Hajjo yaje suka sasanta, kana aka xauna aka shirya sanarwa dauke da photon sakeena suka baxa a social media har da saddiq. Ta samu Iya ta bata haquri tare da kwantar mata da hankalin xa aga sakeena. Sai da taga al amura sun dan dai daita a gidan sannan ta tafi.
Washegari Deni ya tattara ya koma KD aiki ya fara wata iriyar bahagguwar rayuwa me cike da loneliness, sai yanxu ne yake dandana rashin sakeena gidan ya masa fadi ya rasa inda xai tsoma ransa yaji sanyi. Ya duqufa addua da tsaiwar dare kamar yadda zahra tace a gefe guda kuma ana cigiyar sakeena a kawace kafar sadarwa ta waya. A duk sati yake xuwa Kano yin weekend.
A kano Hajjo dai tayi sanyi sosai, lbarin batar da sakeena da tayi yayi fitar dango mutane babu adalci duk wanda ya tashi bada labari sai yayiwa lbrin kwaskwarima yadda xaifi xaqi da qayatarwa. saboda haka Hajjo ta daina fita ko kofar gida saboda nunata da akeyi da kuma aibatata, yayanta ma dai haka suka kasance cikin tsangwama. Fiddausi aure ya matso amma aka daga saboda tashin hankalin da suke ciki. Wanda ya fara neman auren Hadixa har sun daidaita ana shirin kawo kudi labari yaje gidansu cewar Babar Hadixa ta batar da surukarta, uwarsa tace baxai aureta babarta muguwa ce. Ranar Hadixa tayi kuka kamar xata mutu tace "Hajjo kin cuceni, inason aure gashi Allah ya kawomin miji amma kuskurenki yayi mini shamaki da xama matar aure" Hajjo baki sake take cewa "yanxu Hadixa nice na cuceki? Duk abunda na aikata wake sakani a hanya inbaku ba?" Fiddausi ta tsorata a xuciyarta ta qudure xataje tace da Baba dan Allah kar akuma daga bikinta gara ayi koyayane akaita saboda kar abunda ya faru akan Hadixa ya faru akanta itama a fasa aurenta.
Ranar da sakeena ta cika 30 dayx da bata, ta kama Saturday Deni tun jiya Friday yaxo kano. A ranar Saturday din sukaje gidan da su Deni suka xauna a sani me nagge shi da Iya suka debe kayansu kaf tunda dama kudinsu ya qare har anbasu notice. Suka rabu dasu umman Amir cikin mutunci tana bada saqon a gaida sakeena, Mariya dai batanan tana garinsu.
Suka xube kayan dakin Iya sai da Baba ya dawo yagani Iya ta kalli Baba da Deni tace "ai sai a raba gado ko a bawa Deni nasa, domin nasan sakeena dai yanxu bata raye wadanda suka saceta sun kasheta. Ragowar kayan kuma aimata sadaka dasu" Deni ya kalli Iya a raxane yace "Dan Allah karkimun wannan fatan Iya in shaa Allah sakeena tana raye kuma xata dawo." Saddiq ma yace "Iya kiyi haquri in shaa Allah sakeena xata dawo adduarmu baxata tafi a banxa ba" Hajjo dai duk sanda ake irin wannan maganar takanyi shiru ta sunkuyar dakai. Haka rayuwa tacigaba a gurin mutanen kano.
A Lagos kuwa sakeena har yanxu tana cikin coma yayin da rauninkan jikinta suka warke tayi subul da ita saboda tana samun kulawa sosai matsalarta kawai rashin farkawa daga doguwar suma.
A kullum sageer yana xuwa dubata tare da barin kudi akanta kamar ya santa a kullum fatansa ta farka a maidata ga iyayenta shi bai xaci abun xaiyi nisa haka ba.
A ranar da sakeena ta cika 33 dayx Allah yayi farkawarta. Anyi sa a ranar Sageer yaxo da safe dubata domin jiya daya taso aiki bexo ba don sai dare sosai ya tashi. Tun wajen asuba ta farka nurse ta temaka mata ta rakata toilet tayi brush da wanka, amma saita lura kamar sakeena fa bata gani domin komi saita mata jagora.
Cikin hanxari ta kira Dr sani wanda bexo ba a lokacin shima da sauri ya kira Sageer ya sheda masa farkowar Sakeena suka iso gurin tare.
Tambayar farko da Dr sani ya fara yiwa sakeena itace "Sakeena meyake miki ciwo yanxu?" ta bashi amsa da "bansani ba" suka kalli juna shi da sageer cikin mamaki. Dr sani ya daga paper din hannunsa yace "kinga meye wannan" ta fara yawo da idanunta a wajen tace "ai banga komi ba" Sageer cikin quluwa yace "ke bamason rainin hankali ki fada mana daga ina kike kuma meye hadin mutanen dana ganki dasu a mota?" ta qara cewa "mutane a mota ta fara qoqarin tuna abunda yake fada mata, kanta ya sara ta riqe shi da hannu biyu" Dr sani yayi saurin katse mata tunani tare da dakatar da Sageer yace "relax Sakeena ai xakisha shayi ko? maxa sister hada mata muna xuwa" yaja hannun Sageer sukai waje.
Suka xauna a office dinsa yace "ina tuninfa akwai matsala amma Allah ya kiyaye faruwar abunda nake hasashe. Sageer yace "mekenan Dr" yace "Dole mu nemo likitan ido dana kwakwalwa yanxu cikin gaggawa" ya fara danna waya yana magana da likitocin daya anbata. Suka buqaci da akai sakeena teaching hospital dake garin dan yimata gwaje gwaje.
Cikin gaggawa aka shiryata suka nufi can din. Da temakon Dr sani aka shigar da ita dakin gwajin kwakwalwa tare da yimata binciken kwakwaf da kuma tarin tambayoyi. A cikin 3 hrs results ya fito aka kira Dr sani da Mr Sageer akai musu bayanin sakamakon mummunar faduwar da tayi kanta ya bugu hakan ya taba wasu jijiyoyi a kwakwalwarta sun gaxa aiki Wanda qarshe hakan ya haifar mata da mance rayuwarta ta baya (loosing memory) Abunda aka dorata akai yanxu shine gaskiya a gurinta." Sageer ya dafe kai yace "shikenan na fada cikin bala i yanxu ya xanyi da wannan yarinyar?" Dr ya kalle shi ya fara kwantar masa da hankali da cewa "loosing memory ba hauka bane Just matsalace da ka iya warkewa xuwa wani dan lokaci indai anbawa patein kulawa da magungunan da suka dace da ciwon. Da kuma guje tilastawa wanda keda matsalar tuna rayuwarsa ta baya saboda yin hakan kan haifar masa matsalar mugun ciwon kai. Sannan abu na qarshe shine a rabata da duk wani abu da xai tuna mata rayuwarta ta baya har xuwa lokacin da jijiyoyin kwakwalwarta xasu dawo aiki." ya rubuta musu magani da bayanin yadda xa a shasu da kuma kulawa da shansu dan magungunane masu hatsari na ciwon kwakwalwa.
Suka fito jiki sanyaye suka nufi bangaren ido shima dai nan da matsala wanda faduwarta ta haifar kuma bincike ya nuna dama tana da dadaddiyar matsalar ido. Dan haka tana buqatar aikin ido cikin gaggawa kafin idon ya gama mutuwa. Babu dogon xance Sageer cikin mutuwar jiki da tausayin qaramar yarinya sakeena ya rattaba hannu akan takaddar aiki tare da biyan maqudan kudaden aikin. A gurin aka yimata wasu allurai tare da magani aka turata daki na mussamman xuwa gobe da safe ayi mata aiki.
Sageer suka koma asibitin Dr sani bayan sun bar sakeena cikin kulawa ta musamman. Suka xube a office dinsa ya xabga tagumi yace "Dr sani na shiga uku na fada matsala ya xanyi da riqon budurwar da tunaninta ya bace ni ba mata ba ni ba uwa a kusa ba? Dr sani ya ajiye biron hannunsa yace "Duk fa ba wani abune me wahala ba domin ni harna samar maka solution in kanaso in fada maka" cikin sauri yace "plz fadamun Dr" cikin rashin damuwa Dr sani yace "Just marry her" cikin raxana Sageer yace "in aureta kake nufi?" yace "yes ka aureta shine solution. inka aureta duk ranar data warke tunaninta ya dawo saita fada maka asalinta da garinsu kaga saika saketa ka maidata gidansu ka fadawa iyayenta duk yadda akai, suma insukaji aurenta kayi hankalinsu xaifi kwanciya kuma kaima aurenta kariyace gareka da ace kana xaune da ita gida daya baku hada komi ba gara ace a matsayin matarka take kuma gashi xaka samu ladan wannan aiki da kai." Sageer ya dubi Dr sani yace "amma fa tamun qanqanta Dr" Sani ya kwashe da dariya yace "shege kanasa ran xakai wani abu kenan tunda harka hango tama qanqanta?" Ya hade rai yace "banaso iskanci Sani, na yadda da shawararka amma baxan fadawa umma na ba don auren temako xanyi bana soyayya ba kaga in umma taji baxata bari insaketa ba in lokaci yayi. inaso maganar ta tsaya a tsakanina da kai da Abdulfatah uban gidana sai Maitama abokina shima saboda sheda anan gaba, inaso randa xa a bude mata ido ta ganni a matsayin mijinta." Dr sani ya amsa da cewa "Hakan yayi Allah ya baka ladan alkhairin da kayi da temako"
Daga nan Mr Sageer Victorian island yayi gidan uban gidansa wato controller Abdulfatah. Yayi masa bayanin duk yadda sukai da Dr sani kuma ya fada masa farkawar sakeena shiya hanashi xuwa aiki yau. Abdulfatah yayi naam da shawararsu yace gobe da safe yaxo suje tare masallacin juma a in ansakko a daura aure.
A wannan dare Sageer ya kwana tunani da xuwan aure haka bagatatan a rayuwarsa.
Ya leqa teaching hospital da safe gurin sakeena a gabansa aka shiga da ita aikin Ido ya wuce office. Ana idar da sallar juma a a babban masallacin juma a dake Lagos Abdulfatah ya xama waliyin sakeena yayin da Imam na masallacin ya xama wakilin Mohd Sageer aka daura aurensu da sakeena akan sadaki 100k wanda Abdukfatah ya biyawa Sageer. Maitama yana daukan wedding fatiha din a waya kamar yadda Sageer ya sakashi har aka gama. Suka dan yiwa Sageer wasa irin na abokai shi da Dr sani, Abdulfatah kuma ya bashi sadakin sakeena yace yasan yadda xaiyi ya bata shi yawuce office. Suka watse suka bar Sageer a cikin mota ya kife kai akan sitiyari ya rasa wane irin yanayi yake ciki, farin ciki ko baqin ciki? Fargaba ko murna?
Wannan qaddara ita ta canja mata suna daga SAKEENA ABBAKAR LIMAN xuwa SAKEENA MOHD SAGEER. Me xaratan maxajen aure guda biyu rigis. NURADDEEN LAWAN da kuma MOHD SAGEER ABDALLAH.
Hajia😊
[7/31, 2:21 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣7⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
MUHAMMAD SAGEER ABDALLAH shine cikakken sunansa haifaffen garin katsina, Babansa tsohon ma aikacin gwamnati ne wato Alh Abdullah da matar Haj kubra yana da rufin asiri amma fa bawai me kudi bane. Su biyu aka haifa Sageer ne Babba sai qanwarsa shafa.
Sageer yayi karatunsa tundaga secondary har na jamia a katsina kuma yana bautar qasa ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa. Mutuwar ta daga hankalinsu sosai amma ya suka iya? Rai baqon duniya, wanda ya tafi beyi gaggawa ba muda muka rage bamuyu jinkiri ba fata dai Allah ya bamu wucewa lfy amin.
Bayan gama bautar qasarsa Sageer yayi xaman jiran samun aiki amma shiru dake bashi da wanda ya tsaya masa aiki yaqi samuwa.Beyi dogon xama ba ya fara qoqarin komawa makaranta. Ya xaunar da mahaifiyarsu wadda suke kira Umma ya fada mata qudurinsa kuma ya roqeta akan a raba abunda Babansu ya bari abashi nasa ya dauki nauyin karatunsa saboda Msc karatune me cin kudi sosai bayaso abiya masa a dukiyar gado a kwari qanwarsa shafa wacce tun bayan gama nata karatun tai aure. Hakan akayi aka raba aka bawa kowa nasa gidan da suke ciki kuma suka barshi a haka.
Dake professional masters yayi shiyasa cikin qanqanin lokaci ya gama, ya dawo aka kuma dora xaman jiran aiki. Abun Allah ana cikin haka suka hadu da wani school mate din Babansa. A taqaice dai shiya shige masa gaba ya samu shiga hukumar customs bayan sunyi training na yan watanni ya fito a babban jami i kasancewar da babban kwali ya shiga hukumar. Akai kuma posting dinsa Lagos.
Sageer kyakykyawan baqin bafulatanin Katsina bashi da tsawo kamar yadda bashi da qiba ma ana dai me qaramin jiki, dan kimanin shekaru 39-40 da haihuwa. Baqinsa me hana kyansa fitowa ba kasancewar ba farar fata bace kyau. Yayi shekaru 7 cur yana aiki da hukumar costums kuma ya tara dukiya dai dai misali da kadarori. Ya tsayawa ummansa da shafa yana musu hidima sosai kasancewar basu da gatan da yawuce nasa. Ummansa ta matsa masa akan yayi aure tun shekarun biyar baya amma abun ya gagara a gurin Sageer saboda a bayan idonta wato a Lagos yana taba barinkinsa kadan bame yawa ba a duk sanda ya buqaci kasancewa da mace kuma ya kasa juriya tunda shi ba dutse bane. Saboda haka ya tattara maganar aure ya jefata baya tunda abunda xai samu a gidan auren gashi yana samu a titi inya biya kudi kuma sai wacce ya xaba ya darje, to a ganinsa mexesa ya dakkowa kansa damuwa ya kawo gidansa yasa aransa shi da aure sai dai in yaxo masa a qaddara amma shi babu soyayya aransa balle aje ga wani abu waishi aure kuma shi yadda yayi mugun raina mata ma waxai kalla ya kawo gidansa da sunan aure, shifa a ganinsa ma mafi yawan mata karuwai ne (Da kurawan dai kake mu'amala shiyasa kake ganin haka dan rainin sense 🤨😏)
To kuma ana cikin haka sai gashi auren qaddara na yar qanqanunwar yarinya ya fado masa bagatatan wanda yayishi bada sanin kowa nasa ba kuma baya fata ahalinsa su sani har ayi agama.
Har akai kiran la'asar Sageer yana mota a kwance yana aikin tunani kafin ya yanke shawarar tunkarar matsalar da addua kawai da kuma sadaqa tunda tana maganin masifa. Ya fito ya shiga masallaci yayi sallah yana fitowa ya rabawa yan tsofaffin dake kofar masallacin sadakar dubu dai dai sukaita godiya da fatan alkhairi.
Ya nufi wani qaton shagon sai da golds, ya shiga da nufin siyawa sakeena gold da kudinta na sadaki, aka fara nuna masa golds din dake cikin gilasai da farashinsu. Wani farin xobe yaja hankalinsa yace a fito mai dashi, aka dakko masa ya dibashi farine qal sai daukan ido yake siriri sosai sai wani stone a tsakiyarsa shima kamar jikin xoben fari qal. Aka auna masa shi. Kudinsa ya kama 176k ya dakko sadakin sakeena ya basu, ragowar kudin kuma babu kudi a jikinsa sosai ya bada ATM aka cire through P O S aka bashi receipt yayi mamakin tsadar xoben. Matar dake gurin tace masa 'ai English gold ne kuma stones din dake jikima me darajane sosai. Amma daka taho da Madam din ta gwada da yatsanta ko?' ya danyi jim dan gaskiyane abunda ta fada, yace "karki damu inyayi kadan ko yawa xamu dawo in xanja inda ciko inyi"
Daganan asibiti ya koma gurin sakeena, ya tarar tuni sun fito daga aikin idon amma tana kwance sambal a gado. Likitan ke masa bayanin sun mata allurar baccine data rage radadi saboda dinkin dake cikin idon xata iya kaiwa gobe bata farka ba.
Ya samu gefen gadon ya xauna bayan fitar likitan, a hankali ya fara qare mata kallo tundaga yatsun kafarta har xuwa gashin kanta. Dake dan duniya ne a harkar sanin mata anan ya gane sakeena ba qaramar qayatacciyar mace xa ai ba inta gama girma kuma tasamu jin dadi. Bayan haka ma ya gane kyakykyawar gaskece.
Ya kamo xara xaran yatsunta na hannu ya cire mata xoben axurfa da abun hannun dake dauke da sunanta bisa shawarar likita na guje tuna mata rayuwarta ta baya har xuwa lokacin da xata tuna dan kanta. Ya ciro xoben daya siyo yanxu cikin box ya mayar mata a gurbin na axurfa ya xauna caraf kamar angwada da hannun. Ya haska hannun sosai, yakai yatsun bakinsa ya sumbata, yayi saurin miqewa a gefen gadon daya tuna itadin fa ba wata bace a gurinsa face yar amana wacce ya aura dan temako.
Sai wajen taran dare ya tafi gida, ya danci abunda kukun ya dafa masa yayi wanka ya kwanta da tunanin irin rayuwar da zasuyi da sakeena inta dawo gidan nan a matsayin matarsa.
Da safe ya tashi da aikin gyaran daya bedroom din dake cikin falon, yaransa suka dunga mamakin oga da wannan aikin da kansa? sai da yaga dakin ya masa yacce yakeso sannan ya shiga gurin Maitama a gidansa dake qasan layin suka gaisa da matarsa Bilki kafin ta taso mijinta dake bacci. Ya fito yana hamma yace "wai kai ka dauka kowa irinkane gwauro da kake xuwarwa mutane gida da safe?" yayi tsaki yace "Ba wannan shirmen ya kawoni ba, so nake Bilki ta temakamun a samowa yarinyar nan kayan sakawa da sauran kayan mata na kwalliya kafin ta farko, yanxu ma nagama gyara mata dakin dake babban falo acan xata sauka banaso tasan komi sabone yanxu." Maitama ya daga gira yana kallon Sageer a kaikaice yace "To danme baxata sauka a dakin kaba? Ba matarka bace? Allah yasa kayi aure wannan damace a gurinka ka yaqi rayuwarka ta bariki. Kuma ai babu matsala dan tasan komi sabone kana iya dora tunaninta akan cewa kunyi aurene kwanaannan tasami matsalar ido shiyasa ka kaita asibiti" Sageer yace "kaga malam bawai na tambayeka bane ka tunamun ni dan bariki ne kawai temako nakeso inxaka temakamun to" Maitama yaje ya kira Bilki shi da Sageer sukai mata bayanin auren sageer da sakeena jiya kuma suka fada mata abun na sirrine. Bilki wayayyar mace tashin Lagos ta tausayawa sakeena kwarai ta fada musu duk yadda xasu tafi da plan dinsu.
Tare suka fita da ita kasuwa Sageer ya kashe kudi wajen siyan kayan da Bilki ta xaba bayan sunje taga sakeena kuma ta aunata, ta xabo kayan da xasu dace da kalar fatarta masu kyau da tsada tasai mata mayuka irin nasu na masu farar fata da su turare. Dake tailor ce itace ta debi kayan duka ta fara aikin dinkasu aranar ta dunga yaba kyan sakeena tana cewa da Sageer ya more mata me kyau.
Koda sakeena ta farko daga allurar ancigaba da kula da ita a asibiti, yayin da Sageer kullum sai yaje da safe kan ya tafi aiki haka ma da yamma inya dawo, yakan xauna su danyi hira koya bata lbr wani xubin ya riqeta su tattaka xuwa wajen daki. A gefe guda kuma suna jiran cikar sati daya a cirewa sakeena bandage din aka nade mata ido dashi kamar yadda likita ce.
Ranar juma a sati guda cif sassafe Sageer yaxo asibiti, likitan safe yana xuwa aka fara takan masu irin matsalarta, a hankali aka fara ware mata idon har aka gama ta budeshi tar, da farko haske yaso yayi mata yawa kafin a hankali ta budeshi gaba daya. Likitan ya wawwara mata idon ya haska aka tabbatar babu matsala. Ya nuna mata Sageer dake tsaye yace "kin san wannan? Kinsan waye shi?" cikin sanyin muryarta tace "A a yau na fara ganinshi" yace "mr Sageer ka matso kaiwa matarka bayanin kanka" ya matso a darare kamar me tsoron magana yace "Sunana Mohd Sageer kuma ni mijinki ne anyi mana aure wata daya baya kika samu matsalar ido shine akai miki aiki" ta danyi jim kamar tana shakkar abunda ya fada tace "To sannu da xuwa mijina" sukayi dariya shida likitan jin abunda tace. Yadan gyara tsaiwa yace "ki kirani Sageer kawai babu damuwa" tace "to" likita yagama aune aunensa ya bata wani siririn glass din ido wanda xata dunga sakawa xuwa wani lokacin da idon xai sami kwarin da ake buqata ko kuma inxata kalli waya ko TV ko kuma kallon takadda da qarin magunguna sukayo gida.
Gidan Maitama ya ajiyeta gurin Bilki kamar yadda suka tsara xata xauna nadan lokaci a gidan Bilki xata saitata da koya mata wasu abubuwan na gida. Hannu biyu Bilki ta amsheta tayi mata masauki a dakin danta me shekaru 4 wato haidar. Sageer ya nunawa Bilki yadda xa a dunga bawa sakeena maganinta na ciwon ido dana kwakwalwa ya tafi gida yana cewa aransa nima dai na huta na yan kwanaki na kuma fuskanci aikina.
Bilki ta fara aiwatar da aikinta babu bata lokaci dake itama mijinta Maitama gurin aikinsu daya da Sageer kuma bata aikin gwamnati sai business da dinki shiyasa ta samu lokaci sosai, xatakai kimanin shekaru 27 shiyasa cikin qanqanin lokaci ta karanci sakeena yarinya ce me saukin kai da haquri kuma bata da son jiki. Ta fara tafiyar da sakeena a hankali saboda matsalarta komi inxatayi tare sukeyi kuma tana koya mata gayu irin nasu na masu wankewar ido.
Kwanan sakeena bakwai gidan Bilki ta saki jikinta sosai, kuma xuwan Sageer 2 kacal dubata saboda aikinsa.
A ranar data cika kwana 9 tafiya ta kama su Sageer shida Maitama xasuje Edo state yin wani aiki da ogansu Abdulfatah, yaxo sukai sallama da sakeena kamar masu tsoron juna suka tafi. Wannan tafiya taiwa Bilki dadi, ta dunga fita da sakeena gurare na bude ido kuma tana sai mata kayan kwalliya tana yiwa Sageer list din duk abunda ta kashewa sakeena. Satinsu 2 cur suka gama aikin daya kaisu suka dawo amma banda Sageer ya wuce can Katsina gurin ummansa saboda wata yaxo qarshe.
***** ***** ******* ******
A kano kuma a cikin wata na biyu da batan sakeena suka fidda tsammanin ganinta saboda duk cigiyar da ake ta nemanta babu amo babu lbr Deni ya jigita sosai yayi nadamar wulaqanta sakeena.
Dole aka tada bikin Fiddausi, Baba bashi da kudin yimata kayan daki amma yayi iya qoqarinsa ya hada 70k da kudin aurenta 50k ya tashi 120k ya bawa Hajjo yace a siyo mata abunda ya sawwaqa me hali baya fasawa ta raina kudin daya bata tace a wannan xamanin da rayuwa tai tsada 120k mexata siya a kayan auren budurwa? Yace shikam iya qarfinsa kenan. Tace "malam basai kaiwa Deni magana ba ya kawo wani abun ahada" yace "ke me xai hana kiyi masa ko ba danki bane ko kina xaton besan da bikin ba?" taja baki tayi shiru domin yanxu kunyar Deni take saboda abunda tayiwa sakeena kuma abunda ta kakkarba a gurinsa da sunan yiwa Fiddausi siyayyar aure duk sun qare abun malamai na raba sakeena da Deni da kuma mallakewa Fiddausi mijin da xata aura da kishiya. Kafin Deni ya dena bata saboda ta kore masa mata da tayi.
Haka biki keta qaratowa amma Hajjo babu kudin yin bushasha kamar yadda ta qudiri niyya gashi kuma gidan kishiya xa a kai Fiddausi. Dole tasa gonarta a kasuwa amma abun Allah akaqi koda tayawa balle asiya.🤣
Fiddausi kullum sai tayi kuka saboda abunda ya samu sakeena suke dariya na shirin samunta wato aure babu kayan daki. Har gara ma sakeena nata mijin saurayi ne kuma na gida. Ita kuwa gashi bare ga kishiya gashi ta gamayi masa qaryar har gara xa a kawota da ita saboda yayanta na aiki a wani babban company, kamar yadda Hajjo tasha alqawaranta mata.
Daga qarshe dai Iya da suka raina kuma suka dauketa maqiyiyarsu itace taiwa Deni magana ganin daga Baba har Hajjo kowa ya kasa tararsa da xancen kuma biki ya rage yan kwanaki kadan. Lokacin da tayi masa maganar hade rai yayi yace "Iya ai tunda sukai silar rasa sakeena sun dai nacin ko sisina" tace "a a Deni ai hannunka bai rubewa ka yanke ka yar, dole yan uwanka basu da wani sai kai tunda kana da hali ka duba Allah da kuma mahaifinka ka fiddasu kunya" kwallah ta cika idonsa yace "shikenan Iya sunci darajarki da kuma soyayyar da nakewa sakeena xan duba inga abunda xan iya"
A yinin ranar sai ga motar company dauke da kayan Dubai yan dauri set din gado dana kujeru da qatuwar katifa. Aka shiga da kayan mamaki ya rufesu domin basusan wanda ya aiko dasu ba, Fiddausi baki yaqi rufuwa sai washe baki take tana shafa kayan.
Da daddare an xauna cin abinci Deni a gaban kowa ya fadawa Baba Iya ce tasashi ya sayi kayan kuma Fiddausi taci darajar Iya ne da sakeena shiyasa ya saya. Baba yayi godiya da fatan Allah ya qara budawa ya kuma sakawa Iya albarka da kyakykyawan aikin da tayi. Fiddausi ma ta juya babu tirjiya ta godewa Iya da Deni dan tasan badan Iya ba datasha kunya a bikinta. Hajjo ta kuma tsanar Iya da sakeena wato ita da danta bata isa ba har sai wata banxa uwar riqon matarsa tasa baki sannan yayi mata abu ita da yayanta kenan? Suma dai Hadixa da Amina irin tunanin Hajjo sukayi Saddiq kuwa dama bayanan.
Sati na xagayowa akai bikin Fiddausi aka kaita dakin mijinta a tudun yola gidansu daya da kishiyar amma kowacce da part dinta kuma babu lefi dakin Hadixa yayi kyau an fita kunya amma fa ba kamar yadda ta shirgawa mijin qarya ba, a hakan ma dan anhada da sadakinta kuma ba aimata garar da take buri ba.
**** ****** ******* *****
Acan Lagos kuwa sakeena tayi tas da ita a qarqashin kulawar Bilki tayi bulbul saboda babu abunda ke damunta ko dogon tunani ba a bari tayi bisa shawarar likita. Ana gobe xai dawo kamar yadda Maitama ya fadawa Bilki tasa aka gyarawa Sakeena gashi a saloon duk da sakeena tafison kitso amma Bilki tace a barmatashi a tsefe akai retouching aka dora steaming yayi tsaho sosai aga nadeshi a band yana qamshin mayuka, har gida ta kira me qunshi tayi mata ja da baqi yayi tar akan farar fatar ta. Bilki da kanta ta xauna ta cirewa sakeena gashin fuskarta tas, abunda bata taba yiba tunda take a rayuwarta. Tasa ta qalqale duk wani gashi na jikinta.
A ranar Saturday ya dawo bayan ya shafe 6 dayx a Katsina, ya kwanta yayi baccin gajiya har xuwa yamma ya tashi ya gyara bedroom dinsa da baya bari masu aikin gidan su shigar masa. Xuwa magrib yayi wanka ya nufi masallaci har xuwa sallar isha a nufinsa inya fito daga sallar isha xai leqa gidan Maitama duba yarinyar can.
Acan kuma sai da magrib tayi Bilki ta tabbatar Sageer ya nutsu ya huta sannan ta saka sakeena tai wanka ta tsala mata kwalliya cikin wani baqin material cotton da akaiwa riga da skirt wuyan high neck da akayi da net har xuwa hannyen rigar tayi mata light makeup ta baxa mata perfumes masu sanyin qamshi da tsuma xuciya taci takalmi heel wanda Bilki tace dole ta koyi tafiya dashi tunda bata da tsawo sosai. Sakeena tai kyau kamar bestie na ranar award night 😜 tana sallar isha ta hada kayan sakeena tsaf a akwatina masu aiki suka tayata dauka duka nufi gidan Sageer, Bilki aranta tana cewa "ai dole yau gidan mijinki xaki kwana sakeena saboda tsaro irin wannan kyau da kikayi ai xamanki gidana hatsari don baka shedar namiji 😄" suna tafiya a hankali tana qara nunawa sakeena salon tafiyar dauke hankali ba yadda take buga sauri ba kamar be karbo Al jannah.
Sunje sun tadda Sageer bayanan sukai xango a falo Bilki na nuna sakeena yanayin gidan ta kuma shigar mata da kayanta dakin da Sageer ya gyara don sakeenar. Suna xaune kuku nata aikin jera abinci a dinning tana qara fadawa sakeena kullum tayi wanka da kwalliya sau biyu da safe da kuma yamma kan Sageer ya dawo tace "kuma karki adana kaya kiyi ta sakawa mijinki mai kudine shagon sutura guda ma xai iya saya miki indai kika iya jan hankalinsa" ita dai sakeena duk abunda aka fada mata cewa take to kuma tana riqeshi daram a kanta tunda kwakwalwar babu komi a ciki.
Acan kuma su Bilki na fita Sageer yana shigowa, suka danyi hira da Maitama yake fada masa sun tafi gidansa yanxu. Suna xaune a falo sai gashi ya shigo yace "ai yanxu daga gidan naku nake naje ganota akace kun taho" Bilki tana dariya tace "Eh na dawo maka da ajiyarka ne" cikin basarwa yana bude fridge din dinning area yace "kingaji da xama da ita kenan shiya kika dawo da ita ban nema ba" Bilki tai saurin tareshi da cewa "A a wlh ai sakeena bata da matsala balle a gundura da xama da ita, kawai dai naga kyan mace gidan mijinta shiyasa na dawo da ita" yace "hmmm amma dai kin fadawa dalibar taki banason shishshigi da takura da kuma shiga abunda be shafeka ba ko?" tai murmushi cikin duniyanci tace "karka damu na fada mata kuma dama ai nadawo da itane na jarraba kwaxonta inga ko ta dauki karatun dana kusa 1 month ina mata" haka dai sukai hirarsu ya gayyacesu cin abinci Bilki tace "a a munqoshi ko sakeena?" tace "Eh munci wata kaxa me daci da madarar da aka saka magani ko anty Bil... " Bilki tai saurin xungurarta jin xata tauna musu asiri, tai shiru. Ya xunkuda kafada na nuna be damuba.
Bilki ta sunkuya taiwa sakeena radar cewa "kul kika fada masa na baki wani magani inba haka ba xai dakeki, bakomi ake fada ba kinji?" cikin tsoro tace "to" jin ance xai daketa. Ya kallesu yana daga kan table yanacin abinci yace "Allah yasa dai ba gulmata ake ba naga kun koma rada" sukai dariya Bilki tai musu sallama ta tafi.
Sakeena taci gaba da xaman takura irin na baqunta ixuwa lokacin da Sageer ya gama cin abinci ya dawo kan kujera shima ya kunna TV, sai a lokacin ya lura da kwalliyar sakeena da fitinannen qamshin da take yayi saurin dauke idonsa a kanta ya mayar kan TV don karta kamashi yana kallon ta ta rainashi. Sunyi kusan rabin awa suna xaune shi yana kallon ball, ita kuma tana xaman kare a karofi babu rini ba matsa. Ta fara bacci yasa hannu ya kwantar da ita kan kujerar ya qurawa qunshin hannunta ido yakai hannunsa ya shafa, shi dai yana son qunshi. Tara nayi ya kashe kayan kallon, ya dauki sakeena ya kaita dakinta ya qara kallon qunshin kafar ta ya sumbaci tafin qafar ya kashe mata fitila ya fita.
Tana cikin baccinta ta farka a raxane, duhu ya mamaye dakin ta laluba kusa da ita taji babu kowa ta miqe don fita daga dakin ta kwabxa karo da sif din dakin ta quma kanta, ta rangada ihun axaba. Sageer dake shirin fita harkarsa ta bariki ya jiyo ihunta ya doka tsaki yace "abunda nake gudu kenan yanxu xata hanani rawar gaban hantsi, mtseww me ake da aure?" Ya nufi dakinta ya kunna fitila ya sameta tsaye dafe da goshinta tana kuka, yana kunna fitila ta nufeshi ta rungumeshi tana cigaba da kukanta. Yayi seqeqe tsaye da hannaye a sake yanajinta jikinsa dake dama a cikin yanayin yake sai yaji gaba daya ya kasa komi, yayi qarfin halin kai xuciya nesa ya lallabata ya kwantar da ita tare da bar mata fitila a kunne. Sai dai me ?ya kadata dambu taliya taqi xama a dakin ita kadai a fadarta wai tsoro takeji ta riqeshi tamau ta hanashi fita. Ala dole ya tafi da ita dakinsa da yaga tana kuka. Ta samu gefen gadonsa ta xauna shi kuma ya cire kayan da yasaka don fita ya canja xuwa na bacci. Lokacin kuma yarinyarsa wacce sukai yanxu xasu hadu a gidanta ta kirashi me suna chinaxo yar qabilar Ibo, be daga ba sai test yayi mata saboda ganin yadda sakeena ke binsa da ido. Yace mata kawai xasu hadu gobe Sunday yanxu bashi da lfy.
Ya kwanta a gadon ya juya mata baya yayin da take xaune tana kallonsa jimawa kadan ya tashi ya kashe fitila yace "To kinxo kiyumun dundurus inbaxaki kwanta ba ki tashi ki fita falo, kin hanani fita keba wata tsiyar xaki iya bani ba" Ya koma ya kwanta yana mitar "haka kawai daga temako na debowa kaina jangwam tun kan aje ko ina ta fara takuramun" ya tsaya da maganarsa lokacin dayaji sakeena ta qanqameshi ta baya, yayi dib ya fara qoqarin banbare hannayenta amma ta riqeshi kam. Sai datayi bacci sannan ya iya cire hannunta daga jikinsa ya juyo ya shimfideta ya fara aikin binta da kallon qurullah. Tayi masa kyau sosai ya hadiye yawu, yakai bakinsa ya sumbaci lips dinta daga haka ya kasa controlling kansa duk da wata xuciyar na kwabarsa da ya haqura yarinya ce qarama amma kuma sai wata ta kuma cemasa ai itace ta hanaka fita don haka kawai kayi haushin kaxa huce kan dami.
Yabi shawarar xuciyarsa ya fara binta a hankali dake dan duniya ne kuma dan hannu a harkar mata, wasan beyi nisa ba sakeena ta farka daga dan baccin daya sureta ta danyi turjiya kadan saboda abun ya kwanta mata, Sageer dan duniya ya hana turjiyarta tasiri da salonsa. Yacigaba da binta a sannu dan a xatonsa budurwa ce, sai dai yasha mamaki lokacin da yakai gaci duk da ba wata alama ya samu me qarfi ba amma dai yasan tabbas duk inda sakeena ta fito tasan namiji koda kuwa nadan lokaci kadanne. Haushin tarar da ita fanko da yayi bata kawo masa budurcinta ba yasa ya xage qarfinsa sosai ya gurjeta son ransa kamar bada yarinya qarama yake mu'amala ba sai da ta fara kwarara masa ihu sannan ya gyaleta. Ya kwanta kusa da ita yana kallon ta tana shashsheqar kuka be hanata ba kamar yadda be dena mamakin yadda akai yarinya qarama kamar wannan wacce ya haqiqance baxata wuce 18yrs tasan namiji. Bawai ya jita sako sako bane, a matse take amma dai tabbas yasan wani ya rigashi saninta a matsayinsa na mijinta na farko (a tunaninsa) yaja tsaki a xuciyarsa yace "yar iska yanxu haka ma saurayinta ta bawa ya dana garin soyayyarsu ta banxa ta kuruciya, wai meyasa duk mata yan iskane marasa kamun kai? Inyana ganin wadan da yake watsewa dasu manya ne wadanda suka riqa kuma suka maida karuwanci sana'arsu to ita kuma wannan qaramar yarinyar daya tabbata har yanxu tana qarqashin kulawar iyayenta meyasa xata bada kanta wa namiji a titi?" ya dunga jan tsaki, yaji duk mugun haushinta yakeji saboda samunta da yayi fanko. Ya daka mata tsawa lokacin da yaji tana qara sautin kukanta. Yace "Da Allah rufan baki shashasha kukan me xakiyi bayan kin barar tun awaje?" da muryar kuka tace "zafi nakeji sosai abunda kaimun da xafi sosai" yayi mata kallon kin rainamun wayo yace "Lokacin da kika bawa wancan dan iskan ya gama dake bakiji xafin ba sai ni dana biya sadakinki?" ta katse kukanta tace "wa nabawa? Kaima kana ganin abunda nake ganine? Da kana yimun sai nake ganin kamar na tabayi da wani amma kamar a mafarki" yayi saurin katseta da cewa "karki fara yimun shirmenku na masu gotaccen memory ki kwanta kiyi bacci inkika tsawaita tunani kika janyowa kanki ciwon kai ba ruwa na" ya juya baya ya kyaleta.
Sai kuma ya fara tunanin gamsuwar da yayi da ita da xumar daya dandana kamar ba qaramar yarinya ba, xai iya cewa betaba jin hakan ba ga wata mace duk kuwa da yasan mata da yawa. Haushin rashin samunta da budurci shiya hana jin dadinsa tasiri.
Yinin ranar lahadi wato washegari kenan ya yini yana kyararta da hantararta domin duk yadda yaso kauda abun da yaqar xuciyarsa ya kasa sosai yakejin haushin wai wannan yar ficiciyar tasan namiji. Abu kadan intayi cikin rashin sani ko inta mishi magana saiya daka mata tsawa. Ta samu guri ta rakuye akan kujera, ita dama tun tana lfiyayyarta batasan tsawa bare kuma yanxu ga lalura. Ko sallah sai yace tayi takeyi, tun rana taqi cin abinci har xuwa yanxu da yamma ya kada ya raya amma taqi karba gashi bata sha magani ba daga qarshe yace "kinwa kanki domin cikinki xaki kai ba nawa ba" amma abun mamaki rashin walwalarta da cin abinci ya tsaye masa arai.
Da dare yayi yaga abun fa nayi ne saiya watsar da makamansa, ya xauna ya dunga aikin lallashin sakeena. Da kyar ya shawo kanta ta haqura taci abinci ya bata magunguna tasha yace taje tai wanka ta sake kayan data saka tun safe.
Ya sauke ajiyar xuciya bayan tafiyarta a fili yace "matsalar auren qananan yara kenan, abu kadan suyi fushi" To waishi meye nasa na fushi dan bai sameta da budurci ba, ko shi din saurayi ne? Amsar itace a a shiba saurayi bane duk da kuwa yana amsa sunan samartaka amma ai a badini shima ya barar da tasa samartakar a titi. To ta iya yiyuwa itama sakeena hakance ta faru da ita ko kuma wadanda suka saceta ne sukai mata fyade. Inma Kuma ba haka bane may be yawan barikin da yayi ne Allah ya hukuntashi da auren ragowar wani, dole ne yayiwa sakeena uxuri domin besan komi daga tarihinta ba. Wannan shine tunanin Mohd Sageer kuma da wannan tunani nasa ya watsar da makamansa yayiwa kuskuren sakeena kwalliya da cewar tsautsayi ne.
Fitowarta yasashi miqewa tsaye babu shiri, tayi kwalliyarta cikin fitet gown ta atamfa, a ransa yace wai ita wannan yarinyar batasan halittar da Allah yayi mata bane xatayi irin wannan kwalliyar a wannan daren sai tasa nayi mata illah?
Ya jata jikinsa ya biye mata suna kallon tashar Bollywood ana haska wani india. Da wuri ya nemi makwanci saboda duk yadda yaso ya daure ya kasa kawai so yake yaji abunda yaji daga jikin sakeena jiya. Yau kam a hankali ya bita cikin soyayya itama ta bashi hadin kai suka shayar da juna soyayya me shiga rai.
Tun daga wannan rana Sageer ya maida sakeena yar gata domin ya gama yarda itace matar ya dade yana jira ya aura wacce kuma qaddara ta hadasu. Ya gane ashe shi duk shekarun baya da yake bin matan kwararo shirme yayi, domin sai yanxu daya dandani yar baiwa sakeena yasan xaqin mace kuma ya gane banbancin matar aure da matan titi sai yakejin ta xamxam ba kamar wadancan karuwan da yake biba wadanda kwaskwarimar da sukeyiwa kansu bata hana yajisu a rarake kamar ruftacciyar rijiya, shikam yanxu ya gane gaskiya ya dunga godewa Allah da ya hadashi da sakeena cikin qanqanin lokaci suka xama wadansu irin ma aurata masu matuqar so da tattalin junansu barikin da yake yi ma tuni ya tarkatashi ya watsar domin sakeena na bashi fiye da abunda yake samu a waje, gata da biyayya da tsafta da kuma kwalliya, daya abun burgewa shine sai yadda ya juyata bata masa musu a duk abunda ya sakata. Barin kudi yake mata kamar besan xafin nema ba Bilki na dada xugashi.
Itama anata bangaren sakeena ta mace murus akan sabon mijinta Sageer, ita kawai abunda ta sani kenan, dama kuma ita din yar soyayya ce sai yanxu dama ta samu babu takura bare tsangwama babu wahala ko kadan taci abunda takeso intaga dama ta yini tana bacci intasha magani in kuma taga dama ya rakata gidan Anty Bilki inxai fita inya dawo yaje su dawo tare, babu cas babu as ta kwana a AC kuma ko a TV taga abu ta nuna tanaso Sageeer saiya saya mata. Yawanci weekend yakan dauketa da yamma su xaxxaga gari. Ya bude mata a acct a firstbank ya xuba mata maqudan kudade. A irin yawansu da suke wata ranar Sunday taga wata mace na jan mota ta kalleshi tace "Sageer" ya kalleta tana gefensa a mota tana sanye cikin biri da wando na jeans da farar riga aciki ta yafa gyale a kanta tayi kyau over ta qara cika tai fari tas cikin soyayyarta yace "naam my Sakeena" tacigaba da magana "ina sha awar inga ina tuqa mota wlh" ya xare mata medical glass din idonta yaja hancinta yace "ban cika son kisa glass dinnan ba duk da yana qara miki kyau ne, nafison idonki ya saba da gani ba tare da glass ba. Yanxu fadamun kinason iya mota ko kinaso insai miki mota?" tayi dariya tace "nifa kawai iya mota nace xaka canjamun magana" shima dariyar yayi ya kwaikwayi maganarta yace "to xaki iya mota kuma in shaa Allah xan sai miki mota wacce ba gama gari ba, kamar yadda kike, xansa a kawo miki tsaleliya irinki." ta cakumeshi tana murna da godiya ya cireta jikinsa yace "ke bakisan xa a iya samun matsala ba kikaimun wannan cakumar anan?"
A irin wannan ranar suna xaune falo takai wata channel da ake koya kwalliya tasa glass dinta don rage haske ta qura ido tana ganin yadda suke. Cikin nutsuwa ya kwantar da kansa akan cinyarta ya shafa fuskarta yace "kinaso ki iya ne?" tace "sosai ma kuwa anty Bilki ma tana koyamun ai" yace "to ai sai inkaiki inda xaki koya, ki koyo ki dunga yimun ko"
Wannan shine salan rayuwar Sageer da sakeena komi nasa yana sadaukar mata dashi, ya fada soyayyar tsundum yadda be taba xataba
Sakeena Mohd Sageer kamar yadda ake kiranta yanxu me shekaru 19 ta xama ajebo kuma yar gata a gurin mijinta Sageer. Ta samu shiga babbar makarantar koya kwalliya a garin Lagos wacce akeyin 2 months duk rashin fahimtar mutum ya iya. Duk ranakun weekend Sageer ke koya mata mota sunayi suna sheqa soyayyarsu. Cikin qanqanin lokaci ta iya mota, shi kam sageer har mamakin kaifin basirar sakeena yakeyi.
koda wata yaxo qarshe saiya kasa tafiya Katsina yabar sakeena a hannun Bilki kamar yadda yayi niyya, sai yaji sam baxai iya yini cur be ganta ba bare kwana. Dan haka yayiwa ummansa qaryar cewar bashi da lfy baxai samu xuwa a wannan watan ba, Allah sarki uwa ta karbi uxurinshi tai masa fatan samun lfy ya kashe wayar ya qara rungume sakeena dake bacci a jikinsa.
***** ***** **** ****** ***
A cikin wannan lokaci aka gama ginin company su Deni dake Kano kuma ya nemi transfer saboda xaman Kaduna ya fice a ransa tunda ya rasa sakeena acan. An dawo dashi Kano kamar yadda ya nema kuma ya samu qarin matsayi a matsayinsa na accounter na company gaba daya ranar daya samu wannan matsayi yayi kuka yayi fatan inama ace sakeena tananan suji dadin rayuwarsu yanxu tunda an fara kiransa yana amsawa. Ya ware maqudan kudade ya siyawa sakeena yari da sarqa qirar Dubai harda xobuna guda biyu, ya adanasu da burin Allah ya nuna masa ranar dawowar sakeena rayuwarsa ya danqamatasu a matsayin kyautar murnar dawowarta.
Yayi amfani da damar daya samu ta dawowa aiki Kano ya koma makaranta ya fara Msc dinsa yayin da wata xuciyar tasa fara yadda da maganar Iya na cewa sakeena bata raye ganin anshiga wata na hudu da batanta amma babu ko lbrin wanda ya taba cewa ya ganta. Ya daukewa Baba siyan kayan abinci da sauran wahalhalu makamantansu, Iya ya kafa mata jarin kayan masarufi yayin daya bawa Hajjo kudi masu yawa ta qara jarin gasara. A nata bangaren Hajjo tana matuqarso taiwa Deni maganar aure domin batason xamansa haka amma tana tsoron kartai masa magana ta tado maganar sakeena tada fara kwanciya hartasamu sukuni. Amina ma dai ita da Hadixa ya sakasu sun xana jarrabawar jamb tunda xaune suke basa komi.
***** *** **** ******* ****
Sageer xaune cikin office dinsa a ma'aikatarsu yanata aikin dayasha kansha wani gefen kuma ya na tunanin sakeena dason jin muryarta, yayi tunanin kodai ya se mata waya saboda su dunga soyewa inya samu sauqin aiki a office. Yayi saurin kore wannan tunanin saboda bayason ya saiwa sakeena waya ta tuna number wani acikin danginta ta kirashi, donshi yanxu bayajin xai iya rabuwa da ita don haka cigiyarta da yakeyi afarkon tsintarta yanxu ya dena burinsa kawai su xauna tare don yagama macewa akanta.
Yana tsaka da wannan tunani yana murmushi ta turo kofar ta shigo. Ya dago kai ya sauke ido akanta, yasha mur kamar be taba dariya ba ya miqe tsaye yana nunata yace "ke! saboda ke yar iskace yar tasha da wannan shigar kika shigomun office salon ki zubarmun da mutunci? OK kinxo ki taunamun asiri kenan ki nunawa kowa irin mu'amalar da nake dake?" Chinaxo tacigaba da tauna cingam dinta yana qasqas bata kula Sageer ba harya gama banbaminsa sannan ta xauna kan table din gabansa ta xuge Jakarta ta ciro xurmemen hijab tace "calm down my luv, kaga nasako jalbab tundaga gida har xuwa cikin ma aikatarku na shigo kowa yanamun kallon mutuniyan kirki, sai da naxo kofar office dinka sannan nacire na shigo dan kaga kwalliyar danayi maka"
Ya dan sauke ajiyar xuciya jin abunda tace. Batare daya kalleta ba yace "to meye ya kawoki?" ta cire takalman qafarta ta dora kafar akan cinyarsa cikin kwarkwasa tace "kewanka ne ya isheni kai kuma kullum kana cikin bani uxuri kaqi bari mu hadu shiyasa naxo inga zahiri" Ya ture kafarta akan cinyarsa yace "to kin gani nasamu sauqi yau na fara fita kije xan nemeki" ta tsaya seqeqe tana kallon sa tace "Sageer dole akwai wani abu a qasa, baka yaba kwalliyata ba baka rungumeni ba kamar yadda ka saba inmun hadu. A yadda nasanka nasan baxaka iya xaman wata guda cur ba batare da mace ba balle har watanni biyu da rabi. Ta xaro masa idonta ta qarasa cewa, tabbas jita jitan da ake kawomin kayi aure gaskiyane domin last Sunday ma Oyiza ta fadamun ta ganka da wata small girl a bakin beach" ya dan tsorata jin taji xancen aurensa yasan Chinaxo bata da hankali akan kishi yace "ke banason shirme aikinsan aure baya cikin agender ta, nace ki tafi karwani yaxo ya ganki in antashi office xan biyo gidanki, ki dakamun sakwara" itama ta danji dadi abunda yace amma kuma baxata iya haqura da sageer ba don tayi missing dinsa tana mugun sonsa shiyasa tayi watsi da duk masoyanta take dating dinsa gashi yana sakar mata kudi.
Tasawa office din key, ya dago da nufin tambayarta meye haka, ta fada jikinsa ta fara shafarsa. Yakasa kubucewa sharrin tsohuwar karuwa dole badan yaso ba ya biye mata suka tafka masha'a a office dinsa, ya dagata yayi tsaki bayan ya shafe tsawon lokaci yana abu daya amma ya kasa samun gamsuwa yadda ya saba a jikin sakeena. Gashi ta tayar masa da kwadayi kuma ta gaxa kawar masa dashi sannan tasa yayi zina abar da yayiwa Allah alqawari ya dena tun randa ya fara kusantar haliliyarsa sakeena, baqin ciki yasashi ya rufeta da duka da belt din uniform dinsa. Sai da yayi mata lilis sannan yasata tasa kayanta ta dora hijab akai tana kuka tana kallon sa a tsorace dan yau sageer ya fara dukanta a tsahon xamansu. Ta bude baki xatai magana ya hanata ya jawo loka ya ciro damin kudi guda biyu ya watsa mata yace "indai kinason kanki da lfy kibar rayuwata, da gaskene nayi aure kuma duk abunda nakeso ina samu shiyasa na dena nemanki ina matuqar son matata ki dena bibiyata, Allah ya shiryeki kamar yadda ya shiryeni. Napep din da nayi miki alqawari xansa akawo miki in anjima." ya bude office din ya cillata waje ya kulle ya dawo ya shige toilet ya warewa kansa shower.
Yinin ranar yayishi babu dadi, yana gani yaci amanar matarsa kuma ya karya alqawarin da yayiwa mahaliccinsa kuma ga wannan yar iskar ta tayar masa da kwadayi yaji bashi da burin daya wuce ya koma gida ya samu nutsuwa gurin sakeena. 4 tanayi ya tattara komatsansa ya nufi gida.
Ya samu sakeena xaune a falo tana aikin kallon TV. Ya saka hannu ya kashe, tana sanye cikin Ibo gown ta taso da sauri ta rungumeshi tana cewa "sannu da xuwa yau ka dawo da wuri" yana shafa bayanta yace "yawwa my sakeena bana hanaki yawan kallon TV ba saboda idonki?" ta qara shigewa jikinsa tace "ai bayayimun zafi kuma inasaka glasses don rage hasken TV din" yace "Eh ai glasses dinne banaso ki saba da sakawa" tace "to yi haquri sageer xan rage" yaja hancinta ya rataya jakarsa ya sabeta suka nufi daki. Ya kwantarta ya bi bayanta, koda ya nuna mata ga abunda yakeso bata hanashi ba biye masa tayi suka raya sunnah kuma wannan daliline yasa yake qara sonta. Ya kwantar da ita akan qirjinsa yana shafa naked skin dinta yace "my sakeena kiyi haquri kinji naci amanarki yanxu a office" ta dago kanta xata fara magana ya saka hannunsa ya toshe mata baki yace "karki fara yimun tambayar nan taki kamar yar jarida, kiyi haquri baxan kuma ba" tace "to kayimun wannan kiss din da kakemun" yana dariya yaja hancinta yace "ai yau kece xakiyimun tunda kullum ni nake miki kuma kinkasa koya har yanxu" takai bakinta kan nasa yayi shiru ba tare daya shirya ba suka dau tsawon lokaci suna tsotsar juna kafin su sarara su kalli juna suyi dariya, suka rungume juna.
11 dayx da faruwar haka ta kama Monday, Sageer ya fita sakeena taso shiga gidan Anty Bilki dan harta fada masa yace taje, tayi wanka xata fita wani irin bacci ya cika mata ido ta kasa fitar ta kwanta. Ashe tsautsayine ya xaunarta.
10:30 AM Chinaxo taiwa gidan tsinke, ta aiki yarinyar dake aikin goge falon tace ta kira mata Madam dinta ita qawartace gurinta taxo. Yarinya ta shiga dakin sakeena isar da saqon. Chinaxo ta harde tana ganin tsalelen gidan Sageer wanda bata taba xuwa ba ko sanin gidan bataiba yanxu ma sai datayi da gaske kafin ta samu a nemo mata unguwar da yake tayi dariya tana cin cingam ta ayyana wannan gida natane ita da husband to be dinta Sageer.
Sakeena ta fito sanye cikin riga da wando yan kanti iri daya, Chinaxo ta bita da kallo tundaga qasa har sama ta jinjina kai lallai sageer ya cika dan iska wato sai daya gama watsewa da ita shine yaje ya auro wannan tsaleliyar qaramar yarinya ya watsar da ita. Gaisuwar sakeena ta katse mata tunaninta ta juya ta kalli sakeena a tsugune tana gaisheta.
Bata amsa ba sai saka hannu datayi ta waskawa sakeena mari, ta dafe kunci ta dago tana kallon ta tace "me nayi miki?" Chinaxo ta miqe tsaye tace "Ubanki kikaimun, kin dauka shikenan kinmun kwacen saurayi xan kyaleki? ta juya tace dubeni meye kike dashi wanda bani dashi harda xaki dauke hankakinsa? dirine bani da shi ko farar fata ko kuma kyau? me kike bashi wanda yafi wanda nake bashi a baya?" sakeena tana dafe da kunci tanabinta da kallo. Chinaxo ta sunkuyo ta dubi xoben hannun sakeena tace "shiya baki wannan ring dinko? Kunyi alqawari ne ya saka miki ko meye?" sakeena tai baya cikin tsoro. Chinaxo taja hannun sakeena ta xare xoben ta cillashi jaka, tacigaba da bala'i cikin harshenta na Ibo.Cikin sauri kukun sageer ya kirashi a waya yace gida ba lfy wata mata taxo tana ta yiwa madam masifa.
Chinaxo ta ciro wayar da taxo da ita ta fara laftawa sakeena tana cigaba da masifa tana cewa "inkinason tsira da ranki ki gudu garinku ki barmun mijina inba haka ba kullum sainaxo na miki dukan da yafi wannan" Sakeena ihu take tana neman temako amma anrasa me cetonta acikin masu aikin gidan dan suma sun tsorata da lamarin yar tawaye Chinaxo.
Sageer yayi parking a cikin hanxari ya cakumo me gadi yace "meye amfaninka kana ina wata ta shigemun gida tana tayarwa matata hankali" cikin tsoro me gadin yace "wlh oga ta rufe fuskarta bansan kowacece ba tacemun qawar madam ce shiyasa na barta ta shiga" ya sakeshi da gudu ya nufi cikin gidan.
Lokacin daya shiga ciki sakeena ta daku tayi laushi tiqis a hannun Chinaxo. Baiyi wata wata ba yana xuwa ya suri Chinaxo ya dagata sama duk girmanta ya danqara da qasa yasa hannnu da qafa ya dunga jibgarta. Ya juya ya dubi sakeena dake tsugune tana kuka jikinta rudu rudu da shatin wayar wuta. Ya jawo wayar da bai tantace kota meye bace ya shiga shimfidawa Chinaxo tana ihu tana xaginsa sai da ya mata liqis itama sannan ya kyaleta ya dakko waya ya kira police yace suxo gidansa yanxu ya musu kwatance. Chinaxo dajin ance police tasa kururuwa tana bashi haquri ta ciro ring din sakeena data kwace ta bashi tace wlh ta tuba gama xobenta ya bata, ya karba ya kuma kifeta da mari. Police suna xuwa yace su kwashe masa ita ya basu kudi yace su xuba mai a mota ya kalli Chinaxo yace "Inna kuma ganinki a rayuwata kotu ce xata rabamu" suka jata sukai waje da ita tana ihun fadin "Sageer don't do this to me" (hmmm bariki kenan alalan gero inbaka iya ba ta kwabe maka)
Ya sauke numfashi ya nufi sakeena jikinsa a sanyaye yana riqe kunnansa alamun bada haquri. Tai xunbur ta tashi xata gudu, ya damqota ya riqe ta saki ihu ta gartsa masa cixo a hannu ya saketa babu shiri ta gudu daki ta murxa key.
Sageer ya samu wata irin faduwar gaba, mekenan kardai wannan hatsaniyar data faru tayi silar dawowar tunanin sakeena?????? Qaqa qara qaqa.
Hajia 😊
[7/31, 2:25 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣8⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
#™Sagna# inji Anty sis😄
Sageer ya shafe kusan 1 hr yana buga kofa da ban haquri amma sakeena taqi bude kofa, ya haqura ya koma office bayan yawa me gadi warning din karya kuma barin kowa ya shiga sai da ixininsa indai ba Bilki ba don ita kadai sakeena ta sani.
Sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta bude kofar ta fito jikinta duk ciwo yake, tayi wanka da ruwan xafi kawai saboda gurin daya fashe ta koma ta kwanta don batasan abunda xata kumayi na temakon kantaba bayan wannan. Xaxxabi ya rufeta ta qudundune guri daya.
Sageer ya yini xuciyarsa na tuquqin dukan da karuwarsa tayiwa sakeena ya kuma tsanar rayuwar bariki, ana idar da sallar la'asar ya taho gida don ya lallashi sakeena.
Ya sameta a kwance ragab hankalinsa ya tashi sosai ya dakkota ya dorata akan cinyarsa, ya dakko first aid kit ya bata paracetamol tasha ya samu towel yasa a ruwa ya dunga goge mata jikinta. Tana kwance a kansa ta koma bacci, bata farkaba sai wajen 11 na dare ta miqe ta xauna kan gadon, ta tabashi yayi firgigit shima ya xauna ya taba jikinta yaji babu xaxxabin akai hannu goshinta shima yaji sanyi. Cikin sanyin murya tace "yunwa nike ji" da sauri ya sauka kan gadon, jimawa kadan ya dawo da tray dauke da ruwan tea sai soyayyan kwai da jellof rice. Taci ta qoshi, ta miqe taje tai brush ta qara wanka.
Tana fitowa ta sameshi ya xame ya tsuguna ya fara magana "Sakeena kiyi haquri, kuskurena ya jawo an taba lfyar jikin ki wadda tai miki wannan aikin girl friend dinace amma na rabu da ita saboda ke, ina sonki nayi miki alqawarin haka baxata kuma faruwa ba dan Allah kiyi haquri ki yafemun" ta xauna tana masa murmushi, shima ya tashi ya xauna ta kwanta a jikinsa. Yana shafarta yace "bakice komi ba my luv, kin yafemun?" ta gyada kanta, ya kamo hannunta ya saka mata xoben da Chinaxo ta cire mata. Ta danyi dum tana qoqarin tuna lokacin baya da kusan hakan ta faru da ita wani ya saka mata xobe. Amma kuma tana kokarin tunawa kanta ya fara ciwo, tasa hannu ta dafe kanta. Ya tambayeta lfy? Tace "inaso in tuna wani abune kuma nakasa kaina ya fara ciwo." ya kwantar da ita ya fara lallabata da kalaman soyayya yana cewa "karki takurawa kanki kinji my sakeena saboda lfyarki, karki kuma qoqarin tuna komi sakeena wlh ina sonki inaji kamar soyayyar ma tamun yawa baxan taba cutar dake ba duk abunda kikeso sakeena xanyi miki" tana shafa sumar kansa tace "nima ina sonka sageer ba kai daya ne cikin soyayya ba" sukai murmushi yace "to muyi alqawari mana sakeena tunda mun yarda munason juna" tana binsa da kallon mamaki tace "wane irin alqawari kenan?" ya tashi ya xauna ya riqo hannayenta yace "muyiwa juna alqawarin duk wuya duk dadi duk rintsi baxamu rabu ba, koda buqatar rabamu ta taso anan gaba" ta gyara xama tace "su waye xasu rabamu sageer?" yayi saurin gyara kuskurensa yace "kamar iyayenmu in sunji budurwata ta dake ki" cikin xaquwa tace "su waye iyayen namu a ina suke Dan Allah" ya kamota ya kwantar a qirjinsa yace "suna arewa ne mu kuma kinga nan a kudu muke. Mubar wannan maganar plz bani lbr wace irin kalar mota kikeso?" da haka ya shashantar da maganar a wannan dare.
Bangaren su Deni kuwa al amura suna garawa kamar yadda ya xata se matsalar rashin sakeena daya kasa sabawa da ita. Yana xaune ne a gidansu a dakinsa dake soro wanda ya gyarashi yayi dai dai dana matashin me kudi ba jobless ba kamar yadda yake ada, ya sayi motarsa me dan saukin kudi da ita yake xirga xirga tsakanin xuwa office da makaranta.
Shi da Iya da Baba da duk wani masoyinsu kullum suna adduar Allah ya bayyana sakeena amma Hajjo tunda taga an share maganar ta daina damuwa akan batan sakeena kuma ta dawo da wasu daga cikin halayenta ita da Hadixa da kuma Amina.
******* ******* ***** ****
Sakeena angama makarantar koyon kwalliya an karbi certificate da kuma kit din kayan kwalliya. Ta fara tsantsarawa sageer kwalliyar data koyo da kuma dinkin da anty Bilki ke tsantsara mata tana kashe kala dasu, ta gama siye xuciyar sageer da salonta barin kudi yake mata babu ji babu gani, sutura kamar xata bude fashion design ga golds da yake siya mata. Ta qara cika ta xama mace sosai tayi fari tas shi kansa sageer bai gajiya da kallonta yana kuma tasbihi ga mahallicin kyakykyawar matarsa da adduar sakawa iyayen sakeena da alkhairi duk sanda ya kalleta, yakance wannan mata ta iya haihuwa (babar sakeena)
Wata yaxo qarshe dole ya nufi katsina a jirgi ranar Friday bayan sunyi sallama da sakeena cikin wani irin yanayi na qaunar juna, ya barta a gidan Maitama gurin Bilki. A nufinsa yayi kwana 2 ya dawo ranar Sunday.
Amma koda yaje katsina saiya nemi xaman lfy ya rasa, ya rasa inda xai tsoma kansa yaji dadi tunanin sakeena da kewarta ta addabeshi kamar ya shekara be ganta ba. Ummansa ma ta rasa kansa, sai tana masa hira sai ta lura hankalinsa baya gurin dole ta rabu dashi don ta tambayeshi sai yace babu komi. Ya kwana cikin kewa da wani irin hali da baxai kwatantu ba, ya gane infa yanason xaman lfy kawai ya koma ga sakeena. Babu shiri ya hada karonsa washegari yayiwa umma karya cewar anmasa kiran gaggawa ne daga Lagos, ta hada masa kayan girki rankata kaf kamar yadda ta saba bashi inyaxo.
Qarfe ukun rana ya dira a falon gidan. Maitama da Bilki da dansu Haidar suna falo yayin da sakeena kecan daki a kwance ita cikin kewar Sageer, yana tsaye rataye da jaka ya kwallah kiran "my luv Sakeena" kamar a mafarki ta tsinkayi muryar sageer tayo falon da gudu, ya bude mata hannayensa ta fada ciki ta qanqameshi tana cewa "ina sonka Sageer, ban xaci ganinka yanxu ba" ya cirota daga qirjinsa ya sumbaci lips dinta yace "nima ina sonki sakeena rayuwa babu ke xataimun wahala koda na kwana daya ne" Maitama da Bilki suna kallon su da mamaki.
Maitama yayi gyaran murya, suka farga suka Saki juna ya kalli Sageer yace "kai! Dama ka iya soyayya? Lallai sakeena kinyi qoqari Allah yayi miki albarka" ta sunne kai jikin sageer cikin kunya. Bilki tace "ai dalibata babu lefi akwai kwanyar daukar darasi, danma ta dena xuwa makaranta da tuni ta wuce haka" sageer yana qara riqe sakeena a jikinsa yace "nagode haka Bilki baxata dawo makarantarki ba domin inta iya fiye da abunda ta iya yanxu, xaucewa xanyi akanta" sukai dariya suka dan taba hira yaja matarsa suka wuce gida.
Soyayya ruwan xuma Sageer da Sakeena sun xama tip da taya soyayya suke kamar suje a waldacesu. Babu matsala babu takura yana yawan fita da ita guraren shaqatawa da dadadre da kuma weekend sune cinema, eatry da shopping mall.
Matsalar farko data fara kunno kai a xamansu shine qoqarin da sakeena keyi na tuna rayuwarta ta baya da temakon magungunan da aka bata, sau tari in tana abu ko in Sageer yana mata wasan soyayya sai ta dunga tuno kamar hakan ya taba faruwa da ita, amma kuma image din is not clear a dodon photo yake xuwar mata. Ko kuma ta dunga ganin kamar ta taba rayuwa da wasu mutane a baya amma ta kasa tuna kosu waye. Ana cikin haka ta fara tuna rayuwarta ta qauye ita da Nura qaninta, amma kuma bakomi take tunawa ba dai dai kun abubuwa take tunawa.
Ranar data fara tunawa Sageer na dawowa ta tareshi da tambayar "Sageer ina Nura?" cikin mamaki ya dubeta yace "waye kuma Nura" tayi dariya tace "qanina mana Nura, kasan ai Gwaggonmu mu biyu ta haifa ni da shi" ya danyi dum yace "yana nan mana acan ina xashi"
To wannan shine mafari, duk sanda sakeena ta tuna wani abun saita tambayi Sageer wanda shi kuma hakan yake mutuqar daga masa hankali.
Ranar da hankalinsa yayi mugun tashi itace ranar da sakeena ta tambayeshi tace masa "Sageer wai waya aura maka ni?" a kidime yace "wace irin tambayane wannan sakeena?" ta bashi amsa da cewa "saboda naga Gwaggo da Baba sun mutu kuma Inna bata sonmu ni da Nura shiyasa na tambayeka" ya qura mata ido yana tunanin kenan sakeena marainiyace gaba da baya. Ta shafa fuskarsa tace "kaji?" ya dawo hayyacinsa ya daure fuska ya riqo qugunta da hannayensa biyu yace "sakeena kina qaunata da son xama dani?" bata bashi amsa ba sai kallonsa take yacigaba da cewa "indai kina qaunata sakeena ki daina tuna rayuwarki ta baya kuma ki daina tambayata" jiki a sanyaye tace "to na dena kayi haquri" ya rungumeta tsam yace "yawwa my sakeena I luv u"
Matakin da Sageer ya dauka shine dena bawa sakeena maganinta na kwakwalwa sannan ya hanata yawan kallon TV saboda kar garin kallo taga abunda xai tuna mata rayuwarta ta baya, ya rufe duk wasu channels masu shirye shirye ya bar yan kadan suma kuma sai baya nan take kallon. Ya qara kusanci da ita sosai, kuma shi duk yayi hakanne don ya tsira da ita domin tunda ya fuskanci marainyace kuma ta fara tuna wani shashin na rayuwarta ya quduri aniyar kore mata wancan rayuwar da kuma riqeta muddin ransa tunda bata da iyaye ba shikenan ba sai suyi xamansu. Ya kasance ya saba rayuwa da mata yan gayu kuma yan duniya wadanda suka dauki gayu da gyaran jiki kamar ibada dan haka ya maida sakeena irin kalar wadancan matan yar gayu kuma wacce ta kware wajen iya tsara kwalliya da tsafta. Itama ta dauki darasinsa sosai ta riqe tamau ta saba da gayu da jin dadi bata kaunar xafi ko kadan Sageer ya riga ya sangartata da sanyin AC
Hakance kuwa ta kasance domin sakeena koda ta tuna wani abun bata furtawa saboda taga Sageer yana bacin rai inta fada masa? Ranar suna kwance bayan sun gama soyayyarsu yaja hancinta yace "sakeena yar baiwa ke kam Allah ya hadaki in mutum ya fara tarayya dake da matuqar wahala ya iya rabuwa dake shiyasa nake mamakin yadda wanda ya fara saninki yayi sakaci kika kubuce masa" ta kalleshi tadan fara tunani kadan tayi qoqarin kauda tunanin saboda karta batawa Sageer rai amma abun ya gagara ta dubeshi tace "waye wanda na fara tarayya dashi din? Kuma inane garinmu? Yaushe xamuje? Sai nake ganin wasu mutane wanda ban sansu ba kamar a mafarki kamar kuma gaske" ya tureta daga jikinsa ya juya mata baya, ta bishi da kallo kafin tace "Sageer fushi kayi?" yayi mata shiru bai tanka ba, tasa ka kuka wanda hakan ya saka ya juyo a rikice yana tambayarta "meye kuma na kuka?" tace "bakaine ba kake fushi dani ni kuma ina sonka" wani sanyi ya ratsa masa xuciya ya bita ka kallon burgewa yace "wlh nima ina sonki sakeena fiye da yanda kike sona ina iya aikata komi akanki dan Allah ki dena tambayata akan komi daya faru a baya xan kaiki garinmu amma sai mun haihu yadda iyayenmu baxasu iya rabamu ba kodan albarkacin haihuwar da mukai" wannan magana da yayi ya qara jefa sakeena kogin tunani amma dole ta haqura da tarin tambayoyinta dan karta bata masa rai.
Xamansu me dadi ya dora yayin da Sageer ya fara tunanin hanyar da xai fadawa ummansa yayi aure ba tare da saninta ba, ya dunga tsara kalamai da xai fadawa umma da nufin qarshen wata xai dauki sakeena suje can din yayi mata bayanin yadda ya sameta da kuma aurenta da yayi don taimako daga baya kuma ya fada soyayyarta.
Maitama dai kullum cikin sakawa sakeena albarka yake da cewa "wannan yarinya tayi namijin kokari Allah ya saka mata da alkhairi cikin ruwan sanyi ta rabaka da bariki"
***** ***** ***** ********
A kano dai su Iya sun fidda tsammanin ganin sakeena ganin har anshiga wata na takwas da bacewarta. Deni juriyarsa ta qare yanason sakeena kamar yadda ya ke tsanin buqatar mace kusa dashi don gudun fadawa halaka.
Sakeena ta fara wani irin bacci babu ji babu gani, yayin da shi kuma Sageer ya mugun xama mayenta baya gajiya da kusantarta tun tana jure masa har ta fara gaxawa.
Yau ta kasance talata Sageer tun sassafe ya fita aiki a cewarsa suna da meeting, lokacin da ya fita ko tashi daga bacci sakeena batai ba. Ya gama shirinsa ya bubbga cinyarta da cewa "sakeena xan fita fa" idonta a rufe tace "ka siyomin soyayyen kwai na gurin masu shayi da kosai inxaka dawo" yayi dariya ya more jin abinda tace, ya sumbaci kuncinta ya fita yana cewa "Kai sakeena da quruci take, bayan yarinta harda wauta irinta yayan fari a tattare da ita, inba shirme ba mexatai da wani kwai na gurin masu shayi? Har gara kosai yace abun marmarine a gurinta tunda ba ganinsa take yiba"
Bai dawo ba sai wajen qarfe biyar na yamma. Yana shigowa ya hangi sakeena sanye cikin wata yar ficiciyar English gown dark purple armless yakacin tsahonta rabin cinyoyinta daga sama ta kamata a qirji, kanta babu dankwali sai kama gashin kanta da tayi wanda ya qara tsawo saboda mayuka masu kyau da kuma kwanciyar hankali da ribbon kalar rigar.
Ya kalleta yana tunanin me xataje yi kicin da wannan shigar bayan yasan duk kicin din maxane masu aiki a ciki, yayi taku hudu ya cafkota ta kalleshi a raxane tace "yaushe ka dawo?" ya bata amsa "yanxu na shigo naga xaki shiga kicin haka shiyasa na dakatar dake" ta kalleshi da rashin fahimta tace "menene don na shiga haka?" ya qura mata ido yana mamakinta, au batasan intashiga da wannan shigar kicin lefi ne ba? Lallai indai akace mutum lfyar kwakwalwarsa ta tabu sai a hankali. Ya sassauta murya yace "ina kishinki ne my luv, banaso ko namijin kuda ya kalleki a haka balle mutum namiji in kinyi irin wannan shigar ki dunga tsayawa iyakacin falo kinji? Kuma suma xan hanasu shigo miki falon nan kai tsaye" ta fara aikin nata na tunano wanda ya taba fada mata irin wannan magana domin ta tabbatar antaba fada mata ana kishinta, amma kuma waye ya fada mata? Kuma a ina? Shine tunanin data farayi.
Ya dan xungureta ganin hankalinta baya kusa, ta juyo firgigit tace "naam" yace "no ba magana nayiba, ina sone ince u look take away my queen" tayi dan murmushi tace "Nagode da yabawa"
Ta gyara xamanta akan cinyarsa tace "Ina qosan danace ka siyomin da soyayyen kawai?" ya marairaice yana shafa fararen cinyoyinya yace "sry na manta amma bari insa a soya miki kwan a kicin qosan kuma xansa asiyo yanxu" ta cuno baki yace "nifa banason na gida ba dadi na masu shayi nayi mafarki inaci shi nakeso Inci" yace "to ranki ya dade bari a kawo miki" ya dakko waya ya kira yaron gidan ya bashi sallahu ya kawo.
Ya balle botiran rigar jikinsa ya qara mannata jikinsa, tai saurin janye kanta tana toshe hanci tace "Sageer wane irin turare me warin cabbage?" ya waro ido yana dubanta kafin daga baya ya sheqe da dariya yace "wlh yarinyar nan baki da m, nine ke warin cabbage?" ta xame ta sauka daga kan qafarsa tace "wlh da gaske nake" ya tashi ya bita da gudu suka hau xagaye falon suna dariya, sallamar me kawo kosai ce tasa suka saurara, ta karba cikin sauri tasa a gaba ta cinye wainar kwai fefe biyu da kosai fal takadda tasha ruwa, yana dubanta yana mata dariyar me kwalama.
Ko da dare yayi yasaka turarensa bayan yayi wanka qin kwanciya tayi a dakin ta gudu nata dakin tace wlh turarensa warin cabbage yake. Ala dole ya sake wanka ya haqura da saka turaren tunda yanason kashe arna.
Sun cigaba da soyewa kamar majnun da Laila Yayin da Deni kecan kano ya rungumi azumi domin yakai maqura wajen haquri mace kawai yakeso kusa dashi kuma bayajin xai iya aure sakeena nacan ba asan inda take ba shiyasa ya rungumi axumi.
Yau Saturday kuma tun daren jiya juma a sakeena ta kasa sukuni saboda amai daya sakota gaba, har xuwa wayewar garin asabar da ko ruwa tasha saiya dawo duk ta jigata jikinta yayi laushi. Sageer shima duk ya yamutse saboda shike aikin duk aman da tayi ga kuma wani irin tausayinta da yake ji. Sunyi waya da Dr Sani yace su sameshi asibiti qarfe hudu baya kusa yanxu.
Ana idar da sallar asar ya tattageta suka yiwa asibitin tsinke. Dr yana xuwa ta kansu ya fara duk da basu ne farko ba, Dr sani yana ganinsu ya gane abunda ke tattare da sakeena amma yaja bakinsa ya tsuke yanawa sageer duban mamaki shi da yace ta mishi qanqanta ya kuma akai yayi mata ciki?
Suka samu guri suka xauna kan kujerun dake gaban table, Dr sani da sageer suka gaisa suka fara hira yayin da sakeena ta fara qoqarin tuna irin wannan xama data tabayi a rayuwarta. Sageer yayiwa sani bayanin abunda ke damun sakeena, ya dakko takarda ya fara yimata tambayoyi, sama sama take amsawa yayin da duk wata tambaya da yayi take qara bude mata kofar tuna baya. Yayi rubutu a takadda ya kira wata nurse a waya yace suje da sakeena ai mata gwaje gwajen. Ta riqe sakeena suka fita tana cigaba da tunaninta.
Bayan fitarsu Dr sani ya dubi Sageer yace "kai! Wannan yarinyar fa cikine da ita, shege daga auren taimako kana wani babbata rai kana basarwa har kayiwa yar mutane ciki" Baki bude sageer ke kallonsa, ya tashi ya xagaya ya riqewa Dr sani hannu yace "Dan Allah sani banason wasa inkana qaunar Allah ka fadan gaskiya" yana dubansa da mamaki yace "wlh da gaske nake, yaushe rabonta da period? Ko bakasan ta haihu?" ya juya gabas yayi sujjadar godiya ga Allah.
Ya koma ya xauna yace "lallai sakeena alherice gareni, ta rabani da sabon Allah sannan ina tunanin ta yadda xan sanarwa da umma nayi aure sai gashi ta dau cikina a dai dai lokacin, wanda hakan xaisa umma ta karbi wannan aure nawa hannu biyu albarkacin cikin jikin sakeena kuma ta yafemun laifin aure da nayi bata sani ba" Dr yayi dariya yace "hakan yayi sai kayi qoqarin samun lokaci kuje can gida. Amma itama fa in maganar cikin ta tabbata saita daina shan wannan magungunan nata saboda xai iya taba cikin. Fatanmu yanxu ta dawo hayyacinta musamu iyayenta kaga shikenan aurenku xai tabbata itama iyayenta xasu haqura tunda ga xuri a Allah ya baku." sageer yayi saurin cewa "in shaa Allah sani dan ni yanxu bani da burin da wuce xama da sakeena har qarshen rayuwata ina sonta ina qaunarta"
Suna cikin haka nurse ta shigo da sakeena ta miqa masa result din ta fita. Sageer ya kamo sakeena ya xaunar da ita a daya kujerar, Dr ya duqufa duba result dake hannunsa sakeena kuma hanyar tunani ta qara bude mata tana tuna irin wannan lokaci da wani ke xaune da paper a hannu suna sauraron cewarsa ita da wani data kasa tunawa.
Dr ya dago yace da sageer "congrats matanka nada ciki na 6 wks" ya washe baki yana hamdala. Sakeena kuwa kanta ya fara wani irin ciwo tana kuma tuna wani bangare na rayuwarta da Deni. Sauran surutan da sageer da sani keyi duk bata saurara ba tayi zurfi a tunani.
Suka shiga mota suna tafiya sageer yana juyowa ya kalleta a ransa yana tunanin meyasa yaga duk tayi sanyi tunda akai maganar cikin, ko cikin ne bataso? Ita kuwa sakeena a dai dai lokacin da yake kallonta photon Deni ya kawo tar a cikin kwakwalwarta ta tuna lokacin da suke tafiya dashi a mota ana gobe xasu rabu. A dai dai lokacin kuma ta sume saboda kwakwalwarta tana refreshing tunaninta.
Sageer besan halin da sakeena ke ciki yaga ta langabe a xatonsa bacci takeyi dan haka ya kwantar mata da kujera. Koda sukaje gida ya dauketa ya shiga da ita ciki ya kwantar da ita ya rufeta hadi da sumbatarta.
Ya dawo falo ya cigaba da harkokinsa har xuwa lokacin sallah, ya fita masallaci har aka sallaci isha yana ciki masallaci yana adduar neman nasara domin xai tunkari umma da xancen sakeena nan da yan kwanaki kadan kuma yayiwa sakeena adduar sauka lfy ya dawo gida.
Yaxo ya tarar sakeena har yanxu tana bacci, yayi mamakin wannan wane irin bacci ne? Duk baccinta batayi a dai dai wannan lokacin. Amma dai ya kyaleta xuwa goman dare in bata tashi ba xai tada ita.
Ya koma falo ya dauki waya ya kira ummansa. Ta daga suka gaisa duka fara hira tana fada masa abubuwan da suke faruwa a dangi da wanda xai bada gudummawa. Yace "to umma duk ki hada lissafi xanxo nan da kwana 6 sai inbada kudi duk ki basu" ta amsa da cewa "Yawwa Allah yayi maka albarka Allah ya qara budi ya kuma baka mace ta gari" jikinsa yayi sanyi saboda jin adduar da tayi masa batasan shi tuni yayi aure ba har ansamu albarkar ciki.
Ya amsa adduarta da cewa "Amin umma nagode, xanxo miki da wani babban lamari Inna tashi xuwa Dan Allah umma kiyi qoqari kiyimun kyakykyawar fahimta kuma kiyimun uxuri" itama jikinta yayi sanyi dan tasan tunda Sageer ya fadi haka to babban abu ne, sai dai fatan Allah yasa taji alkhairi. Tace "to Muhammadu Allah ya jishshemu alkhairi sai kaxo" ya amsa suka kashe wayar
Ya koma daki ya tarar sakeena na kwance yadda ya ajiyeta ko hannu bata canjawa guri ba balle tayi juyi, ya kasa sukuni abinci ma ya kasa ci, ya fara tsorata wane irin bacci ne sakeena keyi haka kamar matacciya?
A daddafe ya bari aka kai 11 na dare yagafa abun nayine ya shiga girgixata yana kwallah kiranta. 7 minutes yana girgixata da kiran sunanta, harya fara sarewa yana shirin kiran Dr sani, sai kuma yaji hannunta yana qoqarin riqeshi. Ya damqe hannun qam ya kwallah kiran sunanta "Sakeenatu" wannan kira shiyayi sanadiyyar farkawarta daga dogon suman da tayi.
Ta tashi ta xauna dangwargwar tana bin sageer da kuma daki da kallo. Ya sauke ajiyar xuciya yakai hannu xai rungumeta yana cewa "wane irin baccine kikeyi haka wlh har kin firgitani" ta daka tsalle ta diro daga kan gadon tace "karka taba ni, kai waye? Inane nan? Ina yaya Deni?" Sageer yaji wata irin muguwar fargaba ta xiyarceshi yayi qarfin halin hada kalmar "waye yaya Deni?" cikin firgita tace "mijina ne, mun rabu dashi xai fita aiki yace inmasa Dan wake shine kawai na ganni anan"
Ya dafe qirji kamar mace yace "mijinki? Kina da aure?" tai saurin cewa "Eh inada aure sunan mijina Nuraddeen Lawan" Sageer ya nufeta da sauri xai kamata ta kauce tace "kai na fada maka ni matar aurece wlh, karka tabani ina ya Deni?" ya dafe kai yana cewa a fili "innalillahi wa innah ilaihi raju'un. Matar aure na aura kenan?" ta matso kusa itama tana furta kalmar "innahlillahi me kake cewa?" ya miqa hannu xai riqeta yana cewa "sakeena kinga zauna in miki bayanin yadda akai hakan ta faru" ta lalubi wani abu akan center table ta kwada masa a hannu cikin haki tace "kai wane irine nace ka daina tabani ina da aure" taja baya ta dauki wuqa kan dinning table a cikin fruit tace "wlh in kakuma tabani saina caka maka" yayi baya yana daga hannu alamar surrender.
Yayi hanyar waje gidan Maitama ya nufa, har sun rufe gida ya dunga bugawa yaxo ya bude. Hankali a tashe Sageer ya fada musu abunda ake ciki a gurguje. Maitama da Bilki suka bishi gidan cikin al ajabin wai sakeena ta dawo hayyacinta harta rutsa sageer da wuqa to ina soyayyar da take masa?
Suna shiga suka tadda ta tana riqe da wuqar tana xagaye falon. Ganin sun shigo kuma harda mace a ciki yasa ta danji dadi. Ta qurawa Bilki ido tana tunano inda ta santa kuma tana qulla xaren tunaninta. Bilki ta dafata tace "Bani wuqar sakeena" babu musu ta miqa mata. Bilki ta kamata ta xaunarta kusa da ita akan kujera.
Ta dafa kafadunta tace "Sakeena, wancen da kika gani mijinki ne ya tsinceki ne gurin wasu mutane da suka satoki sukaga asirinsu zai taunu suka wulloki daga mota kinyi wata guda a asibiti a sume kafin ki farko, shi kuma gudun fadawa halaka na xama tsakaninki dashi a matsayin wacce tai batan tunani shine ya aureki wata 8 da rabi a baya, yanxu har kina dauke da cikinsa" sakeena tunda Bilki ta fara magana take kallonta tana kuma tunani har Bilki ta gama.
Ta dafe kanta da hannu biyu ta runtse ido, a xatonsu tana jimamin abunda ya faru a kantane. Bilki ta dafata tace "kinji abunda ya faru kema ki fada mana abunda ya fito dake daga gida har aka sace ki kuma inane garinku" sai dai me? Sakeena ta bingire ta fadi a sume.
Suka kwallah kiran sunanta a tare sukayo kanta suna jijjigata Maitama yaje kicin ya dakko ruwa aka fara yayyafa mata. Tun suna ganin abun qarami ya fara girma lokacin da tayi 47 minutes a sume. Maitama yace sageer ya dakkota suje asibiti. Sageer ya fara yunqurin daukanta a lokacin ne kuma ta farka.
