Kibiya ratsa maza hausa novels cmplt

 KIBIYA RATSA MAZA!!!

Littafi Na Biyu (2)

Part A

A CAN BAKIN DAJIN TSAUNIN

LAUHUL-FARRAS

kuwa runduna ce ta sarakai,matsafa

,jarumai da

manyan bokayen duniya suka kakkafa

sansani

tsubi tsubi a wurare dabn

daban.Kowace runduna

ta fito ne domin farautar Jaruma Safirat

ta kasheta

sannan ta rabata da wannan baka data

dauko a

kan tsaunin Lauhul Farras.Wannan

shine kura da

shan bugu gardi da kwashe kudi.Daga

cikin

rundunar sarakan da suka zo har da

sarki Safwan

tare da dakarunsa na yaki mutum dubu

goma

kuma suma sun kafa sansaninsu wanda

shine mafi

kusanci da tsibirin Lauhul

Farras.Lokacin da rana

ta fadi ne sarki Safwan tare da

shugaban

dakarunsa wani barde da ake kira

Barha na tsaye a

bakin tantin sai sarki Safwan ya dubi

Barha yace

amma nayi mamakin abinda yasa har

yanzu Safirat

bata fito ba daga cikin wannan daji na

tsibirin

Lauhul Farras.Koda jin haka sai Barha

yayi gyaran

murya yace haba ya shugabana ai bai

kamata kayi

mamaki ba tunda ka sani cewa babu

wani

mahaluki daya taba hawa kan tsaunin

Lauhul

Farras ya sauko kasa a raye.Babu

mamaki itama ta

mutu ne a lokacin hakan.Sarki Safwan

ya girgiza

kai yace Safirat bata mutu ba kuma nayi

bincike a

cikin madubi tsafina naga cewa zata

rayu bisa duk

irin gumurzun da zatayi da dakarun

dake kan

tsibirin har ta sami nasarar dauko

wannan

sihirtaccen baka na mahaifinta.Sa'adda

barde

Barha yaji wannan batu sai yayi ajiyar

numfashi

sannan ya dubi sarki Safwan cikin

alamun tsananin

damuwa da karayar zuciya yace ya

shugabana

yanzu dai da idanunka kaga runduna

sama da

guda arba'in a bayanmu ta manyan

sarakan

duniya,matsafa da jarumai masu ji da

kansu.Yanzu

koda ka sami nasarar kashe Safirat ka

dauko

wannan baka dake hannunta ta yaya

zamu iya

ficewa daga cikin dajin nan da bakan ta

gaba

wadannan miyagun rundunoni alhalin

suma abinda

suka zo farauta kenan?Dajin wannan

batu sai sarki

Safwan ya bushe da dariya.Al'amarin

daya kara

baiwa barde Barha mamaki kenan.Daga

can sai

sarki Safwan ya hade fuskarsa yace ai

raba Safira

da wannan baka yafi tsare bakan

wahala.Duk

wadannan rundunoni da kake gani na

banza ne

muddin daya daga cikinsu bata rigamu

karbar

bakan ba.Bisa wannan dalili ne yasa

kaga ni nayi

kundunbala nazo daf da bakin dajin

tsaunin Lauhul

Farras saboda ya zama nawa da zarar

Safira ta fito

ya kasance nine mutum na farko da

zatayi arba

dashi.Ninasan cewa indai zamuyi GABA

DA GABA

da ita to saina rabata da bakan tunda

bata finin

KARFIN DAMTSE ba dana tsafi kuma

bata fini iya

yakio ba.Duk abinda take takama dashi

nima ina

dashi ko mafiyinsa.Kuma muna haduwa

zan shaida

mata cewa ubanta ne ya kashe

mahaifina don haka

ina son na dauki fansa a kanta,kaga

bata da ikon

cewa naci amanar soyayyarta.Kao bari

na gaya

maka gaskiya,koda Mahaifinta bai

kashe nawa ba

zan iya zuba idanu ba ina kallonta ta

fini matsayi

ba da daukaka tunda nine sarkinta.Dole

ne ka

kawar da batun soyayya na ceci

mulkina da kasata

tare da duk al'ummata.Babu sani ba

sabo a

tsakanina da Safira saidai KAIFIN

TAKOBI ya

rabamu.A yanzu haka ina zargin cewa

Safirat zata

iya fakar numfashinmu ta fito daga cikin

dajin

Lauhul Farras a cikin wannan dare ta

sulale ta

gudu ba tare da wani ya gantaba.Koda

jin wannan

batu sai Barde Barha ya gyada kai cikin

alamun

shakku yace haba ya shugabana ta

yaya Safirat

zata iya wucewa ta gabanmu ba tare da

ka ganta

ba tunda bata da wani sihiri na bata

wanda baka

da shi.Nidai kawai shawarar da zan

baka itace

kada ka kuskura kace zakayi bacci a

cikin daren

nan domin ta bakin kane a ko yaushe

zata iya

fakar numfashi ta fito din.Koda jin haka

sai sarki

Safwan yayi murmushi yace tabbas

maganarka

dutse ce.Dole ne hakura da bacci gaba

daya a

daren yau.Ai kuwa sarki Safwan bai

yarda ya kara

shiga cikin tantinsa ba.Kujera aka kawo

masa ya

hau ya zauna a waje yana mai fuskantar

cikin dajin

tsaunin Lauhul Farrs kuma takobinsa

nakan

cinyarsa ya dafeta da hannunsa guda

sannan kuma

yasa wata kuyangarsa ta dafa masa

shayi aka zuba

masa sinadaron hana bacci a ciki

yasha.Har gefen

asuba idanun sarki Safwan a bushe

suke ko

alamar bacci babu a tare dashi.

