MIJINA SIRRINA
[7/4, 5:13 AM]
El-hajj
_©HASKE
WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*MIJINA SIRRINA.....!*🌹
_(Labarin K'auna)_
**Based on a true life story**
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Alh .I. Uba family_
*_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN
K'AI,Rabbishrahli sadri, wa yassirli amri, yafqahu
qauli.._*
_Shafin farko nakine pherty b~b.._
*1*
~~~ "Oyoyo yaya kabeer...,oyoyo yaya kabeer.."
Wannan shine ihun da yaran dake zaune cikin
tsakar gida suna wasa suketa faman yi daidai
lokacin da suka ga shigowar matashin saurayin
wanda ke sanye cikin farar shadda kansa babu
hula sai yar kyakkyawar suma da ya dan ajiye,
Fuskarshi dauke da murmushi ya rungume yaran
wadanda akalla zasu kai su kimanin guda hudu,
Daga inda take acikin kitchen ta sake lab'ewa
saboda bata son ya ganta duk da sanin cewar
dominta yazo gidan, sadadawa tayi ta buya a
bayan fridge gamida leka kanta ta window ta
yadda tasan bazai iya hangota ba,
Ganinshi tayi rike da hannun Amira da waleeda
kannenta sannan ga amir da husna atsaye sai
faman jajja masa riga suke suna tsalle,manyan
chocolate samfarin coconut chocolate ya debo
daga cikin aljihunsa ya mimmikawa yaran,
Sunkuyawa yayi wurin Amira saboda itace babba
tafi su husna wayo,
"Amira ina mama?"
"Tana falon abba?"
"Yaya NADIYA fa?"
"Tana kitchen mama tasata aiki.."
Murmushi yayi ya mike saboda yasan aduk inda
take taji shigowarsa shiyasa ta gudu ta buya,
Yana rikeda hannun su Amira ya bi hanyar da
zata sadashi da falon Abba,
Sai da ya tsaya yayi sallama mama ta amsa ta
bashi izini sannan yasaka kai ya shiga cikin
falon,
Mama yasamu zaune kusa da abba suna yin
hira gefe daya kuma kwanukan abincine da
abban yaci kasancewar bai jima da dawowa
daga wurin aiki ba,
Su walida da amira na biye dashi har cikin falon
sai da suka rakashi ciki sannan suka ruga da
gudu suka fita,wuri yasamu ya zauna kanshi a
kasa saboda kunya da kuma girmamawa,
Ganinsa yasa abba sakin fara,a tareda mikewa
daga kishingiden da yake ya gyara zamansa
yana murmushi,
"Kabeeru yanzu kake tafe? Barka da zuwa.."
Cikin jin kunya da sose sosen keya kabeer ya
daga ido ya kalli Abba,
"Ehh wallahi abba, shigowata kenan dama nazo
ne in gaisheku saboda kwana biyu ban samu
damar shigowa ba.."
Murmushi Abba yasake yi ya kalli kabeer din,
"Haba kabeer har yaushene rabonka da gidan,
nazaci ai jiyane kawai baka zoba amma ai
shekaran jiya ma kazo kodai ka manta ne?"
Maganar da abba ya fadice tasa mama tsoma
bakinta tana dan murmushi amma fuskarta babu
yabo babu fallasa,
"To ai Alhaji tunda yasaba zuwa kullum jiya
kuma baizo ba ai dole yaji kamar yafi sati daya
rabonsa damu"
Dariya abba yayi yakoma ya kishingida yana
kallon kabeer wanda ya gyara zama yafara
gaisar da mama,
Shiru falon ya danyi nawani lokaci saboda shi
kabeer nauyin mama da abba yakeji yanzu sam
baya iya sakewa yayi hira dasu yanzu kamar da,
Ganin yanata zaune shiru sai dai dan lokaci
zuwa lokaci abba yana sakoshi cikin zancen da
suke yi da mama yasashi mikewa,
"Abba bari naje waje.."
"To kabeer tafiya zakayi?" Abba yafada yana
gyara zamanshi,
"A'a ba tafiya zanyi ba waje zanje"
Fita yayi daga cikin falon cikeda kunya, yana fita
abba ya dubi mama yana fara,a,
"Nasan dama ba tafiya zaiyi ba wurin mutuniyar
tasa zaije.."
Shiru mama tayi batace komai ba saboda ita
kwata kwata bata son wannan maganar saboda
wani dalili wanda ta barwa zuciyarta ita daya
amma idan hali yayi zata bayyanar dashi ga
abban shima yaji, ganin taki zancen yasa abba
barin maganar ta hanyar shigo da wani zancen
daban domin ya fahimci duk lokacin da zaiyi
magana makamanciyar wannan wadda ta shafi
kabeer da nadiya mama bata bada goyon baya.
Yana fitowa daga falon abba cikin kitchen
yawuce, a bakin kofar kitchen din ya tsaya
saboda ganinta da yayi tsaye tana mopping
bayan ta kammala share cikin kitchen din,
Yarinyace yar budurwa wacce bazata wuce
shekaru goma sha biyar aduniya ba, tanada
hasken fata amma ba farace can ba, tana sanye
da atamfa kalar koriya dinkin riga da zani, daga
inda yake yana iya hango gashinta dake
nannade cikin dan kwalin dake daure akanta,
"Sannu da aiki.." Yafadi yana murmushi har
lokacin yana tsaye akofar kitchen din,
"Sannu da zuwa yaya kabeer" tafada ahankali
sannan maganar ma tayi tane cike da kunya,
"Yawwa sannu sarki aiki.."
Tunowa da tayi cewar bata gaidashi ba yasata
saurin dan rissinawa,
"Yaya kabeer ina wuni?"
"Bazan amsa ba har sai kin jiyo kin kalleni ido
da ido.."
Murmushi yasaki bayan ya furta mata hakan
saboda yasan ba karamin aiki ya hadata dashi
ba domin kunyarshi da takeji bazai taba barinta
ta iya hada ido dashi ba...
_*Ummi Shatu*_
[7/4, 5:13 AM] Humaira Khaleel: _©HWA_
*MIJINA SIRRINA.....!*🌹
_(Labarin k'auna)_
**Based on a true life story**
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Alh .I. Uba family_
_Fatan alkhairi ga k'awata maryam qaumi,
kina raina akoda yaushe yan matan shaddad.._
_*2*_
aishaummi.blogspot.com
~~~Jin abinda ya fada ya sata sake sinne kanta
kasa tana kallon tiles din dake malale a kitchen
din,
"Bazaki gaida ni ba kenan in tafi ko?" Kabeer ya
fada har lokacin fuskarshi tana dauke da
murmushi,
"To ba na gaisheka ba kaki amsawa" nadiya
tabashi amsa tana mai sake juya masa baya
dan kar yaga fuskarta,
"Nadiya kenan wai wannan kunyar yaushe zaki
dainata ne? Kullum idan nazo sai ki gudu ki
buya alhalin nikuma saboda ke nake son zuwa
gidan nan, duk ranar da ban gankiba idanuwana
radadi da zugi suke yimin, kuma nazo sai ki
hanawa idanuwa tozali da kyakkyawar fuskarki?
Uhm nadiya? Dan jiyo mana.."
Badan taso ba ta dan jiyo dakyar tana kallon
kasa,
"Kinga kyankyaso nan a bayanki.."
Tun kafin ya karasa maganar ta dako tsalle
tabar wurin sai gata a bakin kofar kitchen din
kusa dashi, dariya ya fara yimata domin dama
yasan tana mutukar jin tsoron kyankyaso
shiyasa lokuta da dama yake tsoratata dashi,
Ganin yanata dariya yasata gane cewar ba
dagaske yake ba,
Fuska ta bata, "yaya kabeer ashe dama
tsokanata kake?"
Dariya ya sakeyi ya daga mata gira,
"Wasane matar yaya kabeer.."
Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cikeda kunya
domin kowa adangi da haka yake kiranta tun
tana yar jaririya har ta girma, kowa matar
kabeer yake cemata,
"Yau ina ka bar hular taka ka taho haka?"
Sai da ya dan matsa kusa da ita sannan
ahankali yace,
"Wai duk zumudin zuwa ganinki ne yasani
manto wayata da hulata adaki har sai da nazo
nnpc sannan na ankara.."
Dariya itama tafara yi masa, yayinda shikuma
ya tsaya yana kallon yanda kumatunta ke
lobawa, hakan ba karamin burgeshi yakeyi ba,
"Kici gaba da dariyar bana son ki daina"
Tsagaitawa tayi daga dariyar da takeyi,
"Yaya kabeer na kawo kayi min assignment din
biology? Skeleton teacher dinmu yace mu zana
nikuma ban iya drawing ba"
Makale kafada yayi,"nima ban iya drawing ba.."
"Please yaya KB"
Jin abinda tace yasashi kallonta tareda sakin
wani tattausan murmushi,
"Dauko nayi miki"
"Yawwa yaya kabeer thanks.."
Rabawa tayi ta gefenshi ta wuce fuskarta dauke
da murmushi, juyawa yayi ya bita da kallo,
yanzu SS 2 take a secondary school alla alla
yake ta kammala domin so yake ya zama
mijinta sirrinta,
Yana nan a tsaye har ta fito hannunta rikeda
pencil, cleaner da note book dinta sai kuma
modern biology, tsayawa tayi ta bayanshi tana
kallonshi domin a zahirin gaskiya yayi mutukar
tsaruwa sam bashida makusa ko kadan.
Babu zato ya jiyo nan tayi gaggawar dauke
idonta daga gareshi,
"Yaya KB gashi.." Tafada cikeda jin kunyarsa
domin tasan yagane kallonsa ta tsaya yi,
Hannu ya mika ya karbi books din hannunta
sannan ya sakar mata wani murmushi, ahankali
ya furta,
"Ki ware idanuwanki ki kalleni son ranki kidaina
kunya saboda nidin nakine...."
Fuskarta ta rufe da hannayenta ta juya ta nufi
cikin kitchen tana cewa "kai yaya kabeer.."
Murmushi yayi kawai ya nemi wuri ya zauna kan
wani dan dakali dake zagaye da wasu flowers
wanda yake opposite da kitchen din,
Zana mata skeleton din yafara yi yayinda ita
kuma ta kafeshi da ido tana daga cikin kitchen
din bayan ta kammala mopping din da take yi,
Kallonshi ta tsaya take tayi ko kiftawa
batayi,dago kanshi yayi da niyyar yi mata
magana nan ya kamata tana aikin kallonshi,
Saurin kawar da kanta tayi ta juya zata koma
cikin kitchen nan yayi gaggawar dakatar da ita,
"Nadiya zo nan.."
Tana rufe da fuskarta ta karasa gabanshi ta
tsugunna,
"Meye kike satar kallona?? Ba nace miki idan
kina son kallona kawai ki kalleni kanki tsaye
batare da kunya ba..?"
"Nifa ba kai nake kalloba yaya kabeer" tafada
muryarta na rawa dan jin kunyarsa,
"To naji, idan nazana miki skeleton din ai basai
nayi miki labelling ba ko?"
Kai ta daga masa batare da tayi magana ba,
Murmushi yayi yaci gaba da zanen, "to bani
labari inji.."
"Yaya kabeer nikuma wanne labari na iya bare in
baka?"
"Ko na makarantarku ma idan kika bani ina so.."
"Ai makarantarmu babu wani labari acikinta"
"Kedai kawai bakya son ki fada min labarin
makarantarku..."
Kafin ta bashi amsa mama ta zo daf dasu zata
shiga kitchen domin dora tuwon dare, batare da
mama tayi magana ba tasaka kai ta shige cikin
kitchen,
Ganin mama yasa hirar tasu takare sai aikin
murmushi da suke aikawa junansu,
Littattafanta ya mika mata ya tashi tsaye yana
yimata wani murmushi wanda ita kadai ce ta
fahimci sakon da yake son isar mata,
Kitchen yabi mama yayi mata sallama ya wuce
batare da yayiwa nadiya magana ba amma
kuma yana ta kokarin aika mata da sakon
bankwana ta cikin idanuwansa sai dai ita ta
kasa kallonshi, tana tsaye tana satar kallonsa
har ya fice daga gidan,wucewa tayi ta nufi
dakinsu itada su amira,
Akan gadonsu ta zube tana mai tuno yaya
kabeer acikin zuciyarta duk da cewar har yanzu
bai bude baki ya furta mata kalmar so ba amma
tasan soyayya suke yi a boye ita dashi batare
da sun bayyanawa junansu sirrin dake cikin
zuciyoyinsu ba.
*_Ummi Shatu_*
[7/5, 3:35 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*HASKE WRITERS ASSO.*
**True life story**
*3*
aishaummi.blogspot.com
~~~Note book dinta ta bude tafara kallon zanen
skeleton din da yaya kabeer yayi mata, gefe
daya kuma kamshin turarenshi ne yake tashi
daga cikin littafin,
Bin zanen kawai take yi da kallo tana murmushi
wanda ita kanta bata san ko na menene ba
amma kuma zuciyarta tafi aminta da cewar
kawai na tsantsar farin cikine,
"I love you yaya kabeer.."
Tafadi ahankali tareda lumshe idonta,waleeda ce
ta shigo cikin dakin da gudu,
"Yaya nadiya kizo inji abba.."
Ajiye littafin tayi ta dauki hijabinta ta fita
saboda al'adar abbansu ce haka duk lokacin da
ya dawo daga office ko kasuwa to tattara
yaranshi yake yi a falonsa suyi hira masu wasa
suyi wasansu yana zaune yana kallonsu masu
karatu kuma suyi har lokacin sallar magrib yayi
a lokacin ne kowa zai dauro alwala yajasu jam'i,
haka sallar isha ma, wannan dalilin ne yasa su
nadiya basa fita ko ina idan ba makarantar
islamiyya ko boko ba sannan hakan ya haifar da
shakuwa mai karfi a tsakaninsu dashi,
Ahankali ta tura kofar falon abbansu ta shiga,
kishingide ta sameshi yana kallon labaran
yamma a tashar AIT, can gefe daya kuma Amira
ce da amir suke rubuce rubuce ajikin littafinsu
na makaranta da alama home work suke yi, sai
husna da walida daketa aikin mammatsa game
wanda duk karar game din ta cika cikin falon,
"Sannu da hutawa abba.." Nadiya tafada tana
kokarin zama kusa da abban nasu,
"Yawwa nadiya, kabirun har ya tafi ne?"
"Ehh abba ya tafi yanzu bai jima da tafiya ba.."
Shiru abban yayi ya maida hankalinsa ga kallon
labaran da yake yi, ita kuma nadiya wurinsu
Amira taje tasa ido tana ganin yanda suke yin
home work din har mama ta shigo ta iskesu.
K'arfe 9 nadare bayan su nadiya sun kammala
cin abincin dare mama tace suje su kwanta
domin har waleeda da husna sunyi bacci su
amir ne kawai idonsu biyu,
D'aukar husna nadiya tayi zuwa dakinsu ta
kwantar da ita akan katifarsu sannan ta sake
zuwa ta dauki waleeda taje ta kwantar da ita su
Amira suna biye da ita, gyarawa amir wurin
kwanciyarsa tayi ya kwanta sannan itada Amira
suka haye gadon dake cikin dakin suka kwanta,
Wayar mama dake ajiye a karkashin pillow dinta
ta zaro ta yiwa yaya kabeer plashing, kusan
kullum haka suke raba dare suna hira a wayar
mama amma ita maman sam bata taba sani ba
ita dai kawai tasan nadiya bata taba barin
wayarta ta huta mutukar tana gida sai dai idan
makaranta ta tafi to lokacin ne wayarta zata
samu lafiya.
Ko minti biyu da yi masa plashing din bata yiba
ya kirata,da murmushi akan fuskarta ta daga
wayar,
"Yaya kabeer kaje gida lafiya?"
"Lafiya lau nadiya, yasu mama?"
"Suna nan lafiya"
"Ya kunya?"
Dariya tasa saboda jin abinda ya fada,
"Yaya kabeer kenan kaima ai ya kamata ka rinka
jin kunyata.."
"Saboda me?.. "
"Saboda na cancanci hakan.."
Murmushi ya saki kafin ya bata amsa,
"See you, idan a wayane kibi ki isheni da surutu
amma idan nazo sai kiyi shiru ki kasa magana
kamar wanda zan kamaki"
Itama dariyar tayi, "to ba kaine ba"
"Nine me?"
"Kaine idan naganka sai naji nakasa yin
maganar.."
Dariya ya sake yi, "nadiya kenan.."
"Meya faru yaya kabeeru?"
Murmushi yayi saboda jin ta kirashi da kabeeru,
"Kin ganki ko? Bakinki ya iya fadin kabeeru sake
fada naji"
"Yaya KB.."
Dariya suka yi dukkaninsu musamman ma shi
kabeer din wanda yake cike da nishadi cikin
wannan dare,
"Yaushe zaka zo? Zaka zo gobe?"
"Yaushe kike son kara ganina? Duk lokacin da
kike son sake ganina zanzo.."
"Koda kuwa yanzu ne?" Ta tambayeshi tana
murmushi,
"Yes even now i shall come if you wish..."
"To ina jiranka idan har dagaske kake zaka zo
din"
"Dagaske kike kina son ganina yanzun..?"
"Kaji yaya kabeer da dawasa nake? Dagaske
nake mana"
K'arar bude kofa ta jiyo hakan yasata saurin
dakatar dashi,
"Ina zaka zo da tsohon daren nan?"
"Sabon dare dai ba tsohon dareba,wurinki zanzo
ki ganni"
"To yi zamanka na hakura da wasa nake yi.."
"Inama kiyi dagaske kigani idan zanzo ko bazan
zoba"
"Yaya kabeer kenan ai nasan zaka zo"
Murmushi yayi, "to yaushe zan kawo miki
budurwata ne ku gaisa?"
Jin abinda yafada yasata mikewa da sauri bayan
zuciyarta ta harba, nan taji wani shiru ya ziyarci
cikin kunnenta duhu ya mamaye ganinta yayinda
bacin rai ya lullube zuciyarta gaba daya.
*_Ummi Shatu_[7/8, 6:42 AM] Humaira Khaleel:
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*_4_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Hannu tasa ta danne zuciyarta gudun kada
ta faso ta fito waje,
"Nadiya... Yanaji kinyi shiru ko bazaki gaisa da
budurwar tawaba?"
Ajiyar zuciya ta ajiye ahankali, dakyar ta iya
sassaita tunaninta tayi magana ahankali,
"Yaya kabeer me zai hana ingaisa da ita idan
har ka kawo min ita?"
Dan murmushi yayi mai kayatarwa kamar yana
gabanta tana kallonshi,
"Ina fata dai har zuciyarki kika fada ma'ana da
zuciya daya.."
"Yaya kabeer kenan.."
"Nadiya kenan, nadiya yanmata"
Murmushin dole tayi kafin tayi magana,
"Yaya kabeer nafara jin bacci gashi kaga gobe
zanje school"
"Nadiya nifa da wasa nake yimiki banida wata
budurwa so karki dauka dagaske ne.."
Duk da cewar taji dadin maganarshi amma sai
ta basar,
"Kaji yaya kabeer da wani zance, to idanma
dagaske ne ni ba abin in tayaka murna bane??
Sanyayyen murmushi ya saki,
"Hakane to balle ma ba dagaske bane da
wasane"
Itama murmushin jin dadi da farin ciki tayi,
"Shikenan tunda kaji tsoro ka sauya magana.."
Yar dariya yayi wadda har tana iya jiyo sautinta,
"Nayarda naji tsoron..."
Juyi nadiya tayi taja bargo ta dan rufe rabin
jikinta,
"Yaya kabeer zan barka haka yanzu saboda
kasan gobe zan je makaranta"
"To ya nadiya babu komai, Allah ya kaimu goben
sai kin jini" yafada cikeda tsokana,
"Ok tom bye bye" tabashi amsa bayan ta lumshe
idanuwanta, katse wayar tayi lokacin da taji
yace "bye bye good night and have a nice sweet
dream"
Addu'ar kwanciya bacci tayi ta shafe jikinta, da
tunanin kabeer bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari da misalin karfe biyu nadiya ta
dawo daga makaranta dama ba makarantarsu
daya dasu amir ba su akusa da gida suke ita
kuma nadiya makarantarsu da dan tazara da
unguwarsu, a gaggauce ta shiga gida tana shiga
tasan cewar yaya kabeer yana gidan saboda taji
kamshin turarensa sannan ta hango takalmanshi
a kofar falon mama dan haka bata bari kowa
yaji dawowarta ba ta wuce dakinsu ta ajiye
school bag dinta ta fito ta shiga kitchen,
Abinci ta zuba ta zauna tana ci kamar ance kalli
window tana kallon wurin tayi ido biyu dashi
tsaye yana kallonta yana yi mata murmushi,
Sunkuyar da kanta tayi tadaina cin abincin,
murmushi kabeer yayi ya saki karfen dake jikin
window din,
"Kici abincinki dama kawai nazo ganinki ne, bari
natafi inyaso sai nadawo da yamma lokacin kin
gama laumar.."
Bai jira abinda zatace ba ya juya yawuce,
murmushi tayi ta tashi ta leka sai da ta
tabbatar da cewar yatafi baya gidan sannan ta
koma ta dauki abincinta ta nufi dakin mama
tana tafe tana cin abincin,
A falo tasamu mama tana shirya husna da
alama wanka tayi mata,
"A'a kekuma yaushe kika shigo? Jibeki kina
tafiya kina cin abinci, keda zaki yiwa wani fada
amma kece meyi"
Zama nadiya tayi saboda mama kamar yayarta
take sam batayi kamada mahaifiyarta ba kai
idanma ba sani kayiba zaka zaci ya da kanwa
ne domin kamar yadda abba yake jansu ajiki
haka itama maman ke jansu ajikinta musamman
ma nadiya domin kowanne abune yake damunta
to ita take fadawa sannan idan shawarane ma
da ita take yi,
"Hajiya mama kenan wallahi wata yunwa na
debo kuma ina zuwa sai na iske yaya kabeer
agidan shine nagudu kitchen na buya acan
nazuba abincin nafara ci, yanzu kuma da ya tafi
shine nadawo nan dan kisan nadawo.."
Tsayawa da shafa man da take yiwa husna
mama tayi tana kallon nadiya,
"Nadiya wai menene tsakaninki da kabeer ne?"
Nadiya jin maganar tayi tazo mata a bazata dan
haka tayi shiru tagagara bawa mama amsa
wanda har sai da mama ta maimaita mata
tambayar sannan tayi gaggawar zakulo amsa ta
bawa Maman,
"Mama babu komai kawai zumunci muke yi
tunda ni yar uwarsa ce shi dan uwanane"
"Nasani nadiya, amma bayaga wannan bana son
wani abu ya hadaku muddin ba zumunci bane"
"Amma mama saboda..."
Katseta mama tayi bata barta ta karasa abinda
take son tambaya ba,
"Ya isa haka bana son tambaya, ki maida
hankalinki kawai kici abincin da yake gabanki"
Shiru nadiya tayi taja abincin taci gaba da ci
tana ta sakar zuci saboda bata san dalilin mama
na rashin son wani abu ya hadata da yaya
kabeer ba amma
Koma dai menene sannu ahankali zata tambayi
Maman....
*_Ummi Shatu_*
[7/8, 6:42 AM] Humaira Khaleel: ® *HASKE
WRITERS ASSO*
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin K'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*5*
aishaummi.blogspot.com
~~~Bata kara bi takan maganar ba suka cigaba
da hirarsu ita da maman har ta kammala cin
abincin da takeyi ta tashi tabar falon ta koma
dakinta tana rikeda wayar mama, lafewa tayi
akan gadonta suna yin waya da yaya kabeer,
sun dauki lokaci mai tsawo kafin suyi sallama
nadiya ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya
tasaka uniform din islamiyyarta domin karfe uku
suke tafiya su dawo karfe shida na yamma,
Hannen kannenta ta kama suka yiwa mama
sallama suka tafi, sai da misalin karfe shida da
yan mintuna suka dawo, dawowarsu tayi daidai
da zuwan yaya kabeer shi da wani abokinsa,
Nadiya bata bari sunga fuskarta ba tafara
gaidasu,
"Baiwar Allah ya kiketa boye kaine kamar marar
gaskiya,kodai bakida gaskiya?" Abokin yaya
kabeer din yace da ita,
"Kabarta kawai musty domin yar kauye ce" yaya
kabeer yafada cikin barkwanci da tsokana, ita
dai nadiya shiru tayi musu tana jinsu sai dai ta
lura wannan abokin na yaya kabeer wanda aka
kira da musty sai faman binta da kallo yake, duk
inda ta waiga sai taga yanata kare mata kallo,
Ganin haka yasa ta takura ta shige gida yayinda
yaya kabeer ya mara mata baya,
A soron gidan suka tsaya kowannensu fuskarsa
dauke da murmushin kauna,
"Yaya kabeer ina ka samo wannan abokin mai
shegen kallon tsiya?"
Dariya maganarta ta bashi dan haka ya fara
darawa yana kallonta,
"Wai musty? Abokinane unguwarmu daya
sannan tare muka yi karatu dashi"
Dan karamin tsaki taja, "Allah na tsani mutum
ya tisani agaba yayita kallona"
"To yanzu dai nayi laifi tunda har na kawo
wanda yayi miki abinda bakya so, ayi min
afuwa..."
Murmushi tayi, "ni ai ba laifi nace maka kayi
minba amma dai wannan abokin naka gaskiya
ya fiya kallo da yawa"
"To ai nabaki hakuri"
"Nahakura"
"To zan iya tafiya?" Yace da ita cikin tsokana,
"Zaka iya mana yaya kabeer..."
"To fara shiga gida nagani"
Wucewa tayi tana murmushi ta shige cikin gida
sannan shima kabeer din ya juya yafita.
Fuskarta dauke da fara'a ta shiga cikin gidan,
zaune ta tarar da mama da kannenta tana
yimusu shari'a wanda kusan kullum aikin kenan
amir da amira kamar zasuga hanjin cikin
junansu,
"Ke kuma a ina kika tsaya su Amira suka rigaki
shigowa?" Mama ta tambayeta idanuwanta
akanta,
"Mama yaya kabeer ne ya tsayar ni wallahi.."
Shiru Maman tayi ta mayar da hankalinta gasu
amir taci gaba da yimusu sulhu, yayinda ita
kuma nadiya ta ajiye jakar islamiyyarta ta shiga
kitchen domin ta jiyo tuwon da mama keyi ya
fara kauri alamun ya kama,
Itace ta karasa girkin sannan ta fito daidai
lokacin abbansu ya dawo nan kuma dukkaninsu
suka dunguma zuwa falonsa kamar yadda suka
saba.
Tunda musty abokin kabeer yaga nadiya yaji
ta kwanta masa arai domin yarinya ce mai
hankali sannan kuma mai nutsuwa gata da
kunya da ganin girman nagaba, gani daya da
yayi mata yasashi kamuwa da sonta dan haka
batare da ya shawarci abokinsa kabeer ba ya
samu mahaifinsa yayi masa maganar nadiya
domin shi dagaske yake sonta bada wasa ba
sannan son aure yake yimata ba na yaudara ba
shiyasa ma yake son mahaifinsa yaje ya
tambayo masa aurenta,
Aranar da ya sanar da mahaifinsa aranar yaje
ya samu baban nadiya daf da lokacin sallar
magrib, kasancewar abba mutum ne mai
karrama bako sai da ya karrama baban musty
sosai ya fito musu da ruwa sukayi salla kamar
dama sun san juna sannan baban musty
yafadawa abba abinda ke tafe dashi,
Shiru abba yayi kafin ya cewa baban musty zai
tambayi nadiyan ko tasan musty din inyaso duk
yadda sukayi da ita zai kirashi a waya ya fada
masa, anan suka yi exchanging din phone
numbers dinsu abba ya shiga gida,
Lokacin da yashiga falonsa nadiyan ya samu ita
da mama suna cin tuwo tare, su kuma yaran an
zuba musu taliya suna ci,
Sai da abba ya bari sun gama cin abincin
sannan yayi gyaran murya yace,
"Nadiya zo nan"
Kusa dashi ta koma ta zauna, "gani abba"
"Bakon da nayi dazu saboda ke yazo.."
Ras,ras gaban nadiya ya fadi saboda bata san
abinda tayiba,
"Abba laifi yace nayi masa?"
Murmushi abba yayi,
"Ba laifi kikayi masa ba nadiya, yazo nemawa
dansa aurenki ne, sunan yaron wai Mustapha
abokin kabeeru ne yayanki"
Ba karamin faduwa gaban nadiya ya sake yiba,
nan fuskar musty ta bayyana acikin zuciyarta
lokacin da ya kafeta da ido yana yi mata
wannan kallon kurullar....
*_Ummi Shatu_*
[7/11, 7:58 AM] Ummi A'isha *MIJINA
SIRRINAH...!*🌹
_(Labarin K'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*6*
aishaummi.blogspot.com
~~~Shiru nadiya tayi saboda bazata iya fadawa
abba cewar yaya kabeer take so ba,
"Nadiya ya naji kinyi shiru ne?"
Muryar abba ta dawo da ita cikin hayyacinta,
"Abba babu komai.."
"To Mustapha dai ya turo mahaifinsa tunda
babu wata matsala zan sanar dasu inyaso
yafara zuwa har kusamu ku daidaita"
"To abba" ta fada kanta akasa, ita dai mama
tana zaune tana jinsu amma har akayi aka
gama batace ko uffan ba,
Mikewa nadiya tayi ta fita zuwa dakinta gaba
daya tama rasa abinda yake yimata dadi acikin
zuciyarta, gashi bata son fadawa yaya kabeer
domin gudun sakashi cikin damuwa,please call
me ta tura masa nan take ya kirata,
"Yaya kabeer yau ban ganka ba"
"Nidinma yau ban samu ganin fuskar gimbiya
nadiya ba amma nasan dalili.."
"Wanne daliline?" Ta tambayeshi cikin dokin jin
abinda zai fada,
"Yau naje unguwa ne sai dazunnan nadawo
shiyasa ban shigoba, amma gobe sammako zan
dako da sassafe inyi karin kumallo da
kyakkyawar fuskarki"
Dariya abinda yafada ya bata dan haka tafara
dariya,
"Kaji yaya kabeer da abin dariya sai kace wani
abinci da zakace zakayi karin kumallo da
fuskata"
"Ni ai kinfi abinci, da ace za a ajiye min ke inyita
kallonki to da na tabbata bazanji yunwa ba.."
Wata dariyar ta sake yi har tana kokarin fadowa
daga kan gadonta,
"Yaya kabeer zaka sa cikina ya fashe dan dariya
gashi dama naci tuwo na koshi dayawa.."
"Wai wai, wai, overfeeding kikayi ai? Oya tashi ki
fara exercise ina jiyoki daga nan"
Tashi tayi tana dan murmushi,
"Allah yaya KB jina nakeyi nagaji nidai ban son
exercise dinnan.."
"To yi tsalle guda goma ina kirga miki, oya fara"
Tsalle tafara tanayi yana kirga mata har sai da
tayi guda ishirin sannan ya barta takoma saman
gado ta kwanta tana haki,
"Washh, yaya kabeer wlhi kabani wahala da
yawa"
"Waye yasa kici abinci yayi miki over?"
"Kaine.."
"A'a ni karki yimin sharri.."
Murmushi tayi kafin tabashi amsa wayar tayi
shutdown, komawa tayi ta kwanta tana cikeda
farin ciki.
Kamar yadda kabeer yafada kuwa da safe sai
gashi yazo lokacin ko school su nadiya basu
tafiba, asalima lokacin suke shiryawa, kanta
babu ko dan kwali tana cikin kitchen tana cin
soyayyen dankalin da mama ke soyawa sai
gashi ya shigo, ba karamin mamaki nadiya
tayiba domin ta zaci wasa yake yimata da yace
zaizo da sassafe ya ganta,
Dan tsananin kunya kasa gaisheshi tayi tana
jinshi da mama suna gaisawa daga nan yawuce
ciki falon abba,
Bata bari yaji fitarta zuwa makaranta ba ta zare
jiki tagudu.
Abangaren Mustapha kuwa ba karamin dadin
labarin da mahaifinsa yazo mishi dashi yajiba
musamman ma da yaji cewar ba ayiwa nadiya
mijiba asalima ko tsayawa da samari bata fara
yiba,wanka ya dauka ya shirya ya fito ya nufi
gidansu nadiyan,
Tana falon abba tana yiwa su amir homework
yaro yayi sallama yace wai nadiya taje inji
Mustapha, kamar bazata yi motsiba har saida
taji mama tayi magana sannan ta tashi tafita
zuciyarta babu dadi,
Tsaye ta sameshi ya saka hannuwanshi acikin
aljihu yana yimata murmushi sai dai ita ko
kadan bai burgeta ba, sallama tayi masa ya
amsa cikeda kulawa nan suka gaisa yafara koro
mata jawabi,
"Nadiya wato tun ranar farko dana soma ganinki
Allah ya jarrabi zuciyata da sonki da kaunarki
saboda yabawa da nayi da hankalinki da
nutsuwarki,ina fata zaki bani hadin kai har nakai
ga cimma burina da muradina na mallakarki..."
Saida taji yayi shiru sannan tayi magana,
"Yaya Mustapha nagode da soyayyar ka
agareni,hakika duk Wanda yace yana sonka to
ya gama yimaka komai kuma bakada
kamarshi,to amma nikuma inada wanda nakeso"
Cikeda mamaki ya kalleta saboda shidai
mahaifinsa yace mahaifinta ya sanar dashi babu
wanda yake zuwa wurinta,
"Kina da wanda kikeso? Waye?"
"Yaya kabeer ne abokinka"
Jin abinda tace yasashi yin shiru nawasu yan
lokuta kafin daga bisani ya kalleta,
"Shikenan nadiya nagode da kika fada min
gaskiya baki rufeni ba, kuma nayi farin ciki da
jin cewa kabeer ne wanda kike so domin
mutumne shi mai kyakkyawan hali da dabi'a mai
kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi"
Sallama yayi mata ya tafi nan itama ta juya ta
shiga cikin gida tana dauke da farin cikin cewar
tagama da babin Mustapha..
*_Ummi Shatu_*
[7/13, 7:02 AM] Ummi A'isha *MIJINA
SIRRINA..!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*7*
aishaummi.blogspot.com
~~~Hankali kwance nadiya ta koma gida taci
gaba da gudanar da harkokinta, soyayyarsu
itada yaya kabeer kuwa kullum sake yin gaba
take tana kara kulluwa, koda yaushe suna
makale awaya suna hira, sannan kusan koda
wanne lokaci yana gidan mutukar nadiyan tana
nan.
Tunda nadiya ta sanarwa da mustapha cewar
tanada wanda take so yaji hankalinsa ya dan
tashi amma idan yatuno da cewar kabeer ne
wanda take so din sai yaji ranshi ya danyi fari
saboda yasan kabeer zai riketa riko na gaskiya
wannan dalilin ne ma yasashi sanarwa da
mahaifinsa yanda suka yi da ita, shima mahaifin
nasa baiyi k'asa a gwiwa ba ya kira abban
nadiya ya fada masa abinda yafaru gudun kar
aga musty din yadaina zuwa bayan kuma manya
sun shiga, shiru abban nadiya yayi saboda
shidai a iya saninshi nadiya bata da wani
saurayi amma tunda yaji haka to ya zama dole
ya tuntubeta da zarar ya koma gida.
Kamar yadda al'adar gidan take yauma zaune
suke dukkaninsu a falon abba suna kallon tashar
mbc drama, rage karar volume din tv din Abba
yayi yace,
"Yawwa nadiya kafin na manta zo ina son
magana dake.."
Kusa da mama ta dan matsa tana kallon abba,
"Nadiya yaron nan mustapha da yazo wurinki
yace kince masa kinada wanda kikeso hakane..?"
Kai ta dagawa abba, "hakane Abba"
"To waye?" Abba yasake tambayarta, kamar
bazata yi magana ba dan kunya ta daure tace,
"Abba yaya kabeer ne"
Shiru abban ya danyi fuskarsa dauke da
murmushi,
"To kira min kabeer din, dama yau ai naga baizo
gidanba"
Tashi tayi ta fita tana cikeda murna, wayar
mama ta dauka ta kirashi,
"Yan mata.."
"Yaya kabeer albishirinka?"
"Goro" yafada yana murmushi,
"To kazo abba yana kiranka"
"To ai baki fada min albishir din da kika yimin
ba"
"Idan kazo zakaji"
"To gani nan zuwa"
Katse wayar tayi ta koma falon abba tana jin
kamar ta daka tsalle dan tsananin murna,
Tana shiga falon abba ta dan saci kallon mama
nan taga fuskar Maman babu walwala sosai
amma dai batayi magana ba,
Nan kuma taji ranta ya dan sosu saboda tasan
bacin ran mama yanada alaka da maganarsu
itada kabeer tunda tun jimawa Maman ke
yimata gargadin cewar karta bari soyayya ta
shiga tsakaninta da kabeer,
Tana ta tunanin abinda zaije yazo aranta taji
sallamar yaya kabeer nan tayi hanzarin jan
hijabinta ta rufe fuskarta saboda kunya sai dai
amma tun kafin ya karaso kamshin turarensa ya
rigashi karasowa,
Cikin nutsuwa yayi sallama ya shiga bayan abba
ya amsa masa, nan kuma su amir sukayi kansa
suka cuccukumeshi domin yasaba basu sweet
duk lokacin da yazo,
Yau dinma saida yabisu ya basu daya bayan
daya sannan suka kyaleshi ya nemi wuri ya
zauna, cikeda girmamawa ya gaisheda abba da
mama,
"Kabeeru dalilin da yasa kaji nace kazo shine
nadiya ce tazo min da wani zance cewar kai da
ita kuna son junanku hakane?"
Sunkuyar da kai kabeer yayi cikeda kunya yace
"hakane abba"
Dan fara'a abba ya fadada cikeda jin dadi yace,
"To kabeeru babu shakka naji dadin wannan
labari domin hakan zai kara dankon zumunci da
aminci a tsakaninmu domin nadiya yar
uwarkace, sannan ni mahaifinka ne ako ina zan
iya tsayawa in nema maka aure bare
agidana,dan haka ni a matsayina na mahaifin
nadiya nabaka ita a matsayin matar aure ko
bana raye ban yadda nadiya ta auri kowanne
namiji ba face kai har sai dai idan kaine ka
sauya akalarka, dan haka abinda nake so dakai
shine da zarar ka koma gida ka sanarda yaya
cewa ga abinda mukayi dakai saboda sonake yi
nadiya na gama makaranta ayi bikinku da ita
batare da andauki dogon lokaci ba"
Ai kabeer najin abinda Abba yace yaji kamar an
yimishi bushara da gidan aljanna, nan wani dadi
ya rufeshi zuciyarsa ta samu wata nutsuwa mai
kayatarwa tuni yafara yiwa abba godiya,
"Abba nagode madalla, Allah yasaka da alkhairi,
Allah yabar zumunci abba.."
"Babu komai kabeer ai duk abinda nayi maka
kaina nayiwa domin kai d'anane halak malak"
Saida kabeer ya sake jaddada wata godiyar
sannan ya tashi ya fita, cikeda jin kunya nadiya
tabi bayanshi, tana zuwa tsakar gida kuwa ta
iskeshi lafe ajikin bango dama ita yake jira ya
harde hannuwansa ajikin kirjinshi,
Kallonshi tayi yasha gaye cikin wata
rantsattsiyar purple colour din shadda galila
wacce tasha dinkin buba dan haka ba karamin
kyau yayiba,
"Yanzu kaji albishir din da nayi maka dazu?"
Tafada cikeda murmushin kunya,
"Naji wannan dalilinne ma yasani shirya baki
tukwici, rufe idonki"
Rufe idonta tayi tana murmushi, "yaya kabeer
Allah dai yasa nima chocolate din zaka bani irin
wacce kabawa su amir..."
Bata iya karasawa ba saboda jin lebenshi akan
nata, take jikinta yafara rawa tayi gaggawar
bude idonta, nan ta juya zata gudu yayi saurin
rikota,
"Ai abba yace yabani ke ko baya raye nine
mijinki, tsananin farin cikine yasa kikaga nayi
miki haka so karki fassara ni da wata manufa,
ko ba komai dai kin san ni yayanki ne dan haka
bazan taba cutar dakeba"
Har lokacin bata iya yin magana ba saboda
tsantsar kunyar da ya haddasa mata,
"Yaya kabeer nidai.."
Hannunta ya rike ya matsa kusa da ita tareda
leka fuskarta wadda ta kawar gefe guda,
"Kedai me?"
"Nidai kasani jin kunya"
Murmushi yayi ya mike tsaye yana kallonta
zuciyarsa cikeda farin ciki...
*_Ummi Shatu_*
[7/13, 6:59 AM] Ummi A'isha: ® _HASKE
WRITERS ASSO._
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
*8*
aishaummi.blogspot.com
~~~ "Wai kina nufin haka zamuje gidan kina
yimin wannan kunyar?"
Murmushi ta danyi "wai yaya kabeer ni duk ba
wannan ba yaushe zaka zo muyi hira irin wacce
muka dade ba muyiba?"
Daga kai yayi yana kallon sararin samaniya
alamun tunani fuskarsa kuma kunshe da
murmushi,
"Uhmmm, ina jin zanzo a weekend saboda ranar
ne banida aiki da yawa sannan kema kina
gida.."
"To Allah ya kaimu, yanzu dai bari nakoma ciki
saboda kai naga kana cikin farin ciki.."
Dakatar da ita yayi ya hanata tafiya,
"Ina kuma zakije bayan akwai labarai da yawa
da nake burin ji daga gareki"
"Labari kuma yaya kabeer? A wannan daren?"
"To da sai awanne daren?" Ya tambayeta yana
murmushi,
"A'a yaya kabeer karfa ka sauya min maganata
zuwa wata daban"
Murmushinsa ne yasake karuwa, "kaji min
yarinya da wayo, wai ke waye ya koya miki
wayone? Ni ban taba ganin first born mai wayo
irin nakiba"
Dariya tayi ta rufe fuskarta, "har nakaika wayo?
Kaima fa first born dinne amma kafini wayo ma"
"A'a ban fiki wayoba zadai muzo daya,
musamman ma tunda zuciyoyinmu sun kasance
guda daya, sannan nan bada dadewa ba zamu
zama abu daya..."
Dariyace ta kwace mata nan tayi baya da sauri
tana dariya,
"Nidai yaya kabeer natafi da wannan sai
anjima.."
Shima dariyar yayi ya daga hannu alamun bye
bye yana cewa,
"Ok bye yanmatan yaya kabeer"
Har taje daf da dakin mama dariyar take, a kofar
daki taga mama tsaye fuskarta babu walwala
sannan da alama ita take jira,
"Mama..."
"Zo nadiya" Maman ta fada idonta har ya danyi
ja saboda bacin rai, jiki asanyaye nadiya tabi
bayanta zuwa cikin bedroom dinta domin basu
tsaya a falo ba,
Zama mama tayi agefen gado itama nadiyan ta
zauna,
Kamo hannuwan nadiya mama tayi tana
kallonta,
"Nadiya nasan ke yarinyace karama wacce bata
gama sanin rayuwa ba, wadda hankali bai gama
ratsata ba, wacce bata san rayuwar aure ba,
wacce bata san irin gwagwarmayar da kowacce
mace keyi agidan aurenta ba, bawai ina son
rabaki da kabeer bane nadiya a'a sai dai ina son
kisani shi auren zumunci yafi komai gyara
zumunci idan har yayi dadi amma yafi komai
b'ata zumunci mutukar baiyi dadiba shiyasa
zakiga tun farko ban so soyayyarku da kabeer
ba saboda kabeer dan dakinane akwai zumunci
mai karfi tsakanina dashi haka iyayensa, bana
son azo ayi abu ba aji dadinsa ba zumunci ya
baci.."
Gaba daya jikin nadiya yagama yin sanyi saboda
jin abubuwan da mama ta fada dan haka take
taji jikinta ya fara yar rawa,
"Mama kiyi mana addu'a kawai akan Allah
yasanya albarka acikin al'amarin amma ni sam
bazan iya rabuwa da ya kabeer ba saboda
nafara sonsa tun ban san wacece niba.."
Shiru mama tayi tana kallonta batare da tace
komaiba, ita akwai abinda ta dade tana
hangowa wanda ita nadiya ko kadan bazata iya
hangoshi ba domin akwai kuruciya atattare da
ita sosai saboda gaba daya yanzu bazata wuce
shekaru 15 ba aduniya dan haka yanzune tafara
saninma menene rayuwar,
"Shikenan nadiya tunda kin kasa fahimtata
shikenan bazan hanaki abinda kikeso ba Allah ya
sanya alkhairi da albarka acikin tarayyarki da
kabeer"
Idanuwan nadiyane suka ciko da kwalla nan tayi
saurin tashi ta fita saboda sai take jin kamar
yanzu ne zata tafi tabar mamanta da yan
uwanta,
Duk da cewar mama sunyi haka da nadiya bata
iya hakura ba tashi tayi taje ta iske abba a
falonsa yana zaune shida su amir da waleeda
nan ta tashesu tace sutafi dakinsu suje su
kwanta,bayan fitarsu ta samu wuri ta zauna
kusa da abba,
"Abban nadiya wata magana nake son muyi
dakai amma ta fahimta, dafarko ina son ka
fahimceni ka gane cewar ni bawai bana son
kabeer ne ko kuma yana da wani mummunan
tabo awurina ba, kawai nidai bana son maganar
aurensa da nadiya ne saboda auren zuminci
bashida alfanu mutukar ba ayi daceba amma
idan har aka dace yayi dadi to zumunci yana
sake kulluwa,
Ban so lokaci daya farat daya ka amince ka
bawa kabeer nadiya ba saboda gaskiya nidai
auren zumunci baya daya daga cikin abinda
nake son yiwa 'yayana.."
Abba bai tanka ba har saida yaji tayi shiru
alamun ta gama sannan yafara magana da
tausasashiyar murya,
"Haba hajiya bilkisu, ai kabeeru dan dakinki ne,
kin sanshi kin san halinsa sannan kin san ko
wanene shi tun yana yaro dan haka bakida
kokwanta acikin halayyarsa, kuma insha Allah
wannan auren akwai alkhairi acikinsa ba
kadanba da yardar Allah sai kowa yayi alfahari
dashi kedai kawai kiyi musu addu'a kuma ni ina
ganin da ace mu dauki nadiya mu baiwa wani
wanda bamu saniba, bamu san asalinsa ba
bamu san halinsa ba bamu san ko waye shiba
gara mu baiwa na gida wanda muka san
tushensa muka san komai nasa.."
Jijjiga kai mama tayi alamar gamsuwa da
bayanin da yayi mata sai yanzu ta danji ta
samu nutsuwa akan zancen,
"Shikenan to Allah ya tabbatar da alkhairi"
"Yawwa hajiya bilkisu addu'ar da zamuyi kenan,
kinga yanzu tana aji biyar next term zata shiga
aji 6 nan da wata shekarar insha Allah zamu yi
bikinta mu kaita gidan mijinta, amma kafin nan
ina so nayi miki albishir da cewar keda ita yar
taki na biya muku saudiyya zakuje ku sauke
farali sannan ku iyo addu'a akan Allah ya basu
zama lafiya da zuri'a dayyaba"
Murna ce ta kama mama saboda jin albishir din
da abba yayi mata nan ta hau fara'a tana mai
yimasa addu'ar Allah ya kara masa budi acikin
harkokinsa...
*_Ummi Shatu_*
[7/14, 9:20 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Anty maijidda musa (maman twins) shafi na
9 zuwa shafi na 13 nakine ke kadai domin jin
dadinki, ina mutukar ji dake anty Jidda..._
*9*
aishaummi.blogspot.com
~~~Nadiya na shiga d'aki ta kifa kanta jikin
gado tafara rera kuka ahankali wanda ita kanta
bata san dalili ba amma dai tafi zargin cewa na
fargabar rabuwa dasu mama ne, shigowar su
Amira da taji ne yasata yin shiru ta tashi ta
shiga toilet, sai da ta gyara fuskarta sannan ta
fito lokacin harsu waleeda sun kwanta,
Itama kwanciyar tayi ta dauki wayar mama dake
wurinta tafara yin game, kiran yaya kabeer ne
ya shigo nan ta d'aga jikinta a sanyaye,
"Yaya KB ya kaje gida?"
"Ni ai nayi fushi dake, wato ko ki kirani kiji yaya
naje gida ko?"
"Ayya haba yaya KB ai kasan dai inada niyyar
kiranka kawai dai Allah ne baiyi ba"
Jin yanda ta marerece murya ya sashi yin yar
dariya mai dan sauti,
"Dadina dake ba a kada ke a magana mutukar a
wayane amma idan a filine kuma kinfi kowa
shiru"
"Ai kai dinne yaya kabeer kwarjini gareka,
kwarjini kake yimin"
"Wanne irin kwarjini kuma?" Ya tambayeta
ranshi cikeda farin ciki,
"Yaya kabeer in tambayeka mana"
"Allah yasa nasani yanmatan yaya kabeer"
Murmushi tayi ta sake makale wayar a
kunnenta,
"Yaya kabeer kuma idan muka yi aure shikenan
bazaka rinka kawoni gidan mama kullum ba ko?"
Dariya ya fara yi mata saboda jin yarinta afili,
"Haba nadiya kuma idan kikace kullum zan rinka
kawoki ai sai su maman ma su gaji dake"
"To yaya kabeer kazo mu zauna agidan su
Maman mana gaba daya basai munje gidanmu
ba"
"Nadiya kenan, ke karamar yarinyace baki san
menene aure ba, ko kin sani?"
"Nasani mana yaya kabeer"
"To fada min menene aure"
Shiru ta danyi tafara tunani kafin tayi magana,
"Yaya kabeer aure shine idan saurayi yaga
budurwa yake sonta itama take sonshi sai ayi
musu aure.."
"Daga nanfa?" Ya sake tambayarta,
"Sai akaita gidan da ya gina mata, iyayenta su
siya mata kayan daki"
"Uhum daga nan kuma fa?"
Dan shiru ta sakeyi sannan taci gaba,
"Sai ya siyo kayan abinci ta rinka yi masa girki
tana share gida tana yin wanke wanke"
"Shikenan?"
"Ehh" tabashi amsa tana murmushi, shima
murmushin yayi,
"Shikenan kin gama?"
"Nagama mana"
Dariya yafara yi yana dad'awa har na tsawon
wani lokaci domin sai yau yagama tabbatarwa
da nadiya karamar yarinya ce wadda kuruciya ke
dawainiya da ita,
"Ba ayi muku biology ne nadiya?"
"Ana koya mana.."
Shiru yayi saboda baya son yasata taji kunya
shiyasa bai son fada mata kai tsaye,
"To tunda baki san menene aureba nabaki
assignment ki zauna ki nutsu ki gano min
menene aure"
"To yaya kabeer zan yi"
Murmushi ya dan yimata sannan yayi mata
sallama,ajiye wayar tayi tanata tunanin
maganganun da sukayi da yaya kabeer yanzu,
To ita yanzu tayaya zata samo wannan
assignment din da yaya kabeer yace ya bata?
Ta raya hakan acikin ranta, gyara kwanciyarta
tayi taci gaba da tunani can sai ta tuno cewar
yan ajinsu dayawa tana ganinsu suna karanta
littattafan hausa sannan kuma tana yawan jinsu
suna labarin aure ko labarin soyayya amma ita
bata taba tsoma bakinta aciki ba amma itama
daga gobe zata fara aro littattafai tana
karantawa domin ganin abinda ke tattare aciki,
Sati biyu da kiran da abba yayiwa kabeer
mahaifin kabeer suka zo domin su tattauna da
abban nadiya.
***
Alhaji Bashar Usman da Alhaji Mu'az usman yan
uwan junane ciki daya uwa daya uba daya suna
da kanne mata guda uku wadanda yanzu haka
kowaccensu tana can agidan mijinta tareda
yaranta, Alh Bashar shine babba sai mai bi
masa alh mu'az daga nan sai Hajiya Kubra sai
haj sa'ade sai yar autarsu hajiya Maimuna,
Asalinsu yan jahar kano ne cikin wata karamar
hukuma wacce ake kira da Rano, anan suka
taso dukkaninsu sannan har yanzu anan
kowannensu yake zaune tareda iyalinsa hajiya
kubra ce kadai ke zaune a karamar hukumar
sumaila, shi abbansu kabeer yana zaune a
tsohuwar G. R. A, shi kuma abbansu nadiya
yana zaune a unguwar Rano Quarters,
Alh bashar yana da 'yaya guda hudu biyu maza
biyu mata, kabeer shine babba sai Fati wacce ke
binsa daga nan sai Muhammad sai autarsu
A'isha,
Tun lokacin da aka haifi nadiya yan uwa da
dangi keta tsokanar kabeer suna cewa an haifa
masa mata, haka itama nadiyan koda yaushe
dangi da yan uwa cikin tsokanarta suke suna
kiranta da matar kabeer, tun kabeer bai dauki
abun da gaskeba har yazo ya fara yarda da
abinda 'yan uwa ke fadi tsakaninsa da nadiya,
Ita kuwa nadiya lokacin ma bawani kwakkwaran
sani ta yiwa yaya kabeer dinba amma kowa
yazo gidan sai taji yana cewa "matar kabeeru"
duk sanda aka tsokaneta da wannan sunan kuka
take yi domin bata sanshi ba.....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*10*
~~~~Lokacin da nadiya ta dan fara hankali a
lokacin ne ta gane yaya kabeer sai ta tsinci
kanta cikin jin kunyarsa, haka kawai take jin
kunyarsa sam bata yarda suna haduwa dashi,
shikuma gidansu nadiya wurin zuwansa ne koda
yaushe kusan kullum sai yaje gidan tun bai fara
jin son nadiya ba har yaji yafara sonta lokacin
yana makarantar gaba da secondary wato
jami'a, da sonta yayi karatunsa yagama yafito
yazo ya kama aiki a wani kamfanin turawa dake
nan cikin garin rano,
A boye suke gudanar da soyayyarsu ba tare da
kowa ya furtawa dan uwansa ba amma su da
kansu sun yarda cewa soyayya suke yi.
***
Abban su kabeer da kanshi yaje yasamu abban
nadiya domin kabeer ya sanar masa yanda suka
yi da abbansu nadiya, gaba daya iyayen nasu
abin ba karamin dadi yayi musuba musamman
ma mahaifiyar kabeer domin tana mutukar
kaunar nadiya tun lokacin da aka haifeta, kullum
ita kenan aiken nadiya tazo tayi mata hutu
amma ko sau daya nadiya bata taba zuwaba sai
dai lokaci zuwa lokaci suna zuwa agaisa itada
mama dasu Amira,
Tunda mahaifiyar kabeer taji maganar auren nan
tarasa inda zata tsoma ranta dan dadi, nan da
nan tace sai afara tanadi.
Batun soyayyar nadiya da kabeer kuwa abinsu
gwanin sha'awa domin suna gudanar da
soyayyarsu cikin burgewa da kulawa da juna,
Koda yaushe yana gidan wai zai koya mata
karatu amma kuma ba karatun suke yiba
soyayyarsu kawai suke yi, yanzu itama nadiyan
ta tsunduma harkar karance karancen littattafan
hausa dan haka tana karuwa da abubuwa da
dama wadanda ada bata sansu ba.
Term din da suke ciki yana karewa ta shiga SS
3 a lokacin suka tafi aikin hajji ita da mama, ba
karamar tsaraba ta jibgowa yaya kabeer ba tayi
masa siyayya ta burgewa mai yawan gaske
musamman ma turaruka da jallabiyoyi kala kala,
Ranar da zasu dawo kabeer ne yaje airport
domin daukosu, tun karfe 6 yake airport din
amma jirginsu bai sauka ba sai misalin karfe 9
nadare,
Kallon nadiya kawai ya tsaya yi domin hakorin
da tasako ba karamin kyau yayi mata ba, ganin
mama nema ya hanashi magana,
Nan ya daukosu suka nufi gida, lokacin da
sukaje mama fita tayi tana rike da jakarta nan
itama nadiya ta yunkura zata fita kabeer yayi
saurin riketa,
"Hajiya nadiya ina kuma zakije bamu gaisa ba?"
Murmushi tayi saboda jin ya kirata da hajiya,
"Inye muga hakorin Allah yayi miki kyau"
Hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya, "haba
yanmata na mugani mana"
Dakyar ta iya bude bakinta yagani, hannunta ya
saki yana murmushi,
"Kinyi kyau sosai"
"Nagode yaya kabeer"
Tare dashi suka shiga cikin gidan yana rikeda
kayansu da ya dauko musu daga nan yayiwa
mama sallama ya tafi.
Tunda su nadiya suka dawo kuma kabeer yaci
gaba da zuwa gidan koda wanne lokaci,itama
mama yanzu ta hakura tana son auren saboda
ganin irin gata da soyayyar da Maman kabeer ke
nunawa nadiyan sannan dama kabeer yarone
mai biyayya
Nadiya taci gaba da zuwa makaranta sannan
soyayyarsu da yaya kabeer na tafiya yanda ya
kamata sai dai kuma yanzu nadiya ta dan fara
d'ar d'ar da auren yaya kabeer saboda wani
dalili,
Dalilin kuwa shine ayanda ta fuskanta yaya
kabeer yanada yanmata masu yawan gaske, tun
abin baya damunta har yafara damunta domin
akwai lokacin da suka fita dashi ita da waleeda
ta rakasu zai kaita shopping lokacin da sukaje
shopping din suna gab da kammalawa wata
budurwa tazo anan yatafi wurinta ya barsu
nadiya, tun daga irin tsaiwar da sukayi da
budurwar zaka fuskanci cewar saurayi da
budurwa ne baya ga haka kuma sai kwantar da
murya yake yi duk da dai nadiya bata jin abinda
yake fada amna tagane cewar hakuri yake bawa
yarinyar, anan ya kirgo kudi ya bata yadawo
wurinsu nadiya wacce tagama shakar bacin rai,
Ko takansa nadiya bata bi ba taja hannun
waleeda suka fita sai shine ya dauko kayan da
suka siya bayan yabiya kudin,
Motarshi ya bude ya saka kayan sannan su
nadiya suka shiga suka zauna, baiyi magana ba
itama nadiyan haka nan yaja motar suka tafi,
Tana kallonsa anata kiranshi awaya yana
katsewa daga baya kuma ya dauka yace zai kira
anjima,
Wani haushine ya cika mata ciki domin koda
yaushe ahaka yake ayita kiransa awaya yana
rejecting ko kuma ya dauka yace zai kira ko ba
afada mata ba tasan cewa yanmata ne ke
kiransa domin yaya kabeer kyakkyawan namijine
mai jida kyau da kuruciya sannan ga abin hannu
domin aikin da yake yi da turawa yasamu nasibi
sosai acikinsa sannan gashi da ilmi wannan
dalilin ne yasa yasamu karbuwa sosai ake
damawa dashi har kasashen waje suke fita aiki
shiyasa kowacce mace zata yi burin mallakarsa,
Babu wanda yayi magana acikinsu har sukaje
gida amma kafin su karasa an kirashi awaya yafi
sau 30 wanda kusan duk kiran na yanmata ne,
Waleeda yabawa kayan ya rike hannun nadiya
tamau tayadda bazata iya kwacewa ba, sai da
yaga waleeda ta fita sannan ya sawa motar lock
ya kalleta....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*11*
~~~D'auke kai nadiya tayi ranta fal da takaici
ita yanzu jin yaya kabeer take yafara fita aranta
saboda kule kulen yanmatanshi, baya minti biyar
sai mace ta kirashi sannan takasa gane
alakarshi da wadannan tulin yanmatan,
"Yan matanah.." Muryarshi ta katse mata
tunanin da takeyi,
Sam kin juyawa ta kalleshi tayi maimakon
hakama sai kokarin kwace hannunta da ya rike
tafara yi,
"Juyo mana kiji abinda zan fada miki yanmata
na"
Nan dinma dai sake kawar da kanta tayi bata
juya ta kalleshi ba ita bakin cikin da takeyi shine
yanzu saura yan watanni kadan tayi candy
kuma da zarar tagama school bikinsu za ayi ita
dashi to haka zaije yana yimata wadannan kule
kulen yan matan sai kace wani marar aji?
"Haba nadiya ta, ya kamata ki kasance mai
yimin uzuri da afuwa akoda wanne lokaci, dan
Allah ki saurareni kiji.."
Jin ya hadata da Allah yasata juyawa ta
kalleshi,
"Ina jinka"
"Nadiya nifa wadda kika ganni da ita ba
budurwata bace kanwar abokina ce, abokin
nawa ma yanzu ba a kasar nan yakeba to shine
tace wai in dan taimaka mata saboda sha'anin
karatu dalilin dayasa kenan kika ga na dauki
kudi nabata amma tunda bakiji dadiba kiyi
hakuri.."
Shiru ta danyi na dan wasu sakanni tana nazari,
nadiya yarinyace mai wayo da basira da kaifin
kwakwalwa shi kansa ya shaida haka sannan
gata da saurin gano abu shiyasa wani lokacin
har tsoron yimata karya yake yi domin atake
zata gane kuma tafada masa sai dai kawai yaji
tace "yaya KB nagane logic din.."
Dagowa tayi ta kalleshi suka hada idanu abinda
bai taba faruwa ba domin tsananin kunyarsa da
takeji baya barinta ta iya hada idanu dashi,
"Yaya KB idan har wannan budurwar kanwar
abokinka ce baka da alaka da ita meyasa zaku
ware ku koma wuri daya bazaku gaisa ku
tattauna agabanmu ba?
Meyasa zaku rinka maganganu kasa kasa
alamun bakwa son kowa yaji abinda kuke cewa
ciki har dani wacce kake shirin zama MIJINA
SIRRINA, ni aganina ai duk wani abu wanda ya
shafeka nima ya shafeni babu boye boye a
tsakaninmu.."
"Hakane nadiya, amma kisani komai yana son
sirri, yanzu yarinyar nan da agabanku ne bazata
iya rokona kudin ba saboda bani kadai bane.."
"To amma da kuka gama yaya kabeer meyasa
ko gaisawa baka kawota munyi ba a matsayina
na kanwarka mai shirin zama matarka sirrinka?"
"Ohhh nadiya kin fiya rigima, ki yarda dani
wannan yarinyar banida alaka da ita"
"To naji nayarda amma masu kiranka awaya tun
dazu sukuma suwaye?"
Sumar kanshi ya shafa kafin yabata amsa "yan
companynmu ne"
"Yan campanynku ne amma shine ka gagara
daukar wayar saboda ina wurin?"
"Amma dai ai kinga driving nake ko"
Murmushin takaici ta danyi saboda har yanzu
bata yarda da abinda yafada ba, "yaya kabeer
gaskiya nidai bana jin dadin wannan abinda
kakeyi, idan har zaka aureni to meye naka na
kule kulen yanmata? Nasan dama tunda kana da
kyau da kudi yanmata dole zasu soka to amma
ai wannan ba yana nuna cewar ka sakar musu
fuska kayita kulasu ba.."
"Wai nadiya yaushe muka fara yar haka dakene?
Kodai wasu kika samu suke zugaki awaje?"
"Ko kadan ba maganar zuga bace yaya kabeer
maganace ta gaskiya nidai bana son wannan
kula yanmatan da kakeyi"
"Shikenan naji kuma zan kiyaye, shikenan?"
"Shikenan, bude min zan fita"
Juyo da fuskarta yayi yana murmushi,
"To ai baki tabbatar min da cewa mun shirya din
ba"
"Mun shirya karka damu"
"To sai yaushe?"
"Sai da daddare idan kadawo"
"To kiyi min dan murmushi nagani mana"
Yanda yayi maganar ne yasata yin murmushin
ba tareda ta shirya ba, nan ya bude mata kofar
ta fita ta shiga gida, ko mama bata fadawa
abinda ya faru ba tabar maganar aranta shi
dinma da yadawo da daddare bata nuna masa
ba.
Kwana biyu da faruwar haka yace ta shirya zai
zo ya kaita wurin mama su gaisa, nan ta shirya
taci ado cikin wani swiss material blue, tasa
mayafi da takalmi blue da jaka, ba karamin kyau
tayi ba nan yazo suka tafi tareda su husna
wadanda zasu rakata dama ka'idar gidan duk
inda zataje to dasu husna take tafiya ko walida
idan kuma basa nan to Amira ko amir acikinsu
wani zai rakata,
Yana driving suna hira har suka hau titin da zai
sadasu da unguwar, suna karya kwana sukaga
wasu yan mata tsaye a bakin titi su biyu sunci
uwar kwalliya, har ya dan gotasu sukaji
maganar daya daga cikin yan matan tana tsayar
dashi,
"KB, kb, kb.."
Packing yayi agefen titi ya dubi nadiya, "ina
zuwa 2 minutes"
Bata cemasa kala ba har yafice tana ganinsu ta
cikin mirror shida yan matan sai dariya sukeyi,
shida yace tabashi minti biyu saida ya shafe
fiyeda minti 15 awurinsu nan ran nadiya yabaci,
Dakyar suka rabu da yanmatan nan yadawo
cikin motar yana shafa sumar kanshi,
"Yanmata na kiyi hakuri nasan nayi laifi amma ki
yafe min kannen wani abokina ne.."
Ko ci kanka bata cemasa ba saboda shiru ma
amsa ce da haka suka karasa gidansu, tun da
mama taji sallamar nadiya tafara yimata lale
sannu da zuwa, ba karamin dadi nadiyan tajiba
domin mama tana mutukar kaunarta kamar zata
goyata duk lokacin data ganta,
Kafin wani lokaci ancikata da kayan cima kala
kala, mama sai janta take da hira tana
tambayarta mutanen gidansu su mama dasu
Amira,
Duk kannensa sai da sukazo suka gaggaisheta
bayan duk sun girmeta babu sa'anta A'isha ce
ma dai zasu danyi kusan sa'anni da ita amma
daga Muhammad har fati sun girme mata sosai,
Kasa kasa ta kalli kabeer nan taga yamaida
hankalinsa kacokan akan wayarsa wanda ko ba
afada mata ba tasan chaten yake yi....
*_Ummi Shatu_*
[7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*12*
~~~Wani b'acin raine ya sake rufe nadiya amma
bata bari kowa ya fahimta ba, nan ta zauna
agidan har sai da sukayi sallar mangariba
sannan tayiwa mama sallama cewar zata tafi
tareda fito da sabulun wanka wanda ta kawowa
Maman ta bata,
"Ah haba nadiya harda wahala? Ai nice zan baki
bake zaki baniba, haba nadiya keda ba
ma'aikaciya ba bamai Sana'a ba kuma shine
harda dorawa kai wahala?"
Maman tafada zuciyarta cikeda murna, cikin
hanzari ta shiga daki ta dauko wata leda ta
bawa husna tana fadin,
"To ga wannan babu yawa, agaida mama
dakyau dasu Amira nagode madalla Allah yabar
zumunci, Allah ya nuna mana wannan lokaci
yasa ayi damu, agaida Alhaji dakyau.."
Godiya nadiya tayiwa mama sannan tafita, wani
abin haushi kuma tana fita taga yaya kabeer
tsaye ajikin motarsa shida wata budurwa wacce
bata santa ba,
Kamar tasaka ihu haka nadiya taji ita sai yanzu
take gane yaya kabeer, yanzu take fahimtar
koshi waye, mutumne shi mai yawan kule kulen
yanmata shiyasa har tafara kokarin janye
zuciyarta daga gareshi domin gaskiya bazata
juri wannan halayyarba,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa wurin
ta bude gaban motar ta shiga tana kallonsu ta
cikin glass din motar,
"Shikenan zee sai munyi magana kigaida gida"
Yafada tareda bude kofar motar ya shiga,
"Wannan wata yarinyace acan gaba damu kadan
to kwana biyu bamu haduba sai yau shine muka
tsaya muka gaisa"
Yace da nadiya yana kokarin tada motar,
Ko kala nadiya bata furta masa ba saboda abin
yana cin zuciyarta sosai, duk tulin yanmatan
nan na yaya kabeer ko mata goma aka bashi
damar ya aura tasan sai wasu dole sunyi saura
to bare mata hudu kacal aka halasta masa,
Zuciyarta kamar zata fashe dan bacin rai sukaje
gida, fitowa tayi zata shiga cikin gida yayi saurin
shan gabanta,
"Wai nadiya dan Allah meyasa kike son sauyawa
ne daga yanda nasanki zuwa wata tadaban?
Meyasa kike son yiwa soyayyarmu illah? Dan
Allah nadiya kidaina bata ranki akan duk wata
mace da zakiga na tsaya da ita, ki dauka afadin
duniyar nan babu wata mace sai ke, kisawa
ranki cewar kowacce mace abayanki take, ke
kadai nake gani a matsayin matar aurena dan
haka ki daina damuwa kina bata ranki"
"Naji.." Shine kawai abinda nadiya tafada ta
gegeshi zata wuce nan yayi saurin janyota
wanda har sai da tafada jikinsa batare da ta
shirya ba nan ya riketa yaki sakinta,
Jinta tayi cikin wani irin sabon yanayi saboda
tunda take da yaya kabeer haka bata taba
faruwa a tsakaninsu ba tasan dai sau mafiyan
lokuta yana rike mata hannu ko yaja hancinta
ko kuma yaja mata kunne amma bai taba gwada
rungumeta ajikinsa ba sai yau,
Jin tana neman shagala yasata yin hanzarin
zamewa,
"Ai nace maka na hakura ko?"
"To ai gani nayi kamar ba har zuciyarki ba
shiyasa"
Murmushi tayi masa irin wanda zai tabbatar
masa da cewar da gaske ta hakuran, nan ya
karasa sakinta ta shiga gida, tun daga lokacin
maganar ta wuce awurinta domin adaren ranar
ma raba dare suka yi suna hira awaya.
Haka komai yaci gaba da gudana batare da
nadiya ta sake nunawa kabeer damuwarta ba
saboda bata son yasata acikin jerin mata masu
korafi da rashin hakuri, koda yaushe tana lura
dashi domin tana son ganewa ko ya sauya ko
kuma yana nan kamar da,
Kamar da din kuwa yake babu abinda ya sauya
na daga kule kulen yanmatan da yake yi, wayo
tayi masa ta karbi wayarsa aro tace zata kira
kawarta nan ta shige dakin mama taje ta fara
duban wayar ai kuwa sai da taji kamar zuciyarta
zata buga domin bacin rai saboda massages ne
na yanmata, da hotunansu kaca kaca,
Shi kansa kabeer sai da jikinsa yabashi cewar
nadiya bincike ta tafi yimasa awaya bawai
kawarta zata kiraba kamar yadda tace nan ya
tashi ya tsaya yana jiran fitowarta Amma shiru
sai da ta shafe fiyeda mintuna talatin adakin
mama tagama duba wayarsa ciki da waje
sannan ta fito, da mamakinsa sai yaga fuskarta
asake babu alamun damuwa anan ya danji
dama dama saboda watakil zarginsa bai zama
gaskiya ba kila ba bincike tayi masa a waya ba,
Bashi wayar tayi suka dan taba hira ya tafi,
yana tafiya nadiya taje tasamu mama wadda ke
kitchen tana tuka tuwo, tsayawa nadiya tayi
abayan mama,
"Mama.."
"Na'am.."
"Mama nafasa auren yaya kabeer"
"Saboda me?" Mama ta tambayeta cikeda razani
bayan ta juyo tana kallonta,
"Mama haka kawai"
Rufe tukunyar mama tayi ta juyo tana kallon
nadiya har na tsawon wani lokaci,
"Nadiya lafiyarki kalau kuwa? Anya babu abinda
yake damunki?"
"Mama lafiyata lau, babu abinda yake damuna,
nidai kawai yanzu bana son yaya kabeer abar
maganar auren nan kawai ni yanzu karatu ma
nake sonyi ina gama secondary zan tafi jami'a"
Tsayawa kawai mama tayi tana kallonta cikeda
mamaki domin sam nadiya bata taba nuna
sha'awar ta na cigaba da karatu ba sannan tun
farko ita ta nace ta nuna kabeer takeso shiyasa
itama Maman har ta hakura ta amince ta mara
mata baya ta yadda take tayata to amma abin
tambayar shine yanzu wanne abu kabeer yayi
mata har take neman canja ra'ayi akansa....?
*_Ummi A'isha_*
[7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*13*
~~~Jan hannunta mama tayi zuwa cikin dakinta
suka zauna agefen gado,
"Nadiya idan da wani abu ki fada min saboda
bazai yiyu haka kawai babu dalilin komai ki
sauya ra'ayinki akan kabeer ba bayan kuma ada
babu wanda kikeso kamarsa,
Idan kawayene suke zugaki to ki sani zasu kaiki
ne kawai su baroki, idan kuma kuruciyace ke
daukarki to kisani zaki cuci kanki wanda bazaki
gane hakan ba sai nan gaba zaki fahimci cewar
kin yiwa kanki illah domin Allah ya baki dama
ya zabar miki miji nagari wanda ya dace dake
amma kinki amincewa,
Idan kuma fada kukayi dashi to ki sanar min sai
nakirashi naji menene ba'asi daga karshe na
daidaitaku domin daga ke har kabeer ni dayane
awurina babu banbanci.."
Tunda mama tafara wannan maganar nadiya
tafara zubar da hawaye wanda bata san dalili
ba, jin mama tayi shiru yasata yin magana cikin
kuka,
"Mama nidai kawai yanzu bana sonsa ne wallahi
nafasa aurensa.."
"Nadiya kin taba ganin anfasa aure babu dalili?
Karfa ki manta yau saura watanni biyu kacal ki
kammala karatunki kuma kin sani kina gamawa
ko wata daya bazaki kara agidan nan ba za a
aurar dake saboda kece kika nuna haka tun
farko, tun da fari ke kika nuna aure kikeso idan
kin gama secondary har abbanki ya ji ya kuma
yarda dan haka yanzu bakida bakin da zakice
kin fasa"
Kukan nadiya ne ya karu,
"Mama wallahi nidai nafasa auren yaya kabeer,
ni bana sonsa yanzu"
"Ai nadiya ko bakya son kabeer yanzu tunda ada
kin soshi dole ki aureshi, idan har abbanki ma
yaji wannan maganar to kisani sai ranki ya baci
dan haka ina mai shawartarki da kiyi gaggawar
watsi da wannan hudubar ta shaidan.."
Mama na kaiwa nan ta mike tayi ficewarta
saboda ita atunaninta kawaye nadiya tasamu a
makaranta suke hure mata kunne dan haka tayi
komawarta kitchen taci gaba da aikinta tabar
nadiya nata faman kuka,
Har mama tagama tuwon abba yadawo nadiya
na daki tanata faman kuka, sai da abba ya
tambayi mama cewar ina nadiya sannan ta tuna
ashe tabarta adaki nan ta tashi taje dakin nata
tana shiga ta sameta tanata kuka bata daina ba,
"Ke har yanzu kukan kike yi? To kici gaba dayi
karki daina". Mama tafada tareda sake fita
takoma wajen abba,
Tun daga nan nadiya ta sauya kwata kwata,
gaba daya haushin yaya kabeer takeji idanma
yazo gidan bata saurararsa har sai idan mama
na wurin, ko waya yanzu ta daina yi dashi
idanma ya kira bata dauka dama kuma wayar
mamace ita bata da waya har yanzu,
Gaba daya abinda ke faruwa Mama tasani
amma har yau shi abba bai saniba shima kuma
kabeer gidansu basu saniba, yayinda ita kuma
nadiya tafara rubuta jarabawar fita domin har
sun fara practical,
Lokacin da abba yaga sun fara practical tuni
yabada order din gado tun daga kasar Italy,
kaya aka kawo shiryayyu kama tun daga kan
gado, kujeru, dining table da sauran kayan
kawata gida hatta kayan kitchen an siyo, nan
hankalin nadiya ya tashi saboda ganin
wadannan kayan dan haka ta saka mama agaba
tana yimata kuka akan ita wallahi yanzu bata
son yaya kabeer karatu zatayi, da abin ya ishi
mama sai taje ta fadawa abba tace ga nadiya
can tasata agaba tana yimata kuka akan wai
bata son aure karatu take so,
Amir abba ya tura ya kirata ta shigo idanuwanta
jajur alamun tasha kuka ta koshi,
"Nadiya meyake faruwane? Naji mamanki tace
kinzo da sabuwar magana"
"Abba ni yanzu nafasa auren yaya kabeer karatu
nakeso"
"Ai nadiya ko agidan mijinki zaki iya yin karatu
har kikai matsayin professor dan haka kiyi
hakuri ki kwantar da hankalinki kinji, shi aure
baya hana karatu sannan karatu baya hana aure
za a iya hada duka biyun, kabeer yayanki ne ba
bare bane dan haka bazai cutar dakeba"
"Abba ni kawai auren ne yanzu bana so"
"Nadiya kefa da kanki kika kawo min kabeer
kikace shi kikeso nikuma nabashi ke tareda
yimasa alkawarin aure sai yanzu kuma yaji na
canja magana? Ai aure tsakaninki da kabeer
babu fashi, insha Allah kina gama makaranta da
sati biyu zan daura miki aure akaiki dakin mijinki
kamar yanda nayi alkawari ko bayan raina kar
afasa"
Hawayene suka cigaba da ambaliya akan
kumatun nadiya nan Abba yace tatashi tatafi,
tashi tayi tafita taje taci gaba da kukanta
adakinta,
Tsakanin d'a da uwa sai Allah nan itama mama
taji hankalinta yatashi dan haka tabi bayan
nadiya, adaki ta isketa tana kuka dan haka
tazauna akusa da ita ta dafata,
"Nadiya kiyi shiru kinji, ki saurareni kiji abinda
zan fada miki, tun farko nadiya kece kikace
kabeer kikeso wanda nikuma banso hakanba
saboda wasu abubuwa da na hango amma
ganin hankalinki ya karkata akansa yasa na
amince saboda ki samu abinda kikeso, to yanzu
idan muka Mara miki baya muka hanaki auren
kabeer duniyace zata zagemu, shi kansa abbanki
indan har na goya miki baya zaiga laifina, zaice
saboda kabeer ba dangina bane shiyasa nake
kin aurenku dashi,
Dan haka ki nutsu kiyi hakuri kibarwa Allah
ikonsa kedai kawai kici gaba da addu'a kinji"
Tashi zaune nadiya tayi tafara share hawayen
fuskarta tana kallon mama......
*_Ummi Shatu_*
[7/16, 7:30 AM] Ummi A'isha🏻: [7/16, 7:29 AM]
Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Gaisuwa da babbar murya ga masoyan
mijina sirrina ina gaisheku aduk inda kuke,
sannan ina taya kawata Batool Mamman
marubuciyar littafin al'adun wasu murnar samun
karuwa da mukayi, Allah ya raya mana boy cikin
addinin islama yasa yayiwa addinin Allah
hidima.._
*14*
~~~Kallon mama tayi bayan ta share hawayen
dake gudana akan fuskarta, sannan ta bude baki
dakyar tace,
"Shikenan mama naji nayarda zan auri yaya
kabeer kamar yadda kukeso.."
"Ai bamu mukeso ba nadiya, kece kike so bawai
auren dole zamuyi miki ba, yau da ace bakece
kika fito kika nuna kabeer a matsayin wanda
kikeso ki aura ba to da ko yace yana sonki
bazan goyi bayan abashi aurenki ba mutukar
bakya sonshi, to amma BAKIN ALKALAMI ya
bushe dan haka kiyi hakuri ki rungumi kaddara
saboda kabeer shine mijinki..."