Ta xauna tana hawaye tana cewa "na tuna ,kece Anty Bilki. Ta nuna sageer tace shi kuma mijina wlh na tunaku na gane komi" ta matsa gefen Bilki tace "Ni matar aurece ina gama secondary school Mariqina ya auramun dansa Nura kasancewata marainiya iyayena da qanina sun mutu bani da kowa se yan uban da basu damu dani ba, riqona ya dawo hannun yayar Baba a inda ta kasance kishiyar Babar mijina Nura kuma anan na hadu dashi mukayi auren soyayya, amma uwarsa da yan uwansa basa sona. Ya samu aiki a kaduna muka koma can da xama, mahaifiyarsa ta sakoni a gaba wai bana haihuwa bayan kuma itace tasa akaimun allurar hana daukar ciki Nura besani ba, ranar da ya sani a ranar yayi fushi dani kuma a daren mahaifiyarsa taxo gidanmu kaduna haushin jin tasa an rufemun mahaifa yasashi korarta yace karta kuma xuwar masa gida. Ni kuma na bishi na bashi haquri ya haqura yace inmasa dan wake inya dawo xamuyi magana. Yana fita ta koreni tace intafi in barmata gidan danta ni kuma bani da kudin mota a cikin tashar na hadu da wata hajiya ta taimakeni tace garinmu xata ashe saceni tai saida muka kwana muna tafiya driver motar yace mun Lagos nake. Shine ta tunkudo daga mota bayan taji ana binmu har da harbin bindiga"
Sageer, Maitama da Bilki suka dunga maimaita kalmar innalillahi jin wannan almara wai sakeena matar aure ce kuma ga wani auren akanta harda ciki. Sageer ya rasa me xaiyi? Mai xaice? Ina xaisa kansa? Wane irin lamari ne wannan me sarqaqiya?"
Sakeena ta rarrafo gurinsa tace "Ka taimaka ka maidani gida, wlh mijina yana da kishi. Dan Allah karka fada masa nayi aure xai iya kasheni. Ina sonsa dan Allah ku temakeni ku kaini gurin ya Deni" Sageer ya dago yana dubanta idonsa jajur cikin sanyin murya yace "a wane gari kike?" da sauri tace "a Kano cikin Gwale local government"
Ta cigaba da sambatun cewar a kaita gida yanxu ko a barta ta tafi tasan ya Deni yanacan yana nemanta. Tun suna ganin abun nata na hankali ne har suka gane bata cikin hayyacinta. Dataga basu kulata ba saita tashi xata nufi kofar fita a cewarta "tafiya kano xatayi" sageer ya riqota ta tankadashi da cewa "karka tabani ni matar ya Deni ce kuma shi nakeso, kaiba mijina bane kuma ko munje karka sake ka fada masa ka taba aurena"
A wannan dare dai sunga tashin hankali gurin sakeena don kwanatai tana sambatu kamar sabon kamun hauka, da kyar Maitama ya lallabata da cewar yanxu tsakiyar dare ne amma gobe da asuba xasu tafi. Ta yadda da maganarsa sageer na gefe yana kallonsu dan taqi yadda ko kusa da ita yaxo.
Bilki ce ta shiga ta fara hada kayan sakeena cikin manyan jakunkuna kamar yadda mijinta Maitama ya umarceta. Sageer cikin fidda tsammani yacigaba da xaqulo mata da dukkan abunda yasan mallakin sakeena nane. Ya kasa yadda cewar wai yau shine ya auri matar aure, yau shine xai rabu da abunda yake mutaqar so da qauna.
Qarfe hudun asuba Maitama ya nufi airport nemo musu ticket. Yayi sa a ya samu akwai jirgin da xaije kano yau amma sai yayi zango a Kaduna. Ya siyo ticket din ya dawo da sauri saboda jirgin qarfe shida xai tashi.
Da kyar Bilki tasa sakeena tai wanka bayan sallar asuba ko mai bata shafa ba ta xura baqar abaya me kyau da tsada duk jikinta stones ne. Shima sageer yayi wanka ya sako kaya ya fito yana layi. Cikin tausayi Maitama yace "Sageer gyara rigarka a baibai kasa, kayi haquri ka barwa Allah komi" ya kalli Maitama yace "To in ban haqura ba hauka xanyi? Sakeena fa xan rasa, my first luv? Kana ganin yadda ta mantani take xancen wani daban? Maitama tafi sonsa dani fa kenan? Ta manta duk wata soyayya da alqawari da mukasha yiwa juna. Kuma nasan shi xata xaba tabarni ciwon rabuwa da ita ya xama ajalina. Shikenan na tabbatar na rasa ta tunda ai shima wancan ba mahaukaci bane da xaibarmin mace irin sakeena" ya qarasa yana kuka. Shima Maitama share kwallah yayi a sace, lallai duk bala'in daya saka mutum me taurin zuciya irin sageer kuka tofa ba qaramin bala'i bane.
Suka loda kayanta a jeep din sageer suka tafi. Bilki dai bata bisu airport ba itama kuka take. suna xuwa aka fara kira Maitama ya dafa kafadar sageer yace "ka dogara da Allah temakon da kayi baxai tafi a banxa ba, in Allah yayi sakeena rabonka ce sai Kaga ka tsalleke duk wani qalubale da kake ganin zai rabaka da ita ka sameta. Yanxu daganan gidan Abdulfatah xanje infada masa yadda ake ciki sabida karyaga gobe Monday bakaje aiki ba" ya juya ya tafi yabar sageer cikin wani irin yanayi.
Jirgi ya tashi kowa da tunanin dake ransa. Sageer yana ganin kamar da gayya matuqin jirgin ke gudu don ya qara nisantashi da sakeena, tunda yasan dataje Kano ta tashi daga matarsa. Ita kuma sakeena tana jin kamar jirgin baya sauri tanajin kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Kano gurin Iya da ya Deni.
Bai wani jima a Kaduna ba ya sauke passengers jirgin ya daga kano. Suna sauka kano fargaba ta xiyarci sakeena da sageer a lokaci daya. shiyana fargabar shikenan fa ya rasa wannan tsaleliyar yarinyar a matsayin matarsa yayin daya qura mata ido yana kallonta yana jin wata iriyar soyayyarta da bai taba jiba tana shigarsa. Ita kuma tana cikin xurfin tunanin baqin kishi irin na Deni, ta tuna haukan da yayi lokacin da Ahlan ya riqe mata hannu kawai, yana kuma ga tayi aure harda ciki? Gabanta yayi wata irin faduwa tasa hannu ta dafeshi a fili tace "Allah ka sassautawa ya Deni mugun kishin nan nasa, Allah kasa ya fahimceni Allah ka gani inason ya Deni Allah ka hada kanmu" Sageer ya bita da kallo jin abunda take cewa ya tausayawa kansa sannan ya kuma fidda tsammanin samun sakeena dan tana cikin matsannanciyar soyayyar waninsa.
TAB!!!!!! Wannan shine Luv triangle (🔺)
Hajia 😊
[7/31, 2:25 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
1⃣9⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Asabule dukkansu suka fito daga cikin jirgin ta samu guri ta tsaya, ya samo taxi a cikin airport din suka loda kayanta yaxo ya kirata ta shiga baya shi kuma ya shiga gaba suka tafi. Ana shiga gwale qijinta ya tsananta bugu sosai, ta dunga yin kwatance me taxi din yanabin kwatancenta. Yawanci kowa yana gida saboda lokacin ko 8 din safe batai ba kuma lahadi ce ana hutun weekend.
Suka tsaya kofar gida, ta fito a cikin sanyi jiki ta shige gidan. Sageer kuma ya fito da kayanta ya biya me taxi ya tafi.
Da sallama ta shiga gidan, Hajjo da su Amina ana daki domin yanxu ta wuce sai da gasara sai hutu da harkar sai da atamfofi. Baba yana nasa dakin shima, Saddiq ya fita motsa jiki sai Deni kwance yana bacci a dakin soro. Iya keda girki, ita keta xarya tsakanin dakinta da kicin tana hada breakfast.
Ta kuma sallama a karo na biyu cikin sanyin muryarta, Iya ta fito daga daki dauke da sabon food warmer sukayi 4 eyes da sakeena. Ta waro ido tana yiwa sakeena duban mamaki yayin da sakeena ke tsaye tana kallon Iya idonta cike da kwallah. Iya ta isa gurin ta cakumo sakeena ta qanqameta, ta tabbatar dai sakeena nan ce ta bude murya tace "jama'a kutayani ganin abun al ajabi yau sakeena ce a gidan nan" suka kuma rungume juna. Babu wanda yaji abunda Iya ke fada sai Baba saboda duk bacci suke me nauyi. Ya fita cikin hanxari ya ganta rungume da iya, ya furta "Sakeenatu" ta saki Iya tayi gurin Baba ta fada jikinsa tana hawaye. Baba ya dagota daga jikinsa ya share mata hawaye yace "sakeena duk tsahon wannan lokaci kina ina muketa nemanki? Lefin Hajara ya shafemu kenan?" ta qara riqeshi tace "Ba kuyimun komi ba, muna tare da wanda ya kawoni a kofar gida" yayi saurin cewa "jeki ki shigo dashi, bari in kintsa dakin nawa" tayi hanyar waje. Iya ta bita da kallo tana tafa hannu tana cewa "Malam da gaske sakeena ce ko mafarkin dana saba yine?" wannan magana ta Iya itace ta tayar da Hadixa da sauri ta tashi Hajjo da Amina tace naji ana sakeena ta dawo. Suka mutstsike ido sukayo tsakar gida suna tutture juna. Deni ma kamar a mafarki yaji ana ambaton sakeena shima ya fito da sauri dagashi sai dogon wando.
Sakeena ta samu sageer kofar gida tace masa "ance ka shigo" bata qara komi akaiba ta juyo. Ya bita da kallon mamaki wai yau sakeena ce take masa haka? Matar da kamar su cinye juna shi da ita saboda soyayya yau itace ke masa magana kamar baquwa. Ya fara kici kicin daukar jakar kayanta.
Tana shiga soro suna yin kicibiz da Deni da fitowarsa kenan. Suka furta sunan juna a tare, ya iso ya dagata ya mannata a qirjinsa da babu riga. Tayi lub ta qanqameshi, Sageer daya riqo akwatinan sakeena biyu yayi ido hudu da wani xabgegen matashi babu riga rungume da sakeena ya sakesu a qasa yace "innalillahi wa innah ilaihi raju'un" Deni be juyo ba domin bema jishi ba balle yasan da mutum a gurin. Ya dago kan sakeena daga qirjinsa yace "Baby kece koko mafarki ne?" tana hawaye tace "ya Deni nice ba mafarki kake ba" Ya qara rungumeta ita kuma tana shafar fatar bayansa.
Sageer yana tsaye yana kallon su, tunda yaji sakeena ta kira ya Deni shikenan ya kuma yanke qauna da samun sakeena, domin maxa irinsu Deni sunfi kasuwa a yanxu, mata su suke rububi. Bawai dan ya fishi kyauba ko hasken fata, a a kawai dai Deni dogo ne me cikar jiki irinta maxa, ma'ana murdaddan jiki irin na qarfafan maxa. Bayan wannan kam Deni be fishi kyau ba sai dai hasken fata don shi sageer baqi ne yayin da Deni yake wankan tarwada.
Ya dawo hankalinsa lokacin da yaga Deni yayiwa sakeena daukar jarirai ya shige dakin dake soron da ita, yayi sauri xaibi bayansu kafin yayi dan gajeran tunani ya dakata. Tunanin da yayi shine inya shiga yace musu me? Yanda fa yake ji sakeena matarsa ce haka shima Deni keji, yadda yake kishin sakeena haka Deni keyi koma fiye dashi tunda shi ya fara auren sakeena. Yaji wani irin abu me ciwo a saitin xuciyarsa kamar xai fasa qirjinsa ya keto, yayi qoqarin hadiye abun ya kasa, ya tambayi kansa ko wannan shine kishi???? (FANS Ku BASHI AMSA PLZ 😄) Yaja jiki a sanyaye ya shiga cikin gidan.
Deni yayiwa sakeena masauki akan qatuwar katifarsa da ake cewa gado huta. Tadan kalli dakin cikin yan sakanni ta yaba da tsarin dakin duk da dai ta saba ganin gurare masu kyau yanxu. Taji hannun Deni a cikin rigarta tayi gaggawar cire hannunsa ta waro masa manyan fararen idanunta tace "meye haka kuma" ya Kalli idonta da suke jajaye ada amma yanxu sun xama farare qal wanda hakan ya qarawa kyanta armashi, ko sakeena bata fada ba yasan ta samu lfyar ido yanxu. Ya dafe saitin xuciyarsa yace "wash! Sakeena wannan kallon naki ai saiya yasa na sume miki" maganarsa ta bata dariya ta hauyin dariyarta tana dubansa.
Ya nutsu yana kallonta tana dariyar, haqoran sakeena da yake kyankyami tun farkon xuwanta gidansu har xuwa lokacin daya aureta wanda shine dalilinsa na kasa sumbatarta sai dai in itace takai bakinta kan nasa bakin baya iya guje mata saboda kar ya watsa mata qasa a ido ko ta fuskanci yana kyamarta, amma yau saiya ga haqoranta qal abun burgewa da sha'awa badan karyayi qarya ba sai yace har daukan ido suke, dagani suna samun kyakykyawar kulawa daga dentalist. Ya hada bakinsa da nata a Karon farko a rayuwarsu da yayi hakan dan ra'ayin kansa. Ya farayi mata kiss din da yadade yana buri yayiwa matar da yake mafarkin aura.
Sun dau tsawon 3 minutes suna sumbatar juna kafin ya cire bakinsa ya kwanta ya jawota jikinsa. Ta fuskanci abunda yake nufi sarai gabanta ya fadi data tuno badaqalar dake gabanta da kuma abunda ke qunshe a cikinta. Ta janye jikinta a cikin dabara, ya riqota yace "Haba miye haka Baby wlh a mugun matse nake harfa axumi nake saboda rashinki" ta danyi yaqe kawai batace komi ba amma kuma qirjinta kamar xai fashe dan bugawa.
Ya haqura da abunda yayi niyya dan yaga kamar sakeena bataso, shi kuma baxai iya batawa sakeena rai ba yanxu, ji yake kamar ya hadiyeta. Ya tashi daga kwanciyar da yayi yace "sakeena bani lbr ina kika shiga? Ya akai kika canja haka cikin lokaci qanqani? Bani lbr sakeena" Jiki a sanyaye tace "Da wani mukaxo yana cikin gida" ya miqe yaja hannunta yace "ai bansani ba mun bar baqo xo muje" ta bishi suka fita har cikin gida yana riqe da hannunta.
Suka shiga dakin Baba kamar yadda suka tarar kowa na gidan yana can. Sageer na xaune shima cikin dakin, Hajjo dasu Amina suka bi sakeena da kallon qurullah da kuma mamakin canjawar da tayi. Hajjo tai shu'umin murmushi dan ta gano cikin jikin sakeena. Iya ta jawo sakeena jikinta tace "Taho sakeena bangama ganinki ba ai" ta dora kanta akan cinyar Iya yayin da Iya ke shafar kan sakeena cikin soyayya.
Sageer ya gyara xama ya gabatar da kansa da kuma asalinsa har xuwa kan aikinsa. Ya fada randa ya tsinci sakeena da kwanan wata da kuma time din, ya fada musu abunda ya faru bayan nan har xuwa jiya da sakeena ta dawo cikin hankalinta ta kuma fada musu tana da aure har cikin jikin sakeena da kuma aikin idon da akai mata be boye musu komai ba.
Sunyi tsit kowa ya fada kogin tunani muryar sageer kawai ke tashi a gurin. Hajjo ta miqe ta rangada guda "ayyiririri" ta dora da dariyar mugunta sannan tace "Allah ya kawomu shekara ta kawomu, yau xanga batan nono a qirijin budurwa. Aka dameni, aka tsangwameni wai na batar da sakeena har aka rabani da Dana aka janyomin surutun jama'a har ana cewa xa a kaini gurin C E D (C I D take nufi wai🤣) kai harda masu tsinemun akan haka. Ashe yarinya dai yawon bariki ta tafi, ba a tashi dawo mana ba sai da bariki tayi riba aka samu cikin shege yaqi xubuwa shine kika dawo mana da kwartonki xaku raina mana hankali wai kin haukace ya aure ki?" Ta matsa kusa da sakeena ta kalleta cikin ido ta nunata tace "wlh kinyi asara sakeena ban taba ganin tsinanniyar mace irinki ba, gyatuma tayi naqudar banxa ta haifi asara Dan tsinancewa da aurenki ki tafi yawon bariki"
Babu wanda ya tanka mata kowa kansa sunkuye yana hango girman lamarin sai sakeena dake hawaye da kuma sageer dake kallon Hajjo baki bude yana tunanin wannan kuma wacece a gurin sakeena? Kai duk inda wannan mata take bata da hankali kuma bata da tarbiyyar harshe, ji yake kamar ya tashi ya rufeta da duka saboda tasa sakeena kuka.
Deni ya dago kai idonsa jajur ya nufi sakeena duk gashin jikinsa ya miqe. Ta tsorata domin tasan inta ganshi haka ransa yakai matuqa wajen baci kuma baqar xuciyarsa ta motsa, xama ta iya cewa bata taba ganinsa haka ba.
Ta qanqame Iya tamau ta fara bashi haquri. Ya figota yace "ai wlh duk duniya baki da maceci yau" ya saka hannu ya matse mata baki yace "kinsan ba yau muka fara ba ko? Sam ban yadda da wannan dramar din ba, ta kinyi loosing memory har kinyi aure akan nawa auren har da wani tsinannen Da a cikin ki. Ki fadamun gaskiya domin itace xata kwaceki" da kyar tayi magana saboda matse mata bakin da yayi tace "Wlh ya Deni iya gaskiyar kenan wlh aure mukayi loka...... Marin da Deni ya dauketa dashi shiya hanata qarasa maganar. Ya fara magana cikin xafin rai "har ni kike fadawa kinyi aure? Ni xaki rainawa hankali? Nawa kike? shekarunki nawa har da xakiyi wasa da hankalina?" ya daga hannu xai kuma marinta Sageer yayi saurin riqe hannunsa don haqurinsa ya qare baxai juri ganin haka kawai wani banxa na dukan tsadajjiyar mace irin sakeena ba akan wani kishi nasa na banxa da wofi da kuma lefin da ita kanta sakeena batasan ta aikatashi ba domin lokacin da tayi aure kan aurensa bata hayyacinta har ga Allah.
Cikin qarfin xuciya da maxan taka Sageer yace "karka kuma dukarmun mata sannan karka qara kiran dana shege domin aure ne ya samar dashi" cikin hargagi Deni ya daki qirjin Sageer yace "in an kuma me xakayi dan iska bunsuru me taraiyya da matar aure?" Sageer shima cikin tasa xuciyar data yunquro yace "inka kuma xan daureka ne har qarshen rayuwarka dan ubanka domin da xubar hawayen sakeena gara mutuwar irinku mayaudara masu ci da kalmar SO"
Deni ya kaiwa Sageer mari amma ya goce ya damqe hannun Deni yasa qarfi ya murde hannun. Baba ya tashi yana salati, yayin da Iya ke riqe da sakeena wacce ke kuka haiqan gefen fuskarta kuma ga hannun Deni nan kwance a gurin ya fito saboda yanxu fatar ta ta xama ta ajebo.
Hajjo tai hanyar soro da gudu tana kururuwa da ihun a kawo mata dauki kwarton sakeena yaxo har gida xai kashe mata Deni, taci karo da Saddiq a soro ya dawo daga motsa jiki, ya tareta yana tambayarta, ta bashi amsa amma sam be fuskanci abunda take nufi ba ya nufi cikin gidan. Ya samu Sageer da Deni suna dambe a tsakar dakin Baba yayin da Baba ya kasa rabasu don matasa ne kowanne yanaji da qarfi da kuma xuciya. Da kyar Saddiq ya taya Baba suka rabasu aka fice da Deni dakin soro.
Baba ya bawa kowa umarnin yaje ya kama gabansa xuwa wani lokaci wannan lamari ne me sarqaqiya xai nemo malamai masana shari'a su xauna ai hukunci kan lamarin.
Sun fito daga dakin Baba kenan Deni ya kuma kubucewa daga hannun Saddiq ya fito daga dakinsu na soro, sakeena ce da Iya a gaba dan haka suya fara gani. Ya tari gabanta yace "ni xakici amana ko? Ni xaki ha'inta ko sakeena? Ina nan tunda kika tafi ina xaman jiranki cikin azabar kewa da soyayyarki har fushi nayi da mahaifiyata da yan uwana ciki daya akanki a she ke kinacan kina sana'ar karuwanci" ya tofa mata yawu yace "Tur da ke yake wannan me kwadayin duniya wacce ta jefa masoya da danginta cikin bala'i dan son xuciyarta"
Sageer ya nade hannun rigar jikinsa, ya shiga tsakanin sakeena da Deni domin yaga yaron yana da taurin kai kuma ya naji da girman jiki gara ya lafceshi koxai shiga hankalinsa. Ya dunqule hannu ya saukewa Deni a bakinsa yana cewa "nace ka daina aibatamun iyali kaqi ko? To bari inyi maka da yaren da xaka gane tunda kai jaki ne" Dukan ya xowa Deni baxata, be xaci matsakaicin mutum kamar wannan yana da kwarin kai duka irin wannan ba. Ya dago da mamaki yana kallon Sageer ya share jinin bakinsa inda ya fashe yace "kaxo har gidan ubana ka dakeni akan matata?"
Shima ya xage suka fara bawa hammata iska. Hajjo ta hau kururuwar cewa "wannan wane irin bala'ine? Wai sakeena yar gwalce da xa a xauna ana dambe akanta? Kai Deni ka cikashi ka barmasa karuwarsa, kai kuma Allah ya baka tsarkakakkiya irinka" Baba da Iya dai suna gefe suna kallonsu kamar fadan be damesu ba.
Sakeena da farko taso suyi damben don haushin Sageer takeji kamar ta kasheshi don haka taso Deni yayi masa duka a xatonta Deni xaifishi qarfi duba da yanayin jikinsa, amma dataga ana dukan masoyinta Deni kuma yafi jin jiki a fadan saita fara ihun cewa "Baba ku taimaka ku rabasu yana dukan ya Deni" Baba ko motsi beyi ba Saddiq kuwa Hajjo se dura masa xagi take akan ya shigarwa dan uwansa. Yayi tsaki yace "Har dakin soro fa na tafi dashi na riqeshi amma ya kubuce ya gudu don tsabar taurin kai saboda da haka suyi tayi wlh in daya ya kashe daya cikinsu shikenan sun kawo solution sai ta zauna da wanda ya rayu"
Ai sakeena dajin wannan batu na kisa daga bakin Saddiq ta xabura ta shiga tsakiyarsu domin tasan inma kisance Deni xa a kashe. Ta hankade Sageer tace "Babu ruwanka da duk abunda xaicemun, mijinane kuma shi nakeso saboda haka ka fita daga rayuwarmu ka koma inda ka fito" Sageer yayi kasaqe yana kallonta gwuiwarsa tayi sanyi qalau. Ta matsa gurin Deni ta riqeshi tace "ya Deni muje ingyara maka ciwon bakinka, xan maka bayanin komi a nutse" ya daka mata tsawa yace "ke! Karki kuskura ki biyoni dan wlh xan iya kasheki a yadda nakejin tsanarki" Hajjo cikin farinciki ta matso tace "Da kyau dan halak ka burgeni matuqa" ta fusge hannun sakeena daga jikin Deni tace "karki kuma tabamun Da ki shafa mai dattin zina, ki tafican gurin dadironki don da alama har yanxu yana muradinki. Kinga shi Deni ai aure ne ya samar dashi don ga abunsa can a tsaye. Ke kuwa ta yadda aka samar dake ta haka kike samo naki Dan. Gado girman Allah barewa bata gudu danta yayi rarrafe"
Wata irin kunya ta rufe sakeena jin abunda Hajjo da Deni sukai mata a gaban Sageer, taji duk ta muxanta taja jiki ta shige dakin Iya. Baba ya fita waje, Deni ya koma dakinsa sai Hajjo da taja yan majalissarta sukayi daki tana so suje su xauna a fara tattauna matsalar tun yanxu. Aka bar Iya da sageer a tsaye a tsakar gida. Iya tace masa "shigo daga ciki sageeru" yabi bayanta suka shiga dakin. Sakeena na xaune akan sabon Center carpet din dakin Iya wanda Deni ya saya musu ita da Hajjo. Tana ganin Sageer ta shige uwar daki tana kuka.
Ya samu guri a qasa ya xauna, Iya taitai ya hau kan sabbin kujerun falon yaqi, ya sunkuyar da kai. Ta miqe ta fita ta xubo masa funkason datayi a matsayin breakfast a sabon food warmer dinta ta ciko masa jug da kunun tsamiya takai masa da ruwan wanke hannu sannan ta fito tsakar gida tacigaba da aikin raba abinci.
Aka bar Sageer xaune a falo da tray din abinci a gaba, yayin da sakeena kecan daki tana tunani da kuka. Sageer ya janyo abincin gaabansa ya tsiyayi kunu ya fara kurba badan dadi ba sai don karya watsawa Iya qasa a ido. Daga kunu har funkason cimarsa ne amma yau kam dakyar ya iya cin kadan ya rufe. Ya fara tunanin ita Sakeena da Dan cikinta me sukaci?
Iya tana gama rabon abinci ta shigo ta xauna kan kujera ta dubi abincin gaban Sageer tace "ya bakaci komi ba sageeru?" ya danyi murmushi yace "Naci Iya, ita sakeena naga kamar bataci komi ba" Iya ta qura masa ido tana dubansa shi kuma yayi qasa da kansa.
Ta gyara xama cikin nutsuwa ta fara magana. Ta fara bashi tarihin Sakeena tun daga auren Iyayenta da kuma qabilar da uwarta ta fito, bata boye masa komi ba har mutuwar Nura da kuma qiyayyar matar ubanta da yadda ta dakkota har xuwa aurenta da Deni da yadda tasha wuya har aikin da tayi don suyi xaman aure da yadda Hajjo ta uxura mata har korarta da Hajjo tai da abunda ya faru bayan bacewarta. Iya ta qare xancenta da cewa "Dan Allah Sageeru ka dubi girman Allah ka fadamin gaskiyar abunda ke tsakaninka da sakeena komenene xan iya dauka dan sakeena diyatace halak malak bata da wacce ta wuceni duk duniya"
Sageer ya share kwallar tausayin masoyiyarsa ya kuma tsanar Hajjo da Deni ashe wancan mahaukaciyan matan mother in law din sakeena ne shiyasa take mata haka, shi kuma Deni be yadda yana wani yiwa sakeena soyayyar gaskiya ba just mayaudari ne da yake wasa da xuciyar sakeena da sunan soyayya amma kash sakeena bata gane hakan ba, ta makance ta mutu murus akansa kuma ga dukkan alamu da hakan Deni ke amfani yana musguna mata.
Ya dago ya dubi Iya da take jiran cewarsa ya fara magana "Iya ke mahaifiya ce a gareni tunda kina matsayin yayar Baban sakeena innayi miki qarya kamar na yiwa Ummata ne. Wallahil Azim na rantse da mahaliccina auren sakeena nayi kamar yadda na fada muku, ba xaman haramci mukayi da ita ba kuma lokacin dana aureta bata cikin hayyacinta" Iya ta sauke ajiyar xuciya tayi Hamdalah a fili tace "na yadda da kai Sageeru kuma ina bayanka inaso ka taho da yan uwanka dan suxo ayi hukunci a gabansu kuma su bada shedar auren sakeena kayi."
Faduwar gaba da tausayin Iya lokaci daya sukaxo masa, sai a lokacin ya tuna da Ummansa yayi nadamar boye mata aurensa da yayi. Cikin sanyin jiki yace "Iya kiyi haquri nayi kuskure duk dangina babu wanda yasan na auri sakeena daga abokina sai likitan sakeena sai uban gidana a office a boye na aureta" Iya jikinta yayi sanyi murna ta koma ciki kuma ta fara shakkun anya maganarsa gaskiyace ta cewar auren sakeena yayi?
Ta fada kogin tunani har Sageer ya gama magana bataji me yake cewa ba sai da ya miqe sannan hankalinta ya dawo kansa. Ya dau jakar kayansa yace "zanje in nemi masauki xuwa dare xan dawo" ya fita ba tare data bashi amsa ba.
Acan dakin Hajjo kuwa sun nutse ana tattauna matsala har ankira Fiddausi an fada mata kuma itama ta bada tata shawarar. Suka hadu su uku banda Saddiq dan shi yanxu be cika biye musu ba tun akan batan sakeena. Sun qullah abunda suke ganin shine dai dai suka tafa da sakin shewa ga dukkan alamu duniya ta musu dadi. Hajjo ta dubi Amina tace "saura wannan karon ma ki kwayemun baya inkinji wuya" Amina tayi fari tace "wuce nan Hajjo ai wancan Karon ma dan nasara bata hannunmu ne kuma ankamamu dumu dumu wannan kuwa na tabbatar mune da nasara, ai kodan abi miki haqqinki na bata miki suna da akai da kuma maganar auren Hadixa data watse saina jajurce" Hajjo tace "Yawwa auta Allah yayi miki albarka"
Da photon sakeena na wayar Hadixa wanda akai amfani dashi gurin cigiyar batan ta sukai amfani suka shirya kalamai qazamai kuma kausasa na bata suna suka hada da photon cewar matar Dan uwansu data bata aketa cigiya dai ta dawo bayan ta shafe watanni tana yawan bariki a Lagos ta dawo da tarin dukiyar haramun da kuma tsarabar cikin shege da cutar HIV sannan daya abun tur din harda dadironta ta dawo. Taturawa Amina da Fiddausi. Suma suka dora akan dukkan wata kafar sada muxunta ta xamani da grps grps.
Dake sharrine kuma mutanenmu sun lalace wajen yada sharri a cikin awa guda kacal sai da aka samu wajen mutane 738 da sukayi sharing sannan dubbannai sukai liking da comments. Wasu suna tsinewa sakeena da duk ahalinta, wasu suna aibatata da cewar tayi kyan dan miciji wasu ma cewa suke daga ganinta dama karuwa ce. Masu hankali aciki ne suke yimata adduar shiriya. Acikin wadanda sukasan sakeena wanda sukai makaranta tare da ita suka dunga bin diddigin labarin inda suke biyo su Amina ta inbox, su kuma su suyi musu qarin bayani dallah dallah hadi da qarin gishiri a miya.
Yinin ranar abunda yayan Hajjo suka yini yi kenan, yayin da Baba keta yawo a rana daga gurin wannan malami xuwa wajen wancen dan neman fatawa. Ita kuwa Iya tana lallaba sakeena taci abinci kodan albarkacin abunda ke cikinta wanda baisan ma duniyar ba.
Hadixa ta miqawa Hajjo hannu tace "ban musha Hajjo, bana fa burinki ya cika sunan sakeena ya gama baci a duniya wlh kuma yadda naga yaya Deni ya harxuqa da matuqar wahala ya kuma xama da ita" Hajjo ta washe baki tace "in shaa Allah Hadixa an rabu kenan. Tunda kika farantamun yau nima gobe xan miki abunda baki taba xata ba xan faranta miki kuma burunki xai cika" cikin xumudi Hadixa tace "mexakimun Hajjo?" tayi dariya tace "Allah ya kaimu gobe xakiji" tayi murmushin farin ciki tace "Allah ya nuna mana goben"
Wajen qarfe taran dare kowa yana dakinsa baayi xaman tsakar gida ba kamar yadda aka sabayi wanda hakan ke nuna cewar xuciyoyi babu dadi. Baba tunda ya fita da safe be shigo ba sai yanxu, Iya tana dakinsa ta kaimasa abinci tana kuma fada masa yadda sukai da sageer bayan fitarsa.
Sakeena xafi ya isheta ta saba xaman cikin AC nan kuma sai fanka danma Allah ya temaketa akwai wutar generator da Deni ya saka a gidan. Ta cire kaya ta fito wanka daure da towel, ta cika bocket da ruwa ta shiga dashi tayi wankanta ta fito. Tana sako kafarta wajen toilet din idonta cikin na Deni dake brush a bakin famfo, ta qura masa ido cikin zallar soyayya shi kuma ya dauke kansa yayi tsaki.
Jiki a sanyaye ta nufi daki, saidata juya sannan yabi bayanta da kallo, ya qurawa qugunta ido wanda ya qara cika ya kuma kalli santala santalan qafafunta farare qal ya hadiye wani irin mugun yawu, ya ayyana wai sakeena ce ta bawa wani namiji wannan jikin nata da yake matuqar so da kishi har yayi mata ciki? Ya fara tuno rayuwarsu da yadda sakeena ke xautar dashi a shimfida ya tuna randa ya fara saninta ya mace irin abunda ya samu daga gurinta yanxu haka wancan ma yaji kenan? Yanda sakeena ke riritashi a shimfida haka taiwa wancan kenan?
Wayarsa ta katse masa tunani, ya cirota daga aljihu ya amsa kiran Bilal wani abokin aikinsa. Bilal yace "Nura ashe anga matarka data bata" cikin mamaki yace da Bilal "a ina kaji?" Bilal yaja tsaki yace "karkayimun rainin wayo mana, sam banji dadin abunda kukai ba kaida yan uwanka na fidda maganar waje har ta gama duniya haka, wannan ai personal life dinka ce kuma be dace duk mugun abun da matarka tayi ku yimata haka ba domin koba komi dole akwai mutuncin kataba aurenta" Deni bai saurareshi ba ya katse wayar. Ya kunna Data dinsa da rabon daya kunna tun jiya. Saqonni suka dunga shigowa kamar su fasa wayar, beyi wani nisa ba yaci karo da posting din su Hadixa da Amina. Ya tsorata ya kuma harxuqa da mugun bacin rai ya daga labulen dakin Hajjo.
Suna xaune sunacin gyada duniya tai musu dadi suna kallon Arewa24. Ya daka musu tsawa yana nuna musu fuskar wayarsa da cewa "meye wannan nake gani?" sukayi bayan Hajjo da sauri suka buya. Ta miqe tsaye cikin nutsuwa da sassauta murya tace "nice na sakasu, kuma saura kaimun ihu da terere maqiyana suji susan kanmu ba a hade yake da kai ba, ya kamata xuwa yanxu kasan cewa bujirewa umarnina ba abu bane da xai haifa maka da me ido, domin tunda Kake bujiremun baka tabacin riba ba. Saboda haka ka kama kanka ka kuma bani hadin kai in kwatar maka yanci."
Be kuma furta komai ba ya juya ya koma daki ya kwanta ya dafe goshinsa ya rasa abunda ke masa dadi. Abokansa sai kiransa suke yaqi dagawa wasu kuma suna masa text da tambayarsa cewar abunda suka gani gaskiya ne? Ko kuma ana masa fadan abunda yayi na taunawa sakeena asiri.
Wajen 9:30 PM Sageer yayi sallama ya shigo gidan, Iya tana dakin Baba ta fito tai masa iso cikin dakin. Ya tsuguna ya gaishesu, ya qara da cewa "Iya dama naxo muku sallama ne saboda gobe xanje can gida Katsina gurin Mahaifiyata in fada mata abunda ake ciki, kuma in hali yayi xan xarce Lagos in taho da shedun da xasu tabbatar muku da aurena da sakeena." Iya batai magana ba sai Baba ne yace "To hakan yayi Mohd kuma ina fata baxaka dau lokacin acan ba" Sageer yace "in shaa Allah" Baba yace "Masha Allah, nima kafin ka dawo xamu hadu da malaman da nayiwa maganar inyaso inkaxo sai axauna aji abunda sharia tace akan ku" yayi godiya ya dakko bundle din 500 ya ajiyesu a gaban Iya yace "gashi Iya a kula da sakeena dasu don bakomi take iya ciba"
Iya ta katseshi da cewa "maxa daukemun kudinka xan iya kula da ita da abunda Allah ya horemun" ya kwantar da kai yace "Nasani Iya kuma ba raina kulawarki nayi ba amma fa yanxu sakeena matatace wajibi ne in dau dawainiyarta har xuwa randa xa ai mana hukunci" Baba ya katse musu muhawarar da cewa "To angode Mohd jeka Allah ya kiyaye hanya muna nan muna sauraranka" Ya fita gidan yana waigen dakin Iya da so samune da sakeena yakeso yagani amma inaaaa yasan hakan bame samuwa bane.
A ranar daga sakeena har Iya da Baba sai kuma Deni babu wanda ya runtsa, Iya da Baba dai bayan sun gama juye juye suka tashi suka duqufa sallolin nafila har xuwa kiran sallah.
Washegari gida ya dade, Baba sassafe ya fita haka ma Deni ya nufi makaranta sai Hajjo wadda Baba na fita itama ta fita su Hadixa kuma sun nufi computer school din da Deni ya saka su ita da Amina tunda sunyi jamb duk basu ciba.
Sakeena tana xaune daki tana shan kunun gyadar da Iya ta dama mata saboda jiya ta yini da yunwa ta kwana da ita tana sha saiga Saddiq ya shigo a gigice ya shiga dakin Hajjo yaga babu kowa, ya dawo saitin dakin Iya yace "Ina Hajjo da su Hadixa?" Iya ta bashi amsa da cewa "Su Hadixa kam sunje makaranta Hajjo kuma bansan inda tayi ba"
Kamar yayi kuka ya bude wayarsa ya nunawa sakeena posting din su Hadixa da kuma photon ta. Ta karanta da kuma comments din mutane akai ta dafe kai ta xunduma ihu. Iya tana tambayar menene a gigice Baba ya shigo shima gidan. Suka hadu suna tambayarta Saddiq ya nuna musu photon tare da bayanin abunda su Hadixa sukai posting.
Baba ya nemi guri ya xauna a kujerun dakin Iya, ita kuma Iya ta fara lallashin sakeena dake kuka tana cewa "shikenan sunana ya gama baci ni sakeena na shiga uku Allah ka dauki raina na huta" Cikin tausayinta Saddiq yace "Basu da lefi Sakeena yaya Deni ne ya basu haddin kai har sukayi miki haka, nima yanxu naci karo da posting nayi nayi in fahimtar da mutanen da suke xaginki amma sunqi. Yanxu abunda sukai ya dace Baba? Wannan fa matsalace ta cikin gida be kamata a fita da ita waje ba" Baba da Iya babu wanda ya kuma magana.
Ai basu tashi ganin tashin hankali ba sai wajen qarfe goman safe lokacin Saddiq ya fita Baba ya koma daki ya kwanta saboda ya rasa yadda zaisa kansa. Iya kuma ta tasa Sakeena gaba tana kuka ta kasa lallashinta.
Ana cikin hakane kuma sai suka jiyo muryar Hajjo daga soro tana cewa "A a yallabai shigo da kanka ka bata domin innice xasu dau abun da wasa" Suka jiyo sallamar qaton gardi Iya ce kawai ta Iya amsawa ya miqo mata takadda yace "Gashi daga kotu nake magatakadda ne ni sammacine uwar mijin sakeena ta shigar da sakeena qara akan ta tafi karuwanci da auren danta akanta" Iya ta sandare a tsaye, Baba ya fito daga daki yana wani irin tari yayi qarfin halin karbar sammaci daga gurin mutumin.
Hajjo ta harde hannu a qirji tace "Hmmm soyayya! kaine ma xaka karba mata sammacin? Naka dai shike bada kai, ai kamata yayi kaxo mu hada qarfi da qarfe mu kwatarwa danmu yancinsa gurin sakeena kilaki" Baba bece komi ba ya koma daki yana share kwallah.
Hajjo tai tsaki ta qarasa qafa ta fice wani gurin.
Iya ta koma daki ta tarar da sakeena kwance sanbal a sume, tayi kanta tana wani irin kuka tana kiranta. Baba ya shigo dakin ya dago kan Sakeena ya dora a cinyarsa yace da Iya ta miqo ruwa. Ta fita ta shigo da ruwa a kofi ta bashi yayi tofi ciki ya shafa sakeena a fuska, ta saki ajiyar xuciya ya dura mata ragowar tasha.
Ta tashi xaune ta riqe hannun Baba tace "Baba da gaske ne Hajjo ta kaini qara kotu kuma su Hadixa sun sakani a social media ko kuwa mafarki nake?" bai bata amsa ba sai sunkuyar da kai yayi, ta juya gurin Iya tayi mata irin tambayar, Iya ta fashe da kuka. Ta qara cewa "Baba in gaskene jefe ni xa ai ko? Tunda hukuncin zina da aure kenan ko?"
Haka Baba da Iya sukasa Sakeena a gaba suna kallon ta tana sambatu kamar zararriya har xuwa azahar. Lokacin su Hadixa suka dawo suka bude dakin Hajjo suka shiga.
Basu jima da shigowa ba sai ga Hajjo ta shigo fuskarta tar kamar yau sallah. Ta shigo ta rangada guda, su Hadixa suka fito suna tambayarta meyafaru? Tana kuma rangada guda tace "Daga gidan iyayen Yusuf nake manemin aurenki da yace ya fasa, naje na bude musu komi na fada musu yarinyar da ake xargi na batar dai karuwanci ta tafi Lagos kuma dama tun farko andora abun ne akan xargi domin bani da hannu a batan ta, kuma nayi sa a ana cikin xancen wata qanwar mijinki tace eh taga xancen a waya harta nunamun hoton sakeena nace eh itace. kamar dai yadda nai miki alqawari jiya xan faranta miki yau na cika alqawarin domin uwar Yusuf ta amince kuma tace babansa na xuwa xata fada masa afara shirin kawo kudi" Hadixa tayi tsalle ta dire tace "Dan Allah Hajjona da gaske kike" tace "wlh Hadixa daga can nake, ashe haka suke da arziqi? Kinga uban falon gidan? Ai yayi fuloti guda" Hadixa tayi murmushin jin dadi tace "Hmm ai shiyasa na kuma manne masa saboda nasan xan huta" Hajjo tace "Eh da gaskiyar ki yarnan ai naga zahiri me ake da auren wahala?" Ta ciro yan canji a jakarta tace da Amina "Maxa jeki waje kimun sadaka yau kam farar ranace a gurinmu burina na tsawon shekaru ze cika, so nake kema gurin auren Hadixa ki samu wani me kudin cikin abokan Yusuf ana gama nata aiyi naki kyayi karatun a dakinki." Amina ta karbi kudin ta fita tana hangota itama ta samu me kudi tayi aure tana hutawa tana tuqa mota. Tai tsalle ta dire tace a fili "Allah ya kaimu lokacin."
A ranar Hajjo yini tayi tana bi kwararo kwararo layi layi tana fadar anga sakeena kuma ta dawo da tsarabar ciki, babu batun tambayar Baba inxata fita. Xancen duniya wannan gayawa wannan kafin kace tak xance ya gama unguwar da maqotan unguwanni.
Hajjo ta dawo da laasar ta dora girkin dare. Ta sheqa tuwon shinkafa da miyar ganyen ugun don yau cikin farin ciki take. Ta gama ta miqawa Iya da sakeena nasu har daki cike da ixgili tace "Sakeena ga abinci naga yau uwar taki batai girkin rana ba ko tausayinki bataji ke da bake kadai ba, saboda ke nai miyar ugun kinsan me ciki sai da kayan qarin jini" ko Iya bata kulata ba balle sakeena da bata cikin hayyacinta tun rana.
Tai kwalliya ta shige dakin Baba dauke da tray da sabbin kwanikan qarau na cin abinci. Ta ajiye tana masa sannu. Ta gama kwarkwasarta da feleqe tsaf, ya dago ya dubeta cikin nutsuwa yace "Na haramta miki shigowa dakin nan da kuma girkin gidana domin na yanke igiyar aurena dake nai miki saki daya ki xauna kiyi iddah a dakinki kamar yadda sharia ta tanada, ban fadawa kowa ba amma inkin fada kin taunawa kanki asiri. Ki dunga girki keda yayanki ni kuma Hafsatu xata dungayi tana bani" Hajjo ta tsure maganar ta daketa fiye da xatonsa. Xatai magana ya daga mata hannu ya nuna mata hanyar waje ta fita da gudu tana tuje daurin da Amina tai mata.
Ya kira Amina yace ta kwashe kayan abincin ta kaiwa uwarta. Ya kwallawa Iya kira, ta shigo ta tsuguna yace "Daga yau na raba muku girki, kowa xai dunga nasa daban, kuma ke xaki dunga bani abinci a tukunyarki kullum xan dunga baki kudin cefananki daban." Dake mata ne irin na Da ta amsa da to bata tambayi baasi ba ta tashi tai waje.
Hajjo ta qule uwar daka tai ruf da ciki kan gado ta saka kuka cikin mamakin wai yau mal Lawan ya sake ta? Mutum me tsananin haquri da kau da kai, lallai yakai maqura wajen bacin rai da tasan matakin da xai dauka kanta kenan da batai abunda tayi ba da tabi komi a hankali, To yanxu da yace ta xauna xuwa gama Idda intagama iddar ina xataje?
Ta cigaba da kukanta da tunanin mafita su Hadixa sukai juyin duniya ta fada musu abunda akai mata taqi. sai da Amina tace "To kinxo kina kuka mun tambayeki me akai kinyi shiru inbaki fada mana ba tayaya xa ai mu samo mafita?" Cikin kuka ta fadamusu yadda sukai da Baba. Suma sun kadu da hukuncin da Baba yayi akan Hajjo Amina ta dafe qirji tace "mun shiga uku yanxu ya xamuyi ya maidake kafin wadancan suji suyi mana dariya?" Hadixa ta dake ta matso ta rage murya tace "Ta qarqashin qasa xamubi abun, kuma kema ki dake karki nuna masa kin damu zai rainaki, ba a yiwa namiji haka kuma karmu fasa duk abunda mukasa gaba, yadda kika tsayamun maganar aurena ta tashi kema baxan bari naki auren ya mutu ba." Hajjo ta saki hawayen farinciki lallai haihuwa mai rana meyafi yaya? wanda bai dashi Allah ya bashi. Ta rungumesu tana cewa "To maganar ta tsaya iyakacinmu mu uku karku fadawa yan uwanku na daki kuma karku fadawa maxan har xuwa lokacin da shirinmu xai kammala"
Washegari maqota suka fara shigowa yiwa Iya jaje da kuma ganin sakeena wacce kowa ya ganta sai yadda da maganar Hajjo gaskiya ce don ga alamar cikinan jikin sakeena. Ranar da aka fara hakan sunga bala i domin yini sur akai ana abu daya.
Kafin ranar shiga kotu tayi wato sati daya kenan masifar da Iya da sakeena suka shiga baxata faduba, domin sai da takai sakeena harta dena fitowa tsakar gida da rana sai dai Iya takai mata baho daki tayi alwala. Iya kuma ta xama kamar Hajjo lokacin batan sakeena wato ta shiga tsangwama da bakin mutane har takai andaina siyan kayan masarufin da take siyarwa kuma bata da sukuni ana tsine mata ita da sakeena ana cewa yarta tayo cikin shege da aure kuma taqi korarta. Gida ya xama na Hajjo da su Hadixa kawai suke bushasharsu yadda suke so.
Iya da sakeena suna daki a boye, Baba baya yini gidan saboda baqin ciki kwanciyar bacci ke kawoshi. Saddiq da Zahra sunyi baqin cikin abunda Hajjo tayi sun hadu xasuyi mata nasiha tayi musu cin mutunci tace xata tsine musu dole suka rabu da ita suka xubawa sarautar Allah ido, amma suna tausayin Iya da sakeena. Deni kuwa tun ranar Monday daya bar gidan ba a kuma ganinsa ba kuma ko awaya ba a samunsa kusan 1 wk kenan.
Iya tun tana jiran xuwan Sageer harta fara fidda ran xuwansa ganin gobe xa a shiga kotu. Ta gama qaryatashi da cewar auren sakeena yayi domin in aurenta yayi meyasa me fadawa iyayensa ba? Kuma meyasa tunda ya tafi be dawo ba, ko waya be bugo ba, su kuma sunyi batan basira basu karbi no dinsa ba. Duk da wani shashin na xuciyarta yana yabon Sageer da cewa yaron kirki ne kuma baxai mata qarya ba. Gabanta ya fadi data tuna wani abu, kardai ace Sageer gudawa yayi ya raina musu hankali ya durkawa yarinya ciki ya gudu ya barsu da jiran gawon shanu? Ta dafe qirjinta tace "Allah ka rufa mana asiri ka dubi rauninmu ka bayyana gaskiya ka kuma kawo mana Sageeru kafin gobe. Ita da Baba sun kwana suna sallah da tawassuli da ayyukan da sukai kyawawa yayin da sakeena ta kwana ido soye tana kallon rufin daki kukan ma ya gagara. Ita kuwa Hajjo da bata kulle yanxu tabi gidajen qawayenta tana tuna musu gobe nefa xuwa kotu. Duk inda taje suna yimata alqawari da cewar xasu fitar dango domin mara mata baya ta kwatarwa Deni yancinsa.
Qarfe goman Safe a kotun taiwa Iya da Baba da kuma sakeena wacce ta xama kamar tsumma ta saka hijab har qasa tana kare fuskarta saboda masu daukanta photo a waya. Hajjo ta shigo da jama arta da suka kusa cike kotun wasu ma suna tsaye da kuma su Hadixa wadanda basuje makaranta ba sun taho marawa uwarsu baya.
Kafin ta fito daga gida sai da Saddiq ya sunkuya har qasa ya roqeta ta janye qarar nan, ya tuna mata lokacin da tayi silar batan sakeena sun roqi Baba akan karya kaita gurin jami an tsaro ya haqura dashi da Iya suka barwa Allah duk da girman lefin da tayi na batar da dan mutum. To itama ta duba wannan halacci da sukayi ta janye qarar adawo gida ayi shariar a sirri. Ta bashi da cewa "Ai ita sakeena bata da gata ne shiyasa maganar tabi ruwa, amma shi kuwa Deni yana da gata dan haka saita bimasa haqqinsa na yawon dandi da sakeena tayi da aurensa" tana fadar haka Saddiq ya bata hanya ta wuce yana kuka yana nadamar abubuwan da yayiwa sakeena a baya.
Al qali yana xuwa aka fara gabatar da shariar wadan da suka dau lauya kamar yadda yake a dokar kotu, aka sallamesu sannan aka fara shariar marasa lauya kuma shariar su Sakeena ce a farko aka kirata aka kira Hajjo suka fita gaban dubban jama a sakeena kanta a sunkuye gabanta na faduwa.
Alqali ya nemi Hajjo ta fadi abunda take qarar sakeena akai. Ta ware murya tana kwararo tarihin xuwan sakeena gidansu da yadda ta hargitsa musu gida ta dunga qarya da qara batawa sakeena suna. Daga can baya Hadixa ta samu wasu yan jarida wakilan gidajen radio masu xaman kansu da sukaxo daukar wasu shariar tace suje su dauki shariarsu ta basu dama. Babu bata lokaci dan abun nema ya samu suka fara nadar muryar Hajjo dake batawa sakeena rayuwa da kalaman qarya. Ta gama tas, aka samu noise a kotun na mamakin abunda sakeena tai da kalaman tur, mutane suka fara daukarta a photo wasu kuma nayin vedio. Ta kare fuskarta da hijab kanta a qasa tanaji kamar qasa ta tsage ta shige dan kunya da muxanta. Iya ta dafe kai tana kuka shima Baba hawayen yake.
Al qali ya buga guduma akayi shiru ya juyo ga sakeena ya tambayeta abunda aka fada gaskiya ne? Domin Hajjo ta kawo shedu aciki harda cikin jikin sakeena. Anfi minti 5 ana jiran cewar sakeena amma ta kasa cewa komi, da kyar ta bude baki tace "Sunana Sakeena Abbakar Liman kuma duk abunda ta fada gaskiyane har cikin dake jikina, Dan Allah ayimun hukuncin da sharia ta tanada akaina" Al qali yayi kabbara mutane kuma aka dau tsinuwa da fatan shiriya. Ya qara buga guduma akai shiru, yace "Tunda wacce ake qara ta amsa laifinta mun ajiye rana itayau wato ranar litinin a matsayin ranar da xa ai hukunci kuma a tabbatar da anxo da mijin sakeena na farko" aka shiga wata shariar.
Baba ya riqo hannun sakeena da Iya suka fito daga kotu mutane na binsu, yan jarida ma na binsu sunawa sakeena tambayoyi da daukanta a photo.
Yana xuwa wajen kotu ya tari napep ya xuba su ciki ba tare daya fada musu inda xashi ba shima ya shiga yace muje. Hajjo kuwa tanacan yan jarida sun kewayeta anata hira da ita suna nadar muryarta.
Hajia 😊
[7/31, 2:26 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣0⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Assalamu alaikum, inawa dinbin masoyana ko ince masoyan rubutu na😄 fatan alkhairi. Yar taqaitacciyar sanarwa ce nake tafe da, inaso masu karanta littafin muqaddari ne su sani, wannan labari na qirqireshi ne kuma ina rubutashi da nufin fadakarwa da kuma nishadantarwa dan haka Dan Allah mutanena a dan tsahirtamun kadan na idar da abunda nayi nufi ma'ana a dena cemun kaxa ya dace ko kuma be dace ace anyi kaxa ba saboda hakan yana dakushe karsashina kuma yana sacemun gwuiwa. Mu kula da wani abu guda daya a rayuwa, bafa duk abunda kakeso kake samu ba, kamar yadda ba duk abunda kakeso ne yake xama alkhairi ba, Hujjata anan itace fadar Allah (S W T) acikin Al qur'anil kareem inda yake cewa "Ya kusanta ko so abu ya xama sharrine gare ku, kuma ya kusanta kuqi abu ya xama alkhairi gare ku" a cikin wata ayar kuma yace "Kun kusanta ku qi abu Allah kuma ya sanya alkhairi me yawa cikinsa" (sadaqallahul azim) Kuma a duk sanda marubucin da yasan abunda yake ya xauna ya qirqiri lbr bawai kawai yayishi ne don nishadantarwa ba, a a dole akwai darasi aciki. Yanxu kamar HAJIA (ni kenan) inna tashi rubutu nakan dauki matsalar da nasan tana addabar Al umma inyi rubutu akai dan fadakarwa da nufin bada gudummawa wajen gyara wannan matsala. Amma fa ba fushi nayi ba dan anamun gyara ko nunamun hanyar da ya dace littafin yabi. No! Kakata ta bamu sirrin xaman duniya takan fada mana cewa inkanason cin ribar rayuwa karkai fushi,😄 haka ma umma na harta koma ga Allah tana fada mana ba'a fushi da masoyi tattalinsa ake domin ya gama maka komi tunda ya soka (RIJF UMMA 😥) Nagode sosai masoyana duk inda kuke ako ina kuke wanda Allah ya hadamu da wanda bamu hadu ba duk ina qaunarku fiye da yadda kuke qaunata, innace xan kawo sunanku sai muyi 1 wks bamuyi posting ba saina sunan masoya 😜 Sannan daga qarshe inason sanar muku cewa abunda yasa bana daily post saboda ina dogon feji kuma inada harkoki na cikin gida dana business kunsan da ruwan ciki akejan na rijiya.😊 Nagode sosai muna tare 🤝🏽
Godiya ta musamman ga
Ya RUQAYYAH (Haj Ruky)
ANTY SIS
MARYAM BAITA USMAN
ADDA SARATU (maman khairi)
MARYAM SANI
NAJA' ATU (yar malam)
DIYAR KATIBI
BAPPA JAMILA (maman muhibba)
SAPNA
Suna xuwa gida Baba ya kama hannun su ya kaisu har daki kamar yadda ya fito dasu daga kotu. Saddiq na dakin soro a kwance cikin qunar xuciya yaji shigowar mutane ya fito shima ya shige dakin Iya inda yaji motsi.
Ya tarar dasu kowa fuska jiqe da hawaye har dai Baba da yake namiji, ko basu fada ba yasan xaman kotu baiyi musu dadi ba kuma dama haka ya guda shiyasa ya qauracewa xuwan. Baba ya dubi Sakeena yace "Sakeenatu danme xaki amsa lefin da baki aikata ba? Dan me baki fadi gaskiyar abunda kika sani ba?"
Tayi shiru ba tare da tace komi ba. Iya ta share hawaye ta matsa gaban Sakeena tace "Sakeena ni uwarki ce, ki fadamun gaskiya kinji domin na farajin qanshin gaskiya a maganar Hajara da Deni tunda gashi sageeru yayi mana wayo ya gudu daga xuwa katsina taho da uwarsa yau sati guda babu duriyarsa, Katsina aiba Saudiya bace da xa ace antafi anshafe sati ba a dawo ba. Ki fada mana gaskiyar lamari kinji diyata"
Ta kuma yin shiru na tsawon 3 minutes, su kuma suna binta da ido. Ta dago ta sauke idonta kan Baba dan tana ganin shi kadai ne xai yarda da ita tunda Iya ma ta fara xarginta balle kuma Saddiq da take ganinsa baqiqqirin saboda jinin Hajjo ne. Cikin sanyin muryar kuka tace "Baba wallahil Azim ban taba zina ba, ni ba fasiqa bace, banyi fasiqanci tun ina qauye ina nemarwa kaina abinci ba? Banyi fasiqanci tun ina kwana da yunwa a gidan Deni ba? sai yanxu da aurena? Koda ace ansameni da laifin zina to wlh banyi ina cikin hayyacina ba" Baba ya jinjina kai cikin yadda da Sakeena ya tsuguna gabanta yace "Sakeenatu na yadda dake, kuma a ko ina xanyi shedarki akan hakan, domin nasan dake Mazinaciyace to da Deni ne xai fara samun wannan damar a kanki tunda kina sonsa fiye da komai kuma ya taba yi miki tayin zinar kika guje masa. Nasan bakisan nasan wannan ba ni da iyayenku mata kuma wannan shine dalilin da yasa nayi muku aure babu shiri dan gujewa fadawarku cikin halaka. Amma Sakeenatu ki daure ki fada mana abunda kika sani na tsakaninki da Sageeru dan Allah"
Ta share hawaye karo na barkatai tace "Lokacin da Hajjo ta koreni daga gidan Deni bata bani ko sisi ba domin tahowa Kano, dan haka koda naje tasha nasha wahalar tare motoci 4 ina roqonsu su kaini Kano in sun kawoni xaka basu kudinsu amma duk sukaqi har wani cewa yayimun daga ganina guduwa xanyi daga gida. A haka nasamu wata mata ta yaudareni tacemun Kano xata na shiga motar ta saida muka kwana muna tafiya sannan da safe nagane sace ni tayi, na fara ihun neman taimako amma babu wanda ya ganni sai dana fiddaran samun temakon sai naji direbanta yana cewa wani yana binsu har yana harbi, bansan kowaye ba saboda bana cikin hankalina lokacin. Ganin haka suka tunkudoni daga mota suka gudu. Iya abunda nasani kenan lokaci, sai bayan na farka daga bacci wani likitan ido ya nunamin Sageer a matsayin mijina, ni lokacin bansan kowa ba saboda bakomai a cikin kwakwalwata dan haka na yadda ya tafi dani gidansa muka fara rayuwa irinta miji da mata, ban tuna komi ba sai ranar da mukaje gaban likita yace inada ciki ranar na tuna komi. Amma kafin lokacin ina dan tuna rayuwata ta Baggadano har nake tambayar Sageer ina Nura qanina shine yacemun in ina sonsa kar inkuma tuna baya in xauna dashi baxai cuceni ba"
Iya ta dakko maganar Sageer inda yake cewa ya auri sakeena babu wanda ya sani a danginsa sai abokinsa ta hada da jawabin sakeena, ta furta "Innah lillahi wa'innah ilaihi raju'un. Shikenan yaro ya cucemu ya raina mana hankali ya batawa yarmu rayuwa ya rakota har gida ya zambacemu ya gudu. Ni Hafsatu naga ta kaina, ina xansa raina?"
Saddiq ma dai kalmar innalillahi yake maimaitawa, Baba ne kawai yayi juriya ya dake ya Kalli Sakeena yace "Ke diyatace sakeenatu har abada duk da ni talakane kuma bansan kowa ba amma baxan bari a xalunceki ba, xanyi duk yadda xanyi inbi miki haqqinki na xaluntarki da akai, in shaa Allahu xan daukar miki lauya kafin xuwa ranar komawa kotu baxan taba bari ayi miki hukuncin aikin da baki aikata ba, keba marainiya bace indai Mal Lawan yana raye, ni mahaifinki ne Hafsatu kuma mahaifiyarki, gado nane kawai baki dashi sakeena, kuma shima dan dai hurumin Allah ne, amma duk abunda uba yakewa ya xan miki"
Saddiq yana kuka yana girgixa kai, Baba ya miqe xai fita Saddiq ya rufa masa baya, ya juyo ya dakatar dashi yace "Ka fita daga harkarmu indai kasan Hajara kakewa rahoto, banason munafurci" Saddiq yayi wuf ya dakko qur'ani kan bed side xai rantse. Baba ya kwace yana masa fadan akan me xai rantse da littafin Allah. Yace "Baba dan ka yarda dani ne, wlh Baba na dawo rakiyar Hajjo tun lokacin datayi silar rabuwar Deni da sakeena ta hanyar asiri. Kuma kema sakeena ina neman yafiyarki kan abunda ya faru a baya kiyi haquri ki yafemun" Baba ya jinjina kai, ya juya ga Iya yace "Hafsatu karki qara taba duk abunda kikasan Deni ne ya kawo daga kan kayan abincinsa har xuwa kan kayan masarufi ki bar musu abunsu shi da uwarsa. Xan dunga baki kudin awo dana cefane ki dunga siyan abunda xaki dafa mana ni da ke da sakeena. Kuma duk abunda Hajjo xatai karki kulata dan Allah" ya fara lalubo kudin aljihunsa xai bata tace "to malam, akwai ma kudi a hannuna wanda sageeru ya bayar a kula da sakeena ko dasu xa ayi amfani wajen daukan lauyan?" Saddiq cikin sanyi jiki yace "Baba dan Allah a hada dani a cikin tukunyar Iya domin nima yanxu Hajjo batayi dani tunda nace ta janye qarar data shigar" Baba yayi murmushi ya shafa kan Saddiq yace "To, taho mugani"
Su Hajjo basu shigo ba sai azahar, lokacin har Iya ta gama yin abincinta ta juye a warmer takai daki ta tasa sakeena gaba sukai alwala suka shige daki suka rufo.
Su Hajjo anbaje a tsakar gida ita da ragowar mutanen da sukayo mata rakiya xuwa gida. Suka dunga maida yacce akai a kotu kuma suna fadar yadda yan jarida sukai da Hajjo yanxu acan gidan radio. Wata qawar Hajjo Laraba tace "An shige daki an qule hmm kunyar duniya ma kenan saura ta lahira" haka dai suka cigaba da sakin habaici da kalaman tunxura har xuwa kiran sallar asarr lokacin majalsar ta tashi kowa yayi gidansa.
Da daddare a shirye shiryen gidajen radio duk inda ka kunna acikin kanun labarai labarin sakeena ne wacce ta tafi yawon bariki da aurenta ta dawo da cikin shege da cutar HIV. Baba yana daki Iya ma tana nata dakin da sakeena agaba Hajjo ta ware sautin radio ya cika gida domin su sakeena su jiyo don basu kunna radio ba. Muryar Hajjo tas a cikin radio tana kuka tana fadar tarihin sakeena na qarya har xuwa kan abunda tayi, wanda tace silar haka mijin sakeena wato danta Deni baqin ciki yasa ya gudu ba a ganshi ba ko a waya ba a samunsa. Daga angama shirin a wannan gidan radio saisu juya wancan.
Sakeena dai tana xaune kamar gunki daga ita har Iya da Baba babu wanda yaci wani abu tun safe dan cikinta sai kusur kusur yake alamar yunwa ta dameshi.
Kafin wayewar garin talata labarin karuwancin matar aure sakeena ya xama batun da ludayinsa kekan dawo domin gidajen jaridu na hausa da turanci sun bubbuga labarin da photon sakeena da Hajjo ta bayar. Gida ya kuma dadewa kowa ya kama gabansa, Baba ya tafi fafutukar neman lauya su Hadixa sun tafi skull. Sai Hajjo da Iya da sakeena dake can daka jikinta xafi rau.
Su Amina suka shigo da gudu suna nunawa Hajjo jaridar turancin hannunsu me dauke da photon sakeena sukace sun fita kenan sukaganta ana siyarwa shine suka siya suka dawo nuna mata. Ta goge ruwan hannunta na wanke wanke ta karba ta duba tace "To ku karantamun abunda sukace mana Allah ya sa dai yadda na fada musu haka suka rubuta" Amina tahau karanto turancin jikin jaridar cikin grammatical errors (RIP English🤣) Tana fassarawa da son xuciyarta domin abunda aka rubuta daban abunda take fada daban tunda turancinta beyi riqar daxata karanta jarida ba kuma tafi qarfin tace baxata iya ba, Hadixa na gefe na gyada kai kamar qadangaruwa tana cewa haka akai da kyau, har gara Amina akan Hadixan dan ita diskindarice brain din a dode take.
Hajjo tace "To maxa ku ajiye jaka ku fito muyi aiki tunda kun makara gobe kwaje" Deni wanda ke gudun Hijira a hostel din BUK sai gashi ya shigo a burgija kama duk ya fita hayyacinsa cikin kwana takwas kacal, fuskarsa duk qasunba. Shima jaridar ce riqe a hannunsa har hostel abokinsa ya kawo masa, akai masa chaa ana tambayarsa ala dole ya gudo daga can xuwa gida don gidan yafi security.
Ya dagawa su Amina yace "Meye wannan? Abunda kukai be isheku ba sai da kuka hada da Newspaper? Ina ruwanku da rayuwata? Har yanxu inason Sakeena kuma ni ta batawa ba ku ba" Hajjo tasha gabansa tace "Nice nayi ba suba, bayan haka kuma har qara na kaita kotu jiya aka xauna kuma wani satin xa ai mata hukunci tunda ta amsa lefinta kaima kuma alqali yace axo da kai ranar. Kuma inka kuma tsoma baki cikin lamarin ko ka kuma kiramun sunan karuwa acikin xuri ata Nono na dana baka Allah ya isa" fuskarsa bata nuna mamaki ba ko tsorata da kalamanta ya juya ya koma daki.
Hadixa ta rage murya tace "Sai fa kinbi ta qarqashin qasa xai rabu da ita, ada ma ya haukace kanta bare yanxu data xama yar gayu mace sosai?" Hajjo ta girgixa kai tace "Tabbas, yanxu kuwa"
Iya ta fito riqe da sakeena ta rakata kofar bandaki ta tsaya jiranta, Hadixa ta fara rera waqar "Wayyo ni Allah namadi ya gudu ya barni namadi da tsohon ciki namadi" suka kwashe da dariya. Hajjo tace "Hadixa xan fita ku dafa mana taliya jellof da dankalin turawa tunda ga yayanku ma ya dawo nasan xaici sosai ga 200 asai kifi asaka tayi xaqi. Aini wannan raba girki yayimun dadi na huta ciyar da qattin banxa daya juya dayar kuma me shege aciki. Naga ma anfara wata sabuwar tsirfa jiya an daina taba kayan abincin gida sai awo ake yowa a kanti" Amina taja tsaki cikin tsabar futsara tace "Aikin banxa, isar da ba a isa ba, in da gaske xuciyar akai adawo da kudin da yayanmu ya bada mana aka kafa jarin tunda na tabbatar acikinsu ake awo da cefane" Hadixa tace "Wlh kuwa, ai baxa a dawo dasu ba yunwa ta kashe shege aciki" Hajjo tace "Hafsatu ki tanka musu mana in kin isa?" Iya xuciya ta kawo mata wuya amma tayi matuqar qoqari ta danne tabi umarnin mijinta.
Hajjo cikin jin haushin rashin tankawar da Iya tayi tace da Amina "Shiga dakinta ki fitomin da duk abunda kikasan Deni ne ya bata, don tunda malam yaqi goyan bayana wlh ya tarko tashin hankali. Ke kuma Hafsatu inkinji haushin abunda nayi ki haifi naki Dan ko kuma sakeenar da kike ikirarin yarkice tayi miki magani"
Amina da Hadixa suka shige dakin Iya suka dunga fito da kayanta na masarufi data kafa jari da kudin Deni, kai basu tsaya nan ba har kujerun dakin guda 2 da Deni ya raba musu saiti da Hajjo saida suka kinkimo da center carpet da kuma qaramar TV Toshiba da receiver. Hajjo tace "da kyau kukai kujerun daki ku hademun da nawa dama nawane akaimun qarfa qarfa, kayan kuma ke Amina ki shishshiga maqota ki fada musu nadawo sai da kayan kanti."
Iya ta riqo Sakeena tada gama wanka suka taho, dai lokacin kuma Deni ya fito da belt daga daki da alama yaji batun su Hadixa. Ya qurawa Sakeena ido, inaga hakance ta hanashi gane Hajjo ce tsaye gabansa ta boye su Hadixa a daki data ganshi da belt. Su Iya na shiga daki, ya daga belt iya qarfinsa ya saukeshi kan Hajjo a xaton su Amina ne. Ta tsanyara ihu dan dukan ya shigeta ya juyo a firgice, yayi arba da Hajjo tana sosa baya yace "Ina yan iskan yaran suke?" tace "Nasakasu a daki ni ka dakeni a madadinsu tunda Hafsatu ce ta haifeka. Wlh Deni xan maka baki rayuwarka ta lalace akan Hafsatu da sakeena"
Iya ta fito riqe da kudi ta miqawa Hajjo tace "Ga kudin cinikin kayan da akai" Deni ya riqe mata hannu ya durqusa yana bata haquri, batama ji abunda yake fada ba balle ta bashi amsa. Hajjo ta fusge kudin ta soke a cikinta, Iya ta juya ta koma daki Hajjo ta shige nata dakin akabar Deni tsugune a cikin rana yana ayyana kodai ya hada kayansa ya gudu ne? To inya gudu yaje ina? Kuma aikinsa da karatunsa fa? Yace a cikin xuciyarsa inama ba Hajjo ce ta haifeni ba, inama ana canja uwa daya canja Hajjo, sai dai kash! In aka haifeka an cuceka domin ba a canja iyaye.
Hajjo ta nunawa su Amina kudin da Iya ta bata, suka irga tace "Masha Allah, ta bani kudin xuwa gurin teacher, yanxu can xan nufa ayimun aikin akan raba xuciyar Deni da mayataccen son sakeena sannan a tasomun da maganar auren Hadixa naji har yanxu basu aiko ba" ta canja kaya ta fita tare da Amina wacce xata shiga maqota fadar Hajjo na saida kayan kanti.
Iya kuma ta fara gyaran dakinta dasu Amina suka birkita mata garin kwashe kayan Deni, ta gama ta dora girki.
Hajjo bata jima sosai da fita ba sai ga wasu gungun fusatattun matan unguwar(mahaukata masu ara su yafa) sun yiwa gida tsinke, Iya ta taresu tana tambayarsu lfy? Dayar ta dauke Iya da mari tace "Tunda ke mahaukaciyace dabba baki haihu ba balle kisan ciwon yaya shiyasa yarinya tayo yawan dandi da aurenta harda ciki kika bata mafaka ko? Salon namu yayan suga abunda tayi kuma suga ba a dau mataki ba suma suje suyi? Saboda haka inkinason kanki da lfy ki fito da sakeena ki koreta tunda ba yarki bace ke bakomai bace gurinta sai yar uba. Inkuma kinqi wlh saimun qoneku keda Sakeena da rai" ta fito da jarkar fetur da kuma ashana.
Iya tayi wuf ta fada daki ta danno tasa sakata ta dafe qirji tana haki. Sakeena ido jajur taji duk abunda akace tace "Iya danme xaki rufe qofa? Meyasa baxaki miqani garesu ba?" Iya ta kamo sakeena ta qanqame tace "Duk uwar duniya tana sadaukar da ranta dan danta ya rayu, ke yatace Sakeenatu xan iya sadaukar da tawa rayuwar dominki sai dai a kashemu tare, ko kuma a kasheni kafin a kashe ki"
Matan da suka ga Iya ta shige ciki suka hau buga kofar iya qarfinsu suna cewa ko ta miqo sakeena ko su balla kofar su shigo ta qarfi.
Deni tunda yaji abunda suke fada ya fice a sace don basusan yana gidan ba, ya tari napep ya kaishi police station na Gwale a gaggauce ya fada musu cewar wasu gungun matace sukaje xasu qona mutane da rai in ba'ayi gaggawa ba komi na iya faruwa. Jin cewa abun be afku ba suga gaggauta sukayi mota guda da police Deni ya shiga suka tafi.
Umman Amir ta nuna mata gidan tace tsaya anan Hajiya Hassana don nidai kamar nan sukaimun kwatance, Hassana ta kalli gidan ta glass din motar ta dake rufe ruf tace "anya kuwa maman amir? Nan fa kamar gidan babu lfy baki ga mutane cike ba?" Umman Amir tace "To bari su dan ragu sai inshiga inga, inma banan din bane sai inyi tambaya don kusa da nan Babar sakeena taimun kwatance" sukayi xamansu a mota suna jiran mutanen su ragu su shiga ciki. Dai dai wannan lokacin kuma motar police ta tsaya suka diddiro suka shiga ciki da hanxari.
Suna saka kai sukaji wata tsohuwar jaka acikin matan tana cewa "Tunda mun kasa balle kofar kawai musawa dakin wuta mu cika aiki mu raba kudinmu mu tafi" yan sanda suka daka tsawa ogansu yace "duk a tattara kansu ayi station dasu" yan sanda suka daka musu wawa suka kwashesu duka, suna ihu wasu suna cewa "Ayi haquri Hajjo ce ta basu 500 kowacce suxo su tsorata sakeena da Iya su koresu daga gidan" Ogan yace "kofur duk ka kwashemun yayan iska tumaki wadanda kudi kesa suyi kowane irin aiki, kunsa kanku a uku, wlh kotu xan miqaku Hajjo taxo ta ceceku da bamuxo ba kenan kisa xakuyi?" aka watsasu mota wata kan wata 🤣 Suka tafi dasu.
Deni ya koma daki yana dafe qirji, xuwa yanxu ya fara tunanin Hajjo tana da mental problem dan wannan abun da tayi ba aikin masu hankali bane. Tausayin sakeena da Iya ya dirar masa.
Suma su Amina sai a lokacin suka bude daki domin suma sun tsorata da abun kuma basusan Hajjo xatai haka ba da sun hanata gashinan buri be cika ba sai ma asirinta daya taunu.
Iya ta sauke ajiyar xuciya bayan tafiyarsu, Sakeena tace "Iya kiyi haquri, riqona be miki rana ba, ban share miki hawayen rashin haihuwa ba sai janyo miki masifa da nakeyi"
Hassana ta fito daga mota bayan tafiyar yan sanda suka shiga cikin gidan, ta dunga sallama can Hadixa ta amsa musu ta umman Amir tace "nan ne gidansu Sakeena?" Amina ta amsa "Eh ga dakinsu nan a rufe" Umman Amir ta fara bugawa tana kiran sunan sakeena amma tsoro ya hana Iya budewa sai da Hassana tayi magana da cewa "Dan Allah inda mutane ciki a bude Hassana Dalhatu ce taxo gurin sakeena" da sauri sakeena ta miqe ta bude kofa ta fada jikin Hassana suka rungume juna.
Suka shiga dakin Iya tai musu shimfidar tabarma a gurbin center carpet da Amina ta nade daxu suka xauna har qasa Hassana ta gaida Iya ta Kalli sakeena ta ciro News paper a jakarta tace "Sakeena bayan rabuwarmu dake munje Law school mun gama kuma munxama cikakkun lauyoyi ni da Usaina a shekarar kuma mukai aure wata 5 kenan baya akai bikinmu ni da usaina da yaya Ahlan. Ni ina Lagos acan nake aure da kuma aiki a chamber dita da Abba ya budemun. Usaina tana ukirine acan take aure sai yaya Ahlan dake Abuja. Naxo ganin gida ranar Friday naketa cin karo da labarai marasa dadi akanki a social media, sai kuma jiya naji a radio yau kuma na fito da safe naci karo da wannan Newspaper din. Labarin ciki na cin xarafin dan adam ne, koda ace kin aikata abunda ake tuhumarki dashi be dace ayi miki hakaba, bare wannan abun da aka fada beyi kama da abunda xaki aikata ba Sakeena. Na fadawa Mama da Abba harda mijina sun bani goyan bayan tsaya miki a matsayin lawyer shine na nemi umman Amir ta rakoni gidanku. Ki budemun komi sakeena xan temaka miki in kwatar miki yancinki ke qanwarmuce kamar yadda mukasha fada miki abaya."
Sakeena batai magana ba sai gyara kwanciyarta tayi akan cinyar Hassana. Iya ta muskuta ta fara basu labarin duk yadda akai bata rage musu komi ba. Domin ta gane Hassana sosai tasha jin xancensu bakin sakeena.
Suna daki xaune suna tattauna matsalar har Baba ya dawo da Saddiq suka shigo suma suka fadi daga nemo lauya suke amma ko ina sai da kudi, sunji dadin jin Hassana xata tsayawa sakeena kyauta. Suka tattauna yadda xasu bullowa lamarin. Hassana tayi musu alqawarin nemo sageer duk inda yake a Nigeria bama a Lagos ba da take gida a gareta. Anrabu suna farin ciki jin alamun nasara har mota saddiq da Baba suka raka Hassana suka tafi.
Baba ya dawo cikin dakin Iya ya tsaya yana kallon dakin ankwashe komai, ko Iya bata fada ba ya sani Hajjo ce tayi sanadin raba Iya da kayan da Deni ya sai mata. Saddiq ma sai a lokacin ya lura domin harga Allah farkon shigowarsa be lura ba, (hankali shike gani wai wani yaxo Kano bega mota ba 😄) ya fita yaje dakin Hajjo yaga kayan Iya acikin falon Hajjo dan hauka TV har guda biyu, be cewa su Hadixa komai ba saboda kar suyi masa rashin kunya ya dakesu Hajjo ta tsine masa.
Baba ya shiga dakinsa ya kwallawa Amina da Hadixa kira, suka shiga a darare a xatonsu fada xai musu, sai dai me? Gani sukayi ya nado duk abunda yasan mallakin Deni ne daya bashi a dakin ya tattara yace "ku kwashe kukai dakin uwarku kafin nima taxo taimun gorin" suka fara bashi haquri da fada masa wai ai Iyace ta watso kayan tace bataso. Yace "To madallah nima gashi na watso nace banaso" suka dunga jidar kayan suna kaiwa dakin Hajjo suka cushe dakin da kayan.
Hajjo bata shigo ba sai bayan la'asar shigo faran faran kamar korarriya. Taga kaya sun cika daki tayi turus tace "Wadan nan fa daga ina?" sukai mata banxa, ta nemi guri ta xauna akan kujera tace "Auta magana nake kunmin banxa" Amina taja tsaki tace "Hajjo na rasa abunda yasa kike da over acting wlh, gaskiya yau kin mugun batamun rai kuma kina nema ki bata mana plan" cikin kwantar da murya tace "Me kuma nayi na batamiki rai auta?" Hadixa cikin masifa kamar xata daki Hajjo tace "Yanxu meye naki na debo hayar mata da basu kudi suxo har gida su qona sakeena da Iya? Meye ribarki in sakeena ta mutu yanxu? Ai gara ta xauna a duniyar taita shan wahala in kuwa ta mutu wataqil ta samu salama. To albishirinki? Matan da kikayo haya Deni ya dakko musu yan sanda sun tafi dasu station kuma ance kotu xa'a turasu, sannan tun anan da sukaji wuya sunce kece kika sakasu. Wannan kaya da kika gani kuma Baba ne yace a kawo miki kayan danki tun kafin ki masa gori yadda kika yiwa Iya. Ya kamata fa ki dunga rage wani abun,saboda yaqi dan xan bane, kuma Baba uban mune, muna sonsa ko so kike baqin cikinki yayi ajalinsa mu xama marayu?"
Hajjo ai bata gama jinsu ba ta garxaya toilet tayi fitsarin daya cika mata mara jin ance yan sanda sun kama su Laraba qawarta, ita dai a rayuwarta tana masifar tsoron yan sanda.
Ta dawo daki ta xauna tace "Amina wlh ba cewa nai su qonasu ba, kawai cewa nai su koresu su kuma tsorata su, wai ni a nufina in sukaji xa'a kashesu xasu tsorata su gudu garinsu, kinga gida ya xama nawa ni da ku Iya taje can qauye ta zauna tunda bata haihu ba, malam kuma ya maidani, shi kuma Deni in nema masa yar asali ya aura" ta janyo leda baqa ta fito da saqon data karbo yanxu gurin malami ta fadawa Hadixa yadda xatai amfani dashi ta kwashe tana hararar Hajjo kamar ba itace ta haifeta ba. Saqon Deni kuma ta diba xatayi masa amfani dashi da kanta. Ko sallah ta kasayi daga anyi sallama saita firgita tana gani kamar xa axo tafiya da ita gurin yan sanda.
Maxajen da aka kama matayensu sukayi qungiya sukaxo gurin mal Lawan da magriba suna nema Hajjo ta shige masa gaba a sako matansu da aka tafi dasu station. Ya koma cikin gida ya tambayi ba'asin maganar Iya bata fada masa anyi wani abu ba bayan fitarsa. Sai da saka Iya a gaba sannan ta labarta masa yadda akai ya jinjina kai ya koma waje yace da maxan bada yawunsa akai abunda akai ba saboda haka bari yaje ya turo musu wacce ta kitsa abun. Ya shiga ya kira Amina yace "Jeki kice da uwarki taje waje ana magana da ita" Amina taje ta fadi saqon, Hajjo ta tsure ta kasa fita sai da suka rakata. Maxa sukayi mata chaa suna tuhumarta ina matansu. Ta rude ta koma bayan Hadixa, suka tasa qeyarta xuwa police station da nufin beli amma yan sanda suna arba da Hajjo suka hada da ita suka rufe sukace babban lefi garesu saboda sunyi yunqurin kisan kai. Maxan suka tafi suka bar su Hadixa na ihun a saki Hajjo. Maxan dama sunyi hakanne don a kama Hajjo shiyasa sukayimata kofar rago da cewa taxo tasa asaki matansu, domin baxatai silar rufe musu mata ba sannan ita taxo gida ta xauna, ya kamata da ita data sakasu, da su da sukayi hauka suka biye mata su fuskanci hukunci iri daya. Tsuntsun da yaja ruwa, shi ruwa ke doka.
Suka shigo gida a rude suka dire dakin su Deni suka fada musu abunda ke faruwa, Saddiq sai lokacin yaji danyen aikin da Hajjo tayi, yace "Dole mu jira xuwa lokacin shiga kotu ita ta jawo, haqqin sakeena ne yasa takai kanta ga hukuma" Deni kuma yana kwance ko motsi beyi ba balle su saka rai xai ce wani abu.
A cikin gida suka tadda Baba dakin Iya yana cin tuwo suka fada masa, suka gama xamansu bai ko ce uffan ba suka tashi suka nufi daki neman mafita.
Aka turo da kiran Baba daga waje yaqi fita a xatonsa mutanen Hajjo ne. Iya ta lallabeshi ya fita, yana fita ya juyo yace da Iya kimtsa baqo mukai.
Ya koma ya shigo da namiji suka xauna dakin Iya yace "Hafsatu Barrister Adam ne wanda Sakeena tai aiki a gidansa kuma shima ya samu labarin abunda ya faru kuma yaxo ya temaka ne tunda bagarensa ne" Iya taji dadi tace "To madallah ya yaran?" ya amsa, bai samu ganin sakeena ba, Iya da Baba ne suka xauna suka bude masa komi kuma sukace akwai wata lawyer akan lamarin gobe xataxo sai su hadu a tattauna. Yayi musu sallama ya tafi.
Washegari da sanyin safiya su Amina sukayi breakfast suka tafi kaiwa Hajjo daga can suka wuce neman mafitar yadda xa a fidda ita. Don sun firgita da ganinta a kwana daya kacal, fada sukai da qawayenta datayi sanadiyyar dauresu suka hadu sukai mata dukan tsiya yan sandan sunaji sukaqi rabasu.
Wajen qarfe goman safe Hassana taxo riqe da qaton basket cike da nau'o'in abinci ta kawowa sakeena tace inji mama. Sakeena dama da kwantarciyar yunwa da rashin kwanciyar hankali da kuma rashin samun abunda takeso ya Haddasa mata. Tana arba da plantain da chips yawunta ya tsinke taja kwandon ta fito da robobin ta wanko baki ta cika cikinta da soyayar plantain da chips da soyayyan kwai, ta dora da kunun gyada ta kauda kwanikan ta miqe ta kwanta, tana bacci Iya na mata fiffita don dakin da xafi kuma fankar bata bada iska sosai ta tsufa. Hassana tace tana xuwa ta fita, bata jima ba ta dawo da shirgegiyar fanka ta tsaye "OX" sabuwa qal, da kanta ta bareta ta jona iska ta cika dakin cikin yan sakanni. Sakeena ta juya ta bararraje ta gyara kwanciya iskar sabuwar fanka na ratsata, Hassana dai dubanta take da tausayi. Iya ta dunga sakawa Hassana albarka. Iya tana aikinta a tsakar gida Hassana kuma tana danne danne a laptop. Babu jimawa Barrister Adam yaxo aka kira Saddiq suka hadu suka tattauna kana suka fice a motar Hassana. Sakeena dai batasan abunda ake ba tanata biyan bashin baccin da rabonta dayi tun tana gidan Sageer cikin loosing memory.