*Al'amarin Jarum Safirat kuwa tunda ta

kwanata a

cikin tantinta ta kama bacci ko

kyakkyawan motsi

bata sakeyi ba har asuba tayi.Kawai sai

ji tayi ana

tashinta kamar a mafarki.Safirat ta

mike tsaye

Zumbur a dan firgice.Tana bude

idanunta sai taga

ashe Bandaru ne tsugune a gabanta

kansa

sunkuye don biyayya.Ba tare daya dago

kansa ba

ya dubeta yace ya shugabata yanzu ne

daidai

lokacin daya kamata ki shirya ki fice

daga cikin

dajin nan ki durfafi hanyar da zata kaiki

can Dajin

Sarkif domin ki isa kogon mutuwa don

dauko

kuttun kwarinki.Kamar yadda na gaya

miki a baya

cewa masifar dake cikin dajin Sarkif ta

ninka wacce

ke cikin wannan daji namu sau goma

don haka

saiki jajurce kuma kiyi matukar juriya da

hakuri.Duk tarin rundunonin makiyan da

suka

biyoki izuwa nan ba zasu iya binki ba

izuwa dajin

Sarkif amma ina zargin cewa mutum

daya zai iya

binki.Koda Bandaru yazo nan a

zancensa sai

Jaruma Safirat ta tari numfashinsa tace

nasan

kowane ne ba wani bane face sarki

Safwan babban

masoyina a da yanzu kuma babban

makiyina.Koda

jin haka sai Bandaru yayi murmushin

murna yace

ina farin ciki da kika fahimci hakan duk

da cewa

har iyanzu nasan zuciyarki tana miki

wasu wasi

akan hakan.Amma dai na san cewa

lokaci zai

tabbatar miki da gaskiyar alamari.A

yanzu haka

tuni dakaru arba'in da nayi miki

alkawari sun gama

shirin tafiya ke suke jira.Kamar yadda

na gaya miki

a baya,kada ki fita daga cikin dajin nan

goye da

bakanki tsirara face kin lullubeshi cikin

mayafi

saboda hasken sane zai fara

™Abubakar Haleefah Physicist™

tona miki asiri.Yanzu ga mayafin da

zaki lullube

bakan na kawo miki.Nan take Bandaru

ya daga

hannunsa sama saiga wani bakin

mayafi ua

bayyana tsulum a hannun nasa kawai

sai ya mika

mata ta karba yace wannan ne kadai

mayafin da

zai iya boye hasken wannan kwarin

naki.Maza ki

lullubeshi yanzu.Ba tare da wata

gardama ba kuwa

sai Safirata ta mike tsaye ta ciro Bakan

daga

bayanta wanda ta daureshi tamau

kuma ta kwanta

a kansa tayi bacci tun a daren

jiyaSafirat na ciro

bakan sai ta lullubeshi da wannan

mayafi.Nan take

kuwa taga hasken nasa ya bace

bat.Cikin sauri ta

mayar da bakan bayanta ta goyashi

kuma ta

daureshi tamau.Faruwar hakan keda

wuya sai

Bandaru ya sake daga hannunsa guda

sama saiga

wani takalmi fade na fatar damisa ya

baiyana

tsulum akan hannun nasa.Kawai sai ya

mika mata

yace ungo wannan ki sanya a

kafafunki.Indai har

da wannan takalmin a kafarki babu

yadda za'ayi

wani yaji sautin tafiyarki ko

gudunki.Abinda nakeso

dake shine daga nan ke da dakarun

dana baki

guda arba'in zaku fice da gudun tsiya

ku nufi

arewa nan ne hanyar da zata kaiku

izuwa dajin

Sarkif.Kiyi gudu iya karfinki da

iyawarki.Ta gaban

makiya zaku wuce amma babu mai iya

cimmaku

saidai a riskeku a can dajin Sarkif inda

kowa zai

shiga cikin tararrabin rayuwarsa.Ni

kaina ba zan

baku tabbacin cewa zaku tsira da

rayuwarku ba

acan.Da wannan furuci nake yi miki

bankwana

yake sarauniyar Duniya ta gobe.Kuma

inayi miki

fatan sa'a da nasara bisa wannan

gagarumin aiki

dake gabanki.Ina fatan zaki zamo mai

cika alkawari

a gareni bayan bukatarki ta

biya.Bandaru na gama

fadin hakan saiya juya domin ya fice

daga cikin

tantin amma sai Safirat ta kira sunansa

da sauri

tace nagode bisa duk irin wannan

taimako da ka

bani kuma lallai zan zamo mai cika

alkawari a

gareka.Koda jin haka sai Bandaru yayi

murmushi

ya fice.Fitarsa keda wuya sai itama

Safirat tayi yan

kintse kintsenta kuma ta sanya

wadannan takalma

da Bandaru ya bata sannan ta fice da

sauri daga

cikin tantin.Tana fitowa tayi arba da

wadannan

dodanni guda arba'in.Kowannensu ya

goya jakar

guzurinsa a gadon bayansa sai kace

sun kasance

mutane ba dodanni ba.Al'amarin daya

baiwa

Safirat dariya kenan yayi

murmushi,kawai sai ta

juya ta nufi arewacin dajin ta dagawa

dodannin

arba'in hannu tana mai yi musu inkiyar

su biyo

bayanta.Nan fa Safirat ta falfala da

azababben gudu

izuwa cikin dajin dodannin arba'in na

rufa mata

baya suma sunayin gudu na ban al'ajabi

don har

tashi sama sukeyi saboda karfin gudun

nasu.Amma duk da haka Safirat ta

basu yar tazara.

*** A*H*P ***

Sarki Safwan na zaune akan kujera ya

zuba idanu

izuwa cikin dajin Tsaunin Lauhul Farras

a lokacin

da alfijir ya keto sai ya fara

gyangyadi.Nai ankara

ba sai baccin ya kwashe shi gaba daya

har da

minshari.Ashe suma sauran rundunonin

da suka

fito farautar Safirat basuyi bacci ba da

daddare.Abin kamar hadin baki sai

suma suka

kama gyangyadi a wannan lokaci da

alfijir ya

keto.A sansanin sarki Safwan barde

Barha ne kadai

baya yin bacci a wannan lokaci saboda

a daren

jiya kwanciya yayi ya hantse

abinsa,amma gaba

dayan sauran dakaru da hadimansa da

kuyanginsa

duk bacci sukeyi.Koda Barde Barha

yaga kowa

bacci yakeyi hatta sarki safwan kuma

shi kadai ne

idonsa biyu sai hankalinsa ya

DUGUNZUMA

saboda tsoron kada jaruma Safirat ta

fito a daidai

wannan lokaci daga cikin dajin Lauhul

Farras

saboda yasan cewa shi kadai bazai iya

cimmata ba

ya tare ta.Sannan kuma sai yaji tsoron

kada ya

tashi sarki Safwan daga bacci ya zamo

ya aikata

lafin katse masa baccinsa.A karon

banza ya

fuskanci hukunci mai tsananin.Nan fa

barde Barha

ya kama kai kawo a gaban sarki Safwan

wanda ke

fama sharar bacci akan kujera yana

tunanin abinda

zai fishshe shi.Kwatsam sai barde

Barha yaga

giftawar wani abu shuu!Ta gabansu

tamkar giftawar

tauraruwa mai wutsiya.Kafin ya juyo

yaga ko mene

ne tuni Jaruma Safirat da dodanninta

guda arba'in

sun bazu tazara mai yawan

gaske.Barde Barha ya

wangame bakinsa ya kuma ya takarkare

ya kurma

wani uban ihu mai tsananin kara da

firgitarwa.Take

sarki Safwan da sauran dukkanin

jama'arsa suka

farka firgigit a dimauce.Sarki Safwan ya

zare

takobinsa koda ya kallo gabansa sai ya

hango jelar

daya daga cikin dodannin kan tsaunin

Lauhul

Farras ta kule izuwa cikin daji.Kawai sai

sarki

Safwan ya falfala da masifaffen gudu

izuwa

arewacin dajin domin ya gane cewa

Safirat ce tazo

ta giftasu yana bacci.Nan yake kuwa

Barde Barha

da sauran dakaru suka ruga suka hau

dawakansu

suka bi sawun sarki,su kuwa hadimai

da kuyanci a

firgice suka shiga hada kaya sannan

suma suka bi

sawu.Kamar yadda su Jaruma Safirat

suka gifta su

sarki Safwan suna bacci haka suka

gifta sauran

sansanin na sarakai,jarumi da

matsafa,sai bayan

sun wuce sannan ake farga dasu a bi

bayansu.Nanfa aka kasa uban tsere a

tsakaninsu

ba sassauci.Amma aka rasa wanda ma

zai kusanci

su jaruma Safirat.Sai gashi mutum

daya jal yazo

yana ta wuce jarumai,matsafa da

sarakai rike da

zabgegiyar takobi a hannunsa.Nan da

nan ya

baiwa kowace runduna tazara mai

yawan gaske har

ya bace musu bat da gani saboda

masifaffen

gudun da yakeyi amma duk da haka

shima da

kyar yake iya hango dodo na karshen

baya daga

cikin dakarun Jaruma Safirat masu

tsaronta.Haka

dai aka cigaba da tseran gudu tsakanin

su jaruma

Safirat da sarki Safwan tun daga fitowar

alfijir har

rana ta take a sannan ne kowa ya gaji

ainun.Tsananin yunwa da kishirwa suka

addabesu.Amma saboda naci anki a

daina

gudu.Safirat da dakarun nata har

tangadi sukeyi

kamar zasu fadi kasa.Shima sarki

Safwan

haka,wani lokacin ma har faduwa

yakeyi amma

kuma har a san

™Abubakar Haleefah Physicist™

nan takobinsa na hannunsa bata

subuce masa

ba.Ana cikin wannan hali ne Safirat taga

uku daga

cikin dodanninta sun sare sun fadi kasa

suna haki

kamar ransu zai fita,kawai sai ta

sharesu ta cigaba

da gudunta abinta suna kara yin dan

gaba sai

dodannu biyar suka sake sarewa suma

suka zube

kasa.Faruwar hakan keda wuya sai

hankalin

Jaruma Safirat ya dugunzuma domin ta

fahimci

cewar indai aka cigaba da gudun a

haka to za'a

kai munzalin da zata rasa gaba dayan

dodanni,alhalin kuma tasan cewa akwai

lokacin da

zasuyi mata matukar amfani.Bisa sa'a

kuwa sai

Safirat ta hango wata fadama(korama)

a gabansu

kadan.Cikin farin ciki ta karasa gaban

koramar ta

tsuguna ta jika kanta ta sha ruwa.Ai

kuwa sai

suma sauran dodannin suka rugo izuwa

cikin

fadamar suna murna suka kama shan

ruwan.Adaidai wannan lokaci ne Safira

taji takun

sawu da gudu an tsaya a bayansu.A

nutse Jaruma

Safirat ta mike tsaye ta juyo a hankali

saboda

dama tasan wanda ke biye dasu din.Ai

kuwa tana

waigowa tayi arba da sarki Safwan a

tsaye rike da

sharbebiyar takobinsa yana haki kamar

ransa zai

fita.Ga tsananin kishirwa na

damunsa,lebansa ya

bushe sai kallon wannan ruwa na cikin

fadamar

yake.Nan fa aka fara kallon kallo

tsakanin sarki

Safwan da jaruma Safirat.Kawai sai

dodannin suka

yunkura zasu kaiwa sarki Safwan

farmaki amma sai

jaruma Safirat ta daka musu tsawa tace

wannan

yaki ba naku bane shi kadai ya iso nan

don haka

mutum daya ne zai yakeshi kum NI CE!