Jijjiga kai nadiya tayi, "to mama, amma gaskiya
yaya kabeer yanada wata dabi'a wacce kowacce
macen kirki bazata so mijinta ya kasance haka
ba, yaya kabeer shegen son kula yan matanshi
yayi masa yawa baya minti biyar sai kinji mace
ta kirashi nikuma abin yana bani haushi"
Dafa kafadarta mama tayi tana murmushi,
"Haba nadiya, yanzu dama akan wannan zaki
fasa auren kabeer? Ai wannan duk abune mai
sauki da zarar kunyi aure duk zai manta da
wadannan yan matan suma kuma zasu daina
saurararsa su daina kulashi indai sukaji cewar
yayi aure, wannan ba komai bane face halayya
da dabi'un matasan zamani yawanci haka suke
sai kiga wani ma yatara yan mata fiyeda goma
kuma kowacce yana ikirarin cewar budurwarsa
ce sonta yake.."
Murmushi nadiya tayi na karfin hali, itama
Maman murmushi tayi ta mike tsaye amma duk
maganganun nan tayi sune kawai saboda ta
kwantarwa da 'yarta hankali,
"Ki saki ranki kinji karki sake nuna masa
damuwarki ko bacin ranki akan haka, sannan
tun daga yanzu ki zama mace mai daukar
mijinta a matsayin sirrinta wacce bata fallasa
asirin mijinta, ki koyi rufawa miji asiri kinji,
bawai komai zaka rinka fada wanda ya shafi
mijinka ba, shi aure da kike ganinsa nadiya
zallar hakurine acikinsa dole sai ka koyi hakuri
ka ji kaki ji kagani kaki gani sannan dole sai ka
zama mai kawaici da mantuwa kar kayita tara
laifukan da ake yi maka mutukar zakayi haka to
bazaku taba zama lafiya da abokin zamanka ba
domin koda yaushe mai laifine awurinka.."
"To mama"
Juyawa mama tayi ta fita, tabbas maganganun
mama sun saukar mata da nutsuwa da
kwanciyar hankali nan da nan ta nemi
damuwarta ta rasa nan tafara harkokinta kamar
yadda ta saba ta dauko comprehensive book
dinta ta bude domin karantawa bayan taje sunci
abinci da mama da kannenta,
Waleeda ce ta shigo da gudu tana rikeda wayar
mama a kunnenta,
"Yaya kabeer ga anty nadiyan.."
Karbar wayar tayi tana murmushi,
"Yaya KB"
"Ranki ya dade, haka akeyi kuma gaba daya sai
kibi ki manta da kabeer dinki? Anya kuwa
kinyiwa yayanki halacci?"
"Haba yaya kabeer ni na isa, waneni da
mantawa da yayana, mijina sirrina..."
Yanda tayi maganar ne yasashi yin dariya,
"Kajita kamar gaske alhalin kin manta dani
asalima fushi kikeyi dani bayan nikuma baki
sanar dani laifina ba"
"Yaya kabeer kenan wannan maganar ai tawuce
so karma kace zaka tadata.."
Ajiyar zuciya ya saki mai mutukar karfi,
"Wato nadiya nikaina ban san irin son da nake
yimiki ba shiyasa da kika juya min baya gaba
daya hankalina ya kasa kwanciya.."
"Ayya yaya kabeer ai nace maka yawuce ko"
"Nagode matata, yanzu me kike shirya mana
nadangane da hidimar bikinmu?"
"Yaya kabeer ai shiri yana wurinka sai yadda
kace.."
"A'a yadda kikace dai gimbiya.."
Murmushi tayi saboda yaushe rabonta da su
zauna suyi waya ta minti biyu da yaya kabeer,
"Yanzun me kakeyi ne?"
Kin ganni adakina na tura A'isha taje ta kawo
min abinci.."
"Allah sarki gwauro.." Tafada cikin tsokana,
"Gwauraye dai har dake ai ko ke ba gwauruwa
bace?"
"Gaskiya ba ita bace.."
"Nima ai ba gwauron bane tunda inada matata
nadiya saura lokaci kankani ta zama mallakina
nakaita gidana, nakaita dakina...."
Katseshi tayi ta hanyar cewa,
"To ya isa yaya kabeer basai ka lissafa ba"
Dariya yayi, "shikenan tunda kin hanani fadar
sirrin zuciyata.."
"Ba hanaka nayi ba amma basai ka fada ba dai,
yanzu kabani labarin abinda kake shirya mana
na biki"
Sun dade tare awaya suna tattaunawa har
zuwa wani lokaci, koda gari ya waye ma shine
yazo ya kaita makaranta domin ranar tanada
paper,
Daga nan komai yaci gaba da tafiya yadda
akeso domin sun shirya yanzu maganar bikinsu
kawai suka saka agaba,
Kamar da yanzun ma koda yaushe kabeer yana
kan hanyar zuwa gidansu nadiya,
Ita kuma nadiya yanzu gaba daya kanta ya
dauki zafi saboda jarabawar da takeyi gashi gida
sai shirye shiryen biki ake tayi mama kullum
cikin fita take tana zuwa siyayyar abubuwan da
ba asiya ba,
Suma gidansu kabeer din ba abarsu a bayaba
wurin shirye shiryen bikin domin har sun
kammala hada lefe akwatuna bakwai masu
tsananin kyau da tsada,
Saura paper biyu nadiya ta gama jarabawarta
aka kai lefenta, sai kawai dawowa tayi daga
makaranta ta tarar da kaya makota sun shiga
sunata gani,
Mamakine ya kamata saboda yaya kabeer ne fa
ya daukota daga makaranta ya kawota gida
amma shine bai fada mata ba?
Ai mutane naganinta suka hau guda suna cewa
"ga amarya ga amarya.."
Ko takan kayan bata bi ba tawuce daki tana
kokarin cire takalminta,
Dakin mama taje ta dauki wayarta ta kira
kabeer,
"Yaya kabeer shine ko ka fada min ankawo
kayan nan ko? Sai kawai zuwa gida nayi natarar
mutane na kallo"
"Yi hakuri mantawa nayi, haba yanmata na ai
kin san dai haka kawai bazan ki fada miki ba"
"Shikenan dai nagode"
Katse wayar tayi tatafi taje tayi wanka ta shirya,
bata samu damar ganin kayanba sai da dare
yayi bayan ankaiwa abba yagani,
Komai da aka saka acikin akwatinan sunyi mata
domin babu na banza gaba daya masu tsadane.
Haka aci gaba da shirye shirye shiryen biki,
musty abokin yaya kabeer shine babban abokin
ango dan haka shine akan komai,
Ayanda angwayen suka tsara za agudanar da
kamu da walima sai dinner aranar da aka daura
aure bayan ankai amarya dakin mijinta, ita dai
nadiya duk abubuwan da suka shirya bata da
matsala domin yanzu bikin saura sati biyu
saboda yaune zata zana jarabawarta ta karshe,
Kayan taya murna sosai yaya kabeer ya hado
mata su greeting card, calendar, memo, key
holder, handkerchiefs da sauran kayayyaki
tududu wanda har mama sai da tayi masa fada
tace shi da hidimar biki take gabansa meya
aikeshi wannan aiki,
Aranar da su nadiya suka gama jarabawar tun
daga ranar kawayenta yan class dinsu suke
zuwa su rakata rabon iv card domin har yaya
kabeer ya buga ya basu,
Shirye shiryen da ake gudanarwa agidansu
nadiya sai wanda yagani domin gaba daya
angyara gidan anyi sabon fenti abba ya zubawa
mama sabbin furnitures nadiya nagani ta hau
dariya tana cewa,
"Mama Ashe kema kin zama amaryar tunda
harda sabbin kaya"
"Ahh nazama kam, gani uwar amarya sannan
kuma amarya.."
Kullum musty ne ke kaisu rabon iv card din
itada kawayenta har suka kammala nan kuma
tafara sintirin zuwa gyaran jiki wurin kawata
KHADIJA SIDI domin kwararriyace wurin fito da
amare,
Cikin kwana biyu kacal da fara gyaran jikin
nadiya tayi kyau tayi sumul fatarta ta sake
gyaruwa ta dawo kamar bayan kwado dan
tsananin laushi da taushi....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/16, 7:29 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*UMMI A'ISHA*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*15*
~~~A daren ranar kabeer yazo gidan, ganin
nadiya yayi gaba daya ta sauya masa kamanni
saboda tsananin kyawun da fatar jikinta tayi,
gyaran jikin ba karamin karbarta yayiba ya fito
da ita sosai sai kace balarabiya,
"Yan matana.. Irin wannan kyau haka, ai da
ahanya na hadu dake sai kiwuce nawuce domin
bazan iya ganeki ba... Wow"
Murmushi nadiya tayi, "kai yaya kabeer harda su
tsokana haka"
Sajen dake kewaye afuskarshi ya shafa yana
cigaba da kallonta tacikin hasken kwan lantarkin
da ya haskesu,
"Allah ba wasa ba kin sauya min gaba daya,
kinyi wani irin kyau Wanda ada banma san kina
dashiba sai yanzu nagani"
"Ohhh yau dai yaya kabeer tsokana yakeji dan
haka bari nayi shiru nabarshi yayi tsokanarsa
yagama"
"A'a babu wani tsokana fa"
Dariya tayi ta kalleshi, "yawwa namanta ban
fada makaba su zarah maina suna nemanka
saboda wai hall din da kukace za ayi dinner
acan ba lallai ya isa ba.."
"Jama'ar taku har nawace da bazai isaba? Zai
isa harma yayi saura kudai kawai ku zama
ready.."
"Shikenan to zamu zama ready din kamar yadda
kace"
Murmushi yayi ya dan matsa kusa da ita, "har
kin fara kamshin amarcin ne? Naji sai wani
rikitaccen kamshine yake faman tashi.."
Juyawa tayi tawuce tana dariya tana fadin "yaya
kabeer kaganka ko... Hmmm"
Tun daga wannan ranar basu sake haduwa
sunyi mintuna biyar atare ba saboda gaba daya
abubuwa sunyiwa kowannensu yawa
musamman ma kabeer,
Tun ana saura kwana biyu biki gidansu nadiya
yafara cika da yan uwa musamman ma yan
uwan mama wadanda suka zo daga kura domin
mama haifaffiyar garin kura ce,
Aranar musty yazo yakai su nadiya kunshi da
saloon, basu suka dawo gidaba sai dare lokacin
har yan jere sun dawo sunata faman koda gidan
da irin daular da aka ajiye aciki,ita dai nadiya
najinsu batayi koda tari ba saboda dama kabeer
ya nuna mata gidan awaya lokacin da yayi yayi
da ita suje tagani taki sai ya dauko mata hoton
gidan awayarsa yakawo mata tagani, gida kam
ya tsaru babu karya kamar a turai domin gidane
irin tsarin na turawa.
Saura kwana daya afara shagalin biki mahaifiyar
kabeer ta aikowa da nadiya wani kayataccen
leshi mai tsadar gaske a dinke tace tasa ranar
kamu, ita kam nadiya koda yaushe aranta tana
jin cewar tayi sa'ar uwar miji mai sonta da
kaunarta,
Ranar kamu ba karamin kyau nadiya tayiba
tafito sosai domin wani leshi ne ajikinta golden
da gwaggwaro shima golden sai takalmi da jaka,
Nadiya tayi kyau iya kyau nan aka kwashesu
zuwa wani hall wanda acan za ayi shagalin
kamun, daf da za atashi angwaye suka zo nan
kabeer yakasa rufe bakinsa sai fara'a yaketa
faman zabgawa yasha wani yadin boyel brown
da hula sai kamshine yake tashi ajikinsa, hotuna
kam da video sun shasu babu adadi har su
kabeer din suka tafi nan taron ya watse kowa
ya koma gidansa yayinda su nadiya da sauran
dangi sukuma suka koma gida.
Washe gari da misalin karfe 2 aka daura auren
kabeer da nadiya akan sadaki dubu 30 kamar
yanda waliyyinsa ya bayar wato mahaifin
nadiya, shikuma mahainsa yayiwa nadiya
walinci, ana tashi daga wurin daurin aure suka
wuce wurin walimar da abokanshi suka shirya
masa nan akaje aka debo su nadiya ita da
kawayenta,
Yau dinma nadiya ba karamin kyau tayiba cikin
wani jan leshi gashi an lullube jikinta gaba daya
da lifayya wadda daga ganin adon dake jikinta
kasan naira tayi kuka,
Wa'azi aka gudanar awurin walimar sannan
akaci aka sha, ango shima ba abarshi abaya ba
wurin zuba kyau domin wata lafiyayyar farar
shadda yasha wadda taji dinki mai tsada,
Karfe hudu aka tashi daga walimar aka maida
su nadiya gida, suna zuwa gida suka tarar da
har anfara harhada kayan da za akai nadiya
dasu domin abba yace ana yin sallar mangariba
aje akaita,
Ai kuwa nadiya najin haka sai kuka nan mama
tazo ta kama hannunta suka nufi falon abba,
Nan suka zauna tanata gursheken kuka,
"Nadiya kiyi hakuri kidaina kuka kinji domin
kowacce mace hakace take faruwa da ita
arayuwarta mutukar wannan ranar tazo, nidai
abinda zance miki shine kiyi hakuri kibi mijinki
sau da kafa kiyi masa biyayya,ki zama mace
tagari mai rufa asirin mijinta, ina miki addu'ar
Allah yabaki rayuwa mai dadi agidan mijinki
yasa ta silarshi ki shiga aljanna, Allah yayi miki
albarka"
"Amin amin, sannan kuma banda kazanta
nadiya, banda rashin kunya, banda biye makota
ana gulma, banda tona asirin miji, duk abinda
yasaki kiyi abinda ya hanaki ki hanu, Allah yayi
miki albarka yabaki yaya nagari" mama ta dora
bayan abba yagama, nan mama ta kamata ta
maidata inda ta daukota, da kuka da komai
nadiya tasamu tayi wanka ta fito ta shirya
lokacin har yan daukar amarya sunzo dan haka
babu bata lokaci aka fita da ita aka saka a mota
aka nufi gidan mijinta da ita lokacin ba afi karfe
7 nadare ba,
Suna zuwa kuma aka fara shirye shiryen tafiya
dinner, angama shiryata kenan ango ya shigo
cikin wani sky blue din yadi marar kauri, itama
kuma dama shigar blue tayi nan suka bada kala,
Sai faman murmushi yake yimata amma ita duk
idonta yayi ja saboda kukan da tasha gwanin
ban tausayi, hannunta ya kama suka fita yana
yimata magana ahankali,
"Menene yasaki kuka yanmata na? Ko kukan
rabuwa dasu mamane? Kiyi hakuri kinji ai baku
rabuba zaki rinka zuwar musu.."
Ita nadiya dai bata yi magana ba saboda tasan
tana bude bakinta to fashewa da kuka zatayi
dan haka taja bakinta tayi shiru,
Iya kawatuwa wurin dinner din ya kawatu yasha
decoration blue colour,nan aka fara gudanar da
abinda za ayi gadan gadan,
Daga nadiya har kabeer sunsha ruwan nairori
wasu ma masu yimusu likin ita nadiya ba
saninsu tayiba kawai dai tasan gayyar kabeer ce
musamman ma wasu yanmata wadanda suka
daddage sunata zubar musu da ruwan nairori,
Karfe 12 aka tashi daga dinner din aka kwashi
mutane zuwa gida, nadiya ita da kawayenta
suna motar musty shine yakaisu gida yana zuwa
yace kawayen su fito zai mayar dasu gidansu
nan suka yi masa caaaah wai bazasu tafiba sai
anbasu kudin siyan baki, cheque din 20,000 ya
rubuta musu yabasu sannan suka yarda suka
hakura suka fito bayan sun gama tsokanar
nadiya wacce ke lullube ta tukunkune agefen
gado tana risgar kuka...
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/16, 7:29 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*16*
~~~Sai da akayi kamar mintuna ishirin da
tafiyarsu zarah maina tafara jiyo karar mota
alamun yaya kabeer ya karaso gidan,
Sake gyara mayafinta tayi ta lulluba tana
sauraren shigowarsa minti kadan kuwa sai gashi
ya shigo hannuwansa dauke da ledoji manya
guda biyu,
Ajiye ledodin yayi ya karasa wurinda take ya
zauna akusa da ita yana murmushi,
"Yanmata nah.."
Shiru nadiya tayi takasa ko motsi ganin haka
yasashi dagota zuwa jikinsa,
"Kidaina kukan haka kinji? Maza tashi kije kiyi
alwala kizo muyi salla"
Batayi musuba ta mike taje ta shiga toilet din
dake cikin dakin tayi alwala tafito tazo ta
iskeshi yana jiranta nan yajasu salla sukayi
sallar nafila raka'a biyu kamar yadda sunnah ta
koyar,
Ledodin da ya shigo dasu yajawo ya bude ya
fito da gasasshiyar kaza da snacks da drinks
masu mutukar sanyi, "yan matana jeki kitchen ki
dauko mana flate da wuka da cups.."
"Yaya kabeer ban san inda kitchen din yakeba.."
Jin abinda tace yasashi murmushi ya tashi
dakansa yaje ya dauko yadawo ya zauna,
"Ga kaza zoki ci kinji yanmata na"
Duk da cewar nadiya najin yunwa sosai amma
sai taji bazata iya cin kazar ba saboda
kunyarshi dan haka ta jijjiga kai cikin dashewar
murya tace,
"Nakoshi.."
Jan kazar yayi gabansa ya zage yafara cin
abarsa batare da ya sake magana ba nan nadiya
ta sake jin daci aranta saboda halin ko in kular
da ya nuna mata,
Tana kallonsa yagama cin kazar ya dauki juice
yasha ya mike,
"To tashi muje ki kwanta.."
Tashi tayi yabi bayanta zuwa kan lafiyayyen
Italian bed din da aka kafa mata acikin dakin.
***
K'arfe 8 nasafe nadiya ta farka duk jikinta sai
faman yimata ciwo yake saboda gajiyar biki
wacce ta hadar mata da gajiyar da yaya kabeer
ya tara mata adaren jiya,
Dubashi tayi amma baya cikin dakin nan ta
yunkura dakyar ta sauka daga kan gadon ta
shiga toilet tasamu tayi wanka ta fito in banda
yunwa babu abinda takeji nan tayi salla ta
shirya ta zauna tayi tagumi tana jiran
dawowarsa amma shiru babu alamunsa,
Ganin har karfe goma da rabi tayi bai dawoba
gashi tana jin rsananin yunwa yasata tashi taje
ta dauko guntun snacks din da ya bari adaren
jiya tafara ci tana ci tana hawaye saboda bakin
cikin rashin ganin yaya kabeer,
Ita abinda yasata kuka ma shine yasan irin
yanayin da yatafi ya barta aciki maimakon ya
tsaya ya tarairayeta yabata kulawa ya taimaka
mata ya nuna mata soyayya kamar yadda
kowacce amarya take samu daga angonta
washe garin ranar da aka kaita amma ita yayi
tafiyarsa yabarta bata samu wannan kulawar ba,
Sannan ko acikin littattafan da take karantawa
tana jin irin zumudin da angwaye keyi tareda
nunawa amarensu soyayya amma ita sam bata
samu haka ba, da kuka tagama cin snacks din
ta tashi tafita tana tafiya dakyar, gidan tabi ta
ga yanda aka tsarashi dan kyau kam gida yayi
kyau sai dai fatan Allah yasa tasamu farin ciki
mai dorewa acikinsa,
Ganin dagaske yaya kabeer baya cikin gidan
yasata komawa falo ta zauna zuciyarta nata
tunanin inda yatafi, "kodai abinci yatafi siyo
mana?"
Nan ta zauna ita kadai har yan gidansu suka zo
su waleeda da yan uwan mama, ananne ta dan
sake taji dadi ana jimawa kuma sai ga yan
gidansu yaya kabeer dauke da kulolin
abinci,mintuna kadan sai ga kawayenta suma
nan taji tasamu saukin damuwar dake addabar
zuciyarta,
Gidanta cika yayi sosai da mutane nan
kawayenta suka sata ta sake yin wanka tasha
kwalliya domin yan unguwa sai shigowa ganin
amarya suke yi,
Wuni guda cur babu kabeer babu alamunsa
sannan ko waya bai yimata ba dadi daya taji
shine kawayenta da kannenta har dare suka kai
agidan sai daf da sallar isha sannan suka tafi,
nan kuma tsoro ya tisata agaba sa'arta daya
ma da akwai wuta,
Atsorace taci gaba da zama acikin gidan har
karfe 9 nadare sai lokacin taji karar mota
alamun dawowar yaya kabeer....
_Gaisuwa ga masoya masu bibiyar labarin
hakika kune abin alfaharina...._
*_Ummi Shatu_*: [7/17, 8:23 AM] Ummi
A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(home of expert
writers)_
*17*
_Wannan shafin nabaku shi kyauta k'awayen
arziki, Cwt Kausar luv, Besty phertymah Xarah,
Fido sodangi k'awata tareda dukkanin d'aukacin
masoyanku masu sonku suna bibiyar rubutunku
akoda yaushe...._
~~~Tashi tsaye tayi ta karasa bakin kofar falon
domin taroshi amma koda taje sai tayi turus
saboda ganin irin kallon da yayi mata,
"Yaya kabeer sannu da zuwa.." Tace dashi
jikinta asanyaye,
"Yawwa..." Shine kawai abinda yace yabi ta
gefenta yawuce batare da yasake koda kallonta
ba,
Tamkar gunki haka nadiya ta zama sai ido da
tabishi dashi,
Abubuwa biyune suke daure mata kai ahalin
yanzu, nafarko fitar sassafen da yayi ko tashi
bai bari tayiba sannan tunda ya fita bai dawo
gidanba sai yanzu, sannan yanzun ma da
yadawo babu fara'a babu magana mai dadi
kenan da saninsa yatafi ya barta yayi biris da
ita ko waya bai yimata yaji yanda ta wuni ba
tunda yafi kowa sanin acikin yanayin da yatafi
ya barta,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..." Shine kawai
abinda ta iya furtawa taje kan kujera ta zauna
hawaye nata faman ambaliya akan kumatunta,
Tunani daya takeyi Allah yasa ba irin wannan
mummunan zaman zasuyi ita da yaya kabeer
ba, burinta daya Allah yasa bazai sauya mata
daga yaya kabeer dinta mai sonta mai kaunarta
mai damuwa da ita akoda yaushe ba,
Kukan zuci taci gaba dayi har na tsawon wani
lokaci nan ta tashi ta bishi cikin daki ga
mamakinta akwance ta sameshi yanata faman
daddanna wayarsa wadda da alama chaten
yakeyi,
A dan nesa dashi ta zauna tana kallonsa,
"Yaya kabeer lafiya kuwa yau ka tashi tun
sassafe ka fita baka dawoba sai yanzu..?"
"Lafiya lau" ya amsa mata atakaice,
Dan shiru tayi nawani lokaci sannan tasake
magana,
"Yaya kabeer ga abinci can nakawo maka?"
"Ke dan Allah ki kyaleni idan ina jin yunwar ai
zan fada miki haba, ke wacce irin yarinyace kin
tisani agaba sai surutu kike yimin? Kin
tambayeni ina natafi dasafe kinzo kuma kina
sake yimin nonsense question.."
Binsa da kallo kawai nadiya ta tsaya yi saboda
yadda ya fututtuke yana balbala masifa kamar
wacce ta watsa masa wuta, ko a mafarki akace
mata yaya kabeer zaiyi haka bazata taba
amincewa ba amma sai gashi azahiri tagani,
"Allah yabaka hakuri yaya kabeer.." Tafada
idonta cikeda kwalla,
Tashi tayi tawuce taje ta dauki zani ta shiga
bathroom tayi wanka ta fito tazo ta shirya
tasaka kayan bacci ta kwanta,
Bata san iya adadin lokacin da ya kwashe yana
chaten dinsa ba.
Yauma kamar jiya haka tasake tashi da ciwon
jiki, jikinta duk yayi tsami amma koda ta duba
gefenta sai taga wayam babu yaya kabeer babu
alamunsa,
Zama tayi akan gadon tana tunani, to wannan
wacce irin rayuwace? Dama haka auren yake?
Miji sam bazai zauna agidansa tare da matarsa
ba,
Nan da nan hawaye suka fara zubowa daga
idanuwanta ita sai yanzu tagane dalilin mama
da kullum idan tatashi yimata fada akan aure
take cemata tayi hakuri domin gaba daya auren
babu komai acikinsa face hakuri to dama
wannan hakurin ne?
Share hawayenta tayi ta tashi ta dingisa zuwa
cikin toilet tayi wanka tafito tayi salla ta shirya
ta fita falo gidan babu komai na abinci sai ko
danye sannan gas dinma ba aduro ba gashi
babu kalanzir idan risho tace zata kunna, in
banda yunwa babu abinda takeji,
Tana zaune afalo taga an kawo wuta nan taje ta
jona electric cooker ta dora indomie ta dafa ta
zo falo ta zauna taci tana gamawa ta tashi ta
gyara gidan tasake yin wanka,
Tana daki tana kwalliya taji sallamar yan
gidansu nan tafita cikeda murna domin su
waleeda ne da sauran yan biki sukazo yimata
sallama saboda ayau zasu tafi,
Ba karamin dadi tajiba nan ta hanasu waleeda
tafiya tace sai yamma tayi hakane saboda tana
son ta ragewa kanta zaman kadaicin da zata yi,
daidai lokacin sallar azahar suma kannen kabeer
suka zo gidan, nan suka zo mata da abinci
wainar shinkafa da miyar agushi wai inji
mama,ita dai nadiya tasan tayi sa'ar uwar miji
amma abisa dukkan alamu batayi sa'ar mijiba,
Nan suka wuni dasu fati da su husna kannenta
sai mangariba sannan suka tafi ai kuwa suna
tafiya ta shiga damuwa domin gidan tsitttt yake
sai ita kadai kwal kamar mayya.
Yauma kamar Jiya yaya kabeer bashi yadawo
gidan ba sai da misalin karfe 10:30 lokacin
nadiya har bacci ya dauketa akan kujera tana
zaune ta kifa kanta akan hannun Kujerar da take
kai....
*_Ummi Shatu_*
[7/17, 8:23 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*18*
~~~Sai da yafi minti 20 da dawowa sannan
nadiya tafarka nan tsoro ya sake kamata domin
duk a zatonta bai dawoba amma kuma tana jiyo
kamar motsi acikin dakinta,
Tashi tayi tanufi hanyar dakin tana magana
"waye..?"
Shiru taji dan haka ta sadada ta shiga, tana
shiga taga yaya kabeer ne yake tsane jikinsa
yafito daga wanka,
"Yaya kabeer kaine kadawo ashe.. ?"
"Nine" yabata amsa, sanin yanda suka yi jiya
yasata yin shiru bata sake magana ba, nan
itama taje tayi wankan ta shirya ta kwanta,
Tunani ne ya mamaye zuciyarta saboda gaba
daya yaya kabeer ya bata mamaki bata taba
tsammanin cewar irin wannan rayuwar zasuyi
dashiba, ita a zatonta irin rayuwar soyayyar da
ake rubutawa acikin littafi zasuyi ashe abin ba
haka bane sai yanzu tagane cewar rayuwar
datake karantawa a littafi tasha banban da
abinda ke faruwa azahiri amma ita bata fahimci
hakanba sai yanzu,
Da wadannan tunanin bacci yayi awun gaba da
ita, kasancewar tasamu tayi isasshen bacci
yasata tashi da wuri domin ta riga kabeer tashi,
Salla tayi ta zauna tana karatun alqur'ani har
yaya kabeer din yatashi,
Gaisheshi tayi bayan ya idar da salla nan yace
ta dora masa ruwan zafi tace babu gas kuma
babu kalanzir,
Fita yayi can sai gashi da gas din da kayan tea
yazo ya ajiye mata nan taje ta kunna wuta ta
dafa masa ruwan zafin sannan ta dafa ruwan
tea, wanka yayi ya fito yasha tea din akaro
nafarko da yaci wani abu agidan,
Yana kammalawa ya kada rigarsa yafita bai
sake waiwayar gidanba hatta kayan miya sai
aike yayo mata,
Jalop din taliya da shinkafa tayi ta zuba a food
flaks ta ajiye taje tayi wanka, tana fitowa taji
wayarta na kara nan taga mamace murna sosai
ta shiga yi ta dauka suka gaisa nan mama ta
harhadata dasu waleeda dasu amir suka gaisa
sai da suka gama gaisawa da kowa sannan
mama takoma gefe,
"Nadiya ai babu matsalar komai ko? Naji tunda
aka kaiki baki kiraniba sannan baki kira abbanki
ba"
"Ehh mama wallahi wayar tawace babu kudi.."
Dan dam mama tayi sannan tace "to shikenan,
ina kabeer din ko ya fita?"
"Ehh ya fita mama"
"To shikenan, ayita hakuri dai nadiya, zaman
aure dan hakurine Allah yabaku zaman lafiya"
"Amin mama" nadiya tafada tana hawaye domin
ita yanzu sai take jin cewar rayuwar gidansu tafi
ta gidanta dadi domin da agidane da tuni yanzu
tana can cikin kannenta yan uwanta suna wasa
da dariya wani lokacin ma harda mama da abba
acikin wasan amma nan gashi tazo rayuwarta
atakure,
Sai da suka jima da mama suna hira sannan
sukayi sallama ta ajiye wayar tazauna agefen
gado tasha kukanta ta koshi ta share
hawayenta tasoma shiryawa lokacin ba afi karfe
2 narana ba, tana gab da kammala shirinta taji
karar shigowar text nan ta dauka ta duba tana
budewa taga mamace ta turo mata katin waya
har na dubu daya,
"Allah sarki mama.." Tafada idonta cikeda
kwalla,
Falo ta koma bayan tayi salla tajona kayan kallo
ta kunna tafara kallon wata tasha, tunowa da
tayi cewar tana karantawa acikin littattafai tana
jin irin yanda mata ke kulawa da mazajensu
yasata daukar wayarta ta kira yaya kabeer,
Kamar bazai dauka ba sai kuma taji ya daga,
"Hello nadiya.."
Jin ya ambaci sunanta yasanya ta mamaki
domin ada yanmatana yake kiranta amma yanzu
tadawo nadiya,
"Yaya kabeer kana inane?"
"Ban gane ina inaba, sai kace wani yaronki zaki
wani tambayeni ina ina? Menene? Me zanyi
miki?"
Jikinta ne yafara rawa saboda jin masifar da
yake yimata,
"Babu komai dama dai bugowa nayi inji
lafiyarka.."
Bai sake bata amsaba ya katse wayar Kitttt,
Har lokacin da ya kashe wayar jikinta rawa yake
domin fada yake yimata bil hakki da gaskiya,
Tagumi tayi tana rike da wayar tagagara koda
motsi tana tunanin yanda yaya kabeer ya zama
ahalin yanzu.
Wuni tayi acikin damuwa abincin ma bata iya
ciba saboda ita kadaice masu zuwar matan ma
yau babu wanda ya lekota dan haka tawuni
sukuku har dare sai wurin karfe goma yaya
kabeer ya dawo,
Sannu da zuwa tayi masa taje ta kinkimo
abincin data dafa ta kawo masa,
"Yaya kabeer ga abincin.."
"Ke kinci?"
"A'a kai nake jira.."
"To danme zaki jirani? Agidanku mahaifiyarki
tare kikaga sunaci da mahaifinki? Nace
agidanku haka akeyi? Karki sake wani jirana
akan abinci, idan kin dafa kayanki kici kawai
basai kin jiraniba kin gane?"
Tsallake abincin yayi ya wucewarsa zuwa cikin
daki yabarta sakare tana hawaye, jan abincin
tayi ta dan tsakura a flate tafara ci tana hawaye
har ta gama.
Washe gari da sassafe yace taje ta dafa masa
ruwan wanka zai fita, nan ta shiga kitchen ta
dauki ashana kenan ta hango wani murgujejen
bera nan ta yarda ashanar tayi daki da gudu
domin tana tsananin tsoron bera,
"Menene?"
"Yaya kabeer bera ne acikin kitchen din.."
"Akan beran zaki fasa dafa min ruwan wanka?
Ke wacce irin sakarya ce marar sanin abinda ya
kamata? Look kinga nifa bazan dauki wannan
sakarcin na banza da wofiba..."
Bathroom ya shige ya doko kofar yanata bala'i,
falo ta koma ta zauna, tana zaune ya fito cikin
shirinsa nafita yasaka kai yafice bai ko kalleta
ba.........
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/17, 8:23 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*19*
~~~Bin bayanshi da kallo tayi sannan cikin
damuwa tace,
"Adawo lafiya"
Bai amsata ba ya karasa ficewa, haka nadiya ta
zabga tagumi tana tunanin makomar rayuwarta.
Cikin wannan hali suka yi sati biyu koda
yaushe idan kabeer yasa kafa yabar gidan da
safe baya dawowa sai karfe 10 nadare, tunda
akayi bikinsu basu taba zama da nadiya sunyi
hira na minti daya ba, sai dai idan har fad'a
zaiyi mata,
Koda yaushe ita kuma tana kokarin nuna
kulawarta agareshi domin tana yimasa waya taji
yanda ya wuni wani lokacin ya dauka yana tsaki
wani lokacin kuma yaki dauka,
Tana zaune taci kwalliya amma gani daya zaka
yimata kasan cewar akwai abinda yake damunta
yaya kabeer ya shigo, lokacin karfe 5 na yamma,
Abinci ta kawo masa ya zauna ya danci ya tashi
ya shiga cikin daki, wayarsa da yabari afalon ne
tasoma kara nan nadiya ta dauka da niyyar kai
mishi ai kuwa sai gashi ya fito, fautar wayar
yayi yafara yimata fada,
"Uban waye yasaki ki daukar min waya? Danme
zaki taba min waya? Karki kuskura nasake
ganinki kin taba min wayata..."
Yana gamawa yawuce fuuhhhhh yakoma daki
mintuna kadan yazo yawuceta yabar gidan daga
nan bai sake dawowaba sai 11 nadare.
Haka rayuwar nadiya da yaya kabeer ta
kasance koda yaushe babu dadi, tsakaninta
dashi babu kulawa, babu magana mai dadi, babu
tausasawa, babu nuna soyayya babu komai,
kullum cikin yimata fada yake, idan ta kirashi
awaya ya hauta da fada idan bataci abinciba ta
jirashi yazo yayita fada da haka har suka debe
watanni biyu da bikinsu, mai karatu acikin
watanni biyun nan nadiya bata da wani labari
mai dadi wanda zata bayar dangane da rayuwar
aure, ko kadan bata san dadin aureba sai
sabanin haka,
Kasancewar bata cikin kwanciyar hankali yasata
ta rame ta kanjale domin kullum cikin kuka da
damuwa take, lokacin da takai kimanin watanni
uku babu kadan mama tazo mata,
Tsayawa mama kawai tayi tana kallonta saboda
ganin irin yanda ta rame ta zabge, ita mama da
atunaninta zata zo ta iske nadiya tayi kiba ta
hada jiki amma sai taga sabanin haka sai dai
batayi magana ba domin tayi zaton ko dai har
nadiyan tasoma laulayi ne,
Nan mama ta kusan wuni agidan amma abin
mamaki harta taho bata ga kabeer ya koma
ba,duk sai bata kawo komai aranta ba saboda
tasan irin soyayyar dake tsakanin kabeer din da
nadiya.
Acikin satin da mama tazo itama maman su
yaya kabeer tazo taga gida, sosai mamanshi
keson nadiya domin har kayan makulashe ta
kawo mata irinsu alawar madara, gullisuwa,
tsami gaye,yashin madina, hanjin ligidi da
sauransu haka ta kawo matasu cikin leda
viva,bata jima dayawa ba tatafi,
Tun daga nan nadiya bata sake ganin kowa
nagida ba sai dai mamanta kullum tana kiranta
su gaisa da ita sannan ta hadata da kannenta
su gaisa haka kuma duk satin duniya sai mama
ta turo mata kati na dubu daya ko na 750 dama
shi yaya kabeer babu ruwanshi da batun
wayarta ko wani abin bukatarta kullum da safe
da zarar ya kada rigarsa yafita sai dare.
Haka nadiya taci gaba da zaman hakuri zaman
da babu komai acikinsa face damuwa da bacin
rai har ta debe watanni shida lokacin dai ya
kaita gidansu sau daya haka itama yakaita
tagaida mamanta sau daya daga nan sai dai su
waleeda suzo mata a weekend su wuni shiyasa
har burin zuwan weekend take domin abba yana
kawo mata su, duk ranar da suka zo wuni take
cikin farin ciki shiyasa bata barinsu su tafi sai
dare yayi.
Cikin wannan yanayi nadiya tafara amai wanda
abisa dukkan alamu na laulayin cikine, kabeer ko
ajikinsa babu abinda ya dameshi,
Lokacin ma da ya shigo ya isketa tana aman
kallonta yayi yace,
"Ke cikine dake ko?"
Daga nan bai sake magana ba yayi tafiyarsa
yawuce ciki yabarta tana faman kwarara amai,
Satinta biyu tana zazzabi atafe daga karshe
zazzabin ya kwantar da ita, nan ya dauketa
yakaita asibiti likita yana dubata yace cikine da
ita na wata biyu, ga mamakinta sai taga yana
murna harda bawa likita tukwici, daga nan ya
daukota suka dawo gida bayan ya biya ta
kasuwa ya siyo mata fruits su lemo da ayaba da
makamantansu,
Tunda suka dawo gida kuma yarage fada da
masifar da yake yimata yafara dan kula da ita,
komai tace tana so baya k'i shiyasa lokaci
kankani tayi kyau tayi kiba saboda hankalinta
ya dan fara kwanciya,
Yanzu abu dayane ke damunta shine wayar da
yaya kabeer ya tsiri yi acikin kowanne dare,
koda yaushe ta bude idonta sai tajiyoshi yana
waya, kusan kwana yake yana yin waya da
wadda bata san ko wacece ba, bayaga haka
kuma ko wacce safiya ta Allah sai yafita da
sassafe yana tafiya inda bata san ko inaneba,
Wannan dalilinne yasa yau ta daura aniyar
tambayarshi inda yake zuwa, tana kwance afalo
ya shigo lokacin misalin karfe 9 nasafe, akusa
da ita ya zauna nan ta yunkura ta tashi dakyar,
"Yaya kabeer wai ina kake zuwa da sassafe ne?"
"Nadiya shamsiyya nake zuwa nake kaiwa
makaranta, baki Santa ba ko? Yar kanwar
mamace to shine aka kawota gidanmu dan tayi
karatu.."
"Amma yaya kabeer fisabilillahi sai kaine zaka
rinka kaita makarantar? Kullum fa da karfe 6
kake fita, haba dan Allah, gaskiya nidai wannan
abun yana bata min rai.."
Mikewa yayi yashiga cikin daki baiyi magana ba,
nan ran nadiya ya baci domin tagane cewar
tsakaninsa da shamsiyyan akwai wani abu, tana
ganinsa yazo ya sake fita bayan yayi shirin
office,
Tagumi ta zabga tayi shiru, wayarta ce ta soma
kara nan ta dauka taga bakuwar number ce,
"Assalamu akaikum"
Daga daya bangaren aka amsa sallamarta tana
jin muryarsa ta ganeshi ba kowa bane face yaya
Kamal dan gidan wan mama wanda suke zaune
agarin tofa....
*_Ummi Shatu_*
[7/17, 8:23 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of experts
writers)_
*20*
~~~Nan suka fara gaisawa cikeda zumudi
domin rabonta dashi tun tana JSS lokacin da
yake zuwa gidansu hutu, Allah ya hada jininta
dashi sosai,
Hirace ta barke tsakaninsu nan yafara
tambayarta ya rayuwar auren nasu, tsakaninta
da yaya kamal babu boye boye sannan ayanda
take jin zuciyarta sam bazata ji sauki ba har sai
ta amayar da abinda ke cikin zuciyarta dan haka
ta fara zayyane masa damuwarta tun daga
washe garin ranar da aka kawota har yau,
Hakuri kamal yafara bata cikeda tausayinta,
"Nadiya kiyi hakuri, ki dauki Dangana sannan
kisani komai na duniya mai wucewa ne sannan
babu abinda yake dawwama a duniya,
Dadi baya taba dawwama haka shima wuya da
damuwa basa dawwama,
Farin ciki baya dawwama kamar yanda bakin ciki
baya taba dawwama,
Kisakawa ranki cewar ibada kike yi domin
zaman aure ibadane haka kuma abayan
kowanne tsanani to da akwai sauki haka
alqur'ani ya sanar damu,
Kiyi hakuri kici gaba da yiwa mijinki biyayya
karki gaji sannan karki daina,
Kidauka cewar bautar Allah kikeyi sannan
aljanna kike nema kin san kuwa samun aljanna
ba abune mai sauki ba dole sai ansha wahala
sai anshiga damuwa,
Haka kuma kamar yadda baki taba fadawa kowa
ba saini to kiyi hakuri kisake daurewa karki
fadawa kowa wannan maganar domin sirrinki ne
keda mijinki ta shafa kinji..?"
"Naji yaya kamal.."
Nan yaci gaba da bata shawarwari akalla sai da
suka shafe awanni yana yimata nasiha gamida
bata hakuri tareda tausar zuciyarta akan taci
gaba da jurewa gamida hakuri,
Ko ba komai taji dadin shawarwarin da yaya
kamal yabata tareda bada hakuri domin idan
abu yana damunka kasamu wanda ka fadawa
har yabaka hakuri dadi kakeji koda bai baka
komai ba.
Nan taci gaba da rainon cikin da yake tareda
ita shikuma kabeer bai fasa halinshi na daka
sammako ya fita da sassafe ba wai shamsiyya
yar uwarsa yake kaiwa makaranta sannan ga
wayar dare da ya kware akanta kamar gwauro
marar iyali,
Juyi nadiya tayi nan tajiyo muryarsa kasa kasa
afalo yana maganganu ahankali wanda daga ji
wayar tasa yake yi, yunkurawa tayi ta tashi
dakyar ta fita falon nan ta hangoshi akwance
cikin kujera kamar ba dareba sai wayarsa yake,
"Yaya kabeer..."
Juyowa yayi tareda katse wayar yana cewa "i
will call you back latter..."
Tashi yayi yana kallon nadiya,tamkar zai hauta
da duka haka yayi yabude babin masifa,
"Menene? Acikin tsohon daren nan zakizo kina
kirana, me zanyi miki? Ba tambayarki nakeba,
nace uban me zanyi miki, wannan wanne irin
rashin mutunci ne, da rana ba abar mutum ya
hutaba haka da daddare ma baza abarshi ya
hutaba.."
"Haba yaya kabeer, yanzu me yayi zafi da zaka
fara fada da daddaren nan, ni idan nice na bata
maka rai kayi hakuri, gani nayi abinda kake yi
bai daceba sannan bai kamata ba, ya za ayi ni
ka baroni acikin daki sannan kazo nan ka zauna
kana waya, idan wayarka zakayi ai sai kayi da
rana tun kana waje amma bawai sai kadawo
cikin gida..."
Katseta yayi cikin wata irin tsawa,
"Ke karki kuskura kiyi min iyayi kin gane ko,kece
ma zaki tsara min yanda zan rinka gudanar da
rayuwata?, saboda gaki uwata ko? To bari kiji.."
Bai karasa ba yaga ta rike cikinta tareda faduwa
akasa nan da nan yaga tafara murkususu jini
yana bin kafafuwanta, iya tashi hankalinsa kam
ya tashi domin yana mutukar son cikin dake
jikinta nan yaji ya shiga rudu,
Dakyar ya iya kokarin daukarta yakaita cikin
mota yanufi asibiti da ita wanda yake can gaba
dasu kadan,
Cikin wani daki aka sata nan likitoci suka yi
cahhhh akanta suna dubata daga karshe dai
sunaji suna gani babu yanda zasu iya cikin dake
jikinta ya zube,
Kabeer yayi mutukar bakin ciki lokacin da yaji
cewar cikin ya zube, nan ya zauna acikin
asibitin har gari ya waye sannan ya tafi gidansu
yaje ya sanarwa da mamanshi, hankali tashe
mama ta bishi zuwa asibitin bayan tasaka
A'isha ta hadowa nadiya tea da sauran kayan
karyawa,
Tunda mamanshi taje itace take kula da nadiya
domin tana mutukar sonta ko kadan bata son
damuwarta shiyasa kullum cikin yimata hidima
take, karfe 8 daidai yaje ya dauko A'isha da
shamsiyya zuwa asibitin ita nadiya sai yau taga
shamsiyyan ma domin akomai tasan tayiwa
shamsiyyan nisa amma da yake namiji ba dan
goyo bane shine yaya kabeer yake neman fifita
shamsiyyan akanta,
Nan sukayi mata sannu mama ta taimaka mata
ta tashi ta hada mata tea sannan ga farfesun
kayan ciki da soyayyen kwai ta bata taci takoma
ta kwanta, sai da wurin karfe 11 sannan yaje
gidansu nadiya yafada nan mama ta rude ta
shirya tatafi asibitin amma da taje sai taji
hankalinta ya kwanta saboda tasamu maman
kabeer na kula da nadiya,ita nadiyan ma lokacin
bacci takeyi, nan su mama suka shiga gaisawa
tareda jajantawa juna.
Kwanan nadiya takwas a asibitin aka sallameta
bayan anyi mata wankin ciki nan Maman kabeer
tace maman nadiya tatafi da ita Gida tunda
likitoci sunce ta dan samu hutu banda aikin
wahala, ita abinda yasa bazata tafi da nadiya
gidanta ba tasan idan sunje bazata sake kamar
gidansu ba amma idan gidansu ne zatafi
sakewa,
Nan mama ta yarda suka tafi da nadiya bayan
sun biya ta gidanta sunje sun daukar mata
kayan sawarta, komawar nadiya gida ba karamin
kwanciyar hankali ta samuba domin cikin sati
biyu tayi kiba tayi kyau jikinta ya dawo saboda
mamanta tana mutukar kula da ita sannan babu
abinda takeyi daga kallo sai ko taci abinci ta
kwanta, gashi yanzu babu damuwa babu bacin
rai bp dinta ma da yahau ya sauka, babu abinda
takeyi ko mama tagani tana aiki idan tace zata
tayata sai taki, sai dai ta zauna tayita kallo idan
kuma su husna sun dawo daga makaranta
suyita hira suna sata dariya domin suna nan har
yanzu da halinsu na sa'insa, idan yamma tayi
kuma abba yadawo to bazai shigo haka ba sai
ya tahowa da nadiya wani abu na kwadayi, yana
dawowa kuma zasu tattara su koma falonsa
hatta abinci tare za ahadu aci, ana ci ana hira
shiyasa nadiya ta kwammace gara rayuwar gida
sau dubu data gidan aurenta.
Yaya kabeer ma yana zuwa dubata lokaci zuwa
lokaci sannan yana kawo mata abubuwan
bukata, har nadiya ta Karaci zamanta agidansu
tafara shirin komawa gidanta bata taba fadawa
mama matsalarta ba ko kuma damuwarta ba
duk da tasan tana cikin damuwa sannan babu
wanda yafi cancanta da jin damuwarta sama da
mahaiifiyarta amma bata taba sanar da mama
ba, tasan ita babu wani jin dadi ko farin ciki
kwaya daya da zata iya fada wanda tasamu
agidan aure to ina dadin ma yake auren dako
amarci ba asamu anyiba matsalolin rayuwa
suka taru suka yimasa illa,
Watanta biyu agidansu sannan takoma gidan
yaya kabeer bayan abba ya bata kudi har dubu
hamsin yasaka mata acikin account yace idan
tana da damuwa sai ta dauka tayi amfani dashi,
Tunda ta koma gidan yaya kabeer yasamu
abinda yayi missing shikenan suka dawo yar
gidan jiya, baya zama agida idan yafita tun safe
sai dare, baya zama suyi hira da ita to bai
zauna agidan bama bare suyi hirar, wayar cikin
dare, fita sassafe kai shamsiyya makaranta, ita
dai nadiya kawai zaman hakuri take nan tasake
rarramewa, damma dai yaya kamal dan uwanta
yana kiranta awaya koda yaushe yana kwantar
mata da hankali, da haka kwanaki masu yawa
suka shude nan tasake samun wani cikin tafara
laulayi ganin haka yasa yaya kabeer fara bata
yar kulawa saboda cikin da yake jikinta,
Kamar wancan lokacin yanzun ma tayi kiba tayi
kyau saboda hankalinta ya dan kwanta, sannan
kuma fitar da yakeyi sassafe zuwa kai
shamsiyya makaranta ahalin yanzu yadaina
wayar tsakar daren ce dai har yanzu yanayi,
Daga mamanta har Maman shi kowacce na taka
muhimmiyar rawa wurin ganin sun bata kulawa
domin kullum cikin yimata aiken kayan dadi
suke, haka kawai zataga mamanshi ta aiko
A'isha kanwarshi ta kawo mata abun kwadayi,
ko kuma taga Amira kanwarta mama ta aikota,
yanzu bata da damuwa sosai saboda shima
yaya kabeer din yarage masifar da yake
yimatay,nan hankalinta ya kwanta tayi kyau
sosai kowa yaganta yanzu yasan tasamu
kwanciyar hankali sabanin da.
Cikinta yagirma ya shiga wata bakwai sannan
yayi kato kamar wadda zata haifi yaya hudu,
karfe biyu da rabi na dare ta farka tana jin
yunwa da kishin ruwa dama tunda cikin yafara
girma take tashin dare cin abinci da shan ruwa,
yaya kabeer tajiyo afalo yana aikin wayar tasa
ta dare kamar yadda ya saba, nan ta yunkura
dakyar ta fita falon ranta idan yayi dubu ya baci
take zufa ta rufeta jininta yahau mutuka saboda
dama ta dade da kamuwa da hawan jini nan
hawan jinin ya tashi jikinta yahau rawa,
"Yaya kabeer..."
Takira sunanshi cikin radadin ciwo, saurin tashi
yayi ya katse wayar amma kafin yakarasa
wurinta har ta sulale ta yanke jiki tafadi cikin
daukewar numfashi.......
MIJINA SIRRINA...21-32
[7/19, 7:50 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert
writers_
*21*
~~~Arude yaje inda take yafara jijjigata yana
kiran sunanta,
"Nadiya, nadiya, nadiya.."
Jin bata amsaba sannan da alama bata yin
numfashi yasashi cikin sauri ya mike ya fita
arude domin dauko ruwan sanyi saboda abisa
dukkan alamu suma tayi,
Bude idonta tayi tabishi da kallo domin dama
suman karya tayi masa saboda taga alamun
idan har batayi masa hakaba bazai daina
wannan mummunar dabi'ar ta wayar dareba,
Tana jin alamun tahowarsa tayi saurin rufe
idanuwanta tareda dauke numfashinta,yana
zuwa ya kwara mata ruwan sanyi nan ta saki
ajiyar zuciya da karfi ta bude idanuwanta cikin
alamun galabaita,
"Nadiya ko zamu tafi asibiti..?"
Kai ta girgiza masa tana kallon duk yanda yabi
ya rude domin ko kadan baya son ya sake rasa
cikin dake jikinta,
"Bani abinci naci yunwa nakeji"
Cikin hanzari ya tashi yaje ya kawo mata ta
karba ta fara ci, tun daga wannan lokacin
tasamu yadaina yin wayar dare sannan zuwa kai
shamsiyya makaranta ma da yakeyi yanzu
yadaina saboda baya son asake samun matsala
kamar yanda aka samu a wancan cikin,
Cikin kankanin lokaci nadiya tayi kyau tasake yin
kiba saboda yanzu bata da matsalar komai
kabeer yana kula da ita haka mahaifiyarsa itama
tana iya bakin kokarinta wurin faranta mata rai.
Har cikin nadiya ya shiga watan haihuwa
kabeer bai sake yimata wani abu wanda zataji
daci acikin ranta ba domin yana mutukar son
cikin dake jikinta,
Cikin dare nakuda ta kamata nan yashiga firgici
ya kinkimeta suka tafi asibiti gaba daya yakasa
samun nutsuwa yayi nan yayi can har aka samu
ta haifi yaranta yan tagwaye mace da namiji,
murna awurin kabeer abin ba acewa komai, kasa
tafiya yayi sai acikin mota ya kwana, gari yana
wayewa kuwa yaje yakaiwa su mama labari
kafin kace wani abu tuni har asibiti ya dinke da
yan uwa yan gidansu da yan gidansu nadiya,
jariran tubarkalla bul bul dasu kyawawa domin
yaya kabeer shima ba baya bane awurin kyau
haka nadiya,
Kwanansu biyu a asibiti aka sallamesu suka
koma gida, kayan da kabeer ya hado shida
mahaifiyarsa abin ba amagana domin sun
jibgowa mai jego ita da jariranta kaya na kece
reni,
Abban kabeer da abban nadiya tare suka zo
ganin jariran anan suke tambayar kabeer sunan
da zai sawa yaran yace sunan mahaifiyarsu
abban zaisa da sunan mahaifinsu wato usman
da Habiba nan su abba suka yita sawa yaran
albarka dasu kabeer din,
Adaki yasamu nadiya ya fada mata yanda sukayi
dasu abba nan itama tabada goyon baya tace
sai su rinka kiran yaran da nabeel macen kuma
nabeela,
Shagali iya shagali kabeer yayishi awannan
haihuwar, komai da nadiya ke bukata itada
yaranta ya tanadar musu, ranar suna aka
nadawa yara sunan Habiba da usman,
A washe garin suna kuma aka tafi da nadiya
gida domin mamanta ta kula da ita tunda
haihuwar farice sannan yara biyu,
Tunda ta koma gida ta sake samun kwanciyar
hankali, yaya kabeer yana zuwa kusan kullum
yana ganinsu ita da yaranta dahaka har suka yi
watanni biyu agida a lokacin ne abba yace
zaman ya isa haka ya kamata su koma gida nan
nadiya ta hada komai nata ta shirya kabeer yazo
ya dauketa suka tafi.
Komawarta gidanta nan ma babu wani bacin
rai ko tashin hankali zamansu suke yi da kabeer
lafiya babu wata matsala, dan uwanta kamal
kuma kullum cikin kiranta awaya yake yana
tambayarta yanayin zamansu da kabeer kullum
hakuri da nasiha yake yimata yana nuna mata
cewar shi zaman aure ibadane dan haka dole
akwai jarrabawa acikinsa.
Kwantar da hankalinta tayi taci gaba da
kulawa da yaranta har suka yi watanni a
lokacinne kuma kabeer ya bijiro mata da
maganar kara aure.....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/19, 7:50 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*22*
~~~Tashin hankali sosai nadiya ta shiga lokacin
da taji cewar yaya kabeer zai kara aure nan
kuma tabi tafara ramewa amma mamanta da
yaya kamal koda yaushe cikin kwantar mata da
hankali suke suna cewa ai babu komai tadaina
damuwa,
Cikin dan takaitaccen lokaci ya hada kaya ya
kai gidansu yarinyar nan manya suka shiga ciki
yaci gaba da zuwa wurinta suna soyayya, sunan
yarinyar munnira tana zaune acan wata unguwa
wai ita hammaga,
Daurewa nadiya tayi ta kwantar da hankalinta ta
yakice tunanin abin aranta ta rungumi yaranta
fadeel da fadeela wanda ahalin yanzu sun soma
girma,
Neman aurensa yaya kabeer yasa agaba amma
kuma dayake munnira ba matarsa bace sai ta
kwanta rashin lafiya mai tsawo har Allah ya
karbi ranta nan yabarwa gidansu kayan da ya
kai mata yace bazai karba,
Daga nan kuma haka rayuwa taci gaba da
juyawa har yasake haduwa da wata budurwa
mai suna kareemat itama kuma da gaske yake
sonta bada wasaba,
Koda ya sanar da nadiya hankalinta ba karamin
tashi yayiba domin bata san wacce irin mace zai
auro ba saboda tana tsoron sake shiga damuwa
kamar lokacin baya,
Neman aure dagaske yaya kabeer yake yinsa
domin baya son adauki dogon lokaci ba ayiba
wannan dalilinne ma yasashi tura magabatansa
da wuri,
Nan da nan yafara gyaran gida sannan yafara
kokarin hada kayan lefe ita dai nadiya tana
zaune tana ganin ikon Allah amma tayi kokarin
boye masa damuwarta,
Lokacin da yagama gyara gidansa tsaf sai ya
hadowa nadiya kayan fadar kishiya akwatuna
uku ya iyo mata cikeda kaya ya kawo,
Sai da yafara kaiwa mamansa tagani nan taketa
fada saboda ita sam bata son yayiwa nadiya
kishiya saboda bataga laifin yarinyar ba yarinya
mai hakuri da biyayya da ganin girman nagaba,
Haka ya debo kayan ya kawowa nadiya tana
kitchen tana aiki,
"Ga kaya can nakawo miki.."
Jin abinda yafada yasata ajiye aikin da take tabi
bayansa zuwa falonta nan taga akwatuna masu
kyau sabbi dal guda uku, duk da cewar kayan
ciki masu tsadane sannan sunada mutukar kyau
hakan bai hana hankalinta tashiba,
Zama tayi ta bude kayan tafara gani tana jin
wani irin bacin rai acikin ranta tamkar zata
fashe da kuka amma sai ta daure ta boye
damuwarta tafara yaken dole,
"Naga kaya kam kuma sunyi sosai ubangiji Allah
yasaka da alkhairi yasa ayi a sa'a"
Tace dashi tana kokarin hada kayan wuri guda,
"amin" yabata amsa yana dauke dasu fadeel,tun
da taga kayan kuma sai ta shiga damuwa
hankalinta ya tashi nan takira yaya kamal ta
fada masa yayita bata hakuri, maman kabeer
dinma har gida tazo ta rarrasheta tabata hakuri
tace ta kwantar da hankalinta koda ace kabeer
ya kara aure to bazata wulakanta ba.
Hakurin tayi ta dauki dangana ta zubawa
sarautar Allah ido ta zauna tana jiran ranar da
zataji yace ta shirya tazo aje akai kaya amma
kuma shiru daga karshe ma sai yazo yace
yafasa auren,
Duk da cewar lokacin da yace zaiyi aure
hankalinta ya tashi to yanzunma da yace ya
fasa hankalin nata ba kwanciya yayiba saboda
tasan bazata taba fita awurin mutane ba za aga
kamar itace take hanashi auren.
Amma koda ta zauna tayi tunani cewar Allah
yasan gaskiya kuma yasan zuciyarta sai kawai
ta share abin yadaina damunta nan ta kwantar
da hankalinta babu daukar dogon lokaci tayi
kiba ta murmure, haka taci gaba da zama tana
mutukar kyautatawa yaya kabeer musamman
ma yanzu data samu ta yaye su nabeel dan
haka ta zage damtse tana kyautatawa mijinta.
Shima yaya kabeer din yanzu babu laifi ya dan
sauko yana dawowa gida akan lokaci sannan
yana zuwa yaci abinci da rana kuma lokaci
zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji lafiyarta ita
da yara kafin ya dawo gida,
Harkokinsa kuwa koda yaushe sai samuwa suke
suna sake budewa domin yanzu yatara kudi
wanda shi kansa bai zaci zai mallaki irinsu ba
dan haka ya fada harkar business nan yafara
fita kasashen waje yana shigo da kaya ko
wanne iri na amfanin yau da gobe kafin wani
lokacin har yaya kabeer ya zama young
millionaire,
Nadiya kam koda yaushe cikin kyautata masa
take musamman ma yanzu da taga ya nannemi
aure amma Allah bai shirya za ayiba, ita dinma
yanzu tayi fes da ita tayi kyau, duk lokacin da
yafita saro kaya kasar waje yana kaiwa kamar
wata daya acan koma fiyeda haka shiyasa take
dauko su Amira su tayata zama kafin ya dawo.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya har tsawon
wani lokaci, nadiya nazaune cikin kwanciyar
hankali uwar mijinta da danginsa na mutukar
sonta ko kadan basa son laifinta, yaranta har
sun dan tasa domin yanzu shekararsu biyu da
rabi.
Acikin yawace yawacen da yaya kabeer keyi na
fita kasashen waje kwatsam ya hadu da wata
Mata ma'aikaciyar gidan wani radio,asalinta yar
garin jos ce amma saboda tsabar bariki haka
tafito daga gidan iyayenta ta gina gidanta ta
tare tana duniyancinta sannan tana fita waje ta
ziyarci duk kasar da takeso alokacin data
gadama,
Ganin yaya kabeer yasata rudewa nan ta nufeshi
tana kwarkwasa tana faman jujjuya jikinta,
kamshin turaren da ta saka kuwa kamar zaiyi
magana,
Farrr tayi masa da idonta ta kalleshi tana yauki,
"Sunana asabe mc..."
Dagowa yaya kabeer yayi ya kalleta.....
_Gaisuwa da fatan alkhairi ga dunbin masoya
wannan littafin ina gaisheku aduk inda kuke._
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/20, 6:36 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert
writers)_
_Shafi na 23 tukwicine ga yan kungiyar haske
writers association, Allah yakara hazak'a da
basira hadida fasaha mai albarka.._
*23*
~~~Cikin yauki da kwarkwasa gamida jan
hankali asabe mc tasake magana,
"Haba handsome ya naji Kayi shiru bakace
komai ba? Kodai banyi maka bane?
Gaskiya amma idan har kaki kulani bazan ji
dadiba.."
Sake kallonta kabeer yayi yana mai kallon irin
shigar dake jikinta,
Wani material ne mai shegen kyau gashi daga
gani mai tsadane kalar light blue yasha dinkin
doguwar riga wadda ta tsaru tamkar yar kanti,
ta yane kanta da dan siririn mayafi fari idonta
sanye cikin farin face,
"Har yanzu dai banji kace komai ba.."
Dan yake kabeer yayi domin shi ko kadan bai
taba ganinta ba sai yau, yau dinma yanzu,
"Gaskiya ka hadu, duk macen data sameka tayi
saaaa'a"
Yanda taja maganar daga karshe yasa kabeer
zuba mata idanuwanshi yana dan miskilin
murmushi,
"Kema kina da kyau ai..." Yafada yana fadada
murmushinsa,
"Well.. Tunda har ka yaba dani mai zai hana
muyi exchanging contacts so kaga sai mu rinka
gaisawa.."
Kabeer baiyi musuba ya bata phone number
dinshi ya karbi tata daga nan suka rabu kowa
ya nufi wurinda zaije,
Lokacin da yagama harkokinsa zai dawo gida
tsaraba ya tulowa su fadeel da nadiya kamar
gaske,
Ya dawo ya iskesu lafiya nan kuma yaci gaba da
kula dasu, satinshi biyu da dawowa Nigeria yana
office a zaune yana aiki wayarshi tasoma ringing
yana dubawa yaga asabe mc ce,
"Ranka yadade..."
Yaji muryarta bayan ya daga wayar,
"Yakike..?"
"Ranka yadade kuma haka akeyi daga ranar nan
ban sake jinka ba nayi jiran nayi jiran har nagaji
naji bazan jureba shine nace bari ni na kiraka na
gaisheka"
"To nagode asabe.."
"No ka rinka kirana da mc shine daidai"
"To mc shikenan sai kin jini"
Katse wayar yayi yana murmushi wanda bai san
dalilinsa ba,
Haka da yakoma gida ma da daddare sai da
asabe mc ta kirashi sannan kuma ta turo masa
da wani cool massage,
Tun daga wannan rana take kiransa akalla takan
kirashi fiyeda sau biyar arana shiyasa tun baya
kiranta har shima yafara kiranta yana mayar
mata da reply din text massages din da take
turo masa,
Tsawon watanni biyu zuwa uku suka dauka
suna waya amma nadiya ko kadan bata taba
saniba, wata ranar juma'a kabeer ya kira asabe
mc suka gaisa anan ta kashe murya ta marerece
tace,
"Gaskiya handsome ya kamata nazo har garinku
naganka domin wallahi ina son sake ganin
kyakkyawar fuskarka.."
"A'a ai bakece zakizo ba asabe nine yakamata
nazo kuma insha Allah zanzo.."
"Yaushe? Karfa kahanani zuwa kai kuma kaki
zuwar min.."
"Zanzo, kibari zan sanar dake idan natashi
zuwa"
"To ina cikin garin kano dai duk lokacin da
zakazo ka sanar dani.."
Sallama sukayi tun daga wannan lokacin kusan
koda yaushe asabe bata da magana sai ta
tambayar kabeer yaushe zaije wurinta, ganin
tanata damunshi akan yaje yasashi shiryawa
yayiwa nadiya sallama cewar zaije cikin kano
amma bai sanar da ita abinda zaije yiba,
Sabuwar motarshi ya dauka wacce batafi 2
weeks da zuwa ba ya tafi bayan yasha kyau da
kwalliya cikin wani sky blue din yadi mai tsada,
sai da ya shiga cikin garin kano sannan ya kira
asabe mc ya tambayeta unguwar da take nan ta
sanar dashi tareda yimasa kwatancen gidan,
Cikin dan takaitaccen lokaci ya samu gidan ya
karasa, gidane safe contact mai parts dayawa
kusan duk kawayen asaben ne agidan kowacce
da part dinta sannan idan tayi bako sai ta
saukeshi anan kawai dai gidan yan barikine,
Lokacin da yashiga gidan da wata farar
budurwa yafara cin karo tana brush abakin
barandar part dinta daga ita sai gajeren wando
da yar karamar vest, nan ya dauke idonsa yana
jin kamar yakoma kada yashiga amma sai dai
sam yakasa komawar haka ya kutsa kai yawuce
domin dakin asabe mc shine na biyun karshe,
Wata budurwa yasake gani sun fito itada wani
saurayinta suna kokarin rufe kofa nan ya kawar
dakai yawuce zuwa sashen asabe,
Sai da yayi knocking sannan ya bude kofar ya
shiga nan wani rantsatten kamshin turare wanda
bai taba jin irinsa ba ya bugi kofofin
hancinsa.....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/20, 6:35 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*24*
~~~Bin tsarin yanda aka kawata falon ya rinka
yi da idanuwansa, falone babba wanda aka
kawatashi da jajayen kujeru, komai na falon ja
ne in banda kamshi mai sanyaya zuciya babu
abinda ke tashi daga cikin falon,
Bai kai ga karasawa cikin falon ba yajiyo muryar
asabe mc tana magana ahankali,
"Barka da zuwa tauraro mai haskawa, farin wata
sha kallo, yaro mai tashe dan kwalisa,
kyakkyawa son kowacce kin wacce ta rasa ko
tasan bazata samuba..."
Juyawa yayi nan ya hangota tana takowa
ahankali tamkar wata dawisu, wata classic
atamfa ce ajikinta koriya sharr wacce ta dinku
sosai dinkin riga da skirt wadanda suka kamata
mutuka sannan suka fallasar da asirin surar da
Allah yayi mata,
Bakace doguwa mai faffadan hips da cikar kirji,
tana da kyakkyawar fuska mai dauke da dogon
hanci ga manyan idanuwa, iya kyau asabe mc
tana dashi kusanma tana amfani da kyawun
natane tana mallakar mazan da suka yi mata ko
suka burgeta,
Daurin dan kwalin da tayi tamkar gwaggoro yake
ya nadu sannan ya tsaru, ko mayafi bata yafaba
ta nufo inda yake tana murmushin da tasan zai
sace zuciyar kabeer,
"Ga wurin zama.." Ta yi masa nuni da hannunta,
gaba daya kabeer ya yi la'asar kallonta kawai
yake fuskarshi dauke da murmushi,
"Da fatan ka iso lafiya?"
"Lafiya lau.."
"To yagida zance ko ya iyali?"
"Iyali dai ranki ya dade.."
Dan dammm tayi alamun bata ni dadiba ko
kuma bata zaci zataji haka daga gareshi ba
amma da yake gogaggiyar yar barikice sai tayi
wani shu'umin murmushi tayi farr da idonta
wanda yasha eye shadow kalar atamfar jikinta
tace,
"Masha Allah haka nake son ji, ashe dai kai
dinma cikakken mutum ne kamar yanda na
tsammata, gaskiya nayi mutukar farin ciki da jin
haka.."
Tana maganar ne tana kokarin zama akusa
dashi nan fitinannen kamshinta yakai masa
ziyara,
"To yakike ya aiki ya fama da jama'a?"
Yace da ita yana kallonta domin agaskiya ba
karamin kyau tayi ba sosai,
"To ya za ayi gashi nan munata fama.." Tafada
cikin muryar jan hankali,
Mikewa tayi tana taku ahankali ta nufi fridge
taje ta bude ta dauko masa juice na kwali da
battle water ta nufoshi,
"Kar nabar bako babu ruwa babu lemo.."
Shidai kabeer baya magana murmushi dai kawai
yake danyi yana binta da idanuwa duk inda ta
wulga,
Ajiye ruwan da juice din tayi agabansa sannan
ta juya ta nufi kitchen tana juyawa ahankali,
Yanzu kam tasan kabeer ya shiga tarkonta
kamar yanda tasaba danawa sauran maza sai
dai kuma ita awannan karon bata danawa
kabeer tarkon da zai shiga dan kawai suyi
rayuwa awajeba a'a tarkon da ta dana masa so
take ta mallakeshi ta aureshi sannan kuma ta
rayu dashi,
Glass cup ta dauka ta koma falon tana tafe tana
yin wasa da cup din ta hanyar cillashi sama
ahankali tana cafewa,
Daukar juice din tayi ta tsiyayawa kabeer ta
mika masa nan ya karba yafara kurba yana
kallonta,
"To ya aikin naku?" Ya tambayeta,
"Aiki muna nan munata fafatawa amma fa abun
ba sauki aikin namu akwai wahala sannan gashi
da hatsari.."
Ayanda take yin maganar tana yintane cikin
nutsuwa da sigar dauke hankalinshi,
Nan ya tattara hankalinsa ya mayar gareta
tafara shirya masa labari wanda dama tadade
da tanadarsa dominshi,
Sun jima suna tattaunawa kafin ta mike tayi
masa jagora zuwa dining table inda ta shirya
masa hadadden faten doya da kifi wanda yasha
manja da alayyahu, dama wannan shine favorite
food dinshi nan ya zauna yafara kwasa batare
da tunanin komai ba ita kuwa asabe mc dama
ta dade dayin bincike akansa domin hatta
gidansa sai da aka kaita aka nuna mata shi
taganshi shiga cikine kawai batayi ba, bayada
haka duk wani motsinsa saida ta bibiya dan
haka tasan abubuwa masu yawan gaske atare
dashi shiyasa bazai yimata wahalar samuba,
Sai da ya cinye abincin nan cikin flate yasha
lemon data hada masa sannan suka bar dining
table din suka koma falo nan ta dan kalleshi
tana yin fari da idonta,
"Yakamata muje musha ice cream kafin ka
tafi.."
"A'a yanzu tafiya zanje nayi kin gane amma
nayi miki alkawari next time idan nadawo
zamuje.."
"Ok to babu damuwa.." Tafada tana langabe kai
tamkar wata karamar yarinya, tashi yayi tabi
bayansa ayanda take babu gyale har zuwa waje
wurinda motarsa take,ciki yashiga itama ta bude
gefensa ta shiga ta zauna tareda shagwabe
fuska,
"Sam bana son tafiyarka kabeer saboda ina
girmama lokacin da duk muka kasance tare, duk
lokacin da zamu kasance tare to lokacine mai
tsada da muhimmanci agareni, dan Allah kar
kayi nesa dani, ka daure ka amsa gayyatar
zuciyata nason yin kawance tareda kasancewa
da taka zuciyar.."
"Karki damu bazan ki amsa gayyatar zuciyarki
ba domin tuni tawa zuciyar ta dade da aminta
da taki.."
Wani farin cikine ya mamaye zuciyarta wanda
yakasa boyuwa akan fuskarta,
"Yanzu to sai yaushe zaka dawo?"
"Zan dawo bada dadewa ba"
"Dan Allah kar kasa zuciyata adamuwa, wallahi
idan har baka dawoba zan iya makancewa
domin kaine hasken idaniyata..."
Murmushi kabeer yayi tareda janyo cheque
dinshi ya dauki biro ya rubuta mata kudi sannan
yayi signing ya mika mata,
Wal tayi da idonta tareda kallonsa,
"50,000 baiyi yawa ba kuwa? Anya ayi haka?"
"Babu komai is just the begining.."
"Wato next time na tsammaci fiyeda haka
kenan? Tafada acikin ranta afili kuwa sai ta
murmusa tace,
"To nagode Allah yabamu ikon rikewa junanmu
amana, agaida iyali.."
"Zasuji"
Fita tayi ta tsaya tana daga masa hannu har ya
bacewa ganinta....
*_Ummi Shatu_*
[7/20, 6:35 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*25*
~~~Wani irin murmushi tayi wanda ita kadai
tasan ma'anarshi tareda furta,
"Yaro yarone, yaro bai san wutaba sai ya taka,
kabeer kenan da sannu zaka gane wacece asabe
mc.."
Juyawa tayi ta nufi cikin gida cikeda takunta na
k'asaita.
Abangaren kabeer kuwa hankalinshi kwance
yake driving yana sauraron music kusan
kowanne bayan 15 minutes sai asabe ta kirashi
taji ya hanya, nadiya kam tana gida bata san
abinda ke gudana ba amma koda taga 3 na
kokarin yi kabeer bai dawoba yasa ta kirashi
awaya anan yake cemata yana hanya yakusa
karasowa,
Tunda ya dawo yana shiga falonta taji wani irin
fitinannen kamshi wanda ita dai a iya saninta
yaya kabeer bashida turare mai makamancin
kamshin wannan amma sai bata zargi komai
aranta ba nan ta gabatar masa da abincin da
tayi tuwon shinkafa miyar agushi,
Jan bakinshi yayi yai shiru bai sanar da ita
komai ba agameda tafiyar da yayi haka itama
bata tambayeshi ba domin tasan yana yin
yawan tafiye tafiye musamman ma yanzu da
yafara business.
Tunda kabeer yaje gidan asabe sau daya yaji
tayi masifar shiga ransa sam baya samun
nutsuwa har sai ya kirata yaji muryarta, nan
zatabi ta kalaminceshi da zancenta na yaudara
mai cikeda makirci wanda tayi masa ado da
birikanci,
Dolensa babu shiri yasake shiryawa ya koma
cikin kano yaje yaganta nan tabi ta cikashi da
kayan motsa baki sannan ga shiryayyiyar fried
rice wadda taketa faman kamshi,
Sai da yagama cin abincin ya koshi sannan
tayiwa kawayenta waya sukazo suka gaggaisa
dashi domin dama tanata basu labarin cewa tayi
babban kamu tasamu wani alhajin yaro wanda
kuruciya ke daukarsa dan haka ita yanzu aure
zatayi,
Bayan sun gama gaisawa da kawayen asaben
ne kabeer yabasu kyautar dubu hamsin,domin
shi yanzu dan yayi kyautar dubu hamsin ba
wani abu bane,
Daukar asaben yayi suka fita bayan ta shiga
daki ta sake sabuwar kwalliya tareda sabuwar
shiga, cikin wata sabuwar shadda ta fito pink
colour dinkin riga da skirt Wanda yayi mutukar
kamata ta yafa wani dan yalolon gyale sai
kamshi take zubawa nan suka fita, wani babban
store yafara kaita taje ta lodi kayan da take
bukata irinsu man shafawa, sabulun wanka,
cosmetics da sauransu nan kabeer ya biya kudin
daga nan kuma suka wuce wani hadadden park,
Dakyar asabe tabarshi yatafi bayan ya mayar da
ita gida,
Haka yaci gaba da sintiri yana zuwa gidan
asabe hira ita kuma dama ta dade dayin shiri
akansa nan taci gaba da dorashi awata hanya
wadda shi kansa bai saniba, lokaci kadan yaji
bazai iya rayuwaba sai da ita, sonta yakeji
acikin zuciyarsa kamar me,
Babu bata lokaci yafara shirin neman aurenta,
abbanshi ya sanarwa cewar suje jos wurin
iyayenta su nemo masa aure nan abba yace sai
sunyi bincike tukunna saboda sauran auren ma
da ya nannema abaya duk sai da akayi bincike,
Abba da kansa yasa aka bincika masa wacece
asabe mc nan aka fede masa daga biri har
wutsiya, cikeda takaici abbanshi ya shiga gida
ya tarar da mamansu tana aikin girkin tuwon
dare,
Akofar kitchen din ya tsaya ya dafa bango,
"Kinji kuma abinda yaron nan yake son jawo
mana ko?"
Cikin rashin fahimta mama tafito tana cewa
"wanne yaron kuma?"
"Kabeeru mana, wai aure yake nema auren kuma
yarasa wacce zai zabo sai yar bariki, duk yan
matan garin nan basuyi masaba sai yaje ya
auro wadda bata da tarbiyya, wadda tabaro
gidan iyayenta ta taho yawon tazubar.."
Salati mama tafara yi tana tafa hannu,
"Kabeerun ne zai janyo mana wannan abin
kunyar agari?"
"Shi dai.., amma yanzu zan kirashi zan
gargadeshi da babbar murya, wallahi wannan
auren ban yarda dashiba, mutukar nine ubansa
ni na haifeshi kuma yana ganina da wannan
darajar to kuwa bazai auri asabe mc ba.."
"Yo Alhaji ai dama maganar auren wannan
yarinyar ma babu ita, ga matarsa nan yar
mutunci jininsa wacce tataso cikin tarbiyya,
wallahi bazai yiyuba.."
Zaro waya daga cikin aljihu abbanshi yayi ya
kirashi yana dagawa yaji yace,
"Kai kabeeru idan kagama abinda kake kazo
gida ina son ganinka"
Cikeda murna yabar abinda yake yi zai fita
nadiya dake kitchen tana girki sai sallama kawai
yayi mata yace zaije abbanshi na kiranshi,
adawo lafiya tayi masa saboda bata san abinda
ke faruwa ba, cikin kwarin gwiwa ya nufi gidan
iyayensa saboda duk a zatonshi andace akan
maganar aurensa da asabe mc........
_Sakon fatan alkhairi ga masoyan ummi shatu
masu sonta masu kaunar rubutunta akoda
yaushe suna bibiyarsa..._
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 8:23 AM] Ummi A'isha🏻: [7/22, 7:43 AM]
Ummi A'isha *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO*
*26*
~~~Babu b'ata lokaci yaya kabeer ya shiga
motarsa ya figeta bai zame ko inaba sai gidansu
duk a tunaninsa abba da mama sun amince da
maganar auren da zai kara amma koda yaje sai
ya tarar da sabanin haka,
Mama tana ganinsa ta zabga masa wata harara
wacce rabon da yaganta tayi irinta tun yana
yaro karami,
Zama yayi yagaishesu nan kowannensu ya amsa
fuskarsa adaure,
"Kabeeru maganar auren wannan yarinyar da
kayi ina mai baka umarni a matsayina na
mahaifinka ka janyeshi sannan ka nisanceshi
har abada, ko bayan raina ban yarda ban kuma
laminta ba ka auri asabe mc.."
Cikeda fargaba gamida mamaki mai hadeda
tashin hankali kabeer ya dago ya kalli abba
saboda abinda yaji abban ya fada ba karamin
sakashi acikin rudu yayiba,
"Abba saboda me?... "
"Saboda mune muka haifeka ba kaine ka
haifemu ba dan haka yazama dole kayi mana
biyya,
Kabeeru ai kabani mamaki ban taba sanin cewa
haka kakeba sai yanzu, ashe dama baka da
hankali baka da nutsuwa?