Bata tashi ba sai bayan la'asar hakan ma Iya ce ta tasheta saboda sallah. Tayo wanka da ruwan xafi rau, tayi sallolinta. Iya ta shigo ta xauna ta qurawa Sakeena ido tace "Kai wannan yarinya Hassana Allah ya saka mata da alkhairi, dubi ayini daya har kinciko da kika samu kikayi baccin. Temakon Allah ya kan riski bawa a ko ina, mutuqar bawan yayi imani da Allah. Lokacin da Hajara takai maganarku kotu ba qaramin raxani da tashin hankali na shiga ba, amma daga jiya xuwa yanxu da muka samu masu tsaya mana, saina godewa Allah data kaimu kotu, saboda in aka xauna a gida akai shari'ar kamar yadda mukeso to wlh ko an wankeki Hajara da xuri'arta baxasu taba dena kiranki karuwa ba. Amma data kai kotu kinga yadda labarin bata sunanki ya gama duniya in shaa Allahu haka labarin wanke ki daga zargi xai game duniyar. Hankalina yanxu kwance yake sosai na fasara hango mana nasara" Sakeena murmushi kawai tayi batace komi ba, ita bataga wani alamar nasara ba koma da nasarar bata murna. Yo murnar me xatayi kata da shege aciki?
Yamma liqis Saddiq da Hassana suka shigo gidan, idonsu jajur da alama sun gaji, bata xauna ba ta miqawa Sakeena ledar burger da ice cream na qatuwar roba tai musu sallama tace sai gobe. Sakeena tanaji Saddiq nayiwa Iya bayanin guraren da suka xaxxaga, Iya ta hado masa abinci da ragowar abunda Hassana ta kawowa sakeena. Ita dai taja ledar burger (🍔) tanaci tana lakatar ice cream tana hadawa 😋. Saida ji cikin ta dam sannan ta miqawa su Iya ragowar. A daddafe tayi sallar Isha ta qara miqewa a gado ta ware sabuwar fanka ta fara bacci.
Ranar laraba ma haka Hassana taxo gidan kamar jiya da kwandon abincinta, bata xauna ba suka fice Sakeena tai wanka taci peper soup din kayan ciki da bread, Iya mamakin wannan ciki na sakeena take da bata iya tabuqa komi daga cin abinci sai bacci duk kuwa da cewa bata da son jiki.
A ranar dai saiga Zahra dasu Hadixa sun shigo gidan. Zahra taxo har daki ta gaida Iya kuma a bakinta su sakeena kejin wai an canjawa su Hajjo guri xuwa state C I D saboda taunan silili da ragowar matan sukai mata har suka fadi inda tai silar batan sakeena kuma daga qarshe ta kaita qara, jin haka yan sanda suka tasa qeyarsu duka suka miqasu state C I D. Daya tashin hankalin shine anhana belinsu ance saboda sunyi yunqurin kisa kar a bada belinsu kafin ranar xuwa kotu su aiwatar da nufinsu. Yanxu ma taxo neman Deni ne da Saddiq suxo aje can din ko xa'a badasu. Iya ta jimantawa Zahra tace "wlh kam Deni rabona da ganinsa tun shekaran jiya. Saddiq kuma sun fita da lawyern sakeena" Zahra tace "Masha Allah ai gara da aka samu lawyern, Allah ya bayyana gaskiya" ta miqe ta koma dakin Hajjo gurinsu Hadixa da duniya tai musu xafi.
Bata jima ba ta fito, taiwa Iya sallama tace xata gida saboda yara sun tafi makaranta karsu dawo bata nan. Iya tace ta gaida gida. Su Amina suka fito suna qullah daki zahra ta kallesu saroro tace "ku dana barku kwance ina kuma xakuje?" Amina tace "Binki xamuyi, bazamu xauna a gidan nan ba ba'a qaunarmu. Baba baya kulamu, Hajjo bata nan, Saddiq kuma ya hada kai da maqiyanmu" zahra ta kife Amina da mari. Tace "Ki jini da yar iskar yarinya, ba'a qaunarku ku wa kuke qauna? Hajjo itace ta jawowa kanta duk abunda ya faru da kuma xugarku, ai duk abunda take kune ke tunxurata, da kuna hanata da dole xata rage wani abun. Baba kuma dole ya dena kulaku saboda kun nuna ku yayan mace ne be isa daku ba. Wlh ku kiyayi duniya gidan wani xakuje ku matane, tarbiyyar Hajjo baxata xaunar daku a gidan aure ba. Kuma ni babu inda xaku bini ba kuje ku girgidemun nawa auren"
Ganin idon zahra yasa suka koma dan suna shayinta, tana fita suka sa qafa suka fice, a tsakar gida suka tsaya suka qaraci futsararsu da cewa sun tafi gidan Fiddausi tunda zahra ba ita kadaice yar uwarsu ba inyaso in mutum ya cika munafiki in sun dawo yasa a kashesu. Iya bata kulasuba bare sakeena dake sharar bacci.
Bincike yaci gaba kullum sai Hassana taxo sun fita da Saddiq da kuma Barrister Adam sannan tana xuwarwa da sakeena irin cimarta kullum, sakeena dai batasan inda suke xuwa ba ta maida hankali gurin bacci. Yayin da Hajjo kecan tanacin gabxa, Deni kuma baya ma gidan gaba daya kwanciyar bacci da wanka kawai ke kawoshi, su Hadixa kuma sun durfafi xuwa gidan Fiddausi su yini sur sai dare su dawo.
Ranar juma'a su Barrister suka hadu dakin Baba sunawa su Iya bayanin abunda ake ciki, wato sunyi iya yinsu ba a samu Sageer ba a katsina xuwa Lagos gashi saura kwana 3 kachal shiga kotu. Iya da Baba hankalinsu yayi mugun tashi, Barrister Adam ya kwantar musu da hankali cewar ai sun sami mafita mijin Hassana dake Babban ma'aikacine kuma me fada aji xa'a turo masa gaba daya list din ma aikantan hukumar customs dake Lagos shi kuma xai turowa Hassana aciki xasu duba Sageer daga nan kuma sai su damqoshi, koda ba'a samu kamoshi kafin ranar Monday da xa a xauna kotu ba xasu bada uxuri kotu ta sauraresu xuwa sanda xa'a kama sageer a gurfanar dashi.
Hankalin Baba da Iya ya dan kwanta amma kuma tunaninsu iri daya ne na ganin in kuma Sageer qarya yake fa shi ba jami'in hukumar customs bane? Suka rabu akan cewar mijin Hassana yau da daddare sai turawa Hassana, ita kuma da safe xataxo ta kawo su hadu su duba tunda su sukasan sageer.
A wannan dare Iya da Baba basu runtsaba sun kwana akan sallaya suna ibada yayin da sakeena ke baccinta hankali kwance dan tayi loosing hope kuma ita da sunanta ya gama baci me kuma xai dameta yanxu?
Da safe wato wayewar garin asabar suka tashi xuciya babu dadi, su Hadixa sun fice kamar yadda suka saba Deni ma haka akabar Baba da saddiq suna jiran xuwan Hassana da kuma Barrister Adam.
Iya ta tashi sakeena daga baccin da bata gajiya da yinsa ta Kai mata ruwan wanka tayi. Tana uwar daka tana shiryawa suka farajin sallamar mutane lokacin ko taran safe batayi ba. Baqin sukace da Maxa suke a waje Baba yaje ya shigo da maxan sukai masauki a dakinsa daga Iya har Baba bakinsu har kunne ganin SAGEER ne tafe da mutane.
Iya, Baba da Saddiq suka xauna aka gaisa, Sakeena na can daki tunda taji ance sageer ne da mutanensa ta miqe ta kwanta ta rasa abunda ke mata dadi.
Aka bude taro da addua Sageer ya fara magana "Iya kuyi haquri kunjini shiru tunda na tafi. Kamar yadda na fada miki aure nayi babu wanda ya sani hakan yasa da najewa da iyayena maganar na fuskanci turjiya saboda lefin da nayi musu na aure babu saninsu. Kwanana biyar a Katsina ina fuskantar hukunci daga magabatana kafin daga baya su haqura su rungumi qaddara ganin harda rabo tsakaninmu. To daga katsina kuma na tafi Lagos tattaro Hujjojin da xasu tabbatar da aurena da sakeena, kasancewar abun ya hada da harkar asibiti na karbar records din ciwonta shiyasa na jima a Lagos din, sai jiya aka kammala komai na karba muka wuce Katsina muka taho da su Ummata. Gata nan, sai abokina Maimata wanda ya sheda aurena da sakeena gashi, wannan kuma Dr sani ne shine likitan daya karbi sakeena randa tai hatsari, sai yayan Mahaifina gashi (Baffa Ado) sai kuma wakilin oganmu na office wanda shi yaxama waliyin sakeena a waccen ranar, baisamu xuwa ba saboda aiki shine ya turo Ibrahim matemakinsa ya wakilceshi."
Hassana da Barrister suka shigo a tare hannunta dauke da kwandon abincin sakeena, sukai branching a dakin Baba, suka riski abunda ke faruwa. Farincikinsu baxai misaltu ba, suka xauna akaiwa Sageer duk bayanin abunda ya faru bayan tafiyarsa har qarar da Hajjo ta shigar. Hankalinsu ya tashi Sageer ya fito da duk takaddun asibitin sakeena ya miqa musu har da receipt din xoben daya siyawa sakeena da kudin sadakinta da kuma xoben axurfar daya tsinceta dashi da abun hannu. Maitama ya miqa musu vedio din daurin auren suka sauke Hamdala tare kowa hankalinsa ya kwanta. Iya ta debo yan canjinta ta bawa Saddiq tace "maxa jeka kayimun sadaka wannan abun farin ciki haka? Allah maji roqon Bawa." Hassana ta miqe tace "Bari in kaiwa sakeena abincinta" Sageer dai
toxali kawai yakeson yi da sakeena cikin matsananciyar kishirwar ganinta yake.
Umma kuwa mahaifiyar Sageer itama so take kawai taga sakeena yarinyar data hargitsa mata Da har yayi aure bata sani ba, har cikin ranta haushin sakeena keji so take ta ganta taga meya rudi sageer haka? Iya kamar tasan abunda ke xukatan Sageer da Umma tace "Hassana turo sakeena mana ta gaida baqi ta qule daki taqi fitowa"
Acan daki ma sai da Hassana tayi da gaske sannan ta tasa sakeena gaba suka fito xuwa dakin Baba, Idon Sageer akanta baya ko qiftawa ko kuma jin kunyar mutanen dake dakin, kowa ya lura da kallon da yake bin sakeena dashi. Ta xube gaban Umma dan ita kadaice mace acikinsu, Maitama ya dan xunguri Sageer yace "ka dauke idonka akanta malam"
Ta fara gaida Umma cikin girmamawa wanda hakan yayiwa Sageer dadi ya kuma nitsewa cikin tafkin soyayyar sakeena. Umma ta amsa gaisuwar sakeena tana kallon ta, ta nemi jin haushin sakeena da takeyi ta rasa tafar daya taji yarinyar ta shiga ranta kuma ta kwanta mata, ko ita Sakeena mace sakeena ta shiga ranta balle namiji irin sageer. Bataga lefinsa ba dan ya mace a soyayyar kyakykyawa kuma sassanya sakeena. Ta shafa kanta tace "Sannu diyata, Allah ya yi miki albarka, Allah ya baki ikon cin jarrabawar da yayi miki. wannan abu daya faru gareki MUQADDARI NE Allah ya rubuta miki qaddarar aure kan aure." Sakeena ta share kwalla ta amsa adduar umma, ta matsa ta gaida ragowar mutanen ta miqe ta fita. Iya farincikin da bata taba xatoba a wannan lokacin ya xiyarceta ganin Umman Sageer nason Sakeena ta fara tunanin wani abu aranta.
Suma basu wani dade ba suka tafi masaukinsu gidan wani abokin aikin Sageer dake nan Kano, ko tsayawa su karya basuyi ba. Sakeena ta shige uwar daki ta kwanta xuciyarta babu dadi yayin da su Iya da Saddiq suka dasa hira harda Hassana cikin farin ciki. Ita dai da xuwan Sageer da rashin xuwansa duk daya a gurinta abunda kawai takeso kuma take buri ta koma gidan ya Deni sucigaba da xamansu na soyayya. Da wannan tunani tai bacci cike da mafarkin ya Deni as usual. (Dan anace sunan wata waqa 🤣)
Sai azahar Iya ta tasheta sukaci Dan waken da iya tayi ita da Hassana.
****** ***** ****** ****
Ranar Monday wato ranar shiga kotu da karsashi yan jam'iyar Sakeena suka shirya ita kuma a salube take komi saboda tasan yaune ranar da hukunci xai tabbata kodai xamanta da Deni ko kuma rabuwarsu. Hassana taxo da shiegegiyar mota xata debi su Iya da sakeena, ta tarar sakeena bata shirya ba ta daiyi wanka tana xaune. Da azama Hassana ta binciko mata wata doguwar riga ruwan makuba (marun) tasa tana fadawa sakeena wannan rigace me daraja saqar qasar Turkey ce kudinta suna da yawa. Tasata ta saka harda saka powder tayi mata nadi da dankwalin rigar irin na larabawa ta bata cover shoe ta saka ta dakko medical glasses dinta ta bata ta saka tace "Wow haka nakeson ganinki mutuniyar" taja hannun sakeena su Iya na tsaye suna jira Iya ta saki baki tace "ikon Allah yau kunga sakeena ta komamun mahaifiyarta sak, haka Aisha tayi wannan kyan lokacin tana da cikinki kuma a lokacin batafi shekarunki ba"suka fita, Iya na qara kallon sakeena, aka qulle gidan, Su Hadixa sun fice tun sassafe xuwa court.
Lokacin da sukaje kotu ta gama cika har anfara wasu shari'oin . Sageer da Deni suka xubawa sakeena ido lokaci daya tayi kyau harta gaji, Sageer har lumshe ido yake inyana kallonta, sai yanxu ya lura ta danyi rama kadan saboda rashin kwanciyar hankali amma ramar ta yimata kyau farinta ya qara fitowa saboda cikin jikinta. Deni ma idonsa akanta tar yaji wani irin mugun santa da kewarta, amma daya tuna abunda tayi harda ciki a jikinta saiya kauda soyayyar ya galla mata harara anyi sa a lokacin ta dago kanta tana kallonsa ganin ya harereta ta sunkuyar da kai. Umman sageer ta jata ta xaunarta kusa da ita. Ana gama shariar da suka tarar anayi aka kirawo tasu, yan sanda suka shigo dasu Hajjo wadanda sukayi walmukalafatu (sassabawar kamanni 🤣) jikinta baqinqirin duk wani abu ya fito kamar tau tau.
Dan sanda suka yiwa Al qalin bayanin su Hajjo da fada masa shariar da aka kirowo yanxu tana da nasaba da wannan tasu Hajjo, magatakadda ya lalubo qarar su Hajjo da aka shigar ya tashi ya karanta.
Su Hadixa harda Zahra kuka suke ganin yadda Hajjo ta koma cikin kwanakin da basufi 5 ba.
Bar Hassana da Bar Adam suka tashi suka gabatar da kansu a matsayin lauyoyi masu kare sakeena.
Babu musu su Laraba suka amsa lefinsu ganin hakanne kawai xata kwacesu, sukace kuma Hajjo ce ta basu 500 tace suje suyi hakan. Aka juya kan Hajjo tace eh gaskiyane, amma ba cewa tai su qonasu ba tsoratu kawai tace suyi.
Bar Adam ya dakko hirar da Hajjo tayi a gidajen radio wacce yayi recording da kuma kwafin Newspaper din datasa aka bubbuga labarin ya miqawa Al qali yayi bayanin duk yadda Hajjo tai wajen batawa sakeena suna kuma ya bayyana hakan da cin zarafin bil adam.
Yan jaridar da Hajjo ta gayyata farkon shariar batasan reshe xe juye da mujiya ba, harda ma sababbi sun hallara suna ta aikinsu.
Br Hassana ta tashi tayi qarin bayani, Al qali ya nemi Hajjo ta kare kanta ko kuma ta amsa tuhumar da ake mata. Ta kasa cewa komai saboda baxata iya karo da masu ilimi ba kamarsu su Barristers sannan ga qarin shedu muraran dole ta amsa lefinta.
Aka dakko speaker akasa muryar Hajjo kowa yaji qazamar hirar da tayi. Al qali ya gyara xaman glasses din idonsa bayan gama nazari yace "Bisa kwararan Hujjoji da kuma amsa lefi da kuma shedun baki, kotu tana tuhumar Hajjo da lefuka guda 3.
Na farko cin zarafin dan Adam ta hanyar bata masa suna ga wacce take qara wato surukarta sakeena, da kuma yada labarin qarya.
Na biyu. Raina kotu ma'ana magana tana gaban kotu ba'ayi hukunci ba taje tana hira da yan jaridu. Wanda wannan rainine ga famnin sharia.
Na uku. Daukar nauyin ta addanci da tunxura mutane xuwa aikata farmaki ga rayuwar dan adam.
Wannan kotu me adalci ta daure Hajara wato Hajjo na tsawon wata 9 kowanne laifi a ciki wata uku kenan ko xabin biyan tara ta dubu 50 a kowanne lefi jimallar kudi 150k amma dubu hamsin din farko sakeena xata bawa bisa hukuncin bata mata suna da tayi. Su kuma abokan aikinta kowacce xatayi xaman gidan kaso na tsawon wata daya ko xabin biyan tarar 5000 (dubu biyar kowacce su laraba qilu tajawo bau 500 ta jawo musu 5000🤣) Wannan shine hukuncin su" Hajjo ta dora hannu aka ta durqusa (Hmmm rayuwa kenan harshenka xakinka inka sakeshi saiya cinyeka)
Amina ta yanke jiki ta fadi ta fara ihu tana xagin yan sanda wai ita tahau iska, kamar yadda suka shirya ita da Hadixa da Fiddausi a gida tayi hakan dan asaki Hajjo. Mutane xasu fara yimata karatu wani kurtun dan sanda yace su kyaleta yana da maganin korar shedanu yanxu xata tashi. Ya daga wani kulki na hannunsa ya saukwa Amina shi a gadon baya, ta shanye ta juya tacigaba da haukanta tana dura masa xagi, ya Kuma dagawa iya qarfinsa ya shirga mata. Ana ukun saiga Amina a tsaye kyam tana cewa "Nice wlh babu wata iska a kaina sani su Hadixa sukai nayi haka dan a saki Hajjo"
Kotu tadau dariya gaba daya hardasu Labara da suke a tasko saida suka dara.
Aka fara shariar sakeena me maxajen aure biyu, Sageer ya fito ya fadi duk yacce akai har xuwa auren sakeena dashi ya kuma gabatar da shedunsa aka miqa records din sakeena na hospital gurin alqali harda receipt din xoben hannun sakeena na sadaki, wanda ita sai lokacinma ta kula da xoben. Hajjo tashin hankalin da take ciki be hanata bude bakiba jin har xoben 176k ne a jikin sakeena a matsayin sadaki. Dr sani ya fito yayi qarin bayani kan duk yacce akai. Maitama ma ya fito yayi, haka wakilin oga Abdulfatah wato Ibrahim. Bayan gamawa Hassana ta bude laptop dinta aka bude vedio din daurin auren sakeena kowa yagani.
Kotu ta rude da tafi da kuma yabon Sageer bisa aikin alkhairin da yayi wanda ba kowa zai iyaba a wannan xamanin aka kuma fara tsinewa Hajjo data dora qara akan xargi har tana rantsewa akan abunda bata gani ba, sannan aka shiga tausayin sakeena ana fadar rashin dacewarta da auren Deni.
Alqali ya buga guduma akai shiru ya juya ga Sageer yace "Menene dalilinka na auren mace daga ganinta kuma bakai tunanin matar aure bace sannan baka fadada binkice ba?" Sageer cikin nutsuwa yace "Na aureta ne saboda gudun fadawa halaka saboda xama ni da ita amatsayin wadanda ba muharramai ba shedan kan iya shiga tsakaninmu, Sannan na biyu likita ne yace kar a tursasa mata tuna rayuwarta ta baya harsai ta tuna dan kanta saboda yin hakan na iya baraxa ga lfyarta. Na uku kuma, a yadda naganta yarinya qarama banyi xaton matar aure bace duba da qarancin shekarunta shiyasa na aure. Allah shine shedata"
Kotu ta kuma rudewa da kalaman yabon Sageer wani dattijo fadi yake "Wannan yaro da Dattako yake da inada ragowar ya wacce batai aure ba dana aura maka"
Alqali ya nisa ya gama naxartar duk takaddun hannunsa na sakeena yace ya bada hutun awa guda kowa shima xai shiga yayi naxari. Ya tashi ya shige wani daki aciki, kowa ya fita harkarsa wasu kuma suka xauna kamarsu Sakeena kenan.
Iya bakinta har kunne ganin yadda ake wanke sakeena daga zargi. Umma ta Kalli sakeena dake satar kallon Deni shi kuma Sageer yana aikin kallon ta. Tace da Sageer "Muhammadu dan samowa Sakeena dan wani abun mana taci" ya amsa da "To umma" ya tashi da rawar jiki ya fita. Baba da Iya kuwa sai murmushin jin dadi suke ganin sakeena ta samu karbuwa sosai gurin umman Sageer, Deni duk yana jinsu kuma yana gani.
Sageer ya shigo da ledoji niqi niqi, dauke da minerals da snacks ya ajiyewa umma yace "Gashi abata" Umma ta bude tahau rabonsu ga mutanen da suka rage xaune a kotun suma sunci arxiqin sakeena, ragowar ta bawa sakeena, ta bude gwangwanin maltina ta fara sha dan karta gwale umma. Hajjo na gurinta a tsaye amma tana kallon duk abunda suke. Su Hadixa ma haka shi kuwa Deni cewa yake a ransa inama tasa uwarce haka.
Awa dayan da aka diba ta cika Alqali ya fito kotu ta kuma cika maqil.
Alqali yace "Bisa naxartar shedu da kuma xahirin abunda mukaji kuma muka gani wannan kotu me adalci tayi bincike a bisa kafa hujjoji Qur'ani, Hadisai da Sunnar ma aiki (S A W)
Ga kuma hukuncin da shari'ar musulunci ta nadana kamar haka" :
"1.Kotu tayi duba akan takaddun asibitin sakeena kuma ta yadda da ingancinsu saboda haka ta wanke Sakeena daga xargin karuwanci da surukarta tai qararta akai, sannan Hajara xata bawa Sakeena 50k saboda bata mata suna da tayi da kuma korarta daga gidan mijinta wanda silar haka tayi hatsari har qadddarar aure akan aure ta fada mata.
2. Mijin sakeena na biyu yayi kuskure sabida Ya takaita bincike akanta.
3. Ba auren wacce bata cikin hankalin ta.
4. AURE baya tabbata akan wani auren.
Don haka za tayi ISTIBRA'I domin auren ta na biyu bai inganta ba
5. Zata koma dakin mijin ta na farko idan yana da bukatar ta, ba tare da sake daura aure ba.
6. IDAN mijin farko bashi da bukatar ta , ya sawwa ke Mata.
7. Bayan an raba auren su da miji na farko , Miji na biyu yana da damar a sake daura musu aure domin wancan auren ba aure ba ne domin tana cikin alfarmar auren farko, Amma fa idan bai San farko tana da aure ba. Idan kuma Ya Sani tana da aure a halin da tayi hatsari, amma duk da haka ya kutsa ya aure ta , to aure ya haram ta tsakanin ta da miji na biyu domin yayi aure akan aure."
Kotu tai tsit kowa yana nasa naxarin da kuma yadda da hukuncin shari'a kan auren sakeena guda biyu. Sageer ya runtse ido jin aurensa ba aure bane Deni keda hurumin xama da sakeena ya tausayawa kansa da kuma xaxxafar soyayyar sakeena dake cin xuciyarsa.
Shi kuma Deni shima runtse idon yayi yana tunanin lallai shari'a sabanin hankali don so yayi a jefe Sageer saboda ya dandana masa mata har yayi mata ciki.
Yayin da sakeena wani matsanancin farin ciki ya lullubeta jin Deni ne mijinta na yanxu amma sai ta haihu shine cikar ISTIBIRA'INta.
Deni ya bude ido jajur ya kalli Al qali yace "Nikam na haqura da sakeena, nasawwaqe mata, na mata Saki daya banxan iya cigaba da xama da ita ba" Kotu ta dauki surutu na Al ajabin abunda Deni yayi wasu kuma suna cewa gara haka don Deni be dace da itaba saboda uwarsa bata qaunarta. Al qali ya buga guduma akai shiru yace "To sharia ta qare, malama sakeena mijinki ya sake ki saboda haka inkikai haihu wato istibira'inki ya cika xaki iya auren mijinki na biyu ko kuma wani daban."
Sakeena ta farfado daga doguwar suman da tayi na ido biyu, hankalinta yakai kan Deni dake shirin fita daga kotun ta bishi da gudu ta riqeshi xuciyar da idanunta a bushe irin bushewar xuciyar data hangi rasa abunda take tsananin so tace "Yaya Deni ka dubi Allah kayi haquri ka maidani dakina wlh bansan lokacin da Sageer ya aure niba. Kai nakeso ka duba darajar soyayya ka yafemun mucigaba da xama" ya juyo yana hawaye ya cire hannunta a jikinsa yayi waje ya barta durqushe tana binsa da kallon mamaki.
Idon duk jamaar kotu chaa akanta tana kukan rabuwa da autan maxa Deni, wasu na xaginta ganin wannan rashin xuciya tata, wasu kuma sunayi mata uxurin soyayya ce tasata yin duk abunda dai bata da lefi.
Sageer ya xubar da hawayen tausayin kansa da sakeena, ganin duk kansu suna cikin abu daya wato matsananciyar soyayyar wadanda basa sonsu.
Xamu hadu ranar talata in shaa Allah.
Hajia 😊
[7/31, 8:29 PM] Reine Ghana: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣1⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Tuba nake Fadeelatuwa sama Lado
Iya kallon sakeena take cikin takaici kamar ta tashi ta rufeta da duka, Baba kuma duban tausayi yake mata. Yayin da Sageer kejin kamar ya tashi yaje ya kwantar da sakeena a qirjinsa ya lallasheta yasa halshensa ya lashe mata hawayen da take, ya fada mata cewar in da duk mutanen duniya xasu qita toshi xai sota kuma xai riritata.
Yan jarida sukai kan su Hajjo da aka tasa qeyarsu dan tafiya dasu gidan kaso tambayoyi suke mata suna daukarta photo kamar yadda sukaiwa sakeena a wancan xaman. Hajjo dai babu baka sai kunne ta sunkuyar da kanta tana hango ta inda xata samo dubu dari da hamsin ko xaman gidan yari na wata tara. Su Laraba suka xage sunawa yan jarida bayanin mugun halin Hajjo da irin yacce tai asiri na raba Deni da sakeena kamar yadda Hajjon ta fadawa su Laraban lokacin ganyensu yana kore. Suka dunga barwa maxajensu da yayansu wanda suka hallaci xaman kotun sallahu a saida tumakinsu, wasu suce yarinsu na gwal, wasu kuma sutturunsu a hada kudin da sauri axo abiya tarar da kotu ta saka musu a sakesu 🤣 (wuya tallan turmi, kowa ya tuba dan wuya ba lada.)
Su Hadixa kuka suke sunaso suyi magana da Hajjo amma yan jarida sun kewayeta babu dama, Saddiq kuwa yana gefe yana kukan kasancewar Hajjo uwarsa.
Yan jarida sukayi kan Bar Hassana bayan anfice dasu Hajjo, tambayarta suke akan nasarar da suka samu, cikin nutsuwa ta dunga yimusu bayani da kalamai na ilimi ta qara wanke Sakeena tas.
Bar Adam yaje gurin da sakeena ke tsugune har yanxu tana kuka a hankali yace "Ki share hawayenki, akwai duban maxa masu qaunarki da kuma burin samun damar aurenki, Adam yana daga cikinsu, har yanxu ina kan bakana ina qaunarki babu abunda ya ragu ciki, niba Deni bane daxan kasa haquri da qaddarar da Allah ya dora miki. In kin haifi cikin jikinki ki kaiwa Sageer Dansa mukasance ma'aurata ni da ke, inma xaki taho da danki xan riqe miki, nasan yanxu bakya tsoron Bahijja. Xan dunga bibiyarki har xuwa lokacin cikar istibira'inki" ya tafi ya bar sakeena tana bin bayansa da kallo.
Hassana ta gama da yan jarida taxo ta kama hannun Sakeena ta jata suka shiga mota Baba da Iya suka shiga har Saddiq taja suka tafi. Sageer ya sauke ajiyar xuciya bayan yaga tashin motar su. Umma ta kalleshi da tausayin halin da yake ciki na azabar son maso wani, da alama Sageer tasa qaddarar itace haduwa da sakeena da kuma soyayyarta. Maitama, Dr sani da kuma Baffa Ado suma irin tunanin Umma suke.
Sunyi masauki a falon Iya sukayi jugum jugum kowa yana jimantawa wai Deni ya saki sakeena duk halarcin da tayi masa? Iya kuwa sam abun be dameta ba, xaman Deni da sakeena ya gama sure mata tuntuni kuma duk sallar da xatai saita roqawa sakeena xabin Allah akan xama da Deni ko rabuwa dashi. Haukan da sakeena tayi a kotu yafi qular da ita, agaban dubban jama'a ya ya nuna bashi da buqatarta a rayuwarsa, itama kuma a gaban duban jama'a ta nuna ita akuya ce tabi Deni tana roqonsa ya xauna da ita.
Baba ya fara magana "Ashsha! Abu beyi dadi ba, yi haquri sakeenatu banxaci haka daga Nuraddeen ba, nayi fushi dashi na daina amsa gaisuwarsa akan abunda yayi ranar dawowarki, a xatona hakan da nayi xaisa ya nemi yafiyata kuma ya haqura ya xauna dake ganin a dalilin uwarsa iftila'in aure biyu ya fada miki. Ashe duk shirmena nake Nura ya wuce xatona. Kiyi haquri nasan kinason Deni kamar yadda nakeson kasancewarki surukata don hakanne xai baki damar xama cikin xuriyata har abada, amma ba haka Allah ya so ba, yau naji inama na haihu da Hafsatu dana aura miki dan damuka haifa ni da ita." Ya share kwallah yace "Inama ina da wani Dan bayan Deni dana aura miki shi Sakeenatu"
Saddiq ya taso da axama yace "Baba ba gani ba,ka auramun Sakeena kagani na rantse maka da girman Allah xan riqeta hannu bibbiyu baxan bari ko Hajjo taci xarafinta ba balle wasu banxaye su Hadixa, niba Deni bane daxan wulaqanta matata in fifita buqatun san xuciyar Hajjo akan na iyalina, xan bawa kowa acikinsu haqqinsa." kowa kallon Saddiq yake da mamaki har wacce ake abun akanta Sakeena. Baba yayi murmushi me tarin ma'anoni yace "Abbakar saddiqu kaida Deni duk abu daya ne domin kunsha nonon Hajara saboda haka ta saka muku wannan gubar a jininku." Baba da Saddiq suka fita daki ya rage daga Iya sai Sakeena da Hassana.
Iya ta watsawa sakeena mugun kallo ta fita, ta fada jikin Hassana tace "yanxu Anty Hassana lefi ne don xuciya taso abu kuma gangar jiki ta nuna?" Hassana ta girgixa kai ta kalli sakeena cikin hikimar aikinsu tace "A'a abune me kyau sakeena xuciya taso abu kuma gangar jiki ta nuna, amma fa ga wanda yasan soyayyar gaskiya kuma yasan darajar soyayyar, nuna so ga wanda baya qaunarka da gaskiya shirme ne, kuma ba a nunaso tafar daya a xamanin nan musamman ga maxa. Ina nufin hanyar da kike nunawa Deni taki soyayyar ta xama tsohon yayi an daina hakan tun a 19 century. Babu lefi dan kinso Deni amma ki koyi boye soyayya koda anan gaba saboda gujewa fadawa tarkon yaudara. Kuma wlh Sakeena son da kikeso Deni ko rabinsa baya yi miki, da kece haka ta faru akansa nasan xaki rufa masa asiri kiyi masa uxuri ki xauna dashi. Yanxu ta Deni ta qare banaji xai kuma waiwayarki a rayuwarsa kuma hakan tamun dadi kwarai domin bai dace da ke ba ko domin uwarsa da yan iskan qannansa. Dan Allah ki danne soyayyarsa ki bawa Iya hadin kai ku fita harkar Hajjo da yayanta ki fara sabuwar rayuwa, ki tuna sakeena inso cutane haquri magani ne. Kuma akwai dubban maxa sunanan suna jiranki, ga Bar Adam, Sageer sannan yaya Ahlan shima ko yanxu kikace masa kulle xai amsa miki ga kuma sabuwar soyayyar matashi Saddiq" ta qarasa tana dariyar zolaya. Hassana bata gushe ba tana lallashin Sakeena da yimata nasiha cikin hikima har sai da taga jikin Sakeena yayi sanyi kuma kalamanta sun ratsata. Tai musu sallama ta tafi tace acikin satinnan xata koma Lagos tunda angama shariar kan ta tafi xato musu sallama. Sakeena tai mata godiya sosai Iya kuwa har bakin mota ta raka Hassana ta dawo.
Ta samu Sakeena tayi xurfi cikin tunanin rabuwa da Deni kamar a mafarki wai aurensu ya qare, ta tuna lokacin baya da suke kwana da yunwa tare, inya dawo daga kasuwa ya dorata a cinyarsa suyi ta hira ko suyi kallo ta tuno yadda yake wanke mata tufafinta ya goge. Wlh ta gwammace tayi ta xama da Deni tana kwanan yunwa da ya rabu da ita ko kuma suyi irin xamansu na kaduna da baya kulata. A fili tace "Yaya Deni ina sonka ban manta alkhairinka ba har wankin kayana kayimun." Iya dake kanta tace "Ke kam xuciyarki kare ya cinye sakeena kowa ya budi baki sai yace kinason Deni, ban tabajin wanda yace Deni na sonki ba. Wace irin xuciya ce gareki mayatacciya? Menene a jikin Deni wanda babu shi ajikin sauran maxa da kika nace masa haka? Sai anyi magana kice har wanki yayi miki, wankin banxa, menene wanki a cikin sadaukarwar soyayya? Ga wanda daga tsintarki yayi miki hidimar kudi da hidimar gabar da Deni be taba yimiki koda kwatansa ba, kuma ya rabaki da lalurar ido. Wai ku yaran yanxu me kuka dau soyayya? Meyasa kuke nacewa wadanda basusan ciwonku ba? Sakeena ki sani fa inda ake sonka anan kake mannewa ka xauna, kuma duk cikar kamalar mutum, darajarsa, addininsa, nasabarsa da kuma kyansa a inda ake sonsa wadannan abubuwa dana lissafa suke tasiri. Kuma ki sani wlh Sageeru ba ajinki bane yafi qarfinki qaddarace ta hadaku kin xauna kin mannewa wani banxa Deni jikan boka da yar bori. Abu na qarshe shine kin rabu da Deni har abada, kuma idan kika kuma yimun xancen Deni a dakin nan sai naci ubanki, xan gani in sai dashi xaki rayu, shegiyar yarinya kai marar xuciya"
Sakeena ta fashe da kuka a ganinta akan me Iya xatai mata fada akan abunda ba ita ta dorawa kanta ba balle ta yayewa kanta. Tayi fushi taqi cin abinci ta takure sallah kawai ke tashinta daga gurin, idonta yayi luhu luhu saboda kuka.
Xuwa bayan Isha Iya ta gama qulewa da abun na sakeena, ta kaiwa Baba abinci ta shigo daukar wayarta ta jiyo Sakeena tana cewa "Na shiga uku bani da kowa babu Gwaggo, babu Baba, babu Nura gashi na kuma a qarshe na kuma rasa ya Deni"
Iya ta rufe Sakeena da duka iya qarfinta tana cewa "Dan ubanki dan kinga bana dukanki, dan kin rasa Deni xaki yini kinamun kuka da qunci? Kunci ubanku ke da Denin shegiya mara xuciya wacce batasan ciwon kanta ba. Mudai ba gurinmu kikai gadon wannan soyayyar ba ta rashin xuciya, da yana sonki xai rabu dake ne tunda a gabansa akai komai kuma kotu ta tabbatar bakya hayyacinki kikai aure biyu. Ita Hajara yayanta sun goya mata baya sun bata hadin kai duk da cewar ba alkhairi take ba amma ke kinqi bani hadin kai in kwatar miki yanci? Denin qanin uwarki ne kona ubanki?"
Baba da Saddiq ne kawai a gidan sukayo dakin da gudu ceton Sakeena, Iya bata fasa dukanta ba duk maganar da Baba keyi don ta xuciya. Saddiq yace "Iya da ciki fa jikinta kike mata wannan dukan" fadar haka jikinta yayi sanyi Baba ya janyeta, Sakeena ta kwanta a gurin tana kuka da mamakin wai yau Iyace ta daketa abunda bata taba yimata ko fada ba, lallai ta qure haqurin Iya. Ta tuna bala'in da Iya ta shiga akanta har marinta akai a cikin gidan aurenta akan Sakeena. Ta auna taga sam bataiwa Iya adalci ba data xauna tana sakata bacin rai akan Deni, Denin me? saikace Denin farko da taketa fuskantar matsala akansa. Shi ya bawa uwarsa hadin kai da yan uwansa yayi musu abunda sukeso wato rabuwa da ita, amma ita ta kasa marawa tata uwar baya, Hajjo fa har gori taiwa Iya da cewa ta haifi nata Dan ko sakeena ta maganta mata tunda tace yartace.
Wannan shine tunanin da sakeena tayi har xuwa tsakiyar dare, ta miqe jikinta xafi rau kanta na ciwo taje uwar daki Iya tana bacci ta kwanta a jikinta tasa kuka. Iya itama baccin nata rabi da rabi ne saboda da halin da sakeena ciki. Ta tashi ta kunna fitilar wayarta ta dubi sakeena. Sakeena ta saki kuka tace "Iya Dan Allah ki yafemun, na tuba ke kadai nake da ita, inkakai fushi kika juyamun baya wanene xai tallafeni ni da maraicina da kuma raunina? Ko kare bani dashi dana sani daga dangin uwata dangin uba kuma" Iya ta toshewa Sakeena baki ta share mata hawaye tace "Na haqura amma sai kinyi alqawarin xaki cire Deni daga xuciyarki" da sauri Sakeena tace "Nayi miki Iya" ta shafa kan Sakeena ta dakko furar data bayar aka siyo mata saboda tasan bataci abinci ba, ta bata tasha ta bata paracetamol tasha ta kwanta kusa da Iya.
Sassafe saiga su Hadixa faran faran sun shigo, sukaje dakin Baba suka gaisheshi ya amsa musu tare da tambayar a ina suka kwana. Sukace can Bachirawa sukaje gidan kakanninsu suka fada musu abunda ake ciki saboda a hada kudin tarar karbo Hajjo. Ya jinjina kai yace "Ban baku damar kwana a waje ba duk inda yamma tayi ku dawo gida, baxan rabaku da uwarku ba ko hanaku xuwa gareta amma ayi abu na hankali" suka amsa sukayi soro dakin su Saddiq.
Shi kadai suka tarar a dakin suka tambayeshi ina Deni yace "Rabo dashi tun jiya a kotu" Hadixa ta dafe qirji tace "Tun jiya muke kiran wayarsa a kashe, dama xancen biyan kudine dan a sako Hajjo, munje Bachirawa ko dubu biyar ba'a hada ba a duk gidan. Shine mukeso kai da shi ku hada a sakota ta jigata kuma jiya da ana sakata a mota tace duk yacce xamuyi muyi a fito da ita" Saddiq ya dubi Hadixa bayan ta gama magana yace "Hadixa yanxu ni dana gama makaranta nake xaune bana aikin komai me xa a samu a gurina? Wlh ko dubu daya bani da ita balle 150k, ban ajiye ba ban bawani ajiya ba. Ban yadda banyi da Hajjo ba ta janye qarar nan amma taqi saboda kuna xugata, dan haka babu ruwana kuda kuka tayata kai qara saiku fito da ita" suka tashi suka koma daki sukai jugum jugum. Tun jiya suke yawan neman kudin fansar Hajjo amma ko 10k basu hada ba sun xaga ko ina a dangi na kusa dana nesa.
9:13 AM Umman Sageer da kuma shi kansa Sageer din sukai sallama gidan, Iya ta karbesu da fara 'a tai musu masauki a dakinta, Baba ya dan fita yanxu.
Sakeena datai kwanan yunwa jiya yau tayi tashin wuri tayi wanka Iya ta soya mata wainar fulawa tana ci. Idon sageer ita ya fara gani tana xaune a falon sanye cikin doguwar rigar atamfa tana kurbar Lipton ga faranti gabanta shaqe da wainar fulawa da manja, kallo daya tai masa ta dauke kanta, yana sanye cikin shadda ruwan qasa dogon dinki ya kafa hula sai tashin qamshi yake.
Suna xaune ana gaisawa saiga Baba ya shigo, yayi musu iso dakinsa suka shiga can. Sageer dai bai fita yana xaune yana kallon sakeena babu ko qiftawa, ta gyara xama ta takure jikinta dan a takure take da kallon da yake mata, tagaji tace "Nifa wlh natsani mutum me kallo"
Sageer yayi dariyar cin nasara sakeena yau tayi masa magana, ya xuba mata wani murmushi yace "Yi haquri ranki ya dade, ke dince ko mutum beyi niyyaba saiya kalleki" ta murguda baki.
Baba ya kwallo mata kira, ta miqe ta fice Sageer ma ya bita. Ban haquri ne dai Umma tayi akan kuskuren Sageer wanda silar hakan yajawa sakeena mutuwar aurenta. Iya ta amsa bata da babu komai haka Allah ya tsara kuma ya qaddarawa sakeena aure acikin aure kuma harda rabon ciki. Umma tace "To mufa munyi shirin komawa gida yanxu xamu dau hanya in shaa Allah kuma shima Muhammadu xai wuce Lagos saboda aikinsa. Ta dakko kudi ta ajiye tace, gashi wannan inji Muhammadu yace akula da sakeena da kuma abunda yake cikinta, kuma in shaa Allahu xamu dunga xuwa dubata"
Baba ya tari Umma yace "A a aiko Sageeru be bada komai ba xamu kula da sakeena saboda yayi mata wahala tun kafin yasan ko wacece ita mungode kwarai da kulawarku, kuma xumunci ya hadamu xamu dunga yinsa har abada" Sageer ya matso yace "Baba indai ba fushi kukai ba akan nayi silar mutuwar auren sakeena to ku karba saboda haqqina ne inkula da sakeena da abunda ke cikinta tunda Danane" jin haka Baba ya karbi kudin hannun Umma yan dubu dai dai sinqi daya (100k) sun rabu a mutunce anason barka sukai exchangin phone number saboda tuntubar juna, Sageer har yabar gidan yana waiwayar sakeena dake cikin farin cikin ficewar Sageer daga rayuwarta dan ta tsaneshi over saboda yayi silar rabuwarta da Deni, amma fa inta tuna da cikinsa jikinta sai jikinta yayi sanyi taga kuma fa ana jika.
Amina da Hadixa suka sauke labulen dakin Hajjo bayan sunga fitar su Sageer. Da sauri Amina ta doshi uwar daki, ta fara birkito kayan cikin sif din Hajjo da kuma shirgin qarqashin gadonta. Hadixa tana tambayarta lfy? Tai mata banxa, saida ta xaqulo abunda take nema wato takaddar gonar Hajjo sannan ta maida kayan ta xauna tace "Gonar Hajjo xa a siyar a biya kudin fansarta tunda mun buga bamu samu komai ba" Hadixa ta zaro ido tace "Ke kin isama? Gonar da akace sai bikina za a siyar aimun kayan alfarma tunda gidan masu kudi xanje" Amina tace "Haka kema baki isa ba wlh, dole a fito da Hajjo, saboda duk cikinku babu wanda bataiwa rana ba kuma ta mora masa sai ni, saboda haka nima yanxu naga abunda nakeso dole abiya kudin fito da ita taxo ta shiga ta fita ta samomin soyayyar SAGEER"
Hadixa ta qara waro ido tace "Sageer din Sakeena kike nufi?" Amina ta tareta tace "Karki qara hada Sageer da sakeena domin aurensu ba aure bane kuma anrabashi, dan haka sageer na Amina ne bana sakeena ba in shaa Allahu" Hadixa ta qurawa Amina ido tace "Saboda kinga yana da kudi ko? Kinji ya siyawa sakeena xoben 176k a matsayin sadaki?" Amina ta sharce kwallah tace "A a Hadixa, wlh ko Sageer bashi da ko sisi ina sonsa, soyayya nake masa ta gaskiya, xan iya komai dan na sameshi, bantaba ganin namijin da yayi dai dai da tsarin irin mijin danakeso ba sai Sageer dan haka xanyi fafutukar fito da Hajjo ta samamun soyayyarsa." (hmm illar koyawa danka mugun abu kenan, kunji fa don ta samar mata soyayyar sageer xata fito da ita badan ya dace ta fito da itan xata fito da ita ba. Allah wadan naka yayi expire)
Hadixa ta danyi gajeran tunani irin nata na mugunta tace da Amina "Ina bayanki tashi muje" suka rufo dakin suka dau hanyar neman me siyan gonar Hajjo ba tare da shawarar kowa ba ko saka namiji acikin harkar.
Suna tafe Amina na tunanin Sageer tana qissima siffarsa aranta. Handsome wanda duhun fatarsa be hana kyansa tasiri ba, matsakaici a tsawo da kuma qiba kamar yadda hakan be hana nuna kyan dirinsa bayyana ba wato me faffadan qirji da cikar gabobi, a kallon qurullar da tai masa jiya a kotu ta gane jikinsa jike yake da gargasa, ya tara sajensa har xuwa gashin bakin da maxa irinsu yan gayu ke tarawa su kuma gyara, kana kallon idon Sageer xaka gane dan soyayya ne, ma'ana yan gani kasheni a soyayya wanda insuka fara sukan iya yin komi kan abunda sukeso. Haqoransa jerarru ne kamar na Aminan (a tunaninta) kuma masu haske wadanda ke haske fuskarsa inyayi dariya, sumar kansa cike take kamar yadda gashin girarsa suka kusa hadewa saboda cikarsu. Wannan shine tunanin siffar sageer da Amina take. Yayin da Hadixa ke mata bayanin cewar indai har burinsu ya cika, ita ta auri Yusuf ita kuma Amina sageer to ai babu komai dan ansaida gonar Hajjo tasan gidaje ma sai sun saiwa Hajjo tunda duk masu kudi suke hari. Ta qara da cewa "Allah kuwa Amina kinyi dogon tunani da kuma kyan kai da kika hango sageer, in muka samu yacce mukeso ma ai hada bikinmu xa ai mu biyun" Amina tace "In shaa Allahu" a xuciyarta kuwa cewa tai "Ai ina samun nasarar auren sageer fita xanyi harkarku kuda Hajjo over acting, in lallabashi in kwantar da kai mu xauna lfy"
Basu Dade da fita ba Hassana taxo itama dai sallama taxo xata koma Lagos kamar yadda mijinta ya umarceta. Sakeena da Iya sunji babu dadi saboda sabo da sukai na yan kwanakin da kullum sai Hassana taxo musu. Iya ta hada mata kayan miya da kuma kayan kadi ta bata, Sakeena na hawaye Hassana ta ciro 5k ta bawa Sakeena tace ta riqe a hannunta, sakeena tace "Wlh ki barshi inada kudi sosai a hannuna" Hassana tace "Oh! Nafa manta yanxu Sageer ya maidaki babbar yarinya kinfi qarfin kyautata" sakeena tace "Allah ya sawaqe ai kin wuce haka" tace "To karbi" tasa hannu ta karba tayi godiya Hassana tace "Usaina tace xata aiko miki da waya, nima kuma dama inada niyyar saya miki inna nutsu, Mama kuma tace tana gaisheki tunda kinqi xuwa ita xataxo ta ganki ta kuma gaida Iya" sakeena tai murmushi tace "Xanje ne jira nake komai ya lafa"
Ta bawa Iya 5k itama, Baba ma da bayanan ta bada a ajiye masa 5k ta karbi no Iya ta tafi cikin kewar su. Tana fita tasa yara suka dunga shigo da kayan abincin data zo dasu a bayan mota, saboda kar aimata godiya ta bari saida ta fita ta aiko dasu. Ta hangi Saddiq can kan wani benci cikin maxa suna hira tausayinsa ya kamata, matashi kamar wannan daya isa ajiye iyali amma babu aikin yi sai xaman hira tayaya qasarmu xataci gaba a haka? Tayaya xamu rabu da ta'addanci domin ai tunanin mara aikinyi masaqar sharrine. Taya fitoshi da hannu, bema kula da ita ba sai wani ya gani yayi masa magana.
Yaxo ya tsaya a saitin kofar motar yace "Haj Hassana kece da safe haka?" tace "Eh wlh Saddiq antashi lfy? Yau xan wuce Lagos ne shiyasa naxo muku sallama" yace "Lfy lau, Allah sarki Allah ya kiyaye hanya mungode kwarai da temakonki" tayi murmushi tace "Kayi karatu ne Saddiq?" ya sosa kai yace "Eh nayi B ED ban jima da kammala hidimar qasa ba" ta jinjina kai matsalar nan ta xama ruwan dare graduate yanxu kamar yan Candy haka suke xaman banxa.
Tace "In shaa Allah xanwa Abbanmu magana in aka buqaci ka bada takaddunka xan tuntubeka" ta bashi katinta ta karbi no sa, ta ciro 5k shima ta bashi tace yasa recharge card. Ya dunga godiya taja ta tafi suna waving juna.
Ya shige gida cikin murnar jin qamshin samun aikin da ya farayi, yaji dadin kudin sosai ya fadawa Iya yacce sukai da nuna mata kudin data bashi.
Iya ta nuna masa kayan abincin data aiko dasu da kudin data basu suma ta qara da cewa "Wannan yarinya ta haifu Allah ya saka mata da alkhairi da wuya a wannan xamanin kasamu wanda xai temakeka don Allah ba don wata manufa ba" Sakeena tace "Ai Iya kirkin iyalan Alh Dalhatu ya wuce tunanin mutum, karamci garesu, wannan kayan abincin da kika gani haka yake bawa duk wani me aiki a qarqashinsa duk qarshen wata" haka suka dunga hirar iyalan Alh Dalhatu.
Saddiq yace "Iya akwai ruwan dumi in dan watsa a jikina in fita?" Iya tace "akwai bari inxuba maka, ina kuma xaka?" yace "Dan fita xanyi insiyo turare da dan kayan sakawa na gwanjo tunda kudi sun samu kar in kashesu a banxa" Sakeena tace "Bari inbaka turare na Sageer ranar da xan taho ya hadomun dasu garin hada kaya be sani ba, dama warinsu ya isheni banason qamshinsu yanxu" ta miqe taje ta kwaso masa turarurruka kala hudu ya karba yana dubawa yace "Kai! Sakeena kinsan kudaden turaren kuwa? Wlh mugun tsada garesu, kofa ka saka ka xauna a guri ko ka wanke kaya basa dena qamshi"
Tana dariya tace "To rabonka ne riqe" ya dunga xuba godiya yana cewa "Na xama big boy wannan ai sai nai wata biyar ina fesawa."
Sakeena ta yini kwance cikin kewar Hassana xuwa axahar Hassana taiwa Iya waya ta sauka dake jirgi tabi.
Da yamma su Amina suka dawo gwuiwa a sanyaye, sunyi yawo har sungaji basu samu me siyan gona ba. Suka fara kici kicin dora girki, Iya ta cika musu kwano da Faten doyar da tayi ta miqa musu suka amsa a kunyace suka far masa sunaci suna santin ina Iya ta samu kudi haka ta saka busashshen kifi bajaja a cikin faten? Tunda suna ganin ai sun rabata da komai. Amina tace "Hmm kudin mijinane Sageer, ba yaxo daxu ba shine ake tatsarsa saboda shegen cikin jikin sakeena. kinga fa inna aureshi haka Hajjo xata dunga yin girkin alfarma sai dai ta sanwa Iya" Hadixa tace "ai kuwa dai kedai Allah ya cika mana burinmu susha mamaki"
Da safe akaiwa Hadixa waya ansamu mai siyan gonar taxo da takaddun gonar original, amma wai sai dai su karya kudinta cikin sauri tace "Babu matsala biyan buqata ai yafi dogon buri" Ko wanka basu tsaya yiba, sukayi daqale suka rufe daki.
Baba ya tambayesu inda xasuje haka da sassafe? sukace gurin Hajjo xasu a kurmawa prison.
Mutumin da yayiwa Hadixa waya ya rakasu gurin wani azzulumin me kudi me siyan irin wadannan kadarori da matsuwa takesa a siyar. Ya karbi takaddun gonar ya tabbatar da ingancinsu kana yace su tashi suje suga gonar. Ya debesu a mota sukaje har can Gwarxo road gaban BUK new site. Ya ganta yaga girmanta yayi mata kudi 200k. Suka turje da cewa ya qara ko dubu hamsin ne. Ya watso musu takaddunsu yace su diba su tafi temaka musu xaiyi ya siya, yanxu andaina siyan gona ko fili saboda masuyin takaddun bogi, jin haka suka sallama masa gonar da akai mata kudi 500k shekaru biyu baya a 200k ba tare da shawarar kowa ba.
Ya basu kudin cash Haduxa ta xubasu a jaka suka taho, wanda yayi musu hanya yace sai sun bashi nasa kason, dole suka bashi 10k bayan dogon dauki babu dadi da sukaqi bashi ya cirewa Hadixa mayafi babu shiri suka bashi ya tafi gurin Alhajin da ya sayi gonar ya bashi nasa kason kamar yadda suka saba.
Daga nan kotu suka wuce suka biya kudin fansar Hajjo 150k. kudi ya rage saura 40k, aka hadasu da wakilin kotu xukaje prison aka kai takadda aka fito da Hajjo wacce tai fututu kamar an tonota daga rami.
Suka taho bayan ta canja kayanta daga na fursononi xuwa na gida. Tace "Ina Denin kuma ya barmu muna tafiyar qafa basai yaxo da motarsa ba ya daukemu kodan ma aikatan gurin da suka rainani susan ina da Da me kudi gashi ya biya ansakeni kuma yaxo daukata.
Daga Hadixa har Amina babu wanda ya tanka mata har sukaxo bakin titin gidan sarki suka tare Napep suka shiga, sannan sukai mata bayanin bafa Deni ne ya biya kudin fito da itaba, hasalima tun a kotu basu qara ganin Deni ba, gonarta suka siyar 200k suka biya kudin, Hadixa ta nuna mata 40k din datai ragowa a kudin gonar.
Ta dora hannu aka tana dura musu ashariyar sun cuceta sun salwantar mata da gonar da take taqama da ita. Amina ta toshe mata baki ta rage murya saboda karme Napep ya jisu tace "ai akwai babban dalilinmu nayin haka" Hadixa ta labarta mata yadda sukai da Amina da safe harda qaryar cewa Sageer ya laftowa sakeena kayan abinci jiya Iya tayi faten doya da kifi kusan katan daya aciki. Hajjo ta fara tunanin abunda suka fada mata.
Ta share yar kwallar data farayi jin sun siyar mata da gona, wani irin qarfin gwuiwa yaxo mata tace "Dole in dauki fansa akan Hafsatu da sakeena sun min toxarci da yawa a rayuwata qarshe sun kashen aure sun turani gidan kaso (halinki ya turaki dai) Kodan haka saina sama miki soyayyar sageer balle ma kuma ya dace da irin mijin da nake miki burin ki aura, nasan tunda ya biya sadakin Sakeena kusan dubu dari biyu ke naki sai dubu dari biyar tunda ke ba tsintarki yayi ba kuma ke da asalinki gaki kyakykyawa babu abunda xata gwada miki sai farar fata.
Amina tayi murmushin jin dadi tace "In shaa Allah, harna jiyo sautin maroqa ranar daurin auren suna shelar sadakina 500k. Dole a kiyayeni don ansan I'm too step a head" sukai dariya dukkansu Amina ta qara cewa "Amma wannan kudin dasu xakiyi amfani wajen farautomin xuciyar Sageer ko? Kinsan da xafi xafi akan bugi dutse" Hajjo tace "Eh amma yanxu ku fara kaini asibiti a dubani jikina ciwo yake tunda su Laraba suka dakeni ga bakina babu dadi kamar ankadamun sabulu ciki. Muna komawa sai mu tunkari maganarki" Amina cikin murna tace "Ai kuwa nai miki alqawarin ina shiga gidan sageer kyautar farko da xan miki gida xan sai miki ki xuba yan haya"
Kira ya samu Baba daga kotu yaxo da sakeena tasa hannu ta karbi kudinta. Ana sallar azahar ya dawo gida ya tasa sakeena gaba suka fita yana tunanin wanda ya biyawa Hajjo tara, sai kuma ya tuna Deni yayi xaton shiya biya kudin.
Koda su Hajjo suka dawo gida Iya kawai suka tarar, Hajjo tai wanka taci indomie din da suka dafa mata tasha maganin malaria da aka bata a asibiti ta kwanta.
Baba da sakeena suka karbo 50k a kotu kudin bata mata suna da Hajjo tayi. Tace "Baba a ina ake saida fridge?" yace "fridge xaki siya sakeenatu?" Tace "Eh da wannan kudin ba" yace "To sai dai muyi can Beruat road" suka tare Napep suka tafi. A wani shago suka tsaya inda ake sai da kayan wuta, ta xabi freezer matsakaiciya ash colour har ciko tayi akan 50k din me shagon ya tambayi sunan wanda xa a saka ajikin receipt din tace a saka Hafsatu Liman (Iya) ta biya suka tafi. Baba ya dubeta yace "Sakeenatu Hafsatu kika saiwa dama?" tace "Eh Baba naga yanxu bata saida komai kuma xaman haka babu dadi gara mu fara yar sana'ar saida ruwa da kunun aya" yace "Da kyau sakeena, aishi neman nakai dadi gareshi, me ake da xama babu sana'a?"
Suka shigo gida yara na bayansu suna kici kicin shigo da freezer, Iya tace "To ina kuma muka samu fridge?" Baba yace "Freezer ce yarki ta siyo miki da kudin data karbo a kotu yanxu" Iya ta washe baki tace "Masha Allah, sakeena memakon ki bar kudinki keda xakiyi aure nan gaba" sakeena gabanta ya fadi jin xancen auren da Iya tai mata, Baba kuma cewa yayi "Karki sace mata gwiuwa Hafsatu kisa albarka kawai aure ai da arxiqinsa yake xuwa" tace "To Allah ya saka da alkhairi Allah ya yi miki albarka" suka amsa da Amin
Su Hadixa dake jiyosu ta daki tace "Allah ya isa kudin Hajjo"
Su Iya dai sun farke kwalin freezer sun sakata a falon Iya daga gefe tayi kyau sosai ta haska dakin. Saddiq ya shigo yagani shi bema san Hajjo ta dawo ba. Ya fita sai gashi da ledojin pure water yace "Iya ga gudummawata asaka jarin ruwa" ta karba tana godiya, ita da sakeena suka jona aka cikata da ruwa aka kunna. Ya leqa dakin Hajjo ya sameta kwance tana ramuwar bacci, da mamaki yace "kai! Yaushe Hajjo ta dawo?" cikin futsara Hadixa tace "Ba'a sani ba mara xuciya ka rasa da wadanda xaka hada kai saida maqiyanmu wadanda suka ja aka daure mana uwa" Saddiq ya dauketa da mari hagu da dama ta tsanyara qara Hajjo ta tashi a firgice tayi arba da Saddiq yana tumurmusa Hadixa. Ta miqe ta shiga tsakaninsu, cikin farin ciki yace "Hajjo yaushe kika dawo? Wa ya biya miki kudin?" tace "Ubanka ne, wato ku biyu maxa da Allah ya bani baxakuban hadin kai ba ko? Na raba Deni dasu dakyar kai kuma ka koma musu ko?" Yace "Kiyi haquri Hajjo, amma gaskiya guda dayace daga qinta sai bata" ya juya ya fita.
***** **** *** **** *******
Kwana biyu da dawowar Hajjo ta murmure kuma su Laraba suka samu labarin ta dawo sukayo qungiya sukaxo suka tusata a gaba saita biyasu dubu biyar biyar dinsu da sukayo belin kansu. Su Hadixa suka tashi xasuyi musu rashin kunya suka bubbugesu sannan sukace da Hajjo kota biyasu kudinsu ko kuma su kaita qara gurin yan sanda, don babu riba baxasu lamunci faduwa ba. Dajin haka Hajjo ta fito da 40k din data ware na xuwa gurin malamai a kamawa Amina xuciyar Sageer ta raba musu su 7 suka fita suna tsinewa juna. Kudin ya rage saura 5k, Iya tana jinsu tana kuma ganinsu ko tari bataiba.
Bangaren sakeena tana rayuwarta cikin kadaici tana kewar Deni sosai amma babu hali ta nuna saboda Iya da kuma sewa kanta mutunci. Kullum Sageer yana kiran wayar Iya su gaisa ya tambayi sakeena da jikinta. Amma a kullum ya bugo yana buri yaji muryar sakeena wanda yasan hakan da matuqar wahala.
Rayuwarta ta xama salam babu abun debe kewa sai dai tayi bacci ta tashi ta dan taya Iya aikin girkinsu da ba yawa ne dashi ba, ta fara tunanin abunyi, ta fara kunun aya tana qullawa aleda naira goma goma da kuma na ashirin, hakan ya rage mata kewa tasamu abunyi. Tana ciniki, ta fara xubawa a roba na 50 naira yan xaman majalissa suna siya sosai. Abunda ranta keso shi take cire kudi a cikin wanda Sageer ya bayar ta bawa Saddiq ya siyo mata itace kaxa yau, gobe taci shawarma jibi kuma burger in kuma ta dauro a siyo mata gas meat taci ita da Iya da Baba da kuma Saddiq dan aike ta kora da kunun aya. Ta qara cikowa tayi tas da ita irin hasken ciki da cikar dakin da batayi ba a baya, Sau tari takanji inama ace tana dakin miji don ciki yasa tana buqatar namiji kusa da ita kuma duka maxajen data aura kowanne gwanine a fagen sarrafa mace hakan yasa take missing kowanne cikinsu (harda sageer? 😜)
A kwanan Hajjo na biyu da dawowa Deni ya shigo gidan, ya gaida Iya dake shara ta amsa kamar babu abunda ya faru, ya shige dakin Hajjo, lokacin yamma ce kowa yananan Babane kawai da saddiq basa gidan.
Hajjo tayi niyyar yana xuwa taci masa mutunci kamar yadda su Amina suka tsara mata saboda rashin xuwansa ya biya kudi ya karbota. Amma yanayin data ganshi ciki yasa ta fasa fadan, duk ya yamutse ya tara qasumba kamar ba Deni dan gayu ba.
Ya xauna tana binsa da kallon mamaki wai Deni ne ya koma haka akan wata banxa sakeena. Tace "Nura haka ka maida kanka akan ka rabu da sakeena ko? Wai sakeena ce autar mata ne?" Jin ta ambaci sakeena wacce yayi kwana hudu xaune guri daya a kulle dan ya mantata amma bai manta dinba yasa shi bashewa da wani irin kuka na tausayin kansa.
Daga Hajjo harsu Hadixa dake xaune gurin don jin yacce xa'a ciwa Deni mutunci babu wanda be tausaya masa ba. Ya kwantar da kansa akan cinyar Amina yana kuka jurjanjan kamar wanda aka aikowa masa iyayensa sun mutu lokaci guda jikinsu yayi sanyi ganin wannan kuka na Deni akan macen da suka dage ya rabu da ita. Cikin muryar kuka yace "Amina na kasa manta ta, nakasa cireta araina rayuwa tayimun qunci na dainajin dadin komai duk akan rabuwa da sakeena. Ki bani shawara me xanyi?" Amina wacce itama ta fada soyayyar yan kwanaki kadan ta auna yacce takeji a ranta akan sageer, ta kwatanta da yadda Deni kejin dacin rabuwa da sakeena kuma taga indai Deni ya maida sakeena dole sageer ya xama nata, tunda sakeena tayi aure. Cikin tausayi tace "Tunda kana sonta kuma ka kasa haqura da ita kamai da ta dakinta mana kucigaba da xama" kafin Deni yayi magana Hajjo ta daka mata tsawa tace "Karki qara kiramun sakeena cikin xuri'ata, Ni da hada jini da qedarai har abada, can gasu gada wai xomo yaji kidan farauta" Deni ya tashi ya goge hawayen fuskarsa ya gayyato qarfin hali dana xuciya yace "Hajjo naxo na fada miki ne na sami matar aure, wata friend ditace a facebook tun muna kaduna ta nacemun tana sona tun banasonta har muka fara waya to yanxu da hakan ta faru na yanke shawarar aurenta don ta dace sosai da irin matar da nake burin aura kuma yar gayu ce. Babanta Babban Dan kasuwa ne har China yake xuwa da Dubai kuma dan boko ne sosai, ta gama degree dinta a ABU zaria." ya ciro wayarsa yana nunawa Hajjo hotonta. Ta karba bakinta har kunne jin yar masu kudi ce, cikin xumudi tace "To ya sunan surukar tawa Deni? Kaga motoci a bayanta burjik wannan duk motocin gidansu ne?" yace "Eh a gidansu ne xuwana biyu gidansu kuma mun fahimci juna kamar yadda na fada miki tana sona sosai, sunanta Haj Surayya nagaya mata a satin nan xa'a kawo kudi" Hadixa ta rangada guda tace "Allah ya saka da alkhairi ya Deni ka sharewa Hajjo hawaye yanxu ne xakai aure" Hajjo ta maketa tace " Yimun shiru kar suji su farraqa auren (kunsan in mutum yana abu gani yake kowa haka yake) so nake sai komai ya kankama suji anyi baiko" ta juya ga Deni tace "Nura har maka taje kenan yarinyar?" yace "Eh aisu maka da Dubai a gurinsu kamar gida ne har hutu suke xuwa can. Yayan masu kudi nefa sosai kuma yan gayu shiyasa ma xan aureta" ya fito da wayarsa ya bude gallery ya bude mata hotunan Surayya wanda ta tuttura masa yana nuna mata, wasu ma a jirgi tayisu, wasu a harami, wasu kuma a mota tana tuqawa tayi selfie kai wasu ma tasa English wears ta dame jiki babu tsari sam abun. Kuma kyakykyawa ce itama fara doguwa kamar dai yadda yake mafarki tun yana saurayi.
Sun rabu da Hajjo akan xai samu Baba suyi maganar a yau xuwa gobe akai kudin.
**** ***** **** ***** ****
Kamar yadda Hajjo ta tsara haka akayi a cikin kwana uku aka kai kudin auren Deni akai baiko kuma aka saka rana sati hudu kachal wato wata daya. Abun Allah, kuma tsafi gaskiyar meshi sai gashi aikin Hajjo yaci Yusuf saurayin Hadixa suma sun kawo kudin aure 50k Baba ya saka ranar aure kamar ta Deni wata guda cif.
Ranar Hajjo tayi rawa tayi juyi tayi guda, Iya da sakeena sunsha habaici da baqar magana. Sakeena ta shige daki tai kukanta ta share hawaye dan kar Iya ta gani, wai Deni har ya manta da ita xaiyi aure? Lallai ta yadda da maganar da mutane ke yawan fada cewar Deni baya sonta ita kadai ke haukanta da sunan soyayya, kishinsa takeji kamar ya keta qirjinta ya fito. Tayi qarfin hali ta danne tacigaba da harkokinta.
Baba ma yayi murnar kawo kudin Hadixa da auran Deni, bashi da burin daya wuce ya aurar da yan matan yayansa ko sa nutsu su daina shirmen biyewa Hajjo. Yayi farinciki kwarai xai aurar da yaya biyu lokaci daya. Iya kusan sai ince tafi kowa farincikin auren Deni saboda xaibar rayuwar sakeena, kuma itama sakeena nan koda tana sonsa dole ta haqura intaga yayi aure.
Duk wannan murnar da gidan ke ciki banda Amina domin sam bata da sukuni kamar ma baqin ciki take da auran Hadixa. Ita kawai asama mata soyayyar Sageer wacce kullum qara cin xuciyarta take.
Saboda haka ta sakawa Hajjo qahon xuqa har saida Hajjo ta saida ragowar kayan masarufin da suka kwace gurin Iya ga masu kanti arha banxa ta hada ragowar canjin hannunta ta baxama gurin malamai nemowa Amina mafita.
Saddiq kuma ya qara kusanci da sakeena sosai saboda tausayinta yakeji ganin Deni ya watsar da ita xaiyi aure, wannan kusanci na Saddiq da sakeena na matuwar bata Hajjo rai kuma ta dauki aniyar nisanta su da juna da xarar ta kauda matsalar Amina. Shi dai Saddiq besan tanayi ba, yawanci yanxu ya daina fitar dare sai dai ya xauna dakin Iya susha hira da sakeena ko kuma ya tayata aikin kunun aya ko wanke mata robobin xubawa, kai har rabobin ma shike samo mata in yaga ansha ruwa a waje ko lemo saiya tsinto ya ya kawo mata. Cikinta yana motsi sosai kuma yana girma wanda hakan ke nuna yana cikin qoshin lfy.
Malamin da Hajjo taje gurinsa ko ince boka, ya bata tabbacin Amina xata samu xuciyar Sageer xai sota kamar hauka amma sai an rabashi da sakeena ta hanyar xubar da cikinsa dake jikinta don shine tsanin da xai dunga hadasu, Kuma yace a kawo masa number wayar Sageer lallai da ita xaiyi aikin.
Fin kwana uku da yin haka kuma su Hajjo na neman hanyar da xasu xubar da cikin amma sun rasa. Tuni sun tanadi maganinsu na xubar da ciki me guda uku wanda koda ciki yakai wata 5 in akasha xai xube bare na sakeena da ko uku beyi ba.
Rana ta hudu cikin sa a da yamma Iya ta shiga barka maqota, sakeena kuma ta shiga wanka, Amina tai wuf ta fada dakin Iya su Hadixa na yimata security. Ta samu maltina ta roba akan fridge wacce sakeena ta fara sha sanyi ya sanata qarasawa ta ajiye ta shiga wanka. Ta balle maganin duka ukun wanda a qa'ida daya ake sha in cikin ya riqa kuma biyu, ta jefa a robar ta girgixa ya narke ta rufe. Ta qara tarkar wata sa'ar wayar Iya nakan fridge ta barwa sakeena tanayin game ta dauka ta danna number sageer ce farko alamar yana yawan kira dan tsabar bala'i atake ta haddaceta ta fita daga dakin ta koma dakinsu, ta loda a wayarta.
Sakeena ta fito wanka ta shirya ta dauki maltinar ta ta daddake ta kwanta da wayar Iya tana game. Sam bataji dandanon magani ba aciki kasancewar maltina tanada dandanon daci kadan.
7 minutes da sha taji fitsari ya cika mata mara, taje bandaki ta kasayi su Hajjo na kallonta ta taga ta dawo ta kwanta mararta na mugun ciwo.
Iya abunda ta sani kenan, Iya ta dawo daga barka ta shigo ta sameta a kwance cikin jini male male a sume. Ta saka kururuwa ta firgita sosai da ganin jinin dake fita jikin sakeena, tana kiran a temaka mata sakeena ta mutu, su Hajjo na daki na jinta sukai tsit.
Saddiq ya shigo gidan saiwa wani abokina kunun aya ya tarar da wannan tashin hankali. Be saurari kowa ba ya sabi sakeena ya axa a kafadarsa yayi waje da gudu Iya bata tsaya kullle daki ba ta rufa masa baya.
Sun fita kofar gida suka ga Deni ya fito daga mota. Idonsa fes kan Saddiq dauke da sakeena a kafadarsa tana tsiyayar da jini. Ya tari gabansa a gigice yana tambayar lfy? meya sameta? Sakeena meya sameki haka? Saddiq ya kewayeshi ya nufi qaramin asibitin gwale LGA da ita a qafa. Deni ya saki baki sototo yanabin Saddiq da kallo wanda ke falla gudu iya qarfinsa da sakeena a kafadarsa. Ya atambayi kansa Saddiq da sakeena? To me hakan yake nufi?
Suna xuwa aka karbi sakeena ganin yadda take malalar da jini, sukayi ciki da ita. Matar data karbeta ta fito da hanxari ta miqawa Saddiq wata takadda tace "Anemo wadannan Alluran xa ai mata, tasamu miscarriage ne (Bari) kuma a samo jini cikin gaggawa za a samata, ta rasa jini da yawa, yanxu xamu duba blood grp dinta sai mu gaya muku a nemo irinsa"
Daga Iya har Saddiq babu wanda ya fito da kudi dan haka Saddiq yace "Iya xauna inje gida in takko kudi kuma in canja kaya." tace "To nagode Saddiq Dan Allah ka fadawa malam" yace "To" ya fita ya nufi gida canja kayansa da suka rine da jini.
Hajia 😊
DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/21, 12:07 PM] A A Dboy: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣2⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Direct Saddiq dakin Iya yaje ya dakko kudi a inda tai masa kwatance, har ya juyo xai fito ya tsinkayi qarar wayarta dake qasa a yashe kusa da inda jini ya bata. Kafin ya dauka harta katse yaga missed call din Sageer hudu a jere, ya danna kira akace busy, saiga kiran Sageer ya kuma shigowa. Ya daga, ko gaisawa basuyi ba Sageer yace "Na kirane in tambayi jikin sakeena kuma tun daxu nake kira ba a daga ba yace ko lfy?" Saddiq yace "Eh to, wlh sakeena ke bleeding yanxu mun kaita asibiti sukace ta samu miscarriage yanxu na dawo ne in canja kaya xamuje a nemo jini a saka mata" a gigice Sageer yace "Sakeenan tana wane asibiti yanxu?" Saddiq ya bashi amsa da "qaramin asibiti ne na Gwale Local government" Yace "Saddiq nake magana dashi ko?" yace "Eh" Sageer cikin gigita yace "Yanxu xan yiwa wani abokina dake nan Kano magana xan bashi number Iya ka riqe wayar a hannunka xai kiraka duk abunda ya dace xansashi yayi yanxu" yace "To"
Ya fito dakin Iya kenan saiga Baba ya kalli Saddiq a firgice yace "jinin meye haka jikinka?" cikin sauri yayiwa Baba bayanin abunda ake ciki. Su Hajjo na daki sun kasa kunne suna sauraro.
Ya koma daki ya canja kaya cikin sauri ya fito, Baba ma cikin sauri ya tattaro duk kudadensa dake dakin wanda yake hadawa dan bikin Hadixa dake tahowa ya xuba a aljihu da nufin nemawa sakeena lfy dasu, tunda lfy tafi komai.
Har sun fita Baba ya dawo ya kullo dakin Iya ya datse da kwado dan yasan halin Hajjo kamar yunwar cikinsa.
Su Hajjo dake jiran su fita su shiga dakin Iya suyi mata bincike su debi abunda sukeso
suka saki tsaki a tare ganin Baba ya rufe dakin sun rasa damarsu a karo na biyu, lokacin da aka fice da sakeena a gigice suka so shiga saiga Deni ya shigo ganin idonsa yasa basu shiga ba. Ya fita kenan suna shirin shiga saiga Saddiq ya dawo yanxu kuma gashi Baba ya rufe.
Cikin haushi sukaje kicin suka juye miyar da sakeena takeyi kafin su bata magani ta suma. Miyace tayi jajur sai qamshi take ga kuma naman kasuwa da qasusuwa sunji. Hajjo tace "Amina dau taliya kije ki dafa mana muci da miyar yau banxa ta fadi na huta cefane." Ta miqe taje ta dafo taliyar ta juyo musu a tray suka xuba miyar da namamomin sunaci suna santi. Amina "cewa take duk kudin mijinane shegiya ake tatsemun shi, ai wlh naso Baba yabar dakin nan a bude da shiga xanyi in yashe duk abunda nasan daga aljihun Sageer ya fito har suturar alfarma da take sakawa tana taqama dayimana kallon raini" Hajjo tana tauna qashi tace "Hmmm ai jin dadi ba qarya bane, yanxu dan Allah inkanacin wannan ya xa'ai ka tsufa? Shiyasa daga Malam har Hafsatu gashinan sunyi shar dasu sun murje balle sakeena da take yini ciye ciyen kayan otal, ranar fa ina xaune ta dunga aiken a siyo mata kayan kwadayi akanti saida ta kashe dari bakwai tana xaune a guri daya sannan naga da yamma Saddiq ya shigo mata da ledar wannan kaxar me kabeji, nasan shima kwadayine yasa yake tare dasu shege"
Amina tayi kwafa tace "Aikam ya kusa ya dawo tsaginmu ana kawo kudin aurena da Sageer, tunda duk wannan siyayyar mu xai dunga yowa. Ke kuma Hajjo gobe kije ki kaiwa malam number wayar dana kwafo tunda Allah yasa cikin ya xube kuma no tasamu. Ni badan bama wlh kiransa xanyi inji wannan sassanyar muryar tasa" Hadixa data cika baki da tsokar nama tace "To kirashi ki rusa aikin jaka, ke wlh ci da xuci gareki dole fa ki bari sai randa malam yace ki kirashi sannan xaki kira"
Acan asibiti kuma sunje anbada sample na jinin sakeena B+ ne aka auna Baba da Saddiq jinin Baba ne yayi dai dai da nata aka yimasa tests irin wanda akeyi kafin a dau jini dan tabbatar da wanda xai bayar bashi da kowace irin cuta. Ana cikin test din abokin Sageer ya kira waya, Saddiq ya fita ya taho dashi.
Yaxo aka tattara komai ya biya kudin kana ya karbi transfer. Cikin 15 minutes saiga Sakeena a wani private hospital me tsadar gaske da kuma kulawa. Suna xuwa suka karbeta aka shiga da ita akabar su Iya Baba kuma yaje akaja jininsa leda daya shima aka bashi gado da wasu lemuka yasha akace ya huta.
Sun dade a dakin likitar mace ce akan sakeena sai nurses, kimanin 2 hrs suka fito anwa sakeena duk abunda ya dace har wankin ciki in case of akawai wani bangaren cikin da bai fita ba. Suka canja mata kaya xuwa riga da wando blue na asibitin aka daura mata jinin Baba tare da alluran bacci suka barta suka rufo dakin. Sunwa su Iya bayanin cewa, an tsaida xubar jinin kuma anmata wankin ciki da allurar bacci wacce xata iya daukanta 46 hrs tanayi saboda haka a kyaleta ta huta kar ayi hayaniya tana bacci me nauyi.
Sunkai godiya sosai Iya ta buqaci xuwa gida danta shiryo, likitan tace, babu komi tana qarqashin kulawarmu kuje ki kintsa a nutse.
Baba daya danyi bacci ya tashi shima ya fito suka tari Napep suka tafi, Iya dai sai santin asibitin take cewa take "Yanxu Saddiqu duk girman gurin nan da tsaruwarsa asibiti ne haka kamar hotel? Kaga dakin kuwa harda fa fridge da su TV din bango da AC? Kai masu kudi dai sai abarsu yanxu kaida kaje neman lfy ina ruwanka da wani jin dadi? koda yake kuma ai yafi kulawa gashi cikin qanqanin lokaci sun mata komi har wankin ciki wanda dana gwamnati ne saika kwana ka yini kana kai kawo ba ai maka ba" Saddiq yace "Yawwa yanxu kika dawo hanya, ai Iya komai na masu kudi dabanne a qasar nan har lfy, shiyasa yanxu kowa ya dage yakeson yayi arxiqi kodan yafi qarfin wulaqanci, marasa hankalin cikinmu kuma suke neman arxiqin ta kowanne irin hali wato yaki halak yaki haram."
Lokacin da sukaje gida har ankira magrib, Iya ta gyara dakinta inda jini ya bata ta tsaftace shi, taje kicin don ta dora shinkafa suci ita dasu Baba tunda tasan sakeena tayi miya, ta tarar babu miya sai tukunyar da aka cika da bawon gyada aka rufe mata, ko ba a fada ba tasan wanda xaiyi hakan. Ta kunna rusho ta dora ruwan xafi sukai wanka ita da saddiq da Baba sukai sallar magrib da isha. Tana tunanin abunda xata dafa me sauri saboda komawa asibiti saiga Abokin Sageer ya turo sallama da saddiq, ya fita sai gashi da ledoji niqi niqi wai yaje asibiti ne ya tarar sun taho shine Sageer ya masa kwatancen gidan yace ya kawo, kuma idan Iya ta shirya yana jiranta zai maidata asibitin.
Suka bude ledojin daya kayan shayi ne rankatakaf har da wanda basu sani ba, daya ledar kuma abinci ne take away na tuwon shinkafa da sakwara sai su farfesun nama da kaji gasassau. Abincin ko mutum goma xasu iyaci balle su uku.
Iya tai hamdala tace "Sageeru kenan sarkin hidima dan ruwan mutunci" ta xubawa Baba ta miqa masa ta xubawa Saddiq ma, itama taja taci abunda xata iya, sukai nak ta jona ruwan tsafi a kettle ta cika sabon tea flask din sakeena wanda aka dawo dashi daga Kaduna. Sukaci kajin suka ture, abunda taga xai ajiyu a ciki tasa a freezer ragowar kuma ta bawa Saddiq tace ya miqawa su Hajjo. Ya danso yayi turniya tace "Nifa ba gaba nake dasu ba, kuma ko babu komai dole suna da haqqin maqotaka dani dan haka babu ruwanka kayi abunda na sakaka." ya karba yaje ya kai musu, da sauri Hajjo ta fusge ledar dama tunda aka shigo dasu take leqe. Ta bude suka kewaye suka faraci kamar basu taba cin abinci ba.
Iya ta debo kayan sakeena da nata kayan sukaiwa Baba sallama suka shiga motar abokin sageer ya suka tafi.
Suna tafiya Iya na saka masa albarka yace "Haj ai duk sageer ne ya turo kudi ai muku ni babu ko sisi na kuma shima yana tafe inya samu sauqin aiki a office" Iya tace "Duk da haka dannan inyayi hidimar kudi ai kai kuma kayi ta gaba ko?" yace "Hmm Hajiya ai dan anyiwa Sageer haka ba wani abu bane, tare mukai aiki da shi a Imo state kafin ayi mana canjin gurin aiki shi ya koma Lagos ni kuma Kano, mutumin kirki ne sosai inda ni na nemi taimakonsa nasan bayan yayi da gabarsa sai yayi da aljihunsa."
Ya kaisu asibiti ya tayasu shiga da kayan cikin dakin da sakeena ke kwance ita kadai, harda ruwan roba da maltina ya shigo dasu yayi musu sallama yace sai da safe xe dawo duba jikin. Suka tarar har jinin ya qare an daura mata ruwa. Sadduq ya kwanta a 3 sitter, Iya kuma tasa bargo a qasa ta kwanta. Tace da Saddiq kashe mana wannan abun sanyin, ina asanin mutum ya kwanta haka sanyi nata huda masa bargo, ni banga wani abun burgewa a AC ba." Saddiq yana dariya ya rage sanyin AC ya miqe kashe fitila ya kwanta.
Su Hajjo suna tsaka da brush da kaji suna santi lamarin daya qara musu kwarin gwiuwar fafatukar farautowa Amina xuciyar Sageer ta kowane irin hali saiga Deni. Shidinma yunwa yakeji ya kasa samun kwanciyar hankalin shan koda ruwane tunda yaga halin da sakeena ke ciki, sai yanxu daya bisu motarsu baya yaga asibitin har dakin kuma ya hangi sakeena daure da drip ta kofa lokacin da abonkin Sageer ke riqe da kofar dakin yana musu sallama sannan yaji hankalinsa ya kwanta ya juyo gida, amma fa ya firgita kwarai da sabuwar alaqar Saddiq da sakeena har xasu kwana daki daya dashi a asibiti, sauqinta ma da Iya.
Ya xauna yace "Abun dadi kuka samu haka?" Amina ta dakko plates Hajjo ta saka masa sakwara da miyar ganye dayan kuma ta xuma masa kaji da kayan ciki. Yasa cokali ya faraci a xatonsa saurayin Hadixa ne ya kawo mata dan yaga kayan da yawa.
Hajjo tana sakace naman haqorinta tace "Hmm! Allah kai mana arxiqi tsiya taji kunya, shiyasa yarinyar nan tai tas da ita, Allah ne yasan dadin da yake bata acan Lagos din shiyasa ta xo mana kamar Baturiya" Deni ya dago a firgice yace "Wace yarinyar kenan?" cikin rashin lura da halin daya shiga tace "Sakeena mana, ai Sageeru ne ya aiko da wadannan kayan a kawo mata sukaci suka rage suka bamu" ya tashi ya fita da gudu ya saka hannunsa a maqogwaro yayo aman abincin daya faraci tas, ya kuskure baki ya fice waje kan dakali ya xauna. Yana tunanin kenan sageer ne ya canjawa sakeena wancan asibitin me tsada? Shi a xatonsa iyalan Alh Dalhatu ne. Tab da sauran rina a kaba, kenan fa yana sonta har yanxu? Ga kuma Saddiq shima yaga xaqewarsa tayi yawa. To wai sakeena ita kadaice mace ne da idon kowanne namiji ke kanta? Me take dashi na musamman data ke jan hankalin maxa dashi? Yasan dai akwai dubban mata a kusa da nesa da suka damata kuma suka shanye a kyau, to danme maxa ke binta haka? Ya rasa yadda xaiyi ya fidda sakeena a ransa, ta tsaya mai kyam gashi dai shirin aurensa ake da Surayya wacce yake ganin tayi dai dai da tsarinsa amma kuma sakeena tana cikin ransa da ita yake kwana yake tashi. Barin xuciyaraa yace "masa dandai kuna gida daya ne, da xarar kayi aure ka tare a gidanka ka fara amarci da matarka yar gayu xaka mantata" ya yadda da hakan ya ciro wayarsa ya kira Surayya suka fara hira.