Koda gama

fadin hakan sai jaruma Safirat ta cire

battar

ruwanta daga kwankwasonta ta

tsomata cikin

fadamar ta cikata da ruwa sannan ta

tsuke bakinta

ta cillawa sarki Safwan ya cafe.Dama

tazarar dake

tsakaninsu bata wuce taku ashirin

ba.Safira ta dubi

sarki Safwan a lokacin da hawaye ya

subuto mata

cikin tsananin takaici tace bazan yaki

masoyina a

lokacin da yake jigace ba,kasha ruwa

ka gusar da

kishinka.Koda jin haka sai sarki Safwan

ya bude

battar ruwan ya kafata a bakinsa ya

kama

kwankwada har saida ya koshi sannan

yayi jifa da

ita.Ya dubi Safirat fuskarsa a murtuke

tamkar yana

kallon kumurcin maciji mai shirin

saransa.Har ya

budi baki zaice wani abu sai ta tari

numfashinsa

muryarta tana rawa tace ashe zaka iya

sayar da

soyayyarmu saboda abin duniya?Ina

kaunarmu da

amanar dake tsakaninu?Shin laifin

mahaifina ne ya

shafeni har da kakeson ganin bayana?

Koda sarki

Safwan yaji wadannan tambayoyi sai

zuciyarsa ta

karaya kuma kunya ta kamashi sannan

hawaye ya

zubo masa shima ya budi baki cikin

rawar murya

yace,yake Safirat ki dauki

soyayyarmu,kaunarmu,­

shakuwarmu da kuma amanar dake

tsakaninmu

tamkar wani abu daya faru a mafarkin

daya shude

tuntuni a baya.Ki sani cewa a halin

yanzi bani da

wani abokin gaba wanda ya fiki domin

mahaifinki

ne ya kashe ubana kinga dole ne na

dauki fansa

akanki.Abu na biyu dole ne na rabaki da

wannan

KWARI DA BAKA naki domin ceto

Rayuwar kasata

da jama'ar da kuma mulkina.Idan harna

barki kika

mallaki wannan kwari da baka tofa sai

duniya gaba

daya ta koma hannun mata.Sai maza

su koma

hannun bayin mata.Kinga kuwa duk

ranar da

mulkin duniya ya koma hannun mata sai

komai ya

lalace.Zaman lafiya da kwanciyar

hankali sun rushe

kenan.Saboda haka yanzu bani da wani

zabi

wanda yafi na kashe ki na dauke

wannan baka

tunda gaba daya sarakai,jarumai da

matsafan

duniya hankalinsu na kan baka.Kafin

sarki Safwan

ya gama rufe bakinsa tuni Jaruma

Safirat ta daka

masa tsawa tace kaje ka binciki

mahaifiyarka kace

kana son ta gaya maka ko wanene ya

kashe

ubana.To ka sani cewa ubanka ne ya

siye

amintacciyar baiwar ubana ta zuba

masa guba a

shayinsa.Shin rama cuta ga macuci

laifi ne?Hatta

uwata bata san nasan wannan sirri

ba.Koda jin

wannan batu sai jikin sarki Safwan ya

sakeyin

sanyi a karo na biyu.Amma sai

zuciyarsa ta

kekashe ya sake murtuke fuskarsa

yana mai gyara

tsayuwa alamar cewa a shirye yake a

gabza

yakin.Koda ganin haka sai Hawaye ya

sake

subutowa Safirat tace tabbas yau ne na

tabbatar

da cewa NAMIJI BA DAN GOYO

bane,kuma namiji

butulu ne!Idan har nayi nasara kanka

kuma na

sami nasarar dauko tuttun kwari na,na

rantse da

jini ubana saina sa gaba dayan mazajen

duniya

sun zubar da hawaye.Sai na sauke

gaba dayan

sarakunan duniya daga kan karagarsu

ta mulki na

dora mataye akai.Sai kowace matar

aure ta daina

kwanciya a kasan mijinta,sai dai a

samansa.Sannan sai kowace mace ta

daina dafawa

mijinta abinci tare da yi masa sauran

hidima,saidai

shi yayi mata ya zamo bawanta.Saina

maishe da

dukkan mazajen duniya tamkar

karnukan farautan

mata sai yadda suka so zasu

sarrafasu.Safirat na

gama fadin haka sai ta dubi dakarun

dodanninta

tace dasu ko sarki Safwan zai samu

nasarar

kasheni kada ku tayani yakarsa.Duk

wanda ya

tayani yakarsa zan kasheshi da

hannuna.Nan take

Jaruma Safirat ta zare takobinta ta ruga

izuwa kan

sarki Safwan tana mai kwarara uban ihu

da

kururuwa,takobinta na kartar kasa tana

tashin

kura.Suna haduwa suka kacame da

wani masifaffen

yaki mai tsananin ban tsoro da ban

al'ajabi.Nanfa

suka rinka kaiwa junansu sara da suka

cikin bakin

zafin nama,juriya da bajinta.Su kuwa

wadannan

dodanni sai suka zuba musu idanu

kawai suka

zama yan kallo saboda tsoron saba

umarnin

jaruma Safirat.

Toofah!!Nima ganin ana wannan

masifaffen yaki

yasa na tsaya domin na more kallo.

Don't just read and pass,Commenting

and Liking Necessary.

A yanzu ne labari ya fara dadi fiye da


08161272634

KIBIYA RATSA MAZA 🎿

Littafi Na Biyu (2)

