KALLON KITSE CMPLT

 13/12/2019 à 20:33 - Les messages envoyés dans ce groupe sont désormais protégés avec le chiffrement de bout en bout. Appuyez pour plus d'informations.

13/12/2019 à 20:33 - Vous avez créé le groupe “💑KALLON KITSE💑”

13/12/2019 à 20:34 - Vous avez retiré Sis Meerah

13/12/2019 à 20:35 - Vous avez changé l'icône de ce groupe

21/12/2019 à 15:34 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAREN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



_Na karb'i uzurin uwaren gida wannan karan, na kuma fahimci kukan su, sun ce kullum in dai labari ya biyo tsakanin miji da matan shi biyu, to sai marubuta sun yi k'ok'ari sun nuna uwar gida ce marar kirki, a k'arshe sai amarya ta mallake mijin, alhalin kuma a zamanin nan yanzu ba haka bane, dan haka dan Allah mu gyara, zaiyi wuya ace kullum uwar gida ce marar mutunci, duba da dayawa daga cikin maza sai sun k'ara auren ma su ka gane kirkin matan su na farko, ba ma miji kad'ai ba har da dangin shi, dan haka ku share hawayen ku, *Samira* za ta cika mu ku zuciyar ku da farin ciki, a matsayin ta na uwar gida ita ma uwar katarere😉, su momyn Dady *d'ogalawa* ne😂, ku biyo ni muji wa ake wa kallon kitse ne._



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *1*




Cikin kuka ta cire glishin (glass) idon ta ta kalle shi tace " Abban *Bilal* me na yi ma ka? Wane laifi na aikata da har za ka hukunta ni ta hanyar yi min kishiya? Abban Bilal ka dai na so na ne ko me? Me na rage ka da shi da har za ka k'ara aure a wannan lokacin? *Shekara goma sha uku* mu na tare da kai, ba ka k'ara aure ba sai yanzu, sai yanzu da na fi buk'atar ka a kusa da ni? Me ya sa? Me ya sa za ka k'ara aure? Ka gaji da zama da ni ne? Ko kuma dangin ka ne su ka saka ka k'ara aure, saboda har yanzu ban k'ara..."


Yasan me za ta fad'a, dan haka ya yi saurin rufe mata baki, manna kan ta ya yi a k'irjin shi ya na shafa bayan ta ya na fad'in "Haba Momyn Bilal, me ya sa za ki bari har shed'an ya shiga zuciyar ki ya rik'a raya mi ki wannan tunanin? Ni na fad'a mi ki kin min laifi? Ko kuma na fad'a mi ki zan k'ara aure ne saboda na dai na son ki? Haba dan Allah, ki nutsu mana, sannan ki saurare ni, ta hakane kad'ai za ki fahimce ni."


Da k'arfi ta d'ago daga jikin shi tace "Fahimta? Na fahimce kama ka ke cewa? Ai ni da k'ara fahimtar ka kuma har abada, ka riga da ka ruguza yarda da fahimtar da na ke ma ka a baya, Abban Bilal, wallahi ba zan sake sauraren ka ba, ka cuceni, ka zalunce ni, tsawon shekaru na d'auka ina rayuwa a k'ark'ashin yaudarar ka, kullum ka na fad'a min ni kad'ai ka ke so, ba ka da sha'awar k'ara aure a rayuwar ka, ba ka da wani dalilin da zai sa ka k'ara aure, amma shine yanzu za ka zo min da wai za ka k'ara aure, lallai, sai yau na yarda da ake cewa namiji ba d'an goyo bane, kuma duk macen da ta rik'e namiji uba, to tabbas za ta mutu marainiya, gashi na ga zahiri."


Ganin yanda take kallon shi ya san ba ta ganin shi da kyau saboda lalurar ta, dan haka ya d'auki glishin da ke gefe ya fara k'ok'arin saka mata, buge hannun shi ta yi ta zauna kan kujera ta na fad'in "Rabu da ni, macuci kawai."


Da tsantsar mamaki ya kalle ta har ya zauna kusa da ita, ba tare da ya daina kallon ta ba yace "Dan Allah Momyn Bilal ki daina kukan nan, kinfi kowa sanin matsalar ki, dama ya lafiyar idon ki, bare kuma ki na irin wannan kukan, ki daina dan Allah, kinsan kukan ki ya na matuk'ar tab'a zuciya ta, wallahi ba na son ganin zubar hawayen ki ko da na farin ciki ne, da kinsan irin rad'ad'in da na ke jin a game da zubar hawayen nan na ki, to hak'ik'a da kin tausaya min kin share hawayen ki, sannan ki saurari mijin ki."


Cikin share hawaye tace "Ai da kan ka ka je ka ciro min tikitin (ticket) kuka, sannan da hannun ka kama nawa hannun ka d'ora ni a motar tashin hankali, *Usman* wallahi ban yi tsammanin haka daga gare ka ba, ama shine har ka ke wani cewa wai na daina kuka, humm."


Jingina bayan shi ya yi ga makekiyar kujerar cikr da nuna damuwa yace "Assha, ban zaci haka daga gare ki ba, gaba d'aya na ji na rasa k'arfin gwiwar da na shigo da shi gidan nan, gaba d'aya na ji na tsani kai na, na ji ina ma mutuwa ta d'auke ni kafin wannan ranar, ni *Usman*, ni ne yau na yi silar zubar hawayen mata ta, abar alfahari na, farin ciki na, kwanciyar hankali da nutsuwa ta, kuma uwar d'ana mafi soyuwa a zuciya ta, tabbas yau d'in nan na ji kamar rayuwa ta ba ta da anfani, macen da na ke matuk'ar so fiye da komai, wai yau ita ce ta ke kira na da macuci, macen da na ke d'aukar farin cikin ta da mahimmanci, yau ita ce ta ke kira na da azzalumi, macen da bayan mahaifiya ta, ita kad'ai ce na fi d'auka da mahimmanci, amma ita ce ta ke kira na da mayaudari, macen da na ke d'aukar addu'ar ta gare ni tamkar addu'ar mahaifiya ta, amma ita ce ke cewa na yankar mata tikitin kuka, matar da na ke da yak'inin rayuwa ta ba za ta tab'a moruwa ba idan babu ita a tare da ni, ita ce ke k'ok'arin ruguza farin cikin gida na."


D'agowa ya yi daga jinginar ya na kallon ta yace " *Nana Khadija* ta da na sani, ta na da hak'uri, ta na yakana, ta na da fahimta, sannan ta na da uzuri wa mutane, haka ma ta na son duk abin da na ke so, da zan ce wannan abun bak'i ne alhalin fari ne, to ba musu Khadija za tace tabbas bak'i ne, ko da kuwa za'a yanka ta ba za ta sauya maganar ta ba, dan haka ni ba zan bar wannan hawayen na ki su ci gaba da zuba ba, ni mai son ki ne har kullum, k'auna kuma ba k'arya ba  ce, dan haka Nana Khadija ta na fara *auren nan*, in dai har auren da zan yi shine silar fara shiga damuwar ki, to na fasa har abada."


Tun da ya fara magana ta ji jikin ta ya yi sanyi, maganganun shi sun tab'a zuciyar ta sosai, amma sai ta kasa kallon shi saboda kunyar da ta rufe ta, a hankali ya dafa kafad'ar ta ya kwantar da ita a kan k'irjin shi ya na ci gaba da shafa ta ya na fad'in "Abu d'aya da banji dad'in shi ba, shine rashin samun yardar ki, na yi mamaki da takaici da ki ka kasa fahimta ta, ban ji dad'in yanda ki ka rufe idon ki ba ki ka k'i saurara ta, na so ace kinfi kowa sanin mijin ki, na so ace kin fahimci zan k'ara aure ne ba dan na gaji da ke ba ko dan na wulak'anta ki ba, kamar yanda na sha fad'a mi ki kuma yanzu ma zan sake jaddada mi ki, Khadija ba na da burin had'a ki da wata mace a duniyar nan, kin gama min komai a rayuwa ta, kin mayar da ni cikakken namiji, kin bani farin cikin da duk na ke buk'ata, hankali na ya na kwanciya idan har ina tare da ke, idan har ki ka ga na yi aure to Allah ne ya tsare haka, kuma kinsan duka abin da Allah ya hukunta babu mahalukin da ya isa ya tsallake shi ko ya canza shi, amma tun da na ga kin kasa fahimtar hakan, maganar aure na rushe ta saboda farin cikinki, dan dama ba wai zanyi bane dan ina son haka d'ari bisa d'ari, zanyi ne saboda sunna ne, kuma ina sha'awar samun ladar da ake samu ta ciyarwa."



_Me ku ka ce masoya, ta yi farin ciki? Ko kuma ta hak'uri ayi kawai?._



*Sai mun had'u a shafi na gaba.*

26/12/2019 à 11:32 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *2*




D'agowa ta yi daga jikin shi ta na kallon shi a dishi-dishi, karb'ar gilashin ta ta yi da har yanzu ya ke hannun shi ta mak'ala a idon ta, tarau ta gan shi ta ciki dan haka ta kamo hannun shi ta na murzawa tace "Ka sa na ji kunyar kai na, Abban Bilal na hak'ura, ba zan so ka fasa aure ba a kai na, idan na yi haka na zama azzaluma kuma mai son kan ta dayawa, sannan fasa auren na ka zai iya janyo matsaloli da dama, daga ciki kuwa har da dangin ka, dan za su zarge ni, ni kuma ba zan so haka ba, dan haka na amince ka k'ara aure, na san ba za ka wulak'anta ni ba, duk da dai ina d'an jin tsoron yan matan yanzu, amma ina fatan ka mana zab'i na gari, ba zab'en tumun dare ba."


Murmushin gefen labb'a ya yi yace "Na riga da na yanke hukunci, na san kin amince ne saboda kawai ki faranta min rai, ni kuma ba na son tursasaki a kan abin da ba kya so, dan haka ya wuce kawai."


Da sauri ta gyara zama ta na fuskantar shi tace "Haba aljanna ta, ni fa na ce na amince, wallahi babu takura a ciki, wani k'aramin rashin fahimta ne, kuma sai ga shi cikin ikon Allah fasihi kuma nagartattacen miji na ya fahimtar da ni, dan haka in ba so ka ke na maka kuka ba kawai ka amince."


Yanda ta k'arashe maganar cikin shagwab'a ya birge shi, dan haka ya rumgumo ta jikin shi ya na dariya, cikin so da k'auna ya ci gaba da rarrashin ta tare da saka mata albarka, tambayar ta ya yi "To yanzu ina so ki fad'a min duk abin da ki ke buk'ata, ni kuma insha Allah zanyi mi ki shi a matsayin tukuici da kuma fad'an kishiya."


Kasancewar ta mace mai yawan shagwab'a da son jiki ya sa ta turo baki gaba ta kwanta a kafad'ar shi tace "Kaji ka da wata magana, ai ni yanzu ba kai ne za ka min hidima ba, ni ce ma zan bayar da tawa gudunmuwar."


"Ban yarda ba, sai kin fad'a, in ba haka ba kuma zan kama ki ne."


Yanda ya yi maganar cikin sigar rausaya ya sa ta tashi ta nufi d'akin ta ta na fad'in "Na k'i wayon, ka kamani d'in."


Ya na jin haka ya tashi da gudu ya nufe ta, ita ma a guje ta k'arasa shiga d'akin, kasancewar Bilal na wajen kakannin shi (iyayen Khadija) ya sa su ka saki jiki sosai su ka more rayuwar su, dan dama kusan kullum haka su ke.


*Washe gari* kamar kullum misalin *09:30* su ka gama shirin fita, har farfajiyar gida su ka isa tare, ita ma kuma cikin shirin fita ta ke, sai da ya shafi lallausan kumatun ta tare da sumbatar ta kafin yace "Ni zan wuce, ki kula min da kan ki, sannan ki gaishe min da su Mama, tun da ba za ki bani damar da zan kai ki da kai na ba bare na gaishe su."


Masha Allah, duk da cikin gilashi ne ta waina idon ta, amma bai hana su d'aukar hankalin Usman ba, saboda girman idon da kuma farin su tamkar madara, cikin wasa da idon ta ne tace "Na shiga uku, da alama sai an shekara d'ari ka na min gorin wannan maganar."


"Ai dole ne, dan na lura kamar ba kya so na je na kwaso albarka wajen Mama, sannan na sake mata godiya da ta bani ke."


"Gashi kuma ba kya gajiya da godiya kullum."


"Ni kam ina zan gaji da godiya, duk wanda ya baka yar sa ka aura ai ya gama ma ka komai, bare kuma mata irin ki Khadija, ai har duniya ta nad'e ba zan daina mu su godiya ba wallahi, dan na san sun fini sanin ki, amma kuma hakan bai hana su ka rabu da ke ba su ka bani ke, duk da kuwa sun san ba zan tab'a rabuwa da ke ba in ba mutuwa ce ta raba mu ba."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "Idan har na biye ma ka, to hak'ik'a zan tabbata anan ban tafi in da zan je ba, dan haka sai an jima, nima ka gaishe min da Mama na da Abba na, tun da ka k'i bani damar bin ka bare na gaishe su."


Ta na fad'a ta juya ta na dariya shi kuma ya na fad'in "Au! Ramawa ki ka yi? Shikenan ai zan kama ki."


Gwalo ta masa tace "Ka kamani d'in, kafin nan na san in da na kai."


Wata tsandareriyar mota ta shiga bla (bleue) shi ma haka, sai dai ta shi bak'a ce, kowa hanyar da za ta sada shi da na shi iyayen ya nufa, dan su dama a *zarya* su ke, bayan masallacin *sahaba*, Khadija gaba ta yi saboda gidan su na gaban sabon gidan mota na  *Rimbo*, shi kuma Usman gidan iyayen shi ya na nan *sabon gari* a 'yan *banana* (🤸‍♂aradu unguwar mu).



Ko da ya isa mahaifiyar shi kad'ai ya samu a gidan, dan haka su na gaisawa ya d'auko maganar auren shi, tambayar da ta fara mi shi ita ce "Khadija ta sani?"


"Eh Mama, ta sani, kuma ta bada goyon bayan ta d'ari bisa d'ari, yanzu amincewar ku na ke buk'ata."


Cike da kamala tsohuwar tace "Ba ka da matsala da amincewar mu *Fodio* (sunan mahaifin ta ne, dan haka ta ke ma sa inkiya da Fodio), tun da dai har ka shirya, kuma ka na ganin ba wata matsala, sannan matar ka ma ta amince ba tare da tashin hankali ba, ai ka ga Alhamdulillah, sai dai kawai mu bika da addu'a da kuma fatan alkairi."


"Nagode sosai Mama, Allah ya k'ara lafiya da girma, yanzu kenan idan Abba ya shigo za ku iya magana da su, duk yanda ku ka yi zuwa dare idan na dawo na ji insha Allah."


Kasantuwar shi d'an fari ya sa ko ido ba ta son had'awa da shi kamar ta na jin kunyar shi, ba tare da ta kalle shi ba tace "Shikenan ba damuwa, insha Allah zan fad'a ma sa."


D'an gyara zama ya yi alamar zai tashi yace "Mama babu wata matsala ko wani abun da ku ke buk'ata?"


"Ah, Fodio kai ne za ka bar gidan nan da wata matsala? Ai sai dai in ba ka raye, Alhamdulillah wallahi babu komai, Allah dai ya yi albarka, Allah ya sa ka gama da duniya lafiya."


Sai da ya durk'usa k'asa ya amsa da "Ameen Ameen Mama, nagode sosai da addu'ar ki gare ni, ni zan wuce sai anjima idan na dawo."


"To Allah ya yarda, Allah ya tsare, ka gaishe min da waccen mutumin."


Dariya ya yi yace "Watak'ila fa gobe ku gan shi gidan nan, dan mahaifiyar shi ta tafi d'auko shi."


Cikin wasa irin ta kaka da jika tace "Ka ce mi shi ma kar ya kuskura ya zo in har ya san ba zai taho da k'atuwar bak'ar leda ba."


"Zai zo da ita Mama, ai kin san shi da k'ok'arin cefanai."


"Ko dai k'ok'arin jefawa a ciki ba."


Da wannan wasan ya bar gidan zuciyar shi sakayau da ita kamar kullum, dan har abada babu abin da ke dagula mi shi lissafi, b'angaren mace, Allah ya wadata shi da mata kamar Khadija, babu abin da ya nema a gurin ta ya rasa, haka ma iyaye, Allah ya bashi iyayen da su ke son abin da ya ke so, sannan su ke nusar da shi tare da kora shi da addu'a a kullum, hakan na sa shi farin ciki , kuma shima ya na k'ok'ari sosai wajen sauke hakk'ok'in duka b'angarorin, haka ne m'a sanadiyar da ta sa kullum ci gaba ya ke gani babu komawa baya ko rashin nasara, dan Allah ba ya kunyatar ko tab'ar da wanda ya kiyaye hakk'ok'in wannan mutanen a duniya.


Khadija ma a gidan su farin ciki ta ke kamar ba ta farin ciki a gidan ta, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon samun kan ta da ta yi a tsakiyar mahaifiyar ta da kuma d'an ta, sai sauran matan yayyun ta da kuma 'ya'yan su, bayan sun ci abincin rana yan uwan ta maza su uku su ka shigo gidan, anan ta tara su kuma ta fad'a mu su auren da mijin ta zaiyi, ta gaggauta fad'a mu su hakane saboda ta san sune za su iya bata shawara mai kyau wacce ta dace, kuma kamar yanda ta yi tsammani hakane ya faru, sosai su ka kwantar mata da hankali tare ja mata kunne da nasihohi ma su shiga rai, tare da kafa mata misali da matar babban yayan ta wanda da zai k'ara aure ta tashi hankalin kowa, a k'arshe dai sai da ta bar gidan, yanzu gashi nan sai amaryar ke rayuwar ta a b'angaren na su, abin da ba ta son ganin shi ke faruwa a bayan idon ta kuma ba yanda za ta yi, ga yayan ta ma su na hannun uban su sai yaga dama ya ke barin su su je wajen uwar, saboda hure mu su kunne da ta ke, hakan ya k'ara saka jikin Khadija yin sanyi, kuma ta yi niyyar yin aiki da shawarwarin da su ka bata, a haka ita ma ta yi yammacin ta tare da maman ta abar k'aunar ta, zuwa *5:30* na yamma kuma Bilal ya d'auki kayan shi su ka wuce tare da maman shi a motar ta.


Su na isa gida Bilal ya wuce da yan kayan shi d'akin shi tare da canza na jikin shi, ita ma kaya ta sauya ta wuce madafa dan sarrafa abin da za su ci da dare, tare da Bilal su ka shiga ya na kama mata duk aikin da ta ke yi, sai da aka gama sallah magrib ta gama lokacin Bilal ya wuce masallacin da ke had'e da gidan su, ta na gama ajewa a mazaunin cin abinci ta yi wanka ta shirya cikin riga da zane wanda su ka d'auke jikin ta sosai, kasancewar babu wata tazara mai tsayi tsakanin sallah magrib da isha'i ya sa ta yi sallahn ta, ta na kammalawa ta fito falon ya yi daidai da shigowar Bilal daga masallaci tare da baban shi.


Ta na ganin shi ta tashi tsaye ta turo baki tace "Sai yanzu za ka dawo min gida? Ina ka shige haka?"


Kallon Bilal ya yi yace "Yau salon gaisuwar maman ka kenan? To ka fad'a mata ba zan amsa ba."


Ita ma Bilal ta kalla tace "To ka fad'awa Abban ka ya juya ya koma in da ya fito, dan ba ya da muhalli a gidan nan yau."


Dariya ya yi ya kalli Bilal yace "Ka tambayar min ita kaji, wai dama ana korar mutum da gidan sa?"


Da shu'umin murmushi a fuskar ta tace "Ka fad'a ma sa sau nawa aka yi, idan kuma bai tab'a gani ba to yau zai faru a kan shi."


Bilal da ya saki baki ya na kallon su dukan su ne ya matso kusan maman shi ya rik'e hannun ta yace "Momy dan Allah ni dai muje ki zuba min abinci na ci yunwa na ke ji."


Dafa kanshi ta yi tace "Muje ka ji yaro na, kai da gidan ku."


Sun juya za su wuce ta ji ya rik'o hannun ta, juyowa ta yi su ka kalli juna, murmushi ta masa tace "Ina so na rumgume ka, zuciya ta bugawa ta ke da k'arfi."


Jan hannun ta ya yi su ka nufi d'akin shi, Bilal na ganin haka ya k'arasa shi kad'ai ya zuba abincin ya fara ci, dan ba zai iya jiran su ba, su na shiga d'aki su ka k'wak'wume juna kamar sun shekara ba su had'u ba, sumbatar ta ya ke tare da fad'in "Na yi kewar ki sosai, wuni d'aya ba mu had'u ba alhalin ina cikin garin nan, gaskiya ba zan k'ara nesanta kai na da ke ba."


Da k'yar dai su ka rabu ta taimaka mi shi ta cire ma sa kayan ta mi shi wanka kafin su ka fito, zaune ya yi ta zuba mu su abinci a faranti d'aya, amma saboda sabo har Bilal sai da ya sa hannu a na su abincin ya sake ci, cikin farin ciki da k'aunar juna su ka kammala, Bilal ya wuce d'akin shi ya na kallo, su kuma su na nan falo.



*Wannan ita ce rayuwar farin cikin da su ke ciki.*


Bayan mahaifin Usman ya zo mahaifiyar shi ta fad'a mi shi komai, kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "Masha Allah, wannan ai abun farin ciki ne, dan girma ne zai k'aru, fatan alkairi kawai za mu ma sa, zuwa safe kuma idan ya zo sai muji yanda za ayi."



*Allah ka bani lafiya mai anfani.*

27/12/2019 à 20:31 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *3*





Kasancewar maza ne su ka shiga al'amarin, sai akayi komai cikin sauk'i da sauri aka gama, kuma cikin k'ank'anin lokaci aka saka *wata biyu* mai zuwa, dan haka kowane b'angare ya fara shirye shiryen da su ka dace da shi a bikin, amma b'angaren Khadija hankalin ta kwance ya ke,  dan dama tun farko mace ce mai kama jikin ta da tsare gida, hakan ne ya sa ba ta buk'atar d'aga hankalin ta wajen gyaran jikin ta ko wata kwaskwarima, kayan d'aki ne kawai ta ke buk'atar canzawa, shi ma kuma a nutse ta ke so ta yi komai, tunda kud'i ba su ne matsalar ba.


Wajen amarya ma yan uwan ta ne ke tsaye kan kula da gyaran jikin ta, dan mahaifiyar ta dattijuwa ce kuma babu ruwan ta, ita ma kuma ba zaune ta ke ba ta na d'an k'ok'arin ta wajen ganin ta gyara kan ta da kan ta.



*Duk* abin da aka sa ka ma rana to k'ararre ne, sai gashi kamar k'yabtawar ido har an ciye *wata d'aya* da sati d'aya, hakan ne ya sa biki  ya rage saura sati uku, kuma har yanzu uwar gida ba ta tab'a ganin amarya ba, amarya kuma ta ga uwar gida amma a hoto ba'a zahiri ba, shirye shirye ya kankama sosai, sai dai kuma Khadija ta d'an fuskanci wani k'alubale a wajen dangin mijin ta, kasantuwar ta mace mai fara'a da kyauta da kirki ya sa yan uwan ta da yan uwan Usman su ke son yawan kawo mata ziyara, amma tun da aka saka ranar auren shi har yanzu ba ta ga k'eyar kowa ba, ba ma kamar k'anwar shi *Aziza* wacce har kwana ta ke a gidan.


Yau dai sunyi sallama da Usman za ta je wajen bikin k'awar ta *Halisa* da ta haihu, kuma tace za ta fara biyawa ta gidan su ta gaishe da mama, tsaf ta shirya cikin kayan da ta fi son sakawa, leshi (less) ne aka gwangwaza mata d'inki mai kyau riga da siket, sai takalmanta ma su tsini da mayafin da ya dace da kayan, ta na shigar motar ta ba ta zame ko ina ba sai gidan su Usman, cikin sa'a sai ta samu k'anwar Usman d'in da ke bi mi shi wacce da Usman ya had'awa Khadija kayan fad'ar kishiyar ta ya kai mata yace ta kai wa Khadija, ba dan ba zai iya  ba sai dan ya na so ya bata mamaki, ita kuma ganin kayan sunyi yawa ya sa ta taho da su nan d'in dan ta nunawa mahaifiyar su. 


Da isar Khadija a soro taja birki ta tsaya saboda jin muryar aunty *Hassana* na fad'in "To domin Allah Hajia yanzu wannan kayan da mata ne za ki ce ba su yi yawa ba? Ko fa lefen amarya da aka kai wallahi bai kai wannan kayan ba, haba dai, kayan fad'ar kishiya har akwati goma, kuma kowace cike da kaya, gaskiya ni ba zan kai su haka ba."


Tshohuwar ce tace "To ya za ki yi da su? Ragewa za ki yi? Ko kuma me za ki yi?"


Ai kuwa sai muryar Aziza a kunnen Khadija ta na fad'in "To dama ina zai had'a lefen ta dana amarya, kin manta ta gabar goshin ce? Ai ina tabbatar mi ki a yanda na san yah Usee (sunan da su ke kiran shi da shi kenan) ya na tsoron matar nan, wallahi da za ta ce ya fasa auren nan, to ko musu babu zai fasa shi."


Tsaki tsohuwar ta yi tace "Kullum ina fad'a mu ku ku dinga kyautatawa mutum zato, abin da ba ku da hujja da yak'ini a kan shi, amma ku na hukunta yarinya da shi, wannan fa bai dace ba."


Hassana ce tace "Hajia ba kya son laifin Khadija ne kawai, amma duk wanda ya san rayuwar su wallahi ya san da magana a k'asa."


Aziza ce tace "Ku ai duk labari ne ku ke ji, ni da na mayar da gidan fa kamar gidan mu, kar ki so ki ga wani abun haushin idan ya na yi wallahi, su kad'ai a cikin gida sai shegen yaron nan da ba komai ya ke ci ba sai abin da ya ga d..."


Ba ta k'arasa ba tsohuwar nan ta kwashe ta da mari, hararan ta ta yi tace "Dan rashin mutumci d'an yayan na ki za ki sheganta? Kuma a gaba na, dama gulma da d'aukar rahoto ne ke kai ki gidan na su? To kinyi na k'arshe, mutuniyar banza kawai."


Tashi tsaye ta kalli Hassana tace "Ke kuma ki tabbatar kin kai wannan kayan in da aka aike ki da su." shigewa ta yi d'aki ta barsu nan, Khadija kam k'walla ne su ka cika idon ta, juyawa kawai ta yi ta fita ta d'auki hanyar ta zuwa in da za ta je, Hassana kuma tattara kayan ta yi ta rufe akwatinan kafin ta samu yaro aka mayar da su a motar da ta kawo su, Aziza kuma ta ci gaba  da kumburar baki.



Ko da Hassana ta je gidan babu kowa, dan haka ma ta kira Usman d'in dan ta fad'a mi shi, a cewar zai aiko da yaro da makullin falon Khadija ta bud'e ta saka kayan, bayan nan kuma sai da ya mata fad'a wai ba ta kawo a kan lokaci ba har ta fita, hakan ya sake tunzurata ita ma, dan ganin ta ke kawai ba ya k'aunar b'acin ran matar shi bai kuma damu da b'acin ran su ba, haka ta jira yaron shi ya zo ya kawo mata aka bud'e aka jera akwati nan kafin ta bar gidan.



⏩⏩⏩⏩⏩⏩



*Yamma* ta yi sosai *Hassenah* ta kammala girkin ta ta na jiran isowar yayar ta, kallon maman ta ta yi cikin b'acin rai tace "Wallahi aunty *Mariya* ta cika b'ata lokaci, sai da na fad'a mata akwai in da zanje ta yi sauri fa."


Dattijuwar da ke cike da kamala da sanyin jiki wanda da alama hallitar ta ce haka tace "Watak'ila wani abun ne mai mahimmanci ya tsayar da ita, amma ki k'ara hak'uri."


Tsaki Haseenah taja cikin b'acin rai, amma ba ta dire tsakin har k'arshe ba Mariya ta shigo a hargitse da sallama, mahaifiyar kad'ai ta amsa sai kafeta da ido da Haseenah ta yi, ita kam goyon da ke bayan ta ta kwance ta aje kan tabarmar da ke shinfid'e ta na gaishe da maman na su, cikin rashin kunya Haseenah tace "Dan Allah aunty Mariya me ye haka? Na fad'a mi ki fa za mu fita tare da su *Zeinab*, amma shine ki ka b'ata mana lokaci haka."


Cikin d'aga murya tace "Ke dallah can, ke in da kinsan me ya tsaidani ma ko magana kya yi."


"To me ya tsaida ke d'in?"


Sai da ta aje jakar ta da bak'ar ledar hannun ta ta gyara zama da kyau tace "Kishiyar ki na had'u da ita wajen bikin."


Cikin harara ta kalle ta tace "Ke aunty Mariya, ke kuma ina ki ka san kishiya ta da har ki ka gan ta wajen biki? Ko ni fa ban tab'a ganin ta a zahiri ba, bare kuma ke."


Tsaki Mariya ta yi tace "Aikin banza, to tunda na ce mi ki na ganta ba sai ki tambaye ni ya akayi mu ka had'u ba."


"To na ji, ya akayi ku ka had'u."



*Tofa, kinga irin wannan sune yan haddasa bala'i.*

29/12/2019 à 13:46 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



💃💃💃💃💃💃💃💃



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *4*



Saida ta kalli maman su wacce ta ke da yak'inin za ta tsawatar mu su kafin tace "Kawai dai a gurin bikin mu ka had'u, kuma masha Allah wallahi ba ki ganta ba, kyakyawa da ita, musamman gilashin idon ta ya k'ara mata masifar kyau, gaskiya ta birgeni sosai saboda da ganin ta akwai fara'a da kuma kama jiki."


Wani bak'in ciki ne ya tokare Haseenah a wuya, amma sai ta dake tace "Ni dai yanzu ki ban abin da ki ka rage wajen siyayyar."


Hannu tasa a jaka da nufin fito da kud'in, hakan kuma ya yi daidai da tashin maman su ta shiga cikin d'aki, dan haka Mariya ta gyara zama murya k'asa k'asa tace "Haseenah kinsan wacece kishiyar ki kuwa?"


Cikin yamutse fuska tace "Ni kuma ina zan sani."


Gyara zama ta sake yi tace "Hum! Haseenah, wallahi sai kin tashi tsaye tsayin daka, dan kishiyar ki ba ta wasa ba ce, wai kinsan su wanene k'awayen ta?"


Cike da jin haushi tace "To wai ni dan Allah ina zan sani, haba, ki yi magana yin za ki yi kawai."


Sai da ta bubbuga k'afar ta tace "Khadija kishiyar ki, su *Hajia Turai Dubai* da *Hajia Salamatou k'urori* da *Barira nagoma*  da *Hajia Natali*, sune manyan k'awayen ta, shin kinsan ma wacece aminiyar ta?"


"Sai kin fad'a." Cewar Haseenah.


Sai da ta sauke numfashi tace " *Hajia Kaltume*, Kaltume mai kayan dad'i."


D'orawa ta yi da " Haseenah, wallahi sai kin tashi tsaye, kinga matan nan da na lissafa mi ki, gogagggun wayayyu ne, manyan mata ne ma su ji da kan su, duk kishiyoyin matan nan in fad'a mi ki ba su da daraja a wajen majazensu, kinga Kaltume mai maganin mata, to in fad'a mi ki in ba ki cika cikakkiyar mace ba ma ba ki siyan maganin ta, dan k'aramin magani a wajen Kaltume shine na *jikka hamsin* (jaka hamsin), duk wata mace da ta k'oshi kuma ta ke mulki a gidan mijin ta to Kaltume ce sirrin farin cikin ta, dan wani shegen gyaran jikin idan ta mi ki shi, to wallahi tun a daren farkon ki kin gama da mijin ki kenan, duk wata mace da za ta raba ki da shi, to sai dai fa in ta sihiri ne, amma d'and'anon ku ba ya tab'a zama d'aya a wajen shi."


Gaba d'aya jikin Haseenah ne ya yi sanyi da jin wannan al'amari, ganin haka ya sa Mariya cewa "Akwai mafita d'aya da ta rage mi ki."


"Wace iri?" Cewar Haseenah da saurin ta, d'orawa ta yi da "Nasan kishiyar ki a tsume take da had'in Kaltume, kuma tunda ita ce aminiyar ta kinga kenan ba za ki tab'a cin mata ba , amma abu d'aya shine, kema ki samo kud'ad'e a hannun Usee, sai kawai muje mu ga Kaltumen, sannan akwai wata ma da ke kawo min kayan mata, ita ma sai ta had'a mana da nata, koya ki ka gani?"


"Hakan ma ya yi, kuma kinga dama shi mutum ne mai kyauta, ba sai ka tambaye shi ba ya ke yi."


"Dan haka sai ki samo mana kud'i a hannun shi, amma fa duk da haka sai mun d'an k'ara da malamai, ko ba komai su tayaki da addu'a dan ki samu bakali a wajen shi."


Tashi ta yi tsaye tace "Shikenan aunty Mariya, yanzu wannan kud'in ma ki rik'e a fara wani abun da su, yau ko gobe zan sa ya zo sai na samu kud'in, amma kar ki bari mama ta ji, kinsan halin ta yanzu sai tace ba ta yarda ba."


"Ni? Ina zan fad'a mata, ba ki ga sai da ta tashi ba ma na fad'a mi ki."


"To ni zan tafi su Zeinab na jira na."


"Sai kun dawo." Ta fad'a ta na bin ta da kallo.



*Allah ya fidda _Delu_😂 daga rogo.*



⏩⏩⏩⏩⏩⏩



Khadija kam a wajen bikin suna can har yamma, sai da su ka gama zubin da suke na k'awaye kafin su ka fito tare da Kaltume, motar ta su ka shiga ta bata wasu harkokin, kamar yanda ta san Khadija farin sani, ba ta anfani da kowane irin garin magani, musamman wanda za ace ayi matsi da shi, ta na sallamar ta ta fita daga motar ta rufe tace "Sai kin zo k'awata."


Kaltume  ce tace "A'a k'awata, gaskiya ba na so na zo gidan ki yanzu, na fi so sai an fara shagulgulan bikin nan, lokacin na k'ara had'o mi ki wasu kayan."


Dariya Khadija ta yi tace "Ke fa muguwa ce, wato kullum burin ki kiga bawan Allah nan ya na gasa min aya a hannu ko? To daga wannan da na karb'a sai amarya ta zo ta haihu, idan za ta yi arba'in sai mu shirya tare."


Cikin d'aga murya Kaltume tace "Ina, ana babbak'ar gwiwa wa ke jiyo k'aurin zomo, ai dole yarinya ta gane da banbanci wallahi, wanda ya sa ta shigo gidan Khadija ta Usee, shi zai sa ta gane Khadija ta mata nisa na har abada."


Cikin dariya Khadija tace "Dan Allah k'awata ki ragawa yarinyar nan, har yanzu fa ba mu san ta ba bare mu san da me za ta shigo gidan ita ma."


Cike da gadara da tabbatarwa tace "Ai ko ni Kaltume za ta d'aura a k'ugun ta taje dani gidan, wallahi na riga da na bawa Khadija sirrin da za ta mata rata mai tsayin gaske."


"Na yarda, yanzu dai sai anjima, sai munyi waya ko?"


"To ba damuwa k'awata, ina k'ara fad'a mi ki dai, dan Allah banda nuna kishi a fili, ayi komai cikin kissa k'awata, ban da matsala da ke ta wannan fannin , amma kishi masifa ne wallahi."


"Hakane k'awata, kuma insha Allah zan kiyaye, nagode sosai."


"To, ki kula da kan ki."


"Kema haka."


Da haka ita ma ta shiga ta ta motar ta bar wajen, Khadija kuma ta na zuwa gida ta samu wannan kayan arzik'i, gidan su ta kira ta fad'a mu su, zuwa bayan sallah magrib kam sai ga maman ta da matan yayyun ta sun zo ganin kayan, hotunan su ta d'auka ta turawa k'awayen ta dan su gani suma ba sai sun zo ba, anan ne ma har su ka yi magana da maman ta a kan kayan d'aki da za ta canza, mahaifiyar da kan ta ta d'auki alhakin yi mata odar su daga k'asar waje, dan itama ta na so ta kece raini.


Sun fito dan tafiya Usmane ya shigo gidan, da gudu Bilal ya k'arasa ya rumgume shi, har k'asa ya duk'a ya gaishe da mama, mama ce tace "Kai yanzu da girman ka har ka ke wani mak'ale shi kamar yaro."


Hararan wasa Bilal ya aika mata yace "Kaji tsohuwar nan, ke ma fa idan na je gidan ki har d'auka ta ki ke."


Dafe k'irji ta yi tace "Kaji min sarkin sharri, ni kuma ina zan iya d'aukar ka? Ka fad'i abin da hankali zai d'auka mana."


"To ai dai Abba na ne ko." Ya fad'a ya na k'ara sarkafe wuyan Usman da har yanzu ke durk'ushe, ita ma kuma cewa ta yi "Ni ma kuma d'ana ne ba, kaga kuwa ba zan bari nima ka karya min yaro ba."


A hankali Usman ya kalli Bilal ya d'an janye shi daga jikin shi yace "Mama ta fika gaskiya, kowace uwa d'an ta ta sani, dan haka kowa ya je wajen maman sa, kai ma jeka ga ta ka can."


Kallon shi Bilal ya yi yace "Lallai ma Abba, za ka nemi ne ai har in da na ke, kafi kowa sanin cewa ni ne bugun zuciyar ka."


Wajen Khadija ya nufa ta d'auke shi saboda k'arfin hali duk da girman shi, mama kuma kallon Usman ta yi ta k'ara da "Mun ga kaya fa, a gaskiya sunyi sosai, sai dai kuma kayan kamar sunyi yawa, Allah ya k'ara bud'i na alkairi."


Ba tare da ya d'ago ba yace "Ameen ameen Hajia, ai ni ne da godiya, Allah ya saka da alkairi, Allah ya k'ara girma da lafiya."


"Ameen ameen." Mama ta amsa kafin Khadija ta d'ora da "Tofa, yanzu za ka fara godiyar ko?"


D'ago kai ya yi ya kalle ta yace "Ke kuma ba kya so ina godiyar ko?"


Hannaye ta d'aga tace "Allah ba ka hak'uri, ga ka ga su."


Mama kam wucewa su ka yi suna fad'in "Sai da safen ku."


Bilal da ke bayan Khadija ne ya d'aga musu hannu yace "Sauka lafiya, ko k'ofa ba zan raka ki ba bare ki sa ran samun na adaidaita."


Usman ne ya juyo ya kalle shi yace "Haihuwa maganin takaicin duniya, sai da ta haife ni kafin kai ma ka zo, dan haka da kai na zanyi dakon mahaifiyar ta har makwancin ta."


Dariya kawai su ke har su ka isa k'ofar gidan, cikin shagwab'a Khadija tace "Amma fa kar ku jima, ku yi sauri ku dawo."


Kafad'a ya mak'ale yace "Na k'i d'in."


Hararan shi ta yi tace "Za ka dawo ai ka same ni, zan kama ka a hannu."


Ba tare da ya bari mama ta gani ba ya mata gwalo yace "Ki kama ni d'in, ba zan shigo ba sai kinyi bacci."


"Bayan na rufe gida na ba." Ta fad'a kamar mai son tabbatar masa da za ta iya, haka dai ya d'auke su su ka wuce, mama ta so ya yi zaman shi su k'arasa titi su hau adaidaita, dan dama ko da *Naseer* ya kawo su sun fad'a mi shi za su koma da kansu, amma bai bari ba sai da ya kai su har k'ofar gida ya dire su, nan ma sai da ya fito daga motar ya sake mu su sallama kafin ya yi gaba, ya na kan hanyar shi kuma kiran amarya Haseenah ya shigo wayar shi, kashe kiran ya yi sannan ya sake kira da kan shi, ta na d'auka cikin ladabi tace "Amincin Allah ya tabbata a gare ka adali na."