Hajjo da Hadixa suka kalli juna jin kakarin aman Deni. Hadixa tace "Tab aiki ya sameki Hajjo bakiga ta xama Ya Deni fa wlh har yanxu yana son sakeena" Amina batace komai ba sai dariya da tayi dan abun yayi mata dadi, Sakeena da Deni, ita kuma da Sageer period.
******* ****** ******** **
Sakeena sai da tayi kwana biyu tana bacci, ranar na biyun da asuba ta farka da salati a bakinta ta shafo cikinta da hannu tace "Ina cikina?" Iya dake sallah ta sallame taxo ta riqeta tace "sannu sakeena bari kikayi xuwa nayi nasame ki a sume" tace "Maltina kawai nasha sainaji fitsari naje nakasayi naji marata na ciwo" Saddiq yayi sallama yaje ya kirawo nurse suka shigo tare. Ta xarewa sakeena drip din, tace "xan shiga toilet" ta kamata suka shiga tanacewa da Iya "Hajiya kiyi xamanki xan mata komi."
Ta shiga tayi wanka da brush, nurse din ta kamota suka fito. Saddiq dake xaune ya tashi ya fita ya basu guri donta shirya. Nurse din ce ta taimaka mata ta kintsa tasa doguwar rigar cotton material black nd orange, nurse ta gyara gadon ta hau ta kwanta jikinta duk ciwo yake batasan bacci ya dauketaba ma. Iya ta iddar da sallah tace "Sakeena tashi daga baccin nan haka kici abinci, mutum ya kwana biyu sur yana bacci besa ko kwayar hatsi a cikinsa" Nurse tace "Kyaleta Hajiya tayi ya isheta allurar da akai matace kuma bata da yunwa a jikinta saboda ruwan da ake qara mata"
Bata farka ba sai kusan 11 na safe. Tana bude idonta Sageer ta fara gani a tsaye kanta cikin suit baqaqe da alama be dade da sauka ba. Ya hasketa da murmushi tai masa kyau sosai ta rame sai farinta daya qaru saboda jinin data xubar, material din jikinta ya qara haska farar fatarta, ta runtse ido bataji dadin ganinsa ba, itadai taqi jinin Sageer tunda yayi sanadin data rasa Deni. Idonta a rufe tace "Meya kawoka? Waya gayyato ka? Koban fada ba kasan mun rabu cikin qaddarar daya hadamu ya xube saboda haka ka shafamun lfy ka fice daga rayuwata" Salatin da Iya ta saka yasa Sakeena yin shiru, idonta ya rufe batasan Iya da Saddiq na dakin ba. Iya tace "Yanxu Sakeena Sageerun kikewa wannan futsarar? Yaushe kika xama marar kunya bansani ba?" Sageer babu alamar yaji haushi a fuskarsa yace "Yi haquri Iya a cikin ciwo dake" Sakeena ta kalleshi ta murguda baki.
Ta yunqura xata tashi xaune, bayanta ya riqe ta kasa, Sageer ya yunqura xai dagata cikin tsabar futsara tace "Wlh inka tabani Allah ya isa" ya janye hannunsa da sauri. Ta kalli Saddiq dake xaune kafin ma tai magana yaxo ya dagata xaune ya jingina mata filo a bayanta. Ya hada mata tea ya fara bata da cokali tana sha. Sageer ya koma kan kujera jikinsa a mugun sanyaye ko ba'a fada ba yasan Saddiq son Sakeena yake yayin da sakeenan bata lura ba ta daukeshi kamar dan uwanta ciki daya, shi kuma gashi cikin azabar soyayyarta wanda baiga ma fuska gurinta ba balle ya amayar mata ya samu sauqi, kullum da soyayyarta yake kwana yake kuma wayar gari, Maitama haushinsa yakeji akan hakan.
Yananan xaune gurin har ta gama shan tea din Saddiq ya xauna gefen gadon suna hira, shi kuma Iya tana bashi labarin yadda ta dawo daga barka ta samu sakeena kwance a sume.
Hankalin Sageer be gama tashi ba sai da yamma tayi ya dawo asibiti ya tarar da Bar Adam yaxo duba sakeena da kayan dubiya cikin ledoji yana xaune kan kujera a gabanta suna hira yayin da Iya ke waje a xaune. Kishi ya turnuqe Sageer ya kasa dannewa ya hade fuska ganin sakeena ko mayafi babu jikinta gashi rigar jikinta ta matseta daga qirji. Adam ya miqa masa hannu ya share bai bashi ba ya daga masa hannu kawai, Bar Adam yayi dariya cike da duniyanci ya harbo jirgin Sageer yacigaba da hirarsa da sakeena yana bata wani extra ordinary caring. Koda ya tashi tafiya cewa yayi "Ni xan wuce honey sai jibi xan dawo me xan taho miki dashi?" tayi murmushi kawai tana daga masa hannu.
******** ******* *********
Satin ta daya a asibiti aka sallameta ta warke tayi tas da ita, kuma har xuwa wannan lokacin Sageer yana Kano wanda sakeena ta gundura da ganinsa kamar a kanta yake ta matsu ya tafi.
Suna dawowa Iya ta dora qatuwar tukunyar wanka acewar sakeena ta danyace dole ai mata wanka koda na sati biyu ne. Ranar da suka dawo da yamma aka fara wankan sakeena ta tsorata sosai gani take ruwan xai qonata. Amma tayi mamakin da taji ruwan babu xafi yacce take xatonsa. Akai aka gama Iya ta bata xuma a kwalba me yaji tasha cokali biyu. Ranar tayi bacci me dadi duk ciwon jikin da take dana baya ta nemeshi ta rasa. Da asuba Iya ta kuma yimata wankan da towel kamar jiya, sai tafi jin dadin na asuba saboda an danyi ruwa tsakar dare garin da sanyi. Tana fitowa tasha xuma ta shirya ta kwanta.
Batasan iya tsawon lokacin data dauka tana bacci ba taji Iya na tashinta taxo anyi baqo. Ta wanke fuskarta ta nufi dakin Baba inda tajiyo muryar Iya. Taja tsaki a xuciyarta data tarar da sageer ne, tanemi guri ta xauna darajar su Baba dake gurin ta gaisheshi ya amsa yana tambayar jikinta. Yace "Baba jamb ce na saiwa Sakeena, kuma dama tunda Iya ta bani lbrin sakeena da burinta na karatu nayi alqawarin daukar nauyin karatunta amma saina bari saita haihu to kuma Allah yayi Dan baxai taka qasa ba shine yanxu na siya mata gashinan saiki cike a mayar dan ankusa rufewa. Kuma ga waya na kawo miki saboda karatun yanxu dole sai da waya, ya dora kudi akan kwalin wayar yace kisa recharge card" Sakeena duk da bata ko san ganin sageer saida taji wani irin sanyi a ranta daya dauki nauyin karatun ta wanda ta fiddaran samun hakan. Iya da Baba kuwa sun kasa magana saboda mamakin halin sageer. Sakeena tayi godiya kamar xata ari halshe.
Ta kwashe kwalin wayar da JAMB dinta tai dakin Iya, tanaji Iya na cewa tunda tafiya xaiyi saiya tsaya yaci abinci. Ta kaimasa dakin Baba yaci alkubus da stew sosai ya gama ya fito wanke hannu, Amina na jikin window tana leqensa yayin da shi kuma yake leqen sakeena, su Hajjo da Hadixa sun fita tun duku duku. Sukai sallama dasu Baba ya rakashi har qofar gida yana qara yimasa godiya.
Yana tafe yana tunanin sakeena da kuma tunanin yanxu shikenan da gaske sun rabu? Amina wacce ta rigashi fitowa tasha gabansa, ya tsaya yana dubanta da kuma tunanin inda yasan fuskarta. Ta tsuguna har qasa ta gaisheshi cikin magagin sonsa, ya amsa ba tare daya tuna inda yasan face dinta ba, ta karbi jakarsa ta goyo har tana hadawa da hannunsa tace "Kawo in riqe maka in rakaka tasha" yace "A a taxi xan hau ta kaini airport jirgi xanbi" tayi murmushi tace "Baka ganeni ba ko?" a taqaice yace "Gaskiya kam" tace "Amina sunana a gidan su Sakeena nake ni yar gidance nice auta" jin haka ya hade rai, sai yanxu ya tunata ashe wannan yar iskar yarinyar ce wadda tai aljanun qarya a kotu, wadanda su da uwarsu suka tsani sakeenan sa suka sata a gaba.
Ya tsaidata ya ciro kudi ya irga 10k ya bata yace "Ki koma gida haka nagode kar a nemeki" ta washe baki ta karbi kudin tayi godiya tace "Bari in baka number ta" yace "Bani da buqata" bai jira cewarta ba ya tare Napep ya shiga. Amina ta buga tsalle kamar ta manta a waje take, ta shinshina kudin da suke qamshin turaren Sageer ta lumshe ido ta kuma nutso a kogin sonsa ta nufi gida cikin wani irin farinciki.
Sakeena dai yinin yau babu bacci ko aikin kunun aya, Saddiq na tashi daga bacci ta tasashi gaba ya hada mata wayarta Tecno wacce yace sabuwar xuwa ce ko a unguwar mutum biyu keda irinta sai ita ta uku, suka saka layunkan da sageer ya hado dasu MTN da 9mobile kuma duk da kudi a ciki da yawa yayi mata sub, Saddiq ya tuttura mata applications da games ya bude mata watsup din da taketa buri da facebook. Yace ta bari tayi caji sai ta qara kunnata, da kyar ta yadda ta sakata caji don ta matsu ta fara watsup (ina ruwan otondo😄) Suka fara cike jamb form, sai dai gurin saka jami'ar da mutum keso Sageer ya cike sunan wasu universities wanda ko Saddiq be sansu ba balle sakeena. Ta xabi course suka gama Saddiq yace inxai fita xai kai mata Rumfa college yayi submitting.
Ta dakko wayar ba tare data cika ba tace ya nuna mata yadda ake chatting din, yana dariya yana koya mata, ta dakko numbers din qawayenta na skull Saddiq ya mata serving wadanda suke chatting aciki sunansu ya fito, saiga number din Anty Bilki a cikin wayar da alama Sageer ne ya saka har datasa number din. Tai mata magana tace sakeena ce, ai saiga Bilki ta kirata suka sha hirar yaushe gamo. Bilki ta bada number din sakeena aka sakata a grps. Yinin ranar dai yini yai akan waya abunda bata gane ba ta kira Saddiq ya nuna mata. Da yamma bayan angama wanka hartayi tsugunan da Iya kesawa tayi akan garwashin wuta da wani turare saiga umman sageer ta kira Iya a waya, suka dade suna hirar barewar cikin sakeena kafin ta buqaci abata sakeena tayi mata sannu da jiki tace kuma xataxo biki kano watan gobe xata biyo ta dubata.
Da yamman dai su Hajjo suka dawo, Amina ta taresu da xumudi da labarin qarya wai ta raka Sageer har airport kuma sunyi xance harya bata dubu goma ta nuna musu kudin, suka qule daki suka qaraci murnarsu Hajjo ta jinjina kyautar 10k a lokaci daya ta fitowa da Amina saqonta na gurin malam turaren hayaqi ne xata dungayi har tsawon kwana 41 kamar ibada 🤔 kuma karta sake ta tayiwa sageer magana koda ta wayane sai adadin kwanakin gama turaren sun cika. Ta karba da kwarin gwuiwa duk da tana hango wahalar yin 41 dayx ba tare da koda jin muryar sageer ba wanda sonsa ke azalzalarta.
Sakeena dai kusan kwanatai akan waya har ta fara karatun novels din da Anty Bilki ta tuttura mata, da safe bata koma bacci ba, tana gama karatun qur ani da kuma na littafan addinin da Iya ke koya mata da asuba ta kama aikinta na sharar daki da gyarawa ta taya Iya dan abunda tasata ta debo wankinsu xatai Iya ta hanata tace ta barshi akai wankau jego take karta shiga ruwa. Ana gama wankan jego ta kimtsa ta dau waya ta fara chatting. Sageer da bewani damu da harkar social media ba tun jiya yake online yana kallon sakeena itama online duk da be mata magana ba itama kuma batai masa ba amma ganinta online kawai ya isheshi farin ciki.
Yauma dai kamar jiya ta yini chatting da kuma game din "Word cookies" wacce Sadddiq ya koya mata Iya na yimata fadan idonta ta dakko glasses dinta tasa tace "Kinga nasa glasses ba komi da xai faru" koda Deni ya tashi bacci yaxo giftawa ta dakin Iya xai shiga toilet ya hangi Saddiq da sakeena xaune kusa da juna suna duba waya suna dariya. Baqin ciki da wani irin kishi ya qulle masa xuciya ya quduri aniyar daukar mataki akansu.
Da yamma bayan angama wankan jego tana xaune tana yankawa Iya kubewa a kujerar tsakar gida tana sauri ta gama taje tadau wayarta taci gaba da game dinta na word cookies ta wuce inda Saddiq ya batta kamar yadda ta cika masa baki kan ya fita.
Taji anshigo gidan lokacin babu kowa a tsakar gida sai ita, a xatonta Saddiq ne tana cigaba da yanka kubewar tace "Saddiq albishirinka? Naje Banana level 9" jitayi kawai an chafke mata maqogwaro an hadata da bango ana neman kaita lahira.
Ta waro idonta ta cikin medical glasses dinta taga Deni ne ya shaqeta idanunsa jawur ya fara magana "Ni xaki yaudara? Wato kin cuci banxa ko? Shin sakeena meyasa na kasa cireki a xuciyata? Meyasa da kikai aure akan aurena a Lagos da kika dawo hayyacinki baki xubar da cikin jikinki kin dawo mun haka ki buyemun abunda ya faru mucigaba da xama? Meyasa kike axabtar da xuciyata?" Dakyar sakeena ta kwallah qara tace "Iya xai kasheni"
A tare Iya da su Hajjo suka fito tsakar gida sukayi arba da Deni shaqe da sakeena tana qoqarin banbare hannunsa daga wuyanta ta kasa. Iya cikin daga murya tace "Nura cika mata yuwa" Hajjo kuma cewa tai "Deni meya gama ka da ita kai da xakai aure kwanaki kadan masu xuwa?" Babu wacce ya kula a cikinsu yacigaba da yiwa sakeena maganganu. Iya dataga yana neman kai sakeena lahira ta dakko bokitin qarfe ta daga ta kwantara masa a baya tace "Cikata dan ubanka babu abunda ya hadaka da ita yanxu, inka manta in tuna maka ka saketa kuma ta gama iddarka, inamaka albishir cewar kai da sakeena har abada domin ta gama auren wanda besan darajarta ba kuma riqaqqen mayaudari irinka" ya cika sakeena badan xafin kwala masa bokitin da Iya tayi ba sai dan xafin maganarta ta cewa shi da sakeena har abada kuma shidin yaudarar sakeena yake.
Sakeena dai tunda ta samu ya cikata tai bayan Iya tana haki cikin tsoron Deni. Deni ya kalli Iya yace "Yanxu Iya nine ke yaudarar sakeena? Meyasa kowa ya budi baki yake cewa ba sonta nake ba yaudararta nake? Meyasa babu wanda yake duba girman lefin data yimun nayin aure yayin da ni kuma nake xaman jiranta? Meyasa data dawo hayyacinta bata nemi saki gurin wancen tsinannan ba ta xubar da cikinsa ta dawomun a sakeena matata muncigaba da xama?" Iya tana nunashi cikin bacin rai tace "Sageer ba tsinanne bane don yafita qaunar sakeena ko aranar daya fara ganinta a rayuwarsa sai da yayi mata abunda a gaba daya xamanka da ita na fin shekara bakai mata ba saboda haka wlh ka rabu da yata ko kuma nayi qararka kotu shege butulu me mance alkhairi"
Hajjo itama ta harxuqo cikin takaici abunda Deni yayi da kuma xafin maganganun Iya taja Deni itama ta turashi bayanta kamar yadda sakeena ke bayan Iya tace "Ya isheki haka Hafsatu karki qara yiwa Dana baki akan wata banxa sakeena wacce bata da cikakken asali, wannan bala'i da masifa ya isheni akan wannan yarinyar, muna xamanmu lfy kikaje kika dakko mana riqon wannan annobar ta hargitsa mana gida. Tunda sakeena taxo gidannan xaman lfy yayi qaura, ta hargitsamun xaman lfy, ta kashemun aurena, ta silarta na rasa kadarata(gona) da nake taqama da ita sannan ta rabani da xaratan yayana maxa guda biyu da nake tsanin so kuma nake ji dasu sannan na dora duk wani buri nawa akansu" Hadixa ta dafe goshi (🤦🏽♀)) jin Hajjo ta fadi matuwar aurenta da suketa boyewa.
Iya tace "Da mutuwar aurenki da kuma rasa kadararki har xuwa kan rabuwa da yayanki duk babu ruwan sakeena aciki mugun halinki da baqar aniyarki ce ta janyo miki dan dai ke dabbace shiyasa baki ganeba, mugunta ai futsarin fako ce. Sannan karki qara kiramun yata da annoba domin sakeena xuwanta gidannan alkhairi ne daga kan mijinki har xuwa kanki da yayanki babu wanda bataiwa rana ba har aikin da Deni ya samu kike taqama dashi kuma kika rabashi da sakeena saboda aikin ai itace silar sama masa aikin, saboda haka Hajara kece annobar gidannnan ba sakeena ba" Haka dai kowacce ta shigarwa danta fadan ya koma nasu suka cigaba da amayar da abunda ke cikinsu yayin da Deni da sakeena kowanne ke bayan uwarsa a labe.
Deni ya fito daga bayan Hajjo, be wani damu da kukan da Hajjon keyi ba ya tsaya gaban Iya idonsa jawur yana nuna sakeena yace "Saddiq ko? Shine next target dinki ko mayaudariya? To wlh kodai ki samawa kanki lafiya kiyi cutting relationship dinku ko kuma in kashe shi akanki, na shirya tsaf dan fara xubar da jini akanki" ya juya ya fice yabar Hajjo tana ihu da salati a hade.
Iya ta juya saiga Baba a tsaye yana kallonsu da sauri ta nufeshi tace "Yawwa malam wlh kaiwa danka tsakani da sakeena a gidannan ko kuma ayi babban tashin hankali" ya dubeta da takaici yace "Akwai tashin hankalin daya wuce wanda kukai yanxu Hafsatu? Kuntara yayanku kuna hauka a gabansu maqota na jinku kun taunamun asiri kun taunawa kanku, kuma harke da nake yabonki?" Jikinta yayi sanyi ya kewayeta ya wuce daki.
Deni ya dauki mota ya fafareta ya bata wuta ya dunga sharara gudu a titi shi kansa besan inda xashi ba tunanin yake me xurfi wai shin da gaskene abunda mutane da abonkansa ke yawan fada na cewa yaudarar sakeena yake? Kowa ya bude baki abunda yake fada kenan, yawancin abokansa na cikin unguwa sun daina kulashi tunda ya saketa acewarsu beyi hallaciba yadda tasha wuya dashi kafin yayi arxiqi yaxo yayi arxiqin ta silarta sannan kuma Hajjo ta hanata jin dadi shi kuma ya saketa bayan yar wata qaddara ta afka mata. Hatta wasu abokansa na gun aiki wadanda sukaji tarihin soyayyarsa da sakeena sun fita harkarsa. Tambayar kansa yake wai da gaske yaudararta yake ko kuma mutanene suka fahimceshi ba dai dai ba? Wlh shi harga Allah son sakeena yake da wani irin matsanancin kishinta duk da lokacin daya aureta batayi daidai da tsarinsa ba amma kuma ya kasa rejecting dinta, sai yanxu data xama irin macen da yakeso me tsafta da kyale kyale sai Sageer ya fado rayuwarsu duk da ya temaki sakeena yayi mata abunda be taba yimata ba shi Denin amma kuma ta silarsa aurensu ya qare. Haka ya dunga tunani yana driving babu gurin xuwa.
****** ****** ***** *****
Saura sati biyu biki Deni ya kawo kayan lefe daya hada a gidan abokinsa akwati biyar da kit shaqe da kaya donsu gani a kuma kai gidansu Surayya. Suka baje kaya ana gani Hajjo ta gayyato tsirarun qawayenta da suka rage na cikin unguwar wadanda suke kulata aka kuma kira dangi aka yini ana ganin kaya da kuma habaici da yaba bajintar da Deni yayi duk da ba haka taso ba so tayi ya bata kudin hado kayan tayi cuwa cuwarta aciki ta samu kayan fitar biki. Ba'a gayyaci Iya ba kuma itama ko an gayyaceta baxataje gani ba saboda tunda akai fadan Deni da sakeena suka fara xaman gaba.
Deni da Baba sunso a bawa maxa sukai lefen amma Hajjo ta kafe tace sai mata don a qara gano mata gidansu Surayya kuma su samo tukuici. Ta hada gayyar mata da dangi da kuma yayanta mata kaf dan tsabar qauyanci aka tafi rijiyar xaki gidansu Surayya.
Basu wani dade ba sosai ba sai gasu sun dawo jiki a sanyaye suka baje xancen da suke tafe dashi a tsakar gida duk da kwabarsu da Hajjo keyi suyi shiru su shigo daki. Yan kai lefe dai sunje kuma sunsamu gidan su Surayya makeke fiye da yadda Hajjo ke xato amma koda aka gansu sai aka canja fuska aka dunga fesa fresheners wai sun cika falon babu iska sannan kuma aka raina lefen da suka kai a gaban idonsu aka dunga saka masu aiki suna daga kowacce atamfa anai mata kudi a wulaqance. Aka gama wata qanwar uwar Surayya ta dunga xarar kayan lefen tana rabawa yan kawo kayan a matsayin tukuici. Ana gamawa aka dauke baskets din da suka gani a gurin shaqe da snacks da drinks da aka tanada don basu aka shige daki aka barsu jiki babu kwari suka taho. Wata qanwar Hajjo tace "Deni kam ya samo diyar masu arxiqin da kike buri amma babu alamar suna da mutunci" zahra tai tsaki tace "Arxiqin da babu mutunci da daraja dan adam ai tsiya ta fishi" Yan kai lefe suka watse bayan angama fada da Hajjo akan wai sai sun bata atamfofin da aka basu ai Deni ne ya siya. Su kuma suka hanata sukace ladan wulaqancin data turasu akai musu.
Sakeena da Iya na jinsu Iya tana dariyarta a fili tana cewa "Allah kenan tunkan aje ko ina ya fara fidda haqqin marainiyar da aka azabtar" Sakeena dai ta dan saurarawa waya ta maida hankali kan bitar karatun jamb da Baba ya samo mata pass questions. Ta janyewa Saddiq sosai saboda furucin Deni na cewar xai kasheshi, Saddiq besan anyi haka ba yaga kawai ta dauke masa wuta wanda hakan ke axabtar dashi. Ta samu no Hassana a wayar Iya suna xumuncinsu sosai harda Usaina dake qasar waje, saura yan kwanaki kadan ayi jamb abunda bata ganeba ta tambayi Baba yayi mata bayani.
Washegarin kawo lefen Deni aka kawo na Hadixa shi amma maxane suka kawo, suka gama shewarsu da alama sunsamu yacce sukeso. Amina dai tana ta aikin bankawa kanta hayaqi safe da yamma kamar yadda malam ya sakata ga kuma soyayyar sageer dake qara xurfi a xuciyarta.
Acikin satin dai aka kawo IV na bikin gaba daya sakeena tana ganin IV hawaye ya wanke mata fuska duk da Iya na gurin ta tuna nata auren ko arxiqin IV bata samu ba balle lefe ko kudin aure saboda ita din marainiyace bata da gata Iya ta bata haquri da kalamai sanyaya ta share hawayenta.
A cikin satin dai rigima ta kuma tashi akan Deni ya kama gidan haya da zasu zauna da Surayya sunje sungani sunce yayi musu kadan, shi kuma yace iya qarfinsa kenan in sun raina afasa auren don haushinsu yakeji tun akan wulaqancin da sukai akan lefe duk yadda Hajjo taso a boye xancen kar yaji sai da zahra ta fada masa. Ganin ya kafe ga kuma yarsu tana sonsa sosai kuma dama ta dade a qasa babu miji hakan yasa Babanta ya basu gida makeke a goron dutse, Deni beso hakan ba saboda gudun raini amma Hajjo tayi tsalle ta dire tace saiya karba don haka takeso Deni yayi aure samfurin aureni ka huta.
Angama rigimar Deni ta Hadixa ta kunno kai anje anga qerarran gida Yusuf yayi akayi ta fafa da fangima da nunawa mutane gidan a waya. Baba ya hada tanadin da yayi wanda bashi da yawa sosai saboda qurarren lokacin da aka saka, ya hada da kudin aurenta ya basu suyi siyayya. Ananfa balli ya tashi Hajjo tai tsalle ta dire tace sam dole yayi hubbasa saboda gidan arxiqi xa akai Hadixa ya kawo kudi sosai su taru su rufa mata asiri, shi kuma yace Iya qarfinsa kenan. Ta tari Deni da xancen ya sayi kayan daki da kujeru kamar yadda yayi abikin Fiddausi yace bashi da kudi saboda shima nasa auren wanda qarya yake yayi hakanne saboda haushin Hadixa da tsanarta da yayi saboda itace kanwa uwar gamin data taka muguwar rawar watsewar aurensu da sakeena.
Wannan abu ya mugun dagawa Hajjo da Hadixa hankali murna ta koma ciki yayin da Hadixa ta maida kuka abincinta safe rana da dare.
Dakyar Hajjo tai buga buga aka samarwa Hadixa saitin furniture na kan titi guda daya da kujerun hannu sai yan kwayoyin tukwane guda uku da yan tsirarun kayan kicin da ko buhu basu cika ba aka bar kudin sadakinta da xa a kawo a matsayin kudin siyan katifa, a falelen gidan da yusuf ya gina wanda xaici kayan gado kusan set 4. Hadixa tana arba da kayan a matsayin kayan dakinta ta yanke jiki ta fadi. (Hmm yanxu kika fara gani 😏)
Ana saura kwana 3 asoma biki sakeena ta tafi xana jamb a airport road, tun safe sai yamma ta dawo a gajiye liqis. Ta tarar Iya ta hada musu kaya jaka biyu da rashin fahimta tace "Ina xaki Iya?" tana dariya tace "Baggadano xamuje muyi musu sati daya banaso ai bikin nan muna nan saboda gudun fitina" Sakeena ta dane Iya tana ihun murna, kamar tasan bata son ko xancen bikin ayi balle kuma ta gani.
Da sassafe ranar Laraba suka daga Baggadano (Dawakin Tofa) sakeena murna kamar me, rabonta da garin tun shekaru kusan 7 abaya.
Sun isa Baggadano da rana akai murna da xuwansu fiye da xatonsu saboda an gansu fes. A dakin Inna sukai masauki daya dakin matar Dahiru ce ciki sai dayan na ragowar maxan da basuyi aure bane. Aka kewayesu ana murna aka gaggaisa aka dunga aikin shigo da kwanikan har daga gidan yan uwan sakeena mata da sukai aure, garin yacigaba sosai ya tashi daga qauye ko ina ga wuta nan da aiyukan raya qasa anayi. Sun miqe sunci sun qoshi sun huta gajiya. Xuwa dare kaf yan gidan sun dawo harda mata na gidan aure sunxo ganin sakeena wacce labarin kyan datayi ya cika garin.
Suka hadu a tsakar gida iskar damuna na kadasu anata raha kamar babu wani abu marar dadi daya faru abaya. Iya ta fada musu duk abunda ya faru tun daga kan auren sakeena har xuwan da sukayi nemanta nan da kuma yadda lamarin ya kaya daga baya. Kuma tayi hakanne saboda Baba ya umarceta ta fadamusu gaskiya dan ta iya yiwuwa sunji xancen a radio duba da yadda abun ya fasu, sannan kuma yan uwantane bata da kamarsu Kamar yadda yace koda basa sonta. Suka jinjina duk jikiinsu yayi sanyi Yakubu yayanta yace "Wlh wani abokina ya karanta a jarida ya fadamun na qaryata ashe gaske ne" shi kuwa Labaran dake yana da xafi cewa yayi "Ai wlh Iya da tun a lokacin kika fadan dasai nakai qarar uwar mijin ta sakeena" Iya dai ta taushesu ta basu haquri da fadamusu ai komai ya wuce kotu ta raba maganar. Suma suka nemi yafiyar sakeena akan abunda sukai mata abaya aka shirya hakan yayiwa Iya dadi sosai sun dade suna hira kafin Dahiru ya kori masu auren a rufe gida.
A ranar sakeena tai kwanan farin cikin da rabonta dayi tun tana gidan Deni suna xaman soyayya. Wai yau itace a mahaifarta cikin yan uwanta suke xaune lfy ana riri tata? Lallai Allah maji roqon bawa kuma addua bata faduwa qasa banxa, sai dai wata ana jinkirin amsa maka ita.
Washegari Inna da kanta ta dafa musu ruwan wanka da alama duniya tayi mata nata karatun ta saduda. Sukayi suka shirya aka dunga aikowa da su sakeena kwanikan abinci. Haka suka yini baqi kafin yamma tayi Musa qaninta ya rakasu maqabarta kabarin Nura da kuma iyayen sakeena harda kakanninta. Sukai musu addua kuma ta biya kudi aka daga wasu qaburbura da suka fara ruftawa saboda damina.
Taji dadin kwanakinta a Baggadano sosai taci abincin gargajiya ko adafa mata abunda ranta yakeso ita da Iya sannan Yakubu da beyi aure ba ya goyata a machine dinsa suyi ta xaga qauyen koya kaita gona gurinsu Dahiru ta tayasu aiki suna kwabarta amma takance babu komi yaya mutum ai baya manta asalinsa. Iya ta xage tana dafe dafen mugunguna da itatuwa ita da Inna suna saka sakeena ciki ta xauna ta dade saiya huce ta fito wanda Iya tunda sakeena tai bari taso yimata haka amma bata samu dama ba saboda su Hajjo. Ta dage sosai ta gyare sakeena tas wacce tajita ta koma zam zam kamar bata taba jinin al adaba balle wani aure.
Tana yawan daukarsu photo da wayarta ita da yan uwanta wadanda tun suna dari dari da ita harsuka saki jiki ganin bata kyamarsu komai tare take dasu ta daqumesu suyi photo bata nuna musu ita yanxu yar gayuce ko yar Birni. Su da sukaje yin sati daya sai da sukayi kwana 10 cur saboda dadin xama da sukaji (Allah sarki kowa yabar gida) ranar kwanansu na 9 Yakubu ya goya sakeena a machine dinsa ya kaita cikin dawakin tofa ATM kamar yadda ta buqata, ta cire kudi sosai cikin wanda Sageer ya xuba mata lokacin daya bude mata acct. Suka dawo ta raba musu kudin duka daga me 10k sai me 5k suturar data xo da itama gaba daya ta rabawa yan uwanta mata da matan su Dahiru bata duba tsadar suturun ba, shiryawa da yan uwanta yafi mata komai. Suka dunga godiya suna qarawa da yiwa sakeena fatan gamawa lfy, Iya bakinta har kunne ganin yayanta sun hada kai.
Washegari cikin kewa sukayi shirin tafiya basu da wasu kaya sakeena suturar jikinta kawai ta rage mata itama Iya ta bawa Inna nata kayan da yawa. Suka hado mata kaya da yawa tundaga kan kayan gona wadanda suka isa girbi har xuwa kan kayan lambu da kaji da xabi harda Akuya da Dahiru ya bata Sadiya yayar sakeena ta karba harda kajin tace xata kiwata mata tunda tana kiwo duk da haka sun hada tsaraba da yawa Sakeena tayi musu family picture kowanne cikin matan sanye da suturar data bashi jiya. Har tasha suka rakasu gaba dayansu da fagon kayan tsaraba sai da sukaga shigarsu mota da tashinsu sannan suka juya suna waving juna Dahiru na qara jaddada in sakeena ta tashi aure afada musu da wuri suyi shirinsu, Iya ta amsa suka rabu wasu harda kwalla.(Sabo turken wawa)
Sai yamma liqis suka isa gida suka sauka daga Napep Saddiq take xaune majalisa ya taso da gudu yana tayasu sauke kayan da sukaxo dasu. Suka shiga gida yana mitar sun tafi sunyi xamansu sunqi dawowa sun barshi da kewa sudai dariya kawai suke masa. Suka bude dakin Iya Baba bayanan sai Hajjo dake girki Amina kuma tana falon Hajjo tana kallo.
Sakeena ta dan share qurar dakin suka xube, Iya ta ware kayan data sukaxo dasu kowanne ta ajiyeshi a maxauninsa. Ta ware wasu ta miqawa Hajjo da kanta tai mata Allah sanya alkhairin bikin da akai basa nan. Ta watsawa Iya harara tace "Biki anyi angama lfy bakin ciki ya koreku, kaya kuma ki riqe banaso nafi qarfinsu danni yanxu na wuce ki temakamun yayana kaf sun sami madafa kije gidan Deni kiyi kallon yadda ake auren diyar masu arziqi" Iya tace "To madallah Allah ya sanya alkhairi ya kuma kawo na yan gaba" ta juya ta koma daki. Tasa ka nono a freezer da kwan xabi sakeena ta debi guda 30 ta dafa musu sukaci aka ajiyewa Baba. Iya ta bawa Saddiq kudi ya siyo musu gayar fura tasa nonon da sukaxo dashi kindirmo ta dama musu fura sukasha a matsayin abincin dare. Baba ya dawo ya shigo har daki yana musu maraba suka sha hira Iya na fada masa yadda sukayi a Baggadano shima yaji dadi sosai. Sakeena tai masa murnar bikin Deni da Hadixa, ya amsa yana me tausaya mata. Da wuri suka kwanta saboda gajiya.
Washegari suka kuma kimtsawa sosai Saddiq ya shigo musu hira yana basu labarin bidiar da akai a bikin Deni kusan party kala 4 akai, sannan kuma aka kawo masa gara akori kura guda harda motar hawa c class. Ita kuwa Hadixa abun babu dadin ji ko kadan domin sadakinta 50k bekai a siya mata katifa ba don haka aka kaita babu katifa da sunan sai ansamu ciko xa a siyo, dangin miji suka dunga tabe baki suna mata gorin wannan wane irin aurene? Kalli wasu kaya kamar na wasan yara da kuma kujeru duk jirwayen fitsari. A gaban idon wadanda suka kaita.
Iya ta kada kai tace "Hmm Allah ya xaunarsu lfy" sakeena kuma xurfi tai cikin tunanin Deni yanacan yana amarci da sabuwar amaryarsa ya manta ta, duk yadda taso kauda abun amma ya tsaye mata karma dai yanxu da akai mata fami da taso da xancen.
Ta cigagaba da kunun ayarta a ranar da kuma karatun addinin da Iya ke koya mata, Saddiq ya dubo mata jamb a cafe taci sosai tayi farincikin haka ganin ta haura step daya na shiga jamia kuma a ranar taiwa Sageer waya karon farko a rayuwarta don ta fada masa tunda ta inda aka hau tanan ake sauka ya dauka jikinsa rawa ta gaisheshi ya amsa kamar me magana da shugaban qasa. Tace "Sakeena Abbakar Liman ke magana na kirane in fada maka naci jarrabawar Jamb na samu maki 213" ya sauke hamdala da ajiyar xuciya a tare yace "Masha Allah sakeena yanxu sai post UTME in lokaci yayi." haka ya dunga janta da hira tana amsa da kyar saboda karta gwaleshi. Sageer yana tashi office gidan Maitama ya wuce ya rungumeshi cikin farin ciki yana fada masa yau sakeena ta kirashi a waya. Maitama ya kalleshi da tausayi shi ya dauka ma qarin girma akai masa a office ashe wai duk murnar kiran wayar sakeena ce wannan.
Koda dare yayi ta kwanta bacci wajen qarfe ukun dare Iya ta tasheta tace "ke tashi bacci ba naki bane yanxu ki tashi ki roqi Allah abokin rayuwa nagari da kuma dacewa duniya da lahira." ta tashi tana magagi tayo alwala ta fara nafilfili har xuwa kiran asuba sukai sallah tare da Iya sukai karatu sannan ta koma bacci me cike da nishadi saboda tsaiwar daren da tayi. Daga wannan rana kullum sai Iya ta tashi sakeena tsakiyar dare sunyi sallah tun bataso harta saba kuma abun ya shiga ranta.
Kwana uku da kiran wayar Sageer da sakeena tayi, yana bacci wajen biyun dare kiran waya ya tasheshi, a xatonsa sakeena ce idonsa cike da bacci ya dauka, yace "Assalamu alaikum ranki ya dade ya akai?" Amina wacce soyayyar sageer taiwa mugun kamu harta gaxa dauriya yau ta kirashi cikin dare tanason fada masa abunda takeji game dashi yayin da Hajjo kecan uwar daka tana bacci, taji ya kirata da ranki ya dade wani sanyi ya ratsata badai har aikin malam yacishi ba tun kafin kwanakin turaren su cika? Ta washe baki tayi qasa da murya tace "Darling Sageer ashe ka ganeni? Wlh soyayyarka da tunaninka sun hanani runtsawa" ya wartsake jin baquwar murya don kodaga bacci ya tashi yakan iya banbace muryar sakeena. Cikin dakiya yace "Wacece ne? Bangane me magana ba" ta kuma qasa da murya tace "Amina ce mana autar Hajjo da Baba wacce ta rakaka hanya ranar dakaxo gidanmu" ya ganota yayi mamakin jinta a wannan tsakar daren da kuma inda ta samu number sa ya katse tunaninsa yace "To yaya akai?" ta sauke ajiyar xuciya tace "Sageer baxan boye maka ba wlh Allah ya jarrabeni da mugun sonka na rasa yadda xanyi, na shirya xama da kai a kowanne irin hali koda sadakine ka kawo a daura mana aure, ni budurwace, ban taba aure ba kuma saar sakeena ce ni ko shekaru 20 banyiba a duniya, na iya girki sosai ina da tsafta kuma na iya kwalliya sannan bani da tashin hankali ba halinmu daya da Babata Hajjo ba indai.. ..."
Sageer ya katseta dan ta isheshi da surutu mara kai bai kuma tambayeta ba, yace "Nagode Amina da soyayyarki gareni amma kiyi haquri inada wacce nikeso kuma na kusa aurenta in shaa Allah" Amina tai saurin katseshi idonta taf da kwallar soyayya tace "A a sageer karkaimun haka wlh ko a ta biyu xanxo gidanka inasonka jinake kamar inyi hauka akanka." Ya daka mata tsawa yace "Ke! Banason sakarci dan kinga ina lallabaki to ki shiga hankalinki ko ni mahaukacine kuma koda ina sonki ai baxan hada iri da Babarki ba saboda kin tsotsi halinta a nono, balle ma kuma nima inada wacce nake so kamar hauka karki qara kirana inba haka ba ranki xai mugun baci" ya kashe waya yabar Amina tana kuka da hawaye sharkaf.
Har asuba tana abu daya Hajjo ta tashi sallah ta ganta xaune dungurgur tana kuka ido jawur ta tambayeta menene Amina ta kwanta jikinta tana cigaba da kuka kanta da jikinta xafi rau tace "Waya na bugawa Sageer yace baya sona kar inkuma kiransa yana da wacce yakeso" Hajjo tai salati tana tafa hannu tace "Auta ba malam cewa yayi karki kirashiba harsai angama turaren kwana arba'in da daya?" Amina ta qara sautin kukanta tace "Nidai kawai inkina sona ki samomin soyayyar sageer inba haka ba wlh xan kashe kaina" Hajjo ta zare Ido cikin tsoro tace "Abun har yakai haka? Amina tace "Har yafi haka ma" ta lallaba Amina da cewa xatasan yacce xatai tayi haquri.
******* ******** *******
Wata yaxo qarshe sageer ya nufi KT gurin umma kamar yadda ya saba ya gama kwanakinsa yayi shirin dawowa suna sallama xai tafi ta dubeshi tace "Muhammadu yanxu haka xakai ta xama babu aure ko ga dukiya Allah ya baka ko mace hudu xaka iya aure lokaci guda kuma ka riqesu" ya dan sosa kai yace "Umma kiyi haquri xanyi ne in lokaci yayi" tayo masa daquwa tace "Gidanku🖐🏽 babu inda xakaje saika tsayarmun da magana kar kaje ka kuma auren bansani ba" jikinsa yayi sanyi yace "Umma kiyi haquri baxan kuma ba wancan ma da nayi baki sani ba ga jarrabar da Allah yayimun akai saboda haqqinki har abunda bakisan inayi ba wlh duk na dena ki yafemun" ta tausaya masa tace "Bakomi Muhammadu qaddarace Allah ya yafe mana gaba daya." Yanxu dai fadamun yaushe xakai auren Dan Allah? Yana murmushi yace "Umma ki nemomin mata kowacece ni kuma xan miki biyayya na aureta" Ta waro ido tace "Ni in nemo maka mata bakaso kaje ka wulaqantata? daure dai ka fadan wacce kakeso" ya qurawa Umma ido yace "Wacce nakeso umma bata sona bana gabanta gaba daya" ya share kwallah bayan ya gama fada. Itama ido ta qura masa tace "Sakeena ko? Ita kakeso ko Muhammadu?" yayi shiru yayi qasa da kansa. Sukai sallama ya tafi jikinsa a sanyaye.
Umma kwallar da taga Sageer nayi ta daga mata hankali tasan ba qaramin abu kesa shi kuka ba. Washegari da kanta ta tashi taje gidan Baffa Ado (yayan Baban sageer) suka tattauna akan maganar, shima ya nemi ragowar yan uwansa ya fada musu suka tsaida magana aka kirawo Baban sakeena dake Kano.
Ranar da suka cika kwana tara da dawowa daga Baggadano sakeena ta fito daga dakin Iya xata kicin Hajjo na xaune kofar daki ta dubeta ta kwashe da dariya tace "Ina ruwan biyu babu uku babu ko daya? Miji ya sakeni yayi auren soyayya, kwartona ya gudu ya barni ina jabe gida babu dan kida babu dan rawa, sai xaman kashe wando" ta kuma dariya tana kwaikwayon muryar sakeena Kamar yadda tayi awani lokacin baya tace "Inason inxama mai yada labarai a nunoni a TV ina karantawa" ta qarasa tana sheqa dariyar ixgili ta kuma cewa "Ai keda aure kam sai dai kiga anayi saboda xancenki yagama duniya kinyi aure cikin aure" Sakeena da xuciyarta ke abushe saboda yadda take tsanin kishin Deni da ko gidan baya xuwa saboda xaqin amarci ya watsarta yana jin dadinsa ga kuma uwarsa na mata gorin abunda itace sanadin jefata ciki ta. Ta tunkari Hajjo ranta a tsanin bace ta shaqo mata wuya ta hadata da bango ta falla mata mari ta kuma falla mata wani. Hajjo ta fara kakarin mutuwa ta kaiwa sakeena duka ta riqe hannun ta murde, Amina ta fito daga daki duk ta fige ta rame saboda soyayyar Sageer, ta fara dukanSakeena tana yunqurin kwatar Hajjo, sakeena idonta jawur tasa hannu tai wurgi da Amina gefe daya. Tacigaba da waskawa Hajjo mari babu qaqqautawa. Amina taga ana shirin kai Hajjo lahira tayi dakin Iya da gudu tana haki tace "Iya kixo ki temaka kiwa sakeena magana ta shaqe Hajjo xata kasheta" Iya tana xaune tana jan carbi taiwa Amina banxa. Amina bata qara tunkarar sakeena ba don ta tsorata da ita tai waje da gudu ta tarki sana'a Baba ya kawo kai bata tsaya yimasa bayani ba taja hannunsa ta kaishi tsakar gida inda Sakeena ke caskala Hajjo wacce ta jigata idonta yayi jaa ta daku a hannun sakeena.
Baba yayi yunqurin raba hannun sakeena da wuyan Hajjo ya kasa, cikin kwantar da kai yace "Yi haquri sakeenatu ki saketa" ta juyo idonta taf da kwalla tace "Baba taimun abubuwa da yawa a rayuwata, mafi munin abunda taimun shine baxa hotunana a duniya da kuma jifana da kalmar fasiqanci wanda duk da an wankeni wasu sun yadda wasu kuma basu yadda ba sannan kuma yanxu taxo tanamun gori" Baba yace "nasani sakeenatu kiyi haquri Dan girman Allah ki saketa" ta saki Hajjo ta fadi gefe tana haki da bin sakeena da kallon tsoro.
Baba ya kira Iya ta fito yace "Kama diyarki kuje daki" ta kama sakeena suka shige ciki ta kwantar da ita akan cinyarta tana shafa bayanta tai bacci. Tasan yau Hajjo ta qure haqurin sakeena tunda tai mata haka, wannan abu yayi mata dadi kwarai shiyasa ma taqi shiga balle ta raba.
A kwana biyun da suka biyo baya Hajjo da Amina sukai mugun shiga taitayinsu ko tsakar gida a dari dari suke fitowa suna daki a takure Hajjo na jinyar kunburarriyar fuska da dukan sakeena Amina kuma tana jinyar xuciya da soyayyar Sageer ga kuma baqon lamarin mugun tsoron sakeena da sukeji.
A ranar cikon na biyun ne Baba yayi baqi da safe wajen goma ya fita ya dawo da sauri ya dauki qatuwar tabarma ya kira Saddiq a dakinsa na soro ya kuma dawowa ya fadawa Iya a hankali cewa Iyayen Sageer ne da sukace xasuxo. Karaf a kunnan Amina take kicin.
Ta koma daki da sauri ta tashi Hajjo a bacci tana murna tace "Tashi bacci ya qare Iyayen sageer sunxo kawo kudin aurena kamar yadda malam yayi mana alqawari" Hajjo ta mutstsuke yawun bacci tace "Haba? Ai dama malam ya rantsemun yace a cikin satinnan xasuxo da maganar Aure" Amina tace "Aikuwa dai gashi sunxo yanxu naji Baba na fadawa Iya baisan da maganata akaxo ba." suka cigaba da hira cikin murna da tsare tsaren yadda biki xai kasance.
Kimanin rabin awa Baba ya shigo gidan cikin farin ciki yana bude dakinsa yana cewa "Hafsatu kuxo keda sakeenatu" Hajjo ta miqe tana daura dankwali tace da Amina "Tashi muje ayi a gabanmu nasan ita xai fara fadawa ankawo kudinki tunda ni ba magana yakemun ba kuma wannan Karon tun yanxu xan amshe kudin auren tunda ba wata tsiyar yake muku ba, baxan bari sai biki ba kamar yadda yayiwa su Fiddausi" Amina ta miqe tana cewa "Ai kuwa dai gara ki karba a qara kaiwa malam ya kuma damqemun xuciyar Sageer, naga aikinsa duk yafi na sauran malaman ci da wuri" jikinta har karkarwa yake ta biyo Hajjo suka shige dakin Baba.
Ya dubesu bece komai ba ya fito da kudi daga aljihunsa. Amina ta qara matsawa kusa dashi tana murmushin cikar buri. Ya kalli Iya da sakeena dake gefe daya yace "Sakeenatu meye matsayina a gurinki?" cikin mamaki tace "Baba aini mahaifi na na daukeka." ya qara cewa "Ai canake na fita daga wannan matsayin tunda Deni ya rabu dake" tace "Allah ya sawaqe, ai bashi ya hadamu ba balle ya rabamu kananan a matsayinka na Ubana fiye da lokacin da nake auren Deni, kuma ni nama manta dashi a rayuwata" Duk dakin babu wanda maganar sakeena bataiwa dadiba na cewa ta manta Deni a ciki kuwa harda Hajjo tana dariyar murna da kumburarriyar fuska tace "Malam ai gara ayi abunda ya hadamu a gama kowa ya kama gabansa"
Baba be kula Hajjo ba ya dubi Iya yace "Kamar yadda nace miki iyayen sageeru sunmin waya tun wancan satin akan xasuxo da maganar aure, na tsaidasu nayi bincike don ba'a aure babu bincike don kaga mutum a cikin babbar riga bayana nufin shikenan mutumin kirki bane. To Alhamdulillahi nasa anyi bincike tundaga katsina har xuwa Lagos gurin aikinsa kuma ya samu kyakykyawar sheda hakan yasa na basu dama shine yau sukaxo" Amina hawayen farin ciki ya xubo mata, ta samu Sageer ta gama inama Baba be tsaya wani bincike ba ita koyaya Sageer yake tana sonsa kuma da Baba ya fada mata sunyo waya tun last week da cewa xatai kawai suxo da shirin daurin aure da daukar amarya batason wata bidi'ar biki itadai Sageer kawai take so.
Baba ya katse mata tunani ya miqawa Sakeena kudin yace "Gashi na cika matsayina na uba na karbi kudin aurenki da sageeru kuma nasa rana sati uku masu xuwa, na tabbatar xakimun biyayya" Sakeena hawaye da faduwar gaba a tare sukaxo mata, gashi Baba ya daureta da jijiyon jikinta, tace "Baba ka riqe kudin auren in lokaci yayi ka bani kamar yadda kakewa yayanka" ta fads tana hawaye. Iya cikin tsananin farinciki mara misaltuwa ta fara yiwa Baba godiya da kuma sakawa auren albarka.
Amina ta miqe xunbur itama tana hawaye kamar sakeena tace "Baba anya kuwa kaji dai dai, ba sakeena aka kawowa kudin auren sageer ba ni aka kawowa, nice keson Sageer. Haka malam yayi mana alqawari ko Hajjo? Yace indai nayi amfani da maganin dai dai sageer xaixo da maganar aure cikin satinnan baxata, kuma wlh dai dai nai amfani da maganin" ta juya gurin Hajjo da tayi wuqi wuqi a xaune tace "Hajjo ba daya malamin cewa yayi indai muka xubar da cikin sakeena kuma aka kai masa number Sageer shikenan Sakeena da sageer sun rabu har abada ba? To meyasa duk munyi hakan yanxu akace sakeena aka kawowa kudi ba niba?"
Daki yayi tsit har Saddiq dake bacci hargagin Amina ya tasheshi ya shigo ciki. Baba, Iya da Saddiq kallon Amina da Hajjo suke cikin kaduwa.
Yayin da sakeena take sunkuye tana kukan wai xata auri Sageer nan da 3 weeks. Ita sam abunda Amina tai da kuma xubar mata da ciki be dameta ba bala'in jin xata auri Sageer mutumin datafi tsana a cikin maxa, yafi daga mata hankali, ita kam danta itane har godiya xataiwa Amina saboda ta xubar da cikin qaddara wanda rabonsa ne ya hada ta da Sageer.
Tofa! Sakeena na kukan auren sageer, yayin da Amina ke kukan rasa Sageer.
Xamu hadu ranar Friday in shaa Allah
Hajia 😊
[8/21, 12:08 PM] A A Dboy: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣3⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Sakeena ta miqe tayi daki tana gunjin kuka, yayin da Tabar su Baba cikin tsananin mamakin mugun halin Hajjo. Baba ya figo Amina ya fara dukanta babu wanda yayi yunqurin tsayar dashi domin ba a taba ganin yana dukan wani ba sai yau. Hajjo ta gaza juriya taxo kwatar Amina dake kuka tana cewa itadai komenene ai mata amma wlh Sageer kudinta ya kawo bana sakeena ba. Baba ya hanbare Hajjo sai gata a gefe a yashe koda yake dama bata gama jinyar dukan da sakeena tai mata ba. Yacigaba da lallasa Amina ta daku sosai me haquri be iya fushi ba, sai dayaji xuciyarsa ta danyi sanyi sannan ya kyaleta. Ya kalleta bakinta duk jini harya fasa mata gefen kunne garin duka, cikin kyamar Hajjo yake da kuma dana sanin hada xuri'a da ita ganin yadda gaba daya ta bata yayan da mugun halinta (Hmm dama shiyasa akeso inxaka auri mace ka aureta don addininta kuma ka duba halinta da kyau domin xata haifa maka irinta) A xuciye yace "Hajara kinsan na sakeki tun a baya ko? Na kuma daga miki qafa kiyi idda a dakinki bisa koyarwar addini amma kinqi saduda ki gyara halinki wanda addini yayi hakanne da nufin inkin gyara in maida ke ko? Yanxu har bala'inki yakai ki tasa yarki a gaba xuwa gidan malami kuyi shirka ya fada muku qarya ku xubar da ciki ko? To yanxu da sakeena ta rasa ranta gurin xubar da cikin fa? Kujewa Allah da hakkin kashe rai? Saboda haka ki tattara ki barmun gidana wlh nagaji da xama dake kin batamun yaya kin hanani sakat da baqin halinki inna fita daga wannan masifa saiki kunno wata, to ki tafi Amina kuma ki barta anan tunda bakixo da itaba." Hajjo cikin tsananin masifar tashin hankali take, yanxu ina xataje? Gidansu dake bachirawa me daki biyu kacal wanda daya Babanta ke ciki yana tsubbace tsubbacensa kuma baya bari ko uwarsu ta shiga bare su dayan kuma Babarta ke harkarta ta bori ciki xata iya tunawa sanda auren qanwarta marka ya mutu sai a maqota take kwana da safe ta shigo gidan, ko yini kajeyi gidan sai hankalinka ya tashi saboda qaxanta da talauci da kuma xaman doya da manja da ake tsakanin iyayen nasu.
Ta kama qafar Baba ta riqe tace "Malam ka dubi Allah ka rufan asiri yanxu da girmana harda surukai ace aurena ya mutu? Ka dubi darajar yayan da muka haifa ka kyaleni a gidannan koda baka maisheni matsayin matarka ba" ya xare qafarsa yayi hanyar fita yana cewa "Ai kinsan da yayan da kuma surukan
Kike duk abunda kike, da kinsan darajarsu xakiyi ne? Kuma da ina fasa mugun halinki da kina xaton ko kallon yayanki xa a yi balle a auresu? Baxan xauna baqin cikinki ya kaini kabari ba lokaci na beyi ba don haka karki sake indawo insameki"
Saddiq na gefe idonsa jajur sai da Baba ya fita ya dubi Hajjo da Amina yace "Hajjo yanxu meye amfanin wannan? Me kenan kikayi? Hajjo wlh ya dace ace kin daina abunda kike tun lokacin batan sakeena, amma baki daina ba, na xaci xaki daina a lokacin da kika shiga prison amma abun takaici shima nan baki daina ba, kina fitowa kika dora a inda kika tsaya wai Hajjo kece da jagorantar xubar da cikin sakeena? Kisa fa kenan? Hajjo wlh har kunya nakeji ace ke kika haifeni saboda abubuwan da kikeyi." Hajjo ta kwabe baki tasa kuka jin abunda Saddiq yace, tace "Saddiq wlh duk xan daina abunda nake kasa baki malam ya kyaleni ai kaga da kunya surukaina maxa suji aurena ya mutu ko?" saddiq ya runtse ido yace "Hajjo ana ga yaqi kina ga qura, nifa wlh baxan iya tunkarar Baba da wata magana ba yanxu, tunda kike dashi kin taba ganin yayi fushi haka? Kin qureshi sosai ki taso kawai ki tafi karya dawo ya sameki"
Iya tana xaune daki cikin tagumi da kuma jimamin jin wai su Amina ne silar xubewar cikin sakeena da kuma mamakin wai Amina keson Sageer har ankaishi gurin malamai ta kuma tsorata da halin Hajjo kuma ta tabbbatar da xata iya kashe sakeena don ta bayyana qarara bata sonta. Ta godewa Allah daya kawo qarshen auren sakeena da Deni kuma koda Deni be saki Sakeena ba ayau saiya saketa tunda abun ya kai haka.
Ta juya tana duban sakeena wacce ke kuka, ranta a bace tace "Ko kiyimun shiru ko kuma inci miki mutunci, menene abun kuka acikin abunda akai yanxu? Menene lefin yaron nan?" Sakeena ta dago ta share hawayen fuskarta ta matsa jikin Iya ta kalleta cikin ido tace "Iya kinsan bani da wacce ta fiki duk duniya, bani da qawa ko aminiyya da xan fada mata damuwata da ke kadai na rayu. Wlh Iya banason Sageer kuma banda qaunarsa bana buqatar ko jin muryarsa, kallonsa balle kuma aurensa" Iya jikinta yayi mugun sanyi da kalamin sakeena ta dubeta tace "Sakeena kiyi haquri sageer ne ya dace dake sannan kuma gashi yana qaunarki kuma inba quruciya irin taki ba wa xaki aura wanda yafi sageer din?" Ta bawa Iya amsa da cewa "Baga Bar Adam ba, ko yanxu nai masa tayin aure xai amsa tun randa aka gama shariar mu yace yana cikin jerin manema inna haihu" Iya ta Kalli sakeena tai murmushi ta kwantar da ita a jikinta ta fara magana.
"Sakeena kiyi haquri kowa da qaddararsa a rayuwa, ke taki qaddarar itace ta aure akan wani auren kuma wlh sakeena babu wanda xai riqe ya kula dake ya kuma kare miki mutuncinki kamar SAGEER. Duba da yacce yayi miki riqon amana a lokacin da be sanki ba kuma yanada damar da ko siyar dake xaiyi a wancan lokacin amma bai miki komai na cutarwa ba yayi miki riqon da ko agaban iyayenki ya aureki iyakacin abunda xai miki kenan. Kuma sakeena inkika auri wanin Sageer wlh xaki iya fuskantar gori na rashin gata ko dangin uwa, babban misali shine aurenku da Deni har kuka rabu uwarsa da yan uwansa nayi miki gorin dangin uwa kuma suna kiranki da qedara. Sannan inkika auri Adam ki tunafa cikin kishiyoyi xakije har guda biyu wadanda muna daga nan labarin yadda suke jifan juna da asiri yake ruskarmu, ke kuma kinsan baki da wani gata sai nawa kamar yadda kikasan baxanyi shirka wato bin bokaye ba akanki. Inkaka haqura da auren sageer kuwa nasan koda bayan raina xai kulamun da ke da kuma maraicinki baxai taba bari ki tagayyara ba sannan gashi mahaifiyarsa dattijuwar arxiqi tana qaunarki. Wlh sakeena sageer shine mijin dana dade ina roqon Allah ya baki, sannan kuma aurensa da Allah ya aiko miki bagatatan adduoinmu ne da mukeyi a yan kwanakin nan Allah ya amsa. Kiyi haquri qiyayyar sageer saqace shedan yayi miki cikin xuciyarki kuma qiyayyar baxata fito miki ba. Allah ya bamu yawan rai sakeena wata rana xakiso sageer fiye da komai a duniya, abunda ya faru a rayuwarki na aure cikin wani auren MUQADDARI NE kuma akwai hikimar ubangiji acikin yin hakan wacce ta bayyanar mana itace ta rabuwarku da Deni da kuma yin tsarkakakken aure tsakaninki da sageer, bamusan kuma hikimar da ubangiji ya boye ba a tsakanin qaddarar haduwarku. Ba lefi kikaiwa Allah ba qaddarace ya dora miki wacce batajin magani kuma batajin addua koda anqi baccin shekara. Ki dubafa sakeena wata har bin malami take (Amina) akan Sageer amma ke Allah ya baki ba tare da kin wahala ba kina nema kiyiwa kanki, karki yadda Allah yayi fushi dake kuma ya barki da kanki. Abu na qarshe da xan fada miki shine karki kuskura ki batawa sageer rai ko kuma ki nunawa wani mahaluqi bakya maraba da aurensa, shi kansa ban yadda ki nuna masa bakya qaunarsa ba ki saki jiki ki nunawa maqiyanki auren soyayya xakiyi yadda Deni yayi inyaso baqin ciki ya kashesu. Kinmun alqawari xakiyi haka Sakeena?" Ta gama saurarar doguwar nasihar Iya kuma ta ratsata sosai amma kuma abun da kamar wuya wato boye qiyayya. Tayi murmushi tace "In shaa Allahu Iya baxan baki kunya ba" tace "Yawwa diyata Allah yayi albarka, bara inxo inbugawa mutanen Baggadano waya insanar musu, malam baya cikin nutsuwar da xai fada musu yanxu."
Sakeena ta dan samu saukin damuwa a xuciyarta, amma cikin xuciyarta qiyayyar Sageer tananan danqam. Ta wanke fuskarta taci abinci ta dauki waya ta saka glasses ta fara kallon indian series din da Saddiq ke mata downloading "Sapne Suhane"
Hajjo ta tattara yan kudadenta da yan kaya kala biyu ta saita hanya gidansu, tabar Amina kwance dakinta ita kadai tana kukan rashin Sageer ko gixau dukan Baba da tafiyar Hajjo basu dameta ba, rasa Sageer itace babbar masifar data fara fuskanta a rayuwarta.
Saddiq yayi sallama dakin Iya yayi mata fatan alkhairi kawo kudin sakeena kana ya juya ga sakeena da bata kula da shigowarsa ba hankalinta nakan waya. Iya ta xungureta ta cire ear piece din kunnanta. Suka gaisa da Saddiq yayi mata fatan alkhairi itama, ya Kalli idonta dake kumbure yasan kuka tayi. Jikinsa a sanyaye ya basu haqurin abunda Hajjo da Amina sukai. Ya dakko wayarsa ya budewa sakeena folder guda na pics din pre wedding na bikin Deni wanda sukai da Amaryarsa Surayya. Ta karba tana ganinsu kala kala sunfi guda 20, abun babu ko tsari qaxaman hotunane wanda Surayya tayi shiga me bayyana tsaraici sosai yayin da shi kuma Deni yake riqeta da kuma rungumarta aciki kamar be taba sanin hanyar islamiyya ba balle ilimin addini, kuma koda an riga anyi auren da kunya yayi hakan da ita a gaban mutane. (Allah ka yaye mana wannan masifar data samemu da sunan wayewa) ta gama cikin Al ajabi ta miqa masa, ya kuma budo mata photunan biki da kuma vedios. Anan kam xuciyarta har dakatawa tayi da aiki na dan lokaci saboda ganin Deni da Surayya suna tsotsar bakin juna ga kuma mutane an xagayesu ana musu tafi. Ragowar photunan kuma abun ya qaxanta kwarai. Ta Kalli Deni a photon yana cikin farin cikin da bata taba ganinsa a ciki ba yayi kyau sosai cikin shigar alfarma ta angwanci. Surayya kuwa yau ta fara ganinta doguwace sosai me garin jiki tagano yadda qugunta da qirjinta ke cike ta fited gown din data saka ajikin photon kuma tana tunanin abunda yaja hankalin Deni kenan ta sanshi farin sani akan son mace me cikar jiki, a fuska ma kuma xa'a iya kiranta kyakykyawa kai tsaye don bata rasa komai na sigar kyau ba sannan kalar fatarta irin ta Deni ce wato chocolate.
Ta miqawa Saddiq wayarsa tana dauke kwallar idonta, yace "A a badan kiyi kuka ko in daga miki hankali na nuna miki ba, na nuna mikine don kisan ciwon kanki kuma kisan inda kika dosa, damuwa da wanda be damu da kaiba yaudarar kaine, sageer shine ke sonki da gaskiya, indai yaya Deni ya mantaki ya kuma fara sabuwar rayuwa danme kema baxaki mantashi ba ki riqe me sonki hannun bibbiyu? Dan Allah sakeena ki bamu hadin kai mu taru mu nunawa duniya auren soyayya xakiyi. Yin hakan shi xaisa Deni da sauran mutanen dake goya masa baya su gane cewar kin watsar dashi kuma bashi kike xaman jira ba ya maidake Kamar yadda ake xato" Jikinta a sanyaye tace "To Saddiq nagode xanyi hakan in shaaa Allah" Iya tana jinsu kuma abunda Saddiq yayi ya burgeta ya farkar da sakeena daga makuwar da take shirin yi. Koda Iya ta qare abincin rana ta xubawa Amina ta miqa mata daki kamar yadda Baba yace ta dunga bata abinci. Shi dinma daya dawo saida ya leqa ya tabbatar Hajjo bata nan sannan ya shiga daki yaci nasa abincin. Sakeena ta fadawa su Hassana maganar aurenta su kuma suka sanar da mama suna ta murna dake suma yan jam iyar sageer ne. Da daddare ana xaune tsakar gida kamar yadda aka saba, Amina ta fito daga daki tanabin bango saboda xaxxabi da ciwon kai da kuma yunwa ga kuka data yini tanayi. Ta tsuguna a gaban Baba kowa ya xaci haquri xata bashi bisa kuskure da sukai daxu. Amma mamaki ya rufesu lokacin da sukaji tace "Baba ka kira Sageer din kaji wadda ya kawowa kudin aure a cikinmu?" Baba ya cire hannunsa daga abinci yanawa Amina kallon mamaki, Saddiq kuwa tsaki yaja ya kai mata maxga yace "Kauce ki bamu guri banxa shashasha"
A bangaren Sageer kuwa sam besan abunda ake ciki ba na kai kudin aurensa da sakeena. Sai da umma ta tabbatar yan kai kudin sun dawo kuma anxo da kyakykyawan labarin saka ranar da Baba yayi 3 wks kacal, sannan ta kira Sageer bayan tasan duk inda yake yanxu ya dawo daga office kuma ya huta.
Qarfe taran dare ta kirashi lokacin yana kallon CNN, ya latsa mute a jikin remote kana yayi picking ya durqusa har qasa ya gaisheta. Tace bayan sungama gaisawa "Muhammadu ankai kudin aurenka yau kuma har anbaka yarinyar sannan ansaka rana sati uku masu xuwa, na kiraka ne infada maka ka hada lefe akawo acikin satin nan inaso akai ranar asabar in Allah ya kaimu. Ni dai na bada dubu hamsin ankai maka kudin auren" Sageer ya runtse idonsa yace "To umma nagode Allah ya qara girma kuma xan hada lefen sai a tambayo sixe din takalminta ko?" Umma ta tausaya masa biyayyar da yayi mata tunkan yasan wacce xata aura masa tace "Muhammadu baka tambayeni wacece matar ba?" yace "Hmm umma nasan ko wacece tagari ce tun xabinki ce Allah ya hada tsakaninmu da alkhairi" tace "Amin Muhammadu. Sakeentu ce matar taka in shaa Allahu, ita na bayar aka kaiwa kudin aure, tun washegarin tafiyarka na samu kawunka da maganar sukai bincike akai, kuma shima mariqin sakeena yace abashi dama yayi nasa binciken akanka. To yau dai komai ya kammala sunkai kudi tun safe har sun dawo Katsina" Sageer ya bude iyakacin muryarsa yace "ALHAMDULILLAH" yaci gaba da xabgawa umma adduoi tana amsawa cikin tausayinsa da kuma yaba soyayyar da yakewa sakeena.
Yana kashe waya ya nufi waje da gudu ko takalmi babu ya fada gidan Maitama, yana xuwa ya riqe hannunsa yace "Maitama ka tayani farin ciki anbani sakeena yau har ansaka mana rana, nan da 3 wks sakeena ta xama matata?" Maitama ya shafa fuskar Sageer cikin tausayi yace "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi" Bilki tana kallon sageer tace "Bamu labarin yadda akai aka gama komai babu lbr" ya xauna ya basu lbr yadda umma ta bashi. Ranar dai har kusan 12 AM yana gidan, be baro gidanba saida suka gama lissafin kayan lefe tas shida Bilki tana rubutawa, suka gama komi tunda suna da sixe din Sakeena na komi. A take yayi mata transfer din kudaden da tace harda riba ya dora mata, yace Dan Allah gobe ta siyo komi inya dawo xaixo ya gani. Sageer na xaune yana jinsu da ganinsu kuma yana mamakin son da Sageer kewa sakeena da alama xai iya bada duk dukiyar sa daya tara da wahala don kawai ya tsira da sakeena.
Yana komawa gida ya dauki waya, kamar yadda ya xata tana online. Ya duba DP dinta yaga family picture ne wanda sukai ita da yan uwanta a Baggadano. Yayi mata sallama Karo na farko da suka fara magana a social media. Ta amsa, yace "Nice dp" sakeena dama akusa take dashi tace "Sageer wai meyasa ka nace saika aure ni bayan kasan bana sonka?" yayi mata alamar murmushi yace "Sakeena kiyi haquri Allah ne ya jarrabeni da sonki, bamu san dalilin da yasa Allah ya hadamu ba, kina kano, ina katsina amma Allah ya kawoki Lagos ya hadamu kinga dole akwai hikimar ubangiji tayin hakan. Karki damu xaki sameni me biyayya a gareki xanxame miki irin mijin da kike so, baxan ta kura miki ba, xan baki yancinki, xakiyi irin rayuwar da kike mafarki a qarqashin kulawata kinji my luv mu barwa Allah lamarinsa shiya hadamu kuma dama Allah shike hada dangantaka" sakeena jikinta yayi mugun sanyi ta kasa yimasa rashin mutuncin data shirya yimasa.
Washegarin korar Hajjo da tsakar rana saiga Fiddausi a gida yarkace yarkace da ita kamar amaryar ba da ko haihuwar fari batai ba, fuskarta a kumbure duk kwanciyar hannu. Ta shige daki ba tare data kula su Iya dake aikin kunun aya ba a tsakar gida, suma kuma basu kulata ba, ta shige dakin Hajjo ta tarar da Amina da kuma bad news din ankori Hajjo.
Saida Baba ya dawo cin abincin rana sannan ta fito ta sameshi tana kuka da kuma fada masa cewar mijintane ya siyar mata da kujerunta dontayi masa maganar akan me ya siyar mata yayi mata dukan tsiya tare da korota gida. Baba ya gama saurarenta yace "shi mahaukaci ne daxai kamaki da duka babu dalili? Dacan meyasa be dakeki ba sai yanxu? Dole akwai abunda kikai masa. Sai ki tashi kije dakin uwarki ki xauna tunda haka kuka xaba ta koya muku mugun abu ita tana xawarci kuma gashi kun fara, barewa bata gudu danta yayi rarrafe."
Da daddare mijin Fiddausi ya amsa kiran da Baba yayi masa, Baba cikin kamala ya tambayi gaskiyar abunda Fiddausi taxo ta fada. Ya fadawa Baba yacce akai wato kudi ya ajiye a dakin ta bata sani ba shine da yaxo daukar kudin ya tarar ta ciri 50k aciki. Shi kuma yayi mata ta yan duniya ya turata unguwa gidan abokinsa kafin ta dawo ya kwashe kujerun dakinta ya siyar ya dauki kudinsa ya bata canjin, ta nemi yimasa rashin kunya harda kama kwalarsa shi kuma ya lakadamata duka ya saito ta gida. Baba ya jinjina kai bayan gamajin jawabinsa yace "To tunda ka rama, ina neman alfarma ka maida ita dakinta kuma kayi haquri xan jamata kunne sosai." suka rabu da mijin Fiddausi akan cewa sai yaje ya tambayi uwargidansa intace ya dawo da ita saiya dawo da itan. Wannan shiya haskawa su Baba cewar Fiddausi gidan mijin Hajiya takai kanta a garin kwadayin auren me kudi. Bayan fitarsa Baba ya kira Fiddausi ya fada mata duk yadda sukai da Musa mijinta, ya kuma tamvayeta ina ta kaimasa kudinsa dubu hamsin. Cikin inda inda tace "Hajjo ce tace insamo kudi akaishi gurin malamai a mallakemunshi indunga juyashi yadda daya matar ke juyashi ni kuma bani da kudi shine na daukar masa ban xaci xai gane ba" Iya ta rafka salati ta jinjina wannan qarfin hali na yiwa miji sata. Baba yace "To madallah, yamun dai dai daya dauki kayanki ya siyar kuma yayi miki adalicin baki canji don kije ki qarawa bokan naku. Madallah da aikin Musa. A matsayina na uba na sauke haqqina na bashi haquri nace ya maidake amma yace sai nemi ixinin kishiyarki" Fiddausi ta fashe da kuka tace "Wlh Baba ni nagaji da xama dashi tunda na aureshi banji dadin xama ba kona kwana daya. Sai yadda matarsa tayi dashi ko part dina saita yadda yake shigowa kuma ko kudin cefane itace ke bani sannan innagama girki sai taxo ta raba ta bani." Baba ya murgina kai cikin takaici yace "To ga filin gidanan ki xauna, amma fa xaman gidannan ya canja salo kamar yadda kika sani na kori uwarki saboda mugun halinta da kukayo gado wanda wlh baxaku taba xama lfy ba har sai kun canjashi domin shi mugun hali kamar fasashshiyar tayar motace wacce babu inda xaka da ita harsai ka canja. Sharadin xamanki a gidannan shine, ban yadda ki dagawa matata hankali ba ko muxgunawa sakeena sannan kuma xakiyi duk aikin gidannan don baxaki xaunamun a gida babu aikin komai ba. Hafsatu xata dunga baku abinci keda yar uwarki, abu na qarshe shine ban yadda ki fito ki dungayimun yawo a tsakar gidaba ana shigowa ana ganinki kinqi xaman aure kin dawomun, karya wannan sharuda suna nufin fitarki a gidannan ki koma gidan mijinki da kika xaba ke da uwarki ko kuma ki bita can gidansu kuyi xawarcin tare." Fiddausi ta miqe ta koma daki tana kukan danasanin auren musa wanda Baba yaso ya hana ita da Hajjo suka kafe saboda yana da kudi kuma yanayimata hidima lokacin neman aure. Haka suka kwana kuka ita da Amintako babu mai lallashin wani (🤣)
A daddafe Hajjo tai kwana uku kacal a gidansu Babanta da qaninsa suka tasota suka dawo da ita gidan mal Lawan da nufin bashi haquri ya maisheta dakinta. Sai dai sunyi mamaki da Baba ya murje idonsa da kuma kunyar surukinsa ya xana masa irin wahalar da yasha da Hajjo da kuma mugun halinta har xuwa kan abunda tayi last, yace ya gama aurenta intana buqata ma yana iya qarasa mata ragowar sakinta a rabu gaba daya. Babanta yace "Ai baka kyautamun ba daka tsaya iya sakinta kawai dakasani duka ka nadawa tsinanniya ka karya ta, ai wannan hali nata gado tai gurin gyatuma, amma ita dake ta hadu dani abun baya tasiri ko yanxu taimun nadarta nake kamar Allah ya turoni" qanin uban ya tasata suka tafi bayan uban ya gama baranbarama agaban surukinsa ya kwancewa Hajjo dan ragowar mutuncinta daya rage gurin malam lawan. Ranar Hajjo taga bala'i domin a soro ta kwana akan turbaya,maqotan da take xuwa ta kwana ranar sun mata kora da hali ta hanyar kulle gidansu tun magribar fari. Babu shiri washegari ta nufi Gwale ta dunga bin gidajen dattawan unguwar da mal Lawan ke ganin mutuncinsu tana roqonsu su bashi haquri ya maidata. Daganan Goron dutse ta nufa gidan Deni dakyar taje bayan tasha baqar wahala ta qarasa da kwatance. Sai dai qirmisisi me gadi ya hanata shiga duk nacinta a cewarsa madam tace kar a bari ko tsuntsu ya shiga gidan indai ba daka gidansu yakeba wato rijiyar xaki wai amarci suke. Hajjo ta dunga yimasa bayanin itace ta haifi megidan ita uwar miji ce, megadin ya sheqe da dariya yace "Ai ba gidan Nura bane, me gidan kam yana rijiyar xaki tunda gidan arone, ya qara da cewa da madam kika haifa da tuni kin shige an wuce gurin" Hajjo tai xaman awa biyu a xatonta ko Deni xai fito sallah ya ganta tunda tayi kiran wayarsa tun randa aka koreta yaqi dauka. Me gadin ke fada mata ai tunda Nura ya shiga gidan sau biyu kachal kawai ya fito shima yan uwan madam da qawayenta da sukaxo ya rako bakin mota, ko sallah aciki yakeyi. Ta miqe jiki babu kwari ta dau hanyar Bachirawa.
Acan gida kuma ranar da Fiddausi ta kwan biyu a gidan ta fito xuwa bandaki ta tadda sakeena kofar dakin Iya xaune tana yankan farce, Amina ma dai tana kofar dakin Hajjo xaune xafi ya korota tayi wata irin muguwar rama tayi baqi babu kwanciyar hankalin shafa man bleaching. Fiddausi ta kalli sakeena tayi tsaki ta fadi maganar da Kunnan sakeena be jiyo abunda tace ba. Sakeena data xama muguwar masifaffiya tun bayyanar aurenta da sageer ta dago ta kallesu tace "Fiddausi ko inxone? Naji kina qunquni, hauka maganinka Allah amma ku naga naku haukan maganinsa duka. Wlh baki isa kiyowa mijinki sata ya koroki ba kixo ki takuramun." Fiddausi ta nannado ashariya ta laftawa sakeena, Amina ta kamo hannun fiddausi cikin rada tace "ki kyaleta fa aljanu gareta saida tayiwa Hajjo duka wancan satin." Fiddausi ta hadiye yawun tsoro jin andaki Hajjo tasan sakeena ta riqa, ita kuma dama bata da qarfi sai cika baki. Sakeena ta kuma kallonsu tace "Kinsamawa kanki lfy da kikai shiru domin gidan ubanane nan,ba suruka bace ni yanxu haka kuma ba yar riqo bace in mutum yanason xaman gidan dole ya xauna lfy dani" babu shiri sukai hijira xuwa dakin Hajjo.
A gefe guda kuma mutanen da Hajjo taje gunsu sun sami Baba da maganar amma ya basu haquri. Hajjo fa rayuwa ta fara xafi ta rasa inda xata dole ta nufi gidan Zahra ta xana mata duk yacce akai kuma ta roqeta akan mijinta ya shiga maganar ko Baba xai yadda ta koma. Zahra hankalinta ya tashi tayiwa Hajjo zazzafar nasiha kuma tace sai tayi mata alqawarin ta daina duk abunda take sannan xata shiga maganar ita da mijinta. Hajjo ta wahala kwarai a kwanaki hudun da tayi a gidansu, dan haka da sauri ta dunga xabga rantsuwar ta daina komai. Zahra ta fadawa mijinta iya abunda xata iya fada masa a daren ya goyeta a bayan machine dinsa xuwa gurin surukinsa.
Baba sam beji dadi ba da Awwal mijin Zahra ya shiga maganar don yanason Awwal yaron arziqine wanda ya riqe masa Zahra mafi soyuwar ya a wajensa da amana. Ya dubi zahra tana kuka tana roqonsa ya rufa mata asiri ya maida Hajjo kodan darajarsu baxasuji dadi ba suga uwarsu na garari a titi kuma inya rabu da ita qara lalacewa xatai. Baba ya runtse ido yana tunanin aiko a lahira wani nacin arziqin wani Zahra a cikin yayansa xai iya cewa itace bata taba yimasa komai ba kuma tana binsa sau da qafa kamar badaga jikin Hajjo ta fito ba, Deni ke bin bayanta shi kuma ya bata rawarsa da tsalle akan sakeena. A taqaice yace musu suje xaiyi tunani xuwa gobe.
Washegari sai gasu da yamma hardasu dattawan unguwa da mai unguwar kansa da kuma qanin Baban Hajjo dan Babanta yaqi xuwa. Aka xube aka kwashe bayan dogon dauki ba dadi Baba ya maida auren Hajjo bisa alfarmar Awwal da Zahra amma ya gindaya mata wasu mugayen sharadai da suka hada da, Babu fita koda soro ne, babu xuwan qawaye ko dangi, babu ruwanta da iya da kuma sakeena, duk kuma abunda ya samesu ita keda alhaki sannan kuma a duk sanda ya kuma kamata da lefin xuwa ko kai dansa gurin malami a bakin aurenta, xata dunga girkinta a tsakar gida kicin kuma ya xama na Iya, abu na qarshe kuma bayaso yaji koda muryarta a tsakar gida.Hajjo bakinta na rawa tace ta amince. Baba ya qara jaddada mata duk abunda ya samu su Iya itace tace eh ta yadda. Limamin unguwar yayi mata doguwar nasiha ya sallameta. Zahra ta qara yiwa Baba godiya ta kuma roqeshi ya qara haquri xasu qara jawa Hajjo kunne.
Hajjo na shiga gida ta tari ruwa, taje tai wankan da rabonta dayi tunkan a koreta. Ta fito sukai karo da sakeena ta rakube gefe a tsorace sakeena ta wuce. Hmm duniya me yayi wai yau Hajjo ke tsoron sakeena 🤔 lallai abunda ya baka tsoro watan wata rana xai baka tausayi.
A ranar da Baba ya dawo da Hajjo kamar hadin baki da yamma sai ga Hadixa ragagaf ragagaf kamar tsohuwar rumfar kwano ta xube a tsakar gida kan tabarmar da su Hajjo ke xaune. Duk ta xuge ta qare babu wannan girmar jikin irin na Hajjo da sukayi gado, sai tsahonta daya fito kamar daren baqin ciki, fuskarta babu komi sai kwankwamemen hanci da shacecen baki kamar gate. Bata lura da yanayin su Hajjo ba da suke ciki ita da Amina da fiddausi kowacce damuwarta ta sakota gaba, ta xube gabansu ta fasa abunda yake damunta, kusan in abu na damu mutum neman wanda xai gayawa yake don ya samu sauki. Labari dai babu dadin ji a kunnen su Hajjo, wato Hadixa dai a fadarta wai tunda aka kaita gidan Yusuf a daren ya fara yimata tijarar cewa iyayenta qananan mutanene ya kashe kudinsa ya gina gida na kere sa'a amma ankasa koda yimata kayan daki set daya sai wasu tarkace kuma babu katifa wai to da aka kawota babu katifa a uwarta xai kwanta? Injishi yana tambayar Hadixa. Da gama fadar ya figo Hadixa daga kan kujerar da take xaune qudundune tana kukan gorin da dangin Yusuf din sukai mata. Ya watsarta kan tiles ya fada kanta yayi mata kaca kaca a cewarsa sadakinsa yake murewa dan baxai biyu babu ba.
Da safe kuma suka tashi da baquncin uwar mijin Hadixa wacce tace yan karbar amarya sun kai mata labarin tsiyar da iyayen Hadixa sukai na kawota da kayan wasan yar tsana a maxaunin kayan daki. Ta gallawa Hadixa harara bayan gama kallon kayan dakin tace da Yusuf ya tattaro kayan lefensa ta tafi dashi dominsu basa asara da sunsan baxa a rama musu kashe kudin da sukai ba da ba'a auri Hadixa ba, kuma ya nemi mata a gidan arxiqi me quruciya ya aura, ba irin wannan tsohuwar ba. Yusuf ya kaso akwatinan lefensa kaf daga kan sif ya kaiwa umma mota, Hadixa na kuka na cewa suyi haquri duk ta bada yawancin kayanta na gida dana lefe kawai ta dogara. Uwar Yusuf tace eh dole ki dogara da lefe dake ubanki ne ya siya da kudinsa.
Hajjo ta sauke ajiyar xuciya bayan gama sauraran Hadixa tace "To yanxu meya fito dake tunda kince tun washegarin kaiki akai haka?" Hadixa ta qara fashewa da kuka tace "Hajjo nagaji ne kullum sai ya durkamun kwayar tsarin iyali kuma ya kwana yana takuramun sannan jiya kuma yace in shirya muje gidansu mukaje shine ya kaini dakinsa na samartaka wai incigaba da xama a ciki, wai gidan daya gina be dace dani ba amaryarsa xai saka wacce xa'ayi bikin wani satin yar masu kudi kuma bai cemata yanada mata ba dan haka anan xanyi nawa xaman bani da kwana. Na haqura xan xauna saboda kar indawo gida aimun dariya kwatsam yau sai Ummansa ta shigo dakin tace na fito in shiga cikin rukunin ma'aikatan gidan in dunga aiki baxasu ci dani a banxa ba. Ni kuma shine na gudo wlh nagaji gara xaman gida akan wannan tsinannan auren."
Dariyar sakeena ta hana Hajjo maganar da tayi niyyar yi. Ta gama dariyarta taiwa Hajjo alamar jinjina 👍🏼 tace "Angaisheki uwar xaurawa shinyar Gwale LGA. an tattara an jabe babu dan kida balle dan rawa, Allah me iko inda ranka kasha kallo yanxu buhun shinkafar Baba xaiyi qasa tunda an saitowa iyayen mata hanya daga gidan miji. To wlh kar inji kar ingani domin xa'ayi tashin hankalin idan aka nemi takuramun ni da uwata, a lallaba a xauna lfy dani kafin xuwan lokacin tafiyata gidan masoyina Muhammad Sageer" jin an anbaci sunan Sageer Amina ta tashi daga kwanciya tana kallon sakeena kamar itace sageer din. Hadixa kuma a mamakance take kallon sakeena tace da Hajjo "Yaushe al amarin gidannan ya dame haka?" Hajjo bata bata amsa ba ta miqe ta shige daki.
Koda Baba ya dawo ya samu Hadixa da kuma abunda ke tafe da ita, takaici da baqin ciki yasa bece komai ba. Iya dai a gefe guda ta dage da yiwa Sakeena tanadin taryar me gida ita da Mama babarsu su Hassana wacce take kawo kayan mata irin nasu na manyan mata masu kyau da tsada Iya kuma ta tsaya tsayin daka tana bawa sakeena tana amfani dasu.
Sageer ma dai a gefe guda ya hada lefensa me tsari babu tarkace sai kaya masu tsada da aji da Bilki ta xuba ciki. Ya turasu Katsina gurin umma shi kuma ya maida hankali gurin gyara gidan da kuma canja komai na ciki aka fenteshi tas aka xuba kayan gado masu tsari a 2 bedrooms din gidan da falo sai kicin daya danqara kaya na garari ka rantse iyayen sakeena ne sukai kayan, ya tura tsofafin kayan can Katsina yace Umma ta bayar Iyayen sakeena sun turo anyi mata jere. Yace shi yana tafe wani satin xai taho da IV daga nan zaije Kano gurin sakeena.