Part B


                       Post 

                By :----Man Bash ----


     Ana cikin wannan hali ne Safirat taga uku daga

cikin dodanninta sun sare sun fadi kasa suna haki

kamar ransu zai fita,kawai sai ta sharesu ta cigaba

da gudunta abinta suna kara yin dan gaba sai

dodannu biyar suka sake sarewa suma suka zube

kasa.Faruwar hakan keda wuya sai hankalin

Jaruma Safirat ya dugunzuma domin ta fahimci

cewar indai aka cigaba da gudun a haka to za'a

kai munzalin da zata rasa gaba dayan

dodanni,alhalin kuma tasan cewa akwai lokacin da

zasuyi mata matukar amfani.Bisa sa'a kuwa sai

Safirat ta hango wata fadama(korama) a gabansu

kadan.Cikin farin ciki ta karasa gaban koramar ta

tsuguna ta jika kanta ta sha ruwa.Ai kuwa sai

suma sauran dodannin suka rugo izuwa cikin

fadamar suna murna suka kama shan

ruwan.Adaidai wannan lokaci ne Safira taji takun

sawu da gudu an tsaya a bayansu.A nutse Jaruma

Safirat ta mike tsaye ta juyo a hankali saboda

dama tasan wanda ke biye dasu din.Ai kuwa tana

waigowa tayi arba da sarki Safwan a tsaye rike da

sharbebiyar takobinsa yana haki kamar ransa zai

fita.Ga tsananin kishirwa na damunsa,lebansa ya

bushe sai kallon wannan ruwa na cikin fadamar

yake.Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin sarki

Safwan da jaruma Safirat.Kawai sai dodannin suka

yunkura zasu kaiwa sarki Safwan farmaki amma sai

jaruma Safirat ta daka musu tsawa tace wannan

yaki ba naku bane shi kadai ya iso nan don haka

mutum daya ne zai yakeshi kum Nice Koda gama

fadin hakan sai jaruma Safirat ta cire battar

ruwanta daga kwankwasonta ta tsomata cikin

fadamar ta cikata da ruwa sannan ta tsuke bakinta

ta cillawa sarki Safwan ya cafe.Dama tazarar dake

tsakaninsu bata wuce taku ashirin ba.Safira ta dubi

sarki Safwan a lokacin da hawaye ya subuto mata

cikin tsananin takaici tace bazan yaki masoyina a

lokacin da yake jigace ba,kasha ruwa ka gusar da

kishinka.Koda jin haka sai sarki Safwan ya bude

battar ruwan ya kafata a bakinsa ya kama

kwankwada har saida ya koshi sannan yayi jifa da

ita.Ya dubi Safirat fuskarsa a murtuke tamkar yana

kallon kumurcin maciji mai shirin saransa.Har ya

budi baki zaice wani abu sai ta tari numfashinsa

muryarta tana rawa tace ashe zaka iya sayar da

soyayyarmu saboda abin duniya?Ina kaunarmu da

amanar dake tsakaninu?Shin laifin mahaifina ne ya

shafeni har da kakeson ganin bayana?Koda sarki

Safwan yaji wadannan tambayoyi sai zuciyarsa ta

karaya kuma kunya ta kamashi sannan hawaye ya

zubo masa shima ya budi baki cikin rawar murya

yace,yake Safirat ki dauki soyayyarmu,kaunarmu,­

shakuwarmu da kuma amanar dake tsakaninmu

tamkar wani abu daya faru a mafarkin daya shude

tuntuni a baya.Ki sani cewa a halin yanzi bani da

wani abokin gaba wanda ya fiki domin mahaifinki

ne ya kashe ubana kinga dole ne na dauki fansa

akanki. Abu na biyu dole ne na rabaki da wannan

KWARI DA BAKA naki domin ceto Rayuwar kasata

da jama'ar da kuma mulkina.Idan harna barki kika

mallaki wannan kwari da baka tofa sai duniya gaba

daya ta koma hannun mata.Sai maza su koma

hannun bayin mata.Kinga kuwa duk ranar da

mulkin duniya ya koma hannun mata sai komai ya

lalace.Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun rushe

kenan.Saboda haka yanzu bani da wani zabi

wanda yafi na kashe ki na dauke wannan baka

tunda gaba daya sarakai,jarumai da matsafan

duniya hankalinsu na kan baka.Kafin sarki Safwan

ya gama rufe bakinsa tuni Jaruma Safirat ta daka

masa tsawa tace kaje ka binciki mahaifiyarka kace

kana son ta gaya maka ko wanene ya kashe

ubana.To ka sani cewa ubanka ne ya siye

amintacciyar baiwar ubana ta zuba masa guba a

shayinsa.Shin rama cuta ga macuci laifi ne?Hatta

uwata bata san nasan wannan sirri ba.Koda jin

wannan batu sai jikin sarki Safwan ya sakeyin

sanyi a karo na biyu.Amma sai zuciyarsa ta

kekashe ya sake murtuke fuskarsa yana mai gyara

tsayuwa alamar cewa a shirye yake a gabza

yakin.Koda ganin haka sai Hawaye ya sake

subutowa Safirat tace tabbas yau ne na tabbatar

da cewa NAMIJI BA DAN GOYO bane,kuma namiji

butulu ne!Idan har nayi nasara kanka kuma na

sami nasarar dauko tuttun kwari na,na rantse da

jini ubana saina sa gaba dayan mazajen duniya

sun zubar da hawaye.Sai na sauke gaba dayan

sarakunan duniya daga kan karagarsu ta mulki na

dora mataye akai.Sai kowace matar aure ta daina

kwanciya a kasan mijinta,sai dai a

samansa.Sannan sai kowace mace ta daina dafawa

mijinta abinci tare da yi masa sauran hidima,saidai

shi yayi mata ya zamo bawanta.Saina maishe da

dukkan mazajen duniya tamkar karnukan farautan

mata sai yadda suka so zasu sarrafasu.Safirat na

gama fadin haka sai ta dubi dakarun dodanninta

tace dasu ko sarki Safwan zai samu nasarar

kasheni kada ku tayani yakarsa.Duk wanda ya

tayani yakarsa zan kasheshi da hannuna.Nan take

Jaruma Safirat ta zare takobinta ta ruga izuwa kan

sarki Safwan tana mai kwarara uban ihu da

kururuwa,takobinta na kartar kasa tana tashin

kura.Suna haduwa suka kacame da wani masifaffen

yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi.Nanfa

suka rinka kaiwa junansu sara da suka cikin bakin

zafin nama,juriya da bajinta.Su kuwa wadannan

dodanni sai suka zuba musu idanu kawai suka

zama yan kallo 

Saboda tsoron saba umarnin Jaruma

Safirat.Wohoho!Idan jarumtaka ta hadu da

takwaranta,naci da juriya suka game tofa dole ne

yayi yayi tsamari ainun.Saida Safira da Sarki

Safwan suka shafe dakiku masu yawa suna wannan

artabu amma dayansu bai samu nasarar koda

lakutar jikin daya ba.Al'amarin daya dugunzuma

hankalin kowannensu kenan.Shidai sarki Safwan

burinsa shine ya kashe Safirat kafin ragowar

rundunonin makiyanta su karaso wajen ya dauke

bakan dake goye a bayanta ya gudu.Itama Safirat

kokarinta shine ta gama da sarki Safwan kafin

sauran makiyan nata su karaso domin ta isa cikin

dajin Sharkif in yaso su sameta a can.Koda

kowannensu yaga wankin hula zai kaishi dare sai

suka sauya salon fada a lokaci guda suka hada da

kaiwa juna NAUSHI DA BUGU.Nan take kuwa labari

yasha bambam ya zamana cewa sun fara hadawa

kansu JINI da MAJINA.Nanfa suka fara

galabaita.Lokaci guda kowannensu ya fara ja da

baya cikin tsananin fushi sukayi nazarin juna suna

mamakin yadda karfin damtsensu yazo daya gami

da iya yakinsu.Kamar hadin baki sai kuma suka

sake rugowa da gudu izuwa kan juna a karo na

biyu suna masu kwala ihu.Koda ya rage saura taku

uku kacal su hadu sai kowannensu ya daka tsalle

sama ya kaiwa dan uwansa mugun sara.Duk da