Cikin jin dad'i yace "Kema haka, ya amarya ta take?"


Cikin siririyar murya tace "Da dad'i ba dad'i, amma daga yanda na ji karsashin muryar ka sai ya sa na ji wata tabbatacciyar lafiya na shiga jiki na."


Murmushin jin dad'i ya yi yace "Allah na gode ma ka da ka sa Haseenah za ta zama tawa, kalaman ki su na fasa min kai na, shi ya sa ba na gajiya da sauraron ki, yanzu fad'a min, ko zan iya sanin in da amarya ta take? Dan ina jin hayaniyar ababen hawa a in da ki ke."


"Wallahi Abban Bilal mu na wajen mai d'inki ne, amma yanzu za mu koma gida."


"To in dai hakane ki ce kawai na zo na mayar da ku gida?"


"A'a, ba na so na shiga lokacin aunty na gaskiya, kawai ka bar shi zamu koma da kan mu."


Dariya ya yi yace "Allah sarki Haseenah baiwar Allah, a gaskiya ki na birge ni sosai ta yanda ba kya so a takura yer uwar ki, amma duk da haka ki bari zan zo na kai ku gida, dan dama ban shiga gida ba."


Cikin murmushi tace "Yanda ka ce haka za ayi ranka shi dad'e."


"Ina nan k'arasowa nan da d'an lokaci da zaran kin fad'a min in da ku ke."


Tsaf ta kwatanta mi shi in da su ke, sai da ya wuce gidan shi kafin ya d'auki hanya zuwa in da su Haseenah su ke, hak'ik'a har zuciyar shi ya na jin dad'in mu'amula da   Haseenah, duk da ta na da k'arancin shekaru amma ta na da tunani da hankali kamar babbar mace, uwa uba girman da ta ke ba shi da kuma matar shi, hakan na faranta ran shi sosai, shi ya sa yake ji baiyi zab'en tumun dare ba, za ta girmama matar shi sannan ta darajanta yaron shi da yan uwan shi, sannan ya na ji cewar za su zauna lafiya ita da Khadija, dan dukan su babu mai matsala a cikin su, dan da matsala ke sa a k'ara aure, to da shi da k'ara aure sai dai in an had'a shi da matan aljanna, amma Khadija ta gama mi shi komai a rayuwar duniya, lokaci ne idan ya yi ba makawa sai anyi. 


*Kallon kitse ake wa rogo*


Da isar shi ya kira ta suka fito, yan mata uku ne su ka fito daga cikin shagon, kusan dukansu da ledoji a hannu, haka kuma dukan su babu mai hijab a ciki, dogayen riguna ne a jikin su sai kallabin rigar da suka yane kan su da shi, siririyar cikin su ya kafe da ido har ta bud'a gidan gaba ta shiga da murmushi a fuskar ta, sauran ma shiga su ka yi suka zauna, kallon shi ta yi tace "Sannu da zuwa adalin miji."


Da murmushi yace "Barka da fitowa adalar amarya."


Tayar da motar ya yi su ka fara tafiya...



*A samu a addu'a.*


_Duk mai son shiga grp d'ina dan samun littafi kai tsaye ya tuntub'i wannan mutanen._


*Mamienmu.*

*My Heenat.*

*My BK.*

*Ma chérie Hakeema.*

*Momyn Dady.*

30/12/2019 à 12:50 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *5*




Hira su ke ta kwasa shi da k'awayen ta, Haseenah kam dariya ce ta ta, a haka dai su ka isa k'ofar gidan su Haseenah da ke unguwar *Arène da lute*, a tare su ka fita daga motar su ka rufe a tare, sauke gilashi ya yi ya kalli k'awayen yace "To Hajia *Zeinab* saura kud'in taxi ko."


Dariya k'awar ta yi ta juya ido tace "Ina fatan ka na da canji dai?"


"Akwai canji mana, mai sana'a da mata ai baya rasa yan matsabbai."


Dariya su ka sake yi kafin ta kalli Haseenah tace "To ki biya shi, daga baya ni sai na biya ki."


Da sauri Usman yace "La la la, ke dai kawai ki ce ba ki niyyar biya na ba, dan haka na yafe kawai."


Kallon shi ta yi tace "Oho, ashe kud'i na ne za ka iya amsa."


Dariya ya yi yace "Shikenan dai magana ta wuce tunda na yafe, yanzu sai da safen ku."


"Sai da safe." Su ka fad'a su na nufa na su gidanjen da ke unguwar, kallon Haseenah ya yi yace "Ki shiga gida, ba na so k'urar nan na tab'a min ke fa, sai munyi waya."


Cike da rausaya tace "Angama ranka shi dad'e, sai munyi waya. "


Gida ta shige ita ma kafin ya wuce na shi gidan shi ma, ya na zuwa ya sa mai gadi ya rufe gidan gaba d'aya dan ya shiga kenan, tun a k'ofar falo Khadija ta tarbe shi su ka yi cikin d'aki, (to ni wanka ma tare su ka yi shi ko kuwa ita ce ta mi shi oho), amma dai a tare su ka fito kuma suka shirya, kai tsaye wajen cika ciki su ka nufa, tun da ta bud'a kwanon ta d'auki k'aramin faranti ya zura kai cikin kwanon ya na fad'in "Me aka dafa mana yau *Nana*?"


Ba tare da ta kalle shi ba tace "Kan kare."


Yamutsa fuska ya yi yace "Kuma ki na ganin zaiyi dad'i?"


Ita ma yamutsa fuska ta yi tace "Um; ba tabbas, amma ka fara d'and'ana mana tukuna."


Nuna kan shi ya yi da yatsa yace "Ni? To na k'i, ki bawa d'an ki ya fara lasawa."


Murmushi ta yi tace "Ka na so ne na rasa d'ana?"


"Oho, ni ne kenan banda mahimmanci? To nima haihuwa ta aka yi, kuma yanzu haka da iyaye na za su ji me ki ka fad'a, to da kinga yak'in duniya na uku ganin idon ki."


Tunda ya fara magana take dariya har ta gama zuba mishi ta aje farantin gaban shi, janyo kujera ta yi ta zauna daf da shi yayin da Bilal ya zauna a k'afafun Usman, dukansu hannayen su suka saka suna cin abincin, dan a d'abi'ar Usman yace Allah ya hore mu su yatsu har biyar saboda su yi anfani da su ne har wurin cin abinci ba, da hakane su ka saba da ci da hannu in ba abin da ya zama dole aci da cokali ba, su na cinyewa Khadija ta turo baki gaba tace "Duk kun fini k'atuwar loma, kuji fa kun cinye abincin kai da yaron ka."


Kallon Bilal ya yi yace "Yarima ka ji me ta ke fad'a, ka duba ka gani wa yafi k'aton ciki a duk cikin taron nan."


Tsaye Khadija ta mik'e tace "Kai ka fi mu cin mai yawa, dan haka zan k'ara kuma banda kai za mu ci."


"Tab'dijam, na kawo abincin, na sarrafa shi, na dafa shi, kuma ace ba zan ci na k'oshi ba, lallai ma yau za mu tara yan kallo a gidan nan." Ya k'arashe maganar da juya baki, hannu Khadija tasa ta d'auki kwanon miya ta na fad'in "Ai dai abinci ba zai ciyu gaya ba, ni kuma zan iya cinye naman ciki na kuma tsoma bredi a miyar."


Shi ma jan kwanon shinkafar ya yi yace "Ni ma kuma zan iya zuba man gyad'a a shinkafa ta, haka zan iya saka sardine (kinfi gwangwani)."


Bilal ne ya katse su da "Kai, Kai, wannan rigimar ta ku wata rana za ta ja min ciwon yunwa, kaga Abba kawo nan."


Karb'ar kwanon ya yi ya aje ya nufi Khadija ya karb'i kwanon miyar ya aje sannan yace "Yanzu kowa ya d'aga min rigar shi na ga tunbin shi sai na ga wanda ya fi k'oshi."


Dukan su a tare suka turo baki gaba da rumgume hannaye a k'irji, Usman kam har da k'arawa da mak'ale kafad'a yace "Um, um."


Murmushi Bilal ya yi ya rumgume kwanukan ya na fad'in "Dan haka ni kad'ai zan ci abincin nan, kuma na ga mai ja a maganar yarima."


"To shikenan, yanzu ga nawa." Cewar Khadija ta na d'aga rigar ta sama, hannu ya sa ya shafi cikin ta ya marairaice yace "Ayya! Sarauniyar uwa ta ba ta k'oshi ba har yanzu."


Kai ta girgiza ma sa kamar za ta fashe da kuka, Usman ma haka ya d'aga ya shafa cikin, shima a marairaice yace "Sarki ma bai gama k'oshi ba, to ku zo mu ci tare."


Matsowa su ka yi Usman ya kalle ta yace "Kinyi sa'a fa yarima ya ceceki, da gay kin sha miya."


"Kai ma da ka ci gayan tuwo." Ta fad'a har da masa gwalo, cewa ya yi "Amma dai na san ba ki jin ana cewa azo asha miya, sai dai ace azo aci tuwo."


Yatsa Bilal ya d'ora a labb'an shi yace "Ya isa haka to, aci abinci ba magana ba."


Shirun kam su ka yi su ka saka hannu a abincin da ya zuba su ka ci gaba da ci, daga nan kuma kallo su ka tab'a kafin su ka kwanta da fatan wayewar gari lafiya.



Tunda asuba Usman da Bilal su ka wuce masallacin da ke manne a jikin gidan, bayan sun dawo kuma kowa d'akin shi ya nufa, duk da Khadija ta ji dawowar su amma ba ta je in da Usman ya ke ba, saboda ta san abin da zaiyi yanzu ba ya son hayaniya da takura, sai da ta ga k'arfe *07:00* ta buga daidai ta tashi daga sallaya ta nufi d'akin, da sallama ta shiga ta same shi zaune a kan sallaya, d'ago kai ya yi tare da amsa sallamar ya na rufe Qur'anin hannu shi ya aje gefe, zaune ta yi k'asa kusan k'afar shi cikin ladabi tace "Antashi lafiya *babban mutum*?"


Cikin kafeta da ido yace "Lafiya lau na tashi, fatan kema haka?"


Da murmushi tace "Lafiya k'alau na ke tun da dai kun tashi lafiya."


"Masha Allah, Allah abin godiya."


Kallon shi ta yi cike da kunya tace "Zan shiga madafa ne dama, shi ya sa na ke so na ji abin da miji na ya ke sha'awar ci dan na sarrafa mi shi."


Cike da kallon bege yace "Zab'in ku shine zab'i na, za ki iya dafa abin da ran ki ya ke buk'ata."


"Ba na da wani zab'i da ya wuce na ka, duk abin da ran ka ya ke so shine nawa ya ke so."


"To in hakane sai ki tambayi yarima dan ya raba mana wannan gardamar kamar yanda ya saba."


Cikin shagwab'a tace "Shi ma kan shi yarima zab'in mu shine na shi, dan haka a matsayin ka na shugaba kuma ja gaba dan Allah ka taimaka ka zab'a mana abin da za mu ci."


Hannu ya kai ya ja dogon hancin ta ya na fad'in "Kin ganki ko mai wayo, to shikenan yanzu ki je ki samar mana ko da irin wannan wainar da ki ke had'a ta da miyar kayan ciki."


Dariya ta yi tace "Kwad'ai ko? Wato ka ji dad'in ta?"


Kamo hannun ta ya yi ya sumbata yace "Duk abin da hannun nan zai tab'a to ya kan zama mafi soyuwa a gare ni."


"Shikenan to bara na je na fara aikin, tunda har yanzu *Uwani* ba ta dawo ba bare na tsaya jan jiki."


Rik'o ta ya yi yace "Amma dai ban takura ki ba ko?"


Sai da ta waina idon ta tace "Gaskiya na d'an takura da ka k'i fad'a min abin da ka ke so tun da wuri."


Dariya ya yi ita kuma ta mik'e ta juya, tafin hannun shi ya sa ya daki mazaunan ta, da sauri ta dafe ta juyo ta na kallon shi, far-far ta masa da ido ta juya ta sake juya masa mazaunan da kyau kafin ta fice, tashi ya yi ya haura kan gado ya yi ruf cikin bargo, ita kuma aiki ta fara gadan-gadan.



          *A GURGUJE*



Lokaci ya zo na biki, ta kowane b'angare shiri ake yi, yayyun Khadija da mahaifiyar ta sun sake mata kayan d'aki na gani na fad'a, kaya ne yan uban-ubansu, hatta teburin cin abinci sai da Khadija ta cika kud'i aka bata sabo da ya dace da kayan ta, daga falon ta zuwa uwar d'akin ta idan ka shiga sai ka ji kamar ka fito da mai d'akin kai ka zauna, Usman ma kai da kawowa kawai ya ke, tun yanzu Khadija da Bilal su na ganin sauyi a tare da shi na rashin cikakken lokacin shi, amma ta had'e dan ta san na d'an lokaci insha Allah, amarya ma an shafa an goge anyi jawur, ga bala'in magunguna da take ta kaurawa kan ta, Mariya ma taje wajen malam an basu taimako wanda zai sa Usman ya so ta fiye da kowa, hakan yasa dole ta had'a garin maganin da aka bata ta kwab'a lalle da shi ta shafa a k'afar ta kamar yanda aka ce, sai kuma wanda za ta dinga zuba mi shi a abinci ya na ci, sau d'aya ta yi nasarar saka mi shi kuma ya ci lokacin da ya zo gidan su, shi ma sai da ta fara kukan kissa kad'ai ya ci, dan ya fad'a mata shi wallahi bai saba cin abinci a waje ba ko da kuwa gidan su ya je, da k'yar dai ya ci shi ya sa ma ta aje da tunani har ta shiga gidan, da haka har aka fara da shagalin kamu, washe gari kuma d'aurin aure, a ranar in banda dakan uku-uku babu abin da k'irjin Khadija ke yi, amma cikin k'arfin hali haka ta had'e kishin ta ta taimaka mi shi ya shirya cikin manyan kayan shi irin na Bilal komai da komai har takalma da hula iri d'aya suka saka, ta na kallo ya kama hannun Bilal suka fice sai k'amshi suke, su na fita ta zube kan kujera ta fashe da kuka da iya k'arfin ta dan ta rage rad'ad'i, cikin sa'a sai ga Kaltume ta zo tun da wuri, nan fa ta shiga aikin rarrashi da ba ta hak'uri tare da fad'a mata ta taushi zuciyar ta sannan ta dinga anbaton sunan ubangiji, da haka ta samu ta saisaita nutsuwar ta su ka fara hira, angama d'aurin aure kuma wasu k'awayen nata suka dinga zuwa wanda tafi kusa da su, tare suka shigo da Bilal su ka canza kaya wata shaddar iri d'aya, k'awayen Khadija kam bayan gaisuwa murna su ka taya shi tare da mi shi addu'a ta alkairi, rana ta farko a *tarihin* rayuwar su da Usman ya shiga d'aki Khadija ta kasa bin bayan shi, bayan rasa kuzari da ya yi sai ya kasa shirya kansa, domin kuwa Khadija ta saba mishi da shirya shi ko ta taimaka masa, hakan ne yasa ko mab'allin riga bai b'alla ba ya fito, kasancewar Kaltume su na wasa ta dinga masa dariya wai zumud'i yasa ya kasa b'alla mab'alli, Khadija kam da ta san komai tashi ta yi ba tare da ta yarda sun had'a ido ba ta b'alla mi shi, juyawa ta yi za ta wuce ya rik'e hannun ta sam ya manta da mutanen da ke wajen, juyowa ta yi amma ba ta kalle shi ba, dan haka yace "Sai yanzu ne na fahimci k'arfin wuta da tartsatsin da ke cikin idon ki, ki kalle ni ko sau d'aya mana, hakan ne zai sa na kasance cikin karsashi da kuzari."


Kasa tausar zuciyar ta tayi har sai da tace "...



*Allah ka nufe mu da sassauk'an kishi mai tsafta da kyawu, Allah kasa mufi k'arfin zuk'atan mu.*

01/01/2020 à 12:14 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *6*



"Hum! Ai yanzu ba ni kad'ai ba ce hakk'in saka ka farin ciki ke kai na, ka je ka samo farin cikin ka a wani wurin, ni ina da abin yi a gaba na da yafi wannan mahimmanci."


Ta na fad'a ta juya ta koma in da ta ke, sam bai ji dad'i har zuciyar shi,sai dai baiga laifin ta ba in ya yi la'akari da yanda kishi ya ke, fita ya yi shi ma zuciya ba dad'i, rana ta yi k'awayen Khadija sun zage sai girki ake ana hira, sam abin da Khadija ba ta yi tsammanin shi bane ya faru, ganin ba kowa ta gayyata ba amma sai ga mutane na ta b'ullowa daga wurare daban-daban, sai dai da gani kasan wani ya zo ya ga me zai faru ne, daga ciki kuma har da dangin Usman wanda sun san ba biki take ba, amma sai ga shi suna zuwa su na yak'e mata bakuna, ita kam da ta fisu sai ta nuna farin ciki take sosai da hakan, musamman da Aziza ta zo tare da Hassana da yan biyun ta Husseina su ma sun zo gidan, kowa da abin da ke ran shi, haka dai aka yage hak'ora kowa ya bar wajen.



A k'alla k'awayen ta kusan goma sha biyar ne su ka jira har a kawo amarya, masha Allah, ba k'aramin shiri Khadija ta yi ba, shaddar da ke jikin ta da aikin da aka ma shaddar kad'ai zai nuna maka an kashe dala sosai, dogayen takalma da kwalliyar da aka watsa mata, gilashin ta da ya k'ara mata kyau da gani, d'aurin d'an kwalin da sai kace tafiye ya ke daga k'asar waje, dare ya yi kuma an kawo amarya, tun da Khadija ta ji ayiriyiri gaban ta ya fara wani sabon dukan, haka dai aka yi duk wani abu da aka san ana yi, an kawo amarya d'akin uwar gidan an gaisa an kuma mu su nasiha, sun saka ango tsaka an sake mu su nasiha tare da hotuna, in dai har za'a fad'i gaskiya to Haseenah ba ta ko kama k'afar Khadija ba, ta kowane b'angare ma dan babu had'i tsakanin su ma, su kan su danginta da k'awayen ta sun girgiza da ganin ta a haka, sai dai kowa ya san Usman ya yi dacen mata, ganin shi d'in ba wani kyakyawa ba, shi ba hasken fata ba, haka dai aka watse aka bar su kowa ya koma d'akin shi, dan dama babban falo shine na Usman, k'ofa ya yi ta yanda kowace za ta iya shigowa daga falon ta zuwa na shi.


An tafi mayar da mutane aka bar amarya da k'awayen ta kafin a zo a d'auke su, nan fa hira ta b'arke tsakanin su, Zeinab ce ta fara da "Wallahi rabin rai sai kin zage damtse, kinga wannan matar ta shi, ni fa har ta ban tsoro."


*Farida* ce tace "Bari kedai, ashe haka ta ke?"


Murmushi Haseenah ta yi tace " Lallai *kallon kitse ku ke wa rogo*, ni kuma ko kad'an ba ta ban tsoro ba, dan na riga da na san komai."


Zeinab ce tace "Kamar me fa? Dama ku na hirar ta da shi?"


"A'a, amma dai akwai wasu abubuwa da su ka nuna min ita d'in shashasha ce."


"Ban gane ba k'awata, ki min gwari-gwari mana."


Cikin nutsuwa tace "Na fahimci mijin ta na son girmamawa, ya na son a dinga ma sa kalaman soyayya, dan in mu na hira da shi sai mu kai k'arfe *11:00* na dare mu na waya, duk kalmar da na fad'a mi shi sai ya gode min tare da godewa Allah da ya sa zai aure ni, shi ya sa na san cewa ita ba ya samun nutsuwa a tare da ita, kyan d'an maciji ne kawai da ita, kuma wallahi na d'aura d'amarar faranta mi shi fiye da ita."


Ajiyar zuciya Zeinab ta sauke sai wata daga ciki mai sunan *Jamila* ce tace "To k'awata, Allah ya sa dai ba *kallon kitse ki ke wa rogo ba*, dan wasu mazan ba kya iya gane cikin su, watak'ila ma shi d'in mai son kulawa ne kawai, shi ya sa ya ke jin dad'i kema za ki bashi farin ciki."


Kallon ta Haseenah ta yi yi tace "Hum! Ba ko d'aya wallahi."



Kiran Usman ne ya katse ta, ta na d'auka tace k'awayen ta su fito a mayar da su gida, nan su ka tashi su na tsokanar ta wai za su zo cin kaza da sassafe, ita kuma ta na dariya ta na fad'in ba zai yiwu ba ita da shan wahala su da cin kaza, haka su ka bar ta wasu na ganin kamar ta na son yin kuskure na gani-ganin da take wa Khadija, haka dai gida ya yi shiru ba kowa, ango kuma bai shigo ba sai da dare ya raba sosai, lokacin Khadija ta yi shirin kwanciyar ta ta na kwance a d'akin Bilal da shima ya jima da yin bacci, d'akin ta ya fara shiga bai same ta dan haka ya wuce d'akin Bilal, ta na jin shigowar shi ta rufe ido kamar mai bacci, tashin ta ya yi amma ta nuna kawai ta yi nisa a baccin ta, sai da ya tallabo ta ya kalli idon ta yace "Ki tashi mana ki kalle ni."


Ido rufe tace "To me zan maka? Amarya ce da kai fa."


Sake komawa ta yi ta kwanta, ledojin hannun shi ya kalla yace "To tashi ki d'au leda d'aya anan?"


Juyowa ta yi ta kalleshi duk da dai ba ganin shi ta yi da kyau ba haka tace "Tun fa a gidan mu ina ganin bak'ar leda, kuma nasan kaza ce a cikin ta, kuma ba na sha'awar cin ta, dan haka ko dai ka tafi da ita can za ku fini buk'atar ta, ko kuma ka aje watak'ila idan d'an ka ya tashi da safe ya ci kazar siyar bakin kishiyar mahaifiyar..."


Da sauri ya daka mata tsawa ta hanyar fad'in "Kar ki soma Khadija, wallahi kar ki fara sakawa yaro na banbanci  a cikin k'wak'walwar shi tun yanzu, sam ba zan lamunci wannan ba, ke da Haseenah yanzu duk d'aya ku ke a gurin shi."


Juyawa ta yi ta d'auki gilashin ta ta mak'ala ta na murmushi tace "Tun yanzu Abban Bilal? Yaushe rabon da ka d'aga min murya irin haka? Sai yau? Saboda ka yi amarya? Yayi kyau, amma bari ka ji nima na fad'a ma ka, Bilal yaro na ne ban da wata banzar mace da ta shigo gidan nan yau, idan kai ka shirya sadaukar mata da yaron na ka, sai ka bari har a wayi gari, a lokacin ta san komai a kan ka, ma'ana ta gan ka daga ka isai fatar jikin ka, to a lokacin sai na yarda, idan ka fita ka rufe mana d'akin."


Gilashin ta ta cire ta aje ta yi wanciyar ta ta rufe har fuskar ta, da k'yar ya aje d'aya ledar ya fara taka k'afafun shi ya fice daga d'akin, har k'asan zuciyar shi yana jin ba dad'i, kuma ba ya fatan auren shi da Haseenah ya zama silar fara rubuta matsala a tarihin zaman shi da ita, dan Khadija ita ce farin cikin shi, haka ya sallama d'akin amarya ya same ta, da k'yar ya tattara nutsuwar sa ganin Haseenah na neman fahimtar halin da ya ke ciki, ita kuma dad'i ne ya kusa kashe ta saboda ganin halin da ya ke ciki, sun gabatar da duk abin da shari'a ta zo da shi amarya da ango suyi sunyi, bayan nan kuma su ka kwanta dan sauke gajiya, bai yarda ya yi nesa da ita, sai dai tabbas akwai wani bak'on al'amari, in dai har ya na gari bai tab'a raba shinfid'a da Khadija ba ko da kuwa sun samu sab'ani ne a matsayin su na yan adam, dan ko haihuwar Bilal ba su raba shinfid'a ba, haka mai tsohuwar da ta zo ta ke ganin rashin kunyar ta, haka dai ya rumgume ta har bacci ya d'auke shi.


Kiran sallah farko Khadija ta tashi tare da Bilal dan gabatar da sallah, d'akin ta ta koma ta na shirin kabbarawa Usman ya shigo dan ya duba d'akin Bilal bai ganta ba, ba tare da ta had'a ido da shi ba tace "Ina kwana."


Marairaicewa ya yi yace "Ina aka baro sauran mahad'in da ake had'a min da shi?"


"Ban gane ba?" Ta fad'a ta na gyara hijab d'in ta, kallon ta ya yi yace "Kamar Abban Bilal, babban mutum, rabin rai, sarki, jarumin ki, da dai sauran su."


D'agowa ta yi ta kalle shi da murmushi tace "Ina kwana jarumin namiji."


Ta na fad'a ta kabbara sallahar ta, fita ya yi cikin rashin jin dad'i ya nufi masallaci, Khadija na gama sallah da azkar d'in ta kwace ta koma ta yi dan bacci ta ke ji wanda ba ta yi ba, sai da gari ya waye Bilal su ka dawo tare da baban shi, d'akin amarya ya fara wucewa tun da ba ta san tsarin gidan na su ba, kwance ya same ta a kan sallaya ta na bacci, a hankali ya juya ya fita ya koma d'akin *Dije*, ita ma kwancen ya same ta ta na bacci, k'arfin hali ya yi ya tashe ta, ta na bud'a ido ta ya sakar mata murmushi yace "Ammien Bilal, ashe bacci ki ke? Na d'auka ki na madafa ai."


Sai da ta d'auki gilashin ta kafin tace "Yin me a madafa?"


Cikin murmushi yace "Yin girki mana, ko ba za ki mana abin karin kummalo ba? Kinsan fa bak'uwa ce da mu a gidan, watak'ila ita ta na karyawa da wuri ba kamar mu ba."


Gyara zama ta yi tace "Sai kuma aka ce wannan ya zama matsala ta? Me ka ke so na yi? Na je na dafa mata abinci kenan ta ci? To ka yi hak'uri, ban da ra'ayin shiga madafa yau."


Ta na fad'a ta tashi ta shiga ban d'aki, wanka ta yi dan baccin ma ya fita idon ta, Usman kam na fita ya wuce d'akin Haseenah ya d'auko makullin mota dan ya siyo abinci, a farfajiyar gida ya samu mai gadi ya bud'ewa k'anin shi k'ofa ya shigo, musabaha su ka yi kafin k'anin yace "Ango abinci fa Hajia ta ce na kawo mu ku."


"Da gaske *Nura*? Kai amma Hajia ta kyauta wallahi, dan dama duka mutanen gidan a gajiye su ke."


Dariya Nura ya yi yace "Lallai kam, to ko dai za ka d'auke ni ina dafa mu ku abinci har lokacin da za ku huta?"


Hannu ya sa ya karb'i kwanukan ya na fad'in "Dallah ni bani nan ba na son shiririta."


Mik'a mi shi ya yi yace "Dama ba na son shiga ciki saboda ban sanyo manyan kaya ba, kasan halin Dijen nan da son girma."


Kai ya girgiza yace "Allah ya shirya da wannan son girman na ka, wai matar da ta zo gidan nan ka nada shekara biyar a duniya, tun fa ka na yawo ba wando ta ke tare da kai, amma yanzu har ka ke son bud'e mata ido."


"Ni fa matsala ta da kai kenan, yanzu dai sai anjima, sai na zo cin tuwon amarya."


Wucewa kawai ya yi ya shige ciki, ya na shiga a teburin cin abinci ya aje ya d'auko farantai ya jera sannan ya shiga ya taso Haseenah, tare su ka fito ta na sake k'arewa falon na shi kallo, ganin za su wuce teburin abincin ya sa ta tsaya ta na kallon shi, juyowa ya yi shi ma yace "Muje mana."


Binshi ta yi su ka wuce, k'ofar falon Khadija ya bud'a ta shiga, saboda yawan turaren da akewa d'akin ya sa har ya kama d'akin sosai, a hankali Haseenah ta lumshe ido ta bud'e kai tsaye, rarraba ido ta fara ta na kallon ikon Allah, wai, masha Allah, tabbas ba k'arya falon ya had'u kuma ya tsaru sannan ya ga kaya, ba had'i kam nata falon da wannan falon, ta na ganin kyawun falon Usman, amma sai ta ga ashe na shi ma somin tab'i ne, takawa ta fara yi ta ji k'afafun ta ta lumewa cikin shinfid'add'en tappi da ke kai, ta na kallo ya k'wank'wasa k'ofar d'akin tun da ba shi kad'ai bane, amma a wajen Haseenah kawai mulkin da Khadija ke yi a gidan ne ya sa ba ya iya shiga d'akin sai ya nemi izinin ta, jin shiru ya sa ya bud'a a hankali ya lek'a, ganin ta ya yi zaune bakin madubi ta na shafa  hoda (powder), "Mu shigo?"


Shine abin da ya fad'a, ta na jin haka ta san ba shi kad'ai bane, dan haka ma ta saki murmushi  tace "Ku shigo mana."


K'arasa shiga su ka yi Haseenah na d'ard'ar da satar kallon d'akin, ko dan na ta d'akin sabbin kaya ne a ciki sai warin sabintaka su ke, hakan ya sa taji kamar ta yi kwance a d'akin Khadija, zaune ta yi kujerar da ke gefen kwabar saka kaya (wadrob) kanta k'asa, shi kuma tsaye ya yi gaban Khadija yace "Wannan kwalliya haka matar, wa ake ma ne?"


Tsaye ta mik'e ta na gyara d'an kwalin ta ta juyo ta kalli Haseenah da fara'a tace "Amarya ke da kan ki?"


Ita ma murmushin ta yi tace "Ina kwana?"


"Lafiya lau amarya, kin tashi lafiya?"


"Lafiya lau." Ta fad'a a tak'aice, da murmushi Khadija ta d'ora da "Ya kwanan bak'unta kuma? In ce dai kinyi bacci?"


A birkice Haseenah ta kalli maganar Khadija, hakanne ya sa ta d'an d'ago ta kalle ta ido tsaye tace "Ai Abban Bilal bai barni na yi bacci ba, kin san shi da rigima."


Kallon ta Khadija ta yi ta na wani murmushi irin na babba da yaro tace "Ke ma kenan da ki ka zo jiya,   yanzu na san za ki fahimci k'ok'ari na akan mijin ki."


Haseenah kam a zuciyar ta tsaki ta yi, Usman ne yace "To na ji, yanzu dai ai nine rigimammen ko? To nagode, yanzu ku wuce muje mu ci abinci."


Cikin zolaya Khadija tace "Wai har ka gama girkin? Amma gaskiya ka yi sauri."


Hararan wasa ya aika mata yace "Kin d'auka ke kad'ai ce gwana a fannin girki? To ni har lambar yabo aka ban, nuna miki ne ban yi ba saboda tsaro."


Dariya ta yi tace "Ko dai saboda tsoron girki ba."


Takawa ta fara yi tace "Muje to."


Da sauri ya rik'o hannun ta ya mayar da ita gaban madubi ya bud'a ya d'auko wani k'aramin akwatin gilashi yace "Ki saka wannan ya na miki kyau."


Da kan shi ya saka mata kafin suka wuce, Haseenah kuma kamar zuciyar ta za ta harba saboda bak'in kishi na banza da wofi, haka su ka zauna tare da Bilal a faranti d'aya su ka saka hannu dukan su, sai dai Khadija da Haseenah ba sosai su ke cin abincin ba, dan kowa da abin da ke ran shi, haka dai su ka gama ango ya shirya ya fita, amarya ta koma b'angaren ta.




*Yau* ma dai sosai aka gwangwaje walimar damu, mutane sun sha anko gwanin ban sha'awa, haka aka yi abin da ya tara mutane sai dai sisin kwabo ko k'wayar gero Usman bai karb'a ba a hannun iyayen Haseenah, daga k'arshe dai tsofaffi da iyaye sun sake had'a kan Khadija da Haseenah sun mu su nasiha da jan kunne tare da gargad'i, a k'arshe kuma su ka bisu da addu'ar fatan zaman lafiya da kuma zuri'a mai albarka, haka yau ma taro ya watse in da kowa ya koma gefe dan a kalli kalar na su zaman, da dare ma Usman ya shigo tare da manyan aminan shi Alhaji *Murtala* da Alhaji *Adamu* mijin Salamatu, suma dai nasihar su ka sake mu su tare da fatan alkairi daga bisani su ka tafi.



*Allah ya bada hak'urin zama da juna.*

05/01/2020 à 22:11 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *7*



Kasancewar Bilal zai koma makaranta yau ya sa Khadija ta shi da wuri ta nufi madafa dan shirya abin kari, (albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan kasko), tun da ta tunkari k'ofar ta gan ta bud'e ta ke mamakin yanda k'ofar ke bud'e, da wannan mamaki ta k'arasa shiga, turus ta ja ta tsaya ganin oga malam yallab'ai kuma alhaji Usman ya d'auki k'atuwar tasa daga kan gas ya na juye tafasashen ruwan da ya dafa a k'aramin bokiti, da sauri ta k'arasa ta na fad'in "Abban Bilal, me ka ke yi haka?"


Wani abu ya ji tare da kunya dan baiso ya ganta ba ko ita ta gan shi, d'agowa ya yi bayan ya juye ruwan ya na d'an had'e fuska yace "Um, wallahi, wai wanna ce, ina jin dai, kamar dai ba ta cika wanka da ruwan sanyi bane da safe, to shine na..."


Katse shi ta yi da cewa "Uhum! Na gane ma, ka kai mata to kafin su huce."


D'auka ya yi cike da kunya ya fice, sai da ya b'ace ma ganin ta taji hawaye sun cika idon ta, cire gilashin ta ta yi ta share k'wallan, ji ta yi ma ba za ta iya komai ba dan haka ta juyo ta fito, ta na zuwa falon ta taga abin mamaki, da sauri ta saki murmushi tace "Wa na ke gani kamar Uwani?"


Da dariya matashiyar yarinyar tace "Ni da kai na Maman Bilal."


"Uwani yaushe ki ka dawo? Sai kawai na gan ki haka kamar aljana."


Dariya Uwani ke yi har tace "Jiya na shigo da magriba, shi ya sa ma ban zo tun jiya ba."


"Kai, amma ko na ji dad'in zuwan nan na ki, dan yanzu haka da ki ka ganni wallahi na gaji ne, har na shiga madafar kuma na fito da d'aki ne zan koma ba kwanta kuma sai gaki."


Da karsashi Uwani ta mik'e tace "Maman Bilal ba ki da matsala tun da na dawo, yanzu fad'i me za'a dafa sai na shiga da kai na."


"A'a ba za ayi haka ba, ai ganin ki karsashi ya k'ara min, kawai muje tare sai mu d'ora, kinga ma daga nan sai ki bani labarin abinda ya tsayar da ke."


Dariya ta yi su ka nufi madafar, aiki suke su na hira ta na fad'a mata abin da ya tsayar da ita, da haka su ka kusan kammalawa Khadija ta sakar mata aikin ta tafi d'aki dan yin wanka.



Da taimakon Usman Haseenah ta shirya kan ta sai shefiyar shagwab'a take zuba mi shi, shi kam yau ya na jin ya samu sabuwar hanya sai wani biye mata ya ke, ba dan yaji abin da ya saba ji ba, sai dan kawai yau sabuwar hanya ce ya bud'e da kan shi, a k'arshe ma daga d'akin ta zuwa falon shi sai da ya d'auko ta ya fito da ita, ya na zaunar da ita yace "Bara na je na samo mi ki abin da za ki ci ko, na san yanzu ki na jin yunwa."


Cike da kissa da salon iskanci tace "Um, amma gaskiya ba komai zan iya ci ba."


Sai da ya sumbaci hannun ta yace "Ranar ki ce yau amarya, ki fad'i duk abin da ki ke son ci, za'a kawo mi ki shi gaban ki."


Cike da yauk'i tace "Da fari dai ruwan bunu na ke son na fara korawa a ciki na, bayan nan kuma sai na samu tuwon shinkafa."


Wani kallo ya mata da murmushi yace "Eyeee, amarsu, ko dai a dare d'aya har na yi nasarar aika sak'on ke kuma kin karb'a hannu bibbiyu."


K'asa ta yi da kai ta na murmushi, janyo ta ya yi ya rumgume yace "Allah ya sa haka Haseenah, zan fi kowa farin ciki da faruwar hakan, a karo na biyu Allah ya sake nuna min jini na a duniya."


Jin haka ai sai ta shagwab'e tace "Yunwa fa na ke ji sosai rabin rai."


Zunbur ya mik'e yace "Shikenan to, yanzu zan dawo, bara na shiga na ga auntyn ki sai na wuce."


Kwab'e fuska ta yi alamar za ta yi kuka, da sauri ya dawo ya zauna yace "Me ye kuma na kuka? Ciwo ki ke ji har yanzu?"


Kai ta girgiza tace "Ina tausayawa kai na ne dai kawai."


"Da me ya faru?"


Cikin goge ido tace "Ka ce sai ka fara zuwa wajen aunty na, kuma na san kai da aunty na kamar Roméo da Juliette ne, ban san yaushe za ka fito ba."


Murmushi ya yi yace "Yanzu fad'a min ya ki ke so ayi to?"


Cikin turo baki tace "Idan ka dawo ai sai ka je ku gaisa, kai kuma cinye kan ku ni dai ina daga nan ina cin abinci na."


Dariya ya yi yace "Kenan ba ki damu da ni ba ko?"


Hannun shi ta rik'o tana kallon idon shi tace "Da kafin daren jiya ka fad'i haka sai na iya yarda abisa wasu dalilai, amma  banda safiyar da ta tabbatar min mun zama d'aya ni da kai."


Murmushin jin dad'i ya yi ya sumbaci kumatun ta ya mik'e yace "Sai na dawo, za ki sha zallar ruwan madarar soyayya."


Kashe mi shi ido ta yi tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya, Khadija ta fito  cikin wata arniyar doguwar rigar shadda, kwanukan abincin ne hannun ta tare da Uwani a bayan ta, abin mamakin da ba ta tab'a ganinshi ba wai Usman ya fita ba tare da ya lek'a in da take ba, Haseenah da ta ga shigowar su ko kallo babu wanda ta ma, sai da ta aje kwanukan daga in da take tace "Amarya sannu da hutawa."


"Sannu." Ta fad'a ta na wani yamutsa fuska, Uwani ce tace "Ina kwana aunty amarya."


Kallon ta ta yi cikin rashin sanin wacece ita, Khadija ce tace "Sunan Uwani, mai aiki na ce, amma yanzu ta zama mai aikin mu gaba d'aya."


K'ala babu wanda ta tanka ma sai ma d'auke kai da ta yi, d'an cije leb'e Khadija ta yi alamar muje zuwa d'in nan, fita su ka yi su ka d'auko sauran kayan abin karin, ta na cikin jera su Bilal ya fito cikin shirin makarantar shi, da fara'a ta kalle shi tace "Yarima har ka shirya?"


Sai da ya je gaban ta ya sumbaci kumatun ta yace "Ina kwana sarauniya."


Dariya ta yi tace "Ka tashi lafiya?"


"Lafiya lau." Ya fad'a ya na jan kujera zai zauna, ido ta zaro mi shi tace "Kai, ba ka ga auntyn ka bane? Ka je ka gaishe ta mana."


Tsaye ya mik'e yace "Ki yi hak'uri Ammie, ban lura da ita ba."


Wucewa ya yi ya je har in da take, hannun shi ya d'ora a wuyan ta ya kai bakin shi zai sumbaci kumatun ta, ba zato ba tsammani ta ji abun, dan haka ta yi saurin zabura tare da ture shi da k'arfi har ya fad'i k'asa, tsaye ta mik'e tace "Me ye haka? Wannan wane irin iskanci ne? Wannan wani salon tuggun ku ne ko? To ka kiyaye ni wallahi, ni nan da ka ke gani na turmin tsakar gida ce."