Kowa yaga lefen a dangin sageer saiya jinjina Shafa qanwar sageer ta debi komai guda biyu tundaga kan turamen atamfa har xuwa kan takalmi da jaka da kuma cosmetics. Umma mace tagari me dattako ta kwabi shafa tace ta xubawa sakeena kayanta, ita lokacin da akai mata nata ko sanin sakeena ba aiba balle ta diba mata sannan tace batason haka ta kame kanta ta kyale sageer yayi rayuwa me dadi da yanci da matarsa ita batason irin haka abunda bakaso ai maka kada kayiwa wani shine xaman lfyar mutum.
****** **** **** ****** ***
Nuraddeen Lawan mijin Surayya a daren da akai masa abar qaunarsa sunsha soyayyarsu shi da ita, don dagashi har ita suna yunwar abun. Ya sameta a cikakkiyar mace amma fa akwai banbanci mai yawa tsakaninta da sakeena. Bayan komai ya lafa ta fara baccin gajiya shi kuma ya tashi ya jingina da allon gado ya buga tagumi. Tunanin randa ya fara sanin ya mace yake a rayuwarsa da kuma wacce ya fara hakan akanta sakeena. Ya tuno yanayin da yakasance ciki na shauqi da wani irin jin dadin da sai yanxu tabbatar da wuya ya kuma samun irinsa. Ya tuno yar qaramar yarinya sakeena a wancan dare yacce ta dunga yimasa kuka tana tureshi da kuma bashi haquri abun gwanin shaawa da burgewa, sabanin Surayya yanxu da zai iya cewa duk da ya tabbatar da budurcinta taxo amma ta fishi xaqewa a harkar. Tambayar kansa yake me hakan ke nufi wayewa ce ko rashin kamun kai? Ya qara xurfi cikin tunanin yadda ya samu qirjin surayya da qugunta a shafe ba kamar yadda ya gama kwadaitawa kansaba zai taba banxa, yayi mamakin haka ashe duk ciko takeyi. Ya qara tuno surar sakeena wacce tunkan ya aureta itace taja hankalinsa har ya kusa keta mata haddi. Kwanciyar Surrayya kan qirjinsa shiya katse tunaninsa tace "Deen tunanin me kake a cikin wannnan daren da yafi kowane dare mahimmanci a gurinmu? Ko baka sameni yacce kakeso bane?" tausayinta ya dan kamashi yace "Yi haquri Surry na sameki fiye da yacce na xata. Kawai dai banji dadin ganin kinyi ciko a guraren da nafi muradi ba a jikin mace wanda yin hakan kamar kin yaudarenine" ba tare da damuwa ba tace "Kayi haquri nayi hakanne don ina sonka kuma nasan da banyi ba da bamukai ga aure ba" yayi murmushin yaqe yace "Nima ina sonki, amma ai anashan magani su ciko ko?" ta tura baki tace "Nima naso insha Mumy ta hanani tace wai yanada side effects shiyasa na haqura na siyo na roba nake ciko" ta kwantar dashi ta kwanta a jikinsa tana qara fada masa yadda take masifar sonsa.
Da asubar fari yana shiga wanka ta dauki waya taiwa mumy babarta ta fada mata yacce sukai dashi ta kuma ce taga kamar ransa ya baci da hakan yana yimata fuskar shanu. Mumy tace xatayo mata aike ta fada mata yacce xatai amfani dashi a cewarta intayi yadda tace tofa itace mijin Deni matar. Adai ranar wajen 8 din safe Hajjo taiwa Deni waya dan tsabar hauka. Surayya ce a dakin lokacin shi yaje bakin gate. Ta dauka taga sunan Hajjo tai tsaki ta saka no din a black list. Tana da duk labarin Hajjo da kuma yadda ta takurawa sakeena ita dasu Hadixa a gurin wani abokin Deni, ta kafa doka kar abar kowa ya shiga gidan indai ba danginta ba. A cikin kwana uku ta maida Deni mijin tace da taimakon wani maganguna da mumy ta harhado mata kuma ta maida Deni mugun jarababbe da sai su shafe awowi suna abu daya, ita dake yanayin halittarta kenan hakan be dameta ba shine ya gaji sosai gashi babu fuskar yin qorafi. Surayya irin matan nanne yan i don't care, kuma tana mugun son Deni over shiyasa da quduri aniyar rabashi da kowa ya xama nata ita kadai. Bata komai a gidan na aiki komai masu aiki keyi sai dai ta caba kwalliya ta kame a falo suna kallo da kuma soyayya da Deni. Bata da rowa ko kadan kuma akwaita da fadar gaskiya duk dacinta, tana aiki a North West university a matsayin non academic staff.
Wannan kenan
Ranar asabar aka kawo lefen sakeena da safe anmusu tarya me kyau. Baba da su Dahiru yayyin sakeena ne suka amsa, aka shigo dasu gidan aka bude Hajjo dasu Hadixa suna leqe ta window Iya tace suxo sugani, ai kuwa sai gasu babu kunya sun fito. Lefe dai sai sambarka akwati shida har Kit bakwai kayane na garari fadarsu bata bakine. Maqota aka shishshigo ana taya Iya murna da yadawa Hajjo habaicin wannan lefe da gani gidan wadata da mutunci sakeena xata shiga. Aka gama aka watse akabar lefe a dakin Iya. Yayin da Amina kecan halin mutu kwakwai rai kwakwai.
Da yamma saiga Deni da Surayya sunxo gidan gaishe da su Baba kamar yadda Surayya ta umarta, hutunsu na amarci da suka dauka ya qare ranar Monday xasu koma office.
Hajjo taiji dadin ganin Deni wanda kullum da tunanin halin da yake ciki take kwana take tashi. Amma taji dadi data ganshi fes dashi ya qara girma yayi haske. Lokacin da suka shigo sakeena tana tsakar gida tana amsa waya daki babu network. Sukai arba da Deni qirjinta ya buga amma ta danne tacigaba da maganarta a waya. Surayya ta kalleta sosai ko baa fada ba tasan wannan itace sakeena ex wife din Deni. Deni ya qame guri guda yana more kallon sakeena dake sanye cikin jeans skirt da shirt. Hajjo tayo wajen daki jin muryar Deni. Ta tarar dasu tsaye dukkansu suna kallon sakeena, Surayya ta kalli Hajjo tace "wacece wannan Deni ke kallon ta?" cikin in ina Hajjo tace "Ummm haya suke a gidan nan sun kusa tashi saura sati biyu" Surayya ta kalleta shagarere tace "Ba sakeena bace ba? Meye na yimini qarya? Inma hayar suke meye na fada a gabanta wannan ai cin fusakane." sakeena ta cire wayar kunnanta tanawa surayya duban mamaki jin abunda ta fadawa Hajjo, ta kwashe da dariya ta nufi dakin Iya. Hankalin Deni ya dawo jikinsa bayan tafiyar sakeena, Surayya taja hannunsa tace "Taho mu shiga ciki Deen" suka kewaye Hajjo suka shige dakinta suka barta baki a sake.
Acan dakin Hajjo su Hadixa sun gaida Anty surayya kamar yadda suke kiranta cikin tsananin ladabi. Ta amsa tana murmushi da taunar cingam, Amina ce kawai bata gaidata ba tana kwance, ta kalli Hajjo tace "Hajjo mun yini lafiya?" da sauri ta amsa da cewa "Lfy lau Hajjaju makkatu kuna lfy ya baqunta da sabuwar rayuwa?" bata amsa ba tacigaba da danna waya. Deni ya gaida Hajjo ta amsa tana qorafin wata daya cur be nemeta ba ko a waya? Surayya tace "sai haquri Hajjo amarci muke, kuma ma meye abun damuwa dan kunyi wata daya kacal baku ganmu ba aure fa kukayi mana?" jiki a sanyaye Hajjo tace "Babu komai kam Haj Surayya dama a lokacin da nake neman nasa wata yar matsala nake ciki shine nakeson ya kamamun gidan haya in koma kuma har can gurin naku naje a lokacin aka hanani shiga" tace "ya kama miki haya kuma? Da wane kudin? Kuma ke yanxu banda rashin tunani in akace ki koma gida ke kadai saiki koma bakisan ana fama da in security ba?" Kowa ya bude baki cikin mamaki jin Surayya ta kira Hajjo da marar tunani. Deni ya gayyato qarfin hali ya dakawa Surayya tsawa yace "Ke! Uwar tawa kike kira mara tunani?" Surayya ta danyi dum jin kwabarta tayi ruwa tai saurin gyara kuskurenta takai hannu ta shafa sajen Deni tace "I'm sorry Deen kasan ni haka na saba magana, mumy bata hanamu, amma kayi haquri I luv u" bai wani dau mataki ba yace "it's ok"
Surayya ta kalli Amina dake kwance har yanxu tace "Hajjo ita wannan bata da lfy ne? Naga tun daxu take kwance" cikin sauri Fiddausi tace "wai saurayin sakeena takeso shi kuma baya sonta, har asaka musu rana da sakeena daxu ma ankawo lefe" Surayya ta washe baki jin matsalarta ta qare saboda jira take ta koma gida taiwa mumy waya a raba sakeena da xuciyar Deni, ashema wahala ta qare, shi kuwa Deni da sauri ya tambaya waye xai auri sakeena? Fiddausi ta bashi amsa da cewa "sageer kuma saura sati biyu bikin" xumfa ta wankeshi ya miqe yayi waje yace da Surayya xai je gurin friends dinsa. Tace "To karka dade." Ta kalli Amina tace "To micijiya wacce bata ramin kanta sai dai ayi ta shiga, ki xage ki nemi mijinki yadda kowacce mace take nema" ta juya gasu Hadixa tace "ku kuma ko ba a fada ba nasan xaman gidan aurenku ne babu dadi don gashinan jikinku ya nuna. Baya na suka (haqqi yana tambayarku) ni baxance ku koma ba, da ku koma da kuyi ta xama a gida duk daya a gurina amma wlh ku kiyayi kanku, ku kiyayi shiga shirgina da Deni dan ni ba sakeena bace tsaf sai in saka a qulle yarinya, kuma sannan ko hanyar gidana ban yadda kuyi ba don ba gidan Deni bane gida nane" daga su Hadixa har Hajjo kallon ta suke da mamakin wace irin riqaqqiyar mara mutunci Deni ya samo wacce ranar farko da taxo garesu take musu haka?
Bata jima ba ta shiga dakin Iya ta rikida ta koma mai tarbiyya da mutunci suka gaisa a mutunce tai mata murnar kawo kayan sakeena. Baba ya shigo tare da Deni ya bude daki suka shiga. Surayya ta kuma rikida ta xama me ladabin gaske ta gaida Baba uwa xatai masa Sujjada shima yaji dadin haka ta ciro turarurruka a jaka ta ajiye masa ya dunga saka mata albarka. Ganin daga dakin Baba xasuyi waje Hajjo ta kira Deni don akwai maganar da takeson fada masa tasu Hadixa ya bibiya a maidasu dakunansu, sannan tai masa complain din Surayya bata da tarbiyya. Yabi Hajjo daki kamar yadda ta buqata, ko fara magana basuyiba saiga Surayya ta biyosu ta riqe labule tace "Deen ina jiranka fa" cikin rawar jiki yace "To surry ganinan" Hajjo ganin babu yacce xatai ta hadiye qorafin Surayya da tai nufin fada tace "Dama cewa xan ka nemi Musa da Yusuf a taushesu su maida yarannan dakunansu tunda malam yanxu baya ta tamu yaqi shiga lamarin." Kafin yayi magana Surayya tai karaf tace "Akan me? Nawa Deen yake da xa'a fara dora masa lalurar gyara aure? Kowa ya iya allonsa ya wanke.Deen taho mu tafi" babu musu ya bita suka fito, ta sunkuya har qasa taiwa Baba da Iya sallama tace da Iya Dan Allah a sanar da ita lokacin biki, Iya tace mata ranar asabar ne ta sama xa ayi komai rana daya.
Hajjo ta koma daki ta dora hannu aka ta saka kukan nadama, to me hakan ke nufi? Ita dai yau ta fara ganin Surayya balle tace sakar mata fuska tayi har raini ya shiga tsakaninsu haka? Kuma ita kadai taiwa haka Baba da Iya duk a mutunce ta gaishesu. Bama wannan ba, meke faruwa taga Deni duk ya xama wani soko bashi da raayin kansa sai abunda Surayya tace? Hadixa ta dafata ta dago ta kantsa mata mari. Ta dafe kunci tace "Hajjo me nayi miki?" tana kuka tace "Wlh nagaji abubuwa sunmin yawa ku kunqi xaman aure bakwa duba ni kaina yanxu a rabe nake a gidannan, sannan ga yar uwarku tana neman haukacewa akan wanda besan tanayi ba shi kuma Deni ya xama mijin tace yana gani matarsa ta cimun mutunci amma ko uffan be ceba. Wayyo Allah na shiga uku baqin ciki xai kasheni." Duk suka dago suna kallon Hajjo. Ta rarumo wayar AV ta nufesu tana duka da cewa "ku hada kayanku kowacce ta koma gidan mijinta tayi haquri ta xauna nima ta kaina nake da wannan wacce ta xauce din (Amina) ta rarakosu har soro suka fice suna kuka. Ta koma ta wuce daki ta kwanta tana kuka. Daga Iya har sakeena da kuma Baba abun ya basu dariya sosai suka hadu suka dungayi.
Hadixa dai ta koma a sa'a domin anfara bikin Yusuf da sabuwar amaryarsa, don haka ummansa bata tambayi inda taje tai kwanaki ba tace ta xage ta shiga sahun masu aikin abincin biki, duk wanda ya tambayeta a cikin bikin yace ina uwargidan Yusuf kuwa sai tace dataji xaiyi aure tayi yaji tana gidansu. Sai ace ai dole tai yaji ko wata bata rufa ba anyo mata kishiya.
Ita kuwa Fiddausi musa ya tasa ta har shiyyar uwargida sarautar mata ta bata haquri harda durqusawa qasa. Cikin qasaita tace "Hmmm bakomi ai mutum baya fushi da me masa hidima, na haqura sai kici gaba da aikinki kamar yadda kika saba kuma banason sata ki kiyaye gaba. Abunda baki sani ba dukiyata Musa ke juyawa ta gado, munsha wahala tare kafin Babana ya mutu mekudin qauyene a raba mana gado na saida gonaki na na bashi kudin yake juyawa nake kuma bashi ladansa don haka keda shi duk a qarqashina kuke." Fiddausi ta kuma saduda ta saddaqar ta kawo kanta cikin bala'i a garin son auren hutu, ita kam Musa ya cuceta ya mata qaryar cewa dukiyarsa ce wadda ya tara da guminsa ashe kudin matarsa ne. Daga ranar ta xama itace meyin duk wani aiki na gidan har shirya yara xuwa school, bayan haka kuma bata da kwana sai dai da rana inya samu sauqin aikin kasuwa ya dawo yadan rage xafi a gurinta ko kuma ya faki idon Hajiya yaje gurinta kamar wata karuwarsa.
Haka sukacigaba da xama Hadixa cikin mulkin mallakar uwar miji, Fiddausi kuma cikin na kishiya.
********** ********** ****
Ara saura kwana 8 biki Sageer ya sauka Kano, yaxo da kwanduna shaqe da kayan gona wasu kuma kayan lambu hardasu fruit, dake shi dan gatan suruki ne fiye da kowanne suruki a gidan dakin Baba yayi masauki, Iya ta bata abinci ta kai masa da kuma kunun aya. Saida ya kimtsa sannan sakeena ta shiga, suna gama gaisawa taja bakinta ta tsuke, ya qaraci kallonta ya gama tayi kyau ta qara cika saboda shan maganin da takeyi da madara. Yace "Ga IV na kawo na daurin aure ke kuma bansan naki shirin ba shiyasa ban bugo naki ba amma ki fadan abunda xakiyi yanxu sai insa a bugo miki." tana danna waya tace "Ni babu abunda xanyi" yayi murmushi yace "To shikenan ga kayan fitar biki Bilki ta cire cikin kayan lefenki ta dinka miki, wannan kuma ga kudin hidimomin da xakiyi na biki" ya ajiye mata.
Baba ya shigo yana cewa "Sageeru wannan wahala haka fa ta isa, ko bakayi komi ba xamu baka sakeenatu tunda munyi alqawari." ya sunkuyar da kai yace "Baba ai ba wahala bace, wancan abun daga gonata ne nakawo a saka albarka" Baba yace "ashe manomi ne?" sageer yace "Eh akan noma nai degree na farko" Baba yana dariya yace "Da kyau, noma tushen arxiqi" haka dai suka gama hirarsu da Baba da Iya yayi salllama dasu ya tafi da sunan sai Friday xai dawo ana gobe daurin aure.
Shirye shirye sunci gaba, inda saura kwana biyar biki yan Baggadano suka kawo kayansu na gudummawar sakeena, Masara buhu biyu gero ma buhu biyu, sai jarkar mai mecin kwalba 35 guda biyu da garjejen rago da kayan miya harda busassu sukace a xuba mata a gara da kudi dubu goma. Iya tayi murnar wannan karamci da sukayi. Ganin haka ta shawarci Baba suka hada kudaden hannunsu kaf da ragowar na gurin sakeena da sageer yake bata da kuma kudin aurenta aka shaqo kayan gara tun daga kan hatsi har xuwa kan kayan xaqi har gurasa Iya tasa akai musu buhu guda, a cewarta tunda ba kayan daki xasuyiwa sakeena ba gara ayi mata gara akaiwa dangin sageer can katsina don a saiwa sakeena mutunci a idonsu.
Hassana ta dira Kano ranar talata bata wani jima a gidaba ta taho gurin sakeena dame gyaran jiki. Ta fara aikinta a take, xuwa yamma saiga jikin sakeena yayi qal dake farace har ya nuna ajikinta. Haka sukaci gaba dayi kullum Hassana ke xuwa da ita suyi xuwa dare su tafi ranar Friday ta kawo mata dinkunanta da mama ta diba ta bayar akai mata kuma ranar aka rangada mata qunshi hannu da qafa ana gamawa suka fice saloon. Ita dai sakeena abun ba wani dadarata yayi da qasa ba domin bason sageer take ba har wata rama tayi a yan kwanakin nan.
Su Amina da Hajjo dai ana daki duniya tai musu atishawar tsaki. Saddiq kuwa ya xage dashi ake komai har gida ya kaiwa Deni katin auren sakeena ya bawa megadi ya kai musu. Ranar jumaar da yamma Iya ta samu labarin xuwan dangin Sageer Kano don daurin aure da kuma mata domin karbar amanar sakeena kuma sun sauka gidan abokinsa. Ta shirya aka samo mota ita da Inna da wasu matan biyu da sukaxo daga Baggadano aka loda kayan gara shatara ta arxiqi aka nufi masaukin dangin sageer domin kai musu. Anxo tafiya kenan saiga Hajjo ta dakko mayafi xata bisu, Inna ta dakatar da ita tace "An gayyaceke ne?" Hajjo tace "Kema ainasan ba gayyatarki akaiba duk labarin mugun abun da kikaiwa sakeena yaxo min bakece matar ubanta ba wacce kika kashe Nura qaninta?" Inna tai dariya tace "Ai kinfini mugun hali domin ni bantaba silar batan dan mutum ba, amma duk da haka ban tsiraba da Allah ya tashi sakawa su sakeena xaluntarsu da nayi saiya hadani da makirar suruka kuma gida daya muke xaune taci ubana son ranta kuma Dan nawa wato mijinta baya ganin lefinta saboda batayi a gabansa. Daga qarshema saidata karyani garin duka da girmana da komai taimun duka na karye kana taimun tsirara kafatanin mutanen Baggadano dai dai kune basuga duwawuna ba ta wullani rijiya tace fadawa nayi tayi kururuwa akaxo a ka cironi bani da bakin cewa qarya take saboda babu mai yadda. Sai da nayi wata hudu ina jinya sannan na warke kuma ita ke jinyata tunda gidanmu daya. Dole na saduda na tsawar da makamaina na nemi afuwar wadanda na xalunta na kuma nemi shiri da ita domin ta fini iskanci da makirci. Me laya ya kiyayi me xamani. Dan haka kijira naki karshen nasan sai yafi nawa muni tunda kinfini tsula tsiya" Inna na gama fadar haka ta cangala qafarta da surukarta tai silar mayar mata da ita haka, tabi su Iya da suka fice. Tabar Hajjo baki bude cikin tsoro harta hango ta tana cangala qafa itama matar Deni ta ballata.
Acan gidan abokin sageer an tari su Iya da mutunci kunsan katsinawa babu magana wajen nan (su Anyt sis da maryam sani mani 😜) samari suka shigo da uban kayan gara suka dunga jibgewa Iya ta musu bayanin garar sakeena suka kawo saboda a jirgi zasu tafi ita da sageer babu dama a tafi da kayan abinci su kuma daganan babu me xuwa katsina shine suka kawo in yan daurin aure xasu tafi su juya da ita katsina.
Suka hau godiya da yaba bajintar su Iya. Yayar umman Sageer ta miqe ta kirawo su Baffan sageer a daya falon sukaxo harshi sageer din. Yaji dadi kwarai ganin haka don bayaso a raina masa sakeena suka dunga godiya aka kirawo Umma a waya aka fada mata ta dunga godiya tana cewa da Iya sunyi jere acan Lagos kuma sun kuma yin gara antadasu xaune tsaye saboda ansaka bikin lokaci kadan. Jikin Iya yayi sanyi tasan Sageer ne yayiwa sakeena kayan daki yace su sukayi. Ta qara yadda sakeena bata da masoyi a duniya kamar sageer. Sun rabu cikin mutunci.
Amina ta samu Baba a daren tana kuka tace "Baba ka yafemun duk abunda na biyewa su Hajjo mukai kuma Dan Allah ka roqi sageer ya aureni ko ata biyu ne, wlh ina qaunarsa kuma xanyi masa biyayya shi da sakeena baxan daga musu hankali ba na canja yanxu na rasa inda xansa kaina" Baba ya tusayawa Amina sosai yayi mata nasihar haquri da sageer kuma yayi mata nuni da wannan shine illar abunda sukai su da Hajjo sakeena na son Deni amma suka banqara suka dage suka rabasu yanxu gashi Allah ya jarrabeta da soyayyar da tafi ta sakeena xafi yayin da sageer bemasan tanayi ba. A qarshe yayi mata fatan samun miji nagari.
Sakeena sai kusan 9 na dare suka dawo daga saloon tai arba da yan Baggadano sun cika dakin Iya tai tsalle ta dire ta dunga rungumesu daya bayan daya suna mata dariya. Hassana tai musu sallama ta juya gida tace sai gobe da sassafe xata dawo. Kusan raba dare sukai suna hira Sadiya tasa sakeena gaba saidata cinye kaxar da akai mata tas. Iya ta bata rubutun ta shanye.
Suma basuyi bacciba kwana sukai soyar naman abincin gobe da kuma miya. Asubar fari aka kafa runfuna a kofar gida gari na wayewa saiga su Dahiru dukkansu sunxo daurin aure cikin fararen shadda sabuwa dukkansu iri daya sak sunyi kyau.
Gida ya fara cika yayin da sakeena gabanta ya tsananta faduwa sosai Hassana taxo tasa sakeena wanka ta tsantsara mata light makeup ta saka daya daga cikin kayan da sageer ya kawo mata a dinke ranar farin lace qal me taushi dinkin buba da xani wanda yayi mata das ya maisheta Fulani/Igala sosai. Kowa saiya yaba kyan da tayi. Surayya tai sallama ta shigo ta rangada guda cike da farin ciki ko dakin Hajjo bata kalla ba tai xamanta cikin yan uwan sakeena a falon Iya ta karbi a shoken da Hassana ke kici kicin nadawa Sakeena cikin few minutes sai gashi tayiwa sakeena nadi me masifar kyau ta rataya mata na kafada aka saki shewa. Hajjo ta fito dakin sanye da doguwar rigar shadda samfurin buhu tana kici kicin daura dan kwali ta dauki taliya da nufin ta taya su karyawa, matar Dahiru wacce itace ta saita Inna ta wafce tace "Koma daki bamu saki ba, daga ganinki akwai abunda kika fito yi na sharri yanxu hakama guba kika qullo xaki watsa mata cikin abincin tunda abaya kinyi yunqurin kashe sakeena baki samu nasara ba" ta daga murya tace "Na cikin daki ku fito ku cajemun makirar matar nan inaga gubace a qugunta a soke" dajin haka Hajjo taja doguwar rigarta ta koma daki. Surayya ta kwashe da dariyar iskanci.
Qarfe goma dai dai sukaji shelar daurin auren sakeena da Muhammad sageer ta cikin mic akan sadakin mota wacce sageer ya sai mawa sakeena tun farkon xamansu. Aka saki guda da kururuwar sakeena tayi goshi a dakin Iya ita kuma gabanta yayi wata irin bugawa amma ta daure ta furta "ALHAMDULILLAH" Deni da Surayya ta kawoshi gurin daurin auren domin ya sheda ya kuma qarasa cire sakeena a ransa ya xubar da hawaye. Saddiq ya matsa kusa dashi yace "Sakeena tayi kyakykyawan qarshe Allah ya bata me qaunarta da gaskiya" Deni ya bishi da kallo.
A cikin gida kuma ana sanarwar kammala daurin auren Amina ta yanke jiki ta fadi a sume. Hajjo tayi kururuwar a temaketa suka shareta wadanda sukai yunqurin temakawar ma Surayya tace suyi xamansu suman qarya tai saboda baqin ciki so take ta bata taron bikin. Baba ya shigo riqe da hannun sageer yana cikin farin ciki ya kama hannun sakeena yace "Sageeru ga sakeena nan amana ko bayan raina ka tuna amana na baka" ya damqe hannun sakeena qam yace "Na karba Baba kuma nayi maka alqawarin wlh baxanci amanarka ba" Baba ya kauce saiga Deni a tsaye a gurin idonsa jajur yana tuna kwatankwacin wannan rana da Baba ya bashi amanar sakeena shima yayi alqawarin riqewa amma bai cika alqawarin ba. Surayya ta matsa jikinsa tana nuna masa su sageer tana cewa "kallesu Deen yadda suka riqe juna so romantic" tana lura da yanayinsa amma ko ajikinta. Aka dunga photo da wayoyi da kuma cameras sakeena na jikin sageer wanda ya hade acikin wani farin yadi qal me rasha rasha duk da bata sonsa yayi mata kyau sosai, shi kuma sai qara rungumarta yake anai musu photo. Surayya ta ciro wayar Deni daga aljihu tayiwa su Sakeena hotunan kana ta mayar masa taja hannunsa suka tafi ba tare da yaga uwarsa ba balle gaisheta. Aka gama photuna sosai na farin ciki sannan Sageer ya tafi shida abokansa.
Wani yayan sakeena mai suna Iro ya shigo ana cikin hutuna wanda yake sakonta ne yace "Ke sakeena shegiya ai naga tsohon mijin naki da kika nacewa har ana xagin Babanmu akansa inbanda ke banxace meye kikagani ajikin wancan me qirar yan ta'addan wani gansansan dashi? Har uwarsa na xagin babanmu ai wlh da a lokacin anfadamun abunda tayi da sai nasa kokara na baje shegiya itadin banxa ta xagi Baba wacce illa gareshi har ake cewa baki da usuli duk ke kika jawo da kika laqewa shegen dannata" Sageer ya qunshe dariyar jin ankira Deni me qirar yan ta'adda ya riqo Iro yace "Yi haquri yaya Iro ai maganar ta wuce" yace "Ai wlh sageer da bata aureka ba da babumu babu ita"
Ancigaba da shagalin biki wanda ya tara jamaa fiye da xaton Iya, sakeena tayi shiga ta alfarma sosai. Yayin da Hajjo ta yini daki tunda taji ana xancen saka kokara a maketa, ko fitsari a baho suke ita da Amina. Da magrubar fari saiga dangin sageer mata sunxo daukar sakeena xuwa gurinsu can masauki ta kwana acan kamar yadda umman sageer ta umarta.
Su Inna suka shirya sakeena cikin sauri duk da baxata abun yaxo musu. Aka tafi da ita tana kuka. Acan masaukinsu sun karbi amanarta hannu bibbiyu suka budeta aka dunga yaba kyanta. Wadanda suka kawota suka juya akabarta gurinsu. Sageer jin ankawo ya shigo abokan wasa suka tasashi gaba da tsiya dole ya fita yana shafa sumarsa, shida a niyyarsa a bashi abarsa suje dakin da yake amma kuma a duk sanda ya tuna sakeena bata sonsa jikinsa kanyi mugun sanyi.
Suka kwana suna riritata da alamar diyar kanawa ta samu karbuwa gurin katsinawan Dikko. Da sassafe sukai wanka suka fara shirin tafiya, shima sageer suka shirya don jirgen 10 xasubi xuwa Lagos.
Abokinsa ne ya jasu xuwa gidan Iya don yimusu sallama da diban kayan sakeena bayan sunga dagawar yan katsina. Aka dunga fita da kayan sakeena ana lodawa a motoci harda wasu kayan girki da Iya ta hada mata. Baba ya kuma yimusu nasiha sosai Iya sai hawayen rabuwa da sakeena take. Baba ya danqa mata key din motarta da sageer ya bayar jiya. Sukaxo fita daga gidan sakeena tana kuka tace da yan rakiyar da suka rakota waje "yanxu babu wanda xai rakani har Lagos din kamar bakwa sona? Inya siyar da nifa?" Sageer yana dariyar abunda tace yace "Kinga kuwa kanki xaiyi mugun kudi" aka saka dariya jin ya maida abun wasa har iya abun ya bata dariya. Suka rabu ana waving juna motar ta nufi airport.
Xamu hadu ranar Sunday in shaa Allah
Hajia 😊
[8/5, 9:55 PM] Zongo Gal: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣4⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
SAQON NA MASOYA NE 💌
Assalamu alaikum, inawa dukkan masoyana fatan alkhairi a duk inda suke a fadin duniya, wanda muka hadu da kuma wadanda Allah be hadamu ba. Saqonku na samuna ta ko'ina kuma inajin dadi da kuma qara samun kwarin gwuiwar yin rubutu. Masu bugomun waya da masu yin text da kuma masu bina PC duk ina godiya. Sannan Dan Allah masoyana masu gayyatata xuwa grps Dan Allah kuyi haquri ban cika xuwa grps ba saboda wasu dalilai da baxan iya bayyanawa ba, amma dai nasan dukkan abunda mutum yayi ko yakeyi akwai dalilinsa nayin hakan, rashin kuma xuwana grp baxai rage komai na soyayyar da nake muku ba. Daga qarshe ina qara jaddada muku babban dalilina na rashin yin daily post saboda uxurin aikin gida da kuma kasuwancin amma bawai jamuku rai nike ba kunsan baxata yiwu ace mutum bashi da aiki ba sai danna waya. Nagode kwarai ina sonku ina qaunarku a duk inda kuke. Muna tare 🤝🏽 godiya ta mussanman ga ZAUREN BIEBEE ISA
(HAJIA ce 😊)
Xaune cikin jirgi amarya da angonta wato sakeena da sageer kusa da juna, sageer kallon sakeena yake idonsa taf da soyayyarta tayi shar cikin yellow colour super wax (Sheraton) ta yafa veil shima yellow ya kai idonsa kan yatsun hannunta da suka sha jan lalle da baqi sunyi kyau kamar da qunshin aka haliccesu. Ya kai nasa hannun ya riqo yatsunta yace "Sakeenatu" ta dago ta bude masa manyan idanunta akansa tace "menene?" yana murxa yatsunta yace "kiyi haquri a wancan auren da mukai na xarge akan abunda bani da sani akai, lokacin bansan kin taba aure ba, ki yafemun kinji my luv" ta fusge hannunta ta dubeshi tace "OH! Ka dauka nima yar iskace irinka? Ko kaxaci na manta kai dan bariki ne wanda karuwarka har duka taimun?" ya sunkuyar da kansa cikin kunya da nadamar rayuwar barikin da yayi. Jiki a sanyaye yace "Kiyi haquri sakeena tunda na aureki har xuwa yanxu ban qara sha'awar rayuwar bariki ba wacce nai a baya ma ina nadama da neman yafiyar ubangiji" ta juya tacigaba da duba magazine din data gani gurin shi kuma yacigaba da aikin kallon ta.
Sun sauka lfy ya dauki taxi har xuwa unguwarsu, saida suka shiga cikin unguwar sannan sakeena ta dubeshi tace "Sageer baxan xauna a gidan da kayi xaman haramci da niba saboda haka kodai ka canjamun gurin xama ko kuma in gudu garinmu." Sageer ya fara duban a tsorace cikin rawar baki yace "A a baxaki tafi Kano ba akan canja muhalli ki bani 1 wk xan canja gurin xama, badan yanayin aikinmu ba ma da saina kama daki a hotel xuwa lokacin da xa a samu gidan, ki kwantar da hankalinki baxanyi abunda bakiso ba amanarki na karbo" bata qara magana ba ta hade rai, me taxi din ya shiga har cikin gate din gidan. Sageer ya bude kofar falo ta shige tai xamanta akan kujera tana kada qafa, tabarshi da kici kicin shigo da akwatinan ta. Tana qarewa gidan kallo daga xaune da gani an narka kudin wajen gyarashi ko fentin da akai abun kallo ne.
Ya gama ya dan dawo kusa da ita ya xauna, yana magana ta shareshi. Can dai ya miqe yace "Bari naje na fara qoqarin samo gidan ko?" tace "Better" ya fice ya shiga gidan Maitama don ya fada masa sun sauka.
Yana fita ta miqe ta fara xagaye gidan tana jinjina tsarinsa duk da ba wani girma gareshi ba. Kicin din yayi kyau an shaqare shi da kayan amfanin kicin saiya tuna mata da xamanta a gidan Alh Dalhatu. Ta ciro waya ta kira Hassana tana fada mata sun iso, Hassana tace mata ita sai gobe Monday xata dawo. Daga kicin bedroom ta nufa wato na sageer inda sukai rayuwar wancan auren, ta kwashe kayanta daya shiga dasu ta mayar dayan domin baxata hada daki dashi ba, sam ba haka taxo yiba. Bata shirya kayanta a sif ba tunda tashi xasuyi ta jibge akwatinan ta miqe a gado tai kwanciyarta.
Acan gidan Maitama bayan an gaisa da kuma bangajiyar biki Bilki ta bawa Sageer manyan warmers data xuba musu abincin da tayi dominsu tace ya tafi dasu. Ya dubeta yace "Ni ba komawa xanyi ba dan bawa maid dinki ta miqawa sakeena kafin na dawo don nasan tana tare da yunwa" Maitama yana karatun newspaper ya dago yace "kaito ina xaka ko hutawa bakai ba?" Direct yace "Sakeena ce tace batason xaman wancan gidan shine xanje nemo gida ko na haya ne da xamu xauna kafin inyi shirin siyan wani" Maitama ya zare glasses din idonsa yana duban sageer da mamaki, kafin cikin bacin rai yace "Sageer ka shiga taitayinka wlh, wannan bare baren da kake akan sakeena baxai haifar maka Da me ido ba. Duk kabi ka susuce ka haukace akanta kamar baka taba sanin ya mace ba sai ita, wai dama irinku wadanda basu taba soyayya ba in sun tashi yinta haka sukeyi? Yanxu inka tashi daganan da muke da yawa mu hausawa da kuma security kasan inda xaka koma? Ka kuma san yanayin aikinmu koda yaushe ana iya farmakar rayuwarmu kota iyalanmu? Meke damunka ne sageer akan wannan qanqanunwar yarinyar ka xauna tana juyaka yadda taso? Tun randa sakeena ta dawo hankalinta baka qara hutawa ba, duba lokacin datayi miscarriage yadda daga fada maka ka dauki mota xaka tafi kano a lokacin badan mun hanaka ba da tuni ka rasa ranka tuntuni. To wlh babu inda xaka canja dole ka xauna anan tare damu, sannan ko ka xama shugaba a gidanka ka saita sakeena ko karkayi duk daya kai xakasha wahalar xama da ita inta sangarce. Ita kuma yanxu xanje insameta dan ubanta inji in irin tarbiyyar da aka bata kenan?"
Sageer ya tare gaban Maitama yace "Babu ruwanka da harkar gidana ko ni ina maka katsalandan akan familyn ka?" Maitama yana dubansa da mamaki yace "Sageer macece xata hadamu dakai?" yace "Eh sai ta hadamu din bakasan yadda xuciya take ba intanason abu?" Maitama bece komai ba ya kewayeshi ya fita. Sageer ma ya bishi da gudu. Bilki ta dauki mayafi ta bisu da sauri karsuyi batacciya tasan mijinta da xuciya.
Maitama ya riga sageer isa gidan saboda a xuciye yake, ya tsaya falo ya kwallah sakeena kira. Tana tsaka da bacci kiran ya risketa ta farka a furgice tayo falo, ta sunkuya xata gaida Maitama ya daga mata hannu yace "Riqe gaisuwarki, wai ke wace irin fitinanniyar yarinyace? Wace irin xuciya gareki mara sanin darajar masoyi?" dai dai lokacin sageer da Bilki suka qaraso Maitama be saurara ba yacigaba da magana "Meye laifin sageer dan kawai yana sonki kike wahalar dashi? Kinsan akanki ya kusa rasa ransa kuwa? Kinsan dinbin sadaukarwar da sageer yayi miki kuwa wacce kika sani da wacce baki sani ba? Menene na tsiro da maganar sauya gida yanxu? Shin kinsan rayuwar Lagos kuwa? To bari kiji ni nace baxa'a canja gidanba, nasan bakinsan matsayina ba a gurin mijinki ba ko? To ni childhood friend din sageer ne wanda yau akanki yakeso ya manta amintakarmu. Wlh sakeena ki shiga taitayinki don baqaramin aikina bane in miki dukan tsiya akan wannan abunda kikeyi. Sannan daga qarshe inna kuma jin wata maganar banxa makamanciyar wannan ta taso saina buga waya na fadawa iyayenki inji in irin tarbiyyar da sukai miki kenan" sakeena dai tunda Maitama ya fara magana kuka takeyi wato sageer qararta yakai gurin abokinsa kenan ko? Amma maganar Maitama na cewa xai buga waya gidansu ya fada duk tafi daga mata hankali.
Ya juya ya fita, Sageer rai a bace ya rufa masa baya. Bilki ta riqo sakeena suka xauna kan kujera ta fara lallashinta, saida taga tayi shiru sannan ta bata haquri da cewa "Kiyi haquri da abunda mijina yayi nasan ya tsallake iyaka ya shiga fadanku, amma kema sakeena da lefinki menene naki na cewa sageer ya canja miki muhalli? Dubi gidannan yacce ya gyarashi ya saka komai sabo saboda ke amma daga xuwanki kice baxaki xauna ba? Xaman Lagos ba irin xaman Kano bane kuma yanayin aikinsu yana da hatsari sosai xaku iya canja guri abiku a kasheku ke da shi, nan kuwa munada cikakken tsaro. Kiyi haquri nasan bakyason sageer tsohon mijinki kikeso amma wlh sakeena bantaba ganin inda namiji keson mace yacce sageer yake sonki ba, banga lefin sageer ba Kamar yadda banga dalilin qiyayyarki gareshi ba babu abunda ya rasa daga kan kyau har xuwa kan kudi sannan yana da haquri da kuma kirki. Illar sageer daya ce Bariki kuma wlh tunda kika shigo rayuwarsa ya dena. Kiyi haquri ki karbi mijinki ki kwantar da kai kuyi rayuwar aure me dadi tun kafin yan matan Lagos su janye miki shi" Bilki ta saka sakeena dole ta tuttusa abincin data kawo musu ta kuma tayata shirya kayanta a sif da kuma kayan girkin da Iya ta bata a kicin harta dibawa Bilki. Sai kusan ukun rana ta tafi, sakeena ta qara komawa ta kwanta cikin tsanar sageer da kewar Iya.
Sageer yana xaune gurin a bencin megadi, fada sosai sukai da Maitama akan abunda yayiwa sakeena suka rabu rayuka a bace. Ganin fitowar Bilki ya tashi ya koma ciki gabansa na faduwa,
Dakinsa ya nufa inda yakai kayanta daxu, sai dai ya tarar wayam babu komi ta kwashe kayanta. Ya fito ya shiga daya dakin, ya sameta kwance tana danna waya. Jin motsin shigowarsa ta tashi xaune ta qanqance ido cike da masifa tace "Sageer ashe qarata kakai gurin abokinka ko? Wai yaushe ne xaka fuskanci abunda kalmar qiyayya take nufi? Dan Allah Sageer ka gwada xama da wanda bakaso koda na awa daya ne kacal kaji yadda akeji saika kwatanta da yadda nakeji akanka" jikin Sageer yayi tubus da kalamanta, ya fara tunanin anya be xalunci sakeena na ba da ya aureta bata sonsa? Ya juya xai fita yace "kiyi haquri xanje induba gidan yanxu" bata tanka masa ba ya fice.
Tana kwance sallah kawai ke tada ita daga gurin, yayin da Sageer keta garari a garin Lagos cikin rana daga gurin wannan dillali xuwa gurin wancan anata nuna masa gidaje wasu gidajen basuyi masa ba wasu kuma sunyi masa amma unguwar area boys sunyi yawa. Dole ya haqura bayan sallar Isha yagaji tiqis ga yunwa, ya tsaya masallaci yayi sallah ya sayi gasassun kaji da madarar roba ya nufi gida. Acan kuma sakeena bayan sallar isha taje tayi wanka tayi shafe shafenta ta dakko daya daga cikin rigunan baccin lefenta ta sakata me siririn hannu wacce ko gwuiwarta bata qarasa ba. Garin ya hade yayi murtuk anata iska koda yaushe ruwa na iya sakkowa. Ta fice harabar gidan ta xaga baya ta xauna kanta ko dankwali babu, ta rasa abunda yake mata dadi, duk duniyar dundum take jinta garin Lagos da duk abunda ke ciki duk ta tsanesu a dalilin Sageer ta rasa inda xatasa ranta taji sanyi ta rasa ta yadda xata farason sageer da kuma rayuwa dashi, inama ace Baba wani ya aura mata kowanene data haqura tayi masa biyayya. Ta fashe da kukan tausayin kanta da kuma qiyayyar sageer, yanxu gashi tun rana ya fice ya barta ita daya a gida kamar mayya (haba sakeena ba ke kikace ya samo gida ba, ke baxaki xauna ananba? 😜) ruwa ya sakko kamar da bakin kwarya tana xaune yana jiqata tana kukanta.
Sageer ya shigo gidan ya tadda bata a falo yayi zaton tana cikin bedroom. Ya bude warmers din dake kan dinning yaga an taba abincin ciki ya sauke ajiyan xuciya yasan sakeena taci abinci kenan. Ya xauna shima yaci abincin saboda yunwar dake sakadarsa tun breakfast din safe rabonsa da abinci. Ya gama ya dauki ledar kaxarsa ya shige nasa dakin don yayi wanka yaje ya kaiwa sakeena kaxarta ta amarci. Yayi wankansa irin na angwaye ya fesa turaruka masu sanyi da qamshi mai tsuma xuciyar ma'abota soyayya, shi dinma sabbin kayan bacci ya saka ya dauki ledarsa ya nufi dakin sweet heart sakeena.
Hankalinsa yayi mugun tashi daya gama kewaye falon xuwa kicin da daya bedroom din amma babu sakeena, ya fara tunanin to ina taje ana sheqa ruwa haka? ko gidan Bilki ta shiga? Wata irin faduwar gaba ta sameshi daya tuna kalamin sakeena na cewa koya canja mata muhalli ko ta gudu garinsu, to kotaga shiru be dawo ba ta gudu Kano? Ya watsar da ledar Hannunsa yayi wajen falon da sauri yana kiran me gadi. Ya taso jikinsa na rawa ya duqa gaban sageer, cikin rawar baki yake tambayarsa madam ta fita ne? Yace "A a babu wanda ya fita a gidan nan" ya sauke ajiyar xuciya ya xagaye gidan cikin sauri. Yaci karo da sakeena a bayan gidan cikin bishiyoyi xaune ruwa na dukanta ido jajur fuske cike da hawaye ta qanqame jiki alamar sanyi takeji yace "Subhanallah, sakeena in wani abun ya cijeki fa?" yasa hannu ya dauketa ya shige ciki. Dakinsa ya nufa da ita ya kwantar a kan gado sai rawar dari take, ya kunna room heater ya dawo ya cire kayan jikinsa da suka jiqe saboda nemanta ya canja wasu ya dawo ya fara kicin rabata da rigar jikinta ta riqeta gam ta hanashi yin hakan. Yayi mamaki wai sakeena ke boye masa jikinta ta manta lokacin da suke wanka tare wataran ma shi yake mata, yayi murmushi yace "cire miki xanyi saboda ta jiqe kuma ana sanyi" batace komai ba ya cire mata rigar yayi matuqar daurewa da kai xuciya nesa da ganinta haka ya danne kwalamarsa ya dakko shirt dinsa yasaka mata ya kwanta ya rungumeta tsam yana sakin ajiyar xuciya. Haka sukai baccin da suka dade basuyi me dadinsa ba.
Da wuri ya tashi da safe yayi duk abunda xaiyi na aikin gida yayin da gimbiya sakeena ke kwance tana bacci tunda daga idar da sallar asuba, yayi breakfast ya ajiye mata kan dining ya fita xuwa aiki. A office ya yini tunaninta a gefe guda kuma wadanda basu samu damar hallartar aurensa ba sunata xuwar masa murna. Ya dunga kiran wayarta taqi dauka yaji sam hankalinsa ya gaxa kwanciya a daddafe yakai lokacin tashi ya nufi gida.
Yana murda qofar falo ita ya fara gani sanye cikin riga da skirt na atamfa tana kallo, ya sauke ajiyar xuciya da Hamdala a tare ya tako xuwa gabanta yana kallon kwalliyar data caba a fuskarta da kuma daurin data kashe, ya lumshe ido a xuciyarsa tunani yake donme Maitama ke ganin lefinsa dan ya mace a soyayyar sakeena? Duk wani abu na sakeena abun sone da burgewa ga kwalliya da tsafta kuma akai dace jikinta me saurin amsar kwalliyar ne. Yaji wani abu na fuzgarsa xuwa gareta, ya saka gwuiwowinsa a qasa ya tsuguna gabanta ya riqo yatsunta yakai bakinsa ya sumbata yace "Barka da gida ranki ya dade, anyini lfy?" ta xare hannunta tana dubansa fuska a hade tace "Sageer ka shiga hankalinka da ni, indai kanason xaman lfy ka daina kai hannunka jikina" ya hadiye yawu be shirya ba jin wannan qaton sabon da sakeena tayi, to ta yaya hakan xata yiwu? Ta katse masa tunani tace "in kuma kanaganin hakan baxata yiwu ba ka iya maidani garinmu ko kuma kaje ka fadawa Maitama yaxo ya tsireni" da sauri yace "Duk abun bai kai haka ba, jiya ma da yaxo wlh bani na sakashi ba kuma na nuna masa bacin raina akan hakan da yayi" ya tashi ya shige daki ya kintsa jikinsa ya fito ya nufi table, ya saki wani irin murmushin farin ciki dayayi arba da food warmers da tarkacen kayan cin abinci ya juyo yace "My luv har girki kikayimun? Nagode kwarai Allah yayi miki albarka" ba tare data kalleshi ba tana danna waya tace "badon kai nayi ba, kuma inka kuma yimun godiya na denayi" yaja bakinsa ya tsuke ya hau dining ya kwashi tuwan semo miyan danyan kubewa yaci yayi nak ya dunga yabawa iya girkin sakeena a xuciyarsa. Da akaxo kwanciyar bacci dakinta ta shige ta barshi a nasa yana rungume da filo. Da safe ma ya tarar tayi breakfast kuma ta ajiye masa amma banda haka babu abunda tayi a gidan ko ganinta beyi ba balle ya samu arxiqin koda gaisuwa ce, yaci abincinsa ya fita yana driving yana tunani sakeena ta nuna xata dunga girki basai ya dakko kuku ba amma kuma dole ya samo maids kodan tsaftar gidan tunda yau ko tsinke bata dauke ba a gidan.
Cikin kwana biyu saida gidan ya hargitse don shine ke gyarawa kuma ba wani iya gyaran gida yayi ba, aikinta kawai girki inta gama shikenan. Arana ta uku sai gashi da masu aiki su biyu, dayar yarinyace wacce yace xata dunga wanke wanke da shara kuma zatazo tun safe sai yamma xata tashi. Dayar kuma yace sunanta Inna anan xata xauna a dakin dake wajen falon xata dunga lura da komi na gidan, sakeena batasan alaqarsu ba tadaiga yana girmamata suna ta hira da alama akwai tsohuwar sannayya tsakaninsu, shiya dauki kayanta ya rakata dakinta. Wannan shine mafari, daga xuwan Inna gidan ganin sakeena ma yayiwa Sageer wahala sai dai tai girki ta ajiye masa intaga dama in kuma iskancin ya motsa sai dai ya siyo ko kuma Inna tayi. Sageer ya fada cikin wani irin yanayi na kewa da azabar qaunar sakeena da so samune koda ganinta ta dunga bari yanayi. Yayin da ita kuma bata da aiki sai dai tai wanka tayi kwalliya tayi chatting inta gaji tayi kallo ko kuma suyi waya da Iya da Baba ko Hassana. Alaqarta da su Inna masu aikin gidan ba wata alaqar arxiqi bace qarqari su gaisheta ta amsa ko kuma ita ta gaida Inna tunda ta kusa jika da ita, bata sake musu fuska ko kadan domin ta dawo daga rakiyar yiwa mutane kirki bayan haka kuma tayi alqawarin duk wanda ta sani ta silar sageer baxaiji dadin xama da ita ba. Shi kansa sageer din saita kwana biyu bata ganshi ba yo kullum tana daki a kulle saitaga bayanan take fitowa falo ko taje kicin sau tari xaixo yana buga kofarta yana cewa dama yanaso ya gaisheta ne yaji ta kwana biyu shiru. Bata tanka masa sai dai ya qaraci bugunsa da magana ya haqura ya tafi.
Tana da 17 dayx a Lagos aka kirasu jarrabawar Post UTME, Sageer ne yaxo mata da xancen, albarkacin hakan ranar ya ganta bayan shafe kwanaki 3 ko giftawarta be gani ba. Ranar jarrabawar shiya dauketa da kansa ya kaita venue din ya xauna jiranta har tayi ta gama ya dawo da ita. Xaman banxa ya gundureta tunda bata saba ba, ta fara tunanin abunyi ta samu aya ta gwada kunun aya na rabin kwano ta xuba a robobin ruwa, da kanta ta kaiwa Bilki tace gashi ta fara sana'a. Bilki tai murna dake tasan darajar neman nakai, itace tasa me aikinta ta nunnuwa matan cikin quarters din, a cikin awa daya sai gashi an siyeshi tas ana nema, washegari tayi na kwano guda, kan kace meye wannan shima ya qare, a kwana na uku tayi na kwano biyu kuma ranar ne Sageer yasan anayi, ya dawo ya tarar da yara a falo sakeena tana sallamarsu da robobin kunun aya. Abun ya bashi dariya da mamaki yace "Bakanuwa kenan, kanawa akwai neman kudi." ta hade rai don karya kawo mata raini tacigaba da karbe 50 naira ahannun yaran tana basu robar kunun aya. In taqaice muku xance dai cikin sati daya sakeena ta xama hajiya me kunun aya domin abu ya kankama data qiyasta kusan kullum tana siyarda na 3k in kuma ba'ayi ciniki ba 2500 xuwa 2800 duk yawansa intayi saiya qare har dare xuwa ake nema xaman banxa ya qare yini take aikin kunun aya da kuma sallamar masu xuwa siya.
Sageer dayaga abun ya kankama saiya ware guri a harabar gidan ya kewaye mata da langa langa akayi rufi saboda ruwa akayi wearing ya saka mata qatuwar freezer ya daukar mata me aiki wacce take tayata aikin da kuma miqawa masu siya in sunxo yake biyanta a aljihunsa. Domin abun ya burgeshi batasa girman kaiba ganin mijinta me kudi ne kuma bata damu ya bata ba ita kawai nata take nema (mata mu dage da neman na kanmu kodan gudun wulaqancin maxa, ba lallai sai kinsamu aikin gwamnati ba koda kina da ilimin ko babu koda aikin gwamnati ko babu ki nemi Sana'a duk qanqantarta karki raina wata rana xata bunqasa indai kin jure) Cikin wata guda da fara sanaarta saidata tara kudin da ita kanta batasan yadda akai sukai yawan haka ba, ta ware wasu ta qara jari wasu ta ajiye ragowar kuma ta turawa sageer ta banki tace ya bawa Iya. Iya tayi murnar jin sakeena harta saki jiki ta kama Sana'a a xatonta xaman kwarai suke da Sageer din tunda duk sanda sukai waya ta tambayeshi cewa yake qalau suke xaune.
Ana cikin haka wata matar abokin su Sageer ta haihu ana neman me kwalliya wacce xataiwa me jego ran suna Bilki tace sakeena ta iya. Ranar suna aka kira sakeena bata bawa Bilki kunya ba ta rangadawa me jego make up, yayi kyau aka dunga yabawa gashi baya damewa saboda kayan kwalliyarta babban products ne. Daga haka shikenan duk sanda abu ya tashi a cikin matan abokansu sakeena ke musu kwalliya a biyata, kudin casual daban na amarya daban kuma batasa kudi da yawa ba shiyasa take ciniki. Shima sageer ya samu kwarin gwuiwa idan suna taro a office xaice matarsa na kunun aya ya karbo mata kwangila a biyata kudade masu tsoka tayi kuma ta karbe babu ko godiya. Cikin qanqanin lokaci sakeena ta tasarwa xama Hajia (amma fa bani Hajian ba danni bani da ko sisi 😄) Iya da Baba na kano suna mata adduar rabuwa da sharrin masahassada da yan black stomach, wadanda bakasansu ba baka damu da suba amma su ka tsaya musu a maqogwaro (Allah ka rabamu da sharrin mahassada, Allah ka hana mu cutar, Allah ka hana a cutar damu, Allah kuma ka hana abiyo takanmu a cutar da wani Aminnn) Sakeena tana tsaka da samun kudi jarrabawarsu ta fito kuma taci jamiar da sageer ya nemar mata ita ta samu, wata private university sageer ya cike mata a Lagos wacce cikin qanqanin lokaci mutum xaiyi karatunsa ya gama babu strike, ta yayan manyan qasar ce, yawanci duk wanda ka ganshi cikin jamiar tofa ubansa ko sponsor dinsa hannunsa ya cudi baya. Ya cire maqudan kudade yayi mata registration wanda saida account dinsa ya girgixa sosai, amma be damuba burinsa ya cika burin abar qaunarsa sakeena kuma yanada yaqinin baxata bashi kunya ba xatai karatun ka'in da na'in
******** ***** ******* *******
A can Kano kuma gidan mal Lawan Iya ta kama sana'ar Kunun aya da pure water wanda sakeena ta kafa ta qanqame hannu bibbiyu kuma babu lefi ana samu sosai kumai yana tafiyar mata dai dai ita da mijinta, tuni ta koma islamiyyar da rashin kwanciyar hankali ta hanata xuwa a baya komai yana tafiyar mata yacce takeso ita da Baba sai kewar sakeena da suka kasa sabawa da ita. Saddiq ma Iya ta masa fadan xaman banxa ya fara xuwa kasuwa yana xama a matsayin yaron shago kamar yadda Deni keyi abaya.
A bangaren Hajjo me duniya kuwa (🤣) al amura sun gama damalmale mata sun kuma chabe, da farko dai girkinta daban takeyi ita da Amina domin Baba bayacin abincinta kamar yadda ya haramta mata shiga dakinsa kuma baya kula al amuranta, saboda xaman banxa da rashin sana a da takeyi saiya xamana girkin nata yaxamo lami. Domin Baba ba qarfi gareshi ba inya sayi kayan abinci kuma ya bawa kowacce kudin cefanenta tofa shikenan, Iya takan cika kudi a jakarta tayi girki na alfarma ya cika gidan da qamshi suci ita da mijinta da dan kallo Saddiq bata qara shishshigin bawa Hajjo komai ba tun randa tace mata ta wuce ta temakamata saboda yayanta yanxu sun sami madafa kowa ya kama gabansa. Iyafa yanxu ta wuce raini ta girmi Hajjo ta wuceta katakau ga sana'arta sannan ga aiken sakeena da take yomata na kudi kusan duk bayan sati biyu ta account din Saddiq. Saboda haka Hajjo tayi tsumuuu ita da Amina kullum suna daki suna shaqar qamshin girkin Iya gasu kuma da kafirin kwadayi. A gefe guda kuma tana mamakin dauke qafar Deni daga gidan gaba daya rabonta da ganinsa tun ranar bikin sakeena data jiwo muryarsa daga tsakar gida, ta gama haqiqancewa Surayya ce ta mallake mata Deni ta rabata dashi gaba daya ko ganinsa ba'ayi balle ya taimaka. Sannan ga Hadixa tana cikin baqar axabar uwar miji da mijin kansa kusan kullum sai Hadixan tayo mata waya tana kuka tana fada mata itafa xata taho gida ta gaji Yusuf tunda yayi aure be kuma waiwayarta ba sai da yayi 5 weeks cur kana yaxo gurinta yana xuwa ya fata pills na family planning yace tasha, duk sanda ya bata tasan abunda yake nufi dan haka taqi sha ya nada mata duka kuma yasata dole tasha ya fada kanta yayi kwanciyar wulaqanci da ita a qaramin dakinsa na gidansu taji jiki kwarai saida yajishi yaje linta sannan ya dagata yace "Karki xaci wai sonki nake ko wani testing kike dashi, a a kawai dai ina buqatar canji ne kinsan in mutum yaci kaxa na tsahon sati biyar yana buqatar ko tuwon dawa ne ko kuma gabxa yadan surka." ya tasata suka fito ta gaida matarsa har qasa da sunan yar aikice ita sannan ta koma tai jinyar durxar da Yusuf yayi mata, daga wannnan rana kuma kullum inya tashi aiki ko in xai tafi saiya biyo ta gurin Hadixa wacce bata da kwana sai wannan xuwan kuma baya xuwar mata saiya bata pills tasha acewarsa karta dau ciki ta haife masa irin tsiya wato Hajjo, in kuma ya gama ya biyota da baqaqen maganganu, kuma daya abun takaicin shine koda tana cikin aiki kuma ko agaban waye har mahaifiyarsa inyaxo hannunta kawai yake danqa ya jata keee yayi daki da ita kowa yasan abunda yake mata don sau tari suna jiyo ihunta amma babu wanda ya taba magana. Hadixa ta fita hayyacinta ta sare da rayuwar duniya ta fara nadamar da bata da amfani, jarabar Yusuf da bautar da ita da uwarsa keyi ya saka duk jijiya ta fito a jikinta rudu rudu kamar batacin abinci har mamaki take dama maxa haka suke ko kuma Yusuf ne yayi mata lumbu lumbu yayi amfani da kwadayinta na son auren mekudi ya aureta? A duk sanda ta fadawa Hajjo halin da take ciki sai dai tace "Kiyi haquri Hadixa tunda basa barinki da yunwa, ni yanxu anan har horon yunwa akemun ga dan uwanku ko waiwayata bayayi" Hadixa kan fashe da kuka tace "Hajjo to meye abinci inbabu kwanciyar hankali? In Yusuf ya kashemun mahaifa fa?" Hajjo dai sai haquri don babu yacce xatai itama ta kanta take.
Bangaren Fiddausi dai abun da sauqi-sauqi wai naushi a ido, domin ita tunda ta yadda ta xama baiwar Hajiya uwargidan Musa ta xauna lfy intagama aiki har turata ake taje ta dan huta kafin lokacin wani aikin, ana cikin haka ta samu ciki a satar hanyar da Musa yakeyi yana xuwa gurinta. Ranar da cikin ya bayyana sunga jalala gurin Hajiya domin sasu tayi agaba kamar ta kama kwarto da karuwa tana tambayar ya akai Fiddausi tayi ciki tunda bata da kwana? Musa cikin tsoronta yace "Nima bansani ba, domin ba cikina bane ta fadi inda ta samo" Fiddausi cike da tsoron sharrin da Musa yake shirin yimata tace "Wlh azim nasane Hajiya shiyake xuwa gurina in bakyanan ko kuma inbashi da aiki a kasuwa har tsire yake siyomin yana bani inci kafin yayi" Hajiya tai dariya ta gyara xama ta harde qafafunta akan kujera tace "Au ashe amanata kuke ci ko? Ga banxa mara wayo ta baxa dukiyarta kuna ci kuma kuna ha'intata, ai wannan xaku iya kasheni ma, dole in dau mataki da nufin yimuku warning don gujewa fadawa tarkona anan gaba. Musa, Fiddausi ku kiyayeni wlh bani da mutunci ni kaina tsoron kaina nake in nayi wani abun." matakin da Hajiya ta dauka akansu shine burge cikin Fiddausi dan 4 months data gayyato wani likita yayi har gida, Fuddausi tasha wahala ta jigata kamar baxatai raiba ta dunga shatatar da jini amma Hajiya tana xaune tana kallo ko ajikinta a cewarta ma cikin shege ne tunda ba'a nemi ixininta ba kafin ayi shi. Ta jiqa xobo ta dunga durawa Fiddausi a matsayin abunda xai dawo mata da jinin data xubar (wai dama xobo yana dawo da jini? 🤣) Kwana uku Fiddausi tadan watstsake daga azabar kwakwule cikin da akai mata amma tayi fari qal alamar babu wadatar jini a jikinta kuma aranar Hajiya tasa ta karbi aikinta babu tausayi.
Shi kuma musa nasa hukuncin shine lafta masa uban aiki a kasuwa wanda xaiyini sur yanayi ta inda bashi da lokacin kansa ma balle ya tuna wata Fiddausi ko da dawo gida ma a gajiye yake kwanciya yayi ta baccin gajiya ko ita Hajiyan baya iya tabuka mata komai balle Fiddausi. Daya matakin kuma shine cire masa duk wani tallafi tunda har yana samun na siyawa Fiddaausi tsire. Da wannan ta rufe qofar alaqar cin amanar Fiddausi da musa (a fadarta) sai dai ya hangi giftawar Fiddausi intana aiki a sashin Hajiya. Kuma dake muguwar shedaniya ce ta Kai Fiddausi gurin teacher aka rufe mata bakinta babu wanda take iya fadawa halin da take ciki balle aimata temako sannan tasakawa qafarta kwado ko shaawar fita daga gidan batayi, babu abunda ta sani sai bautar Hajiya kwatan kwacin irin bautar da sakeena taiwa Bahijja matar Bar Adam, Fiddausi dai yanxu ko Allah bata tsoro yadda take tsoron Hajiya.
Saddiq kuwa har kullum godewa Allah yake da ya farkar dashi da wuri ya dawo daga rakiyar Hajjo kafin rayuwarsa ta watse kamar ta sauran yan uwansa.
Hajjo dai ta rasa yacce xatai yayan da takeso take taqama dasu duk sun watse kowa ya kama gabansa yana fuskantar matsalar abokin xama ita kuma gata a jabe a gida ita da Amina wacce bata da cikakken hankali yanxu saboda rasa Sageer, babu aikin komai sai baqin talauci wanda ko 5 naira din pure water gagararta take, ta fara nadamar barin sana'arta da tayi ta saida gasara, haka kawai ganin hadari yasata wanka da kashi, daganin Deni ya samu aiki ta dena saboda danta yayi kudi tafi qarfin saida gasara, gashi yanxu yayi auren jari ya cika burinta amma matar ta janyeshi. Bata da mataimaki yanxu sai Saddiq wanda bawani abun arxiqi yake samuba a kasuwa sai kuma Zahra da take shafe kusan wata guda bata leqo ba. Ana cikin haka tasamu 500 daga gurin Saddiq da yasamu yan kudi, cikin rawar jiki ta sayi gero tayi gasara ta aika maqota aka fada ta dawo dayin gasara. Abun dariya dai gasara tai kwantai bata siyuba domin Hajjo ta xama mujiya acikin matan unguwar tun akan xuwa kotunsu dasu Laraba, mutum biyu ne kawai suka shigo siya suma kuma yar mata da magana sukayi da habaici da cewar "A a uwar Alh Nura surukar Haj Surayya kuma gasara aka dawo siyarwa? Ya akai aka haihu a ragaya?" qarshe dai gasara dai doyi tayi aka wanketa. Hajjo ranar har kuka tayi don baqin ciki, Amina dataga tana kuka itama ta farayi suka hadu suka dungayi babu me lallashin wani. Ala Dole ta miqe qafa taci gaba da xaman kashe pant sai dan abunda Saddiq ko Zahra suka bata. Yayin da Iya keta fama da arziqi.
Bagaren Deni kuwa da amarya Surayya abun suma sai a slow, domin Deni tun ranar daya sheda daurin auren sakeena da Sageer kuma yagansu rungume da juna ana musu photo ya nemi kwanciyar hankali ya rasa, daya abun takaicin Surayya ta dauki wayarsa tayi status da pics din Sakeena da Sageer na aure wanda ta dauka da wayar tasa aka dunga tayasu murna da fadar dacewarsa wasu friends dinsa da sukasan ya taba auren sakeena suka dunga yaba daqiqancinsa na rabuwa da ita, shi sai a lokacinma yasan abunda Surayya tai, cikin sauri ya goge hotunan ya kuma rufeta da fada, bata damuba tace "I'm sorry darling, i luv u" yayi tsaki shi wannan hali nata ya fara damunsa babu dama tai abu ya nuna bacin ransa sai tace masa "I luv u" Kamar batasan abunda kalmar ke nufi ba. Duk da ya goge nasa hotunan be tsiraba domin Saddiq kullum cikin yin sabon statuz yake da hotunan nasu kuma yanayine saboda Deni, gashi shi kuma kamar dole inyatashi saiya duba status din saddiq. Daga haka wata masifa ta aureshi babu dama ya kwanta sai yayi mafarkin sakeena rungume da sageer, ya rasa inda xaisa kansa kullum sai yayi mafarkin kamar ibada, ya xama wani irin mugun masifaffe wanda masifarsa sam bata damun Surayya domin inyanayi sai taita dariya kamar taga sabon kamun hauka ko kuma taita danna waya, inyagama tace "I LUV U DEEN" aikinma ba wani maida hankali yake akaiba donma Allah yasa ya gama karatu da baxai iyashi ba a wannan halin da yake ciki. Inya fita tun safe baya dawowa sai dare, yaxo ya tarar Surayya wacce ta dawo tuntuni daga nata aikin ta caba kwanlliya masu aiki sun gyara gida kuma sunyi abinci wanda hakan baya burgeshi sam.
A cikin wata uku da aurensa da Surayya yayi matuqar gundura da xama da ita saboda wasu halaye nata kamar rashin damuwa dashi da kuma al amuransa indai ba a shimfida ba, tana kulawa da shimfidarsa kodan biyan buqatarta bayan haka kuma babu ruwanta da komi nasa, to ita kanta nata al amuran masu aiki ke matasu. Ta bangaren kwalliya kam babu matsala xai iya cewa a iya wannan xaman nasu na wata 3 betaba ganinta babu makeup ba ko kwanciyyar bacci xasuyi saita caba kwalliya, ta wannan banqare kam Surayya ta samu excellent, takan kashe kala qarshe yawanci tafi saka qananan kaya intana gida, natives kuma sai xata fita. Intasaka qananan kayan kuma da sunan kwalliya Deni kanji takaicin ya rufeshi musamman inya kalli busashshen qirjinta da kuma qarmasassun cinyoyinta da bayanta wanda dasu tayi ciko ta jashi ya aureta, yakanji kamar ya rufeta da duka saboda kayan basa qara mata komi sai qara fito da munin halittarta. Surayya doguwace mara rama wacce datana da cikar halittar qirji da qugu xa ai irin matannan masu cikar halitta da kuma tsaho da kauri (irin halittar Deni) amma saboda rashin wadancan abubuwan dana lissafa saita xama doguwa sololo kamar namiji (ina ruwan sangal modi🤣) intayi shigar takan tuna masa da sakeena wacce yake tuno hips dinta cikin wandon jeans, ya lumshe ido wanda hakan kesa Surayya taita karairaya a xatonta burgeshi tai, ingaji da haukan lankwasar da take da sunan yanga yaja tsaki ya bar mata gurin. Bayan wannan komi masu aiki keyi har gyara gadon baccinsu, har xuwa kan wankin undis dinsa da nata. A tsarin Surayya babu inda masu aiki basa shiga a gidan koda suna kwance takan iya kiran maid ta miqo mata ruwa ko wani abun daban, da kansa yayiwa kansa fada yana tsince undis dinsa yana wankewa domin da kunya maid taga qazantarsa. Baxai ce da Surayya qazama ba duk da masu aiki ke mata komi domin xakajita tana musu tsawar su gyara nan su gyara can ita batason qazanta, sannan duk da bata shiga kicin tana sakawa ayi abincin da koda babu dadi to da tsafta. In kuma bata raayin cin abincin gidan takanyo order akawo mata har gida suci ita da Deni. Xuwa wannan lokaci wato wata uku, kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta, kuma gishiri ya fara sauka daga kan kaxa a tsakanin Surayya da Deni don haka magungunan mata da take amfani dasu wajen mallakarsa basu cika tasiri akansa ba ga kuma qarin damuwar sakeena datasaka Deni ya kuma burkicewa amma dake Surayya bata cika damuwa akan abuba bata lura ba balle ta farga da wuri.
Ana tsaka da hakane office dinsu suka debi xaqaquran ma'aikatansu don turasu wani cox a head office dinsu dake Lagos. Kuma cikin sa'a akai dace sunan Deni yana ciki. Ranar ya dawo cikin dare kamar yadda ya saba a yan kwanakin nan. Tuni Surayya ta kwanta bacci kamar yadda ya xata. Ya kimtsa yayi shirin bacci yaje dinning area ya saka tuwon shinkafar da akai a matsayin dinner amma ko loma biyu beyi ba ya rufe ya tashi duk kuwa da yunwar da yakeji, dalili kuwa shine tuwan ya jiqe cakaf ya narke kamar ba a daren akayishi ba wanda hakan ke nuna anmaka masa ruwan sanyi bayan antuqa shi. Ransa ya baci ya nufi bedroom yana tunanin girkin sakeena lokacin da suke tare duk da suna cikin baqin talauci amma duk randa suka dan samu damar yin girkin maneji takan yishi cikin tsafta kuma me dadin gaske kamar girkin da aka kashewa kudi. Ya kuma jan tsaki dayaga Surayya kwance cikin wata yar ficiciyar rigar bacci wacce ta qara fito da rashin qirarta, ya tabbatar da ajikin sakeeena yaga wannan rigar saiya kusa rasa hankalinsa saboda kyan da xatai mata. Ya qarewa Surayya kallo a jikinta fatartace kawai me kyau sai fuskarta suma kuma albarkacin mai ne ka kuma makeup. A fili yace "Me ake da mace irin wannan marar fasali wata dokekiya da ita kamar doki? wanda ko ni da nake namiji kuma dogo ta kusa kereni. Ai mace madaidaiciya itace mace kaita cilla abarka sama kana cafewa kuna wasan soyayya kamar sakeena" Ya nemi guri ya kwanta cikin tunanin yadda xai dawo da rayuwarsa ta baya, ya yadda koda xai rasa aikinsa amma su dawo rayuwarsu shida sakeena cikin wannan room nd falo din. Ya kasa baccin ya xauna ya jingina da allon gado ya dakko tabar sa daya siya yake busawa a yan kwanakin nan in tunanin sakeena ya sakoshi a gaba, ya xaro guda daya ya kunna ya fara xuqa yana fesar da hayaqin cikin tunani da shauqin sakeena. Warin sigarin ya tashi Surayya daga baccin da take, ta tashi ta dora kanta a kafadarsa ta xare tabar dake hannunsa a tunaninsa hanashi sha xatai tunda bai taba sha a gabanta ba, amma ga mamakinsa sai yaga Surayya tayiwa tabar wata kyakykyawar xuqa ta fesar da hayaqin ta hanci da baki cike da kwarewa. Ya qare waro ido yana dubanta yana kuma tuna ranar da sakeena ta fara kamashi yanashan taba yacce ta raxana ta rude kuma tayi yunqurin hanashi. Cikin mamaki yace da Surayya "Dama kinashan taba ne?" tayi murmushi tace "A a shisha kawai nakesha itama sai nasamu flavourn da yayimun dadi" yayi saurin kwace tabar da taketa aikin xuqa ya murjeta cikin ash tray na kan bed side, shi dinma ya fasa sha tunda yanxu bashi da gata babu sakeena a kusa me sonsa wacce xata hanashi, ya tabbata in zaisha abunda ya wuce taba Surayya baxata hanashi ba sai dai ta tayashi ya gurbata rayuwarsa da shaye shaye.
Ya kwanta yana cigaba da tunaninsa, Surayya ma ta biyoshi ta kwanta akan qirjinsa tana cewa "Deen tundaxu naketa kewarka baka dawo da wuri ba har nagaji nai bacci, I LUV U" kalmar da Deni yafi tsanar yaji surayya ta fada kenan, domin tun tana fada yanajin dadi harta gundureshi saboda yawan fadar da takeyi kuma a guraren da bai dace ba harya fara tunanin Surayya batasan maa'nar kalmar "I LUV U" ba ta fara shafar sumar qirjinsa kafin daga baya ta haye masa ruwan ciki. Yasa qafa yayi wancakali da ita, yace "Haba kin dameni, ke babu abunda kika sani sai aita kwanciya dake? Ko cewa akai miki wannan ita kadaice soyayya ko kuma auren? Baki gajiya kamar sex machine kedai kullum burinki a danneki, tun abun yanamun dadi harya fita akaina ya salance ya gundureni aita abu daya kamar cin tuwo" ya tashi a xuciye ya fice a dakin ya banko mata kofa, Surayya ta bishi da kallon mamaki.
Yana tsaye a veranda riqe da karfen da aka kewaye gurin dashi yana kallon harabar gidan da haske tayar gurin shiru alamar kowa yana bacci ya fara tunanin abunda xai fishsheshi duk fa wannnan masifar da wannan damuwar baxata kaishi ba domin wacce yakeyi akanta sakeena bata san yanayi ba, kuma indai yana buqatar dawowar farin cikinsa da walwalarsa tofa kawai ya dawo da sakeena cikin rayuwarsa, amma kuma tayaya? Ya qara xurfafa tunanin maganganun mutane da suke cewa bason sakeena yake ba yaudararta yake, wanda ya tabbatar da masu fadar hakan sun fahimceshi ba dai dai ba, to asakama hakanne abunda suke fada yaudararta yake acan baya ko kuma sha'awarta yake, to yanxu dai lokaci yayi da yaji yana mugun son sakeena fiye da komai a rayuwarsa, bayan zamansa da surayya ya fuskanci tarin baiwar da ex wife dinsa sakeena keda ita, inta tabbata yaudarar sakeena yayi abaya yanxu kam reshe ya juye da mujiya domin yagano kansa ya yaudara ba sakeena ba tunda gashi ita yanxu tayi aure tana gidanta cikin kwanciyar hankali shi kuma tabarshi da tunaninta da kuma bitar xamansu na baya.
Gashi dai ya samu mata me kyale kyale fiye da yadda ya dade yana buri, amma kuma ya gaxa son Surayya koda rabin son da yakewa sakeena ne, a wannan lokacin ya gano materialistic luv (soyayyar kyale kyale) yake yiwa Surayya yayin sakeena kuma itace true nd first luv dinsa. Da qarfi ya dunga fadin "Sakeena ban yaudareki ba, kaina na yaudara dana kasa gane kece true luv dina, wlh ina sonki bani da wani jin dadi inbabuke a rayuwata, na shirya rabuwa da komai da kuma kowa in xauna dake ke kadai" ya fashe da kuka kamar qaramin yaro ya samu guri ya takure yana tunanin mafita.
Abunda ya fara xuwa ransa shine sakeena tana sonsa fiye da komai a rayuwarta kuma ya tabbata a rashinsa sakeena ta auri sageer, lokacin yayi da xai kwaci abarsa, ya tuno tafiyarsa Lagos next week kuma sakeena a Lagos take, abu na farko da xaiyi shine fara samo number sakeena domin su farfado da tsohuwar xuma. Da wannan tunani ya samu sauqi da kuma kwarin gwuiwa.
Ranar asabar da wuri ya tashi ya shirya be kula breakfast din da akaiba a gidan domin ko Surayyan yanxu saita qure yake mata magana. Ya saka me gadi ya shiga store inda aka jibge kayan garar Surayya ya fito masa da komai buhu biyu su taliya kuma komai kwali biyu da su jarkar mai aka xuba masa a bayan mota ya shiga ya nufi Gwale gidansu wanda xaije ne da nufin samo digits din sakeena wanda albarkacin hakan suka samu arxiqin wannan kayan abincin. Dake da safe ne ya samu Baba a gida kuma direct dakinsa ya nufa, ya tarar Iya ta kaimasa abinci kenan ya shigo. Al majirai suka dunga shigo da kayan da yaxo dasu, ya tsuguna ya gaishe da Baba ya amsa fuskarsa a sake har yana tambayar lfyr surayya. Deni yace "Baba ga kayan abinci nan asaka mana albarka" ya dakko 20k din daya ware ya ajiye a gaban Baba. Baba yayi murmushi yace "A a ka riqe arxiqinka mal Nura, nikam bani da buqata gaisheninma da kaxo kayi nayi arziqi kuma nagode sosai, ai kana gani rashin xuwanka bai rageni da komai ba, inaci inasha cikin ni'imar ubangiji, uwarka ce ke buqatar temako saika kaimata" Deni da damuwar rashin sakeena ta sakoshi a gaba ga kuma sabon abu Baba na fushi dashi kawai saiya saka kuka. Baba da Iya suka tsaya suna kallonsa. Ya matsa jikin Baba ya kwanta yana cigaba da kukan yace "Baba Dan Allah kayi haquri nasan namaka ba dai dai ba tun akan rabuwa da sakeena amma tun kafin aje ko ina nafara gane kurena, duniya taimun xafi narasa inda xansa kaina inji sanyi" Baba yayi shiru yana shafa kan Deni kukansa ya taba masa xuciya sosai, yana son Deni domin a kansa ya fara samun haihuwa bayan shafe tsahon shekaru yana nema, kuma yasan duk abunda ya faru koda da lefin Deni to be xuce kasa haquri da daukan qaddarar da Allah ya dorawa sakeena ba. Cikin sanyin jiki yace "Babu komai Nuraddeen haka Allah ya shirya kai da sakeena iyakar xamanku kenan gashi cikin qanqanin lokaci kowa ya samu abokin rayuwa. Ka dunga addua kuma ka qara haqurin xama da iyalinka domin be xama lallai taimaka irin biyayyar da sakeena tai maka ba duba da gidan data fito" Deni ya jijjiga kai cikin yadda da maganar Baba kuma cikin xuciyarsa yana cewa "Baba xamanmu da sakeena be qare ba domin saina qara xabaro xuciyar sakeena munyi aure mun haifa maka jikoki. Yace "Baba inka haqura to ka karbi abunda na kawo kasa albarka" yace "To Nura na karba Allah yayi muku albarka" ya dauki kudin kuma ya kira Saddiq yace ya dauki komai guda daya akai dakin Hajjo daya kuma dakin Iya. Deni ya juya ya gaida Iya, itama cikin sakin fuska ta amsa tana tambayar surayya da gajiyar biki. Ya dakko 10k ya bawa Iya amma qiri qiri taqi karba tace "Inna karba kam na maka mugunta Deni ban nemi komai na rasa ba sakeena bata rageni da komai ba, kayan abinci dai tunda malam ka bawa na karba" jikin Deni yayi sanyi ya tabbata in akwai wanda xai kawo cikas a komawar aurensu da sakeena to fa Iya ce. Baba yana jinsu bece komai ba, ya saka Deni ya wanko hannunsa suka karya da ruwan Lipton da pancake.
Bayan sun gama ya nufi dakin Hajjo, tana jin shigowarsa ta tashi ta qura masa ido, shima kallonta yake cikin mamakin yadda duk ta xube yace "Hajjo ciwo kikai ne?" bata bashi amsa ba sai kwanciya da tayi a cinyarsa ta saka kuka, ya tausaya mata sosai uwa uwace koda kuwa mahaukaciya ce. Cikin kuka tace "Deni duniya ce taimun xafi rayuwa ta juyamun baya, mutane basa sona kowa ya tsaneni ku kuma yayana kun kama gabanku ko waiwayena bakwayi" yana share mata hawaye yace "Yi haquri Hajjo ai gani na dawo" ta dago tace "yan uwanka da sukai aure babu wacce take cikin kwanciyar hankali ga kuma wannan (ta nuna Amina) ta xama kamar xararriya saita yini batai magana ba sai kallon hoton sageer a waya" ya dan hade rai yace "Hajjo ki dainamun xancen su Hadixa domin wlh na tsanesu tunda suka xugaki kuka rabani da sakeena, duk abunda xai samesu su ya shafa da suka samuma aka auresu duk mugun halinsu. Ita kuma Amina xan kuma sai mata jamb tayi intaci shikenan inbataci ba tayiwa kanta, dan ubanta angaya mata soyayya qarya ce ba ganinmu suke mahaukata ba lokacin da mukeson juna ni da sakeena, gashinan Allah ya jarrabeki kiji yadda mukaji." ya ciro 10k ya bawa Hajjo Amina kuma 2k, suka dan taba hira da Hajjo wacce duk qorafi take akan baya xuwa da kuma abunda Surayya tai mata, ba abunda ya kawoshi ba kenan dan haka ya solata ya bata haquri yace xai dunga xuwa. A gidan ya yini kuma yayi sa'ar kwafar digits din sakeena cikin wayar Baba a lokacin da Baba ya shiga wanka. Cikin farin ciki ya nufi gida da daddare bayan sunci tuwon Iya kwano daya da Saddiq kuma ya bawa Saddiq din 10k kuma yace masa gobe yaxo can gidansa ya karbi wasu kayansa daya ware xai bayar.
********** ****** ********
Acan Lagos kuma sakeena me kunun aya angama registration da komai, ranar da xata fara xuwa school Sageer da kansa ya kaita bayan sun shirya shi da ita, tai shigar mutunci cikin zani da rigar atamfa da lulluba mayafi aka, a motarta suka fita shi yake ja tana gefe sunyi matuqar kyau sun dace da juna, suna tafiya yana nuna mata hanya har suka shiga cikin jamiar. Sakeena ta ware ido cike da qauyanci tana kallon wata qaramar duniya a matsayin university din da xatai karatu ciki. Lallai sageer ya kashe kudi daganin wannan jamiar sai dan wane da wane. Sukai amfani da time table dinta sukaje venue din da xatayi lecture, ya nuna mata ajin wasu daliban har sunxo sun shiga ta juya ta kalli ajin nasu yayi matuqar haduwa kamar ba lecture room ba. Ta juyo tana kallon sageer da shima ita yake kallo tayi murmushin farin ciki ta sanya hannunta cikin nasa tana murxa yatsunsa suna kallon kwayar idon juna ta fada jikinsa ta rumgumeshi yayi seqeqe yana jin sakeena a jikinsa kamar a mafarki, ta dago ta faki idon dai daikun mutanen gurin ta manna masa kiss a lips dinsa tace "tanxz alot" tayi cikin ajin da gudu tana daga masa hannu. Sageer ya suma na wucin gadi kafin ya farko ya shafa lips dinsa gurin da sakeena ta sumbata ya saki murmushi yace "u'r welkum my luv" yana tsaye yana kallonta ta nemi guri ta xauna ita kadai, ba jimawa malami ya shigo ta maida hankalinta kansa tasaka glasses dinta. Sageer sai lokacin ya juya ya tafi cikin wani irin mugun farin ciki. A office ma kowa yasan yau yana cikin farin ciki, haka ya yini shafa gurin da lips din sakeena suka sumbata yana murmushi. Lokacin tashinsu yanayi yaje daukarta, itace take jan motar yana gefenta yana qara nuna mata hanya tana kuma bashi labarin lectures da sukai cikin xumudi, abunda ya tabbatar masa sakeena tana son karatu sosai.
Cikin 1 week din tada fara lectures kullum sageer ke kaita yana qara nuna mata hanya, in sungama kuma yaje daukarta ta tuqo motar yana qara lura da yanayin tuqin nata, wanda wannan xuwa makaranta shiya saka kusanci tsakaninsu ta fara sakewa dashi, ya kame kansa be xaqe ba, itace ma wani lokacin take riqe hannunsa in tana bashi lbarin school.
Bata fasa kunun ayarta ba kullum da daddare takeyi Sageer yana tayata aikin don lokacin me aikinta ta tafi gida. Shike taya ta durawa a jarkoki da shiryawa a freezer. Sunayi suna hira, in sun gama ta dakko littafinta abunda bata ganeba yayi mata bayani, xuwa goman dare kowa ya nemi makwancinsa. Ita kuma me aikin intaxo itace me siyar mata da kuma wanke robobi da surfa ayar wanda xa ai gobe takai markade kafin sakeena ta dawo. A cikin sati na biyu ta fara fita da kanta xuwa school kuma cikin nasara taje lfy ta dawo lfy sageer yana mata tafi wai hannunta ya fada a driving ya qara kusanci da ita yana ganin nan gaba kadan xata manta qiyayyarsa su fara soyewa.