Ai kabeeru ko mutuwa mukayi bai kamata kaje
ka cusa kanka acikin abinda zai dameka ba,
kana zaune da matarka lafiya babu tashin
hankali babu komai shine zakaje ka auro
gantalalliya marar mafadi,wadda bata samu
yabo ba, yarinyar da bata gaban iyayenta zaman
kanta take..."
Mama ta karasa maganar tana faman
numfarfashi,Kafin ta dora da cewa,
"To wallahi baka isa ba, ba zaka shigo mana da
ita cikin zuriyarmu ba muddin mune muka
kawoka duniya.."
Tana rufe bakinta abba ya dora daga inda ta
tsaya nan suka hadu suketa yimasa fada ta inda
suke shiga ba tanan suke fitaba,
In banda gumi babu abinda yake hadawa domin
babu abinda yake so yanzu kamar asabe, nan
su abba suka yimasa kaca kaca ya tashi ya tafi,
Hankalinsa ya tashi iya tashi, amma bai bari
nadiya ta ganeba haka ya daure yabar abin
acikin ransa shi kadai da niyyar idan su mama
sun huce zaije ya shawo Kansu.
Sati daya yabasu kullum yana zuwa gidan
amma bai kara tada maganar ba har sai da sati
daya yacika da fadan da suka yimasa aranar
yaje gidan yafara lallashin mama,
"Mama dan Allah kubarni nayi auren nan, kuyi
min afuwa domin kamar jihadi zanyi..."
"Kai kabeeru idan baka tashi kadaina yimin
maganar nanba wallahi sai naci mutuncinka"
Abba ne yafito daga cikin dakinsa yana kallon
kabeer din ransa abace,
"Kabeeru maganar nan bata wuceba? Ai mun
gama magana aure nace bazaka yishiba
mutukar nine na haifeka dan haka katashi kafice
karka kuskusa ka sake zuwar min da magana
makamanciyar wannan, kaje ka kula da matarka
yar uwarka da yayanka idan kuma kaki zan
sassaba maka.."
"Kayi hakuri abba.." Kabeer yafada tareda tashi
ya fita,
Abubuwane suka hadu suka dagula masa lissafi
domin kullum asabe damunshi take akan
maganar aure sannan gashi iyayensa sunki
amincewa alhalin shikuma yana mutuwar sonta,
Shiryawa yayi yaje wurin asabe ya sanar mata
da halin da ake ciki nan ta rinka famfashi tana
zugashi tana nuna masa cewar ko babu yardar
iyayensa zai iya aurenta dafarko bai yarda ba
amma koda tafiya tayi tafiya sai ya amince, nan
yabata makudan kudi yace ta hadawa kanta
lefe,
A Tsakaninsu suka saka date din daurin aurensu
sati uku masu zuwa,
Sati ukun na cika kuwa shida abokansa suka tafi
jos aka dauro masa aure da asabe mc batareda
iyayensa sun saniba ita kuwa nadiya dama ko
zance makamancin wannan bata taba saniba,
Aranar da aka dauro auren suka dawo shida
abokansa, nadiya na cikin daki ta fito daga
wanka tana shiryawa ya shigo cikin gidan nan
ya iske su fadeel afalo da fadeela suna wasa
akan motar wasansu,
Wasa ya danyi musu sannan ya shiga wurin
nadiya, tana kokarin daura dan kwali kenan ya
shiga nan ya zauna agefen gadonta yana
kallonta,
"Nadiya magana nazo muyi.."
Zama taje tayi akusa dashi, "to gani"
"Nadiya dan Allah ki fahimceni, karki ga laifina,
ba laifina bane haka Allah ya kadararta ki dauka
cewar wannan abun kaddara ne.."
Gaban nadiyane yafara faduwa saboda sai ta
zargi cewar ko rasuwa akayi ko kuma wani abu
makamancin haka,
"Yaya kabeer wai menene? Dan Allah ka
gaggauta fada min.."
"Nadiya na kara aure yau, an daura min aure da
asabe m..."
Tsaye ta mike tana kallonsa afirgice nan
hankalinta ya tashi,
Bakinta yana rawa ta furta, "yaya kabeer aure
ka kara? Shine baka sanar dani zaka kara
aureba..?"
Tashi yayi ya rikota zuwa jikinsa nan ta fincike
tana zubarda hawaye, ko takansa bata biba ta
fita tana kuka, hijab dinta ta dauka afalo ta
saka su fadeel agaba suka fice nan yabiyota
yana kokarin tsayar da ita amma taki,
Kafafuwansu fadeel ko takalmi babu amma haka
ta tisasu agaba suka hau titi....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 7:49 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*27*
~~~Ko sauraron kiran da yake yimata nadiya
batayiba tayi tafiyarta tareda tare adaidaita sahu
nan ta shige itada yaran, da hannu take yiwa
mai adaidaita sahun kwatance saboda kuka take
yi har sukaje kofar gidansu kabeer,
Mama tana daki tana salla su aisha nafalo sai
ga nadiya na kuka, dukkaninsu rudewa sukayi
saboda basu san abinda ke faruwaba gashi
kuma sun ganta sai kuka take,
Kafin mama ta fito har abba yashigo yana cewa,
"Wacece tazo tabar dan adaidaita sahu awaje
bata bashi kudinsa ba..?"
"Anty nadiya ce.." A'isha tafada tana kallon
nadiya cikeda tausayawa, komawa abba yayi
yaje yabiya dan adaidaita sahun sannan ya
dawo cikin gida,
Fitowa mama tayi tana yin sallama daga sallar
da takeyi ko addu'a bata zauna yiba,
"Nadiya menene? Meya faru? Keda kabeerun
ne?" Mama tayi mata wadannan tambayoyin
cikin rudewa,
Kai nadiya ta daga alamun ehh,
"To meya hadaku?"
"Wai aure ya kara shine sai bayan andauro
auren yazo yana fada min.."
Salati mama ta rafka tareda rike habarta, nan
abba ya shigo cikin falon cikeda mamaki,
"Kikace aure yayi? A ina?"
"Abba a jos, yanzu yazo yana fada min"
Kafin wani yasake magana sai ga kabeer din ya
shigo afirgice,
Fada abba ya rufeshi dashi tun kafin ya zauna,
"Auren da muka hanaka sai da kaje kayi ko
saboda baka daukemu da muhimmanci ba baka
ganin mutuncinmu, to tunda ka zabi haka kaje
kayi duk abinda ka gadama amma kasani
yazama dole ka saki nadiya, dole ka sakar musu
yarsu domin bazaka hadata da cutar hawan
jiniba"
"Cutar hawan jini kuma ta nawa? Ai yadade da
dora mata ciwon hawan jini sai dai aguji ciwon
zuciya kuma.." Mama tafada cikin fada,
Cikeda bacin rai abba yasake magana cikin
tsawa,
"Ka saketa nace, ka sakar musu yarinyarsu tun
kafin bakin cikinka ya kasheta.."
Zubewa kabeer yayi akasa ya fara rokon abba,
"Dan Allah abba kayi hakuri wallahi ina son
nadiya, dan Allah karku raba auren nan wallahi
ina sonta.."
"Tashi ka fice daga gidan nan, ko bakaji?
Katashi ka fita tun kafin ranka ya baci"
Abba ya nuna masa hanyar fita, nan kabeer
yatashi yafita nadiya kuwa inbanda kuka babu
abinda takeyi, fada mama da abba suka cigaba
dayi abba yana cewa bazai yarda ba kuma
yazama dole sai yasaki nadiya,
Kowa nagidan saida hankalinsa yatashi amma
gidansu nadiya har lokacin su mama basu san
abinda ke faruwa ba, cikin wannan tashin
hankalin aka kwana, yanda nadiya taga rana
haka taga dare sai kuka data kwana tanayi
domin hankalinta yatashi sosai,
Washe gari da sassafe saiga yaya kabeer ya
dawo gidan nan abba yasake fatattakarsa yatafi,
A'isha da Fati abba yatura sukaje suka debowa
nadiya kayanta da kayansu fadeela, daukarsu
yayi zuwa gidansu nadiya,
Tunda mama tagansu tasan ba kalauba nan
jikinta yabata cewar da akwai abinda yafaru,
rungume mama nadiya tayi tana kuka mai ban
tausayi nan itama maman tafara hawaye mai
zafi,
Abbansu nadiya abban kabeer yasamu ya
kwashe duk abinda yafaru yafada masa sannan
kuma yace raba auren nadiya da kabeer zaiyi
tunda kabeer ya nuna masa bai isaba,
Nan mama tasake jin wani tashin hankalin, iya
jiya kadai har nadiya ta fita hayyacinta tayi
wata iri da ita,
Saboda tsananin tashin hankali hawan jininta
saida ya tashi gashi kwata kwata takasa cin
abinci ko ruwa takasa sha,
Nan abban kabeer yace tatashi sutafi itada
yaran, ko uffan batace ba tatashi tabishi nan ya
kwashesu sai garin sumaila gidan kanwarsu
hajiyan sumaila,
Can yabaro su nadiya ya juya yakoma rano,
hajiya wacce su nadiya ke kira da umman
sumaila saka nadiya tayi agaba tayita yimata
nasiha tana bata hakuri, dakyar tasamu taci
abinci dan kadan ta kwanta bayan ta kashe
wayarta domin kabeer sai faman kiranta yake
shiyasa takashe,
Sai da tayi sati lokacin hankalinta yafara
dawowa cikin jikinta sannan ta kunna wayarta
nan taga massages rututu na yaya kabeer naban
hakuri, ko kulawa batayi ba bare tabada reply,
Shikuwa kabeer ya shiga damuwa mutuka domin
abba da mama sun juya masa baya, hatta
kannensa babu wanda yake kulashi, yaje
gidansu nadiya kuwa yafi sau ishirin mama tana
cemasa wallahi bata san inda abbanshi yakai
nadiya ba,
Sati biyu ya dauka yana zirga zirga amma babu
me kulashi, duk da yana cikin damuwa haka ya
karasa gyaran part din asabe wanda yake dauke
da babban falo da bedroom da toilet aciki kamar
na nadiya amma kitchen dinsu awaje yake saidai
kowa da nata,
Ana gama gyaran gidan akazo aka yiwa asabe
jere nan aka kawota gidanta, Sam kabeer baya
cikin hayyacinsa amma saida asabe tasan yanda
zatayi ta kalallameshi ya kulata nan kuma suka
fada duniyar soyayya koda yaushe suna tare
suna shan soyayya amma kullum yana zuwa
gidan iyayensa duk da babu wanda yake kulashi
idan yaje.
Nadiya kam yanzu zuciyarta ta dan huce tayi
sanyi saboda kullum umman sumaila cikin
yimata nasiha take tana kwantar mata da
hankali hakan yasata sakin ranta abu dayane
yake damunta yawan tambayar dasu fadeela ke
yimata kullum wai ina abbansu su suna son
ganin babansu,
Duk lokacin da suka yimata wannan tambayar
kuka take domin bata da amsar da zata basu.
Tunda asabe mc ta tare babu wani wanda ya
leka gidan daga cikin dangin kabeer babu wanda
yasanta itama babu wanda tasani acikin
danginsa, sai dai koda yaushe cikin soyewa suke
basa aikin komai sai soyayya, ko girki batayi sai
dai suci take away,
Watansu uku da aure komai yafara sauyawa
domin hankalin kabeer yafara tashi da rashin
nadiya saboda yasan itace sirrinsa, gashi ko
kusa bazaka taba hadata da asabe ba, domin
asabe irin matan nanne masu son jiki ko kadan
bata son aiki, bata girki sai dai aci take sway ko
sharar dakinta bata iyawa nan gidan ya kazance
idan yayi mata magana tace bazata iyaba dan
haka dole yabarta tasamo yar aiki wata
dattijuwa mai suna hajjo,
Fushin da su mama sukeyi dashi har yanzu basu
huceba sannan kuma yanzu tunaninsa gaba
daya ya raja'a akan nadiya da yaransu dan haka
yafara nemarwa kansa mafita wato hanyar da
zaibi yadawo da nadiya.....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 7:54 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*28*
~~~Gaba d'aya hankalin kabeer yanzu ya koma
kan nadiya domin sai mutum baya nan kake
gane amfaninsa, sai yanzu yagama tabbatarwa
da cewar nadiya itace jin dadin rayuwarsa, itace
farin cikinsa, itace sirrinsa,
Gidansu yaje duk da cewar yasan babu mai
saurararsa, abba yasamu akofar gida yana
kishingide akan tabarma yana sauraren radio
nan ya tsugunna agabansa yana gaidashi amma
abba ko kallonsa baiyiba daga karshema sai ya
tashi ya kwashe shimfidarsa ya shigewarshi gida
yabarshi, cikin damuwa da tashin hankali kabeer
yabi bayan abba amma ko saurararsa baiyiba,
Wurin mama yaje wacce ke cikin kitchen tana
fere doya nan itama tayi watsi dashi kamar bata
san yana wurinba ko kallonsa batayi ba bare ta
amsa masa gaisuwarsa,
Iya tashin hankali yashiga domin yasan fushin
iyaye ba abun wasa bane, rokon mama yafara
cikin muryar nadama kamar zaiyi kuka abin d'a
da uwa sai ita ta dan sakko ta saurareshi nan
yaketa rokonta akan ta taimaka masa nadiya
tadawo gareshi, cemasa tayi yaje yasamu
nadiyan yabata hakuri idan taga zata dawo to
idan kuma bazata dawoba shikenan,
Tashi yayi yafita da niyyar zuwa gidansu nadiya,
cikin sa'a itama ranar suka zo gida itada
umman sumaila dasu fadeel domin umman
sumailan ta fahimci cewar nadiya tana bukatar
ganin gida shiyasa tace su shirya suzo,
Koda yaje gidan nadiya banza tayi dashi amma
su fadeela na ganinshi suka tafi dagudu suka
fada jikinsa nan ya rungumesu yana jin sonsu
har cikin ransa,
Bin nadiya yayi daki bayan sun gaisa dasu
mama Allah sarki mama mace mai kirki da
kawaici domin tunda abunnan yafaru bata
nunawa kabeer komaiba ko canjin fuska bai gani
atare da itaba,
Tana kwance akan gado Amira na zaune tana
assignment ya shiga, tashi Amira tayi ta fita
shikuma yakarasa bakin gadon da take kai,
jinshi tayi kawai ajikinta ya rungumeta kamar
zai mayar da ita cikin cikinsa, ko daga idonta ta
kalleshi batayi ba nan taji yafara rokonta bayan
yasake kankameta,
"Dan Allah nadiya ki kara yimin alfarma, ki sake
bani second chance, kiyi hakuri ki dauki kaddara,
wallahi ke ce rayuwata, nashiga damuwa na
rashinki domin na tabbata babu macen da zata
iya kula dani kamar ke, dan Allah kiyi hakuri ki
koma dakinki.."
Har yayi ban hakurinsa yagama nadiya bata
kulashi ba, duk yadda yaso ta saurareshi haka
ya hakura yatafi batare da nasara ba, nan kuma
tun daga wannan lokacin ya shiga kai kawo da
sintiri agidan, ita nadiya yanzu haushinsa takeji
sosai sannan bata jin sonsa ko digo acikin ranta
dan haka ranar da umman sumaila zata tafi tace
zata bita amma mama da umman suka hanata
sukace tayi hakuri ta zauna nan tayi kuka kamar
wadda aka yiwa mutuwa, ko hucewa daga kukan
batayi ba sai gashi yazo nan ya tisata agaba da
lallashi yana bata hakuri, yau dinma bata kulashi
ba dai haka suka cigaba dayi kullum sai yazo
amma bata yimasa magana sai yaransa ne
kurum ke maraba da zuwansa,
Ahaka sai da suka dauki sati biyar yana wannan
zirga zirgar daga karshe abba da mama suka
kirata suka yimata nasiha akan tayi hakuri ta
koma dakinta tunda mijinta nasonta, bata son
tona masa asiri domin akoda yaushe ta
daukeshi a matsayin sirrinta shiyasa tayi shiru
bata fada musu irin rayuwar da suka yi dashi
tun daga farkon aurensu ba, dayake abbanta
yana son ta koma dakansa yaje ya zabo mata
set din kayan daki masu kyau da kujeru, komai
na daki sai da abba ya sauya mata sabo babu
abinda yabari, kayan kitchen ne kawai yabata
kudi yace ta siyi abinda take so,
Kannen kabeer fati da A'isha da Amira kanwarta
sune sukaje suka shirya mata kayanta nan
dakinta da falonta yafito tamkar na sabuwar
amarya domin komai sabone, har suka gama
aikin suka tafi asabe bata nan,
Adaren ranar yazo ya daukesu, ko kallansa
nadiya batayi ba har sukaje gidan, dama dakinta
shine na karshe na asabe na farko nanma ko
kallon sashen asaben batayi ba tawuce abinta,
Har wani rawar jiki ta lura yakeyi amma ta
shareshi, baiyi fushiba yabita dakinta lokacin
tana kwantar dasu fadeela bayan sunyi bacci,
Zama yayi agefenta jikinshi cikin nata, jelar
kitsonta yakamo yadora kansa akan kafadarta
yafara bata hakuri,
"Nadiya kiyi hakuri ki yafe min kidaina wannan
fushin dani dan Allah.."
Juyawa tayi ta kalleshi tareda zuba masa
kyawawan idanuwanta......
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 8:01 AM] Ummi A'isha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*29*
~~~Ta dade tana kallonsa idonta cikin nashi
batare data yi magana ba ganin haka yasashi
rungumeta ajikinsa yana shakar daddadan
kamshin jikinta,
"Kiyi hakuri nadiya dan Allah.."
Jin yanata bata hakuri yasata yin magana,
"Shikenan na hakura.."
Bai bari takarasa ba ya rufe mata baki da nasa,
shi kansa yasan nadiya macece irin wacce
kowanne namiji zaiyi burin mallaka to amma shi
bai san abinda yake damunsa hakaba kawai dai
ya tsinci kansa acikin wani irin yanayi.
Da safe nadiya bata nuna masa komai ba ta
tashi fuskarta asake nan ta fita ta shiga kitchen
ta hada musu breakfast tafito anan taga asabe
akaro nafarko tana tsaye abakin kofar dakinta ta
dafa bango tasha kwalliya sosai ga wani uban
dauri da tayi samfarin ture kaga tsiya tana ta
faman aikin taunar cingam,
Ko kallonta nadiya batayi ba ta wuce cikin
dakinta tana dauke da farantin data doro kayan
karyawar akai,
Cikin bedroom dinta ta shiga inda yaya kabeer
yake kwance yana bacci shida su fadeel sun
sakashi atsakiya yana rungume dasu,
Tsayawa tayi tana kallon dakin nata yanda ya
hadu komai light purple haka ma kayan cikin
falonta suma komai kalar light purple ne,
Ruwan wanka ta shiga ta zuba tayi tafito tafara
shiryawa, tana cikin yin shirin yaya kabeer ya
farka nan ya zauna ya zuba mata ido domin
nadiya itace rayuwarsa,
Murmushi tayi masa ta cikin mirrior, "har ka
tashi?"
"Nasamu natashi dakyar..."
Tashi yayi ya sauka daga kan gadon ya nufi
wurinta,
"Kin yi kyau.."
Murmushi tayi ta kalleshi, "nagode"
Wucewa yayi zuwa cikin toilet yayi wanka ya
fito ya shirya suka koma falo yaci breakfast,
Tunda tadawo dai abubuwan da dan dama
dama babu tashin hankali har tayi sati uku da
dawowa nan kuma al'amura suka fara sauyawa
domin wani iskanci asabe ta tsiro dashi, duk
ranar girkin nadiya sai ta rike kabeer adaki ta
hanashi fitowa,da ranar girkinta da ba ranar
girkinta ba koda yaushe tana manne dashi,
Sannan idanma ta barshi yatafi wurin nadiyan to
kwana zatayi tana yimusu hayaniya ta hanasu
bacci ko kuma ta kunna kida ta cika gidan da
kara,
Ko kadan nadiya bata taba tankawa asabe ba
domin shima kabeer din bashida yanda zaiyi
kullum cikin bawa nadiya hakuri yake yana cewa
ta rufa masa asiri karta tafi ta barshi domin
idan har ta rabu dashi baisan yanda rayuwarsa
zata kasance ba,
Tun nadiya tana hakuri har abin yasoma isarta
domin asabe ta iya duk wani salo na bariki, sai
ta daidaici kabeer zai shigo gida idan girkin
nadiyane sai tafito half niket tazo ta tsaya
akofar daki tana taunar cingum yana shigowa
zata janyeshi zuwa dakinta,
Wannan abun yana mutukar kona ran nadiya
amma duk lokacin da suka kebe dashi bata
hakuri yake yi, dole take zaune dashi kawai dan
babu yanda zatayi amma yana mutukar
kyautatawa yaransa yana sonsu sosai haka
itama asaben tana masifar son fadeela da fadeel
uwarsu ce kawai bata so,
Yau kam tunda yamma nadiya ta tafka tagumi
tana jin ihu ihun dake tashi daga cikin dakin
asabe ita sam bata san abinda yafaru ba sai
kawai ihu takeji gamida sautin kida daketa
faman tashi,
Jin abin ya isheta yasata komawa cikin bedroom
dinta ta dauki alqur'aninta tafara karantawa
anan taji zuciyarta tayi sanyi,
Kabeer ne yashigo yana rikeda su fadeel
yazauna akusa da ita ya riko hannunta,
"Nadiya kiyi hakuri nasan mun dameki.."
"Dame?..." Ta tambaya domin ta nuna masa
abinsu bai dameta ba,
"Da ihun da mukeyi na birthday din asabe..."
Shiru tayi masa taci gaba da karatun
alqur'aninta nan ya tashi yafice, haka suka raba
dare suna bikin birthday dinnan har nadiya tayi
bacci wurin 12 basu gamaba daga karshema
bata san lokacin da suka tashiba.
Haka taci gaba da zama da asabe zaman hakuri
da kunci domin kusan kullum sai kawayen
asaben sunzo sun kafa daba suna zagin nadiya
tareda aikamata da habaici ita kuwa bata taba
tanka musuba idanma a kitchen take taji abin ya
isheta sai ta kashe wutar data kunna tayi
komawarta daki ta kwanta inyaso idan sun
gama sun tafi sai tadawo ta karasa,
Ita aduk iskancin da asabe keyi babu wanda
yake kona mata rai kamar rike yaya kabeer
datake har sai tagadama zata barshi yazo
wurinta koda kuwa ranar girkinta ne,
Wannan abu ba karamin yiwa nadiya ciwo
yakeba, yauma kamar koda yaushe dakinta yake
amma sam asabe ta hanashi fitowa sai hirarsu
da shewarsu take jiyowa nan ta tashi tafita
ranta abace ta nufi dakin asaben wanda bata
taba shiga ba sai yau, su fadeel da fadeela ne ke
zuwa subi babansu saboda yaga tana sonsu
amma shi fadeel idan akwai wanda ya tsana
aduniya to asabe ce idan sunje ya rinka kuka
kenan har sai sun baro dakin,
Afusace ta bude kofar dakin ta shiga nan taga
asaben daga ita sai wando three quarter da
wata yar bingilar riga tana kwance akan cinyar
kabeer sai dariya take kyalkyalawa can kuma
gefe mai aikinta ce keta faman goge goge,
Ai asabe tana ganin nadiya ta shigo ta daure
fuska,
"Yaya kabeer kaifa naketa jira.."
Zuruf asabe ta mike ta nufi nadiya tareda bude
fefen bala'i,
"To mahaukaciya, jahila wacce bata san hakkin
aureba mai son shiga tsakanin masoya, idan
bakida hankali ni zan koya miki, uban waye
yabaki izinin shigo min daki..."
Iya wuya nadiya tazo domin zagin da asabe ta
tisata agaba tana yimata ba kadan bane dan
haka itama ta rama,
"Gaki nan babbar jahila, ai idan ana maganar
mai raba masoya to bazaki saka bakiba domin
da mijina kika ganni amma kike burin ganin kin
rabamu, banza yar bariki marar tarbiyya wadda
tabaro gaban iyayenta tafito yawon karuwanci.."
Wani mari asabe ta zabgawa nadiya tana
kokarin kai mata na biyu kabeer yatashi ya
riketa,
"Ka sakeni in koya mata hankali, wallahi da sai
na yimiki shegen duka acikin gidan nan.."
Mai aikin asaben ce ta taso tazo tana basu
hakuri tareda rike nadiya, "hajiya kiyi hakuri kinji,
dan Allah kuyi hakuri.."
Wata ashar asabe ta mulmulo ta jefawa hajjo
mai aiki nan jikin hajjon ya dauki rawa tabar
wurin da Sauri, fita nadiya tayi tana kuka ta nufi
dakinta.....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 8:20 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*30*
~~~Nadiya nafita asabe taci gaba dure duren
ashar tana zage zage shidai kabeer yarasa me
ma zaice yayi shiru yana jinta,
Nadiya tana daki tana kuka ta dauki waya ta
kira abbansa ai kuwa lokaci kadan sai ga abba
agidan nan yazo kabeer din yafito abba ya ringa
surfa fada ta inda yake shiga bata nan yake fita
ba dama asabe bata fitoba domin abba yace shi
ba wurinta yazo ba wurin yayansa yazo,
Saida abba yayiwa kabeer wankin babban bargo
sannan yatafi da sharadin indai aka sake
batawa nadiya to zaizo yatafi da ita kuma
bazata dawoba sai dai yasaketa,nan ita kuma
nadiyan abban ya bata hakuri yatafi,
Abba na tafiya kabeer yabi nadiya daki shima ya
bata hakuri dama kuma yaji dadin zagin da
tayiwa asabe domin shima ta isheshi saboda
kazantarta da rashin bashi girma ga wulakanci
da rashin mutunci,
Iya kuluwa asabe ta kulu dan haka ta shirya
tanata masifa ta fice bayan ta kira kawayenta
awaya tanata dure duren ashar tana sanar
musu da abinda yafaru,
Tana fita hajjo mai aikinta tazo kofar dakin
nadiya ta kwankwasa nan nadiya tazo ta bude
mata, hakuri tafara bawa nadiya gamida karfin
gwiwa domin ita hajjo kirkin nadiya take gani
sannan gata da hakuri sabanin uwar dakinta,
nunawa hajjo cewar babu komai nadiya tayi
domin dama lokuta da dama idan asabe bata
nan hajjo nazuwa wurin nadiya suyi hira,
Tunda haka tafaru asabe tasake shirin rashin
mutunci agidan koda yaushe kawayenta da wasu
yara guda biyu yanmata wadanda take ikirarin
cewar kannenta ne sai suzo gidan suyita shewa
da zage zage kadan suke jira nadiya ta tanka
musu suyi mata duka amma nadiya bata taba
kulasu ba haka zasu karaci abinsu su tafi,
domin ita yanzu abinsu bai dameta ba saboda
yan uwan mijinta na tsananin sonta, kowa
wurinta yake zuwa babu wanda ya taba zuwa
wurin asabe sannan har yanzu mamansu kabeer
tana yimata hidima kamar da kuma tana ji da
ita,
Haka suka cigaba da zama asabe koda yaushe
tana kule acikin daki itada kabeer koda kuwa
ranar girkin nadiya ne, nadiya kam ta zubawa
sarautar Allah ido kallonsu kawai take, mamanta
kuwa koda yaushe cikin bata hakuri take tana
nuna mata cewar komai mai wucewa ne haka
shima yaya kamal dan uwanta koda yaushe
hakuri yake bata yana nuna mata cewa ko
wanne mutum da irin kaddararsa,
Yau dai bata san abinda yahada asabe da
kabeer fada ba amma tanata jiyo hayaniyarsu
domin hayaniyar tasuce ma ta tasheta daga
bacci nan kuma tafara jiyo karar alamun duka
kabeer yana dukan asabe sai da yayi mata lilis
sannan ya kyaleta yafice daga gidan gaba daya,
yana fita babu jimawa itama asaben ta hada
kayanta ta fita,
"Auren bariki kenan.." Nadiya tafada acikin ranta
domin ita tunda take da kabeer bai taba
yunkurin dukanta ba sai dai fada kawai amma
ita asabe ji yadda ya nada mata duka kuma
tasan yadaki banza,
Tunda asabe tatafi gidan yayiwa nadiya dadi
suka dawo rayuwarsu ta da babu takurar kowa
nan zama yayi dadi har kabeer yana cewa zata
koma makaranta tunda bata sake samun wani
cikinba nan yaje ya siyo mata form din jami'a ya
cike yayi submitting, bikin cousin dinta kamal ya
tashi a kura nan kabeer yakaita gidansu mama
saboda tare zasu tafi sannan yabata 30,000
yace takaiwa kamal gudun mawa,
Bayan dawowar nadiya daga bikin kamal da sati
uku sai ga asabe mc ta dawo amma wannan
dawowar kamar da lumana tadawo saboda ko
fita zatayi sai ta yiwa nadiya sallama cewar
tafita haka idan tadawo ma zata leko tace mata
tadawo sai dai kuma wannan bai hanasu kulewa
acikin daki ita da kabeer ba wannan abu shi yafi
komai yiwa nadiya ciwo, gashi ko abu zai siyo
agidan to bai isa ya siyowa nadiya ba sai asabe
tayita tijara tana zage zage gamida dure duren
ashar,
Makarantar ma da yace nadiya zata koma
lokacin da admission din ya fito nan asabe ta
tada rikici dolensa yahakura itama nadiya tace
bazata yarda ba nan tatafi taje ta fadawa su
abban kabeer din fada abba da mama suka fara
sukace dole sai tayi karatu ko bayaso, abu dai
ya zama rigima da tashin hankali ganin yana
neman yayi yawa abban nadiya yakirata yabata
hakuri yace ta hakura da karatun tunda shima
kabeer din yanzu baya so, nan nadiya tayita
kuka itafa gaba daya yanzu tagaji da zamanta
da yaya kabeer, zaman gidansa yagama isarta,
Ahaka ta hakura ta dawo gidan amma kullum
cikin bacin rai take domin ada kome kabeer zaiyi
yana fada mata kuma yana neman shawararta
amma banda yanzu, yanzu duk abinda zaiyi sai
dai kawai taganshi da abinsa sun gama magana
da asabe,
Kudin kunshi da na gyaran kai ya bata yau ta
fita tatafi gidansu mamanshi domin a unguwar
takeyi, can tawuni agidan mama tareda su
A'isha sai yamma suka dawo itada yaranta
suna shigowa gidan suka iske asabe mc ta dora
daya akan daya akan farar kujera akofar dakinta
tana taunar cingum tayi daurin nata kamar
yadda ta saba na ture kaga tsiya,
Kallon nadiya tayi tana farfara ido, "Ashe bakya
nan?"
"Ehhh" nadiya ta amsa mata,
"To sannu da zuwa"
"Yawwa" nadiya ta amsa a takaice tawuc,
Tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira
kabeer tana tambayarsa yana ina, nan yace
mata mota yaje daukowa amma yakusa
dawowa,
Tana daki tana shiryawa tafito daga wanka taji
knocking nan taje ta bude, asabe ce ta shigo har
cikin falonta yau tana kallon falon cikin mamaki
domin bata taba zaton haka falon nadiya yahadu
ba bata san nadiya tanada gata hakaba,
"Lafiya?" Inji nadiya,
"Ehh lafiya kiranki nazo kije kiga sabuwar motar
da muka sake.."
Asabe nagama fadin haka ta juya tafita, hijab
nadiya tasa ta nufi packing space nan taga
sabuwar mota dal hadaddiya mai tsada,
tsayawa kawai tayi tana kallon kabeer cikeda
takaici domin lokacin da yake neman shawararta
tasha fada masa cewar ya runka adana kudinsa
yana alkintawa domin yanada yara sannan nan
gaba zai sake haifar wasu kuma ya rinka yiwa
gidansu da yan uwansa abin arziki ba
albazzaranci ba,
"Kizo muje dani.."
Asabe tace da nadiya tana murmushin naci gari,
"A'a sai kun dawo"
Nadiya tafadi tareda juyawa tayi tafiyarta, nan
asabe da kabeer suka fita asabuwar motar,
ahanya asabe take ta tambayar kabeer wai
dama nadiya iyayenta suna da kudine ko shine
yayi Mata wadannan kayan falon shi kuma
yabata amsa da cewa ai baban nadiya yafishi
kudima domin tun duniya tana kwance yake da
arzikinsa,
Al'amura sun sake kwabewa abubuwan babu
sauki nadiya kawai tana zaune agidan kabeer ne
amma asabe ita ke juya gidan domin duk
lokacin data raya mata zata biyawa kabeer
kudin jirgi da ita kanta suyi tafiya sai sun dade
sannan su dawo, duk lokacin da sukayi tafiyar
sai dai nadiya tatafi gida idan yadawo sai ta
dawo nan zaita bata hakuri,
Haka take zaune zaman hakuri tun tana ganin
saukin abin har abu yazama babba domin yanzu
sunkai matsayin da kabeer ko abincinta baya ci,
baya zuwa dakinta, baya kulata koda yaushe
Allah take kaiwa kukanta tunda ada duk da
masifar asabe kabeer yana kwana adakinta
sannan yana cin abincinta domin nadiya mace
ce mai tsafta amma yanzu gaba daya ya sauya,
Ita kanta nadiya jin zaman gidan take ya isheta
kamar tana kan kaya, burinta kawai shine tabar
gidan nan takira mama take fada mata, kamar
koda yaushe nasiha mama tayi mata ta bata
hakuri tace taci gaba da addu'a, haka ta hakura
ta zauna amma rayuwar babu dadi atattare da
ita,
Fada kuwa tsakaninta da asabe kullum ne sai
dai idan bazata fito wajeba, yauma daga
fitowarta zata kitchen asabe tafara zaginta akan
wai kawai dan jiya yaya kabeer ya siyo musu
lemo da ruwa dukkaninsu wai akanme zai
siyowa nadiya, zagi sosai asabe keyiwa nadiya,
dama nadiya tagama gajiya nan tafara ramawa
asabe tazo ta kamata da kokawa wai zata
daketa itama tarama tuni suka kaure da fada
nadiya ta jefarta tahau ruwan cikinta tana duka
ahaka kabeer yazo ya iskesu nan ya janye
nadiya, dakinta ta koma ita kuma asabe taci
gaba da zage zage, daga karshe takoma daki ita
da kabeer nadiya bata san me asabe ta fadawa
kabeer ba kawai tana zaune adaki sai ganinsa
tayi ya shigo nan ya juya mata baya ya mika
mata takarda,
"Nadiya na sakeki saki biyu.."
Wata mummunar faduwar gabace ta dirarwa
nadiya duk da tagama gajiya da zaman gidansa
sannan yanzu ta tsaneshi bata sonshi amma
saida hankalinta yatashi, juyawa yayi ya fita ita
kuma ta hada kayanta tana kuka taja yaranta
suka bar gidan suka nufi gidan mahaifinta........
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/23, 7:40 AM] Ummi A'isha🏻: [7/23, 7:37 AM]
Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert
writers)_
*31*
aishaummi.blogspot.com
*D*a kuka nadiya taje gidansu mama na
ganinta ta tashi agigice domin tasan ba lafiya ce
ta kawota ba,
Cikin kuka mai ban tausayi nadiya ta mikawa
mama takardar sakin da kabeer yayi mata,
mama na karantawa tafara hawaye, daga mama
har nadiya kuka suke babu mai rarrashin wani,
Sai da sukayi kuka mai isarsu sannan mama ta
goge hawayenta tace,
"Babu komai nadiya kiyi hakuri kinji ki dauka duk
abinda yafaru dake kaddara ce sannan
jarrabawace daga Allah kuma insha Allah zakiyi
farin ciki agaba, insha Allah zaki samu ribar
hakurin da kikayi, kiyi hakuri kidaina kuka kinji.."
Tashi mama tayi taje ta damawa nadiya kunun
gyada mai zafi ta kawo mata amma ko kadan
nadiya takasa sha,
Ahaka abba yadawo ya iskesu, shi kansa yayi
mamakin sakin da kabeer yayiwa nadiya lokaci
guda dan kawai sunyi fada da asabe,
Waya abba yayiwa abban kabeer ya sanar dashi
abinda ya faru nan ran abban ya baci iya baci
babu shiri yataho zuwa gidansu nadiya fada
yake yi sosai daga karshe yace koda kabeer
yadawo bikon nadiya to kar akuskura
asaurareshi sannan tunda kabeer yayi haka to
babu ruwanshi da shi ya fita sabgarsa,
Haka suka gama jajantawa juna abban kabeer
yatafi yaje ya sanarwa da mama abinda yafaru,
iya tashin hankali itama mama ta shiga ranta
duk ya baci akan wannan maganar, ita kuwa
asabe danma kar kabeer yace zai dawo da
nadiya sai ta biya musu kudin jirgi suka bar
kasar.
Tsabar damuwar da nadiya tashiga sai da tayi
kwana 7 bata bacci, mama koda yaushe cikin
yimata nasiha take haka ma kamal cousin dinta
lokacin data fada masa cewar yaya kabeer ya
saketa takanas yazo har gida yayi mata nasiha
akan ta dauki kaddara sannan ta manta da
batun kabeer,
Da taimakon Allah da taimakon addu'ar iyayenta
tasamu tafara rabuwa da damuwa da bacin ran
dake damunta, dangana tafara yi ta dauki
kaddara domin tasan komai yasamu bawa daga
ubangijine,
Cikin yan satittika ta fara mantawa da kabeer
babu laifi tafara murmurewa, nan ta danyi kyau
tayi fari domin yanzu ta rage yawan tunani,
Kabeer kuwa shida asabe sai da sukayi sati
biyar akasar Holland sannan suka dawo Nigeria
lokacin da suka dawo yaje gidansu mama yi tayi
kamar zata dakeshi saboda tsananin bacin ran
abinda yayi, nan yayita bata hakuri amma bata
saurareshi ba bare kuma abba wanda dama shi
yadade da zare hannunsa daga al'amuran
kabeer,
Cikin lokacin bikin fati kanwar kabeer ya taso
nan su nadiya sukaje itada mama akayi komai
dasu basu nuna komai ba nan kabeer ya rinka
bin nadiya da kallo domin ba karamin kyau
tayiba,
Hankalin asabe ne yatashi da taji yana ta
ambaton nadiya nan tasan yanda tayi ta zugeshi
ya rubutawa nadiya cikon saki ukun domin bata
son yadawo da ita,
Yaro ya tura ya kira masa nadiya nan tafito
ganin shine yasata niyyar komawa amma sai ta
daure taje envelope ya miko mata ta karba yaja
motarsa yayi tafiyarsa, duk a tunaninta wani
abune ko kuma takardar bada hakurice amma
koda ta buda sai taga cikon saki dayanne da ya
rage a tsakaninsu nan ta fashe da kuka,
Bata nunawa kowa ba hatta mama sai da suka
koma gida sannan ta bata takardar tagani, itama
mama da abba yadawo takai masa,
Nasiha sosai mama da abba suka hadu suka
yimata cewar tayi hakuri ta dauki kaddara insha
Allah bazata shiga halin kaka nakayi ba,
Kiran abban kabeer abban nadiya yayi yafada
masa yanzu babu aure tsakanin kabeer da
nadiya, bakin ciki iya bakin ciki abban kabeer ya
shiga amma babu yanda ya iya tunda dan yanzu
ka haifeshi ne amma baka haifi halinsa ba.
Nadiya ta shiga damuwa sosai duk wanda
yaganta sai ya tausaya mata amma kuma da
yake tana yin addu'a sai ta samu nutsuwa nan
ta tattara kabeer da duk wani bacin ran da ya
kunsa mata da tunaninsa tayi watsi dasu, tunda
ta cire damuwa aranta tayi kyau tayi kiba tayi
fari ta rungumi yaranta,
Koda yaushe tana cikin kannenta suna hirarsu
domin yanzu kowa yagirma amir har yayi candy
zai shiga jami'a ita kuma Amira tana SS 3
yayinda waleeda da husna sukuma suke SS 1,
Rayuwar gidansu dama tun fil'azal rayuwa ce
mai tsari da dadi kuma har yanzun ma ahaka
take shiyasa nadiya ta kwantar da hankalinta
daga ita har yaranta sunyi kyau sosai,
Wata bakwai da mutuwar aurenta tana zaune
agida da yamma amir yashigo yake cemata tayi
bako, fuskarta ta gyara tafita nan taga musty
abokin kabeer,
Gaisawa sukayi yayi mata jajanton abinda yafaru
sannan yace shi idan zata bashi dama har
yanzu yana sonta zai aureta duk da bawani
jimawa yayi da aureba, nan ita kuma nadiya
tace yayi hakuri ita wallahi ba yanzu zatayi
aureba zata dade bata sake aureba, haka musty
ya hakura yatafi, nadiya na shiga gida tabawa
mama labarin yanda sukayi da musty sannan ta
kara da cewa,
"Ni yanzu duk aure ya fita akaina karatu ma zan
koma wallahi, zan dade banyi aureba"
"To Allah ya zabi abinda yafi alkhairi" inji mama
domin ita yanzu ta yiwa zuciyarta alkawarin
bazata sake takura nadiya ta shiga rayuwar
kunci ba,
Ko sati daya ba ayi da zuwan musty ba sai ga
yaya kamal yazo cousin din nadiya shima kuma
wai yana sonta zai aureta, shima hakuri tabashi
tace ita yanzu ba aure zatayi ba karatu zata
koma, ita nadiya yanzu duk ta cire maza acikin
lissafinta saboda gani take tunda yaya kabeer
yayi mata butulci ya juya mata baya babu
wanda bazai yimata butulci ba,
Kasancewar yaya kamal yasan irin halin data
tsinci kanta yasa bai matsanta mataba gashi
kuma tace ita yanzu ita da auren zumunci har
abada, ko yaranta bazata yimusu auren zumunci
ba,
Haka dai abubuwa suka cigaba da tafiya koda
yaushe zawarawa suna yimata sallama amma
taki amincewa da ko daya acikinsu, ahaka har
ta kwashe watanni 10 agida ganin zawarawa
suna yawan damunta yasata yiwa abba magana
akan tana son zata koma makaranta, abba bai
hanata ba asalima da kanshi yasamo mata form
din KUT tayi filling akayi submitting nan ta
zauna zaman jiran admission, su fadeel kuwa da
fadeela har abba yasasu awata nursery school
batare da ya fadawa abban kabeer ba domin
acewarsa shi mai kula da yaran kabeer ne koda
kuwa ba nadiya ce ta haifesu ba tunda kabeer
dansa ne.
Cikin ikon Allah lokacin da aka fitar da
admission sai ga sunan nadiya sun bata zata
karanci biology kuma dama ita yar science class
ce a secondary school nan abba yabata kudi ta
shirya ita da amir yakaita tayi registration
tagama suka dawo, sai kuma tafara jinjina
tafiyar da zatayi zuwa wudil tabar gida domin
dole sai dai ta zauna a hostel amma taso ace
amir ma a kut yasamu admission da sun tafi
tare amma ina shi a north west university ya
nema kuma yasamu inda zai karanci law,
Tunda taji ance anfara lectures ta fara shirin
tafiya, kudi mai yawa abba yabata yace taje ta
hado provision nan ta shiga kasuwa taje ta
sissiyo abubuwan da suka kamata sauran kuma
tace sai taje wudil din ta siya saboda kar
abubuwan suyi mata yawa....
_Gaisuwa marar adadi ga masoya na masu
bibiyar labarin,no one be like you my fans..._
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/23, 7:37 AM] Ummi A'isha🏻: _HASKE
WRITERS ASSO._ (Home of expert writers)
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_Writing by_
*_UMMI A'ISHA_*
*32*
*B*abu b'ata lokaci nadiya tagama duk wani
shirye shiryen tafiya da zatayi komai wanda
tasan zatayi amfani dashi ta tanadi abinta, ranar
lahadi tayi sallama dagida bayan su mama da
abba sun zaunarta sunyi mata nasiha akan ta
tsare mutuncinta sannan tasan da irin mutanen
da zatayi mu'amula,
Ji tayi kuma kamar tafasa tafiya makarantar
saboda irin yanda taji zuciyarta ta karye lokacin
da su abba nayi mata nasiha,
Saida ta hadesu fadeel ta rungumesu tana jin
kwalla acikin idonta sannan tafita duk da cewa
tasan yaranta zasu samu kulawa awurin mama
amma dole zasuyi missing dinta musamman ma
da yaya kabeer ba zuwa ganinsu yakeba domin
tunda suka rabu dashi bai kara zuwa ganin
yaranba,
Misalin karfe 3 na yamma ta isa makarantar nan
ta shigar da kayanta taje ta shirya kayanta ta
fita cikin gari ta iyo provision, saboda halin data
tsinci kanta abaya yanzu ta sakawa ranta cewar
ba zatayi aureba har sai tasan wanda zata aura
domin auren da tayi abaya aurene na kaddara
wadda ta riga fata ko kadan bata ji dadinsa ba
saboda tayi auren batare da tasan waye wanda
zata aura ba,
Wannan dalilinne yasa nadiya ta ajiye maza
agefe tayi facing din karatunta tayanda zatayi
shi tagama successfully batare da wata damuwa
ba musamman ma dataga mama da abba sun
mara mata baya,
Tunda nadiya tazo makarantar bata da kawa ko
guda daya ita kadai take al'amuranta wannan
dalilinne yasa dayawa suke yimata kallon mai
girman kai,
Zuwanta jami'a yasata tasake gogewa ta waye
saboda tana ganin hadaddun yanmata yan gayu
masu class shiyasa itama yanzu tazama mai
class sosai dama bata da matsalar kudi ko
nawa take so da zarar ta tambayi abba zai turo
mata haka shima yaya kamal koda yaushe cikin
yimata hidima yake, lokacin data yi wata daya
da tafiya sai gashi yaje mata yakai mata
hadaddun mayuka da sabulai da turaruka masu
tsada, ita dai harga Allah tasan yaya kamal
bashida makusa to amma ita kawai yanzunne
bata jin zata sake son wani da namiji bare harta
aureshi ya wahalar da rayuwarta,
Nan suka sha hirarsu taje ta iyo masa girki ta
kawo masa yaci sai kallonta yake domin nadiya
sam jikinta bai nuna ta taba aureba bare har
ace tanada yara guda biyu, duk wanda yaganta
kallon budurwa zaiyi mata,
Sai da yamma tayi sannan yaya kamal yatafi,
acikin satin itama nadiyan ta shirya taje gida
weekend, wannan shine karo na farko da taje
Gida tun bayan tafiyarta,
Lokacin da amira taganta dariya ta shiga yi
saboda sai taga nadiyan tayi kiba tayi kyau
abinta kamar ba daliba ba, waya tayiwa amir
tace tazo weekend shima yazo ranar friday
kuwa sai gashi ita dai mama duk murna ta
cikata saboda ganin nadiya ta kwantar da
hankalinta tayi kyau tayi bul bul,
"Anty nadiya ya anayin rama a school ke kuma
kina yin kiba..?" Inji amir,
"Wallahi yaya nima haka nace Anty nadiya
kamar ba student ba mu da muke gidama tafimu
kiba.." Amira ta cafke zancen tana dariya,
"Yara kwayi kwa gama dai" nadiya tafada tana
dora fadeela akan cinyarta wadda tunda taganta
taje ta kankameta taki matsawa ko ina,
Haka nadiya tagama hutunta takoma makaranta
ranar monday da sassafe, tunda takoma kuma
ta sake maida hankalinta akan abinda tajeyi
wato karatu nan tayita raba dare tana karatu
tun kafin exam tazo,
Lokacin da suka fara jarabawa kuwa daina bacci
tayi saboda karatu, bata wuni a hostel koda
yaushe tana library domin bata son damar data
samu yanzu ta wuceta,
A ranar da suka gama exam aranar ta tafi gida
bayan ta jibgawa su mama tsaraba ta kifi,
Ba karamin dadin hutunta tajiba domin tsakanin
dawowarta da dawowar amir kwana biyune,
cikin wannan hutun har gidansu kabeer taje
babu wanda yayi mata maganar kabeer haka
itama bata yiwa kowa maganarsa ba,
Sumaila ta tafi wurin umman sumaila canma
tayi kwana biyu sannan tadawo gida tafara
shirin komawa school wato zangon karatu na
biyu wanda bature ke kira da second semester.
****
"Yaya amadi yaushe zaka fara zuwa university
dinne ko har yanzu baka shirya ba..?"
Wata farar mata tas tafadi hakan lokacin da
taga shigowar wani matashin saurayi kyakkyawa
wanda ke sanye da green din t shirt da three
quarter din wando iya gwiwarsa,
Zama yayi akusa da wata yar dattijuwar mata
fara wacce ke sanye da farin glass tana shirya
beat gefenta kuma wannan matashiyar matarce
wadda tayi magana da farko hannunta rikeda
fork tana daukar kankana tana jefawa abaki,
kallo daya zakayi musu kagane cewar suna cikin
jin dadi da hutu domin tsarin falon kadai ya isa
ya tabbatar maka da gidan na masu abinne,
"Washh wallahi Anty kina takura min da yawa.."
Matashin saurayin yafada yana kokarin janye
flate din kankanar dake gabanta,
"Kai wannan yaron dadina dakai iya sharri yanzu
da badan agaban tsohuwarka akayi ba da sai ka
kunna min wuta ta dauka gaskene..."
"Hajiya kina jin anty siyama ko..?" Yafada cikin
shagwaba,
"Autana kyaleta kayi harkar gabanka kaji" yar
dattijuwar ta fada tana cigaba da shirya beat din
da takeyi.
"Allah hajiya ke kike kara ahagwaba yaron nan
abu kadan sai ki goya masa baya.."
"Ke kuma hakanne bakya so?" Hajiya ta
tambayeta tana gyara glass din dake sanye
akan fuskarta,
"To hajiya amma dai yaron nan yariga da ya
girma fa ai ya kamata ki rage shagwabashi
haka.."
"Nak'i na rage din.."
Juyawa gun amadi hajiya tayi wanda ya dauki
remote yana canja channel,
"Auta na me zakaci da daddare tuwo ko me?"
"Hajiya tuwo zanci.."
"Tuwon me? Na semo ko na alkama ko na
shinkafa?"
"Tuwon shinkafa.." Yabada amsa yana kallon
yayarshi anty siyama wadda tayi shiru tana
faman kallonsu shida hajiya domin idan akwai
abinda hajiya keso a duniya to bayan amadi ne
autanta, duk a yayanta tafi sonshi sannan tafi ji
dashi ko kadan bata son laifinsa,
Tashi yayi yana yin mika ya nufi dakinshi wanda
ke jikin na hajiya,ba karamin tsaruwa dakin
yayiba kamar dakin mace komai fes fes ga
hadaddun furnitures,
Akan tangamemen gadonshi ya zube ya jawo
laptop dinshi wadda ke jikin charge ya bude,
kwanciya yayi ya tallafe kumatunsa da
hannunshi yana latsa laptop din,
Acan falo kuwa lokacin da yaya amadi ya tashi
ya shiga dakinshi kallon hajiya anty siyama tayi
tace,
"Hajiya to yanzu dan Allah idan yaya amadi ya
tashi aure yaya zakiyi tunda naga yagama
karatu kuma gashi yasamu lecturing.."
Murmushi hajiya tayi, "ga dakinsa nan akusa da
nawa sai su zauna da matar anan.."
"Haba hajiya ai yayi musu kadan.."
"To basai kiyi tayiba yar nema.."
Tashi anty siyama tayi ta nufi dakin amadi
domin ta tsokanoshi da abinda baya so wanda
tasan tana fada masa zasuyi fada dashi take
awurin,tura kofar dakin tayi ta shiga fuskarta
kunshe da murmushin tsokana.....
*_Ummi ShatuMIJINA SIRRINA..33-43
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert
writers_
*33*
aishaummi.blogspot.com
*J*in alamun bude kofa yasa amadi dagowa
ya maida idanuwansa kan kofa nan yaga anty
siyama ta shigo fuskarta dauke da murmushi,
Zama tayi agefen gadon tana kallonsa, earpiece
din dake kunnensa ya cire ya kalleta,
"Yaron nan kana hutawarka, koda yaushe baka
fita ko ina daga gida sai gida.."
"To anty siyama ina kike son na rinka zuwa?
Club ko hotel..?"
Murmushi tayi takai masa duka yagoce,
"Idan ka kuskura muka ganoka a club ko hotel
basai mun karyaka ba.."
"To tunda bakya son na rinka zuwa wadannan
wuraren basai nayi zamana agida kusa da
hajiyata ba.."
"To naji yanzu dai maganar zee nazo yimaka.."
Shiru yayi mata saboda baya son wannan
maganar ta yarinyar nan zee ita kuma anty
siyama ta dage koda yaushe sai tayi masa
maganarta,
"Wai anty ni waya fada miki zanyi aure
yanzune? Kin san hajiya ma dai bazata bari nayi
aure yanzuba sai nanda wasu shekaru.."
"Ai dama yaya amadi ba yanzu ba sai lokacin
yayi, kawai dai yanzu daurewa zakayi karinka
kulata kana nuna mata kana sonta har kasamu
ka kamu da sonta.. Wallahi zee tana sonka
sosai"
"To anty naji amma akyaleni nayi tunani
tukunna"
Mikewa anty tayi saboda ganin yanda ya hade
rai dama tasan baya son maganar zainab ko
kadan amma ita zainab din ta dage cewar shi
take so,
"To kasaki fuskar taka mana.."
Murmushi yayi wanda ya bayyanar da kyawunsa
har kumatunsa sai da ya lotsa sosai, jan lips
dinsa ya lasa,
"Anty dan Allah kije mayi maganar wani lokacin"
Juyawa anty siyama tayi tafita tana cewa "ai kai
koda yaushe ahaka kake indai akan maganar zee
ne narasa meyasa baka son yarinyar nan.."
Komawa yayi ya kishingida bayan fitar anty
siyama yaci gaba da tsara lecture note din da
yake son fara gabatarwa a gobe litinin,
Ajiye laptop din yayi yafita falo wurin hajiya nan
ya tarar anty siyama bata nan tatafi gidanta,
zama yayi akusa da hajiya yana cewa,
"Anty siyama shine harda tafiya babu ko
sallama.."
"To ai autana kai dinne taga kanata kwallo da
kanwarta shiyasa baza ku na shiri da itaba.."
"Hajiya yarinyar ce sam ni bata yimin ba
wallahi.."
Murmushi hajiya tayi takawar da zancen domin
zee kanwar mijin anty siyama ce tadade tana
fama da radadin ciwon son amadi amma
shikuma baya sonta ko kadan saboda batayi
masaba,
"Yawwa miyar me kakeso ayi maka ne..?"
"Hajiya ai ni kin san miyata bata wuce miyar
kuka musamman ma idan taji man shanu.. "
Murmushi hajiya tayi "Allah yabar autana,
magajiya... Magajiya"
Hajiya tafara kwallawa yar aikinta kira domin
taje ta dorawa Amadi tuwo.
***
Alhaji Nasiru musa hamshakine kuma sananne
wanda yayi suna ta fuskoki daban daban a
Nigeria, ya rike mukamai daban daban ciki harda
babban minister na harkokin kasashen waje,
daga baya kuma ya koma ambassador na
Nigeria akasar Japan,
Matarsa daya hajiya Farida sai yaransu guda
biyar biyu maza uku mata,
Yaseen shine babba sai anty Dija dake binsa sai
anty siyama sai anty hameeda daga nan sai dan
autansu Ahmad wato yaya amadi wanda haka
suke kiransa tun yana dan karami, dalilin da
yasa suke kiran amadi da yaya amadi shine tun
lokacin da yana dan karami sai yayita kuka wai
shima sai ance masa yaya saboda yaji kowa
agidan yaya ake cemasa ko anty, da dafarko
anty amadi suke cemasa hajiya ta hana saboda
tace baza a bata mata sunan dan autanta ba,
Gaba daya gidan a kasar japan suka taso kusan
acan ma duk suka yi karatunsu, sai da
mahaifinsu ya rasu shekaru hudu da suka wuce
sannan suka dawo Nigeria amma anty Dija ita
har yanzu tana can zaune da mijinta da yaranta
guda biyu,haka itama hameeda tana can akasar
Turkish itada mijinta,
Ayanzu suna zaune ne acikin garin kano a
unguwar sabuwar gandu, ginin gidan kadai abin
kallone domin ginine na zamani kuma na masu
hannu da shuni.
Amadi bai jima da dawowa daga Oxford
university dake birnin London ba inda yayi
degree dinshi da masters amma yayunshi sunce
zai sake komawa yakaro karatu domin gidansu
yan boko ne na karshe hatta yayunshi mata
basa aure sai sunyi masters bare kuma namiji
shi kansa babban yayansu yaseen matarsa sai
da tagama Masters sannan ya aureta shiyasa
shima amadi sukace yanzu ya dan huta kafin
yakoma, shi dama kwata kwata ma babu wanda
yake yimasa maganar aure yanzu saboda
aganinsu har yanzu shi yarone tunda gaba daya
shekarunsa 28 yanzu aduniya, anty siyama ce
kadai ke tsokanarsa da maganar aure saboda
akwai wata kanwar mijinta zee datake masifar
sonshi duk da anty siyama ta fada mata cewar
amadi bazaiyi aure yanzu ba domin ita kanta
anty siyaman sai da takai shekaru 30 sannan
tayi aure haka babbar yayarsu ma anty dija,
haka itama hameeda sai da takai 31 domin su
yan bokone kuma dayake sun dade a turai yasa
rayuwar turawa sukeyi gaba daya kuma dama
gasu farare sosol kyawawa kamar larabawa.
K'arshen gata amadi yana ganinsa sosai amma
kuma duk da gatan da yake samu hakan baisa
ya iskance ba domin tarbiyar gidansu tarbiyace
mai kyau sannan kuma iyayensu sun tsaya kai
da fata sun kula da rayuwarsu, har yayi Oxford
university yagama bashida aboki ko daya bare
kawa mace domin yayansu yace duk ranar da
yaganshi da mace sai ya targadashi tun yana
shekararsa tafarko a jami'a yaseen yayi masa
wannan gargadin shiyasa babu ruwanshi da
mata asalima ko kulasu bayayi duk da yana
ganinsu a school fal dasu da yawa yanmata
suna cewa suna sonshi saboda yanada kyau
amma baya shiga harkarsu kwata kwata ma shi
bai taba yin budurwa ba domin yayansa yace
masa bazaiyi masa aure yanzu ba sai ya mallaki
hankalinsa da abin hannunsa yanda zai iya kula
da kansa da iyalinsa sannan idan ya tsaya kula
yanmata kaishi zasuyi su baroshi, wannan
dalilinne yasa amadi baya kula kawaye da
abokai sai ko cousins dinsa domin mahaifinsu
dan asalin kano ne nasarawa local government,
hajiya kuma yar borno ce.
***
Ranar Monday amadi ya shirya yasaka
manyan kaya blue din yadi mai tsada da takalmi
baki yafito,
"Autana ina hular kuma? Ai yakamata kasaka
hula saboda kar daliban naka su rainaka.."
Hajiya tafada tana zuba masa breakfast, kanshi
ya shafa ya shafo sumarsa sannan ya kalli
hajiya,
"Wallahi hajiya ni banson saka hula gaba daya.."
"Daurewa zakayi autana, kasani ma ko kasamo
matar acan..."
Dariya yayi yaja flate din farfesun kayan ciki
yafara ci, yana cin abincin suna hira da hajiya
har yagama yaje ya dauko blue din hula kalar
yadin dake jikinsa yasa yayiwa hajiya salla
yafita yana rikeda laptop dinshi da iPhone
dinshi,
Wata rantsattsiyar mota sabuwa fil kirar BMW 7
new series yabude ya shiga kalarta black nan
yafita daga gidan ya tasamma KUT wudil wato
university of wudil, kasancewar ya iya gudu a
mota yasashi zuwa da wuri domin a ka'idar
time table din daliban da zaiyiwa lecture karfe
10 ne daidai, 9:55 ya shiga cikin makarantar
yaje admin block ya ajiye motarsa ya fito yana
rikeda iPhone dinshi,
Daidai lokacin nadiya tafito daga admin din tana
sanye da bakar riga doguwa mai stones ajiki
tayi rolling da jan gyale,
Karaf idanuwansu suka hadu da juna, b'ata rai
nadiya tayi yayinda shikuma amadi ya tsaya ya
zuba mata manyan sexy eyes dinshi.......
_Sakon fatan alkhairi ga dunbin masoyan ummi
A'isha aduk inda suke.._
*_Ummi Shatu_*
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*BY*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert
& perfect writers)_
_Every day begins with new hopes and
dreams, but not all of them make it to the most
memorable days of my life list, The day we met,
is one of them, It will always be one of my most
favourite days. Have a very happy birthday and
may God bless you with everything_
*HBD DAUGHTER MEENAL*
*34*
aishaummi.blogspot.com
*T*sawon yan sakanni masu yawa
idanuwansu sarke cikin juna, nadiya ce tayi
gaggawar dauke idonta daga cikin nasa bayan
ta sake tamke fuskarta,
Binta da kallo Amadi yasake yi bayan ta wuceshi
tana mai yin dan siririn tsaki domin ta tsani
taga namiji yana kallonta yanzu,
Wucewa tayi ta nufi ajinsu dama time table taje
ta gano,
Rufe kofar motarshi yayi ya dauko wayarshi ya
kira class rep din wadanda zai yiwa lecture din,
Cikin makarantar ya nufa ya tasamma ajin da
daliban ke zaman jiransa, nadiya tana zaune ta
dukufa tana neman bironta acikin jakarta amadi
ya shigo, jin ajin yayi shiru kowa ya nutsu yasa
nadiya dagowa nan suka sake yin ido hudu
dashi gabansu ne ya fadi atare a lokaci guda,
Mamakine yakama nadiya saboda jin gabanta
yanata faduwa saboda kawai sun hada ido da
wannan malamin, dauke idonsa yayi ya nutsu
saboda duk dalibai sun zuba masa ido shi kadai
kawai suke kallo,
Cikin nutsuwa yayi musu sallama abinda yayi
mutukar burge daliban, nan yafara bayani a
nutse dangane da course din da zai daukesu
sannan yace kafin yafara zai so kowa da kowa
ya gabatar da kansa, ciki kuwa har dashi dan
haka yafara da kansa cikin kwarewa da wayewa
ta masu ilmi,
"Am Ahmad Nasir..." Sannan ya nuna wani dake
zaune agefensa na dama sit din gaba alamun
shima ya gabatar da kansa, nan daya bayan
daya kowa yafara mikewa yana fadar sunanshi,
Duk amadi ya kosa azo kan nadiya domin yana
son yaji sunanta,iPhone dinshi ya kunna ya dora
akan stand din da yake tsaye yafara kokarin
lalubo lecture note din da ya shirya, yana
dagowa sai ganin nadiya yayi kawai ta zauna
nakusa da ita zai tashi nan ya dakatar dashi ya
nunata da yatsa, yace,
"Sorry, ke meye sunanki?"
Sai da ta hade rai sannan tayi magana, "Nadiya
mu'az.."
Yanda tayi maganar ahankali yasa baijiba kawai
dai yaga lebenta ya motsa,
"Sorry.." Yasake fada yana kallonta,
"Nadiya mu'az" yan ajin suka maimaita da karfi
nan ya jijjiga kai, haka daya bayan daya suka
gama gabatar da kansu,
Course outline ya zayyano musu sannan ya
dauki topic guda daya yafara yimusu bayani
akai, komai nashi yana yine cikin nutsuwa babu
hayaniya, dama kana ganinsa kaga mai cikar
kamala domin yanada suffa ta mutanen kirki,
Kowa a ajin sai da amadi ya burgeshi domin
turancin shi kadai abun burgewa ne irin yanda
yake fitar da kalmomi,
Tsawon awa daya da rabi ya dauka acikin ajin
sannan ya fita bayan ya amsa tambayoyin
daliban,
Tunda yafita zuciyarsa take nuno masa hoton
nadiya, har ga Allah shidai bai taba ganin wata
halitta wadda ta dauki hankalinsa lokaci daya
kamar nadiya ba, gaba daya ta tafi da tunaninsa
wanda har yanzu bai gane abinda hakan yake
nufiba,
Har yaje admin block ita kawai yake gani acikin
idanuwansa, office din shugaban makarantar
yaje sannan ya shiga wurin sauran lecturers din
wadanda yakeda alaka dasu yan department din
da yake suka gaggaisa ya fito,
Jikin motarshi ya tsaya ko zai sake ganin
nadiya amma hakan bai faruba ganin babu
alamunta gashi yanata tsaye a rana yasashi
bude motarshi ya shiga, hakura yayi ya tafi
amma kuma zuciyarsa cike take da hotunan
nadiya wanda taketa tunato masa dasu, tun a
lokacin yasan lallai maganar hajiya ta tabbata
da tace masa kila acan zai samo matar...
Nadiya kuwa duk haushin amadi takeji saboda
ya cika kallo gaba daya ya hanata sakewa ya
takura mata da kallo dan haka take ganin
dakyar idan zasu daidaita dashi,
Lokacin da yagama lecture ya fita ba karamin
dadi tajiba saboda ita yanzu duk wani namiji
mai kallonta baya burgeta saboda ta dawo daga
rakiyar maza yaya kabeer ya shafawa sauran
maza kashin kaji awurinta,
Sannan har yanzu yaya kamal cousin dinta bai
hakura da itaba domin kusan koda yaushe yana
yawan yimata waya ga turo katin waya da kudi
da yake yimata,Wannan ya tabbatar mata da
cewa yana nan akan bakansa har yanzu,
Tun daga ranar ita nadiya ta manta da batun
wani amadi amma shi amadi fa? Wai..! Ai ranar
da tunaninta yakoma Gida sannan shi duk a
tuninsa budurwa ce bata taba aureba bare harda
yara 2,kasa bacci yayi tunaninta ne kawai ke
addabar zuciyarsa,
Kwana biyu da ganinta duk tunaninshi ya sauya,
zuciyarsa ta kamu da kaunarta babu abinda
idanuwansa keson gani sai ita, shi bai san ai
haka so yakeba, daga ganinta sau daya sai
kawai tunaninta ya hanashi sukuni?.
Yammacine mai cikeda dadi domin wata
sanyayyiyar iskace kawai ke kadawa yayinda
tsuntsaye keta faman shawagi a sararin
samaniya, amadi yana kwance akan three sitter
a falo sanye yakeda jar t shirt da bakin boxer ya
kunna tv yana kallon kwallon kafa amma kuma
sai tunanin nadiya yafara kwankwasa masa kofa
dole tunaninsa ya rinjayi zuciyarsa yafada kogin
tunanin nadiya, har hajiya ta shigo bai saniba
domin yatafi duniyar tunani,
"Auta kosai za ayi maka ko alale?" Shiru taji
yayi bai amsa,
"Autana.., autanah.."
Sai a lokacin yaji kiran da hajiya keyi masa,
"Autanah lafiya kuwa? Kodai yunwar ce.." Hajiya
tafada tana murmushi domin azumi yakeyi duk
litinin da alhamis baya wuceshi,
"Haba hajiya yunwa sai kace wani yaro.."
"Ato nasani, ai nazata yunwace ince ko bazaka
iya kaiwa ba ka karya.."
Dariya yayi ya tashi zaune yana dafe da kansa,
"cewa nayi alale za ayi maka ko kosai?"
"Hajiya ayi kosan kawai.." Juyawa hajiya tayi
zuwa kitchen inda magajiya mai aiki take tana
ta kiciniyar hadawa amadi kayan shan ruwa,
Bin hajiya yayi da kallo aransa yana jin cewa
anya kuwa zai jure har kwana hudu batare da
yaga wannan yarinyar nadiya ba saboda yau
alhamis shikuma sai Monday sukeda lecture
dinshi....
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert
and perfect writers_
_Ina kuke? Momcyn Anas, Boddo Alka,
Hafsat mai sheriff, kunfi kowa son mijina sirrina
shiyasa nabaku page 35 tukwici kyauta, Allah
yabar zumunci.._
*35*
aishaummi.blogspot.com
*J*ingina yayi da jikin kujerar da yake zaune
azuciyarsa kuma yana tunanin cewa gaskiya ya
zama dole gobe yaje makarantarsu nadiya
yaganta ko yasamu sassauci daga radadin da
zuciyarsa keyi masa saboda ita.
Washe gari da safe yayiwa hajiya sallama
yatafi bayan ya cab'a kyau cikin wata coffee
colour din t shirt da bakin jeans, ba karamin
kyau yayiba domin ya fito akamarsa sak,
Yana fita anty siyama na zuwa gidan itada zee
kanwar mijinta, jin baya nan yasa Anty siyama
kiranshi a waya lokacin har yakusa fita daga
cikin Kano,
Yana tuki yaga Kiran anty siyama ya shigo,
dagawa yayi yana murmushi,
"Anty amadi ya muka tafka sabani?"
Yaji anty siyama tafada cikin tsokana,
"Anty siyama natafi wudil neman aure.."
Dariya yaji tayi saboda duk azatonta wasa yake
yi,
"Kaji yaro da rainin wayo,to dama zee nakawo
maka kuyi sallama saboda gobe zata koma
Malaysia hutunta ya kare.."
"Allah ya kiyaye hanya anty.."
"Ba Allah ya kiyaye hanya zakace ba zuwa
zakayi idan ka dawo kuyi sallama kaji..?"
"To anty naji.."
"Dan Allah yaya amadi karka shanyamu kaki
zuwa fa.."
"To anty sai nazo"
Katse wayar yayi yana dariya saboda yasan idan
bai amsawa anty da to ba yau wuni zatayi tana
aikin yimasa waya.
A b'angaren nadiya kuwa tun ranar laraba ta
tafi gida saboda su fadeel basuda lafiya nan
hankalinta ya tashi duk da mama tace mata
sunji sauki dama zazzabi ne amma hankalin
nadiya kasa kwanciya yayi sanin idan ta zauna a
makarantar ma ba iya karatun zatayi ba yasa ta
shirya kawai tatafi gida,tana zuwa ta samesu
suna wasansu Amira tana yi musu wainar
fulawa,
Da gudu suka zo suka dale jikinta ajiye jakar
hannunta tayi tana kallon su gaba dayansu
huciyar zazzabi ta fito musu a kan lebensu,
"Fadeelan momy kawo bakin mu gani.."
"Momy nima kinga.." Fadeel ya matsa jikinta
yana nuna mata,
Tsalle suka fara suna murna saboda ganin
nadiya suna kiran "momyn mu tadawo, momyn
mu tadawo.."
Jin ihunsu yasa mama fitowa daga dakinta nan
kuwa taga nadiya,
"Ashe dagaske suke, ni ai nazaci wasa ne.."
Mama tafada tana kokarin karasa fitowa daga
cikin dakinta,
"Wallahi dagaske ne mama gani nayi kawai gara
nataho..."
"Kai anty nadiya dama dai kina son zuwa
inbanda haka ai sun samu sauki.." Amira dake
zaune acan gefen kitchen tana suyar wainar
fulawa ta fada tana dariya,
"Yarinya dan dai ke agida kike ne baki san zafin
barin gidaba.."
Tunda nadiya tazo gida tace bazata koma
school ba sai ranar Sunday, dan haka koda
amadi yaje makarantar sai bai samu ganinta ba
haka ya dawo gida yana cikeda damuwa,
Gaba daya amadi yana cikin damuwa dan haka
alla alla yakeyi litinin tayi yaje yaga nadiya,
kwanakin ma ganinsu yakeyi sam basa gudu
sunki yin sauri,
Ranar lahadi da yamma nadiya tayi sallama da
gida takoma makaranta, ranar litinin ta fita
lecture, wata maroon din atamfa tasaka ta yafa
bakin mayafi mai stones ajiki, ba karamin kyau
tayiba tayi makeup dinta daidai misali,
Tana shiga class ko minti biyu batayi ba amadi
ya shigo,farin yadine ajikinsa da hula ko kadan
yau bata yarda ta kalleshiba bare su hada ido
amma kuma tana jin gabanta yanata faduwa,
Lokacin da yagama lecture yace ayi question
kowa sai yayi shiru jin haka yasashi rubuta
musu snap test,
Nan kowa ya dauki paper ya rubutu test din
wadda yace 10 minutes test ce kawai,
Lokacin da nadiya tazo yin submitting ta mika
masa kin karba yayi yabarta atsaye har saida
yagama karbar ta kowa sannan ya juya ya
kalleta nan yaga ta wani hade rai ta tamke
fuska kamar zatayi kuka,
"Lafiya?" Ya tambayeta tareda karbar paper
dinta,
"Lafiya lau.." Tabashi amsa tareda saurin barin
wurin,
Cije lip dinshi yayi nakasa yabita da kallo, bai
san meke faruwa ba amma ya lura kamar bata
son yin koda maganane dashi domin ranar farko
da yafara ganinta haka yaga ta bata rai ta hade
fuska,
Tattara takardun yayi ya dauki iPhone dinsa
yafita aransa yana son sanin wacece nadiya.
Kasancewar anbashi office yasashi nufar office
din nasa bashi ya bar school dinba sai yamma,
saboda bai tafi da wuri ba ahanya ma yasha
ruwa.
Daga nan bai sake dawowa makarantar ba sai
da wani satin yayi bayan yayi marking din test
din su nadiya, sosai yaji tasake burgeshi domin
yaga tana da kokari sosai, boye test dinta yayi
acikin motarsa yabarta anan dan haka koda
yaraba test din nadiya bataga tataba dan haka
ta daura niyyar binshi tayi complain bayan
yafita,
Shi kuwa dama amadi da saninshi yayi haka
yasan dolenta zatayi magana mutukar bataga
test dinta ba, komai rashin son maganarta sai
tayi,
Yana fita daga class din tafita tabishi, yana
sanye cikin wata shadda light brown, ita kuma
nadiya doguwar riga ta atamfa tasa kalar
atamfar farace sai ko digon kaloli ajiki ta yafa
jan mayafi,
"Excuse me sir.."
Yi yayi tamkar bai jitaba har saida ta sake
maimaitawa anan ya jiyo caraf suka hada ido
take gabanta ya fadi,
"Ya akayi..?" Ya tambayeta yana tafiya batareda
ya tsayaba saboda office yake son kaita,
"Sir banga test dinaba.."
"Bakiga test dinki ba?" Yayi mata wata
tambayar maimakon yabata amsar tambayarta,
"Yes Sir.."
"Ok biyoni office.."
Jin abinda yace yasata yin dan turus kamar
bazata bishiba, nan tafara tunanin to tabishi
kodai tayi tafiyarta, shikuwa tuni har yayi gaba
bai jira tagama shawarar ba....
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert
and perfect writers_
_Gaisuwa mai kima ga k'awata takaina
kuma aminiyata Maryam Qaumi ina yimiki fatan
alkhairi aduk inda kike.._
*36*
aishaummi.blogspot.com
*G*anin har yayi mata dan nisa yasata daga
kafarta tabishi zuciyarta nacemata,
"Tunda kece akasa ya zakiyi, ai durkusawa wada
ba gajiyawa bane.."
Da sake sake cikin ranta har ta isa office din
nashi wanda shi tuni har yabude ya shiga ya
zauna,
Ahankali itama ta bude ta shiga, idonsa fes
akanta domin dama k'ofa yake facing kuma nan
ya ajiye idanuwanshi,
Ji tayi kamar ta koma saboda irin yanda taga ya
kura mata ido,sannan office din nashi ba
karamin haduwa yayiba,
"Sir gani.."
"To zauna mana.." Yafada yana mai yimata nuni
da hannunshi izuwa wata kujera dake gaban
tabur dinshi, zama tayi batare data kalleshi ba,
"Mema kikace..?"
Jin tambayar rainin hankalin da yayi mata
yasata saurin kallonshi amma babu shiri ta
dauke idonta saboda ganinshi tayi dafe da
kumatunsa yana kallonta,
"Sir cewa nayi ni banga test dinaba.."
"Kuma kinyi test din?"
Kallonshi tayi tace "ehhh nayi.."
"Kinyi?"
"Ehhh"
"Waye shaidarki idan har dagaske kinyi..?"
"Sir kaima shaida ne cewar nayi.."
"Tayaya?"
"Saboda ranar sai da ka gama collecting din ta
kowa before ka karbi tawa,
Hular kanshi ya cire ya shafa sumarsa,
"Ohhh anyi haka.."
"Ok let me check.."
Nan yafara bincike binciken karya dan haka ya
Karaci bincikensa yagama batare da yagani ba,
kallonta yayi yanda tasha kunu sai abin yanemi
bashi dariya,shi yarasa bata ran me takeyi,
"Nadiya... Kinyi satar amsa ko?"
Cikin sauri ta kalleshi, "wallahi Malam a'a"
"To ya akayi taki ta bata amma ta sauran bata
bata ba..?"
"Shine ai nima abinda yabani mamaki"
"To kodai kina da aljanun sata ne?"
Ba karamin bata mata rai maganarshi tayiba
dan haka ta sake daure fuska tana deciding
cewar gara kawai ta hakura ta tashi tatafi tabar
masa test din,
"Bari nasake yimiki wata yanzu saboda gaskiya i
think bazan kara yimuku second test ba.."
"To Malam bari naje na dauko biro da paper.."
Drawer dinshi ya jawo yaciro biro da plane sheet
ya ajiye mata,
"Basai kinsha wahalar komawa ba inada su
anan.."
"Wannan wanne irin rainin wayone?" Ta tambayi
zuciyarta, "yama rainani.."
"Sir gaskiya am not ready yanzu..."
"Ok duk ranar da kika zama ready sai kizo inyi
miki.."
"Ok" tashi tayi ta nufi hanyar fita nan yaji
tamkar ya tsaidata ya sanar mata da sirrin dake
cikin zuciyarsa amma kuma yagagara yin hakan
haka yanaji yana gani ta bude kofar office din
tafita.
Naushin iska yayi cikeda takaici,
"Meyasa nakasa fada mata irin son da nake
mata?"
Zuciyarshi ce tabashi amsa,
"Ai yanzu idan ka fada mata yayi wuri kabari
kabata lokaci tukunna.."
Shawarar zuciyarsa ya dauka na zai cigaba da
bibiyarta inyaso sannu ahankali sai ya amayar
mata da sirrin zuciyarsa.
Tun daga lokacin babu abinda yasake hadasu
sai dai idan yaje yimusu lecture yaganta, ita
kuma nadiya duk yabi ya takura mata saboda ko
question ya tashi yi a class to ita zai fara
jefawa wannan abu ba karamin bata mata rai
yakeba gashi koda yaushe idan taganshi
gabanta ya rinka faduwa kenan,
Wannan dalilin ne yasata niyyar fara saka nikab
a fuskarta domin amadi yana mutukar takura
mata,
Amadi kam yanata son yasamu kofar da zai
yimata magana amma yarasa sannan kuma
haduwarsu a iya class ne ba ganinta yake awaje
ba nan yafara tunanin yanda zaiyi yaganta,
Dabarace tafado masa nan ya kira class rep din
su nadiya yace masa wacece nadiya mu'az, nan
class rep din yace watace itama a ajin take,
"Ok kace ta kirani yanzu.."
Nadiya tana zaune tagama hada kayanta ajaka
tana shirin fita class rep yazo ya fada mata
sakon amadi,
Karbar number din amadi din tayi tai saving
sannan ta mike ta fita,
Gabanta ne yafara faduwa lokacin da zata kira
number, tana shiga taji gabanta ya tsananta
faduwa,
"Hello.."