Hararan shi ta yi ta koma ta zauna  cikin tsawa tace "B'ace min da gani malam."


Tashi ya yi ya gyara jikin shi yace "Ki yi hak'uri aunty, dama zan gaishe ki ne kamar yanda na ke gaishe da Ammie na."


Tsaki ta yi ta harare shi sama da k'asa ta d'auke kai, wucewa ya yi ya koma wajen maman shi ya zauna kujerar da ita ce  kujerar zaman shi dama, ta fara zuba mi shi a faranti kuma Usman ya shigo, daga in da Khadija ke tsaye ta sakar masa murmushi, shi ma mayar mata ya yi tare da nufa wajen su, Haseenah da kallon mamaki ta bishi, aje ledar hannun shi ya yi akan teburin ya sumbaci kumatun Dije yace "Sarauniya ta tashi lafiya?"


Karo na farko da Dije ta ji kunyar abin da ya yi gaban mutane, cike da kunya tace "Ina kwana babban mutum."


Kallon kwanukan ya yi yace "Ashe kin mana abin kari?"


Murmushi ta yi tace "Jiya ma ai gajiya ce ta hana."


Juyowa ya yi ya kalli Haseenah da ta daina kallon su dan bak'in ciki yace "Haseenah."


Ba tare da ta juyo ba tace  "Na'am."


"Ki zo ga tuwan ki."


Mik'ewa ta yi ta juya ta kalle shi tace "Ya ma fita a rai na wallahi, kawai ka bar shi."


Za ta nufi k'ofar da za ta sada ta da d'akin ta ya yi saurin tare gaban ta ya kamo hannun ta ya nufi wajen teburin da ita ya na fad'in "Idan ba za ki ci tuwon ba ai ga sarauniya ta dafa mana wani abun, kuma zaiyi wuya ki ce ba za ki so shi ba, dan na yarda da girkin mata ta."


Khadija da ke kallon hannun shi dake cikin na Haseenah wani nauyayyen abu ta had'e a mak'oshin ta, yayin da ita kan ta Haseenah taji kamar ta fasa ihu, haka ta zuba abincin ta zauna ita ma, sakin baki Haseenah ta yi ganin Bilal ya haye k'afafun Usman ya sa hannu a farantin da ke gaban Usman d'in, haka ma Khadija ita ma ta saka na ta hannun a ciki, kallon ta Usman ya yi da dariya yace "Ki saka hannun ki mana, haka mu ke cin abinci anan."


A hankali ta zura hannu duk sai ta ji kan ta kamar bak'uwa a gidan, kamar ba gidan mijin ta ba haka ta ji kan ta, dan haka ma bata wani ci mai yawa ba sai kallon shiriritar su ta ke, haka aka gama kuma ya tashi ya tafi kai Bilal makarantar islamiyya, tun da ta shiga d'aki ta d'auki wayar ta, yanar gizo ta shiga manhajar WhatsApp, sak'onni ta samu masu yawa daga mutane da k'awaye, ta yi sa'ar samun k'awar ta Zeinab ta na kai ita, bayan sun gaisa ta tambaye ta ya amarci ne ta ke fad'a mata wai da matsala, duk abin da ya faru ta kwashe ta fad'a mata, shawarar da ta ba ta ita ce ta saki jikin ta ita ma yar gida ce aure ta ke, sannan ta canza wannan tsarin na cin abinci, dan ba zai yiwu ace ko ranar girkin ta sai dai aci tare duka ba, da irin haka su ka jima su na hira kafin Usman ya dawo ta taya shi ya shirya zai fita, jikka biyar  (jaka biyar) ya bata kud'in girki duk da babu abin da za ta nema ta rasa a madafa, amma sanin akwai abin da za ta iya nema ya bata su, sallama ya mata kafin ya wuce d'akin Khadija, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito ya fita.



*11:00* daidai na rana Haseenah ta fito dan fara girkin rana, kamar yanda Usman ya fad'a mata cewa duk abin da ta ke buk'ata ko za ta yi ta nemi taimakon Khadija ko ta tambaye ta, kai tsaye falon Khadija ta shiga, ganin ta zaune ya sa ta yi sallama ciki ciki kamar an sata dole, da fara'a Khadija ta amsa ta na fad'in "Amarya kin fito?"


Wani shegen murmushi ta yi tace "Um."


D'orawa ta yi da "Dama zan fara girki ne, kuma yace na tambaye ki idan ina neman wani abu."


Cikin sakin fuska Khadija tace "Ayyah, kar ki damu kan ki, ga Uwani sai ku je tare ta taimaka mi ki."


Da sauri tace "A'a, ba na buk'ata, nagode, kawai ki fad'a min in da zan samu kayan, dan yace akwai duk abun buk'ata."


Cike da iko ta kalle ta tace "Hakane, kije to su na madafar."


A gadarance tace "Madafar a ina?"


Murmushin gefen labb'a ta yi ta mik'e tace "Muje na nuna mi ki."


Bin bayan Khadija ta yi har madafar, k'atuwar frigi (fridge) ta bud'a ta nuna mata tace " Za ki iya samun duk naman da ki ke so."


Haka ta nuna mata komai ta fice, ita kuma d'akin ta ta koma ta dauk'o wasu daga cikin kayan miyar da aka had'o ta da su, cire hijabi ta yi ta dauk'o naman zabbi dan wankewa ta fara aikin, ta yi k'ok'ari sosai wajen yin abin da ba ta saba yi ba, sai da ta ga miyar ta ta kusa kammala kad'ai ta d'ora ruwan silalar macca, d'akin Khadija ta je ta tambaye ta adadin wacce za ta dafa? Cike da sakin fuska tace " Eh to, za ki iya saka leda biyu, idan kinsan ba za ki yi bak'i ba."


Biyu ta saka kamar yanda ta fad'a mata, sai dai kuma a maimakon ya zo gida cin abinci sai ya kirata wai ta fidda mi shi abinci mai yawa zai aiko a d'aukar ma sa, gashi Aziza ta zo tare da k'awar ta, ga kuma wasu daga  cikin dangi su na zuwa, ga kuma k'annan ta su uku sun zo, ga kuma mutanen gida.



*Za mu ga idan ki na da wayo ai.*🤪

08/01/2020 à 17:09 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *8*



Jin ba za ta iya d'ora wata tukunyar ba ya sa ta aiki Bilal d'an unguwar ya siyo mata bredi mai yawa, maccar da ta dafa sai ta juye wa mijin ta, bredi kuma ta had'a Khadija da shi tace ta  rarraba, da mamaki Khadija tace "Amma Haseenah da ba ta isa ba aida wata ki ka d'ora, tun da akwai sauran lokaci bare ace a matse ake."


Shiru ta yi ta ba tanka ta ba, haka ta raba miyar wa sauran mutanen da ke wurin, ficewa ta yi daga madafar in da Aziza ta bita da harara, tab'e baki ta yi tace "Kiji wani iyayi kuma, ko ina ruwan ta da abin da ki ka ga damar yi, sai ka ce ke ba gidan mijin ki ba."


Cikin sanyin jiki Haseenah tace "Ke, wannan ai ba komai bane, gaskiya ta fad'a."


"Tab'." Cewar Aziza tare da kallon k'awar ta, farantin abincin su ta d'auka ta d'auki bredin tace "Muje d'aki sai mu ci ko."


Tashi su ka yi su ka bi bayan ta, abinci su ke ci su na hira, Haseenah dai na sauraren su sai dai ta yi dariya, har su ka gama su ka d'ora daga inda su ka tsaya, ko da yamma ta yi su ka kama mata aikin dare ta yi, da su ka gama za su tafi kyaututtuka ta ba su, turaruka da sauran kayan kwalliya da kud'i wai su shiga adaudaita, da k'yar su ka karb'i kud'in da ta dage sosai, su na tafiya ta koma d'aki ta yi wanka ta shirya dan tarbar mijin ta, ta na gamawa ta d'auki d'aya kwanukan abincin ta sallama har falon Khadija, amsawa ta yi Bilal na zaune kusa da ita ya na karatu, da murmushi ta amsa ta na fad'in "Amarya ke da kan ki?"


Sunkuyawa ta yi ta aje kwanukan ta d'ago ta kalle ta tace "Ga abincin ku nan."


Juyawa ta yi za ta fita Khadija tace "A'a, ban gane abincin mu ba, ni da wa? Ko kin manta ba'a raba abinci a gidan nan? Ai Abban Bilal bai yarda da haka ba, duka iyalinshi su na cin abinci tare ne."


Juyowa ta yi cike da gadara da ido tsakar kai tace "Eh, na sani, amma waccen ai tsohon yayi ne, yanzu kuma na shigo gidan, dole za'a samu canje-canje da dama, daga yanzu in dai girki na ne gaskiya miji na zai ci abinci a nawa b'angaren ne ba na shi ba."


Juyawa ta yi har ta fara takawa Khadija ta gyara zama tace "Haseenah, nasan kinsan abinda ki ke shirin aikatawa kamar k'ok'arin rusa farin cikin gidan nan ne, dan haka kar ki ce za ki biyo min ta wannan hanyar, da ba zan d'auka ba, kin ganni nan? Wallahi ba na d'aukar raini ko rashin kunya, zaifi mi ki tun wuri ki fara taka tsantsan, abinci kuma ki d'auki kayan ki ba zan ci ba, ba kuma zan bawa yaro na ba, dan bansan me ki ka saka mana a ciki ba."


Wata dariya Haseenah ta yi tace "Ikon Allah na kwance ya fad'i, wato ke yanzu tunanin ki kenan? Nima zan yi abin da ke ki ke yi ne, hum! To ki farka, ni ba boka ba malam zan mallaki miji na, ke kuma da ki ke barbad'e a abinci sai ki yi ta yi, da sannu k'aryar ki za ta k'are a gidan nan."


Tsaye ta mik'e da mamaki a fuskar ta tace " Au! Kema tunanin ki kenan? Hhhhhhhh, lallai yarinya, in kuwa har wannan shine tunanin ki, to ki zanca tun wuri, dan wata rana zuciyar ki za ta iya raya mi ki kema ki bi boka da malam dan samun zuciyar babban mutum, kinga kuwa har abada ba za ki san sirri na ba."


Matsowa ta yi kusan ta dafa kafad'ar ta tace "Haseenah, ina kishin miji na, amma duk da haka bai sa na ji a raina cewa zan iya cutar da ke ba, ki kwantar da hankalin ki sannan ki nutsu, sannu a hankali sai kema ki ciri tuta a wajen mijin ki, ni zan taimaka mi ki kamar yer uwa ta."


Matsawa ta yi nesa da ita yace "Me? Taimako? Ki na kishiya ta za ki taimake ni dan na samu soyayyar mijin mu? Allah ya kiyaye, to me ki ka d'auke ni? Ban cika mace ba ko me? To ba na buk'ata, nasan hayoyin da zan shawo kan miji na, ba sai wani ya taimaka min ba."


Murmushi Khadija ta yi wanda har ya fito da haurun makkar ta guda biyu, Haseenah kam juyawa ta yi ta koma na ta falon ta zauna, ta na kallo Haseenah ta shigo da kwanon ta aje mata a kan teburin ta ta fice, tab'e baki ta yi tace "Ina daidai ke wallahi, sai dai duk abin da zai faru ya faru."


Ba jimawa kam sai ga Usman ya shigo, kai tsaye b'angaren Khadija ya nufo da tunanin zai tarar da duka iyalin na shi anan, Khadija da ran ta ke b'ace kasa tashi ta yi ta tarbe shi kamar yanda ta saba, da gudu Bilal ya k'arasa ya rumgume shi, tare su ka k'araso wajen ta ya na fad'in "Yarima wa ya tab'a min mamanka ne haka?"


Hannu ya mik'awa Khadija alamar su yi musabaha, dan in Bilal na tare da su suna kiyayewa wajen tab'a juna tun da ba k'aramin yaro bane, hannun ta ba shi lokacin da ta ke kallon Bilal da shi ma ya ke kallon ta, murya k'asa k'asa yace "Ba komai Abba."


Zaune ya yi kusa da ita ya na kallon ta yace "Ba gaskiya ka fad'a ba yarima."


Kallon shi ta yi tace "Sannu da zuwa."


"Sannu da gida, ya kuka wuni?"


"Lafiya k'alau." Ta fad'a a tak'aice, dariya ya yi ya kalli Bilal yace "Ka gani ko? Na fad'a ma ka akwai wani abu, ba haka Khadija ta ke amsa min ba."


Murmushin yak'e ta yi tace "Kai ma kasan in dai ka na lafiya to mu ma mu kan kasance cikin k'oshin lafiya."


D'an juyawa ya yi yace "Ina amaryar ki ne ban ganta ba?"


D'an canza fuska ta yi tace "Ta na b'angaren ta mana."


Mik'ewa ya yi tare da kamo hannun ta da na Bilal yace "Muje to mu ci abinci ko, dan yunwa na ke ji sosai."


Fizge hannun ta ta yi tace "Kaje kawai ka ci, mu har munci abincin mu ai."


Da tsantsar mamaki ya ke kallon ta, amma sam ta k'i had'a ido da shi, hannun ta ya sake kamawa su ka nufi d'akin ta ya maida k'ofar ya rufe ya juya ya na kallon ta yace " Ina jinki, fad'a min me ya faru?"


Zaune ta yi akan gado tace "Ba komai."


Had'e fuska ya yi yace "Khadija kar ki min k'arya, gaskiyar abin da ya faru na ke so na ji."


"Nace ba komai ko, ba komai, kaje kawai ka ci abincin ka, ni da d'ana har munci."


Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kusa da ita yace "Khadija, wannan ba d'abi'ar ki ba ce, dan Allah kar auren da na yi ya sa ki canza daga yanda na sanki, kinji ko."


Shiru ta yi har sai da ya janyo ta ya na shirin kai bakin shi a nata ta yi saurin rufe bakin ta da hannun ta, wani tuhumammen kallo ya mata yace "Meye haka? Ba kya so ne?"


"Eh." Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, fizgo ta ya yi ta koma kan gadon da k'arfi, kafe ta ya yi da ido yace "Me ya sa?"


Juya mi shi baya ta yi, sake juyo da ita ya yi yace "Nace me ya sa ba kya so? Sai kin fad'a min dalili na rabu da ke."


Zuciya a wuya sai kawai Khadija ta fashe da kuka ta fad'a kan k'irjin shi, cikin kukan tausayi tace "Ba na so kawai, Abban Bilal ba na so ka na kusanto ni, haushin ka na ke ji Abban Bilal, na k'arar da rayuwa ta wajen killace ma ka kai na da mutunci na, amma kai a dare d'aya tak ka kusanci wata mace, zuciya ta bugawa take, ji na ke kamar zan mutu dan bak'in ciki wallahi."


Usman kam jikin shi ne ya yi sanyi sosai, tunawa da yanda auren su ma ya kasance, duk da kusan had'a su ne akayi amma ko sau d'aya duk da matsayin Khadija na mace, ba ta tab'a nuna ma sa k'iyayya ba ko a idon ta, amma yau gashi ta na fad'in ba ta son yana zuwa kusa da ita, a hankali ya d'ago ta ya share mata hayawen fuskar ta ya na girgiza mata kai, hannayen ta ya had'e ya rufe idon shi ba tare da ya had'a ido da ita ba yace "Ki yi hak'uri Khadija, ki gafarce ni idan hakan da na yi ya b'ata mi ki rai, har zuciya ta banyi haka dan muzguna mi ki ba, ba kuma na yi bane saboda wani kaso daga cikin kason da ki ke da shi a zuciya ta ya ragu ba, babban k'arfin gwiwa ta akan auren nan shine, Nana Khadija mai halin girma da hak'uri za ta taya ni kare hakk'in da ke kai na, sannan a lokacin da aka d'ora min nauyin Haseenah a kai na wallahi zuciya ta ta fad'a min cewa Khadija na tare da kai, da izinin ubangiji za ta taimaka maka wajen ganin ba ka k'untatawa yarinyar mutane ba, amma kash! Shed'an na ta k'ok'ari sai ya kutso cikin gida na ya tarwatsa min kan su, babban abun bak'in cikin shine, ya na so ne ya shigo ta hanyar mata ta Khadija abar so da k'auna ta kuma abar alfahari na."


Tafin hannun ta tasa ta goge hawayen, murmushi ta masa mai d'aukar hankali, matuk'a tasan mijin ta na son ta, kalaman shi kullum suna k'arfafa mata gwiwa da kuma sace mata gwiwa, ganin wannan murmushi ya sa ya kama kumatunta yana murmushi yace "Dariya a fuskar ki shine abin da Usman ke son gani a kullum, murmushin ki kuma shi ne silar nawa murmushin, ki ci gaba da murmushi irin haka har lokacin da zamu koma ga ubangijin mu."


K'asa ta yi da kan ta tace "Kalaman ka su na sani jin kunya."


Tallabo fuskar ta ya yi yace "Ke ce sarauniya, na baki zuciya, ke ce guda d'aya duniya ta masoya."


Yanda ya rera mata baitin ya sa ta sake fad'awa kan kirjin shi ta na murmushi, d'agota ya yi yace "To a bani sumbata kafin na fara zanga-zanga a gidan nan."


"Me ya yi zafi? Ba sai an kai ga haka ba, bani bakin ka nan."


Sai da su ka gama lobayyar su kad'ai su ka fito, Haseenah da ta ji shigowar shi ta gaji da jiran shigowar ta shi kasa jura ta yi, falon Khadija ta shigo sai Bilal kad'ai ta samu ya na karatun shi, tun ta na zaune har ta fara kai da kawowa tsakiyar falon kamar za ta had'e zuciya ta mutu, ta na jin bud'a k'ofar ta juya da k'arfi, taushe b'acin ran ta tayi ta tafi a guje dama ba nauyi ba kamar ni😉, ai kuwa sai ta d'ane a jikin shi ta na fad'in "Rabin rai na, na yi kewar ka sosai, har zan fara kuka."


Bilal da Khadija kallon su suke da ido, a hankali ya d'ago ta daga jikin shi da nufin mata magana, sai kawai Haseenah ta fashe da kukan shagwab'a ta na fad'in "Wallahi da k'yar na iya riskar wannan daren saboda kewar ka, a gaskiya ba za ka sake bari na gidan nan ni kad'ai ba."


Sake fad'awa ta yi jikin shi, Khadija da ta ji wasu hawayen na neman taho mata ne ta juya ta kamo hannun Bilal su ka bar falon, lallab'a ta ya yi su ka koma na su falon, duk k'ok'ari Haseenah ta yi shi ta saka shi kalar nata farin ciki, wanka ta mi shi ta saka mi shi kaya marar nauyi, har uwar d'akin ta kai mi shi abinci a bakin gado ta aza akan k'aramar kujera, sam bai iya tuna su Khadija ba haka Haseenah ta dinga yanka masa loma ta na aika masa a baki ya na wucewa da ita ta mak'ogoro, ita kam dad'i ne ke kashe ta saboda ya na sake cin abincin da ta zuba garin maganin da malam ya bata, sai da ya k'oshi kad'ai ta bar shi ta ci nata a zuwan ta k'osar da wanda yafi mahimmanci a gare ta, falo ya koma ya na kallo ita kuma ta na d'aki ta d'auko garin maganin matan ta wanda sai za'a kwanta ake sha, duk da madara ta sha su kafin ta shiga ban d'aki ta sake zaunawa a cikin tafasashen ruwan bagaruwa, sai da su ka huce ta fito ta d'auki wani arnan magani na matsi emergency, k'anana ne fari kamar k'wayar magani, matsawa ta yi haka ma miski sannan ta fito ta saka kayan bacci ta shek'a kwalliya, minti sha biyar ta koma ta kama ruwa da ruwan zafi k'a'idar maganin kenan, fitowa ta yi cikin sand'a ta rufe mi shi ido ta baya,  murmushi ya yi yace "K'amshin nan da na ke ji ya sa babu abin da na ke son gani sai ke."


Bud'e mi shi idon ta yi cikin karairaya ta dawo gaban shi, k'are mata kallo ya yi yace "Iyeh! Wow, wane irin kyau ne wannan? Tabarakalla ahsanul-kalik'ine, Allah abun godiya."


Janyo hannunta ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi, k'amshin humrar ta ne ya tafi da imanin shi, tuni ya fara aika mata da wasu sak'onni wanda take ta ke karb'ar su, dan magungunan da tasha masu k'arfi ne sosai, da k'yar dai su ka iya kai kan su uwar d'aki su ka kashe wuta, surukina gyara kimtsi mana, ina fa taya 'yata kishi.😎



Abunka ga ba saban ba, sosai Haseenah ta yabawa aya zak'inta, amma dai tun da taji Usman na gurnani ya na sambatu da surutai har ya na neman shid'ewa, hakan ya sa ta ji kwalliya ta biya kud'in sabulu, dama kuma *ado gwanja* yace "Rai ba'a bakin komai ya ke ba wajen biyan buk'ata."😂


Haka dukansu su ka yi baccin gajiya rumgume da junan su, washe gari kam bai bari Haseenah ta shiga madafa ba, kuma ba ya so yace Khadija tayi, fita ya yi ya samo mu su soyayyen k'wai da dankalin turawa, ya na zuwa kuma ya samu Khadija har ta had'a abin karin da ta san  d'an ta ya fi so, falon ta ya same ta suna karyawa da yaron ta, gaisawa su ka yi kafin yace "Yarima har ka shirya ne?"


"Eh Abba."


"To idan ka kammala sai ka fito mu wuce."


Kallon shi Bilal ya yi yace "Abba yau ina so na je da d'an moto na, kaga ba sai na jira ka je d'auka ta ba."


D'an b'ata rai ya yi yace "Kai Bilal, mahaukaci ne ni da zan barka ka tafi a hanyar ababen hawan nan kai kad'ai akan moton ka, bana so, kuma na fad'a maka hawan moton ka kar ya wuce cikin unguwar nan, duk da cazashi ne ake amma ba na so, kar kuma ka kuskura na gan ka ko a bakin titi ne, dan ran ka zai b'ace."


Mik'ewa Bilal ya yi ya matsa kusan shi yace "Ka yi hak'uri Abba, ba zan sake ba."


Kan shi kawai ya shafa bai ce komai ba, jakar shi ya d'auka mai d'auke da littafanshi yace "Na gama."


Kallon shi ya yi yace "Ka tabbata ka k'oshi?"


Kai kawai ya d'agaalamar Eh, hannun shi ya kama yace "To muje."


Juyowa ya yi ya d'agawa mahaifiyar shi hannu yace "Sai na dawo sarauniya."


Murmushi ta masa tace "Allah ya tsare, a kula sosai ka ji ko?"


Usman ma kallon ta ya yi yace "Ni ma na tafi ba zan dawo ba."


Ba alamar wasa a tare da ita tace "Sai na bika duk in da ka ke ai."


Dariya ya yi yace "Kar ki damu sarauniya zan dawo ai, ke ce fa."


"Ah to, sai na ma riske ka duk in da kaje." Ta fad'a ta na tashi dan had'a kayan da su ka karya.



*Kafin mu ci gaba, za mu waiwaiya baya mu ji yanda wannan soyayyar ta fara ta Khadija da Usman.*



_Sai mun had'u a shafi na gaba._✋

10/01/2020 à 12:20 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *9*



*Alhaji Ahmad*, dattijo mai dattako, mutum ne da Allah ya wadace shi da komai, dukiya, ilimi da 'ya'ya, matar shi d'aya *Hajia Sadiya*, suna zaune lafiya cikin farin ciki, mutum ne shi da bai da ra'ayin tara mata, hakan ya sa suke zaune daga Sadiya sai yayan ta,  Allah ya azurta su da yaya maza guda biyar, *Ashir* shine babba, sai *Bashir* sai kuma *Habib* da *Mansur* da *Naseer*, Naseer na da shekara biyar aka samu cikin da ya wahalar da Sadiya, tun a lokacin su ke ji a jikin su cewa Allah zai musu sauyi ne, cikin ikon Allah kam bayan laulayin da ta sha sai gashi ta haifo kyakyawar yarinya mai kama da ita, *Nana Khadija*, yarinya ce da ta zama tamkar wata zinariya a cikin mutane, kowa soyayya ya ke nuna mata, lele kawai da gata take gani, su kan su yan uwanta suna matuk'ar k'aunar ta, dan har fad'a suke akan wanda ya fi sonta ko wanda zai d'auke ta, haka Khadija ta taso cikin gata da kulawar iyaye da yan uwa, sai dai tun da ta fara tafiya suka lura kamar tana da matsalar ido, basu b'ata lokaci ba wajen ziyartar likitoci, nan aka sanar da su tana da matsalar gani, bata iya gani da kyau sai dishi-dishi, sosai mahaifinta ya damu kuma yake yawon nema mata magani, amma sam ba'a dace ba har k'asar waje an fita da ita, haka dai suka hak'ura aka d'ora ta akan saka gilashi mai k'ara gani, wannan laurar sai tasa iyayenta da yan uwanta sake tausaya mata da k'ara k'aunar ta, sam larurarta bata tab'a damunta ba bare tasa damuwa, tana jin dad'in kasancewarta a yanda take, duba da wasu sam idon ne ma basa da su, tana da shekara *goma sha biyu* a duniya ranar wata alhamis da dare, suna zaune a farfajiyar gida su na ta hira Khadija na kan k'afafun mahaifin ta, da sauri ta juya ta kalli baban ta tace "Baba, ka ga wani ya shiga d'akin ka."


Da mamaki ya juya ya kalli k'ofar d'akin na shi ya gan shi rufe, murmushi ya yi ya kalle ta yace "Auta ni banga kowa ba, gashi ki na gani ma d'akin a rufe ya ke."


Naseer ne yace "Wallahi nima Baba sai na ga kamar giftawar mutum."


Sake juyawa ya yi ya kalli k'ofar yace "To wa zai shigo cikin gidan bayan ga k'ofar nan a gaban mu kuma ace ba mu ga shigowar shi ba."


Almajirinsu da ke zaune nesa da su ne ya na cin abinci ne yace "Baban Khadija wallahi nima na gan shi, wani dogo da fararen kaya, amma banga fuskar shi ba, kuma na so inyi magana saina kasa na ji tsoro."


_Wallahi wannan wani abun al'ajabi ne da ya faru da wata baiwar Allah da na sani, za mu iya cewa mala'ikan mutuwa ne_


Sadiya ce tace "Kai Ashir tashi ka duba mana."


Kallonta ya yi yace "Mama, ni kad'ai? Kawai ki bar shi idan ya ga ji zai fito ai mu gan shi."


Dariya aka saka sai Baba ne yace "Ki bar shi kawai, watak'ila fa gizo idon su ke musu, na ga ai ga k'ofar shigowa nan, babu wanda mu ka ga ya shigo."


Haka aka share wannan magana aka ci gaba da hira, Khadija ce bacci ya dauke ta a k'afafun shi, a hankali ya d'auke ta ya kai ta makwancin ta ya shafeta da addu'a, fitowa ya yi su Ashir ma har sun tashi, dawo da su ya yi suka zauna, ya jima ya na musu nasiha da su rik'e Khadija da kyau su zama gatanta ita kad'ai ce k'anwar su mace, har sha biyu na dare ta wuce kad'ai suka tashi, d'akin shi ya shiga ya yi shirin kwanciyar shi sannan ya d'auro alwala, raka'a biyu ya samu damar yi wani nauyayyen bacci ya sure shi akan sallayar, daga wannan bacci ne Allah ya karb'i abin shi.


Mutuwar nan ta girgiza mutane sosai, musamman Sadiya da ke kwance asibiti ba ta san me ake yi ba, Khadija ma yan uwan ta kad'ai take iya yarda da su, amma haka ko da lokaci ya tafi kowa ya manta, sai dai ciwon na nan a zuk'ata, dukansu mazan babu wanda bai da aikinyi mai kyau, hakan ya sa suke matuk'ar kula da k'anwar su, sosai suke shagwab'a ta, ga yarinya na girma amma gatan da take samu yasa kullum kamar yarinya.



 Tun Khadija na da shekara sha biyar Ashir ya gwangwaje ta da moto, duk da sauran yan uwan kowa ya so ace shi ya siya mata, amma haka suka hak'ura tun da ya fisu zafin nama, wannan lokacin ne aka musu rabon gado, kowa ya tashi da na shi kason mai tsoka, na Khadija kuma tace a bawa Ashir da Mansur su ci gaba da juyawa dan sune suka fi sha'awar kasuwanci, mamansu ma dama ta na nata kasuwanci, dan haka ta ci gaba daga inda ta tsaya.


*Duk* wata ba'a daina abin da Alhaji Ahmad ya fara ba, ana yanka rago ayi sadaka, sannan akanyi waina ayi miya sai su aika inda mahaifinsu ke zama da yamma wajen abokanan shi, haka rayuwar ke tafiya har lokacin da Khadija ta ci jarabawarta kuma sakamako mai kyau, babbar walima yayyun ta suka shirya mata a bazata, kayan da suka shirya mata suka sata ta saka suka tafi da ita babban wajen cin abinci, k'awayenta da maza da dama ta samu wanda su ka yi karatu tare, ta ji dad'i sosai a ranar, anan ta yanka  (😂bansan me zan kira cake da hausa ba, amma bara nace mu ku panke) saida ta bi duka yan uwanta biyar ta saka mu su a baki kafin k'awar ta *Kaltume* da *Salamatu*, haka aka gama shagali aka yi murna sosai aka watse.



*Komai na da mafari a rayuwa*, matar Ashir da Bashir da mama sun gama waina, sai dai babu mai kaiwa, Habib kad'ai ke gari kuma shi ma ya na wajen d'aurin auren abokin shi a wani k'auye *Dak'oro*, hakan ne ya tilasta mama cewa Khadija ta shirya sai ta kai a kan moton ta, shiryawa ta yi tare da Kaltume da su ke kusa da juna suka tafi, Kaltume ita ke rik'e da kwanukan abincin a baya, sun isa lafiya su ka kai abincin, cikin ladabi su ka gaishe da dattawan, da kansu su ka wanke babban faranti suka zuba mu su wainar sannan suka d'aure kwanukan su ka mu su sallama, kasancewar akwai rairai kafin su hau titi ya sa Kaltume ba ta hau ba ta na jiran Khadija ta fita daga rairain, cikin rashin sa'a wani tsoho ya taho zai shiga shagon d'inkin shi, tana murd'awa sai kuwa ta bige tsoho ya fad'i, dukan su suka fad'i k'asa da azama aka kawo mu su d'auki, duk da masuburbud'ar zafi  (shagama inji salim, salansa inji mak'obtanmu) ta tab'a ba bai dame ta ba, tsohon mutane data bige shine a gabanta, kuka take ta na tambayar tsohon bai ji ciwo ba, duk da k'afar shi da ta buga yaji ta na masa ciwo haka ma gwiwar hannun shi daya fad'a samanta, amma sai ya nuna ba komai kawai ta tafi, cikin abokan mahaifin nata ne ya lura da hannun shi har jini ya d'an fara fitowa ta cikin riga, nan aka ce a kai shi likita Khadija tace ita ma za ta je, da k'yar suka lallab'a ta dan ta tafi gida, amma duk ta d'aga hankalinta sosai sai hawaye take, wani daga cikin dattawan ne yace "Kinga Khadija ki daina kuka, zai samu sauk'i, kinga ciwon ai kad'an ne, Allah ne ya aiko dole hakan ta faru, yanzu kije gida ki huta, zuwa gobe sai kije godanshi ki dubo shi ko, hakan ya yi?"


D'aga kai ta yi alamar eh, sai da ta hau moton Kaltume ma ta hau sannan tace "Ina ne gidan?"


"Gidan ya na nan yan banana wajen masallacin ladan."


Ta na shan majina ta wuce zuciyar ta ba dad'i ko kad'an, tun da suka je gida daf da magrib sun samu duk yan uwan ta sun dawo daga uzurirrikansu ban da Naseer dake karatu a *France*, yanda ta shigo tana kumboro baki ta na murzar ido ta cire gilashi ne ya sa Ashir zaburowa ya kamo hannun ta yana fad'in "Auta lafiya? Me ya same ki kike kuka?"


Zaunar da ita ya yi ya karb'i gilashin ya maida mata ya kalli Kaltume yace "Umma waya tab'a ta?"


Cikin taushin murya Kaltume tace "Wani tsoho ta bige, ita ma kuma ta fad'i, amma duk ta damu."


Bashir da Mansur a zabure suka matso Bashir na fad'in "Subhanallah, auta ba ki ji ciwo ba?"


Dukansu duba jikin ta suke ko sunga ciwo amma shiru, Mama na gefe tana kallonsu ta yi shiru, a hankali Khadija ta janye siket d'in ta ta nuna musu in da take jin zafi, wajen har ya yi bak'i ai sai suka zabura da ganin wannan d'an ciwo, da gudu Habeeb ya wuce d'akin shi ya d'auko maclean dan a shafa mata, tuni kuma Bashir da Ashir sun umarci matansu da su d'auko musu suma, sai ga abun wanke hak'ora har hud'u a gaban su, nan dai suka shafa mata akayita lallab'a ta har zuwa dare.


Kwance take a d'akin ta cikin bargo yayin da suk yan uwan ke kewaye da ita sai kanta dake kan k'afafun mama, d'aya hannunta na sak'ale cikin hannun Habeeb ya na shafawa, sai mama dake shafar kanta Ashir kuma na karanta mata wani littafi mai sunan *magana jari*, lumshe ido take sosai ta na so tayi bacci, janyo hannun ta tayi daga hannun Habeeb ta tusa shi ta k'asan gilashinta ta murza idon ta tana turo baki gaba, ganin ta rufe ido ya sa Ashir matsowa kusan fuskarta yace "Auta."


Bud'a ido ta yi ta kalle shi, cikin murya k'asa k'asa yace "Albishirinki."


"Goro." Ta fad'a ta lumshe ido, d'orawa ya yi da "Na biya mi ki kujerar hajj, tare da Mama za ku tafi wannan karan insha Allah."


Zunbur ta tashi zaune tace "Da gaske yah Ashir? Kai amma naji dad'i sosai, nagode."


Da k'arfi mama ta maida kanta akan cinyar ta tace "Dan Allah ki kwanta ki yi bacci ko muma mun samu mu rintsa."


Daddab'a ta ta ci gaba da yi har bacci ya d'auke ta, addu'a mama ta shafa mata Mansur ya cire mata gilashin ya aje mata gefenta kafin suka kashe mata wutar d'akin suka fita, har ga Allah wannan kulawar da suke nuna mata Mama tasan ta yi yawa, haka kuma matar Bashir da Ashir suna jin haushin hakan, saboda kai tsaye suna nuna musu farin cikinta yafi nasu, kulawar da suke nuna mata basa nuna musu kwatankwacin ta, shi ya sa mama ke fatan su rage ko dan kasancewar ta ya mace, dan ma ita d'in yarinya ce mai son aiki da kazar-kazar.



*Allah ka k'ara mana k'oshin lafiya, sis Alawiyya Allah ya baki lafiya.*

12/01/2020 à 22:18 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *10*




Washe gari da safe Khadija ta shirya su ka tafi tare da Habeeb ya kai ta gidan tsohon da ta bige, sai da aka mu su kwatance su ka isa gidan, a k'ofar gidan Habeeb ya tsaya ita ta wuce ciki ta na rabka sallama tun daga soro, kasancewar safiya ce kusan matasan gidan ba su riga sun tafi harkokinsu ba, dan wasu ma su na cin d'umamen tuwo ta same su, izini aka mata ta shiga ciki, gaba d'aya ta had'e tace "Ina kwanan ku."


"Lafiya k'alau." Aka amsa mata, d'orawa ta yi da "Antashi lafiya."


"Lafiya lau mu ka tashi."


"Ya mai jiki?" Ta fad'a ta na d'an kallon tsohuwar, da fara'a tsohuwar tace "Mai jiki da dama."


Da mamaki tsohuwar ta kalleta a nutse tace "Sannu ko yan mata?"


"Sannu Mama." Ta fad'a da murmushin ta, tsohuwar ce tace " Sai dai kuma ban shaida ki, gashi na ji har ki na tambayar jikin malam ko?"


Da k'ayataccen murmushi tace "Eh mama, na zo duba jikin su ne, ba za ku shaida ni ba dama, ni ce hatsarin nan ya faru tare da ita."


"Ayyah! Sannu ko, mai jiki ai da sauk'i, yanzu ma haka fitowa ya yi zai fita shago, babban yaron na shi ne ya hana shi yace ya koma ya kwanta, ya na ciki, muje na rakaki ki gan shi."


Ledar hannunta ta sake mayar da ita d'aya hannun saboda nauyin ta kafin ta wuce, ta cire takalmi za ta shiga kenan Usman shi kuma ya fito, saida jikinsu ya had'e da sauri ta ja baya, sai dai kuma ta na ja da baya ta kai wa tsohuwar karo, da azama ta sake matsawa ta na fad'in "Yi hak'uri, yi hak'uri dan Allah."


Wani banzan kallo Usman ya mata ya rab'ata ya wuce ya saka takalmin shi, Khadija kam ajiyar zuciya ta saune ta k'arasa shiga ciki, zaune ta yi kusan katifar da tsohon ke zaune ta aje ledar hannun ta, da murmushi tace "Baba ya jiki?"


Shima da murmushin yace "Jiki da sauk'i 'yata, ya na ki jikin? Ince dai ba ki ji ciwo ba ko?"


"A'a Baba, ban ji ciwo ba."


"To Allah ya k'ara kiyayewa, Allah ya kare mu daga sharrin k'arfe."


"Amee Baba, kuma dan Allah ka yi hak'uri, laifi na ne abin da ya faru."


"Ah haba haba, 'yata ba laifin ki bane, Allah ne ya aiko ai, sai dai Allah ya k'ara kiyayewa, kuma ku dinga kula ku na tafiya a hankali."


"Insha Allah Baba, nagode, ni zan wuce."


Tsohuwar ce tace "Sai tafiya y'ar nan, ko ruwa baki sha ba."


Da fara'a tace "Ba komai mama, ai daga na ke, kuma tare da yaya na mu ke, ya na sauri zai fita aikin shi na tsayar da shi."


"Kuma gaskiya hakane kam karki tsayar da shi."


Tashi ta yi ta fito ta musu sallama, tun ranar kuma Khadija ba ta sake samun damar dawowa gidan ba saboda shirye shiryen tafiyar su k'asa mai tsarki, haka lokacin tafiya ya yi kuma su ka tafi sama tare da mama da matar Ashir da ta Bashir, dan dama an had'a su da mama ne saboda dukansu zuwan su ne na farko, masha Allah sun je lafiya kuma sun dawo lafiya, dukansu sun canza musamman Khadija da dama Allah ya hallice ta da kyanta, inda ta k'awata haurunan ta da hak'oran makka guda biyu, saida su ka yi sati su na karb'ar bak'i da huta gajiya, sai dai har lokacin nan Khadija na tunanin tsohon da ta buge, tunanin ta kawai ita ce silar kwantawar shi, dan haka ta shirya da dare tare da ware kayan tsaraba dan ta kai mu su, sanye take cikin bak'ar doguwar riga har k'asa mai walkiya da kwalliya, takalma sai d'an kwalin da ta mi shi sassauk'an aji a saman kan ta, farin gilashin ta mai kewaye da bak'ar kala ya dace da fuskar ta da kuma rigar, farin man leb'e ne kawai ta shafa, yau kuma Naseer ne ya shirya zai kai ta wanda ya zo hutu, har k'ofar gidan ya dire ta shi kuma ya fito ya tsaya bakin motar, ta na zura kai cikin soron sai duhu, wayarta ta fara k'ok'arin fitowa da ita daga cikin k'aramar jakarta sai kawai ta ji ta zube a k'asa, 😂 "Ahhhhhh."