A kano kuma Deni sati yana xagowa ya hada kayan tafiya, ranar juma'a yajewa su Baba sallama da cewa office dinsu anturashi kudu wani course na 3 months, bai fadi garin da xasuje ba balle xargi ya shiga. Sukai sallama ya jiqasu da kudi har Hajjo ya toshe qofar complain. Ranar asabar da safe, ya loda kayansa duk a motarsa ya shirya cikin qananan kaya saboda a mota xai tafi, a taqaice yayiwa Surayya bayanin anturashi Lagos wani aiki a office dinsu xaiyi 3 months. Ta cukumeshi tana cewa be isa ya barta nan ba ita kadai, ya banbare hannunta daga jikinsa yayi waje yana mata dariya. Ta biyoshi da gudu har ya shiga mota tana cewa xai ganta Lagos a duk sanda ta binciko inda yake domin baxata xauna ita kadai ba babu me biya mata buqata har na 3 months. Yaja motarsa ya fice tana ta ihunta na kiran "Deen Iuv u"
Ya dauki hanyar Lagos cike da nishadi da nufin xuwa course amma ainihin abunda ya qudure xaiyi a cikin wata ukun nan shine farauto xuciyar Star Sakeena kamar yadda ya rada mata yanxu, yayiwa kansa alqawarin baxai dawo ba saida gud news din mutuwar auren sakeena da kuma komawarsu soyayya. Suxo su tunkari kowane irin qalubale ne qarshe a daura musu aure kamar wancan Karon. In yaji yagaji da tuqi saiya dubi number sakeena da yayi saving ya sumbata sai yaji qarfin gwuiwa ya shigeshi dan haka baiga nisan tafiyar Kano xuwa Lagos ba. Hmmm garin masoyi baya nisa.
Xamu hadu ranar talata in shaa Allah.
Hajia 😊
[8/7, 7:38 PM] Zongo Gal: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
RAHMATULLAH (Hajia)
WANNAN SHAFI NAKU NE
Anty sis
Meela Adeel
Haj Aysha
Xclusive Ladies
Rahma Novels
Taskar Fiddausi Sodangi
Ina matuqar godiya da soyayyarku da kuma kulawarku wanda shike qaramun kwarin gwuiwa, Ina sonku ina qaunarku sosai ❤
Ya isa Lagos a cikin gidajen company dinsu dake Lagos ya sauka yayi wanka ya kwanta yana huta gajiya yanajin wani irin dadi marar misaltuwa ji yake kamar ya samu Sakeena ya gama. A daddafe yakai washe garin xuwansa, Ranar Monday da safe wajen 10:00 PM ya kira wayar sakeena bayan ya tabbatar da duk inda mijinta yake yana office yanxu. Lokacin daya kira tana lectures wayar na silent, yayi mata 3 missed call bata dauka ba ya haqura jikinsa a sanyaye ya fita office dinsu yin report na xuwansa.
Sai 2 PM suka gama lectures ta shiga masallaci ita da wata qawarta da tayi Qudrat yar qabilar Yoruba, sukayi sallama bayan sun fito daga sallar kowacce ta shiga motarta, sakeena ta dakko wayarta dan duba tym taci karo da missd call har uku da baquwar no din dabata sani ba. Tayiwa motar key dai dai lokacin data kira wayar tasa a kunnenta. Yana cikin ma'aikatar kiran ya riskeshi da rawar jiki ya daga wayar yayi sallama tare da kiran sunanta. Baxata muryar Deni ta xowa sakeena, kobai fada ba tasan shine don harta mutu murya Deni baxata bace mata ba, ta nemi gefen hanya tai parking, cikin sanyin muryarta tace "ya Deni kaine da gaske?" ya lumshe ido cikin jin dadin muryarta yace "Nine Sakeenatu, nakira baki daga ba har jikina yayi sanyi" tace "Ayya sry ina lecture ne wayar kuma tana silent cikin jaka." ya sauke ajiyar xuciya yace "OK kice Babyn tawa ta xama yar jamia" ta danyi murmushin yaqe jin ya kirata Babyn sa. Ya katse shirun da sukai yace "wane university kike?" ta fada masa sunan makarantar. Tace "ya Kano da kuma iyali?" yace "Ai ina Lagos" ta maimaita "kana Lagos? Mekaxo yi?" cikin sanyin jiki yace "Saboda ke naxo sakeena, akwai muhimmiyar maganar da nakeso muyi, ki fadamun inda kike yanxu inxo in sameki" ta jinjina maganarsa cikin dakiya tace "Yanxu kam na gama lectures gida xanje ina hanya ma sai dai inna samu lokaci" cikin sauri da muryar shagwaba yace "Plz sakeena dan Allah ki temaka mu hadu gobe wlh maganar tana da mahimmanci sosai" tayi jimmm sannan tace "OK goben muhadu 9:30 AM a jamia, inada lecture 10:00" ya sauke numfashi yace "To sakeena nagode da kika bani lokacinki" suka rabu Deni yana murna tsallake matakin farko sakeena kuwa tana tunanin wace maganace xata taso Deni tun daga Kano har yaxo Lagos don fada mata kuma a inama ya samu no ta?
A salube ta qarasa gida ko abinci bata nema ba, tace da Inna duk wanda yaxo nemanta ace tana bacci kar a tasheta, ta shiga ciki ta wullar da mayafi da jaka akan gado ta kwanta. Baccin da takeji ma batayi ba saboda tunanin maganar da Deni yace xasuyi me mahimmanci. Dabara ta fado mata ta dauki waya ta bugawa Iya suka gaisa suka taba hira har suka gama wayar Iya batai masa xancen Deni ba balle na xuwansa Lagos, don haka tasan lallai Deni tasace ta kawoshi.
Har Sageer ya dawo tana salube, bayan ya gama cin abinci ne suka fita can gurin da take aikin kunun aya suka fara, amma yau ba hirar makarantar data saba yimasa, ya kalleta yaga ko wanka batai ba kayan data fita dasu ne da safe a jikinta. Cikin kulawa yace "Sakeeena ko baki da lafiya ne?" batajiba domin hankalinta baya gurinsa. Ya kuma maimaita abunda yace tai firgigit tace "Na'am" yayi shiru yana naxarinta tabbas akwai abunda ke damunta. Bayan sun gama aikin kunun ayar, ta matsa gefe guda ya share gurin da yabaci ya wanke kamar yadda ya saba, suka tafi cikin gida. Ya xauna kan center carpet yace "Dakko littattafanki muyi karatun ko?" ba tare data dubeshi ba tace "yau kam babu karatu ma hadu gobe" ta juya ta nufi bedroom. Yayi wuf ya riqo tsintsiyar hannunta ta juyo suka hada ido yace "Sakeena ki fadamun abunda ke damunki in shaa Allah xanyi qoqarin samar miki mafita, ina sonki kuma ki tuna baki da kowa anan saini amanarki aka bani." batace komi ba tai masa murmushin yaqe ta xare hannunta ta shige ciki ta barshi da kallon qofa.
Daga ita har Deni a wannan dare basuyi wani baccin arxiqi ba suna tunanin haduwa da juna. Qarfe tara cikin jamiar su Sakeena tai masa, ya sanya manyan kayan da sakeena tafi qauna wato jamfa da wando na sky blue din material ya kafa farar hula, ya dunga kallon gine ginan makarantar yana kuma yabawa qoqarin sageer na iya biyawa sakeena kudin wannan tsadajjiyar jamiar.
Acan gida kuwa Sageer ya riga sakeena fita tun 8 wanda kuma har ya fita beyi toxali da ita ba, ko breakfast Inna ce tayi. Ta tsala kwalliya cikin wani omo blue din lace swiss me taushi wanda yasha dinkin wrapper skirt da yar ficiciyar riga, yabi jikinta ya lafe ya bayyana qirarrata sosai tayi simple makeup tasha dauri ta yafa veil kalar xaren jikin lace din me shara shara ta nufi makaranta, ko breakfast batayi ba. 9:17 tayi parking a car park na cikin skul din. Ta dauki waya ta kira Deni, ta fada masa ta iso, jikinsa yana bari yace mata shima yana gurin. Tai masa kwatancen motarta. Ya fito daga tasa motar ya qulleta yana tafe da wayar tana masa kwatance harya hango motar tata wata yar dunqulalliya baqa sai kyalli take.
Ya bude ya shiga yana jinjina lallai Sageer ya maida sakeena big girl tunda ya iya sai mata wannan motar. Ya lumshe ido bayan ya xauna ya shaqi qamshin turaren da duk kwakwarsa be gane wanne bane da kuma sanyin AC. Ya dubi sakeena wacce ta dan kalleshi na few seconds ta dauke kai tana duba agogon hannunta tace "Nuraddeen Lawan antashi lfy? Ya gari? Ka fadamun abunda ke tafe dakai domin bani da lokacin batawa xanje lecture" ya kalli sakeena ido bude da mamakin wannan sudden changes din ya jinjinnawa wayewarta irin ta mata masu aji dole sai yayi amfani da ilimi kafin ya samu kanta domin sakeenan daya sani da bafa itace yanxu ba.
Yayi murmushi cikin kwantar da kai yace "Lfy lau Sakeena Abbakar Liman, kuma kamar yadda kika sani naxo ne inbaki haquri akan abunda ya faru abaya har takaimu ga rabuwa, dan Allah sakeena kiyi haquri ki yafemun kuma kiyimun aikin gafara" tayi murmushin da yasa numfashin Deni ya kusa daukewa tace "Ai ban riqeka da komi ba, dana riqeka ai dabanxo nan ba domin ka. Haka Allah ya rubuta gashi ya hada kowanne daga cikinmu da masoyinsa na gaskiya cikin qanqanin lokaci?" Ya qara kyara xama ya fuskanceta yace "Ba shikenan maganar da take tafe dani ba wannan shimfidace kawai. Ainihin maganar itace inaso mu farfado da alaqar soyayyarmu ne ni da ke, saboda nagane kuskuren da nayi na rabuwa dake kamar yadda nagane baxan iya rayuwa da kowacce mace ba saike." Sakeena ta xare glasses din idonta tana kallon Deni cikin kaduwa da mamaki. Ya jijjiga kai yana nuna alamar gaskiyar magana dataji daga bakinsa. Tayi dariyar rainin hankali tace "Vry funny, Nura kenan kuma gashi ka makara domin sakeena yanxu matar Mohd Sageer ce kuma tana matuqar son mijinta saboda shi yana sonta ya fuskanceta baya bugunta kan abunda bai taka kara ya karya ba, sannan uwar mijinta na qaunarta bata da qannan miji balle su uxxura mata."
Deni yayi murmushin samun nasara, acikin kalaman sakeena ya gano bakin xaren kamar yadda quruciyarta tasa ta bayyana abunda yake damunta a tattare da xama dashi, ya kuma haqiqance sakeena ba sonsa ne batayi ba su Hajjo take tsoro. Yayi dariya yaci serious yace "Sakeena ina sonki da qaunarki wanda ban taba xaton sunkai haka ba sai bayan na rabu dake. Nasan ke matar aurece saboda ina daya daga cikin mutanen da suka sheda hakan, abunda kawai nakeso dake shine ki shaqe wuyan wannan auren naki ki kasheshi, In kikai haka kingama naki aikin, ki barmun ragowar xanji da komai. Na shirya rabuwa da komai da kowa akanki, xan baki mamaki kuma xan nunawa duniya ina sonki, xan qaryata masu cewa yaudararki nake wlh sakeena" maganganunsa sun ratsata sosai amma ta shanye ta gayyato qarfin halin tace "Nura fitarmun a mota, banason sauraren wannan shirmen naka" babu musu ya maida hularsa daya cire ya kama murfin motar yana murmushi ya sa qafarsa daya a waje yace "Ina jiranki gobe a dai dai wannan lokacin" ya fice ya shiga motarsa ya bar sakeena cikin wani irin baqon yanayi da tunani.
Daga gurin sakeena gurin bitarsu ya wuce, cikin farin ciki yake ya bude kwanyarsa yana nade duk lecture da ake musu. Ita kuwa sakeena bayan tafiyarsa a salube ta wuce lecture, wanda saidatai da gaske sosai kafin ta yakice tunanin abunda Deni ya fada mata kana ta maida hankali kan darasin da ake musu na English literature. Da suka tashi wajen 4, bata tsaya ko inaba taja motarta tayi gida. Yaukam abun yafi jiya, duk da Sageer ya dawo ya sameta tayi wanka tasa dogon wando pink me bin jiki da white top hakan be hanashi gane cikin damuwa take ba, daya lura sosaima saiyaga tayi zuru zuru daga jiya xuwa yau. Shi kadai yayi aiki kunun ayar tana xaune tana tunani, har ya gama ya shirya a freezer ya wanke gurin suka tashi suka shige ciki. Ta nufi bedroom kamar jiya tare da cemasa "sai da safe" yaji hankalinsa bai kwanta ba ya barta cikin wannan yanayin, ya miqe ya riqo qugunta da yaketa tsole masa ido tun daxu, kafin tayi aune ya hadata da qirjinsa ya rungumeta tsam, batai qoqarin kwacewa ba domin tausayinsa takeji ganin yadda yake bata lokacinsa wajen tayata aikin sana'arta wacce ko sisi baya samu a ciki. Jikin sanyin murya yace "Sakeena ina sonki, na tabbatar akwai abunda ke damunki ki daure ki fadamun xanyi iya qoqarina insamar miki solution" ta qara kwanciya a jikinsa domin abokin shawara take nema kuma da abunda ke damunta be shafi Sageer ba da ta fada masa domin ta yadda da soyayyar da yake mata. Ya qara matseta tsam cike da shauqi da fatan sakeena ta saki jiki dashi ya nuna mata irin soyayya da yake mata. Yace "My luv kinci abinci kuwa?" tai shiru babu amsa, ya qara cewa "Bari inkawo miki tea kisha duk kin rame kuma rama bata yimiki kyau sai idanunki suyi xuru xuru" ya nufi dinning ya hado mata tea ya dakko chocolate cake a fridge ya kawo mata kan center carpet. Ya fifta mata ya huce, yana mata kalamai sanyaya har ta shanye tas yace taje ta kwanta. Ta miqe ta nufi daki yabi bayanta da kallo saida ta murda kofar dakin sannan ta juyo tace "Nagode Sageer" ta sarkar masa murmushin da yasa ya kusa shidewa. Ya tafa hannusa bayan shigewarta dakin yace "YES"
Kwana tai tunani kafin ta yanke shawarar da take ganin itane dai dai. Duk da sai 11 take da lec, amma tun 9 ta nufi makaranta saboda karsu hadu da Deni. Da nufin taje ta danyi bitar karatunta kafin 11. Tayi parking tana tattara takaddunta na cikin motar kwatsam taji anbude motar an shigo, gabanta yayi wata irin faduwa. Ya dubeta yana murmushi yace "Kinso ki gujemun ko? Ai kin makara tun 8 nakenan ina jiran xuwanki sakeena jiya dake na kwana a raina" ta daga masa hannu tace "Nura ka sauraramun ni matar aurece kuma ina matuqar son mijina kamar yacce yake sona kamar ya mutu, dan haka dan Allah ka fita daga rayuwata" Sakeena ta tsinci kukan Deni cikin kunnuwanta harda shashsheqa, ta qara kallonsa karo na barkatai ta tabbatar kukan yake. Cikin rawar baki tace "Ya Deni dan Allah kayi shiru, meye haka?" yana share hawayen da suke masa anbaliyya a fuskarsa yace "Sakeena wlh ina sonki bada wasa nake ba, indai har kina sona da kuma son in rayu to kawai ki xama tawa, rayuwata tana dab da gurbacewa inbabu ke. Munci talauci tare nasamu aiki saboda ke amma baki mori komai cikin arxiqi na ba, yanxu lokaci yayi nasamu kudi dai dai gwargwado kixo mu rayu tare mu haifawa Baba da Iya yayan da suke buri suyi alfahari dasu." tana kallon cikin idonsa tace "Kasan Iya batason xamanka dani yanxu? Kamar yadda nasan Hajjo baxata taba sona ba" ya qara marairaice mata yace "Hajjo yanxu bata da halin takuraki domin ta kanta take, inma ta nemi ta kura miki na shirya rabuwa da ita akanki, Iya kuma ki barni da ita xanji dasu su da Baba." tayi dan jimm ta qara cewa "karatu na fa da nakeyi a nan? Kasan bani da burin daya wuce karatu a rayuwata wanda ka kasa cikamun shi sai Sageer ne cikin qanqanin lokaci ya cikan wannan burin. Bayan haka ma kuma banajin kanada kudin biyamun wannan makarantar da nake." ya danji babu dadi akan batunta ya hade rai yace "Saboda ga matsiyaci ko? Wlh sakeena koda xan rasa rigar sakawa xancigaba da daukar nauyin karatunki dan kawai incika miki burinki, kuma xancen da kike acan baya bansamu damar cika alqawarin karatunki bane saboda asirin Hajjo dake dawainiyya dani a wannan lokacin, amma yanxu indai kika temakeni kika kashe wannan auren xan baki mamaki xan nemi transfer a gurin aikina a dawo dani office dinmu na nan don kawai ki ida karatunki, xan maidaki matar so wacce duk duniya saita shaida ina sonki" tayi murmushi tace "Amma dai kasan abunda muke yanxu haramci ne ko? Inada aure kana soyayya dani? Cikin saurin ya bata amsar daya dade da tanada intaimai tambayar inda yace "Shi ba haramcin ya aikata ba? Da aurena fa akanki ya keta alfarmata ya hada shimfida dake." tayi qasa da kanta, ya lura da maganarsa tayi tasiri akanta, ya kuma cewa "Sakeena ki temakamun dan Allah wlh xan xama gagarumin dan kwaya akanki" ya fito mata da tabar wiwin daya siya saboda hakan. Ta toshe baki da hannu cikin tsoro tace "A a karkayi haka, kanada ilimi kasan illar shaye shaye kaban 1 wk xanyi tunani" ya tare da sauri yace "Wane irin 1 wk kuma babu dadin ji? Ni da nakeso kiyi sauri ki kashe auren ki fara iddah inason muna komawa gida ayi wacce xa ai daga qarshe a daura mana aure" tace "OK to bani 24 hrs gobe xamu hadu anan" yayi murmushin nasara yace "Yawwa ko kefa, Allah ya kaimu." suka rabu yayi office ita kuma ta shiga library ta xauna tana tunani da kuma karatu a tare.
Koda ta koma gida yau abun ya xanja salo domin yau ita kebin Sageer da kallo yayin da shi yake aikin kunun ayarta. Cikin xuciyarta tunani take wayafi sonta tsakanin Deni da kuma Sageer, ita dai tasan batason sageer sai dai tausayinsa da takeji saboda son da yake mata da kuma kyautatawa kamar yadda take xaton son Deni ma ya kwanta dama. To wa xata xaba cikinsu? Amsar data kasa samu kenan har garin Allah ya waye ta nufi makaranta. Kamar jiya tana parking ya bude motarta ya shigo. "Ya xakai da matarka in har na amince da buqatarka?" wannan itace tambayar da sakeena ta fara taron Deni da ita ko gaisawa ba suyi ba. Ya ciro wayarsa da sauri yana cewa "Sai in rabu da ita akanki, ko yanxu kikeso insaketa wlh saina buga waya in saketa agabanki, ki fadi saki nawa kikeso in mata?" Ta dakatar dashi da sauri tace "A a bansaka ba, nima macece in anyimun haka akan wata baxanji dadi ba, kuma sannan ina tausayin sageer yana sona yana kyautatamun kamar bawa haka yake a gurina" ya qara saka mata kuka kamar jiya yana cewa "Wlh Sageer ba sonki yake ba tunda har yabi son xuciyarsa ya aureki bayan yasan bakya sonsa, quriciyace ta hanaki gane hakan" ta danyi tunani na 2 minutes ta jiyo qamshin gaskiya a maganar Deni. Tace "To ya isa kabar kuka, amma yanxu ka fadamun ta wace hanya xanbi in saka sageer ya sakeni?" ya share hawayensa cikin jin har wasan ya qare haka da wuri ya tabbatar da Sakeena tana mugun sonsa. Ya dunga tsara mata duk yadda xatai har lokacin shiga lec ya kusa yi, tace "Bari na tafi class" yace "To, Baby" ya xaro kudi sabbi fil bundle na yan 200 ya bata yace "gashi a sai mai a xuba a mota." ta sheqe da dariya ta buga sitiyari tace "Ai baka da kudin da xakasai xuciyata dasu yanxu, in xan soka dan Allah xan soka badan wani abun hannunka ba, Sageer babu abunda bayamun ko banasonsa baxan mance alkhairinsa ba kuma baxan masa sharri ba, koda can da nike sonka wani abu ka bani?" Yayi saurin girgixa kai ta burgeshi matuqa kuma dole ya canja taku yace yana kama kunnuwansa "Tuba nike Baby. Amma bari inbaki breakfast din dana siyo miki nasan baki karya ba kika fito." ya fita yaje motarsa ya dawo ya bata ledojin take away biyu na wani gidan abinci, ta karba da farin ciki tana godiya, lallai Deni yana sonta yanxu tunda har ya iya sanin bataci abinci ba ya kawo mata.
Aka kwankwasa glass din barinta, ta xuge Qurat ce tsaye tace "Keena (kamar yadda take kiranta) ki fito muje class munyi latti fa karya rigamu shiga, tun daxu naxo ina mota saboda naga taki motar inata jira ki fito baki fito ba" sakeena tace "OK sry dear muna tare da bros dinane" suka gaisa da Deni ya fito ta qulle motar sukai sallama, Qudrat ta jata suka tafi, Deni yana tsaye yana kallon star sakeena wacce yanxu ko tafiyarta da tufar jikinta xuwa kan dressing dinta abun kallo ne, Lallai Allah ya sakawa sakeena abunda shi da su Hajjo sukai mata ta hanyar kawo sageer cikin rayuwarta. Sageer aikene daga Allah ya kawowa sakeeena shi don ya cika burinta da share hawayen maraicinta. Yasan baxai taba iya daukar nauyin karatun sakeena ba a wannan jamiar sai dai in xai sallanwantar da yar kadararsa da ya mallaka wacce bata taka kara ba balle ta karya, amma kuma harga Allah ya shirya rabuwa da kadarar tasa domin cika burin sakeena da kuma farin cikinta.
Ranar laraba ba wacce ta xama cikon kwana 3 da haduwarta da Deni hakance ta kuma kasance, tana xuwa taga Deni ya bude motar ya shigo ya xuba mata ledojin breakfast din daya siyo mata a sit din baya, ya dubeta tana murmushi ya xuba mata ido, sanye take cikin doguwar riga baqa me stones dinkin Dubai ta nade dankwalin rigar a kanta ta sanya medical glass dinta qafarta ma cikin takalmi dake cover shigarta a mutunce baka ganin komi sai yar kewayayyar fuskarta da tafukan hannayenta kasancewar antashi da sanyi. Yace "Naga kin qara haske, kardai har wannan banxan mijin naki ya miki ciki? Don naga shi akwai himmar yiwa mace ciki" tayi dariya tace "Ai hakan ke nuna shi gwarxo ne ba rago bane" ya matsa dab da ita yayi qasa da murya yace "To waye ragon? Kinsanni dai farin sani kuma kinsan nafi qarfin a kirani rago domin ke kanki duk da jarumtarki lokuta da dama qureki nake" ta janye jikinta tace "To naji matsa banason irin wannan xancen" ya matsa tare da cije l
[8/21, 12:27 PM] A A Dboy: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣7⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Haqiqa ko a lahira wani yanacin arxiqin wani, ina sonku masoyana kuma naji kiraye kirayenku na kuma amsa. Jinjinar ban girma ga ANTY SIS nagode da kulawa, Allah ya raya mana Sultee da khalil. 😊
Daga Sageer har xuwa kan ma'aikatan gidansa a tsorace suke, suna xaton bayan tafiyarsu Iya sakeena xata balle rashin mutuncin dayafi na baya, amma sai sukaga ba haka ba domin tanan da wannan sanyin nata wanda tayi tun xuwan Iya. Inna taji dadin hakan tace "abun na sakeena ashe qarami ko kuma xugar gurbatattun qawaye tunda an isa a tankwarata kuma tanajin maganar na gaba da ita" shima dai Sageer yabi sahun Inna bayan yaji dadin dawowar ainihin sakeenar daya sani a baya, harma da qarin wani sanyin halin nata da bai gama sani ba. Ya gama yadda da cewa abunda tayi a baya lallai sakata akeyi tayi kuma wannan friend din nata wanda har xuwa yanxu duk bincikensa begano kowaye ba shi yake sakata, amma yana jiran ranar da zasuyi resuming lectures xai bita ba tare da saninta ba domin ganin waye haka yake abota da matar aure kuma yake qoqarin tarwatsa masa gidansa da rayuwar jin dadin da yake musu tanadi shida Sakeena.
Suna dawowa daga kai su Iya ta wuce dakinsa ta hado kayanta tsaf tana mayarwa nata dakin tunda sun tafi, yana xaune a falo yaga wucewarta da fagon kaya, ya kuma gani ta koma ta debo wasu, yayi gaggawar tashi ya riqeta yace "Sakeena dan me yasa xaki raba mana makwanci? Kiyi haquri mana mu mayar da bedroom dina namu ni da ke, naki kuma saimu barshi a na baqi in munyi, basai anyi baqi ki dunga kwashe kaya ba kina mayarwa nawa" ta dubeshi yana riqe da kayan daya karbe daga hannunta, ta danyi tunani kadan, ya kuma cewa "Baxan miki abunda bakyaso ba, nayi alqawari, ranar ma da kikaga nayi na gaxa juriya ne" batace komai ta juya ta mayar da kayan data dakko shi kuma ya koma dakinta ya kwaso wanda ta riga takai. Shiya tayata suka shirya kayan a makekiyar drawer dakin me guda 6 tayi nata barin daban shima nasa daban. Ta kai kayan wankanta toilet din dasu brush suma ta shirya. Yinin ranar dai tare sukayi komai yana tayata har xuwa dare suka kwanta.
Wayewar garin Monday bayan ya fita aiki ta kwaso undis dinsa gaba daya wanda ta ciccirosu jiya gurin gyaran kayansa ta hada da nata masu dirty ta jiqasu da bleach ta wankesu tsaf ta shanya, sannan taje tasa hannu a aikin kunun aya, yau kam batai aikin gidanba tunda ga aiki ya samu. Ta tambayi Inna akwai tsamiya, (tamarind) Inna ta amsa mata da eh akwai taje ta dakko mata. Ta wanketa tsaf ta daka kayan qamshi da dan barkono kadan ta dora a wuta. Cikin awa guda sai gashi tayi lemon tsamiya wanda yaji kayan qamshi da sugar, ta ciccika robobi ta kuma quqqula a leda saboda masu siyan na 20 naira. Ta cika jug ta sawa Sageer a fridge. Inna dai mamakin sakeena take tana binta da kallon burgewa yarinyar akwai xafin nema gashi kuma tayi dace tana da hannun kasuwanci wanda juriya da haquri akan kasuwancin ya haifar mata, da wuya ta kasa abu bata siyar ba. Da kanta ta shiga gurin Bilki kamar wancan karon ta kuma kai mata. Bilki tace "Da kyau qanwata haka nakeso duniya bata auren rago, ai da xaki daure ma da dinki xan koya miki tunda naga kinada haxaqa" sakeena ta xauna kusa da ita tana cewa "A a Anty Bilki banaji inada rabo a dinki, baya burgeni da dai gyaran gashine dana koya inaso na iya" Bilki tace "To ai shidinma babu matsala akwai school guda da ake koyawa sai ki shiga. Dama kuma inaso in miki magana wata matan uncle dina ne xatai birthday na yaranta su biyu next week shine takeson xaki masu makeup ita da yaran nata, inatason yimiki batun ina tsoro naga lefin sageer ya shafemu yanxu bakyayi damu" Sakeena ta sunkuyar da kanta batace komai ba, Bilki ta qara cewa "Kiyi haquri na shiga personal life dinki amma kinyi ba dai dai ba duk da naga yanxu kin fara gyarawa, daga shiga jamia saiki falle ki xama tantiriya ki fitini kowa? Ai kinga wannan shi xaisa a tsoraci yan matan jamia kuma duk wanda yaga kinyi haka xai hana yarsa ko matarsa shiga, dan karta xama yacce kika xama. Kinga nima nayi karatu har matakin degree a Uni Lag kuma a hannun Maitama na qarasa karatuna amma ko kadan ban sauya masa ba, jamia gurine me hadari saboda ta tattara mutane iri iri amma in kika tsaya kika nutsu kika janyewa friends barkatai kika xabo wadanda tarbiyyarku tayi dai dai xakiji dadinta. Dole ba kowane kare da doki xaki kula ba kamar yadda ba kowa xaki budewa sirrinki ba karmadai a taku makarantar da take ta kudi. Dan Allah qanwata ki nutsu kinji ki dena bari xancen mutane da xugarsu na rudarki, ke yanxu ba yarinya bane domin da wancan cikin be xubeba da tuni kina shirin xama uwa, ki bar wannan quruciyar ta masu irin shekarunki shi girma yana xuwar maka koka shirya ko baka shirya ba"
Sakeena ta share kwallah bayan gama sauraren Bilki tace "Nagode Anty Bilki kuma in shaa Allah xanyi amfani da shawararki" Bilki ta qara duban sakeena tana tunanin matsalarta fa koda quruciya da akwai kuma rashin wanda xaiyi guiding dinta ya nuna mata yacce duniya take ciki, shiyasa sarrafata baxaiyi wahala ba kuma tabbas wata aka samu a waje ta shiga jikin sakeena take kangarar da xuciyarta kamar yadda Sageer yake fada, rashin masharwaci yasaka duk abunda aka gaya mata to akansa take doruwa. Ta dafata tace "Dena kuka ai munxama daya, nasan matsalarki bata wuce bakyason Sageer ba wanda kuma ni har yanxu yarda ba, domin soyayyar da kukaiwa juna a baya hujja ce kuma ba qarya bace, sannan babu yacce xa'ai wannan soyayyar taku tashin farko ta rikide ta koma qiyayya, kawai dai abunda na yadda dashi shine akwai wanda kikeso fiye da Sageer, wanda in kinso cikin qanqanin lokaci xaki koyawa kanki son Sageer kuma xaki maye gurbin wancan dashi" Sakeena ta qurawa Bilki ido tana jiyo qamshin gaskiya a maganarta. Ta miqe tace "Nagode da shawara Anty Bilki bari in koma gida ban gayawa ma Ya sageer xan shigo ba" Bilki tai dariya tace "kaji manyan masoya har sabon suna aka saka masa? To nagode Babyn ya sageer sai mun turo siyan tamarind kuma xan nunawa maqota."
Da sauri ta nufi kicin don dora girkin rana, ta tarar Inna ta dora tace "Yi tafiyarki kiyi aikin sana'arki ai munyi arxiqi tunda gidanmu ya koma xaman lfy kin nuna kin haifu tunda an tsawatar miki kuma kinyi biyayya. In kina da aikinyi ko makaranta sai ni kuma in dunga girkin" ta fita ta bar mata girkin dama kuma tanada wani aikin, ta kwaso undis dinsu data wanke ta gogesu tsaf ta fesa turare ta shirya masa nasa a guri guda daga qasan kayansa. Tana cikin shirin ne taci karo da kwalin laptop din daya siyo mata taqi tai masa iskanci taqi karba, ta rintse ido tana tuno abunda ya faru a waccan ranar taji kwallar tausayin sageer ta kuma ji tayi mugun tsanar kanta. Tasa hannu ta dakkota ta bareta taje dakinta ta sata chaji ta dawo tai sallah ta kwanta.
Qarfe 4 ta tashi, ta diro daga kan gado, taji dadin baccin sosai taji kwakwalwarta ta kuma washewa, da sauri tayo alwala tayi sallah da azkar din yamma, ta shiga kicin ta dora girki, Inna tace ta barshi. Ta marairaice tace "Ya sageer nakeson yiwa burabusko dan Allah ki barni" tana dariya tace "To na barki maxa yiwa mijinki kirki Allah ya qara hada kanku ya xaunarku lfy." ta fita ta barmata kicin din. Ta fara kici kicin dorawa, saidata dora turaren barxajjiyar shinkafar ta kuma dora stew wacce taji busashshen baqin kifi ta badeta da qayan qamshi da jajjagayyiyar albasa don kore qarnin kifin, ta lura sageer yafison kifi akan nama shiyasa tasa kifin, sannan ta fita ta kira Deborah me aikin gidan tace ta kuma gyara falon ita kuma ta koma daki ta qara kyareshi tsaf ta fiddawa sageer kaya marasa nauyi. Cikin rabin awa gidan ya dinke da qamshin girki da kuma na turaren wuta da freshners masu sanyin qamshi, ta shirya table sannan taje tayi wankanta tsaf tai kwalliya cikin wani material orange riga da skirt rigar irin wacce ake doro tattara daga qasan qirji ce, tayi fes cikin dinkin Bilki da yake kamar na maxa yabi jikinta ya lafe saboda taushinsan material din, tasa sarqa me cika wuya ta kalli kanta a madubi tayi murmushin burge kai, ta fita falo ta xauna tana kallo.
Shida tana gotawa taji qarar shigowar motarsa, ta danyi jiran shigowarsa har tsawon 5 minutes be shigo ba, ta fito harabar gidan dan ganin abunda ya hanashi qarasowa ciki, ta hangeshi can tsaye bayan mota ya juya baya, ta nufeshi a hankali saidata je dab da su sannan ta gane shida Maitama suke magana suna tsaye sun bata baya, ta riga ta taho dan haka bata koma ta lallaba a hankali ta bayansa ta rufe masa ido da hannayenta. Yayi dib ya daina maganar da yake, duk da jikinsa yana bashi cewar sakeena ce kuma ga qamshinta nan amma sai xuciyarsa take neman qaryatashi da fada masa sakeena batai masa soyayyar da xatai masa wannan wasan kawai tana xaune dashine da kuma kyautata masa saboda kashedin Iya.
Ya banbare hannunta tare da juyowa, sukai 4 years ta sakar masa murmushi tai qasa da idonta tana cewa "Ya sageer sannu da xuwa, naji baka shigo bane shiyasa na biyoka ashe kaida Baban Haidar ne (Maitama)" ya kafeta da ido babu ko qiftawa, gaskene sakeena ce ta tsala kwalliya harta fito taryarsa ko kuwa mafarki yake? Ta katse masa tunaninsa ta hanyar karbe jakar hannunsa tace "Kawo in tayaka riqewa" ta juya ta gaida Maitama, ya amsa a mutunce da nuna jin dadin daidaito da suka samu ita da abokinsa. Ta juya ta tafi cikin gida tabar Sageer tsaye kamar ya hadiyi rodi yana binta da kallo harta shige. Maitama ya karkada masa maqulan hannunsa a fuska sannan ya dawo da hankalinsa kansa yana cewa "Na'am yaushe kake cewa xamu bulla mu gano gurin?" ya dakawa Sageer harara yace "Ka da Allah can, waya kawo xancen guri anan? Muna xancen xuwa duba marar lfy daga ganin sakeena duk ka burkice ka dimauce kamar baka taba ganin mace ba" yayi murmushi ya shafa kai yace "To kaga laifina? Ka dubafa salon dataxomun dashi" shima Maitaman dariya yayi yace "Allah ya qara danqon qauna, kuma naji dadin xuwansu Umma dan alama xuwansu ya gyara xamantewar aurenku da sakeena data kusa rushewa, kuma kaima kasa ido a kanta da kuma wadanda take mu'amala dasu acan makarantar sannan ka koyi tsawatar mata intayi ba dai dai saboda kaine shugaba dole saikana motsa kwanjinka kan wasu abubuwan, ba koda yaushe xaka dunga barin wannan makahon son da kake mata ya tasiri da kuma yana fitowa ba" Sageer ya daga masa hannu yace "To naji afakhallahu, ware gidanka" ya qarasa yana nuna masa hanyar gate. Maitama cikin dariya yace "Au korata kake?" Sageer yace "Eh mana kai bakasan sabon aure nayi ba kaxo ka tsare ni da xance marar tushe har sweetie na ta gaxa haquri ta fito" yana gama fadar haka ya shige ciki yabar Maitama tsaye yana dariya da cewa "Kafin ai daran dai akai kwandi, xakaxo ka taddani har gida"
Bai taddata falo ba ya shige bedroom acan ya sameta a bathroom tana hada masa ruwan wanka, har tagama ta fita ta barshi yana kallonta ya daka tsalle bayan fitarta yace "YES" Cikin farin ciki ya sallo wankansa ya fito ya kuma tarar da kaya a gefen gado, yana murmushi ya dauka ya saka a gaggauce ya shirya ya nufi masallaci. Yaukam be tsaya jiran ayi sallar isha ba ya taho gida, sakeena itama ta iddar da sallar kenan ta fito, tana murmushi ta riqo hannunsa ya bita kamar soko ta kaishi kan dinning, ya xauna yana binta da kallo ta shaqe masa plate da burabuskon shinkafa da jar miya tasa mai spoon ta tura masa gabansa ta dakko cups ta cika masa daya da ruwa dayan kuma tamarind shima ta tura masa. Cikin sanyin muryarsa yace "Baby wannan duk ni kadai?" ta danyi murmushi iyakacin lebenta tace "Ya sageer ka daure kaci abinci plz" be kuma magana ba yayi bisimillah ya faraci. Ta xuba nata itama kadan ta xauna tanaci tana satar kallonsa. Tayi mamaki kwarai dataga ya cinye abincin kuma ya shanye tamarind din duka, ta miqe tace "In qara maka?" ya cikin sauri "Haba ai sai kice jaki ne mijin naki, wannan lemon dai kawai xaki qaramun yamun dadi a ina aka samoshi?" tana tsiyaya masa tace "Kai ya Sageer banda santi dai, lemon tsamiya ne fa yau na gwada kadan nagani ko xaiyi kasuwa" saida ya shanye sannan yace "Lallai yar kasuwa, gaskiya yayi dadi sai naki yafi na kanti armashi saboda kayan qamshin da kika saka a memakon flavour. Allah ya kawo kasuwa me albarka. Nagode da girki, ya akai kikasan inason wannan abun?" tayi qasa da kanta tace "Amin nagode da addua, kuma umma ce da muna hira tacemun kanason duk wani abinci dangin dambu shiyasa nayi maka" ya riqo yatsunta da take wasa dasu yace "nagode sosai Sakeenatu yau kinsani farin ciki, nayi qoshin dana dade banyi ba" Suna xaune yana mata hira tana amsa masa da Eh ko kuma A a har ta fada masa daxu ta leqa gidan Bilki, aka kira sallar Isha ya fita ita kuma ta shige daki yin tata.
Koda ya dawo sallah bata fitoba ya nemi guri a falo ya xauna ya kunna TV yana kallo, ta budo qofa ta fito riqe da laptop ta qara gyara fuskarta tasha pink din lipstick ta kuma baxo turare. Ya bita da kallo hartaxo ta tsuguna gefensa jiki a sanyaye tace "Ga computer na dauka daxu acikin kayanka, dan Allah kayi haquri da abunda ya faru a baya inka huce saika fara koyamun" Yabita da kallon burgewa harta gama magana, yasa hannu ya riqota ta taso ya direta akan cinyarsa yana shafa fuskantar yace "Baxan taba fushi dake ba sakeena, kuma naji dadin karbar kyautata da kikayi kuma ko yanxu ai saimufara koyon ko?" tai murmushi tayi qasa da kanta don har yanxu tana kunyarsa na abunda tayi a baya, xamanta akan cinyarsa saiya tuna mata da xamanta da Deni domin shi indai xasuyi hira akan cinyarsa yake dorata, tai saurin kauda tunanin Deni a ranta ta maida hankalinta ga sageer wanda ya bude system din ya kunna yana nuna mata yacce ake shooting down, ya bar mata ta gwada yaga ta iya, sannan suka qara gaba. Ya dubeta yace dakko wayarki mana ki kunna in yi connecting dinta da system in koya miki wani abu. Tai saurin girgixa kai tare da cewa "A a baxan kunna waya ba gaskiya" ya kalleta da mamaki, yasan tabbas akwai abunda ya hanata kunna waya duba da yadda waya ta shiga ranta, amma ya basar sukacigaba, saidayaga ta fara hamma xuwa lokacin kuma ta koyi abubuwa da yawa sannan yace suje su kwanta.
Taje ta tsaftace bakinta ta canja kayan bacci ta miqe ta kwanta don a gajiye take. Ya bude drawer xai dau kayan bacci ya tarar da undis dinsa da sakeena ta wanke, yakai hannusa ya shafosu ya juya ya kalleta harta fara bacci, ya sako kaya yaxo ya kwanta kusa da ita ya kira sunanta cikin muryar bacci ta amsa yace "Yau har wanki kikaimun?" tayi murmushi kawai, yakai bakinsa kan goshinta ya sumbata yacigaba da shafa gashinta yana saka mata albarka, tana jinsa tana lumshe ido daga qarshe tajishi ya kwanta a jikinta tai bacci ta bashshi shi dai dakyar ya samu baccin begen sakeena ya hanashi sakat.
***** **** ******* ********* ****
Kwana biyar da suka biyo baya, rayuwa suke me dadi gidansu xaune lfy qalau kowa ya sake yana harkokinsa, Sageer dai kusan yafi kowa farin ciki biyayya sakeena ke masa kamar ta kwanta ya takata har wani lokacin saiyace mata ya isa haka shi mijintane kuma best friend dinta bawai boss dinta ba don haka ta dena sunkuya masa, so yake su gina gidansu da soyayya da kuma tarbiyya don haka ta sake da shi. Duk da babu abunda ya hadasu dashi ta bangaren auratayya amma dai suna cikin farin ciki da kuma nishadi. Kusan kullum sai Iya ta kirashi ta tambayeshi yanayin xaman nasu tare da hadashi da Allah karya boye mata inda akwai matsala domin ice tun yana danye ake tankwarashi. Kullum dai amsa daya take samu shine suna xaune lfy babu matsala, sai lokacin taji hankalinta ya kwanta.
Sakeena anata bangaren rayuwa take kadaran kadahan wato babu farin ciki kuma bata baqin ciki, tana matuqar qoqarin ganin ta tusawa kanta son sageer kamar yadda Bilki ta shawarceta amma ina sai a hankali saboda so ba'a dole, itadai kawai abunda ta sani shine tana matuqar tausayin Sageer saboda son da yake mata da kuma kyautatawa gami da sadaukarwa wanda hakan yasa take matuqar girmamashi da kuma bashi wani irin matsayi na musamman a xuciyarta. Deni tuni ta share babinsa a ranta kuma tadau matakin guje masa shiyasa ma bata kunna wayarta ba har kawo yanxu. Tayi keeping kanta busy don karta bawa xuciyarta damar tuna Deni balle taji sonsa. Inta tashi tun asuba bata komawa, tana idar da sallah xata dora karatun qur ani sannan ta hadawa sageer breakfast saiya fita take samun damar gyara dakinsu da wanke undis dinsu sannan taje tayi nata breakfast din, ta fita aikin kunun aya da kuma tamarind data samu karbuwa yanxu, sai sun gama tas sannan taje tai wanka ta xauna bitar abunda Sageer ya koya mata na computer bata tashi sai anyi sallar zuhr, sannan taje tai sallah ta kwanta, Inna ke girkin rana ita kuma tayi na dare saboda sageer. Bata tashi sai anyi laasar tayi sallah ta dora girki, saita gama daf da dawowar sageer sannan take wanka ta chaba kwalliya, yawanci tafiyin traditional food saboda yafi sonsa, wani time din ya kirawo Maitama suci tare suna santi da yaba mata tana musu dariya. Bayan sallar isha kuwa lokacin da suke naxarin computer ne da sageer wanda hakan ke masa dadi domin sai yaja sakeena jikinsa sosai suna manne da juna yake koya mata.
Sakeena saidata saki xuciyarta sosai sannan ta gane ainihin wanene mijinta Muhammad Sageer. Da farko ta fuskanci mutum ne mai kirkin gaske da kuma kyauta, hakama a bangaren addini bashi da aibu, yana dadin mu'amala da matuqar sanyin hali wanda koda da house maids dinsa yakewa magana da wuya kaji tashin muryarsa kamar ba namiji ba. Data kwatanta halinsa da Deni saitaga halayensu su biyun kishiyoyin juna ne, domin Deni sam bashi da haquri kuma akwaishi da maida qaramin abu babba kuma sam baya iya controlling din kansa yayin da yake fushi. Data auna a mixanin hankali da adala sai taga Sageer kam yafi Deni dadin xama wanda ko babu komai xa'a soshi kodan mutuncinsa da kuma sanyin halinsa. (To sakeena kodai kin fada tarkon qaunar dan katsinawa ne? 😜) Sana'arta tana garawa fiye da yadda ta xata kuma tana hadawa da addua. Ranar Monday suke shirin komawa makaranta bayan hutun 3 wks da sukai tsakanin first nd second semesters, kuma ta gama shirinta tsaf na sake taku a school kamar yadda ta shirya gujewa Deni. Shima anasa bangaren Sageer ya gama nasa shirin domin bin sakeena a boye da kuma ganin waye namijin da take abota dashi.
Ranar Monday taxo mata cikin wata irin fargaba da faduwar gaba, tun tsakar daren jiya qirjinta ke bugawa bacci ma dai inya dauketa saita farka cikin firgicin yadda haduwarsu da Deni xata kasance. Dataga babu sarki sai Allah ta kasa baccin saita dena yaudarar kanta ta miqe ta shiga toilet ta dauro alwala ta shimfida pray mat tahau yin sallolin nafila da roqon Allah ya yaye mata wannan mugun tsoron da taji tanawa Deni sannan kuma ya gina katangar qarfe tsakaninta dashi. Duk abunda take Sageer na lura da ita tunda kan kasa baccin da tayi har xuwa kan sallar da taketa xabgawa kamar ance mata xaa tashi qiyama. Kuma yasan tabbas akwai abunda ke damunta wanda keda alaqa da komawarta makaranta gobe domin bata da wayon da xata danne abu inyana damunta.
Tana idar da sallar asuba ta fara aikin breakfast, xuwa 8 har Sageer ya shirya yaci abinci ya fita, ita kuma tace masa sai 10 tunda yau suka koma sai taje taga time table. 9:30 ta shirya ta fita xuwa lokacin faduwar gaban ta galabaitar da ita, tayi wani xuru xuru da ita saboda fargaba kuma ko abinci ta kasaci da kyar ta kurbi ruwan tea rabin cup.
Matakin data dauka shine canja gurin da take ajiye motarta, ta samu wani gurican yamma da car park din tayi parking da hanxari ta fito ta nufi department dinsu tana buga sauri kamar xataci da baka, batai nisa ba taci karo da Qudurat suka gaisa ta nuna mata time table suka shige venue din da suke da lec, acan suka tarar da wata qawar Qudurat yar Maiduguri Maijidda suka gaisa aka xauna ana dan taba hira, ita dai sakeena tayi xukudi tana tunani sai dai in sunyi dariya tayi yaqe dan karsu gane hankalinta baya gurin. Suna xaune malami ya shigo sannan ta hada hankalinta ta fara sauraranshi.
Sai a lokacin Sageer ya fito daga maboyarsa ya juya ya koma mota ya koma office. Tun 9:30 yake school din cikin wata motar abokin aikinsa daya aro me baqin glass don kar yazo a tasa sakeena ta ganshi, akan idonsa taxo har ta shiga department, ya fito a motar yana binta a baya, har haduwarsu da Qudurat, yaje bord din department din ya kwafi time table sannan ya juya da nufin xai dawo in anjima domin sai yaga wanda ke hurewa matarsa kunne wanda har fargaba ko murnar haduwa dashi ta hanata bacci jiya.
2 suka gama lecs din ranar gaba daya kuma xuwa lokacin ta jigata kwarai da yunwa, suna fitowa suka nufi wurin cin abinci suka siya duka su ukun Qudurat ta biya kudin har sun xauna a kan wani table a gurin Sakeena tace musu su shiga daga ciki suci nan maxa sunyi yawa, sukabi shawararta suka shiga suka take cikinsu kana suka fito suka nufi Masjid sukai sallah, duk wannan abunda suke Sageer na biye dasu, tun 1:45 PM yayiwa school din tsinke dan yasan lokacin xata gama lecs kuma babu intervals. Yaji dadi kwarai data nuna baxataci abinci a gaban maxan gurinba hakan ya qara nuna masa kamun kanta. Yana xaune gefen masallacin sanye da baqin glasses ya basar kamar yanayin wani abune, suka fito suka wuce kowacce ta shiga motarta suka jero suka fita tare suna waving juna. Yana biye da motarta har kwanar gidansu tanata xabga gudu, wanda da tana cikin nutsuwa xata lura da motar dake binta tun daga school, amma ina hankalin yayi gaba wajen cimma burin gujewa Deni. Saida yaga ta shiga gida sannan ya sauke ajiyar xuciya ya juya tasa kan motar ya nufi gurin aiki da nufin sai gobe kuma domin yaci burin saiyaga kowaye wannan.
Itadai tunda ta samu ta kubuta yau sai hankalinta ya kwanta ta gama sakawa a ranta Deni yagaji da jiranta da kuma kiran wayarta a kashe ya haqura ya Kama gabansa. Cikin kwanciyar hankali ta kwanta tai baccinta me dadi, wanda bata tashiba sai qarfe biyar din yamma, tai miqa da salati taje tai sallah da azkar din yammaci ta nufi kicin. Taji dadi data tarar Inna harta dora mata sanwa, cikin farin ciki tace "Nagode Inna kamar kinsan baccine ya kwashe ni harna makara" Inna itama cikin nata murmushin tace "Bakomi sakeena, ai tunda naga hudu ta gota baki fitoba nasan gajiya ta hanaki tashi aike kam ba daganan ba akwai himma" ta karbi girkin ta qarasa taje tai wanka, yau kam cikin farin ciki take kwalliyar qananan kaya tayi riga da skirt iri daya dark green masu kama jiki, bata daure dankwali ba sai hula data saka ta bayan hular kana gano jelolin kitson kanta na igbira style. Shigowar Sageer tayi dai dai da dauke burner din turaren wuta datayi, da sauri ta ajiyeta kan tiles ta tafi da gudu ta daneshi. Ya saki ajiyar xuciya yana mata dariya, yasa hannu ya ciccibeta yana rataye da jakarsa suka nufi bedroom, tunani yake meyasata farin ciki haka? Shidai tun daga jiya har xuwa fitarta school a burkice yake ganinta, amma yanxu menene dalilin wannan canjin da aka samu? Ya tabbatarwa kansa cewa akwai abunda ke faruwa kuma hakan ya qara masa axamar gano wanda yake mata famfo.
Cikin nishadi sukayi dinner tare sukayi darasin computer suka kwanta, yau dai babu juye juye baccinta tayi lakadan ta barshi da kallonta da kuma tunani kafin nasa baccin ya kwasheshi. Da safe lfy lau tayi ayyukanta tare sukai breakfast dashi ya rigata fita ita sai 9 take da lec.
Yana xuwa office be xauna ba ya ari mota kamar jiya yayiwa school din tsinke. 8:30 dai dai ta isa makaranta, yaukam hankalinta kwance tayi parking a gurin da tayi jiya, ta kashe motar tana qoqarin xare key Deni ya bude motar ya shiga, ta juyo a firgice cikin wata irin muguwar faduwar gaba ta dubeshi.
Sageer da yaga fitowar Deni daga wata mota da kuma shigarsa motar sakeena shima ya samu kansa cikin faduwar gaban data nunka ta sakeena, yayi mugun Al ajabin wannan abun domin ko a mafarki be xaci Deni ne friend din sakeena ba, gabansa ya dunga wata irin faduwa babu qaqqautawa kamar ba namiji ba, bai taba xaton haka ba, besan bala'in sakeena yakai haka ba, ta rasa abunda xatai masa sakayya dashi sai hada Kai da Deni suci amanarsa? Wato ranar data kasa bacci da kuma farin cikin da take jiya na murnar xata dawo makarantane su hadu da Deni sucigaba da cin amanarsa da kuma keta alfarmar aure. Hawaye suka xubo masa lokacin daya qara kai kallonsa akansu suna cikin mota xaune a kulle da alamun magana suke, xuciyarsa baqiqqirin ya raya kawai ya fita da bindigarsa ta aiki yaje ya harbe sakeena da Deni yayi maganin fasiqai maciya amanar aure domin hukuncinsu kenan wanda duk wanda yayi yunqurin cin amanar aure inyaji hukuncin daya dauka akansu xai bari koba dan Allah ba. Sai dai kuma daya barin na xuciyarsa ya kwabeshi da karya dau doka a hannu abunda dai ya kamata yayi shine ya haqura da sakeena ya sakarwa Deni ita sujecan su qarata. Wannan shawara tafi kwanta masa kuma yayi na'am da ita, yaji wata irin muguwar tsanar sakeena ta darsu a xuciyarsa. A fili yace "Sakeena ko sonki xai kasheni, ko kece autar mata kuma koda gold aka halicceki na haqura dake" ya lalubi biro a aljihunsa ya fara bincikar takadda a motar amma dake ba tasa bace motar bai samu takaddar ba, dole ya haqura da rubuta sakin da yayi niyya a lokacin da nufin sai yaje gida xai rubuta ya bata kuma ya turata Kano a gobe tare da rufamata asirin abunda tayi da kuma alqawarin cigaba da daukar nauyin karatunta. A fili yace "In shaa Allah yau baxaki kwana da aurena a kanki ba, tunda har takai Deni ya baro nasa iyalin a Kano ya biyoki garin da kike aure Allah ne yasan abunda kuke aikatawa, baxan iya ba gara in bar masa ke"
Acan cikin mota kuma sakeena tayi shiru tana gayyato dauriya da kuma dakiya kar Deni ya gane ta furgita da ganinsa kuma tanajin tsoronsa. Kamar xararre ya fara magana "Nasan kwace miki waya yayi saboda kar muyi magana ko? Wlh sakeena nasha wahala a tsahon sati ukun nan har kwanciya nayi a asibiti. Kullum sai naxo makarantar nan saboda ke, sai jiya akacemun wai an ganki a aji ashe kin canja gurin ajiye motane? Alhamdulillah daga qarshe dai gani gaki. Na gama yanke shawara duk wannan kewaye kewayen baxai kaimu ba gara kawai muje court ai muku KUL' E, (mayarwa da miji sadakinsa ko abunda ya kashe a aure domin fansar kai) ya fadi duk abunda ya kashe ni kuma xan baki a ki bashi ki fanshi kanki, a lokacin sai a daura mana aure tunda babu iddah tsakaninku. Munyi magana da wani Barrister xai tsaya mana a court har mu cika burinmu, kinga saimu koma can gida Kano a matsayin ma'aurata su gama bambaminsu su kyalemu tunda mun riga munyi aure, ita kuma waccen mahaukaciyar muna komawa xan danqara mata saki uku ta mabu fili mu koma xamanmu irin na baya"
Sakeena tunda Deni ya ambaci kalmar "KUL E" take kallonsa baki bude cikin tsabar al jabi da mamaki, ta qara nutsuwa a dubansa taga duk yayi wani dugujunjun ya tara suma a fuska da kansa kuma sumar babu gyara yayi wata irin rama da alama baya cikin nutsuwa. Batace masa komai ba yacigaba da cewa "Yanxu ina sauri ne xamuyi test acan gurin aiki, amma xamu hadu in kingama lectures, kuma inkin koma gida kiyi lissafin duk abunda ya kashe miki ki rubuta sai ki fito dashi goben qarfe goma mu hadu anan sai mu wuce court din" abunda ya qara tabbatar mata da kan Deni ya kwance shine, yana gama fadar haka be jira cewarta ba ko maganarta balle shawararta ya bude mota ya fita yana daga mata hannu da cewa "Allah ya kiyaye minki gimbiyata ayi lectures lfy" har ya shiga motarsa yaja beji koda tarinta ba balle muryarta. Ta dafe qirji bayan ya tafi, cikin rashin takamemen abunyi, yanxu ya xatai da wannan gagarumar matsalar data haqiqance da baxata taba iya maganinta ita kadai ba? Waxata fadawa? Ta shiga uku, qilu ta jawo mata bau ya xatai da Deni? Ita kadai ta kitsa masifarta ta cin amanar aure gashi ta kwabe mata, ya xatai da Deni da kuma alamun haukar data fara bayyana gareshi? Ta kwanta kan sitiyari ta fashe da kukan nadamar abunda ta aikata na biyewa Deni. Taci kukanta ta qoshi babu mai lallashi, dole ta haqura ta share hawayenta ta maida glasses dinta ta rufe motar ta nufi aji. Sageer saida yaga tafiyar Deni da kuma shigar sakeena aji sannan ya nufi gurin aiki.
Ko a gurin aiki be iya komai ba sai aikin tunani da kuma xubar hawaye a duk sanda ya tuna girman cin amanar da sakeena tai masa domin shi baiga lefin Deni ba, itace babbar me lefi da bata bashi dama ba da hakan bata faru ba. To itama a nata bangaren Sakeena ta kasa tsintar ko kalma daya a darussan da ake musu a ranar, gashi har 4 xasukai suna lectures, kanta gaba daya a qulle yake cikin rashin sanin matakin dauka da kuma tarin nadamar cin amanar sageer da tayi na boye masa alqarta da Deni. Hawaye suka wanke mata fuska ba tare da saninta ba, Qudrat ta jijjigata tace "Lfy keena? Naga kina kuka" dake ba yawane dasuba a ajin sai maganar Qudrat ta janyo hankalin duka yan ajin da malamin dake musu darasi. Suka fara tambayarta abunda ke damunta har malamin, ganin anyi mata chaaa yasa ta girba qarya da cewar kanta ke ciwo, suka dunga jero mata hannu kuma akai mata afuwa taje gida tasha magani ta huta. Tayi godiya ta miqe tadau jakarta ta fita dama xaman nata bashi da amfani tunda bata fuskantar komai. A hanyama tana tafe tana shatatar da hawaye wanda ta kasa dakatar dasu, Wani irin mugun xaxxabi da ciwon kai ya saukarta mata lokaci daya, dakyar takejan motar dan ko gabanta bata gani sosai ikon Allah ne kawai ya kaita gida.
Bata iya shiga bedroom ba a falo ta kwanta kan center carpet tanajin wani irin sanyi yana ratsa bargonta kuma ta kasa tashi ta kashe AC. Inna ta shigo falon daukar abu a fridge ta samu sakeena a cure guri daya ko takalmin qafarta sau ciki bata cire ba sai rawar dari takeyi haqoran na hadewa. Da sauri ta nufota tana salati da tambayar lfy? Sakeena bata iya yimata magana ba kawai dai tayi mata nuni da hannnu ta kashe AC, da sauri ta kashe ta nufi dakin sakeena ta yayimo blanket ta rufa mata, sai lokacin taji sanyin ya ragu. Har xuwa axahar tana kwance gurin ta kasa tashi tayi sallah kuma Inna ta matsa mata akan taci abinci tasha panadol saboda wannan xafin jikin, dole data dameta tasata hado mata tea da Milo kawai babu madara ta jingina jikin kujera dakyar tasha tea din da magani, aiko 2 minutes beyi ba ta amayoshi tas, jikinta ya qara mutuwa saboda yunqurin aman da tayi, ta tashi tsam ta wanko bakinta gami da alwala tunabin bango saboda jiri tai sallah a xaune ta koma kan doguwan kujera ta kuma qudundunewa sai lokacin wani wahalallen bacci ya dauketa.
Qarfe biyar Sageer ya kamo hanyar gida shidinma ciwon kai yake sosai, bema kula da mutum a falon ba yasa kai xai shige bedroom, Inna tai saurin cewa "Yawwa sageeru ka dawo ba? Sannu da xuwa, kaga yarinyar nan tun kusan shadaya ta dawo take kwance babu lfy ko ruwa tasha sai tayi amai." yadan dubi Inna a taqaice yace "Allah ya sawaqe nima banajin dadin" ya shige daki ba tare daya ko kalli sakeena dake kwance tana hawaye ba tana binsa da kallo. Ya jima a daki don saida yayi wanka ya shirya tsaf sannan ya fito da nufin daukar ruwa a fridge. Inna tai saurin tashi tsaye cikin bacin rai tace "Banason haka sageeru, meke damunka ne? Na fada maka yar mutane babu lfy baka damuba ka shige daki kayi xamanka? Sam baxan lamunci ka wukaqanta iyalinka ba ina gani, duk daya kuke a gorina saboda haka ka dauketa ka kaita asibiti domin ta jigata" saboda kar Inna ta fuskanci abunda ake ciki yace ba tare daya dubi sakeena ba "Yi haquri Inna ta shirya ta sameni a mota" ya fita, Inna ce ta temaka mata ta riqeta har xuwa cikin motar tana mitar batasanshi da rashin tausayi ba inyacigaba da nuna haka ga iyalinsa xata fadawa Umma.
Yaja mota suka tafi, Sakeena tana mamakin wannan hali daya tsira yau ko kallon sashin da take beyi ba balle yayi mata sannu. Ta kwanta a jikin kujerar motar tana numfashi dakyar gami da qanqame jikinta saboda sanyin AC daya kunna gashi bataga fuska balle tace ya kashe, yau gaba daya Sageer ya canja mata ya hade rai kamar ba shiba.
Dake private hospital ne basu bi layiba suka sami ganin likitan bayan ya mata yan tambayoyi ya kira nurse taja jinin sakeena a sirinji ya fada mata kusan tests biyar yace tai mata ta kawo result din. Kimanin 20 minutes ta kawo result din wanda ya nuna qarara Sakeena nada shigar ciki na yan satittika. Daga ita har sageer baxata lbrin yaxo musu, fuskarta ta washe sosai ta sunkuyar da kanta cikin kunya tana cewa a ranta "Shikenan raba gardama yaxo nasami makamin yaqar Deni domin inyaji inada ciki dole ya fita daga rayuwata ya kyaleni da uban dana sageer, Allah ya kaimu gobe a dai dai lolacin da yace mu hadu xanje" Sageer kuwa mutuwar xaune yayi, sam baya maraba da wannan cikin domin yanada shakku akansa nasa ne kona Deni, ya dubi sakeena yaga tana cikin farin ciki, ya qara tabbatar da xarginsa na cewa cikin Deni ne domin haihuwa da Deni ita kadaice xatasa sakeena wannan farin cikin ba shiba da batasonsa takecin amanarsa gami da ha'intarsa. Yayiwa likitan godiya ya hadasu da kwayar paracetamol kawai yace ta daure taci abinci tasha.
Suna tafiya a hanyan dawowa gida Sageer cikin kogin tunani tsundum ta yadda xai bullowa wannan lamari me sarqaqiyya shi dai yasan tunda sukai aure sau daya kawai ya kebanta da sakeena a shimfida, to ba abun mamaki bane intayi ciki daga wannan haduwa tasu inda babu alaqarta da Deni kenan, amma yadda yasan sakeena da rashin wayo da kuma mayattar son da takewa Deni yasan ba abun mamaki bane inya yimata wayo ta mallaka masa kanta yayi mata ciki. To shi yanxu meye abunyi? Titsiye sakeena xeyi ta fada masa waye uban danta ko kuma sakawa xaiyi a cire cikin ya hadata da takaddar saki ta nufi garinsu?
Yakai kallonsa gareta tana jingine jikin kujera tana murmushi idanunta rufe tana shafa cikinta. Koda sukaje gida ya rigata fita daga motar, tabishi da kallo saroro harya shige falo, ta kashe motar ta qulle tana tafiya cikin gida tana tunanin kodai sageer bayason haihuwa ne taga ya canja haka cikin qanqanin lokaci? To amma ai bai nuna haka lokacin wancan cikin daya xube. Ta bishi bedroom kai masa key din motarsa ta sameshi kwance dafe da goshinsa. Ta xauna gefensa tace "Ya Sageer naga kamar baka murna da cikin ko? Ko bakasan haihuwa ne?" ya dubeta fuska murtuk yayi murmushin takaici yace "Wane me kamar shekarunane xaiqi haihuwa indai Dan da xa aifa masa Dan halak ne" tai dan jim tana naxarin maganarsa, batagano komai ba ta miqe ta fice tana cewa "Nidai inma bakason haihuwar ne nikam inason Dana kuma ko babu temakonka xan haifeshi sai in kaiwa Iya ta shayar dashi indawo mucigaba da xama" Tas yaji abunda tace kuma wannan magana ita ta kuma tabbatar masa da cikin Deni ne a marar sakeena domin da nasa cikin ne ai Umma xatace xata kaiwa Dan ba Iya ba.
Taje kan dinning cikin farin ciki ta saka tuwon alkamar da Inna tayi taci tai nak, tasha paracetamol da tamarind roba guda, sam farin ciki yasa ta dena jin kowane irin ciwo, cikin nishadi tai shirin baccinta taje kusa da Sageer dake tunani ta kwanta tare da dora kanta akan qirjinsa. Ya kalleta bayan tayi bacci ya tabbatar da sakeena ta mugun rena masa wayo tayo cikin shege da kwartonta ta kawo masa gida kuma shine harda kwanciya a jikinsa? A xuciye ya toreta a jikinsa shi kyamarta ma yakeji yanxu.
Da safe kamar ragowar kwanakin da suka gabata itane tai breakfast duk da batajin dadi sosai amma ta daure tayi, tare da Sageer suka karya wanda tun asuba ya gama yanke abunda xai aiwatar har kuma ya rubuta takaddar sakinta ya boye a jakarsa ta office sannan ya saka aransa da yamma yana dawowa xai dauketa suje asibiti acire cikin gobe da safe ya yankar mata ticket ya tura Kano da takaddar saki ba tare daya bayyana abunda tayi ba xai rufa mata asiri da cewa Allah ne kawai ya qari xamansu. Kallon juna suke babu qiftawa kowa da cup din tea a bakinsa tana masa kallon mutum shi kuma yana mata kallon biri.
Har mota ta rakashi ya tafi office ta dawo ciki a gurguje tai wanka ta shirya cikin riga da skirt ta saka hijab wanda yakai har gwuiwarta ta dauki key din mota ta fice, Sageer dake hanyar school dinsu tun daxu cikin cikin wata baquwar motar yaga giftawarta da sauri ya rufa mata baya har xuwa gurin datai parking ya tsaya gefenta, tana xaune shiru cikin motar tare da duba agogo da alamar wani take jira, 17 minutes a tsakani sai ga Deni a tasa motar yayi parking ya fito ya bude motar sakeena ya xauna ya rufe. Sageer ya jinjina kai wannan kadai ta isa hujjar cewa cikin Deni sakeena keso ta qaqaba masa, ya fita ya barta a gida xaune dake munafukace bata nuna masa xata fita ba amma yana fitowa ta dakko mota ta taho fadawa kwartonta sun sami ciki xasu haihu.
Yana rufe motar ta dubeshi ranta a matuqar hade ta daure fuska tamau, kafin tayi magana ya rigata da cewa "Bari inwa Barrister waya inji ya isa court din" ta daga masa hannu da cewa "Dakata Nura! Ba wannan shirmen nakane ya kawoni nan ba, naxo ne infadamaka ni Allah ya shiryeni kuma nadawo rakiyarka, dan Allah dan darajar al qurani ka rabu dani inyi xaman aurena kayi nesa da rayuwarmu ni da sageer domin munason juna, kuma ba kwace wayata yayiba kamar yacce kake xata nice na kasheta saboda karka kirani. Nasan kasan darajar aure saboda shiya samar dakai, kuma baxakaso wani namiji ya dunga bibiyar matarka ba yacce kake bibiyata don haka kaji tsoron Allah ka kama gabanka ka koma inda ka fito👏🏽"
Baki bude Deni ke kallonta harta gama magana, yayi dariya yace "Haba sakeena ki denamun irin wannan wasan plz saida abu yaxo gangara xaki shigo da shaqiyanci ciki? Nasan baxaki tabason wani namiji a duniya bayana. Kinga duk abar wannan batun naxo da maqudan kudi suna mota koda xa a buqata a court din, inkinaso ma ayau xa a iya daura mana aure tunda babu iddah tsakaninku"
Ta katseshi da cewa "Baxanso kowanne namiji ba bayan kai saboda tare aka haliccemu? To xuciyarka ta fada maka qarya wlh domin yanxu tsuntsun son ya tashi daga kanka ya koma kan sageer. Xancen iddah kuma tare da daura aure da kake fada babu shi domin ina me sanar maka ina dauke da cikin Sageer" cikin matuqar kaduwa Deni ke kallonta tunda tai batun yanxu sageer takeso har ixuwa kan tana da ciki.
Ya xaro mata idanunsa da tashin hankali ya mayar dasu jajaye cikin qanqanin lokaci yace "Kina nufin kin bashi kanki? Kina nufin harya miki ciki? Kincifa amanata kenan?" kafin takai ga bashi amsa ya damqo hannunta yana kici kicin rungumarta yana cewa "Ai tunda kika bashi jikinki nima sai kin bani, sai dai ki haifi dan mutum biyu kuma ai nima da nawa auren yayi miki ciki" Ta fara kici kicin kwatar kanta amma ta kasa saboda a mota suke.
Duk abunda suke akan idon sageer, lokacin dayaga Deni ya riqo sakeena ya runtse ido ya kawar da kansa gefe guda. Ta samu ta kwace hannunta daya dakyar ta xabgawa Deni wani bahagon mari, babu shiri ya cikata ya dafe kunci yana mata kallon mamaki. Ta fara magana idonta jajur tana kwallah "Nura ka nutsu dan ubanka, shege dan akuya haihuwar kasuwa, yauma halin naka na akuyanci xaka gwadamun? Tabbas baka da lefi duk lefinane da nabari soyayyarka ta karya da yaudara tayi tasiri akaina. Na manta cewa tun farkon alaqarmu dakai batamun rayuwa kaso kayi, na cika jaka dabba dana manta kai tsatson Hajjo ne matar data tsaneni fiye da komi a duniya, namanta lokacin da kake dukana a gidan haya aimun dariya da gori, na manta lokacin da kace baka qaunata acikin dubban mutane da yan jarida a kotu ka sakeni kuma kaje ka auro kalar matar data dace da kai kabarni cikin qunar xuciya. Tur da wannan makauniyyar xuciya tawa wacce ta kasa gane cewar kaine babban maqiyina wanda ya taso gari e gari tundaga Kano xuwa Lagos don gurbata rayuwar aurena da kuma rabani da masoyina na gaskiya, andade ana fadamun ba sona kake ba yaudarata kake da kuma muguwar sha'awar da kakemun, amma kash bangane ba sai yanxu daka qara fitomin da halinka kuma duniya taimun nata karatun wanda dole nagane ko naqi ko naso, na cuci kaina dana biyewa shege tsinanne mayaudari irinka naci amanar mijina kuma na sabi ubangiji na, wlh inbaka daina bibiyata ba xan kaika kotu infadi lefin da muka aikata ni da kai duniya tai maka tofin Allah tsine kuma in bata maka suna"
Ta fashe da kuka bayan gama fadar haka, ta bude motar ta fito. Deni shima yayi wuf ya fito ya tare gabanta ya tsuguna, Sageer yayi qasa da glass din motar don ya jiyo abunda suke cewa. Cikin tsananin tashin hankali Deni ya fara magana "Sakeena kiyi haquri nayi kuskure amma wlh na tuba ki yafemun baxan iya rayuwa babu keba xan iya rasa raina akanki, duk abunda kikace naji nayi amma kiyi haquri karki hukuntani ta hanyar datse alaqarmu, raba xuciya da abunda dakeso quntatawa xuciya ne sakeena karkimun haka" ya fashe da kukan gaskiya, sabanin wanda yakeyi a baya na yaudara. Ta kewayeshi tayi gaba itama nata kukan take na nadamar abunda tayi da kuma yunqurin fyaden da Deni yaso yimata yanxu. Yadda Allah ya taqaitama gurin babu motane sosai tunda gurin parking ne, da sauri Deni ya miqe yabi bayanta yana ihun kiran "I LUV U Sakeena" ya fada yafi sau shurin masaqi. Ta qara sauri don karya tadda ita, ganin haka shima ya xura da gudu yasha gabanta ya xube qasa yana kuka da wasu kalaman da tashin hankali da kuma tsanar datai masa yasa ta kasa jinsu.
Ganin yana xube gabanta durshan ta kwasa da gudu ta fada motarta wadda bata kashe ba tai mata key taja ta da gudu, kafin ya koma tasa motar ya bita harta bace masa. Sageer kansa ya kuma daurewa, to mekenan? Da alama dai fada sukai tunda yaji Deni yanata bata haquri kuma suna kuka duk su biyun.
Sakeena ta samu kanta cikin wani irin yanayi irin wanda ta kasance lokacin da Hajjo ta bata mata suna, ta shige dakinta ta xauna a qasa dirshan tana kuka cikin tsantsanar nadama da kuma mugun tsanar Deni irin tsanar da bata tabayiwa wata halitta ba, tai kuka ta kuma yi, ta jingina da drawer ciwon kai da xaxxabi sun rufar mata kanta yana cikin tsakiyar gwuiwoyinta tana raxgar kuka, sallace kawai take data ita a gurin wacce acikin sallar ma ta rasa abunda xata roqa domin kunyar Allah takeji na saba masa da tayi ta hanyar cin amanar aure.
Tana xaune har bayan sallar la'asar kanta wani irin ciwo yake jijiyoyin kan duk sun tashi sunyi rudu rudu, idonta yayi wani irin jaaa babu kyan gani ko gani batayi sosai. Tana wannan halin taji shigowar Sageer, ta bada rabin awa da shigowarsa ta tabbatar da ya kimtsa xuwa yanxu. Ta miqe ta dauki wayarta wacce ta dade akashe acikin drawer ta nufi dakinsa da nufin aiwatar da abunda xuciyarta ta fada mata.
Tana bin bango harta murda kofar dakinsa ta shiga, yana tsaye jikin madubi yana saka riga, dan haka ta cikin madubi ya ganota, yayi saurin juyawa don ganin yadda idonta da fuskarta sukai jajur suka kuma kumbura. Ba tare data dubeshi ba, kanta yana qasa ta miqa masa wayar hannunta tace "Gashi kayi haquri, naci amanarka batare da saninka ba, ta hanyar qullah alaqa da Deni da nufin mu kashe aurenka in koma gidansa. Banda haka ban aikata komai wallahil azim, Allah shine shedata ban bari anshiga gonarkaba kuma ban keta alfarmarka ba ta hanyar maganar batsa ko kuma wasan banxa. Wannan wayatace inka duba xaka sami hujjar duk abunda na fada maka. Kuma bani da buqatarta domin itace shedaniyar data kuma hadani da Deni. Inka tabbatar da gaskiyata kayimun hukuncin da duk kaga ya dace dani, domin naci amanar aure kuma na toxartashi." ya karbi wayar jikinsa a sanyaye shima, ta qara share hawaye ta juya ta fita tana hada hanya.
Jikin Sageer yayi wani irin mugun sanyi ya xauna dabas a qasa shima, ya kunna wayar sakeena yana tunanin kodai ta ganshi ne yau a makaranta? Yana kunnawa text messages suka dunga shigowa duk na Deni ne saina Hassana da Qudurat. Ya fara bibiyar texts din yawanci na jaddada qauna ne da kuma kalaman soyayya sai kuma na yadda yake fada mata hanyoyin da xatabi ta gallaxawa shi sageer din, ya saketa. Ya tafi kan chats dinta na wtsaup, ba tare daya kunna data ba shima dai duk daya, kalaman soyayya ne tsantsa wanda da wahala a fadawa mace su bata rufta ba, sai audios da yake mata na muryarsa yana fada mata ya kasa bacci itana sonsa kawai ta fito su koma aure. Bai kama sakeena da lefin komai ba domin yawancin amsarta bata wuce Eh ko kuma A a inkuma yayi mata Kalaman soyayya tayi murmushi ko kuma insakata tayi abu tace to. Ko shi kansa Denin baxaice yana mata maganar batsa ba balle kuma sakeena da maganganunta basu da yawa a gaba days chat din.
Yayi Hamdala bayan ya gama caje wayar tsaf kuma sakeena ta kubuta daga xargin da yake mata, ya gane dalilin fadansu ayau da Deni donta fada masa tana da ciki ne. Allah sarki, saita bashi tausayi shiyasa baa son xato domin xunubi ne. Yayi wa Deni text message da wayar sakeena yace su hadu a can wani kebattacen guri awata unguwa gobe da misalin 11 AM zasu tattauna akan makomar rayuwarsu. Ko minti uku beyiba da turawa saiga amsar Deni.
"To Baby, ko kefa Allah ya kaimu goben, xan bar duk abunda nake inxo saboda kinfi komai mahimmanci a duniyata yanxu, ina qara baki haquri kan abunda ya faru daxu wlh bada niyya nakai hannuna jikinki ba na gigitane da naji kina dauke da cikin Sageer. Sai goben ki fito da shirinki daga nan mu wuce court mu shigar da qara sai kawai acire cikin muyi aure, I LUV U"
Sageer ya jinjina kai cikin yaba jahilci da kuma taaddancin Deni, ya kashe wayar gaba daya ya cire layukan ya cillata jakarsa ta aiki. Yayi dariya yace "Yaro bakasan wuta ba saika taka, bakasan Lagos ba shege dan qauye ka kawo kanka mayanka, Area boyz xansa su dakko min kai su koya maka hankali a gabana inda ko sunan sakeena kaji an ambata saika raxana." ya xaro takaddar sakin daya rubutawa sakeena ya fita kicin ya qonata qurmus ya watsar da tokar a shara, yasan a guntun iliminsa na addini da yake dashi sakin beyiba tunda bai bataba kuma babu wanda yagani koya sani saishi. Cike da farin ciki ya dauki mug ya hada mata tea me kauri da xafi ya nufi bedroom dinta da nufin ya kaimata tasha dan ya tabbatar da bataci komai ba, ya kuma lallasheta yaji dumin babynsu wanda zargi ya kusa yasashi ya xubar dashi da kansa.
Xamu hadu ranar litinin in shaa Allah.
Hajia 😊
[8/21, 12:27 PM] A A Dboy: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣8⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
Sakeena ta dawo dakinta bayan miqawa Sageer wayarta ta samu guri ta takure akan gado tana rawar dari garin gaba daya yayi sanyi ga AC a kunne ta kasa kashewa, xaxxabin jiya da ciwon kai ya dawo mata saboda kukan datasha. Mamakin toshewar basirar da tayi takeyi, wai itace yau da aurenta take dating wani har yayi rape attempt dinta? Kuma waninma wai Deni mutumin da ya wulaqantata tayi wani irin xaman aure na wahala a gidansa kafin yayi arxiqi ya fara kunyar nunata a matsayin matarsa, mutumin da ya kasa nema mata lfyar ido duk da yasamu halin yin hakan, mutumin da agaban Iya da Baba ya daketa kuma ya xaxxageta tare da yimata iqirarin tayi xina, mutumin da shi da uwarsa da yan uwansa sukai mata rubdugu suka sakota a gaba ita da uwar riqonta akan abunda ta silarsu ya sameta, mutumin da ranar daya fara ganinta a rayuwarsa ya kafa mata dokar hana taba komi na gidan kamar kuturwa, mutumin da uwarsa tai sanadin da bacin sunanta da fantsama hotunanta a duniya wanda dalilin hakan ita da Iya saida ko xaman tsakar gida ya gagaresu. Ita kuwa wace irin daqiqiyace data dauki Deni masoyi? Ina iqirarin da tayi agaban su Iya da Baba na cewa ta manta dashi? Wai meye ajikin Deni naso da take masa wannan soyayyar ta rashin xuciya? Da farko dai Deni ba asaline dashi me kyau ba balle ace xaa soshi kodan asalinsa, sannan shi bawani addini gareshi ba, gashi kuma bashi da dadin mu'amala saboda saurin fushinsa, baxata kirashi mummuna ba kai tsaye domin baya cikinsu, sannnan gashi sangangan babu fasali kamar tsani, ta bakin Iro yace me qirar yan ta'adda. To wai shin meye abun so ga Nura Lawan ne data kwallafa rai akansa tana sabawa Allah tana kuma baqantawa magabatanta da masoyanta rai akansa? Ta nisa cikin tunanin cewa tsoron Deni takeji, tabbas tsorone irin wanda soyayyar quruciya take haifarwa, wannan dalili shiyasa duk abunda ya sakata sai tayi koda kuwa bataso kuma koda xata batawa kowa rai.
Amma ta godewa Allah daya saka ta farga kuma ta dawo rakiyarsa kana ta warke daga mugun tsoron da take masa a yau. Ta dakko tunanin Sageer wanda tsoron Deni ya hanata tasa soyayyar tasiri aranta, Allah sarki bawan Allah me sanyin hali da sonta da kuma kyautata mata. Ta tuno maganar Nura qaninta ana saura yan kwanaki ya mutu, inda yake cemata "Ya Sakeena Allah ya cika miki burinki ya kuma kawo me temakonki" to kodai Sageer ne wanda Nura yake nufi me temakon nata? Tabbas babu makawa sageer ne domin ta hanyarsa kawai take ganin cikar burinta, a qarqashin inuwar aurensa ne ta samu cikakken yanci har ta samu damar yin iskanci don tsabar rashin sanin ciwon kai. Haqiqa Sageer ne, amma meyasa bata gane ba sai yanxu da komai ya tasamma kwabewa? Ta tuno yanayin Sageer tun bayan dawowarsa aiki jiya inda ya dunga hade rai da kuma basar da ita har xuwa kan cewar da yayi indai cikin jikinta dan halak ne yanaso. To meye dalilin wannan furuci nasa? Kodai ya gane tana da gurbatacciyar alaqa da Deni? Menene dalilin waccan magana da canjawarsa tafar daya jiya? Innalillahi wa'innah ilaihi, wane irin bala'i ta janyowa kanta mijinta na aure yana xarginta da yo ciki daga waje ta kawo masa? Lallai tsuntsun da yaja ruwa, yanxu duk haqurin sageer da soyayyar da yake mata ta qureshi kenan? Me gari ya waya? Ta xubar da mutuncinta, ta sabi ubangijinta, ta bata xaman aurenta mijinta yana xarginta. Shikenan ta shiga uku ta lalace, haqiqa duk wanda ya toxarta aure saiya wulaqanta.
Ta qanqame jikinta ta qara sakin kuka, ta kwanta kan gadon tana riqe da gwuiwoyinta haqoranta suna hadewa tana cewa "Sageer kayi haquri ka yafemun wlh banyi fasiqanci ba, cikinka ne a jikina bana Deni ba, ta'addanci na be kai inyi haka ba" Wannan taita maimaitawa har qaramar kwakwkwalwarta ta gaxa daukar damuwar da take ciki ta sume a gurin.
Sageer ya turo qofar dakin ya shigo da sallama, ya fara kiran sunanta a xatonsa bacci take, ya ajiye tea din akan loka ya hauro gadon yana cewa "Tashi sakeenatu kisha tea sai muyi magana" ya dagota, yayi matuqar raxana da yasamu idonta a bude hancinta da yana tsiyayar da ruwa bakinta kuma a datse, jikinta wani irin xafi wanda ya wuce kima. Ya fara jijjigata yana kiran sunanta a raxane, amma ko gixau batai ba. Ya kwantar da ita ya nufi falo da gudu, Maitama da Bilki sun dawo daga unguwa suka biyo ta gidan suna tsaye a falo ganin babu kowa, Sageer ya wucesu ya nufi kicin suna tambayarsa amma be kulasu ba, ya dawo da robar ruwa ya koma daki da sauri suka rufa masa baya.
Sukayi mugun ganin sakeena a sassanqame, ya dagota Maitama ya bude ruwan ya watsa mata a fuska. Bilki ta fita da sauri taje maqotansu ta kira matar abokin su Sageer wacce ke aikin asibiti, jin cewa sakeena ce babu lfy ta debo kayan aiki a chemist dinta dake cikin gidan suka juya tare da Bilki. Sun tarar dasu Sageer sunata aikin watsa mata ruwa amma ko gixau batai ba. Da sauri nurse din ta xauna suka bata guri ta fara auna BP din sakeena sannan ta dakko wata allura ta hada tayi mata. Ta qara dakko wata allurar ta dubi Sageer tace "Tana da ciki ne?" cikin sauri yace "Eh na sati 3 ne cikin" Maitama da Bilki suka kalli juna a tare. Ta maida allurar, ta dakko drip tayi wata allurar aciki ta jona mata, ta qara auna BP dinta da kuma bugun xuciyarta, tasa Sageer ya kawo jiqaqqen towel ta ninkashi ta dora mata akan goshinta saboda xafin da kan yayi. Ta miqe tana hada kayan aikinta tace "Babu damuwa stress ne yasata suma ga kuma xaxxabi jininta yadan haura kadan, amma babu damuwa komi ya dai daita namata allurar bacci"
Suka hada baki gurin yimata godiya, Sageer ya bita ya ciro kudi ya bata kudinta amma taqi amsa tace kudin kayan aiki kawai xata amsa ai xaman tare yafi komi. Ya dawo ya dora kan sakeena akan cinyarsa, su Maitama suna masa tambayar yadda hakan ta faru, yace ya dawo office ne yayi wanka ya shigo daki ya sameta haka.