cewa kowannensu yayi yunkurin kaucewa harin da

aka kawo masa,amma sai da hakan ya faskara

domin sarki Safwan ya sami nasarar saranta a

gadon bayanta,ita kuma ta samu nasarar saransa a

kirjinsa.Lokaci guda duk su biyu suka rusa ihu

sakamakon tsnanin zafi da zogin da sukaji a

lokacin da jini yai tsartuwa daga jikinsu suka fado

kasa a matukar galabaice suka kasa koda mikewa

tsaye.Adaidai wannan lokaci ne suka jiyo sukuwar

dawakai a bayansu.Suna waigawa suka hango

rundunonin daruruwan mahaya sun tunkaro su

daga can nesa sai kara yiwa dawakansu kaimi

suke domin su riskesu cikin kankanin

lokaci.Sawayen dawakan nasu na tashin

gagarumar kura.Koda ganin haka sai daya daga

cikin dodannin ya suri jaruma Safirat ya dorata a

gadon bayansa,ya falfala da wani azababben gudu

irin nasu.Ai kuwa sai sauran yan uwansu suka rufa

masa baya.Kafin rundunonin abokan gabar Safirat

su iso wajen tuni dodannin sun kule a cikin dajin

tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen.Koda sarki

Safwan yaga Safirat ta tsere saiya kurma uban ihu

na bakin ciki kuma ya dafe raunikan kirjinsa mai

bulbulo da jini.Adaidai wannan lokaci ne ya bingire

kasa sumamme.Koda dakarun sarki Safwan suka

iso sukaga halin da yake ciki sai suka

dimauce.Nan tahe aka kafa tanti aka shigar dashi

ciki,likitansa ya kama aikinsa.Sauran sarakuna da

jarumai da mayakan da suka iso kuwa suka cika

da tsananin bakin ciki saboda sun san cewa koda

ma sunbi bayan Safirat a yanzu ba lallai bane su

risketa kafin ta isa cikin dajin Sarkif.Dajin da babu

wani mahaluki da baya tsoransa a duk fadin duniya

walau MUTUM ko ALJAN.Nan take gaba daya

sarakunan kimanin su arba'in gami da manyan

bokaye su ashirin da takwas da kuma

zakwakwaran jaruman da suka fito daga manyan

birane na duniya su talatin da biyu suka shirya

taro na gaggawa aka zauna ana tattaunawa.Sarkin

Misra ne ya fara da fadin cewa a halin yanzu babu

abinda ya kamata muyi face mu jira farfadowar

sarki Safwan na birnin Kisra tunda shi kadai ne a

cikinmu ya sami nasarar cimam wannan

takadariyar yarinya har suka fafata.Kuma dama

shine mafi sanin siriinta tunda tun suna yara suke

tare.Shine kadai zai iya bamu shawara da wannan

baka kafin ta dauko kuttun kwarinsa.Koda sarkin

Misra yazo nan a jabawabinsa sai wani shahararren

boka na kasar Yemen ya tari numfashinsa yace kai

bazai yiyu ba,domin a bari ya huce shike kawo

rabon wani.Kuma da zafi zafi akan bugi karfe.Ba

muki ta shawararka ba amma ga wata

shawarar.Kowacce runduna ta zabo wakilanta guda

goma goma a turasu subi bayan jaruma Safirat da

dakarun dodanninta,su cimma kafin su shiga cikin

dajin Sarkif.Tunda dai itama Safirat akwai rauni

babba a jikinta yanzu,nasan ba zasu shiga cikin

dajin Sarkif da ita a wannan hali ba.Dole ne su

tsaya suyi jinyarta ta farfado kuma ta dawo cikin

haiyacinta.Boka Inzuba ne yayi wannan

jawabi.Koda jin haka sai sansanin ya rude da

shewa kowa na cewa ya amince da shawarar boka

Inzuba.Nan take kowace runduna ta zabo dakaru

goma daga cikin mayakanta wanda take takama

dasu.Kuma ganin cewa ta yarda dasu,zasu iya yin

duk abinda ake ganin ba zai yiyu ba,kowane

badakare kallo daya zakayi masa ka tabbatar da

cewa ya cika gwarzon mayaki abin kwatance

saboda suna da kwarjini,haiba da cikar zati gami

da sura irin na manyan jarumai.Kuma kowannensu

na dauke da mahaukacin makami.Har wadannan

zababbun dakaru sun yunkura zasu bi bayan su

jaruma Safirat sai sarkin birnin Farisa ya tsaida su

yana mai daga hannu sannan ya dubi gaba daya

jama'ar dake wajen yace yanzu a misali idan

wadannan wakilan dakaru namu suka sami nasarar

karbo wannan baka a hannun Safirat wa za'a barwa

Bakan?Koda jin wannan tambaya sai kowa ya

shiga taitayinsa aka kama muzurai ana kallon

juna.Aka rasa wanda zaice kala.Da ganin haka sai

sarkin Farisa yace tunda an rasa mai bada amsar

tambayata ni zan baiwa kaina amsa.Amsar itace da

zarar an zo da bakan,sai a shirya GASAR

JARUMTAKA a tsakanin dakarun jaruman

namu,wanda suka yi nasara su za'a barwa

bakan.koda jin haka sai aka dada rudewa da

shewa kowa na cewa ya amince da wannan

tsari.Nan take dakarun wakilcin suka zaburi

dawakansu da gudu izuwa cikin daji domin su

riske su jaruma Safirat kafin su isa dajin Sarkif.

Bayan tafiyar wadannan dakarun wakilci da kamar

kimanin rabin sa'a ne sarki Safwan ya farfado daga dogon suma da yayi. habawa ai kwa sai .........h'm 


      Sai tomorrow kuma in sha'allah amma kafin wannan 


        Nidin ne dai Man Bash Nake cewa Asuba ta gari

08161272634


KIBIYA RATSA MAZA 🎿

Littafi Na Biyu (2)

Part C


                       Post 

                By :----Man Bash ----


     Yana bude idanunsa yaga raunin kirjinsa a dinke kuma ya tsinci kansa kwance a

cikin tanti.Take ya gane cewa dakarunsa ne sualka

iso suka ceci rayuwarsa.Kawai sai ya tuno da

yadda Safirat ta kubuce masa,nan fa bakin ciki ya

turnuke shi ya rasa abinda ke masa dadi a

duniya.Cikin tsananin karfin hali sarki Safwan ya

yunkura domin ya mike zaune daga kwance amma

saiya kasa bisa tsananin zafi da zogin da yaji

tamkar kasusuwan kirjin nasa zasu kakkarye.Bisa

dole ne ya koma ya kwanta.Faruwar hakan keda

wuya saiga likitansa ya shigo cikin tantin da sauri

saboda dama yi kiyasta iya tsawon lokacin da

sarki Safwan zaiyi ya farka daga bacci.Da shigowar

likitan yana duban sarki ya gane cewa yayi

yunkurin mikewa zaune don haka saiya dubeshi

cikin alamun tsananin damuwa da fargaba yace ya

shugabana ka sake yunkurin zauna zaka iya rasa

rayuwarka gaba daya domin kuwa dukkan

kasusuwan jikinka ne zasu kakkarye saboda

jijiyoyin dake rike da kirjin naka ne zasu

tsintsinke.Kayi sani cewa ka auna arziki daya

zamana cewa saran da jaruma Safirat tayi maka

baikai ga datsa kasusuwanka ba,naman wajen ya

dare kuma ya dan taba kashin kadan.Dole ne a

kallah ka sami kwana tara a kwance kana jinya

kafin kashin ya hade ka iya motsi sosai ko ci gaba

da tafiya.Koda jin wannan batu sai zuciyar sarki

Safwan ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda

bakin ciki domin yasan cewa kafin cikar kwanakin

tara jaruma Safirat zata iya dauko kurtun

kwarinta.Idan kuwa har haka ta kasance tofa babu

wani mahalukin da ya isa ya tare da yaki don ko

mutanen duniya ne da aljanunta zasu hadu a kanta

sai ta karar dasu.Koda sarki Safwan ya gama

aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai sabon bakin ciki

ya turnukeshi har kwallar takaici ta cika masa

idanu yayi sauri ya kauda kansa ga barin kallon

likitan nasa don kada ya gane damuwarsa.