Tana jin muryar ta tabbatar da cewar shi dinne
nan taji tana neman rikicewa,
"Sir nadiya mu'az ce class rep ne yace wai kace
na kiraka yanzu.."
Shiru yayi yana jinta har sai da yaji tayi shiru
sannan yasaki ajiyar zuciya mai nauyi tareda yin
mika daga kwancen da yake akan gadonshi,
"Nadiya bakiyi test ba sannan nace kizo kiyi kin
k'i zuwa ko kina son kiyi carryover din course
dinne next year kidawo ki gyara?"
"No sir"
"To meyasa da kikace zaki dawo baki dawoba.."
"Am sorry Sir.."
"Ok to next week ki tabbatar kin zo kinyi.."
"Ok sir nagode.."
Katse wayar yayi tareda yin saving din number
dama dabararshi ya samu contact dinta to
kuma gashi ya samu yanzu saura stage nagaba.
Kamar yadda tafada masa ranar monday
bayan yagama yimusu lecture ta dan zauna ta
dudduba lecture note dinta sannan tatashi
tabishi office dinshi,
Zaune ta sameshi ya kishingida yana waya
cikeda barkwanci, katse wayar yayi ya kalleta,
"Are you ready..?"
"Yes Sir.."
Murmushi yayi tareda jan drewar dinsa yaciro
test dinta da ya boye ya mika mata,
"Ga test dinki.."
Mamakine ya bayyana a fuskarta bayan ta karbi
takardar,
"How comes..?" Ta furta har afili batare data
saniba,
"Uhm nadiya ina son zanyi miki wasu yan
tambayoyi..?"
Kallonshi tayi, "To Allah yasa nasani"
"Nadiya ke yar wanne garice?"
"Rano.."
"Anyi miki miji?"
Tambayar tasa jinta tayi tayi mata zuwan
bazata hakan yasata kallonshi da sauri tareda
girgiza kanta,
"A'a"
Wani farin cikine ya ziyarceshi,
"Nadiya ina sonki kuma so na aure bana wasa
ba, bana yaudara ba...."
"Kana sona?" Ta maimaita hakan tana kallonsa,
"Ehh ina sonki.."
Ya maimaita hakan with full confidence.....
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert &
perfect writers_
_This page is for you Nana Hafsat (miss
xoxo), & your fighting partner Hafsat Rano,nice
to meet you.... One love_
*37*
aishaummi.blogspot.com
*K*allonsa nadiya tayi cikeda takaici gamida
jin haushinsa,
"To kayi hakuri kadaina sona saboda bazan taba
sonka ba, kuma bazan iya aurenka ba.."
"Ko menene dalili?" Ya tambayeta yana yimata
kallon mamaki,
"Babu ruwanka da dalilina kawai dai kabawa
zuciyarka hakuri tadaina sona.."
"Bazan iyaba nadiya, bani nasakawa zuciyata
sonki ba dan haka banida ikon hanata ko kuma
cireshi daga cikinta.."
"To nidai bana sonka kuma bazan soka ba"
Tana kaiwa nan ta mike tabarshi da mamaki,shi
mamakinta yakeyi yanda take fada masa kiri kiri
cewar wai bata sonshi kuma bazata soshi ba,
Ganin tana kokarin fita daga office din yasashi
hanzarin mikewa yaje yasha gabanta,
Nan ta kankace ido ta sake bata rai tana
kallonshi,
"Nadiya meyasa bakya sona? Banyi miki bane
kokuma da akwai wani abu atare dani wanda
kike ganin baiyi miki ba?"
Kallonsa tayi babu annuri akan fuskarta ko
kadan,
"Ni kawai sonka ne banayi"
"Naji bakya sona amma menene dalili?" Yana
maganar ne zuciyarshi na radadi saboda yanda
take fadar cewar wai bata sonshi kanta tsaye ko
dan sayawa batayi,
"Nafada maka haka kawai nidai baka yimin ba
kuma bana sonka.."
"Kenan bakida dalilin tsanata kamar yadda
bakida dalilin kin karbar soyayyata..?"
Zuba mata ido yayi yana kallonta yana son
yagane menene asalin damuwarta da har bata
sonsa domin ayanda take yin maganar tana
yinta ne cikin fushi da damuwa hadeda bacin rai,
"Nadiya.." Yakira sunanta tareda matsawa kusa
da ita,
"Kisani wallahi ban taba soyayya ba, ban san ya
ake yinta ba sannan bansan yanda takeba,
kwatsam sai idanuwana suka ganki zuciyata tayi
na'am dake har ta kamu da sonki"
Wani bakin cikine ya sake turnuke zuciyar nadiya
domin yaya kabeer ma da irin wadannan
dadadan kalaman yayi amfani ya gurbata
rayuwarta, ya wahalar da zuciyarta, ya sanya
damuwa acikin ranta, ya rabata da farin cikinta
ya maye gurbinsa da bacin rai tareda damuwa
dan haka take ganin anyi nafarko kuma na
karshe, yanda yaya kabeer ya lahanta mata
rayuwa akaro nafarko to bazata sake bawa wani
dama yazo ya dora daga inda yaya kabeer ya
tsaya ba,
Shiyasa duk wadannan kalaman na amadi take
ganin na yaudara ne wanda babu komai acikinsu
face karya da yaudara,
"Ai nafada maka kayi kokari ka bawa zuciyarka
hakuri domin ni bana sonka sannan bazan taba
sonka ba"
Runtse idonsa yayi cikeda takaici ya budesu sun
danyi ja saboda dacin da maganarta keyi masa,
"Naji bakya sona kuma nayarda amma kiyi min
alfarma guda daya, kiyi hakuri kibarni na aureki
nikuma nayi miki alkawarin zan koyar dake
yanda zaki soni, zan mantar dake kiyayyata.."
"Ni bazanyi aure ba har abada kaga kuwa idan
hakane to babu amfanin naci gaba da
saurarenka.."
Bata sake jiran abinda zaice ba tayi gaba abinta
zuciyarta na zugi,
Kamar yadda zuciyar nadiya ke zugi da radadi
haka ta amadi shima ke zugin tana yimasa
radadi,
Kan kujerarshi yakoma ya zauna yana tunanin
abinda ke damun nadiya,
"To Kodai yarinyar nan tanada aljanu ne?" Ya
tambayi kansa domin aganinshi idan ba mai
aljanu ba wacece zatace bazata yi aureba har
abada,
Ya dade zaune a office dinsa abun yanata
damunsa sannan yatashi ya tattare kayansa ya
rufe office din yafita.
Ita kuwa nadiya abubuwan da ta fadawa amadi
tsakaninta da Allah tafada domin har cikin
zuciyarta abinda tafada gaskiyane, sam yanzu
bata da burin sake aure kwana kusa sannan ta
cire soyayya aranta bata tunanin zata sake son
wani da namiji domin tunda dan uwanta jininta
yaci amanarta ya ha'inceta gani take babu kuma
wanda bazai yimata haka ba,
Yanzu ta dade da sakawa ranta cewar ba ita
babu soyayya sannan ai ba a saran mumuni sau
biyu a rami guda daya.
Amadi cikeda damuwa yabar makarantar yafita
yana tuki yana tunanin nadiya amma ko da
wasa kalaman da ta farfada masa basusa yaji
sonta ya ragu daga cikin ransa ba shi yanzu ne
ma yake jin cewar yafara sonta,
Koda ya samu ya karasa gida, da lokacin
kwanciya baccinshi yayi wayarta yayita kira
amma taki dagawa,daga taga shine sai taki
dauka daga karshe sai ya tura mata da text
massage,
_pls peak my call, just to hear your voice
please.._
Sai da yasake kira fiyeda sau biyar sannan ta
daga,shiru tayi lokacin da ta daga wayarma taki
magana,
"Nadiya, dan Allah kiyi min magana.."
Kememe tayi taki amsawa, shiru shi dinma yayi
kamar yadda tayi suka bar kstinshi yanata
konewa,
Sunfi minti 20 ahaka taki tayi magana shikuma
yaki kashe wayar yana jiran yaji tayi magana
yaji muryarta ko zai ji sanyi acikin ransa,
"Nadiya.." Yakira sunanta ahankali wanda kanaji
kasan damuwace aranshi domin muryarshi har
tayi wani irin sanyi kalau,
Jin yana neman matsa mata yasata amsawa
saboda so take yayi ya kashe wayarsa domin
tanada uzuri amma ita ko kadan bata jin zatayi
nadama ko dana sanin wannan abun da tayiwa
amadi domin itama abaya bataji da dadiba
shiyasa yanzu dole ta dauki matakin hana sake
komawa gidan jiya.....
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
Perfect writers)_
*38*
aishaummi.blogspot.com
*S*ai da yayi fiyeda mintu biyu da kiran
sunanta sannan ta amsa,
"Ina ji.."
"Nasan kina ji ai.."
Shiru tayi sanin bazata sake magana ba yasashi
cigaba,
"Yaushe kike free inzo in ganki?"
"Babu rana"
"Meyasa?"
"Saboda ni karatu nazo yi ba soyayya ba"
Dan shiru yayi na tsawon wasu sakanni,
"Nasani, nima bance soyayya kika zo yiba.."
Daga nan shiru ta sake yi masa taki magana,
agogon dake kafe a bangon dakinsa ya kalla,
karfe 12 saura yan mintuna kuma tun 10:40 ya
kirata,
"Shikenan saida safe.."
Tun kafin yakarasa ta katse wayar kittt, ko
kadan baiji ciwon abinda tayi masa ba bare har
ransa ya baci, asalima shi dadi yaji da yasamu
zarafin jin muryarta a wannan dare.
Washe gari da safe ma bai iya hakura ba haka
ya kirata amma bata dauka ba, ganin yayi mata
2 miss called bata dauka ba yashi hakura
saboda yayi tunanin ko ta shiga lecture ne tunda
lokacin 10:30 nasafe,
Barinta yayi tayi lectures tagama sai wurin karfe
5 nayamma sannan yasake kiranta, yanzun ma
dai dakyar ta dauka tayi shiru,
"Kin fito daga lectures din..?"
"Uhm..." Tabashi amsa wanda kanaji kasan ta
dolece,
"To sannu"
Shiru tayi masa nan suka cigaba da zaman
kurame, ko tari babu wanda yayi acikinsu fiyeda
mintina 20,sai can tayi magana,
"Ina son zanje nayi uzuri"
"Adawo lafiya" shine kawai abinda yace tayi
hanzarin katse wayar, ko kadan bata son taci
gaba da kulashi balle har takamu da sonshi
yazo ya wulakantata kamar yadda yaya kabeer
yayi mata,shiyasa bata jin zata sake yin soyaya
acikin rayuwarta domin tayi tun tana yar karama
daga karshe bata ci ribaba kuma bata samu
alfanu ba to me zaisa yanzu ta sakeyi alhalin ta
mallaki hankalin kanta,
Ko kusa abinda tayiwa amadi da yamma bai
dameshi ba bare ya hanashi kiranta da daddare,
sake kiranta yayi bayan ya kwanta yayi shirin
bacci,
"Bakiyi bacci ba baby..?"
Yafada ahankali, shiru tayi bata amsa ba dama
shi dinma yasan ba amsawar zatayi ba dan
haka ya kyaleta bai matsa dole sai tayi magana
ba maimakon hakama sai kawai yajawo iPhone
dinshi ya kunna ya hau Facebook ga wayar
kuma makale a kunnenshi yasa earpiece,
"Ko kina jin bacci?"
"Eh inaji" tafada cikin kaguwa domin alla alla
take yace sai anjima,
"To kwanta kiyi baccinki basai kin kashe wayar
ba saboda ina son naji ko kina yin minshari..."
Jin yafadi haka yasata cewa, "banida charge sai
anjima"
Tun kafin ya amsa ta katse wayar ta kasheta
gaba daya ta tura karkashin pillow, wannan
dalilinne ma yasa washe gari taki kunna wayar
gaba daya saboda kar amadi ya dameta dama
kuma tafara tunanin sake layi saboda shi.
Tun safe yake kiran wayarta akashe har wurin 1,
kawai sai yaji hankalinsa yatashi bazai iya
hakura ba har sai yaje wudil ya gano lafiyarta,
Hajiya tana falo idonta sanye cikin glass tana
karanta littafi mai tsarki sai gashi yafito cikin
bakar t shirt mai gajeren hannu da blue din
wando,
"Hajiya zanje wudil yanzu nadawo.."
Dagowa hajiya tayi ta kalleshi,
"Autana lafiya? Inji dai kalau?"
"Hajiya lafiya lau, ba jimawa zanyiba"
"To ai bakaci abinci ba ka zauna magajiya ta
karasa abinci kaci sai ka tafi"
Girgiza kai yayi, "a'a hajiya barshi kawai sai
nadawo.."
Tashi hajiya tayi takama hannunsa, "to kaga
tunda bazaka jiraba zo ka cinye guntun farfesun
nan maza.."
Babu yadda ya iya haka yabita zuwa kan table,
nan ta mika masa bread da farfesun hanta
guntun wanda sukaci da safe, tana tsaye akansa
har saida ya cinye sannan ta mika masa tissue
da ruwa tana fadin,
"Yawwa kaga ai yanzu sai nafi yarda da cewar
sai kadawo sannan zaka ci abincin.."
Murmushi yayi acikin ransa yace "no body will
be like mother.."
Afili kuma yace "to hajiya sai nadawo,bye.."
Fita yayi ya tasamma wudil cikin lokaci kankani
sai gashi acikin makarantar,class rep din su
nadiya yakira domin har lokacin ita wayarta
akashe take,
Cewa yayi yaturo masa nadiya, office dinsa yaje
ya bude yashiga,
Yayi kamar minti 10 da zama sai gata ta shigo
bayan tayi knocking,
Fes ya sauke idanuwansa akanta, tana sanye
cikin pink din doguwar riga tayi rolling da farin
mayafi dan madaidaici,
Ahankali ta bude bakinta tayi sallama takarasa
ta zauna akujerar dake gaban tebur din amadi,
Kallonta yayi kafin yayi magana,
"Meyasa kika kashe wayarki?"
"Saboda ina da lectures kuma banson
adameni.."
Murmushi yayi ya lashi pink lips dinshi,
"To kidaina kashe waya, is better kisata a silent
akan ki kasheta gaba daya,
Saboda idan ankira anji akashe sai ayi tunanin
ko ba lafiyaba, kinga ni yanzu ina zaman
zamana agida kika saka nataso nataho saboda
tun safe nake kiranki amma wayar akashe
shiyasa nazo naga meya faru.."
Cikeda mamaki ta kalleshi nan suka hada ido,
ita abin nasa kamar almara take ganinsa, yanzu
kenan yana nufin purposely itace dalilinsa na
zuwa wudil yau?
"Tunda naganki kina lafiya shikenan yanzu kinga
sai nasamu damar gudanar da duk abubuwan da
zanyi.."
Ita dai nadiya shiru tayi tana tunanin wannan
kaddara, wannan wanne irin sone Allah ya
jarrabi amadi dashi akanta bayan ita kuma ba
sonshi zatayi ba,
Kallonta kawai yake yi batare da yasake yin
magana ba kamar yadda ita dinma batayi
magana ba,sai hade rai da tayi ta bata fuska
taci magani,
Sun dade ahaka kafin yace shikenan taje tatafi
shima tafiya zaiyi, batayi magana ba ta tashi ta
fita,
Murmushi yayi sannan yatashi yafita ya rufe
office dinsa,
Kafin yamma har yakoma gida, yana kan dining
yana cin abinci bayan hajiya tatashi ya kira
nadiya,
Ajiyar zuciya yayi saboda jin ta bude wayar tata
amma har yakaraci kiranshi yagama bata dauka
ba, sai text ya tura mata cewar yaje gida lafiya.
Haka al'amarin nasu ya kasance koda yaushe
yana kiranta awaya amma idan ta dauka sai dai
tayi masa shiru kudinsa yayita tafiya abanza
amma wannan bazai hanashi sake kiranta idan
anjima ba,
Yau kam ranar lecture dinshi ce, lokacin da ya
shiga class yi yayi kamar bai san tana ajinba
yayi lecture dinshi yagama, yana tsaye agaban
stand ya dauki wayarshi yafara latsawa bayan
ya gama lecture din yana jiran questions daga
daliban,
"Kizo office ina son ganinki.."
Shine abinda ya tura mata, din din, taji shigowar
text nan taga shine tana budewa taga abinda ya
rubuta, bata yi reply ba saboda dama batayi illa
dai kawai kallonsa da tayi taga ya maida hankali
wurin yiwa wani dalibi da yayi masa tambaya
bayani,
Bata fuska tayi saboda tasan duk kyawun yaya
kabeer amadi yafishi, sannan yafi kabeer
wayewa yafishi komai na rayuwa, to kabeer ma
da bai kai amadi kyau ba yayi wannan tururuwar
yan matan bareshi, sannan yaya kabeer da bai
kaishi ajiba yayi mata wannan kwarya kwaryar
wulakancin to inaga amadi?
Lokacin da taga ya kammala ya fita itama tashi
tayi tafita tana tsakin matsantawa rayuwarta da
amadi yake yi....
_Fatan alkhairi gareku masoya masu bibiyar
labarin.._
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
perfect writers)_
_Sak'on fatan alkhairi ga yayata mai sona,
(Maman meenal), Allah ya albarkaci rayuwarki
da zuri'arki gaba daya, I dey over love you my
aunty.._
*39-40*
aishsummi.blogspot.com
*B*in bayanshi tayi yana tafiya ahankali
kamar wani marar lafiya,
Kusan atare suka karasa office din nan yabude
ya shiga tareda bar mata kofar a bude saboda
yaganta tana binshi a baya,
Barin kofar a bude itama tayi taje ta zauna
ganin haka yasashi tashi da kansa yaje ya rufe
kofar ya dawo ya zauna,
"Nadiya, wai har yanzu baki sauya ra'ayinki
akaina ba? Har yanzu baki ji aranki cewar ni
masoyinki ne na hakika ba?"
Kamar bazata yi magana ba sai kuma ta bude
bakinta,
"Gaskiya banjiba, shiyasa nafada maka tun farko
cewar ka hakura dani saboda bana jin zan
soka.."
"Har yanzu bakya sona kenan..?"
"Bana sonka gaskiya"
Murmushi yayi,
"Nadiya kenan, nikuwa kina bani mamaki irin
yadda kike fada min wai bakya sona kanki tsaye,
ke ko yar karantawa ma babu, bakya tsoron
nayi miki halinmu na lecturers in kadake?"
Shiru tayi bata amsaba,
"Shikenan you can go, sai munyi waya.."
Mamaki ne yakamata saboda ita duk tunaninta
yayi fushi bazai sake bi takanta ba amma sai
taji sabanin haka,
Tashi tayi tafita yabita da kallo ya tattara inasa
inasa ya tafi,
Tun daga nan yaci gaba da yimata waya, text
da sauransu, dai dai da rana daya basu taba yin
hira ta minti dayaba sai dai kawai ta dauki
wayar tayi shiru idan yagaji yace mata sai
anjima ya kashe,
Text massage kuwa ko ya aiko mata bata
yimasa reply, gashi da zarar ya kirata yaji bai
sameta ba hankalinsa zai tashi nan zai bar duk
abinda yakeyi yatafi ganinta, har sai yaganta
lafiya lau sannan zai koma yaci gaba da
harkokinsa,
Ita abin nashi mamaki yake bata saboda lokuta
da yawa sai taganshi yazo makaranta idan tazo
sai yace kawai ita yazo gani bawai wani
uzurinne ya kawoshi ba, wannan abu yana
mutukar daure mata kai amma koda ta tuna
yaudara irinta maza sai take ganin ai wannan ba
komai bane domin zasu iya yin fiyeda haka ma,
Ganin abin nashi bamai karewa bane yasata
shirya yanda zatayi masa wanda tasan cikin
ruwan sanyi zai rabu da ita, dakansa ma zai ce
mata ya hakura,
Ranar da zai zo yayi musu lecture ya kirata da
safe,
"Yawwa dama Ina son zamuyi magana dakai.."
"Inajinki, ai gani"
"Dan Allah dan annabi ka rabu dani.."
"Saboda me?" Ya tambayeta,
"Saboda ni ba sa'ar aurenka bace"
"Kamar ya kenan?" Ya bukata,
"Ni bazawara ce harda yara biyu, yarana har
sun fara zuwa school, kai kuma kaga saurayine
dan haka aurenmu bazai yiyu ba.."
Shiru taji yayi dan haka tafara tunanin daga yau
zasuyi bankwana dashi, bankwana na har abada,
"To kibari idan Nazo makaranta bayan mun
gama lecture sai inganki ko 10 minutes ne"
"Ok" shine kawai abinda ta fada ta kashe wayar,
Kamar yadda yafada bayan yagama yimusu
lecture tabishi zuwa office dinshi, kallonta ya
jima yanayi sama da kasa yana son yagano
banbancinta da budurwa amma yakasa, shi har
yanzu kallon budurwa yake yimata,
"Kikace kin taba aure?"
"Ehh har inada yara ma guda biyu.."
Murmushi taga yayi ya kalleta,
"To ina babansu? Rasuwa yayi?"
"A'a rabuwa muka yi"
"May be saboda in sameki ne shiyasa Allah ya
rabaku,rabona ne ya danne nashi..."
Mamaki maganarshi tabata nan takasa koda
kwakkwaran motsi tayi shiru tarasa abinda
zatace.
Zuba mata ido yayi yana kallonta shidai yasan
bawai son nashine bata yiba akwai dai dalili mai
karfi wanda bazai barta ta amshi soyayyarshi ba
bawai dan baiyi mata ba, shida mata ke binsa
suna cewa suna sonshi to tayaya ita da yace
yana sonta da bakinsa zata ce bata sonshi,
"Indai akan cewa kin taba aurene sannan kinada
yara yasa bakya sona ko kuma kike son kin
amsar soyayyata to kisa aranki cewar yanzu ne
ma nasake jin ina sonki fiye da yanda nake
sonki ada, zan aure ki ahaka sannan zanci gaba
da sonki ahaka..."
Dafe goshinta tayi tana al'ajabin wannan abu na
amadi sai kace abin asiri, ga yan mata nan a
makarantar kyawawa hadaddu masu aji amma
duk yarasa wacce zai so sai ita?
"Kayi hakuri fa, ni sonka ne kawai banayi.."
Tashi tayi ta dauki jakarta har taje bakin kofa
taji yace,
"Nikuma ina sonki sannan insha Allah sai na
aureki.."
Bude kofar tayi tafita tana jin haushinsa saboda
ita tagama dawowa daga rakiyar maza tasan
mafi yawansu abinda yake bakinsu bashine
acikin zuciyarsu ba, abinda yaya kabeer yayi
mata kadai ya isheta example a rayuwa domin
yasota awaje ya kaunaceta kamar zaiyi hauka
amma daga ranar da aka kaita gidanshi tayi
sallama da farin ciki ta shiga damuwa, rashin
mutuncin da yayi mata ko wacce taje gidan miji
babu budurci sai haka,
Shiyasa shima amadin zuciyarta takasa aminta
dashi, takasa yarda da cewar son gaskiya yake
yimata, dan haka tasaka aranta cewar bazata
taba sonshi ba sai dai yayi yagama inyaso idan
yaga babu riba sai ya hakura.
Shi kuwa amadi koda wasa baiyi fushiba
sannan wai dan tace ta taba aure harda yara bai
sauya komai na daga son da yake yimata acikin
zuciyarshi ba, sai dai kawai yana jin kishin koma
waye wanda ya rigashi auren nadiya sannan
kuma yana yimishi kallon soko wawa marar
tunani da har ya iya rabuwa da mace kamar
nadiya,
Koda yatafi tun yana hanya bai karasa cikin
kano ba yake kiranta yace mata yatafi amma
bata dauka ba, packing yayi agefen titi yatura
mata text,
_Baby natafi, ki dauki wayar kiji abinda zan
fada miki please.._
Bayan yatura mata text din da yan mintuna
yasake kiranta anan ta dauka tayi shiru kamar
yadda ta saba,
"Baby.. Kina jina?"
"Uhm.." Shine amsar data bashi,
"Wai ko sayar min da muryar za ayine? Ko sai
na siya sannan za arinka yimin magana.."
Tana jinsa amma tayi shiru bata yimasa magana
ba,
"Shikenan dama kira nayi nafada miki natafi,
yanzu ma haka ina hanya nakusa shiga cikin
kano..."
Idan wayar da take hannunta tayi magana to
itama tayi,
"Sai kinji ni anjima ko?"
"Uhm" dama amsar kenan koda yaushe uhm
bata yimasa magana wadda tawuce wannan,
"To sai anjima" yafada tareda katse wayar yana
murmushi.
Kamar yadda yafada mata cewar babu abinda
zai sauya soyayyarta acikin zuciyarshi hakance
kuwa ta faru domin kullum cikin yimata waya
yake ko text amma sai ta gadama zata dauki
wayar, idan text ne kuwa iyakaci ta karanta ta
ajiye wayar babu amsa, a ka'ida sau daya zaije
wudil a sati amma saboda ita sai yaje sau biyu
ko sau uku saboda kawai yana son yaganta,
Rashin yimasa magana a waya kuwa idan ya
kirata harma yasaba domin yanzu idan ya kirata
sha'anin gabansa yake yi yana rike da wayar
saboda yasan ba magana zatayi ba haka zasu
bar credit din yayita tafiya a banza har zuwa
lokacin da zai cemata sai anjima, ita kanta tana
mamaki tarasa gane ko amadi wanne irin
mutum ne wanda baya fushi, duk abubuwan nan
da take yimasa rana daya bai taba nuna mata
cewar yayi fushi ba gashi wani lokacin da gayya
zata kashe wayarta ai yana jin wayar akashe
zata ganshi a wudil,
Akwai wata rana da takashe wayar da daddare
saboda tasan yasaba kiranta da daddare dan
haka tun 8 takashe, 9 ya kirata yaji waya
akashe, yasake kira yaji akashe adaren yafito
zai tafi wudil nan hajiya ta hanashi tace koma
menene yabari sai da safe saboda ita bata
sonshi da tafiyar dare haka ya hakura yakasa
bacci,
Ita kuma karfe 2 ta kunna wayar saboda babu
wuta gashi tana son tayi karatu, ai tana
kunnawa sai ga kiranshi,
"Dan naci.." Tafada aranta, daukar wayar tayi
badan tasoba,
"Meyasa nakira wayarki naji akashe..?"
"Na kashe ne saboda ina son yin bacci da
wuri.."
"Kin kashe kinyi bacci nikuma kin hanani bacci
ko?"
"Kamar ya?" Ta tambayeshi cikin rashin fahimta,
"Saboda banji muryarki ba shiyasa nakasa bacci
da tuni ma sai dai ki ganni a wannan daren
hajiyace ta hanani tace dare yayi..."
"Ohhh" shine kawai abinda tace,
"Yanzun me zakiyi?"
"Karatu" tafada atakaice,
"To shikenan nikuma tunda naji muryarki yanzu
bacci zanyi sai da safe"
"Uhm" tafada tareda katse wayar.
Haka amadi keta fama da nadiya akan tasoshi
amma taki, har semester ta kare babu wata
gamsasshiyar magana da tayi masa, ana igobe
zata tafi gida sai da yaje makarantar yayi yayi
da ita tafada masa dalilinta na rashin sonsa da
batayi amma tayi shiru, address din gidansu ya
tambaya nanma taki fada, tamkar kurma haka
take zame masa dama duk lokacin da yazo,
Murmushi yayi ya saka hannunshi a aljihu ya
dauko rafar yan dari bibbiyu ya dauki jakarta ya
bude yasaka mata aciki,
"To ga kudin mota Allah ya kiyaye hanya saboda
nasan idan nace zanzo nakaiki ba yarda zakiyi
ba, amma ki shirya ganina agidanku akoda
wanne lokaci.."
Ko kadan maganarsa bata dauketa da gaske ba
domin tayaya zai san gidan har yaje? Sallama
yayi mata yatafi ita kuma ta koma hostel
takarasa shirya kayanta tafita cikin gari taje ta
siyo kayan tsaraba tayiwa twins dinta siyayya
sosai washe gari tatafi gida inda zatasha dogon
hutu domin hutun nasu da yawa.
Komawarta gida yasa ta mance da wani amadi
saboda hatta wayarta ma sai ta gadama take
kunnawa saboda kar ya takura mata, ita yanzu
bata da wani bazawari ma domin hatta yaya
kamal ma ya hakura saboda yaga ba aurensa
zatayi ba, yanzu iya amadi ne kawai ke yimata
naci,
Satinta uku da dawowa gida tana zaune da
yamma a tsakar gida tana yiwa fadeela kitso ita
kuma ameera tana yimata tsifa mama tana
kitchen tana aiki, fadeel da husna da walida da
amir suna yin ball,
Wayarta ce tafara kukan neman agaji, kamar
bazata dauka ba saboda ganin amadi ne amma
sai ta dauka,
"Ki fito gani a kofar gidanku.."
Jin abinda yafada yayi mutukar sata mamaki,
"Wanne kofar gidan namu?"
"Kunada wani kofar gidanne bayan wanda kuke
ciki? Ke da wai kin dauka bazan biyoki ba?"
"Ni bana gida"
Murmushi yayi,
"Hmm nidai nace miki ina kofar gida ina jiranki".
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert &
perfect writers_
_Fatan Alkhairi ga yan k'ungiyar haske writers,
this page is for you...!_
*41*
aishaummi.blogspot.com
*A*jiyar zuciya ta ajiye sannan ta sake hade
rai kamar yana ganinta,
"Nace maka bana gida naje unguwa.."
"To ina nan ina jiranki, sai kin dawo.."
Kasancewar duk abinda take fada mama tana
jinta yasa mama fitowa daga cikin kitchen,
"Nadiya keda waye ne?"
"Mama wallahi wani nacaccen mutum ne.."
"Haba nadiya, kefa yanzu ba karamar yarinya
bace akan me zaki rinka yin abu irin na kananan
yara, ko Amira ce tayi haka ai zakiyi mata fada
bare ke da kanki, ina ga mai sonka wanda
yatako yazo har inda kake? Ki tashi maza ki
shirya kije"
Jin abinda mama tafada yasata sakin kitson da
take yiwa fadeela ta tashi tawuce daki,
Kallon amir mama tayi tace masa,
"Amir maza fita kofar gida kacewa bakon nadiya
yayi hakuri tana zuwa, kabashi hakuri kaji, ai ba
ayin haka.."
Fita Amir yayi yana fita yaga wani handsome
jingine jikin motarsa baka sai sheki take, gayen
yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda kalar
ruwan toka, da hula akansa itama ash colour
amma ya zameta ya turata baya can keyarsa,
hannunshi daure da agogon azurfa fari,
Gaba daya kamshin turarensa na one man
yagama cika ilahirin wurin, amir ji yayi gayen ya
shiga ransa lokaci guda sannan gashi dan gayu
dashi,
Sallama amir yayi masa, dagowa amadi yayi ya
amsa tareda mikawa amir hannu sukayi
musabaha,
"Mama ce ta aikoni tace kayi hakuri anty
nadiyan zata fito yanzu"
Murmushi amadi yayi har lokacin yana rikeda
hannun amir,
"Karka damu abokina, ai babu wani abu sai dai
kawai yayarka bata sona ta tsaneni babu
namijin da take jin haushi ahalin yanzu kamar
ni"
"Ba tsanarka tayiba, kawai dai halin rayuwa ne
ya mayar da ita haka" amir yabashi amsa,
"Amma dagaske wai ta taba aure?"
"Ehh tayi aure harda yaranta twins, sun rabu da
mijinne"
Jijjiga kai amadi yayi, "nasan dai ba laifinta
bane sai dai laifin mijin saboda nadiya tanada
kalar mata nagari"
"Hakane, gaskiya kam laifin ba a ita bane a
mijinta ne kuma cousin dinmu ne ma amma
yanzu babu aure a tsakaninsu saboda saki uku
yayi mata, kaga kuwa duk macen da irin wannan
kaddarar ta hau kanta dole ta nisanta kanta da
maza musamman ma anty nadiya wacce ko
kadan bata tsinci wani dadiba acikin rayuwar
aure.."
Amadi ya dago kenan da niyyar sake yin
magana sai gata ta fito fuskarta adaure tasha
kunu sai faman cika take yi tana batsewa
saboda tilastata din da mama tayi ta fito ba
ason ranta ba,
Hannun amir amadi ya saki yana murmushi,
"abokina sai mun sake haduwa, meye ma
sunanka?"
"Sunana amir"
"To amir sai mun hadu next time, nagode"
Wucewa cikin gida amir yayi ita kuma ta karasa
fuskarta babu fara'a,juyawa yayi ya dora
hannunshi asaman mota ya jingina yana
kallonta fuskarshi dauke da murmushi,
Ba karamin kyau yaga ta kara yiba domin tayi
kumatu ta yi haske, tana sanye da atamfa kalar
ruwan toka da hoton dutsin guga ajiki, ta yafa
mayafi ash colour tasaka flat din takalmi baki,
Haushi taji saboda ganin sunyi anko da amadi, ji
takeyi kamar ta koma gida ta sake wasu kayan,
"Meye kuma harda sako kaya kalar nawa?"
Yafada cikeda tsokana yana kallonta, sake daure
fuska tayi,
"Ni ban ma san kalar kayan da kasako kenan
ba.."
"Bawani nan kin sani kawai dai kidai nagane so
kikeyi muyi anko"
Sake k'uluwa tayi nan ta juya tana harare
harare shikuma abin dariya yake bashi, sake
niyyar tsokanarta yayi ya kalleta,
"Har kin dawo daga unguwar? Ai da kin yi
addressing dina naje na dauko ki"
"Nagode.." Tafada batare data kalleshi ba
saboda ta gane tambayar rainin hankali yayi
mata tunda ai yana gani ta fito daga cikin gida,
"Ina twins dina?" Ya tambayeta,
"Dama kanada twins ne?"
"Au da ke baki saniba?"
Shiru tayi masa, dan haka ya kalleta yayi dan
murmushi,
"Kizo mu shiga mota karki gaji da tsaiwa ni
kinga nasaba tsayawa a aji"
"Basai na shiga ba, nifa aiki nakeyi ka fito
dani.."
"Daga dawowar taki daga unguwa kika hau
aiki?"
Sake yin shiru tayi dan haka ya kalleta yana
duba agogon dake daure a hannunshi,
"Nima ba zama nazo yiba dama ganinki kawai
nazo nayi sannan naga gidanku, tunda nagani
shikenan zanje natafi amma karki dauka natafi
kenan, no i will be back soon, ko yanzu dai
nasan kinyi believing cewar bazan taba barinki
ba har sai kin zama mallakina koda kuwa bakya
sona tunda ni ina sonki shikenan.."
Juyawa tayi ta kalleshi fuskarta a tamke,
"Nagode da sona da kakeyi amma kasani auren
matar da bata sonka babban kuskure ne,
sannan budurwa itace tafi dacewa dakai ba
bazawara mai yara har biyu ba, Allah ya kiyaye
hanya.."
"A'a ni bazawara ce tafi dacewa dani ba
budurwa ba saboda manzon Allah ma da
bazawara yafara kinga kenan idan nayi haka na
dabbaka sunna babba.."
"Allah ya kiyaye hanya.."
Tun kafin ya amsa tayi gaba abinta, binta da
kallo yayi yana jujjuyawa kalmominta acikin
ma'auni,
Duk maganganun da take fada masa yana ji
acikin ransa cewar akwai wani abune da yake
damunta acikin zuciyarta wanda yakeda alaka
da wannan sannan kuma ga maganar da amir
ya fada masa dangane da ita cewar bataji dadin
rayuwar aurenta nafarko ba, to indai hakane
bawai sonshi dinne batayi ba kawai dai akwai
wani abune wanda ta ajiyewa ranta,
Waya yayi mata ta dauka dakyar murya a dakile,
"Please turo min amir zamuyi sallama"
Katse wayar tayi ta kalli amir, "kaje yana
kiranka"
"Wai waye wanda yazone?" Mama ta bukata,
"Wallahi mama wani classic guy ne anty
tasamu.."
Daukar takalmi tayi ta jefeshi yayi saurin fita
yana dariya,
A tsaye jingine da mota yasamu amadi,
"Abokina yi hakuri nasake fitowa dakai ko"
"A'a wallahi babu komai"
Kallonsa amadi yayi, "amir ni dagaske nake son
yayarka amma kuma taki kwata kwata bani
hadin kai mu fuskanci juna ban san dalili ba,
shin mijinta nafarko ya cutar da itane?"
"Gaskiya bakai kadai yaya nadiya ke yiwa
hakaba, kaga bayan mutuwar aurenta manema
da yawa sun fito suna sonta amma taki tace ita
karatu zatayi saboda kamar yadda nafada maka
abaya ko kadan bataji dadin aureba,
Wannan dalilinne yasa yanzu bata sha'awar
sake yi kwana kusa saboda kasan bahushe yace
naji dadi shine gari ba na saba ba, abubuwan da
anty nadiya tagani agidan aure suna da yawa,
taga rayuwa kala kala daga karshe suka rabu da
mijin babu arziki, to kaga wanda yaga haka ai
fiyeda irin wannan ma zai iyayi"
Jijjiga kai amadi yayi, "na fuskanceka amir,
nagane dalilin nadiya na tsanata da kin amsar
soyayyata, nikuma nayi maka alkawarin mutukar
na auri yayarka bazata yi kuka daniba sai ko na
farin ciki, bazan wulakantata ba, zan kula da ita
sannan zan bata gatan da bata samu a aurenta
na farko ba.."
"Allah yasa, Allah ya tabbatar da alkhairi"
"Amin"
Hannu yasa a aljihu ya dauko kudi sabbi fil yan
500 na dubu biyar yabawa amir yace ya siyawa
twins sweet daga nan ya shiga motarshi yatafi
yana mai jin son nadiya yana sake ratsa duk
kofofin jinin jikinsa,sannan yanajin wani
tausayinta yana shigarshi,
Tunda amir ya kawo sakon mama ke kallon
nadiya tana son jin yanda zata karbi zancen
amma ko uffan batace ba shikuwa amir sai
yabon amadi yake tayi yana cewa mama wallahi
guy din ya hadu sannan ga hankali ga class
gashi dan gayu.
Tunda yatafi nadiya bata kirashi ba ganin haka
yasa shi ya kirata, kamar koda yaushe shiru tayi
masa har fadeela ta shigo ta haye jikinta tafara
yimata surutu jiyo surutun fadeela da yayi yace
tabashi ita, mikawa fadeela wayar tayi ta kara
mata ajikin kunnenta,
"Momy waye?"
"Dady ne" yabawa fadeela amsa ai kuwa nan ta
hau tsalle saboda tazata dadyn tane duk da
tafara mantawa dashi....
*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of perfect &
expert writers_
_Jinjina ga babbar yaya anty maijidda musa,
nagode da kokarinki agareni, Allah yabarmu
tare.._
*42*
aishaummi.blogspot.com
*T*salle fadeela tahau yi tana yiwa amadi
surutu, nan yasamu abokiyar hira tanata yimasa
labarin school dinsu harda su abcd da sauran
karatun da ake koya musu a makaranta,
Ita kanta nadiya sai da abin ya bata mamaki irin
yanda amadi ya biye fadeela taketa yi masa
surutu, shima fadeel ya shigo nan fadeela
tabashi wayar tana cewa,
"Ga daddy"
Karba shima yayi nan hirar takoma amadi da
fadeel, daga karshe ita nadiya ma baccine ya
dauketa tabarsu sunata faman surutu bata san
lokacin da suka gama ba,
"Ina momyn take?" Amadi ya tambayi fadeel,
"Gata nan tana bacci"
"To kyaleta karka tasheta",nan yayi sallama da
yaran ya kashe wayarsa.
Tun daga nan kullum idan ya kira wayar dasu
fadeel suke shan hirarsu suyi tayi masa surutu
suna sashi dariya,
Satinshi biyu da zuwa yasake shiryawa ya dawo
acikin weekend ranar asabar, sai kawai waya
yayi mata yace yana waje, amir ta kira tace yaje
da bako awaje saboda ita tana kwance cikin
bargo tana baccinta,
Amir na ganin amadi ne yamaza ya koma cikin
gida yafadawa mama, nan mama tace ashigo
dashi falon baki,
Amira mama tasa tayi masa girki nan Amira ta
shiga cikin kitchen ta dora,
Dakyar nadiya ta tashi tayi wanka ta shirya
bayan mama ta leko tayi mata kaca kaca,
shiryawa tayi cikin leshi dark brown da
mayafinsa ta fita,
Lokacin da zata shiga sai ga Amira itama rikeda
faranti zata shiga, bata hanya tayi ta fara shiga
sannan tabi bayan amiran,
Sai da Amira ta gaisheshi sannan ta tashi ta fita
kallon nadiya yayi yau dinma fuskarta adaure,
"Wannan kanwar taki tanada hankali kamar
amir.."
Shiru tayi masa bata tanka ba,
"Ina twins dina.."
"Basa nan sunje islamiyya"
Murmushi yayi bai kara cewa komai ba illah
kawai kallonta da yake yi,
Babu wanda ya kara magana haka suka cigaba
da zaman kurame sai da suka dade ahaka
sannan amadi yayi magana saboda yasan ita
dai ba magana zatayi ba,
"Nadiya....,ina so kiyi hakuri ki bani dama
saboda komai arayuwa da kika ganshi kaddara
ne sannan kuma bawai yana nufin cewa saboda
mutum daya yayi maka butulci kowama butulu
bane, a'a ita rayuwa ahaka take tafiya, yayinda
wani ya bata maka sai wani ya dad'ad'a maka,
nidai indai nine nayi miki alkawarin bazan taba
cin amanarki ba.."
Duk wannan maganganun da yayi bawai sunyi
tasiri agareta bane kawai dai ta daukesu a
matsayin zallar karya irinta yaya kabeer,
"Dan Allah nadiya kibani dama domin na nuna
miki irin son da nake yimiki"
Har lokacin dai bata ce dashi ko ci kanka
ba,shiru yayi yazuba mata ido kawai yana
kallonta,
"Bakaga an kawo maka abinci bane.." Tafada
batare data kalli gefen da yakeba,
"Kin damu da naci ne? Ai baki damu da koshina
ko yunwata ba.."
Bata sake tanka masa ba dan haka yajawo
farantin abincin nan yabude yaga potatoes mix
da wata hadaddiyar sos wadda tasha curry da
hanta sai kamshi take,
Kwallo biyu kacal ya dauka ya debi sos din
yafara ci,
"Kanwarki ta iya girki, ko kece kika yi?"
"Bani bace.." Tafada tana sake hade rai,
Shiru yayi yaci gaba da cin abincin yana binta
da ido,
Ihun sallamar su fadeel ce ta cika musu kunne
sai gasu sun shigo cikin falon aguje suna ihu wai
dadynsu yazo,
Zuwa sukayi suka rungume amadi suna ihun
murna, amir dake biye dasu yana cewa "karku
bata masa kaya ku cire takalmin"
Kasancewar milki colour din yadi ne ajikin
amadi,
Tunda su fadeel suka dawo amadi yasamu
abokan hira bai sake bi ta kan nadiya ba, mama
ma tashigo sun gaisa daga nan kuma amir ya
rakashi wurin abba suka gaisa ai nadiya ji tayi
kamar zatayi kuka da bakin ciki saboda ita bata
da burin sake yin aure kwana kusa,
Fita yayi zai tafi yana rikeda su fadeel amir yana
binsu abaya, boot din motarshi ya bude yace
amir ya kwashe kayan ciki yakai gida na twins
ne yakawo musu, ita kam nadiya tana tsaye
tana kallonsu kayane sosai yasiyo irinsu bobo,
biscuit, chocolate, indomie da sauran kayan
makulashe na yara,
Bin amir sukayi zuwa cikin gida dan haka amadi
ya matsa kusa da ita,
"Baby zan tafi.." Wani haushi taji ya rufeta
saboda ta tsani baby dinnan da yake kiranta
dashi,
"Allah ya kiyaye hanya"
"Amin nagode da addu'a, sai yaushe?"
Jin tayi masa shiru yasashi yimata sai anjima
yatafi,
Haka sukaita fama koda yaushe yana kiranta
awaya sannan yana tura mata da kati,
Har yanzu ita bata ji alamun zata soshi ba
saboda zuciyarta ta dade da cire soyayya daga
cikinta,
Tana kwance taji yana kiranta awaya, dauka tayi
bayan tayi tsaki,
"Baby kina lafiya?"
"Lafiya"
"Dama fada miki zanyi zanzo ranar Thursday ko
Friday"
"Bana nan"
"Ina kika tafi?"
"Basai kajiba, sai anjima yanzu aiki nake"
Kitt takashe wayar bata san mama na tsaye
tana jinta ba,
"Ke nadiya wai meyake damunki ne? Ashe dama
bakida wayo? Allah ya dubi zuciyarki da irin
halin da kika shiga yakawo miki wanda yake
sonki tsakani da Allah shine kuma zaki butulce
masa?
To wallahi ki zauna kiyi karatun tanutsu saboda
wannan yaron da gaske yake sonki idan har kika
wulakantashi kika koreshi to bazaki samu wanda
yakaishi ba agaba,
Kuma wallahi idan har ke bazaki aureshi ba to ni
ashirye nake da in bashi Amira ya aura, wallahi
indai bazaki aureshi ba ki fada min sai ince
masa yazo ya auri Amira, haba yaro mai
mutunci mai son yayanki, ya dauki yaranki
kamar nasa amma kekuma babu wanda kike
ciwa mutunci sai shi, to yakamata ki yiwa kanki
fada.."
Juyawa mama tayi tafita tabar nadiya tana
kuka, ita kwata kwata yanzu auren ne bata
so,sannan maganar mama ta tsaya mata arai
wai zata bawa amadi Amira idan ita bata
sonshi,
Koda yasake kiranta yace zai zo cewa tayi to,
ranar kuwa na zuwa sai gashi yazo da misalin
karfe 12 narana,shiryawa tayi cikin wani material
ja mai kyau ta fita,
Acikin mota ta sameshi dan haka ta tsaya daga
waje tana faman ciccin magani, ta cikin mirror
ya hangota yayi murmushi ya bude ya fito, tana
ganinsa tajuya tafara tafiya batare da tayi
magana ba, binta yayi abaya tiryan tiryan har
zuwa cikin gidan falon baki,
Zama tayi anesa dashi ranta ahade, suna zaune
haka shiru husna tashigo dauke da faranti kato
wanda aka doro kayan abinci aciki,
Fried rice da hadadden salad wanda yaji kwai da
sauran kayan hadi sai juice,
"Zo muci abincin" yafada cikin tsokana,
"Na koshi" tabashi amsa, murmushi yayi yafara
cin abincin yana kallonta tareda nazarinta sam
shi abinda take yimasa baya bata masa rai bare
ya daga masa hankali asalima hakan sake
burgeshi yake yana kara rura wutar sonta acikin
ranshi,
Suna nan zaune zaman kurame har yagama cin
abincin ya kalleta,
"Baby ko babu komai ai yakamata ace mun
gaisa ko?"
"Mantawa nayi" tafada tana dauke kanta,
murmushin da yasaba yi kowanne lokaci yanzun
ma shi yayi,
"Na sameku lafiya?"
"Lafiya"
Shiru suka yi na dan wani lokaci,
"Ina budurwata Amira yau ban ganta ba?"
"Tana ciki" ta amsa masa fuskarta adaure,
"Wannan ciccin maganin da kikeyi yakamata ki
daina shi saboda nima yau ba wurinki nazo ba
wurin Amira nazo domin na sauya shek'a....".
*_Ummi Shatu_*🏻
🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*BY*_
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
perfect writers)_
_Special gaisuwa ga aminan kwarai abin
alfaharina, Pherty Xarah, Fido sodangi, Kausar m
Hassan, Khaleesat Haidar, Mom Shakur, Sadiya I
Bala,Khadija Sidi, Teemah Cool, Hafsat Bunxa,
Aisha Dansabo,Zee Ruma,da duk wadanda ban
ambata ba, ina alfahari daku kawayena..._
*43*
aishaummi.blogspot.com
*J*i tayi gabanta yafadi bata san daliliba,
saurin kallonsa tayi nan taga shi ba ita yake
kallo ba ma sam, wayarshi yake kallo yana
daddannawa,
Maimaita maganar take yi acikin zuciyarta nan
take kuma maganar da mama tafada ta sake
dawo mata inda mama take cewa idan har bata
sonshi bazata aureshi ba to zata bashi Amira,
Faduwar gabanta ce ta tsananta nan tasake
kallonsa still dai wayarshi yake kallo ba itaba,
"Dama Amira ai itace tafi dacewa dakai baniba,
Allah yabada sa'a.." Tafada cikin k'uluwa tareda
tashi zata fita,
"Amin, dan Allah ki turo min ita idan kin shiga
ciki.." Ya fada da niyyar sake tunzurata, bata ko
waiwayo ba tayi gaba abinta amma kuma haka
kawai sai take jin wani irin haushi yana
bakuntar zuciyarta,
Cikin dakinta ta shiga nan taga Amira tana
zaune tana gyara kayan sakawar su fadeel tana
shirya musu shi acikin wardrobe, kamar bazata
yi magana ba sai kuma tace da Amira,
"Amira kije Ahmad yana kiranki.."
"To anty.." Amira tafada gamida mikewa da
sauri,
"To Kodai dama yarinyar nan tasan da zuwanshi
ne?"
Ta tambayi zuciyarta, zama tayi taci gaba da
aikin da amiran tatafi tabari.
Amira nashiga falon baki ta iske amadi azaune,
"Yaya Ahmad ina wuni?" Tafada cikin ladabi,
"Lafiya Amira, yasu mama?"
"Suna nan lafiya"
"Yawwa dan Allah so nake ki shirya min su
fadeela zamuje unguwa dasu.."
"To yaya Ahmad"
"Yawwa nagode"
Fita tayi zuwa dakin mama inda Maman ke
shiryasu bayan tayi musu wanka nan Amira
tafadawa mama sakon amadi na ashiryasu zai
kaisu unguwa,
Kayansu Amira tasa musu tayiwa fadeela
kwalliya sosai takama mata gashinta da ribom
kalar kayanta pink din riga da bakin jeans skirt,
shikuma fadeel pink din t shirt da bakin jeans ta
fesa musu turare,
Kama hannunsu tayi takaisu wurin amadi tace
gasu nan sun fito,
Kallon yaran kawai ya tsaya yana yi domin ba
karamin burgeshi suka yiba ji yake aransa
inama yaranshi ne,inama shine ya haifesu shida
nadiya amma kowaye ya auri nadiya dafarko
yayi masa overtaken ne kawai da tuni yanzu
yaran nan nashine,
Kama hannunsu yayi suka fita yayinda Amira ita
kuma tafara tattare kwanukan abincin da yaci.
Nadiya kam tana daki bata san abinda yake
gudana ba amma jitake aranta amadi yama yi
mugun raina mata hankali, daga ganin kanwarta
sai yace ita yake so yanzu?
Tsaki taja tayi juyi, "koma menene shi yajiyo dai
dama ni ba sonshi nake yiba.."
Shigowar Amira ne ya katse mata tunani, "su
fadeel sunbi yaya Ahmad unguwa"
"Kuma meye nawa ni aciki?" Nadiya ta bata
amsa cikin fada, fita Amira tayi daga cikin dakin,
jin karar shigowar massage awayarta yasata
dubawa,
_Wasafa nake yimiki babu wata shek'a da na
sauya, so karki fara kishi da kanwarki dan naga
har kishi ya bayyana acikin idonki karara,munje
unguwa da twins dina nasan ke ko nace kizo ki
rakamu ba zuwa zakiyi ba shiyasa banyi inviting
dinki ba, sai mun dawo,1,4,3.._
Gyara kwanciyarta tayi tana hararar wayar
kamar yana wurin, "ruwanka kuma"
Amadi wurin wasan yara ya nufa dasu fadeel,
kowa yagansu zaiyi tsammanin cewar yaranshi
ne gashi suma sun fara shakuwa dashi sosai,
Wasa suka rinka yi cikin farin ciki shikuma yana
yimusu pics wani lokacin kuma ya shiga yayi
musu tare, shi kansa bai san adadin yawan
hotunan da yayi musu ba,
Sai da sukayi wasa mai isarsu suka gaji tikis
suka fara kiran yunwa sannan ya daukesu zuwa
wani restaurant dake gaba kadan da wajen
wasan yaran,
Fito dasu yayi suka shiga ciki yayi musu order
din abinci, amala da miyar ganye da kaza, shi
yarinka basu abincin har suka koshi sannan yaci
yabiya kudin abincin suka fito,
Maimakon yakaisu gida sai ya nufi supermarket
dasu nan suka shiga ya lodo musu kayan dadi
kala kala yafito yana rikeda fadeela daya hannun
kuma ledar da ya iyo shopping ce fadeel kuma
yana biye dasu,
Kamar a mafarki kabeer ya hango yaranshi wani
rike dasu lokacin da yake packing acikin harabar
supermarket din, duk da yadade rabonshi da
yaran domin ba zuwa ganinsu yakeba amma ai
bazai iya mantasu ba, cikin gaggawa ya fito
daga cikin motarshi ya nufi wurinsu amadi,
Amadi yana kokarin bude motarshi kabeer ya isa
wurin,
"Fadeel,fadeela...."
Kabeer ya kira sunan yaranshi yana karewa
amadi kallo,
"Bawan Allah kai kuma waye da zaka dauko min
yara ka kawosu nan wurin batare da izinina ba?"
Kabeer yafada cikin gadara,
Kallonsa amadi yayi "banfa ganeka ba, waye kai
please"
"Ohhh tambayata ma kake ko waye ni? Ok to
nine mahaifin wadannan yaran kai kuma waye"
"Allah sarki, ni nine wanda yake shirin zama
babansu ta hanyar auren mahaifiyarsu"
Ai take zuciyar kabeer ta tsananta bugu kishi ya
bayyana a fuskarsa karara, haushin amadi ya
kamashi musamman ma da yaganshi handsome
babu alamun kauyanci ko shirme atare dashi,
"To bani yaya na inyaso kaje ka auri uwar tasu
ita kadai amma yaya tunda nawane babu wanda
zaiyi min gadara dasu"
Murmushi amadi yayi wanda ya bayyanar da
beautiful point dinshi,
"Amma dai kasan ai ba kai kadai ka haifi yaran
ba ko? Dan haka tunda bakai kadai ka haifesu
ba to baka da iko dasu kai kadai, idan yaranka
kakeso ka karba kaje gidansu nadiya ka karbesu
acan, amma nidai yanzu bazan baka yaraba
yanda nafito dasu sai na mayar dasu wurinda na
daukosu.."
Kabeer najin haka yatada fada yana daga murya
kamar wani zautacce,
"Wallahi sai kabani yarana saboda bakai ka
haifa min suba, kai fadeel kuzo mu tafi nine
ubanku ba wannan ba"
Zuwa yayi zai kama hannun yaran anan suka
fashe da kuka suka kankame amadi suna makale
kafada alamun bazasuje wurinsa ba abinda yayi
mutukar sake daga hankalin kabeer,
Nan mutane suka fara taruwa kabeer sai fada
yake yana zagin amadi kamar wani marar
hankali, ko takansa amadi baibi yasaka su
fadeel a mota yashiga yatashi motarsa yabar
kabeer yana cewa,
"Wallahi yarana zan karbo, sai anbani yayana.."
Wannan shine mafarin nadamar kabeer saboda
yahadu da yayanshi na cikinsa amma sunki
zuwa wurinsa daga yakai hannu zai tabasu sai
su saka kuka.
Nadiya na daki azaune bayan tayi wanka ta
shirya tana kwalliya su fadeel suka shigo
dagudu, fadeel ne mai kokarin dauko ledar
siyayyar da amadi yayi musu,
"Momy kinga uncle ya siya mana, kuma mun
hadu da wani a supermarket sunyi fada da uncle
yace wai shine babanmu.."
Fadeela tafada tana zama akan cinyarta, sake
tambayar fadeel tayi nan yafada mata kamar
yadda fadeela ta fada,
Tashi tayi tafita waje wurin amadi, yana saman
motarshi azaune,
Tsayawa tayi ajikin motar tana son ta
tambayeshi abinda su fadeela suka fada mata
amma takasa saboda basa doguwar magana
dashi.
Zuwa can tadaure ta kalleshi tace,
"Naji su fadeel suna fada min wani zance"
"Name?" Ya tambayeta,
"Wai kun hadu da abbansu a supermarket"
Shiru yayi mata baiyi magana ba,
"Ya kayi shiru?"
"Ehhh"
Yace da ita yana kokarin dirowa daga saman
motarsa,
"Dagaske ne mun hadu dashi may be ma
kiganshi yazo anjima.."
Sai da taji kanta ya sara saboda ita yanzu bata
son duk wani abu wanda zai hadata da yaya
kabeer,
"Zanje in tafi amma wannan shine tafiyata ta
karshe bazan sake dawowa gidanku ba har sai
naji matsayina awurinki, dan haka nabaki dama
ki zauna kiyi shawara da zuciyarki sannan ki
yanke hukunci akan maganarmu, idan har zaki
aure ni kifada min idan bazaki aure niba karki
boye min ki sanar dani gaskiya, nabarki lafiya"
Bai jira amsar da zata bashi ba ya wuceta yaje
ya bude motarsa ya zabureta yabar wurin.....
*Fatan Alkhairi ga k'awar kirki maryama
qaumi...*
_Gaisuwa mai yawa ga masoyan littafin mijina
sirrina, khairat dan dawaki,heedah, hajjaju
chuchu, Nasma, kadija mai kano, Billy reality,
mom amir,ummy aysha, meenah 4eva da duk
wata masoyiyar MS..__*
MIJINA SIRRINA.. 44-56
[8/13, 3:00 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
perfect writers)_
Your birth day is the perfect day to say I
care, because you will remeber me when u
certainly make it a big affair, and when you do
hold a party... I bet you will be the one who
would care
to make ur special day a costly affair!!!!HBD
MARYAM QAUMI.
_Fatan alkhairi ga masoyan Anty amadi, Hawwa
mudi, baddo alka, salma luv and others.._
*44*
aishaummi.blogspot.com
*K*asa motsi nadiya tayi illah kawai kallo data
rinka bin motar amadi dashi har ta daina
hangoshi, gabanta ne taji ya tsinke yafara
faduwa wanda bata san dalili ba,
Dakyar tayi ta maza taja kafarta tabar wurin ta
nufi cikin gida, da amira tafara cin karo tana
kokarin hada kayan wanke wanke, daf da zata
wuce ta shiga daki taji maganar mama daga
kofar kitchen tana yimata magana,
"Bakon naki yatafi?"
"Ehh mama yatafi.." Tafada jikinta asanyaye,
Kallonta mama tayi dakyau anan tagane cewar
akwai abinda yake damunta dan haka tasake
yimata magana,
"Nadiya ya kamata dai ki zauna kiyiwa kanki
karatun ta nutsu domin wallahi ina jiye miki yin
nadama aduk ranar da kika bari wannan yaron
ya subuce miki, kiduba kiga irin dawainiyar da
yake yi da yaranki, ko haka ai yasa ki
saurareshi.."
Shiru tayi tana sauraren mama,itafa kowa
yakasa gane matsalarta ne, ita gaba daya
mazanne yanzu sun gama fita aranta, gani
takeyi tunda yaya kabeer yayi mata wannan cin
mutuncin to kowanne namiji ma hakan zaiyi
mata,
"Kinji abinda nafada miki ko..?"
Muryar mama tadawo da ita cikin hayyacinta,
"Ehhh naji mama.." Tabawa mama amsa,
juyawa Maman tayi ta nufi cikin kitchen tana
cewa,
"Yawwa yadai fi miki"
Daki ta shiga nan tasamu su fadeel duk sun
wargaza kayan siyayyar da amadi ya iyo musu
suda su waleeda da husna,
Ko takansu bata biba ta nemi wuri ta zauna
tana tunanin abinda zaije yazo nan gaba acikin
rayuwarta, da ace su mama zasu barta to da ita
da sake yin aure sai a lahira amma aduniya dai
kam tagama,
Tadade tana tunani acikin ranta har na tsawon
wani lokaci,shigowar Amira ce ta katse mata
tunanin da takeyi,
"Anty nadiya wai ana sallama dake awaje.."
"Amira dan Allah ku kyaleni kaina ciwo yakeyi.."
Juyawa Amira tayi tafita,Amira bata jima da
fitaba mama tashigo dakin,
"Haba nadiya ki leka mana kiga ko wanene
inyaso sai kibashi hakuri tunda bakya jin dadi.."
Mikewa tayi ta fita batare da tayi magana ba,
Kamar acikin mafarki ta hangoshi tsaye yasha
wani black space (no respect) kamar kada ta
karasa wurin sai kuma taga cewar gara taje
inyaso sai ayi wacce za ayi,
Yanda yasha kunu ya hade girar sama da kasa
haka itama tasha kunun ta daure fuskarta
tamau fiyeda yadda ya daure tasa,
"Lallai yaya kabeer dinnanma dan rainin
wayone.." Tafada acikin zuciyarta gamida
karasawa wurinda yake zuciyarta cikeda
tsanarsa tareda jin haushinsa, ita sai yanzuma
take nadamar kasancewarta matarsa ada,
Ko sallama bata yimasa ba ta tsaya tareda rike
kugu,
"Naji ance ana sallama dani dama kaine? Idan
Kaine to gani kayi kafadi abinda ya kawoka
domin sauri nake.."
Mamakine ya kama kabeer ganin yanda nadiya
ke faman kallonshi shekeke tana yimasa kallon
hadirin kaji,
"Waye wanda naga yakai su fadeela
supermarket...?" Yafada cikin kunar rai tareda
gadarar cewar yaranshi ne,
Saida ta dan yimasa wani kallo mai taken ka
rainawa kanka wayo sannan tace,
"Saurayina ne wanda zan aura, da magana ne?"
Wani takaici da haushine suka ziyarci kabeer
lokaci guda,kallonta yayi ta cikin bakin glass
dinshi,
"Saurayinki?"
"Kwarai kuwa domin ba bazawari bane
saurayine sabo fil..."
Saurin dakatar da ita yayi, "ya isa haka, kina
jina, kibude kunnenki dakyau kiji daga yau sai
yau, kar wani wanda ya sake gigin daukar min
yarana domin ba wani dan iska bane ya haifar
minsu, nine na haifi abina.."
"Dakata yaya kabeer, kai har kana da bakin da
zaka kira su fadeel da sunan yaranka? Yaran da
kayi watsi da rayuwarsu ka banzantar dasu,
yaran da harma sun manta da cewar kaine
ubansu, tunda muka rabu dakai daidai da rana
daya baka taba zuwa ka gansu ba bare ka dauki
dawainiyarsu, kaga kuwa indai hakane to baka
da bakin da zaka kirasu da 'yayanka..." Ta
karashe maganar tana yin hucin bacin rai,
"Haka kikace? Nadiya ni kike fadawa haka? To
tunda abin babu mutunci aciki wallahi sai kin
bani yarana, zanzo zan tafi da yayana inyaso
kije ki auri duk uban wanda zaki aura.."
"Wannan ne kuma baka isaba, sannan ni ba
uban wani zan aura ba saurayi zan aura mai
sona wanda babu abinda yasani na yaudara
baima taba auren ba bare har ya zama uban
wani.."
Tana gama fadin haka ta juya tafara tafiya
batare data sake sauraron kabeer ba, in banda
daci babu abinda makogaron kabeer yakeyi
saboda yasan nadiya magana ta fada
masa,sannan gashi zatayi aure zata auri wani
wanda bashiba,
"To tunda kin zabi ayi rashin mutunci kisani
wallahi sai na karbi yayana ko da karfin hukuma
ne.."
Tana jinsa amma bata waiwayo ba saboda ita
yanzu bata kaunar koda ganin fuskarsa ne,
kanta kuwa in banda ciwo babu abinda yakeyi
saboda tashin hankalin yaya kabeer,
"Ohh ni nadiya ko sai yaushe zan samu
kwanciyar hankali?" Ta tambayi zuciyarta, ko
mama bata fadawa cewar kabeer bane bare
tafada mata yanda sukayi dashi ta shige daki ta
kwanta.
Tana kwance adaki har lokacin sallar isha
yayi, tana jin dawowar Abba amma bata iya fita
taje tayi masa sannu da zuwa ba saboda ciwon
da kanta keyi mata.
Abangaren amadi kuwa abinda yafadawa nadiya
kawai yafada ne saboda yana son ta amince ta
aureshi amma yasan bazai iya rabuwa da itaba
koda kuwa zata cigaba da fada masa bata
sonshi kamar yadda ta saba,
Karfe 5 da yan mintuna ya isa gida, lokacin da
yayi packing din motarshi yana kokarin fitowa
yaji ihun murnar su inteesar da hamid yaran
anty siyama,
Fitowa yayi ya rike da hannunsu,
"Uncle amadi tun dazu munata jiranka kadawo
ka kaimu..."
"Ohhhh hamid rigima kai kullum a zuwa yawo
kake ne..?"
Falo suka shiga inda su hajiya ke zaune itada
anty siyama suna kallon labarai,
Zama yayi acikin kujera sharaff alamun agajiye
yake,
"Anty Amadi daga ina haka?" Anty siyama ta
tambayeshi tana rikeda juice a hannunta,
"Anty daga zance nake.."
Murmushi tayi ta kurbi juice din dake hannunta,
"Kaima wasa kake, yaya zakayi da zee?"
"Nidai anty mubar wannan maganar, yanzu dai
yaushe zanzo nakai su inteesar yawo..?"
"Haka dai kake koda yaushe baka son maganar
aure, ban saniba ko haka zaka zauna babu aure,
ai tun yanzu ya kamata kafara neman kaga idan
lokacin yazo shikenan sai kawai atada maganar
aure.."
"To anty" yafadi tareda mikewa kasancewar
agajiye yake liss, dakinsa yawuce domin watsa
ruwa amma kuma zuciyarshi sai tuno masa da
rabin ransa takeyi wato nadiya,
Bayan yafito daga wankan ne yaji bazai iya yin
komai ba har sai ya kirata yaji muryarta,
Tana tukunkune ciwon kai na azabtar da ita taji
karar wayarta sharewa tayi taki dauka duk da
cewar bata san wanene mai kiran ba,
Kasancewar yasan halinta na kin daukar waya
idan bata gadamaba yasashi hakura bai sake
kiraba ya ajiye wayar yafita zuwa falo wurinsu
hajiya, kusa da hajiya ya zauna,
"Hajiya yau me kuka dafa ne?"
"Autana ai yau girkinka nayi maka daban, abinda
kafi so nasa aka dafa maka..."
"My hajiya kince yau inji dadina kenan.."
Yafada yana murmushi tareda tashi ya nufi kan
dining yana jin anty siyama tana cewa,
"Kaga dan gatan hajiya"
Murmushi yayi baice komai ba saboda idan da
sabo to yasaba da tsokanar da anty siyama take
yimasa.
Duk da cewar ya kira nadiya bata daga ba
hakan bai hanashi sake kiranta ba da misalin
karfe 9 nadare, amira ce ta dauki wayar saboda
ita nadiyan tayi bacci, ai amira nafada masa
nadiya bata da lafiya ya gigice ya rude,
"Yanzu tana ina?"
"Gata tana bacci.."
Katse wayar yayi yazauna abakin gadonshi duk
sai yake jin jikinsa yana sauya masa, bai san
wanne irin so yake yiwa nadiya ba, kasa aiwatar
da komai yayi ya zauna shiru har na wani
lokaci,
Ganin karfe 11 saura yasa yasake kiranta,
lokacin ta farka tana dafe da kanta wanda yake
yimata zazzafan ciwo....
*_Ummi Shatu_*
[8/14, 12:58 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA..!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO* _(Home of expert &
perfect writers)_
*Gaisuwa mai yawa ga HAJARA MAMI (Natty
girl) ina yimiki fatan alkhairi aduk inda kike..*
_Fatan alkhairi ga Easha Bagwai & Dshanty..._
*45*
aishaummi.blogspot.com
*D*a k'yar ta iya daukar wayar tana mai
runtse idanuwanta saboda zafin ciwo,
"Sannu nadiya... Ya jikin naki?" Yafada muryarsa
asanyaye kamar shine bashida lafiyar,
"Da sauki.."
"Meke damunki?"
"Kainane yake ciwo"
"Kinsha magani?"
Duk ta kosa da wadannan maganganun da
sukeyi saboda sarawar da kanta keyi mata,
"Uhmmm, kinsha magani?"
"Nasha.."
"Sannu, Allah yabaki lafiya"
"Amin"
Shiru kowannensu yayi shi yana tsoron kar ya
cigaba da magana ya dameta ita kuma dama
duk tagama kosawa da maganar da sukeyi,
ahaka suka cigaba da zaman kurame har na
tsawon minti ishirin sai can ya dan saki ajiyar
zuciya yayi magana,
"Baby ko kinyi bacci ne?"
"Uhm, uhm.." Ta amsa masa,
"Kinci abinci ne?"
"Uhm" tasake bashi amsa, shirun suka sake yi,
Tana rike da kanta bata iya komawa bacci ba
saboda baccin da tayi dazu har dare ya raba,
Yanda batayi bacci ba haka shima amadi baiyi
baccinba sai dai idan ya danji shiru yace ko tayi
bacci tace a'a ahaka suka zauna har wurin karfe
4 sai lokacin tasamu barci ya dauketa, jin yayi
magana shiru bata amsaba ya tabbatar masa da
tayi bacci sai lokacin shima yasamu ya dan
kwanta kafin asuba ta karasa.
***
A fusace kabeer yabar gidansu nadiya yana
driving yana tsaki gamida masifa shi kadai,
"Harni yarinyar nan zata cewa wai saurayi zata
aura? To ta auri jariri ma karewar yarinta..."
Shi gaba daya maganganunta babu abinda ya
bata masa rai kamar auren da yaji zatayi nan
yaji tsohuwar soyayyarta ta motsa masa take
sonta ya dawo sabo fil acikin zuciyarsa yaji
yanzu babu wata wadda yake son kasancewa da
ita a matsayin mata sama da nadiya,
Packing yayi agefen titi ya tsaya yafara tunanin
abinda yake shirin faruwa dashi, abubuwa sun
hadar masa goma da ishirin nafarko saki uku
yayiwa nadiya gashi yanzu Allah yasake
jarabtarsa da sonta akaro na biyu a lokacin da
bashida wata dabara, ga zumuncin da yayi watsi
da fatali dashi gamida watsi da yaranshi da yayi
wanda harma sun manta dashi sannan yanzu
kuma yana son kasancewa dasu,
Tsakaninsa da iyayensa babu alaka mai kyau
tsawon shekaru suna fushi dashi sannan asabe
mc kullum cikin zugashi take tana cewa ya rabu
dasu basai yaje wurin da sukeba sannan zasu yi
masa fushin ba, koda yaushe cikin bashi
gurguwar shawara take, yanzu bashida kowa sai
ita, duk tabi ta kanainayeshi ta dorashi akan
hanya marar bullewa.
Kamar zaiyi kuka haka ya lallaba yaja motarsa
ya nufi gida duk da cewa idan yaje babu abinda
zai samu na farin ciki awurin asabe sai ko
damuwa saboda bata da lokacinsa sai na kanta,
bata da tsabta, babu komai atare da ita sai
damuwa shi kansa akoda yaushe yana yiwa
kansa ala wadarai saboda rabuwa da yayi da
nadiya,
Mace mai tsabta da biyayya komai nasa tana
tattali amma banda asabe,
Lokacin da ya kutsa kan motarsa cikin gidan da
asabe yayi arba ta rako wasu kawayenta guda
uku sai shewa sukeyi suna guda daga ita sai
wata yar ficikar Riga kalar ta bacci, kullum aikin
kenan yawo da kayan bacci wuni zatayi dasu
ajikinta,
Ko kallonsu baiyi ba ya wuce packing space yaje
ya faka motarsa ya fito yawuce ciki,
Cikin sauri tabi bayansa zuwa cikin falonta
wanda yake cike da datti domin mai yimata aiki
ta yi tafiya zuwa garinsu ita kuma bazatayi ba,
Akan kujera ya zauna cikeda damuwa, kusa
dashi taje ta rabu tafara farfara idanuwa,
"Barka da zuwa, sannu da dawowa, nima
kawayena na raka, su atika ne sukazo wai
bikinta za ayi shine ta zo yimin maganar anko.."
"Yanzu me kikeso inyi miki?" Yafada akufule
domin acikin haushi yake,
"50 thousands zaka bani.."
"To kibari sai naje na sato kamar yadda nasaba
sai inbaki.."
Yafada cikin fada tareda mikewa, saurin shan
gabansa tayi taci kwalar rigarsa....
***
Misalin karfe 8 nasafe amadi ya fito cikin wata
blue din shadda,rigar iya gwiwarsa ta tsaya mai
dogon hannu, kafarsa sanye da takalmi baki,
sumar kanshi yake tajewa da cumb hajiya ko
fitowa batayi ba tana daki sai mai aikinta ce ke
cikin kitchen tana kiciniyar hada musu break,
Ruwan tea yasha kawai ya fita, bai zame ko
inaba sai kasuwa,koda yajema mutane basu
firfito ba sai kalilan abinda yakaishi yayi ya fito
ya nufi rano,
Lokacin da ya isa garin ba afi karfe 10 nasafe
ba, gidan daga amira sai mama sai nadiya
amma gaba daya yaran an shiryasu sun tafi
makaranta,
Nadiya tana kwance a falon mama akan
doguwar kujera amira ta shigo rikeda wayar
nadiya,
"Anty nadiya yaya Ahmad ne yake kiranki.."
"Mayena kenan.." Tafada acikin zuciyarta amma
afili kuma sai batayi maganaba illa kawai hannu
data mika ta amshi wayar,yanda muryarta take
asanyaye haka shima tashi muryar take sanyi
kalau,
"Ya jikin naki?"
"Da sauki"
"To gani awaje nazo dubiya..."
Mamakine ya isheta saboda jin cewar wai yazo
da wannan sanyin safiyar, amma koda ta tuno
naci da juriya irin nashi sai taga wannan ba
komai bane awurinshi,
"To ai ni bazan iya fitowa ba yanzu ma kaga
akwance nake.."
Juyawa amira tayi ta fita saboda kiran da taji
mama tana kwala mata daga cikin kitchen,
"To ya za ayi kenan?" Taji ya tambayeta, shiru
tayi saboda bata san abinda zatace masa ba,
"Kodai injuya inkoma bakya son ganina?"
Nan dinma shirun tayi bata amsaba,
"Shikenan bari naje natafi.."
Dif taji ya kashe wayar tana kokarin juyawa ta
gyara kwanciyarta kuma taji maganarsa atsakar
gida suna gaisawa da mama,
"Ohhh wannan kowanne irin mutum ne shi oho,
ban taba ganin mutum mai hakurin Ahmad ba.."
Tafada acikin zuciyarta amma kuma tarasa
dalilin da yasa har yanzu bataji tana sonshi ba
domin ko maganar data fadawa yaya kabeer
cewar zata auri amadin kawai tafada ne dan ta
tura masa haushi amma bawai dan tana son
amadin ba,
Tare da Amira suka shiga cikin falon inda nadiya
ke kwance, hijab din dake jikinta ta sake
gyarawa saboda rigar bacci ne ajikinta,
Wajen kanta yaje ya tsaya ya dafa hannun
kujerar da kanta ke kai yana kallonta, tsabar
naci irin na zuciyarshi sai yaji tayi masa yimasa
kyau a wannan yanayin duk da fuskarta akode
take babu kwalliya, idanuwanta arufe, dan
sunkuyawa yayi,
"Baby...."
"Uhmm" ta amsa dakyar saboda bata son sunan
nan da yake fada mata,
"Sannu..., jikinne?"
Kai ta girgiza masa,
"Kinji sauki?"
"Uhmmm"
"To Allah ya kara baki lafiya.."
"Amin.."
Haka yaci gaba da tsaiwa akanta ita kuma tana
kwance ko bude idonta bata yiba bare taganshi
sai dai kamshin daddadan turarenshi gaba daya
ya cika mata hanci,
Sai da Amira ta shigo dauke da tiren abinci
sannan tayi masa magana,
"Yaya Ahmad ka zauna mana.."
Wuri yasamu yaje ya zauna, yaci gaba da kallon
gimbiyar wacce ke kwance jikinta lullube da
hijabinta.....
_*Ummi Shatu*_🏻
[8/15, 1:04 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert
& perfect writers)_
*Gaisuwa mai tarin yawa ga Dije uwar
hawwa, Salma m,Maman humy,pheey tareda yan
matan Amadi Zeebells & Fatima Dasuki,nagode
Allah yabar zumunci...!*
*46*
aishaummi.blogspot.com
*Z*ama yayi akan kujera ya zubawa gimbiyar
ido wacce ke kwance ta lulluba da hijabinta,
"Yaya Ahmad ga breakfast.." Amira tace dashi
tana ajiye masa tiren agabanshi,
"Amira ita nadiya din taci abinci ne?" Ya
tambayi amira muryarsa asanyaye,
"A'a bata ciba amma ai zata ci"
"To ai ita yakamata afara bawa baniba"
"Tom bari naje nakawo mata nata"
Fita amira tayi shikuma yaci gaba da kallon
nadiya wadda ke kwance tana jin duk abinda ke
faruwa,
Babu jimawa amira ta dawo rikeda cup mai
dauke da ruwan zafi sai filet wanda aka doro
soyayyen kwai akai,
"Anty nadiya gashi tashi kici.."
Ko motsi batayi ba bare asaka ran zata tashi,
"Anty nadiya..." Amira tasake kiran sunanta,
tashi amadi yayi yaje ya karbi cup din da filet
din dake hannun amira,
"Kawo amira jeki kawai.."
Bashi amira tayi ta juya ta fita, magana yafara
yimata ahankali cikin sanyin muryarshi,
"Baby.."
"Uhm.."
"Tashi kisha tea din kinji.."
Shiru tayi masa sannan batayi ko motsi ba,
"Yi hakuri baby kitashi, ko bazaki iya tashiba?"
Sake yin shiru tayi har lokacin idanuwanta suna
rufe,
"Tashi kinji.."
"Zan tashi"
"To tashi.."
Hijabinta ta gyara sannan ta tashi ta zauna sai
lokacin ta kalleshi gaba daya haushinsa takeji
saboda ya takurawa rayuwarta karfi da yaji yana
neman ya rusa mata plan dinta da ta shirya,
Akusa da ita ya zauna ya mika mata tea din nan
ta karba fuska adaure kamar dole,
Shikam murmushi yakeyi ganin ta tashi sai wani
cin magani take, idan da sabo yasaba ganin
wannan cin maganin nata sai dai kuma shi
yadau alwashi bazai taba barinta ba har sai ya
mallaketa ya koyar da ita sonshi sannan sai ta
kamu da tsananin sonshi fiyeda yanda yake
sonta duk da zuciyarshi tana fada masa cewar
tana sonshi kawai damuwarta ce ta rinjayi son
shiyasa takasa bayyanar mishi,
Yanda take shan tea din kamar magani takesha,
"Baby bazaki ci kwan ba?"
"Zanci.."