K'arar da ta saki kenan lokacin da Usman ya yi gaba da ita ta fad'i zaune a k'asa, wayarta da ledar hannun ta da kuma gilashi duka sun kama gabansu, da sauri Usman ya kunna wutar ta shi wayar dan ganin wacece, " *mai gilashi*." Abinda ya fad'a kenan, sai dai mamaki ne ya lullub'e shi ganin Khadija nata lalubar inda gilashinta ya ke, tambayar da ta zo mi shi ita ce "Ba ta gani ne? Ko kuma har yanzu duhun take gani?"


Ya na kallon ta har ta kai hannunta kan gilashin ta, da saurita d'auka ta mak'ala a ido, tarau taga Usman zik'au a gabanta da hasken fitila, da sauri ta mik'e tsaye ta na tattare kayan da su ka zube, shi kam sai ya ji ta ma ba shi haushi, guntun tsaki ya yi ya wuce ta cikin b'acin rai ya fice daga gidan yana fad'in "Idan dai ki ka ci gaba da anfani da gilashi haka kawai, wallahi kin kusa zama makauniya, in banda hauka har cikin dare ma sai kinyi fama da gilashi, kuma yanzu haka ma na masu larurar ido ne take sakawa."


Ya na fitowa ya ga Naseer tsaye, gaisawa su ka yi cikin sanin juna, dan da Usman da Ashir sunyi aji d'aya a makarantar boko, hakan ya sa su ka zama abokai sai dai ba abota irin sosai d'in nan ba, ita ma data shiga ciki k'anan Usman da suke uba d'aya ne ya mata iso har d'akin babansu, bai gusa daga wajen ba ya na kallon fuskarta da murmushin ta ya na jin kamar yace ya na son ta, har ta taso ta fito ya rakota k'ofar gida, kallon juna su ka yi ita da Usman da suke ta hira da Naseer, sallama su ka yi Naseer ya shiga mota ita kuma ta juya ta kalli *Mannir* tace "To sai anjima ko."


"Sai anjima, sai yaushe kuma?"


D'an wasa ta yi da idon ta tace "Kowane lokaci ma za ka iya gani na."


"Shikenan to, sai anjima."


Bud'a k'ofar motar ta yi za ta shiga sai kuma ta ga Usman sai wani kallo ya ke mata kamar irin ya na jin haushin ta, dan haka ta rufe k'ofar ta zagayo wajen shi ta kalle shi cikin taushin murya da nutsuwa tace "Na ga kamar haushi na ka ke ji saboda abin da ya faru, dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min, duk da nasan laifi na ne, amma kuma Allah ne ya aiko, ka gafarce ni idan na b'ata ma ka rai."


Juyawa ta yi ta shiga motar, shi kuma juyawa ya yi ya na jan wani tsakin, bin Mannir ya yi da harara yace "Sai ka rufe bakin to sakarai, har da wani sai yaushe za ta dawo, to uwar me za ta maka idan ta dawo?"


Bai jira me zaice ba ya wuce sabgar gaban shi, tun daga ranar kuma Khadija ba ta sake komawa gidan ba, dan lokuta da dama ta kan ji ta na so taje saboda tsohuwar da tsohon masu kirki da kuma saka mata albarka, amma idan ta tuna Usman sai ta share kawai, a cewar ta wannan ba shi da kirki ko kad'an, gashi da d'acin rai da zuciya, alhalin Usman kuma ba ma mazauni bane, baya cikakken sati a gida bai tafi sabgar gabanshi ba, musamman ma da iyayen ke yawan mi shi magana akan ya yi aure, shi ya sa ba ya son zaman gidan dan duk motsin shi sai suce da ya na da aure da anyi kaza, aure ba shine gabanshi ba, ya na so ya taka wani mataki kafin ya yi aure, shi ya sa ma shekarun shi *talatin da d'aya* ba sa damunshi, k'annan shi mata yan biyu da suke bi mi shi tuni suka hayayyafa a gidajensu, sannan d'aya k'anan shi da suke uwa d'aya ma yayi aurenshi shekara biyu data wuce, k'annan shi mata kuma hudu ne a gidan mazajensu, duk iskancin da suke mi shi ko a jikinshi kam, neman sisi da kwabo yasa a gaba.



*Bayan wata bakwai* Khadija har ta fara karatunta na jami'a (lycée) hankali kwance, ta yi sababbi k'awaye sosai a ciki ne ta had'u da *Barira nagoma* wacce unguwarsu ke kusa da gidansu Usman, duk da Khadija ce ta bige tsohon amma ta manta da abin da ya faru, ranar kawai sun taso daga boko da yamma ta kawo Barira gida akan moton ta, layinda ta shiga dan ya sadata da titi ne ya kawota k'ofar gidan, har zata wuce sai kuma tace bara ta tsaya ta shiga, har ta shiga soron sai kuma ta ji ba ta so ta samu wannan mai d'aure fuskar, da k'arfi ta juya dan ta koma wajen moton ta sai kawai wata yarinya k'arama data shigo da gudu su ka ci karo, fad'uwa yarinyar ta yi ta fashe da kuka saboda buguwa da kanta ya yi da bango, yanda ta tsala kukan ne ya sa Khadija yin saurin durk'usawa ta rumgumo yarinyar ta na lallab'a ta, gidan kuma akwai mutane har da Hassana ma ta zo, kuma d'iyar tace aka bige, da sauri su ka fito soron dan gani me ke faruwa, har da Usman wanda zuwan shi kenan daga *zinder* ko d'aki bai shiga ba, lafiya lafiya? Kowa ke tambaya, Khadija kam tsaresu ta yi da ido sai da Usman ya daka mata tsawa yace "Wai ba tambayar ki ake ba? Me ki ka mata?"


Tsaye ta mik'e lokacin da Hassana ta d'auke yarinyar daga jikin Khadija, kallon tsohuwar ta yi tace "Dan Allah ku yi hak'uri, wallahi ban lura da ita bane, kuma ta shigo ta na gudu."


Hassana ce tace "Ba komai haba, ai yaran kenan, bare ma *Fadila* da bata tafiya sai gudu."


Usman ne yace "Baiwar Allah, in dai har za ki ci gaba da saka wannan gilashin, to fa ki sani wallahi kullum ki na cikin karo da mutane ki na ji musu ciwo, me zai hana ki cire shi ki aje ko kuma ki dinga hutawa? Shi fa gilashi ba dan sakawa kullum bane, yawan anfani da shi ya na b'ata ido, wanda su ka san abun ma za ki ga akwai lokacin da kad'ai suke anfani da shi, amma ba kamar ke ba sai kace makauniya kina ta fama da abu kullum a ido, wallahi za ki ragewa kanki kud'i ne idan idonki su ka samu matsala."


Khadija da tunda ya fara magana ta kafe shi da ido, sai da ya gama tasa hannu ta cire gilashin tasa hijabinta ta share k'wallan da suka taru a idonta, kallonshi ta yi amma sam ba ta iya ganinshi da kyau, wasu hawayen ne suka sake taho mata, kallonshi tayi tace "Ni ma ba haka kawai na ke sakawa ba, larurar ido gare ni, sai da shi ne na ke iya gani, ku yi hak'uri dan Allah idan na b'ata ran ku, zan wuce ne dama nace bara na biyo mu gaisa, da nasan haka za ta faru da ban biyo ba."


Ta na fad'a ta juya ta na ci gaba da share k'walla, ta na sauke hannunta k'asa ashe har ta kai wajen moton ba ta sani ba, sai kuwa ta kai mi shi karo motonta fad'i ita ma ta fad'a mi shi, duk da taji zafi haka ta tashi, da saurin mutanen cikin soron su ka fito dan taimaka mata, banda Usman da ya kasa motsawa sai kallonta ya ke, Mannir zai taimaka ya d'aga mata moton tace mi shi "Ka bar shi kawai nagode."


Gilashin ta saka ta d'aga moton ta tayar ta wuce, daga wannan ranar ta yanke ba zata sake zuwa gidan ba ko da hanya ta d'auko ta, yayin da Usman kuma ya sha fad'a sosai wajen malam Ali ya kuma ce sai ya je har gidansu ya bata hak'uri, baiyi musu ba yace zaije, dan ya faranta mu su kamar yanda ya saba, a daren ranar yaje gidan ya kuma aika aka mi shi sallama da ita, da farko kamar ba zata fito ba saboda ba ta yanayin dad'i, sai kuma mama tace taje ta gani watak'ila bak'o ne, fitowa ta yi da doguwar rigar shadda da mayafi, ta na ganinshi ta daskare wuri d'aya har saida ya sauko daga kan moton ya same ta, ita dai kallon shi take yayin da yace "Sannu ko?"


Da kai kawai ta amsa tana ci gaba da kallonshi, gyara tsayuwa ya yi yace "Kin yi mamakin gani na ko? Ba abun mamaki bane, na zo ne na baki hak'uri akan abin da ya faru d'azu, bayan dogon tunani da nazari na gane ban kyauta ba, ina afuwar ki dan Allah ki gafarce ni, rashin sani ne da kuma rashin fahimta."


Ko ba komai ta ji dad'i da ya bata hak'uri, cikin taushin murya tace "Ba komai wallahi ya wuce ai."


D'an sunkuyowa ya yi yace "Kin tabbatar ya wuce?"


Kallonshi ta yi da murmushi tace "Na tabbatar."


Saida ya sake nuna ta da hannu yace "Kin tabbata ba za ki sake kallo na a matsayin marar kirki ba?"


Da murmushin da ya fito da hak'oran ta tace "Na yi alk'awari."


"To shikenan nagode sosai da ki ka yafe min."


"Ni ma nagode." Kallonshi ta yi tace "Sai anjima."


Ba ta jira ta ji me zaice ba ta juya za ta shiga kuma sai ta ji oda a bayan ta, ta na juyowa ta ga yayan ta ne Ashir, kashe motar ya yi ya fito daga cikin, "inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Cewar Usman, dan har zuciyar shi bai so Ashir ya gan shi k'ofar gidan nan ba kuma tare da k'anwar shi, sai ya d'auka akwai wani tsakaninsu ne, matsawa Khadija ta yi kusan shi ta rik'o hannun shi tace "K'afafu na sannu da zuwa."


Dariya ya yi yace "Yau ko k'afafun nan na ki sun gashi sosai dan sun sha yawo."


"Sai muje nasa aunty *Rahama* ta gasa maka su ai." Ta fad'a ta na jawo shi, zaro ido ya yi yace "Kai, ka kai, ka kai, wa na ke gani kamar Usman."


Murmushi kaxai Usman ya yi kafin Ashir ya ba shi hannu su ka yi musabaha da gaisuwar anjima ba'a had'u ba, saida suka gama ya saki hannun Khadija yace "Auta zan shiga ciki, idan kin gama sai ki zo kiga tsarabar ki."


Turo baki ta yi ta juya masa baya, dariya ya yi ya aza duka a kafad'ar ta yace "Ayi hak'uri, Nana Khadija baiwar Allah."


Juyowa ta yi ta na fara'a tace "Wannan sunan ya fi dad'i, amma wani auta auta kamar k'aramar yarinya."


Kallonta ya yi yace "Um! Wato ke kin girma ko? To ya ki ke dani tsoho."


Tura shi ta yi ya nufi cikin gidan tace "Dallah ni dai ka shiga ciki."


Dariya ya yi ya wuce ya na ma Usman sallama, sai da ya shige ta kalli Usman tace "Ni zan shiga ciki, sai anjima."


Shigewa kawai ta yi ta bar shi nan, saida ya ga shigar ta ya hau moton shi ya wuce shi ma, daga shi har ita babu mai jin wani bak'on alamari a game da d'an uwan na shi, tana shiga ciki ta samu yan uwanta su ka baje suna hirarsu kamar yanda su ka saba kullum, Khadija ce ta fara tashi ta je ta kwanta, har za su tashi sauran Ashir ya dakatar da su, bayan ya mu su bayani akan abin da ya gani ne ya d'ora da "Nasan Usman sosai, dan mun yi aji d'aya da shi, har yanzu baiyi aure ba saboda abin da ya sa a gaban shi, ganin shi tare da yer uwar mu alkairi, dan gaskiya na yarda da tarbiyar shi da kuma dattakon iyayensu, sai dai Usman ba kamar sauran maza bane, zai iya nuna cewa kamar Khadija ba tsararsa bace irin tafi k'arfin shi, ni kuma a gani na Khadija ce za ta yi sa'ar samun miji kamar shi, sannan burin mu anan dukanmu bai wuce mu bawa Khadija mijin daya dace da ita ba, sannan mun wa mahaifin mu alk'awarin kula da ita har zuwa lokacin da za mu damk'a ragamar kula da ita a hannun mijin da ya dace, da wannan nake neman shawararku da idan kun amince, sai mu je har gidansu Usman sannan mu nema wa yer uwar mu auren nagartattacen mutum, ba fad'uwa mu ka yi, kuma ba abun kunya bane dan mu muka fara zuwa da maganar, hakan ba yana nufin mun arhantar da ita bane, sai dai ma k'ok'arin kare mutumcinta, ko ya ku ka gani?"


Bashir ne yace "Tunda dai har ka yarda da shi ai ina ganin ba wani abu, kawai ayi d'in, burinmu shine ganin Khadija ta dawwama cikin farin ciki."


Kallon mama Ashir ya yi yace "Mama ba ki ce komai ba?"


Murmushi ta yi tace "Me zance ni, bayan iyayenta kuma yan uwanta sun gama magana, babu abin da zance sai dai addu'a da kuma fatan Allah sanya alkairi."


"Ameen mama." Suka amsa a tare, Ashir ne yace "Yanzu tunda dukan mu mun amince, gobe zan je na samu kawu *Kabir* na fad'a ma sa, in ya so sai muje tare, amma ku sani dukanmu za mu tafi neman auren nan."


Naseer ne yace "Kar ka damu ai, ni ne ma gaba saboda munfi kusa da ita."


Habeeb ne yace "Kai dallah can malam, kowa a gidan nan ai yasan Khadija tafi shak'uwa dani."


Wani wawan tsaki Ashir ya yi yace "Aikin banza, ai sai kuyi kuma, amma da yanzu za'a tambaye ta na tabbata ni ne farko."


Bashir ne yace "Hum! Kun manta sunan da ta ke kira na da shi ne?"


Dariya su ka yi sai Mansur ne yace "Dan ta kira ka da hannayenta sai me?"


"Sai ya na nufin mahimmanci na a gareta." Ya fad'a har da juya baki, dariya Mama ta yi ta Mik'e tace "Sai da safenku."


"Sai da safe mama." Su ka amsa.


*Wannan* k'aramar magana ita ce ta girmama har aka fara shigar da maganar aure tsakaninsu, sai da komai ya daidaita ana shirin kawo akwatina kad'ai yan uwan su ka sanar da Khadija a tunaninsu sun mata (surprise) za ta yi murna, Khadija ta girgiza, amma jin dalilinsu na yin haka domin farin cikin ta ne kawai, a lokacin kukan da take bawai na farin ciki bane, amma saita share ta nuna musu na dad'i ne take, dukansu ta had'a ta rumgume tace "Na yi sa'ar samunku a matsayin yan uwa."


A wajen Usman kuma har ya fara bore ya na nuna baya so, ya fad'a mu su kuskuren fahimta ne kawai, amma ko zaiyi aure yanzu ba yarinya kamar Khadija ya ke so ba, sai mahaifiyar shi ce ta zaunar da shi ta nusar da shi alfanu da alkairan da zasu iya tasowa sakamakon auren shi da Khadija, amma duk da haka sai da yace "Hajia, wallahi na tabbata ita ma yarinyar nan bata so na, zaifi kyau ku bar kowa ya zab'i wanda ya masa, amma kar ku ce za ku had'a mu saboda rashin fahimtar da Ashir ya yi."


Sosai ta tank'wara shi har ya samu ya sauko ya amince, amma yace saboda sune kawai, ita kuma mahaifiyar ce tace "In dai kuma har saboda mu kayi, to ka sani ba kai ba nadama har abada, insha Allahu wannan auren zai zamar maka alkairi, ba za ka tab'a kuka da zab'in mu ba."


Magana ta kankama sosai, amma ango da amarya babu wani mai shiri ko farin ciki, an saka wata *hud'u* mai zuwa, yan uwan amarya da mahaifiyar ta sun dage wajen shirin bikin autar su, gaisuwa kad'ai ke had'a Usman da Khadija a waya, su na gaisawa zata aje wayar ko shi ya aje, kuma kamar an k'yasta ashana sai gashi an cinye wannan lokacin da aka saka, ba dan Usman ya so ba ya baro harkokinshi ya zo sabgar bikin shi, fad'an irin tartsatsin da aka yi a bikin ma b'ata lokaci ne, dan yan uwa biyar sun yi bajinta sosai wajen k'ayatar da yer uwarsu, sai dai kamar yanda Usman ya ke ganin baiyi wani bajinta ba sosai, hakan ya sa yace ba ya buk'atar komai daga gare su shi ma sai amaryar kawai, hakan kuma ya birge mutane da dama, haka akayi wannan walima aka kai amarya d'akin mijinta, kuma duka yan uwa biyar d'in su suka saka k'anwar su tsaka suka iza k'eyar ta har ta shiga d'akin ta.


Gidan malam Ali da shima ya gada a wajen na shi tsohon, matsakaicin fili ne sai d'aki ciki da falo, sai ban d'aki a farfajiyar gidan da kuma k'aramar runfar da aka yi ta tôle aka aje kayan abinci ya zama wajen girki, d'akin nan tamtsam aka mi shi da kaya na gani na fad'a, bayan yan kai amarya su tafiyar su aka bar ango da amarya, shima fita ya yi kafin dare ya k'ara yi ya dawo gidan.


Zaune ya same ta akan gado fuskarta rufe, k'arasowa ya yi tare da "Amincin Allah ya tabbata a gare ki."


Wayu ta had'e ta rintse ido gabanta na fad'uwa tace "..



*Allah ka mana kyakyawan k'arshe.*

14/01/2020 à 14:03 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *11*




"Kai ma haka."


A hankali ya zauna bakin gadon ya aje ledojin hannun shi, kallonta ya yi ya d'anyi shiru, dama dai fuskarta a rufe take, dan haka ita ma ta yi shiru, kowa da abin da yake sak'awa a ran shi, kusan minti sha biyar su ka d'auka a haka kafin ya sake kallonta ya d'anyi gyaran murya yace "Ko za ki iya bud'e fuskar ki."


Shiru ta yi kamar ba ta ji ba kuma bata bud'e ba, numfashi ya sauke cike da nuna kasala ya zuro hannayenshi ya yaye mayafin, fad'uwar gabanta ne ya nunku, shi kuma ya kafe fuskarta da  babu ko d'igon kwalli da ido, sai dai lumshe ido ya yi saboda matsowar da ya yi kusanta k'amshin turaruka ne suka bigi hancin shi, ajiyar zuciya ya sauke yace "Ya kamata muje mu yi alwala ko?"


Ba tare da tace komai ba ta fito da k'afafun ta daga tank'warewar da ta mu su ta sauka daga kan gadon, bin bayanta ya yi su ka samu buta su ka yi alwala su ka dawo, hijab ta saka ta shinfid'a sallaya ya shiga gaba ya kabbara sallah, raka'a biyu su ka yi su ka sallame, juyowa ya yi ya na fuskantarta ya zuro hannunshi zai dafa kanta dan yin addu'a, zabura ta yi taja baya sosai, da sauri ya janye hannun shi yace "Lafiya?"


Girgiza kai ta yi alamar ba komai, shima girgiza kan ya yi yace "Kar ki damu, ba abinda zan miki, addu'a zan mana."


Gyara zamanta ta yi shi kuma ya rik'e kanta ya yi addu'a kamar haka _"Allahuma inni as'aluka khairuha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi."_ Sakin ta ya yi ya juya ya janyo ledar gabanshi ya bud'e, har zata tashi yace "Zauna."


Yanda ta ji muryar shi ya sa ta zauna ba musu, gasassar kazar ya d'auka yakalle ta yace "Bismillah, ki ci."


Murya na rawa tace "Na k'oshi."


Da mamaki ya kalle ta yace "Kamar ya kin k'oshi? Nasan ki na jin yunwa, ga cikin ki nan ma ya nuna."


Da sauri ta k'ara k'udundune cikinta cikin hijabi ta na kallon k'asa, juyin duniya Usman ya yi amma tace ba ta cita k'oshi, abu d'aya ya fahimta shine tsoron shi take, sai dai tsoron me bai sani ba, saboda yanda had'uwar su ta kasance ne ko kuma tunanin zai mata wani abu a daren nan? Idan har hakane zaifi ta kwantar da hankalinta, ba ya da tunanin tauye hakk'in ta ko d'aya, sai dai ba zai kusance ta da wuri ba, dan haka ya mik'e yace "Zan fita waje, ki samu ki ci ko kad'an ne, idan kin gama za ki iya kwanciyar ki, ni zan kwanta a falo."


Ko d'agowa ba ta yi ba bare ta kalle shi, ta na ganin ya fita ta mik'e ta tura k'ofar d'akin ta rufe ba tare da ta saka makulli ba, rufe ledar kazar ta yi sannanta canza kayan jikin ta ta kashe fitila ta kwanta, ba tare da ta cire gilashinta ba ta shiga duniyar tunanin irin zaman da za ta yi da mutumin da ba ta so, da wannan tunanin bacci ya d'auke ta ba tare da ta cire gilashin ba, shi ma a falo ya zauna tunani iri-iri a zuciyar shi, daga bisani ya gaji ya kwanta bacci ya d'auke shi.



*Kiran sallah farko* Khadija ta farka, bayan ta yi salati tare da addu'ar tashi daga bacci _"Alhamdulillahi-lazi ahayana, ba'ada ma amatana, wa'ilaihi-nushur."_


Gefen damanta ta lalaba dan d'aukar gilashinta amma sai ta ji ba komai, da sauri ta gyara zama zamanta ta ci gaba da lalabawa kowace kusurwa, Usman da ya gama saka kaya a falo ne ya shigo da niyyar d'aukar sallaya ya fice, ta sauko daga kan gadon kenan dan ta lalaba akan coiffeuse (dressing miror), da sauri ya k'arasa gaban madubin inda ya cire ya aje mata, d'auka ya yi ya mik'o mata yace "Karb'i gashi nan."


Hannu ta zura dan dama ga duhun d'aki ga kuma matsalar idon ta, a k'irjin shi ta d'ora hannu da tunnin ta kai hannunta daidai, rik'e hannunta ya yi ya d'ora mata gilashin ta bud'e shi ta saka, kallon shi ta yi tace "Nagode."


Ba wata fara'a yace "Ba komai, laifi na ne da na mi ki nesa da shi."


Jin kiran sallah ya sa yace "Na tafi masallaci, sai na dawo."


Murya k'asa k'asa yace "A dawo lafiya."


"Allah ya sa." Ya fad'a ya na ficewa daga d'akin, fita ta yi ita ma ta d'auro alwala a tsakar gidan ta dawo ta yi sallah ita ma, ta na kammalawa ta koma d'akin ta d'an gyara in da ta kwanta sannan ta shiga wanka, ta na shigowa falon da d'aurin k'irji da hijab ta samu Usman zaune a falon, sinne kai ta yi ta shige ciki dan ta shirya, doguwar rigar shadda ta saka da d'an kwalinta ta fito da tunanin d'ora mu su abin kari, har k'asa ta durk'usa ba ta had'a ido da shi ba tace "Me za'a dafa?"


Kallon ta ya yi yace "Ina kwana?"


K'ara k'asa da kai ta yi saboda kunya, dan ta san gatse ne ya mata saboda ba ta gaishe shi ba, cikin rawar murya tace "I...na, kwa...na."


Tab'e baki ya yi yace "Ba sai kin damu kan ki ba, yanzun nan za'a aiko da abin karin kumallo wa ke inji Hajia."


"Nagode." Tace ta na mik'ewa ta koma d'aki, ba jimawa Mannir ya kawo mu su abinci, sai da ya gama zubawa in da ya dace ya shiga d'akin ya same ta zaune bakin gado yace "Ki zo ki ci abincin."


Tashi ta yi ta sake d'aukar hijabinta ta fita, a tsakiyar falon ta samu ya aje abincin, juyawa ta yi ta kalli teburin da aka siya mata mai kukera shida, matsawa ta yi ta zaune daga gefen shi yanda basa fuskantar junansu, har ta d'auki cokali ta ji yace "Ki ci da hannu yafi."


Kallon shi ta yi sai kawai ta aje cokalin tasa hannu, haka dukansu suke cin abincin a hankali babu mai magana har Khadija ta cire hannu za ta mik'e yace "Zauna."


Zaunawa ta yi ta na kallon shi da sauraren shi, kallonta ya yi sosai ya matsa kusa da ita ya deb'o lomar abincin da hannun shi ya nufi bakin ta, kawar da kai ta yi tace "Na k'oshi fa."


Wani iska ya fuszar yace "Nana Khadija."


Yanda sunanta ya fita daga bakinshi ya tilasta mata kallon fuskarshi ita ma, da sauri ta d'auke nata idon saboda kallon da ya ke mata, d'orawa ya yi da "Ke amana ce a gare ni, ba zanyi duba da yanda auren mu ya kasance ba, dole na sauke duk wani hakk'in ki da ke kai na, jiya ba ki ci komai ba, yau ma gashi ba kici mai yawa ba, anjima aka fara shagalin damu zai iya saka ki jin jiri, dan haka bud'a bakin ki na ba ki abinci, ba wani abu bane a gare ni, ina da burin bawa duk matar na aura abinci da kai na, kuma ke ce wannan matar."


Sake d'aga ido ta yi ta kalle shi, a hankali ta kai bakinta ga hannunshi da ya mik'o mata abincin, sosai Usman ya dinga d'irka mata abincin nan ta na amsa, ta k'oshi sosai, amma ta kasa fad'a masa saboda yanda fuskar shi ke had'e ko kallonta bayayi, lomar da ya saka mata a baki k'in had'e ta tayi, wata ya d'ibo zai saka mata a baki ta k'i bud'a bakin, d'an k'aramin tsaki yaja yace "Karb'i mana, sai na ga cikin ki ya taso, ko ki na so yan biyar su fara jin haushi na tun ba aje ko ina ba?"


Da k'yar ta tura lomar zuwa mak'ogwaro ta amshi wacce ya mik'o mata, ta na fara taunawa sai kawai ta ji amai ya taho mata, da gudu ta mik'e ta fita farfajiyar gidan ta amaye kaf abincin da ta ci, da sauri Usman ya bi bayanta cike da tausayi, dan tunanin shi ba ta cika cikinta irin haka shi ya sa, ruwa ya bata ta kurkure baki ya na jera mata sannu, da kan shi ya had'a mata ruwan shayi tasha, har zai tattare kwanukan ta tashi ta hana shi da kanta ta d'auke, ganin dai ba wata matsala ya sa ya mata sallama ya fita dga gidan, kamar kuma fitarshi ake jira dama sai ga Kaltume da Barira sun zo, dan mama ce tace su zo kafin rana mutane su zo, tun da ba ta da yer uwa mace da za ta iya zuwa kafin zuwan mutane.



*Yau* ma haka aka yi shagalin damu aka gama, da dare kuma Rahama matar Ashir da *Aisha* matar Bashir su ka mata kwalliya kafin su ka bar gidan, har *11* dare ba Usman ba labarin shi, sai kawai bacci ya suri Khadija ba tare da ta shirya masa ba, ta na nan har sai da ya shigo, yanda ya same ta saita bashi tausayi, mayafin jikin ta ya fara cire mata a hankali kafin ya cire mata takalmin k'afar ta, a hankali ya tallabo k'afafun da nufin d'ora su akan gadon sai ta farka, da k'arfi taja baya ta had'e da gadon har tana neman fad'uwa, yanda ta ke kallonshi a tsora ce ya sa yace "Khadija, tsoro ki ke ji?"


Girgiza kai ta yi alamar a'a, tab'e baki ya yi yace "Shikenan, ki tashi ki cire kayan jikin ki sai ki zo ki kwanta."


Ganin ya juya zai fita ya sa tace "Kai fa?"


Juyowa ya yi yace "Ni fa me?"


"Ina nufin ina za ka kwanta kai?"


Murmushin mugunta ya saki ya kalli gefen ta yace "Anan mana, ko ki na so na sake kwana a falo ne?"


Shiru ta yi ba za iya cewa eh ba, saboda kar ya ji ba dad'i, kayan bacci ya d'auka ya fita falo dan canzawa, ita kuma k'in sauya kayan ta yi har ya sake samunta a haka, kashe wutar d'akin ya yi ya kwanta gefe ya na satar kallon ta, ba ta kwanta ba sai ma k'ara rakub'ewa da ta ke, kallonta ya yi yace "Ki kwanta Khadija, daga ni sai ke ne fa a gidan nan, kuma a cikin d'akin da babu wanda zai iya taimakonki, idan na so ai zan iya yin komai a d'an k'ank'anin lokaci, amma ba yanzu ba kinji, ki kwanta ki yi bacci kawai."


Ya na fad'a ya juya mata baya ya na ci gaba da murmushin gefen labb'a, bacci ne kad'ai ya fizgi Khadija yasa ta kwanta ba tare da ta sani ba, sai dai baccin bai je ko ina ba Usmn ya tashe ta yin sallah.


Ko da ta yi sallah ya fita a runfar nan ta samu akwai kayan abinci sosai, sassauk'an girki ta yi har ta gama bai shigo ba, akan teburi ta aje ta shiga wanka, ta na fitowa yau ma kamar jiya zaune ta same shi, d'aki ta wuce ta shirya cikin riga da siket na shadda sun mata kyau, ta gama shafe jikinta da turare za ta fito Usman ya shigo, cak ta tsaya dan ya tare k'ofar fitar, k'asa take kallo shi kuma ya na kallon fuskarta, kamar daga sama ta ji yace "Ki je ki yi kwalliya, ko da ba kya ra'ayinta ni ina so."


Galala ta bishi da kallo kafin ta zauna gaban madubi, da k'yar ta iya shafa hoda (powder) da d'an jan baki ta tashi ta bar d'akin, ta na zaune akan kujera taga fitowar shi, da sauri ta mik'e ta fara zuba abincin a k'aramin farantin da zai wadaci mutum d'aya, zan kujera ya yi ya zauna ya na kallon ta har ta gama zuba mi shi, wani farantin ta d'auka za ta zubawa kan ta yace "Ba buk'atar ki zuba na ki, mu fara cinye wannan."


Ta gilashi ta d'aga manyan idon ta ta kalle shi ta buntsuro faffad'an labb'an ta, zaunawa ta yi ta d'auko cokali za ta saka yace "Na fad'a mi ki ai, ba na cin abinci da cokali, zan so ki saba da hakan, dan ci da hannu ma sunna ce."


Mayarwa ta yi ta aje ta na kallon k'asa, hannu ya sa ya fara ci tare da bismillah ya kalle ta yace "Sa hannun ki mana."


Kamar wacce zai cinye haka ta saka hannu ta na tsakuro abincin tana sakawa a baki, ganin haka ya sa yace "Ki na so sai na baki da kai na kenan?"


"A'a." Ta fad'a da sauri ta na kai wata lomar bakin ta, d'an gyaran murya ya yi ya cire hannun shi ya na kallon ta yace "Nana Khadijatul Kubra."


Kallon shi ta yi jin wani cikakken suna da ya kira ta da shi, a hankali tace "Na'am."


Cikin nutsuwa yace "Kinga wani ikon Allah ko? Auren mu za mu iya kiran shi a bagtatan, domin kuwa babu wanda ya tsammani hakan daga mu har iyayen mu, amma Allah ya sa mun zama miji da mata sanadiyar had'arin da ku ka samu ke da mahaifi na, zan iya kiran haka da k'arfin da ke cikin rubutun *alk'alamin k'addara*, Khadija, tunanin hakan kad'ai ya isa ya samu mu rumgumi wannan k'addarar, dan ina da tabbacin wani babban al'amari zai faru tsakanin mu, sannan iyayen mu sun bimu da addu'ar mu da fatan alkairi, da wannan na ke rok'on ki da ki kwantar da hankali mu yi zaman aure, ina so mu yi zaman da iyayen mu za su yi farin ciki da mu, idan mu ka yi haka insha Allah Allah ba zai barmu mu wulak'anta ba, sannan maganar karatunki wannan ba matsala bane, za ki ci gaba insha Allah, sai dai kamar yanda ki ka sani ni ba mazauni bane, ba lallai na dinga sati d'aya ko biyu a cikin gidan nan ba."


Cikin ladabi tace "Na yarda na yi auren nan saboda yan uwa na, dan haka zaman ba zai gagare ni ba insha Allah."


"Alhamdulillah, hakan ya yi kyau, Allah ya bamu zaman lafiya, Allah ya azurtamu da zuri'a ta gari."


Da sauri ta kalle shi wanda shi ma ita ya ke kallo, da azama ta sauke nata idon ta na murmushi, shi ma murmushin ya yi ya lek'a fuskarta yace "Ya dai Hajia, ko ki na mamaki ne?"


Girgiza kai kawai ta yi, loma ya yanko ya nufi bakinta da fad'in "Maza bud'a bakin."


Amsa ta yi cike da kunya kafin yace "Wai ni ne ba'a lele kenan?"


Kallon shi ta yi cikin rashin fahimtar maganar shi, d'orawa ya yi da "Eh mana, har yanzu ke ba ki saka min a baki ba, ko kunya ta ki ke ji?"


Ai kuwa kunyar ce ta rufe ta ta mik'e da sauri za ta bar wajen ya rik'o hannunta, ba tare da ta juyo ba yace "Zo zauna to na hak'ura."


Janyo hannunta ya yi bai direta ko ina ba sai a kan cinyarshi, wani numfashi ta saune ta rufe idon ta ruf ta kasa ko numfashi bare motsi, shi kan shi wani sabon al'amari ne ya ziyarce shi, amma sai ya share saboda ya na so ta saki jiki da shi, dan ya lura har yarinta ma na damunta, cikin zolaya yace "Kinga ki bud'a idon nan, ko kuma dai..."


Shiru ya yi ya juya bayan ta ya saka bakinshi a zip d'in rigarta ya jashi k'asa, jin ya na zame mata zip ya sa tayi wni dogon numfashi ta bud'a ido, ta so ta d'aga daga jikinshi sai ya k'i bata dama, jin ya na ci gaba da zame shi ita kuma a ganinta abun kunya ne ya ga rigar nonon da take sakawa sai kawai ta fashe da kuka, jin yanda ta b'arke baki ne ya sa ya tsaya ya na kallon fuskar ta, da sauri ya mayar mata ya fara goge mata hawayen yana fad'in "Dan Allah ki yi hak'uri Khadija, banyi haka da wata manufa ba, ki yi hak'uri ki daina kukan to, na daina, shikenan?"


Share hawayen ta yi ta tashi daga jikin shi ta koma d'aya kujerar ta na ci gaba da share hawaye shi kuma yace "Ki rufa min asiri Khadija, yanzu me ki ke tunanin zai faru idan yan biyar d'in ki su ka shigo su ka same ki kina kukan nan? Ina tabbatar mi ki rataye ni za su yi a jikin pankar nan." Ya fad'a ya na nuna pankar sama da ke falon.


Kallon shi ta yi tace "Ka yi hak'uri to." Yanda ta yi magana cikin shagwab'a ba k'aramin birge shi ta yi ba, murmushi ya yi yace "Ai ni ne da baki hak'uri, tun da na fahimci ba kya so mu k'ara samun kusanci."


Haka dai suka kammala ya mik'e zai fita ya fito da jikka uku ya bata, kallon shi ta yi tace "Na miye wannan?"


Murmushi ya yi yace "Da taimakon Ashir ni ma yau gashi ina bayar da kud'in cefane."


Dariya ta yi tace "Ai ba sai ka bayar ba, akwai duk abubuwan buk'ata."


Sunkuyowa ya yi yace "Sai abin da ba'a rasa ba ko?"


Shiru ta yi ya janyo hannun ta ya d'ora mata kud'in yace "Kar ki rage min darajata mana."


Murmushi ta yi tace "Angode, Allah ya saka da alkairi."


D'agota ya yi tsaye ya rumgume ta, yarrrrr, dukansu suka ji saboda dukansu shine karo na farko, shiru su ka yi kowa da abin da ya ke ji a game da d'an uwan shi, kamar ba za su rabu ba sai kuma suka raba jikin su, ba su yarda sun kalli juna ba sai Usman ne yace "Wannan ranar ita ce iyaye na ke min burin shiga, su na yawan fad'a min idan na yi aure ko kud'in cefanai na bayar idan har na yi sa'ar samu mace ta gari, to tabbas za ta gode min akan hakan tare da min addu'a."


Shiru ta yi ita dai har yace "Ni zan tafi, sai na dawo."


"Allah ya kiyaye, Allah ya tsare ka ya bada abin da aka je nema."


"Ameen ameen, nagode sosai." Har ya juya zai fita ya sake juyowa ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta, ficewa ya yi ya bar ta tsaye ta na tunanin sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a cikin k'ank'anin lokaci, kayan da suka b'ata ta fito da su ta wanke ta gyara wurin sannan ta d'an zauna ta huta, ba jimawa sosai ta d'ora girkin rana, ita kad'ai ta gama aikinta ta yi wanka ta shirya, ta na zaune ita kad'ai yaran mak'otansu suka shigo su ka tayata hira, har la'asar ba Usman ba labarin shi, ta idar da sallah ta d'ora girkin dare kenan Hassana da Husseina su ka zo tare da Aziza lokacin ba ta fi shekara uku ba a duniya, wannan abincin ta juye mu su suka ci suna ta hira, zuwa k'arfe *biyar* na yamma su ka tashi tafiya, turaren wuta da na jiki da kud'i ta basu su shiga taxi, haka suka fita su na fad'an ta da alkairi cike da k'aunar ta dukansu, har suna mamakin yanda ta so su bar Aziza wajen ta, aikinta ta ci gaba da yi har ta na daf da k'arasa miya, kamar jiran fitarsu ya ke sai gashi ya shigo gidan, cike da gajiya da kasala ya zauna akan kujera kusa da ita ya na sauke numfarfashi ya na cire hular kan shi yace "Wallahi na gaji sosai."


Cike da kulawa ta kalle shi tace "Sannu, aiki ka yi sosai?"


Ido rufe yace "Wallahi ina fita *Murtala* ya fizge ni mu ka tafi wani k'auye, na d'auka zamu dawo da wuri amma Allah bai nufa ba."


"Ayyah! Sannu." Kallon ta ya yi yace "Ko zaki had'a min ruwan wanka?"


"To, to." Ta fad'a ta na tashi kamar za ta ruga a guje, ta na kai mi shi ruwan ta d'auki kwandon sabulu ta kai mi shi da towel, dawowa ta yi ta d'ibo ruwan sha ma su sanyi ta durk'usa gaban shi tace "Ga ruwa ka fara sha to."


Karb'a ya yi yace "To zan sha saboda daga hannunki su ka fito, amma bayan wanka na fi buk'atar abinci gaskiya."


Sororo ta kalleshi ta had'e yawu, rarraba ido ta fara yi gabanta na fad'uwa, dan ba ta saune miya ba ma bare ta d'ora macca, ko da yasha ruwan ya mik'e zai wuce tace "Ka fad'a min me za ka iya ci yanzu na dafa maka?" Ta fad'i hakane ko da zai ci wani abu mai sauk'in sarrafawa.


Juyowa ya yi da mamaki yace "Ban gane ba, ki na nufin ba ki d'ora komai ba tun da na fita?"


Cikin nutsuwa tace "Wallahi na d'ora, na yita jiran shigowar ka amma shiru, sai kuma su aunty Hassana su ka zo kawai sai na juye mu su abincin."


Murmushi ya yi yace "Wai su aunty, Hassana fa k'annai na ne su, ba sai kin kira su da aunty ba."


Cikin jin kunya tace "Amma ai ni sun girme ni."


"Duk da haka, dan na tabbata da zasu fita da ke aka tambaye su wacece ke? Za su ce matar yayan su ce, ke ma kuma dole ki kirasu da hakan."


"To na ji, yanzu dai ka shiga ka fito."