Al'amarin Jaruma Safirat kuwa itama tun sa'adda

ta fadi kasa sumammiya daya daga cikin dodannin

ya sureta ya aza a bayansa suka ruga izuwa cikin

daji bata farka ba sai bayan sa'a uku da rabi,tana

bude idanunta ta tsinci kanta kwance akan wata

bishiya mai yawan duhuwar ganyaye kuma a cikin

wani irin daji wanda ko a labari bata taba jinsa

ba.Da farko saida Safirat ta shafa gadon bayanta

taji an dinke rauninta kuma an shafa mata wani

magani a kansa me maiko.Koda ta dubi gabas da

yammanta sai taga ashe akwai wadannan dodannin

kimanin su goma akan bishiyar sun yi mata

KAWANYA suna gadinta.Bisa mamaki sai jaruma

Safirat taga ta iya mikewa zaune alhalin a zatonta

ba zata iya mikewa ba zaune sai bayan yan

kwanaki.Koda taga ta mike zaune daram ba tare

da taji wani ciwo ko wani zogi ba a bayanta sai ta

dubi dodannin tace,maza kuzo mu wuce izuwa

cikin dajin sarkif saboda na tabbatar da cewar

makiya suna biye damu,kuma idan suka riskemu

anan ban san yadda karshen gumurzunmu zai

kasance ba.Koda jin wannan batu sai wannan dodo

wanda ya goyata a bayansa ya dubeta yace,ya

shugabata ai dama ba wani abu bane yasa muka

yada zango ba anan face ganin halin da kike ciki

na suma da wannan rauni dake jikinki.In badon

mun kware akan ILMIN LIKITANCI ba da ba zamu

iya ceto rayuwarki ba har ma ki iya mikewa

zaune.Kuma gani mukayi idan ma muka shiga

cikin dajin Sarkif dake a cikin wannan mugun hali

babu abinda zaki iya bisa batun dauko kuttun

kwarinki.Kinga kenan shigar tamu bata da wani

amfani.Koda jin haka sai Safirat tayi murna kuma

ta yiwa dodannin godiya bisa ceto rayuwarta da

sukayi.Nan take ta duro kasa daga kan bishiyar

suma sai suka duro.Nan take taga ragowar

dodannin suna fitowa daga inda suka lallabe don

tabbatar da TSARO.KAfin Jaruma Safirat tayi

yunkurin cigaba da tafiya sai kawai sukaga

wadannan dakarun wakilci sun durfafo su a guje

bisa dawakai su da yawa suna masu zare

takubbansu suna kwarara uban ihu mai tsananin

firgitarwa.Kuma tazarar dake tsakaninsu bata wuce

taku goma ba.Har jaruma Safirat ta yunkura zata

zare takobinta sai wannan dodo daya goyata yai

wuf ya sureta ya sake° goyata a bayansa yace ya

shugabata bai kamata kiyi yaki ba yanzu domin

raunin gadon bayanki bai gama hadewa ba da

warkewa.Dinkin raunin zai iya warewa idan kikayi

kyakkyawan motsi.Ki kyalemu da wadannan dakaru

zamu iya dasu.Kafin wannan dodo ya gama rufe

bakinsa tuni sauran yan uwan nasa sun ruga izuwa

inda dakarun wakilcin suke suka tare su.Nanfa aka

ruguntsume da azababben yaki sai gashi dodannin

suna daka tsalle sama suna shawagi akan dakarun

wakilcin suna kai musu yakushi,sara da suka da

miyagun faratan hannayensu.Su kuma suka wanzu

suna karewa gami da maida martani.Nanfa kowa

ya zamewa kowa alakakai domin babu bangaren

dake samun wata nasara.Duk saadda makaman

dakarun ya hadu da jikin dodannin saikaga

tarwatsin wuta na tashi.Da yake suma wadannan

dakarun wakilci sun cika jarumai masu karfin

sihirin tsafi gami da matukar juriya da tsagwaron

iya yaki sai karfi ya kusan zama daya.Koda

donannin suka ga haka sai suka rinka huda cikin

dawakansu suka rinka faduwa kasa matattu suna

kayar da mahayansu.Nanfa aka bude kasuwar

KASUWAR YAKI ta gaba da gaba.Abinda ya

dugunzuma hankalin dakarun wakilcin shine ganin

yadda KAIFI da TSINI baya tasiri a jikinsu.Duk

wannan abu dake faruwa dodon dake goye da

Safirat yana ta kokarin samun hanyar da zai tsere

da ita ne ya nausa cikin dajin Sarkif amma ya kasa

saboda dakarun wakilcin sunyi musu kawanya

ne.Saida aka shafe sa'a daya da rabi ana yin

wannan bakin artabu ba tare da kowane bangare

sun sami wata nasara ba.Kwatsam bisa tsautsayi

sai tsinin takobin

daya daga cikin dakarun wakilcin ya soki idon daya

daga cikin dodanni.Faruwar hakan keda wuya

dodon yayi wani uban ruri a lokacin da jini ya

kama feshi yai tsalle ya runtuma da kasa ya kama

kakarin mutuwa.Koda dakarun wakilcin suka ga

haka sai suka cika da murna saboda sun gano

lagon dodanni ai kuwa sai suka kara kaimi wajen

yakarsu.Sai gashi sun cigaba da soke musu idanu

suna zubewa kasa matattu tamkar ana sassabe a

gona.Nan da nan cikin kankanin lokaci suka kashe

kimanin dodanni ashirin da bakwai su kuwa

dodanni da kyar suka iya kashe ashirin da daya na

dakarun wakilcin.Koda Safirat taga irin mummunar

barnar da dakarun sukayi musu saita fusata ainun

bata san sa'adda ta daka tsalle sama ba daga kan

gadon bayan dodon daya goyata.Tana saman iska

ta zare takobinta ta afka cikin dakarun wakilcin ta

hausu da sara da suka ba kakkautawa.Take salon

yaki ya sauya domin a cikin dakika arba'in ta

shaftare makogwaron dakaru kusan hamsin suka

zube kasa matattu.Ana cikin haka ne wani

badakare mai mugun naci ya sadado ta bayan

Safirat ya doki gadon bayan nata da kafarsa guda

da dukkan karfinsa.Jaruma Safirat tayi tsalle sama

tamkar an janyeta da majaujawa a lokacin data

kurma uban ihu sakamakon mugun zafin da taji a

gadon bayanta kuma sai fuskarta ta gwaru da jikin

wata bishiya ta fado kasa sumammiya.Kafin daya

daga cikinsu ya sami damar cafkarta tuni wannan

dodo ma'abocin goya Safirat ya dauketa daga

wajen ya sake goyata ya falfala da azababben gudu

ta tsakiyar dakarun wakilcin yana tarwatsasu da

karfin tsiya su kuma suna yi masa lugudan sara da

suka suna kokarin hallaka Safirat da dauke

bakanta.Amma sai suka kasa saboda dodon yafi

gaba dayansu zafin nama da karfin gudu da kuma

tsananin karfin damtse.Kafin su ankara tuni ya fice

fit ta tsakiyar tasu ya basu tazara mai yawa.Nanfa

suka bi bayansa da gudu a lokacin da tsirarun

dodannin ma suka rufa masa baya.Haka dai

dakarun wakilcin suka cigaba da bin wannan dodo

mai goye da Safirat suna karawa dawakansu

kaimin gudu wanda gudun nasu gudu ne na SIHIRI

amma har dodon ya iso bakin dajin Sarkif basu

sami damar riskarsu ba.Koda sukaga dodon ya

fada cikin dajin Sarkif da kafafunsa sai suka ja

linzamin dawakansu sukayi turjiya da haniniya.Jin

turjiyar dawakan nasu ne yasa dodon ya tsaya cak

ya waigo yana yiwa dakarun wakilcin murmushin

mugunta sannan ya yafutosu da hannu yana maiyi

musu nuni da cewar idan sun isa su biyoshi cikin

dajin sarkif din.Amma dukkaninsu sai suka noke

aka rasa wanda zai saida ransa.Ta gaban dakarun

wakilcin sauran dodannin suka zo suka wuce da

gudu suka fada cikin dajin Sarkif suka bi

dan'uwansu a baya lokacin daya juya ya cigaba da

tafiya a hankali cikin Izza,Kasaita da kwanciyar

hankali. bayan Kulewar Dodannin ne a Cikin dajin sai

dakarun wakilcin suka dubi junansu cikin tsananin

takaici.Daya daga cikinsu ya dubi sauran cikin

alamun matukar damuwa yace bamu da ilimin

komai akan dajin Sarkif,duk wanda yayi gangancin

shigarsa a cikinmu tabbas mutuwa zaiyi.Yanzu

kuzo mu koma sansaninmu wajen shugabanninmu

mu sanar dasu duk abinda ya faru,amma dole ne

mu dauki gawar dodo ko guda daya ne domin su

gasgata zancenmu su tabbatar da cewar munyi

iyakar kokarinmu.Gama fadin hakan keda wuya sai

dakarun wakilcin suka juya da baya da gudu izuwa

cikin dajin da suka baro,wato can inda suka fara

yin gumurzun farko dasu jaruma Safeerat.