"To ci"
Karba tayi tafara gutsira ahankali tana ci har ya
isheta,
Mamace ta shigo, ganin amadi baici breakfast
dinba yasata fara fadin,
"Yaya kuma zakazo ka zauna baka ci abincin ba,
dan Allah rabu da ita kaje kaci abincinka, ita ai
ba karamar yarinya bace da sai an lallabata.."
Murmushi yayi saida mama tawuce sannan yayi
magana ahankali wanda iya nadiyan ne kadai
taji abinda yace,
"Mama bata san ni lallabaki nake yiba fiyeda
yadda ake lallaba karamin yaro ko jariri..."
Sake daure fuska tayi ta kawar da kanta, tashi
yayi daga kusa da ita yaje ya zauna akujerar
dake fuskantarta yafara shan tea din data rage
yana cin guntun wainar kwan da ta bari,
Iya Wanda ta rage yaci ya ajiye cup din da filet
din nan amira ta shigo tace masa mama tace
yaje su gaisa da Abba saboda abban fita zaiyi,
Tashi yayi yabi bayan amira zuwa falon Abba,
suna zaune shida mama amadi ya shiga suka
gaisa har zai tashi Abba ya dakatar dashi,
"Ahmad dama ina son zanyi magana dakai.."
"To Abba"
"Ahmad kasan da cewar nadiya dai ba budurwa
bace dan haka babu bukatar ayi dogon nema
akanta saboda yanzu tawuce wannan lokacin,
kasancewar ta taba yin aure harda arzikin yara
guda biyu sannan dan uwanta ta aura wanda
dani da mahaifinsa uwarmu daya ubanmu daya"
"Hakane Abba"
"To idan har dagaske ka shirya auren nadiya ina
son ka turo magabatanka duk da cewar ban san
yanda kukayi da itaba, amma naji komai awurin
mahaifiyarta dan haka yanzu abinda nake so
dakai shine ka turo magabatanka, amma kaji ka
amince zaka aureta ahaka?"
"Ehh Abba zan aureta ahaka kuma insha Allah
magabata na zasuzo, nagode madallah, Allah
yakara girma"
"Amin, Allah yasanya albarka acikin neman,
zaka iya tafiya"
Tashi amadi yayi yafita zuciyarsa tayi masa
wani irin sanyi duk da yasan akwai matsalar da
zai fuskanta daga ita yar rigimar tasa amma
yasan insha Allah wannan mai saukine domin
zai jure komai indai daga gareta ne.
Tana zaune a inda yabarta bata san abinda yake
faruwa ba saboda koda wasa bata zaci mama
zata kaiwa Abba maganarba, shiga falon amadi
yayi ya dan saci kallonta nan yaga ta hade rai
kamar zatayi me,
"Baby banfa kawo miki kayan dubiya ba"
"Dama ai ban nemaba"
Murmushi yayi yaje kusa da ita ya sunkuya
saitin fuskarta,
"Allah ya huci zuciyarci da wasa nake nakawo
miki me zaki sha aciki? Lemo ko ayaba?"
Kawar da kanta tayi tayi banza dashi,
"Baby bazaki amsa minba? To bari naje na
shigo miki dasu saboda yanzu zan koma gida
akwai abu muhimmi da naci karo dashi da
sanyin safiyar nan.."
Nan dinma shirun tayi dan haka yafita yaje
wurin motarsa ya bude yafara fito da siyayyar
da ya iyo mata, kayan marmari babu abinda
babu, lemon kwali da na gwangwani da malt, ga
madara, da kanshi ya shigar da kayan cikin
gidan nan amira ta tayashi kasancewar amir
baya nan yatafi sumaila hutu gidan umman
sumaila,
Atare mama da Abba suka fito,lekawa falon
Abba yayi yai mata sannu nan ta gaisheshi ya
fita yatafi wurin aiki bayan yayiwa amadi
godiyar wahalar da ya iyo ta siyayya,
"Baby bari naje nakoma sai munyi waya ko?
Allah yabaki lafiya kinji"
"Amin" tafada fuskarta aturbune, duk sai amira
dake tsaye taji babu dadi saboda ita bataga
laifin amadi ba,saurayi mai class irinshi
kyakkyawa mai ilmi komai nashi na classic guys
amma sai faman wahalar dashi nadiya take,
"To baby bye"
Fita yayi yana yiwa amira sallama, "amira sai
anjima Allah yakara sauki"
"Amin yaya Ahmad Allah ya kiyaye hanya
angode madalla"
Kallon nadiya Amira tayi, "Anty nadiya gaskiya
wallahi abinda kike yiwa yaya Ahmad yayi yawa,
kiri kiri fa kike nuna bakya sonsa gashi yayita
yimiki magana amma kiyi banza dashi sai kin
gadama zaki amsa masa..."
"Ke ina wasa dake? Ni sa'arki ce? Karki yimin
rashin kunya wallahi yanzun nan jikinki zai gaya
miki.."
"Idan kuwa kika kuskura kika dakar min'ya nima
sai na yimiki dan banzan duka" mama tafada
bayan ta shigo cikin Falon saboda taji duk
abubuwan da suka fada,
Fada mama taci gaba dayi,
"Haba abubuwan naki sun wuce hankali, narasa
wanne irin kafiya da shegen taurin kai Allah
yabaki, yarinya sai kace mutanen farko ataurin
kai, shi wannan yaron meye nashi aciki da zaki
rinka wulakantashi, sai kace shine yaje yace
kabeer din ya sakeki? Akanki aka fara rabuwar
aure da zakibi ki tsangwami yaro kamar shine
yayi miki silar mutuwar auren, to bari kiji abinda
amira tafada miki gaskiya tafada sannan wallahi
mutukar baki so mai sonki ba to kuwa zakiso
makiyinki, haba kaji min yarinya mai masifar
taurin kai kamar baki san kaddara ba?"
Hawayene sharrrr suka fara bin kumatun nadiya
ita bacin ranta wato harsu mama summa manta
da bakar azabar da tasha da damuwar da ta
tsinci kanta ashekarun baya ata sanadiyyar da
namiji, har ciwon hawan jini sai da yakamata da
tazo da karar kwana ma tana iya mutuwa amma
shine yanzu tun ba aje ko inaba har sun manta
suna ganin laifinta saboda kawai wannan yar
karamar yaudarar da amadi ya shiryo mata,
"Yanzu mama laifina kuka gani kenan? Kun
manta halin da nashiga abaya, kun manta
damuwar da yaya kabeer ya jefani?"
"To ai nadiya mutane basu taru sun zama
dayaba, kowa da halinsa, kimanta da kabeer ki
fuskanci Ahmad mai sonki nagaskiya.."
"Wallahi nidai mama bana sonshi, ni bana
sonshi, bana sonshi, haka yaya kabeer ma sai
da nace bana sonshi amma aka matsanta min
har sai da na aureshi daga karshe yayi min
butulci,ni bazan yi aure yanzu ba.."
Tafada cikin kuka tareda kifa kanta ahannun
kujera tana kuka....
*_Ummi Shatu_*🏻
[19/08, 7:22 p.m.] Ummy Aysha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert
& perfect writers)_
_Page 47-49 nayi shine domin jin dadinku
Aunty's din anty amadi, ANTY MAIJIDDA, ANTY
BARAKA, ANTY SIS & MOMCYN ANAS.._
*47*
aishaummi.blogspot.com
*T*sayawa kawai mama tayi tana kallonta
amma acan k'asan zuciyarta tausayinta take ji
saboda tasan tsoron sake shiga irin halin data
shiga abaya take yi sai dai amma kuma tunda ta
samu mai sonta da gaskiya ai bazasu zuba
mata ido har ya sub'uce mata ba,
Juyawa mama tayi ta fita bata sake magana ba
tabar nadiya tanata faman shasshekar kuka,
Amira ce taje kusa da ita ta zauna tafara bata
baki,
"Anty nadiya dan Allah kiyi shiru, Allah ya baki
hakuri amma wallahi yaya Ahmad yana sonki ni
tausayinshi ma nake ji saboda gaba d'aya
bashida buri sai na kyautata miki, baya son
b'acin ranki nasan ma wallahi ko auren ma
kukayi sai yanda kikayi dashi tunda yana son
farin cikinki.."
D'agowa nadiya tayi fuskarta shabe shabe da
hawaye,
"Haba Amira ai bai kamata yanzu ace dole sai
nayi aureba tunda nayi auren nan naji abinda ke
cikinsa, yanzu dan Allah ko a mafarki kin tab'a
zaton cewar yaya kabeer zaiyi min haka? To shi
da yake dan uwanama jinina ga abinda yayi min
inaga wanda yake bare banida hadin komai
dashi? Yaya kabeer fa jiya yazo gidan nan yace
min wai dole sai nabashi yaranshi har da su
zancen zai kaink kotu akai.."
Baki bude dan tsananin mamaki Amira ta
kalleta, "yaya kabeer din? Dan rashin mutunci ko
dan me? Mutumin da bai sake bi takan yaranba
amma shike ikirarin abashi su?"
"Wallahi Amira dagaske nake ba karya ba,
tsabar bacin ranshine da fargaba ya haifar min
da rashin lafiyar da nake ciki yanzu"
"Allah ya rufa asiri amma ai babu alkalin da zai
bashi su fadeel yanzu.."
Mama dake waje tana jin duk abinda suke fada
amma batace komai ba sai dai ta cika da
mamakin kokari irin na kabeer.
Lokacin da Amadi ya koma gida yayi niyyar
sanar da hajiya maganar aurenshi da nadiya
amma sai yaji ta tareshi da maganar cewar
gobe yayyunshi zasu zo saboda dama sukan
ware lokaci na musamman suzo gidan gaba
dayansu su dan tattauna su sada zumunci
bayan kamar sati biyu sai kowa yakoma inda ya
fito jin haka yasashi yin shiru har sai yan uwan
nashi sunzo sannan zaiyi maganar,kiran nadiya
kuwa tunda ya dawo yake kiranta duk da idan ta
dauka bata yimasa magana da yawa daga uhm
sai um um amma hakan bai hanashi sake
kiranta yaji jikinta ba, kowacce rana yana yi
mata waya sau 8 koma fiyeda haka.
Washe gari tunda safe baki suka fara sauka,
anty dija itace tafara zuwa itada yaranta guda
uku biyu maza mansur da muhsin sai mace
guda daya Amal, hajiya rasa inda zata saka
jikokinta tayi dan murna, dakin amadi sukaje
suka tasheshi daga baccin da yake ta hanyar
yin tsalle akansa dole babu shiri ya tashi, zuwan
anty Dija da kamar minti 20 Anty siyama tazo
domin ita agari take tana zuwa yaya yaseen na
zuwa shima amma shi baizo da matarshi da
yaranshi ba shi kadai yazo nan gidan ya
gauraye da hirarsu da shewarsu yaran anty Dija
da anty siyama kuwa sai wasansu suke suna
tsalle ajikin amadi,
Girke girke kala kala hajiya tasa aka shirya
musu amma kuma duk da murnar ganinsu bai sa
ta manta da shalelenta amadi ba domin komai
tace autanta komai autanta.
Sai bayan sallar azahar sannan anty hamida
tazo wacce ita amadi ke bi nan gida yasake
hargitsewa da murna, cikeda murnar ganin juna
suka shiga gaggaisawa kafin su hau table domin
diban garar da hajiya tasa aka shirya musu,
kowa acikinsu tsokanar amadi yake yi sai kace
wani kakansu daga kowa ya debo tsokanarsa
sai yace autan hajiya ko anty amadi kaza,
Har dare suna tare afalon hajiya suna shan hirar
yaushe gamo sai misalin karfe 11 sannan suka
fara kokarin neman makwanci,
"Anty amadi adakinka fa zamu kwana yau sai
dai ka dawo falo kan doguwar kujera.." Anty Dija
ta fada tana rikeda amal akan kafadarta,
"A'a babu mai kawo min auta falo yana dakinsa
kuje ku k'ak'aba adakina kuda 'yayanku" hajiya
ta fada,
"To hajiya" anty Dija ta amsa mata tawuce
dakinta, dakinshi shima amadi yawuce yaje yayi
shirin bacci yana son ya kira nadiya yana tsoron
ko tayi bacci kar ya tasheta daga karshe dai
yayi hakuri ya kyaleta bai kirata ba.
Kamar koda yaushe yanda suka saba suna
tattauna abubuwan da suka shafesu akowanne
zama yauma sunyi irin wannan tattaunarwa
saida amadi yaji kowa ya gama fadin abinda
yake son fada sannan yace yanada magana,
"To autan hajiya muna jinka meya faru?" Yaseen
yace dashi,
"Yaya dama wata yarinyace nake so kuma
iyayenta sunce naturo magabata na.."
Shiru dukkaninsu suka yi babu wanda yayi
magana shi kuwa yaseen zubawa amadi ido yayi
kawai yana kallonsa,
"Kai anty amadi me yakaika nemo aure tun
yanzu?" Anty Dija ta fada tana mamakinsa,
"Anty wacce nake so Nagani shiyasa.."
"Ai ko zakayi aure sai kabari ka cika 30 years
tukunna ko" anty hamida ta fada,
"Nifa badake nake ba" yace da hamida saboda
ita yake bi sakonshi ce,
"Kar dai kayi min rashin kunya" tafada tana
harararshi,
"Waima duk ba wannan ba kai yanzu ko ance za
ayi maka aure sai ka yarda? Iya masters fa
gareka kadai, sannan baka da gida bakayi gida
ba, baka jima da fara aiki ba, haba anty amadi
kadai sauya shawara" anty siyama ta fada,
"Anty nidai ko banida gida zanyi aure yanzu"
"Baza kayiba, babu wanda zaiyi maka aure
yanzu, ka bude kunnenka dakyau ma kaji karatu
zaka koma nanda next month dan haka karka
sake yimin maganar aure yanzu.." Yaseen yace
dashi cikin fada, jin babu wanda ya goya masa
baya yasa idanuwanshi kadawa suka yi jajur
zuciyarshi ta soma radadi...
_*Ummi Shatu*_
[19/08, 7:22 p.m.] Ummy Aysha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert &
perfect writers_
*48*
aishaummi.blogspot.com
*Z*uciyarshi na wani irin rad'ad'i ya dubi
yayan nashi idanuwanshi jajur,
"Yaya to idan banyi aure yanzu ba sai yaushe
zanyi?"
"Sai lokacin da ka girma ka isa aure, kai bama
tun dadewa nayi maka gargadin kula yan mata
ba? Wato sai da ka kula su ko har wata tayi
nasarar janye hankalinka, to bari kaji in fada
maka wani abu kai da yin aure sai nan da 5 ko
6 years amma banda yanzu"
"Yaya ni wallahi bazan iya kara ko nanda
shekara daya batare da nayi aure ba"
Jin abinda yace yasasu dukkaninsu kallonsa cike
da mamaki,
"Kai yanzu har ka isa aure? Lallai amma wallahi
kayi kankanta da yin aure yanzu.." Anty hamida
ta fada tana jijjiga kai,
"Idan nayi kankanta da aure amma ai banyi
kankanta da yin iskanci ba..."
Wata tsawa yaseen ya daka masa, "wallahi
karka kuskura, idan har ka kuskura kayi abinda
bakinka yake fada wallahi sai na raunata ka sai
nayi maka illa, harmu zaka duba kace ka isa yin
iskanci? To bismillah ga wurin nan kaje kayi,
tunda abin naka ma hakane to wallahi kasar
zaka bari karatu zaka koma.."
"Yaya ni bance zan zama dan iska ba amma
maganin hakan kawai ayi min auren nan kuma
ko karatun zan koma to afara yimin aure
tukunna"
"Idan bakinka yasake ambaton kalmar nan sai
na fasa maka baki, wai yaron nan yaushe ka
zama haka ohhhh lallai kam kaje jami'a kaga
yan mata dole kazo gaban idona kana fada min
haka amma to kasani bamu shirya yi maka aure
yanzu ba karka ji da wai" yaseen yafada cikin
fad'a,
Tashi amadi yayi ya wuce dakinsa idonshi yana
kokarin kawo kwalla,
Ita dai hajiya tunda aka fara maganar batace ko
k'ala ba saboda yaseen shine babba kuma
yanzu shine kamar uba ga amadi shiyasa
bazata goyi bayan amadin ba gudun kar wata
matsala kuma ta kunno kai amma ita tana jin
zata goya masa baya tunda auren yake so gashi
da bakinsa yana cewa idan ba ayi masa ba zai
zama dan iska,
Tunda Amadi yabar wurin su anty Dija suke
tattauna maganar da yayansu yaseen amma ita
anty hameeda ta dan sauko tana ganin gara ayi
masa auren tunda ya nuna yana so sai dai
yaseen ya kafe kai da fata yace ko zai yi masa
aure sai ya shekara 35.
Tunda amadi ya shiga daki ya zauna yake
kuka rabon da yayi kuka har ya manta domin
tun rasuwar mahaifinsu amma yau akan nadiya
ya zauna yana kuka, har hajiya ta shigo kukan
yake hakan yabata mamaki,
"Autana kuka? Kuka kamar ba namiji ba, haba
auta yi shiru akan auren ne? Indai aurene za ayi
maka daina kuka"
"Hajiya amma kinaji ai yaya yace wai sai dai
inkoma makaranta amma bazai yimin aure
yanzu ba, ni babu karatun da zan koma wallahi
har sai anyi min auren nan"
"To ya isa ai nace za ayi maka ba shikenan ba"
"Hajiya tunda yaya yace bazaiyi ba ai nasan
bayi min zaiyi ba"
"Ai ni nace za ayi maka kama daina damuwa
akan wannan kaji, share hawayenka"
Jin hajiya ta goyi da bayansa sai yaji hankalinsa
ya kwanta zuciyarshi tayi sanyi nan ya saki
jikinsa saboda yasan yanzu bashida matsala,nan
takama hannunshi zuwa kan dining.
Washe gari da safe bayan sun gama yin
breakfast yaseen ya kalleshi,
"Na turo maka link din da zaka cike foam din
makarantar da zaka koma ka duba email dinka"
"Yaya baki nayiba amma nifa bazan koma
karatu ba har sai nayi aure.."
Azuciye yaseen ya tashi zaiyi kansa Anty siyama
tayi gaggawar shiga gabansa,
"Yaron nan naga alamun duka kake so inyi
maka wallahi, ni kake fadawa cewar bazaka
koma karatu ba har sai kayi aure? Kai har wani
karatun kirki kayi? Masters din da kayi shine har
kake ganin karanka yakai tseko? Mata nawane
masu masters yanzu, banza shashasha"
"Nidai ko secondary gareni ya isheni inyi
aure,kuma indai ba lalata yaran mutane akeso
infara ba to abarni inyi aure"
"Karka fasa kaje kayi duk abinda zakayi" yaseen
ya fada azuciye,
"Kai yaya amadi wai bakinka bazai yi shiru ba?"
Anty Dija ta fada,
"Anty ai ni ba rashin kunya nake yi masa ba, ni
kawai aure nake so, wallahi idan har banyi aure
ba komai yana iya faruwa..."
"Auta tashi kaje" hajiya tace da dashi saboda jin
yana kokarin yimusu tabargaza,
"Matsalar yan auta kenan wallahi basu da kunya
ga shegiyar shagwaba" anty hameeda ta fada,
"Ai wanda kikaji kadanne nifa daga cemasa baya
yawo sai cemin yayi wai to zai fara zuwa hotel
da clubs yana hutawa" anty siyama tafada tana
dariya,
"Zanyi maganinsa ai, wallahi karatu zai koma
nanda wani month din.."
"Yaya abinda nakeso dakai tunda yaron nan ya
nuna auren yake so to muyi masa saboda mu
kare masa mutunci sannan mu karewa kanmu,
domin indai bamu yimasa aure ba kuma yana so
to fa shaidan bazai barshi ba zai ta ingizashi
daga karshe azo ashiga halin da ba aso,dan
haka kayi hakuri muyi masa auren tunda yanuna
yanada bukatarsa kuma karatu yace zai koma
amma sai anyi masa aure" hajiya tace dasu
tana rikeda kumatunta,
"To hajiya shikenan za ayi kamar yadda kikace
amma kifa tuna shekarun yaron nan kwata
kwata 28 ne kacal fa ko 30 baiyi ba" inji yaseen,
"Ehh babu komai mudai yimasa shikenan mun
fita hakkinsa" hajiya tabashi amsa,
"To shikenan hajiya"
Akan haka suka tsaya na za ayiwa amadi aure
amma har lokacin yaseen bai huceba haushin
amadi yakeji saboda duk barazanar da ya dade
yana yimasa akan cewar babu shi babu kula
yanmata amma shine sai da ya kula su.
Amadi kuwa duk da bai san abinda su hajiya
suka tattauna ba bayan tafiyarsa hakan bai saka
yaji son auren nadiya ya ragu acikin ranshi ba
shi yanzu ne ma yake jin wani shaukin sonta
acikin zuciyarshi,wayarshi ya dauka ya kirata,
fitowarta kenan daga wanka kamar ba zata
daga ba ta daure ta dauka,
"Baby nah.., ya jikin?"
"Da sauki"
Shiru yayi yana sauraren muryarta har yaji tayi
shiru,
"Yanzu me kikeyi? Uhmmm?"
Sai da yafi minti miyar da tambayarta sannan
tabashi amsa,
"Abu nake yi?"
"Menene shi? Fada min sai inzo in tayaki"
Shiru tayi masa har sai da yasake maimaitawa,
"daga wanka na fito zan shirya, sai anjima"
"Dan Allah tsaya kiji, karki kashe dan Allah,
kinga da ina kusa nine zanyi miki wankan,nine
zan shiryak..."
K'ittt ta kashe wayar acikin zuciyarta tana
mamakinsa dama haka yake shima, afuska
kamar salihi ashe ashe, shika A ne,
Murmushi yayi saboda shi kansa bai san lokacin
da ya soma sakin layiba.
Kwana uku da tsayar da maganar yiwa amadi
aure yaseen yasake tarasu yafara tambayar
amadi wacece yarinyar da yake so,
"Sunanta nadiya"
"A ina gidansu yake?"
"A rano suke"
Dukkaninsu mamaki ne ya kamasu saboda sun
zaci zaice a abuja sai sukaji sabanin haka,
"Good, wacece ita sannan waye mahaifinta?"
"Mahaifinta babban dan kasuwa ne sannan yana
aiki a state government, ita kuma dalibata ce a
KUT amma bazawara ce ta tab'a aure kuma
tanada yara biyu"
Atsorace yaseen ya kalleshi yayinda yayunshi
Mata suka hau salati da sallallami,
"Auta bazawara?" Hajiya tace dashi cikin
mamaki,
"Anty amadi bazawara fa kace, kanada hankali
kuwa?",anty Dija ta fada cikin zaro ido,
"Da hankalina anty, ai ba haramun bane, ni
wallahi ita nakeso kuma ita zan aura"
"To kuwa bazaka aureta ba koda kuwa zaka
mutu, kaji yaro da shashanci, sai kace marar
mafadi? Karasa wacce zaka so sai bazawara?"
Yaseen yafada cikeda mamaki,
"Gaskiya auta nima anan ban goyi bayanka ba,
kaje ka sauya shawara saboda nima bazan goyi
bayan da ka auri bazawara ba, ai sai ta rinka yi
maka wayo.." Hajiya ta dora nata jawabin,
"Hajiya..."
"Kai tashi ka fita daga nan, tashi ka fice ko inzo
inyi ball dakai.." Yaseen yafada azuciye, tashi
amadi yayi ya fita hankalinsa yakai kololuwar
tashi, ransa kuwa idan yayi dubu to ya b'aci.....
*_Ummi Shatu_*
[19/08, 7:22 p.m.] Ummy Aysha: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*49*
aishaummi.blogspot.com
*K*o gabansa dak'yar yake gani saboda
tsananin damuwa da b'acin rai, dakinsa ya
shiga ya zauna zuciyarsa tana faman yimasa
zugi da zafi, gaba daya yama rasa abinda zaiyi
kuka ko me? Tagumi yayi jikinsa sai tsuma
yake,
Gaba daya babu wanda ya goyi bayan amadi ya
auri bazawara har hajiya wannan karon taki bin
bayansa, anty siyama kuwa cewa tayi ai ga
kanwar mijinta nan zee dake mutuwar sonshi a
aura masa ita kawai anan ne kuma hajiya bata
bada goyon baya ba tace adai kyaleshi yasake
nemowa da kanshi.
Tunda amadi ya shiga daki bai fitoba su hajiya
sunyi tsammanin ko fushin ne har lokacin bai
huce ba ashe ba haka bane zazzabi ne mai zafi
ya rufeshi dan haka babu shiri ya kwanta ya
lulluba da bargo, yana nan kwance har la'asar
tayi ganin bai fitoba yasa hajiya lekawa dakin
nasa nan ta hangoshi kwance cikin bargo,
Hankali atashe hajiya taje gaban gadon tana
kiransa, "auta..!!! Auta na, meya sameka?"
Jin jikinsa tayi zafi zau lokacin data yaye
bargon,
"Baka da lafiya shine baka fada min ba auta?
Meyasa?"
Kamar hajiya zatayi kuka ta fita ta kira yayunsa
nan ta taho masa da abinci da magani, kamar
karamin yaro haka ta sakashi agaba ta bashi ya
dan ci yasha magani, wani irin ciwo kansa yake
yi masa kamar zai bar gangar jikinsa.
Kasancewar autane shalele kowa sai da ya nuna
damuwarsa akan rashin lafiyar amadi nan aka
manta da batun maganar auren da yace zaiyi
amma shi abin yana nan acikin ransa, har dare
yayi dukkaninsu suna dakinsa ana hira shikam
yana kwance kansa akan cinyar hajiya tana
shafar kansa kamar wani jariri,
Lokacin da yaga kowa yafice sai iya hajiya
yasamu damar yimata magana,
"Yanzu hajiya kun k'wammace inje inyi zina
akan ku aura min wacce nake so? Hajiya idan fa
bakuyi min auren nan ba tunda ina son yarinyar
nan kuma ace itama tana sona to fa shaidan zai
iya ribatarmu mu aikata abinda bashi kenan
ba,saboda zamu rinka ganin ai tunda baza
abarmu mu mallaki junanmu ba gara mu aikata
komai, amma idan har kuka amince na aureta
hajiya kun taimakawa rayuwata sannan kun
tamaka mata itama, kuma ni banga abin gudu a
auren bazawara ba tunda annabinmu ma da ita
yafara alhalin shima bai taba yin aure ba, dan
Allah hajiya kiyi min wannan alfarmar a
matsayinki na mahaifiya ta, ku barni na auri
nadiya.."
Shiru hajiya tayi na wani dan lokaci sannan ta
shafi sumar kansa,
"To autana kabari zan duba Nagani kasan nafi
kowa sonka shiyasa bazan taba bari wani abu
ya cutar dakai ba, zanyi maka istihara nagani
idan har aurenka da ita alkhairi ne Allah ya
tabbatar idan kuma ba alkhairi bane Allah ya
sauya maka da wacce tafita alkhairi"
"Yawwa hajiyata, insha Allah ma alkhairi ne.."
"Allah yasa haka"
Sallama hajiya tayi masa ta tashi tafita ta ja
masa kofar, shiru amadi yayi yana tunanin
nadiya acikin ransa, shi ko zai koma karatu to
yafi son sai andaura aurensa da ita saboda gani
yake muddin ya tafi bai aureta ba to kafin
yadawo wani ya aure masa ita.
***
Kallon asabe kabeer yayi zuciyarsa cike da jin
haushinta nan ya fincike hannunta daga jikin
kwalar rigarsa amma bata hakura ba sai da ta
sake cakumar wuyar rigar tasa,
"Sakeni.., sakeni nace ko jikinki ya fada miki
yanzun nan.." Yafada cikin karaji, maimakon ta
sakeshi sai jan rigar tasa tayi ta ketata nan ya
rufeta da duka itama tana ramawa amma da
yake karfinsa da nata ba d'aya bane yasa yayi
mata lilisss, zaginsa ta hau yi tana cewa dole
dai sai ya zauna da ita ko yana so ko baya so,
Cikeda bakin ciki yaje ya sauya kayan jikinsa
yabar gidan, kusan koda yaushe hakace take
faruwa, kullum acikin fada suke ta zageshi tass
shikuma ya nada mata na jaki, shi kansa idan
ya zauna sai ya rasa gane wacce irin musiba ce
ta sauka akansa, nadiya ce ta fado masa nan
kuma yaji hankalinsa ya sake karkata agareta
take zuciyarsa tafara aiyana masa wani abu...
***
A b'angaren nadiya kuwa tun tana fushi akan
fadan da mama tayi mata har ta hakura ta ware
amma bata taba sanin cewa Abba yayi magana
da amadi akanta ba,
Yau da safe misalin karfe 9 amira tazo ta kirata
tace taje Abba na kiranta, fita tayi daga cikin
bargonta ta dauki hijab dinta ta nufi falon Abba,
Yana zaune shida mama ya kammala karyawa,
Zama tayi ta gaidashi, cikin fara'a ya amsa
sannan ya dubeta duba irin na maganar da za
ayi mai muhimmanci ce,
"Nadiya wannan yaron Ahmad tun yaushe yake
zuwa wurinki?"
Gabanta ne ya fadi ras rass domin jikinta yafara
bata cewar Abba maganar aure zaiyi mata,
"Abba bamu dade tareda shi ba kuma ni wallahi
bani nafada masa gidanmu ba haka kawai
naganshi yazo.."
"To nadiya in banda abinki ai mai sonka shi
yake zuwa Inda kake,sannan agaskiya ni na
yaba da nutsuwar yaron wannan dalilinne ma
yasa nabashi dama domin ya turo magabatansa
ayi maganar aurenku tunda kedai yanzu ba
karamar yarinya bace.."
Hawaye ne suka fara bin kumatun nadiya wanda
takasa magana,
"Kiyi hakuri nadiya nasan ke mai biyayya ce
sannan mai hakuri ce akan komai, to yanzun ma
wannan biyayyar taki da nasanki da ita zaki
yimin ki auri wannan yaron domin nagari ne,
nasan abaya kinyi mana biyayya kin auri
kabeeru wanda bakiji dadin zama dashi ba to
yanzu kuma insha Allah zakiji dadi ko dan
biyayyar da kike yimana.."
"To Abba" shine kawai abinda nadiya ta iya
cewa sai ko hawaye dake faman bulbula daga
idanuwanta,
"Allah yayi miki albarka nadiya, Allah yasa
yaranki kema suyi miki irin biyayyar da kike
yimana,kiyita hakuri kinji"
"To Abba"
"Allah yayi albarka,shikenan tashi kije.."
Tashi tayi tafita tana faman hawaye, tana zuwa
daki ta zauna ta shiga kuka, kuka take sosai
kamar wacce aka rafkawa mutuwa, ita bakin
cikinta ma amadi fa ko ta bakinta baiji ba amma
shine zai tafi wurin Abba kai tsaye kenan auren
dole yakeso ayi mata ko me??
Ta dade tana rusar kuka kafin ta dauki wayarta
ta tura masa text massage,
_Yaushe mukayi haka dakai, yaushe nace zan
aureka da har zakaje wurin Abba kace zaka turo
Manyanka,ka tab'a ganin inda aka yiwa
bazawara auren dole? Ni nafada maka bana
sonka ka rabu dani ko dole ne auren? Nidai
kasani muddin na aureka to auren dole akayi
min domin ban taba jin sonka acikin raina ba..._
Ganin massage dinta yasa amadi shiga cikin
mamaki domin bata taba tura masa da text
massage ba, yana karantawa yaji hankalinsa
yatashi nan yayita kiran wayarta amma taki
dauka daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba
daya, duk da cewa bashi da lafiya yana zazzabi
haka ya figi mota ya tafi rano saboda fushin
nadiya agareshi babban abune ko kadan baya
son fushinta,
Karfe 11 nasafe ya isa kofar gidansu sai dai yau
baizo da niyyar shiga cikiba domin kananan
kayane ma ajikinsa ga zazzabi dake damunsa,
Wayarta ya kira taki dauka domin ta bude wayar
lokacin, text ya tura mata cewar yana kofar gida
tayi hakuri ta fito, dama kamar wadda take jira
nan ta dauki hijabi ta fita afusace domin sai ta
tsattsageshi sannan zataji dadi, kofar motar ta
bude ta shiga yana zaune ya dora kansa ajikin
sitiyarin motar saboda wahalar da yakeji,kansa
ya daga ya kalleta yasake dorashi akan sitiyarin
yana kallonta,
"Baby meyake faruwa ne, laifin me kuma nayi?"
"Au ba kasanma abinda kayiba kenan? Yanzu
kayi min adalci da har zakaje wurin Abba ka kai
kanka kace zaka turo ayi maganar aurenmu
bayan bani nabaka wannan damar ba? Ka taba
jin nace ina sonka bare har nace zan aureka? Ni
ba sonka nakeba,wancan auren ma da nayi
shima ba son mijin nakeba ko ahaka zan kare a
auren mazajen da bana so basa sona? Ni
shikenan bazanji dadin aure ba kowanne aure da
akwai matsalar da zan fuskanta?"
Kallonta kawai yake yi da jajayen idanuwansa
wadanda suka yi ja saboda wahalar zazzabi har
lokacin kansa yana bisa sitayarin motar
akwance, sai da yaji ta tsagaita daga masifar da
take balbala masa sannan yayi magana cikin
muryarsa mai masifar sanyi,
"Allah yabaki hakuri baby, wallahi bani nakai
kaina wurin Abba ba, shine ya kirani yace inturo
manyana amma kiyi hakuri, sannan idan kikace
wai bana sonki bakiyi min adalci ba, da ace
yanzu kin san halin da nake ciki saboda ke
wallahi da sai kin tausaya min"
"Wanne so kake min? So ko sha'awa? Babu
wani sona da kake kawai kai dai kana sone
kasamu wani abu daban atare dani daga nan
kuma wulakanci ya biyo baya.."
Murmushi yayi ya kalleta, "sha'awa fa kikace?
Haba baby idan sha'awace ke damuna ba so ba
ai da sai in nemi budurwa in magance
sha'awata shikenan.."
"To koma dai menene bari kaji koda ace zan
aureka sai munyi yarjejeniya dakai sannan sai
kayi min alk'awai guda daya.."
Har lokacin fuskarsa dauke take da murmushi,
jijjiga mata kai yayi, "yarjejeniyar me zamuyi
sannan wanne alkawari kike so inyi miki? Zanyi
miki shi ko na menene mutukar atare dani abun
yake".
*_Ummi Shatu_*🏻
[8/21, 3:30 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert
& perfect writers)_
_Fatan alkhairi ga daukacin masoya masu
bibiyar labarin.._
*50*
aishaummi.blogspot.com
*S*ai da ta hade rai sannan tace,
"Koda na amince munyi aure to ba zaka
kusanceni ta karfi ba har sai da yardata da
amincewata.."
Duk da cewar yaji maganar tata wata iri amma
sai yaji tazo masa da sauki saboda bai zaci
wannan maganar zata fada ba,
Shiru yayi yana nazari amma kuma zuciyarshi
tana ta tausarshi ta hanyar cemishi,
"Tunda kana sonta kawai ka amince da kanta
zata nemeka badai mace bace ai mata akwai
rauni.."
Ganin yaki yayi mata magana yanata murmushi
shi kadai yasata yin magana,
"Kai nake jira fa kayi magana"
"Ni ai na amince karki samu damuwa..."
Galala tayi tana kallonsa domin koda wasa bata
dauka zai amince acikin sauki ba duba da cewar
shi saurayine ba taba yin auren yayiba,
"Shikenan tunda ka amince amma kasani
alkawari fa ka dauka.."
"Nasani.." Yabata amsa,
"Shikenan yayi kyau" tafada tana kokarin bude
kofar motar domin fita,
"Baby zan samu maganin zazzabi agidanku?
Wallahi zazzabi ke damuna yanzu ma ba kiji
jikina ba"
"Za a iya samu bari naje na duba.."
Fita tayi yabita da kallo "baby riigima" yafada
acikin zuciyarsa.
Paracetamol ta dauko masa sachet daya
sannan taje falon abba ta dauko bottle watar
guda daya marar sanyi tafito,
Yana nan kamar yadda ta tafi tabarshi haka ta
dawo ta sameshi,mika mishi tayi yatashi ya
karba ya balli maganin guda biyu yasha yana
yamutsa fuska,
Sake kwanciya yayi ajikin sitiyarin, dukkaninsu
sunyi shiru babu wanda yake cewa komai da
haka har bacci ya dan fara daukarshi sama
sama,
Juyawa tayi ta kalleshi da niyyar tayi masa
sallama ta koma gida amma kamar da wasa sai
taga wai yayi bacci, zuba masa ido tayi tana
kallonsa, hakika duk inda ake neman cikakken
namiji to amadi yakai matsalar kawai ita har
yanzu bata sake dashi bane gudun kar akuma
sake maimaita abinda yafaru abaya.
Sai da yashaki baccinsa ya more sannan ya
bude idonsa bai zaci zai ganta ba amma sai
yaganta zaune,
"Baby yi hakuri wallahi ban ma san time din da
baccin ya daukeni ba"
Shiru tayi bata tanka ba dama kuma yasan ba
tankawar zatayi ba,
"Bari naje na tafi.."
"Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda bude kofar
motar ta fita, ko akwalar rigarsa abin da tayi,
tashin motarsa yayi yakara mai ya nufi gida.
Kwana biyu da faruwar haka hajiya tace masa
ta amince ya auri bazawara mutukar hakan zai
samar masa da kwanciyar hankali duk da bata
so tayi nesa dashi,
Tara yayunshi hajiya tayi tace musu subar
amadi ya auri nadiya kamar yadda yake so
kuma itama yanzu taji auren ya kwanta mata
arai, babu wanda yayi magana acikinsu saboda
dama sun san hakace zata faru tunda dan
gaban goshi ne.
Murnar da amadi yayi kamar zaiyi me, nan
yaseen yace duk da haka dai zai koma karatu,
amadi bai damuba saboda yasan idan har aka
aura masa nadiya angama mai wahalar ko bata
tare ba.
Lokacin da yayi mata waya yace manyanshi
zasu zo bata yi wani murna ba shi kadaine
kawai ke murna, nan ta kashe wayar ta ajiye
gefe tana dan karamin tsaki,
"Anty nadiya nifa ina jiye miki wani abu guda
daya, karfa yanzu yaya Ahmad kawai lallabaki
yake sai kunyi aure yazo ya rama duk wadannan
abubuwan da kike yimasa ko kuma yabari sai
kin kamu da sonshi sannan ya rama koma har
yayi doubling.." Amira dake gefe tana yin sak'a
da kwarashi ta fada,
"Amira kenan idan har yayi min haka ko fiye da
haka zan barshi ne da Allah kawai kamar yadda
nabar yaya kabeer da Allah, nasan haushina
kukeji kuna ganin kamar bana kyautawa Ahmad
saboda abubuwan da nake yi masa, Amira shi
so yanada wahalar gaske sannan duk zuciyar da
ta samu kanta acikin halin da na samu kaina
dole ta tsani soyayya, Amira banida wani labari
mai dadi da zan bayar Wanda na tsinta acikin
auren da nayi abaya, kawai dai bautar Allah nayi
amma bawai samun farin cikiba.."
"To amma anty nadiya ai shi yaya Ahmad
yanada banbanci da yaya kabeer, halayensu ma
ba iri daya bane.."
"Amira kenan ke yarinya ce, to bari kiji su maza
gaba daya halayensu iri dayane sunane kawai ya
banbanta su.."
"A'a anty nadiya ni yanzu inada kwakkwaran
dalilin da Zan iya fada wanda ya banbance yaya
Ahmad da yaya kabeer"
"Menene shi?"
"Son yanmata, yaya Ahmad bashi da kule kulen
yanmata, amma shi kuwa yaya kabeer kamar na
mamajo"
"Shi Ahmad din waye yafada miki baya kula
yanmata? Ai ni yanzu banida yakini akan namiji
domin bashida tabbas"
"Da yana kulawa ai da zaki sani"
"Tayaya Zan sani Amira? Gidanmu daya dashi?"
Dariya Amira tayi "kai anty nadiya kina bani
dariya.. Amma dai ya kamata ai ki sani"
"Hakane" nadiya tafada,acikin ranta kuma wani
tunani takeyi.
Ranar asabar da safe yayan amadi yaseen da
kanin mahaifinsu da yayan hajiya sukaje gidansu
nadiya domin nemawa amadi aurenta, abba
baiyi doguwar magana ba yace kawai yabashi
sannan iya sadaki kawai zai kawo nan da
karshen wata mai Kamawa sai adaura aure duk
da sunyi yarjejeniyar cewar ba yanzu zata
tareba har sai yadawo daga karatunshi wanda
zai tafi zuwa London,
Batare da matsalar komai ba baki sukayi
sallama suka tafi, tunda su yaya yaseen sukace
an bashi nadiya harma an tsayar da ranar aure
ya rasa inda zai saka kanshi dan farin ciki.
Ita kuwa nadiya tana gida babu yabo babu
fallasa, tana kwance a tsakar gida da yamma
tana karatun littafin Hausa kissa ko magani yaro
yayi sallama yace wai ana kiranta awaje,
hijabinta ta dauka ta fita duk da bata san waye
yazo ba,
Gabanta ne ya yanke yafadi saboda ganin yaya
kabeer da tayi domin yau bata san da wacce
yazo ba....
*_Ummi Shatu_*
[8/23, 12:30 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
perfect writers)_
_Gaisuwar yau takice ke kad'ai STYLISH
BITCH, wanna shafin tukwicine agareki together
with Baby Rashid_
*51*
aishaummi.blogspot.com
*T*unda nadiya tafito kabeer ya zuba mata
ido yana jin wani irin sonta yana yawo acikin
jinin jikinsa, fatan shi daya Allah dai yasa ta
amincewa bukatarsa,
Yau ganinshi tayi fuska asake ba kamar wancan
lokacin da yazo ba dan haka ta dan saki
fuskarta babu yabo babu fallasa,
"Barka da fitowa.." Taji yace da ita wanda
wannan ya haifar mata da tsananin mamaki
domin bata zaci maganar kirki daga gareshi ba,
"Kina mamakine nadiya? Bai kamata kiyi
mamaki ba saboda duba da irin matsayinki da
muhimmancinki acikin rayuwata da kuma
rayuwar 'yayanmu.."
"Hakane" tafada tana kallonsa har lokacin
fuskarta tana dauke da mamaki,
"Nadiya nasake shawara, naga kamar bai
daceba in rabaki da yaranki adaidai lokacin da
suke bukatar kulawarki shiyasa ma nafasa
karbarsu zan bar miki su amma kuma ni ina
ganin yanada kyau muyiwa kanmu adalci mu
koma yadda muke ada"
"Ban fahimceka ba yaya kabeer.."
"Yawwa, nadiya abinda nakeso dake shine ni ina
ganin mai zai hana mu rufawa kanmu da
yaranmu asiri muce saki biyu nayi miki mukoma
muci gaba da rayuwarmu da bawa yaranmu
kulawa"
Wani murmushin takaici nadiya tayi sannan ta
kalleshi,
"Lallai yaya kabeer, wato dai so kake mu jefa
kanmu acikin halaka, mukoma muci gaba da
zaman zina domin ba zaman aure zamuyi ba.."
"Nadiya ba nufina kenan ba, dan Allah kiyi
hakuri ki amince da wannan bukatar tawa,bafa
wani abu bane sabo,da yawa daga cikin
ma'aurata wadanda suka samu matsala irin
tamu suna yin haka su rufawa junansu asiri su
koma suci gaba da rayuwarsu..."
"Yaya kabeer dan Allah mubar wannan maganar
domin ba mai yiyuwa bace saboda ni ahalin
yanzu ma da ranar auren wani akaina.."
Ido kabeer ya kwalalo take fuskarshi ta sauya
ya dubeta cikin tsantsar kishi,
"Yanzu nadiya kinfi son ki auri wani daban
baniba, nadiya kiyi hakuri ki yarda mu maida
aurenmu"
"Yaya kabeer idan mun ha'inci mutane da
iyayenmu mun maida aurenmu ai bamu isa mu
ha'inci Allah ba domin yasan komai, sannan
kuma nifa yanzu bana yimaka tsananin son da
har zan aikata babban sab'o.."
"Nadiya...." Yakira sunanta cikin danuwa,
"Sai anjima...."
Bata sake sauraronsa ba tayi tafiyarta ta shige
cikin gida tana mai jin tsanar kabeer tana sake
shiga cikin zuciyarta domin inbanda ma ya
rainawa kansa hankali yaushe zai tunkareta da
wannan maganar,babu wanda ta fadawa ko
mama bata fadawa ba tabar abin aranta ita
kadai.
Cikin satittikan da basu wuce 2 zuwa 3 ba
Amadi ya kammala komai nashi na tafiya
karatun da zai koma lokacin saura sati 2 daurin
aurensa da nadiya wacce har yanzu tana nan
akan dokin rigimarta bata sauko ba,
Duk da mahaifinta yace sadaki kawai amadi zai
bayar amma hakan bai hanashi niyyar yi mata
lefe ba idan taje gidanshi.
Ita kuwa nadiya tana can agida tafara shirye
shiryen komawa makaranta domin hutunsu
yakusa yakare saura kadan,ga damun da kabeer
yaketa yimata akan dole sai sun hada baki
sunce saki biyu yayi mata ba ukuba takoma
gidansa,
Ita sam bata shirin biki takeyi ba ta shirin
komawa makarantarta take,
Ana saura kwana biyar daurin auren amadi yaje
gidan da yamma, babu yabo babu fallasa ta
karbeshi, kaya yakai mata masu aji da matsayi
swiss lace da material wai ta dinka tasa ranar
biki,
Adakile tayi godiya ta karbi kayan ta koma gida
shikuma ya shiga ya debi su fadeel ya fita dasu,
mama takaiwa kayan nan mama tahau cewa,
"Ohh wannan yaro ai da kokari yake duk da abba
yace sadaki kawai zai kawo amma bai hakura
ba har saida ya kashe kudinsa ya siyo
wadannan kayan, bai san mu ba taro zamuyi ba,
aure kawai za adaura babu wanda zan gayyata,
nida sake yin taro kuma sai Allah yakaimu bikin
Amira.."
Murmushi nadiya tayi "wallahi mama nima
hakan yayi min daidai dama bana son ni aji ma
zan sake auren..."
"Allah dai yasa ayi cikin nasara"
"Amin" nadiya ta amsa tareda daukar ledar
kayan tashiga daki.
Tunda kwanakin bikin suka karato nadiya take
jin gabanta yana faduwa Wanda ko a lokacin
aurenta nafarko bataji irin haka ba, har saida ta
kasa daurewa ta fadawa mama irin faduwar
gaban da take ji nan mama tace mata tayita
addu'a insha Allah babu komai sai alkhairi.
Ranar daurin auren kuwa nadiya tana kwance
bata da niyyar tashi domin dama tace babu
abinda zatayi ko kunshi baza tayiba bare wani
kitso, dama kuma a masallacin kofar gidan
abbansu kabeer za adaura auren domin shine
waliyinta,amma tunda safe mamansu kabeer da
kannenshi suka zo gidan sannan umman
sumaila itama tazo da sauran dangi na kusa,
shiyasa gidan ya danyi mutane sai shewarsu
kakeji,
Duk da bata so sai da Amira tayi mata kunshi
domin dama ta iya babu kalar kunshin da bata
iyaba daga kan baki har zuwa ja,
Lallabata mama tayi tace ta daure tayi kitson
ma tunda dai abune na lokaci guda sannan
gashi gidan da mutane, haka ta zauna badan
taso ba Amira tayi mata kitson, shuku biyu
sannan anzubo wani tagaba wanda yabada style
mai kyau,fati kanwar yaya kabeer sai tsokanarta
take,
Wanka tayi ta shirya tasaka wani leshi golden
tasa sarka da dan kunne, karfe 2:30 amadi ya
kirata dama kuma amir yashigo yana guda yana
cewa "ina Anty amarya take? Mun dawo daga
daurin aure har andauro,sadakinki dubu 50.."
Gabanta ne yasake tsananta bugu nan ta tashi
tayi salla raka'a biyu tazauna tana addu'a,
shikuma amadi yasha kwalliya domin komai fari
yasaka, farar shadda, farin takalmi, farar hula da
Agogon azurfa, sai kiranta yake awaya saboda
yana son yazo yaganta amma bata dauka ba
gashi a can gidansu biki akeyi sosai, yayunshi
sun hada mishi dinner ta musamman a ni'ima
guest palace domin tayashi murna, duk
danginshi na uwa da na uba sunzo dan haka
gidan acike yake da baki,
Bai hakura ba yaci gaba da kiranta saboda yana
son taje dinner din amma yasan dakyar idan
zata amince, jin ta daga wayar yasashi maida
hankali kan wayar,
"Baby ina kika shigane?"
"Meya faru?"
"Babu komai, kawai dai naga inata kiranki ne
shiru bakiyi picking ba"
"Bana kusa ne"
"To shikenan, alhamdulillah yau dai gashi burina
ya cika nazama mijin nadiya, yanzu alfarma
daya zaki yimin ki shirya za azo adaukeki
saboda da akwai dinner da..."
"Wacce irin dinner? Ni ai kasan bazanje ba,
kaine saurayi dan haka zuwa kai yakama"
Murmushi yayi "yi hakuri dan Allah ki shirya.."
"Nifa babu inda zanje.."
Haka yayita rarrashinta amma taki furr tace ita
bazata jeba, katse wayar yayi ya kira amir yace
yaturo masa da number din mama, babu bata
lokaci amir ya tura masa, kiran mama amadi
yayi awaya suna gaisawa yafada mata yana son
zai turo adauki nadiya saboda akwai dinner din
da yan uwanashi suka shirya masa, sam bai
fadawa mama cewar ya kirata taki amincewa
ba,
Kiranta mama tayi tace in anjima lallai lallai
tazama cikin shiri itada Amira za azo adaukesu
zasuje dinner,da to ta amsa takoma daki tana
cije lebe gamida yin kwafa saboda jin amadi
yakai kararta wurin mama.
K'arfe 6:30 na yamma Amira tagama cancada
mata kwalliya kamar a shago kasancewar duk
irin kwalliye kwalliyen nan na zamani ta iya,
acikin kayan da ya kawo mata tasaka wani pink
din leshi ba karamin kyau tayi ba amma fuskar
nan murtuk babu fara'a ko kadan....
*_Ummi Shatu_*🏻
[8/24, 9:50 AM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
perfect writers)_
*52*
aishaummi.blogspot.com
*K*owa agidan yiwa nadiya dariya yake yi
k'asa k'asa saboda yanda ta cunbure fuska ita
adole an takura mata amma kuma ba karamin
kyau tayiba fa,
Umman sumaila ce ta shiga dakin bayan tayi
alwala,
"Haba'yarnan ki saki fuskarki mana irin wannan
shan mur haka, dan Allah ki saki fuskarki sai kifi
kyau"
Sai lokacin ta dan saki fuskarta, wayarta ce ta
fara kara nan taduba taga shine,
"Baby Ku fita anzo daukarku,yana jiranku
awaje.."
Ko amsawa bata yiba tayi yunkurin katse wayar,
"Karfa ki kashe min waya, saboda ban gama ba"
"Ina jinka.."
"Ke haka akeyi ne, sai guduna kikeyi bakya son
jin koda muryata meyasa? Yanzu fa mijinki ne
ba saurayi ba.."
"Naji" tafada tana yatsina fuska,
"To shikenan sai kunzo"
Katse wayar tayi ta tashi ta fita tana kiransu
Amira wadanda ke can dakin mama sunata
faman shiri itada aisha kanwar kabeer domin
itama tace zataje, dukkaninsu suka fito har amir
da husna walida dasu fadeela ne kawai ba aje
dasu ba, wata hadaddiyar jeep ce aka zo
daukarsu da ita wadda ta yaya yaseen ce
drivernsa ne ma yazo daukarsu,
Basu san irin gudun da drivern yayi ba saboda
kafin 8 sukaji su acikin kano tsilin,
Adaidai wani round about drivern yayi packing
saboda dama akwai wata lafiyayyiyar croutoure
black agefe tayi packing tana jiransu,
"Yawwa amarya ga motar da zakije can Ahmad
din yana ciki nikuma zan karasa da wadannan
din can wurin dinner din.."
"To, Amira zo ki rakani.." Tafada kamar wadda
take jin tsoro,
Tare da Amira suka fita zuwa wurin motar suna
karasawa amadi ya fito daga bayan motar,
"Amma kunyi sauri baby, Amira ashe kema
zakizo?"
"Yaya Ahmad ba dole ba"
"To baby ku shiga mutafi"
"Yaya Ahmad ni kaga motarmu can A'isha na
cikima tana jirana"
Bata jira komaiba ta juya ta koma motar da aka
kawosu tabar amadi da nadiya tsaye awurin,
Dan kallonta yayi, ba karamin kyau tayiba sai
dai babu annuri akan fuskarta sannan babu
wanda zai kalleta yayi tunanin ta taba yin aure
sai dai wanda yasani,
"Baby muje ko?"
Bude mata kofar mortar yayi ta shiga ta zauna
ya rufe ya zagaya daya side din shima ya shiga,
sai lokacin ta dan kalleshi har taga shigar da
yayi, milk colour din wani hadadden yadine
ajikinsa mai manyan zane marar kauri mai
tsananin haske sannan yasa hula itama milk
colour, sai zuba kamshi yake kana ganinsa babu
tambaya kasan angone,
"Baby bamu gaisa ba"
Shiru tayi masa ta dauke kanta hakan da tayi
yasashi matsawa kusa da ita,
"Haba baby yanzu kuma ai ya kamata ace ana
bani matsayina na miji, idan ina yimiki magana
ya kamata ki rinka amsa min kidaina yimin
wannan fushin..." Yakare maganar yana kai
mata wani sanyayyen kiss awuyanta domin ba
karamin kyau tayi masaba sannan yadade yana
kwadayin yin hakan agareta,
Jin bakinsa akan wuyanta yasata sake daure
fuska amma bata yi magana ba,
"Wannan yaron wai meyake nufi ne?" Tafada
acikin zuciyarta saboda jin har lokacin bata kiss
yake asassan wuyanta,
"Baby..." Yakira sunata cikin tsokana,
"Uhmmm"
"Kinyi kyau wallahi sosai kamar kada nabarki ki
koma gida, ko zaki zauna.."
"A ina? Ai ba haka mukayi dakai ba"
Murmushi yayi ya kamo hannunta, "to ai basai
munyi haka dakeba, ra'ayinane.."
Bata sake yimasa magana ba tayi shiru abinta
saboda taga fitina yakeji da ita wayaga sabon
shiga dama kuma tasan dole haka tafaru tunda
shi ba taba yin auren yayiba,
Har sukaje wurin dinner din yana rike da
hannunta, dakanshi ya fita ya bude mata kofa ta
fito suka shiga ciki wanda tun daga waje masu
camera suka fara haskasu.
Sai yau nadiya ta tabbatar da cewar amadi
cikakken dan gatane agidansu, suma yayun
nashi dukkaninsu sai da sukayi mamakin ganin
nadiya domin basu zaci zasu ganta hakaba
tunda sunji yace ta haihu har yara biyu duk
azatonsu zasu ganta ta tsofe amma sai sukaga
sabanin haka anan dukkkaninsu suka yaba da
zabin nasa,
"Lallai anty amadi dole arude ace aure akeso.."
Inji anty hamida,
"Kedai kibar yaron nan kina ganinshi silent.."
Anty Dija ta fada tana dariya,
"Gaskiya yayi zabe, matarshi kyakkyawa da ita
wallahi amma kuma zanga yanda zasu kwashe
da zee kanwar dad din su jawahir.." Anty siyama
ta karbi zancen,
"Bata san yayi aure bane?" Anty hamida ta
tambaya,
"Wallahi bata saniba, ai kin fada mata nayi
saboda ba karamin aikinta bane kiganta ta hado
kayanta ta taho domin tana sonshi wlhi kuma
koni naso ace ya aureta.."
"Ai autan hajiyanne kalar asararru da sakalai
gareshi badan hakaba ai da zai iya yin mata
biyu.." Inji anty Dija,
"Wallahi fa, ai bazai iyaba.." Inji anty siyama,
hirar tasuce ta katse sakamakon kiran dangin
ango da akayi zuwa cikin filin, nan suka fiffita
kowaccensu tana sanye da swiss lace maroon
wanda sukayi iri daya sunsha head baki,
Hannun nadiya amadi ya kama ya rike yana
murzawa ahankali,
"Wadancan duk yayuna ne baby uwar mu daya
ubanmu daya, kinga waccen wadda ke rike da
babyn itace babba sunanta anty Jidda ta kusa
da ita kuma anty siyama ita ke binta dayar
kuma ita nake bi sunanta anty hamida.."
"Allah sarki.." Tafada ahankali saboda gaba
daya jikinta yagama yin sanyi haka kawai,
"Ko bakya jin dadi?" Ya tambayeta yana shafa
hannunta,
"Ikon Allah, wai meye haka?" Tafada tana
kallonsa,
"Allah yabaki hakuri, nadaina" tashi yayi yafita
zuwa wurinsu anty Dija yahau yimusu ruwan
nairori,
Koda aka kira ango da amarya dakyar yasha
kanta ta yarda suka fita tsakiyar filin, daga ita
harshi babu Wanda ya taka tsayawa kawai
sukayi, kallonta yake tayi k'asa k'asa yana jin
sonta na karuwa acikin zuciyarshi.
K'arfe 10 aka tashi daga dinner din, hannunta
yakama suka fita bayan tagaisa da yan uwanshi,
mota ya bude mata shima yazaga ya shiga ya
zauna tareda matsawa kusa da ita,
"Wai menene haka?" Tafada tana ciccin magani,
"A ina? Kodan na matso kusa dake?" Ya
tambayeta yana murmushi,shiru tayi masa ta
dauke kanta ta rabu dashi, kamar dazu yanzu
ma haka ya dameta da kiss, gaba daya ya
takurawa wuyanta da hannunta,
"Wayaga ba sabinba" tafada acikin zuciyarta,
har sukaje round about din da aka sauketa dazu
yana manne da ita,
"Baby ai ba yau zaki tafiba ke"
"Saboda me? Wallahi tafiya zanyi tunda
bancewa mama zan kwana ba"
"To shikenan zaki tafi, kin yarda gobe inzo?"
"Um um" ta bashi amsa,kiss yakaiwa bakinta
nan yagogi jan bakin dake kan lips dinta bai
saniba,
"Daga yanzu indai muna tare nayi miki magana
kika ki amsawa haka zan rinka yimiki idan kuma
awaya ne to zan barki da Allah.."
"Nifa gida nake son tafiya.." Tun kafin ta rufe
bakinta jeep din dazu tayi packing agaba dasu,
"To ai gashi nan yazo, zaki tafi yanzu kiyi hakuri
ba cinyeki zanyi ba.. Kinji..."
Ganin yana shirin kaiwa bakinta kiss yasata
fadin "naji" amma duk da haka bai fasaba sai da
yayi kissing dinta abaki son ranshi,
Har motar dasu Amira ke ciki ya rakata sai da
yaga tafiyarsu sannan ya koma motar da yake,
gaba daya yanayin yau na musamman ne
awurinsa lallai aure babbar ni'ima ce ba kadan
ba,
Yana shiga gida su anty siyama ma na shigowa
kasancewar akwai haske sosai yasa suka ga jan
bakin dake bakinshi wanda ya goga a lips din
nadiya,
"Anty amadi meye abakinka?" Anty siyama ta
tambayeshi tana yimasa dariya,
"Ni kuma?" Yafada yana kallonta,
Dariya yaga sun saka gaba dayansu sunyi gaba
hakan yasa ya tsargu, dakinsa ya shiga yaje
gaban mirror ya kalli fuskarshi nan yaga
bakinshi dama dama da jan bakin nadiya,
Murmushi yayi ya zaro wayarshi daga cikin
aljihunsa yafara kiranta.........
*_Ummi Shatu_*
[8/26, 3:14 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert &
perfect writers_
_Fatan alkhairi ga Maman Samha, zee gajouh,
Maman humy, firdaus, pheey,Maman haneef,
Maman Fati,da duk wani masoyin Amadi &
Nadiya.._
_Gaisuwa ga aminiya maryam qaumi, u are
always in my mind...._
*53*
aishaummi.blogspot.com
*L*okacin da ya kirata suna hanya dan haka
taki dagawa, cigaba da kiranta yayi harta dauka
amma fa ba don ta so ba,
"Baby shine kika b'ata min bakina da jan bakinki
ko?..".
Abinda taji yafada kenan cikin muryarshi mai
sanyi domin amadi ko kadan bashida zafi
shiyasa muryarsa take sanyi kalau,
"Uhmmm baby.." Taji yasake magana,
"Ban gane abinda kake nufi ba.." Tabashi amsa,
"Kin gane mana, kuma nasan kin gani kawai
rabuwa kikayi dani nashiga cikin mutane
ahaka.."
"Wai me?" Ta tambayeshi,
"Jan bakinki da kika goga min abakina.."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi magana acikin
zuciyarta, "nagoga maka kodai ka goga.."
"Nidai nan gaba idan kin goga min dan Allah ki
rinka goge min karki barni na fita ahaka ko
kuma ma ki daina shafawa gaba daya..."
"Saboda...?" Ta tambayeshi cike da gajiya da
yin maganar,
"Saboda indai muna kusa bakinki zai sha
tsotsa.."
"To sai da safe.." Tace dashi tana hararar shi ta
cikin wayar kamar yana ganinta,
"Ai ban sallameki ba, wallahi karki kashe idan
kika kashe kuma.."
"Kuma me?"
"Nabarki da Allah tunda kinki jin maganata.."
Fasa kashewa wayar tayi ta jingina kanta da
jikin kujera tana sauraronsa bawai don tana son
hirar ba sai dan babu yadda zatayi,
"Baby kiyi min alfarma guda daya ki yarda gobe
nazo naganki"
"Yau ba gashi ka ganni ba..?"
"Ai ganin da nayi miki yau bai isheni ba shiyasa
nake son sake ganinki gobe.."
"To gaskiya nidai ba sai kazo ba"
Murmushi yayi ya zauna abakin gadonshi,
"Yanzu baby ko nauyin fadar Kalmar bakiji ba?
Cewa fa kikayi basai nazoba, nikuma ina son
nazo saboda ina son ganin matata..."
Shiru tayi hakan yasashi sake yin magana, "idan
nasake yimiki magana kika rabu dani keda
Allah.."
"To wai dan Allah me kakeso ince maka ne? Ni
agajiye nake ko gida fa bamu jeba muna
hanya.."
"To ai laifinki ne tunda sai da nace ki zauna ki
kwana amma kika ki furr kikace ke tafiya
zakiyi.."
Shiru tayi batayi magana ba, jin taki yin magana
yasashi fadin,
"To yanzu so kike inbarki sai kinje gida?"
"Uhmmm"
"To shikenan zan barki amma da sharadi.."
"Name?" Tafada agajiye domin tagaji da yin
maganar ma,
"Gobe zanzo naganki.."
"Naji" tabashi amsa amma acikin zuciyarta cewa
take "zaka zo ka dameni dai malam ina zaman
zamana"
"To shikenan sai goben, Allah yakaiku gida
lafiya"
"Amin.." Tafada tana mai alla alla da taji
yakashe wayar amma bai kasheba kun san
mutumin naku da d'an karen naci,
"Sai anjima..?" Taji ya tambayeta,
"Uhmmmm"
"To sai anjima, i love you....!"
"Uhmmmm" shine kawai abinda tafada, jinshi
tayi yabata wani kiss na musamman ta cikin
wayar sannan yakashe,
"Ikon Allah.." Tafada ahankali bayan ta cire
wayar daga kunnenta. Basu suka karasa gida ba
sai 11:30 lokacin harsu mama sun kwanta,
In banda yunwa babu abinda takeji nan taje tayi
alwala tayi salla tana idarwa ta zubo abinci taci,
ko kayan jikinta bata cireba ta kwanta saboda
tsabar gajiyar da ta kwaso,
Washe gari umman sumaila ta tafi haka suma
su A'isha kannen kabeer sun tafi shiyasa yanzu
gidan babu kowa sai su yasu,
Fitowar nadiya kenan daga wanka tafara jiyo
maganganu atsakar gida, hijabi tasa ta fita nan
taga yaya kabeer zaune ra'as yanata faman
gursheken kuka agaban mama, mama sai hakuri
take bashi akan yadaina wannan kukan,
"Mama dole inyi kuka tunda har narabu da
nadiya, ashe nadiya zata iya auren wani mijin
baniba? Ashe aure aka daura mata jiya? Ni
najawowa kaina amma har yanzu ina son nadiya
wallahi, ina kaunarta, dan Allah mama ki
taimaka min nadiya tadawo gareni.." Yafada
yana kuka kamar ba namiji ba,
"Kayi hakuri kabeeru kadaina kuka, ka dauki
kaddara, haka Allah ya zabar muku kasan kowa
da iri tasa kaddarar, kayi hakuri kaci gaba da
addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.."
Mama tafada jikinta asanyaye,
"Mama wallahi rabuwa da nadiya bashine
alkhairi ba arayuwata.."
"A'a kabeer ya isa karka yi sab'o kayi hakuri
kayi shiru"
Ita dai nadiya tsayawa tayi kawai tana ganin
ikon Allah,ganin kabeer ya kura mata ido yana
kallonta yasata saurin juyawa takoma daki
saboda yanzu ita matar wanice gashi daga
wanka tafito, bata san yanda suka kwashe ba
tadai jiyo gidan yayi shiru alamun ya tafi, ko
tausayinsa bataji ba domin tasan abin da zaisa
taji tausayinshi yana gaba lokacin da duniya tayi
masa atishawar k'uda.
Shiryawa tayi cikin wata shadda ja mai
mutukar tsada in banda maiko babu abinda
takeyi, kwalliya ta danyi sama sama tasha
turare ta fito tana kokarin daura dan kwali anan
mama take sanar da ita wai kabeer ya dauki
fadeel da fadeela yatafi dasu sai yamma zai
kawosu,
"Damuwarsa.." Tafada acikin ranta amma afili
sai ta amsawa mama da to,dakin Abba ta shiga
ta gaisheshi, bayan sun gaisa ya dauko mata
kudin sadakinta yabata yace gashi nan hakkinta
ne, rasa me zatace tayi saboda idan ta karba
bata san abinda zatayi dashi ba daga karshe dai
tacewa Abba ya ajiye mata awurinshi.
Amadi bai samu zuwa da wuriba saboda yana
can gida anata biki domin sai yau bikin yakare
baki duk sun tattafi amma yayunshi duk suna
nan babu wadda yatafi,
Karfe 2 yasamu ya karasa gidansu nadiya koda
ya kirata awaya ma sai da tagama jan ajinta
sannan ta dauka duk da yanzu ma taji tarage jin
haushinsa acikin zuciyarta, cewa tayi ya shigo
lokacin da yace mata yakaraso,
"Dakinki zan shigo?" Yafada cikin zolaya,
"A'a kamanta kan gadona zaka zo.." Tana gama
fadin haka ta kashe wayar, dariya yayi yafita
daga cikin motarsa ya rufe ya shiga cikin gidan,
yau tsakaninshi da mama 'yar surukunta sukayi
dan dakyar ya iya gaisheta tareda yimata godiya
daga nan yatashi ya shiga falon baki ya zauna,
wayarshi ya zaro ya shiga Facebook yana duba
sakonnin taya murnar da friends dinshi suka
turo masa na auren da yayi, husna ce ta kawo
masa ruwa da abinci da lemo,
Yana nan zaune gimbiyar tasa ta shigo sai
faman kamshi take budadawa gashi shaddar
jikinta ba karamin kyau tayi mata sannan skirt
din ta bayyanar da hips dinta sosai kasancewar
dinkin riga da skirt ne,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna suka
gaisa daga nan tayi shiru bata kara magana ba,
"Baby zo muga kunshin naki..." Yafada yana
kallonta,
"Wanne kunshi kuma? Tun jiya bakaga kunshin
nawaba sai yau" ta bashi amsa tana latsa
wayarta, bai kuma yin magana ba ya rabuda ita
yaci gaba da kallonta, ita kuma tanata faman
latsa wayarta,
Tashi tayi taje ta zuba masa abincin, faten doya
sannan ta tsiyaya masa juice,juyawa tayi zataje
ta zauna ya kirata,
"Baby zo"
Kasa yimasa musu tayi saboda ayanda yayi
maganar babu alamun wasa, kamar kazar da
kwai ya fashewa aciki haka ta karasa tana zuwa
yasa kafarshi ya hardota jikinshi,
Akanshi ta fada yasa kafa ya hardeta ta yadda
bazata iya tashiba,
"Shine nace kizo naga kunshin naki kika ki zuwa
ko? Uhmmm?"
Ita gaba dayama tarasa me zatayi kunya ko
haushi? Shiru tayi taki amsa masa, hannayenta
duka biyu yakamo yana jujjuyasu cikin nashi
yana kallon kunshin, kamar zata saka kuka dan
takaici,
Bata gama wannan bacin ranba taji ya zame
dan kwalin kanta,
"Wowwww, baby kitsonki yayi kyau, waye yayi
miki?" Yafada yana shafa kitson, hancinshi yakai
bisa kitson yana shakar kanshin man kitson
dake tashi akan nata,
"Baby ashe dai kema kinada gashi, wowwww..!"
Shiru tayi kawai tana jinsa sai tafiyar tsutsa
yake yimata akanta wai shi ala dole shafawa
yake,
"Baby waye yayi miki kitson?"
Shuru tasake yi,
"Idan har baki amsa ba keda Allah.."
Jin yahadata da Allah yasata amsawa, "Amira
ce.."
"Gaskiya dole nabawa Amira tukwici saboda ta
fito min da ke sosai, ji kunshinki ma yanda yayi
kyau..." Yakarasa maganar yana shafar
hannayenta,
Rungumeta yayi gaba daya acikin jikinshi nan
kuma tace bata san zance ba tafara yimasa
mutsu mutsu,
"Allah idan kika tashi ban yafe ba.."
Komawa tayi ta lafe ajikinsa tana turo baki,
"Ai da sai kace min damuna zaka zo kayi,
shiyasa dama ka matsa sai nabarka kazo.."
Ko amsata baiyi ba saboda ya tafi wani uzurin
daban a wuyanta,
"Wallahi Ahmad dinnan bashida kunya ashe ana
ganinsa haka.." Tafada acikin ranta saboda ita
dai arayuwar aurenta na baya bata san wani abu
waishi soyayya ba amma shi wannan gashi daga
jiya da aka daura musu aure zuwa yau yana
nuna mata kauna kamar zai hadiyeta.
Babu yanda ta iya haka taci gaba da zama
ajikinsa har yagama fitinarsa, juice ya tsiyaya
yasha tareda jan jelar kitsonta, hade fuska tayi
ta kalleshi nan suka hada ido fessss taji ya fesa
mata juice din bakinshi afuskarta,
"Kai, kai.." Tafada cikin masifa,
"Allah yabaki hakuri.." Yace da ita sannan yafara
goge mata da hannunshi.......
_Jinjina ga babbar yaya mom minal..._
_*Ummi Shatu*_
[8/28, 10:48 AM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Gaisuwa mai tarin yawa ga sadeeya sunusi
umar (antyn hafsat), this page is for you..._
*54*
aishaummi.blogspot.com
*H*ad'e fuska tayi taki koda sake kallonshi
ne, ahankali yake share mata fuskarta da tafin
hannunshi yana murmushi saboda ganin yanda
ta daure fuska tasha kunu,
"Irin wannan shan kunu haka baby, Allah yabaki
hakuri bazan sake ba.."
Bata bashi amsaba tayi shiru abinta amma
fuskar nan murtuk take, koda ya kammala goge
mata fuskar tata kin sakinta tatashi yayi nan ya
sake hadata da jikinshi tsamtsam.
Sun dade ahaka har sai da yaji an kira salla
sannan ya dago kanta yana kallon fuskarta,
"Baby kinji ana kiran salla.."
Kamar dazu yanzun ma shiru tayi masa har
saida yasake maimaitawa,
"Naji"
"To tashi nayi alwala muyi sallah ko..?"
Dama kamar jira take dan haka cikin hanzari ta
tashi daga jikinshi ta dauki mayafinta da dan
kwalinta tana kokarin daurawa,
"Ina zakije ne?" Ya tambayeta,
"Ciki zan shiga inyi salla" tafada fuska abace,
"Tsaya tare ai zamuyi.."
Dayake akwai bathroom acikin falon nan ya
shiga yayi alwala yafito, idonshi akanta fuskar
nan tashi sai murmushi ketashi ajikinta,
"Baby nafito shiga kiyi alwalar.." Tana jinshi
amma tayi masa shiru nan yasake maimaitawa
amma bata kulaba,
Matsawa yayi gabanta yana balle maballin
hannun rigarshi,
"Baby..., baki jina ne? Nace kema kije kiyi
alwalar sai muyi sallar tare, yau ina son inyi
salla da iyalina ne.."
"Banayi.." Tafada batare data kalleshi ba,
murmushi yayi ya sunkuya asaitin fuskarta
bayan ya dafa gwiwowinshi,
"Baby kenan, wallahi lada zaki samu indai kikayi
salla tareda mijinki, ni nasan abinda kika fada
ba gaskiya bane dan haka ki tashi.."
"Me zanyi idan natashi? Ba na rigada nafada
maka ba, ko ahaka zanyi sallar.."
"A'a....." Yafada tareda mikewa tsaye,
"Idan har ba dagaske kike ba kije keda Allah.."
Sororo tayi tana kallonshi saboda jin abinda
yafada,
"Wai komai sai kayi min Allah ya isa? Wannan
wanne irin abune?" Ta fada cikin jin haushi,
"Ehh nasan hakanne kadai zaisa ki rinka bin
umarni na saboda kin rainani, bakya sona bakya
kaunata, tunda bakya sona kuwa nasan bazaki
rinka yimin abinda nake so ba.."
Jin yace yabarta da Allah yasata tashi ta shiga
toilet, nan ya zauna yana jiran fitowarta amma
dama tun lokacin da tayi maganar yasan cewa
badagaske takeba,
Kamar zata fashe dan bacin rai haka tafito,
shikam murmushi kawai yake, sallah yajasu ta
la'asar raka'a hudu, yana yin sallama ta tashi ta
koma can gefe taci gaba da addu'o'inta.
Tashi yayi yana gyara agogon hannunshi yana
kallonta yanda taci magani ta bata fuska,
"Baby zanje na tafi.., wai ina twins ne banji
motsinsu ba ko zunje school ne?"
"Abbansu ne yazo ya daukesu sai anjima zai
dawo dasu.."
Kai yagirgiza "ina fata dai bai kalle min fuskar
matata ba..?"
Sanin bazata amsa ba yasashi saka takalminshi
ya nufeta, mikewa tayi tana gyara mayafinta,
Hannunta taji ya kama, "muje to ki rakani
intafi.."
Batace komai ba yajata suka fara tafiya, dakin
mama taje ta sanar da ita zai tafi nan mama
tafito suka yi sallama, su Amira kuma basa nan
sun fita itada husna walimar wasu kawayensu
da sukayi saukar alkur'ani mai girma,
Yana ganin mama ta juya daki ya kama
hannunta yana kallon fuskarta,
"Muje ki kaini mota sai ki dawo..."
Tafiya sukayi suna zuwa daf da soro sai ga
fadeela da fadeel da abbansu yana rikeda
hannuwansu, ganin kabeer baisa amadi yasaki
nadiya ba dan haka kabeer ya harzuka ya cika
dam, su fadeela na son zuwa wurin amadi
amma haka ya hanasu furr ya kada kan yaranshi
zuwa cikin gida,
Ita kanta nadiya da ba wai son amadi takeba
saida abin yayi mata ciwo saboda tasan ya
shaku da yaran gashi ko yanzu ma kafin ya fito
sai da ya tambayesu,
Ji tayi ya matsa hannunta tareda tsayawa a
cikin soron,
"Nima idan kin tashi haifa min yara twins nake
so kamar su fadeela.."
Yace da ita bayan ya jinginata da jikin bango ya
kama dukkan hannayenta ya rike,
"Ai ba nice mai...."
"Shhhhhhht..." Ya katseta bayan ya dora dan
yatsanshi akan lips dinta,
"Insha Allah nima twins zamu haifa.."
Bata kai ga yin magana ba suka jiyo alamun
takun tafiyar kabeer, dama amadi yana son ya
rama abinda yayi masa yanzu dan haka yayi
gaggawar zira hannunshi ta kugunta ya
rungumeta, kokarin zamewa tafara yi,
"Baby idan kika gudu wallahi bazan yafe miki
ba..." Ya rada mata acikin kunne, daidai lokacin
kabeer din ya fito, ganinsu haka suna bawa
soyayya hakkinta yasa kishinsa motsawa,
Ko kallonsa amadi baiyi ba,
"Wai dan Allah meyasa kake yimin haka..?" Tace
dashi ahankali kamar mai yin rada,
"Saboda ina sonki baby..." Yabata amsa bayan
ya kai bakinshi jikin kunnenta,
Karshen bakin ciki kabeer yajishi saboda yasan
da biyu suka yi masa haka, sunyi ne domin su
kona masa rai kuma gashi sunyi nasara,ganin
nadiya da amadi ahaka shine gani mafi muni
agareshi,
Cikin hanzari yawuce su ya fita daga soron
zuciyarsa tana suya tareda tuno masa da
wacece nadiya acikin jerin mata.
Duk da kabeer ya fice baiza amadi ya saketa
ba sun dade atsaye acikin soron domin sam
baya son tafiya yabarta dan dai babu yanda
zaiyi ne,
Har bakin motarshi yajata yabude ya shiga
sannan ya kalleta yana rikeda hannunta,
"Baby sai nadawo ko?"
"Uhm" ta amsa masa ciki ciki,murmushi yayi
yasaki hannunta bayan ya sumbaceshi,
"Agaida twins dina sai kinjini.."
"Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda juyawa ta
nufi cikin gida, ta mirror ya kurawa hips dinta
ido yana kallonta har ta shige ji yayi yana kishin
wasu mazan su ganta shiyasa ya kuduri niyyar
hanata saka mayafi.
Cike da kaunarta yatafi, koda yaje gida ma kasa
samun sukuni yayi har saida ya kirata yaji
muryarta, tun daga ranar kullum idan ya kirata
yace zai zo sai tace a'a, lokacin da ta gama
shirin tafiya makaranta ma yace zai zo ya kaita
shopping tace ita dai a'a, yace zaizo ya kaita
makarantar nanma tace a'a,
Hak'ura yayi ya tura mata 50 thousands ta
account dinta yace gashi nan ta siyi duk abinda
take bukata dama ya rigada yayi mata
registration tun tuni,
Ranar monday da safe ta shirya ta tafi, koda
yaushe amadi cikin kiranta yake da yimata text,
shi dinma yana can yanata shirye shiryen tafiyar
da zaiyi.
***
Cikeda damuwa kabeer yabar kofar gidansu
nadiya ya tasamma gidansa,
Lokacin da ya shiga gidan asabe mc na daki
itada kawarta Lola suna tattaunawa akan
kabeer,
"Ni matsalata dashi yanzu tunda ya rabu da
matar nan tasa abubuwansa suka dagule, yanzu
maganar da nake yimiki hankalinsa yafara
komawa kan yaransa domin dazu dazun nan sai
gashi yazo min dasu..."