Dariya ya yi ya wuce, ta na ganin shigarshi ta gaggauta k'arasa miyar ta, da sauri ta d'ora ruwan macca, ya na fitowa ruwan sun taso ta zuba maccar, cikin sauri ya shirya ya fito zai fita, rik'e shi ta yi da hira tace ya koma ya zauna za ta bashi wani abun mamaki,  zaune ya yi ya na kallo yana jiranta, baifi minti sha biyar ba ta shigo da kwanuka masu kyau da gani ta aje gaban shi ta d'auko ruwa da lemo da faranti ta aje masa, sai da ta zauna gaban shi zata zuba mi shi yace "Amma ina ki ka samu wannan?"


Ba tare da ta kalleshi ba tace "Abincin dare ne za ka ci tun yanzu."


Dariya ya yi yace "To idan daren ya yi kuma ya zanyi?"


"Sai na girka maka na safiyar gobe ka ci."


Dariya ya yi sosai yace "Da alama zan cinye abinci na kafin kwana na ya k'are."


Dariya ta yi sosai har hak'oran ta na fitowa waje sosai, duk da ba ta jin yunwa sai da ya takura ta ta ci abincin tare da shi, daga lokacin kam ta yarda cewa ba zai iya cin abinci ba tare da ita ba, ya na gamawa hira su ka dinga yi kamar dama sun saba har saida magrib ta gabato kad'ai ya fita.



*Allah ka mana kyakyawan k'arshe.*

18/01/2020 à 17:42 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *12*



Da dare ma tare su ka ci abinci su ka ida su ka tab'a kallo, ko da dare ya k'ara yi Khadija ta fara tashi ta yi shirin kwanciya, ta na gamawa ta kwanta ta rufe ruf dan ta nuna ta yi bacci, sai da aka d'auki lokaci kafin ya shiga d'akin shi ma ya shirya, kashe wuta ya yi ya kwanta gefen ta, daga yanda Usman ya ji canzawar numfashinta ya tabbatar mi shi ba bacci ta ke ba, dan ya tsoratar da ita ya yaye zanin rufar daga fuskar ta cikin taushi murya yace "Allah yasa matsoraciyar nan ta yi bacci, sai na samu yanda na ke so."


Zunbur ta mik'e zaune ta kafe shi da ido duk da ba ganin shi takeda kyau ba, zaune ya yi ya janyo hannun ta ya na fad'in "Ashe ba bacci ki ke ba, to matso kusa da ni."


Girgiza kai ta yi alamar a'a, k'in matsawa ta yi sai da shi ya matsa daf da ita ya rumgumea jikin shi, shafata ya ke ya na fad'in "Khadija, kinsan me ye aure?"


D'an tureshi ta yi daga jikin ta tana so ya rabuda ita, matseta ya yi sosai yace "Ki nutsu mana, me ya sa ki ka cika tsoro ne? Ni fa mijin ki ne."


Kamar za ta fashe da kuka tace "Ni dai dan Allah ka sake ni, ba na jin dad'i."


Kallon fuskarta ya yi yace "Khadija ba na da tunanin tauye mi ki hakk'in ki, kar ki ga kamar ina takura ki, ina so ne kema ki shaida kinyi aure, sannan ki zama babbar mace, ba zan so ace kin wuce kwana uku a gidan nan ba tare da kinsan a wane matsayi ki ke ba, kumada safe na fad'a mi ki ni matafiyi ne, gobe ko jibi tafiya za ta iya taso min, kuma ba na dawowa k'asa da sati biyu, kinga kenan idan banyi abin da ya dace ba na zama kamar lusari kenan."


Khadija dai shiru ta yi ba tace komai ba sai sauraren shi, daga nan kuma sai ya samu dama ya kuma yi anfani da ita wajen mayar da Khadija babbar macen kamar yanda yace, dukansu sun san bak'on al'amari ne a gare su, shi farin ciki tare da jin wani sanyi a zuciyar shi, Khadija kuma kuka na rad'ad'i da zafin da take ji da ya zama sabon abu a wajen ta, da taimakon shi ya taimaka mata ta gyara kan ta ta tsarkake jikinta, har bacci ya fara d'aukar ta tajiya k'wak'ume ta kamar zai mayar da ita ciki, haka bacci ya rideta amma banda Usman da ya kwana ya na kallon fuskarta ya na shek'a mata sawar albarka da tunanin yanda rayuwarshi ta canza sanadiyarta cikin k'ank'anin lokaci, har aka kira sallah idon shi biyu, sai da ya yi alwala sannan ya zo ya tashe ta a hankali, masallaci ya nufa ita ta yi sallahnta a gida, tun akan sallaya ta kwanta saboda zafin da har yanzu take ji a k'asan ta da kuma bacci, ko da ya same ta bai tashe ta sai da ya tabbatar ya had'a mata ruwan shayi da soyayyen k'wai, tashin ta ya yi da kan shi ya mata wanka duk da ta cije akan bata so amma bai barta ba, haka ya saka mata kaya suka karya, yinin ranar babu inda ya je duk da yaran mak'wabta na shigowa, ya na zaune ya na kallon matar shi na kai da kawo ya na jin dad'i da sabon abu a game da ita.



*Muje da sauri fan's*, sati biyu kad'ai da auren su, amma shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanin su sosai, a cikin k'ank'anin lokaci suka saba da junan su, dan sosai Usman ke sakin jiki da Khadija ya na janta a jikinshi, *sabo tirken wawa*, sai gashi ita kanta Khadija ta saba da shi sosai ta yanda ba ta kl cin abinci in ba tare da shi ba, dan ji take kamar ya zamar mata yan uwan ta biyar, cikin wannan rayuwar farin ciki Usman ya shirya tafiya *zinder*, matuk'a Khadija taji ba dad'i, tunanin ta ya za ta yi rayuwa a gidan ita kad'ai babu shi, ya yi k'ok'ari sosai ya kwantar mata da hankali, amma hakan bai mata ba har sai da tace ya d'auko Aziza ya kawota nan, ya ji dad'in tunanin ta sosai, kuma haka akayi kam, a ranar da zai tafi a ranar aka kawo Aziza da kayan ta, haka ya tafi suka rabu cike da kewar juna.


Ta ji dad'in zaman ta tare da Aziza duk da yarinya ce, ita ke kula da duk d'awainiyar ta, haka ma yan uwan Usman d'in na yawon kawo mata ziyara, haka ma jefi jefi yan yan uwan ta su kan lek'o dan su ga halin da take ciki, a haka har aka kwashe *kwana goma sha biyu*, a kwana na sha uku Usman yace ya na nan tafe, duk da ba ta san ainahin abin da ta ke ji a ran ta ba a game da shi, amma haka ta ji farin ciki ya mamaye ta sosai, a ranar Kaltume ta zo gidan, kuma Kaltume yarinya ce da Allah ya bawa basirar sanin kan tsiyar maza😂, idan ta fad'i wata magana sai ka d'auka babbar mace ce, haka ta samu ta had'awa Khadija wani had'add'en lemun kayan marmari sannan ta zuba mata madara a ciki da *garin raihan*, wuni ta yi ta na shan shi bayan tasha lalle da kitso na tarban miji, bayan nan kuma da kan ta ta taimaka mata suka canza zaman duka kayan d'akin, kuma duk su na aikin ne ta na k'ara fad'a mata irin shiri da kwalliyar da za ta yi, duk Khadija na sauraren ta har ta gama, girki ta d'ora su ka ci kafin ta tafi gida.


Kasancewar shigowar rana zaiyi ya sa tun k'arfe *d'aya* na rana Khadija ta kammala girki ta aje in da ya dace, dama tun da safe Hajia ta aiko Mannir ya d'auki Aziza, hakan ya bata damar sakewa sosai ta yi aikin ta, wanka ta yi ta jima ta na shafawa ta na zanawa da dangwalawa, k'ananan kaya ta saka riga da siket na kanti masu kyau da suka dace da ita, turaren tsintsiya ta kunna sannan ta turara na wuta mai dad'in k'amshi, sai kuma na ruwa (airfreshner) shi ma mai k'amshin lemon tsami ta fesa, ko ina ya d'au harama mai gidan kawai ake jira, k'arfe *uku* cip-cip ta na zaune ta ji sallama, shaida muryar ya sa ta ja dogon numfashi lokacin da ta tuna hud'ubar Kaltume, mik'ewa ta yi ta fice da gudu ta yaye laluben, ba ta tsaya tunanin komai ba ta fad'a jikin shi ta rumgume shi k'yam, cikin farin ciki take fad'in "Sannu da zuwa miji na, sannu da dawowa, na yi farin ciki da dawowar ka gare ni."


Ajiyar zuciya Usman ya sauke ya d'an juya ya kalli *Kabir* k'annan shi da ya d'auko shi daga gidan mota, karb'ar jakar hannun shi ya yi yace "Nagode ko, ka gaishe da su Hajia sai na shigo."


Baki bud'e ta d'ago a hankali dan ganin waye, ta na ganin Kabir ta sake saurin sunne kan ta cikin k'irjin shi ta cakumo rigar shi ta rufe fuska da ita, dariya su ka mata Kabir yace "Matar yaya wai ba dai sati biyu da ya yi baya nan ne ya saki wannan farin cikin ba kamar ya yi shekara?"


Ita kam kunya ce ta sake rufeta ta kuma tusa kan ta cikin k'irjin shi dan ba za ta iya d'agowa su had'a ido ba, murmushi Usman ya yi ya na shafa bayanta yace "Dallah malam ka wuce ka yi abin da na saka ka, sai ka takura min yar..."


Shirun da ya yi ya sa Khadija d'agowa ta kalle shi, had'a goshinsu ya yi wuri d'aya yace "Yar yarinya ta na ke nufi."


Cikin dariya Kabir yace "To sai anjiman ku amare, sai ka shigo d'in, amma ni banga alamar za ta barka ka fito ba."


"Saboda me?" Cewar Usman ya na kallonshi, shafa kan shi ya yi yace "Ai na ga ta yi kewarka ne sosai."


Wannan maganar ce ta sa Khadija juyawa da k'arfi za ta koma d'aki Usman ya fizgota ta fad'a kan shi, dariya su ka saka Usman ya juyo ya kalli Kabir yace "Kai wai za ka fice min ko sai na raka ka ne?"


Sosa k'eya ya yi yace "To ai ba ka ban tsaraba ta bane, ko ka manta yanda mu ka yi da kai kafin ka tafi?"


Sakin Khadija ya yi ya aje jakunkunan hannun shi ya tunkari Kabir ya na fad'in "Ina zuwa, bara ka gani d'an hancin uwa kai."


Maimakon ya fita daga gidan sai ya daka da gudu ya yi hanyar ban d'aki ya na dariya ya na fad'in "Amma fa sai da na fad'a maka banda mai a moto na, kace idan mu ka zo za ka ban kud'i na saka, ka bani kawai sai na tafiya ta na barku ku soyewar ku."


Dawowa ya yi ya kama hannun Khadija ya sunkuya zai d'auki jakunkunan ta tu saurin karb'a ta na fad'in "Bara na shigar ma ka da su."


Kabir ne ya sake fad'in "Dan Allah ka fito ka sallame ni kafin ka shiga d'akin nan, dan bansan me zai faru ba idan ka shiga."


Juyowa ya yi ya kanne shi Khadija kuma k'arasa shiga ta yi saboda kunya,  suna shiga Usman ya tsaya ya na k'arewa d'akin kallo, komai a d'akin kalar kayan d'akin ta ne ma'ana fari da maron, sai telebijin da k'aramin teburin tsakar d'aki ne kad'ai bak'ak'e, ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta yace "Duk wannan shirin na zuwa na ne?"


Cike da kunya tace "Eh mana, sati biyu ba ka gidan ka, ya na da kyau ka tarar da sabon abu dama."


Hannunshi ta kama tace "Muje ka cire wannan kayan ka yi wanka, idan ka fito sai ka zo ka ci abinci."


"Na ci abinci ko ki ba ni abinci?" Ya fad'a ya na tsare ta da ido, murmushi ta yi ta kalle shi tace "Duk yanda ka ke so ai girman ka ne, ka cancanci fiye da haka ma."


Wani basaraken murmushi ya yi ya nufi d'aki yace "Godiya na ke Nana Khadija."


Zasu shiga d'akin Kabir ya d'aga murya daga waje yace "Kai fa na ke jira, wallahi yah Fodio kar ka manta da ni anan waje ka shiga harkar gaban ka, kasan dai nima matar ce da ni ko."


Shima d'ago muryar ya yi yace "Naji me mata, amma aljihunka ba ka da kud'in da zaka saka mai a moto, to waye zai ciyar maka da matar kenan, ko dai hak'uri take ci?"


K'arasa shiga d'akin su ka yi, k'amshin da ya daki hancin shi ne yasa shi lumshe ido, a hankali ya bud'a ido ya sauke akan gadon da shi ma zanin da aka shinfid'a sama fari da maron ne, kallon ta ya yi yace "Khadija kin wahalar min da kan ki dayawa fa."


Murmushi kawai ta yi ba tace komai ba, zai fara cire kaya Khadija ta nufi wajen wata k'aramar jakar ta ta hannu ta d'auko ta fito, a tsakar gida ta samu Kabir ya na ta shawagi shi kad'ai, bud'a jakar ta yi ta ta ciro yan jikka jikka har guda biyar mik'akk'u ta mik'o mi shi tace "Gashi wai a baka."


Da mamaki ya kalli hannunta yace "Inji shi?"


"Eh." Ta fad'a da murmushi, jim ya d'anyi kafin ya karb'a, dan shi dai a iya saninshi Usman na k'ok'ari da su sosai wajen yi mu su buk'atunsu, amma kyauta irin haka dai ta shiga tsakanin shi da su gaskiya da wahala, saboda shi kan shi ma ai ba k'arfi bane da shi, da wannan mamaki yace "Ki masa godiya matar yaya, nagode sosai, ni na wuce."


"Amma ai da ka jira shi sai ku ci abinci ko."


Cike da zolaya yace "Me ki ka dafa ne? Kinsan ni fa ina son abu mai dad'i."


Dariya ta yi tace "To ka tafi tafi kawai, dan nasan abin da na dafa ba lallai ya birge ka ba."


"Da alama dai ba kya so na ci ne, to na hak'ura ma bana ci."


Jin motsin Usman ya sa ta dawo ciki, da sauri ta karb'i abun tsane ruwan hannun shi ta d'auki kwandon sabulu ta kai ban d'akin ta dawo ta cika bokiti da ruwa ta kai mi shi, kallonta ya yi yace "To na shiga na yi ne? Ko kuma madam ce ke da wannan alhakin?"


Dariya ta yi kawai ta kama hannun shi su ka nufi ban d'akin, shine ya fara shiga ita kuma ta tsaya baya tana tunanin ta mi shi wankan kamar yanda k'awar ta tace? Ko  kuma dai ta bar shi ya yi da kan shi, wata zuciyar ce tace ma ta to ai mijin ki ne, ya sanki kin san shi, dan haka babu kunya a wannan fanni tsakanin ma'aurata, shiga kawai ta yi ta fara gurza shi soso da sabulu, haka su ka fito ta gama shirya shi cikin k'ananan kaya na kanti, sai dai la'asar ta matso ya sa shi yin alwala ya nufi masallaci ya fara sallah, ya na dawowa su ka ci abinci tare kamar yanda su ka saba, daga kan teburin ya kashe ta da wani kallo yace "Khadija."


"Na'am." Ta d'ago ta na kallon shi, cikin taushin murya da nuna buk'atar shi yace "Kinyi kewata kuwa?"


Da idon ta nan masu kama da na mai jin bacci ta kalle shi tace "Dan ba ka gan ka akan gado na bane ka fad'i haka?"


Sai da ya d'an lashe baki yace "Da gaske? Kenan kema yanzu haka ki na jin abin da na ke ji?"


Da gangan ta d'auki kofin (cup) lemun shinkafar da ta yi ta zuba a rigarta a tsakiyar maman ta tana kallon shi tace "Ya ma fi wanda ka ke ji."


Taso da ita ya yi tsaye ya d'aga kan shi ya na kallon ta ya soma cire mata mab'allan rigar ta har sai da ya rabata da ita, rigar nonon da ta kamata ya cire ita maya jefar kafin ya sa harshe ya na lashe jikinta in da lemun ya zuba... *gyara kimtsi*.



*Misalin* 05:54, su na kwance akan gado ya kalleta yace "Khadija, kin mayar da ni babban mutum, ina godiya ga Allah da ya k'addara had'uwa ta da ke a lokacin da babu wanda ya yi tsammanin faruwar wani abu tsakani na da ke, sannan ina godiya a gare ki da ki ka zama yarinya mai hak'uri da zab'in iyayen ta da kuma tawwakali da hukuncin ubangiji, ina kuma godewa Ashir da ya yi tunanin had'a ni da ke har yanzu mu ke kwance akan gado d'aya a matsayin mata da miji, sannan ba zan manta da k'ok'arin iyaye na a kai na wanda su ka jajirce har sai da su ka ga kin zama mallaki na, tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayen shi ba ya tab'ewa, ni shaida ne kuma na gani a zahiri, Khadija, zuwan nan da na yi na taho mi ki da tsaraba mai yawa, amma babbar tsarabar da na ke so na ga ta k'ayatar da ke ita ce *kyautar zuciya ta*."


Tashi ta yi daga kxance ta na kallon shi tace "Ka na nufin ka mallaka min zuciyar ka gaba d'aya?"


Sai da ya jinjina kai alamar tabbatarwa kafin yace "Hakane, kin cancanci fiye da wannan ma, dan da akwai abin da ya fi zuciya ta mahimmaci a gare ni, to da shi zan ba ki, dan a gaskiya ba zan iya ba ki rayuwa ta ba."


Da sauri ta kalle shi tace "Ka na nufin ba zaka iya sadaukar da kan ka ba wa ni?"


Da fuskar tausayi yace "A gaskiya ba zan iya ba."


Cikin rashin jin dad'i tace "Kenan akwai wata da ka ke so?"


"Akwai mana." Ya fadada murmushi, sai lokacin ta rarumo gilashin ta ta saka ta kalle shi da kyau, ganin idonta sun kawo ruwa ya sa ya saki dariya ya rumgume ta yace "Ina da wacce na ke so mana, ga ta a gaba na, Nana Khadija *baiwar Allah*, Khadija ke ce na ke so, ba zan iya sadaukar da rayuwa ta ba wa ke saboda da ke kad'ai na ke so na yi rayuwa, ina so na na k'are rayuwa ta tare da ke cikin farin ciki."


D'agowa ta yi daga jikinshi ta kai mi shi duka a k'irji ta na fad'in "Har ka tsorata ni."


Dariya ya yk yace "Hakan na nufin nima na samu shiga kenan a cikin wannan tattausar zuciyar?"


Sai da ta rumgume shi tace "Sosai ma, kai ne farko da ka fara shigar ta, kuma insha Allah kai ne za ka zama na k'arshe, saboda ka na shiga na rufe ta na kuma jefa makullin a cikin tekun maliya."


Sumbatar ta ya fara yi daga nan dai aka sake juyewa ni kuma na sake juyowa na fito😎,haka su ka dinga gudanar da rayuwar su abar sha'awa, sun manta da yanda ma aka yi su ka had'u, soyayyar su suke barjewa kawai, zan iya cewa daga cikin biyayyar da Usman ya wa iyayensa akan auren Khadija ce ta sa k'ofofin arzik'i su ka fara bud'e masa ta ko ina, ga kuma addu'a da kullum ya ke samu daga matar shi da iyaye da yan uwa akan k'ok'arin da ya ke da kowa, sosai ya ke samun  ci gaba ta fannin kasuwancin da ya saka a gaba, duk da su na d'an samun k'arancin lokacin juna hakan bai hana Khadija taya shi murnar samun ci gaban ba, dan ta lura mutum ne mai son samun na kan shi ba ya kuma buk'atar taimakon kowa, dan ita kan ta yawan kyautar da take wa yan uwan shi da iyayen shi lokuta da dama ya na nuna rashin jin dad'in shi, musamman idan Kabir ko Mannir ko Nura da ke k'arami su ka zo ya ga ta d'auki kud'i masu yawa ta basu wasu lokuta ma har da sabulan wanka da turaruka, sai yai ta fad'a wai ta lalata su har Kabir da ke da aure, ita kam tausayin shi take ganin koyarwa ce ya ke sai wata a baka, duk da ya na fad'a ba ta daina ba saboda a ganinta ita ta na da halin da za ta yi mu su tun da yan uwan mijin ta ne, sannan duk wata ita ma yan uwan ta su kan turo mata kud'i daga cikin ribar da ake samu na kud'in ta da suke juya mata, haka dai har lokacin hutunta ya k'are ta ci gaba da zuwa makarantar ta cikin kwanciyar hankali, duk da mijinta ba mazauni bane, amma ta na gamsuwa da kulawar da ya ke nuna mata.



*Wata biyu* da komawa makaranta Khadija ta kwanta rashin lafiyar da ta jijjigata sosai, dan sai da ta kwana hud'u asibiti ba ta cikin hayyacin ta, ta galabaita da mugun zazzab'i da ciwon kai, ga kuma ciwon ciki da ya murd'ata dole ta yi amai, allura kam tasha ta har ba adadi, haka K'arin ruwa har sai da hannayenta su ka kumbura saboda sukar da ya sha, duk da jikin ya yi dama amma sai da ta cika sati d'aya a asibiti kafin aka sallame ta, cikin ikon Allah kuma sai jiki ya yi kyau sosai, tun daga ranar kuma Khadija ba za tace ga ranar da ta sake kwantawa rashin lafiya ba, sai dai kawai abin da ba'a rasa ba irin su ciwon k'ugu, ciwon baya da d'aurewar mara, kullum Usman godiya ya ke wa Allah da Khadija da ta zama silar sauyawar rayuwar shi, bai tab'a tsammanin auren shi da ita abu neda zai kallo ba, duba da babu maganar soyayya tsakaninsu, sannan ita mai kud'i ce kuma matashiyar yarinya mai ji da kyau, amma ta aure shi babu kud'i babu kyau, kuma duk da haka ta zauna da shi da kyautatawa, wannan ya sa lokuta da dama ya kan fi kiran ta da Nana Khadija baiwar Allah, lokacin kuma arzik'i ya hab'ako sosai, sai kawai ya fara da iyayen shi ta hanyar canza mu su fasalin gida, in da ya gwangwaje su da bila (villa) mai kyau yar zamani, ya d'aukarwa mahaifiyar shi wacce za ta dinga girka mu su abinci sai dai su ci kawai,  lokacin da cikin Khadija ya girma ne ya samu wani babban aiki, wata kwangila da aka mallaka mi shi milyoyin kud'i, a lokacin ne ya fara mu su sabon gini su ma, ginin da a lokacin ya amsa sunan gini, ta wani fannin kuma dije na zuwa makarantar ta hankali kwance.


Lokavin dacikin ta ya isa haihuwa ne wata tafiya ta taso mi shi zuwa Dubaï, shine karo na farko da zai fara zuwa, hakan ya sa a ranar Khadija ta wuni ta na kukan ba zai tafi ba, rarrashin duniya ya yi amma ta toshe kunne ta k'i fahimtar shi, a k'arshe dai dole ya yanke shawarar kaita gida ta zauna tare da su mama har ya dawo, ita kuma bud'ar bakin ta cewa ta yi "Aiko sai dai ka tarar na haihu wallahi, dan ba zan jira ka ni."


Dariya ya yi yace "Ba za ki haihu ba insha Allah har sai na dawo."


Haka ya kaita gida ya aje shi kuma ya wuce, tun a mota Murtala ya lura yanayin abokin shi ya canza sosai, cike da kulawa yace "Aboki na lafiya dai? Ya na ga ka yi wani iri ne?"


A hankali ya kalleshi ido sunyi jawur kamar zaiyi kuka yace "Khadija, ita na ke tausayi, sai ta haihu kafin na dawo, ba na jin za ta wuce sati ba ta haihu ba, dan duk alamu sun nuna haka, kwana hud'u ko bacci ba ta iya yi saboda ciwon baya da mara, mtss." Ya k'arashe da d'an guntun tsaki.


Murtala ne yace "To ya za ayi sai hak'uri? Kuma gashi ba ka fad'a mata gaskiyar magana ba cewa tafiyar nan za ta iya d'aukar ka wata d'aya ko fiye da haka."


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Sati d'aya ma na fad'a mata amma ta damu sosai, ina ga na fad'a mata wata d'aya zanyi? Shi ya sa ma na riga na barwa Hajia komai su kula idan ta haihu, kuma na gode Allah da na iya fad'awa yan uwan ta adadin lokacin da zan iya yi."


"Hakan ma da ka yi ya yi daidai, kaga za su dinga kwantar mata da hankali."


A haka su ka isa kuma su ka rabu suma cike da kewar juna, a daren wannan ranar Khadija nak'uda ta taso mata, da su ka tafi asibi har sai da gari ya waye rana ta yi fatsal-fatsal kafin ta haihu, duk abin da ake Usman na da labari, lokacin da Husseina ta bawa Khadija waya ya mata magana da ta kasa, wata k'ara tare da kuka had'i da salati da ta yi sai da ya ji kamar ya bud'a ido ya ganshi gabanta, a k'arshe dai *bayan wuya* sai dad'i, ta haihu lafiya haka ma yaro, lokacin wani mugun bacci ne ke d'ibar Khadija amma sai Usman yace Hajia ta bata waya su yi magana, daga kwance ta karb'i wayar ta d'ora a kunne, shiru ta yi sai shine yace "Barka baiwar Allah, daga k'arshe dai Gashi kin haifo min yaro, Khadija ina cikin farin ciki sosai, godiya ko dukiya ba za su iya biyan ki ba, amma ina so ki fad'a min duk abin da ki ke so? Ni kuma zan baki shi a matsayin tukuicin wannan kyautar."


Cikin muryar jin bacci tace "Ina hushi da kai kafin minti ashirin da su ka gabata, saboda ka k'i zama tare da ni a lokacin da na ke buk'atar ta, da ka k'ara kwana d'aya tak da na haihu a gaban idon ka, amma bayan minti ashirin da ya wuce, lokacin da na d'ora ido na akan yaron ka, sai na ji komai ya yaye a zuciya ta, dan haka ka d'auka yaron nan shine tukuicinka gare ni."


Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi hak'uri Khadija, haka Allah ya so, kuma duk da kin ce ba jya buk'atar komai, amma akwai wani abu da zan ba ki, kinsan me ye?"


Cikin lumshe ido tace "A'a."


"Khadija, nine ya cancanci na yi wa yaron nan hud'uba, kuma gashi bana nan, dan haka babu wanda yafi cancanta sai ke, na d'ora mi ki wannan nauyin a kan ki, idan kin ma sa hud'uba sai ki rad'a masa sunan da ki ka ga ya dace kuma ki ke so."


"Da gaske ka yarda na saka mi shi suna da kai na?" Ta tambaya da fara'a.


"Sosai ma, wannan hukuncin na jima da yanke shi ai, ba kawai dan bana nan bane."


Shiru ta yi kamar mai bacci kafin tace " *Abban Bilal*., hakan ya yi?"


Da farin cikin jin sunan da ta sakawa yaron ya sa yace "Masha Allah, Bilal, sunan da ke birge ni, sunan da ya nake da burin sakawa yaro na shi, hakan fa ya na nuna k'arfin soyayyar da ke tsakanin mu ne."


Jin bcci na son surarta ya sa tace "Ka gafarce ni Abban Bilal, bacci na ke ji sosai a ido na, za mu yi magana anjima."


"Ayyah sannu momyn Bilal, zan barki haka to, amma anjima za mu yi magana, kin yarda?"


Cikin hamma tace "Na yi alk'awari."


Da haka su ka yi sallama, kamar yanda ya bar komai hannun Hajia haka ta dage sosai ta yi takamata, dan mawasu lokutan maman Khadija da yan biyar ba sa tsayawa komai da an nemi abu za su siyo su kawo, haka dai aka yi shagalin biki babu uban yaro, a lokacin Khadija ta fara damuwa da rashin dawowar Usman, da k'yar yan uwanta da mama suke kwantar mata da hankali, tun suna waya ya na cewa zai zo aiki ne ya rik'e shi har ya kai ya rasa me zai ce mata, sai kawai zuciyar shi ta bashi ya daina kiranta, ita kuma idan ta kira jar ya d'aga sai an kwana biyu, wannan dubarar ce ta jefa Khadija a wani hali na daban, da ta kwashe kwanaki ta na kira bai d'aga ba, damuwar ta ta nunku sosai, mama kuma sai take cewa tayi hak'uri mana da yanda Allah ya hukunta mata, hakan ya sa Khadija tunanin ko Usman ya mutu ne dai, kawai sai ta yanki jiki ta fad'i, sai da ta kwana asibiti, a ranr Usman bai shirya tahowa ba amma dole ya taho, dan cewa ya yi neman kud'i ba zai ja mi shi rasa matar shi ba wacce ya ke da yak'inin ba zai samu kamar ta ba a wannn k'arnin, sai lokacin kad'ai Khadija ta samu sauk'i ta kuma huce.