Sakeena ta bude idonta a firgice ta kalleshi sannan ta maida idonta kansu Maitama tace "Anty Bilki kubawa Ya Sageer haquri na masa lefi yayi fushi dani kuma Allah baya yafe haqqin wani saiya yafemun Allah xai yafemun, inna mutu a wannan halin wuta xan tafi" suka dubeshi da alamar tambaya, ya waske da cewa "xafin xaxxabi ne yasata surutai" Maitama ya qura masa ido yace "Wannan maganartata ba sambatu bane, gaskiyan abunda ke xuciyarta take fadi, kuma da alamu ta dalilinka ta shiga wannan halin, be dace ace xaka wulaqantata ba a daidai lokacin data saduda ta kwantar da kai danku xauna lfy" ya sunkuyar da kai yace "Eh wai wayarta ta yar inata kira ba a daga ba ni bansan ma ta yar ba saidata dawo dake fadamun wayan ya fadi shine nayi mata fadan sakacin da tayi saboda wayar me tsadace"
Bilki ta riga Maitama magana "Haba Sageer mecece waya acikin arxiqinka da har dan tayar xakai mata fada? Ai ko ita da kanta tana iya sayawa kanta waya duk tsadarta bare kuma kai, dan Allah karka qara Sakeena qaramar kwakwkwalwa gareta yanxu dubi yadda ta xama adalilin wata banxa waya" yayi saurin cewa "In shaa Allah baxa a kuma ba Haj Bilki" Maitama dai bai yadda da maganar Sageer ba yayi shirune kawai saboda qure mutum babu dadi kuma kowa yana da sirrinsa wanda bayaso kowa yasani amma yasan tabbas ba haka xancen yake ba. Sakeena kuwa kallon Sageer take babu ko qiftawa cikin yadda da soyayyar da yake mata, ya rufe lefinta don kare qimarta da martabarta ga babban amininsa ya dorawa kansa lefin, lallai ta kusa taiwa kanta asarar rasa babban masoyi irin Sageer. Da haka har allurar da akai mata ta soma aiki bacci ya kwasheta, ya gyara mata kwanciya suka fita dasu Maitama xuwa masallaci ya kira Inna yace ta kula da ita kan yadawo karta cire drip din.
Koda ya dawo masallaci sata yayi agaba riqe da hannunta yana kallonta cike da soyayyarta da kuma tausayi, bai iya saka komai a cikinsa ba har lokacin da ruwan ya qare ya cire mata ya samo towel da ruwa ya goge mata jikinta tas kamar yadda nurse din tace sannan ya saka mata rigar bacci marar nauyi ya gyara mata kwanciya shima ya kwanta kusa da ita. Ta farka can tsakiyar dare, ta tashi xaune takai dubanta ga Sageer dake bacci a gefenta ta qura masa ido kafin tunanin qalubalen dake gabanta ya fado mata, ta sauka daga kan gadon a hankali saboda karta tadashi, ta fita falo jikinta yayi sauki babu xaxxabin sai dan ciwon kai kadan, ta qara bude qofar falon wacce ake rufewa saboda dare ta fita ta xauna akan barandar gurin iskar damuna na kadawa tana ratsanata, ta lumshe ido ta fada kogin tunanin yacce xatai Sageer ya yadda cikinsa ne a jikinta, tayi iyakar tunanin ta taga bata da mafita da wuya ya yadda da ita tunda ya fara xarginta kuma aurensu ya gama lalacewa tunda zargi ya shigo ciki. Ta fashe da kuka irin na rashin tudun dafawa.
Acan daki kuma Sageer ya juya tare da bude ido, yakai dubansa makwancin sakeena yaga wayam babu ita, ya tashi da sauri ya leqa toilet bata nan, ya fita falo nanma babu ita, hankalinsa yakai kan qofar shigowa falo dake bude da sauri ya nufi kofar yana ayyana kardai sakeena fita tayi a cikin wannan tsohon daren. Yana fito yaci karo da ita xaune dirshan tana sanaar tata wato kuka. Jiki a sanyaye yakai hannu bayanta ya tabata yaname xargin kansa da sakata cikin wannan halin, ta juyo a firgice tai arba dashi cikin muryar kuka tace "Ya Sageer wlh banci amanarka ba, na rantse da Allah cikinka ne a jikina, ni din tun ina kwana da yunwa tun bani da me bani koda ruwan sha ne kyauta, tun ina gararin bauta da aikatau, tun ina daukar nauyinmu ni da Nura qanina, tun ina daukar nauyinmu ni da Deni banyi fasiqanci ba sai yanxu? inbaka yarda ba kaban Al Qur ani in rantse dashi" ya runtse ido cikin tausayinta a xuciyarsa yace "Lallai Deni xai dandana kudarsa tunda yayi sanadin xubar hawayenki tundaga jiya xuwa yau" ya riqo hannunta ya dagota xuwa jikinsa suka shiga ciki, ya ajiye kan kujera ya tsuguna a gabanta yace "Sakeena bana xarginki wlh, kuma koda na xargeki a baya yanxu gaskiyarki ta fito kin kubuta daga xargina, kiyi haquri ki daina kuka ina sonki ina kuma son abunda ke cikinki" yakai hannunsa kan mararta ya shafa, ta ware ido tana kallonsa tana tunanin da gaske yake ko kuwa dan ya kwantar mata da hankali ya fadi haka? Ya katse mata tunani da cewa "Bari in hado miki shayi kisha ko?" ya tashi yaje ya hado mata cikin mug da cake a plate, amma qiriri taqi sha tace sai dai susha tare, hakan yayi masa dadi don shima yanajin yunwa, ya dunga diba da spoon yana bata shima yana sha sunacin cake din har suka gama, ya dauketa suka koma dakinta suka wanke baki suka kwanta tana rungume dashi.
Koda safe shine ya temaka mata tayi wanka ta shirya batasa a ranta xata makaranta ba shima kuma beyi niyyar taje ba don bata gama watstsakewa ba, yasa kayansa na aiki suka fito kan dining sukasha tea tare yaci dumamen tuwon shinkafar da Inna tayi jiya basu ci ba, ita kuma tana gama shan tea din ta kame akan kujera tayi tagumi tana kallonsa. Ya dubeta yace "Baby wannan kallon duk ni daya? Naga bakici me nauyi ba nasan kuma kina tare da yunwa" tayi murmushin jin kunya ya kamata tana kallonsa, tace "Ni dan wake xanci shi nake sha'awa" ya waro ido yace "Dan wake yanxu da safe Baby?" tayi dariya gami da marairaicewa tace "Yaya tun jiya da dare nake mafarkinsa" ya danyi dariya yace "Sry Baby, bebina yanxu xaitasaki ciye ciye ko baki so" ya miqe ta miqa masa tissue paper ya goge bakinsa, ya ciro wayarsa a cikin aljihu qarama ya miqa mata yace " Ungo riqe a hannunki wayatace da layina ciki ba kowane ya sanni da layin ba, xan kiraki inji jikin naki" tayi baya da sauri tana girgixa kai tace "A a Ya Sageer ni yanxu banason waya tsoronta nakeji, xamana haka babu ita yafiye mun kwanciyar hankali" ya kamo hannunta ya danqa mata wayar yana cewa "Haba haj sakeena me kunun aya karbi mana babu komi da xai faru tunda kina da Muhammad Sageer, in banji yanayin jikin naki ba hankalina xai gaxa kwanciya" ta karba don karta bata masa rai ta riqe a tsorace gani take kamar Deni xai kirata duba da yacce suka rabu jiya.
Suka fito tana rungume a gefen jikinsa tayo masa rakiya, yasa jakarsa a mota ya dago ya sumbaci goshinta, don ya gwadata yace mata "Yanxu me xakiyi?" tace "xuwa xanyi inyi danwaken inci sai in kwanta bacci nikeji sosai" yace "yawwa Baby, to ki ajiye wayar a kusa xan kiraki" tace "To" yana shirin shiga mota ta sumbaci lebensa ta xura da gudu tai cikin falo, ya saki murmushi cikin mamakinta ya shiga mota yana goge lip dinsa inda ta shafa masa lipstick.
Kamar yadda ta fada dan wake tayi na fulawa taci da manja da yaji tasha kunun aya ta koma bedroom ta miqe a gado.
Wajen qarfe goma Sageer ya dawo gidan ya ajiye motarsa a waje, yaxo ne domin ya tabbatar da gaskiyar abunda ta fada masa na cewa bacci xatai karyaje ya yadda da ita ta fice su hadu da Deni. Yayi sa'a bakowa a falon, direct ya wuce dakinta ya sameta kwance tanata sharar baccinta. Ya saki ajiyar xuciya ya koma da baya a hankali ya qara tambayar me aikinta dake xaune harabar gidan yace "Madam ta fitane?" tace "A a tunda ta rakoka daxu ta koma ciki bata qara fitowa ba" ya jijjiga kai ya fita ya kirawo yaran da yasaka su dakko masa Deni ya fada musu inda xasuje da kuma gurin da xasu kaishi in sun dakko shi.
Ya koma office yaci gaba da aikinsa hankali kwance, ya gama yadda da matarsa ya tabbatar da nutsutstsiya ce wannan dan iskan ke neman kangarar da ita. 11:17 AM suka masa waya da cewa komai ya kammala, ya xari key din mota yayiwa gurin tsinke.
Ya shiga dakin da yasa aka kai Deni, suna tsatstsaye shi kuma yana xaune a kujera bakinsa a fashe, ya kallesu yana tambayarsu yadda akai, Babbansu yace "Oga ya danso yayi mana taurin kaine akan waccan gwangwanin (mota) shine muka mommolata muka dan silalashi saboda ya nemi ya kawo raini shine ka ganshi haka fa, shege ashe mugun ragone, ajawo kawai, gashi da jikin qarfafa amma ana tabashi yayi tubus."
Sageer yayi dariya ya xare glasses din fuskarsa yana kallon Deni, shima Denin shi yake kallo ya miqe yana nunashi yana cewa "Dama kaine kasa aimun haka? Kaine ka kawoni nan gurin?" Sageer cikin murmushi yace "Eh nine nai amfani da wayar sakeena nasa aka dakko ka domin amsa wasu tambayoyi da kuma yimaka tarbiyyar da gyatumarka ta gaxa yimaka" Deni cike da fada ya tasowa Sageer yana cewa "Karka qara sako uwata cikin wannan maganar, sannan inka isa kai namiji ne mukara ni da kai ba wadannan qartin banxan xakasa su dakkoni su dakeni ba, Sakeena kuma tawa ce kuma na tabbatar indai tasan abunda kaimun wlh ta gama xama dakai" ogansu ya tashi ya nufi Deni, Sageer ya daga masa hannu, ya daga qafa ya kaiwa Deni wani duka a qirji sai gani a qasa wanwar, ya dago da mamaki yana duban Sageer. Sageer yayi dariya yace "Ai ba girman jiki bane abun, qarfin xuciya ne. Sannan ka fadamun dalilin da yasa kake bibiyar matata da kuma son kashemun aure"
Deni yayi qoqarin shanye dukan Sageer, yayi dariyar qarfin hali yace "Kana nufin dan wannan abunda kaimun shi xaisa in saduda? To bari kaji na shirya shanye duk wata aquba akan Sakeena" Sageer yayi dariya yaja baya yace dasu "Ku tambayeshi" ogansu ya matsa ya cire tabar da yake xuuqa ya mutstsukewa Deni ita a tafin hannunsa, ya saki qarar axaba, ogan yace "bashi amsar tambayar da yayi maka" Deni cike da ixxa yace "Baxakaji komi ba duk abunda xakaimun" daya daga cikinsu ya sheqe da dariya yace "Lallai wannan besan Area boys ba, guys mu tambayeshi" suka rufar masa da duka kota ina suna takashi da banyan takalman qafafunsu yana ihu cikin tsabar axaba daga qarshe daya a cikinsu ya kaiwa hantsar Deni bugu da qafarsa, Deni ya shide cikin axaba yace "Kuyi haquri xan fada. Wlh sonta nake nakasa jure rashinta shiyasa nasaka ta kashe aurenta mu koma aurenmu saboda nasan itama tana sona"
Sageer ya tako a hankali ya hanasu dukansa yace "Kayi kuskere Nura domin yanxu sakeena ta tsaneka kuma da hannunta ta kawomin wayarta tare da yimun bayanin duk abunda kasata tayi" Deni ya share hancinsa da jini ke fita yace "Indai gaskiya kakeson ji to wlh nine wanda sakeena keso kamarta mutu kuma na tabbatar da baxata qara son wani ba bayan ni" Sageer yayi murmushin takaici yace "Ni bana abu babu Hujja bari in tabbatar maka da Sakeena yanxu bata sonka.
Ya ciro wayarsa ya kira layinsa daya bawa sakeena daxu ya sakata a hands-free. Tana bacci kiran wayar ya tasheta, ta dauka cikin sassanyan murya tace "Ya Sageer ina sonka" Ba Deni ba hatta Sageer kalmar ta dokeshi kuma ta bashi mamaki, ba don ya tabbatar da sakeena batasan ya dauke Deni ba da sai yace da gayya ta fadi haka. Ya shanye mamakinsa yace "Sakeena nima inasonki, ya jikin naki? Ya kuma Baby na?" cikin muryar shagwaba tace "Jiki da sauqi, ina cikin baccina me dadi da mafarkinka ka tasheni, Babyn ka kuma lfy sai duminka da yayi missing" yace "Ayya! sry my luv koma baccinki nima sonki ne ya addabeni shiyasa na kiraki inji muryarki" Deni ya fara ihu da kiran sunanta, Sageer yayi saurin disconnecting kiran ya dubi Deni dake ihu yana cewa "Wayyo Sakeena ki ceci rayuwata, karkimun haka ina sonki munsha wuya tare kixo muji dadi yanxu, karki yaudareni ki yafemun abunda nai miki abaya inkika barni rayuwata xata watse"
Sageer kallonsa yake da mamaki, yaran kuwa dariya kawai suke ganin duk akan mace yake wannan ihun banxan. Yace "musu ku cika aikinku ayi masa tarbiyyar dauke ido daga kan matar wani" suka fito da gorori suka rufar masa, ya fara ihu yana ambaton sunan Sakeena, Sageer ya qara cewa "Aita dukansa har saiya daina kiran sunan sakeena" sukacigaba da dukansa tun qarfinsu, sai gashi Deni ya fara kiran "Wayyo Allah na" Sageer ya kwashe da dariya yace "Ku kyaleshi ya dawo hanya, wannan ba dukan lefin da kayimun bane kawai, harda dukan da kaiwa sakeena lokacin da tana kurkukun gidanka." ya dakko bundle na 1k ya cilla musu, suka chafe tare da ambaton "Sai oga da girman kujerar ka" ya qara cemusu "Nagode sosai, ku daukeshi ku sakashi a akwalar motarsa ku ajiye inda kuka tabbatar baxa'a ganshi ba balle a temakeshi sai xuwa lokacin da jikinsa yayi tsami" suka amsa da "angama oga" ya juya xai tafi Deni ya bishi da kallon tsoro yana cewa "Dan Allah karka barni da wadannan marasa imanin qarasa kasheni xasuyi, kaga kai musulmi ne dan uwana kuma dan arewa kodan haka ka taimakeni" Sageer ya kuma yin dariya ya juyo ya dawo yana kallon Deni yace "Yawwa na manta ban fada maka ba, inkanaso in tabbatar da kai dan iskane to ka kaini qara ka fadi abunda nai maka kaga daganan sai reshe ya juye da mujiya irin yadda mahaukaciyar uwarka tai qarar sakeena qarshe abun ya dawo kanta" Deni ya kuma tsorata da Sageer kamar yasan abunda yake shiryawa kenan yana fita daga nan gurin, amma kuma yanxu ya fasa domin Sageer yana iya budewa hukuma abunda yayi kuma sakeena ta bada shedar cewa gaskiya ne daga nan a cillashi gidan yari. Cikin rawar baki yace "Wlh indai har ka temaka ka rabani da wadannan yaran babu wanda xan fadawa, kuma sakeena na bar maka ita har abada" Sageer ya juya ya fice Deni na kwallah masa kiran "Oga Sageer na tuba kaimun rai zasu kasheni" Aikuwa suka kumayi masa qawanya suka qara tumurmusashi har saida ya suma sannan suka debeshi kamar kayan wanki suka kai mota, suka xare masa waya da yan kudaden jikinsa suka kaishi can gurin da babu mutane suka sashi a motarsa suka ware.
Sai qarfe biyun rana Sakeena ta yakice baccin ta tashi da kyar tayi sallah, batajin yunwa ko kadan dan haka malt kawai tasha ta kuma komawa baccin da har yanxu ya kasa isarta. Qarfe biyar din yamma ta tashi dakyar taje tai wanka tayi sallah tayi axkar ta tsantsara kwalliya saboda tasan duk inda Sageer yake ya kusa dawowa. Ta fito falo tayi kan dinning ta bude food warmer, tai karo da taliya da miya, tai saurin rufewa, ko kadan bata burgeta ba, ta nufi kicin tasamu Inna na aikin girkin dare ta durqusa har qasa ta gaisheta ta amsa tana tambayarta jiki, tace taji sauqi. Ta hada golden morn saboda yunwa takeji, cokali daya tayi ta ajiye taji yana qoqarin sakata amai. Tadau waya ta kira Sageer, ya daga yana cewa "Ran gimbiyata ya dade" tace "Ya Sageer dan Allah inbabu damuwa ka tahomun da shawarma mana" yace "Wace irin damuwa kuma? Ai kawai umarni xaki bayar in cika ranki ya dade, ki jirani nan da qanqanin lokaci" ta kashe wayar tana dariya. Harya karyo kwanar gidan ya juya ya koma yaje ya siyo mata sai da ya jira aka hada tukun sannan ya taho.
Yana sallama ta nufeshi da sauri ta rungumeshi, shima rungumeta yayi suna dariya a tare. Ta jashi bedroom, suka baje ledar shawarmar sukaci tanaci tana bashi abaki shima yana gutsura, saida sukaci ta ishesu sannan ta fitarwa su Inna da ragowar. Suka dawo suka dasa hira tana kwance jikinsa kamar mage, saida lokacin sallah ya taho sannan ya tashi yayi wanka ya fita.
****** ******** ******** ****** ****
Washegari juma a ya fita aiki bayan tayo masa rakiya kamar jiya suka rabu cikin kewar juna, duk da har yanxu bataga sakin jikinta ba tana kunyar abunda tai masa. Amma ta qudure aranta yau xata fada masa abunda takeji game dashi inya dawo.
Acan kuma Deni sai wayewar garin yau wani bawan Allah ya ganshi kwance a mota kamar matacce, ya duba ID card dinsa na aiki yaja motar ya kaishi ma'aikatarsu, sun kidime da ganin haka aka kira police ya tsaya musu asibiti suka karbeshi yace musu suyi haquri daganin wannan aikin Area boys ne ya shiga sabgarsu sukai masa haka. Ya samu kulawa a asibiti sosai suka gyara masa targaden da yayi gurare kusan biyar a jikinsa da kuma muggan raunuka, amma har xuwa wannan lokaci a sume yake be farko ba.
Ta tsefe kanta ta shiga kitso maqotansu daga can tai gidan Bilki, Bilki tace "Ai kuwa dai naji kunya sakeena, ban shiga dubaki ba sai gaki kin shigo" tana dariya tace "Babu komi Anty Bilki komi sai Allah ya nufa, kuma na warke sosai ma ko yatsana yanxu bayamun ciwo kitso ma naje shine na shigo mugaisa" tace "Allah sarki nako gode qanwata ya gida yadan Babyn mu?" Sakeena tai shiru tana murumushi cike da kunya, Bilki tace "Dama na fada miki sakeena xakiso sageer indai har kika saka kanki, inda ake sonka nan kake gyara xama kayi dirshan, daka so gara a soka, mata yanxu muna bata lokacinmu gurin soyayyar banxa ta wadanda ba sonmu suke da gaskiya ba, munabin kyale kyalen banxa yayin da ga masoyanmu na gaskiya can na jiran yar dama qanqanuwa su gwada yadda suke qaunarmu. Gashi yanxu da kika dau shawara har kun samu rabo, Maitama mamaki yake wai daga ke har Sageer din munafukai ne kunyi cikinku babu wanda yasani" Sakeena tai dariya tace "Hmm nagode Anty Bilki" a gidan Bilki takai har qarfe dayan rana sukaci wainar fulawar da Bilki tai mata sukai sallah sannan ta koma gida, tayi wankanta tai kwalliya tana mamakin meya hana sageer dawowa har qarfe biyun rana tunda yau juma a?
Tagaji da jiransa har kwalliyar tai sanyi, ta kwanta a falo bacci ya dauketa. Be shigo gidanba sai 6 PM, lokacin harta qara wata kwalliyar cikin qananan kayan data lura yanaso, suka nufi dakinsa tana masa qorafin meyasa be dawo ba yau. Ya bata uxurin cewa meeting sukayi sai yanxu suka gama. Ta dakko masa abinci ta kai masa har dakin yaci suna dan taba hira har aka kira magrib, yayi wanka ya fita, itama ta qara gyare jikinta bayan tayi sallah.
Sai bayan sallar isha ya dawo hannunsa dauke da ledojin fruit, ta karba taje ta wankesu ta yanko ta kawo sukasha, tace masa tana xuwa xataje yin aikin lemon tsamiya saboda yarinyar har yanxu bata gama iyawa ba, yatashi yace "muje intayaki" tace "No yi xamanka kaida ka yini xaune a office, kabari ba wani dadewa xanyi ba na hada kawai duddurawa xanyi a robobin" yaqi haqura saidaya bita.
Ko acan dinma ya hanatayin aikin komi, yace kawai ta xauna har yanxu bata gama warwarewa ba. Shiyaketa durawa a jarkokin yana qullewa yana yimata hirar makaman da suka kwace yau anyo fasa kwaurinsu daga qasashen qetare. Itadai tai shiru tana dubansa cike da soyayya da kuma burgewa, can dai ta kasa jurar abunda takeji akansa batasan yadda akaiba sai ganinta tayi xaune kan cinyarsa ta riqo fuskarsa da tafukan hannyenta cikin sanyin jiki dana murya tace "SAGEEER" ya dakata da maganar da yake da kuma dura lemo a jarka yana kallonta, takai bakinta kan nasa ta fara sumbatarsa kamar xararriya, ya watsar da lemon daya debo a cup shima ya riqota yanawa bakinta wani mugun tsotsa, suka sarqe guri guda sai gasu a qasa kwance, tuni sun watsar da lemon dake cikin bokiti basu sani ba, wanda aka dura cikin jarka aka rufe ne kawai ya tsira (🤦🏽♀) da kyar Sageer yayi qarfin hali ya dagata sukai cikin gida suka yada xango a bedroom dinsa, yana balle shirt din jikinsa ya dubeta a burkice yace "Maimaita abunda kika fadamun jiya dana kiraki a waya" idonta cike da kwallah tace "Ya Sageer ina sonka" ya qura mata ido yace "da gaske kike sakeena? Karfa kisa in haukace miki?" ta dubeshi cikin ido tace "Na rantse da wanda ke busamun numfashi ina sonka" bai qara cewa komai ba sai sumbatarta daya farayi tana mayar masa da martani. A wannan rana dai sunsha shagalin da basu taba irinsa ba, Sakeenatu tasa sageer kuka wurjanjan tare da wasu alqawura masu nauyi da yayi mata. Sukai bacci riqe da juna cikin farin ciki.
Acikin wannan weekend din sukai wata irin dinkewa da wata kalar soyayya me gardi da suke gwadawa juna, kowa a gidan ya fuskanci haka, xuwa masallaci kawai ke fidda Sageer daga gidan cikin kwanaki biyu. Ranar lahadi da daddare ya bata sabuwar waya qal da sabbin layuka, ya bude mata sabon account na watsap da facebook ya fada mata ya xubar da wadancan layukan nata bayan ya kwafe mata contact dinta wayar kuma ya bawa wani yaronsa a office. Tayi murna sosai don tanason waya Deni kawai take tsoro karya qara binciko number ta amma tunda yanxu sabuwa ce shikenan. Ta dunga zabga masa godiya yana murmushi yace mata gobe xata koma makaranta, ta danyi jimm tace "Ya Sageer nifa na haqura da karatun, xan xauna inyi bautar aure innemi aljanna ta" yasa yatsansa a bakinta yace "shiii, Denin banxa, ai bai isa ya hanaki cika burin da kika girma dashi ba, tun randa naji kinason karatu naiwa ubangiji alqawarin tsaya miki kiyi karatu har sai kince ya isheki, kuma bayan haka ni kaina inason inga matata da ilimi saboda yayanmu" idonta cike da kwallah ta fada jikinsa tace "Nagode ya Sageer" yace "Yawwa qanwata ki shirya gobe xaki koma makaranta ki fara sabuwar rayuwa, ki kwantar da hankali Deni baxai kuma dawowa rayuwarki ba domin nasa anyi maganinsa" tana rungume jikinsa bata tambayeshi beyayiwa Deni ba domin ko sunansa bataso taji an ambata.
Tare suka fita washegari Monday, ya kaita har school kamar yadda ta buqata, suka tsaya a car park ta marairaice tace "To ka rakani class mana" yayi dariya yace "Wannan yarinya da shagwaba take, to muje" suka fito suka jera tana riqe da hannunsa saboda tsaro 😜 har cikin class dinsu, sai dai ajin babu kowa ta fara tunanin ko ancanja venue ne, sai ga wani dan department dinsu, ya kalleta tun kan taimasa magana yace "LIMAN (kamar yadda malamai da wasu daliban ke kiranta) kin dubo result ne?" ta dafe qirji tace "Yaushe aka kafe?" yace "yanxu nima daga gurin nake duk ragowar yan ajin suna can suna dubowa" tai masa godiya taja hannun sageer suka juya duk ta firgice gani take batai abun kirki ba.
Sageer yanata kwantar mata da hankali har sukaje gurin, ya tsayar da ita saboda da maxa a gurin ya kutsa ya shiga dubo mata. Ya jima a ciki tana tsaye a gurin cikinta a qulle su Qudrat na mata magana ma bataji ba. Ya fito ya hada gumi, tayi saurin xuwa gurinsa tace "Ya Sageer yaya akai? Nasamu C/O ko a English Literature?" ya dubeta bece komai ba, ta kwabe baki tana shirin kuka.
Ya kyalkyale da dariya yace "To sarkin shagwaba congrats, result dinki yayi kyau sosai kece ta uku a department dinku a mata" ta daka tsalle ta rungumeshi, ya cirota a jikinsa ya manna bakinsa a nata yana tsotsa yace "Kinga yadda akeyi in farinciki ya samu banason choge" Gaba daya kallo ya dawo kansu ganin abun nasu ya wuce runguma harda kiss a bai nan nasi, ta toshe baki cikin kunya ganin idanu akansu, suka kuma kallon juna ita da Sageer suka saki dariya a tare. Qudrat uwar gulma ta matso ta xunguri sakeena cikin rada tace "Keena waye wannan handsome din naga kuna kissing juna?" Sakeena ta fallara mata harara tace "Banason kallon qurullah mijina ne" Maijidda ta matso tace "Shege Liman daman ke matan aurene baki taba fada mana ba?" Sakeeena tai fari 🙄 tace "Bagashi yau kun gani ba" Sageer yana jinsu yana musu dariya, suka gaisa dashi a mutunce xai tafi ya yafito sakeena, cikin sauri taje tace "Nagode ya Sageer, Allah ya saka maka da gidan aljannah Allah ya jiqan mahaifinka" yaji dadin adduarta yace "kema Allah ya jiqan naki, kuma nine da godiya da kika dage kikai karatu naji dadin ganin result dinki kin qaramun qarfin gwuiwar biya miki kudin makaranta, tunda ba asarar kudina nake ba" tana murmushi tace "Ya Sageer na maka alqawari saina buge mutum biyu matan da sukasha gabana saboda ka kawarmun da rudanin da xai hanani karatu (Deni)" yace "Yawwa keena haka nikeso baby na. Yanxu ki jira in kun gama lectures xanxo daukarki ko muje shopping, wannan kyakymyawan result naki ai saida kyauta" tace "To Ya Sageer xan jiraka, I luv u" ya amsa da "Luv u too my angel" suka rabu suna waving juna.
******** ******** ***********
Bangaren mal Deni kuwa saida yayi kwana biyu cur a sume sannan ya farko, ya faracin abinci da magana, koda yan office dinsu suka tambayeshi abunda ya faru dashi sai gilla musu qarya da cewa wasu ne suka tareshi sukai masa fashi suka kuma yimasa duka, koda aka tambayeshi ko xai iya gane fuskokinsu, da sauri ya girgixa kai domin ya tsorata a aika aikar da akai masa kuma garin Lagos ya fita a ransa gani yake kamar xasu qara biyoshi su dakeshi.
Ranar kwana ta biyu da farkowarsa wanda yayi dai dai da kwanakinsa hudu cur a gadon asibiti tsakar dare me jinyarsa yana bacci ya sulale ya gudu daga asibiti ya nufi gidan da suke ciki na ma'aikata ya tattara komatsansa kaf ya loda a molalliyar motarsa ya nufi Kano ba tare daya kammala course din daya kawoshi ba, da nufin shi da Lagos sai dai a kawo gawarsa ko ragowar kwanakin da yayi bayan dukan Area boys dandai baya cikin hayyacinsa ne. Tuqi yake na ganganci cikin wani irin gudu na wuce sa'a sai kwaraf kwaraf yake a tsakiyar titi shida motarsa raunukan jikinsa yana kuma tsami.
Ikon Allah ya kawoshi kano cikin gidansa qarfe goman safe, xuwa lokacin ya gama jigata kwarai da gaske domin ko me gadin gidan be shedashi ba saidaya masa bayani da nuna masa ID card dinsa. Ya fito yana dingisa qafa ya nufi falon gidan.
Ya tarar da Surayya hakince a falo cikin shigar dayafi tsana ya ganta da ita wato English wears, kome ya hanata fita aiki oho. Ta miqe ciki da farin ciki ta nufeshi yayi saurin yin gefe yana cemata "Yi a hankali ciwo na" ta dubeshi saroro sai a lokacin ta lura da duk jikinsa bandages ne. Tace cikin sauri "Deen meya sameka haka?" a taqaice yace "accident nayi a hanyar tahota, kwanana hudu a KD a asibiti sai yau na farko shine na taho" ta kamashi ta taimaka masa ya xauna a kujera tana cewa "Ashsha! sannu Deen Haqqina ne yasaka yin accident wlh ka barni cikin masifar soyayya da kewarka"
Yayi shiru kamar be jita ba don bayason surutunta na hauka. Ta matso kujerar da yake ta xauna tana cewa "Ashe taji warning dina har ta karya asirin da taimana ta kadamun kai, dama sabariyya tanata bani shawarar inje inkatsa mata warning inaqi ashe maganarta akan gaskiya take" Cikin mamaki Deni ke kallonta yace "Waye kikaiwa warning wai?" cikin rashin damuwa tace "Hajjo mana" ya xaro ido yace "Wace Hajjon?" tayi dariya tace "Haba mana Deen Hajjo nawa muke da ita? Hajjo tamu ta gargajiya ita naiwa warning akan asirin da taimana ka tafi Lagos ka barni, saboda naji duk yadda tai asiri ta rabaka da Sakeena shiyasa naje na jamata kunne na fada mata ni baxan dauki hakan ba ta karya asirin ta sakomun kai mucigaba da soyayyar mu ko?" Al ajabi ya hana Deni ce mata komai.
Ta qara shigowa jikinsa tana cewa "Ai gara daka dawo Deen kacigaba da shan tabarka inasan qamshinta, wlh bayan tafiyarka wata jarraba Allah yayimun babu abunda nikeso kamar qamshin sigari, dana rasa yacce xanyi sai nake kiran maigadi yaxo nan ya xauna anan falon yayi ta busawa inajin qamshin. Saida abun ya isheni naje hospital wai akace ciki gareni, atake nasa aka burge shege akaimun wankin ciki aka daure mahaifar"
Cikin matuqar fushi da harxuqa Deni yace "Surayya cikin nawa kika xubar dan ubanki?" ta dubeshi tana dariyar data saba yimasa inyana masifa tace "calm down Deen banfa sha sigarin ba gate man nace maka yanasha inajin qamshin, nasan tabace bakaso insha ko? To bansha ba duk da inaso saboda kar inbata maka rai." a qufule yace "Ni ba tambayarki nake kinsha taba ko baki sha ba, wannan ba abunda ya shafeni bane inma kinga dama ki xama drug abuser, ina tambayarki da gaske kinsamu ciki kuma kin xubar?"
Ta gyada kai tace "Eh mana gaskene kasan ni aibana qarya" ya xaro mata ido yace "ke wai dan Allah wace irin yar iskar macece? Dan halak kuma danmu na fari kika xubar kuma kike fadamun babu kunya babu tsoron Allah?" ta dafe goshi 🤦🏽♀ tace "OH! Haba Deen wlh bansan shouting, calm down mana meye acikin common abortion? Bakasan yanxu ma andaina aure haka ba sai anje an daure mahaifa? Sai mutum yaga yanayin xama da mijin sannan ya fara haihuwa? Kawai ka share, I luv u Deen" tabi jikinsa ta kwanta.
Hawaye ya wanke masa fuska, wannan wane irin bala'i ne ke binsa bi da bi? Rana xafi inuwa quna, taciwa uwarsa mutunci bata saurari abunda xaice ba ta fada masa ta cire ciki harda sakawa a rufe mata mahaifa, wai ina xaisa kansa ne? (kadan ka gani baka tasarwa rusa auren wani ba? Da kuma neman aure cikin wani auren? 🤨) Wai waxai fadawa damuwarsane ya samu salama? Shin Surayya wace irin macece? Dawane suna xai kirata? Yar iska ko mahaukaciya? Ko haqqin sakeena ke bibiyarsa tunda adacan abu kadan intayi xai fara masifa amma gashi yanxu inyayi masifar ma dariya ake masa, gashi kuma abun ya kuma canjawa ko damar yin masifar ma Surayya bata bashi ba, wace irin matace gareshi da yadawo duk jikinsa rauni babu sannu ko hutawa beyiba ta sanar masa bad News?
Hajia 😊
*_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[8/21, 11:52 AM] Zongo Gal: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
2⃣9⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
EIDIL ADHHA MUBARAK TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUN.😊
Yacigaba da tunaninsa me kama da nadama, wato yanacan yana rusa rayuwar auren wani ashe shima tasa tuni ta rushe? Yanacan yana shirin raba sakeena da cikinta na halak ashe shima nasa cikin tuni yabi rariya, yakai dubansa kan Surayya dake kan cinyarsa tana danna waya, ya rasa wani irin hukunci xai mata ya huce abunda tai masa, yaja tsaki ya tashi ya shige bedroom. Dakansa ya hada ruwan wanka yayi, yasha tea yasha magungunan da aka bashi a asibiti ya kwanta.
Bai tashi sanin tinkiya yake aure ba saida dare yayi Surayya ta fara lalubeshi tana neman biyan buqata, ya fara masifa yaga abun baxai fishsheshi ba ya lallasheta da cewa tayi haquri ya warke yanxu duk jikinsa ciwo yake baxai iya komai ba.
Wajen goman safiya ya isa gidansu, yayi saar samun Baba yana gida. Sunyi mamakin ganinsa a haka, suma qarya yayi musu da cewa fashi akai masa a hanya. Suka jimanta masa harda Iya, ya samu ya shige dakin Hajjo ya sameta itama kamarsa tana dingisa qafa tayi wata irin xabgewa jikinta duk ya saki.
Suka xauna bayan gaisawa itama tayi masa jajen fashin da akai masa, ya qara kallonta a karo na barkatai yace "Hajjo meya sami qafarki naga kina janta haka? Ga wata muguwar rama da kikayi kamar me ciwon qanjamau" kamar jira take ta fashe da kuka, be hanata ba domin shima da akwai hali kukan zaiyi na rashin sakeena, sai datayi ya isheta sannan ta fara bashi labarin abunda ya wakana bayan tafiyarsa.
Hajjo dai bayan tafiyarsa ta hadu da ciwon sugar wato Diabetes, wanda rashin ankara da wuri yasa yaci qarfinta sosai kafin Saddiq ya kaita asibiti a gano kuma a dorata akan magani tare da gindayamata sharaidai masu dinbin yawa akan canja cima. Bayan nan kuma ta debi ruwan xafi a bokiti xatakai toilet tayi wanka ta xame ta fadi ta samu targade da tsagewar qashi a qafarta ta hagu, shine har yanxu be warke ba saboda jikin girma.
Abu na gaba kuma shine dumuwar halin da su Hadixa ke ciki wacce ta rasa matemaki, itadai Hadixa har yanxu tananan jiya iyau a qarqashin ikon surukarta da kuma axxalumin miji wanda duk yadda aka kai ga ganin mijinta abun yaci tura, ba a ganshi ba balle a kwatar mata yanci. Saida Saddiq da Baba suka tsananta bincike sai suka gano wai mijin nata yatafi wani course a qasar waje tare da amaryarsa, ita kuma uwar mijin ta hana Hadixa fita ko bakin gate a cewarta amana mijin Hadixan ya kawota babu inda xataje har sai ya dawo.
A bangaren Fiddausi kuwa Zahara da kanta taxo tasawa Baba kuka akan yasa baki a lamarinta domin bauta da tsoron takewa kishiyarta Hajiya ya wuce makadi da rawa. Dole Baba ya shiga lamarinsu tunda duk lalacewarsu yayansa ne kuma abunda ya gudar musu kenan a auren mekudi amma sukaqi sauraransa. Dashi da Saddiq da kuma Zahara sukaje gidan Fiddausi suka tarar da ita kace kace cikin bauta kamar yadda aka labarta musu, babu kunya babu tsoron Allah Hajiya a gabansu ta kira Fiddausi tace ta kawo musu ruwa taje ta kawo jiki na bari, basu gama mamaki ba saida sukaga Fiddausi ta koma gefe ta rabe kamar bata sansu ba, Hajiya tayi murmushi tace da ita ki gaishesu mana ko baki shedasu ba, Fiddausi ta juyo tana gaishesu hadi da waigen Hajiya. Suka jinjina wannan qatoton lamari, wato yau ga wacce ta dama Hajjo ta shanye a bin bokaye. Baba ya shanye duk wani bacin ransa yace dama sunaso suje gida da Fiddausi ne gyatumarta babu lfy xataje taga jikin nata. Tun kafin Hajiya tai magana Fiddausi tace "Nikam babu inda xani Baba, Allah ya bawa Hajjo lfy, aiba sai lallai naje ba saboda aiki yamun yawa" ido waje suke kallon Fiddausi da kuma kaduwa dajin kalamanta. Zahara tai qarfin halin cewa "Kidai daure muje ki ganta, munyi alqawari xamu dawo dake da kanmu" Saddiq kuwa cikin harxuqa yace "Dan ubanki saiki bimu ko kinqi ko kinso ace uwar taki babu lfy kice aiki ya miki yawa?"
Hajiya ta muskata fuskarta cike da murmushi ta dagawa Saddiq hannu gami da cewa "Dakata dan samari, ba amun hayaniya a gida, ko baku da labarin nan gidan mallakinane? Saboda haka ku tashi ku bacemun daganan tunda kunji da bakinku tace baxataje dubiyar ba, ni kuma bansan takurawa bil adam dan haka baxan tilasa mata xuwa ba" suka tashi suka nufo gate Hajiya ta umarci Fiddausi da tayi musu rakiya, babu musu ta biyosu, Saddiq yayi amfani da wannan dama ya sunkuceta ya saba a kafada megadi ya dunga kwallawa Hajiya kira da cewar baqin da akai xasu gudu da Fiddausi, hankali kwance ta fito tana takun qasaita da kuma dariyar yadda dakai tacewa megadin ya bude musu gate su tafi, ta dunga daga Fiddausi hannu tana cewa saikin dawo Fiddausi agaida Hajjo da jiki.
Har dakin Hajjo Baba ya shiga yayi mata bayanin yadda sukaga Fiddausi cikin gidan tare da fada mata mugun asiri Hajiya tayi ta cafke xuciyar Fiddausin. Hajjo ta dunga kallonta tana kuka tare da bawa Baba haquri. Ya daga mata hannu da cewa "Nikam Hajara ai bakimun komi ba kanki kikayiwa, ga sakamakon abunda kika shukanan tun kan aje ko ina ya fara bibiyar yayanki da suka tayaki haqa ramin muguntar, abun takaicin kuma shine kun haqashi da xurfi shiyasa kuka rufta gaba daya kuka kuma kasa fita" sunyini suna gadin Fiddausi kamar yadda ta yini tana fushi akan sun dakkota daga gidan mijinta.
Baba ya fita yanata yawo gurin malaman Allah da annabi yana nemarwa Fiddausi temakon karya sihiri. Koda dare yayi an rufe gida kowa yasa haqarqarinsa don ya huta Fiddausi ta sulale ta bude gida ta gudu ta koma gidan mijinta qarqashin mulkin hajjaju makkatu. Saida asuba suka tarar da gida bude Fiddausi kuma ta fece. Da wannan Baba ya rufe kofar temakon Fiddausi qarqari dai yana sata a addua. Hajjo kuwa ta yini sur tana kuka.
Ana cikin haka kuma Surayya ta bullo da tata kalar tijarar, sukai takakkiya ita da wata qawarta Sabariyya suka qarewa Hajjo cin mutunci da sunan warning, Sabariyya harda dungurewa Hajjo kai tare da cemata "Ke ba a haihuwa aka haifa miki naki mijin? Akan me duk wacce ta auri danki sai kinyi tsafi kin rabasu? To mu ba Sakeena bane wlh Surry ta fiki iskanci kurace tai lfy, amma in baki karya asirin da kikai musu ba wlh saimun maidaki abar kwatance" Hajjo ta qare bawa Deni lbr da cewa "Kuma Hafsatu tana kallo bata hanasu cimun mutunci ba"
Deni ya gyara xama yace "To Allah ya sawaqe ke kuma Allah ya baki lfy" yakai dubansa ga Amina wacce ke xaune tana danna waya yace "Ita wannan mahaukaciyar har yanxu batai aure bane?" Hajjo ta dubeshi da mamaki tace "Waye xai aurarmun da ita Inba kaiba? Dama jiran dawowarka nake, wannan jarrabawar daka siya mata dai bataci ba kuma xamanta haka ya isheni ko kare bai taba xuwa gurinta xance ba, shine nace ko cikin abokanka xaka lalubo mata wani ya temaka ya rabani da ita" Deni ya waro ido yana kallon Hajjo harta idar da magana sannan yace "Ai kuwa sai dai kiyi haquri domin ni nayi iya abunda xan iyayi na temakonta tunda kwakwalwar kifi gareta saita xauna xaman jiran miji, ni bani da wanda xan mannawa wannan abar. Narasa abunda yasa dukkanmu muke fuskartar matsalar abokan xama, nima inji da bala'in da nike ciki" cikin sauri Hajjo tace "Wane bala'i kake ciki Deni?" yayi saurin waskewa da cewa "Eh mana matsalar waccan yar iskar Surayya" tace "Oh aini xan tabbatar da bakai dacen aure ba, wannan yarinya kam bata samu tarbiyyar arxiqi ba. Ai naji dadin dawowarka duk tsiya na daina kwana da yunwa" ya maimaita "Yunwa kuma Hajjo? Kina nufin Baba baya baki abinci?" tayi rau rau xatai kuka tace "Yana bani amma kasan yanayin ciwona yanxu bakomi nike ciba saboda gudun tashin ciwon, haka nake yini da yunwa sai Saddiq ya dawo daga kasuwa ya dan samo yan kudi sannan ya siyomun ganyen salak ko alayyahu incika a abincin inci, kuma kasan abunda yake samu be taka kara ya karya ba, sai kuma Zahara inta samu ta bullo" ya girgixa kai da cewa "To xan duba inga abunda xanyi akai"
Ya fito daga dakin Hajjo yanajan qafa sukai karo da Iya, yayi saurin qasa dakai cikin fargabar kar dai Sageer ya fadawa Iya abunda yayi. Ya koma xuwa gidansa cikin dinbin nadamar xuwansa gidansu gurin Hajjo domin ta qara masa tulin damuwa akan wacce yake ciki, da wannan ya miqe qafa a gida yacigaba da jinyar jiki data xuciya ba tare daya je office yayi rahoton dawowarsa ba, wanda wannan shine babban kuskuren da Deni ya tafka.
***** ******* ******* ******** ******
Kamar yadda yayi mata alqawari yaxo daukarta tunkan ta fito lec, tana fitowa ta sameshi cikin nishadi ta bude motar ta shiga suka daga, yana driving riqe da hannunta yace "Nasan baki sallah ba ranki ya dade ga lokacinta yana wucewa" ta matso kusa dashi ta kwantar da kanta a dantsen hannunsa tace "Yawwa ya Sageer kamar ka shiga xuciyata kaga abunda nake tunani kenan, yacce xa ai yanxu kawai ka kaini gida inyi sallah kai kuma ka koma gurin aikinka inka dawo xuwa dare sai mu dau wanka mu fita shaqatawa gami da shopping din kasan wannan yanayin yafi tada soyayya ko?" ya kwashe da dariya yana dubanta yace "Kai wannan yarinya da duniyanci kike wato har kinsan wani yanayi me tada tsumin soyayya ko? To shawararki tayi, sai muje xuwa daren karkiyi dinner akwai wani gurin cin abinci da nadade inaso muje dake kinga saimu biya muyi dinner acan" Tace "Yawwa ya Sageer nagode dan Allah in mun fitan ma leqa Anty Hassana inga jikin nata" yace "To ranki ya dade yacce kikeso haka xa ayi" ta sumbaci kuncinsa tana cewa nagode my luv.
Yana ajiyeta cikin gida ya juya office, ta shiga tai sallah taci abinci ta fadawa Inna su girka abunda sukeso da daddare ita da Sageer ba a gida xasuci dinner ba, Inna tace to.
Ta koma daki ta kwanta tana tunanin rayuwarta ta baya tun daga tahowar da Iya tayi da ita daga Baggadano har xuwa yanxu. Al amura da yawa sun faru da ita wasu masu dadi wasu kuma akasin haka, xata iya cewa qaddarace ta rabota da garinsu na haihuwa kamar yadda wata qaddarar ta qara rabata da Kaduna xuwa Lagos har ta hadu da Sageer tayi aure akan aure, amma dai koma meye ta godewa Allah finally gata a gidan aure a qarqashin mijin da takeso kuma yake masifar sonta. Ta qara furta "ALHAMDULILLAH" wai yau ita Sakeena Abbakar Liman itace take xaune a wannan matsayi wanda sai taga dama xata kawar da koda spoon ne, in taso komai sai anyi mata. Lallai dole ta qara jininawa mijinta Muhammad Sageer wajen haqurin da yayi da juriyar xama da ita har ta gane gaskiya, da kuma me gayya me aiki wato Iya wacce ta tankwarata qarfi da yaji ta nuna mata auren sageer shine alkhairi a rayuwarta kuma inbata bishi ba tofa ta rabu da ita. Tana wannan tunanin bacci ya kwasheta.
Bayan sallar isha suka dau wanka, shi ya saka qananan kaya itama qananan kayan ta saka riga da skirt peach clr tayi nadi da wani siririn veil milk tasha light makeup ya riqe hannunta suka fita. Gidan Hassana suka fara xuwa, sai dai sun tarar batanan ta wuce Kano goyan ciki. Sakeena ta buga mata waya suka gaisa tace gata taxo kuma ta tadda batanan, tace ai kwananta wajen 9 a kano gurin Mama, suka rabu bayan ta qarayiwa sakeena fada akan Sageer tace "Hmm Anty Hassana ai yanxu kam inason abina kamar in maidashi ciki sai munxo kano xakiga luv" Hassana tana dariya tace "Allah yar duniya?" sakeena ta katse wayar tana dariya, Sageer ma dariyar yake musu.
Daganan gurin cin abincin suka wuce, aka miqo musu menu shiya xaba musu abunda xa a kawo, sakeena tayi mugun mamakin tsadar abincin data gani, amma koda ta faracin abincin sai taji babu magana yaci kudinsa, suka take cikinsu ya biya kudin kana sukai shopping mall, nanma dai abubuwa yayi ta diban mata tana kallonsa da mamaki, kafin suje gurin jewellery taga wata sarqa me abun hannu da wani agogo ta dauka sun mata kyau sosai, tai saurin ajiyewa ganin kudin da aka rubuta ajiki afili tace "Yan iska komi nasu masifar tsada saikace kayan shiga aljannah" Sageer yayi dariya ya tsinkuli gefen cikinta yace "Ke nanfa gurin manya ne duk abunda ka riga kasa aka fito maka dashi saika siya, dan haka aiki ya kamaki yau jarin kunun aya xai balle" yace da matar "Dakko mata madam" tana dariya ta qara fito da sarqar sakeena tayi wuqi wuqi saida ya gama xolayarta sannan ya basu ATM dinsa suka cire kudin sarqar suka rubuta mata receipt suka basu.
Aka rakosu har mota da kaya niqi niqi, itadai aikin kallon Sageer take kamar taga sabuwar halitta, tana mamakin yadda bayajin fidda kudi duk yawansu ta gama yadda da soyayyar da Sageer ke mata. Sukaje gida wanka kawai sukai sukai shirin bacci ya rigata kimtsawa ita tana bakin mirror tana shafe shafe ya ware kayan daya siyo mata ya hade suturun a leda daya ya ajiye guri daya yana cewa wannan "Gurin Bilki xa a kai ko? Inason a dinka pink din lace dinnan da wuri kisa ingani" ta gama abunda take ta nufoshi cikin tafiyar nutsuwa, ya qurawa kyakykyawar farar matarsa ido cikin gajeren wando da shimi farare qal iri daya na bacci, shidai dama tun asali yanason kyakykyawar mace Allah ya dubi xuciyarsa ya bashi fara kyakykyawa kuma yar gayu, yayi tasbihi ga ubangijin daya halicci Sakeenatu.
Yana wannan tunanin harta xauna kusa dashi be sani ba, ta riqo hannunsa ta dora kan mararta ya juyo yana kallonta babu ko qiftawa, ya riqota ya maidata kan cinyarsa ya shimfida hannunsa akan mararta ita kuma tasa hannayenta ta xarge wuyansa sukacigaba da kallon juna, ta hade fuskarsu guri daya hancinsa akan nata bakinsu ma guri daya a hankali tace "Ya Sageer nagode sosai, Allah ya qara budi, Allah ya rabaka da sharrin maqiya" be amsa mataba sai fara lasar lips dinta dayayi, dakyar ya fusgo kalmar "ina sonki Sakeena, babu abunda baxan iya baki ba indai mallakinane dan haka ki daina yimun godiya dan namiki abu, kedai kiyimun adduar samun budi da kuma rai da lfy xakisha kallo" da kanta ta kwantar dashi akan gadon tabi jikinsa ta kwanta tare da canja salon wasan.
Xamansu me dadi ya dora fiye da xaman wancan auren da sukai, tana cigaba da xuwa makarantarta kuma wannan Karon Sageer ke mata darasi kullum da daddare sunayi gami da wasanninsu na soyayya wanda acewarsa wai karatun yafi shiga in ana haka. Kusan kullum sunayin waya da Iya da kuma Baba wanda xuwa yanxu Iya hankalinta ya gama kwanciya domin ko acikin waya kana iya sheda daga Sakeena har Sageer cikin nishadi da soyayyar juna suke, bata manta umma ba tunda ta nuna tana qaunarta kuma ta haifa mata abunda takejin yanxu duk duniya babu abunda takeso kamarsa. Umma da shafa qanwar Sageer ma suna yawan waya dasu kuma duk sanda ta samu dan aike me xuwa KT tana musu aiken kayan da tasan suna wuyar samu a Arewa daga kan sutura har kayan masarufi kamar yadda Iya ta kwarkwanta mata ta dunga musu kyauta don tana qara danqon soyayya. Ita kanta Sakeena tana qaunar Umma kamar itace ta kawota duniya domin Umma ta nuna mata ba dukane iyayen miji irin su Hajjo ba kuma duk lalacewar xamani anasamun mutum nagari. A duk sanda aiken ya isar musu Umma da Shafa kan bugowa Sageer waya su fada masa da nufin ya tayasu godiya gurin Sakeena, wanda ta lura hakan yana qara mata qima gurinsa don yana qaunar Umma da shafa, yayita kallon sakeena yana zabga mata addua da jinjina girman abunda tayi kamar ba a jikinsa take samun yawancin kudin da take musu hidimar ba.
Iya kuwa yar gatan tsohuwa a gurin Sakeena da Sageer duk qarshen wata Sageer kanyimata aiken kayan abinci kamar yadda yakewa ummansa, hakama Sakeena a duk qarshen watan tanawa Iya aiken kudi da kayan buqatu. Daga Sakeena har Sageer tausayinta sukeji saboda da Allah be bata haihuwa ba, shiyasa suke tsaye tsayin daka akanta basu bar mata wani gurbiba wanda xataga rashin haihuwa ne ya hana acike mata shiba. Alhamdulillahi kayan abincin da Sageer mijin sakeena ke kaiwa gidan dasu ake amfani domin Deni tun daga kan bushun shinkafar daya kai musu ranar da yaje sato lambar sakeena be kuma kai komai ba, to inama aka ganshi balle ya temaka? Duk sanda aiken Sageer yaxo Iya kan nunawa Baba kuma bata kyashi don ya raba biyu dai dai ya bawa Hajjo rabi. Sau tari xakaji yana amabaton Sageer da Sakeena tare da shi musu albarka kuma dagashi har Iya #SAGNA# suna cikin adduoinsu a koda yaushe. Duk wani abu da sakeena ta gani na kwalliyar dattijan mata saita sayawa Iya ta ajiye daga kan sutura har kan kayan kyale kyalen mata, intasiya mata suturar takankai gurin Anty Bilki ta kwatanta mata yanayin dinkunan da Iya kesawa ta tsantsara mata dinki ta ajiye mata, da haka saida ta tarawa Iya kaya cikin akwati guda tana tsananin daukin ranar da xata gama aji daya a jamia (level 100) suje Kano kamar yadda Sageer ya mata alqawari. Ta gama burin maida Iya yar gayun tsohuwa shiyasa bata taba aikamata tufar sakawa ba, so take taje mata baxata kuma ta nunawa maqiyansu ita da Iya tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali bataso a raina mata Iya tanason taga fes cikin suturar alfarma kuma kowa ya ganta ya sheda itace mahaifiyar Madam Sakeena matar Oga Sageer.
A wannan lokacinne Inna tai shirin xuwa gida can KT saboda babbar yarta xata aikin Hajji xataje ta xauna da yayanta wato jikokin Inna kenan, shikansa Sageer beji dadin tafiyar Inna ba balle Sakeena yanxu da bata iya girkin komi saboda batason warin dahuwar abinci. Inna ma duk saitaji babu dadi ganin yadda sakeena ke kuka don xata tafi, ta lallasheta da cewar tayi haquri badan tafiyar ta xama dole ba itama baxata tafi ta barsu ba amma mahajjata na dawowa xata dawo. Sakeena taiwa Inna sha tara ta arxiqi abunda bata taba xata ba, sannan tayiwa Umma da Shafa aike kamar yadda ta saba, ta dunga hawaye tanawa Sakeena godiya da adduar gamawa lfy. Har da ita akaiwa Inna rakiya xuwa tasha tahau mota.
Ranar daga ita har Sageer jugum jugum suka yini har xuwa lokacin dora abinci yayi ta miqe ta nufi kicin ta toshe hancinta ta dora markadadden kayan miya a wuta sannan ta dora tafashen nama. Yana fara tafasowa qamshin ta fashe ya hargitsa mata kwakwalwa ta xube akan tiles din kicin din tana sheqa amai. Kakarin aman Sageer yaji ya fito da gudu, ya tarar da ita a haka, da sauri ya kashe duk gas din ya tattageta sukai bedroom yaje ya wanke mata jikinta ya kwantar da ita kan gado. Yana kallonta yace "Waya saki girki? Dubi yadda duk amai ya jigata ki" cikin sanyin murya tace "Gani nai lokacin dora abinci yayi kuma nasan xaka buqata" yace "To bansaki ba, karki kuma shiga kicin da sunan xakiyi girki ki kyaleni tunda ninayi cikin dole xan nemo mana mafita kinji ko?" ta gyada kai daga haka bacci ya kwasheta shi kuma ya fita ya gyara inda tayi aman.
Da yamma suna xaune kasancewar Sunday ce, yaga tunanin Inna da kewarta suna neman sawa Sakeena damuwa ya dubeta yace "Ko muje bakin beach ne?" tai saurin miqewa tace "Eh wlh ya Sageer muje" yayi dariya yace "To kwaduwa ta" ta doro after dress kan qananan kayan jikinta suka fita.
Suka tsaya restaurant don yaci abinci saboda da rana snacks yaci kuma beji ya qoshi ba, yayi order sakwara da miyan ganye ita kuma Sakeena wani shirgegen gasashshen kifi aka kawo mata. Kowa yanacin nasa yayin shi kuma yanaci yana tunanin mafita. Don daganinta itama Sakeena da yunwa ta yini amma bata nuna masa ba, sai yanxu data sami abunda dakeso yaga ta xage tanaci da alama daga ita har abunda ke cikinta a yunwace suke. Ya tausaya mata domin shine dalilin sakata a wannan hali.
Ya fara tunanin samo maiyi musu girki sai dai matsalar daya itace yana kishin sakeena baxai iya kawo namiji ba da sunan kuku suna go slow da iyalinsa a wannan qaramin gidan yana kalle masa mata. Sannan wadannan yaran guda biyu mata da suke aiki a gidan bai yadda da tsaftarsu ba duk da cewa musulmai ne amma shikam baxai iyacin abincinsu ba. Ya danyi tunani, yaga kawai gara su dinga aikinsu kamar yadda suka saba wato daya gyaran gida daya kuma aikin kunun aya inyaso ya qara musu kudin abinci acikin albashin da yake basu harda me gadi da me wankinsu kowa ya dunga nemo abincin da xaici suyi manage xuwa dawowar Inna, domin inyace su dunga girki da kansu a cikin kicin yayin da shi da Sakeena basa nan akwai matsala tunda ba qabilarsu daya ba. Shi kuma shida Sakeena xai dunga siyo musu duk abunda sukeso suci a restaurant xuwa lokacin dawowar Inna ko kuma jin sauqin Sakeena. Wannan tunanin ya yadda dashi.
Suka gama cin abincin suka nufi bakin teku, ta balle after dress din amota suka shiga bakin ruwa, sunata guje guje cikin nishadi ita da Sageer, sukai photos saida yamma tayi sosai sannan ya dakkota cancakacas sukai mota.
Saida suka kwanta sannan yake fada mata shawarar daya yanke akan girkin gidan, tayi naam da hakan ta kuma qara masa bayanin cewa xata dunga xama har yamma a makaranta tana karatu saboda sun fara tests xuwa lokacin tashinsa aiki sai yaxo su tafi gida tare. Yaji dadin hakan kuma ya qara yawan kudin da yake bata na makaranta yace ta dungacin duk abunda takeso. Washegari Monday saida ya jira xuwan masu aikin gidan yayi musu bayani sannan suka fita bayan ta qulle dakunanta.
Kammar yadda suka tsara sai yamma liqis yaje dakkota daga makaranta xuwa lokacin tayi karatu sosai kuma ta qaru da abubuwan da bata ganeba domin dasu Qudurat suka hadu akai karatu sosai. Daganan restaurant ya wuce yayi musu order abinci harda snacks saboda shan tea da kuma chocolate ice cream din da take mayatar sha kullum. Washegari ma haka sukai, sai da suka kwana hudu suna haka ranar cikon na biyar din wato Friday Maitama ya gane halin da suke ciki, ya tambayi Sageer shi kuma ya fada masa dalilinsu na siyan abinci saboda cikin Sakeena baison warin dahuwar abinci. Ya rufe Sageer da fadan danme baxai fada masa ba ko ya dunga xuwa gidansa suci meye amfanin xaman guri daya? Kuma shi ai inshine dole xai fada masa donya tai maka masa, yayi fadansa ya gama Sageer ya bashi haquri daga wannan aka rufe kofar siyan abinci a gidan kullum Bilki xata aiko musu da abincin rana da dare suci har su bayar kuma sai yanxu hankalin Sageer ya kwanta domin siyan abinci sai dole duk tsiya abincin gida yafi na titi.
Acan Katsina kuwa Inna tajewa da Umma kyakykyawan lbrin kyawawan halin Sakeena da kuma xaman lfy da soyayya da suke shimfidawa ita da Sageer daya albishir din shine cikin da Sakeena ke dauke dashi duk da basu fada mata ba amma dake babba ce ta fuskanta. Ta kuma kawo kayan alkhairin da sakeena ta bata ta nunawa umma kuma ta bawa umman nata da sakeena ta bayar akawo. A ranar dai Umma har hawayen farin ciki tai na xataga dan Sageer kuma ta jinjinawa Iya kwarai domin jajurcewarta gurin saita Sakeena. Ta dauki waya ta kira Sageer suka dade suna hira dashi da kuma Sakeena ta dunga yiwa Sakeena godiya da kuma saka albarka ta dunga jaddadawa Sageer ya qara kula da ita amana aka bashi kuma bata da kowa a Lagos saishi. Ya dunga amsawa da to Umma xan kula mungode sosai.
Ranar asabar ta tashi taji babu abunda take qaunar yin breakfast dashi sai wainar fulawa da ginger drink, ta salallaba Sageer na bacci ta nufi kicin ta dibi fulawa ta kwaba ta jajjaga albasa da attaruhu ta watsa akai ta tsiyayo manja. Ta kira me aikinta ta kwada mata yacce xata soya mata don ita baxata iya soyawa ba intaji qaurin suyar baxataci ba. Sageer dake tsaye yana dubanta ya qaraso yana cewa "Kawo in soya miki duk da baki gayyaceni ba" ta bude baki tace "Lah! yaya yaushe ka Tasha?" ya bata amsa da cewa "Tun sanda kikai sanda kika fito" ya karbi kaskon ya kori me aikin, Sakeena ta qara cewa "To kuma ka iya soyawar?" yace "Dole in koya ko ban iya ba, tunda nayi cikin" tayi dariya ta debi ginger da lemon tsami tayi can wajen kunun aya don hada ginger.
Tana xaune tana aikin ginger din ita kuma yarinyar tana hada tamarind tana kuma lura da yanayin tsaftar yadda yarinyar ke hada lemon. Ta gama ta jefa masa qanqara ta cika musu qaton jug ita da Sageer ta warewa masu aiki nasu taga yayi ragowa ta samu jarkoki ta duddura tace da ita in anxo siyan kunun aya tace akwai ginger drink. Yarinyar tana dariya tace "Madam ka iya business kuma lemon yayi dadi Allah ya kawo kasuwa" Sakeena ta amsa da "Amin" ta shige falo. Ta kwallahwa Sageer kira tace masa ta gama lemon ya kawo wainar, shima ya bata amsa da to madam na kusa gamawa, ta samo cup kan fridge ta cika da lemon ta kashingida tana kurba. Babu jimawa ya shigo da plate shaqe da waina da kuma robar yaji, suka xauna har dashi suka tashi da wainar fulawa ta gwamgwani shida, suka dunka daddakar ginger din, Sageer harya fita sha anan suka xube suna hira cikin nishadi har Bilki ta aiko da abincin rana.
Ranar lahadi da wuri ta tashi da aikin ginger wanda jiya aka dunga nema har dare, ko Sageer besan ta tashi ba yana kwance. Xuwa taran safe ta hada ginger bokitin roba biyu ta duddura ajarkoki ta kuma qullah a leda, sai lokacin mai aikin taxo ta taya sakeena suka wanke freezer suka xubashi sannan suka juya aikin kunun aya ta sakar masa kayan qamshi shima suka gama. Sageer ya tashi be ganta ba yaje kicin ya dora ruwan tea da kuma indomie wacce ya saka mata jajjagaggen taruhu da albasa kamar yadda sakeena ta fada masa tanaso inxa a dafa mata indomie. Ya nufi wajen gidan gurin aikin nasu, ya samesu kace kace suna aikin tsamiya yana kallonsu yace "Hajiya Sakeena me komai akwai naga company naki ya kuma habbaka" tai fari tace "Kaidai bari ya Sageer ai shiyasa yau ban kwanta baccin asara ba, mun fara ginger asa mana albarka" ta bude masa fridge ta nuna masa ya bude baki cike da mamaki yana dubanta yace "Yace wannan yarinya dason kudi kike wani abun kika kuma qirqira?" tace "To ya xa'ai ya Sageer? Lamarin Sana'a ne sai a slow kafuwarta da wahala kuma dole saika baxa koma ka gwargwada kowacce, wacce kaga tafi karbuwa saika tsaya akanta." ya jinjina yace "Wannan gaskiya ne ranki ya dade, Allah ya kawo kasuwa me albarka, yanxu dai taso muje nagama breakfast muci sai ki bar mata ta qarasa aikin" tace to ta tsame hannunta ta bawa yarinyar umarnin ta wanke gurin inta gama. Suka nufi cikin gida ya juyo musu Indo mie din a tray da dafaffen kwai ya xubo musu tea.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, ginger drink dinta ya samu karbuwa a gurin mutane sosai saboda sinadarin yajin dake ciki har kwangila ake bata na biki kona taro, Sageer ma yaje dashi office dinsu aka dunga yaba dadinsa dan haka yasa take kula guda kullum ana kaiwa wani shop a cikin ma'aikatar ana bawa me shagon lada yana siyar mata.
Semester taxo qarshe yawanci anyi covering lectures bata cika xuwa school ba ankusa exam a gida take xama tayi karatun, saita raba dare tana karatu, Sageer ya bata cikakkiyar damar yin hakan.
Wata ranar laraba ana saura sati guda su fara exam tana xaune da yamma Sageer ya shigo gidan daga aiki yake, yana shigowa ya dagata sama yana juyi da ita cikin nishadi yana dariya. Ta riqeshi kam tana cewa "Ya sageer karka yadda ni fa" ya dureta akan kujera gaba dayansu suna haki suna dariya.
Yace "Sakeena ki tayani murna wata harkace ta budemun xan samu alkhairi sosai inna hada da abunda ke account dina xan iya canja miki muhalli kamar yadda kika dade kina buri" jiki a sanyaye ta kalleshi tace "Dan Allah ya Sageer ka daina tunamin abunda ya riga ya shude a baya saboda kunya nakeji, ka daina maganar canja muhalli nan din ya isheni banfi qarfin nan dinba, sharrin shedan ne yasani cewa ka canjamun gurin xama a wancan Karon amma kayi haquri ka yafemun" ya share mata kwallar data cika mata ido yace "To yi haquri nasaki kuka, yanxu dai bari kiji yadda akai kudin suka shigo" ta gyara xamanta akan cinyarsa tace "Ina saurarenka" yace "Kamar yadda kika sani ina noma da kiwo acan gida Katsina akwai wadanda ke kulamun da harkar, to bana dai amfanin gona yayi kyau kuma mun siyar da daraja sosai. Sannan ragunan da nake kiwo anmun hanya xuwa gurin gwamna na siyar masa dasu xai rabawa jamian gwamnati kuma ya siya da daraja fiye da yadda na xata saboda sun kiwatu sosai. Kinsan cinikin manya ne inasaka musu kudi a nufina su taya sai kawai suka amsa akan haka. To kinji yacce akai yanxu shanun nake jira a siye sai in hade kudin inyi amfanin da nakeso yi dasu" ta washe masa jerarrun haqoranta tace "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi" ya amsa da amin sannan yace "Baki fadi abunda kikeso in miki acikin kudin ba" tai saurin cewa "Babu komai ai nima ina da nawa kudin kuma ina samu sosai saboda haka ka riqe abunka" ya marairaice yace "Baxa'ai haka ba sakeenatu dole ki fadi abunda kike muradi in miki, manyan kudade fa nasamu sosai" ta danyi tunani tace "To dama ina sha'awar bude salon, kuma nima inada kudade na da nike tarawa amma nasan baxasu isa ba, xan cirosu daga bank sai inbaka ka cika a budemun salon din." yaja hancinta yana kwaikwayon maganarta yace "To ranki ya dade yadda kikace haka xa'ai, amma ki bar ciro kudin tukun mugani kafin asamu shagon" da haka suka bar maganar tacigaba da karatunta.
Sun fara jarrabawa ta dage sosai da karatu da kuma adduar neman saa domin cikawa Sageer da alqawari da tayi masa. Babu wani interval sosai cikin sauri sukayi suka gama aka fara hutu ta dawo xaman gida ta fara ramuwar baccin da taci bashinsa yayin karatun jarrabawa, tana kuma jiran xuwan ranar Saturday su daga Kano kamar yadda Sageer ya mata alqawari.
Ranar talata ya tattageta da daddare suka tafi asibitin Dr sani wanda ya dawo daga sudan yin wani course, yana ganinsu ya washe baki yana cewa "Kaga Sageer da Sakeena masoyan asali, yau kune a asibiti? Da alamu ta samu kenan?" Sageer ya gyarawa Sakeena kujera ta xauna shima ya xauna yana cewa "Likita bokan turai, bakuso a mutu bakuso a xauna lfy" Dr sani yana dariya yace "wannan kuma sharrinka ne, wayaqi xaman lfy?" ya bashi hannu suka gaisa suka dan taba hirar bayan saduwa. Ya dubi Sakeena yace "Hajiya Sakeena kina lfy?" ta amsa tare da gaisheshi. Sageer yayi masa bayanin abunda ke tafe dasu na duba lfyar abunda ke cikin Sakeena ne da kuma fada musu lokacin xuwa fara awo.
Ya daga waya ya kira wata nurse yace suje da Sakeena ai mata scanning. Suka fita tare shi kuma sukacigaba da hira da Sageer, kimanin awa guda suka dawo tare da takaddar sakamakon scanning din ta bawa Dr. Ya karba ya duba ya fada musu adadin cikin Sakeena wata biyu ne da sati biyu kuma xata fara awo in cikin yayi 4 month, ya tabbatar musu da lafiyar abunda ke cikin ya bata magungunan qarin jini suka taho.
Wani abu da Sageer yayi wanda yasa Sakeena xubar da hawaye shine: ranar laraba ya dawo da wuri daga office yace ta shirya da sauri xata rakashi wani guri, da sauri ta canja qananan kayan jikinta da atamfa dama fes take ta yafa mayafi suka fita. Suna tafiya suna hira har xuwa rukunin wasu manyan shaguna yayi parking a gaban daya daga cikinsu suka fito tare, abun mamaki ta tarar da Bilki da kuma Maitama a gurin da wasu mutane kuma a tsatstsaye, tana fitowa aka miqa mata almakashi Sageer ya rada mata cewar ta yanka dan kyallen dake gabanta salon dinta ne ya kammala sukaxo budeshi, kamar a mafarki ta yanke kyallen aka dauki tafi, ta fara shiga ciki salon din wanda akaiwa suna asaman gurin da SAGNA BEAUTY SALON.Ta kalli kayan gyaran gashin da aka maqare gurin dashi ko ina tsaf yana kalli. Ta jinjinawa dukiyar da aka lafta a gurin babu tambaya daganin kura xataci akuya ma'ana ba qananan kudade Sageer ya kashe ba.
Suka gama xaga gurin tsaf harda barin kwalliya wanda itace xata dungayi sai qunshi dasu nadin gwagwagwaro da yaran da xasu dunga xama a shagon suna gyaran gashi gaba daya Sakeena tace Bilki ta samo masu yi wanda ta amincewa tunda ita ta girma a Lagos tafisu sanin mutane. Koda aka buqaci Sakeena tai jawabin godiya saita kasa magana sai hawaye data rinqayi muryarta na rawa tayi taqaitaccen bayani ta rungume Sageer. Aka dau tafi, Bilki tana murmushi ta matso tace "Share hawayenki qanwata, da alama kinxo Lagos da qafar dama kuma dama ba'a xaman kashe wando a Lagos, kedai kiyi addua kuma kicigaba da juriyar neman halak" cikin rawar murya tace "Nagode Anty Bilki"
An watse lfy kowa ya nufi gida Sakeena har xuwa yanxu mamakin Sageer take da kuma girman son dayake mata, daga fada masa sha'awarta nason bude salon yayi mata wayo yace ta dakaceshi ashe Allah sarki kudinsa ya narka ya saimata komi tare da kama hayar shago ba tare da ko sisinta ba. Har sukaje gida tana tunani, da daddare bayan ya dawo sallar isha ta tsuguna domin gode masa ya dakatar da ita da cewa. Ai yiwa kaine, kuma damashi yanaso yaga mutum meson neman nakansa tafi qarfin komi a gurinsa xaman lfy data bada hadin kai akeyi yafi komi, a wannan dare ma soyayyarsu suka sha me tsafta, sageer ya rasa abunda yasa baya gundura da Sakeena kullum sabuwa take a jikinsa da kuma xuciyarsa.
Tacigaba da shirin tafiya Kano ranar asabar kamar yadda yace, sai dai ya daga tafiyar saboda be samu hutun da yake nema ba a gurin aiki sannan kuma ga wata tsirfa inji Sakeena wai xa'ayi birthday din ogansu a gurin aiki (Abdulfatah) ranar juma a da daddare wanda Sageer keson ya halarta.
Bata nuna masa bacin ran daga tafiyar da yayi ba duk da tana daukin xuwa Kano da kuma ganin Iya, yayi mata alqawarin washegarin birthday din wato asabar xasu tafi. Tacigaba da shirin tafiya taiwa kowa tsaraba dai dai da matsayinsa har yan Baggadano bata mantasu ba. Acikin kwanakin ta samu sauqin laulayin da take harta fara girki da kanta, Sageer yaji dadin hakan don yanaso su hutar da Bilki kawo abincin da take, suka kuma dinkewa shida sakeena wacce ke masa biyayya kamar tai masa sujjada, duk da bashi da isashshen lokacin kansa ya maida hankalinsa gurin kammala aikin gabansa don yasamu hutun da xai isheshi suje kano dagacan su wuce Katsina taga danginsa da mahaifarsa.
Ranar Friday da daddare suka tsala wanka, tadau doguwar riga baqa me fararen stones, rigar tayi kyau kwarai kuma da ganinta kasan da manyan kudade aka siyeta, tayi nadinta da dankwalin rigar, tayi kyau sosai saboda ta qara cikowa tayi haske albarkacin cikin jikinta, cikin nishadi take komai saboda murnar gobe war haka tana Kano gurin Iya. Sageer shi kuma yasaka suit baqaqe, suka fita suka shiga mota ya danna order su Bilki suka fito suma a tasu motar suka daga.
Sun samu guri tuni ya dinke da mutane ga maji'an tsaro a baje ta ko ina suka nuna katinsu sannan aka bude musu suka wuce da mota, Suka samu guri sukai Parking suka fito kowa hannunsa sarqe dana matarsa. Sakeena kallon gurin take cikin qauyanci da mamakin tsaruwa da girman gurin. Cikin rada tace "Ya Sageer dama a Lagos ana samun guri me girman wannan? Wane hotel ne wannan?" yayi dariya yana qara sarqe yatsunta da nasa yace "To yar qauye ba hotel bane gidane, in kinji ana cewa family mansion to shine wannan, Oga da iyalansa mamansa da kuma danginsa na kusa ke xaune ciki, kinsan babban me kudine ya riqe muqamai da yawa a hukumar mu sannan ga business da yake ciki da wajen qasarnan" tace "Tabdi aida ganin abun na manya ne" suka samu guri suka xauna su duka hudun akan table daya kamar yadda aka tsara, Sakeena ta dunga kallon yadda aka qawata gurin tana mamakin ace duk girman nan ace gidane, itakam xataso taga mutanen dake rayuwa ciki da kuma oga Abdulfatah daya shagala da duniya ya tanfatsa wannan gida kamar baxa'a mutu ba. Ta qara riqo hannun Sageer tace "Yanxu ya Sageer duk akan wani banxan abu birthday aka narka wannan uwar dukiyar aka tsara wannan guri? Kuma birthday din ma na babba bana yaro ba" Su Sageer a tare sukai mata dariya, Bilki tace "Hmm kedai bari Sakeena nima kaina mamaki nake, masu kudi suna sha'aninsu kamar bada wahala ake tara kudin ba" suna ciye ciyen kayan da aka cika table din dasu kuma Sina taba hira har akaxo yanka cake aka yanka hade dayin hutana, Sageer da Maitama sukaje gurin oga suka gaisa hadi da tayashi murnar cikar xagayowar ranar haihuwarsa, Sageer ya fada musu da iyalansu suke tafe, Abdulfatah yana dariya yace "Ya baku qaraso dasu nan ba? Kuje kuxo dasu mu gaisa inga madam din Sageer wacce ke wahalar dashi" sukai dariya a tare suka juya dan kirawo su Bilki.
Suka taho tare kowa riqe da matarsa suka tarar yana gaisawa da wasu baqin, suka dan jira ya gama sai kuma ya kuma yin gaba gurin wasu, Sakeena ta fara mitar itafa tagaji so take su koma gida tai bacci don tafiyar dake gabansu gobe. Suka bata haquri Maitama ya kuma matsawa ya kira Abdulfatah da cewar dare ya farayi xasu tafi. Ya basu haquri tare da biyo bayan Maitama din.
Sakeena ce ta fara gaisheshi, tundaga nesa yake mata kallon mamaki dajin muryarta ya qara qura mata ido tare da yadda da abunda yake xargi a firgice ya furta "LINDA?" yakai hannu a gigice ya riqo hannun Sakeena yana cewa "Sister Linda kece da gaske?" Sakeena dasu Sageer gaba daya kallonsa suke da mamaki kafin ta fincike hannunta dagudu ta buya a bayan Sageer tana riqeshi cike da tsoro. Andulfatah ya xagaya bayan Sageer tare da qara riqo hannunta ta kwallah qara ta koma bayan Maitama, yana shirin binta Sageer ya shiga tsakaninsu cikin mamaki yake tambayar Abdulfatah meke faruwa. Cikin sauri yace "Sageer wannan yarinyar qanwata ce Linda wacce muke nema sama da shekaru ashirin a ina ka samota?" Sageer ya girgixa kai yace "A a Oga ba ita bace wannan, matatace wannan wacce ka sheda daurin aurenmu wancan karon kuma ka xama waliyyinta sunanta Sakeenatu" Abdulfatah har yanxu be yadda ba yace "Karkai musu dani mana Sageer wannan Linda ce har muryarta be bacemun ba inajin muryarta naganeta"
Haka suka dunga tafka musu har hankalin mutane ya fara xuwa kansu, Abdulfatah ya jasu xuwa Main falo na gidan gurin mamansa. Acan dinma ankuma kwatawa domin maman tana ganin Sakeena ta cikin medical glasses din idonta tace "Linda? Dama xan ganki kafin na mutu?" mutanen dake xaune falon sukaiwa Sakeena caaa suna wani irin yare. Ta qanqame Sageer dake tsaye cikin Al ajabin abunda ke shirin faruwa, tana kuka cikin tsoro tana cewa ya fita da ita xasu cinyeta.
Wani dattijo fari qal ya fito yana dogara sanda dagani ubane ga Abdulfatah, ya dubi Sakeena a nutse sannan ya juya gurinsu yana musu yare tare da ambaton sunan Linda. Abdulfatah ya basu gurin xama ya fuskanci Sageer yace "Babanmu ne wannan, kuma ya ankarar damu abunda muka manta, yace wannan kam ba Linda bace domin Linda yanxu duk inda take ta girma ya wuce ace tanada quruciya kamar wannan amma yace duk inda wannan yarinyar ta fito jininmu ce" ya dakko masa family pictures dinsu saiga masu kama da sakeena sak kamar twins dukkansu sunyi mamakin hakan.
Cikin sanyin jiki Sageer ya fadi yacce ya auro Sakeena da kuma lbrinta kamar yadda Iya ta fada masa. Suka hau kukan jin cewa Linda ta mutu wannan ta tsayen kuma yartace, suka bayyanawa Sageer yadda yarsu ta gudu tabi wani musulmi dan arewa sukai neman duniya basu ganta ba. Suka dunga daqumar Sakeena suna shafata da sumbatarta da cewa in waccan Linda din ta mutu aiga wata. Ta fusgewa ruqonsu ta koma jikin Sageer ta maqale tana cewa Ita sunan mamanta Aisha ba Linda ba kuma musulma ce. Suka hau yin yare da cewa suma ai duk sun musulunta shekaru da yawa tun abaya.
Ta kalli Sageer tace "Nifa gaskiya mutafi babu abunda ya hadani da wadannan mutane ni tsoronsu ma nakeji" Batasan akwai masujin hausa cikinsu ba, wata mata tai karaf ta amsa da cewa "Uwaka kai, xaka xagemu da Hausa bakasan munaji ba, ai Igala ma Hausa ne hijira sukai daga arewa, kuma babu inda xaka kaxo kenan nan gidanku ne" Sakeena tai fiki fiki tana raba ido, su Bilki dai dariya suke cikin mamaki wai kamar wasa anga dangin maman Sakeena.
Bayan dogon tarihi da dauki ba dadi dakyar suka bari Sageer ya tafi da Sakeena da alqawarin cewa ranar Sunday xasubi su Sageer har Kano dan tabbatar da Sakeena jininsu ce. A hakanma saida suka hadoshi da mutane sukaga gidansa a daren dan gani suke kamar xai gudu da ita kafin jibi Sunday. Ala dole ya daga tafiyarsu xuwa Sunday din dan sunce Saturday ya musu kusa xasu fadawa ragowar dangi anga yar Linda. Ranar daga Sageer har su Maitama sunga ikon Allah da qarfin hali gurin mutanannen domin nema sukai su hana Sageer Sakeena saida Abdulfatah yayi da gaske suka barsu suka taho.
Ya xabga tagumi yana kallon Sakeena bayan dawowarsu, mamaki yake Allah me iko wai Sakeena yar qanwar Abdulfatah ce uwa daya uba daya wato a taqaice yace gurin ubangidansa, kuma ikon Allah basu taba haduwa ba sai yau duk da tun abaya ya dace ayi hakan lokacin daya daura mata aure da kuma lokacin shigarsu kotu, amma Allah bai nufa an hadu ba ya kawo uxuri tare da tura wakili. Jikinsa yayi sanyi qalau daya tuna family din uwar Sakeena suna da kudi da kuma madafun ikon da xasu iya rabashi da Sakeena ganin cewar shi talaka ne tiqis akansu, su kuma aura mata me kudi kuma yarensu. Gabansa ya fadi fargaba da tausayin kansa lokaci daya suka ratsashi, yayi murnar bayyanar dangin mahaifiyar matarsa amma kuma yana fargabar rasa macen da yake masifar so a rayuwarsa.
Ta fito ta kwanta a jikinsa tace "Ya Sageer kaxo mu kwanta mana kaxo nan kayi tagumi" ya shafo fuskarta idonsa cike da kwallah yace "Sakeena yadda naga suna qaunarki da kuma yacce suke kallona sai nakega kamar xasu iya rabamu ko" tai saurin dagowa tana kallonsa gami da girgixa kai tace "Su wane su da xasu rabamu? Har yaushe nayi musu sanin da xan yadda su rabani da kai? Wace sadaukarwar sukaimin wacce tafi taka da xan bari hakan ta faru? Nifa ko? banma yadda cewa su yan uwana bane kuma inma kanaso yanxu saimu hada kayanmu mu dau hanyar Kano a daren nan in sukaxo sukaga gidan a rufe ba shikenan ba?" baki bude yake kallonta yace "Sakeena dangin mahaifiyar taki xakice mu guddar musu?" ta qara gyara kwanciyarta a jikinsa tace "Meye amfaninsu indai xasu rabani da kai? Ai lokacin da bansansu bama na rayu cikin jin dadi da kulawa kuma nasan ko babu su xakaci gaba da riqe amanata daka karbo gurin Baba, ni a duniya ta yanxu, Iya ce mahaifiyyata, Baba mahaifina kai kuma jigo mijina kuma dan uwana, uban yayana. Wlh indai basu karbeka ba amatsayin mijina ba to babu ni babu su saboda ina sonka kuma in shaa Allah aurenmu mutu ka raba" Sageer ya qura mata ido cikin burgewa da kuma alfahari da soyayyar da take masa, sai yanxu ya qara yadda Sakeena tana qaunarsa, yaji hankalinsa ya kwanta duk wannan fargabar ta rasata ta kau, ya dauketa sukaje suka kwanta yana rungume da ita tsam kamar xa'a kwaceta masa ita.
Hajia 😊
[8/21, 11:52 AM] Zongo Gal: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
3⃣0⃣
RAHMATULLAH (Hajia)
FINALE
EIDIL ADHHA MUBARAK TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUN.😊
GORAN SALLAH NE GA DAUKACIN MAKARANTA WANNAN LITTAFI MUSAMMAN
Aunty sis
Maryam Baita Usman
Marbab
Sapna
Sultana N Usman
Meela Adeel
Maryam Saddi
Diyar katibi
Khadija Bala Dandara
Amina Lamba
Maman ikhram
Maman Zahra
Wasila A Labo
Rahma Novels
Taskar Fiddausi Sodangi
Xclusive Ladies
Matan Aure only
AMITY Beauty salon
Naseeba's Novels place
Zauren Bibie Isa
Pure moment of life writers (PML)
Kainuwa writers association (Anty Fauzah)
jama'ata dake qasashen Niger da kuma Ghana (Da duk wanda lokaci be bani damar ambata ba 😊)
Da wuri suka tashi washegari asabar, suka shiga kicin tare ya tayata fere dankali ita kuma ta soya, ya dafa tea suka hado suka xauna akan center carpet suna karyawa. Hankalin Sageer be gama tashi ba sai da me gadi yaxo ya fada musu anyi baqi yace masa ya shigo dasu, saiga mutane qungiya guda, dagashi har Sakeena suka bar cin abincin suka miqe cikin mamaki. Duk da cewa falon ba qarami bane amma saida suka cikashi taf kuma dukkansu wai sunxo ganin Sakeena ne.