"Wannan duk mai sauki ne mc, yanzu dai
maganin dukan da yake yi miki nake so muyi
sannan kuma malam mai dogon zamani yace
inyi miki albishir da cewa da zarar ya ketara
wannan abun da zaki ajiye akofar daki shikenan
kin gama dashi sai yanda kika juyashi..."
"Lola naji dadin wannan batu to amma duk ba
wannan ba, kudinsa fa yanzu basa shiga
hannuna.."
"Mc kenan ai duk wannan mai saukine da zarar
kin fara juyashi shikenan sai yanda kikayi da
dukiyarsa.., amma ni menene kasona aciki?"
"Babu bukatar kiyi gaggawa wajen jin kasonki
lola domin kinada kaso mai tsoka.... Kinji ma
kamar yadawo"
Mikewa lola tayi ta leka window nan kuwa taga
kabeer dinne, mayafinta ta saba da jakarta
asabe ta rakata ta kofar baya ta fita bayan ta
ajiye wani dan siririn bakin abu kamar gashi
akofar dakinta......
***
Satin nadiya daya da komawa makaranta amadi
yaje amma shi akwai abinda ya kaishi, tunda ya
shiga makarantar yayi mata waya tace lecture
zata shiga, sai 2 tagama lectures dinta sannan
ta nufi office dinsa yana zaune ya dora
kafafuwanshi bisa table dinshi, da sallama
abakinta ta shiga, ansawa yayi ya dago yana
kallonta,
"Baby sai yanzu?"
"Uhmmm"
Murmushi yayi "nima har yanzu kinga ban samu
na kammala ba kuma inajin gobe ne tafiyata
fa.."
"Allah sarki..." Tafada batare da ta kalleshi ba,
"Meyasa kika yafa mayafi bayan riga da skirt ne
ajikinki..?" Ya tambayeta bayan ya kura mata
ido, shiru tayi bata amsa ba,
"Ko kina so ne wasu mazan su rinka kalle min
halittarki? Dan Allah kidaina saka mayafi.."
"Naji..."
Shine amsar da ta bashi, ta dan jima a office din
amma kusan shi kadai yake zancenshi saboda
sai yayi magana uku kafin tayi guda daya, daga
karshe ta tashi ta tafi hostel, girki tayi masa
farar taliya da miyar danyen kifi, sai da tayi
wanka ta sake kwalliya ta saka wasu english
wears riga da skirt bakake sannan ta dauki
abincin ta fita bayan ta saka babban hijabi ash
colour....
_*Ummi Shatu*_🏻
[8/29, 8:21 AM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert &
perfect writers_
*55*
aishaummi.blogspot.com
*L*okacin da ta shiga office din nashi baya
ciki da alama ya dan fita,
Wuri ta samu ta zauna tana kallon yanayin
office din nashi,
Tashi tayi taje ta leka ta window nan dinma
babu alamun tahowarshi hakan yasa tasake
komawa ta zauna tana jiranshi,
Jin zaman ya isheta ita kadai yasata daukar
phone dinta ta kira mama suka gaisa ta hadata
da fadeel suka fara hira,
Tana cikin yin wayar amadi ya shigo shima
wayar yake yi amma shi da hajiyarshi yake
wayar saboda taji yana cewa,
"Hajiya may be fa ni anan ma zan kwana
saboda har yanzu ban gama dasu ba wallahi..."
Bata san me hajiyan tace ba tadai ji yace,
"Ehhh Gata yanzu ma muna tare bari na bata ku
gaisa.."
Kashe tata wayar tayi shi kuma ya matsa kan
kujerar dake kusa da wacce nadiya ke zaune ya
zauna tareda kai wayar jikin kunnenta, karba
tayi ta makala a kunnenta,
Sake matsawa yayi sosai da kujerar shi kusa da
tata dama kuma kujerun suna facing juna, gaba
daya kafafuwanshi da gwiwowinshi manne suke
da nata, tsareta yayi da ido yana kallonta
saboda yadda ta saki jiki sosai suna gaisawa da
hajiyarshi,
Mika mishi wayar tayi bayan sunyi sallama da
hajiya nan ya hada da hannunta ya saka wayar
a kunnenshi, basu wani jima suna magana ba ya
cire wayar daga kunnenshi har lokacin yana rike
da hannunta,
"Me kika kawo min baby..?" Ya tambayeta yana
kallonta,
"Abinci ne.." Ta fada fuskarta babu yabo ba
fallasa,
"Me kika dafa min?"
Sauke idonta tayi a kasa bata bashi amsaba
haka kuma bata bari sun hada ido ba,
"Ni ai baby nafi son..." Kiss ya kai mata akan
lips dinta ya dago yana murmushi,
"Kinci abincin ke?"
Kai ta daga masa, "no ban yarda ba Allah sai
dai muci tare.." Yayi magana cikin shagwaba irin
tasu ta yan auta,
Shiru kawai tayi tana jinshi irin yanda yake yi
mata shagwaba da sauran abubuwa kamar wani
karamin yaro,
Sai da ya sake sumbatarta a kumatu sannan ya
mike yaje wurinda ta ajiye masa abincin a
saman fridge,
"Baby ina zuwa.."
Fita taga yayi, bai jimaba sai gashi ya shigo
rikeda babbar dadduma, shimfidata yayi ya
sauke abincin ya dora akai sannan yaje ya riko
hannunta,
"Tashi muje muci abincin.."
"Nifa na koshi.."
"Allah tare zamuci bazan ci ni daya ba.."
Tashi tayi tabishi har zuwa kan carpet din, zama
tayi shima ya zauna yana facing dinta,
"Tun kafin naci abincin naji kamshinshi ya cika
min ciki, baby kin iya girki sosai.."
Ita dai bata yi magana ba ta bude abincin ta
saka miya ta dauki spoon tafara juyashi,
Kallonta yake yi ganin ta dan tsakuro zata kai
bakinta yasashi saurin kamo hannunta tare da
sauya akalar spoon din zuwa bakinshi,
"Wai wai... Baby wannan abincin da kifin kan
tudu kikayi amma ba da kifin ruwa ba saboda
naji dadinsa yayi yawa.."
Duk da bata son tayi dariya sai da yasata yau ta
dan dara akaro nafarko da yaga tayi murmushi
har hakoranta sun bayyana kuma wai shine silar
sata dariyar, ba karamin dadi yaji ba ganin ta
dan murmusa,
"Dan kara bani inji.." Yafada yana langab'ar da
kai, kamar bata jiba tayi,
"Baby kibani nace... Ko sai nabarki da Allah zaki
bani?"
D'iba tayi ta kai bakinshi nan ya debi rabi ya sa
mata rabi abaki,
"Yawwa baby ai haka akeyi, kibani inbaki kinji...
Uhm babyn amadi..."
Babu yadda ta iya haka taci gaba da diban
abincin tana bashi idan tasa mishi abaki sai ya
ci rabi ya bata guntun, tasan idan bata bashi ba
yanzun nan zai cemata yabarta da Allah ita
kuma bata son Allah yayi fushi da ita akan ta
sabawa mijinta,
Taliyar bakinta ce ta nemi zubowa saboda
yunkurin magana da tayi sakamakon babban
dan yatsanta da taji yaja, ta bude baki kenan
taliyar da ya sa mata ta taho,bakinshi yakai kan
nata,
"Baby rigimammiya idan kika b'ata min darduma
ta sai kin wanke min.."
"Ni tashi ma zanyi tunda dama na k'oshi.."
"To ai ni ban koshi ba dan haka ba zaki tashi
ba.."
Haka ya hanata tashi taci gaba da bashi abincin
yana ci, yaya kabeer ta tuno shi sam bai taba
cin abinci tareda ita ba duk lokacin da ta jirashi
ma inyazo masifa zai tisata agaba yanayi.
Dan mugunta haka tayita tura mishi abincin
yana ci har sai da ya cinyeshi tsaf ai kuwa ba
karamin mugun koshi yayiba shi kansa jin
cikinsa yake yayi masa nauyi,
"Baby akwai juice a fridge idan zaki sha.."
Tashi tayi ta dauko ta cika cup ta mika mishi,
"Baby wallahi na koshi da yawa.."
"Ai kuwa sai kasha.."
Karba yayi ya dan kurba ya fara bata a baki
tasha,
"Washhhh, baby bazan iya tashi ba kamani in
tashi.."
Dakyar ta iya dagashi ya mike tsaye, "gaskiya
nayi over feeding... Zo kiji"
Matsawa tayi batare da ta kalleshi ba,
"Rufe office din kizo kiji.."
Saida gabanta yafadi saboda bata san nufinshi
ba,
"Rufe mana.."
Zuwa tayi ta rufe ta dawo, sunkuyawa yayi,
"Cire hijabinki in goya ki inyi exercise,wallahi na
koshi da yawa dakyar nake motsi..."
Tsayawa tayi sororo tana kallonsa saboda jin
abinda yace,
"Dan Allah baby cire kizo ki hau..."
"Kayi tsalle kawai.."
"Wallahi baki isaba bayan kece kika dura min
abincin.."
"Nidai gaskiya a'a.." Tafada tana daure fuska,
"Wallahi sai kin hau idan kuma baki hau ba kije
keda Allah"
Zunbura baki tayi ta kama hijabinta ta cire ta
ajiye,
"Ni kayi min tudu ka sunkuya sosai.." Tafada
tana turo baki,
Tsugunnawa yayi, "to zoki hau.."
Cikeda bacin rai ta tattare skirt din jikinta ta
dale gadon bayanshi, mikewa yayi yafara kai
kawo acikin office din, jin taki rikeshi yasashi yin
baya kamar zai kada ita babu shiri ta
rungumeshi sosai,
"Baby ashe dai kinada tsoro gashi bakida nauyi
da yawa... Nauyinki nawa ne?"
"Nima ban saniba.."
"To baki fi 50 ba gaskiya, jifa yanda kike shafal
dake duk kibar nan taki..."
Ita dai bata kara maganaba tana kwance a
bayanshi tana shakar kamshin turaren black
man dake tashi daga jikinsa,
Ya dade yana zagaya cikin office din da ita
abayanshi sannan ya direta,
"Baby sauko haka nagaji...."
Juyawa yayi yana kallonta, kayan jikinta sunyi
mutukar kamata sannan sunyi mata kyau
kasancewar roba ne,
Kan kujerarshi yaje ya zauna ita kuma ta dauki
hijabinta ta saka, drewar ya bude ya dauko
chewing gum ya dauki daya ya mika mata
sauran,
"Ashe ma inada chewing gum namanta.."
Kwanukanta ta tattara ta nade mishi
dardumarshi ta ajiye,
"Bari natafi, idan ka tafi shikenan Allah ya kiyaye
hanya.."
Kallonta yayi yana murmushi,
"Wai kina nufin sallamar kenan? Lallai, to
shikenan sai anjima...."
Fita tayi shima yabi bayanta ya rufe office dinshi
yayi wani wurin.
Bata sake jin duriyarshi ba sai bayan sallar
isha wurin karfe 8 yakirata wai tazo yana jiranta,
"Wai dama bai tafiba?" Ta tambayi kanta,
hijabinta kawai tasa ta fita, akusa da library ta
sameshi yana tsaye ajikin motarshi,
"Baby zuwa nayi na daukeki muje ki tayani
kwana, anan garin zan kwana yau saboda ban
gama abinda nazo yi ba sai gobe da safe.."
Saida ta daure fuska ta hade rai sannan tace,
"Gaskiya kayi hakuri ni babu inda zan bika"
"Haba baby, dan Allah kizo muje.."
"Kasan Allah babu inda zanje.."
"Amma dai baby idan kika barni naje na kwana
ni daya baki yimin adalci ba, iya yaune fa kurum
zaki rakani.."
"Zancen kake so, nidai ko nan da gate ban
binka.."
Bai sake magana ba taga ya ciro wayarshi daga
cikin mota ashe mama zai kira kawai sai jinshi
tayi yana cewa,
"Lafiya lau mama dama nadiya ce nace ta
rakani unguwa shine tace sai kin amince.. Gata"
Mika mata wayar yayi yana murmushi, nan ta
karba,
"Mama..."
"Ke nadiya haka akeyi dan mijinki yace ki
rakashi wani wuri shine zakice sai na amince ba
yafini iko dake ba yanzu, maza kije ki rakashi
karki sake cewa sai an tambayeni..."
"To mama..."
Mika mishi wayar tayi tana kallonshi cikin bacin
rai, haushinta daya ko wanka fa batayi ba kayan
dazu ne ma ajikinta,
Ko kulashi bata yiba ta zagaya daya side din ta
bude ta shiga fuskarta adaure,
Murmushi yayi ya shiga ya zauna yana kallonta
tareda yiwa motar key......
*_Ummi Shatu_*
[8/30, 9:07 PM] Ummi Liman: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert &
perfect writers)_
_Kina ina? Nana fiddausi (Feedohm), wannan
k'warya k'waryar shafin nakine ke kadai yar
d'akina....._
*56*
aishaummi.blogspot.com
*J*uyawa yayi ya kalleta kafin yafara driving,
"Baby... Ya naga kinbi kin bata rai kodai bakya
son bina ne?"
Rabuwa tayi dashi saboda jin tambayar rainin
hankalin da yayi mata,
"Uhmmm baby..?"
"Kafi kowa sanin idan ina son binka ko bana
so.." Ta bashi amsa cikin fada,
"Wowwww....! Dadina dake masifa, baby gaskiya
kemafa masifaffiya ce, ohhh shiyasa akace ba
ahada biyu dole sai kasamu daya mai fada daya
marar fada..."
"Naji ni masifaffiya ce" tafada a k'ule,
"A'a baby ni bance ba..." Ya fada harda daga
hannuwa,
Reverse yayi ya fita daga cikin makarantar nan
kuma yafara tunanin wurin zuwa domin babu
inda yasani acikin wudil bai taba shiga cikin
garin ba iyakacinsa makaranta sai ko bakin titi,
"Baby babu wani guest house da kika sani
anan...?"
Juyawa tayi ta kalleshi cikeda masifa shikuma
harga Allah zuciyarshi daya yayi maganar bada
wata manufa ba,
"Ohhhhhh ga yar iska ko? Dole ka tambayeni
guest house tunda ni cikakkiyar yar bariki ce..."
Packing yayi agefen titi ya kunna fitila yana
kallonta, fuskar nan tata sam babu fara'a ta
daureta tamau,
Sai da ya kamo hannunta ta kwace ya sake
kamowa ta kwace ya kuma kamowa nan ma ta
fisge sai kawai yajata zuwa jikinshi,
"Baby wallahi ba nufina kenan ba amma tunda
kinji haushi dan Allah kiyi hakuri, ni wallahi ban
taba kawowa komai araina dangane dake ba
wannan tambayar ma bada wata manufa nayiba
amma kiyi hakuri..." Yafada cikin cool voice
dinshi,
Yanda yafara magana har yagama bata tanka
mishi ba,
"Kin hakura..?"
Yasake tambayarta yana kallon fuskarta,
"Idan fa baki hakura ba zamu zauna ananne
inyita baki hakuri har sai kince kin hakura
sannan zamuje mu nemi wurin kwana..."
"Nahakura.."
"Yawwa nagode to, dan Allah kidaina fushi dani
baby, ban son ganinki cikin fushi ko kadan
wallahi..."
Zame jikinta tayi ta koma kan kujera ta zauna
bayan ta sassauta daurin da ta yiwa fuskar tata,
Cigaba da driving yayi har suka danyi nisa da
makarantar nan ya hango symbol din wani guest
house _Meenal best guest lodge_,
"Yawwa baby kinga wani guest house can bari
muje, ni gaba daya nagama gajiyane ma..."
Ko uffan batace masa ba saboda ita haushinta
daukotan da yayi ya kawota guest house sai
kace wata karuwa saboda tunda uwarta ta
kawota duniya bata taba zuwa wani wuri mai
kamada wannan ba,
Ciki ya shigar dasu yayi packing ya fito itama ta
fito tana ciccin magani, reception sukaje ya
karbi daki bayan ya biya kudin aka bashi key
suka nufi inda jerin dakunan suke,
Shi yafara shiga bayan ya bude dakin, bayanshi
tabi itama ta shiga,
"Baby ina zuwa bari naje na dauko system dina
a mota.."
"Wai kana nufin fita zakayi kabarni? Tab.."
"Tsoro kikeji? To zo muje tare.." Hannunta
yakama suka fita tare suka koma motarshi, nan
ya kwaso wasu tulin takardu da laptop dinshi,
saida ya tsaya a reception yayi musu order din
abinci sannan suka wuce,
Kayan ya zuba akan gado ya nufi toilet saboda
agajiye yake, wanka yayi tana zaune tana duba
wata takarda acikin takardun da ya shigo dasu
sai gashi yafito babu kunya daga shi sai wani
gajeren wandonshi iya cinya,
Tana ganinshi tayi saurin saka hannuwa ta rufe
fuskarta,
"Subhanallahi, meye hakan?" Ta fada
idanuwanta arufe,
"A ina? Wanka fa nayi ina son nasha iskane.."
Zama yayi agefen gadon ya dauki wayarshi,
"Kema kije kiyi kisha iska.."
Sai lokacin ta tuna da bata salla gashi ya
kinkimota ya kawota nan babu shiri da ita har
ta manta ma saboda yau tafara,
"Ohhh kaga ka kawo ni nan gashi ban dauko
komai ba, sai kaje ka fita ka siyo min.."
"Menene..?" Ya bukata yana kallonta saboda da
anufinshi bazai sake fitaba sai gari ya waye,
"Pad.." Tafada ahankali domin kawai sai taji
tana mai jin kunyarshi,
"To bari nasa kayana naje na siyo miki.."
Komawa yayi cikin toilet din yasako kayanshi ya
fito, tashi tayi tabishi saboda mugun tsoron
dakin takeji, tare suka fita suka shiga cikin gari
wurin bakin titi, packing yayi ya fita ya shiga
wani shago wanda babu abinda ba a siyarwa
aciki,
Jim kadan sai gashi rikeda leda yadawo, zama
yayi ya mika mata ledar, bayan pad din harda
pant guda biyu da rigar barci guda daya light
blue,
"Duba kigani sunyi miki?"
"Sunyi.." Tabashi amsa batare da ta kalleshi ba
amma kuma cike take da tsananin kunyarshi,
Komawa guest house din sukayi lokacin har
ankai musu abincin da yayi musu order, tuwon
shinkafa miyar agushi,
Suna shiga ko zama baiyiba ya yage kayan
jikinshi ya watsar akan gado saboda shi kwata
kwata baya kaunar zafi shiyasa agida koda
yaushe da three quarter da yar body hug zaka
sameshi sune kayanshi hajiya tayi fadan tayi
fadan har tagaji ta hakura,
"Baby ga abinci kizo muci idan kin gama.."
"Uhmmm" tace bayan ta nufi toilet, laptop dinshi
ya dauka ya bude, saida tayi wanka sannan ta
saka rigar baccin da ya siyo mata wacce bata
karasa gwiwarta ba, skirt dinta ta saka sannan
ta zira hijab ta fito,
Yanzun ma tare suka ci abincin duk kuwa da ita
bata so,suna ci yana tsokanarta har suka
kammala,
Ak'asa ta kwanta kan carpet bayan ta dauki
pillow shikuma yana saman gado azaune,
"Baby anan kika kwanta? Shikenan idan nagama
sai indawo dake kan gadon.."
Jin abinda yace yasata tashi takoma can
karshen gadon ta kwanta.
Murmushi yayi yaci gaba da aikinshi,
"Baby kinyi bacci ne?" Ya tambayeta, tana jinshi
amma tayi shiru,
Matsawa yayi yaje ya leka fuskarta tareda
lakuce mata hanci,
"Ai nasan ba bacci kikeyi ba idonki biyu kina
jina..."
"Dan Allah ka rabu dani inyi bacci.." Tafada tana
sake tukunkunewa cikin hijabinta,
"Baby ke rigimammiya ce wallahi.."
"Naji" ta bashi amsa, hijabin yaja nan ta tashi
afirgice tana kallonshi, wani sanyayyen
murmushi ya aika mata....
_Fatan alkhairi ga Khadija magaji bk tawa ni
daya..._
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*57*
*S*ai da ta hade rai ta daure fuska sannan ta kalleshi tana kokarin fincike hijabinta daga hannunshi,
"Kai baby...... Dan Allah kiyi hakuri please...."
"Amma ai ba haka mukayi dakai ba ko?", ta tambayeshi cikin bacin rai,
Kai ya daga mata cikin kalar tausayi,
"Ba haka mukayi ba baby amma ai abu daya dama kikace nayi miki alkawari akai kuma na amince nayi....wallahi bazan karya alkawarin da nayi miki ba, kuma ma baby inbanda rikici irin naki ai ba wani abu zanyi mikiba tunda fa a off kike..." Yakarasa maganar cikin rad'a,
Jin abinda yafada yasata rabuwa dashi bayan ta dauke kanta sai faman b'abb'ata fuska take, k'asa k'asa yake kallonta yana murmushi saboda sai yau yagane bata da wayo bare dabara,
Cikin doki da farin ciki ya zare hijabin tareda fara nuna mata wata soyayya mai mutukar sanyi, duk da tana nuna mishi cewar bata sonshi kuma bata son abinda yake mata hakan bai hanata samun kanta cikin dunbin farin ciki da nishadi ba,
Ya kwashe lokuta masu yawa yana gwada mata so daga yaji tafara yimasa masifa zai fara rarrashinta,
"Baby kiyi hakuri iya fa nayau ne kadai kinga gobe tafiya zanyi, dan Allah kiyi min wannan alfarmar..... Kinji baby"
Da haka yasamu yasha kanta ya lallabata har yasamu ta kyaleshi yasamu farin ciki mai tarin yawa, har karfe 2 nadare yana manne da ita ganin abun ba na karau bane yasata yin magana,
"Gaskiya nifa bacci nake ji...."
Sai da ya rungumeta tsam tsam ajikinshi sannan yayi mata magana ahankali cikin yanayin rada,
"To baby ai ma kinyi min halacci, kinyi kokari, yi baccinki babu mai tashinki har sai gari ya waye, nagode baby, Allah yayi miki albarka, Allah yabarni dake har karshen rayuwata, Allah yayi miki albarka baby...."
Yatsun hannunta na dama yakama yana murzawa ahankali sai faman godiya yake yimata wanda har sai da taji kanta ya daure da wannan godiyar da yadage yanata yi mata banda saka mata albarka da yaketa faman yi kamar wadda tabashi wani abu, nan ta tuno first night dinsu da yaya kabeer,sam baiyi mata irin wannan karramawar ba amma shi amadi da ba a budurwa ya aureta ba kuma ba komai ne ya shiga tsakaninsu ba yadage yanata faman lallabata tareda saka mata albarka, jin irin godiya da rarrashin da mijinta keta faman yi mata yasa tayi fatali da tunanin kabeer tama manta dashi gaba daya, babu bata lokaci bacci mai mutukar dadi ya dauketa.
Amadi kam sam bai yi barci ba yakasa yanata faman juyayin tafiyar da zaiyi yabarta, zaije ya kadaice shi kadai batare da itaba, zaiyi nesa da ita a daidai lokacin da yafara shakuwa tareda jin dadin zama da ita, har aka kira sallar asuba idonshi biyu bai runtsa ba, ahankali ya tashi daga jikinta ya shiga toilet.
Yana idar da salla ya tashi bayan yayi addu'o'inshi kamar yadda ya saba, kan gadon yakoma ya zauna ya jawo laptop dinshi yaci gaba da ayyukan jiya wadanda ya fatalar bai karasa ba, har karfe 6 tayi gari yayi haske nadiya bata farka ba, sai misalin karfe 7 sannan tayi juyi ta bude idanuwanta,
Jikinta ta kalla sannan ta juya ta kalli amadi wanda ke zaune yanata aikinshi,fuska ta daure tafara dabarar yanda zata tashi, hijabinta ta daura ta mike fuskarta a daure,
Waiwayawa yayi ya kalleta nan yaga irin yanda ta daure fuska, murmushi yayi ahankali ya furta,
"Duk ciccin maganinki dai sai da naga yanda matata take kafin natafi...."
Toilet ta shiga sai da ta dade sannan ta fito tana sanye da kayanta na jiya wanda tazo dasu,
Can daya gefen gadon taje ta zauna, "ina kwana...?"
"Yes my baby, ai ba ahaka zamu gaisa ba, bari nazo na debi gaisuwa, just 1 minute....." Yafada idanuwanshi na kan laptop dinshi, ajiye laptop din yayi ya tashi ya nufi wurinta, tana ganin haka ta dauke kanta tareda sake bata rai,
Agabanta ya tsugunna ya kamo hannuwanta masu mutukar taushi,
"Baby ya kika tashi?, ina fata kin tashi lafiya....?"
"Lafiya lau..." Tabashi amsa batare data kalleshi ba,
"To ki kalleni mana baby..." Yace da ita yana murmushi,
"Tunda mun gaisa ni ka tafi"
Murmushi yasake yi saboda jin abinda ta fada maimakon ya tashi sai ji tayi ya kwantar da kanshi akan cinyarta,
"Idan natafi ina zanje inda yafi nan? Haba baby ya zaki rinka korata alhalin kuma kin san banida wurin zuwa...."
Shiru tayi masa bata amsa masa ba, yadade kanshi bisa cinyarta kafin ya dago yana kallonta,
"Baby masu duniya...."
Nan dinma dai shirun tayi,
"Kina jin yunwa ko? Bari nasa akawo mana breakfast.."
Ita dai batace komai ba shi kadai yake maganarshi,tashi yayi yana rikeda hannunta yana kallonta,
"Zoki rakani to..."
"Kaje ka dawo"
"To shikenan ina zuwa"
Sakin hannunta yayi yafita nan tabishi da kallo, "maza babu ta ido.." Tafada ahankali,
Bai wani jimaba ya dawo, zama yayi agefen gadon yana kallonta,
"Dan matso nan dan Allah..."
Yi tayi kamar bataji ba, "baby... " yasake kiran sunanta,
"Na'am.."
"Cewa fa nayi ki matso kusa dani..."
Shiru tayi batayi ko motsi ba,
"Shikenan ni bari nazo tunda ke kin ki zuwa..."
Matsawa yayi wurinta,
"Bari na daukeki nakaiki tunda kin ki zuwa..."
"Dan Allah kabari bana so...."
Kokarin daukarta yafara yi nan suka shiga kokawa dama abinda yake so kenan tahaka yasamu damar rabata da hijabin da ta saka yabarta da sexy dress din dake jikinta,
Duk da bata so sai da ya dauketa yakaita side din da yake zaune dazu, ajiyeta yaje yi nan yaci tuntube tayi saurin rikeshi suka fada kan gadon tare,
Kura mata ido yayi yana dariya,
"Baby karfa mu karya musu bed, ko zaki iya biyansu idan wannan ya karye? Uhm.....?"
Fuskarta ta dauke ta soma tuttureshi wai yatashi, gyara kwanciyarshi yayi ajikinta, nan taci gaba da faman tureshi, laptop din shi ya mika hannu ya dauko, kokarin zameshi tafara yi zata tashi,
"Wallahi idan har kika tashi ban yafeba kuma sai Allah ya tambayeki garama ki zauna..."
Hakura tayi ta zuba masa ido tana ganin isa da mulki irin ta maza inbanda tsabar nuna isa ajikinta fa ya kwanta rub da ciki kuma yake danna laptop dinshi yana yin aikinshi,
Dole haka ta hakura har ya kammala aikin da yake yi lokacin har karfe 8:30 tayi, breakfast aka kawo musu wanda yayi musu order, nan ya fita ya karbo yadawo dakin inda take,
Sauko da ita yayi daga kan gadon ya zauna itama ta zauna yafara ciyar da ita, soyayyen dankali da kwai sai farfesun hanta, sam bai damu da kanshi ba ta ita yakeyi har sai da yaga ta koshi sannan yace itama sai ta ciyar dashi, tana cika tana batsewa fuska a daure haka tabashi yaci ya koshi,
"Nifa ina son komawa makaranta da wuri...." Tafada tana hararar wani wuri,
"Karki damu yanzun nan zamu tafi baby..."
Tattara kayanashi yayi suka fita, duk ta damu da irin kallon da mutanen wurin suke yi musu ita dashi musamman ma ita ko sun dauka budurwarshi ce ba mata ba oho hakanne yasake bakanta ranta, koda suka shiga mota yafara driving yanata janta da hira amma taki kulashi abunku da marar fushi ko da wasa bai damu ba, lokacin da suka shiga makarantar hannunta ya kamo yafara yi mata magana cikin sigar lallashi,
"Baby dan Allah ki shirya mu koma kano tare dake saboda ina son hajiya ta sanki before natafi...."
Shiru tayi kamar bazata amsa ba amma jin ya ambaci hajiya yasata amincewa,
"Shikenan zan shirya..."
"Yawwa baby nagode Allah yayi miki albarka"
Bude kofar motar tayi ta fita shikuma yakarasa administrative block.
Karfe 2 na rana ta fito cikin shirinta,wata jar atamfa ce ajikinta mai zanen akwati da ratsin yellow ajiki, dan tsabar jan fada saida ta caba kwalliya a fuskarta sannan kuma ta yafa mayafi a kafada gashi dinkin fited ne riga da skirt,kai idan kaganta zaka rantse cewar budurwa ce,
Tunda ta taho yake kallonta ta cikin mirror har ta karaso, lokacin da ta shiga cikin motar kuwa wani fitinannen kamshi yaji ya doki hancinshi,
Kallonta ya juya yana yi kawai baice komai ba, yadade yana kallonta baiyi magana ba,
"Ya lafiya...?" Ta fada batare da ta kalleshi ba,
"Amma dai baby ai kin san nahanaki saka mayafi ko?"
"Ohhhh kenan kwata kwata bazan saka ba kake nufi?"
Key yayiwa motar batare da yayi magana ba, har saida suka yi nisa da makarantar sannan ya kalleta,
"Kita sakawa idan kinada ra'ayi ni ban hanaki ba, duk abinda kike so kiyi kanki tsaye..."
Kallonshi tayi saboda tana son ta tabbatar da gaskiyar abinda yafada ko gatse yayi mata, kallonta yayi tareda yimata murmushi nan tayi saurin kawar da kanta, hannunta ya kamo ya rike cikin nashi,
Lokaci lokaci yana yimata hira amma ba sosai take amsawa ba da haka har suka shiga cikin kano,
"Wowwwww ga wata hadaddiyar....."
Yafada sai kuma yayi shiru, kallonshi tayi shima ya kalleta,
"Bafa wani abu zance ba cewa nayi ga wata hadaddiyar riga can wadda nasan idan kin saka zata yimiki kyau... Kin ganta can"
Juyawa tayi gamida tabe baki.
Lokacin da suka karasa gidansu amadi nadiya ba karamar karramawa ta samu awurin hajiya ba kamar hajiya ba zata ajiyeta a kasa ba dan farin ciki, ita kanta hajiya saida ta yaba da zabin amadi lokacin da taga nadiyan, nan dadi ya rufeta saboda ganin surikar tata,
Gabatar musu da abinci hajiya tayi bisa table nan amadi ya dakinshi yafito bayan yasha wanka yana sanye cikin wata t shirt lemon green agaban rigar an rubuta _big guy_ da bakin three quarter sai kamshin turaren _axe_ ne ke fita daga jikinsa,
Table din yakarasa yana kallon nadiya tareda jan kujerar dake kusa da ita, hajiya kam sai murmushin farin ciki take ganin wai yau autanta ne yayi aure gashi tareda matarsa,
Dambun shinkafa da sos ya zuba musu cikin flate yasaka spoon guda biyu yatura gabanta, ita dai nadiya akunyace taci wannan abincin saboda ga hajiya na zaune awurin gashi kuma sai kokarin wai sai yabata abaki yakeyi, lokacin da suka kammala cin abincin mikewa yayi yana kallonta,
"zo muje ki tayani shirya kayana baby"
Bata yi musu ba saboda hajiya dake zaune, hannunta ya kama zuwa bedroom dinshi wanda ke kusa da na hajiya......
_Fatan alkhairi ga Anty Baraka & Meenarh parrot sannunku na yaba mutuka da kokarinku wajen kwaikwayon salon rubutun ummi shatu...._
*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO* _(Home of expert & perfect writers)_
_Fatan alkhairi ga anty Jidda musa this page is yours..._
*Masoya masu karanta mijina sirrina dan Allah kuyi min uzuri na rashin ganin post akan lokaci ina cikin hidima ne amma insha Allah komai zai zama normal, gaisuwa agareku mai tarin yawa...*
*58*
aishaummi.blogspot.com
*Y*ana rike da hannunta har cikin dakinshi wanda ke dauke da kayan ababen more rayuwa kala kala,
Akan tamfatsetsen gadonshi ya zaunarta ya tsugunna agabanta gamida kama hannuwanta yana kallonta,
"Dan Allah baby idan natafi ki kula da kanki sosai kinji? Duk da dama nasan ke mai nutsuwa ce..."
Karo nafarko data iya kallonshi kallo na nutsuwa nan taga idanuwanshi sunyi ja, can lungun idonshi kuma ruwane kwance, ko ba afada ba tasan kuka yake kokarin yi mata, duk da bata damu dashi ba sannan ba sonshi takeyi ba saida taji jikinta yayi wani irin sanyi,
Shiru suka yi gaba dayansu daga shi har ita,
"Kayan nan sunyi miki kyau sosai baby, muga dinkin...." Yace da ita bayan ya koma jikinta ya zauna,mayafin ya janye yana kallonta tako ina,
Bata iya cemishi komai ba saboda irin sanyin da taji jikinta yayi illa sunkuyar da kanta kawai da tayi tana jin yanda yake kissing din wuyanta asanyaye,
Yau dai dayake yan zaman lafiyar nata suna kusa kasa hanashi tayi har sai da ya kyaleta dakanshi,
"Baby kinga jakar da zan zuba kayan can akusa da wardrobe..."
Mikewa tayi domin taje ta dauko nan yabita ya rungumeta ta baya, ahaka sukaje ta dauko jakar suka dawo gaban gadon,
"Kayan suna cikin wardrobe..." Yasake fada har lokacin yana rungume da ita ta baya, tare sukaje tafara debo kayan tana cillawa saman gado, shine yake nuna mata wanda zata dauka har sai da yace sun isa tabarshi haka,
"Baby saura vest da short nicker..."
Ciro masa gajerun wanduna tayi da vest nan suka koma wurin kayan yana makale da ita, zama tayi shima ya zauna a bayanta ya zagayeta da hannuwanshi ya rungumeta tareda dora kanshi bisa kafadarta,
Jera masa kayan tafara yi acikin jaka shikuma yafara yi mata magana acikin kunnenta,
"Baby ki gama ki zana yanda kike son gidanki ya kasance saboda kafin nadawo za agama ginin ayi komai da komai ina dawowa tarewa kawai zamuyi aciki nida ke....., zan nuna miki filin da za ayi mana ginin yanzu idan kin gama shirya min kayana"
"Uhummm" shine kawai amsar data bashi ta cigaba da zuba masa kayan cikin jaka, abayanta taji ya kwanta ya dora kanshi ajikin wuyanta,shiru taji yayi kamar mai yin bacci, ita dai batayi magana ba aikinta kawai takeyi,
Daf da zata gama taji anbude kofar dakin anshigo da sauri ta kalli kofa saboda duk azatonta hajiya ce nan taga yayarshi ce anty siyama, kokarin zameshi daga jikinta tafara amma yaki saima sake kankameta da yayi kamar zai mayar da ita cikin cikinshi,
"Sorry nashigo muku kai tsaye...." Anty siyama tafada tana murmushi,
"Babu komai anty ai ba wani abu bane..." Inji amadi,
"Ahhh dan dai ban san ku biyu neba nayi tunanin kai kadai ne.. Ashe kaida amarya ne" ta karasa maganar tana kallon nadiya,
"Sannu da zuwa.." Nadiyan tafada akunyace,
"Yawwa sannu amarya, yagida?"
"Lafiya lau"
"Anty amadi amma dai ba yau zaku tafi ba..."
Dariyar sunan yaso bawa nadiya wai anty ita bata taba jin ancewa namiji anty ba sai shi,
"Haba anty yau bazaki ce yaya amadin ba sai anty kinga gashi nan kinsa matata tana yimin dariya....."
Dariya anty siyama tayi, "to ai bakina yasaba ne, tun kana yaro lokacin..."
"Kai anty dan Allah basai kin tona min asiri ba..."
Juyawa anty siyama tayi tana dariya,
"Kiji antyn nan zata fasa min kwai agabanki..." Yafada yana sake kwantar da kanshi akan wuyanta, batayi magana ba har ta gama shirya kayan ta rufe jakar,
Tashi yayi yakama hannunta zuwa gaban window dinshi wanda ke kallon baya, ya dage labulen nan ta hango fili kato mai girman gaske,
"Kinga filin da zan gina miki gidanki can, hajiya tace bazan yi nisa da ita ba dole tare zamu zauna..."
Kai ta daga batayi magana ba,
"To zo muje ki zana gidan..."
Abakin gado ya zaunarta yabude drewar din jikin gadonshi ya dauko plane sheet da pencil ya bata, abayanta ya zauna ya rungumeta,
"To zana ingani, nafi son ki zana da kanki saboda kar ayi miki wanda bashi kike so ba..."
Zanawa tafara duk da bata san yanda ake yiba, falo ta fara fitarwa sannan sai bedrooms guda uku, biyu suna opposite da juna daya kuma takaishi can gefe da nisa shi kadai kwal,
"Baby wannan bedrooms din guda biyu nasu waye?"
"Nawane daya, guda dayan kuma na baki.."
"Shikuma wancan wanda kika kai gefe fa?"
"Naka ne.."
Murmushi yayi, "wato ni aka kai gefe kenan..."
Mika mishi takardar tayi wai tagama,
"Baby baki zana bathroom ba, baki fitar da kitchen ba bare store..."
Ita shaf ta manta sai lokacin ta tuna,
"Nuna min a inda kike so asaka miki kitchen din..."
Nuna mishi tayi ya zana, haka yayita tambayarta idan ta nuna sai ya zana mata har zanen gida ya kammala.
Da dabara ta samu tafita daga dakin ta koma falo wurinsu hajiya da anty siyama saboda tasan idan zamansu yayi yawa a daki itada amadi su hajiya zasu zargi wani abu,
Tana zaune awurinsu hajiya har amadin yafito daga dakinshi idonshi fes akanta,
"Anty siyama kinzo da driver ne ki ara min shi ya mayar min da baby school..?"
Kunya maganarshi tasaka nadiya jin agaban hajiya da yayarshi yana kiranta da baby,
"Ehhh yana nan yaya amadi, yaushe zata tafi?"
Anty siyama tabashi amsa,
"Sai zuwa anjima..."
"To shikenan"
Zama yayi akusa da nadiya ita duk sai take jin nauyinsu hajiya tana ganin kamar zasu ga rashin kunyarta amma shi sai sake matsawa yake kusa da ita.
Har misalin karfe 6 na yamma tana gidan saboda shi amadi tashin tsakar dare zasuyi, ganin 6 ta dan gota yasa nadiya tace mishi zata tafi, albarka sosai hajiya ta shiga sanya mata tareda yimata godiya kamar wacce takai musu wani abu, sallama sukayi da anty siyama wacce keta faman janta da hira kamar ba yayar miji ba,
Hannunta yakama bayan sun fito daga falon hajiya,
"Baby ki kular min da kanki dan Allah, ki kular min da kanki,nasan zanyi missing dinki mutuka but ako ina nake akuma duk inda na tsinci kaina kina nan acikin zuciyata, soyayyarki daga Allah ne bani na sakawa zuciyata ba, namanta ban fada miki ba shekaran jiyafa naje rano nayiwa su mama sallama,baby zan tafi nabarki a lokacin da nake da tsananin bukatarki amma babu komai insha Allah kamar yaune zaki ganni nadawo gareki, zan kiraki anjimabkafin mu tashi..."
"To shikenan Allah ya kiyaye hanya" tafada batare data iya kallonshi ba, kiss ya manna mata akan lips dinta sannan ya rakata wurin motar anty siyama inda drivernta malam mudi yake tsaye yana jiran karasowar nadiya, amadi da kanshi ya bude mata kofar motar ta shiga ta zauna ya mayar ya rufe, gefe yakoma ya tsura mata ido ta cikin glass din motar daga karshe yafara daga mata hannu yana yimata sai wata rana......
_*Ummi Shatu*_
[9/8, 9:28 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*59*
aishaummi.blogspot.com
*T*saye yayi ya harde hannuwanshi a kirjinshi yana kallonta, dagowa tayi itama ta kalleshi nan ta hangoshi ta cikin glass din motar yana yimata murmushin shi mai tsananin tsada,
Saurin kawar da kanta tayi bata sake kallonshi ba har suka fita daga gidan,
Shima bai bar wurin da yake tsayeba har saida yaga fitarsu nadiya sannan ya juya ya koma ciki wurinsu hajiya,
"Kai yaron nan gaskiya kanada matsala yanzu saida ka dauko yarinyar nan kaji dadi.." Anty siyama tace dashi tana daddanna wayar dake hannunta,
"Anty kenan to wani abune? Ni jiyama awurinta na kwana"
Yabata amsa yana kallonta yana dariya,
"To ya isheni haka marar kunya kawai"
Dariya yayi yatashi yabi hajiya cikin kitchen inda take soya masa dambun nama wanda zai tafi dashi.
Bayan sallar magrib sosai su nadiya suka shiga wudil, har cikin makaranta drivern yakaita, fita tayi tashiga hostel, tana zuwa dakinta ko zama batayi ba amadi ya kirata,
"Dan naci..." Tafada ahankali kafin ta daga wayar,
"Baby kunje ko?" Taji yafada cikin muryarsa mai sanyi,
"Ehhh mun sauka harma drivern yatafi"
"To naji dadi tunda ya mayar min da matata lafiya..."
"Uhmmmmm" tafada,
"Kin san abinda anty siyama tace bayan kin tafi? Wai saida na daukoki nikuwa nace mata ai jiyama awurinki na kwana..."
"Kafada mata haka?"
"Ehhh mana ai ba karya nafada ba ko ba tare muka kwana ba?"
Shiru tayi masa saboda taji yafara neman sakin layin da suke,
"Uhmmmm? Baby ko bahaka bane?"
Nan dinma shiru tayi masa bata amsaba, kasancewar idan da sabo yasaba da halinta yasashi cigaba,
"Jiya najini acikin wata duniya ta daban, ban taba samun kaina acikin wannan yanayin ba, naji dumin jikin matata Sosa...."
"Kaima wallahi ka iya maganganun...." Sai kuma tayi shiru bata karasa ba saboda nauyin da kalmar tayi mata abakinta,
"Meyasa baki karasa ba? Wata nafadawa ba matata nafadawa ba? Idan banyi hira dake ba dawa zanyi? Uhmmmm"
"Uhmmmm" tafada,
"Uhmmmmm?" Yasake fada,
"Uhmmm" itama tasake bashi amsa,
"Uhmmm?"
"Nace uhmmmm"
"Haba baby kiyi magana mana.." Yafada yana dariya saboda tabashi dariya sosai,
"Umhum.." Tabashi amsa,
"To tunda bazaki yimin magana ba shikenan sai anjima, yunwa nakeji abinci zanje naci"
"Toh"
"To sai anjima, ki kular min da kanki, i love you..."
Ko jiranta baiyi ba ya katse wayarshi saboda yasan ba amsa mishi zatayi ba,
Tun 9 ya kirata yake yimata hira wacce kusan shi kadai yake yin kayarshi domin ita daga uhm sai um um, bashi yayi sallama da itaba sai karfe 2 nadare saboda lokacin zasu tafi airport domin 2:30 zasu tashi,
Lokacin da yaje airport dinma saida ya kirata yasake yi mata sallama daga karshe kuma taji yayi shiru kamar wanda yake jiran wani abu,
"Shikenan baby sai nadawo..." Yafada tareda goge kwallar idonshi, duk sai taji wani iri,
Ita dai tasan bata sonshi ko yaya amma kuma saita gagara bacci, daren ranar gaba daya kasa bacci tayi tun lokacin da yace mata yatafi sai yaje zai kirata.
Haka tatashi da safe duk jikinta sanyi kalau kamar marar laka ajiki, duk da bata damu dashi ba sai da taji hankalinta ya tattara yatafi kanshi gaba daya,
Haka haka dai ta wuni ranar har dare yayi shiru bai kirata ba, ta karfi da yaji tasamu ta yakice damuwar taci gaba da al'amuranta,
Tunda yayi kwana biyu da tafiya kuma sai tafara mantawa da tunaninshi saboda dama bawai wani shiga ranta yayi ba domin yanzu bazata yi gaggawar sakashi aranta ba har sai ta fahimci wanene shi,
Kwananshi 5 da tafiya tafito daga lecture sai taga number din waje na kiranta domin akwai plus ajiki,
Jikinta ne yabata cewar amadi ne,
"Hello..."
"Baby nah..." Taji yafada cikin muryarshi kamar mai jin bacci,
"Na'am.."
"Baby ya kike? Inata missing dinki sosai,ke kuwa bakya missing dina ko?"
"Hmmmm"
"Ban gane hmm ba, kinga daga zuwana har mura ta kamani"
"Allah ya sawwake"
"Amin baby, abar sona, ina sonki baby..."
Shiru tayi tana jinshi, ya dan jima yana fada mata kalamai na soyayya zalla amma har yayi yagama bata mayar mishi da martani ba daga karshe dai yayi mata sai anjima ya kashe wayar wai yayi fushi tunda bata taba cemishi tana sonshi ba,
Bata kirashi ba har dare, shi da baya zuciya shine ya sake kiranta,
"Har ka huce kenan?" Tace dashi lokacin da ta dauki wayar, murmushi mai sauti taji yayi,
"Da anfada miki nayi fushi dake ne? Ni ai bazan taba yin fushi dake ba arayuwata... Ni yanzu bacci ma zanyi shine naji baccin bazai yiyu ba har sai naji muryar matata, ki cemun you love me..."
"Uhmm"
"Uhmm ki fadi abinda nasaki mana..."
Shiru tayi batayi magana ba,
"Baby..."
"Na'am"
"Kiyita fada min kalaman so har sai nayi bacci, idan kuma bakiyi ba Allah zai saka min..."
"Ni gaskiya ban san me zance ba..."
"Tunda baki saniba to kiyita cewa kina sona, kinga nasanar dake abinda zaki fada.."
Shiru tayi shima yayi shirun yanata yimata dariya kasa kasa tayadda ba zata jiba,
"Baby kina son nabarki da Allah? Idan bakya so kiyi abinda nace kinga mu dare yayi sosai anan, oya start...."
"Me zance?"
"Kice kina sona, kuma kiyita fada har sai nace ya isa haka.."
Kamar zatayi kuka taji saboda ita gaskiya bata son fadin abinda yace,
"Nidai gaskiya ka sauya wani.."
"Wallahi wannan zaki fada kuma idan baki fada ba ban yafeba..."
"I love you..." Tafada tana bata fuska kamar yana ganinta,
"To ai fada zakiyi tayi har sai nace ya isa..."
Cigaba da fada tayi shikam har wani lumshe ido yakeyi saboda yanda Kalmar take yimasa dadi duk da yasan adole take fada bawai dan tana son nashiba.
Saida tafada fiyeda sau 20 sannan yace mata ya isa haka, shiru tayi fuskarta akumbure dan takaici da bacin rai,
"Nagode my baby, sai munyi magana gobe kinga yanzu bacci zanyi, nagode Allah yayi miki albarka, I love you..."
Katse wayar yayi yana dariya ita kuma ta katse tata cikeda takaici, tun daga wannan ranar kullum haka yake mata shiyasa wata rana har bata son bude wayarta kuma idan yakira yaji arufe idan yasake kira sai yace mata idan takara kashe masa waya itada Allah, babu yanda ta iya dolenta haka ta hakura ya zatayi da nacin amadi.
Akwana atashi ahaka wannan semester din takare akayi musu hutu ta koma gida yanzu semester daya ya rage mata, time din watan amadi 3 a birnin London,
Kullum cikin kiranta yake sannan kuma ya tsareta lallai lallai sai tayi masa kalaman soyayya ko kuma tace masa i love you, amma wani lokacin bama ya kulata da ya kirata zaice ta hadashi da twins susha hirarsu,
Ganin har yanzu bata kamu da son amadi ba abin yabawa Amira mamaki, gaba daya takasa gane nadiya wacce irin mace ce mai tsaurin rai da taurin kai tunda ai kodan kyautatawarsa agareta itada yaranta ya kamata ace tafara sonshi Sannan bai rageta da komai ba duk karshen wata kudi yana shiga account dinta saboda yace mata yanzu nauyinta akanshi yake,
Wurin nadiyan ta nufa a inda take zaune tana gyara fuskarta su fadeela kuma sun tisata agaba suna son suyi mata kuka wai sai sun bita ita kuma tace babu inda zataje dasu,
"Anty wai sai ina da yamman nan?" Amira ta tambayeta tana kamo hannayen twins,
"Amira gyaran gashin nan zanje saboda wallahi kaina yacika da yawa.."
Karar da wayar nadiya tafara yine yahana Amira yin magana, dauka nadiya tayi saboda ganin amadi ne dama tana son kiranshi ta tambayeshi cewar zata fita,
"Hello baby" taji yafada lokacin data daga wayar,
"Na'am, dama yanzu zan kiraka"
"Sai kuma gashi na kiraki, meya faru?"
"Ina son zan fitane"
"Ina zakije?"
"Gyaran gashi zanje"
"To, waye naji yana kuka?"
"Su fadeel ne wai sai sun bini nikuma bazanje dasu ba.."
"Akai suke kuka kenan?"
"Ehhh"
"To kema bazaki jeba nahana, idan kuma kina son zuwa ki tafi dasu.."
"Ni bazanje dasu ba"
"To shikenan kema ban yarda kijeba dama ai gashin nawane so abar min kayana ahaka basai an gyara ba"
"Bazanje ba kace fa?"
"Ehhh" yabata amsa,
"Hmmm" tafada tareda katse wayar wadda ko ba afada masaba yasan fushi tayi, kallon su fadeel tayi ta hararesu,
"Sai na zaneku idan baku daina yimin kuka ba, shima harda wani cewa bazanje ba to kar Allah yasa yabarni naje din sai me.."
Tafada cikin bacin rai tareda cire dan kwalin dake kanta ta wulla kan gado ta sulale awurin tayi kwanciyarta.
Ba afi mintuna biyar da faruwar hakaba sai gashi ya sake kiranta, kin dagawa tayi shikuma bai hakura yadaina kiraba har saida taji karar ta isheta sannan ta dauka,
"Baby fushi kikayi ko? Kiyi hakuri to, kije nabarki,sai kin dawo..."
Shiru tayi masa tana cije lip dinta nakasa,
"Baby kije nace, kiyi hakuri tunda ranki ya baci, karki yi fushi dani kinji... Uhmmm baby, kinji?"
"Naji"
"To adawo lafiya, ki kular min da kanki"
Kit ya katse wayar, zama Amira tayi akusa da ita,
"Anty nadiya nikam Yaya Ahmad yana bani tausayi, wai har yau kinki sonshi bare ki nuna masa kulawa"
"Lallai Amira bakida hankali, anfada miki ni sakarya ce da har zan sake garajen fara sonshi? Idan ku kun manta da butulcin Yaya kabeer agareni ni ban manta ba,ni yanzu babu filin so acikin zuciyata"
"Karki ce haka anty, ni ina ganin kibawa Yaya Ahmad dama domin ki gane irin son da yake miki, idan kina son fahimtar shi waye akwai hanyoyi da yawa da zaki iya gudanar da hakan"
Lipstick ta dauka tana gogawa lips dinta, "kamar wacce kenan?"
"Kina iya gwadashi ta hanyoyi da dama, ma'ana ki rinka kiranshi ko yi mishi text da wata number ta daban wacce bazai taba tunanin cewa kece ba kinga ta haka zaki fahimci inda yasa gaba"
"To Amira kin kawo shawara kam, bari amir ya shigo zan bashi kudi ya siyo min sabon sim.."
"Yawwa anty ko kefa"
Karasa shiryawa tayi ta mike tayiwa su fadeel wayo ta zare jikinta ta fita bayan ta yiwa mama sallama..
Jama'a wai ina labarin kabeer ne da asabe mc? Mu hadu a page nagaba domin jin inda suka makale.
*_Ummi Shatu_*🏻
[9/10, 8:07 AM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*60*
aishaummi.blogspot.com
*K*amar yadda amira tabawa nadiya shawara haka ta dauki shawarar acikin kwana biyu tabawa amir kudi ya siyo mata sabon sim special number,
Dayake wayarta 2 sim ne sai kawai tasashi acikin wayar,kiran amadi tafara yi Amira na zaune akusa da ita amma abin mamaki koda wayar ta shiga sai yaki dauka, kira taci gaba dayi nanma bai daga ba har saida ta kira sau hudu ana biyar dinne taji ya dauka,
Sai da ta lankwashe muryarta ta yadda bazai ganeba sannan tayi magana,
"Hello Ahmad..."
Shiru ya danyi kafin yayi magana,
"Wacece?"
"Amma ai kabari dai ma gaisa ko? Kamata yayi mufara gaisawa kafin nasanar dakai ko ni wacece.."
Kitttt taji ya kashe wayar, dariya Amira tafara yi harda rike ciki saboda jin yadda nadiya ta wani kashe murya dan kar ya ganota,
Sake kira tayi nan ya dauka,
"Haba Ahmad ya zaka kashe wayar bayan bamu gama ba? Dan Allah kayi hakuri wallahi ban son bacin ranka, sunana jalila ni daliba ce a makarantar wudil.."
"To meya faru kika kirani? Sannan waye yabaki number ta?"
"Hmm yaya Ahmad kenan ai duk wannan mai saukine tunda kasan bahaushe yace mai son kayanka yafika dabara, dalilin kiranka kuwa shine agaskiya ka dade kana burgeni gashi ina mutukar sonka.."
Sake kashe wayarshi yayi bai karasa jin bayananta ba, kallon Amira tayi tana dariya,
"Ji yasake kashewa,bari nabarshi haka sai zuwa gobe sai insake kiranshi inji"
Dariya Amira tayi "Allah sarki yaya Ahmad daga jin maganar so sai kuma akashe waya"
"Ke kyaleshi wai shi nan Jan aji, zan kureshi ne ai.."
"Anya kuwa? Anty banga alama ba"
"Kya gani ai..."
Rufe sim din tayi tabar wanda take amfani dashi kawai a bude, shi kam Amadi ko takan maganar ma bai kara bi ba bare ya binciki ko wacece saboda da farko ya tsammaci zee ce kanwar mijin anty siyama amma kuma daga baya sai yagane cewar ba ita din bace nan yayi watsi da maganar domin bama yason yasan ko wacece.
Bayan sallar isha tana tsaka da shirin bacci sai gashi ya kira,
"Baby" yakira sunanta cikin so domin akoda yaushe jin sonta yake yana sake ratsashi,
"Na'am.."
"Bakiyi bacci ba?"
"Yanzu zanyi shiryawa nake.."
"Shiri kuma? Baby wanne irin shiri bayan bana nan? Ki tattara duk shirye shiryenki ki ajiye har sai nadawo"
"Hakane"
"Ko baki yarda ba?"
Bata bashi amsa ba takarasa saman gado tayi kwanciyarta abinta,
"Baby ina yimiki magana shine kika rabu dani ko?"
"To me kakeso ince?"
"Ohhh aiki kike nema kenan ko? To bari inbaki kiyi, kiyita kissing dina har sai nace ki daina ya isheni.."
"Nidai gaskiya wallahi a'a.."
Murmushi yayi, " a'a fa kikace, kifara tun kafin kiyi laifi awurin Allah"
"Wallahi nidai indai haka zaka rinka yimin zan daina daukar wayarka.."
"Idan kin daina daukar wayata ma wani laifinne dai kikayi gara ma ki dauka.."
"Indauka kayita sakani aiki.."
"Menene aikin aciki? Ai ban fara saki aikiba sai nadawo tukunna, yanzu dai fara ina jinki"
Wani haushi ne ya turnuketa saboda jin yana yimata dariya wadda tun yana boyewa har yafito fili,
"Ahmad" takira sunanshi,
"Na'am baby love"
"Meyasa kake yimin hakane?"
"Saboda ke matatace nikuma mijinki ne sirrinki..."
"Shine dalili?"
"Ehh shine, fara ina jinki"
Kamar mai shirin yin kuka haka tafara kissing dinshi ahankali ta cikin wayar, tafi minti biyar tanayi amma baice ya isa ba sai da ta kusan mintuna goma sannan ya dakatar da ita,
"Baby barshi haka dan wallahi za a iya samun matsala idan kikaci gaba dayi gashi kuma bakya kusa"
Shiru tayi masa saboda yanzu taga yagama zama marar kunya bata san meyasa ba kwanan nan wasu maganganu yake zarowa yafada mata kuma idan yafada ko a kwalar rigarshi babu ruwanshi da jin kunya,
"Washhh, baby wallahi yau akwai matsala..."
"Nikuma meye nawa aciki?" Tace dashi tana turo baki kamar yana ganinta,
"Meye naki aciki? Kekuwa kikeda ruwa da tsaki aciki tunda mijinki yana bukatarki yanzu gashi bakya kusa dashi"
Shiru tayi masa tana sauraron yanda yake yi mata wani ajiyar zuciya akunne,
"Nifa kaga ka cika min kunne gaskiya idan ka gama wannan ajiyar zuciyar taka ka kirani.."
Shiru taji yayi wanda tasan kasa maganar yayi badan hakaba da tuni ya bata amsa,
"Ina magana kayi min shiru..."
Har lokacin dai bai iya yimata magana ba yayi shiru abinshi sai ajiyar zuciyar da yake ta faman ajiyewa daga bisani kuma yafara wani tari babu kakkautawa sai da yajima yana yi sannan tarin ya tsaya sai kuma shakuwa, shak'uwa yake yi sosai,
"Maganinka ai, gobe ma dan Allah ka kara.." Tafada ahankali, ashe yaji abinda ta fada,
"Baby..." Taji yakira sunanta amma kuma sai yayi shiru saboda shakuwar da yaketa yi,
"Ya?" Tafada tana dariyar mugunta,
"Da biyu kikayi min wannan abun ko?"
"Bawani da biyu, bakaine kasani ba? Harfa rokonka nayi akan karnayi amma kaki kace sai nayi maka"
"Hmmmm" yace yana murmushi,
"Kaje kasha ruwa ko zaka daina wannan shakuwar.."
"Babu ruwanki dani malama.." Yace da ita wanda har lokacin shakuwar taki barinshi, jin abin bamai karewa bane yasashi tashi yaje ya dauko ruwa yadawo ya kwanta,
"Kaima ance maka kasha ruwa kaki"
"Gashi ai zan sha"
Saida ya shanye robar ruwa guda daya amma shakuwar bata barshi ba, nan kuma nadiya tasan abin nashi ba karami bane,
"Wai baka sha ruwan ba?"
"Wallahi nasha, roba dayafa na shanye baby"
"Ohh to zata daina"
Shiru yayi mata yaci gaba da shakuwarsa zuwa can sai yaji ta tsaya yadaina yi kwata kwata,
"Tunda kadaina shakuwar to saida safe ni bacci nakeji"
"To baby saida safe, i love you"
"Uhhhum"
Katse wayar tayi ta turata karkashin pillow, dariya ce ta subuce mata lokacin da ta tuno amadi,
"Yaro yasha tafi karfin cikinsa, maganinka ai" tafada tana dariya, nan bacci ya dauketa tayi abinta cikin kwanciyar hankali shikuwa bawan Allah yana can yakasa bacci sai juyi yake yi saboda kewar matarshi data dabaibayeshi.
Washe gari da safe nadiya ta sake kiranshi da sabon sim din da ta siyo nan yaki dauka tayita kira amma bai dauka ba daga karshe sai ta tura masa da massage cewar ita masoyiyarshi ce kuma sonshi take, ko takan text din baibi ba bare ya turo mata da reply,
Hakura tayi ta rufe sim din tunda taga alamun kamar bazai kulaba ai kuwa bai kula dinba shi duk da bai san wacece ba bata burgeshi ba domin mace daya ce kacal ke burgeshi a duniya itace nadiya kuma ya rigada ya mallaketa,
Kiranta yayi awaya lokacin tana kitchen tana soya miya, fadeela ce takawo mata wayar tana yimata surutu,
Karba tayi ta kara akunnenta,
"Baby yakike?"
"Lfy lau"
"Yau banji kiba, kina lafiya?"
"Lafiya lau"
"Ya twins dina?"
"Lafiya"
"Me kikeyi yanzu?"
"Aiki nake"
"Nikuma kin ganni nadawo gida duk agajiye da ace kina kusa da kinyi min tausa ko?"
"Uhmm" tafada tana juya miyar da takeyi,
"To yanzu me zaki bani duk da bakya kusa?"
Shiru tayi batayi magana ba,
"Baby"
"Na'am"
"Kice you love me"
"Dan Allah kayi hakuri basai nafada ba"
"Why? Gaskiya bazan hakura ba har sai kin fada sannan kiyi kissing dina.."
"Ka manta jiya ko?" Ta fada afili amma acikin zuciyarta cewa take "babu abinda zanyi maka bare ka cika min kunne da wannan shakuwar taka da ajiyar zuciya"
"Baby yi mana ina jinki.." Taji yafada a marairaice,
Daga murya tayi tace "na'am mama, to gani nan"
Jin haka yasashi rabuwa da ita saboda a tunaninshi mama ce ke kiranta,sallama yayi mata ya kashe wayar anan ta ajiye wayar taci gaba da aikinta. Tun daga wannan lokacin duk sanda ya kirata aikin da yake sakata kenan amma sai taki sai taji yana neman barinta da Allah sannan sai tayi amma kuma da zarar tafara zataji ya dameta da ajiyar zuciya ko shakuwa shiyasa ma bata son ta rinka biyeshi tana yimishi abinda yasata din,
Daren yau kam akalla sai da ya shafe awanni biyu yana wannan shakuwar,duk rashin tausayinta akanshi yau sai da taji yabata tausayi wanda bata san dalili ba,
"Sannu Ahmad.."
"Yawwa baby"
"Kasake shan ruwa"
"To baby"
Tana jinshi yana shan ruwa amma koda ya shanye sai yaci gaba da shakuwar, dakyar yasamu ya daina,
"Baby da zaki yarda da na turo miki kudin jirgi kin biyoni"
"Ka manta alkawarin da kayine? Idan na biyoka me zanyi maka?"
Ajiyar zuciya ya saki mai karfi,
"Kuma fa hakane, sorry mantawa nayi"
Jin yadaina shakuwar yasashi yi mata sai da safe ya katse wayar.
Akwana atashi har amadi ya kwashe watanni 8 a kasar london wanda yanzu har yafara lissafin dawowa,ita kam nadiya basu koma makaranta ba saboda yajin aiki da aketa gudanarwa,duk abin baiyi mata dadiba domin bata son ta tare bata gama makaranta ba,
Shiryawa tayi ta tafi sumaila gidan umman sumaila bayan ta sanarwa da amadi dama shi ba hanata fita yakeba daga tace zataje wuri kaza zaice adawo lafiya babu ruwanshi da yimata kulle,
Lokacin da taje gidan umman sumaila, umman murna tayi sosai da ganinta saboda dama tanada niyyar zuwa ranon itama domin kayan gyaran da tasa aka tanada musamman saboda nadiyan,tunda takai kanta kuwa nan umman ta shiga tula mata abubuwa, wasuma bata taba saninsu ba bare ganinsu,
Shikuma dan nacin nata akoda yaushe yana tareda ita a waya, ko abinci yake ci sai ya kirata kome yake yi sai ya kirata,
Sabon sim din da ta saka domin kiranshi kuwa harma ta daina kiran saboda baya dagawa ita abin har daure mata kai yayi.
Gyara na musamman umman sumaila ke yimata baji ba gani, ita duk ma tagaji da dure duren da ake yimata gashi umma ta hanata tafiya, ita da taje da niyyar sati uku saida ta shafe fiyeda sati shida har saida akace an janye yajin aiki sannan umman ta kyaleta ta tafi amma tace zata rinka yi mata aike kuma lallai lallai duk abinda aka kai mata tayi amfani dashi,
Tana komawa gida tafara shirin tafiya makaranta saboda Allah Allah take yi tagama makarantar kafin amadi yadawo amma tasan hakan ba mai yiyuwa bane tunda shi yanzu saura watanni biyu kacal yadawo.
Sai da ta tanadi komai na bukata sannan ta tafi wudil can dinma dai da kayayyakin umman sumaila ta tafi wadanda yanzu har ta saba dasu,
Kan karatunta ta mayar da hankali sosai, koda wanne lokaci amadi yana kiranta, wata rana ai fada wata rana ayi dadi kun san halin mutuniyar taku da taurin kai, amadin ne kadai ya iya da ita saboda shi mai hakuri ne sannan bashida riko domin ko fadan akayi ba ayin minti biyar zai sake kiranta nan zai shiga lallashinta yana bata hakuri koda kuwa shi dinne da gaskiya, yawancin fadan ma shine mai gaskiyar amma sai yayi hakuri ya dauki laifin ita yabata gaskiyar yayita rarrashinta yana bata hakuri har sai ta hakura, ita kanta ta san yana tsananin sonta kawai dai zuciyarta ce har yanzu bata sauko ba daga fushin baya.
Yau da gobe babu wahala awurin Allah domin amadi har ya kammala abinda yaje yi yafara shirye shiryen dawowa, wani boutique yashiga ya rinka jibgowa nadiya sexy dress, duk kayan da ya siyo mata babu wanda zata iya sakawa ta fita koda tsakar gida sai dai adaki domin kayane na garari,
Koda wasa bai fada mata dawowarshi ba shiru yayi mata, kullum yana yi mata waya kamar yadda ya saba amma ranar da zai dawo sau daya ya kirata daga nan sai bata kara jinshi ba.....
*_Ummi Shatu_*
[9/11, 9:22 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
_Kuna ina? A'isha chuchun gaye, A'isha Dansabo, A'isha Gambo, A'isha (Maman khadija),A'isha (mom minal) wannan shafin nakune takwarorin Ummi Shatu.._
*61*
aishaummi.blogspot.com
*K*asancewar shigowar yamma yayi sai bai samu zarafin kiranta da wuri ba,
Yana ajiye jakarshi ya nufi part din da aka gina musu shida nadiya domin baya son asamu kuskure daga yanda ta zana,
Part din ba karamin kyau yayiba amma babu abinda aka zuba na furnitures, yanda nadiya ta zana haka akayi shi babu abinda aka sauya,
"Wowwww.." Yafada bayan ya zira hannuwanshi acikin wandon jeans dinshi,sai da yabi ya dudduba ko ina sannan yafito yakoma part din hajiya,
"Autana ina kaje ne inata nemanka, kazo kayi wanka kaci abinci mana"
Hajiya dake tsaye cikin falon ta fada,
"Hajiya part din baby naje nagano, bana sone ayi mata ba yanda ta zanaba asamu problem, amma naga komai yayi daidai.."
"Ohhh autana da rawar kai kake, tunda ka dawo ai sai akawo maka ita ku tare kowa ya huta"
"Yawwa hajiya dan Allah kisa baki nanda 2 weeks ta tare.."
"To shikenan autana, yanzu dai shiga dakinka kayi wanka kafito kaci abinci, nayi maka mutumin naka wato tuwo"
"Woohhhhh" yafada harda dan tsallenshi sannan yawuce dakinshi.
Nadiya kuwa koda taji amadi shiru bata kawo cewar yadawo ba kuma bata kirashi ba, har dare yayi shiru bata jishi ba,
Bayan ta kwanta ne misalin karfe 9 sai ga kiranshi koda ta duba ba number din waje bane dan haka taji mamaki ya kamata,
"To shi wannan ya haka?" Ta tambayi kanta tareda kara wayar acikin kunnenta,
"Baby.."
"Uhmm"
"Shine ko ki nemeni ko bayan kuma kinji ni shiru"
"To ai nasan lafiya kake tunda najika shiru"
"Hakane, to nadawo dazu, yaushe zaki zo yimin sannu da zuwa?"
"Kadawo?"
"Wallahi nadawo baby"
"Sannu da dawowa"
"Yawwa yaushe zaki zo kiyi min sannu da zuwa? Ko nine zanzo?"
Shiru tayi tana tunani,
"Sannu da zuwa kuma? Bayan wanda nayi maka yanzu"
"Haba baby yanzu ai ba sannu da zuwa kika yimin ba, idanuwana fa suna bukatar ganin fuskar matata ko kin manta yau rabona dake 11 months da yan kwanaki akai? Allah ina son ganinki.."
"To yanzu ya kakeso ayi?"
"So nake kizo gobe, zan turo driver ya daukeki, wallahi son ganinki nakeyi"
"Allah ya kaimu goben idan banida uzuri da yawa to"
"Insha Allah ma bakida shi baby"
Dakyar dai yasamu ya dan lallasheta ya shawo kanta harta amince cewar zataje din nan yayi mata sallama ya katse wayar saboda bacci yakeji.
Washe gari kuwa koda ya kirata saida ta gama jan ajinta sannan tace yaturo drivern, shidai ta inda take so tanan yake binta, lallabata yakeyi saboda baya son taki amincewa da zuwan,
Wurin 12 daidai na rana suka karasa gidan, iya hajiya ta tarar a babban falonta ita da mai aikinta, hajiyan tana sanye da glass a idonta suna shirya bit,
A kunyace nadiya ta shiga cikin falon,cikeda murna gamida soyayya hajiya ta tarbeta,kai idan ba sani kayiba bazaka taba cewa hajiya surikarta ce ba saboda irin tarbar arzikin da tayi mata,
Lokaci kankani aka cikata da kayan marmari gamida kayan jika makoshi, jin bataji motsinshi ba yasa ta fara kiranshi awayarta amma kuma wayarshi akashe,
Ta jima zaune afalon itada su hajiya lokaci lokaci hajiya tana dan yimata hira har tsawon mintuna 20,
"Autan yana dakinshi yanata faman bacci tashi ki shiga" hajiya tace da ita tana murmushi,
"Wai dama komawa yayi?" Mai aiki ta tambayi hajiya tana dariya,
"Kema kuwa ai kin san halin auta da shegen baccin safe sai yakai azahar yana baccin nan, aida ya fito sake komawa yayi.."
Ita dai nadiya tana zaune bata tashiba har saida hajiya tasake ce mata ta shiga sannan ta tashi akunyace ta nufi dakin nasa,
Ahankali ta bude ta shiga,nan wani kamshi mai dadi ya doki hancinta wanda ya gauraye da sanyin air condition din dake sanyaya dakin,dakin ya tsaru mutuka kamar dakin mace,
Kwance ta hangoshi akan gadonshi daga shi sai gajeren wando da round neck t shirt sai sharar bacci yake yi abinshi batare da damuwar komai ba,
Karasawa tayi zuwa bakin gadon ta zauna, tashinsa tafara yi,
"Ahmad.... Ahmad" ta kira sunanshi ahankali,
Ko motsi baiyi ba bare yasan tanayi, hannu takai jikinshi tafara dan dukanshi,
"Ahmad..."
Idonshi ya bude wadanda suka yi ja saboda tsabar bacci,
"Uhm uhmmm baby..." Yafada yana kokarin tashi zaune, bata ankara ba kawai sai ji tayi ya rungumeta,
Binta da kallo yakeyi sosai domin ba kadanba ta canja mishi, kamar yadda itama take ganin ya sauya sosai, dama shi farine sosai to farinshi na yanzu yafi nada sannan ya danyi yar kiba amma ba mai yawa ba,
Shi kam ganin nadiyan shi yayi ta cika sosai tako ina, wata atamfa ce kalar purple ajikinta,dinkin ya zauna daram ajikinta, riga da skirt, sannan tayi simple daurin dan kwali tana sanye da wani gyale shima purple colour,
Jikinta take kokarin janyewa bayan ta bata fuska,
Riketa yayi kam yana murmushi nan yafara kokarin lalubar bakinta amma taki tanata faman kawar da kanta, murmushi yayi,
"Baby nadawo zamu fara ko? Za afara yimin rowar da aka saba..."
Ganin taki yarda yasashi fara kissing din wuyanta, tureshi tafara yi har tasamu nasarar tureshi din ta matsa gefe,
Kallonta yayi fuskarshi dauke da murmushi baiyi fushi ba yasake matsawa kusa da ita nan ta matsa shima yasake matsawa,
"Dama dalilin da yasa kasa a daukoni kenan?"
"A'a baby ba dalilin kenan ba but kin san dai nayi missing dinki da yawa shiyasa..."
"To nidai gaskiya a'a.." Tafada tana zumbura bakinta,
"Baby pls karkiyi min haka.."
Dauke kanta tayi, ya bude bakinshi kenan da niyyar yimata magana yafasa saboda tarin da ya sarkeshi nan yafara yinshi babu kakkautawa,
Juyawa tayi ta kalleshi,
"Sannu"
Kai ya daga mata kafin yafara shakuwar da yasaba,
"Indauko maka ruwa?"
Hannunta ya kamo yajata jikinshi, yanzu kam maganar daru takare tunda taga halin da yake ciki, shiru tayi tai luf ajikinsa amma har lokacin wata irin shakuwa yake yi k'wat,
Bakinta ya luluba da nashi cikin doki abin mamaki ko minti daya ba ayiba taji yadaina shakuwar,
"Nikam yau nashiga uku kuma" tafada acikin zuciyarta,shikam amadi tunda har yasamu dama bai tsaya awuri daya ba.
Sai da yaji nutsuwarshi ta dawo mishi sannan ya kwantar da ita ajikinshi,
Hannunta Yakama acikin nashi,yafara yi mata rada akunnenta,
"Baby ga maganin shakuwar awurinki amma da zakice wai zaki dauko min ruwa..."
Murmushi ya sake yi yana kallon fuskarta, idanuwanta arufe fuskar nan gata nan dai babu yabo babu fallasa,shi gaba daya yarasa nadiya wacce irin macece wadda bata da saurin manta abu koda yake yasan sai ahankali zata manta da wulakancin kabeer har takarbi soyayyarshi domin dauriya da hakurin da tayi ba kowacce mace ce zata iyaba,
Kissing din wuyanta yayi sannan yafara jan dan kwalin kanta nan tarike hannunshi,
"Karka cire min dan kwali.."
"Saboda me?"
"Kawai"
Murmushi yayi, "baby rigima, badai kawai ba,ina son ganin kalar kitson dake kan matata ne"
"Ni babu kitso akaina"
"To zan gani haka"
Juyi tayi zata matsa daga jikinshi yayi saurin rikota ya mayar da ita,
"Baby dadina dake rikici kuma rikicin ma narashin gaskiya, inbanda haka nida mallakina amma ahanani?"
Saida ta zunbura masa baki sannan ta bude da niyyar yimasa magana, ruf ya rufe bakinta da nashi, neman kwacewa tafara yi amma kuma takasa dolenta ta hakura domin yau tasan ita takawo kanta gareshi,
Idonshi dake lumshe ya bude ya kalleta, mayar da kanshi yayi saman kirjinta ya kwantar yana sauke mata ajiyar zuciyar da yasaba yi mata awaya,
"Ka matsa zan tashi" tace dashi tana dan harararshi,
Baiyi mata magana ba illa kankameta da yasake yi,
"Nace ka matsa zan tashi.."
Nan dinma shirun yayi mata sai wata ajiyar zuciya da yake ajiyewa ahankali,
"Ai da nasan haka ne da bazan zo ba, daga zuwa na shikenan kuma kawai...." Hannunshi yakai ya rufe mata baki,ture hannun nashi tayi,
Baice da ita komai ba saida yagama sauke ajiyar zuciyarshi sannan yajuya kanshi akan kirjinta yana murmushi,
"Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki baby, karfa ki manta raboda dake shekara guda kenan kuma yanzu zuciya taga abinda take so take kauna sannan take bege bazata yi wani feelings ba?, wallahi wannan sakonnin badaga gareni bane daga zuciyata ne, ita keso itake muradi.."
Hannunshi yakai saman kirjinta nan ta buge hannun,yasake mayarwa ta sake bugewa yasake mayarwa ta kuma bugewa,
"Idan kika sake buge min hannu ban yafe miki ba har lahira.."
Ta inda yake cin galaba kenan idan ya hadata da Allah, tana ji tana gani dole ta rabu dashi tunda yace bai yafeba idan tasake buge masa hannu,
"Allah nan gaba ko kace inzo bazan zo ba" tafada kamar zata saka kuka,
Kiyi hakuri.." Shine abinda ya iya cemata, shiru tayi masa ta dauke kanta,
Har lokacin sallar azahar yayi suna nan tare ita dai nadiya duk yagama takurata, dan tureshi tayi,
"Dan Allah kabari ni fita nake son yi"
"Ina zakije inda yafi nan?"
"Wurin hajiya zanje.."
"A'a, ita hajiya babu ruwanta da dadewarki anan tunda tasan wurin mijinki kika zo sannan yadade bai ganki ba..."
"Nidai dan Allah kabarni intafi"
"To zan barki amma sai kinyi kissing dina sau 30"
"Gaskiya a'a" tace dashi tana zunburar baki,
"To narage miki kiyi guda 20"
"A'a"
"Allah sai kinyi, fara tun kafin mala'iku su fara tsine...."
Tashi tayi tana harararshi fuskarta babu fara'a, nan tafara abinda yace ta shiga kissing din bakinshi mai dauke da jajayen lips,
"Ai nayi sai anjima kaga tafiyata"
Daukar mayafinta tayi da dan kwalinta ahannu saida taje bakin kofa sannan ta tsaya tafara daura dan kwalin,
"Bari nataso..." Taji yafada ba shiri ta bude kofar da sauri zata fita, dariya taji yayi, toilet ya nufa yana cewa,
"To da wasa nake yimiki.."
Duk da haka dai bata koma cikin dakin ba falo tawuce wurinsu hajiya, hajiyan na kokarin tashi nadiyan tafito bedroom dinta ta shiga mintuna kadan ta leko tace nadiya ta shiga tayi salla.
Amadi kam cikeda farin ciki yayi wanka ya fito yayi salla sannan yasa kayanshi ash colour din t shirt da yellow din rubutu ajiki manya anrubuta _FUN TIME_ sai yellow colour din trouser, hatta belt din da ya daura yellow colour ce, turarenshi na axe yafesa sannan ya fita, fitarshi tayi daidai da fitowar su hajiya itada nadiya,
Kan table suka wuce direct amadi sai kallonta yake yana yi mata murmushi amma ita taki koda kallonshi ne, hajiya diban abincin ta tayi a flate tabasu wuri ta nufi falo taje tayi zamanta tana kallon labarai a CNN,
Matsawa yayi kusa da ita ya dauki flate ya zuba musu jalop din couscous wanda yasha hadin kayan lambu yayi kyau sosai,
"Kaga ka kori hajiya daga nan" tafada tana kallonshi, dan lips dinshi ya lasa,
"Baby bani fa nakoreta ba, kawai dai tabamu wuri ne..."
Bata sake magana ba tayi shiru, abincin yafara diba yana bata shima yana ci amma yasha daru da rigimarta kafin ta yarda taci abincin, diba yake a spoon ya bata idan ta diba taci sai yaci wanda ta rage acikin spoon din,
Suna tsaka da cin abincin anty siyama tayi sallama zee kanwar mijinta na biyeda ita cikin wata shiga ta alfarma.....