*Allah ka k'ara mana lafiya mai anfani.*

20/01/2020 à 12:38 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


💕💕💕 *My Heenat, My BK, My Meelat*💞💞💞


_Alkhairin Allah ya lullub'e min ku, ina k'aunar ku._😘



```Fatan alkairi masoya```


*MOMYN DADY, KI JI DAD'IN KI WANNAN PAGE TA KI CE KYAUTA.* 😉


_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *13*



Kullum taresu ke idan dare ya yi har ba ya son rabuwa da iyalin shi, kuma bai sake wani tafiya ba har sai da ta yi arba'in, sabon gidan da ya gina mu su matsakaici daidai da rayuwar su suka tare, haka suke rainon Bilal cikin kulawa da so da k'auna, ta b'angare d'aya kuma ta na ci gaba da zuwa makarantar ta, kasancewar babu nisa da gidan su da makarantar ya sa take aje Bilal nan kafinta wuce, idan ta sauko ta biyo ta d'auko shi, a haka dai har ta kammala karatunta lafiya, haka ma Usman ya na k'ara samun hab'aka a kasuwancin shi, a lokacin da ya ke tunanin nemawa Khadija aikin karatun da ta yi, sai kawai ta shawarce shi kan ta na son fara kasuwanci, ta na so Ashir ya fara kawo mata kwanuka da karap (jug) da sauran kayan anfanin mata ta na siyarwa, ya ji dad'in haka kuma yace nauyi ne a kan shi ya mata hakan, Ashir ya nema su ka yi magana sannan ya fara bashi *million d'aya* dan a fara da ita, cikin ikon ubangiji kuma sai Allah ya sawa kasuwar albarka, duk da komai bashi ne, amma dai ana samu sosai, lokaci na tafiya kamar walk'iya in da abubuwa ke faruwa, ta na taimakon danginshi da danginta da ita kan ta ma da kasuwancinta, in da Aziza kuma ta zama kamar ba k'anwar Usman ba, dan ya zama Khadija ita ce komai na ta, har tafi son zama gidan nan akan gidan su, a lokacin kuma Khadija su na ta sake zuba ido akan samun wata haihuwar amma shiru, abu d'aya shine kasuwancin ta ya na d'aukar hankalin ta sosai.


*Shekarar Bilal takwas* sai kasuwar ma ta durk'ushe, sakamakon wata mata da ta shigo rayuwar ta da sunan kasuwanci, da farko sai da ta sa Khadija ta yarda da ita ta hanyar yi mata ciniki na milyoyin kud'i sau ba adadi, sun saba sosai ta na bata kaya za ta biyata kud'i a take, daga k'arshe sai ta nemi ta bata kayan milyoyin kud'i, ba fargaba Khadija ta kwashe duka kud'in ta ta bayar aka siyo mata kaya, wannan karan matar cakin (check) kud'i ta bata da nufin ta je banki ta cira, sai da ta d'auki kayan sannan Khadija taje cirar kud'i, cakin k'arya ne na bogi, hakan ne ya jefa Khadija matsala har aka mata taro ana neman mik'a ta hannun kwalawa🤣, sai da Usman da Ashir su ka zo kad'ai aka samu matsalar ta mutu anan su ka dawo gida, ba girgiza ko damuwa a tare da ita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Ta ci kad'an wallahi, ita da Allah, ya na sama ya na gani, dan haka na barta da shi."


Usman ya si bata wasu kud'in amma tace kawai ta hak'ura da kasuwanci, tun da dama ta na yawan samun irin wannan matsalar, wannan karan dai ne abun ya girmama, tunda ba ta rasa ci da sha ba da duk abun buk'ata, dan haka ta hak'ura tun da akwai wanda ba sa son ta da arzik'i, ya nuna mata wannan ba shine maslaha ba amma ta rufe ido tace ba ta so, dole ya rabu da ita kawai ba dan ya so ba, a lokacin ta rage hada hada da jama'a Aziza kuma ta k'ara girma an zama yan mata, lokacin ne ta fara sakawa rayuwar su ido saboda yanda ta ga d'an uwan ta na rawar k'afa akan Khadija da d'an ta Bilal, in dai har yayi tafiya ya dawo to na tsawon kwana biyu ko uku Khadija ba ta girki in ka cire ranar da zai dawo, saboda Usman na da buk'ata sosai, idan ya dawo sai ya yi kwana uku bai lek'a waje ba idan ba masallaci ba, hakan ne ya sa yace ba ita ba shiga madafa sai dai in ruwan zafi za ta d'ora mu su na wanka, a cikin kwanakin da zaiyi kusan kullum sai sun fita cin abinci ko shan ice crime ko ya mu su siyayya ko kuma sada zumunta gidan yan uwan shi da yan uwan ta, yayin da su ke jin dad'in rayuwar su sai Aziza ta fara zargin akwai wani abu a k'asa, yanda ya ke komai dai matar shi da d'an shi abun na bata mamaki, musamman idan Kaltume ta zo ta ga sun shige d'aki ana ta dariya da ba ta yan k'unshe k'unshe, sai kawai tace sun mallake shi ne, (d'an adam butulu), a hankali sai ta fara fad'awa yan uwan ta su Hassana, su kuma ba tunanin komai su ka yarda, dan suma sun fahimci hakan, musamman idan ya zo daga tafiya ba ya fita wani lokacin gidan su ma sai ya kwana ya hantse baije ba, su kuma iyayen da yake su na da hankali sai suke ganin wata buk'atar ce ta sa haka, a hankali sai suka fara canza mata fuska, ko alheri ta musu sai su k'i karb'a, ana haka wata rana k'anwar shi *Rabi'a* ta zo neman jari wajen shi za ta fad'ad'a kasuwancin ta, rashin sa'ar da ta yi Usman kwanan shi biyu da dawowa, sai yace mata ba ya da kud'i yanzu, amma ta yi hak'uri ta dawo nan da kwana uku, ita kam a ganinta wannan k'aton gidan da suka sake ta kalli Khadija ta ganta mulmul cikin rantsetsen leshe, sai taga ai k'arya ne ma ace babu kud'i a gidan nan (🤣🤣🤣), sai kawai ta tashi rai b'ace ta na gunguni, Khadija ce ta dawo da ita ta zauna ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko kud'in da yan uwan ta ke bata ta mik'a mata, sai da ta kalle ta sama da k'asa ta kalli Usman tace "Dama akwai kud'in kawai tsoron bani ka ke saboda ba ta yarda ba, to ki bar shi nagode."


Ta na fad'ata mik'e ta bar gidan, Usman kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "Waya saki? Keta tambaya ko ni? Yanzu gashi kin ja k'aramar yarinya za ta fad'a mana magana."


Murmushi ta yi baiwar Allah ta b'oye abin da ke ran ta tace "Allah huci zuciyar ka, ba na fatan ganin b'acin ran ka a lokacin da ka ke cikin yanayin farin ciki."


Tun fa daga ranar su ka sake kafawa Khadija k'ahon zuk'a, sai dai ba su tab'a yarda sun bari iyayen su sun sani ba, dan sun san iyayen su yan a mutun Khadija, za su iya b'ata mu su fiye da tunani Saboda ita, amma kullum buri da addu'ar su Allah ya kawo wata gidan wacce za ta fanso d'an uwan su daga sharrin Khadija, babban abun haushi shine lokaci da su ka had'u da Usman gida su ka saka Kabir da ke bi mi shi a cikin maza ya mi shi magana ya k'ara aure, murmushi ya yi ya kalle shi yace "Me ya sa zan k'ara aure?"


Shi dai Kabir ya fad'a ne ba da wata manufa ba, dan shi ba ya manta alkairi kuma ya na k'aunar Khadija, cewa ya yi "Ko ba komai ai ka k'ara saboda ka samu zuri'a dayawa."


Cikin bacin rai Usman yace "Wallahi, da ace wani ne ba kai ba ya fad'i wannan maganar, da sai na fad'a maka kalmar da har ka mutu ba ka manta ba, kai ba dan ma butulu bane har Khadija ce za ka yi fatan a k'arawa kishiya? To jini da kyau, kar ka sake min wannan maganar, sannan duk wani mai wannan banzan tunanin a gidan nan ma ya daina, dan za mu iya samun matsala da mutum."


Hussei na ce tace "Yanzu yah Fodio saboda an ma ka maganar aure shine ka ke wannan kumburin? Na ga dai da ba'a aure ai da ba ka aure ta ba, kuma k'ara aure sunna ce ta *ma'aiki*, bugu da k'ari za ka k'ara samun ya'yan da za su gaje ka."


Murya kasa k'asa yanda ba zaiji ba Rabi'a tace "To ba sai ta ba shi damar yin hakan ba, shi fa a d'aure ya ke ba ya da katab'us sai yanda ta yi da shi."


Duk da ba duka Usman ya ji ba, amma dai ya ji kalmar k'arshe ta sai yanda ta yi da shi, cikinjin zafi ya juyo ya kife ta da mari, zai k'ara mata wani marin Hajia ta d'aga mi shi hannu, huci ya dinga yi kafin yace "Wallahi dukanku butulu, kun manta alkairi kuma kun manta hallaci, Khadija bata cancanci wannan daga gare ku ba, ko ba komai ita uwar d'ana ce, ita da Bilal sun fiye min komai a duniyar nan, ita kad'ai ta bani farin cikin da ku ma da ke yan uwana ba ku ba ni shi ba kafin zuwan ta rayuwa ta, dan haka in dai har ku na son zama da ni to dole harshenku ya san me zai dinga fad'a akan mata ta."


Ya na fita Hajia ma ta mu su fad'a sosai tare da tuna mu su baya, daga ranar kuma ba su sake yarda sun b'ata Khadija ba a gaban iyayen su bare kuma Usman, amma abin takaicin shine k'iyayyar da su ke ma Khadija sai ta shafi har Bilal, dan yanda su ke ganin Bilal na wahalar da mahaifin shi, yaro ya zama saurayi amma kamar k'aramin yaro, ba ma in sun had'u da shi gidansu Hajia, ya kan zo da kayan ciye ciye ma su tsada da kyau da dad'i, duk abincin da za'a mi shi tayi ba zai ci ba, haka mahaifin su malam Ali zai dinga biyewa yaron ya na siyo mi shi duk abin da ya ke son ci, to fa ana hakane har Allah ya had'a Usman da Haseenah, lokacin ya na yawan zuwa wajen wani shago da ke can wajen filin kokawa saboda wasu kaya da ya ke kawowa mai shagon, a nan ya had'u da Haseenah wacce a lokacin ta samu exam (brève) d'in ta ta na zaune gida, baban ta ne ya tilasta mata komawa makarntar islamiyya dan ta k'ara samun ilimin addini, a lokacin har nik'abi take sakawa da dogon hijab, wannan nutsuwa da hankalin na tane su ka sa Usman jin kamar ya samu wata Khadija, fatan shi shine ta zama kamar yanda ya ke tunani, bayan ya yi tambaya a kan ta an fad'a mi shi yarinyar kirki ce daga gidan mutanen k'warai, sai kawai ya gabatar da kan shi a matsayin yana son auren ta, duk da bai cika magana akan matar shi ba, amma ya fad'a mata ya na da mata d'aya da yaro d'aya, kuma ya na matuk'ar son su, a lokacin da su ka fara soyayya Usman na bata lokaci wajen waya da Haseenah har dare, sannan duk abin da ta yi ya kan yaba hakan kamar d'abi'ar shi ce, amma a tunanin Haseenah matar shi ba ta da kulawa ne shi ya sa har za ta yarda ya na waya da ita tsawon dare ko ya na gari, abin da kuma ba ta sani ba shine duk lokacin da ya ke wayar da ita to ba ya gida, Khadija kuma ba ta damuwa saboda ta san in baya gida yana tare da su Murtala, ta na ba shi lokaci sosai da ya ke jin dad'in rayuwar shi shima kamar yanda ya ke wuni tare da ita da safe har zuwa yamma, ko kwalliya ta yi taji yana kod'ata sai tace wai uwar gidan shi ba ta yi shi ya sa idan ya ganta da kwalliya kamar ya ga matar aljanna, hakan ya sa ta sawa ranta ta na zuwa gidan za ta cinye yak'in ba tare da tasha wahala ba, amma kuma gashi Mariya ta kawo mata wani labari da ya sa har ta fara had'awa da malamai.



_Toh, ko tunanin Usman ya fad'a mi shi daidai? Shin Haseenah za ta zama kamar yanda ya d'auka? Ko kuma dai *kallon kitse ne ya ma rogo*?_



       *Mu koma labari*



Ko da ya dawo daga kan Bilal kai tsaye falon shi ya wuce, sak'o ya turowa Khadija ta same shi falo haka ma Haseenah da ke d'akin ta, hakimcewa ya yi ya na jiran zuwan su, (da alama Usmanu yan mulkin sun motsa, yau kam duk wacce ta yi wasa za ta gane shayi ruwa ne 😉), kusan a tare su ka shigo falon sai Khadija da ta k'ara da sallama, zaune su ka yi su na fuskantar shi su na kallon shi, d'ago kan shi ya yi ya kalli Haseenah ya kalli Khadija kafin yace "Kun gaisa ne da safen nan?"


Khadija da tasan waye mijinta ne ta yi saurin cewa "Sosai ma, har falo ta same ni ai, mun gaisa da ita."


"Da kyau." Ya fad'a ba annuri kafin ya d'ora da "Ku zuba mana abinci mu ci."


Satar kallon shi Khadija ta yi dan tasan ya same ta tana karin kummalon ta, amma jin haka daga bakin shi da kuma ganin yanayin shi ya sa tasan yau ba ya yanayin wasa, dan haka ta mik'e tare da Haseenah da ke ta wani yauk'i kamar za ta karye, murmushi ta mata tace "Kinga amarya zauna, ki zauna zan zuba."


Ci gaba ta yi da zuba ma kowa har ta gama ta aje farantin a gaban shi kafin ta matso kujerar ta kusa da shi, sai da ya fara saka hannu tare da bismillah sannan su ma suka saka, Haseenah dama haushi ne kamar ya kashe ta, Khadija kuma a k'oshe take neman agaji take, a tare su ka cire hannun su suna kallon shi, shi ma kallon su ya yi yace "Me ku ke nufi?"


Cikin wata shegiyar shagwab'a Khadija tace "Mun k'oshi."


Duk daba kuzari a tare da shi sai da ya murmusa yace "Ku na nufin ni kad'ai za ku bari? Ai ba ku isa ba, dan haka ku mayar da hannuwan ku."


Kamar za ta fashe da kuka ta shafa cikin ta tace "Ciki na fa zai fashe, ka ci kawai sai ka had'a da nawa ka ci."


Sama da k'asa ya harare ta yace "Sannu mai wayo, kenan ni na cika cikin nawa? To na k'i wayon."


Mik'ewa ta yi tace "To bari na je na amaye wanda na ci sai na dawo mu ci gaba ko?"


Da gayya Khadija ta dinga tafiya ta na wani juya k'ugunta, mazaunan ta na kad'awa yanda su ke so, sai da ta kai k'ofar fita ta juyo ta kalle shi dan dama a sanin da tawa mijinta ba ta ba da baya bai bita da kallo ba, su na had'a ta ga ya wani  saki baki ya na kallon ta, cije leb'e ta yi ta kashe ma sa ido d'aya ta fice da murmushi, Haseenah Usman ta bi da kallo ganin ya wani wagale baki har da rumgume hannaye ya na kallon ta, sai da yaga ficewar Khadija ya sauke wata sayayyar ajiyar zuciya da murmushi a fuskar shi wanda shi kad'ai ya san ma'anar shi, a hankali ya zuro hannun shi cikin farantin da nufin ci gaba da cin abincin shi sai ya lura da Haseenah da ta kafe shi da ido, saita nutsuwar sa ya yi yace "Ya dai?"


Ita ma had'e abin da ke ran ta tayi tace "Ranka shi dad'e, wai me ya sa aunty Khadija ke jin dad'in anfani da gilashi a kowane lokaci? Ba ta tsoron ta samu matsala a idon ta."


Kallon ta ya yi ya na tunani, bayan gamsuwa da zuciyar shi sai kawai yace "Haseenah kema yanzu iyalin gidan nan ce, ba wani abu da za'a b'oye mi ki, Umman Bilal na fama da larurar ido ne, kuma anyi neman maganin amma har yanzu shiru ba labari, sai dai har yanzu ba mu cire rai da rahamar ubangiji ba, mu na sa rai wata rana za ta samu lafiya da yardar Allah."


D'auke idon ta ta yi daga kan shi ta kalli k'asa da murmushin jin dad'i a ran ta kuma ta furta "Ashe ma makauniya ce, gilashi shine idon ta, hum."


D'agowa ta yi tace "Allah sarki, Allah bata lafiya."


"Ameen." Ya fad'a ya na cire hannun shi ya wanke cikin wata k'aramar roba mai d'auke da ruwa, mik'ewa ya yi ya kalle ta yace "Zan d'an shiga d'akina na kwanta, misalin *11:00* sai ki tashe ni."


Mik'ewa ta yi cikin kwarkwasa tace "Ni kad'ai kenan zan zauna? Gaskiya a'a sai dai na bika mu je tare."


Kallon ta ya yi ya na sauke ajiyar zuciya yace "Haseenah kenan, kedai kawai ki na so ki hana ni bacci ne, amma idan ba haka ba me zai hana ki je wajen yayar ki."


Cikin sanyin jiki tace "A'a gaskiya, gwara na zauna d'aki na ni kad'ai."


Da mamaki sosai ya kalle ta yace "Me ki ke nufi? Haseenah akwai wani abu da ake mi ki a gidan nan da ba kya jin dad'i ne?"


Wani murmushi ta yi da bai kai zuci ba tace "Ba komai fa, kawai ka je ka kwanta abin ka."


Rumgumo ta ya yi jikin shi su ka nufi d'akin na shi ya na fad'in "Ai sai kin taimaka min kafin na yi baccin ko?"


Su na shiga d'akin ya cire doguwar rigar shi ya kwanta, hijabin ta ta cire k'ananan kayan ta su ka bayyana, bayan shi ta kwanta ita ma ta na shafa kan shi har zuwa kunne, ba tare da magana sai kuwa bacci ya d'auke shi, a hankali ita ma sai bacci ya yi awon gaba da ita, daga nan fa su ka shiga baccin su hankali kwance.



Khadija kuma na falo ita da Uwani su na ta hira su na kallo, har ita ma Khadija ta kwanta a kan kujera bacci ya soma d'aukar ta, *12:15* Uwani ta daddab'a k'afar Khadija ta farka, agogo ta kalla tace "Aunty, na ga sha biyu har ta wuce amma Bilal bai dawo ba."


Da sauri ta zabura ta mik'e zaune ta na fad'in "Abban shi ya fita ne?"


"Gaskiya ban ga fitar shi ba, dan har yanzu motar shi na waje."


Wayar ta ta d'auka ta kira shi amma ta na silent, dan haka ba ta sake na biyu ba kawai ta kira lambar Naseer, ya na d'auka ya fara da "Autar Hajia ya ake ciki ne?"


Cikin shagwab'a tace "Yaya na, Bilal ya na makaranta har yanzu ba'a d'auko shi ba, kuma na kira wayar Abban shi ba ya d'agawa, shine na ce ko za ka saka cikin yaran shagonka su d'auko min shi?"


Daga in da ya ke ya mik'e yace "Abu mai sauk'i, dama zaune na ke ina kallon titi, bara na isa da kai na na d'auko shi."


"Yawwa yah Naseer nagode."


"Uhum! Kar ki damu."


Aje wayar ta yi ta na mamakin abin da ya sa Usman mantawa da gudan jinin shi a makaranta, sharewa kawai ta yi ta kalli Uwani tace "Uwani, ki duba madafa ki ga idan babu kowa sai ki d'orawa Bilal indomie kafin ya dawo, dan kinsan abinci ya ke fara nema da ya sauko."


"To aunty." Ta fad'a ta na tashi ta nufi madafar, ba kowa a ciki dan haka ta fara abin da ya kai ta, sallama ta ji tun daga tsakar gidan, lek'owa ta yi dan madafar a bakin k'ofar shiga duka b'angarorin take, su Rabi'a ne da kuma matar Kabir *Jauza'u*, amsawa ta yi ta na fad'in "Aunty Rabi'a sannun ku da zuwa."


"Yawwa Uwani sannu, aiki ake?" Cewar Rabi'a, k'ofar Haseenah su ka nufa Rabi'a ta sa hannu ta bud'e sai ta jita a rufe gam, kallon Uwani ta yi tace "Amaryar ba ta nan ne?"


"Ta na nan, amma ina jin kamar ta na d'akin Abban Bilal." Ta fad'a da nuna mu su falon na shi, Jauza'u ce tace "Shikenan bara mu shiga wajen aunty Khadija to."


Da sallama su ka shigo a bakin su, Khadija da ke zaune ta na danna waya ne ta d'ago ta kalle su, sharrin shaid'an da zafin kishi ya sa Khadija tuna irin k'iyayyar da yanzun su ke mata, a ganin ta suna matuk'ar farin ciki da k'ara auren Usman, su na jin dad'i saboda an mata kishiya, sai kawai ta ji ba ta buk'atar sakar mu su fuska kamar baya, fuska ba fara'a ta amsa da "Wa'alaikum salam."


Suma k'asa su ka zauna Jauza'u na fad'in "Aunty Khadija ke kad'ai zaune?"


Kallon ta ta yi tace "Umm."


"Ina kwana aunty Khadija?" Cewar Jauza'u, ta na ci gaba da danna wayar ta tace "Lafiya k'alau, ya ki ke?"


Duk da Jauza'u ba haka ta saba gani ba ammata dake tace "Lafiya lau, ina Bilal?"


Ba tare da ta d'ago ba tace "Bilal ya na zuwa yanzu daga makaranta."


Sai lokacin Rabi'a tace "Ina kwana?"


D'agowa ta yi ta jefe ta da wani banzan kallo kafin ta yi k'asa da kan ta tace "Lafiya, ya gida?"


Sai da ta harare ta ta wutsiyar ido kafin tace "Lafiya lau."


Shiru ne ya d'an ratsa wajen kowa da abin da ke sak'awa a ran shi, Jauza'u kam duk ta ji ba dad'i dan har ga Allah ta na k'aunar Khadija, saboda ta mata abin da ko mijin ta bai iya yi mata ba a lokacin da baya da k'arfi, su na haka babu mai magana shiru kamar ba gidan wannan Khadija ka zo ba wacce ke washe baki idan ta yi bak'o har ya tafi ta na rawar jiki, amma yau gashi sai wani shan k'amshi take.



Usman ne ya zabura ya tashi ya na rarraba ido, da sauri ya kalli agogon da ke fuskantar shi, " *12:45*." Shine abin da ya fad'a da k'arfi har ya sa Haseenah tashi zaune ita ma, da hanzari ya sauka daga kan gadon ya na d'aukar doguwar rigar shi ya zura, makulin mota ya wawura a gefen gadon ya juya zai fita Haseenah tace "Wai saurin me ka ke ne haka?"


Ba tare da ya juyo ba yace "Yarima zan d'auko, lokacin tashin su ya wuce sosai."


Da sauri ta duro daga kan gadon ta tari gaban shi tace "Amma haka za ka fita ko wanka ba ka yi ba?"


Ture ta ya yi daga gaban shi yace "Wani wanka dallah, yaro na can tsaye ya na jira na, ban san a wane hali ya ke ba."


Fita ya yi daga d'akin ta bishi da kallo, k'wafa ta yi ta fita daga d'akin ita ma kai tsaye madafa ta nufa da tunanin d'ora silalar nama sai ta yi wanka, ta na bud'a k'ofar ya yi daidai da Uwani ma za ta fito, hakan ya sa Uwani bige ta ba ta sani ba, rik'e hannun ta tayi da ta bugu ta na ma Uwani kallon tsana, cikin jin zafi da b'acin rai ta kife Uwani da marin da ya sa farantin indomien zubewa k'asa saboda yanda ya zo a bazata , dafe kunci ta yi ita kuma ta na fad'in "Dan uban ki ni za ki bige? Wacece ke a gidan nan? Me ma ya kawo ki madafar nan? Ko kin manta yanzu ni ke aiki a ciki ko wacce ta aje ki sai na yarda za ta shigo? To ki saurare ni da kyau, daga yau ba na son sake ganin k'afar a madafar nan in har aiki na ne, in ba haka ba kuma zan ci uwar ki a gidan nan sannan na sa mai gida ya yi waje da ke, kinji ni ko?"


Kai Uwani ta d'aga alamar ta ji, da hannu ta mata alama tace "Fitar min daga nan, k'azama kawai 'yar matsiyata."


Kasancewar Uwan irin mutanen nan ne masu jin zafin magana, wanda da ka zage su yafi sauk'i ka yanke su da wuk'a, hakanne ya sa ta fito tana kuka tana jin k'una na kalmar 'yar matsiyata da ta yi da cewa za ta ci uwa ta, ta na nufowa falon Khadija ta tsinkaye ta, dan haka ta tashi da sauri ta nufe ta, sai da ta rumgume ta a jikin ta ta fara tambayar ta lafiya? Cikin kuka ta ke fad'in "Aunty amarya ce tace wai kar na sake shiga madafa in ta na aiki."


Shiru Khadija ta yi tana sauke huci kafin ta d'ago Uwani daga jikin ta tace "Haka ta fad'a mi ki?"


Kai kawai ta d'aga mata, d'orawa ta yi da "Shikenan Uwani yi hak'uri, yanzu ina indomien da na saki dafawa?"


"Ta na can ta zube." Ta fad'a tana share hawaye da hijabin ta, da k'arfi tace "Ta zube kamar ya?"


"Lokacin da ta mareni ne faranti ya sub'uce a hannu na ta zube."


Da k'arfi ta dafe k'irji tace "Mari kuma? Ta mare ki fa ki ka ce?"


Kai Uwani ta d'aga alamar eh, share mata hawayen fuskar ta ta yi tace "Wuce d'aki Uwani ina zuwa, zanji dalilin marin ki, in ba ta san darajar mutane ba ni na sani."


Za ta wuce madafar Uwani ta rik'o hannun ta tace "Dan Allah aunty Khadija ki yi hak'uri, na yafe mata wallahi, ba na so saboda ni ku samu matsala."


Fincike hannunta ta yi tace "Uwani kin tab'a ganin b'acin rai na?"


"A'a." Ta fad'a har da girgiza kai, "To ki wuce d'aki kamar yanda na ce." Ta na fad'a ta nufi madafar a matuk'ar hassale, daidai lokacin kuma mai gadi ya bud'e k'ofa da  motar Usman da ta motar Ashir ta danno ciki, Ashir na kusa da gidan ya ga motar usman, dan haka ya kira shi ya fad'a mi shi ya na tare da Bilal dan haka ya juyo su ka dawo.


Khadija kam na shiga ta samu Haseenah ta wanke naman zabbi ta zuba a tukunya za ta kunna wuta, sai da ta tsallaka indomie da ke zube k'asa kafin ta isa gare ta, cikin gadara ta tsaya bayan ta tace "...



_Wata yau za ta gane kuren ta fa._😉


*Allah ka sa mufi k'arfin zuciyar mu.*

21/01/2020 à 13:34 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *14*




"Haseenah, Uwani ta fad'a min abin da ya faru, kuma har ta fad'a min ma wai kin mare ta, shin hakane?"


Juyowa Haseenah ta yi cike da rainin wayo tace "Ki cire wai, gaskiya ne abin da ta fad'a, ko za ki rama mata ne? Sai ki tabbatar min yar aikin gida tafi matar gida."


Wani murmushin gefen labb'a Khadija ta yi kafin tace "Ko kinsan kin mana b'arin abincin da yarima zai ci?"


Ba tare da ta juyo ba tace "Ban san wani yarima ba a gidan nan, sai Bilal kawai, wanda na ke da tabbatacin ba shi kad'ai bane yaron da zai rayu a gidan nan, k'annan shi na nan zuwa duniya nan gaba kad'an."


Wata dariya Khadija ta saki har da rik'e ciki kafin tace "Nagode Allah da ki ka iya tuna Bilal shine babban yaron da ya fara zuwa duniya kuma a gidan nan, hakan ya tabbatar min da mai hankali na ke zaune."


Kallon ta ta yi sosai tace "Kasancewar Bilal d'an farko a gidan nan ba shi ke nuna zaifi sauran yaran da za su zo daraja ba, kamar yanda jimawar mahaifiyar shi a gidan bai sa matsayinta yafi nawa ba, dukan mu mata ne kuma matan Usman a gidan nan, aljanna ki ke nema haka nima ita na ke nema."


Juyawa ta yi ta d'auki wuk'a hakan ya sa Khadija fizgo wuyan rigar ta da ko hijabi babu a jikin ta, sosai ta shak'e ta tace "Dama abu d'aya na zo fad'a mi ki, Uwani ba wai yar aiki ba ce a gidan nan kamar yanda ki ka d'auka, kuma mai gidan ma yasan da haka, ko shi bai isa ya mata abin da ki ka mata ba, dan haka ya zama na k'arshe da kalma marar dad'i za ta shiga tsakanin ki da ita bare duka, na yarda ki mata fad'a idan har ta yi ba daidai ba, amma banda cin zarafi a ciki, ki kiyaye nan gaba."


Sakin rigar ta ta yi za ta fita kawai Haseenah ta ja tsaki tace "Idan shi tsoronki ya hana ya mata magana, ni nan Haseenah zan iya, kuma ki sani shigowa ta gidan kamar shigowar rahama ne da sauyi."


Murmushi Khadija ta yi tace "Ina fatan dai ki na da kud'in biyan bokan na ki, dan in ba ki shirya ba za ki sha wahala wajen karb'ar gidan nan a hannu na."


Juyawa ta sake za ta fita Haseenah ta kuma cewa"Aikin banza, ai ba boka ba malam wallahi zan karb'i gidan nan, makauniyar banza makauniyar wofi, ai ba a banza Allah ya hana ki idon gani ba."


Wannan maganar ta makauniya ita ce ta tsayawa Khadija a rai, da k'arfi ta juyo ta matso daf da ita tace "Me ki ka ce?"


Yanda taga idon Khadija sunyi ne ya sa ta kasa cewa uffan, lumshe ido ta yi ta bud'e ta sauke su a kan ta tace "Haseenah ina da yak'inin ban tab'a yin fad'a ba tun da k'uruciya ta har zuwa girma na, sai dai ina ji a jiki na cewa fad'a na zai yi matuk'ar muni, dan haka ina so ki kiyaye, ba na so na yi abin da zai b'ata min suna ko kuma zuri'a ta."


Cikin rashin gamsuwa da abin da ta fad'a tace "Wai ke Khadija me ki ke d'aukar kan ki? Mummuna ko me? Akan komai sai kin nuna ke dabance, to ba zan d'auka ba wallahi, kar ki k'ara cewa za ki nuna min izzar ki dan ba ta shafe ni ba."


Matsowa Khadija ta yi ta sa hannu ta ture ta baya ta na fad'in "So ki ke kisan me na d'auki kai na? Na ce ki na so ki sani ne?"


Hankad'ar da ta mata ce ta sa ta yi baya sosai har ta bige tukunyar da ke kan wuta ruwa da naman  ciki ya watse, lokacin da hannun Haseenah ya bugi tukunyar ta ji zafi, hakanne ya tilasta mata sakin razananniyar k'ara har duk gidan na amsawa, Usman, Naseer da su Rabi'a da ke zaune su ka hanzarto su ka nufo madafar, ganin Khadija tsaye ta na kallon Haseenah da ke rik'e da hannu ta na kuka ne ya sa Usman saurin k'arasawa, rik'o hannun Haseenahr ya yi yana kallon abin da ya zube ya kalli Khadija yace "Lafiya? Me ya faru ne?"


Cikin tafasar zuci tace "Kallon me ka ke min? Ka tambaye ta mana, ni ce za ka tambaya?"


Rabi'a ma matsawa ta yi kusan Haseenah tace "Haseenah me ya faru ne wai? K'onewa ki kai?"


Girgiza kai ta yi cikin zubar da hawaye tace "A'a, ba k'onewa na yi ba."


Usman ne ya d'ora da "To me ya faru?"


Fashewa ta yi da wani kukan, hakan ya sa Usman mayar da kallon shi ga Khadija yace "Khadija me ya faru, naga ai daga ke sai ita ne a madafar ko? Me ki ka mata haka?"


Kallon shi ta yi cikin ido da niyyar fad'in abin da ya faru, amma ta na kallon shi sai wannan kwarjinin da haiba da rashin sabo na rashin samun matsala da ba su tab'a yi ba ta yi k'asa da kan ta, cire gilashin ta tayi ta fashe da kukan da babu sauti, ai tuni sai hankalin Naseer ya tashi, da gaggawa ya matso kusanta shima ya kalli Haseenah yace "Wai me ya faru ne? Ke ki fad'a mana."


Cikin kuka Haseenah ta kalli Naseer d'in tace "Ni ban san me ya faru ba, na dai san na yiwa mai aikin nan magana kan cewa kar ta sake shigowa madafar nan in ina aiki, banji shigowar aunty Khadija sai ji na yi ta tura ni gaba kawai, shi ne na..." Sai kumata fashe da kuka.


Da tsantsar mamaki Khadija ta kalle ta, kallon ta Usman ya yi yace "Gaskiya ne abin da ya faru kenan?"


Mayar da gilashin ta yi ta kalli Usman tace "Babu abin da zan fad'a ma ka, ka d'auki mataki kawai."


Kallon Haseenah ta yi tace "Ba zan ce ki ji tsoron Allah ba, amma zan mi ki kashedi da kar ki sake kira na da makauniya, in ba haka ba kuma wallahi zan mugun sab'a mi ki fiye da tunanin ki."


Juyawa ta yi ta kama hannun Bilal da na Naseer da nufin fita, k'yam Naseer ya tsaya ya kalli Haseenah yace "Kamar k'anwa na ke kallon ki, dan Allah kar ki bari wani abu na rashin kyautatawa ya shiga tsakanin ki da yer uwa ta, ita d'in kamar rayuwar mu ce, ban tab'a jin wanda ya yi k'ok'arin kiranta da makauniya sai yau, dan haka ki kiyaye dan Allah, ku zauna lafiya sai mijinku ya yi farin ciki da ku."


Juyawa ya yi su ka fita, a daidai k'ofar shiga falon Khadijar su ka tsaya, dafa kan ta ya yi yace "Ki yi hak'uri kinji yar autar mu, ina tabbatar mi ki hakan ba zai sake faruwa ba, ki daina kuka kinji ko."


Cikin shashek'ar kuka tace "Shikenan yaya na, kar ka damu na dain, ka tafi gida kawai, amma dan Allah kar ka bari kowa ya ji a gida, wannan matsalar gidan nan ce."


"Shikenan zanyi, amma ki min alk'awarin hakan ba zai sake faruwa ba."


"Nayi." Ta fad'a da murmushi, shafa kan Bilal ya yi yace "Yaro na sai anjima ko, yaushe za ka shigo wajen matar?"


Ba walwala a tare da shi yace "Tonton (uncle) da Momy za ta yarda da na bika gida, gaba d'aya yanzu gidan nan ba dad'i, Abba ma ya daina cin abinci da mu kuma ba ya..."


"Bilaaaal." Khadija ta kira sunanshi, wucewa kawai Naseer ya yi su ma suka koma ciki, d'akin Bial su ka nufa dan ta taimaka masa ya canza kaya Uwani ta yi sallama, juyowa ta yi ta kalle tace "Uwani ki je gida kawai, ki bari sai gobe ki dawo."


"To aunty, amma Abban Bilal yace wai ki same shi a d'akin shi yanzu."


Sai da ta d'an kawar da kai kafin tace "Shikenan, ina zuwa."


Kallon Bilal ta yi tace "Ka je ka cire wannan kayan sai ka watsa ruwa ka canza wasu, ina zuwa yanzu ka ji."


Ciki ya shiga ita kuma ta wuce d'akin Usman, a falon shi su ka ci karo da su Rabi'a za su tafiya, amma ko kallon ta Rabi'a ba ta yi ba saboda a tattaunarwa da su ka fara da Usman sai kare Khadijar ya ke, Jauza'u ce tace "Sai anjima aunty Khadija."


"Ki gaida gida Jauza'u." Cewar ta ta na shiga d'akin, zaune ya ke akan kujera da ke gaban madubi in da Haseenah ke zaune bakin gado, ita ma bakin gadon ta zauna kamar yanda ya nuna mata, ya na kallon fuskokin su ya gyara zama yace "Baiwar Allah, a gaskiya yau d'in nan na ji kunyar abin da ya faru a gidan nan, sai da zuciyata ta wahala kafin na yarda Khadijata ce ta aika abin da ta aika ta, saboda ni dai nasan tawa Khadijar mai hak'uri ce da kawar da kai, amma ban san ya akayi wannan karan hak'urin ta ya gaza ba, ni da na ke mata fatan ta kai k'adamin da za ta dafa dutse har ma ta shanye romonsa, amma gashi shaid'an na san min yawo da hankalin ta wajen tilasta ta yin abin da bai dace ba, Khadija, ya haka? Ya akayi ki ka bari haka ta faru? Me ya tunzura ki haka?"


Tabbas a kowane lokaci kalaman mijinta su na tasiri a kan ta fiye da yankan wuk'a, hakanne ma ya sa ta kalle shi a ladabce tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, ni ma sai yanzu na ke jin kunyar abin da na aikata, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, wannan alk'awari ne."


Sai da Usman ya lumshe ido saboda tsabar jin dad'i, ji ya yi kamar ya rumgumota jikin shi, sai dai a yanayin da ake ciki hakan bai kamata ba saboda tsaro, murmushi ya yi yace "Hakan ya yi kyau, Allah ya ba ki ikon cika alk'awarin nan da ki ka d'auka, kuma sai a ci gaba da kiyaye saboda gudun b'acin rana, wata rana ba'a san me zai faru ba a irin haka."


"Insha Allahu za'a kiyaye." Ta sake fad'a a ladabce, mayar da kallon shi ya yi ga Haseenah yace "Ke kuma Haseenah, ba wai zan tambaye ki me ya faru ko kuma waye mai laifi ba, a'a, zan fad'a mi ki wani abu ne da na ke ganin ya kamata ace tun farko kin san shi kafin ki shigo gidan nan, Haseenah."


Yanda ya kira sunan ta yasa ba ta da zab'in da ya wuce d'agowa tace "Na'am."


D'orawa ya yi da "Khadija dai matata ce tsawon shekara goma sha uku, shekara sha uku ba kwana goma sha uku bane Haseenah, kinga kenan k'arshen sanin juna munyiwa kan mu shi ni da ita, a wannan shekarun da mu ka d'auka Haseenah, wallahi, wallahi na rantse mi ki da Allah ba zan iya tuna ranar da zan ce mi ki wannan baiwar Allahr ta min ko da kallon raini ne bare tsaki ko bak'ar magana, Haseenah, kin ganta nan ki tambaye ta kiji yanda auren mu ya kasance, amma sau d'aya ba ta tab'a nuna min k'iyayya ko tsana ba, idan har na ce eh, to eh ne a wurin ta ko da a'a ne, idan na ce a'a haka ita ma za tace a'a, a iya zama na da ita ban tab'a ji ko a labarin ta ba cewa ta na da abokin fad'a ba, d'azu ma na tambayi me ya faru ne saboda shine adalcin da zan iya yi, amma a gaskiya ni nasan Khadija ba ta da tashin hankali ko kad'an, dan haka Haseenah ki kiyaye dan Allah, Khadija dai ita ce gaba da ke a shekaru da ma zuwa gidan nan, kuma nasan kinsan karin maganan da ake cewa *duk wanda ya rigaka bacci dole zai rigaka tashi*, ba na so ki sawa zuciyarki irin tunanin matan yanzu cewa, wai ko shekara d'ari ka samu mata a gidan mijin ta, to wata na shigowa gidan kuma tasan mijin sun zama d'aya, eh tabbas dukan ku matana ne kuma d'aya ku ke, amma ki sani Khadija ta riga kwana a gidan nan har da ma tashi, duk da Allah bai bamu 'ya'ya dayawa ba, amma dai ita ce uwar d'an da ni a yanzu na ke kallo kuma ina jin dad'i, sannan Haseenah duk da ki na ganin kamar kinsan komai a kai na har yanzu da saura, sani na a namiji ba shine sanin da ya kamata kuyi alfahari da shi ba, me na ke so?Me  ye ba na so? Me ke sani farin ciki? Me ya ke b'ata min rai? Me yafi saka ni nishad'i da akasin haka? Wannan shine ya kamata ki zage damtse wajen sani, sai maganar makauniya da ki ka kira ta da shi, a gaskiya ba zan b'oye mi ki ba Haseenah rai na ya b'ace fiye da yanda ki ke tunani, me ya sa ba ki yi tunanin larura ce da Allah ya d'ora mata ba, wacce ke ma ba ki wuce ya jarabce ki da ita ba? To wannan ya zama na k'arshe da ko a mafarki za ki sake kiran da makauniya, kin fahimta?"


Haseenah da zuciyar ta ke tafasa ta ke jin kamar ta fashe da ihu, saboda ganin duk ya tattara laifin ya d'ora mata, hakanne ya sa hawaye su ka zubo mata ta d'ago kai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri, insha Allah za'a kiyaye."


Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, sai ki bata hak'uri, da fatan hakan ba zai sake faruwa tsakanin ku ba."


A hankali ta kalli Khadija tace "Ki yi hak'uri aunty Khadija, insha Allah ba zan k'ara ba."


Hannun ta Khadija ta rik'o tace "Ba komai yer uwa, ki gafarce ni nima kinji, sharrin zuciya ne da b'acin rai, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."


Cire doguwar rigar shi ya yi ya fad'a ban d'aki dan yin wanka, mik'ewa Khadija ta yi tare da hannun Haseenah tace "Ki je ki taya shi wanka, zai iya wuni bai saki maganar nan ba, amma da kin mi shi abin da ya dace sai komai ya wuce."


Tura ta tayi ban d'akin ita kuma ta fita, ta na rufo k'ofar ta jingina a jikin k'ofar ta lumshe ido, a hankali ta ji zuciyar ta na hasko mata mijin ta da Haseenah a ban d'akin, yanda ta san mijin ta da sauk'in kai da raha da barkwanci ta san yanzu har sun fara juyewa, da sauri ta bud'e ido har sun cika da hawaye, "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim." Ta furta ta bar wajen, ta na zuwa ta samu Bilal har ya shirya cikin gajeran wando da riga, *cornflakess* ta d'auko da kofi da madara ta yamutsa mi shi, ba dan ran shi na so ba ya karb'a ya na turo baki, shafa kan shi ta yi tace "Yi hak'uri mana yarima, yau ne fa kawai, kuma yanzu za'a kammala abinci."


Cikin turo baki yace "Mummy ni da wannan abun gwara ki bani ayaba na ci."


"Shikenan to." Ta fad'a ta na mik'ewa, friji (fridge) ta nufa yar k'arama da ke d'akin na ta wacce ita ta siyi abar ta, ta d'auko ayaba biyu da gwanda da ke yanke a faranti ta dire gaban shi tace "To maza ka ci."