Al'amarin su jaruma Safirat kuwa lokacin da aka

shigar da ita cikin dajin sarkif sa'adda take cikin

suma na biyu goye a bayan wannan dodo,tafiyar

dakika dari biyu da sittin kacal akayi ta farfado

daga suman da tayi.Amma sai taji gadon bayanta

yana yi mata mugun radadi da zogi sakamakon

naushin da akayi mata wanda ya zama ya fama

mata raunin,amma sai taji cewa zata iya yin tafiya

da kafafunta,Sai ta budi baki tace ka ajiyeni na taka

da kafafuna.Koda jin muryar Safiray sai farin ciki ya

kama dodon ya tsaya cak ya sauke ta saboda

tsawonsa.Koda ya direta kasa a gabansa yaga ta

fara kallon dajin Sarkif tana murmushi saboda

ganin irin ni'imar dake cikinsa ta korayen

ganyaye,ruwan duwatsu dake kwaranya wanda ya

kasance garai garai gwanin ban sha'awa da kuma

yayan itatuwa irinsu inibi,baure da sauransu sai

yace ya shugabata kyawun wannan daji ya daina

birgeki domin kyan dan maciji ne.Idan kinsan

masifun dake cikinsa da bakiyi sha'awar shigarsa

ba.Mu kanmu a yanzu ba karamin ganganci mu

kayi ba da muka biyo dake izuwa nan kawai,don

bamu da yadda zamuyi mu kawo kanmu GIDAN

MUTUWA,kuma ako yaushe a ko ina ajali zai iya

zuwa ya shammacemu a cikin wannan daji.Koda

jin wannan batu sai mamaki ya kama jaruma

Safirat tace to wai shin menene abin tsoro a cikin

wannan daji?Ni tun da muka shigo cikinsa ko

mugun kwaro guda daya ban gani ba.Gama fadin

haka keda wuya sai safirat taji wani irin huci a

bayanta mai dumi kamar an kunna gagarumar

wuta sannan kuma taji wani irin gurnani mai

matukar ban tsoro.A firgice ta waiga bayanta da

sauri,koda tayi arba da abinda ke bayanta sai taji

kamar ta saki fitsari a tsaye saboda tsananin

razanar da tayi duk da jarumtaka irin tata kuwa.Ba

komai jaruma Safirat ta gani ba face wata irin

katuwar macijiya mai girman gaske,amma kuma

kanta irin na macen bil'adama ne rafkeke tamkar

tunkuyar girki irin ta mutanen da.Tna da idanuwa

manya manya kamar tulu,hancinta wawakeke za'a

iya zura mutum a cikin kowane kofar

hancin.Bakinta kuwa kamar kofar shiga wani

gari.Hakoranta gabza gabza ne kamar hauren giwa

ne aka jera sama da kasa kuma guda dari ba daya

ne.Saboda girman jelarta da nauyinta ko yaya ta

motsa sai dajin gaba daya yayi girgiza.Tunda

Jaruma Safirat tazo duniya ko a mafarki bata taba

tunanin cewa akwai wata halitta mai mummunar

siffa irin wannan ba.Nan take sai jikin Safirat ya

kama karkarwa.Su kuwa wadannan dodanni

abokan tafiyar Safirat tuni sun arce daga wajen sun

shige cikin kogunan duwatsu da cikin ramuka sun

buya suka bar Safirat ita kadai a tsakiyar dajin a

gaban wannan muguwar Macijiya 🐍 Nima fah na feceee kar tayi loma daya dani lol 😜 😜


      Sai tomorrow kuma in sha'allah amma kafin wannan 


        Nidin ne dai Man Bash Nake cewa Asuba ta gari

Suleiman zidane kd


KIBIYA RATSA MAZA 🎿

Littafi Na Biyu (2)