_Get well soon luvly sister @Khairat Dandawaki_
_Fatan alkhairi agareki stylish bitch_
_Gaisuwa mai yawa ga duk masoyan anty amadi... Musamman kawata maryama qaumi_
*_Ummi Shatu_*
[9/12, 9:50 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*62*
aishaummi.blogspot.com
*T*un daga nesa zee ta kafe amadi da ido tana kallonshi domin ba karamin kyau yayiba, yayi mutukar tafiya da hankalinta gamida tunaninta gaba daya cikin lokaci kankani,
Dan kallon nadiya tayi nan ta fahimci itace matar shi dan haka tayi saurin dauke idonta daga gareta ta mayarshi kan amadi,
"Anty amadi duri aketa yine haka?" Anty siyama tafada fuskarta dauke da fara'a tana faman karkada key din motarta dake hannunta,dago da kanshi yayi shima fuskarshi dauke da fara'a ya kallesu, saida gabanshi ya dan harba sakamakon ganin zee da yayi domin bai so ganinta ba kwata kwata a wannan lokacin saboda yasan zaiyi wahala idan batayi abinda zai b'ata mishi shirinshi ba,
Kallonta yayi sosai tayi kyau cikin wani dark blue din material dinkin doguwar riga, fuskar nan sai sheki takeyi saboda kwalliyar da tasha, kanta daure da wani hamshakin gwaggwaro, tamkar wacce zataje dinner ko kuma zaben sarauniyar kyau, dan mayafinta kuwa akafadarta guda daya kawai ta ajiyeshi batare da ta koda yafashi ba,
Saida yasakawa nadiya abinci abakinta sannan yayiwa anty siyama magana,
"Kai anty dan Allah, wai ya akayi kika daina fadin yayan ne.."
"Saboda kai ba yayana bane..."
"Sannu da zuwa anty siyama" nadiya tafada wadda maganarta ce ta katse hirar anty siyama da amadi,
"Yawwa amaryar mu, har anzo tarbar angon ne?"
Sunkuyar da kai nadiya tayi tana murmushi abinta cikin kunya,
"To ba dole ba, aini dan gatane.."
Dariya anty siyama tayi tajuya tawuce falo wurin hajiya, ita kuwa zee tana tsaye rikeda waya a kunnenta tana magana ahankali sai wani kashewa amadi ido takeyi,
Koda wasa bai nuna ya santa bama bare nadiya ta kawo wani abu acikin ranta, ci gaba da bata abincin yayi har suka cinye wanda ya zuba musu,
Cikeda yanga da jan aji zee tabar wurin itama ta nufi falo batare da tayiwa amadi magana ba,
Kallon nadiya yayi, "baby akara abincin ko kin koshi?"
"Nakoshi"
Murmushi yayi ya tsiyayo juice acikin glass cup yakai saitin bakinta nan ta sha sannan ya tsiyayi ruwa yabata,
"Baby anya yau ma baki sa nayi over feeding ba, kinga nakasa motsi..."
Hannunta ya kamo ya mike tsaye nan itama ta tashi suka nufi falo, suna zuwa daf da falon ta fincike hannunta daga cikin nashi, juyawa yayi ya kalleta,
"Haba baby..." Yaceda ita tareda langabe kanshi gefe guda,
"To ahaka da kakeso muje wurinsu hajiyan.. " tafada tana harararshi,
"Ehhh mana" yaceda ita da nufin tsokanarta,
"Wallahi a'a"
Janta zuwa jikinsa yayi nan tasa iya karfinta ta tureshi,
"Kai kika ture ni? Kamota nan..."
Da sauri tayi wuf ta fada falon tabarshi atsaye awurin yana yimata dariya, duk abin nan dake faruwa akan idon zee yafaru nan taji zuciyarta tayi baki saboda tagama kwallafa ranta akan amadi sannan tana mutuwar sonshi shiyasa lokacin da anty siyama tace mata yayi aure haukane kawai batayi ba,
Kusa da anty siyama nadiya taje ta zauna tana gaidata nan suka gaisa kowannensu fuskarshi asake,
Cikin falon yakarasa hannunshi rikeda robar ruwa yana sha, akusa da nadiya ya zauna,
"Autan hajiya ansauka lafiya ?"
"Lafiya lau anty.."
"Ai dama nace bari muzo sannu da zuwa tunda wuri kafin mu shiga bakin list"
Dariya ya danyi ya kalli zee wacce tawani kafeshi da ido ko kifatawa bata yi,
"Ashe dai kema kin san idan baki zo dawuri ba hajiya zatayi fushi dake.."
Dariya hajiya tayi "auta abin harda su fushi kuma"
"To hajiya ai duk wanda baizo ba ya cancanci fushinki.."
"To wannan kuma da hamida kake itada anty Dija yaro tunda nikam nazo"
Murmushi yayi ya kalli nadiya, "baby ga ruwa"
"Girgiza masa kai tayi, nifa tafiya ma zanyi.."
"Ko zaki tafi sai munje kinga part dinki tukunna, taso muje kiga"
Ayanda suke maganar babu wanda yajisu balle yasan abinda suke cewa, mikewa yayi itama tatashi, kallonsu anty siyama tayi,
"Matar auta sai ina?"
"Anty ginin gidanta zan kaita tagani"
Murmushi anty siyama tayi, "dakyau autan hajiya"
Bai jira komai ba yajata suka fice daga falon, kallon zee anty siyama tayi,
"Zee muma zo muje mugani, nifa kullum ina gidan nan amma ban taba zuwa Nagani ba"
"Ai kuwa dai kuma kuje ku gani kar ayi babu ku" inji hajiya,
Mikewa sukayi suma suka fita suka marawa su amadi baya,
Su amadi na fita daga cikin falon ya dubi mutuniyar tashi,
"Baby yanzu fa idan akace kije can acikin 5 minutes bazaki iyaba..."
"Ehhh saboda ga giwa ko"
Kafadarta ya sakalo hannuwanshi akai ya karata da gefen jikinshi,
"To tunda kina tantama mu gwada mana, wallahi tsaf zan rigaki zuwa.."
"Ni babu wani gudu da zanyi yanzu"
"Allah sai kinyi, tsere zamuyi so get ready..."
"Gaskiya ni kana wahalar dani"
"Yi hakuri muyi, idan kuma kinki kin san sauran kawai zan barki da Allah ne"
Sakinta yayi ya sunkuya,
"Get ready, 1...,2...,3..."
Gudu yasa yayi gaba yabarta, badan tasoba ita dinma tabi bayanshi aguje, saida ya karasa ya tsaya sannan ita kuma ta isa tana haki,
Sunkuyawa tayi ta dafa gwiwowinta saboda har ta dan gaji a wannan gudun da tayi,
Dago da ita yayi yadauketa abayanshi yayi ciki da ita,
"Baby ke raguwa ce, daga yin dan wannan gudun shine zaki fara yimin haki kamar wacce ta shekara tana gudu..."
Lumshe idonta tayi har lokacin tana gadon bayanshi agoye,
"Dama ai nafada maka wahalar dani kawai kake son yi.."
"Ba wahalawar bane baby, kidai shirya domin agidan nan kullum nida ke sai munyi wasan tsere.."
"Gaskiya bazan iya ba kuma zai iya saka min ciwon kirji.."
"To naji, amma daga bedroom zuwa falo fa?"
"Shima bazan iyaba"
Murmushi yayi yasake rungumeta,
"To acikin daki fa akan bed..."
Shiru tayi saboda ta gano Inda maganar tashi tasaka gaba,
Kitchen yafara kaita har lokacin bai sauketa ba tana bayanshi,
"Nayi miki magana kinyi shiru ko?"
Nan dinma shirun tayi masa amma kuma ta bude idonta tana kallon irin dukiyar da aka zuba acikin kitchen din, komai na amfani da wuta gashi nan burjik abun ba acewa komai, suna kokarin fita daga cikin kitchen din su anty siyama suka shigo, saurin sauka tayi daga bayanshi cikeda kunya, ita anty siyama ma sam bata luraba amma zee ita taga lokacin da nadiya ta sauka daga bayanshi,
Nan suka rankaya gaba dayansu suka fara zagaya dakunan da dukkan sauran wuraren dake cikin part din,
Wani pipe amadi ya hango tawaje nan yabi ta dan corridor din dake tsakanin falon da dakin shakatawa yafita,
Dama zee alla alla take ta kebe dashi dan haka ta faki ido tabishi, yadawo kenan zai shigo sai gata adaidai corridor din tana rikeda kofa tana kallonshi, ja yayi ya tsaya yana dubanta,
"Zee ya akayi kuma?"
"Amadi bakayi min adalci ba, ka cutar da zuciyata ka wahalar da ita bayan kuma kasan irin dunbin son da take yimaka..."
"Zee kiyi hakuri kinga yanzu ina tare da wife dina bana son ta zargi wani abu.."
Sakin kofar tayi ta taka ahankali ta karasa gareshi idanuwanta suna zubar da kwalla,
Tana zuwa batayi wata wata ba ta fada jikinshi ta rungumeshi, shikuma ganin halin da take ciki sai bai hanata ba yakyaleta dan ko zata samu sassauci acikin zuciyarta domin shima yasan so yasan zafinsa kuma yasan dafinsa musamman ma idan kai keson mutum shi baya sonka,
Hannuwanta ta sakala ajikin wuyanshi hawaye na malala akan kuncinta,
"Wallahi Ahmad kaine namijin da nake so arayuwata, ina jin sonka har cikin jijiyoyin jikina..."
"Zee kiyi hakuri, shi aure mukaddari ne.."
"Nidai ina son ka aureni, nayarda zan zauna da matarka..."
Daidai lokacin nadiya ta nufo wurin domin ta hango wasu shuke shuke abaya wadanda suka yi mutukar jan hankalinta,
Cikeda tausayawa amadi ke kallon zee musamman ma da yaga tana kuka, dagoda idonta tayi ta kalleshi, batayi wata wataba ta manna bakinta kan nashi,
Nadiya da tafito dan zagayawa baya nan idanuwanta suka gane mata amadinta rungume da zee bakinshi kan nata......
*_Ummi Shatu_*🏻
[9/14, 8:59 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin K'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_
_Gaisuwa ta musamman ga aminiyar kwarai cwt KAUSAR LUV.._
_Fatan alkhairi ga STAR GIRL.._
*63*
aishaummi.blogspot.com
*C*ikin kissa da jan hankali zee tafara kissing din bakinshi,
Tsaye nadiya tayi tana kallonsu gabanta yana faman dukan uku uku, jikinta har wani rawa yake yana tsuma, bazata iya tantance yanayin da take cikiba saboda rudun da ta shiga,
Kamar ance ya kalli wurin da nadiya take nan ya hangota tsaye babu shiri yayi azamar ture zee daga jikinsa hankalinsa atashe,
Tun kafin ya ture zee daga jikinsa nadiya ta juya tabar wurin cikin tashin hankali,
Baibi takan zee ba ya nufi wurin da nadiya ta nufa har yana cin tuntube, shi kansa yasan yayi kuskure da har yabar zee ta rungumeshi tayi kissing dinshi yanzu yasan gaba daya plan dinshi yagama rushewa sannan nadiya dakyar idan zata amince dashi har ta soshi tunda ada ma ya aka kare,
"Baby... Baby..." Yakira sunan nadiya wanda har yana hadawa da dan gudu akan saurin da yake yi,
Ko sauraronsa batayi ba ta nufi part din hajiya, sauri ya kara akan wanda yake yi da,
"Baby dan Allah ki tsaya kiji, dan Allah.."
Ko kulashi batayi ba illa tafiyarta da taci gaba dayi,
"Baby..." Yafada yana biye da ita cikin sauri wanda har yana buge kafarshi da wani katon dutse amma baiko tsaya ba duk da irin zafin radadin da yaji yana shiga cikin kafar tashi,
Jan kafar tashi ya rinka yi tana yimasa zugi da haka har ya cimmata, gyalenta ya riko nan ta tsaya cak batare da ta jiyo ba,
"Baby dan Allah ki tsaya inyi miki bayani.."
"Bayanin me? Bayan abinda idona ya gane min harda sauran bayanin da zakayi min? Ai shi bayani ana yinshi ne a inda ba aga zahiri ba amma yanzu ni babu bayanin da nake bukata daga bakinka tunda idanuwana sun gane min komai..."
"Ohhhh my God! Haba baby karki bari shaidan yayi tasiri acikin zuciyarki.."
Juyawa tayi ta kalleshi idanuwanta sunyi mutukar ja kamar wacce ta jima tana kuka,
"Idan ni ban bari shaidan yayi tasiri agareni ba kai ai kadade da barinshi yayi tasirin agareka tunda har ka iya rungumar matar da bataka ba kuma baka tsaya a iya nanba har saida ta kaika ga shan bakinta, shiyasa nabaku wuri ai kuje ku karasa abinda kukayi niyya..."
Gabanshi ne yayi mutukar faduwa nan take zuciyarshi ta harba saboda jin abinda tafada badai zarginshi da neman mata nadiya takeyi ba? Tambayar tazo cikin kwakwalwarshi batare da ya shirya ba,
"Baby dan Allah karki yimin zargin zina ko neman mata wallahi tallahi haka bai taba faruwa daniba, wallahi ban taba rungumar kowacce maceba sai ke itama wannan din wallahi yaune hakan tafaru dan Allah ki tsaya ki saurareni..."
"Yayi kyau kuma ni dama bance kana aikata zina ba, sakar min mayafi zan tafi.."
Sake rike mayafin nata yayi sosai ya matsa kusa da ita nan taja baya da sauri kamar wacce taga wani abun tsoro,
"Baby, baby karki yimin haka dan Allah, dan Allah ki saurareni kiji abinda zan fada miki, wallahi kece mace tafarko da nafara romancing kuma wallahi bayan ke ban taba gwada yi da wata maceba, wallahi yau ma bada nufin naji dadi ko wani abu makamancin haka nayi ba.."
Tana niyyar bashi amsa kenan ta hango su anty siyama da zee suna tahowa dan haka tayi shiru ta dauke kanta,
"A'a anan kuke tsaye..." Anty siyama tace dasu daidai lokacin da sukazo daf dasu,
"Ehhh anty" amadi yafada yana kallon fuskar nadiya,
"Wallahi wuri yayi kyau Allah yasanya alkhairi yasa wurin zamanta ne har abada..."
"Amin anty" ya amsa mata still dai idonshi nakan nadiya,yana rike da mayafinta tamau,
"Amaryar mu yaushe zaki tare to?"
Murmushin dole nadiya ta kakalo tayi amma batace komai ba,
"Anty sai nanda 3 weeks" inji amadi,
"Ato Allah yakaimu"
Wucesu sukayi zasu shige nan zee ta kalli nadiya, itama nadiyan kallonta tayi idanuwanta jajur, wani dan malalacin murmushi zee ta jefeta dashi sannan ta dauke kanta,
Saida taga shigewarsu anty siyama cikin part din hajiya sannan ta dubeshi,
"Nifa kaga duk tawa mai sauki ce, nidama ba wai sonka nake ba bare abinda nagani ya dameni, sannan dama ni banyi trusting dinka ba bare nace kayi disappointing dina,kula yanmata dai dama halinka ne shiyasa yau Allah ya toni asirinka..."
"Ohhh God" yafada tareda dafa goshinsa,
"Sakar min mayafi zan tafi.."
"Baby yanzu ni zaki yiwa haka?"
"Akan me bazanyi maka haka ba? Ni bakaga abinda kayi minba? Tafiya zanyi yanzu inbaka wuri gata can kaje ka dauketa kutafi inda kuka saba zuwa..."
"Baby wai meyasa kike yimin kallon dan iskane? Meyasa kike yimin kallon mazinaci?"
"Saboda halinka ne..."
"Halina?"
"Ehhh tunda gashi naga alamu da idona, da ai nunawa kayi baka santa ba saida kabari kuka kebe sannan...."
"To ya isa haka, naji ni mazinaci ne kuma halina ne nasaba...." Yafada tareda sakar mata mayafinta, tafiya tafara yi yana biye da ita abaya har suka shiga falon hajiya,
Dukkaninsu suna zazzaune suna faman shan dariyar wani film da akasa a African magic mai suna Jennifer's diary,
Wurin hajiya nadiya taje tace zata tafi nan hajiya ta kalleta cikeda mamaki domin ta zaci kwana zatayi,
"Dama ba kwana zakiyi ba?"
"Ehh hajiya saboda inada lectures gobe da sassafe.."
"To ai shikenan, Allah ya taimaka yabada sa'a" hajiya tafada bayan ta mike zuwa cikin bedroom dinta, wata leda ta dauko cikeda kaya ta bata, dakyar ta karba duk da tayi kokarin boye damuwar dake kan fuskarta,
Sallama tayiwa anty siyama ta fita ko kallon inda zee take batayi ba,
Bin bayanta amadi yayi suka fita har zuwa compound din gidan nan ya kwallawa driver kira yataso da gudu yazo,
"Wudil zaka kaita.."
"To ranka ya dade.."
Daga ita harshi babu wanda yasake yiwa wani magana har ta shiga mota driver yaja suka nufi gate din fita, juyawa yayi ya koma falon hajiya yana jan kafarshi wadda yaji ciwo, shi kansa bai san meya samu kafar ba amma jinta yake tana yimasa wani zugi gashi kamar kumbura take yi,
Cikeda jin haushi sosai yake kallon zee, ko magana baiyi ba yanufi dakinshi yaje ya fada kan gado ya kwanta yana jin kamar ya zubar da kwalla ko zai samu saukin kuncin dake cikin zuciyarshi.
Tun acikin mota nadiya keson zubar da hawaye amma ta gagara saboda bata son drivern su amadi ya fuskanci akwai matsala, gaba daya jinta take kamar acikin mafarki,sai tambayar zuciyarta take wai dagaske amadi tagani yana rungume da wata budurwa?
Tsaki taja ta dauki wayarta tafara kiran mama, mama na dagawa suka gaisa nan tace ahada ta dasu fadeel mama tace basu dawo daga islamiyya ba sun tafi,
Amira tace ahadata da ita suna gaisawa tacewa Amira zata tura mata text massage yanzu saboda ahanya take,
Abinda yafaru ta kwashe gaba daya ta fadawa amira ta cikin text din, nan amiran ta dawo mata da reply tana bata hakuri sannan tace zasuyi waya idan ta sauka.
Amadi Amira ta kira bayan sun gaisa sai yaji tayi shiru,
"Amira lafiya kuwa?"
"Lafiya lau yaya Ahmad nakiraka ne ingaisheka dama ina fata kowa lafiya?
"Amira ba lafiya ba wallahi, nadiya ta burkice min kin san halinta sam taki ta karbi uzurina.."
"Yaya Ahmad mai yafaru?"
Babu abinda ya boye mata nan yafada mata dukkan abubuwan da suka faru babu tantama ko kadan amira ta yarda da bayaninsa domin tasan yana mutukar son nadiya dan haka zaiyi wahala yaci amanarta,
Hakuri amira tabashi sannan sukayi sallama, babu jimawa nadiya ta kirata ta inda take shiga bata nan take fita ba harda cewa bazata zauna da amadi ba sai ya saketa,
"Haba anty karfa ki manta yaya Ahmad yana sonki kuma lokacin da abun yafaru tare kuke, idan da ace yayi niyyar aikata hakan ai ina ganin da bazai yi ananba tunda yasan zaki iya ganinshi, wallahi ya rantse min da Allah akan shi ba halinsa bane kuma bada wata manufa yayiba... Dan Allah kiyi hakuri ki saurareshi"
"Haba amira taya zan saurareshi bayan da idona nagansu.."
"Duk da haka dai ki danni zuciyarki kitsaya kiji abinda zaice"
"Shikenan amira nagode"
Katse wayar tayi tafada kogin tunani ta kusa yarda kadan da kalaman amira amma kuma tasan halin maza na iya maida baki yakoma fari,
Tana zaune tarasa abinyi taji shigowar massage,
_Baby am so sorry, pls kidaina fushi dani dan Allah..._
Tsaki tayi ta mayar masa da reply,
_Malam kadaina rokona kar ka hadani da Allah, dama kawai halinka ne kariga da ka saba bin yanmata._
Reply ya dawo mata dashi,
_Wallahi ba halina bane, dan Allah ki yarda dani kinji baby_
Kyaleshi tayi taki mayar mishi da reply nan yafara kiranta amma taki dauka saida yayi mata 15 miss called amma taki dauka,
Jawo kafarshi yayi ya fito falo lokacin harsu anty siyama sun tafi sallama yayiwa hajiya wai zaije wudil yadawo ita kanta hajiya saida abin yabata mamaki saboda taga dazu nadiya tatafi,
Jan kafarshi yayi wacce ke sanye da silifas domin bazai iya saka wani takalmin gayuba,
"A'a auta ya naga kana jan kafa, zo mugani me yasamu kafar?"
"Hajiya bugewa nayi amma idan naje zanje aduba min ita"
"To Allah ya kiyaye"
Fita yayi ahaka ya shiga motarshi yayi mata key, dakyar yake iya taka motar saboda zafin da kafar keyi, lokacin da ya isa wudil makarantarsu nadiya kuwa tuni har kafar ta kumbura tayi suntum wanda shi kanshi saida abin yabashi tsoro,
Text ya tura mata,
"Ina cikin makarantarku ina jiranki, idan kuma baki fitoba Allah ya isa...."
Haushine ya kamata lokacin da taga text din nashi domin badan yayi mata Allah ya isaba idan taki fita to da babu abinda zaisa taje wurinshi, cikeda takaici ta dauki gyalenta ta fita fuska adaure cikeda fushi wanda ita kanta bata san dalilinshi ba....
_Fatan alkhairi ga yan groups din,Duniyar makaranta 1&2,Duniyar littattafan hausa, Zauren karatu,da sauran wadanda ban ambata ba, Ummi Shatu ta gaisheku kyauta._
*_Ummi Shatu_*🏻
[9/16, 7:53 AM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_
_Godiya mai yawa ga 'yan kungiyar haske writers association wannan shafin sadaukarwa ne agareku..._
*64*
aishaummi.blogspot.com
*Z*uciyarta ahargitse ta fita wurin amadi, fuskar nan tata babu walwala ko kadan bare alamun fara'a,
Zaune ta hangoshi acikin motarshi ya bude kofar sannan ya ziro kafafuwanshi waje,
Fuska adaure ta karasa jikin motar ta tsaya batare data kalleshi ba,
"Baby...." Yakira sunanta,
Wani kallo ta juya tayi masa sannan ta dauke idonta batare data amsaba,
"Dan Allah baby ki daure kiyi min uziri ki saurareni sannan ki yarda da duk abinda zan fada miki, da ace zee budurwata ce kamar yadda kike zargi da wallahi kin fahimta tunda jimawa, ni ba sonta nakeba itace dai ke sona ki tambayi anty siyama kiji, wallahi kawai tausayinta ne ya hanani taka mata burki daga rungumar da tayi min har kika zo kika samemu..."
Sake dauke kanta tayi bayan ta gyara tsayuwarta,
"Shine kawai abinda kazo ka fada min?"
"Shine.."
"To naji.."
"Dan Allah kiyarda dani shine kawai fatana.."
Wani malamine yazo wucewa a cikin motarshi wanda suke department daya da amadi, ganin amadi yasa malam munnir tsayawa tareda yiwa amadi hon,
Mikewa amadi yayi ya nufi wurin malam munnir yana dingisawa wanda kusan ma ko daga kafar bayayi illa janta da yakeyi sai lokacin nadiya ta kula da dingishi yakeyi,
Hannu yabawa malam munnir suka gaisa malam munnir yace,
"Yaushe agari?"
"Wallahi jiya jiyan nan.."
"Ok sannu da zuwa, yaushe zaka fara shiga aji?"
Dariya amadi yayi "sai nanda wani month din.."
"To Allah ya nuna mana agaida amarya.."
"Zataji"
Sake musabaha sukayi malam munnir yaja motarsa yayi gaba shikuma amadi ya nufi wurin nadiya,
K'afarshi ta zubawa ido tana kallo wacce ta kumbura suntum tana kokarin tsinka silifas din dake kafarshi,
Zama yayi ya dan kalleta,
"Kinga saboda kina fushi dani kafata tana yimin ciwo amma haka najanyota nataho wurin.."
"Ai dai banice na jimaka ciwon ba"
"Wallahi Allah kece sanadi, lokacin da nayita kiranki kika ki tsayawa lokacin ne naji wannan ciwon, ina jin targade nayi.."
"Allah sawwake.." Tafada kanta na kallon wani wuri,
"To zaki rakani agyara min?"
Shiru tayi batayi magana ba wannan ya tabbatar masa da cewar watakila idan yayi sa'a ta rakashi din, ATM dinshi ya dauka saiko wayarshi yafito daga cikin motar ya kulleta,
"Muje to..."
Kamar ba zataje ba sai kuma yaga tafara tafiya,
"Baby dan Allah ki tsaya ki rikeni.."
Tsayawa tayi batareda jiyo ba har yakarasa kusa da ita yana zuwa ya dafa kafadarta,
"Muje baby.."
Ahaka suka fara tafiya yana dafe da kafadarta duk inda suka wuce mutane sai sun kallesu musamman ma daliban makarantar wadanda ke farfajiyar cikin makarantar a wannan lokacin,
"Washhhh kafata..."
Taji yafada cikin raki, tausaya masa tayi ta rikeshi sosai ta hanyar zagayeshi da hannunta guda daya dayan hannun kuma ta rike hannunshi dake kan kafadarta, shi kansa yasan ciwon dake kafarshi ne yasata saukowa daga dogon fushin da tayi da wuri badan Allah ya rufa masa asiri yaji wannan targaden ba dako kallo bai isheta ba,
Da haka suka fita har gate suka tsaya suna jiran adaidaita sahu, suna nan tsaye suka samu ta taimaka masa ya shiga sannan itama ta shiga ta zauna,
Hannunta ya kamo ya rike cikin nasa,
"Hajiya ina zakuje?" Inji mai adaidaita sahu,
Bude baki tayi da niyyar bashi amsa amma sai amadi yayi saurin rufe mata baki da hannunshi,
"Ni yakamata ka tambaya ba itaba saboda ita matar aure ce.."
"Yi hakuri mai gida ai naga kamar kai din bakada lafiya ne shiyasa.."
"Ai ciwon ba abakina yake ba, cikin gari zaka kaimu gidan gyaran targade"
"To yallabai.."
Saida suka gama magana da dan adaidaita sahun sannan ya dauke hannunshi daga kan bakin Nadiya,
Da ido take kallonshi kawai har Allah yakaisu gidan mai gyaran targaden.
Sauka sukayi yasoma labuba aljihunsa,
"Baby kinga ashe ma banida ko kwandala ajikina sai dai amma ga ATM card dina.."
"To yanzu yakake so ayi?"
"Muje can may be akwai ATM machine"
Sake rikeshi tayi ya dingisa suka tafi duk da cewar mai adaidaita sahun yace zai kaisu amma fur amadi yaki amincewa saboda ganinshi rike jikin nadiya abun na mutukar burgeshi,
Yana rike ajikinta har suka je wurin da suka samu ATM machine nan ta taimaka masa ya haura yar barandar dake wurin,
20,000 taga ya cira yasaka a aljihunshi sannan ta sauko dashi suka tafi, duk inda suka wuce idon jama'ane ke rakasu wanda har shi kanshi amadin yafara kosawa da wannan kallon,
Dan adaidaita sahu yabawa kudinshi sannan yasamu wuri ya zauna ita kuma ta shiga gidan, mintuna kadan tafito,
"Zo mu shiga" tace dashi batare da ta kalleshiba,
"Mace ne ke gyaran ko namiji?" Ya tambayeta yana dan murmushi,
"Namiji ne.." Tabashi amsa, hannunshi ya mika mata alamun ta tayar dashi tsaye nan ta kama ta jashi ya mike tsaye, rikeshi tayi suka shiga cikin gidan gyaran targaden,
Mai gyaran na zaune akan tabarma da jerin wasu kwalabai agabanshi wadanda ke dauke da magungunan gargajiya aciki,
Zama sukayi mai gyaran yafara duba kafar amadi wacce tazama wata himmm kamar anhura tattali
"Yaushe kaji wannan ciwon?" Mai gyaran ya tambayeshi,
"Dazun nanne na buge da dutsi"
"Wannan ba targade bane tsagewar 'kashi ne amma yanzu za agyara da yardar Allah"
Ba karamin wahala amadi yasha ba amma abin mamaki ko gezau baiyi ba babu raki babu komai har aka gama gyaran,
"Wannan yayan naki namijin gaske ne ba nawasa ba kodai soja ne?" Mai gyaran yafada cikin raha saboda ko manya yazo yiwa gyara ihu suke bare yara,murmushi kawai tayi batace komai ba shi kuma gogan sai aikin binta da na mujiya yake kamar yaune yafara ganinta,
Magani yabasu a kwalba yace ta shafa masa akafar idan sun koma gida bayan ta gasa masa kafar da ruwan zafi,
Dubu daya ya ajiyewa mai gyaran suka mike itada shi, yana rike ajikinta suka fita,
"Baby yauma fa inajin guest lodge dinnan zamu koma mu kwana acan saboda wallahi bazan iya komawa Kano da kaina ba"
Batace masa komaiba sakuci gaba da tafiya har suka samu dan adaidaita nan suka shiga yakaisu minal guest lodge,
Wannan karon ma shine yaje ya biya kudin daki yadawo da key din a hannunshi suka nufi dakin da aka basu,
"To yanzu da ka kawo mu nan a ina zamu samu ruwan zafin da za agasa maka kafar?"
"Za akawo mana, nafadawa wani ma'aikaci a reception din cewar ina son ruwan zafi"
Goshinta ta dafa saboda tasan ma'aikatan abinda zasuyi tsammani daban,
"Baby menene naga kin dafa goshi? Ko afasa kar akawo?"
"A'a akawo"
Kwanciya yayi akan gado ruf da ciki ya dage kafar tashi mai ciwon yana jijjigata,
"Baby zoki daddanna min kafar tawa please"
"Kabari akawo ruwan zafin sai ingasa maka ita.."
"Tom.." Yabata amsa yana faman jujjuya kanshi saboda zafin da kafar keyi masa.
Zaman jiran ruwan zafin sukaci gaba dayi har aka kawo musu cikin wani dan karamin bucket din roba, itace tafita ta karbo ta dawo,
K'asa ya sauka ya zauna itama ta zauna tareda zame dan kwalin kanta domin babu tsumma awurin, ruwan inbanda tururi babu abinda yakeyi nan ta tsoma dan kwalinta aciki ta nado ruwan tafara matsewa take yafara kokkonata saboda zafinshi yarfe hannu tafara kafin ta dora akan kafar amadi.....
*_Ummi Shatu_*
[9/17, 2:46 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin K'auna)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Wannan shafin nakune yan group din baby Isah together with sidiya and friends group especially mama 4h...._
*65*
aishaummi.blogspot.com
*J*in saukar ruwan zafin akafarshi yasashi sakin wata yar kara kadan wacce kanaji kasan ta shagwaba ce,
Hannunta ya rike cikin raki yace,
"Baby da zafi..."
"Komai zafinshi ai hakuri zakayi"
Bata sake sauraronshi ba ta kara jiko dan kwalin tadora akan kafarshi wata kara yakuma yi harda bata fuska tamkar zaiyi mata kuka,
"Baby bakijin tausayina ashe? Allah zanyi miki kuka.."
Jin yanda yayi maganar ashagwabance tamkar karamin yaro yasata yin murmushin da bata shirya ba,
Kafarshi ya janye saboda ganin tana sake tsoma dan kwalin nata acikin ruwan,
"Dan Allah ka tsaya.."
"To bakece ba kinki rarrashina.."
"To yi hakuri ka tsaya ingasa maka, kaga Allah ruwan yafara hucewa"
Mika mata kafar yayi yana yimata karar shagwaba,
"Ni banma taba ganin ragon namiji ba irinka, daga gashin kafa harda su neman yin kuka.." Tafada amaze kamar ba itace tafada ba,
Kallonta yayi tareda rike hannunta,
"Nidai ba rago bane, ke dince bakya tausaya min kawai"
Hannunshi ta ture taci gaba da gaggasa masa kafar tashi har ruwan yayi sanyi, mikewa yayi yana dingisa kafarshi yakoma kan gado ya kwanta,
Binshi kan gadon tayi ta zauna ta dauko maganin da zata shafa masa akafarshi tafara shafa masa ahankali bayan ta dora kafar tashi akan cinyoyinta,
Daga kanshi yayi ya kalleta domin wani abune yake ratsashi idan tana murza masa maganin akafarshi,
"Baby...."
"Uhmmmmm"
Mayar da kanshi yayi ya kwantar,
"Zaki fara yimin wannan uhmmm din naki kamar wata bebiya ko?"
Shiru tayi masa taci gaba da shafa kafarshi tana lailayawa musamman ma tafin kafarshi,
"Baby baki gama bane?"
"Ya akayi?"
"Nan zaki zo dan Allah.."
Kafada ta makale, "hum ummmmm"
"Please baby, badan niba dan Allah nace.."
Kin tashi tayi taci gaba da abinda take tana kallon kafar tashi, shikam komai nashi mai kyaune ita kanta ta shaida da hakan domin kafar tashi kamar bata taka kasa dan kyau da laushi, kusan ma laushin ne yahanata daina shafar kafar tashi, sabanin wasu mazan da zakaga kafarsu duk kaushi da faso wanda har acikin matan ma ana samun haka,
Lumshe idonshi yayi saboda yanzu kuma tafiyar tsutsa take yimasa atafin kafar tashi,
"Baby..."
"Uhmm"
"Kina son nafara wannan shakuwar marar magani?"
Saida tayi murmushi saboda jin abinda yace sannan tace,
"Uhmmm"
"Kikace uhmm ko?"
"Uhmmm" tabashi amsa,
"To shikenan.."
Wayarta ce ta shiga tsuwwa nan ta dauka sakamakon ganin sunan umman sumaila ajiki,
Dauka tayi suka gaisa nan umman take fada mata da ta aiko da sako lallai lallai tatafi gida wannan satin sannan kuma ta tabbata tayi amfani da duk abinda ta aiko mata daga karshe umman takare maganar da cewa,
"Kina shan wanda kika tafi dashi dai ko ba jibge min su kikaje kikayi ba dan nasan halinki"
"Wallahi umma ina sha"
"To shikenan Allah yabada sa'ar karatu"
Sallama sukayi ta kashe wayar tana dan kunkuni,
"Ita umman nan wallahi ta cika cikawa mutum ciki da abubuwan da zasu dameshi..."
Batayi auneba tajita luuuuu ya jata zuwa jikinshi, kallonshi tayi idanuwanshi a lumshe,
"Zo ki fada min abinda umman kebaki wanda har zai dameki"
Bude idanuwanta tayi sosai akan fuskarshi shikuma idanuwanshi arufe,
"Uhmmmm baby, fada min..."
"Babu koma...."
"A'a, da komai... Fada min mana"
"Nace maka babu komai"
"Ni ban yarda ba"
Kallonshi kawai taci gaba dayi tana mamakin kanta domin bata san lokacin da tafara sakin jiki dashi hakaba,
"Bazaki fada minba ni infada miki?"
Ido ta kwalalo tana kallonshi,badai yagano ba? Ta tambayi zuciyarta,
"Uhmmm baby? Ni kin bani dama infada miki?"
Shirun dai tasake yi hakan yashi bude idonshi akan fuskarta nan ita kuma tayi gaggawar lumshe nata idon,
"Baby babu magana?...."
Jin yafara sauke mata ajiyar zuciya yasata saurin bude idonta,
"Menene kuma?"
Ta tambayeshi, gashin kanta yashafa sannan yasake matseta jikinshi wanda tana iya jiyo bugun zuciyarshi,
"Wai menen...."
Hanata karasawa yayi ta hanyar kai bakinshi kan nata, zabura tayi kamar ya tsikara mata allura ta tashi fuskarta adaure,
"Menene haka? Ni karka sake sa bakinka akan nawa"
Murmushi yayi yasake janta jikinsa da hannunshi guda daya,
"Haba baby, wannan wanne irin horo ne? Ni ban taba jin macen dake yiwa mijinta rowa irin wannan ba kamarki, ke komai naki hanani kike.."
"Ai ban taba hanaka wannan ba sai yau"
"To meyasa zaki hanani? Ai horon zaiyi min tsanani da yawa"
"Ni ba horo nakeyi maka ba, laifinka ne tunda da idona naganka kana kissing din wata..."
"Dan Allah baby kiyi hakuri..." Shine abinda yake ta maimata mata, shiru tayi tana sauraron ban hakurinsa,
Yabata hakuri yafi sau dari amma batace komai ba domin yagama kashe mata jiki da salon da yake yi mata, ita kanta bata ma san ya akayiba itadai kawai taji bakinta cikin nashi nan ta manta ma da batun wai taganshi yana kissing din zee dazu.
Tunda suke da amadi bata taba sakin jiki dashi irin yau ba, yaune kadai ta taba biye mishi aduk zamansu dashi, ko da wasa kuma yau bataji haushinshi ba bare tayi fushi dashi,
Duk abubuwan nan dake faruwa shikuma amadi bai taba gwada karya alkawarin da ya daukar mata ba,
Bayan sallar magrib ta kalleshi yana jikinta idanuwanshi a lumshe, sai yau ta sake tabbatarwa da amadi yarone karami,
So take ta tashi saboda anyi salla tun tuni amma kuma takasa tashi domin tama rasa awanne yanayi take, yanayin da take jinta ciki harda kunya ta kawo mata gudun mawa,
Idonshi taga ya bude yafara mika,
"Kayi mika da kyau.." Tafada acikin ranta,
"Baby..."
"Uhmmm"
"Dan Allah baby kiyi hakuri kinji, kiyi hakuri akan abinda yafaru dazu wallahi bazan sake ba.."
Ita tausayi ma yake bata yanzu saboda tunda yaga tayi fushi yakasa samun sukuni Kalmar hakuri taki fita daga bakinsa ko yanzun ma da suke duniyar so kalmar hakurin taji yanata furtawa,
"Kinji baby? Kiyi hakuri dan Allah"
"Nahakura"
Jin abinda tace yasashi sake rungumeta sai kuma ya sassauta rikon da yayi mata,
"Baby duk kinbi kin faffama min kafata wallahi..."
"Yaushe..?" Tafada bayan ta bude idonta arazane,
"Lokacin da..." Sai kuma yayi shiru,
"Meyasa da tun lokacin baka fada ba sai yanzu?"
"Ai lokacin banji zafinba sai yanzu take yimin zafi..."
Tashi tayi ta dago kafar tashi tana gani, sam ta ma manta da cewar babu riga ajikinta,
"Su baby budurwa, wallahi kamar baki shayar dasu fadeel b..."
Saurin jan rigarshi tayi ta rufe kirjinta tana harararshi,
Wata kunyarshi ce take saukar mata asannu asannu, kawai sai tagagara kallon ko wurinda yake kwance,
"Katashi bafa muyi salla ba.."
Tashi yayi ya dingisa ya shige toilet,tana ganin haka tajawo rigarta tasa ta shirya kafin ya fito,mintuna kadan sai gashi ya fito,
"Baby zo muje muyi tare.."
Kai ta girgiza masa alamun a'a, har inda take yaje yaja hannunta,
"Dan Allah kiyarda yau daya dai mu yi tare.."
Duk da bata so saida yajata zuwa cikin toilet din.....
*_Ummi Shatu_*
[9/19, 2:49 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_
_Fatan alkhairi agareki Hawy, this page is for you dear...._
*66*
aishaummi.blogspot.com
*I*danuwanta alumshe har suka shiga cikin toilet din,
D'aga idonshi yayi ya kalleta fuskarshi dauke da murnushin farin ciki gamida jin dadi,
"Baby bude idonki ki gani..."
Sake runtse idonta tayi a maimakon ta bude, juyin duniya yayi da ita amma takasa bude idonta, yagane tsaf kunyarshi wai takeji dan haka yasaketa ya fara kokarin tara musu ruwan da zasuyi wankan dashi,
Cikeda kunya ta zame jikinta tafita daga cikin toilet din tana murmushi amadi kawai sai juyowa yayi yaga bata nan, bai matsa sai yasake dawo da ita ba saboda yasan ko yanzu yasamu dama dayawa wacce ada bai samuba,
Wankanshi yayi ya gama sannan ya fita yana shafa sumar kanshi hannunshi daya rike da jeans da t shirt dinshi,
Acikin dakin ya sameta tana zaune agefen gado,
Saida yaje kusa da ita ya lakuce mata hanci sannan yayi magana,
"Raguwa mai tsoron yin wanka da mijinta kawai..."
Kafarta ta dora akan kafarshi mai ciwo,
"Kana sake kirana da raguwa zan fama ciwon nan yanzu..."
Murmushi yayi,
"Ki fama mana ai ke zaman jinya zai kama.."
Dauke kafarta tayi ta mike nan yaja hannunta,
"Inzo inyi rakiya..?"
Makale kafada tayi tazare hannunta ta shiga toilet, jiranta ya zauna yi harta fito sannan ya saka kayanshi sukayi sallar tare,
Kwanciya yayi yadora kansa bisa cinyarta,
"Baby...."
"Uhmmm"
"Dan Allah kiyi min wani taimako"
"Ina jinka"
"So nake kitare nanda 3 weeks.."
Saida ta danyi shiru na wasu yan sakanni sannan tayi magana,
"Bazaka bari ingama makaranta ba tukunna?"
Hannunta yakama acikin nasa yadan daga kanshi yana kallonta,
"Baby zamu rinka tahowa tare, inada bukatarki ne kusa dani, rashinki atareda ni gaskiya tsautsayi ne..."
Shirun ta sakeyi sannan tace,
"Shikenan amma dai kabari indanyi shawara.."
"To shikenan nabari.."
Janta yayi ya kwantar da ita ajikinsa yafara lalubarta, hannunshi ta rike,
"Ya akayi kuma?"
Murmushi yayi,
"Yi hakuri baby na"
Kawar da kanta tayi tana lumshe idonta,
Saida lokacin sallar isha yayi sannan suka tashi sukayi suna idarwa yace tatashi sufita yadan take kafarshi,
Rufe dakin sukayi yakama hannunta suka fita wajen guest house din domin ganin gari, ahankali suke tafiya yana rike da ita yana yimata kalamai masu sanyaya zuciya na irin son da yake yimata,
K'arfe 9 da wani abu suka koma guest house din bayan ya siyo musu balangu da soyayyen kifi, suna shiga kuma yayi musu order din abinci,
Tare suka zauna suka ci yana bata abaki, langabe kai yayi ya kalleta,
"Baby nifa?"
"Me fa?" Ta tambayeshi,
"Abincin? Dan Allah kibani"
Diba tayi tafara bashi shima yana bata da haka har suka kammala.
Washe gari da misalin karfe 9 nasafe suka bar hotel din suka nufi cikin makarantarsu nadiya,
"Baby tafiya zanyi yanzu sai yaushe?"
Mayafinta ta gyara tana kallon wani wuri,
"Nima gida nake son tafiya ranar friday umma tace lallai lallai inje"
"To kibari zanzo inkaiki"
"Kaida kake ciwon kafa, kabarshi kawai zan shiga mota intafi"
Girgiza kai yayi, "ban yarda ba, zanzo inkaiki"
"To shikenan, Allah yakiyaye hanya"
"Amin baby, shikenan intafi babu special sallama?"
Shiru tayi kamar bata jishi ba saboda tasan abinda yake nufi,
"Kagaida hajiya"
"Zataji" yafada yana murmushi saboda shi yarasa dalilinta najin kunyarsa,
Shiga cikin motarshi yayi yai mata key tana tsaye tana kallonshi har saida taga yafara tafiya sannan tabar wurin tawuce zuwa hostel.
Tun yana hanya yake kiranta baima bari yakarasa cikin kanon ba,
"Baby Allah yayi miki albarka, Allah yabaki aljanna, nagode sosai da abinda kika yimin..."
"Amin, ka karasa gidane?"
"Nakusa dai.. Yanzun nan zan shiga kano"
"Ok Allah yakiyaye hanya"
"Amin baby i love you"
Katse wayar tayi tana murmushi, koda amadi yaje gida hajiya tsokanarsa tai tayi tana cewa daga rakiya kuma sai ya kwana acan, dariya yayi yawuce dakinsa saboda shidai yasan Allah ne kawai yayi masa nasibi nadiya ta sauko.
Ranar yakirata awaya yafi sau a kirga, bini bini sai ya kirata da haka har dare yayi, bai sake haduwa da itaba sai ranar juma'a ranar da zai kaita rano,
Har cikin makarantar ya shiga yayi packing yana jiranta, fitowa tayi cikin doguwar riga ta Arabian gown orange colour da dan mayafinta, ba karamin kyau rigar tayi mataba, kafarta sanye cikin flat shoe shima Orange colour,
Kallonta yayi bayan ta shiga ta zauna acikin gaban motar,
"Baby bakya jin magana ko? Dubi shigar jikinki, wai meyasa kike yimin wasarere da halin ko inkula da kayana?"
"Dan Allah yanzu meye laifin wannan shigar?" Tafada tana kallonshi, ba karamin kyau yayiba cikin Skye blue din wani yadi mai kamar tissue marar kauri wanda yabata damar ganin farar singiletin da yasaka,
Dinkin half jamfane mai dogon hannu, kansa yasa hula amma yaturata baya, kamar wani balarabe haka ya fito,
Bakinta ya kalla wanda yasha jan janbaki rangadadau, pink lips dinshi ya dan lasa,
"Ohhh wato ke baki ma san laifin kayan ba ko??"
"Gaskiya ni banga laifinsu ba"
Tace dashi tana tura baki,
"Zo kiga wani abu.."
"Ina zanzo?"
"Dan matsawo nan zakiyi.."
"Gaskiya a'a..."
"Kina ki wallahi Allah ya isa zanyi miki"
Matsawa tayi tana tuttura baki nan ya cafke bakin nata da nashi, 24 hours din data shafa gaba daya saida yayi dama dama dashi agefen bakinshi da nata.
Sakinta yayi yana sauke ajiyar zuciya ahankali, kasa kallonshi tayi amma ta dan hade rai kadan wanda yaushe rabon da yaga tayi,
"Baby muje ko..."
Yafada cikin jan magana, shiru tayi masa dan haka sai kawai yayiwa motar key yabata wuta, saida suka bar cikin makarantar sannan ya kula da jan bakin da ya bata masa fuska mirror yasake kallo nan yaga fuskarshi tayi baja baja,
Packing yayi agefen titi ya kalleta,
"Baby goge min to jan bakin da kika shafa min"
Ita kanta tasan dan neman magana yafadi hakan shiyasa bata kulashi maganar tayi tsaho ba, tissue ta yago tafara goge mishi duk wurin da jan bakin ya taba,
"Kafar taka tawarke..?" Ta tambayeshi tana mai goge masa fuskarshi,
"Ehh baby tagama warkewa saura kadan, kin gani.."
Nuna mata yayi tagani sannan yadaura belt yahau titi bayan ta kammala goge mishi jan bakin, ita dinma belt ta daura ta jingina mintuna kalilan barci ya dauketa, kallonta amadi yayi yai murmushi,
"Rigimammiya daga fara tafiya kuma sai barci.."
Wa'azin sheikh jafar Mahmud Adam ya kunna yana saurara mai taken tambayoyi da amsoshi, har sukaje cikin rano nadiya bata farka ba har saida suka shiga layinsu sukaje kofar gidansu yayi packing sannan ya matsa kusa da ita yafara hure mata ido da bakinshi,
Dan motsi tayi amma bata bude idonta ba, saitin kunnenta yakoma yafara hurawa, sake juya kanta tayi har lokacin dai bata tashi ba,
Idonta yasake busawa da iskar bakinshi nan ta dan bude idonta kadan ganinshi yasata bude idanuwan gaba daya tana kallonshi, murmushi yayi mata,
"Baby yar kauye shine harda su yin bacci acikin mota.."
Daure fuska tayi, "waye yar kauyen?"
"Wai da.." Yafada yana murmushi,
"Hmmm" tafada tana dauke kanta,
"Dadina dake iya daure fuska.."
Bata tanka ba tafara kokarin bude kofar, komawa sit dinshi yayi yacire belt din daya daura yabude kofar ya fita lokacin nadiya har ta shige cikin gida,
Bayanta yabi ya isketa atsakar gida tana daga su fadeel shida fadeela wadanda dawowarsu kenan daga makaranta domin ko cire musu uniform dinma ba ayiba, ai suna ganin amadi suka bar nadiya suka tafi wurinshi,
Yasamu kyakkyawar tarba mai kyau awurin su mama, shi kam dama yasan yayi sa'ar surukai kuma duk yan uwan nadiya kowa na sonshi shiyasa shima yake son bin duk wata hanya dayake ganin zai kyautata musu suji dadi,
Wata katuwar jaka yakawo musu cike da kaya wai tsarabarsu ce, kowa na gidan akwai tsarabarsa aciki amma duk tsarabar twins tafi yawa domin bayan kayan sawa harda kayan wasa kala kala yasiyo musu, shi dai Allah ne yadora masa son nadiya da yaranta domin yana jin son yaran har cikin jininsa tamkar shine ya haifesu,
Nadiya kuwa babu ita acikin tsarabar da yakawo ko kyalle babu nata acikin kayan sai su amira da husna da sauran mutanen gidan, yana tare da twins har lokacin sallar juma'a yayi nan ya daukesu suka tafi masallaci tare basu suka dawo gidan ba sai wurin 3 lokacin har abba yadawo shima,
Nadiya ce tayi masa jagora zuwa falon abba, tana gaba yana binta abaya yana shakar kamshin turarenta na beautiful woman sannan adon da tayi awannan lokaci ba karamin daukar hankalinsa yayiba domin wata doguwar rigace ta atamfa coffee colour ajikinta, rigar tayi mata das sannan ta bayyanar da kyawunta afili dan haka kasa hakuri yayi harsai da ya cimmata ya rungumeta ta baya,
Cikin mutuntawa da girmamawa ya gaida Abba, bayan sun gaisa abban yayi masa maganar tarewar nadiya nanda sati biyu tunda yadawo,
Satar kallonta yayi yaga kanta akasa bata ko dagoba ajiyar zuciya yasaki saboda Allah yarufa masa asiri agabanta abba yayi maganar da abayan idonta ne cewa zatayi shine yafadawa Abba haka, saida ya danyi jim sannan yacewa abban adai barshi asati uku ba sati biyu ba saboda yana jira akawo masa furnitures din da yayi order daga kasar Italy wadanda zasu zo nanda sati biyu sannan baya son asiyawa nadiya ko cokalin cin abinci domin yagama siya mata komai wanda duk zata bukata na amfanin gida,
Duk da Abba yaji haka saida yace a'a shima zai sake siya mata wasu nan amadi yace a'a idan ansiya ma asara zai zama domin yagama siyan komai, albarka Abba yasa mishi tareda yi masa godiya anan suka bar maganar tarewar nadiya nanda sati uku.
Tare suka taso suka fito da ita sai ciccin magani take fuska babu nishadi, shidai bai ce komai ba domin lallabata yake yasan babu wuya tahau sama, danma kar yayi mata laifi sai yayiwa mama sallama yace zai tafi, mayafi ta dauka ta rakashi waje sai kumbure kumbure take,
"Baby ke taki tsarabar tana gida na ajiye miki sai kinzo zan baki kinji"
"Uhmmm naji, nagode, Allah ya kiyaye hanya, agaida hajiya"
"Zataji baby.."
Dahaka suka rabu yashiga motarshi yatafi cikeda murnar nan da sati uku yana tareda ita, gida ta koma tana kukkumbura baki.
***
A bangaren kabeer da asabe mc kuwa abin sai wanda yagani, duk wanda yaga yanda kabeer yakoma sai ya tausaya masa domin tun lokacin da ya tsallaka bakin asirin da asabe ta ajiye masa shikenan yazama kamar bawanta, komai shine yake yimata, maganarta kuwa bai isa ya musanta ba, daga tace masa abu jiki yana rawa zaije yayi mata, gaba daya dukiyarsa ta koma hannunta, takardunsa nagidaje da filaye duk ta karbe daga gareshi, aiki kuwa tuni yadade da sallama shi wannan dalilinne yasa kamfanin da yake aiki suka bashi takardar sallama saboda wasa da aikinsa da yakeyi,
Hankalinsa gaba daya yabar jikinsa sai abinda asabe tace, ita kuwa yanzune ma take shanawa ita da kawayenta saboda ansamu dukiyar banza, amma duk da haka tana sonshi shiyasa take dan raga masa awani abun, shidai yazama shine matar itace mijin sai abinda tace, rabonsa da iyayensa da kannensa kuwa har ya manta domin asirin da asabe tayi masa harda wanda zai rabashi da danginsa,
Suma iyayen nashi sunyi watsi da harkarsa babu Wanda yake nemansa, A'isha da Fati ne kawai suke son zuwa su gano halin da yake ciki dan haka awata ranar litinin da safe fati ta shirya taje gidan A'isha suka wuce gidan kabeer din.
*_Ummi Shatu_*🏻
[9/21, 3:03 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Home of expert & perfect writers_
_Gaisuwa ta musamman ga iyalan Alh Ali Bukar Dalori Borno state,na sadaukar da wannan shafin agareku tareda Rashidat Abdullah Kardam..._
*67*
aishaummi.blogspot.com
*L*okacin dasu fati suka shiga gidan kabeer sai da hankalinsu yatashi domin gaba daya gidan yagama sauyawa sannan hatta motocinsa duk babu asabe mc ta salwantar dasu, mota guda dayace kawai tayi saura wadda itace take hawa,
Asabe najin sallamarsu amma tayi burus dasu taki koda amsawa ne domin acewarta tasan munafurcine ya kawosu,
Basu yi fushi ba suka tura kai zuwa cikin falon, tana zaune akan 3 sitter ta dora daya akan daya tana chaten tamkar bata jisu ba,
Kallon juna A'isha da fati sukayi,
"Asabe ashe kina ciki..." Fati tafada cikin rashin girmamawa domin yanzu aduniya su asabe ce matsalarsu,
"Ehhhh gashi kuwa kingani" asabe tabata amsa tana turo dan kwalinta gaban goshi,
Kabeer ne yafito daga kitchen yana yiwa asabe girkin faten wake da alayyahu wanda tasashi,
Kallonsa suka tsaya yi cikeda tausayawa domin duk yazama wani sakarai sannan babu alamun hutu ko jin dadi atare dashi yanzu sabanin da wanda kabeer ada cikakken dan gayune mai aji mai jida kyau da kudi,
"Yaya kabeer... Haka kadawo? Haka kazama? Yanzu yaya kabeer ka kyautawa rayuwarka kenan? Ka manta da iyayenka da yan uwanka da danginka da kowa naka kazo ka tare akarkashin mace, haba yaya kabeer Kaduba kaga yanda kadawo fa kamar ba kaiba, yaya kabeer baka kyautawa kanka ba iyayenka sun dade suna fushi dakai, fushinsu ne yake bibiyarka..." Fati tafada tana zubar da hawayen tausayinshi,
Karasawa wurinsu yayi shima yana jin kamar zaisa kukan,
"Fati, A'isha dan Allah ku tayani da addu'a nikaina ban san abinda yake damuna ba, ban san yanda akayi nadawo haka ba... "
Wata tsawa asabe mc ta daka masa sai kace uwarsa,
"Kai, wuce kaje ka karasa min girkin da nasaka..."
Jiki narawa kabeer ya juya kamar zai kifa yana waiwayen su A'isha yashige kitchen,
Wata kwalla mai zafi A'isha ta fara fitarwa ta kalli mc,
"Insha Allah sai kinga karshenki, yanda kika mayar dashi bawa sai Allah yasaka masa.."
Mikewa asabe tayi cikin fada,
"Kai ku fice kubar min gida, sannan karku kuskura kusake zuwa gidan nan, banzaye mararsa kunya, idan kunje gida ku fadawa tsohuwa sako injini danta ni ta haifawa dan haka tsakaninta dashi sai ido.."
"Karya kike jahila,kinyi kadan ahaifa miki yaya kabeer.." A'isha tabata amsa, kan A'isha asaben tayi tana huci,
Duk da haka bakin A'isha bai mutuba, dakyar fati ta janyeta suka bar cikin falon dukkaninsu suna zubar da kwalla, nan asabe ta mayar da kofarta tasaka key ta kulle,
Ta cikin window din kitchen kabeer ke lekensu amma bashida bakin yin magana domin asabe tadade da gamawa dashi.
***
Tunda amadi yatafi nadiya taketa kumbure kumbure marar dalili domin ita tafi son sai tagama karatu sannan zata tare amma tunda Abba yayi maganar tasan dolenta sai tatare din koda kuwa bata so barema bata da halin da zata musanta maganar Abba,
Duk mama nakula da ita da kumbure kumburen da take ta faman yi, shi kansa amadi din fushin ya dan fara shafarsa domin ko ya kirata awaya baya samun kanta yanzu shiyasa duk yabi yadamu,yana murnar zata tare yana kuma fargabar fushin da takeyi,
"Wai ke meke damunki ne? Yarinya kamar mai iska, daga wannan sai wannan.."
Mama tace da ita cikin fada tana zaune akofar kitchen ita kuma nadiya tana wurin wanke wanke tanayi,
"Babu komai mama"
"Badai babu komai ba, tunda kika dawo shekaran jiya kalau amma daga ji anyi miki maganar tarewa shikenan kika bi kika damu kanki, keda haka zaki zauna da aure akanki kina gida? Ai bazai yiyuba nadiya, ita mace duk gatanta da asalinta da nasabarta to gidan mijinta shine gatanta in fada miki"
Shiru tayi taci gaba da sauraron fadan da mama take tayi mata har tagama wanke wanken mama bata daina fada ba, daki takoma ta kwanta.
Yarage saura sati biyu tarewarta amadi yaturo mata da 50,000 yace gashi nan ta yi duk wani abu wanda zatayi na shirye shiryen tarewa,
Kayan cosmetics da turaruka ta siyo masu dadin kamshi, sai turaren wuta da humra kala kala,
Duk da bata son yin gyaran jiki saida umman sumaila ta tilastata dole tafara zuwa gidan wata mata yar sudan aka fara yimata gyaran jiki safe da yamma,
Umman sumaila kuwa tunda tazo dama da guzurinta tazo shiyasa sam nadiya bataso zuwanta ba domin hadaddun kayan gyara tazo dashi kuma agaba take tisata sai ta shanye,
Haka lokaci yayita karatowa, shi kuma amadi yana can yana gyara mata gidanta inda zata zauna, komai sai yakirata yaji wanda takeso saboda kar asa mata wanda baiyi mata ba, hatta labule da carpet da komai na kwalliyar falo da bedrooms saida ya tambayeta kalolin da takeso nan tace purple colour take so.
Cigaba da gyarata umman sumaila tayi tako ina, ita dai mama yar kallo tazama kallonsu takeyi saida taga gyara yaki karewa sannan tayiwa umma magana,
"Dan Allah ahakura haka nan karku rikita musu yaro..."
"Ba maganar hakuri anan, gyara ban ma gamaba saura yana baya.."
Tashi mama tayi tana cewa, "duk dai gyara tsoho bazaiyi kamar ya saboba"
"Waya fada miki? Ko za asamu banbanci to kalilan ne"
Ita dai mama bata sake magana ba tafita tana dariya,
Nan umman sumaila ta dora daga inda ta tsaya,
Saura kwana biyu tariyar aka yiwa nadiya gyaran gashi da kunshi, zanen kunshi mai kyau na ja da baki yar sudan tayi mata,
Ranar alhamis da daddare Abba da mama harda umman sumaila suka zaunarta suka yimata fada da nasiha akan tabi mijinta tayi masa biyayya kuma tarikeshi hannu bibbiyu domin masoyinta ne na hakika,
Cikin sanyin jiki tatashi tafita bayan su Abba sun sallameta, kwanciya taje tayi amma saita gagara bacci saboda fargaba,ko alokacin aurenta nafarko batayi fargaba kamar wannan ba ko dan yanzu ta san yanda auren yake ne,
Har asuba tayi idonta biyu saida tayi sallar asuba sannan bacci ya dauketa,
Gaba daya kayanta amira tagama shirya mata su tun kafin ta tashi daga bacci, gaba daya ranar kashe wayarta tayi domin jikinta yayi mata sanyi, haka tawuni bata um bare um um,
K'arfe takwas na dare anty siyama sukazo daukar amarya ita da wasu kawayen hajiya guda biyu,
Motoci guda uku sukazo dashi domin amadi yana mutukar kimanta nadiya shiyasa ako ina yake nuna ita din mai daraja ce agareshi,
Fito da nadiya umman sumaila tayi itada maman su kabeer domin sune zasu rakata nan tayiwa mama sallama aka fita da ita, fadeel da fadeela dama tuni sunyi bacci tun bayan sallar magrib.
8:40 suka shiga cikin Kano suka wuce gidansu amadi kai tsaye, part din hajiya aka fara kaita hajiyan na zaune tasha kwalliya cikin wani leshi mai tsada ja takafa dauri ko ina najikinta gwalagwalai ne ke daukar ido,
Cikin faran faran hajiya ta karbi bakinta nan su umma suka damka mata amanar nadiya tace ta karba Allah yataya su riko dama kuma ita nadiya yarta ce halak malak, ita da amadi duk dayane awurinta,
Fita akayi da nadiya zuwa part dinta wanda abin sai wanda yagani saboda mutukar tsaruwar da yayi, sai santin gidan su umma keyi domin ya tsaru karshe,
Dakin dake hannun dama suka kaita domin shine nata, komai nacikin dakin purple colour ne, abakin gado suka zaunarta suka fita domin ganin tsarin gidan,
Saida suka gama ganin ko ina sannan sukazo suka yimata sallama suka tafi, itama anty siyama tafiya tayi bata zauna ba,
Kallon dakin nadiya ta daga kanta tanayi, komai ya burgeta yanda aka ajiyeshi akan tsari,
Bude kofar dakin taji anyi an shigo, amadine sanye cikin wata shadda kalar ruwan kasa kanshi babu hula yayi mutukar kyau fuskarshi kumshe da murmushi sai zuba kamshi yake,
Kallonta yake yi tun daga nesa har yakaraso kusa da ita,akan bedside drewar dake kusa da ita ya zauna yana kallonta,
"Baby..." Yakira sunanta tareda kamo hannayenta wadanda suka sha kunshi yarike acikin nashi yana bin zanen yana shafawa,
Kallonta yayi,wani blue din material ne ajikinta dinkin riga da skirt, takalmin kafarta shima blue sai babban mayafi data rufe jikinta dashi, dago habarta yayi ya kalli cikin idanuwanta,
"Nazata ai kuka kike yi..."
Shiru tayi bata yi magana ba,
"Baby Ina yimiki sannu da zuwa cikin gidana gidan dake kunshe da dunbin farin ciki da soyayya, da kauna tareda kulawa ta musamman, ina mai yimiki albishir da samun tsantsar soyayya ta gaskiya da samun farin ciki marar yankewa domin ni amatsayin abokiyar rayuwa na daukeki, sannan kuma na daukeki a matsayin abokiyar zamantakewa, abokiyar shawara, abokiyar gudanar da komai tare, ban daukeki a matsayin mata kawai ba, a'a har matsayin juya akalar rayuwata duk yana hannunki, dan Allah baby ki rikeni amana nikuma nayi miki alkawari insha Allah zaki sameni mutum nagari mai cika alkawarinki akoda yaushe..."
Dan tsagaitawa yayi yabar kan drewar din dayake zaune ya matsa kusa da ita,
"Daren yau darene wanda yake cike da tarin albarkatu masu yawa, domin daren juma'a ne haka kuma darene wanda nadiya ta kasance cikin dakin mijinta amadi, yanzu me yarage?"
Yi tayi kamar bataji tambayar tashi ba hakan datayi yasashi murmushi tareda yaye mayafin dake rufe ajikinta, karkatar da kanshi yayi zuwa gefe guda,
"Baby am asking you, yanzu me yarage agaremu? Me yakamata muyi?"
"Ban fahimceka ba?" Tayi magana muryarta can kasa,
"Cewa nayi yanzu meya kamata muyi?"
Shiru tasake yimasa ta dauke idonta daga kanshi,
"No idea...?" Ya tambayeta yana murza yan yatsunta,
Jin tayi shiru yasashi mikewa,
"To yanzu tashi zakiyi muyi salla sannan ina mai tabbatar miki da cewa ban manta da alkawarinmu ba so fell free...."
Tashi tayi yana rikeda hannunta suka fara tafiya,
"Ko indaukeki?"
Ya tambayeta bayan yayi kasa da muryarshi,
Bata kai ga yin magana ba kawai taji yayi sama da ita ya dagata, har cikin toilet din yakaita sannan ya ajiyeta,ba karamin kyau cikin toilet din yayi mata ba bayan haduwar da yayi gashi katon gaske,
Fanfo ya kunna ya daura alwala sannan ya jawota gaban sink din,
Hannuwanta ya kama yafara yimata alwalar, saida ya kammala wanke mata kafafu sannan ya kashe fanfon yasake daukarta zuwa cikin bedroom din,
Wata babbar dardumar salla sabuwa yadauko ya shimfida musu yajuya yana kallonta,
"Yi hakuri ki daure kizo muyi sallar sai kici abinci ki kwanta ki huta.."
Mayafinta ta dauka ta nade jikinta dashi taje bayanshi ta tsaya yajasu salla,
Salla sukayi raka'a biyu bayan sun idar yadafa kanta yafara karanto addu'o'i wadanda bata taba zaton ya iyasu ba, yajima yana yimusu addu'a sannan ya shafa yana kallonta, fuskarshi kadai zaka kalla kagane irin dunbin farin cikin da yake ciki,
Tashi yayi yafita babu jimawa sai gashi yashigo da wani babban farantin silver, agabanta ya ajiye farantin, robar sanyayyen laban ce babba sai glass cup guda biyu sannan sai wani filet dauke da gasasshiyar kaza mai romo wacce tasha kayan hadi sai kamshine yake tashi da turiri daga jikinta,
"Baby ga abinci kici..."
"Naci abinci..."
"A'a baby ko kinci zaki kara..."
"Nace maka nakosh..."
Shiru tayi sakamakon jin yasa mata naman acikin bakinta, dolenta tahadiye maganar tafara taunar tsokar naman,
"Ban son magana kawai dai kici kaza malama.."
Harararshi ta danyi ta dauke kai nan yafara rarrashinta sai kace cikinsa zata bawa, ahankali yake saka mata naman tana ci har saida ya tabbatar taci fin rabi sannan ya tsiyayo laban cikin cup ya bata, jinta take ta koshi dam dan haka kadan tasha ta dauke kanta,
Murmushi yayi ya dauke kayan yafita jim kadan sai gashi yadawo,
"Baby saura wanka daga nan sai ki kwanta kiyi bacci ko..?
Cikin toilet ya leka ya ciro mata babban towel guda daya, janta yayi jikinsa ya rungumeta sannan yafara yin kasa da zip din rigarta, rikeshi tayi,
"Kabarshi zanyi da kaina.."
"Ayya baby ban son ki wahala nefa shiyasa..."
Ji tayi ya daura mata towel din sannan yasaki rigar tafadi, saurin rike towel din tayi nan taji yayi sama da ita yanufi toilet,
"Ajiye anan zan shiga inyi, basai ka kaini ciki ba..."
Ajiyeta yayi yana yimata dariya,
"Babyn nan tawa akwai tsoro da yawa..."
Shigewa cikin toilet tayi bata mayar masa da martani ba, komai wanda zata bukata gashi nan an ajiye bisa kan wata yar kanta ta silver wacce ke daure ajikin bango kama tun daga kan sabulan wanka,gel, shampoo, maclean, brush da duk wani abu na bukata lokacin wanka,
Ruwan zafi ta tara ta surka da na sanyi tayi wanka da sabulu mai dadin kamshi sannan tayi brush ta fita,
Amadi baya cikin dakin amma ga sleeping gown nan ya ajiye mata akan gado, saida ta shafa dan cream marar maiko sannan ta shafe jikinta da body fantasy sannan ta dauko rigar,
Iya haduwa rigar ta hado amma kuma rigar bata da kauri bare duhu, pink ce pink dinma mai haske, dan siririn hannu gareta sai wani ado da aka yimata daga kirji bayan an danyi tattara kadan,
Kafada ta daga ta dauki fararen inner wears din da ke ajiye tareda rigar tasaka sannan ta zira rigar ta dauki towel din takai bisa kofar toilet ta rataye ta dawo ta kwanta,
Lumshe idanuwanta tayi tana jin wani irin sanyi yana ratsata,
Bata fi minti goma da kwanciya ba taji shigowar amadi, sanye yake da kayan bacci na maza maroon colour riga arm less da wando iya cinya, kan gadon ya hau ya matsa kusa da ita yafara mammatsa mata jikinta,
"Baby inyi miki tausa ko...?"
Bata iya amsa mishi ba illa sake lumshe idanuwanta da tayi bacci yasoma fisgarta sama sama.....
_Fadi kalma daya tak akan amadi, nidai nace gwani at fannin so....kufa?_
_*Ummi Shatu*_
[9/24, 7:39 AM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*68*
aishaummi.blogspot.com
*Z*aman dirshan amadi yayi yana aikin yiwa nadiya tausa har saida yaji alamun bacci yayi gaba da ita sannan ya danyi magana ahankali cikin muryarsa mai mutukar sanyi,
"Baby.... Baby kinyi bacci ne?"
Jin bata amsaba ya tabbatar masa da cewar tayi bacci, tashi yayi yaje ya kashe light yadawo bayanta ya kwanta tareda kanannadeta acikin jikinshi,
Yajima baiyi bacci ba saboda tsantsar farin cikin da yake ciki,
Misalin karfe 2 nadare bacci yasamu nasarar daukarshi asuba nayi kuma ya farka,
Jikinsa ya zare yaje ya shiga toilet ya dauro alwala bayan yayi brush sannan yafito, kusa da nadiya yaje ya fara shafa fuskarta ahankali, jin sanyin ruwa akan kumatunta yasata sake tukunkune jikinta wuri guda tafara jan bargo zata sake lulluba,
Bargon ya rike da hannunshi,
"Baby...." Yakira sunanta ahankali,
Sake lumshe ido tayi ta yunkura zatayi juyi, riketa yayi,
"Baby tashi muyi salla sai ki koma baccin..."
Idonta ta bude ahankali tana kallonsa,
"Sallah...? Sallar yaushe?"
Murmushi ya danyi,
"Sallar asuba"
"Har lokaci yayi?" Ta tambayeshi tana mayar da idanuwanta rufe,
"Lokaci yayi..."
"Ba yanzu zanyi ba.."
Yaye bargon yayi ya kinkimeta ya saba akan kafadarshi yayi cikin bathroom din da ita,
"Wai kai baka gajiya da daukar mutum ne?"
"Ya za ayi ingaji da daukar ki? Ai bakida nauyi"
Bata yimasa magana ba har ya ajiyeta acikin bathroom din sannan yafita, brush tayi ta daura alwala ta fita tana lullumshe ido saboda bacci,
Hijabi taga ya ciro mata da zani,karba tayi ta daura zanin tasa hijab din, saida suka fara gabatar da sallar nafila raka'a biyu sannan suka yi sallar asuba,
Bata jima azaune ba ta shafa addu'a takoma kan gado ta kwanta batare data cire hijabin dake jikinta da zanin data daura ba.
Shi kam amadi zama yayi yafara karanta littafi mai tsarki,sai da ya karanta rabin suratul bakara sannan ya rufe alqur'anin ya mike daga kan abin sallar,lokacin har gari yayi haske sosai domin karfe 6 nasafe,
Wurin nadiya yaje nan yaganta tayi rub da ciki agefen gadon, ahankali ya dagata ya juyata yacire mata hijab din yazare mata zanin dake jikinta ya kwantar da ita,
Ac ya kunna mata ya fita, baccinta ita dai take sosai bata ma san abinda ke faruwa ba, ba ita tatashi ba sai misalin karfe 9 nasafe,
Zaune tatashi tana kallon gefenta ko amadi na nan amma bata ganshi ba, jikinta ta kalla taga babu hijabin da ta kwanta dashi sannan babu zanin data daura nan ta tabbatar da cewar amadi ne ya cire mata su,
Sauka tayi daga kan gadon ta nufi toilet, wanka tayi tafito tana daure da towel, gaban mirror taje ta zauna tafara shafe jikinta da lotion mai kamshi,
Kwalliya ta danyiwa fuskarta, body spray ta dauka tafara feshe jikinta dashi,
Jin alamun bude kofa yasata dan juyawa, amadi tagani tsaye yana kallonta yana sanye da t shirt yellow anyi rubutu da pink din kala anrubuta have a nice day, sai bakin jeans da yasa fuskar nan tashi annurin kyau ne kawai ke fita daga cikinta,
"Good morning baby?.."
Yace da ita yana murmushi, ahankali yafara takawa zuwa gareta yana yimata murmushi,
Ta bayanta yaje ya tsaya yana kallonta ta cikin mirror, ita dinma kallonshi ta danyi,
"Ina kwana?"
"Lafiya lau baby na, how was your night...?"
Bata amsaba dan haka yayi hugging dinta ta baya yafara kissing din wuyanta,
"Dan matsa zanje na saka kaya.."
Matsawar yayi kamar yadda tace nan tawuce zuwa wurin drewar din kayanta, tana budewa taga wasu hadaddun english wears ajere kamar boutique, kayan tabi tana dagawa amma kaf babu na hausawa,
Juyawa tayi ta kalleshi yana tsaye ya harde hannuwanshi akan kirjinshi yana kallonta,
Batayi magana ba ta ciro wata dark blue din doguwar riga mai hannu daya sannan anyi tsaga tun daga wurin cinya har zuwa kasa ta gefe daya,
Inner wears ta ciro ta juya ta kalleshi,
"Ka fita zan sa kaya"
Murmushi yayi yajuya yafita, inner wears din ta saka sannan ta saka rigar,
Gaban mirror taje tafara gyara gashin kanta da cumb, sake dawowa cikin dakin amadi yayi,
"Wowwww....baby you look..."
Ji tayi ya rungumeta yana kissing dinta cikin so da kauna,
Wata yar siriryar sarka da dan kunne tasa,
"Zo muje kiyi breakfast.."
Hannunta yakama sai faman binta da kallo yake yi har suka fita falo suka wuce kan dining,
"Hajiya ce tayi mana dazu naje na karbo.."
"Allah sarki ai da bata wahalar da kanta ba ni sai inyi.."
"Karki damu baby kin cancanci haka"
Kulolin dake ajiye akan table din ya fara budewa, wainar shinkafa ce fara tas da ita sai miyar agushi wacce taji naman rago, gefe daya kuma kayan tea ne da ruwan zafi acikin tea flask,
Wainar ya zuba musu yafara bata tana ci,
Cikeda kulawa ya ciyar da ita takoshi sannan shima yaci,
"Wai ina kayana ne? Ina son zuwa ingaida hajiya.."
"Zakije ba yanzu ba sai da yamma.."
Batayi maganaba tayi shiru, ji tayi ya kinkimeta yayi daya bedroom din da ita wanda yake can gefe daya,
Suman zaune takusa yi saboda tsabar haduwar da dakin yayi, komai naciki pink and ash colour ne, daga gani shine dakin amadin,
Akan gado ya kwanta da ita yabita ya kwanta asamanta,
"Kallo zamuyi ko labari?"
Rufe idanuwanta tayi bata amsa ba, remote yajawo ya kunna tv yakamo tashar zee world, cakulkuli yafara yi mata tun tana daurewa saida tayi dariya,
"Dan Allah bari.."
"To kibude idonki muyi kallo.."
"Zan bude.."
"To bude"
Budewa tayi sannan yadaina yimata cakulkuli din, pillow yaja yatasa kanshi dashi sannan yasata ajikinshi ya rungumeta,
Ita dai kawai kallon take amma bawai dan tana so ba, har azahar tayi suna tare suna kallon, sakinta yayi taje tayi alwala, tana cikin daura alwalar yashiga toilet din,
Shima alwalar yayi suka fito atare,salla suka yi sannan suka koma falo, wainar da sukaci da safe ita suka kara ci,
Janta yayi suka zagaya gidan taga yanda aka kawatashi da ababen more rayuwa na zamani, ko ina yayi ba karya, hatta dan corridor dinnan wanda tagansu yana kissing din zee aciki an kawatashi da wasu kyawawan flowers sannan anzuba kujeru da dan table atsakiya domin hutawa,
Bayan sun gama zagaya ko ina yajata suka koma cikin falo,
"Zo inyi miki doki.."
Makale kafada tayi alamun bata so,
"Ko bakya so sai nayi miki saboda jikina yayi min nauyi.."
Sunkuyawa yayi ta haye bayanshi yafara zagaya falon da ita.
Saida yaji yagaji sosai sannan ya zame ya kwanta tareda birkitota kanshi, ajikinshi ya rungumeta sosai yafara lumshe ido alamun bacci ga mamakinta kuwa mintuna kadan taji ya fara ajiye ajiyar zuciya ahankali yana fitar da numfashi cikin nutsuwa alamun bacci,
Zama taci gaba dayi ajikinsa har na tsawon wani lokaci kafin ta janye jikinta takoma dakinta, wanka ta sake yi tasha kwalliya, tunowa tayi da tunda tazo bata leka dakin dake opposite da nataba dan haka batare da bata lokaci ba ta nufi dakin,
Komai nacikin dakin sak irin natane sai ko kala da ta banbanta domin shi wannan milk and coffee colour ne kayan ciki,
Akwatunan kayanta tagani ajiye agefe guda nan farin ciki yakama ta,bude akwatin taje tayi ta dauko wata atamfa Holland dark green mai zanen buta ajiki ta saka,
Sarka da dan kunne da bangles tasa ta koma falo wurin amadi yana nan ayanda tatafi tabarshi yanata shakar baccinshi,
Kan doguwar kujera tahau ta mike tana bin falon da kallo, komai na gidan amadi yafi na gidan kabeer kyau da haduwa sannan shi kansa kabeer din amadi yafishi kyau da gogewa irinta gayu, ta tabbata Allah ne yayi mata zabi har yabata amadi domin ya maye gurbin kabeer bawai iyawarta ko dabarar ta ba,
Ita dinma baccin ne yadan fara daukarta sama sama sai kuma taji motsin mutum ajikinta, bude idonta tayi ahankali nan taga amadi yana aika mata da tsadadden murmushi mai sanyaya zuciya da kashe jiki,
"Baby kinyi kyau...." Bai kai ga barinta tayi magana ba yakai lips dinshi kan nata,
"Shine kika tashi baki tasheni ba ko.."
"Ai naga bacci kake"
Mikewa yayi ajikinta, yana shakar kamshin da jikinta yake fitarwa, ganin lokacin salla yakusa yasashi tashi yaje yayi wanka yasake kaya yafito,
Sallar la'asar suka yi sannan suka tafi part din hajiya domin gaidata,
Ba karamin murna hajiya tayiba lokacin data gansu, har kasa nadiya ta tsugunna ta gaisheta shi kuma amadi sai wata shagwaba yake zubawa hajiya kamar wani yaron goye,
Basu suka bar part din hajiya ba sai bayan sallar isha, yau ma kamar jiya shine ya timaka mata tayi komai sannan ta kwanta sai lokacin shikuma yaje ya shiryo yadawo dakinta, rungumeta yayi yana shafar kanta,
"Baby yau dai bazaki yi bacci da wuriba dan haka kiyi min tatsoniya.."