Da sauri Bilal ya fara ci dan yunwa ya ke ji sosai, kuma a k'a'ida ya na zuwa gida zai samu maman shi har ta kammala abincin, fita Khadija ta yi ta bar shi ta nufi madafa, sai da ta gyara ko ina kamar babu abin da akayi b'ari a ciki sannan ta d'ora ruwan zafi, cikin sauri ta ke komai in da ta b'areye doya ta zuba sannan ta fara had'a sauce d'in.


_Tukunya ta d'ora ta zuba mai, bayan ya yi zafi ta zuba silalallan naman ragon da ke fridge wanda ya ji albasa attarugu da maggi, soya shi ta yi sosai ya soyu kafin ta kwashe, albasar da ta yanka mai yawan gaske ta zuba a cikin man, haka ma tumatiri d'anye da ta yanka da fad'i ta zuba a  ciki, rufewa ta yi ta fara b'are tafarnuwa, zuwa lokacin albasa da tumatir sun rusuna sosai, kayan k'amshi da gishiri ta zuba kafin ta jajjaga ataru da tafarnuwa da poivron kafin ta jujuya sosai, maggi ta saka da yan ruwa kad'an sannan ta sake rufewa, a lokacin kuma doyar ta ta silala ta juye ta a mataci kafin ta zuba ta in da ya dace, komawa ta yi kan miyar nan ma komai ya yi daidai, k'wai ta d'auko guda uku d'anye ta fasa shi cikin wata k'aramar roba ta kad'a shi sosai, cikin miyar ta zuba ta na motsawa saboda kar ya yi gudaji-gudaji, ta na zubawa kuma ta kawo soyayyen namanta ta zuba sai ta rage wuta dan ta k'arasa dahuwa, doyar ta d'auka ta kai kan teburin d'akin Usman ta dawo ta juye miyar bayan ta fitarwa da mai gadi na shi, tsaf ta jera su akan teburin._


Ta juyo za ta fita dan yin wanka ta ji fitowar su daga d'akin, juyawa ta yi ta kalle su da murmushi tace "Barka da fitowa."


Sai da ya kalli teburin yace "Barka baiwar Allah."


Haseenah ta kalla tace "Amarya ki yi hak'uri na yi karambani, na kammala mi ki girki amma fa mai sauk'i ne, ban san ko zai birge ki ba."


Ta wutsiyar ido ta harare ta amma sai ta yi murmushi tace "Haba aunty Khadija ya ki ka wahalar da kan ki? Gashi kuma da fitar da zaiyi yanzun abinci ne zai siyo mana."


Da mamaki Khadija ta kalle ta tace "Siyowa kuma, haba dai amarya, gidan nan cike da abinci Allah ya hore, ga kuma mata ma su rai da lafiya, amma ya fita siyo abinci, a'a gaskiya sai dai in da wata larura."


Usman da ke kallon ta da murmushi ne ya taka ya isa ga kujera ya ja ya zauna, tangale hab'a ya yi ya kalli dukan su yace "Ku taimaka ni ku zuba min abincin to na ci."


Haseenah da ranta ya gama b'acewa saboda abin da Khadijar ta fad'a d'akin ta ta nufa tace "Aunty kawai ta zuba, tun da dama ita ta yi girkin, ni wanka zanyi."


Da sauri Khadija tace "Ni ma fa wankan zan yi." Amma ina Haseenah har ta fita ta shiga k'ofar da za ta sadata da na ta falon, abu d'aya da Khadija ta fahimta shine Haseenah ba ta ji dad'in abin da ta yi ba, ita kuma ta yi ne saboda ita ce silar zubar mata da girkin da ta d'ora, juyawa ta yi ita ma za ta tafi sai kuma ta juyo, idon su ne suka had'u da na Usman da ke kallonta, kamar yanda tasan ba ya iya shirya kansa da kyau in ba ita ta taimaka masa ba, hakan ta ke da yak'inin ba zai iya zuba abincin nan ba in ba wani ya zuba masa ba, dawowa ta yi ta zuba mi shi ta zauna nesa da shi tace "To maza ka bada himma."


Kwab'e fuska ya yi yace "In dai ba za ki ci ba ni ma haka."


Kallon shi ta yi tace "Gaskiya sai dai ka jira Haseenah ta zo ku ci, wanka yanzu kawai na ke son yi."


Rumgume hannaye ya yi a k'irji yace "Da alamar maganar ki ke so."


Wata dubara ce ta fad'o mata dan haka ta mik'e tace "Shikenan to ina zuwa, bara na kira Bilal."


Ta na fita ta samu Bilal a falo tace "Bilal, tashi mahaifin ka na jiran ka ku  ci abinci, ina zuwa yanzu ka ji."


"To Mummy." Ya fad'a yana nufa falon, wanka ta shiga shi kuma ya na zuwa Usman ya rumgumo shi jikin shi ya na fad'in "Yarima na ya ka ke?"


Baice komai ba ya kalli Usman d'in ya na turo baki, lab'e baki Usman ya yi yace "Ko dai yaro hushi ya ke da baban sa ne saboda bai je d'aukar shi ba?"


Sai lokacin ya saki fuska yace "A'a Abba, bacci na ke ji."


Duk da girman yaron amma haka ya zaunar da shi akan cinyar shi yace "To idan mun ci abinci sai ka yi baccin ko?" A tare suka saka hannu su na cin abincin su na hira, har sun ida su na nan zaune suna ci gaba da hirar su irin ta d'a da uba Haseenah ta shigo, kallon ta Bilal ya yi yace "Sannu aunty."


Da murmushi har kunne ta amsa da "Sannu yarima, ya ka ke?"


"Lafiya lau." Ya fad'a ya na saukowa daga k'afafun Usman, fita ya yi daga d'akin Usman bai hana shu saboda ya na so ya yi magana da ita, ya na ganin fitar shi ya kalle ta da kyau lokacin da take shirin zaunawa, riga da siket ne na kanti wanda su ka kama jikin ta sosai, siket d'in ko k'asa bai gama sauka ba, sannan babu d'an kwali a kan ta, sai da ta zauna yace "Haseenah, yanzu ki na ji a jikin ki wannan kayan sun dace ki saka su a yanzu kuma har ki fito da su?"


Da mamaki tace "Ban gane ba? Me wannan kayan su ka yi?"


Murmushi ya yi yace "Ba fa mu kad'ai bane a gidan nan, wannan kayan da ya dace ki saka ne da dare lokacin da mu ka rage daga ni sai ke."


Cike da tsiwa irin ta yan zamani tace "Matsala, wannan ita ce matsalar da ake magana in dai har ka auri me mata, ba ka isa ka sake ka wataya yanda ka ke so ba, yanzu dan Allah me wannan kayan su ka yi? Na ga kai miji na ne, me ye dan na saka wannan kayan a gida na?"


Har kas'an zuciya maganar ta ta tsaya mi shi a rai, amma sai ya kawar da kai kawai ya mik'e yace "Zan fita ni sai anjima."


Binshi kawai ta yi da harara, dan yau ita zuciyar ta fal take da tarin k'unci, wani faranti ta janyo gaban ta ta bud'a kwanukan, sai da taja numfashi saboda k'amshin da ya daki hancin ta, ai kuwa zubawa ta yi sosai ta kuma ci ta k'oshi ta ma manta waya girka, dan har ga Allah abincin ya mata bala'in dad'i, ko dan ta na jin yunwa ne oho.


Khadija ma na gama shiryawa sai da ta yi sallah kafin ta cika cikin ta da kayan marmari da yan dubaru, daga nan kuma bacci ta shiga dan a huta ma rai.



Kiran sallah ne ya tashe su duka gidan, Bilal masallaci ya nufa kafin ya dawo ya shirya zuwa makaranta, Usman da kan shi ya zo ya d'auke shi su ka tafi lokacin Haseenah har ta shiga girkin dare. 



*Mummyn Sultan*

*Mamienmu*

*My sweet Hawwer*

*My lovely Hawwer*

*Mummyn Ameer & Khairat*

*Sis Alawiyya*

*Sis Fusseina*

*Momyn Rasil*


_Da duk wanda baiji sunan sa ba, zaiji anan gaba insha Allah._

23/01/2020 à 13:43 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *15*



Haseenah dai a shirye take da samu zuciyar mijinta ita ma, hakan ya sa yau ma abinci ware mu su na su ta yi ta kai falon ta, sannan ta zuba maganin saboda ta na so yau ya ci na uku kenan, Bilal ta k'walawa kira tun daga madafar, hankalin shi ya tafi kan kallon da ya ke a *mbc action*, Khadija da ta fito daga d'aki cikin doguwar riga ta shadda ne tace "Bilal ba ka ji auntyn ka na kiran ka ne?"


Da sauri ya mik'e ya nufi k'ofar ya na fad'in "Banji ba Mummy." Ganin ya nufi k'ofar falon ta ya sa tace "Ta na madafa ina jin."


Da sauri ya nufi can, ya na zuwa ta mik'o mi shi kular abinci tace "Abincin ku kai da maman ka."


Jiki a sanyaye ya karb'a ya na kallon ta da mamaki, haka ya juyo ya fito ya kawo abincin maman shi na zaune, aje kwanan ya yi gaban ta ya d'ago ya fad'a kusan k'afafun ta yace "Mummy abincin mu ne wai inji aunty."


"Abinci kuma?" Cewar Khadija ta na yamutsa fuska, "Eh." Cewar shima Bilal d'in, gyara zamanta ta yi kamar wata hamshak'iya matar shugaba akan kujerar tace "Ka kaiwa mai gadi shi."


Ba musu ya d'auki kwanon ya fita da shi, ya na zuwa ma har ya samu ya na cin na shi abincin, cike da ladabi ya aje kwanon gaban shi yace "Baba *Garba* ga abincin ka."


Da mamaki ya kalle shi yace "Abinci na kuma d'an Alhaji? Ai gashi nan har na kusan kai shi k'arshe ma, ko dai makuwa ka yi."


Da dariya Bilal yace "A'a Baba, wannan Mummy  e tace na kawo ma ka."


Jim ya d'anyi kafin ya janyo kwanon gaban shi ya na fad'in "Allah sarki, Hajia ta d'auka ba a aiko min da shi bane ina ga? To ka ce angode ka ji ko, ai ba'a maida abinci ba, ko almajirai na bawa tun da na koshi ma."


Juyawa Bilal ya yi Garba ya bi shi da "Sai da safe d'an Alhaji." Duk abin da ya faru akan idon Haseenah wacce ke shirin rufe madafar, k'wafa ta yi tare da mirmushi ta rufe kafin ta wuce d'akin ta, sai da ta gama shirinta tsaf cikin riga da wando masu shegen kyau kafin ta zauna zaman jiran shi.


Kamar yanda ya zamar masa jiki haka yau ma, ya na dawowa da matsananciyar yunwa kai tsaye falon Khadija ya nufa, da sallama d'auke a bakin shi, da gudu Bilal ya tare shi ya na fad'in "Sannu da zuwa Abba."


Cike da rangaji ya d'an rumgume shi yace "Sannu yarima, ya ka ke?"


Mik'ewa Khadija ta yi ta d'auko ruwa da kofi lokacin ya zauna in da ta tashi ya cire hular kan shi, durk'usawa ta yi gwiwarta d'aya a k'asa ta fara tsiyaya ma sa ruwan ta na fad'in "Ko ba ka fad'a ba alamun sun nuna a gajiye ka ke, sannan ka na tare da matsananciyar yunwa wacce ke neman jigata min kai, amma yanzu ka fara da ruwa ma su sanyi." Ta fad'a hakane lokacin da ta mik'o masa kofin ruwan.


Da tattausan murmushi a fuskar shi ya karb'a ya kafa a baki, sai da ya shanye duka ruwan kafin ya sauke numfashi mai k'arfi ya mik'a mata ta karb'a, aje wa ta yi gefe ta janyo k'afar shi ta soma cire masa takalman sa k'afa ciki, zaunawa ta yi kusan shi ta na kallon shi, ido lumshe ya ke kallonta yace "Uwar gida na sarautar mata."


Da wani tsadadden murmushi ta amsa da "Labbaika."


Cike da kasala yace "Wanka na ke so na yi, amma kuma yunwa ba za ta barni ba, yanzu ki zab'a min wanda zai fara yi."


Sai da ta d'an saci kallon Bilal da ya ke tsaye gaban telebijin ya na kallo sannan ta kalle shi tace "Ka k'arasa shiga mana wajen amaryarka, ita ce za ta zab'a ma ka, ko ka manta har yanzu kwananta ka ke?"


Wata doguwar hamma ya yi kafin ya kalle ta yace "Wai ni ban tambaye ki ba ma, yaushe ne kwananki zai zo ne?"


"Me ya sa ka tambaya?" Ta fad'a ta na shafa wuyanta, saida ya rufe ido yace "Ina so na san ranar da zan dawo hannunki ne kawai."


Shiru ta yi ba tace komai ba shi kuma ya mik'e yace "Zan shiga ciki na yi wanka, amma ki tabbatar kun shigo akan lokaci dan mu ci abinci."


Da kallo kawai ta bishi har ya shige ciki, takalman shi ta d'auka ta shiga da su d'akin ta, ya na shiga can ma wata tarairayar ya samu wajen Haseenah har sai da ya yi wanka ya canza kaya kafin su ka zo kan teburi, kallon ta ya yi yace "Ki saka hijab sai ki kirasu su zo mu ci abinci."


D'an jim ta yi kafin ta zagayo kujerar shi ta zauna akan k'afar shi ta na shafa d'an gajeran gemunshi tace "Hubbi na, ban san ko tunanin da na yi zai gamsar da kai ba, amma ina fatan ba zai zama kuskure a gare ka ba, ka ga ni amarya ce, kuma kowace amarya ta na so taga ta more amarcinta babu takura da matsi, wallahi har zuciya ta ba na jin aunty Khadija da Bilal a matsayin takura a gareni, sai dai ina so na sati d'ayan nan mu dinga cin abinci tare da kai, amma kuma na san hakan ba zai yiwu ba saboda ka saba cin abinci da iyalinka, amma gaskiya idan ba ka min wannan alfarmar ba zai sa na ji kamar ba ka d'auke ni a matsayin..."


Da sauri ya rufe mata baki yace "Wa ya fad'a mi ki ke ba iyali na bace? Ai tun ranar da aka d'aura mana aure mu ka zama iyali ni da ke, dan haka kar ki sake fad'in haka, yanzu ba dai maganar cin abinci tare bane?"


Kai ta d'aga cike da shagwab'a alamar eh, d'orawa ya yi da "Angama da wannan buk'atar, sai kuma wata idan akwai, zan wa Ummyn Bilal magana za ta fahimta, sai dai yanzu ki zuba mu su na su abincin sai ki kai mu su, ko ya ki ka gani? Tun da ai ba sa zauna da yunwa ba."


Shiru ta yi kamar za ta fashe da kuka ta kalle shi tace "Ban san me ya sa ba, amma dai da ido na naga Bilal ya kaiwa mai gadi abincin da na ba shi su ci, watak'ila bai mu su dad'i bane."


Shiru ya d'anyi kafin ya kalle ta yace "Shikenan, zuba mana abincin."


Zubwa ta yi amma kuma sam ta k'i yarda ta ci wai ita ta k'oshi, ba dan ran shi na so ba ya ci sai dan kar ta ji ba dad'i, amma har ga Allah abincin bai masa ba, domin kuwa yau ma dai shinkafa ce da jar miya, shi kuma bai fiya cin shinkafa ba da dare, sannan kuma ga ya ji da abincin ma ya yi, da k'yar ya d'an tuttura ba tare da ya nuna mata ba, su na kammalawa yace su je falon Khadija, cikin shagwab'a tace "Wanka fa zan shiga yanzu na yi shirin bacci."


Murmushi ya mata yace "To a shirya da kyau kafin na dawo."


Cikin kwarkwasa tace "To amma fa kar ka jima sosai, wallahi idan ka jima ni bacci na zanyi."


Sai da ya janyota jikin shi yace "To ki ba ni minti talatin, ya isa?"


Waro ido ta yi tace "Talatin? Ai na d'auka saida safe za ka musu, ashe wajen aunty Khadija za ka je ku sha soyayyar ku."


Yanda ta yi maganar da shagwab'a ya sa shi darawa, rusunawa ya yi yace "To ki ban minti ashirin, hakan ya yi?"


Turo baki ta yi tace "Gaskiya sai dai in ka amince da minti sha biyar, shi ma fa daurewa ne na yi wallahi, dan ban cika son yin nesa da kai ba."


Haka kawai ya tsinci kansa da kasa yi mata musu, a cewar shi kam "Angama ranki shi dad'e."


D'aki ta nufa shi kuma ya nufi falon, ya na shiga ya same su a d'akin Bilal ya yi shirin kwanciyar shi, amma da littafi a hannun shi na addu'o'i Khadija na karanta masa ya na maimaitawa, Bilal na ganin shi ya yi saurin daka tsalle ya mak'ale a wuyanshi, cike da zolaya Usman ya fad'a kan gadon ya na fad'in "Wai wai wai, wannan yaron me ka ci hakane da ka yi nauyi? Kaga ka na shirin karya ni."


Tsaye Bilal ya yi ya d'aga rigar shi ya na shafa cikin sa yace "Sarauniya ta cika min ciki na da kayan dad'i."


Tashi ya yi zaune ya na ma Khadija wani kallo yace "Me ki ka ba shi ya ci?"


Bilal ta kalla tace "Ka tambaye shi mana ga ka gashi."


Jayo Bilal ya yi ya kwantar da shi ya ja zanin rufa ya rufe shi, da kan shi ya tofa addu'a a hannu ya shafa mi shi kafin ya sumbaci kan shi yace "Yi baccinka yariman mahaifin shi, safe lafiya."


Kallon shi Bilal ya yi ya sumbaci hannun shi yace "Saida safe Abba."


Murmushi ya masa ya mik'e, zagayawa ya yi wajen da Khadija ke zaune ya kamo hannunta yace "Muje ko kema na shinfid'e ki."


Da sauri Bilal ya juyo ya kalle shi yace "Abba, yau ma ba za ka kwanta tare da mu ba?"


Dukansu ne su ka kafe shi da ido, cikin rashin kuzari yace "Zan kwanta mana, me ka gani?"


"Ka fad'a masa gaskiya, ka ce wajen amaryarka za ka koma, ba na so ka fara sawa yarona wani tunani na daban." Khadija  ce ta yi maganar fuska a had'e, juyawa ta yi ta fita daga d'akin, kallon Bilal ya yi yace "Ka kwanta kaji ko, banda tambaya akan abin da bai shafe ka."


"Ka yi hak'uri Abba." Ya fad'a ya na k'ara jan zanin rufarsa.


Ya na shiga ya samu Khadija har ta cire rigar ta za ta shiga ta watsa ruwa, ta na ganin shi ta sa kai za ta wuce ban d'akin, da sauri ya rik'ota ta fad'a jikin shi ya na kallon fuskar ta yace "Me ye haka wai? Me ya ke damunki ne?"


Da k'arfi ta ture shi daga jikinta ta na fad'in "Dallah ni rabu da ni, ka koma wajen amaryarka mana, nasan ai ta na can ta na jiranka, me ka zo yi mana anan? Saida safe? To mun gode Allah tashe mu lafiya."


Ta na fad'a ta juya dan shiga ban d'akin ya sake rik'o ta, had'e fuska ya yi yace "Haseenah ta aiko mu ku da abinci, amma ba ku ci ba kin bawa mai gadi, ko me ya sa?"


Cikin k'unar zuci da wani zafi da ke cikin zuciya tace "Eh, ba zan ci ba, kuma d'ana ma ba zai ci ba, sannan ka fad'a mata karta sake aiko min da abinci dan ba zan ci ba, tun da ai bata ga yunwa a tare da mu ba."


Cike da mamaki yace "Khadijaaa, me ya sa ba za ki ci ba?"


Rik'e k'ugu ta yi tace "Kai me ya sa ka daina cin abinci tare da mu? Ita ce ta buk'aci hakan ko? To ya yi kyau, amma ka sani ni ba sakarya bace da za'a rainawa hankali, kai da ita ku ci na ku tare, ni da d'ana kuma ta ware mana na mu, ma'ana mu kad'ai ne ake son bala'in ya samemu, to ba zai yiwu ba wallahi, abincinta har abada ba zan ci ba."


A hankali ya zauna bakin gadonta dafe da kanshi ya kalle ta yace "Khadija a haka ki ka fahimci abun? Haba dan Allah, me ya sa ki ke haka? Karfa ina yabonki sallah kuma alwala ta gagare ki."


"Sai me?" Ta fad'a har da hararan shi, zunbur ya mik'e ya had'a da jikinshi da k'arfi ya had'e ta da bango ya na kallon k'wayar idonta, k'asa tayi da idon dan haka yace "Kalle ni nan."


Kallon shi ta yi kai tsaye kuma ta sake k'asa da idon ta, cikin daka tsawa yace "Kalle ni nan nace."


A hankali ta d'ago ta kalle shi, hawayen da suka taho mata ne yasa shi cire mata gilashinta ya wurgar da shi akan gado, duk da ta na ganinshi tsaye a gabanta, amma ba ta iya ganin shi da kyau, sassauta murya ya yi yace "Khadija, tun da muke da ke kin tab'a ko da hararan baya na bare kuma gaba na?"


Girgiza kai ta yi alamar a'a, k'ara tausasa murya ya yi yace "To me ya sa zuwan Haseenah gidan nan zai zama sanadin da raini zai shiga tsakanina da ke?"


Shiru ta yi sai hawayen da suka sake bulbulo mata, ganin shirun ya sa yace "Me ya sa idan dare ya yi b'acin ranki ke nunkuwa ne? Wani abu na ke mi ki da ba kya so?"


Da k'arfi tace "Eh, dubi can." Ta fad'a da nuna mi shi makeken gadonta da yatsa, kallo ya yi ita kuma tace "Na yi rashinka akan shinfid'a ta Abban Bilal, kwana hud'u ne kawai mu ka yi nesa da juna, amma jinsu nake tamkar shekara hud'u ne, Abban Bilal na..."


Had'e bakin shi ya yi da nata, dan gaskiyar magana akan abin da take magana baida kalaman da zai iya tausarta da su, tun da bai isa yace bai kusanci Haseenah ba, bai kuma isa yace ba zai k'ara ba, kamar yanda ba zai iya cewa ya datse kwanan Haseenahr ba, tsayuwar ce ya ji ta gagare shi hakan ya sa ya gangara zai kwantar da ita, da k'arfi ta ture shi daga jikin ta ta kalle shi tace "Kar ka sake had'a jikinka da nawa, ba na buk'atar ka."


Ban d'aki ta nufa tana goge bakin ta, shi kam fad'awa ya yi akan gado ido lumshe, ya yi iya k'ok'arin shi wajen gayyato nutsuwar shi amma ya kasa, haka ya mik'e ya fita daga d'akin amma har zuciyar shi ya na sha'awar kasancewa da Khadija, dan ita kad'ai ce ta iyashi yanda take samar mi shi da nutsuwa, ta na jin fitar shi ta fito ta zura farar doguwar riga mai kauri ta kwanta, kuka sai da ta ci ta k'oshi har ta godewa Allah, a k'arshe dai mik'ewa ta yi ta d'auki Qur'ani ta fara karatu, cikin k'ank'anin lokaci sai zuciyarta ta washe ta yi wasai da ita babu ko d'igon damuwa a tare da ita.


Usman kam na shiga dama a rikice ya ke, har d'aki ya samu Haseenah ta shirya cikin arniyar rigar bacci, ta na jin an bud'a k'ofa ta juya, amma abin da ya fito shine ya d'auki hankalinta, a tsaye ya ke k'yam abun har ya bata tsoro saboda ba ta tab'a ganin irin haka ba a rayuwarta, kafin ta ankara ya cakumota jikin shi ya manne bakinta da na shi ha haura da ita kan gado, dama dai rigar wata d'ogal ce, dan haka baisha wahalar cire ta ba, ya na shirin kaiwa ga gaci Haseenah ta dakatar da shi ta hanyar sauka daga kan gadon, kallonta ya yi a raunane yace "L...afi..y.a?"


Kayan ta ta bud'a ta d'auko riga ta zura, da sauri ya sauko daga kan gadon ya rumgumota ya sumbatar wuyanta, dan  ba zai iya magana ba, d'an ture shi ta yi taja baya ta na kallon shi tace "Ka je kawai ka kwanta ka yi bacci."


Kamar wanda ya sha kuka haka idon shi su ka yi jawur, girgiza mata kai ya yi da k'yar ya had'a kalmar "B...ba ...zan iya ba."


Ba tare da shakka ko tunani ba tace "To ka je wajen wacce ta d'ora ka sai ta sauke ka."


Banza ya yi da ita ya kumo janyota jikin shi, ture shi ta kuma yi ta kalli idon shi tace "Wallahi kaji na rantse ko ba za ka samu abin da ka ke so ba, a gaskiya ba zan iya d'aukar wannan wulak'ancin ba, haka kawai ranar kwana na amma kaje wajen wata har ka bari ta ribace ka, shine sai ka dawo min kamar kasha wani abu, to ba zai yiwu ba gaskiya."


Ta na fad'a ta kwanta kan gadon ta ja zani ta rufa, kan gadon ya haura ya dinga shafarta ya na rarrashi, amma ko kallo bai isheta ba bare ta kalli idonshi ta tausayawa halin da yake ciki, duk da ranshi ya b'ace haka ya danne ya rumgume ta har baccin wahala marar dad'i ya d'auke shi.


😂😂😂 *Surukin sis Chappa fa yau ba kanta*


Washe gari da safe haka Khadija ta gaggauta had'a sassauk'an abin karyawa, Haseenah ma haka shayi kawai ta had'a da k'wai sannan ta yi wanka, a tak'aice dai safiyar babu mai farin ciki ko karsashi, haka Bilal ya tafi makaranta Khadija kuma ta zauna kafin Uwani ta zo.


Bayan Uwai ta zo yau Khadija ta ji bata buk'atar raini a wajen Haseenah, hakanne ya sa ta d'auko tsohuwar ajiyar gas d'in ta mai d'aukar tukunya d'aya ta sa Uwani ta d'ora silalar nama dan suyi na su girkin, su na cikin aikin kam sai ga Kaltume ta sallamo, da farin ciki Khadija ta tarbi k'awar ta, sun jima suna hira anan wajen kafin aikin ya yi nisa Khadija ta barwa Uwani ta k'arasa kula da shi, d'aki su ka koma suka dinga hira har Khadija ta tsegunta mata abinda ya faru daga zuwan amarya har zuwa jiya, nan Kaltume ta jinjina al'amarin kafin ta d'ora da "Kinsan me na ke so dake k'awata?"


A raunane Khadija tace "Sai kin fad'a k'awata, wallahi kaina ya kulle."


Gyara zama Kaltume ta yi tace "Da alama yarinyar da fitsara ta shigo, amma ki bita ta bayan gida, ki nuna mata na gaba ya yi gaba, na baya kuma sai tsinkaye, ki nuna ke ba wai shekaru ku ka yi tare da shi ba, ki nuna mata ke goggagiyace a fannin sanin mijinki, ki nuna mata na ku ba irin na su bane, sannan *wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa*, kissa, k'awata yanzu kishi ma cikin kissa ake yin shi, kada ki kuskura ki bari yarinyar nan ta gane kina kishi da ita, bare harta fahimci kuna samun matsala da mijinki, k'awata abun ya na da wuya sosai, saboda ya na buk'atar k'arfin zuciya, amma ni nasan za ki iya, saboda kin jure fiye da wannan ma, yanzu ki fad'a min yaushe ne Usman zai dawo hannunki."


"Na yarda Hajiata, amma ai ko ban fad'a mi ki ba ai kin sani"


"Hakane kuma fa." Cewar Kaltume, matsowa ta yi ta rad'a mata abu a kunne, a tare suka bushe da dariya harda tafawa da hannu, Khadija ce tace "Banda mastala dake k'awata, nasan za ki gyara ni."



Bayan fitar Usman kam gida ya nufa, ya samu mahaifinshi ma na shirin fita, saida ya duk'a k'asa ya gaishe su kafin ya zauna kan tabarmar da Hajia ke zaune, fita malam ya yi Usman ya bishi da "A dawo lafiya."


"Allah ya sa." Ya fad'a fita,  kallon Hajia ya yi yace "Su Nura har sun fita ne?"


"Sun fita tun safe." Cewar Hajia, d'orawa ya yi da "Ba wani abu da ku ke buk'ata?"


Ba tare da ta d'ago ba tace "Babu komai Fodio, Allah ya yi albarka."


"Ameen Hajia."


Shiru ne ya d'an ratsa kafin Hajia ta kalle shi da kyau tace "Jiya su Rabi'a sun zo nan su ke fad'a min wani abu da ban ji dad'in sa ba ko kad'an, sai dai kuma na yi mamaki da hakan ta faru a gidan ka, duba da tsayawarka akan iyalinka da kuma hak'urin ita Khadijar."


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Hakane Hajia, nima abun ya ban mamaki, sai dai koma miye ni nafi ganin laifin Haseenah, tun da Khadija ai ba yau mu ke tare ba, ko tsakani na da ita bamu tab'a samun matsalar da za ta saka mu d'agawa juna murya ba."


"Toh, haka kai ka ke gani, amma yan uwanka ba haka su ke gani ba, sunfi ganin laifin Khadija."


Murmushi ya yi yace "To Hajia koma me su ke gani ai wannan matsalar su ce, tun da dai ni ga yanda nake gani kuma na sani."


"Hakane, Allah dai ya kyauta, amma dan Allah a saka ido sosai saboda gudun abin da zaije ya dawo."


"Insha Allahu Hajia."


Mik'ewa ya yi ya zura takalmin shi yace "Hajia ni zan wuce, amma anjima da dare zan dawo, dan mun kwana biyu bamu had'u da yan rigamar nawa ba (k'annan shi)."


Daroya ta yi tace "Gaskiya kam, dan tuni ma su ka fara k'orafin amarya ta b'oye ka."


"Na sani dama ayi hakan." Ya fad'a ya na dariya, har ya juya Hajia tace "Yawwa har na sha'ada ban fad'a ma ka ba."


Juyowa ya yi ya dawo ya sunkuya, d'orawa ta yi da "Jiya matar *Issoufou* (d'an k'anin baban shi) ta haihu, an samu 'ya, idan ka samu dama sai ka je, su ma kuma matan sai ka fad'a mu su."


"Ah masha Allah, insha Allah kam Hajia zanje, amma na yi mamaki da bai kira ni ba."


"Watak'ila ya manta ne."


"Ba shakka kam." 


Da haka ya bar gidan kuma ya na shiga mota ya kira Issoufou, take yace mi shi su had'u gidan yanzu zai je, haka ko akayi, ka zuwan nashi alkairi ne, domin kuwa kud'i ya bashi ma su yawa ayi hidima, bayan tafiyar shi kuma sai ya ya sa aka kawo mi shi kayan abinci, daga nan kuma makaranta ya wuce d'aukar Bilal. 


Suna ta hirar su cikin farin ciki sai ga Usman tare da Bilal, sannu da zuwa suka ma sa in da ya dinga tsokanar Kaltume su na wasa da dariya, da haka ya lek'a wajen Haseenah, ya samu ta na girki ba ta gama ba, dan haka ya fita yace sai ya dawo, saida ya dawo su ka yi sallama da Kaltume, sai dai mamaki ya kama shi ganin su na cin abinci har da Bilal ma, dan shigowar shi ya ga gas a waje da tukunya, sam bai kawo a ran shi abinci su ka girka ba, haka ya fita da tunani iri iri da kuma niyyar tsayar da wannan abun, dan ba zai yarda tun yanzu su raba mi shi kan gida ba ta hanyar raba abinci.


_Ah to banga laifinka ba._🤷‍♀


*Luv u guy's*

24/01/2020 à 21:19 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_


_*ALLAH GATAN BAWA*_



                      *16*




Farar miya Haseenah ta yi da shinkafa, ba wai miyar ba ta yi bane a wajen Usman, sai dai ji ya yi cin shinkafar ta gundure shi, kuma hakan baya rasa nasaba da sabon da Khadija ta mi shi na girka abinci kala kala, musamman da tasan ba ya san shinkafa sosai, sai ta yi wata d'aya ba ta girka ta ba, yanzun ma bai wani ci mai yawa ba ya bar shi, ko da ya yi wanka ya shirya falon Khadija ya shigo, Uwani na ganin haka ta mik'e ta fita, Bilal kuma dama ya na ciki ya na shiri, Kaltume kam ta na sallah la'asar ta wuce gida, zaune ya yi kalle ta ta na fad'in "Har ka fito?"


"Um." Ya fad'a ya na sake kafe ta da ido, ita kam gyara gilashinta ta yi ta kalle shi tace "Ya dai? Da magana ne? Wannan kallon haka."


K'asa ya kalla kafin ya kalle ta yace "D'azu da na shigo sai na ga kamar girki ku ka yi ko?"


Ba tare da shakka ba tace "Eh, girki na yi, da matsala ne?"


Gyara zama ya yi kamar zai had'e ta yace "Sosai ma, Khadija kar ki ce min ba ki hango matsalar da ni na hango ba, hakan bai dace ba, kuma gaskiya ba na so, idan har zai yiwu, to cikin d'aya dole ku yi d'aya, ko dai ku had'a kanku ku dinga girki tare, ko kuma dai duk ranar girkin d'aya to d'aya ba za ta tab'a d'ora min tukunya ba da sunan girki ba, wannan hukuncin yankakke ne, kuma umarni."


Mik'ewa ya yi ya juya ya kalli d'akin Bilal ya kalli agogon hannun shi, mik'ewa ta yi ta kalle shi tace "Ban k'i ta taka ba, amma kafin ka yanke wannan hukucin ya kamata ka fara fad'awa amaryarka cewa ba'a raba abinci a gidan nan, in dai har za ta ci gaba da ware mana abinci ni da yarona, to wallahi ba zan ci ba haka ma d'ana, kuma ko kaga ai bama zauna da yunwa ba alhalin Allah ya hore abinci ta ko ina, wannan shine."


Ta gaban shi ta rab'a za ta wuce ya rik'o hannunta, kallon ta ya yi yace "Na fad'a mi ki ba na so, raba abinci kuma na yan kwanaki ne da ba su taka kara sun karya ba, idan ki ka duba tsawon lokacin da mu ka d'auka tare hakan bai tab'a faruwa ba, me ya sa yanzu za ki gagara fahimta Khadija? D'an lokaci fa kawai tace a bata ita ma ta san ta na da miji, me ya sa za ki zama mai son kan ki dayawa, me zai rage ki idan ki ka hak'ura ki ka ci abincin, nan da lokacin da kwananta zai k'are fa shikenan komai ya wuce."


Rik'e k'ugu ta yi da hannu d'aya tace "Uhum! Anzo gurin, yau kuma sai gashi ka na fad'in wai ni ce mai son kai na, ni ce mai son kai na yau? To na ji kuma nagode, amma ka sani in dai wannan ne son kai to tabbas ni mai son kai na ce, wallahi ba zai tab'a yiwuwa ba ta barbarad'a min iskanci a abinci sannan ta bani na ci, wallahi ka ji na rantse ko ba zai yiwu ba, rai a baran mai shine, lafiya kuma uwar jiki, daidai da ciwon hannu wannan idan ya same ni akwai abin da za ka iya yi min ne? Ni fa zan ji zafin kuma na yi jinyata, hasalima duk soyayyar da ka ke sauki burutsun cewa kana min wallahi babu abin da za ka iya tsinana min, haka kawai kuma sai na jefa kai na a motar da na tabbatar ba ta da birki, rai fa guda d'aya ne."


Yanda take masifa sai abun ya ba shi dariya da mamaki, a zaman shi da ita bai tab'a ganin ta na fad'a haka ba sai yau, b'ata rai ya yi yace "Wallahi ba da wasa nake ba, kar ki sake d'ora min tukunya indai har ana girki a gidan nan, kinji na fad'a mi ki."


Za ta yi magana Bilal ya fito daga d'akin, sai kawai ta yi murmushi ta sa hannu ta shafo d'an gemunshi ta kashe masa ido tace "Ban ji da kyau, d'an sake maimaita min."


Dariya ce ta so sub'uce mi shi sai ya dake ya matsa kusan ta ya rad'a mata a kunne "Wallahi karki sake na sake ganin kin aza girkin ki, in ba haka ba rai zai b'ace fa."


Bilal ne ya shiga tsakansu ya na fad'in "Idan na bi taku sai na makara islamiyya, muje Abba."


Hannun shi ya kama ya na juyowa ya na kallon Khadija, ita kam wani shegen murgud'a baki ta yi irin ai ba ka ma isa d'in nan ba, daga yanda ya motsa bakin shi ya tabbatar mata da k'wafa ce ya yi, gwalo ta masa tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki wayar ta, su na fita ta ci gaba da latsa wayar ta hankali kwance, kamar daga sama ta ke jin k'amshin daddawar kalwa na bad'e ko ina na gidan, tashi ta yi ta fito farfajiyar gidan sai ta fahimci daga madafar su ne ya ke fitowa, kai tsaye ta shiga ta samu Haseenah ta zage ta na tuk'a tuwon shinkafa, da murmushi Khadija tace "Amarya sannu da aiki, yau kuma tuwo ake mana?"


Wani takaici ne ya taso ma Haseenah wacce ke wahalar tuk'a tuwon, k'ala ba tace mata ba sai Khadija ce ta sake cewa "Sai dai kuma mijinki baya cin tuwo da dare, ko bai tab'a fad'a mi ki ba? Musamman ma na ga wake ne ki ke miyar da shi, kuma ba ya cin wake ko kad'an, amma za ki iya had'a ma sa wani sassauk'an abun, mu sai mu ci tuwon dan munyi kewar shi."


Ran Haseenah ne ya yi mugun b'aci tace "Kutumar uba, baiwar Allah na fad'a mi ki ina neman taimakon ki ne? Kinga Khadija, gaskiya ba na son haka, mijin ki ba ya cin tuwo a lokacin da ke kad'ai ce cikin gidan, yanzu kuma Haseenah ta shigo, dan haka ki barni na yi rayuwa ta mana, ki barni ni ma na kafa salon nawa tarihin a gidan nan kuma a zuciyar miji na, amma ba ki dinga min shishigi ba, ba lallai dan kin saba mi shi da saka kalar fari ba ki ce nima wannan kalar ki ke so na saka mi shi, ki barni na yi abin da ya dace, nan gidan miji na ne."


Wani warrr Khadija ta yi da manyan idon ta kafin ta sa hannun ta tana fifita da shi tana fad'in "Wash Allah, zafi."


Kallon Haseenah ta yi da murmushi tace "Sannu mai miji, Allah ya bar k'auna."


"Ameen." Ta fad'a har da zaburowa, fita Khadija ta yi, tsaf Haseenah ta gama tuwonta ta mulmule, da kan ta ta kawowa Khadija na su tuwon, ko k'ala ita ma ba tace da ita ba har ta fita, Uwani ce ta tashi tafiya tace "Uwani d'auko wani kwano a d'akin can ki tafi da abincin nan."


D'aya d'akin ta shiga da ke da tarkacai abubuwan buk'ata ta fito, juye tuwon ta yi ta tafi da shi bayan sun yi sallama, Bilal ne ya shigo gida shi kad'ai da takarda a hannun shi, rumgume maman shi ya yi ita kuma tace "Wa ya dawo da kai ne?"


" *Bilyaminu* ne Abba ya tura ya d'auko ni, Mummy karb'i wannan." Ya fad'a bata takardar, ta na dubawa tace "Har wata ya k'are kenan?"


Kai kaxai ya d'aga mata, ba shi ta yi tace "To ka aje wurinka idan Abbanka ya dawo sai ka ba shi, amma ni zan iya mantawa."


A tare su ka tashi ita ta shiga d'akin ta saboda magriba ta gabato sosai, kaya kawai Bilal ya canza ya wuce masallaci, Khadija ma na idar da sallah ta shiga wanka, shiryawa ta yi sosai kafin ta lalabi gilashin ta na jiya da Usman ya cilla kan gadon, dan tun jiya bata waiwaye shi, shi ta saka dan ya fi mata kyau sannan ta fito, zaune suke ita da Bilal su na kallo su na hirar su, bayan sallah isha'i ko da su ka yi sallah abincin ranar da Uwani ta kwashe mata a kula ta d'auko ta zuba, tare su ka ci hankali kwance su ka k'oshi, hamdala su ka yi kafin su ka tashi kamar ba su ci ba.


Kamar yanda ya yi alk'awarin komawa gida haka ya wuce, ya kuma samu su Kabir Mannir da Nura, hakan ya sa suka bud'a babin hira su ka dinga yi, Haseenah da ke jiran shigowar shi taga shiru sai da ta kai ga kira, amma sai ya d'aga yace ya na gida zai zo ba da jimawa ba, amma fa bai zo d'in ba saboda suna tattaunawa da ahalin shi, sai wajen *22:20* ya baro gidan ya nufi gida, Khadija har sun kwanta ita da Bilal ya shigo, ko da ya ga babu wuta a falon sai ya wuce falon shi kai tsaye, Haseenah na ganin shi ta d'ago kai ta kalle shi, ba fara'a ko sakin fuska tace "Sannu da zuwa."


Sai da ya kamo hannun ta tayi tsaye ya rumgume ta yace "Sannu da gida."


Kamar ba ta son magana ta amsa da "Yawwa."


Kallon fuskarta ya yi yace "Ki yi hak'uri na barki ke kad'ai ko? Ina can gida tare da yaran nan su na ta min shirme."


Cikin shagwab'a tace "Na ji to, yanzu dai mu je ka yi wanka sai ka zo ka ci abinci."


Rimgume ta ya yi yace "Wallahi kamar kinsan kam na d'ebo yunwa, muje ki kintsani yanda ya kamata."


D'akin shi su ka nufa, bayan ta taya shi wanka ya canza kaya su ka fito, ya na jan kujera ya kalle ta yace "Da alama su Bilal har sun kwanta ko?"


Kallon shi ta yi tace "Eh to ban sani ba dai, amma tun da na ji shiru babu hayaniyar tv na ke tunanin haka."


Ba tare da ya kalle ta ba yace "Haseenah me zai hana idan ba na nan ki dinga zuwa wajen su ki na zama ku na hira? Ina ga hakan ai zaifi ko? Tunda daga ke sai sune a gidan, kuma sune abokan rayuwar ki a yanzun."


Ta na aza marar tuwo a farantin ya kalle ta, bai kai ga jin amsarta ba yace "Haseenah tuwo ki ka dafa?"


Kallon shi ta yi tace "Eh, da matsala ne?"


Ya na ci gaba da kallonta yace "Khadija ta ga ki na aikin nan?"


Sam Haseenah ta ma manta da abin da Khadija ta fad'a mata, sai kawai tace "Eh, me ya faru?"


Da wani irin kallo yace "Kuma ba ta fad'a mi ki komai a game da hakan?"


"A'a, wai me ya faru ne?" Ta fad'a cike da k'aguwa, a hankali yace "Shikenan kawai, zo zauna nan."


Janyota ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi ya na kallon fuskarta yace "Haseenah, ki yi hak'uri kinji, ina ganin laifi na ne da har mu ka yi soyayya da kai ba tare da kinsan abubuwa da dama a kai na ba, kuma hakan ya samo asaline saboda ba mu jima tare ba, sannan ni mutum ne da bai cika fad'an abin da ya shafe shi ba, amma a gaskiya ni ba na cin tuwo da dare, ba kuma shi kad'ai ba, akwai abin da ma kwata-kwata ba na cinsu kamar wake da nasan sa, sannan kinga shinkafa ma ban cika son ta ba haka, sannan kifi ma ba na cin shi da dare, wannan shine."


Bushewa ta yi da dariya ta sauka daga cinyar shi taja kujera mai fuskantar shi, da k'yar ta tsayar da dariyar tace "Miji na, ka na d'an africa, a africar ma a niger, kuma ka ce ba ka son shinkafa, lallai ka na jin dad'in ka."