Ta dunga sunkuyawa tana gaishesu kamar yadda Sageer ya umarceta, sukayi masa bayani sunxo ganin yadda Sakeena ta kwanane da kuma neman alfarmar ya barta taje can gurinsu akwai yayar kakanta wacce bata iya fita saboda tsufa aka dakkota dan ganin Sakeena. Sageer a xuciyarsa yace kodai kunxo ganin ko na gudu da ita ba. Bai kulasu ba sai fita da yayi harabar gidansa can inda Abdulfatah ke tsaye da wasu mutanen yayi masa bayanin cewa Sakeena fa matarsa ce kuma tana dauke da ciki saboda haka baxata juri xirga xirga ba dan Allah koma menene su dakata xuwa goben aje can Kano. Abdulfatah ya shiga falon yayi musu bayanin da Sageer yayi masa da yarensu, suka gama maganganunsu wanda daga Sakeena har Sageer baji suke ba kana suka tashi suka shishshiga motocin da sukaxo aciki suka koma.
A tare suka saki ajiyar xuciya bayan fitarsu, Maitama ya shigo falon yana kallonsu da mamaki yace "wadannan fa Sageer? Naga convoy na motocin Oga sun fita yanxu" cikin dumuwa yace "wai duk sunxo ganin yadda Sakeena ta kwanane Maitama, nifa na fara tsorata wlh so suke su rabani da ita" Maitama ya dafa kafadarsa yace "Karkai wannan tunanin mana, kasan oga mutumin kirki ne kuma yanasonka baxai bari ayi maka haka ba, kawai dai suna murnar ganin diyarsune da suka dade suna nema. Shawarata yanxu ka buga wayacan Kano gidan su Sakeena ka fada musu abunda ke faruwa sannan itama Umma ka sanar da ita, don ayi a wuce gurin hankalinka ya kwanta"
Sageer yayi naam da shawarar Maitama ya ciro wayarsa ya fara kiran Umma, Allah sarki tana dauka lfy Sakeena ta fara tambaya. Sakeena ta matso jikinsa ta karbi wayar ta fara gaishe da Umma tare da cemata lfy ta qalau umma. Sageer ya amsa yayi mata bayanin abunda ya faru jiya xuwa yau. Tayi Hamdala tace "To meye abun damuwa Muhammadu? Ai murna ya kamata kayi anga yan uwan matarka" yace "Umma masu kudi ne fiye da xatonki kuma sunada manyan jamian gwamnati a cikinsu kuma fa Sakeena yace ga shugaban hukumarmu gaba daya Abdulfatah, gani nake in sun ganni talaka kuma bahaushe xasu iya kwace sakeena su aura mata yarensu me kudi" Umma tai dariya tace "Muhammadu kenan ashe har yanxu baka girma, ko son sakeena ne ya maidaka yaro? To ka kwantar da hankalinka, bana xaton Sakeena xata bari a rabaku saboda wani abu arxiqi ko banbancin yare, sakeena yar halak ce nasan baxata taba butulcewa hallaccin da kai mata ba ita da uwar riqonta, ka kwantar da hankalinka kaji ko kuma xan muku addua kai da ita" ya sauke numfashi cikin jin dadin kalamin umma yace "Wlh umma kamar kina gurin haka sakeena tacemun jiya baxata taba bari su rabamu ba inma nufinsu kenan" tace "Yawwa kaji xancena ba Allah yayi muku albarka" ya amsa suka rabu ya kira Iya.
Sakeena ce ta fara magana da cewa "Hajiya Iya" tana dariya tace "Allah amin Sakeenatu, bani da burin daya wuce xuwa dakin Allah kafin in mutu" Sakeena tana dariya tace "To Allah ya sa aikin Hajji bana dake xa ai" Iya tace "Kayya dai Sakeenatu, abu da anfara tafiya tuntuni" tace "Lah Iya karkiyi mamakin kina daga cikin masu xuwa wannan shekarar in Allah yaso" tace "To tunda kikace Allah nayi shiru ikonsa yafi gaban komi. Ni kintareni da surutu kina lfy? Ina sageerun?" ya karbe wayar yace "Assalamu alaikum Hajiya Iya ganinan" tana dariya tace "Au Sageeru harda kai a zolayar tawa?" shima dariyar yayi suka gaisa kana ya sako mata dalilin kiran, jikinta yayi sanyi fiye da xatonsu tace "Sageeru cewa xakai masu rabani da Sakeenatu sunxo? Nasan dauketa xasuyi ko kuma suyi qararmu akan danmu ya gudar musu da diyarsu tunda kace yanxu sunyi arxiqi, kasan dama tun asali bason auren uwar sakeena da Ababukar suke ba shiyasa ta gudu ta biyoshi" ta qarasa tana share kwallah, Sakeena tai saurin matsowa ta amshi wayar dake hand free tace "Dena kuka Iya, babu wanda ya isa ya rabani dake koda kuwa shugaban qasa ne, ki kwantar da hankalinki" duk da wannan kalami na Sakeena jiki a sanyaye suka rabu tace xata fadawa Baba xuwansu gobe.
******* ******* ******** ********
Bangaren Deni mijin Hajiya Surayya kuwa ya miqe qafa gida yana jinya sai dayayi wata guda cif sannan ya nufi xuwa office bayan gaba daya ciwokan jikinsa sun warke. Monday yayi wanka yasha suit ya baxa turare ya nufi office yana shan qamshi kamar company din ubansa, abun mamaki agurin Deni shine ya tarar da wani a office dinsa yanata aiki, baiyi magana ba ya koma da baya ya qara duba sunan dake jikin katakon kofar shiga office din, ya tarar da wani baqon suna ba nasa ba. A sanyaye ya fito ya nufi office din DG domin jin ba'asi, acan ya tarar da takardar sallamarsa daga aiki, Deni da yaxo yana shan qamshi sai gashi tsugune gaban DG yana hawaye tare da roqon a temaka masa abarshi da aikinsa.
DG din ya dubeshi yace "kaika jawowa kanka Nura, mun qona kudade mun turaka Lagos don yin course domin kaxo ka koyar da ma'aikatanmu na nan sai mukaji lbrin acan din baka maida hankali kayi abunda aka turaka ba, ba kullum kake xuwa gurin bita ba asha ruwan tsuntsaye kakeyi, sannan kuma daga baya ka tattaro ka gudo batare da sanin company ninmu na can ba kamar xaman kanka kakeki, munata jira anan muji kaxo kayi report na abunda ya sameka acan Lagos din amma sai mukaji shiru ka miqe qafa kayi xamanka sai daka shafe wata guda cur harda kwanaki shine yanxu danka rainawa kanka hankali xaka dakko qafa ka taho aiki saboda company naka ne ko?" Deni ya fara sharbar hawaye duk dan DG ya tausaya masa ya maidashi aiki harda shada karyar cewa wai a hanyar dawowarsa daga Lagos ya kuma haduwa da accident har karyewa yayi akai masa dorin gida shiyasa baixo yayi report ba.
DG ya girgixa kai yace "Hakan yayi dai dai gara daka xauna kayi jinya da kyau kuma gara kaje ka qarasa warkewa saboda naka har yanxu kana dingishi. Kamar yadda ka gani dai an sallameka aiki, saboda akwai biliyoyin matasa da suka qare karatu da sakamako me kyau suke neman irin damar daka samu ka wulaqanta, sakamakon haka muka maye gurbinka da waninka domin baxamu xauna kai daya kana wahalshemu ba, Saboda haka mungode muna maka fatan alkhairi" Deni ya dade a office din yana koke koke tare da roqon DG ko wani aikin ne ya bashi wanda be kai nasa ba domin yasha wahala kafin ya samu wannan aikin. Ko kallonsa DG beyi balle ya tanka masa.
Dole ya fito daga office din yana tafe yana kuka be damu da masu kallonsa ba, ya shiga mota ya kifa kai yasaka kuka kamar mace. Wai meke shirin faruwa dashi ne? Yana daya daga cikin matasan da xasu dorar da wahalar samun aiki ga dan talaka a qasar nan, domin ya wahala ba kadan ba kafin Allah ya axurtashi da wannan aikin ta silar Sakeena. Yanxu shikenan ya rabu da aikin dayake taqama dashi kenan? Yanxu xai koma irin rayuwarsa ta baya kenan kafin samun wani aikin? Wai meyasa tunda ya rabu da Sakeena masifa ke binsa daga wannan sai wannan? Yanxu yayi biyu babu kenan uku ba ko daya? Babu aiki kuma babu Sakeena? Ta wace hanyar xai kuma samun wani aikin? Ya kunna mota ya nufi gida cikin mawuyacin hali.
Surayya ta fita aiki dan haka ya samu sukunin shiga bedroom yana tunanin mafita akan wannan abu daya sameshi. Yana kwance ko sallah beyi ba har Surayya ta dawo aiki ta sameshi kwance cikin wannan halin. Ta taba kansa tana tambayar meya sameshi taga idonsa haka? Cikin muryar kuka ya bayyana mata an sallameshi aiki. Taja tsaki tace "To saime? Dan kawai an sallameka aiki xaka xauna kana kuka kamar mace? Wannan ai ba abun damuwa bane saika koma qarqashin Daddy na dama yana neman sabbin ma'aikata" Deni ya harxuqe yace "Waike wace irin mahaukaciyace? Ince an sallameni aiki kice ba wani abu bane? Kuma Allah ya sawaqe inyi aiki a qarqashin Babanki mutumin da akace baisan darajar mutane ba, shiyasa kullum ma'aikatansa suke guduwa saboda wulaqancin da yake musu" ta gyara tsaiwa ta riqe qugu cikin futsara tace "Yayi wulaqancin ca nike shiyasha wahalar tara dukiyarsa ba uban wani ya tara masa ba, kuma duk tsiya arxiqinsa kake ci koka manta nan gidansa ne kake xaune? Kuma abincinsa kakeci? Ko kataba siyan koda kwayar gero a gidan nan?" Deni sarkin rashin haquri ya tashi ya dauke Surayya da maruka guda biyu hagu da dama ta kwantsama ihu, ya dora da cewa "Ke har kin isa ki xagi ubana dan ubanki? Kuma gida da kayan abinci ai ba nema nayi ba, rainawa nawa kukayi shiyasa na haqura naxo naku lokacin ina sonki bansan shapeless bace ke kuma mahaukaciya" ya koma ya kwanta Surayya kuma ta juya xuwa gidansu ta fadi duk yacce sukai da Deni babu qarin ko kallama daya domin ita duk iskancinta bata qarya.
Babansu bayanan yayi tafiya xuwa China dan haka babban wansu wanda yafi Deni xafin kai shine ya kira waya akaje har cikin gidan aka daqume Deni kamar barawo. Yanata tambayarsu me yayi babu wanda ya kulashi saida sukaje station sukai masa mugun dukan da akewa yan fashi sannan sukace Surayya ya mara shiyasa aka danqoshi kuma inyanason fansar kansa saiya bada 100k diyyar marin Surayya sannan a sakeshi. Hawaye ya xubawa Deni cikin nadama, ba kukan dukan da akai masa yake ba a a kukan tuno rayuwarsu da Sakeena yake yacce abu kadan xai mareta in bai manta ba har da belt ya taba zane ta kuma babu wanda ta fadawa balle ayi masa jan kunne, sai dai tai kukanta ita kadai ta share hawayenta hakan kuma baxai hanata yimasa abunda ta saba ba na biyayya. Amma yau gashi duniya juyi juyi wai shine a rufe a police station don kawai ya mari Surayya. Lallai ya gazgata maganar dake cewa sakayyar aure tun a duniya Allah yake yinta, kuma auren baya sadakin na gaba, ma'ana duk abunda ka shuka a aurenka na baya tsaka tsinci sakamakonsa a gaba. Saida ya kwana ya wuni xuwa yamma yaga basu da alamun sakinsa saiya bada 100k din da sukace, ya basu no wayar Saddiq suka kirashi da fada masa station din da Deni yake, cikin rabin awa saigashi shida Hajjo hankali a tashe, ya fada musu duk yacce akai ya bawa Saddiq ATM dinsa da pin din yace ya ciro 100k din ya kawo a sakeshi. Hajjo ta samu guri ta xauna tana kuka har Saddiq ya dawo da kudin suka amshe babu kunya suka sakeshi.
Hajjo ta riqeshi tana kuka, Deni yace "Ina Baba naga be xoba?" Saddiq ya bashi amsa da cewa "Cewa yayi baxaixo ba babu ruwanshi domin bashi ya aikeka ka mari yar mutane ba, sannan ba tunyau yake gargadinka akan xafin xuciya ba kuma bayan haka ai Surayya xabinka ce kai da Hajjo shiyasa ya bar Hajjo mukaxo belinka tare" Deni yayi shiru idonsa cike da kwallah, Hajjo tana kuka tace "Deni ka saki yarinyar nan kawai mu huta ni da kai tunda ita ba haihuwa take ba, sannan ga dankaren rashin tarbiyyyarta daya addabemu" Saddiq yayi saurin daga mata hannu yace "Dakata Hajjo, in maganar gaskiyace duk halin da Deni ya shiga kece sila" ta dafe qirji tace "Ni kuma Saddiq? Tayaya kenan?" yace "Ta hanyar buri da kuma adduar da kike masa tun yana yaro na Allah ya bashi yar me kudi ya aura yacce basai yayi hawalar neman arxiqi ba yana xaune ubanta xai axurtashi, wannan buri naki shine yasa kika tilasawa Deni xama a gidan uban Surayya wanda tunkan auran yaci talatarsa da laraba aka fara samun matsala, kinga yadda auren sanfurrin aureni ka huta yake qarewa ko? Kinga irin tarbiyyar wasu daga cikin diyoyin masu kudi ko? Tayaya baxata rainashi ba yana xaune qarqashinta? Yana xaune da matar arxiqi kuka kafa mata qahon xuqa kuka xalunceta kuka rabasu, ai wlh ko haqqin Sakeena ya isa ya hanaku xaman lfy. Gashinan kowa a cikinku yana fuskantar hukunci dai dai da abunda ya aikata daga gurin ubangiji yayin da Sakeena kecan tana xaman lfy a gidan aurenta. Tanxz God dana farga na dawo rakiyarku da tuni hardani acikin wannan sakayyar"
Deni ya gyada kai domin yasan maganar Saddiq gaskiyace tsakwaronta, shima makantar xuci da xafin rai gami da tsautsayi sune sukashi sakin Sakeena. Jiki sanyaye ya fada musu an koreshi aiki kuma daya dawo daga Lagos ya tarar Surayya ta cire ciki. Hajjo ta rafka salati ta koma ta xauna dabas a gurin. Saddiq ya share xuffa saboda cikin rana suke tsaye yace "Kinga tasirin adduarki akansa ko? Kinga tasirin bakin uwa akan danta ko? Shikenan burinki ya cika Hajjo Deni ya gama xama mijin Hajiya yanxu ne xai xama yadda kike buri domin xai xauna qarqashin mulkin Surayya tunda bashi da aiki, taci dashi, ta sha dashi, ta bashi muhalli, kana yayi mata gadin gida ta fita aiki, wannan shine cikakken aure saffurin aureni ka huta, baxai wahalar komai ba ammafa sai yadda akai dashi ya xama matar ta xama mijin. Shiyasa akeson kyakykyawar addua ga yaya" Hajjo ta riqo hannun Deni tace "Mu wuce can gida Gwale baxaka xama mijin Hajiya ba wlh, ban haifi marar xuciya ba muje kai wanka ka huta ka rubuta mata takaddar shika kuje da Saddiq kukai mata ya rakaka gidan ka kaso dukiyarka da kayanka" Saddiq yayi saurin cewa "Sakinta fa ba shine mafita ba, kuma ni baxan xama baqin jakada ba wato wakilin mutuwar aure kiyi haquri kawai muje gida shiya tafi nasa gidan mu dingi adduar nemarwa matarsa shiriya domin a binciken da nayi akanta kafin ya aureta ance wlh basa sakuwa, ko mijin yayarta daya saki yayar surayyar haukatashi sukai tuburan, sannan naji ana cewa ma iyayenta babu aure tsakaninsu xaman haramci suke, uban surayyan ya dade da sakin uwar amma taqi fita kuma har saki uku"
Abunda ya daure musu kai duk su ukun shine ganin motar Surayya ta shigo cikin station din tayi parking a gabansu taxo inda suke tace "Deen yanxu dan sandan yayimun waya yace ka biya kudin tarar har sun bada belinka shine naxo daukarka mutafi" babu wanda ya tanka mata kallonta suke da mamaki, ta juya tace "Saddiq baka da kirki ko leqomu bakayi, Hajjo muna lfy ya qafar taki?" Hajjo tai shiru dan ita yanxu tsoron Surayya take, Saddiq kuwa amsa mata yayi da cewa "Wlh kuwa Hajiya Surayya abubune sukai yawa amma inna sami lokaci xan shigo" taja hannun Deni tana cewa "To muna barama da baquntarka domin nasan kai baka raba raba sunnar ma'aiki" Deni ya daqire yaqi binta Hajjo ta turashi tace "Bita mana domin dasu haukatamun kai gara ka bita" Surayya ta kalli Hajjo tana murmushi tace "Madallah, lbr yaxo muki kenan? Bayan shima muda wani tambarin daya fishi muni in aka nemi kawo mana turjiya domin mu duk masifa da bala'i aurenmu baya mutuwa dan haka aurena da Deni xama daramdam" babu shiri shima Denin ya bita ziiii kamar raqumi da akala suka shiga mota suka daga. Saddiq yaja Hajjo sukai gida tana kukan nadama.
Ya miqe qafa ya fara xaman banxa a gida, sai dai ya yini bacci ko kallo ko chatting kamar ba magidanci ba (Haba mal Deni, ai yanxu ko mata sun daina xaman banxa balle maxa) yayin da Surayya ke fita aiki ta barshi, babu shiri ya cire girman kai ya nemarwa kansa mafita lokacin dayaga abun na Surayya yayi yawa domin yanxu inxata fita saitace "Deen ka wanke mana undis dinmu mana tunda babu uwar abunda kakeyi a gidan, da xaman banxa ai gara mugun tunani ko? Ni nafita ka kulamun da bedroom din sosai" ai babu shiri Deni ya tattaro dan abunda yake dashi a account dinsa ya hada da tsohuwar ajiyar sarqar gold din daya saiwa sakeena tun lokacin data bata da nufin inta dawo ya bata, wacce yaketa ajiyarata har yanxu a haukansa yana jiran ranar komawarsu aure ya bata ita a first night dinsu.(🤣) Xuwa yanxu ya tabbatar da mafarkinsa baxai xama gaskiya ba saiya dena yaudarar kansa yaje ya saida ita ya hada kudin ya kaiwa Baba yace masa yanason bude provision store a cikin nan unguwar dan yaga xaman haka baxai yiwuba.
Baba yasa albarka kuma ya shige masa gaba ya samoma masa hayar wani shago babba daura da gidansu Denin aka maqare store da kayan provision yayi kyau harda qatuwar freezer, Deni ya fara xama a kantinsa, yana xuwa goman safe amma kafin yaxo 7 AM Saddiq ke fara xamar masa yayi masa cinikin safe, yana yini a shagonsa in lokacin cin abinci yayi ya shiga gida yaci ko a miqo masa, qarfe takwas din dare yake tashi ya nufi gidansa yayin da shi kuma Saddiq xai karba har xuwa 11 na dare sannan ya rufe ya shiga gida, kuma suna ciniki babu lefi kuma dan abunda yake samu dashi yake sayawa Hajjo irin cimarta ta masu Diabetes da kuma magunguna in abun ya tashi. Sai surutan mutane da suke xuwa takanas dan ganin Deni a kanti wasu suyi dariya masu hankali kuma su qara kiyayyar lamarin duniya wacce ke xuwa da sauyi kala kala. Ranar da Surayya ta biyo Deni a baya dan ganin inda yake xuwa ya yini kullum har weekend taganshi a kanti, ta tsaya a qofar kantin tana kallonsa tana sheqa dariya ta gama dariyarta kaf tace "Ina ruwan birin kanti, kai yanxu da wannan xaman naka anan ai gara xamanka a qarqashin Babana daka raina domin koba komai duk tsiya xakaci me kyau, nan kuwa nasan sai dai Hajjo ta miqo maka gabxa kaci" ta gama iskancinta be kulata ba duk kuwa da xuciyarsa na tunxurashi ya tashi ya nada mata duka, amma dole ya taushi xuciyar tasa don karya daketa ya kuma ballowa kansa tarar 100k wacce yanxu besan ta inda xai sameta ba. Ta shige cikin gidansu gurin Iya shan kunun aya kamar yadda take xuwa sha intayi ra'ayi, Hajjo na ganinta ta gudu daki, a mutunce suka gaisa da Iya ta kawo mata robobin kunun ayar tasha ya isheta ragowar ta xuba a jaka, ta juya ta fice tana cewa Iya agaida Baba inyadawo, ko dakin Hajjo bata kalla ba balle ta shiga gaisheta. Iya dai tanashan mamakin wace irin surukace wannan? Duk da dai ita bata taba yi mataba, girmamawace a tsakaninta da Surayya dan haka ta xama yar kallo kuma ta tabbatar da Surayya ce dai dai da Hajjo shiyasa suke gogawa.
Ranar Sunday suka dira kanon dabo da misalin qarfe goman safiya, motocin hukumar custom ne sukaxo suka debesu daga airport. Dangin Abdulfatah sun kusa mutum hamsin itadai Sakeena sai yaqe take ganin yadda suketa nan nan da ita, ta dan sake kadan a dalilin samun sa'anninta kuma masu kamarta sak acikin xuriar dasuka kira kansu dangin mamanta. Wata matashiyar budurwa yar kimanin shekaru 25 wacce taji suna kira Maryam kuma wacce ta kira kanta a matsayin yar autarsu Aisha (maman sakeena) itace ta mannewa sakeena sosai kuma ta fadawa Sakeenan ita tana karatu ne a jamiar Abuja jiya taxo adalilin jin ansamu yar yayarta, sakeena ta sake da ita saboda ita tanajin Hausa kuma tana mayarwa a dalilin xaman hostel da take a jami'a, ta fadawa Sakeena yacce dangi hankalinsu ya tashi da aka rasa Aisha duk da a lokacin ita maryam din bata da wayo yarinya ce sosai amma ta tashi taga ana yawan xancen bacewar Aisha. Sannan ta bayyanawa Sakeena yadda suka sha fama da talauci sosai amma kuma duk da haka suna karatu saboda a kudu da wuya kaga matashi babu ilimi duk wahala suna tsayawa suyi, suna cikin wannnan xaman Allah yasa wani uncle dinsu ya samu kujerar gwamnan garinsu bayan lashe xabe a farkon dawowar mulkin farar hula, hakan yasa ya dunga ciccibasu suna samun aiki ya baxa matasan da sukai karatu a yayan yan uwansa wasu aikin soja wasu kuma police wasu custom a irin haka Abdulfatah wansu yaje hukumar custom kuma ya fito a babban jami'i saboda iliminsa. Wannan shine tushen kafuwarsu wato albarkacin ilimi sukeci, kafin shekara 10 sun kafu yawanci kowanne gida a xuriar sunada babban jami'in gwamnati, yan boko ne sosai masuci da biro. Sageer ya matso yace da Sakeena "Naga taku taxo daya da Anty Maryam kamar yadda kikafi kama da ita fiye da kowa a xuriarku har muryarku iri dayace" Sakeena da Maryam suka kalli juna tare sukai dariya yace "Lah har dariya wlh iri daya kukeyi, kinsan Allah babu wanda xaice ba yan biyu bane ku" Suna wannan hirar har suka isa gidansu Sakeena da Sageer ya musu kwatance. Lokacin xuwan Deni kenan gidan ya shiga sun gaisa dasu Baba xaije ya karbi Saddiq xaman kanti saiga mutane suna shigowa, Sageer ne kadai namijin daya shigo riqe da akwatinan da Sakeena taxo dashi, Deni na ganin Sageer ya kama kansa yayi gefe, haba saiga sakeena da Maryam sun shigo riqe da hannun juna, cikin rawar baki yace "Dama Sakeena yan biyu ne?" sai kuma ga manyan mata da yaran mata masu kama da sakeenan sai cuccudowa suke cikin gidan.
Acan waje mutane sun cika kofar gida don jin jiniya da kuma uban motocin da suka cika kofar gidan mal Lawan, aka kaiwa Saddiq lbr yayi saurin rufe kantin yayo gida ganin abunda ke faruwa.
Baba da Iya suka fito tsakar gida a tare Iya tana cewa "Eh wannan dagani babu tambaya yan uwan Aisha ne domin ga kama nan" Baba ya fito ta tabarmi yana shinfidawa a tsakar gida saboda yawansu yace da Saddiq yaje ya shigo da maxan ciki. Hajjo da Amina suma sukayo waje jin muryoyi da qamshi ya cika gidan.
Babane ya bude musu taro da addua aka shafa, Sageer ya miqe ya maimaita abunda ya faru a daren ranar Friday, Iya ta miqe tai musu bayanin yadda qaninta Abubakar yaxo da mace ta musulunta aka sakamata suna Aisha da kuma auren da sukai, tana fada Abdulfatah na fassara musu da yaren Igala. Iya ta dakko musu hoton Aisha da Abubakar wanda suka dauka ranar sunan Sakeena tana riqe da Sakeenan. Suka rude da yare wasu kukan jin yar uwarsu ta mutu, suka tabbatar da Lindace a jikin hoton sannan dayan shine drivern motar daya gudu da ita lokacin Abdulfatah yana walda a tasha. Ana haka saiga tawagar yan Baggadano sunxo qarqashi jagorancin babban yaya Dahiru, suma jiya Baba ya fada musu a waya anga dangin uwar Sakeena, su dinma harda megari suke tafe wanda ya fada musu shida liman suka musuluntar da Aisha suka kuma aura mata Abubakar.
Gida ya kuma cika da kuke koke domin angama warware komai, Sakeena hawaye ya xubo mata wai yau itace haka kuma wadannan da suka cika gidan dangin uwarta ne dana uba? Allah me yacce yaso, a sanda yaso, ga kuma wanda yaso. Ta matsa gaban mama wato karkata tace a nuna mata matsayin kowa a gurin. Maryam ta riqe hannunta ta dunga nuna mata kowa tare da matsayinsa gurinta, tun daga kan Mama har kakanta namiji da suke kira Daddy, yawancin manyan matan gurin yayyun mahaifiyartane su 9 mama ta haifa amma maryam tace mata guda biyu basanan dayar tana Ghana tana aure dayan kuma namiji ne sojan ruwa(navy) yana can gida Kogi kuma yanakan ruwa suna sauka xaixo, Abdulfatah shine babban namiji a gidan, yan matan gurin kuma da samari duk cousins dinta ne wato jikokin mama. Sakeena ta share hawaye ta matsa gaban Mama da Daddy ta riqo hannunsu a tare tace "Dan Allah ku yafewa Gwaggo na lefin da tayi na guduwa daga gurinku, ba laifinta bane soyayya ce taja ta aikata hakan kuma da kun amince da aurenta da Baba da baxata gudu ba" Mama taja Sakeena ta rungume tana cewa "Babu komi Sakeena mun yafe mata, munsan rabon shiga musulunci da kuma rabon haihuwarku ya sata ta gudu, Allah ya jiqanta ita da Abbakar kuma daga yanxu ke yata ce ba jika ba xan dunga kallonki a matsayin Aisha" Sageer ya yaba da hankalin Sakeena na nemarwa mahaifiyarta gafara gurin iyayenta.
Baba ya kuma tashi ya fada musu tun daga kan mutuwar Nura da dakko Sakeena da Iya tayi har xuwa kan aurenta da Deni da yadda auren ya lalace saboda shigowar auren Sageer da yadda ta kuma auren Sageer a karo na biyu. Yayi bayanin komai babu san xuciya kuma babu tada husuma. Suka dunga kallon Hajjo da Deni cike da kyama aka kuma yiwa Sageer caaa ana rungumarsa tare da yaba masa, haka Iya da Baba sunsha yabo wajen dangin Aisha bisa jajurcewarsu da riqon marainiya, Abdulfatah shima ya fadi abunda ya sani akan aurensu na farko da kuma xuwa kotu. Ya dafa Sageer yace "Mungode Sageeru dakai da Iya da Baba xakusan kun riqe yar gata kuma yar dangi" Mama kuwa sai daqumar Sageer take tana cewa ya xama danta tunda ya riqe mata Sakeena da amana kuma yasakata a makaranta. Shima sai yanxu ya samu nutsuwa ganin ya samu karbuwa a gurinsu.
Iro yayan Sakeena ya miqe ya watsawa Hajjo da Deni mugun kallo yace "To ya kukaga abun? Yaudai gashi Allah yayi ikonsa Sakeena ta samu danginta na uwa sannan gamu mukuma na uba, daga yau sai adaina yimata gorin asali da gata ko?" sukai wuqi wuqi, Iro yacigaba da bawa su mama lbarin abunda Hajjo taiwa Sakeena ita da yayanta, Maryam na interpreting masu abunda basu gane ba, Saddiq ya runtse ido beso wannan taunan sililin da Iro yayi musu domin ya qisma wani abu a ransa wanda wannan magana ta Iro tana Iya kawo masa matsala acikin abun.
Abdulfatah yasa akai shiru ya matso ya dafa kan Sakeena yace "My daughter kene kika xauna da muttanen nan kisan abunda kowa yakeso saboda haka ki fada mana abunda kikeso aiwa kowa acikinsu, a matsayin tukwuicin riqonki da sukayi da amana" tai shiru tana kallonsa cikin tunani yayin da Deni ya kafeta da ido yana ayyanawa a ransa inama tasan ansallameshi daga aiki da tasa an samo masa wani. Sageer ya lura da kallon da yake mata yayi gyaran murya ya fallara masa harara, ba shiri ya janye idonsa daga kanta ya mayar qasa. Abdulfatah ya katse mata tunani da cewa "Komeye ki fada indai a duniya yake xanyi iya qoqarina insamar musu dashi" ta dago tana kallonsa matarsa wacce suke kira Mummy tace "Fadi sakeena Babanki ya tara kudi kuma yanada alfarma sosai xakiyi mamakin alfarmarsa"
Cikin sunkuyar da kai tace "Baba inda hali dan Allah akai Iya da Baba da kuma Umman Sageer qasa me tsarki suyi aikin Hajji, sannan asamawa Baba wata sana'a da xata dunga samar masa da kudin da xai dunga daukar nauyin iyalinsa kafin xuwan fansho, yan uwana kuma da muka hada uba basuyi karatu ba amma manoma ne dan Allah a sauqaqe musu hanyar neman abincinsu sannnan suma a basu jari, ga Saddiq nan ya gama karatu babu aiki shima a sama masa aikin yi" Kowa kallonta yake da mamaki domin ta fadi abunda kowa ke buri kamar ta shiga xuciyarsu. Abdulfatah ya matsa yace da Iya da Baba "Kun shirya xiyarar qasa me tsarki wannan shekarar?" cikin sauri Baba ya share hawaye yace "kullum cikin shiri muke amma ai munga anrufe biya har anfara tafiya ko?" Maryam ta matso tace "Baba ai akwai kujerun da ake bawa manyan jam'ian gwannati duk shekara wanda suke tafiya a jirgin yan alfarma kuma sune tashin qarshe to yawanci yayanmu in xamu tafi anan muke tafiya yan gidanmu duk shekara, bana tunda kagu baku taba xuwa ba sai amaye gurbinmu daku sai kuje, wadanda kuma yake biyawa duk shekara tuni sun tafi dama iyamu yan gidane dashi muke tafiya a jirgin alfarma.suka jinjina kai a tare, Mama tace "Sakeena ke da Sageer bakusan xuwa aikin Hajji ne ko kuntaba xuwa ne?" Sakeena tace "Munasan xuwa Mama wai dama kar abun yayi yawa ne" sukai mata dariya a tare domin da alama batasan waye Abdulfatah ba. Yace "To duk ku shirya xuwa gobe xakuje can office din immigration don yin passport wanda kuma yake dashi a cikinku shikenan saiya kawo, sannan yace kai kuma Dahiru kuyi haquri xuwa wata shekarar sai a fara kai wasu acikinku sauke farallin" ya kalli su Deni yace "Waye Saddiq?" da sauri Saddiq ya xube gabansa yace "Gani yallabai" yace "Wane aiki kake so?" cikin sauri Saddiq yace "Duk wanda ya samu inaso yallabai amma dai B ED na karanta" ya jinjina kai yace "kanason irin aikinmu na custom xaka iya jure training?" yace "Eh inaso xan iya duk wahala" yace "To in an bude portal na hukumarmu xan sanar maka kayi registration saika kawomun takaddunka" ya fara godewa oga da kuma Sakeena tace "Bakomi Saddiq ka godewa Allah shiya baka ba niba"
Iro ya harari Sakeena yace "Waike wace irin xuciya gareki harda xakice a samarwa irin matar da taso watsa rayuwarki aiki? Shin wai kinmanta axabar da kikasha a hannunta? Kin manta qazafin zina da sukayi miki suka bata miki suna ita da yayanta?" Sakeena tai murmushi tace "Yi haquri yaya Iro, ai lefin wani baya shafar wani kamar yadda ko a lahira wani yanacin arxiqin wani. Ni Saddiq bemun komai ba wlh kuma suma wadanda sukaimun na yafemusu ragowar hakkin kuma ya rage tsakaninsu da wanda ya haliccesu. Sannan kuma inka tashi temako ko alheri ai baka duba cewa lallai sai mutum ya maka kirki ko kuma xaka moreshi bayan ka temaka masa, indai muna duba hakan kam baxamu taimaki kowa ba, abunda kawai nakesawa xuciyata shine: a duk sanda naga wanda ke buqatar temako ina kuma da ikon taimaka masa to xanyi iya qoqarina in temaka, baxan duba ya taba yimun wani abuba na bajinta, ko kuma innai masa temakon shima saiya dawo ya ramamun, xan qudure a xuciyata nayine domin Allah kuma sakamakon abunda nai xai riskeni ko a duniya ko a lahira indai na tsarkake niyya, sannan shima wanda aka taimakawa inyana hankali inya samu dama xai temaki wani kwatankwacin irin temakon da akai masa, kaga ko ban mori ribar ba al umma ta mora. Yanxu dubi Saddiq ya kammala karatu shekaru biyu baya amma yana xaune babu aiki, akwai kuma biliyoyin matasa irinsa a kusa da nesa wadan da basu da aiki, fisabilillah tayaya qasarmu xataci gaba haka ana dakushe tomorrow leaders? In mutum yayi karatu ya rasa aikin da xaiyi da iliminsa to dole fa yayi amfani da ilimin nasa ta muguwar hanya domin tunanin mara aikinyi masaqar shedan. Kamar yadda naji wani malami yana fada cikin wa'axinsa a watan Ramadan yake cewa "Wlh da kason kudin da ake warewa tsaro a qasarnan ake warewa ilimi da samar da aikinyi ga matasa da tuni anyaqi ta'addancin dake haifar da rashin tsaron, domin mafiya yawan masu shiga ta'addancin xaman banxa kesa su shiga" Dan Allah mu dage wajen temakon wadanda basu da masu taimaka musu, ba sai lallai daukar aiki ba, ko sana'ar hannu kika iya temaka ki koyawa wata karki baqin cikin xata fiki daukaka ko yin suna wannan duk na Allah ne, kuma in kika temaka kin yaqi xaman banxa kuma kin bada gudummawa a society. Allah ya gyara qasarmu ya kuma bamu shugabbanni nagari masu tausayinmu"
Kowa a gurin kallon sakeena yake cike da burgewar wannan dogon sharhi da tayi, Sageer ya harde hannu a qirji yana kallonta cikin alfaharin kasancewarta matarsa, ashe haka take da fasaha? Yarinya qarama ta dakko babban maudu'in dake damun mutane tayi fashin baqi akai da kuma kawo mafita. Abdulfatah ya tako ya qara dafa kanta yace "sannu Sakeenatu, haka akeson tunanin mutane ya xama me kyau, da ace tunanin mafi yawan mutane irin naki ne da tuni qasarmu tacigaba tuntuni, ina alfaharin kasancewarki cikin xuri'armu" Baba yace "Ai Sakeenatu kam tafi gaban haka akwai kyakykyawar xuciya da kuma fasahar harshe"
Abdulfatah yasa bodyguard dinsa ya miqo jakarsa a mota ya bude ya raba kowa dake gurin 50k har Deni da Hajjo, da Amina suka karba suna godiya sakeena ta karbarwa Umman Sageer nata tace daganan can xasuje gobe don fada mata tayi shirin sauke farali, babu kunya Hajjo tace akwai wasu yayanta guda 3 da basanan suna gidan aure suma abasu nasu ta ajiye musu. Saddiq da Baba suka runtse ido cikin kunyar abunda tayi, Labaran yayan sakeena yace "Baxa'a basu ba, ko kinmanta duk abunda kikaiwa Sakeena ne har kike xaqewa haka?" Maryam tayi dariya tace "Kyaleta koma miye taiwa Sakeena kanta tayiwa domin ga sakayya nan baro baro ta bayyana, kudi kam xa'a basu sunci arxiqin Sakeena" ta karbi 150k a gurin Abdulfatah ta miqawa Hajjo tace "ga kudin mutum ukun da kikace basanan" ta karba cike da kunya jiki na rawa tana godiya. Sukai shirin tafiya da sunan xasu masauki bayan anyi musayar lambobin waya, wasu kuma yau xasu koma saboda gobe Monday akwai aiki.
Saddiq yabi bayan Abdulfatah kamar yadda ya buqata suka tsaya a waje wani gida dake jikin gidansu wanda ya xama kango saboda ruwan sama daya rusheshi meshi kuma talakane bashi da kudin daxai gyara shine yakeso asiya abashi kudin ya fita wajen gari ya sayi qarami su koma da iyalansa amma kuma duk tayin wulaqanci ake masa ganin ya matsu a siya shiyasa be siyarba har yanxu, sukai maganganu da Saddiq ya bashi lambarsa ya karbi ta Saddiq din sannan suka tafi, Sageer da Sakeena suka dawo cikin gida, Amina tai saurin matsowa ta riqe hannun Sageer tana dariya tace "Sageer naji dadin ganinka" Sakeena tai saurin cire hannun Amina daga jikin Sageer tace "Amina ki kiyayeni wlh haukana yafi naki, karki qara tabamun miji, ki tafi kema ki nemi naki naki mijin, domin wlh Sageer nawane ni kadai yafi qarfinki" Sageer dariyar jin dadi yake wai yau Sakeena ke fada akansa? Lallai mahaqurci mawadaci. Shi kuwa Deni yana tsaye yana mamakin wai yau gashi ga Sakeena amma kamar batasan yana gurinba har take fada akan wani namijin, tabbas ya yadda yanxu bata sonsa kuma tayi xurfi wajen son waninsa. Jiki a sanyaye ya shige dakin Hajjo hannunsa dauke da 50k din da aka basu albarkacin Sakeena. Hajjo ma taja hannun Amina suka shige daki tana shafa damin kudaden hannunta.
Sageer da Sakeena da mutanen Baggadano suka shige dakin Iya, yayin da Baba ya umarci Iya ta kawowa Sageer abincin da akayi dominsu dakinsa. Ta tashi ta hada masa komai takai masa sannan taxo ta fada masa Sakeena tai masa jagora xuwa dakin ta xuxxuba masa ta shammaceshi ta gudu ta barshi wai xataje su gaisa da yan uwanta. Yayi dariya yace "xan kamaki ne, ke sarauniyar son jiki nan da jimawa xakixo ki farabin jikina kina kwanciya" tai masa gwalo tace "Yau dai ajikin Iya xan kwanta" ya sake sosai a dakin Baba kamar gidan ubansa, ya kwashi girkin Iya me dadi da tsafta.
Acan dakin dakin Iya kuwa an kacame cikin hirar yaushe gamo, Iya ta xubo musu abinci suka hadu su duka anaci ana hira cike da nishadi. Sakeena ta jawo akwati ta dunga fitowa da kowa tsarabarsa tana bashi harda Inna da bataxo ba, suka karba cikin yabawa karamcinta suka dunga godiya da qara neman yafiyarta kan rashin kulawar da suka nuna mata a baya.
Haka suka kasance cikin nishadi har xuwa lokacin sallar azahar suka fita sallah harda Sageer suna dawowa sukayi haramar komawa D/Tofa kowa riqe da tsarabar sakeena da kuma 50k din Abdulfatah kudin da mafi yawansu basu taba riqe kamarsu ba, Sadiya ke fadawa Sakeena cewa kiwonta fa yanata Habbaka akuyarta harta haihu yaya biyu, Sakeena tace "Nagode yaya sadiya Allah ya qara habbaka kiwon ammafa inta kama ku dunga yankawa koda kajin ne kunaci" Sadiya ta riqe haba tace "Allah ya sawaqe dan inamiki kiwo sai naci, kuma mu a gidan da nake aure abun kunyane kaci abunda kake kiwo sai ace maka baka da xuciyar tara abun duniya, ko kasawa xaiyi sai dai ka sayarwa mahauta" Sakeena ta riqe haba tana dariya tace "Wani abu dai sai a qauye meye abun kunya cikin cin halak dinka?"
Har kofar gida ta rakosu dukkansu har Sageer da yace xaije gidan abokinsa ya huta xuwa yamma, suka dau hanya tana daga musu hannu. Sageer ya dawo soron yana cewa "Sakeena bakiji ba?" ta juyo tace "Menene?" yayi saurin hada bakinsa da nata, Saddiq ya fito dakinsa yayi karo dasu a wannan halin, yayi gyaran murya yana sosa qeya, Sageer ya dago yace "Au kaine?" ya riqo kunnansa yace "Haba bros yaxakaimun haka? Sallama muke fa ka fito" Saddiq yace "wash tuba nake ya Sageer a sarkarmun kunnan karya tsinke" Sakeena tai musu dariya ta gudu cikin gida.
Dakin Iya ta nufa taje ta jawo qatuwar trolley din data cikowa Iya da kaya ta dire agaban Iya tace "To haj Iya ga taki tsarabar, shaddodin ciki kuma na Baba ne" Iya jiki a sanyaye ta bude akwatin ta ciro galla gallan shaddodi uku na Baba, sannan ta dunga fito da ragowar dinkakkun kayan ciki dasu mayafai ta dubi Sakeena tace "Yanxu Sakeena wannan lefen duk nawane?" tayi dariya tace "kwarai kuwa Hajiya Iya, so nake ki dunga fallewa sosai domin ke yanxu Hajiya ce kin kama qasa kin xama yar gata tunda kika haifi Sakeena" Iya ta share hawaye tace "Sakeenatu maganarki gaskiya ce, gashi kamar wasa maganar tafiyarmu Hajji ta tabbata, ke din diyar arxiqi ce kuma ina alfahari da riqonki, nagode da biyayyar da kikayimun kika gyara rayuwar aurenki, Allah ya baku qara baku xaman lfy da xuria tagari, ko yanxu na mutu burina ya cika na barki hannun da na yadda baxai cutar dake ba, sannan ansamu dangin mahaifiyarki" Sakeena ta share mata hawaye tace "Baxaki mutu yanxu ba Iya sai kin dauki jikokinki in shaa Allah" Iya ta qurawa Sakeena ido tace "Wannan fari da cikar da kikayi sakeena anya na lfy ne? Kodai ciki gareki?" Sakeena tai shiru ta sunkuyar da kai cikin kunya, Iya cikin farin ciki tace "Masha Allah aure yayi albarka, Allah ya rabaku lfy" Sukacigaba da hira da Iya cikin farin ciki har Baba da Saddiq suka shigo suma aka basu tsarabarsu, Baba har kuka yayi ya qara yadda da lamarin ubangiji wai yau shine xashi aikin Hajji adalilin yar marainiyar daya riqe, hmm Allah me iko shiyasa bahaushe yace Da da dukiya ba a qetarsu domin bakasan wanda xaka mora ba, yanxu mutanenmu basa qaunar riqon maraya, sai kaga uba ya mutu ko uwa marayu suna watse abun tausayi babu me tallafa musu ko daukar nauyinsu domin ragewa uwar wahala. Lallai gaskiya ne, alkhairi baya faduwa qasa banxa, ya riqe marainiya da amana da kuma kyakykyawar niyya gashi tun a duniya Allah yayi masa sakamako ga kuma dinbin lada a gobe qiyama. (Allah ka bamu ikon temakawa marayu domin muma bamu da tabbacin xamu rayu da namu yayan)
A dakin Hajjo kuwa ta tasa kudin da aka bata tana ta kallonsu kafin ta magantu "Yanxu Deni da gaske wadannan yan gayun masu kudin yan uwan Sakeena ne?" yaja tsaki yace "Eh mana ga sheda nan kin gani tunda har arxiqinta kin faraci" tayi tagumi tace "To yanxu kuna gani Hafsatu da bata haihu ba zata tafi maka ni kuma da nake daku ko airport ban taba xuwa ba?" ya juyo yana kallonta yace "Au Hajjo baki saduda ba har yanxu? Duk ba ke kika jawo ba, da ace kin haqura kin karbi Sakeena a matsayin matata kin kyautata mata ai da tuni yanxu keda Iya xaku tafi makan tunda agabanki kinji tace asaka uwar mijinta cikin tafiyar, amma haka kawai kika tsanarmun sakeena inason matata kuka hanamu sakewa har saida kuka rabamu" ya fada yana hawaye, Hajjo jiki babu kwari tace "To ai dai bani na sakar maka itaba ko? Kai kasaki abarka da kanka" yace "To waye sila inba keba da wadannan tsinannun yaran? Da tuni yanxu wlh sai dai kiyiwa wani silar arxiqi, domin daga gani Sakeena macece me qashin arxiqi, ina aurarta na samu aiki sannan gashinan shima Sageer din yanxu daga dukkan alamu ya kusa xama hamshaqin me kudi ta dalilinta tunda suna qaunarsa don ya kula da ita sosai" cikin fushi Hajjo tace "Ka daina tsinewa yayana akan lefin da harda kai muka hadu muka aikata, domin da kana qaunarta kaima ai da baka saketa ba"
Ya share hawaye ya miqe xai fita, da sauri tace "To kadan ban wani abu mana cikin naka kudin in riqe a hannuna" ya kalleta yace "Na hannunki kuma fa kiyi me dasu?" tace "Wai dama xan hadasu ne gaba daya in ajiye saboda yiwa Amina kayan daki inta tashi aure" ya bude baki yana duban Hajjo kafin yace "To ni bada niba wannan shirmen, yarinyar da ko kare bata dashi da sunan yana sonta itace xa'ai xancen ajiyawa kudin kayan daki? Saboda haka ko sisi baxan bakiba a ciki, xuwa xanyi insaro kaya inxuba a kantina daya fara ramewa saboda siyan maganin ciwonki, sannan kuma tunda kinsamu kudi ki dunga amfani dasu wajen saiwa kanki abinci da magani, na daina asarar ko kwabo na akan ciwonki tunda naga so kike ki qarar dani gaba daya" kafin Hajjo tai magana Amina ta matso tace "Hajjo ga nawa kudin ki hada dana gurinki akaiwa malam ya qarayin aiki akan aurena da Sageer don wlh ni shi kadai nakeso" Deni yayi tsaki yace "Kinji irin taba? Dama asibitin Dawanau kikaita da kudin aka bata maganin tabin hankali a memakon kayan daki" yasakai yayi ficewarsa waje, Hajjo tasa kuka tana cewa "Yau na shiga uku, shima Denin ya dena tausayina yau da bakinsa ya kira siyamun magani da cewa asarar kudinsa yake, Allah na tuba ka yafemun"
Xuwa yamma Sageer ya dawo suka fita da Sakeena xuwa gidan Alh Dalhatu gurin Hassana wacce ta haihu kwanaki uku baya, sun tarar da Usaina taxo qasar suka kacame da murna dole Sageer ya tafi ya barta don taqi fitowa su tafi, har bayan Isha suna hira sai wajen taran dare yaxo daukarta suka rabu dakyar Sageer ya bata kudi ta bawa Hassana wai a saiwa Baby diaper.
Washegari Monday da wuri sukaje immigration office aka fara yiwa Sakeena passport suka wuce KT ita da Sageer, shi da Umma suna da passport, basu da buqatar sake wani beyi expire ba.
Gida ya cika da dangi yan ganin matar Sageer, suka dunga kallonta suna yabawa ita kuma tana gaishesu cikin girmamawa, da kyar umma ta yakice mutanen suka barsu sukaci abinci, shafa qanwar Sageer kuwa kamar ta goya Sakeena sai nan nan take da ita tare da kiranta Anty Sakeena duk da cewa xata girmewa Sakeenan sosai, Sageer yayiwa Umma duk bayanin yacce akai a Kano, Sakeena ta bata 50k dinta data karba mata, Umma ta dunga kuka da hawaye tana shiwa Sakeena albarka da tayi silar komawarta saudia don sauke farali, a karo na biyu a rayuwarta. Gida ya kuma cika da yan taya murnar xuwan Umma saudia, xuwa yamma aka dan ragu shafa da sageer sukayiwa sakeena rakiya gidan dangi na kusa suka gaisa daganan sukaje gonar Sageer wacce ke hade da gidan gona daga gefe.
Sakeena ta dunga kallon girman gonar tace "Ashe Sageer mugun kudi gareka haka? Wannan uwar gona ai xa a iya noma abincin da xai ishi qaramar hukuma daya a shekara" yana dariya yace "banda sharri baby, ina wani kudi rufin asiri dai" tace "gaskiya garin Katsina yamun kyau sosai ko ina tsaf tsaf" yayi mata dariya yace "Yau yar qauye ta shigo birni xamusha sambatu"
Washegari suka daga Kano harda Umma, kuma aranar passport dinsu ya fito, xuwa dare xasu tafi Abuja a jirgi tacan xasu tashi. Baba yayi amfani da kudin daya samu ya saiwa su Hajjo komai na abinci da abun layya ya barshi a hannun Saddiq kuma ya danqa masa amanar gidan. Har daki Iya ta tasa Sakeena sukaiwa Hajjo sallama, ta dunga kuka tana neman yafiyarsu, sukace aisu sun yafe mata tuntuni.
Qarfe 1 dare suka sauka Abuja guess house din Abdulfatah, shima yaxo sukai shiri cikin sauri ana idar da sallar asuba suka fita screening, ana gama tantancesu sukai airport. Xuwa qarfe biyun rana sun daga qasa me tsarki a jirgin yawo (international) ana saura sati guda ayi arfa kuma sune jirgin qarshe. Sakeena ta kalli cikin jirgin da tsaruwarsa da kuma manyan mutanen dake ciki ta saka kuka tana godewa Allah da ni'imominsa gareta, ta juya ga Sageer tace "Nagode ya Sageer haduwata dakai alkhairi ce a rayuwata, ka sama mini lafiyar ido, ka bani ilimi, sannan a dalilinka na hadu da dangin mamana" yasa hannu ya share mata hawaye yace nine da godiya my queen "Kin rabani da rayuwar bariki, kinyi silar xuwana qasa me tsarki sauke farali sannan kuma gashi xaki haifamun yaya, thank u very much Sakeenatu, ke alkhairice gareni"
********** ******** ******** ****
Sunsha ibada, sunyi aikin hajji an qare lfy sun xama alhaxai, iyayenta sunsha addua sosai da dukkanin al ummar musulmi (Allah ka axurtamu da xiyarar dakinka) sun dawo kuma a Abuja suka sauka, su Sakeena dai Lagos xasu wuce saboda tuni sunkoma makaranta, ta ware tsarabar yan Baggadano ta bawa Iya ta tafi da ita, na yan Katsina kuma ta bawa Umma suka rabu kowa yayi garinsu.
Su Iya dai sun tarar da baqon al amari domin cikin sati 3 da kwana 5 da sukai basanan sun tarar an bige gidan an shigo da kangon jikin gidan an tsantsara musu ginin xamani qaton tsakar gida da toilet sai kicin, part din Iya falo babba wanda yasha kayan alatun xamani da kujeru sai bedrooms biyu kowanne da toilet ciki kuma da furnitures, sai kicin madaidaici dauke da kayan kicin, sada lalulayen dakin Iya abun kallo ne. Dakin Hajjo ma taci arxiqin Iya anmata qaton falo da 1 bedroom da toilet ciki. Baba ma ya samu room nd parlour da toilet aciki daga tsakar gida har xuwa soro an lailayeshi da tiles. Sai dakin Saddiq na soro shima da aka gyareshi akai masa toilet a ciki.
Iya da Baba suka tsaya suna mamaki Baba yace "Saddiqu gidanne kuwa mu shigo, ya dire kayansu a tsakar gida ya budewa kowa dakinsa yana dariya yace "Ku shigo mana Baba, aikin Baban Sakeena ne Abdulfatah tun ranar da yaxo ya siya gidan mal Bukar daya rushe da daraja sosai, shine bayan tafiyarku aikin ya tashi." suka shiga dakunansu kowa yana mamaki, Iya cewa take wannan duk dakina ne kamar na amarya. Saddiq yana dariya yace "Akwai wani abun mamakinma kudai ku huta gajiya tukun"
Washegarin xuwansu Iya ta bude tsaraba ta bawa kowa tasa harsu Hajjo da mutan unguwa, aka dunga shigowa ganin gida da kuma godiyar tsaraba. A ranar Saddiq ya samo musu napep suka hau xuwa wata unguwa a gabansu kadan, ya bude wani guri ga mamakinsu gidan gona ne shaqe da kaji da kuma tanki na kifi qato guda biyu. Yana murmushi yace "Baba ga muqullin gidan gonarka inji Abdulfatah kamar yadda sakeena ta buqata asamar maka hanyar shigowar kudi shine ya nemi shawarata ni kuma nace a bude maka gidan gona saboda yana kawo kudi, kuma lokacin wannan gurin ya shigo anaso asiyar, nakai masa ya siya ya xuba maka kaji masu kwai da marasa kwai da kuma kifi" Baba yayi xukudi yana duban Saddiq yace "Anya kuwa ba muyi rashin hankali ba Saddiqu hidimar tayi yawa" yace "Kawai kayi fatan alkhairi Baba, mai jinin arxiqin ka riqe shiyasa lokaci daya gidanka ya cika da arxiqi" ya jinjina cikin yadda da maganar Saddiq ya juya ga Iya yace "Hafsatu kinga aikin Alh Abdulfatah ko?" tace "Nagani malam, Allah yayi musu sakayya da gidan aljanna, sai a buga waya ayi musu godiya" yace "A a Haj Hafsatu, wani kiran ai yafi gaban gani, takawa zamuyi muje har can Lagos din muyi musu godiya" Saddiq yana nuna musu gurin yake cewa "Baba kafa haye kwananan xa a fara saka sahun masu kudin unguwarmu"
Acan Lagos kuwa suna sauka Bilki ta aiko musu da abinci xuwa yamma sun huta ta ware tsarabarta ita da Haidar da Maitama takai musu sukasha hira tana cewa Haj Sakeena daga xuwa ganin gida kuma sai mukaji tafiya saudia. Ta dakko mata xancen salon dinta da tace anxuba masu aiki kuma yare saboda ya samu karbuwa domin in ankasa hausawa xamu samu taxgaro gurin samun customers xasuyi mana qabilanci. Ta bawa Sakeena cinikin da akai a rubuce da kuma sunayan yaran dake aiki a shagon tare da albashin tayi alqawarin xata basu. Sakeena tayi godiya ta warewa Bilki nata kason da xata dunga bata duk wata. Bilki ta dunga godiyar tsaraba da kuma wannan kaso da sakeena ta ware mata.
Bata manta da su Hassana ba duk da tasamu duniya domin suna cikin mutanen da har ta mutu baxata manta da alherinsu ba, har gidan kakanninta takai Hassana aka karbeta hannu bibbiyu kamar su goyata jin labarin alherin da family dinsu sukaiwa Sakeena. Itama ta samu alheri gurinsu sosai.
Ta koma makaranta a washegari, tsarabar yan uwanta kuwa Mama ta kaiwa ta raba musu, sun fara karatu babu wasa kuma result dinsu na level 100 ya fito kamar yadda taiwa Sageer alqawari ta watsar da matan ajinsu, ta xama ta farko, kuma ta 5 a cikin ajin gaba daya, wannan dalili yasa taga gaba daya matan ajin sun canja mata sun daina kulata, itama ta tattarasu ta watsar take harkarta ita kadai.
Sati guda da dawowarsu suka tashi da baquncin Baba, Iya harda Saddiq sunxo godiya kamar yadda sukace, ranar tayi murna da farin ciki mara iyaka, lokacin Inna ta dawo itace ta dunga jigilar girke girke. Sakeena taiwa Mama waya ta fada mata xuwansu Iya, Mama tace Dan Allah suxo gaba daya suyi dinner dasu da daddare. Xuwa yamma sun huta dake saukar safe sukayi. Aka xauna hira anan Saddiq yake fada mata wai shifa Maryam yakeso. Sakeena ta dubeshi anutse tace "Anya kuwa Saddiq soyayyarku xatayi tsaho? Saboda banbancin yarenku sannan kuma Hajjo baxataso ka auri qabila ba" ya marairaice yace "Haba Sakeena karki sacemun gwuiwa mana, soyayya ai batasan banbancin yare ba, wlh ban taba ganin macen da nake qauna ba kamar Maryam kuma nayi nasarar samun xuciyarta yanxu manya kawai mukeso su shiga maganar" Sakeena ta bude baki cikin mamakin jin wai sun dai daita da maryam to aina suka hadu har suka qullah soyayyar?" ya bude wayarsa yana nuna mata chats dinsu da ita da kuma hotunan maryam da suka cika wayarsa jiki a sanyaye tace "To Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina" ita dai tana ganin akwai gagurumar rigima agaba irin ta aurenta da Deni saboda sanin halin Hajjo da kuma tsanar da dangin Mama sukaiwa Hajjo saboda jin abunda taiwa Sakeena.
Da daddare suka cakare har su Bilki sakeena ta gayyata sukaiwa gidan kakanninta tsinke. An hadu an gaiggaisa Baba yayi godiyar data kawoshi tare da yiwa xuriar adduoin alkhairi. Aka hadu a qaton table anayin dinner bakajin qarar komi sai cokula da wuqaqe Iya da Baba dai Sakeena ce ta koya musu yacce ake riqe wuqa da fork anacin abinci. Wajejen goman dare Sakeena ta buqaci su Iya su taso su tafi amma Mama ta hana tace anan xasu sauka gasunan da dakuna burjik da akai domin baqi yaushe xasu bita gidanta. Tace to Saddiq ya taso su wuce shima yaqi tashi suna satar kallon juna shida maryam da taxo hutu ya rage murya yace da Sakeena "Barni infara kafa gwamnatina gurin in laws dina tun daga yanxu"
Suka tafi ita da Sageer tana xunbura baki wai mama ta hana su Iya biyota, Sageer ya dunga yimata magana taqi amsawa yasa hannu yana mata cakulkuli ta fara dariya tana cewa "Wlh xakasa inma futsari a mota" kafin suje gida ya shawo kanta sunata hirarsu cikin soyayya.
Su Iya dai da sukaxoyin kwana biyu saida suka kwana 5 sannan dakyar mama ta bari sukai haramar tafiya akai musu sha tara ta arxiqi, xuwa lokacin sun daina mamakin dangin Mama in sunyi abu, saboda ganin gida da rayuwar jin dadin da suke ciki, Saddiq jikinsa ya fara sanyi yaganin anya Maryam batafi qarfinsa ba kuwa? Gashi Allah ya jarrabeshi da santa.
******* ****** ******* ******** ***
Haka rayuwa tacigaba da garawa Sakeena da Sageer suna soyayyarsu me shiga rai, sannan tana sana'arta bata fasa komai ba ga kuma karatunta ta qara xage dantse data fuskanci ana mata baqin ciki komai yana gara mata da temakon addua. Yawanci duk weekend suke xuwa can family house gurin su Mama Abdulfatah yanason Sakeena sosai xuwa yanxu ta mallaki kadarori da yawa ta dalilinsa. Acikin hakan Saddiq ya tafi training din aikin custom yayin da Maryam tai graduation ta dawo gida suka kuma dinkewa da Sakeena. Bata fasa alherin da takewa su Umma ba wacce sukaxo last month ita da shafa sukaga yan uwan Sakeena kuma suma anmusu alheri me yawa.
Sunyi jarrabawar first semester sun gama suka samu hutun kwana tara kacal, a lokacin ta fara xuwa awo cikinta 5 months scanning dinta na ranar ya tabbatar da twins ne a cikinta, ta dunga Hamdala tana qarawa domin da kanta ta roqi haihuwar yan biyu a dakin Allah kuma gashi ya amsa mata. Sageer ma yayi murna amma kuma sai yakega kamar Sakeena tayi qanqanta baxata iya haihuwar yaya biyu ba, tun a lokacin ya fara tausayinta kuma ya qudure baxata haihu a qasarnan ba, haba gaskiya mana shiyasa cikin yayi wani irin mugun girma ashe mutum biyu ne a ciki.
Daga ita harshi sukaja bakinsu sukai shiru basu fadawa kowa yan biyu xata haifa ba, ya qara bata kulawa sosai kusan komai shiyake mata duk da tana yawan fada masa lfyarta qalau, shikam tausayinta yakeji. Tafiya ta kamashi xuwa jahar Ekiti xiyarar aiki, baison tafiya ya barta ita kadai yace ta koma can gurin Mama ko Maryam taxo su xauna, ta tubure ita Kano xata gurin Iya itace ta kusan wata uku bata ganta ba amma mama kullum suna tare ai, yaqi yadda da tafiyarta Kano tasa masa kuka babu shiri ya yanko mata ticket ya kaita airport ta tafi a ranar yayiwa Saddiq dake aikin custom a Kano waya yaje daukarta a airport, saida ya tabbatar da xuwanta sannan ya samu kwanciyar hankalin yin tasa tafiyar a ransa yana cewa "Sakeenatu danger"
[8/21, 11:52 AM] Zongo Gal: 🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
🙆🏽♀MUQADDARI NE🙆🏽♀
🙆🏽♀2018🙆🏽♀
🙆🏽♀
3⃣0⃣ (part B)
RAHMATULLAH (Hajia)
Iya tana ganin Sakeena ta shigo da qaton ciki ta fara salati tana cewa "Yanxu Sakeena da wannan qaton cikin kika keto haxo kika taho dan tsabar kuruciya? Wannan ai kin kusa haihuwa, cikin nan naki bakuyi lissafi dai dai ba domin ko yanxu kina iya haihuwa" ta samu guri ta xauna tana cewa "Iya hutu nasamu kuma shima tafiya ta kamashi xuwa Ekiti shine nace inaso inxo in ganki, kuma wlh wata biyar ne cikin ko wannan satin mun kumayin scanning" ta qurawa sakeena ido tana cewa "To ni Hasfatu wane irin ciki ne wannan gaba daya ya cika duniya a wata biyar? Allah ya rabaku lfy"
Ta yini kwance tana baccinta cikin gata da soyayyar Iya da Baba harda yar karoro Hajjo, da daddare ana koda xafi aka tada inji aka saka tabarma a tsakar gida aka xaxxauna, aka fito da qatuwar fankar qasa aka jona ta cika gurin da iska. Iya tayi tuwon dawa da miyar kobewa busashshiya da sakeena tace tana so, yaji naman kajin gidan gonar Baba da yajin daddawa kowa yaci yana santi. Yau dai harda Deni a wannan xaman kan tabarma da kuma zahara wacce taxo ta yini yau sur tana jiran mijinta yaxo daukarta su tafi, kuma Sakeena ta sake tana hidimarta kamar batasan da wata halitta wai ita Deni ba a gurin. Sakeena ta kalli Baba tace "Baba nayi missing wannan xaman sosai, ina yawan tunashi kuma duk sanda na tuna sai naji inama har yanxu ina attending dinsa. Baba yace "Allah sarki sakeenatu ai babu komi aurene ya kaiki can din kuma dama shi babu inda baya kai mutum, ki godewa Allah kinyi arxiqi mijinki yana da imani kuma yana qaunarki" Saddiq yayi karaf yace "kwarai kuwa nima shedane Baba, domin yanxu ma tashi xanyi in siyo mata ice cream din da yace kullum sai tasha kafin ta kwanta kuma yace in kula da ita sosai asamar mata da duk abunda takeso" Iya tai tsaki tace "Ai nikam Allah Sageeru bemun dai dai ba daya bari ta taho da wannan uban ciki haka" Saddiq ya katseta yace "To ai rigima tasa wai saitaxo ta ganki harda kuka shine ya barta ta taho kisan sarauniya ce ba a son bacin ranta"
Wannan magana ta Saddiq kamar da gayya yake yinta saboda Deni wanda yaketa kallon sakeena da qaton cikinta yana qissima girman asarar da yayi, wai shin wane tsautsayine yasashi sakin Sakeena ne?
Sakeena ta tarar da Hadixa taxo kuma wai ta dade a gida kamar yacce Iya ke fada mata wai mijin ne ya sameta da ciki duk da kwayar planning da yake bata Allah yayi ikonsa ta dau ciki kuma bai farga da cikin ba sai da yayi wata biyar, ya dauketa yakai asibiti da nufin acire cikin amma akai allurai da magunguna yaqi fita, qarshe likitan ya shawarce shi daya haqura in aka takura sai an cire xata iya rasa ranta, ganin haka Yusuf ya rubuta mata takaddar saki 3 cis ya hadota da rubabbun kayan dakinta a fadarsa tare da kashedin ta nemarwa dan cikinta uba domin shi baxai haihu da itaba ta haifa masa irin Hajjo annoba. Sakeena ta qara kai dubanta ga Hadixa wacce tai wata iriyar qaxamar rama tsufa duk ya kunno mata, fuskarta har ta karkace saboda rama, tayi wani mugun sanyi kamar ba yar tawaye Hadixa ba. Kuma wai a hakanma Iya tace tayi kyau saboda ta samu cimar abinci me gina jiki domin lokacin data dawo ko numfashi dakyar takeyi saboda wahalar alluran da Yusuf yasa akai mata don xubar da ciki, ta xubar da jini abanxa kuma cikin be fita ba saima qara girma da yayi yana rinjayar Hadixan.
Ita kuwa Fiddausi har yanxu tana can qarqashin mulkin Hajiya har yanxu asirin bai saketa ba. A gefe guda kuma Amina ta dan nutsu harta fara xuwa makaranta koyon dinki da Baba yasakata tunda babu brain din karatu, kodai Hajjo ta bi shawarar Deni ne ta karbawa Amina maganin tabin hankali a asibitin Dawanau? 🤔
Sakeena ta nisa bayan gama wannan dan guntun tunanin, ta miqe qafarta Baba yayi saurin saka mata filo a bayanta ta kashingida tace "Iya gobe dai alalan gwangwani xaki min da manja da yaji" kafin Iya tai magana Hajjo tai karaf tace "Haj Sakeena ai koni sai in miki don dai alala?" daga Sakeena har Iya sukayi mata shiru. Zahara tace "Sha kuruminki Anty Sakeena na hutar da Iya in shaa Allah gobe xan kawo miki" tana murmushi tace "To Anty Zahara nagode sosai" har xuwa 9 na dare suna hira kafin Baba ya kori Deni gidansa, Zahara kuma mijinta yaxo suka tafi. Hadixa dai har aka tashi kallon sakeena take cike da sha'awa ganin kowa yana nan nan da ita da abunda ke cikinta, ita kuwa gata ta xama mujiya kamar wacce tai cikin shege sannan matan unguwar gulmarta suke wai mijinta ya saka mata ciwon qanjamau ya korota da ciki.
Washegari wajen azahar saiga alala samira guda Zahara ta aiko da ita, Sakeena taci harta ture tanawa Zahara addua, ta aika kantin Deni a siyo mata lemon Vinto sai gashi da kansa ya xubo guda 6 a leda ya kawo mata, taqi karba tace baxata karyashi ba ya bata na kudinta kawai, ya xauna kofar dakin Iya duk yayi wani dugujunjun babu wannan gayun da tsafta, ya dunga roqon Sakeena ta karbi lemon tafi qarfin komi a gurinsa, harda Hajjo asaka bakin ta karba, saida Iya tasa baki sannan ta karba tayi godiya, shima godiyar yake yana murna sakeena ta karbi abunsa.
Kwananta biyu da xuwa ta nufi Baggadano Saddiq ya kaita a qaramar motar Baba daya siya yake jigilar diban kwai yana rabawa masu siya da ita. Iya bataso taje ba saboda cikinta da kuma kumburin da qafarta keyi, amma Baba yasa baki ta barta, tayi mamakin ganin an gyare musu gidansu tsaf anyi ginin xamani ya qara girma, sunyi murnar ganinta kamar su goyata, aka dafa mata gujjiya da makani da take ta kwadayi taci ta more, taji dadin ganin yan uwanta kowa ya kama qasa ya dogara da kansa bisa tallafin Daddy (Abdulfatah) kwananta daya ta juyo da tsaraba niqi niqi da suka hada mata ita dasu Mama sukace ta kai musu.
Ranar data cika kwana 5 Sageer ya dira a garin ya gama aikin daya kaishi Ekiti kuma ya biyo tafiya da sakeena. Yana sauka yace ta hado shirginta su tafi, tana xunbura bakin hutun be isheta ba ta hada kaf suka tafi bayan Iya ta qara bata kayan miya nata danasu Mama. Saddiq ne ya kaisu airport suka tafi. Suna xaune a jirgi Sageer ya shafo hannunta yace "Muje gida in maki tausa kinji baby na dade ban tausheki ba" tana hararsa tace "Ba wani tausa ka riqe abarka nagode wayo xakaimin kaita dannemun cikin nan kai ko tausayina bakaji" yaja hancinta yana dariya yace "sry Baby ina tausayinki mana, ke dince kin hadu jollof rice ce ke komai yaji shiyasa bani da haquri akanki"
Sun koma makaranta rayuwa tacigaba xuwa yanxu ta bunqasa manyan kudade take riqewa ta bangaren business dinta wanda ya qara kafuwa saboda tagomashin su Mama yanxu kam kunun aya, ginger da tamarind sari take bayarwa ga masu kantina saboda anmata NAFDAC number.
Cikinta yayi wani irin mugun girma dakyar take xama da tashi, ganin haka yasa Sageer ya shawarceta data jingine semester din, amma fur taqi tace bata da burin daya wuce kammala karatu yanxu dan haka xata jure ta gama semester din bayan haka kuma bata aikin komi kuma batajin ciwon komi. Watan haihuwarta ya tsaya lokacin suna exam har EDD dinta ya xarta tai wani irin qazamin kumburi tuni shirye shiryen tafiyarsu Egypt ya kammala inda Sageer ya shirya xuwanta haihuwa. A makarantarma kowa tausaya mata yake da mamakin qarfin halinta na jure karatu da wannan abun ciki
Ranar data kammala jarrabawar level 200 da daddare suka daga xuwa Egypt din ita da Iya da kuma Maryam wacce ace ake tsaka da rigimar aurenta da Saddiq. A asibiti suka sauka wanda yake kamar gida kuma atake aka karbi sakeena aka fara bata kulawar data dace ganin ta xarta date din haihuwarta. Cikin ikon Allah kwanansu uku da xuwa ta haihu da taimakon kwararrun likitoci da suka tsaya tsayin daka akanta da temakawa harta haifi yayanta biyu maxa santala santala masu kama da Sageer sak sai farar fatar sakeena da suka debo, daganin girmansu kasan sunci dadi aciki.
Daga Sakeena har jariran suna cikin kulawar doctors komai suke musu, acan 9ja kuwa murna ba a magana, gurin dangi da uban twins, Umma sai sadaka take tana murnar wai yau Sageer ne da yaya har biyu, Allah me iko. A daddafe Sageer ya kai ranar suna a 9ja, ya matsu yaje yaga matarsa da yayansa duk da kullum cikin turo masa vedion su maryam take. Ya salami umma dasu mama masu suna babu yaya da me jego. Ya radawa yayan suna ABDALLAH da ABBAKAR wato babansa da baban sakeena.
Ya sauka a Egypt cikin dare ya dauki yayansa masu matuqar kama dashi ya dunga sumbatarsu ya fada musu sunan daya rada musu, sunyi farin cikin jin hakan suka fara kiransu da Saddiq da Abdul. Ya koma gurin Sakeena wacce tai tsaf kamar bata haihu ba ya rungumeta yana sumbatarta.
Kwanansa 10 acan ya dawo bayan ya kama musu gida qarami ya biya kudade da yawa don su xauna har hutun su Sakeena na qare na school kafin nan yaransa sunyi kwari kar suje dasu 9ja yanxu ayita daukarsu.
Sunyi xamansu na jin dadi su uku, Maryam, Iya da Sakeena har xuwa lokacin da Mama taxo kuma ta duqufa yiwa sakeena jego irin na yarensu. Sun dawo 9ja lokacin Saddiq da Abdul sunada wata 2 da yan kwanaki. Masu raino biyu Sageer ya dauka mata, ta koma school an shiga level 300 karatu ya fara xafi kuma har yanxu ita ke riqe da kanbun mace ta farko a department dinsu wanda hakan ya qara mata baqin jini a gurin wawaye masu fushi da yin Allah. Karatu take babu wasa cike dason cimma buri, bata xuwa da yayan makaranta a gida take barsu gurin masu raino qarqashin jagorancin Inna ana basu madara inta dawo kuma susha nono. Salon dinta ya qara habbaka sosai yasamu karbuwa gurin yan gayun Lagos.
Tana samun hutun first semester suka nufi Kano ita da Sageer lokacin har su Abdul sun fara rarrafe. Ranar taga soyayya gurin mutane aka yanyameta kowa nason daukar yayan. Xuwa yamma mutane suka dan sarara Baba ya shiga ya debo yaran duka biyu a hannunsa sunata tsalle jikinsa cike da qoshin lfy, ya fito dasu tsakar gida. Deni yana alwala yayi saurin tasowa ya jikinsa na rawa yace "Baba dan Allah bani su in daukesu, tun daxu nakeson daukarsu wlh" cikin tausayi Baba ya miqa masa su. Ya rungumesu tsam yana shafar kansu. Hajjo dake yanka salad ta taso itama tace "Kawosu in shafi tabarraki Deni, yan biyu kyautar Allah, wadannan yaya dakyau suke" Baba yana dariya yace "Abbakar da Abdallah jikokin haj Hafsatu kenan" ya karbesu daga hannunta ya shige daki, Hajjo tai xukudi tana kallon Deni tace "Kaga ya karbesu memakon ya bar mana mugama ganinsu" Deni yayi murmushin takaici yace "Duk wa ya jawo Hajjo? Da tuni wadannan kyawawan yaran jikokinki ne babu wanda ya isa ya rabaki dasu, gashi yanxu ni haihuwarma ta gagareni inaji ina gani Surayya taqi yadda ta haihu kuma ban isa inyi komai akaiba" ya share hawaye ya fita. Itama ta koma daki ta xauna jabar kusa da Hadixa wacce ta haihu watannin baya amma dan babu rai, kuma daga ita har Amina har yanxu babu manemin aure, wata irin nadama ta kuma sarqar Hajjo, itadai tana qaunar yan biyu a rayuwarta kuma ta bakin Deni da batai abunda tayi ba da tuni wadannan yayan yanxu jikokinta ne.
Satinsu guda a Kano sukai haramar tafiya katsina kuma daga can xasu wuce Lagos. Sun fito soro suna riqe da yayan ita Abdul Sageer kuma Saddiq sukayi clashing da Deni ya tsaya gabansu kyam yana kallonsu kafin hawaye su wanke masa fuska cikin kuka yace "Sageer, Sakeena dan Allah ku yafemun abunda nayi muku" sukai shiru suna kallon juna can kamar baxasuyi magana ba, Sageer ya dafa kafadarsa yace "Dena kuka Nura, mun yafe maka, nima ka yafen abunda nasa akai maka" yayi saurin cewa "Bakaimun komai ba Sageer hukunci kawai kaimun kan ta'asar da nake shirin yimaka na rabaka da nagartacciyar mace irin Sakeena, kuma nayafe maka wlh. Ya dubi sakeena yace baxaki iya yafemun ba ko Sakeena?" tana murmushi tace "Na yafe maka yaya Deni, kuma har yanxu kananan a matsayin yayana" Sageer yace "Yawwa Nura ka turon CV dinka ta gmail dina mu duba koda inda xa a sama maka ka nemi abinci" ya bashi gmail din, ya dunga godiya kamar xai kwanta musu.
A katsina ma dai sunga gata, sakeena batasan Sageer dan dangi bane sai ranar suka hada mata kayan barka fago guda, can dai kwanansu 10 cif umma ta riqesu tana manne da jikokinta, sakeena saita yini bata gansu ba, domin Umma ta fara basu abinci.
Sun dawo Lagos anjuya fafutukar rayuwa, kuma lokacin ne akai bikin Saddiq da Maryam bayan doguwar turjiya daga dangin Maryam din qarshe suka haqura ganin tana shirin kashe kanta akan Saddiq. Ansha biki kuma ta tare a Kano Jan bulo inda Saddiq ya tamfatsa gida domin yana samu sosai saboda ya riqe gaskiya. Hajjo dai babu yacce ta iya domin har akai auren aka gama ko tari bataiba balle ta hana yo koda ta hanama hanin baxai tasiri ba tunda duniya ta juya mata baya. Allah sarki sai saka albarka ma take, ta gama tsorata da lamarin ubangiji ganin tanaqin Sakeena wacce uwartace kawai yare, sai gashi danta ya auro yare gaba da baya wacce bata iya maganar awa daya da hausa bata saka yare aciki ba. Sun fara rayuwarsu me dadi cike da soyayya tasamu Saddiq fiye da yadda ta xata yana sonta da kyautata mata, tuni aka samar mata aikin lecturing a Kano poly tana fita aikinta shima ya fita nasa. Wata goma cur maryam ta haifewa Saddiq ya mace me kama da Sakeena sak kowa saiya fadi kamarsu da sakeena, ranar suna taci sunan Aisha babar Sakeena. Kowa yaji dadin wannan kara da Saddiq yayi, sakeena akwati guda ta hadowa Maamaa kamar yacce suke kiranta. Abdulfatah shiya dauki nauyin komai na haihuwar saboda sunan Aisha da Saddiq ya saka. Yan uwan Maryam sunxo rankatakaf kuma sukai bikin suna irin nasu a gidan maryam ita kuma Hajjo tai nata a gwale ita da Iya da yan uwanta. Sun sake sosai kuma sun rage gabar da suke yiwa Hajjo saboda ganin kyautatawar da Saddiq kewa yarsu sannan sun yadda da ba kowane bahaushe bane baya riqon aure tunda sunga xahiri akan Sageer da Saddiq.
Sakeena ta tarar da Fiddausi a gida itama dakyar aka kubutar da ita a qangin bautar Hajiya aka kashe auren, duk su uku suna jibge dakin uwar suna xaman kashe wando babu Sana'a babu aure, ta tausaya musu ta basu 50k kowacce tace suja jari su daina xaman banxa. Abun mamaki da tausayi har qasa suka sunkuya suna mata godiya harda kuka. Tace musu babu komai haqqinta ne ta taimaka musu kodan darajar Baba.
Bangaren Deni kuwa Sageer ya sama masa aiki a wani bank kamar yadda yayi alqawari, hannu biyu ya riqe aikin kuma be saki harkar kantinsa ba yasa amintaccen yaro yake xamar masa a ranakun aiki, weekend kuma ya xauna da kansa. Bai fadawa Surayya ya samu aiki ba sai dayayi 3 months lokacin kudinsa ya fito ya kama hayar gida ya tattara komatsansa ya koma sai lokacin ya fadamata intana iya cigaba da xama dashi ta biyoshi, in kuma bataso hanya a bude take taje gidansu Allah ya hada kowa da rabonsa, domin yabar xama qarqashinta shima yanxu ya samu aiki. Ai babu shiri ta bishi sukacigaba da xama a qaramin gidan daya kama me dakuna biyu da falo a tsakiya. Dole ta dan rage wani iskancin tunda yanxu ya xama najimi ya fara riqe kudi.
Haj Sakeena angama jamia da degree me daraja ta farko kuma lokacin Sageer ya samu qarin girma ya xama controller a aikinsu na custom amma ya koma garin Abuja da aiki, yayin shima Maitama yasamu matsayi irin na Sageer amma shi yana Lagos. Dagani kasan basuyi dadewar da xa a basu wannan matsayi ba a aikin kawai dai dan sunada uwa a bakin murhu ne (Abdulfatah) lokacin komawarsu Abuja yayi dai dai da tafiyarta service kuma aka tura Abuja kamar yadda ta nema.
Suka tattara suka koma Abuja suka rabu da Lagos cikin kewa, Umman Sageer tafi kowa murnar komawarsu Abuja tayo waya tana cewa "Aikam yanxu na baku su Abdul dama saboda karsu tashi a wannan barikin garin (Lagos) na kwashesu, ni tarbiyyar gurin batamun ba, in kun koma Abujan kun nutsu ka turo mota a kwashemu ni dasu" ita da Sageer dai dariya suke mata domin tun daga yaye ta riqe su Abdul, Sageer yayi nacin duniya ta basu su ta hana har cewa yayi xai sasu makaranta, tace xata sakasu a katsina, ashe ita xaman Lagos ne bataso suyi. Sakeena ta barwa Bilki amanar Salon sannan ta bar mata cinikin su kunun aya ya dawo nata. Maitama yana musu tsiyar cewa sun fiya son kudi, duk da sun xama matan manya baxasu dena neman kudi ba
Acan Abuja ma bata xauna ba ta baxa neman kudi,tayi camping kuma akai posting dinta NTA Abuja don yin primary assignment dinta, suna ganin jamiar data fito da kuma yanayin turancinta suka bata me karanta labarai
Ranar da aka fara haskata tana karato labarai tasha kuka ita da masoyanta da sukasan burinta, Sageer yayi recording daukar ya turawa Baba ta watsap shi kuma ya nuna Iya da sauran mutan gidan, shi kansa yayi kuka lokacin daya ganta cikin shigar mutunci ta yan Arewa wato xani da riga na atamfa da babban mayafi akanta da glasses a ido tana karanto labarai cikin turanci me tsafta ga sunanta nan a qasa baro baro SAKEENA ABBAKAR LIMAN. Amina jikinta yayi sanyi qalau data tuna lokacin da takecewa sakeena me kwakwalwar kifi da kuma gorin datayi mata lokacin da tace tanason xama me karanta lbarai. Lallai duk wanda ka raina kake ganin ba komi bane watarana sai ya xama wani abu.
A ranar Baba da Iya yini sukai suna nunawa mutane videon sakeena na karanta labarai, Deni daya gani a wayar Iya ya jinjina kai yace "Sakeena xata iya abunda yafi haka domin yar baiwace, kuma ta girma da abun a ranta"
Acan Abuja tana fitowa dakin karanta labarai aka hau tafa mata wai tayi namijin qoqari bata kallon camera kamar kwararriya. Idonta cike da kwallah ta nufi mijinta controller Sageer ta fada jikinsa tace "Ya Sageer ina sonka, tunda Allah ya hadani dakai wahalata ta qare a rayuwa, Allah yacigaba da bamu xaman lfy me aminci" shima yace "Amin, kuma nima ina sonki sakeenatu"
Yasa hannu ya sabeta anata kallonsu wasu har photo suke musu, yayi cikin mota da ita suka nufi gida. Anqawata farabar gidan da decoration me kyau an taru sosai sai kida ke tashi. Ta kofar baya suka shiga Sageer yasata cikin sauri tayi wanka tasa wata gown fara qal tayi kwalliya taqaitacciya shima yasa farin yadi dinkin taxarce da hula suka fito harabar gidan inda tayi mamakin jin wai Birthday dinta ake na cika shekaru 24 a duniya. Tana fitowa Abdul da Saddiq suka taho da gudu suka daneta suna kiran Mamanmu oyoyo, sunyi fes sun qara girma kamarsu daya sak inba mugun sani kai musu ba baxaka banbancesu ba suna sanye da irin yadin jikin Sageer suma harsa hula. Ta sunkuya ta rungumesu tsam tana sumbatarsu cike da soyayya tace yaushe kukaxo? suka nuna mata Umma sukace "Daxu da safe a jirgi mu da Umma" Sakeena ta matsa ta gaishe da Umma, ta amsa cike da farinciki tana shafa kan Sakeena tare da saka albarka a shekarunta na 24.
Haka ta dunga xagawa tana gaida mutanen gurin wanda yawanci family dinta ne sai friends din Sageer. Aka fara gudanar da abunda aka tsara, suna xaune a gurin da aka qayata ita da Sageer da yaronsu anatayi musu photo gwanin shaawa, MC ya kirata yanka cake ta dauki Saddiq Sageer ya dau Abdul sukaje suka riqe hannunta ta yanka ta sassaka musu a baki suma suka bata, anata yimusu photo sun burge mutane da yawa a gurin tana kwance jikinsa da mic a hannunta tace "Allah ya saka maka da alkhairi ya Sageer, Allah ya albarkaci yayanmu da dukkanin yayan alummar musulmi ya shiryesu irin shiriyar addinin musulunci" Mutanen gurin da MC suka Amsa da "Ameeen Mrs Muhammad Sageer"
Yakau da mic din hannunta ya rada mata "Naga kinyi fam dake kamar ana buga miki iska, kodai munsamu qaruwa ne?" tayi masa farr da ido tace "Xauna wasa yaro kwananan xakaji haihuwa" yaja hancinta yace "Allah matar arxiqi? Haka nikeson ji tuntuni kika tsaya kinamun wayo da sunan karatu kikeso ki qarasa"
ALHAMDULILLAH. Nagodewa Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa, ina fatan wadanda suka karanta xasuyi koyi da kyawawan darusan dake ciki, mu kuma guji ragowar, domin ansakasu ne don fadakarwa.
Sai mun hadu awani sabon littafin nawa in Allah ya bani iko a 2019 in shaa Allah.
Hajia tanawa baki daya Al ummar musulmai a fadin duniya BARKA DA SALLAH, dafatan xa aci nama lfy, kuma ina jiran Barka da Sallah da kuma Sallah Meat dina gurin duk wanda ya karanta wannan page din 😜(Lol)
Hajia 😊
*_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
0 Comments