"Ni ban iyaba.." Tabashi amsa,
"Ni na iya bari inyi miki.."
Tatsoniya yashiga yi mata wanda tun tana amsawa har dai yaji tayi shiru alamun tayi bacci, addu'a yayi musu ya lullubesu, gaba daya kasa baccin yayi sai tunane tunane kala kala dake addabar zuciyarsa.
Haka suka kasance har na tsawon kwana biyar, kullum hajiya ke aiko musu da abinci har nadiya tafara girki da kanta sannan idan tayi sai ta zubawa hajiya nata daban a kula akai mata,
Iya soyayya amadi yana nuna mata, komai tare suke yi dashi baya barinta tayi ita kadai.
Fitowarta daga wanka bayan tagama aiki ta zauna tayi kwalliya, towel dinta ta sauke domin saka kaya,
Burum amadi yashigo kamar wanda aka koro,
"Ahmad menene haka.." Tafada batare data jiyo ba,
"Baby abu nake nema yi hakuri..."
Riga ta saka sannan ta juya tana kallonsa yana bincike acikin drewar din gadonta,
"Wai me kake nema?"
"Wani sim pack da nashigo dashi nan jiya"
Murmushi tayi tajuya takarasa shiryawa sannan ta dauko sim pack din ta nuno masa,
"Ka ganshi nan amma tunda kashigo min daki batare da excuse ba bazan baka ba..."
Tsalle yadaka sai gashi agabanta, daga shi sai short nicker babu ko riga,
"Yi hakuri baby bazan sake ba.."
Yace da ita tareda langabe kanshi,juyawa tayi zata matsa daga wurin yayi gaggawar rikota,
Hannuwanta ta boye abaya bayan ta matse sim pack din atafin hannunta, janta yayi zuwa jikinshi yana kallon fuskarta,
Gam tarike sim pack din tahanashi turata baya yayi tafada kan gado yabita nan yafara kokarin kwatar sim pack din,
Sun dade suna burgima akan gadon kafin ya rufe bakinta da nashi, difff sukayi daga shi har ita sai ko numfashinsu dake cin karo da juna wurin fita,
Sun debe lokaci mai tsawo cikin wannan yanayi, amadi ne yafara sassauta rikon da yayi mata, tashi yayi jikinsa a mace ya fita daga dakin, sim pack din da bai dauka ba kenan yakoma dakinshi ya kwanta rub da ciki akan gado, ajiyar zuciya yake ta faman saki ahankali yana jin wata irin matsananciyar bukatar nadiya a wannan lokacin,
Saida yadanji nutsuwa sannan yatashi yashiga wanka,
Itama acikin yanayin mutuwar jiki yatafi yabarta, ahankali take sauke numfashi har numfashin nata ya daidaita, kasa fita tayi dan haka taci gaba da zamanta acikin daki har amadi ya shigo,
Blue din t shirt ce ajikinsa sai farin jeans, batare da ya karasa wurinda takeba yayi mata magana yana murmushi,
"Baby abinci...." Yafada cikin shagwaba, tashi tayi ta sauko daga kan gadon tazo zata wuce ta gefenshi, sim pack din dazu ta mika masa batare data yi magana ba, karba yayi yana murmushi,
Koda sukaje dining dinma domin cin abinci nan dinma wani sabon yanayin ne yarinka ziyartar su,
Akoda yaushe hakace take faruwa tsakaninsu, satinsu uku da tarewa yan gidansu nadiya suka zo harda mama ganin gida, wuni suka danyi mata sannan suka tafi,da kuka suka rabu itada twins dinta kamar wata yarinya haka ta zauna tana kuka, rarrashinta amadi yafara yi,
"Yi hakuri baby, tunda babu twins ai gani..."
Jin batayi shiru ba yasashi manna bakinsa kan nata, shiru tayi batare data shiryawa hakan ba,nan yashiga rarrashinta a aikace bada bakiba,
Daren ranar dakyar amadi yasamu bacci, tunani yafara yi aranshi kodai yadaina zuwa dakinta ne saboda kullum awahale yake barci sannan koda rana ne idan suna tare hakanne ke faruwa shikuma baya son karya alkawarin da ya daukar mata,dan baya baya yafara da ita, ko zuwa kusa da ita yadan rage to amma kuma shakuwar da ta dade da shiga tsakaninsu ita ke hanashi nisantarshi domin ko yawo bai iyaba kullum daga wurin aiki sai part din hajiya sai ko gida, koda yaushe suna kusa da juna sannan komai tare suke yi, ko makaranta sukaje basa iya rabuwa, daga yaji baiji motsinta ba zai lalubota awaya ko ita ta kirashi, haka daya baya iya cin abinci batare da daya ba wannan sabonsu ne,
Irin zaman da suka cigaba da yi kenan, kullum tare suke tafiya wudil su dawo tare, aikin gidan tare suke yi, girki, shara, wanke wanke,cin abinci komai tare suke gudanarwa,wannan dalilin ne yasa suka shaku mutuka.
Kasancewar yau weekend ne duk suna gida shida ita, farcenta yagyara mata ya kankare mata shi, itama tagyara masa nashi,
Part din hajiya yatafi ita kuma ta shiga kitchen ta sauke girkin da ya kammala na rana,
Daga ita sai wata yar farar yaloluwar riga iya cinya,dakinta takoma ta kwanta akan gado tafara tsifar kitson dake kanta, tun tanayi har tagaji ta kwanta sai bacci,
Ahaka amadi yashigo ya sameta, gefen kanta yaje yazauna ya dora kanta akan cinyarshi yafara yi mata tsifar, har yagama bata tashi ba yana kokarin zameta yatashi ne yaga ta bude ido,
"Baby kin tashi? Nayi miki tsifa saura abu daya.."
"Me?" Ta tambayeshi,
"Wanke gashi.."
Baj jira amsarta ba ya ciccibeta sai bathroom, ajiyeta yayi ya debo man wanke gashi kala kala yasoma wanke mata,
Rigarta ya sabule,
"Saura wanka.."
Rigar tarike, "nidai a'a"
"Wallahi sai nayi miki wanka yau.."
Jin abinda yace yasata kyaleshi ruwa ya sakar musu akansu, ganin yafara zare rigarshi yasata saurin lumshe idonta,
Sai da yayi musu wanka tas shida ita amma yakasa daina saba mata soso da sabulu, sunfi awa daya dakyar ya iya daura mata towel ya ciccibeta zuwa cikin dakinta, idanuwanshi sun gama sauya kala jikinsa duk babu kuzari amace,
Akan gado ya shimfidar da ita, ita dinma tana jinta cikin wani irin wahalallen yanayi domin dure duren umman sumaila yau kam sunce sai anfitar dasu, har wani hajijiya takeji da hajijiya tana daukarta banda murdawar da mararta tafara yi kamar wacce zatayi period,
Jin ya ajiyeta yana kokarin tafiya yasata bude lumsassun idanuwanta wadanda ke jike jalaf da ruwa sunyi wata kala tadaban,
Hannunshi ta riko......
_Sakon fatan alkhairi gareki mamu Allah yaraba lafiya..._
*_Ummi Shatu_*
[9/27, 7:50 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Home of expert & perfect writers_
_Fatan alkhairi ga masoyana masu karanta labaraina aduk inda suke, wannan shafin kyauta ne agareku,duk wata masoyiyar Ummi Shatu wannan shafi natane... Ina alfahari daku_
*69*
aishaummi.blogspot.com
*J*uyowa yayi yana kallonta, ganin irin kallon da yake yi mata yasata saurin lumshe idanuwanta,
Dawowa yayi zuwa gaban gadon ya tsugunna yana rike da hannunta jikinsa yana digar da ruwa,
"Baby ya akayi..?" Ya fada acan kasan makoshinsa,
Ita maganar ma gaba daya bata jin zata iya dan haka tayi shiru sai sake matse hannunshi da tayi cikin nata,
"Baby..."
Yasake kiran sunanta domin yana son gasgata abinda zuciyarshi ke raya mishi,
Mikewa yayi nan taja hannunshi, ajikinta ya samu masauki ya daga kanshi yana kallonta, bakinta takai bisa nashi,
Dakyar ya iya raba bakinsa da nata,
"Baby kin amince? Bazaki zargeni da laifin karya miki alkawari ba..?"
Kai ta daga masa, cikeda farin ciki hadida doki yafara warware towel din dake nade ajikinta.
***
Abangaren kabeer kuwa al'amura sun fara sauki domin tunda su fati da A'isha sukaje suka ga halin da yake ciki suka koma suka sanarwa da mama da abbansu daga mama har abban babu wanda ya kula maganar domin sunce sun dade da cireshi daga sahun yayan da suka haifa,
Kuka A'isha da fati suka shiga yi suna rokon su abban amma basu sauraresu ba daga karshe saida maganar taje kunnen abban su nadiya da umman sumaila, taruwa sukayi gaba dayansu suka tattauna tareda bawa juna hakuri tunda dai kabeer dansu ne babu yanda zasuyi sannan hannunka baya rubewa kace zaka yanke ka yar, dan haka yazama wajibi su tsaya su taimaki rayuwarsa su rabashi da asabe ko zai samu damar fita daga halin hau'ula'in da yake ciki tunda dai Allah ya rufa asiri ta sanadiyarsa zumunci bai rabu ba,
Dakyar aka samu Abba da mama suka sauko suka yarda da abinda yan uwa suka fada, nan aka dukufa ka'in da na'in wurin rokon Allah tareda yin sadaka akai akai domin Allah ya raba kabeer da masifar da yake ciki,
Cikin ikon Allah hankalinsa yafara dawowa jikinsa tun da ya kyalla ido yaga asabe agidansa hankalinsa yatashi domin bai san ya akayi ma har ya aureta ba, jinsa yake kamar wani sabon mutum wanda ya shafe shekaru aru aru cikin halin lalurar tabin hankali, jinsa yake kamar dogon barci yayi mai tsawo sai yau ya farka,
Tamkar zautacce ya zama sai faman kiran nadiya yake, nan hankalin asabe yayi kololuwar tashi domin bata tsammaci aikin boka na kududu zai karye da wuri ba,
Cikin dare kabeer yaketa aikin zuba mata masifa yana zaginta yana cewa sai tabar masa gidansa, ina nadiya? Wannan tambaya yayi mata ita tafi sau dari cikin wannan dare,
Daren ranar basu runtsa ba saboda tashin hankali, zagi kuwa asabe ta shashi agun kabeer yafi akirga sai kiranta da karuwa yake,
Lokacin da asuba tayi yafita salla lokacin ne tasamu damar kiran kawarta teemah ta zayyane mata abinda yake faruwa nan teemah tabata shawara, sosai taji dadin shawarar teemah kuma tayi na'am da ita,
Shi kuwa kabeer yadade yana addu'a a masallaci domin yaushe rabonsa ma da zuwa masallacin? Shi kansa bazai iya tuna lokacin ba domin tunda asabe ta shigo cikin rayuwarsa komai nasa ya lalace,
Yana fita daga masallaci yaje ya figi mota sai gaidansu, ganinsa sassafe yasa mama cikin tashin hankali domin tayi zaton ba kalau ba,
Kuka yasata agaba yafara yi yana neman gafararta tareda rokon cewar ta yafe masa,
Mama cewa tayi ta yafe masa duniya da lahira, cikin wannan hali abba yashigo ya riskesu shi dinma gafararsa kabeer ya nema yana kuka hawaye bibbiyu akan kumatunsa,
Dukkaninsu iyayen nasa sun yafe mishi amma Abba yabashi shawarar cewar ya tsaya yadage da addu'a sannan indai yana son ya zauna lafiya to ya zama dole yarabu da asabe, shiru yayi yana goge hawayen fuskarshi domin dama ko abba bai fada ba yanada wannan tunanin na sakin asabe,
Har karfe 10 tayi yana gidansu tareda iyayen nasa suna dorashi akan hanya mai bullewa, 10:30 ya tashi ya tafi da niyyar zai dawo gidan anjima,
Koda yakoma Gida tun daga get ya hade rai domin yau so yake ya nunawa asabe cewar tayi babban kuskure amma kuma koda yashiga cikin gidan sai me??
Komai an hargitsa shi baya bisa ka'ida, fuskarshi ahade yashiga falonta nan dinma anyi kaca kaca dashi, haka bedroom dinta ma amma kuma ita bata nan, nan yashiga dubata amma babu ko alamarta, ganin babu wasu muhimman kayanta ya tabbatar masa da cewar bata gidan, gaba daya ta tattare kayanta da nasa masu amfani ta gudu.
Zama yayi cikeda takaici gamida dana sani mai tsanani tareda bacin rai dake faman ziyartar zuciyarsa, in banda tafarfasa babu abinda zuciyarsa keyi, sannu ahankali wasu hawayen nadama suka fara bin kumatunsa,
Yadade zaune yana kukan takaici kafin ya iya tashi, yama rasa abinda zaiyi domin idan yace zaibi asabe mc to bai san ta inda zai fara nemanta ba domin ko yaje jos zaiyi wuya yaganta,
Sake rufe gidan yayi yafita ya nufi masallaci domin har azahar ta kusa, daga can gidansu yasake komawa nan ya zauna tareda su mama, mama sai nasiha take yimasa tana yimasa fada akan rayuwa domin ko yanzu yaga darasi irin na kaidin mata.
Sai dare yabaro gidan yakoma nasa, kasa bacci yayi sai aikin tunani, can karfe 2 nadare yaji alamun dirgowar mutane cikin gidan, ta window yaleka nan ya hango mutane guda hudu da bakaken kaya hatta fuskarsu rufe take da bakin abu, mai gadin gidan yaga suna kokarin daurewa dan haka yayi gaggawar neman wurin buya.
Cikeda da sand'a hannuwansu rikeda bindigogi suka shiga dakin nasa amma neman duniya sunyi basu ganshi ba, ko ina na gidan saida suka caje tsaf amma babu kabeer,
"Ya oga yakamata fa mu ware tunda bamu ga wannan gayen ba, kar asuba tayi mana anan.."
D'aya daga cikin yan fashin ya fada,
"Haka za ayi zaki bari nakira waccar mata..." Ogan yafada yana latsa wayarshi, mintuna kadan yakara wayar a kunne,
"Ya kun kasheshi..?"
Asabe mc ta tambayeshi ta cikin wayar,
"Ai bamu ganshi ba, da ace mun ganshi da tuni mun dade da hallakashi.."
Dan shiru yayi yana saurarenta kafin yace,
"Shikenan bari mu faso.."
Juyawa yayi ga yaranshi, "ya kuzo mubar gidan nan kun san tafiyar mu mai nisa ce.."
Basu kara bi takan mai gadin ba suka kama katanga suka tsallaka bayan yan mintuna kuma yaji sun sake dawowa sun dauki motarsa kwaya daya wacce tayi saura, duk abinda yake faruwa akunnen kabeer ne domin yana makale cikin rizabuwa yana jinsu, dama rizabuwar babu ruwa yanzu aciki ita yabude yashiga ciki ya buya,
Duk da yaji tafiyarsu amma bai iya fitowa ba har saida asuba tayi, duk yabi yahada zufa,
Mai gadi yaje ya kunce wanda duk yajigata.
Gari yana wayewa kabeer ya sallameshi sannan shima ya hada duk kayanshi wadanda sukayi saura wanda yasan zai bukata ya kulle gidan yanufi gidansu,
Al'ajabi sosai su mama suka shiga domin abin al'ajabine wai asabe mc tasa ana farautar rayuwar kabeer, tun daga wannan rana yakoma gidan da zama, gashi babu aikin yi nan yashiga fafutukar neman wani,
Duk da yanajin kunyar abban nadiya da mamanta haka ya daure ya cije yaje gidan ganin yaransa, yaji dadin yanda aka karbeshi babu wanda ya nuna masa koda afuska, tun daga ranar yasamu wurin zuwa, kusan kullum sai yaje gidan yaga yaransa.
***
Soyayya mai sanyi amadi ya shiga nunawa nadiya, ita kanta tasan tayi sa'ar miji domin komai nashi cikin nutsuwa yake aiwatar dashi sai dai abinku da sabin shiga dole sai ya nuna rawar kai,
Ita dariya ma yake bata amma bata samu zarafin yin dariyar ba har saida nutsuwarta ta dawo gareta,
Hannunshi takama tana dariya kasa kasa, idonshi ya bude ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya ahankali,
"Baby dariya..." Yafada ahankali cikin sanyin murya yana kallonta,
Girgiza masa kai tayi tana kunshe dariyarta, jikinta ya matsa ya rungumeta yana gyara mata gashin kanta wanda yake ajike jalaf ya zubo ya rufe mata fuska,
"Baby Allah yayi miki albarka, Allah yasa ki haifa min twins..."
Kallonshi tayi ta mayar idanuwanta ta lumshe,
"Saboda baka san wahalar dawainiyar yan biyu ba ko shiyasa kake yimin fatan..."
"Meye wahalar aciki?" Ya katseta,
"Rainonsu.." Tabashi amsa,
"Zan tayaki.."
Yatsanshi yadora akan lips dinta ya hanata magana, wani sanyayyen kiss ya manna mata akumatu sannan yafara nuna mata soyayyar da yake mata akaro na biyu, sam bata yi yunkurin dakatar dashi ba domin shi bai taba aure ba yaune rana mai daraja agareshi,
Jinsa yayi acikin wata duniya ta daban wacce bazai iya fassara yadda takeba,
"Baby indai hakane amma kin dade kina cutar damu, meyasa baki bari mun samu wannan farin cikinba tun farkon auren mu... Kar Allah ya maimaita min rayuwar da, baby da batayi ba, yanzu ne nasan ni dan gatane cikakke..."
Rungumeta yayi yana jin sonta yana sake ratsashi,
"Amadidi tashi..." Yaji tafada,
"ba amadidi ake cewa ba, amadi zaki ce" yabata amsa idanuwansa arufe,
"To didi..."
"Meye kuma wani didi sai kace yaro..?
"Dafa? Koda yake yau ka dan fara girma ashe.."
Ya fuskanci tsokanarshi take yi shiyasa ya rabu da ita yana murmushi shi kadai,
"Kaida wa?"
"Muje inyi miki wanka.."
"A'a nagode..."
Ko saurarenta baiyi ba ya dauketa zuwa toilet,duk da itace ta nema da kanta saida taji ya isheta saboda wankan ma bai yiyuba, yau ta barowa kanta aiki,
Sai da aka dade iya dadewa sannan wankan yasamu suka fito yana goye da ita abayanshi.
Towel yadauka yafara goge mata jikinta dashi yana aika mata da murmushinsa mai sanyi,
"Baby.... Ince wani abu?"
"A'a karka ce"
"Saboda me?" Ya tambayeta yana yi mata murmushi, cumb ya dauka yasoma taje mata gashinta,
"Saboda nasan abinda zaka ce.."
"Taya akayi kika sani?"
"Nidai nasani dan haka basai kafada ba..."
Dariya ya danyi yalashi jan lips dinsa,
"Allah baby yau kin sa nazama kamar maye..."
"Shine"
Tabashi amsa bayan ta kwace cumb din, bai hakura ba yakoma bayanta ya zauna tareda rungumeta,
Rabuwa dashi tayi taci gaba da taje gashinta tana gyarashi,
Daure gashin tayi da blue din ribom ta mike taje ta dauko wata doguwar riga mai santsi yar kanti mai karamin hannu tasa,
Amadi ta kalla wanda ke zaune ya langabe kai yasa yatsanshi daya abaki, murmushi tayi,
"Wallahi yan auta dama sai ahankali, kalleka fa yanda kayi kamar wani dan karamin yaro..."
"Su kuma yan fari fa? Fada min su yasuke" yabata amsa bayan ya mike,
"Ai kasan dai yan fari sunfi yan auta ako ina..."
"Sharafffff malama.." Yace da ita tareda ficewa daga dakin, dakinshi yaje ya shirya mintuna kadan sai gashi ya shigo, tana gaban mirror tana saka dan kunne bayan tayiwa fuskarta kwalliya,
Ta cikin mirror din ya nuna mata rubutun dake gaban rigarsa, rubutun ta kalla _Yes I did it_ shine abinda aka rubuta, murmushi tayi masa wanda ya ratsa zuciyarsa har yakasa hakuri saida yakai ga bata tukwici ta hanyar shanye gaba daya jan bakin da ta shafawa lips dinta,
Duka ta dan kai mishi akirji ta harareshi,
"Biyani jan baki na..."
Saida yasake tsotson bakin nata sannan yashafa mata wani yana yi mata gwalo,sake shagwabewa tayi nan ya dauketa cak yayi falo da ita,
Sallar azahar suka yi tare sannan suka ci abinci, matseta yayi tsam ajikinshi yau gaba daya ya hanata ko fita nan da can, ko part din hajiya yahanata lekawa, duk inda tayi yana biye da ita kamar wani jela har dare yayi,
Yau ko yar hirar ma da suka saba yi bai barsu sunyi ba saboda fitinarshi, ita nadiya duk yagama isarta,
Da safe da zazzabi yatashi, dariya nadiya tayi,
"Maganinka, anfada maka haka akeyi? Kabi komai asannu kaki"
Kallonta yayi yatashi zaune,
"Dariya kike yimin ko baby? Dariya ko? Nagode.."
Tashi yafara kokarin yi nan tahanashi tashige cikin jikinsa tana murmushi,
"Yi hakuri didi na, wasa fa nake yimaka, anjima zakaji zazzabin yatafi ai, sannu"
Daga mata kai yayi, haka yawuni bai fita ko compound din gidan ba har yamma sai lokacin yaji jikinsa yayi masa daidai sannan zazzabin ya sauka, wanka yayi yasa kananan kaya na hutawa,
Kan doguwar kujera yahau ya kwanta ya tasa kanshi da cinyar nadiya, yar hira yake yimata kadan kadan yana lalubarta,
Dabara tayi masa tace yatashi suje su gaida hajiya, tashi yayi suka fita zuwa part din hajiyan, suna zuwa sukaga anty siyama sunzo itada yaranta guda biyu da zee din amadi,
"Lahhh anty dan waken zagaye akayi mana yau?... "
Amadi yafada yana rungume yaran ta,
"Dama na jira ku fito ne, kun san ba ashiga gidan amare kai tsaye... Ko ba hakaba anty amadi??"
Murmushi yayi ya kalli nadiya nan tayi saurin wucewa tabarshi,
Saida suka gaggaisa sannan suka dunguma suka koma part din su amadi, nadiya ko kallon zee batayi ba bare su gaisa,
Abaya amadi ya tsaya, yana ganin Anty siyama tawuce yajawo nadiya, ita dinma dayake tana son bawa zee haushi bata ki ba harda su bashi kiss akumatu,
Su anty siyama sun dan jima sannan suka tafi nadiya sai cewa take abar mata yaran suyi kwana biyu amma fur amadi yaki yace a'a angonci yake yi, anty siyama kam jan yaranta tayi tace itama bazata barsu ba dama.
Babin rayuwa mai dadi suka bude domin itama nadiyan yanzu tafara sonshi wanda ita kanta bazata ce ga lokacin data faraba,
Komai tare suke gudanarwa shiyasa suka shaku da juna sosai,saida sukayi sati uku agida suna gudanar da soyayya sannan suka fara fita.
Yau juma'a da misalin karfe 9 nasafe nadiya na kitchen tana shirya musu breakfast,
Amadi ne yashigo yana mika daga shi sai gajeren wando da riga armless milk colour amma duk da haka ba karamin kyau yayiba kamar badaga bacci yatashi ba,
Rungumeta yayi ta baya tareda kashe gas din datake girki,
"Didi meye haka?" Tafada tana harararshi awasance,
"Zo muje kiji, magana zamuyi.."
Bata musuba tabishi zuwa cikin bedroom dinshi, zaunarta yayi agefen gado shima yazauna yana facing dinta,
Yadauki mintuna masu tsawo yana kallonta batare da yayi magana ba,
"Didi menene? Kafada min mana"
Idanuwanshi ya lumshe nan kyawunsa yasake bayyana,
"Baby kina sona?"
Kallonshi tayi cikin rashin fahimta,
"Meya faru?"
"Kawai kibani amsa.."
Kai ta daga mishi,
"Ehhh ina sonka"
Ajiyar zuciya yasaki,
"Baby kiyi hakuri da abinda zan sanar dake ahalin yanzu, idan kabeer yadawo yace yana son ki koma gareshi zaki amince?"
Hankalinta ne yasoma tashi ta kalleshi,
"Haba didi, inkoma wurin kabeer inyi me bayan inada kai ahalin yanzu, meya kawo wannan maganar?"
"Baby zaki koma ga kabeer nanda dan lokaci takaitacce, yau ranace wadda zan fito infada miki gaskiyar koni waye... Yau zan bayyanar miki da wani labari wanda ke baki saniba..."
Hannuwanta da suka fara rawa ya rike yana kallonta, gaba daya jikinta rawa yake kamar mazari alla alla take taji abinda zai fada mata domin hankalinta yatashi mutuka,
"Didi ka sanar dani, me yake shirin faruwa ne?"
Kallonta yayi ya sunkuyar da kai,
"Nadiya nasan ada bakya sona kuma bakya kaunata, to ni dinma ban aureki dan kisoni ba domin inada wacce take sona kuma zan aurota mu zauna nan bada jimawa ba, ni dama na aureki ne kawai domin inyi taimako guda daya.. "
Idanuwa ta zaro tana kallonshi, tuni goshinta ya jike da gumi duk da sanyin ac din dake kadawa, wannan shine bazata, bakinta yana rawa tace,
"Didi taimakon me? Dalilin wanne taimako ka aureni?"
Nikaina Ummi Shatu tambayar da take makale akan fatar bakina kenan,haka kuma masu karatu nasan kuna bukatar wannan amsa....
*_Ummi Shatu_*
[9/28, 8:49 PM] Ummi ~ Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Home of expert & perfect writers_
_Ina mika sakon gaisuwa da babbar murya ga masoyan anty amadi musamman wadanda basa son rabuwarshi da nadiya, anty amadidi yagaisheku kyauta, haka duk wata wacce page 69 ya girgizata ko ya taba zuciyarta to ummi Shatu tabata page 70 kyauta tukwici agareta,sannan masoya kuyi hakuri kuma kuyi min uzuri domin littafin mijina sirrina labarine wanda yafaru agaske bawai kirkirar labarin nayi narubuta ba dan haka banida damar canjashi dole yanda yafaru haka zan rubuta saiko yan abubuwan da baza arasa ba, masu yimin text da masu kirana da wadanda suka nemi contact dina basu samuba duk nagode da kokarinku sannan ina gaisheku aduk inda kuke..._
*Ke din ta dabance maryam qaumi, hakika banda kamarki kawata, Allah yabarmu tare,*
*70*
aishaummi.blogspot.com
*G*aba daya jikin nadiya karkarwa yake yana rawa, so kawai take taji labarin da Amadi yace zai sanar da ita wanda ita bata saniba,
"Didi karka yimin haka, amadi idan ka yaudareni kayi wasa da zuciyata har nafara sonka bayan ada ba sonka nake yiba wallahi sai Allah yayi min sakayya..." Tafada idanuwanta sunyi jajur kamar gauta amma bata bar hawaye ya disa daga idanuwanta ba,
"Kiyi hakuri nadiya, nima ba ason raina zan barki ba sai dan babu yanda zanyi,
Abune wanda yazama dole sai nasanar dake, dan Allah ki nutsu ki saurareni sannan ki yarda da kaddarar data riski rayuwarmu adaidai lokacin da muka shaku da juna, muka aminta da juna, zuciyoyinmu sukai tarayya awuri guda..."
Shiru yayi na dan lokuta yana kallonta wanda shi dinma idanuwanshi sun kada sunyi jajur kamar gauta,
Jin yayi shiru yakasa magana yasata kallonshi da jajayen idanuwanta, idanuwanshi akasa suke yakasa koda kallonta,
Yau nadiya jinta take kamar acikin mafarki take, gaba daya nutsuwarta bata tare da ita,
"Ka fada min abinda zaka fada min ina sauraronka.." Tace dashi bakinta yana rawa da jikinta gaba daya,
"Nadiya kabeer ne yasani in aureki,
Mun hadu dashi ne akasar misra lokacin hajiya bata da lafiya an kwantar da ita, shikuma ban san uzurin da yakaishi ba, anan mukayi sabo dashi har takaimu ga kulla alkawarin taimakawa juna,
Nadiya ba auren kisan wuta nayi dake ba..."
Katseshi tayi cikin karaji,
"Karya kake macuci azzalumi, idan ba auren kisan wuta kayiba me kayi..?"
Kwalarshi taje taci tana girgizashi,
"Ina tambayarka idan ba auren kisan wuta ba me kayi? Kafada min abinda kayi.."
"Nadiya wallahi nafi karfin nayi auren kisan wuta, kin san dai munada kudi bare kice ko dan kudi nayi, inada ilmi bare kice dan neman wani abu nayi ko dan jahilci, inada duk wani abu wanda dan adam yake nema acikin rayuwa..."
Kukan data fashe dashi shine yakatse maganar da yake yi,
Kifa kanta tayi ajikin gado tana kuka,kafin ta dago ta rungumeshi tana fadin,
"Ni bana son kabeer yanzu kai nake so, meyasa zaka koya min sonka bayan kasan ba son gaskiya kake yimin ba...?"
"To ai kinki bari inyi miki bayani sai faman kuka kike..."
"Wanne bayani zaka yimin? Bayan kaci amanata.."
Zame hannuwanta yayi daga jikinshi ya mike zuwa wurin bedside drewar nan ya bude ya ciro wata zungureriyar takarda wadda dama da alama yajima da tanadarta,
Ajiye mata takardar yayi akan hannunta yafita daga dakin, dafe takardar tayi tana kuka batare data dauka ta karanta ba,
Kukanta taci gaba dayi bata ko motsa ba daga inda yatafi yabarta, tsabar kuka idanuwanta duk sun kumbure sunyi jajur, kanta kuwa kamar zai fashe da ciwo ga yunwa da take faman damunta domin bataci komai ba,
Haka tawuni a durkushe tana kuka, shikuwa amadi abisa dukkan alamu ma baya cikin gidan sai yamma yadawo da misalin karfe 3,
Dakin da yabarta aciki yaje ya bude yashiga, har lokacin tana sulale awurin taci kuka tagaji tana jan numfashi dakyar,
"Baby wai har yanzu baki bar..." Ganinta ayashe akasa yasashi kasa karasa maganar da yasoma,
Agaugauce yaje inda take yadagata zuwa jikinsa,
"Baby... Baby..."
Bude idonta tayi tana ganinsa tasake fashewa da kuka gamida kara rungumeshi,
"Dan Allah didi kace ka janye sakin da kayi min, wallahi ina sonka, bana son kowa yanzu sai kai,kaine MIJINA SIRRINA..."
Idanuwanshi ne suka cicciko da kwalla, kinkimarta yayi ya dora akan gado yakwanta ajikinta,
"Baby wai tun lokacin da natafi kike awurin nan baki tashi ba?? Meyasa zaki yimin haka?"
Jin jikinta yafara daukar zafi yasashi tashi arazane ya riketa,
"Baby zazzabi? Zazzabi zakiyi? Ko inyi miki wanka?"
Girgiza masa kai tayi alamun a'a, mintuna kadan jikinta ya gauraye da zafin zazzabi kamar garwashi,
Hankalinsa ba karamin tashi yayiba, Dr Salaha yayi azamar kira, yana gama kiranta yakoma jikinta ya kwanta yana jijjigata kamar jaririya,
Duk yarasa inda zai tsoma ransa yaji dadi ganin halin da take ciki,
Zuwan Dr salaha ne yasashi mikewa daga kan gadon yaje ya shigo da ita,
Duba nadiya tayi tabashi maganin da zai bata idan taci abinci sannan ta jona mata karin ruwa,
Sallama yayi da dr salaha ta tafi shikuma yakoma kusa da ita ya zauna yana shafar gashin kanta, har fuskarta ta dan fada saboda tsabar tashin hankali,
Ta dan jima tana bacci sannan ta farka, idanuwanta ta bude taga amadi akusa da ita yana rike da hannunta, jin tayi dan motsi yasashi tashi zaune yana kallonta,
"Baby kin tashi? Inkawo miki abinci kici kisha magani?"
Kai ta daga masa idonta dauke da kwalla, ruwan dake hannunta ya cire mata saboda yakare, sauka daga kan gadon yayi ya fita zuwa kitchen,
Bai wani bata lokaci ba sai gashi yashigo dauke da filet da cup,
Dankali da kwai da sos ya zubo mata sai dan ruwan tea acikin cup, zaune ya tadata yafara bata dankalin abaki tana ci, kallonsa kawai takeyi idonta cikeda kwalla,
Girgiza mata kai yayi yana rikeda hannunta guda daya,
"Baby meyasa baki nutsu kin karanta takardar da nabaki ba, da kin karanta da duk haka bata faruba saboda nasan zaki fahimci abinda nake nufi kuma zaki gane komai acikin sauki.. Dan Allah kiyi hakuri karki yi kuka, kidaina kwallar nan haka"
Goge mata kwallar yayi yaci gaba da bata dankalin tana ci, saida taci da yawa sannan yabata ruwan tea din tasha yabata magani tasha har lokacin jikinta akwai zafi amma dai taji saukin ciwon kan da yaketa azazzalarta kuma ciwon da jikinta yake yi mata shima ya dan ragu,
"Zanyi wanka kuma banyi salla ba.."
Tafada muryarta adashe, ahankali ya dagota ya riketa ajikinshi yazuge zip din rigar jikinta ya cire mata rigar, shi dama baijin kiwar daukarta akoda yaushe dan haka ya dauketa cak yayi toilet dinshi da ita,
Ruwa mai dan dumi yatara mata yasata aciki yayi mata wanka amma dakyar ya iya controlling kanshi,alwala yayi mata bayan yagama yimata wankan ya daura mata towel dinshi ya fita da ita, agefen gado ya zaunar da ita sai faman binshi da ido take yi, fita yayi zuwa dakinta ya dauko mata kayan da zata saka,
Wata jar doguwar riga mai mutukar kyau ya dauko mata, rigar bata da kauri dayawa sannan kuma irin mai mannewa ajikin mutum dinnan ce sannan anjera wasu duwatsu ajikinta,
Pant da bra ta karba tasa da kanta sannan yazira mata rigar yafesa mata turarenshi na axe, daga zaune tayi salla tana idarwa ya mika mata wannan takardar ta dazu, gabanta ne yasake faduwa ta daga ido tana kallonshi zuciyarta tana yimata wani irin suya wato dai amadi yadage sai ya rabuda ita ko?,
"Kiyi hakuri ki karba ki karanta baby..."
Jikinta yana rawa ta karba ta warware tafara karantawa, yana ganin haka yatashi yafita daga cikin dakin, cikin rawar jiki nadiya tafara karanta takardar kamar haka:
_Farawa da dunbin gaisuwa agareki yake kyakkyawa kuma mace mai mutukar daraja awurina, hakika nayi farin ciki mai tarin yawa kasancewarki mata agareni, nasan abinda nayi miki ban kyauta ba kuma na sanya zuciyarki acikin wani hali amma ina neman afuwarki abisa laifin da nayi, kisani nayi hakane domin auna adadin irin soyayyar da kike yimin, actually ayau ina cikeda farin ciki mai yawan gaske saboda jin da bakinki kince kina sona yanzu, wannan kalmar da kika furta min bazan barta tatafi abanza ba shiyasa na tanada miki tukwici mai yawan gaske, dafarko ki duba cikin bedroom dinki zakiga tukwici nafarko, tukwici na biyu kuma idan nadawo zaki ganshi, tukwici na uku kuma sai kin kammala karatunki zan baki shi, kiyi hakuri duk abubuwan da nafada miki dangane da kabeer wallahi ba gaskiya bane am joking,kisani babu wata mace da nake iya gani sai ke kadai, i luv u...._
Yours for Eva
didi
Tukwikwiye takardar tayi ta mike tana jin wani irin karfi ajikinta, dakinta ta nufa tana zuwa tabude ta shiga, akwatina set biyu tagani guda 24 masu dan banzan kyau pink and purple kowanne anrubuta A & N ajiki da manyan harrufa,
Kobata budesu ba tasan kayan ciki bana wasa bane,
Juyawa tayi tafita ta nufi falo saboda daya tukwici din dama yace sai yadawo,
Key din mota tagani ya ajiye mata akan center table din dake tsakiyar falon tareda yar karamar farar takarda,
_Baby kije waje kiga motarki..._
Shine abinda yarubuta ajikin yar takardar da ya ajiye mata zama tayi sharaff akan kujera batare data je taga motar ba,
Duk da cewar zuciyarta tayi sanyi amma har yanzu bugawa zuciyarta keyi bata daina ba ga ciwon kai, dafe goshinta tayi tana jiyo motsinshi a corridor,
Tana zaune acikin falo yashigo yasha jeans brown da blue din t shirt anrubuta awesome ajiki,
Zama yayi akusa da ita yana zuba kamshi fuskar nan sai annuri ne ke fita daga jikinta,
"Baby ga wayarki da na canja miki, kedin fa yar gatace..."
"Malam ni ka rike duk kayanka bana so, wancan dinma gara kaje ka kwashe abinka domin bana bukatarsu..."
Murmushi yayi yakai mata kiss ta tureshi batareda tabarshi yayi ba,
"Shiyasa akarshen takardar nabaki hakuri saboda kukan da nasaki,
Baby yanzu ke idan nace zan rabu dake sai kiyarda? Kisawa ranki cewar mutuwa ce kadai zata iya nasarar rabamu, idan har zan iya yaudararki ko naci amanarki ashe so karyane, da mutanen duniya sun daina yarda da kowa, da sun daina bawa kowa amana,
Abinda yasa kikaga na bullo miki ta wannan hanyar shine, ranar farko dana fara baiyanar miki da soyayyata agareki sai kika nuna min cewar bazaki taba sona ba har abada kuma da bakinki ma kin furta min hakan,
Har yanzu abun yana raina kuma yana damuna, zuciyata takasa tabbatar min da cewar kina sona ko kuma sabanin haka shiyasa nayi haka domin na samu tabbaci... Sorry baby"
"Kaga nifa yanzu duk wadannan kalaman naka bazasu yi tasiri ba agareni, sannan ina son kasani nima yanzu nadaina sonka..."
Katseta yayi ta hanyar dora yatsanshi akan lips dinta,
"Ai karma kiyi wannan maganar, nida ke ahalin yanzu duk muna son juna dan haka babu amfanin mu tsaya muna wahalar da zukatanmu,
Kuma ma inbanda abinki baby tayaya zan iya sakinki alhalin na dandani zumar dake tare dake? Kin san kuwa yanda nake kishinki? Wallahi ko kinyi min laifi babba zaiyi wuya in inya rabuwa dake saboda ban son kisake komawa kabeer, ina bakin cikin kasancewarshi mijinki nafarko, naso ace nine nafara aurenki, da nabaki jin dadi marar yankewa wanda zaisa bazaki kara kallon wani namiji ba domin zaki rinka kallonsu a matsayin mata yan uwanki,amma duk da haka ai nasan yanzun ma nayi kokari.."
Kicin kicin tayi da fuska ta hade rai kun san mutuniyar taku akwai iya tsare gida,
"Nidai nafada maka, nima yanzu bazan zauna dakai ba gidan tsohon mijina zan..."
Saurin rufe mata baki yayi da hannunshi yajata jikinshi ya matse,
"Me zaki koma kiyi agidan wannan bakauyen? Wani baki mummuna dashi, ni haushinsa nakeji yagama sanin sirrina.."
"Karka kara zagar min uban yayana.." Tafada bayan tasake daure fuska, jijjiga kai yayi yana murmushi,
"Nidai bazanyi fada dake akan wannan kucakin gayen ba saboda nasan ba iya kyau kadai nafishi dashi ba hatta bawa mace nutsuwa nafishi..."
Shiru tayi masa tafara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata,
"Kin san Allah haushin wannan kabeer din nakeji, Allah yasa sai yamutu sannan zan mutu saboda kar na rigashi mutuwa yasake maye gurbina yahanani kwanciyar kabari"
Bata sake kulashi ba illa fuska data hade ta bata rai, hijabin jikinta ta cire ta koma kan carpet ta kwanta,binta yayi kasan ya jingina da jikinta yayi ruf da ciki asamanta,
"Baby bai kamata alkhairi yazama mugunta ba, ya kamata ki karbi tukwicin da nabaki hannu bibbiyu.."
Jin tayi shiru bata tanka masa ba yasashi birkitota ya shige jikinta, koba komai dai taji dadi da ba gaskiya bane abubuwan da yafada mata da safe,
Shareshi taci gaba dayi sai shan kunu take tana ciccin magani har yagaji yatashi yatafi part din hajiya, sanin tana fushi dashi yasa yaki dawowa saida dare yayi,
Lokacin da yafita akwatunan da ya ajiye mata taje ta dan dudduba wadanda zata iya domin kayan sunyi yawa ita kanta tasan kayan nan sun lashe dukiya mai yawan gaske domin akwatun english wears daban, na shadda daban, na less daban, na atamfa daban, na hijabai daban, na gyale daban, na inner wears, komai dai da akwatinsa, sannan ga wasu kit guda biyu cikeda gwala gwalai,
Tea taje tahada ta dafa indomie da kwai ta ci tayi wanka ta kwanta, ko rigar bacci yau bata tsaya sakawa ba saboda jikinta babu karfi,
Jin alamun tafiya ya tabbatar mata da dan rigimar ne yadawo, dakin yashigo yana sanye da kayan bacci,
"Baby yau da towel za ayi baccin?" Yace da ita bayan ya sunkuya yana leka fuskarta,
Fuska ta daure ta kalleshi,
"Menene haka?"
"Baby kenan, wai maimaikon kiyi murna amma sai faman fushi kike yimin har yanzu kinki hucewa.."
"Akan me zan huce? Ai nafada maka nima yanzu bazama zanyi dakai ba gidan mijina zan koma.."
Jin kalmar yayi ta soki kirjinshi kamar kibiya,
"Kinga baby bana son irin wannan wasan, kibari ya isheki haka, kuma indai nine zan sallameki ki koma gidan wannan banzan to har abada kuwa bazaki koma ba.."
Ture hannunshi tayi daga shafa ta din da yakeyi,
"Nafada maka kadaina zagar min uban'yaya..."
Murmushi yayi ya rabu agefenta ya kwanta,
"Yakamata dai nima inyi zuciya na haifi yayan nan ko za adaina yimin gori.."
"Da wacce take sonka zaka haihu amma bada..."
Baki ya rufe mata,
"Insha Allah dake zan haihu kuma twins zamu haifa kodan inhuta gori.."
"Ai twins dinma ba kowanne rago ne yake iya bayar dasu ba.."
Fuskarshi yakai kan tata yafara shafarta yana dariya domin shi kome zaka fada masa baya fushi sai dai yayi dariya ko murmushi ita kanta tunda take dashi bata taba ganin fushinsa ba,
"Me kike nufi to? Kina son kice ni bazan iya bada twins ba? Wannan jemammen ma yabayar da twins bare ni, ni idan kika yi wasa ma nayi zuciya uku zan baki ko hudu alokaci daya.."
"Sai kayi kuma.."
Tashi yayi ya ciro mata rigar bacci pink colour yar karama marar nauyi mai siririn hannu yazo yasa mata yazare towel din da yake jikinta,
"Nima dai nakusa zama uban yayan..."
"Ko?"
Tace dashi cikin yatsina fuska,
"Ohhh tambaya ma kike? To kodai tabbaci kike nema.."
"Watakil.."
Janta da fada yaci gaba dayi yanata kushe kabeer ita kuma sai kare kabeer din take domin tana son ta cusa masa haushi, ai kuwa saida tayi nasarar cusa masa haushin sannan tayi shiru ta rabu dashi, sakinta yayi ya juya mata baya alamun yayi fushi,
Tana jinshi tayi luff kamar mai bacci, tashi zaune yayi saboda yagaji da kwanciyar,
"Mtswww Allah kasa badagaske take ba, wallahi ko zaku mutu daga ke har kabeer din bazan sakeki ba..."
Dariya ce ta taho mata tayi saurin toshe bakinta,
"Ohh saboda ni bamu haifi yaya ba shiyasa har ake yimin gori..., bari ki samu sauki nima ai ba iya yimiki cikinne zaifi karfina ba"
"Wai meye haka? Kafa dameni da surutu kuma bacci nake ji..."
Komawa yayi ya kwanta, yajuya yana kallonta,
"Baby..."
"Menene?"
"Ban saniba..."
"To shikenan" tafada tareda juyawa, juyo da ita yayi tana fuskantar shi fuskarshi dauke da kishi bayyananne.....
*_Ummi Shatu_*
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Home of expert & perfect writers_
*71*
*S*ake murtuke fuska tayi tana kallonshi ta cikin dan hasken da yayi saura acikin dakin,
"Baby akan wannan maganar fa ina iya batawa dake garama tun wuri ki bari.."
"Kaga ni ka kyaleni bacci nake ji.."
"Dama zan kyaleki kiyi bacci amma sai nagama yimiki kashedi da gargadi akan wancan mutumin..."
Kwace jikinta tayi ta koma ta kwanta gamida juya masa baya,
Duk da adan cikin fushi yake hakan bai hanashi rungumeta ta baya ba bayan ya kwanta,
Da asuba ta rigashi tashi bata tasheshi ba sai bayan ta iyo alwala domin ka'idane tare suke yin salla, tashinshi taje tayi,tashi yayi yana kallonta yana dan harararta alamun bai huce ba daga fushin da yayi adaren jiya,
Yi tayi kamar bata ga hararar da yake aika mata ba, sauka daga kan gadon yayi ya nufi toilet yana fitowa yaganta akwance taja bargo ta lulluba,
Bargon yaje ya yaye yana kallonta,
"Sallar fa?..."
Dan juyi tayi sannan ta waiwayo ta kalleshi,
"Kayi sallarka kai daya ni banayi.."
Wata hararar yasake jifanta da ita baice komai ba yatafi kan dadduma yatada kabbarar salla,
Bayan ya idar ne yayi addu'o'i kamar yadda yasaba sannan yatashi yakoma kan gadon,
"Gaskiya ni kin gama dani gaba daya, wai dama kin san yau zaki tashi da wannan abun shine zaki sakani agaba jiya da masifa ki hanani samun farin ciki, abu kadan ki wani hade rai kina ciccin magani dan kawai anfadi gaskiya akan wannan...."
"Yau kuma da abinda katashi kenan?? Lallai" tafada tana sake gyara kwanciyarta,
"Ehhh da abinda natashi kenan"
Shiru tayi masa ta lumshe idonta kamar mai yin bacci, tana jinshi sai faman juyi yake har gari yayi haske tun tana jin motainshi har bacci ya dauketa,
Ganin tayi bacci yasashi komawa falo ya kunna labarai yana gani anan shima baccin ya daukeshi bashi ya farka ba sai misalin karfe 8 nasafe,
Motsinta yajiyo acikin kitchen alamun tana hada abun karyawa, tashi yayi yabita zuwa cikin kitchen din ahankali ya sadada yaje ya rufe mata idanuwanta,
"Malam meye haka?"
Murmushi yayi ya matsa kusa da ita tareda kallon fuskarta, tasha kwalliya sosai sai kamshi take zubawa, tana sanye da atamfa maroon mai zanen hang bag ajiki,
"Kinyi kyau amaryata..."
Baki ta turo batare datace komai ba,
"Baby wai maganar jiyanne har yau bata wuceba, kinga fa sabuwar wayar da na siyo miki can har yanzu baki dauka ba idan bakya so ki fada min sai inkaiwa budurwata..."
Jin abinda yafada daga karshe yasata hada girar sama data kasa sannan tabashi amsa,
"Ka kai mata nima mijina zai siyo min idan nakoma gidanshi..."
Bai san lokacin da yakaiwa bakinta damka ba,
"Kinada wani miji ne bayan ni, har alahira nine mijinki bama a duniya ba..."
Ture hannunshi tayi tana kallonsa,
"Sakar min bakina,karka sake matse min baki tom.."
"Koma dai me zakice ki fada amma keda kabiru jagwal sai kallo"
Yafada yana kokarin barin cikin kitchen din, har yakai bakin kofa yasake waiwayawa,
"Kallon ma ko ahanya kuka hadu ya kalleki Allah ya isa tsakanina dashi.."
Karasa ficewa yayi daga cikin kitchen din ita kuma taci gaba da aikinta acikin zuciyarta tana cewa,
"Kaji dashi dai sarkin kishi kawai.."
K'arfe 9 daidai tagama kammala hada breakfast din dan haka ta kinkimo ta nufi kan dining,
Zaune ta sameshi akan dining din yana hada mata sabuwar wayar da yasiyo mata, daga ganin wayar mai tsada ce domin tahango tambarin kamfanin HTC ajiki,
Kalar wayar golden ne yar shafal shafal kalar ta mata amma kuma katuwa ce ba canba,
Zama tayi akujerar dake kusa dashi tana kallonshi sakamakon kamshinshi da yacika kofofin hancinta, ba karamin kyau yayi ba awannan lokaci domin pink din riga yasa ta polo da bakin trouser, sumar nan tashi tasha gyara sai kyalli take, ya daura agogon silver ahannunshi na hagu,
"Baby ga wayar zan jona miki ita a charge.."
Bai jira amsarta ba yatashi zuwa socket yajona ajiki ya dawo wurinta lokacin har tasoma kurbar tea din data hada,
Daukarta yayi cancak daga kujerar datake ya maye wurin tareda dorata asaman cinyarshi,
"Wannan fushin dai da kiketa yi dani sai kin dainashi ayau..."
"Fushi ai kai kasiya.."
"Nawa na siya? Fada min inji"
Yace da ita yana zame dan kwalin dake daure akanta,
"Ya zaka cire min dankwali na? Kasan kuwa dadewar da nayi agaban mirror kafin indaura shi?"
"Zanyi miki wanda yafi wannan.."
"Tayaya?"
"Zaki gani ai.."
Gashinta yafara sinsina,
"Serious baby yakamata ki daina fushin nan dani haka karkisa inshiga wani hali.."
Tureshi tasoma yi saboda jin yana niyyar hada bakinshi da nata,
"Ni kabari kar kasa tea dina yahuce.."
Baiyi magana ba wayarshi tafara ringing, karkacewa yayi ya cirota daga aljihunshi yana kallon screen din wayar, ganin sunan zee yasashi kallonta yana murmushi, bai dauki wayar ba ya ajiyeta akan table din dake gabansu,
"Ni ina nawa tea din? Ko tare kika hada mana.."
"A'a.." Tabashi amsa,
Wayar tashice tasake daukar kara,
"Kinga ke kin sameni sai faman wahalar dani kike amma ga wata can agefe tana son samuna domin tabani kulawa.."
Baki ta zumbura cikeda takaici ta kalli wayar tashi nan taga sunan zee baro baro,
"Ko zaki daga kuyi magana?"
Ko kallonshi batayi ba ta juyar da kanta, shi bai son yayi laifi awurin gimbiyar tasa shiyasa ma yaki daga wayar daga karshema kashewa yayi gaba daya ya ajiyeta,
Tea dinta ya dauka ya kurba, ya kula tunda yayi mata maganar zee ta sake tunzura, dan haka har suka kammala bata sake cedashi ko uffan ba,
Tana jikinshi ya dauketa zuwa falo,
Kallonshi tayi saboda jin yafara yimata ajiyar zuciya akunne,
"Lafiya..?"
"Itace ta kawo haka.." Yabata amsa, hannunshi ta buge daga kan kirjinta,
"Meye haka? Baby dan Allah kibari"
"Ni bana so.."
"Ni ai inaso.."
Harararshi tayi shima ya rama amma tashi awasance yayi,
"Bari idan andan jima zamuje kiga motar taki kinji, uhmmm baby.."
"Banjiba.."
Gwalo yayi mata,
"Duk abinki dai nine nan..."
"Bakai bane..",
"Wallahi nine kuma bari ma kiji, idan kika kara ambatar sunan wannan..."
Murtuke fuska tayi ta katseshi,
"Amma dai kasan ko babu maganar su fadeela yaya kabeer dan uwana ne najini dan haka babu mai rabani dashi..."
"Allah ya isa idan kika kara yimin maganarshi..."
Hawaye yaga tafara yi,
"Amma ai kaine kafara ko, shine sai yanzu nikuma zaka hanani.."
Rungumeta yayi yafara lashe hawayen nata dake silalowa bisa kuncinta,
"Yi hakuri baby, nine ko? Yi shiru, mubar maganar kinji..."
Rarrashinta yaci gaba dayi bai barta tasake yin magana ba har tsawon wani lokaci,
Zamewa tayi daga jikinshi ta tashi,
"Bari naje nagyara maka bedroom dinka nagyara ko ina shi kadai ne kawai ban gyara ba.."
Gyara kwanciyarshi yayi yazuba mata fararen idanuwanshi mayalwata masu dauke da bakin yalwataccen gashi,
"To sai kin dawo..."
Mikewa tayi ta nufi dakinshi mintuna kadan sai gata tafito tana kallonshi,
"Haba didi,Kaine kuma mai aikin gidan yanzu?"
Murmushi yayi ya kalleta,
"Meya faru?"
"To naje zan gyara naga already har ka gyara..."
"To kuma menene baby? Rage miki aikin nayi fa.."
Juya mishi baya tayi,
"Nidai kadaina yimin irin wannan, duk wani aiki idan kaga banyi ba kafin nafarga kayishi, ai sai inzama marar tausayi, bayan kafita ka nemomin abinda zanci kuma sannan harda su aikin gida"
Tashi yayi yakarasa inda take ya rungumeta ta baya,
"Baby wallahi ni ban dauki hakan amatsayin wani abu ba, ahar kullum ina fada miki na daukeki ne a matsayin abokiyar rayuwa bawai baiwa ba, wallahi idanma akwai abinda yafi haka zan iya yimiki saboda bazan iya kwatanta miki matsayinki agareni ba, wani irin sonki ne Allah ya jarrabeni dashi..."
Jin alamun saukar kwallarshi akan kafadarta yasata juyawa tana kallonshi kumatunshi ta fara shafawa,
"Didi na, nima ina sonka, ba son maso wani kakeyi ba, kadauka aranka cewar ban taba son wani da namijiba sai kai, bana ganin ko wanne da namiji sai kai kadai..."
Murmushinshi mai tsada taga yayi mata kafin yadagata sama yafara juyawa da ita, gaba dayansu shida ita dariya sukeyi, yau yana cikeda farin cikin da bai taba yin irinsa ba,
Sauketa yayi yana rikeda kugunta,
"To saura ni, nima adagani.."
Yafada cikin shagwaba, hannayenta tasa wai zata dagashin amma maimakon haka sai ji tayi sun fadi akan center carpet din dake shimfide afalon,
Dariya suka fara yi babu kakkautawa,
"Wai dama babyn tawa bata da karfi?"
"A'a inada shi"
"Gashi kuwa kin kasa daga mijinki.."
Hannunta yaja suka mike tsaye,
"Dauko gyalenki muje yawo amotarki.."
Fuskarta dauke da farin ciki ta shiga bedroom dinta ta ciro mayafi da takalmi kalar kayanta tafito bayan ta fesa turare,
Afalo ta sameshi yana kunna wayarshi wadda yakashe dazu,
"Baby anya kuwa fitar nan zata yiyu?" Yafada idonshi akan screen din wayarshi,
"Meya faru?"
"Wani kamshi naji Wanda yatayar min da..."
"Dan Allah kayi hakuri muje mudawo.." Tafada tana kamo hannunshi,
"Gaskiya dakyar, kar muje mutafi nutsuwata ta tafi atsakiyar titi kinga ke kuma ba driving kika iyaba"
Kallonshi tayi bayan tadago fuskarshi,
"Wai dagaske kake ne?"
"Au da dawasa kika dauka? Bari dai kawai nayi ganganci nadaukeki mutafi idan kuma ansamu matsala shikenan asan yanda za ayi"
"Bama wata matsala da za asamu.."
Jan hannunshi tayi suka fita hannayensu sarke cikin juna, saida suka fara zuwa suka gaida hajiya sannan suka wuce wurin motar tata, kusan suman tsaye tayi saboda ganin haduwar motar, ko da wasa bata taba kawowa zata mallaki irin wannan motar ba,
Motar yar karama ce ta mata kalarta blue sai sheki take, budewa yayi ya shiga itama ta shiga ta zauna kasancewar glasses din masu duhu ne yasashi janyota zuwa saman cinyarshi bayan ya kwantar da kujerar tashi,
"Infara koya miki daga yanzu?"
"Didi tsoro nakeji..."
"Babu wahala fa baby, bari kiga, taka muje ahankali.."
Tafiya suka fara yana rike da sitiyarin itama ta rike suna juyashi ahankali, ahaka suka fice daga farfajiyar gidan, saida yaga sun kusa zuwa babban titi sannan yamayar da ita kujerarta yaci gaba da driving din shi kadai,
Wuraren shakatawa kala kala suka ziyarta daga karshe yakaita gidan anty siyama, ba karamin murna anty siyama tayiba da ganinsu nan tahau tsokanar amadi,
"Anty amadi kadai zama jela duk inda nadiya take kana bibiyarta abaya.."
"Anty siyama ni ai nafi jela ma, ki kirani da kowanne suna zan amsa"
Dariya sukayi dukkaninsu, har yamma suna gidan sai daf da magrib suka tafi, ba gida yanufa dasu ba, lovers garden yakaisu,bude ido kawai nadiya tayi tana ganin yanda masoya ke guje guje wasu kuma yan tsalle tsalle,
Kallonshi tayi bata san lokacin datayi kissing dinshi a baki ba,
"Baby wannan babban tukwici haka ai sai kisa na sume.."
Dariya tayi, "wannan somun tabi ne sauran bayani sai munje gida.."
"Kice duk ranar da nashiga hannunki sunana sorry"
Dariya tayi tajashi suka fita zuwa filin wurin, babu laifi suma sun dan wataya sosai, karfe 7 suka koma gida.
Tunda suka koma kuma yadameta da mitar fashin sallar da takeyi, juyawa tayi ta kalleshi,
"Dadina dakai rashin hakuri didi, kwana uku nefa amma duk kabi ka damu kanka.."
Shiru taji yayi mata baiyi magana ba, janshi tayi tasashi ajikinta tafara shafa sumar kanshi,dagewa tayi wurin bashi kulawa tunda tarigada tasan halin kayanta,da yan dabaru tasamu har yasamu nutsuwa yayi bacci dama haka yakamata mata su kasance bawai kawai dan kina period ba ki kauracewa miji wata ma sai ki samu mijin yana gabas ita tana yamma wannan babban kuskure ne.
A daddafe dai yasamu yahakura har kwana ukun tayi, kamar wani marar lafiya yazame mata har saida yasamu abinda yake kulafuci sannan yaware yakoma kamar da,
Lokaci zuwa lokaci yana daukarta sufita su zagaya gari amma har yanzu bata gama koyon motarba kasancewar kullum suna hanyar zuwa wudil gashi anfitar musu da time table na exam,
Yanzu bai fiya zama a part dinsu ba yafi zama a part din hajiya saboda yabata damar yin karatu sai dai abunda yake damunsa yanda yanzu duk tazama wata lazy, shi kanshi yanzu bata iya hidimta masa kamar da abu kadan sai tace masa tagaji, ana cikin haka kuma sai tafara yawan amai daga taci abinci sai amai babu abinda take jin dadinshi sai lemon zaki shikam koda yaushe cikin shansa take,
Amadi ko kadan bai san abinda yake damunta ba amma dai yaga canji atareda ita musamman ma ajikinta wanda yake sashi kasa hakuri ita kuma yanzu idan da abinda ta tsana to abinda yake shaukin ne, kusan koda wanne lokaci sai yasha aikin rarrashi kafin yasamu karbuwa,
Rigarshi yake sakawa yana kallonta tana kwance akan gadonshi,
"Dan Allah didi kayi sauri karka dade.."
"To antyn lemon zaki yanzun nan zan dawo.."
Fita yayi ganin motar anty siyama yasashi shiga part din hajiya, gaisawa sukayi kawai yajuya zai fita,
"Anty amadi ina zuwa ne?"
"Anty ina zuwa lemon zaki zanje in siyowa mutuniyar, yanzu bata iya cin komai da zarar taci sai amai narasa gane meke damunta..."
Dariya anty siyama tayi tace,
"Allah yabata lafiya"
"Amin anty"
Ya amsa mata tareda yin gaba hankalinshi akwance domin shi bai fahimci abinda anty siyama ke nufi ba....
*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITER ASSO.*
_Home of expert & perfect writers_
_Wannan shafin sadaukarwa ne agareku masoyana, nagode Allah yabar zumunci._
*72*
aishaummi.blogspot.com
*A*hanzarce yake tuki bayan yadawo daga siyo mata lemon zakin kamar yadda tace, sauri yake yakoma gidan da wuri domin yakai mata,
Packing yayi yashiga cikin part din nasu amma sam baiji motsinta ba, cikin bedroom dinta yashiga nan dinma bata nan, dayan bedroom din yaleka ananma bai ganta ba dan haka yayi gaggawar nufar dakinshi koda yaje can dinma wayam,
"To ina baby ta shiga?" Yatambayi kansa, tunani yayi ko tana bathroom dan haka ahanzarce yaje ya dudduba, gaba daya kaf bata nan hakan yasashi zuwa part din hajiya ko tana can amma abin mamaki hajiya sai cemasa tayi ai yau kwata kwata ma nadiya bata shiga part dinta ba,ganin anty siyama tatafi yasashi juyawa batare da ya zauna ba,
Part dinsu yasake komawa yana shiga idanuwansa sukayi arba da wata farar takarda akan dan madaidaicin Stoll din dake gefen kujerun falon,
Da saurinsa ya karasa yadauki tskardar ya warwareta yafara karantawa,
_Zuwa ga didi na abin alfahari na, nasan kanata nemana amma baka ganni ba to kayi hakuri kuma kayafe min duk da nasan kai dama mai hakurin ne sannan nasan kabawa rayuwata gudun mawa ta bangarori daban daban, ni nadiya ina mai bakin cikin sanar maka da cewar natafi inda bazaka sake ganina ba, na zabi inbarka saboda wasu dalilai..._
Kasa karasa karantawa yayi yazauna sharafff akan kujera idanuwanshi jajur, tunani yake aransa shin wanne laifi yayi mata da har zata yanke masa wannan mummunan hukuncin, baiyi zatoba kawai yaji kwalla na neman cika masa ido, goge kwallar yayi yasake duban wasikar tata,
_Kayi min afuwa didi na nasan hankalinka yatashi idan kadawo daga siyo min Orange din kasameni a corridor zanyi maka wani albishir, duk abinda nafada da farko ba gaskiya bane am joking..._
Cillar da takardar yayi ya nufi corridor da gudu gudu, kwance ya hangota kan doguwar kujera tana sanye cikin bakar doguwar riga ta materia taci kwalliya abinta sai kamshi ne mai dadi yake fita daga jikinta,
"Baby..." Yakira sunanta yana girgizata, bude idanuwanta tayi tana murmushi,
"Meyasa zaki yimin irin wannan wasan, kin san kuwa yanda hankalina yatashi?"
"Didi kenan nima ai haka kayi min, ramawa nayi.."
Zama yayi agefenta yakamo hannunta yarike,
"Shikenan anyi 1-1 yawuce, ki fada min albishir din da kikace zaki yimin.."
Dan yatsina fuska tayi ta muskuta,
"Ina lemon zakin yake..?"
"Yana falo.."
"To dauko min sai infada maka amma fa ka yanko min shi"
Tashi yayi mintuna kadan sai gashi yadawo rikeda filet wanda ya yanko mata lemon akai,
Tashi tayi ta dauki lemon takai bakinta tana kallon amadi wanda shima yabada attention yana kallonta,
"Kasan me? Kakusa zama dady..."
Kallonta yayi cikin rashin fahimta,
"Baby ban ganeba"
"Ina nufin nakusa inhaifa maka baby.."
Rungumeta taji yayi sosai cikin farin ciki kwalla fal acikin sexy eyes dinshi,
"Baby dagaske kike, kin gama yimin komai baby.."
Sakinta yayi yakai hannunshi yadora akan mararta yana shafawa,
"Allah yaraya min kai baby na, Allah ya fito dakai lfy.."
"Abin nema yasamu ko? Ansamu nayi.."
"Sosai kuwa domin nima nakusa nahaifi dan kaina adaina yimin gori.."
Murmushi tayi tana tsotsar lemon dake hannunta,
"Allah sarki.."
"Yes fadi ki kara, may be ma gaskiya sai dai kihakura da exam dinnan har sai kin haihu"
Kallonsa tayi afirgice,
"So kake insake maimaici? Wallahi bazai yiyu ba, kabarni kawai inyi abina ingama ni zan iya"
"Baby bana son yarona ya wahala ne"
Sakin baki tayi tana kallonshi tun daga ranar ya hanata aikin komai babu abinda takeyi abu kadan sai yace shi baya son babynshi ya wahala, ko girki yanzu tadaina yi hajiya ce ke basu sai dai kawai ita tadafa dan abinda take kwadayi,rigarta kuwa kullum cikin dageta yake yana kallon cikinta kamar wani mudubi,
Daurewa tayi sosai tayi karatun jarabawar da zatayi amma duk dare amadi cikin yimata mita yake idan yaga taki yin bacci tana karatu, ahakan dai ta samu ta kammala exam din anan kuma hutu yasamu domin babu abinda takeyi ahalin yanzu, amadi kuwa yadauki son duniya yadorashi akan wannan cikin wanda sai yanzu ne ma zai shiga wata na hudu,
Koda yaushe cikin yiwa cikin hira yake, yayi ta magana shi kadai kamar wani zautacce idan tayi magana kuma yace shida babynshi yake hira, idan zai fita aiki da safe sai yayiwa cikin sallama haka idan yadawo ma sai yace masa yadawo,
Nadiya dai kallonshi kawai take tana jin wani sabon sonshi yana ratsata saboda ko acikinta nafari bata samu irin wannan kulawar awurin kabeer ba amma shi amadi saima ya tambayeta abinda zataci, me zata sha, me take sha'awa, kullum idan zai fita tambayarshi kenan,
"Baby me zan taho miki dashi? Yau mekike sha'awar ci..?"
Ko tace babu abinda take sha'awa baya yarda sai yataho mata da kayan makulashe, ko shakka babu tasan tayi sa'ar miji mai kaunarta wanda ya share mata hawayen da suka jima suna gudana akan kumatunta, duk sanda zai tafi wudil kuwa dakyar take rarrashinsa yatafi domin baya son yayi nesa da ita,
Cikin weekend ya dauketa suka tafi rano saboda tunda tatare bataje ba, tsaraba sosai amadi yayiwa su mama su amira da twins,
Kowa agidan saida yayi murnar ganin nadiya saboda tayi bul bul takara kyau fatarta inbanda sulbi babu abinda takeyi,
Wuni cur sukayi saida yamma suka tafi wanda harda su fadeel saboda anyi hutun makaranta, nadiya jin hankalinta tayi ya kwanta saboda yanzu bata da matsalar komai,
Tana kwance acikin bedroom dinta tajiyo hayaniyar su amadi a kitchen shida su fadeel, tashi tayi tafita wurinsu daga ita sai rigar bacci iya gwiwa ash colour cikinta yadan bayyana kadan,
Kallonta amadi yayi ya hadiyi yawu,
"Baby gaskiya yau fa zanyi tawaye, gaskiya yau ina bidar wani abu.."
"Kaga ni zubo min kwan inje inci yunwa nake ji, yanda kake da ci haka babynka yake kamar gara.."
Murmushi yayi yadauki filet yana saka mata kwan da yake soyawa, rungumeta taji su fadeel sunyi suna cewa,
"Good morning momy"
"Morning fadeel, morning fadeela na.."
Karba tayi tafita falo tazauna tahada tea tafara karyawa, ita kanta mamakin yanda akayi amadi ya iya girki take saboda idan yayi maka abinci sai ka rantse itace tayi bashi ba,
Har tagama basu fitoba, tashi tayi takoma bedroom dinta ta dauki towel tashiga wanka, dama kamar jira amadi yake wuf taji yafado cikin toilet din,
"Baby kawo intayaki wankan..."
"A'a barshi basai ka tayani ba"
"Uhm uhm nidai sai natayaki.."
Babu yanda ta iya dole tabarshi yafara tayata din wanda daga karshe ya bige da abinda yafi muradi wanda dama tasan abinda yakeso kenan shine ya bullo ta haka,shiryata yayi shima ya shirya cikin kananan kaya,
Tana gani suka fita suka barta agidan shida twins yace banda ita ayawon saboda baison babynshi ya takura, jin zaman kadaici yadameta yasata shiga part din hajiya, acan suka dawo suka isketa nan ya goyeta ganin hajiya bata cikin falon ya tarkatosu suka koma part dinsu yakawo mata tsarabar kwakwa da dabino, zuba masa ido tayi tana kallonsa suna boxing shida fadeel,
"Meye ne kiketa kallona..?"
"Ina son haifar baby mai kamada kaine shiyasa"
Murmushi yayi mata,
"Ko baki kalleni ba dama na tabbatar dan da zaki haifo min mai kamada nine sak dan jinina yafi naki karfi"
Dabinon ta dauka tana ci tana kallonshi,
"Inji waye...?"
"Inji ni saboda jinin last born yafi na first born karfi"
Dariya tayi taja pillow din kujera ta kwanta taci gaba da kallon boxing din da suke yi.
"To yanzu dai fada min dalilinka na siyo min wannan kwakwar da dabino"
"Kinfi dan dako sanin tasha,Saboda tunda nabaki babyn nan kika zama wata lazy..."
Pillow tadauka ta jefeshi nan yakare dukan da hannunshi yana dariya.
***
Al'amarin kabeer yanzu yadan samu wani aiki na wucin gadi awani companyn sarrafa auduga, amma har yanzu yana jin radadin abinda asabe mc tayi masa musamman ma rabashin datayi da abar sonshi nadiya,
Haka dai ya daure ya rungumi kaddara domin babu yanda ya iya yasan nadiya tayi masa nisan da bazai taba cimmata ba,agaba abbanshi da mama suka sashi kan dole sai yanemo aure saboda zamanshi ahaka bazai yiyuba tunda Allah yasa yasamu abinyi,
Acikin unguwarsu yasamu wata yarinya murja kawar Aisha kanwarshi suka daidaita har aka yanke ranar aure, shi dai yasan samun madadin nadiya arayuwa abune mai wahalar gaske shiyasa duk lokacin da yatuna da asabe sai yaja mata Allah ya isa.
***
Awurin nadiya su fadeela suka gama hutunsu sannan amadi yamayar dasu rano, sati daya da tafiyarsu fadeel yayi mata albishir da cewa alkawarin da yayi mata da jimawa wanda yace sai ta kammala karatu zai bata shine nanda sati biyu zasu tafi kasar Paris domin bude ido, shiru nadiya tayi dan tsananin murna tama rasa me zatayi sai kawai tafashe da kuka ta rungumeshi tana yimasa addu'ar samun babban rabo acikin rayuwarsa ta duniya da lahira,
"Nidai abu daya zaki bani tukwici" yarada mata a kunnenta,
Acikin yan kwanakin suka shirya yakaita rano da sumaila tayi sallama suka bar kasar, gaba daya amadi yasata tamanta da kowa bata iya tuna kowa sai shi sai yanzu ta gasgata maganarshi da yayi mata tun kafin aurensu lokacin tana tsaka da bashi tension cewar zai sota zai kula da ita kuma itama zata soshi tabbas kuwa hakance take faruwa domin yanzu babu wani wanda take kauna sama dashi in aka dauke mahaifanta,
Sun rabarbashi soyayya kamar babu gobe sun ziyarci wurare daban daban dan shakatawa, kasancewar cikinta yakai kimanin wata takwas yasa suka jibgo kayan babies acan,
Satinsu bakwai suka dawo nigeria, koda suka dawo dinma wata kulawar yashiga bata ta musamman har Allah ya sauketa lafiya lokacin yana wudil bai dawoba sai a standard hospital ya tarad dasu yana zuwa yasamu ta haifi yaranta maza guda biyu Ku kanku masu karatu nasan basai nafada muku irin kyawun yaranba domin kyawun amadi ne yahadu da nadiya yabada wani kyawu nadaban,
Amadi rasa inda zai cusa kanshi yayi dan tsananin murna nan yashiga kaffa kaffa da yaranshi da matarshi har aka sallamesu suka koma gida,koda wanne lokaci zaka sameshi rikeda yaran yana kissing dinsu,
Amira da husna sune suka zo domin zama awurin mai jego saiko umman sumaila wanda kunsan ita kuma dalilin zuwanta shine sabinta tsoho yakoma sabo, nan tafara bawa yartata kulawa ta musamman domin haskakata azuciyar amadi,
Abdullah da abdurrahman shine sunan da aka radawa yaran ranar suna,raguna biyu da babban Sa amadi ya yanka musu, sunan yatara dunbin mutane masu yawa domin hatta anty Dija da anty hamida yayun amadi sunzo haka Yaya yaseen shima yazo da iyalansa wannan dalilin ne yasa masaukin hajiya yacika dam dan haka tace wasu suje part din nadiya su sauka acan domin itama yan uwanta sun zazzo tunzuro baki amadi yayi kamar wani karamin yaro domin yasan takurashi za ayi shida nadiyanshi sam bazai sake ba da ita,
Ansha shagalin suna sosai sannan taro yawatse kowa yakama gabanshi sai iya umman sumaila kadai da Amira, cigaba da gyarata umman sumaila tayi har suka cika kwana 40 ranar ta hada nata yanata itada amira suka tafi bayan amadi ya hada musu sha tara ta arziki. Amadi zaucewa ne kawai bayiba saboda irin yanda nadiyan shi ta sauya,kwana yayi yana yi mata sunbatu ita kuma ta wuni tana zolayarshi da tsokanarshi, bashida bakin ramawa sai dai murmushi, ko ina tayi yana biyeda ita, sati daya yadauka agida bai fita ko inaba sai renon twins dinsu da yake tayata sai kuma fitinar da yasakota agaba da ita, itama din sam baya isarta saboda tana mutukar sonshi ahalin yanzu, wata soyaya mai wuyar fadi suke yiwa junansu.
Soyayya mai tsayawa arai amadi yashiga bata itada yaransu lokaci kankani yaran suka zama kamar basu ba saboda girma, shiryawa sukayi sukaje rano suka wuni, har gidansu kabeer nadiya taje tana rikeda abdallah shi kuma amadi yana rike da abdulrahman akan kafadarshi yasha dark blue din danyen boyel da hula ita kuma nadiya tana sanye da wani swiss les pink colour kai idan kagansu sai kaji sun burgeka, agidan kabeer ya samesu yaje gaida mamanshi ganin nadiya da iyalanta yasake tayar masa da hankali amma yasan babu yanda zaiyi tunda ta rigada ta subuce masa har abada, shi kuwa amadi ganin kabeer yasashi murtuke fuska yafara ciccin magani yana yiwa abdurrahman wasa, dakyar ya yarda suka gaisa da kabeer,cewa nadiya yayi tatashi su tafi domin yaga kamar kallonta kabeer yake yi. Har acikin mota sai faman fushi yake ta yimata duk tagane dalilinshi nayin fushin dan haka tasoma lallashinshi,
"Ayya didina kayi hakuri kadaina fushi wallahi ko bayan ranka bazan iya rayuwa da kowanne namiji ba saboda kai kadai nake so.."
Sai lokacin yaji yasamu nutsuwa, "idan kina son nahakura nidai sai kin bani abinda nafi so"
"Zan baka.." Murmushi yayi yashiga saka mata albarka.
Sosai amadi ya mayar da nadiya yar gata kuma sarauniya acikin dukkan mata, mota ya koya mata saboda baya son idan zataje wani wuri ace sai driver ne zai kaita, cikin kankanin lokaci ta kware tana iya kai kanta duk inda zataje,
Tunanin maganar da amadi yafada mata takeyi tana murmushi cewar wai next year iyanzu tasake haifa masa wasu yan biyun, dafata taji anyi tana juyawa taganshi tsaye, girarshi ya daga mata,
"Ya akayi.."
"Maganarka nake nazari da kace wai zan sake haihuwa wata shekarar.."
"Insha Allah"
"A'a gaskiya, zee tazo sai ta dora daga inda natsaya.."
Kai yagirgiza ya rungume ta,
"Ai Allah ma cewa yayi fa inkiftum fa wahidatan au mamalakat aimanikum.."
"To me kake nufi kenan? Ashe kai ba adali bane.."
"Sosai kuwa, duk matar da tashigo bayanki to bazan iya yin adalci ba domin zanyita fifitaki kinga maganin kar ayi kar asoma" yafada yana bata wani cool kiss agefen wuyanta.
Kamar kuwa yafada da bakin mala'iku shekara na zagayowa ta haifi yan biyunta mace da namiji, ranar suna aka radawa yara abdulrahim da amatullah domin dama amadi yace mata bismillahir rahamanur rahim yake son hadawa shiyasa yasawa yaran abdullah, abdurrahman da abdulrahim,
Amadi hade kan iyalanshi yayi yana basu kyakkyawar kulawa ta musamman da tafiya tai tafiya ma sai ya debo su fadeel yahada su da nashi sam baya nuna banbanci komai tare yake yi musu, shi kansa kabeer yadauki hakuri yabar musu yaran sai dai idan anyi Hutu duk term ana kaisu gidanshi hutu saboda su saba da yan uwansu,domin matarshi har ta haifi yara biyu yanzu macen sunan nadiya yasa namijin kuma Mohd.
Sam amadi baya gajiya da nadiyanshi haka kuma bai taba nuna mata cewar wai ba a budurwa ya aureta ba, koda yaushe cikin nacin son kasancewa da ita yake wannan dalilin be yasa umman sumaila sake zage dantse wurin gyara yartata domin mata saida gyara,amadi kam kullum cikin sonshi yanmata suke amma ko kusa basa gabanshi nadiyanshi ita kadai ta isheshi rayuwa.
Familyn amadi abin burgewa ne ga kowa koda yaushe cikin farin ciki suke suna ziyarta wurin bude ido, cikin yawace yawacensu sukaga asabe mc tana bara abakin titi da sanda wacce take dogarawa domin yanzu kafa daya gareta saboda ayawon barikinta taje ta dauko cuta mai karya garkuwar jiki yanzu bata da komai kawaye duk sun gujeta, mazan da take hulda dasu sun daina yayinta, dama haka duniya take yau gareka gobe ga waninka.
ALHAMDULILLAH
Anan nakawo karshen labarin mijina sirrina, labarin yafaru agaske ba kirkirarren labari bane dafatan Allah ya amfanar damu darrusan dake cikinsa ya yafe mana kurakuran da nayi nidaku baki daya.
Littafin mijina sirrina sadaukarwa ne gareki Nasiba I uba (the writer of kannen mijina)
Tukwicine agareki Feedohm (the writer of bakonmu hasken mu)
Godiya ta musamman ga yan kungiyar haske writers Allah yasake hade kawunanmu amin.
Masu karatu sai mun hadu acikin labari nagaba idan Allah ya amince, duk wata masoyiyar ummi shatu, ko wacce taji tana kaunarta,ko son ganinta ko kuma take son jin muryarta, to ummi shatu tana mutukar kaunarta itama, gaisuwa mai yawa agar
eku masoyana hakika da bazarku nake rawa, ina sonku har cikin zuciyata aduk inda Luke fatana Allah yabarmu tare.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
0 Comments