Part D


                       Post 

                By :----Man Bash ----


     Lokacin da macijiyar taga yadda jaruma Safirat ta firgice kuma

ta dimauce sakamakon yin arba da ita sai ta bushe

da wata irin mahaukaciyar dariya mai kama da

saukar kwaran kwatsa sannan ta hade bakin a

lokacin da wani irin turirin dafi ke fita ta dakawa

Safirat tsawa tace ke karamar kwaruwa wane irin

taurin kai gareki gami da ganganci da rayuwa har

da zakiyi tunanin shigowa cikin wannan daji domin

ki dauki wani abu?To ki sani cewa ko shi kansa

mahaifin naki boka Saiham daya tabbata shugaban

bokayen duniya bai taba shigowa nan ba,saidai ya

aiko da abu ta hanyar sihiri shi kansa yasan ya

turoki ne izuwa AJALINki.Kafin macijiyar ta gana

rufe bakinta tuni jaruma Safirat ta tari numfashinta

tana mai cewa ke tsohuwar azzaluma,ki sani cewa

koma girman halitta,komai jin kanta da karfinta sai

an sami wadda ta fita komai.Tabbas na firgita da

ganinki saboda shi tsoro wajibi ne,amma dana

gane cewa ke azzalima ce sai naji duk tsoronki ya

gushe daga cikin zuciyata.Duk abinda yai farko a

cikin wannan duniya yana da karshe,babu mamaki

zuwana nan ya zama sanadin karshen

zaluncinki.Nayi imani cewa sai na sami abinda

nazo nema a cikin dajin nan kuma sai na fita a

raye don haka ke baki isa ki hanani daukar abinda

nazo dauka ba.Koda Safirat tazo nan a zancenta

sai Macijiyar ta wangame katon bakinta ta bushe

da dariya a karo na biyu,iskar bakin nata ta daga

Safirat sama har saida ta daina dariyar tsuke

bakinta sannan Safirat ta fado kasa tim.macijiyar ta

dubeta cikin kallon raini tace hakika yaro bai san

wuta ba sai ya taka ta.Tunda kikayi mini rashin

kunya yau saidai uwarki ta haifi wata amma dai ke

taki ta kare.Idan kina da wasiya ta karshen rayuwa

ki fadi kafin ki sheka barzahu.Kuttun kwari da

bakan da kika zo nema bama ke ba wasunki ma

basu isa susan inda yake ba a cikin wannan daji

bare su dauka daga nan har izuwa rayuwa idan

akwaita.Kafin Safirat ta bude baki tace wani abu ko

kuma tayi wani yunkuri tuni majiyar ta shammaceta

ta wangame bakinta.Take wata irin iska mai karfi ta

fito daga cikin bakin ta zuke Safirat ta

hadiyeta.Kawai sai macijiyar ta rufe bakin nata

sannan ta daka tsalle ta tsunduma cikin wani

tafkeken kogi tayi nutso izuwa karkashinsa.A

ka'idar wannan macijiya duk abinda ta hadiye a

cikin dakika biyar kacal yake narkewa ya zagwanye saboda

tsananin zafin dake cikin cikinta,amma sai gashi

Safirat bata narke ba kuma bata mutu ba amma

tsananin zafin cikin macijiyar yasa jikinta yayi luguf

kuma numfashinta ya fara sarkewa saboda rashin

shakar iska.Koda Safirat taji zata hallaka saita

mike tsaye a cikin cikin macijiyar ta zare wata

wuka dake daure a jikin cinyarta ta hagu ta kama

saran hanjin cikin macijiyar.Ai kuwa sai macijiyar

ta rinka jin kamar zata mutu don haka bata san

sa'adda ta wangame bakinta ba tayi wata irin

muguwar kara wacce tasa gaba dayan halittun

dake cikin karkashin tekun suka mace nan

take,wadanda ke saman kogin suka sume,wadanda

ke cikin dajin bisa turba dole suka toshe

kunnuwansu,wasu kuwa suka rinka tona kasa suna

binne kansu da kansu a karkashin kasa.Safirat ta

cigaba da saran hanjin cikin macijiyar duk da cewa

kuwa hanjin baya katsewa amma macijiyar bata

daina mutsu mutsu da juye juye ba tana ruri da

ihu tana gwara jikinta a jikin duwatsun dake cikin

karkashin kogin.Sakamakon haka ne Safirat ma ta

rinka faduwa tana gwara kanta da jikin macijiyar

amma saboda tsananin naci da juriya sai ta cigaba

da mikewa tsaye zumbur tana ci gaba da saran

hanjin macijiyar,nanfa ya zamana cewa da ita da

macijiyar duk sun wahala sun jigata ainun.nan da

nan idanun macijiyar suka kada sukayi jawur,suka

fara zubar da hawayen wuya,kai da bala'i yai bala'i

macijiyar taji cewa tabbas hallaka zatayi sai ta taso

sama daga karkashin kogin ta fito bakin gabar

kogin ta fito bakin kogin ta kama kakarin amai

domin ta watso Safirat waje daga cikinta ta huta da

azabar da take ji.koda Safirat taji an zukota za'a

wastota waje daga cikin macijiyar don haka saita

saki jikinta ta taho da gudu tana fitowa bakin

macijiyar saita wurkila jikinta ta haye saman kan

macijiyar ta zauna daram.Kafin macijiyar ta wurkila

jikinta ta jeho Safirat kasa tuni ta daga wannan

wuka dake hannunta ta caka mata ita a tsakiyar

madigarta.Nan take jini ya kama tsiri sama a

lokacin da macijiyar tayi wani irin uban ruri wanda

bata taba yin kamarsa ba.Kawai sai ta langwabe

kasa tayi wanwar ko shurawa batayi ba.Ashe ruhin

wannan macijiyar a cikin tsakiyar kanta yake cikin

madiga.Ita kanta jaruma Safirat da taga ta sami

nasarar kashe macijiyar tayi matukar mamaki

domin bata san cewa ruhinta a tsakiyar kanta yake

ba kawai dai tsananin sa'a ne da rabo ya kaita ga

samun wannan nasara.Saboda jikin Jaruma Safiray

ya hadu yayi lugub sakamakon tsananin zafin da

cikin macijyar yake dashi saita yanke jiki ta fadi

kasa sumammiya.Adaidai wannan lokaci ne

wadannan dodanni suka fito daga cikin ramuka da

kogunan duwatsun da suke boya da gudu suka

rugo izuwa inda take kwance.Nan dai suka fara

kokarin ceto rayuwarta.Saida suka shafe kusan

rabin sa'a suna yi mata fifta da dan yayafa mata

ruwa amma bata farka ba.Al'amarin dayai matukar

dugunzuma hankalinsu kenan suka fara tunanin

cewa lallai ta mutu saboda babu alamar inda yake

motsi a jikinta.Nan fa dodannun suka kama kuka

suna zubar da hawaye na takaici da bakin ciki

saboda a ganinsa bai kamata ace jaruma kamar

Safirat ta mutu ba wacce tasha wannan bakar

gwagwarmaya tayi bajintar da ba'a taba samun

mahalukin da yayi taba a nahiyar gaba

daya,sannan kuma suna matukar bakin ciki bisa

ganin cewa duk wahalar da suka sha a baya ta

raka Safirat izuwa cikin dazuzzukan biyu da kuma

yan uwansu da suka rasa duk sun zamo a banza

kenan.Dodannin na cikin wannan tsananin bakin

ciki ne ma'abocin goyata a bayansa ya lura da

yadda jikin Safirat ya hadu yayi lugub har a sannan

tururin zafi bai daina fita ba daga cikin kofofin

gashin jikinta.Koda ganin haka sai yayi wuf ya

sureta ya azata a bayansa ya runtuma da gudu

izuwa wani bangare daban na dajin wanda shi

kansa bai san inda hanyar zata kaishi ba.A

dimauce sauran yan uwan nasa suka rufa masa

baya domin suga inda zai kaita.Haka dai dodon ya

cigaba da gudu dauke da Safira yana waige waige

da dube dube ko zai ga abinda yake nema wanda

yake ganin cewar shine kadai zai iya ceto rayuwar

Safirat.Duk da cewar wannan dodo da sauran yan

uwan nasa suna matukar tsoron wannan daji na

Sarkif sai gashi sunfi jin tsoron mutuwar Safirat

akan dajin.Burinsu kawai shine su ceto rayuwar

tata koda kuwa zasu rasa tasu rayuwar.Saidai

wadannan dodanni suka shafe sama da sa'a guda

suna guje guje a cikin wannan dajin Sarkif suna

fadawa cikin tsaunuka suna jin raunika a jikinsu

saboda komai na dajin daban yake basa iya kare

jikinsu.Nan da nan suka jigata ainun suka sha

bakar wahala.Duk wanda ya kalli wadannan

dodanni a lokacin da suke cikin wannan hali dole

ya tausaya musu kuma babu abinda zai burge

mutum face yadda suka nuna tsananin tausayinsu

da kaunarsu akan jaruma Safirat.Sai bayan sun sha

wannan muguwar wahala ne kwatsam suka hango

dusar kankara a gabansu a bakin wani kogi.A guje

suka karasa wajen wannan dodo dake goye da

Safirat ya sauketa daga kan gadon bayansa ya

turbutsata a cikin dusar kankarar ya binneta a ciki

yabar iya fuskarta a waje sannan suka ja da baya

suka tsuguna suka tsurawa gangar jikin Safirat

idanu suna jiran tsammani,ba don komai ba kuwa

sai saboda sunsan cewa idan Safirat ta shafe

kamar rabin sa'a a cikin Dusar kankarar bata

farfado ba to ta mutu kenan ba zata taba tashi

ba.Koda rabin sa'a ta shafe kuwa sai zuciyoyinsu

suka karaya suka fashe da matsanancin kuka kai

kace mutane ne su ba dodanni ba.Cikin tsananin

bakin ciki suka mike tsaye tamkar wadanda suka

tashi daga zaman makoki suka nufi inda Safirat ke

kwance da nufin su cirota daga cikin kankarar su

haka kabari su binneta.Da isarsu gabanta

wannan dodo ma'abocin goyonta yakai hannu da

nufin ya zarota sai kawai yaga idanunta sun bude

nan take ta yunkura ta taso zaune daga cikin dusar

kankarar.Koda dodannin sukaga haka sai suka

kaure da shewar farin ciki suka kama tsalle

tsalle.Koda Safirat taga yadda wadannan dodanni

ke murnar ganin ta rayu bata mutu ba sai itama ta

kamu da tsananin farin ciki,nan take ta mike tsaye

ta daka tsalle ta fada kan kirjin wannan dodo

ma'abocin goyata suka rungume juna kuma sai

suka fashe da kukan farin ciki.Saida suka dan jima

a kankame da juna sannan dodon ya ajiyeta kasa

tamkar ya ajiye yar tsana saboda kankantarta akan

girmansa.Kawai sai Safirat ta dubeshi cikin

murmushi tace waishin menene sunanka ne?Koda

jin wannan tambaya sai mamaki ya kama dodon

ya maida mata martani da murmushi yace,ke kuwa

menene dalilin da yasa tuntuni baki san suna ba

tun a farkon haduwarmu sai a yau?Sa'adda Safirat

taji wannan tambaya sai ta sake yin murmushi tace

saboda ayau ne na tabbatar da cewa kai masoyina

ne na kwarai domin kuwa ban taba haduwa da

mahalukin daya taba nuna mini tsantar kauna ba

kamarka hatta masoyina sarki Safwan kuwa.Domin

shi ya kasa hakuri da komai na duniya a kaina.kai

kuwa gashi ka sallama rayuwarka don ceton

tawa,kayi kuka ka zubar da hawaye saboda ganina

a cikin mugun yanayi.Inda ace kai mutum ne

kamarni da babu abinda zai hanani aurenka face

mutuwa.Amma duk da haka zan nemi alfarma daya

a wajenka inaso idan har na sami nasarar dauko

kuttin kwarina zan fara karbar karagar mulkin

Safwan na zama sarauniyar Birnin Kisra.A sannan

ne nake son ka zama shugaban dakaruna ma'ana

ka zama sarkin yakina amma lallai ka koma can

mazauninku ka dauko matarka idan kana da

ita.Idan kuma baka da mata to lallai kayi sabon

aure.Koda Safirat tazo nan a zancenta sai dodon

ya bushe da dariya yace suna nan Gargus kuma

dama can nine mataimakon shugabanmu

Bandaru,Ban taba aure ba amma saboda na faranta

miki rai bayan kin cimma burinki zan koma can

dajin tsaunin Lauhul Farras na auri daya daga cikin

irin matayenmu.Ya shugabata ina ganin zaifi kyau

mu nemi inda zamu kwana a cikin wannan daji

tunda yanzu dare ya soma yi gashi babu hasken

FARIN WATA.Kin sani cewa wannan daji na Sarkif

yana da tsananin hadari kuma babu wanda yasan

iyakar mugayen abubuwan dake cikinsa.Koda

Gargus yazo nan a zancensa sai Safirat tayi

murmushi tace na aminta da wannan shawara taka

dari bisa dari.Nan take suka dunguma gaba

dayansu suka kama neman inda zasu kwanta su

huta kuma suyi bacci.Cikin sa'a kuwa basu dade

ba suna nema suka sami wani kogon dutse.Saida

suka shiga cikin kogon suka cajeshi tsaf suka

tabbatar da cewar babu wani mugun abu a

cikinsa.Sannan suka yiwa Safirat shimfida ta

kishingida.A sannan ne Gargus ya shiga duba ko

ina a jikin Safirat domin yaga yadda raunikan

jikinta suke yayi mata magani.Bayan ya gama

nazarin raunukan ne ya kwanto jakar guzurinsa ya

ajiye a gabanta ya shiga yi mata magani a lokacin

ne ta kura masa idanu ta shiga zancen zuci.Ba

komai bane ya fado mata a rai face tunowa da

cewar Gargus shine kadai namiji daya taba jikinta

itama ta hada jikinta da nasa hatta sarki Safwan

kuwa.Waishin yaushe ne zatayi aure ta sami mijin

da zai iya sallama rayuwarsa domin tata kuma ta

sami magaji tare dashi?Koda Safirat tazo nan a

tunaninta sai hawaye ya zubo mata,takaici ya

turnuketa ta sami irin wannan masoyi.Haka dai

Safirat ta cigaba da wannan tunani har Gargus ya

gama aikinsa bacci ya saceta bata sani ba.Safirat

bata farka ba daga bacci saboda tsananin gajiya

da jigata saida gari ya waye har rana ta

kwalle. Nima dai sai a lokacin na fara yin gyangyadi har wayar ta fado ta fashe ban sani ba lol 😂😂


      Sai tomorrow kuma in sha'allah amma kafin wannan 


        Nidin ne dai Man Bash Nake cewa Asuba ta gari

Suleiman zidane kd

08161272634



Post a Comment

0 Comments