Ganin ta mayar da abun kamar wasa ya sa ya d'an gimtse fuska yace "Ni dai ban son ta, na fad'a mi ki ne dan ki kiyaye."


Ita ma had'e fuska ta yi tace "To yanzu tuwon nan fa ya zanyi da shi?"


Shima dariya ya yi yace "Ku ba kun ci ba? Kawai ki samar min wani abu na ci."


Cike da kasala tace "Kamar me fa?"


"Ko taliyarku ta yara ki d'ora min." Yanda ya yi maganar da zolaya ya sa ta taso ta na dariya ta rumgume shi ta baya ta na fad'in "Yanzu ni yarinya ce a wurin ka?"


"Sosai ma." Ya fad'a ya na dariya, cikin kunne ta rad'a ma sa "Ni kam banyi tsammanin za ka iya kira na da yarinya ba."


D'ago kai ya yi ya kalle ta yace "Shekarar ki nawa ne wai dan Allah?"


Saida ta waina idon ta tace "Sha takwas."


Da sauri ya mik'e tsaye ya na k'are mata kallo, har zagayata ya ke ya na kallonta, tab'e baki ya yi yace "Lallai ina da sa'a, gani tsoho amma sai Allah ya dinga had'a ni da yara yan sha takwas shakaf."


Juyawa ta yi ta nufi madafar, d'ora tukunya ta yi duk da ba wani sanin kan indomie ta yi ba, amma dai wani lokaci ta d'an dafawa yayan ta *Mubarak*, yanzun ma yanda take yi a gida haka ta dafa, sai dai da ta zuba a faranti sai ta ga abun bai birge ta ba, dan indomien duk ta dahu sosai kamar za ta narke, to amma ya ta iya haka ta d'auko ta kawo mi shi, dakewa kawai ya yi tamaza ya d'ura indomien nan, amma bai ci sosai ba, ya na gamawa ya mik'e yace "Zan lek'a na ga su Bilal."


Kallon shi ta hi ta kalli farantin indomien, k'ala ba tace masa ba ta tashi ita ma ta wuce d'akin ta dan shirin bacci, shi ma ficewa ya yi bai kula ta ba, d'akin Bilal ya fara shiga, sai da ya k'arewa yaron kallo ya shafi kansa kafin ya fito, da sallama ya shiga d'akin amma shiru, kujerar gaban madubi ya janyo ya zauna bayan ta ya daddab'a ta, bud'a ido ta yi ta tashi zaune ta janyo gilashin ta ta sanya, kallon shi ta yi shi kuma yace "Hajia Khadija ki na lokaci, yanzu har an daina sona ta yanda ba'a jira aga na shigo lafiya ko akasin haka."


Murmushi ta yi tace "Abban Bilal ma ya na lokaci, tun da har zai shigo gidan nan amma ya kasa neman mu."


Da mamaki ya bita da kallo ita kuma tace "K'warai, na ji shigowarka ai."


"Hum." Ya fad'a ya yi shiru, ita kuma tace "Ka daina mantawa, yanzu mu biyu ne da hakk'in kula da kai, in da lokacin kwana na ne zan iya jiran ka har gari ya waye."


"Amma in ba kwananki bane kuma ko oho ko?"


"Kai ma kasan dole zan damu da kai, sai dai ba na son shiga hurumin da ba nawa bane."


Mik'ewa ya yi ya nufi frije d'in ta ya bud'a, wani k'aton cake ya d'auko mai suffar zuciya tare da yagourt mai kauri da sanyi, komawa ya yi ya zauna ya fara ci ya na shan madarar, Khadija dai kallon shi take har ya sai da ya cinye duka kafin ya mik'e, ban d'akin ta ya shiga ya wanko bakin shi ya dawo, kallon ta ya yi yace "Umman Bilal ya yarinyar can ta fad'a min kinga lokacin da take tuwo ko?"


Gyara zama ta yi akan gadon tace "Eh, na gani."


"To amma me ya sa ba ki fad'a mata ba na cin tuwo ba? Tunda ke kin sani." 


Da mamaki ta kalle shi tace "Au! Wai dama duk soyayyar da ku ka yi ba ka tab'a fad'a mata abin da ka ke so ba da wanda ba ka so? Dole sai ni ce zan dinga fad'a mata?"


Matsowa ya yi kusanta yace "A gani na ya zama dole tunda ke ce gaba da ita, me ya sa ba za ki d'ora ta a hanya ba a matsayinki na babba?"


Da k'arfi ta zaburo daga kan gadon ta sauko ta na fad'in "Oho, wato babba juji ko? Komai tunda ke ce babba ke ce babba, to daga yau na bar mata girman ta d'auka, kuma ka je ka tambaya ta idan ban fad'a mata ba ka cin tuwo ba, amma sai tace a dole ita ma sai ta d'ora ka a tsarin da ya mata, saboda ita ma matarka ce, haka kawai za ka zo ka d'ora min laifi ka cika ni da surutu."


Komawa ta yi kan gadon ta kwanta ta ja zani ta rufa, shi kam baki bud'e ya ke kallonta har ta kwanta, sunkuyawa ya yi ya sumbaci kumatun ta ya d'ago yace "Saida safe masifata."


Zunbur ta tashi tace "Masifar ka kuma? Abban Bilal ni ce ma masifar yanzu? Lallai ka kyauta."


Gimtse dariyar shi ya yi yace "To in ba tawa ba ta wacece? Ai Khadija sai Usman, Usman kuma sai Khadija, kinga dole na kiraki da masifa ta tunda na ga kin fara koyon masifar."


Cinno baki ta yi gaba ta bishi da kallo har ya kai k'ofa, sai da ya bud'e ya fita ya juyo yace "Allahya huci zuciyar Umman Bilal, ta Usman bada kanka a sare kaje gida ka ce ya fad'i, na Khadija ba ni shan furataba nono, hakan ya yi ko? Saida safe, ina son ki."


Dariya ce ta kubce mata, sumba ta aika masa tare da fad'in "Ina son ka ni ma, saida safe."



_Ni ma dai saida safen nan gaskiya._😉



*Washe gari* ta kama alhamis, hakan kuma ya sa duk yan islamiyya na hutu ba karatu, k'awayen Haseenah na su ka zo gidan tun misalin *11:00* bayan fitar Usman ba jimawa, in da Bilal ma ke gida ya na wasan shi, dan ya so ya je gidan su maman Khadija amma ta hana, a madafa suka tare su na ta hira abinsu, kasancewar *Zeinab* na da k'ok'arin aiki ya sa yau ita taja ragamar girkin gidan, abinci su ka had'a kala har uku da kuma abin sha, bayan sun gama su ka dawo falon Haseenah dan cin abinci, kiran Usman ta yi ya aiko a d'aukar mi shi abinci ta na da bak'i a gida, ba d'aukar lokaci ya aiko da yaron shi Bilyamin ya d'auka, su na ci su na kwamtsa hirarsu sai ga Mariya, sai da suka gama ta shiga da ita ciki inda ta kwashe komai ta fad'a mata, bud'ar bakin Mariya cewa ta yi "Lallai Haseenah ina tausaya miki, dan wallahi kishiyar nan ta ki ba k'aramar muguwa bace, kawai ki hak'ura ki bita sau da k'afa, domin kuwa ita da d'an ta ne da gidan nan wallahi."


Cike da damuwa Hassenah tace "Ni ma na fahimci hakan, kar ki tona raina ki ji me na ji ranar, ita ce da laifi amma ya rufe ido ya d'ora min laifin, wai shi ya san matan shi."


"Ai kad'an ma ki ka gani in dai ba ki tashi tsaye ba, yanzu dai ina magani da na baki? Kinyi aiki da shi?"


"Duka na yi, kuma ya ci abincin? Amma ni banga wani sabon abu ba."


Gyara zama ta d'anyi tace "Kinsan me zai faru, ki sake kawo kud'i a kaiwa malam ya sake mi ki wani maganin, ko da na bakali ne da kuma samun soyayyar shi."


"Kamar nawa?" Ta fad'a ta na kallonta, ita ma kallonta ta yi tace "Eh to, iya kud'in ki ai iya shagalinki."


Da alamar tambaya Haseenah tace "Ki na nufin idan na bayar da kud'i dayawa zaifi kyau aikin?"


"Sosai ma." 


Mik'ewa ta yi ta bud'a jakarta da take zuba kud'in da yake bata tun da ta zo, yan biyar biyar ko karyawa babu guda hud'u ta bata, aifa baki har waje ta karb'a suka fito daga d'akin, sallama su ka yi ta tafi ta barta da k'awayen ta, yamma ta yi suka sake tashi kama mata aiki, sai dai suna buk'atar bredi dan soya shi da k'wai, babu yaron da za'a bawa ya siyo sai Bilal ta kira dake farfajiyar gida tare da mai gadi, kud'i ta bashi ya siyo mata bredi, cikin sanyin jiki yace "Aunty nan ba'a siyar da bredi sai can nesa tsallaken titi, kuma Abba ya hana ni fita har can wajen."


A gadarance tace "Kenan ba ka da wani anfani cikin gidan? Sai dai a dafa a baka ka ci? To k'arya ka ke, maza wuce ka d'auko wannan shegen moton na ka da baida anfani sai dai ka yi yawo da shi cikin gida ko k'ofar gida ka je ka siyo ka kawo min yanzun nan."


Cikin sanyi ya juyo ya nufo wajen uwatai, d'akin da ya ke aje moton ya fito da shi, Khadija na gani tace "To, to ina kuma zuwa da wannan tuk'a-tuk'ar?"


Sai da ya zo gabanta cikin turo baki yace "Ba aunty amarya ce ta aike ni siyan bredi ba."


Da mamaki ta kalle shi tace "Bredi fa? Amma ba ka fad'a mata ba ka tab'a zuwa ko bakin titi kai kad'ai ba bare gaban shi?"


"Na fad'a mata, amma tace wai ni ban da anfani a gidan sai dai na ci abinci, kuma wai dole na je na siyo."


Wata shegiyar dariya Khadija ta bushe da ita ta  kalle shi ta kalli Uwani, mik'ewa ta yi tace "Ku biyo ni har da ke Uwani."


Fita su ka yi har madafar ta same su, sai shewa da hira su ke, suna ganin ta kowa ya yi shiru sai wani kallo ake mata, ko ta kan su bata bi ba ta kalli Haseenah tace "...



*Ku yi hak'uri da wannan.*

29/01/2020 à 13:36 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```





_INA K'ARA TAYA 'YAR UWARMU KUMA D'AYA DAGA CIKIN 'YAR GIDAN AMANA WATO MEMBER'S D'IN K'UNGIYAR *🇸🇦ZAMAN AMANA* MAI SUNA *MARYARHMAH UMMISIDDIQUE* MARUBUCIYAR *MINTI KARU'NYI YE* DA KUMA *NAGA TA KAINA* TA'AZIYYAR RASHIN UWA MAHAIFIYA DA TAYI, INA ADDU'A GA UWAR KIRKI HAR KULLUM ALLAH YAKAI RAHMA K'ABARINTA, ALLAH YA K'ARA MANA HAK'URIN RASHINTA, MUNYI RASHIN UWAR K'WARAI😰_





_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *17*



"Haseenah, ga Uwani ki bata kud'in ta siyo mi ki bredin, amma Bilal mahaifin shi ya hana a aike shi ko kusa da titi."


Sai lokacin ta juyo ta kalle ta tace "Yanzu kamar Bilal ne za ace ba'a aikin shi, shi kad'ai ne yaro cikin gidan nan, kuma ace ba'a aikin shi, to me ya sa? Me ye anfanin haihuwar shi kena..."


Ba ta sauka daga abin da za ta fad'a ba Khadija ta ji ba za ta iya d'auka ba, zuciya ce kawai ta d'ebe ta ta kife ta da mari, kafin ta ankara ta shak'o wuyan rigar ta cikin d'aga murya tace "In ke ba ki san zafin haihuwa ba ni na sani, in ba ki san darajar 'yaya' ba ni na sani tunda na haifa, idan ba ki san anfanin haihuwa ba, to ki bari har ki bari ki haifi na ki sai ki zuba cikin shara, dama ya fad'a min kin ce wai sai dai a dafa a bashi ya ci, to ki sani Bilal ba jinin matsiyata bane, ko gidan uban shi babu abinci ba zai rasa abincin da zai ci ba daga dangin uwar shi, ki kiyaye ni, sannan ki fita ido na."


Sakin ta tayi ta juya ta fice, Zeinab ce ta yi saurin kallon Haseenah tace "Wai k'yale ta za ki yi? Jar uban nan, ai wallahi babu macen da ta isa."


Wannan magana ce ta sa Haseenah d'aukar k'aramar tab'aryar da ke madafar ta fita, su na ganin haka su ka tashi da sauri su ka bi bayan ta, Khadija na daf da shiga falon ta Haseenah ta sauke mata tab'aryar nan a kai, dafe kai ta yi ta juyo ta na fad'in "Kai kai kai kai." 


Ta na ganin Haseenah ce sai kuwa ta cakume ta da kokawa,😂 (Allah ya kyauta, mata mu na bawa kan mu wahala wallahi, wata sai ki ga ma mijin da su ke fad'a akai kamar kalangu, amma haka za su yi ta bala'i a kan shi maimakon kwantar mi shi da hankali), k'awayen Haseenah na ganin haka su ka shigarwa k'awar su saboda tuni aka aza Haseenah ga k'asa ana shirgarta, Uwani na ganin haka ta fita da gudu zuwa gidan mak'wabtan da Khadija ke abun arzik'i da su, Bilal kam wayar shi ya d'auka k'arama ya kira mahaifin shi ya fad'a mi shi, mai gadi na daga gefe ya na dan Allah ayi hak'uri amma ko jin shi ba su yi, jin zafin dukan da k'awayen ta ke mata ne ya sa Khadija finciko wata daga cikin k'awayen ta had'a su ta taushe, wuri fa ya kaure ana ta bawa hammata iska sai ga mak'wabtan sun shigo, da gudu su ka k'arasa su ka d'aga Khadija daga kan Haseenah da *Farida*, anyi jina jina sosai kamar filin yak'i, cecekuce aka shiga yi tare da aikawa juna ashar, Khadija na k'ok'arin k'wacewa ta koma ga Haseenah amma an rik'e ta, su na haka fa gida ya kaure Usman ya baro mota waje ya kutso ciki, ganin su duk a yamutse ya sa ya tsaya ya sa hannu ya rufe fuskar shi, ya d'an jima a haka kafin ya k'araso wajen, k'awayen Haseenah ya fara kallo yace "Yamma ta yi, za ku iya tafiya."


Cikin sanyin jiki duka aka watse aka bar shi da matan shi, har Uwani ma ba ta tsaya ba tafiyar ta ta yi gida, falon shi ya nufa ya na fad'in "Ku same ni a falo na."


😂 *Aiki ya samu Usmanu, yanzu ma ka fara cewa a biyo ka falo ai*


Su na shiga daga zaman da Khadija ta yi zai tabbatar maka ba arzik'i, cikin b'acin rai ya yi tsaye yace "Me ku ka zama? Me ku ke son mayar min da gida? Wannan wane irin dabbanci ne?"


Tsaye Khadija ta mik'e tace "Dakata malam, dakata min, a sani na irin haka ba ta tab'a faruwa ba, to akan me sai yanzu haka za ta faru? Akan me ye amaryar ka za ta nemi ta raina ni? Ni sa'ar ta ce? Ko kai ka ce ta raina ni? Saboda rashin sanin darajar mutane har ta bud'e baki tace min wai mi ye anfanin Bilal a gidan nan, bayan kin fad'a ma sa bai da anfanin komai sai dai a dafa a ba shi ya ci, to uwar ki ce ke dafa mi shi ya na ci? To ki kama bakin ki ki dinga sanin me za ki fad'a."


Mayar da kallon ta ta yi ga Usman tace "Kai kuma dan Allah idan kun shiga ciki ka yi k'ok'ari ka sanar da ita mahimmancin d'an ka gare ka da anfanin shi gare ka, ni ba buk'atar sai na fad'a mata anfanin d'ana gare ni, amma ka fad'a mata shi kad'ai gare ni, dan haka bana had'a yaro na da kowa da kuma komai a duniya, a matsayi na na uwa kuma zan iya yin komai saboda shi."


Ta na gama fad'a ta fice ta bar su, juyowa Usman ya yi ya na kallon Haseenah, a hankali ya furta "Haseenah, ki na tambayar anfanin haihuwar Bilal a gidan nan? Ni fa uban sa ne, duk fafutukar da na ke yi saboda shine na ke yi, amma ki bud'e baki ki ce me ye anfanin haihuwar shi."


Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya dafe k'ugu da hannu d'aya yace "Maganar gaskiya Haseenah ba na so na nuna mi ki b'acin rai na, amma ki sani ko Khadija ba na buran b'acin ran ta bare kuma Bilal da ya fito daga tsatso na, ina k'aunar iyalin nan nawa matuk'a, su ne ni, su suka mayar da ni mutum da har ki ka so ni a haka, ki kiyaye furta abin da zai iya ja mi ki matsala, sannan k'awayen nan naki in har kinsan zuwan su gidan nan ba alkairi bane, to zaifi kyau ki fad'awa kowace ba na son sake ganin k'afar su a gidan nan."


Ya na gama fad'a shima ya fita ya barta, kallon shi ta yi a matuk'ar hassale ta mik'e ta nufi madafa, kashe wutar ta yi ta gyara abin da ya sawak'a ta koma d'akin ta, wayar ta ta d'auka ta kira Mariya ta fad'a mata duk abin da ya faru, nan dai ta girmama abin tare da k'ara tunzurata sannan tace ta bar komai a hannun ta, da haka su ka yi sallama ta yi wanka ta shirya, sai dai ba wata kwalliya ta yi ba dan duk jikin ta ma ciwo ya ke na tsinannan dukan da ta sha.


***************


Bayan sallah isha'i Khadija na zaune tare da Bilal a falo Nura ya shigo gidan da rahar shi kamar yanda ya saba, tun daga bakin k'ofa ya ke fad'in "Dije, Dije ba ta jina ne? Na shigo amma ki kasa tarba ta tun daga k'ofar gida."


Ganin Khadija zaune ta yi shiru sai kallon shi take ya sa yace "Ah lallai ma matar nan, ashe ki na jina na ke ta kwaroronton nan amma ki ka share ni? Ko dan yau ban baki kud'in cefanai ba?"


Khadija da har yanzu ran ta a b'ace ya ke k'ala ba tace mi shi ba, Bilal ne ya tarbe shi da murna sosai, tare su ka zauna ya na kallon Khadija ya kalli Bilal yace "Yaro waya tab'a min maman ka ne haka ta ke ta kumbura?"


Shiru Bilal ya yi ya na kallon ta, a hankali ta maido kallon ta gare shi tace "Sannu ko."


"Ai na ba za ki yi magana ba, da na tabbatar mi ki mijin gaske ne ni."


"Ya su Hajia?" Ta fad'a ba yabo ba fallasa, saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Lafiyar su k'alau, kai kawo min lemu mai sanyi na sha." Ya k'arashe da kallon Bilal.


D'auko masa ya yi ya kawo ya ba shi ya amsa, sai da ya fara sha ya kalli Bilal yace "Ina auntyn ka take?"


"Ta na d'akin ta." Cewar Bilal ya na kallon k'ofar falon mahaifin shi, tura shi Nura ya yi yace "Je ka ce ina kiran ta, ka ce ta fito ta kwashi gaisuwa tare da albarka mai gida ya dawo."


Da dariya Bilal ya nufi k'ofar falon mahaifin shi, cikin daka tsawa Khadija tace "Kai Bilal, ka na da hankali kuwa? Dallah malam dawo ka zauna min nan."


Da mamaki duka su ka kalle ta, in da ta nuna masa da hannu ya zauna hakan ya bata damar kama kunnensa tace "Wallahi ka sake zuwa in da matar can take sai na b'ata ma ka rai, kaji ko?"


Yanda ta d'aga murya tare da k'ara murd'e kunnen shi ya sa yace "Na ji Mummy, ki yi hak'uri ba zan k'ara ba."


Nura da ke kallon ikon Allah ne yace "Khadija me ya sa za ki ma sa haka? Naga da ke da ita ai duk d'aya ne, iyayen shi ne ku."


Tsaye khadija ta mik'e tace "Dakata min Nura, ni daban ita daban, wallahi duk yanda za ta kyautata mi shi ba za ta tab'a zama kamar ni uwar shi ba, dan haka kar ka sake had'a min yaro da wata banzar mata da ba ta san darajar shi ba, idan ka zo gani na ne na gode, idan wajen ta ka zo ka shiga ta na ciki."


Juyawa ta yi ta shige uwar d'akin ta, mamaki ne ya kusa kashe Nura, dan shi dai a sanin shi wani ma ba su tab'a samun matsala da Khadija ba bare kuma dangin mijin ta, cikin sanyin jiki ya aje robar lemun hannun shi ya mik'e zuciyar shi na tunanin wane irin kishi ne da Khadija haka? Bilal ne ya mik'e yace "Tonton (uncle) Nura zan bika wajen Hajia."


Shafa kan shi ya yi yace "To ka fara fad'awa Maman ka, idan ta amince sai ka d'auko kayan ka mu tafi."


"To." Ya fad'a ya juya da k'arfi ya shiga d'akin, zaune ya same ta yace "Mummy, tonton Nura yace na d'auko kaya na mu tafi gida wajen Hajia."


Cikin jin haushi tace "Babu in da za ka je, ka wuce d'akin ka ka kwanta ko kuma ka yi karatu."


Hawaye ne su ka cika idon shi saboda shi dai haka ba ta tab'a faruwa tsakanin shi da maman shi ba sai yau, juyawa ya yi zai fita sai taji ya bata tausayi, amma kuma hushin ta da duk dangin Usman da suke murnar an mata kishiya, a hankali tace "Bilal."


Juyowa ya yi ya dawo ya tsaya, hannun shi ta kama tace "Ka had'a kayan ka zan kira tonton Naseer ya zo yanzu ya d'auke ka, hakan ya yi?"


Ba tare da sakin fuska ba ya d'aga kai alamar eh, fita ya yi Nura na tsaye yace "To ya? Za mu wuce ne?"


Kamar zai fashe da kuka yace "Mummy ta hana."


Ji ya yi kafin yace "Shikenan kar ka damu, ai gobe juma'a, watak'ila ku tafi gidan tare da Abban ka."


Shiru bai ce komai ba har ya fita daga gidan ba tare da ma ya shiga wajen Haseenah ba, ta na kiran Naseer kam dama bai shiga gida ba, dan haka ya taho d'aukar shi, sai dai lokacin Usman ya shigo gidan, sun gaisa kamar yanda su ka saba tare da wasa da dariya, amma har Khadija ta had'awa Bilal kayan shi su ka tafi babu fara'a a tare da ita bare ta yi magana, a tak'aice dai haka duka gidan su ka gudanar da daren su babu armashi a ciki, dan Usman ya nunawa Haseenah kuskuren ta ma ko abincin ta bai ci ba, haka ma a d'aki da suka kwanta juya mata baya ya yi, dan in har za ta iya cin zarafin d'an shi har haka to fa akwai yiwuwar ya nuna mata ba'a mi shi wasa da gudan jini.


Washe gari da safe ma haka abin ya ke, kasancewar Khadija ta san a wannan lokacin ya na d'akin shi ya na karatu ya sa ta shiga har can ta gaishe shi, bai wani yi karin kummalo ba ya yi shirin masallaci, *11:00* cif ya fita ya bar gidan zuwa masallaci kamar yanda ya saba, bai dawo cin abinci da rana ba sai aikowa da ya yi aka d'aukar ma sa, da yamma kuma ya kira Khadija yace su shirya dukan su za su je su yi barka gidan Issoufou, tunda magriba Khadija ta gama shirin ta tana jiran shi, Haseenah ma ba ta b'ata lokaci ba wajen shirin duk da fitar ta ta farko kenan, watak'ila ta na zumud'i ne saboda yace zai aje ta har gidan su ma su gaisa da mutane, ana idar da sallah isha'i ya shigo gidan, shi ma sai da ya sake shiri kafin su ka fita gaba d'aya, Haseenah ce baya tare da kwanukan abincin da zata kai gidan su.


Babu mai magana a motar dan kowa da abin da ke ran shi, sai Khadija da ke latsa wayar ta hankali kwance, gidan su Haseenah su ka fara tsayawa dan ya fi kusa da gidan Issoufou, Usman da Haseenah ne su ka fita, amma ganin Khadija ba ta da niyyar fitowa ya sa ya kalle ta yace "Uwar gida sarautar ta motsa ne? Ko sai na fito da ke?"


Ko kallon shi ba ta yi ba tace "Ku shiga kawai zan jira ku."


Wani murmushi ya yi yace "Ke ma kinsan ba zan lamunci haka ba ai, fito mu wuce dallah."


Cike da damuwa tace "Ba na cikin yanayin dad'i, ba na so kowa ya fahimci hakan har a dasa min hak'ora, dan ina fitowa za ace ba na da mutumci na fiya kishi da yawa."


Bud'e murfin motar ya yi ya kamo hannun ta ta fito, bai saki hannun ta ba har sai da su ka shiga cikin gidan, sakin ta ya yi ya saci kallon ta yace "In dai ina da mahimmanci a wajen ki, to ki kankaro min mutunci na a gurin mutanen nan, kar ki bari laifin 'yar su ya shafe su."


Kallon shi ta yi da farko turo baki ta yi, amma da ya marairaice sai ta saki fuskar ta na murmushi, Haseenah da tuni ta shiga gidan su ba ta ma san tsiyar da ke faruwa ba, sallamar su ce ta sa ta mik'e ta d'auko mu su kujeru su ka zauna, mahaifin ta na daga gefe zaune akan kujera, sai mahaifiyar ta na cikin sange zaune akan katifa da alama sunyi shirin bacci kenan, sosai su ka gaisa cike da mutunci da girmamawa, jim kad'an su ka mik'e Khadija na fad'in "Mama mu za mu wuce, saida safen ku."


"To Allah ya bamu alkairi, Allah fisheku dare." Cewar maman.


Da "Ameen." Su ka amsa, Haseenah kamar kar ta tafi take ji haka dai ta taso su ka fito, su na d'aukar hanya Usman ya kalli Haseenah ta madubi yace "Ke Hajia haka ake harkar duniya, daga kawo ki ku gaisa sai ki yi ta wani mak'alewa ba kya so ki tafi."


Cikin turo baki tace "Ni wallahi da ka bar ni na kwana anan ma da zanji dad'i, gidan mu ne fa."


"Wai ki na nufin har kinyi kewar gidan da har ki ke so a bar ki ki kwana anan?"


"Sosai ma, ai tun ranar da aka kaini gidan ka na fara kewar gidan mu."


Kallon Khadija ya yi yace "Hajia ki na jin ta fa, yanzu ke dan Allah za ki yarda ace ki je gidan ku ki kwana?"


Fuska ba annuri tace "Saboda ni banyi shak'uwar da zan iya kewar 'yan uwa na ba kenan? Ai ko yanzu ka ce tafi to sai dai ka aje ni na d'auki adaidaita, dan gani zanyi kamar motar nan ba ta gudu sosai."


Maida hankalin shi ya yi kan tuk'i yace "Kenan idan na fahimce ku duk cikin lamarin ni ne bare, kun nuna min har yanzu ba ku d'auka ta kamar yanda na ke d'aukar ku, kun nuna min har yanau babu wacce ta ke jin za ta iya k'arar da rayuwar ta a tare da ni."


Wata shegiyar harara Khadija ta masa tace "To me za mu zauna mu yi da tsoho, ka na so ne mu kai lokacin da za mu fara goge ma ka majina a hanci."


Hannu ya kai ya damk'o wuyan ta ya na dariya ya na fad'in "Ni ne ma tsohon? Yanzu ke mijin na ki ne tsoho? Lallai ma yarinyar."


Gwalo ta mi shi ta na fad'in "Gashi kai ma ka fad'a da bakin ka, har yanzu ni yarinya ce, tunda sai nan shekara biyu zan cika *talatin da biyar*."


Juyowa ya yi ya kalli Haseenah yace "Ke kin yarda mijin ki tsoho ne?"


Haseenah da haushi ya fara kashe ta ne tace " A zahiri wanda bai san ka ba zai iya kiran ka da tsoho, amma ni a wuri na ba tsoho bane, dan ni nasan k'arkon miji na."


Dariya Usman ya yi ya juyo ya bata hannu alamar su bige ✋ tare da fad'in "Ban biyar amarya ta." Bashi ta yi su ka bige su na dariya.


Kallon Khadija ya yi yace "Sai yanzu ai na fahimta, ashe ke ce ki ka tsufa ba ni ba."


Dariya ita ma ta yi tace "Amarya kam dole ta fad'i haka, amma da tasan waye kai lokacin da ka ke ji da k'uruciya, to fa da za ta gasgatani d'ari bisa d'ari, amma da ya ke zuwan shekaranjiya ce ita ba za ta gane komai ba, ko ba haka ba?"


Ta fad'a ta na kashe masa ido d'aya, turo baki ya yi gaba yace "Za ki yi magana ne idan ki ka shigo hannu na."


Bushewa ta yi da dariya tace "Yanzun haka ina matakin shekarun cikakkiyar mace ne da ke jin jini a jika, dan haka ba za ka tab'a tsorata ni ba malam Manu."


Wani mayan kallo ya mata ya na d'an cije labb'an shi na k'asa, sake tsinkewa ta yi da dariya har da kai mi shi duka a hannu ta na kwantar da kan ta a kafad'ar shi ta na fad'in "Ka tuna? Ka tuna wannan ranar da ka fad'a min haka? To nima na rama, yanzu ina kan shekaru na ne, dan ni yanzu ma ji na ke kamar yanzu ne na balaga, dan haka ka zama tsoho a wuri na."


Shi ma dariyar ya ke sosai yace "A ranar kam sai da na k'ara gyara tsayuwa ta sannan na ce mi ki, yanzu fa sai kinyi hak'uri da ni, dan ina ganiyar shekara talatin da biyar ne, shekarun hura wutar..."


Da sauri ta rufe ma sa baki su na ci gaba da dariya, d'an k'aramin tsaki Haseenah taja da ya sa su ka kalle ta, saita nutsuwar su su ka yi Khadija tace "Yi hak'uri amarya."


Take ta kalli Usman ta saisaita murya tace "Abban Bilal, munga shekaran jiya tare da kai, haka ma munga jiya da yau, insha Allahu da izinin ubangiji za mu ga gobe."


Wani fari ya mata da ido alamar wai ta sumbace shi, ita ma mayar masa ta yi da idon alamar a'a, Haseenah da abin duniya ya isheta ne tace "Wai har yanzu ba'a kawo gidan ba ne?"


Babu wanda ya kalle ta sai Usman da yace "Halan bacci ki ke ji?"


Banza ta yi da shi daga haka har su ka isa gidan, nan ma da suka shiga wata sabuwar hira aka dasa Khadija da Usman da Issoufou da mai jego kasancewar babu kowa a gidan sai yaran su da kula mai tayata kwana, da ganin yanda suke hira kasan akwai shak'uwa da fahimtar juna da kuma mutunta juna, saida dare ya yi su ka taso su ka dawo gida, kowa d'akin shi ya nufa ya yi shirin kwanciya, sai da Usman ya zo ya wa Khadija saida safe kafin ya koma, duk da Haseenah ba ta bashi hak'uri ba akan abin da ya faru, amma da ya neme ta sai ya sa ta sake jin girman kai, hakan ya nuna mata ko ka wa namiji laifi ran shi ya b'ace dole shi zai neme ka ko dan biyan buk'atar shi, da haka gari ya waye. 



*Yau kuma da wacce aka wayi gari? Sai kun biyo ni.*

02/02/2020 à 20:58 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```


*Godiya masoya, 😂na yi dariya sosai ganin comment d'in ku rututu, Haseenah no fan's.*😂


💕 _A sannu a hankali sai cinye shekaru na na ke tamkar yanda nake cinye abinci na, damuwa ko tunanin hakan ba shine mafita ba, domin kuwa babu abin da zai dakatar da ita idan har ta zo, fata na bai wuce na gama da duniyar nan lafiya ba, sannan na rabu da iyaye na lafiya da 'yan uwa da masoya, ba na buk'atar tsawon shekaru, na fi buk'atar k'arancin su in dai masu albarka ne da anfani, *ina taya kai na bak'in ciki*, domin ba na ce farin ciki ba, domin har yanzu banyi wani tanadi dan ranar gobe ba, amma abun mamaki dayawa su na murna ne har da shagali saboda sun k'ara shekara, basa la'akari da shekarun su ne suke tafiya basu ankara, sai sun wayi gari sun jisu cikin k'abari, Allah ka bamu shekaru ma su albarka._💞



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *18*



Ya shirya zai fita ya shigo wajen Khadija ya same ta zaune a falo sai Uwani da ke aiki, bayan sun gaisa ne tace "Babban mutum ina neman izinin ka zanje wajen kitso da lalle?"


Murmushi ya mata yace "Ko ban tambaya ba nasan za ki fara shirya min kan ki ne, dan haka kin samu izini na, sannan..." Ya fad'a ya na saka hannu aljihu ya ciro kud'i, mik'a mata ya yi yace "Ga wannan ko, sai a k'ara ayi kwalliya da kyau."


Sunkuyar da kai ta yi ta rufe ido da hannayen ta, sunkuyowa ya yi ya lek'a fuskar ta yace "Iyeee! Kunya ce wannan? Kin tuna amarcin kenan? To shikenan bara ki gani."


Tsakiyar maman ta ya tusa mata kud'in tare da sumbatar goshin ta yace "Ni na tafi sai na dawo."


Sai da ya ksa kaiwa ga k'ofar fita ta d'ago tace "A dawo lafiya, godiyar kuma na mik'o ta zuwa wani lokacin." Yanda ta k'arashe maganar da fari ya sa ya saki murmushi yace "Ina jira, dan nasan abun zai k'ayatar tunda ke ce za ki yi shi."


Ya na fita ta tashi ta k'arasa shirin ta, tare da Uwani su ka tafi a motar ta gidan kitso da lalle da ma sauran gyaran jiki, kasancewar babu mutane a wurin ya sa aka fara mata abin da ya kai ta, sun jima sosai a wajen, dan sai kusan k'arfe biyar na yamma su ka koma gida ita da Uwani, tun a hanya ta tsaya ta siye salade dan ta ci, su na zuwa gida Uwani ta shiga gyaren shi ita kuma ta shiga wanka, ko da ta gama shiri Uwani har ta fara yankawa, zaune ta yi su na hira su na aiki har magriba, kuma har lokacin ba ta ga Haseenah sai motsin ta da su ke ji a madafa, a haka duka suka gama aiyukan gaban su suka koma d'aki. 


Tunda wuri ta yi shirin baccin ta yau saboda ta huta dan gobe ita ce da aiki, doguwar rigar bacci ce a jikin ta da ta sauka har k'asa haka ma hannayen rigar, sanin Usman zai shigo ya sa ta k'i saka komai daga cikin rigar, ma'ana dai babu komai daga ciki bayan rigar, ai kam ta na jin motsin shi ta yi sauri ta mik'e ta fara kai da kawon iska, ya na bud'a k'ofar da sallama a bakin shi, da sauri ya d'ora da "Wai wai wai, kar dai na shigo lokacin da bai dace ba?"


Juyowa ta yi da murmushi tace "Wane lokaci ne bai dace Abban Bilal ya ga Umman Bilal ba?"


Takowa ya yi zuwa gaban ta ya na kallon ta yace "Ba na tunanin akwai lokacin gaskiya."


"Kuma ka fad'a?" Ta fad'a da kafe shi da ido.


Hannu ya kai zai kamo ta ta janye ta zauna kan gado ta na fad'in "Dama ina son magana da kai."


Zaunawa ya yi ya na fad'in "Uhum, akan me?"


Satar kallon shi ta yi tace "Akan maganar kwana ne dama."


Da sauri ya kalle ta yace "Me ya faru da kwanan ki? Ina ce gobe ne ko?"


Ajiyar zuciya ta sauke tace " Eh gobe ne, amma kuma da matsala."


Gyara zama ya yi ya na kallon ta yace "Matsalar me? Ki yi magana mana dan kinsa hankali na ya fara tashi."


Mik'ewa ta yi tsaye kamar marar gaskiya ta na kallon shi ta na wasa da yatsunta tace "Eh to, gaskiya dai ba na sallah, shi ya sa na barwa amarya kwanan na wa."


"Me?" Ya fad'a ya na tashi tsaye, janyo ta ya yi jikin shi yace "In dai ba b'ata na yi ba ai tunani na lokacin zuwan bak'on ki baiyi ba, me zai sa ya canza lokacin zuwa yanzun? Saboda ya san ina buk'atar ki ne a kusa da ni kome? Ko shi ma haushi na ya ke ji ya na taya ki kishi ne?"


Da sauri ta janye daga jikin shi ta yi baya ta na fad'in "A'a ba ko d'aya, gaskiya na ke fad'a ma ka fa, ka yarda mana."


Had'e fuska ya yi yace "Naga tafin hannun ki."


Da sauri ta mayar da hannayen baya tace "Um um."


Murmushi ya yi yace "Wata kala ce kawai ki ke so ki min kuma na gano ki, dan haka ki ci gaba da min shirye shirye kawai."


Juyawa ta yi ta nufi ban d'aki ta na fad'in "Ni fai na fad'a ma ka na barwa amarya kai, dan yanzu har na saba da bacci ni kad'ai."


Har da gudu ya had'a wajen janyo ta jikin shi ya na shafa ta ya na fad'in "Kenan ba ki yi kewata ba ko kad'an?"


Cikin narkakkun idon ta ta kalle shi ta gilashi tace "Idan ma na yi ko banyi ba, idan ka shigo hannu na za sani."


A hankali ya matso kan shi ya na son had'e bakin su da sauri ta fizge daga gare shi, juyawa ta yi ta nufi ban d'aki ta na juya mazaunai da gayya, lumshe ido ya yi ya d'an cije lab'en k'asa ya bita da kallo, ta na shigewa ya matsa bakin k'ofar yace "Ni zan wuce sai da safe, ki kula min da kan ki dan Allah."


Shiru ta yi har ya fice daga d'akin, ta na jin ya fita ta fito dan dama ba komai ta ke yi ba, kashe wuta ta yi ta zauna bakin gadon ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin ta cire gilashin ta ta kwanta abin ta.



**************


Bilal na zaune tare da duka iyayen shi yan uwan mahaifiyar shi da kuma kakar shi, dan har yanzu ba su daina had'uwa a falon mahaifiyar su ba suna hira, hira ce ta yi hira har ta sa Bilal fad'a mu su fad'an da mahaifiyar shi ta yi da kuma auntyn shi, rashin jin dad'in abun ya sa Naseer cewa "Ni wallahi dama nasan sai anyi haka, dan tun ranar da suka samu sab'anin nan nasan yarinyar nan ba ta da kunya, in ba rainin hankali ba taya za ki bud'e baki ki ce wai ina anfanin yaro a cikin gidan uban sa? Wallahi ta yi wasa ni sai na ci uban wanda ya d'aure mata gindi ma."


Mama ce ta katse shi da cewa "Kamar ya ka ci uban ta? Matar mutane za ka daka har gidan ta? To ba na son sake ji daga yau, ku na so ace ku na taya 'yer uwar ku kishi ne?"


Naseer d'in ne dai ya d'ora da "Hajia ba ki san me ta ke mata bane, ranar fa har kuka ta saka ta da hawaye, ce mata ta yi wai makauniya, ki ji fa Hajia, ni tunda na ke ban tab'a jin wanda ya kira ta da makauniya ba."


Ashir ne yace "Makauniya fa? Khadijar ce makauniya?"


"Wallahi haka ta fad'a mata shegiyar figaggiya."


Habeeb da Bilal ke kwance kan k'afafun shi ne yace "Wallahi ni tun ran kan amarya da na ga idon yarinyar nan a tsaye da kuma k'awayen ta masu ido tsakar ka nasan dama za ayi haka, amma dai ta kiyaye b'atawa auta rai, dan ba lallai mu d'auka ba."


Bashi ne ya karb'e da "Ba maganar ba lallai bane, magana ce ta ba zamu d'auka ba ko kad'an, wallahi ba za ta shiga gidan ta ba kuma ta nemi ta raina ta, dan haka dole Usman ya sake zagewa wajen tsayawa akan gidan shi, in ba haka ba kuma to zamu ziga ta ta dinga jibgar ta mu kuma a shirye mu ke da mu tsaya mata a kowace kotun duniya."


Tsaki Mama ta yi ta mik'e ta nufi d'akin ta ta na fad'in "Saida safen ku, tunda naga dukan ku babu mai hankalin da zaiyi magana ta hankali har kai da ke babba a ciki."


Nan ta bar su suka ci gaba da tattaunawa akan al'amarin gidan da kuma 'yer uwar su, bacci Bilal ya yi Habeeb ya kwantar da shi kafin suma su ka nufi wajen na su matan tare da tattara k'ananan yaran su da su ke tare da su anan.



*****************



Washe gari ma Haseenah ce ta shirya abin karin kummalo, Usman da kan shi ya zo ya kira ta dan su ci tare amma tace wallahi ba za ta je ba, tunda dai har ta nuna abata kwanaki ita ma ta ci amarcin ta to ta bata, su biyu kad'ai su ka karya haka da rana ma da ta gama girkin aikowa ya yi aka d'aukar ma sa, tun k'arfe uku na rana Khadija ta shiga madafa ita da Uwani da wasu matasan 'yan mata biyu yaran mak'wabtan su, hakan ya sa gidan ya kaure kamar su na aikin wata hidima, kowa da abin da ya ke yi, Haseenah na iya hangen su ta k'ofa sai tsaki take da hararn su, cikin hukuncin ubangiji sai gashi zuwa k'arfe shida sun kammala komai sun gyara wurin kamar ba su yi aiki ba, a falon shi ma gyara su ka shiga yi in da Khadija ta sa suka gyara zaman komai da ke d'akin zuwa wata kusurwar ta daban, amma uwar d'akin shi da kan ta ta shiga ta yi gyaran, koda aka fara kiran sallah tuni har sun kammala musamman da ya zama akwai masu kamawa, ko da su ka yi sallah duka yaran abinci ta zuba mu su suka ci su ka k'oshi, sannan ta had'a su da kyautar turare wai su shafa tunda yan mata ne, har Uwani ma ba ta bari ba sai da ta mata, haka yaran su ka tafi bayan ta had'a su da jikka jikka, hakan ya sa duk abin da suke in dai ta tura a kira su to ko ba su yi niyyar tahowa ba iyayen za su ce su zo, saboda irin alherin da ta ke mu su, su na tafiya ta shiga uwar d'akin ta ita ma ta d'auko wasu robobi da blanda (blander) ta zauna gaban frigo (fridge).


_Kankana ta d'auko wacce ta gyara ta da kyau ta zuba a blandar ta markad'a, wata k'aramar rariya ta sa ta taceta tare da rage wata a cikin wani kofi sannan ta d'auki dabinon da ta jik'a shi da ruwan rake tare da kanunfari ta zuba, shi ma markad'awa ta yi sannan ta tace shi cikin ruwan kankanar, madara peak ta d'auka ta juye a cikin had'in sannan ta d'auki gwangwanin maltina ta juye a ciki shi ma, ta na gama had'awa ta d'auki zuma cokali d'aya ta zuba a ciki, cikin frigon ta aje robar dan ya yi sanyi kafin ta shirya._


_Wani babban kofi ta d'auka ta d'auko ayaba manya guda biyu ta fereta ta yanka a cikin kofin k'anana k'anana, saida ta gama sannan ta zuba madara peak a ciki, kafin ta d'auko wata roba mai d'auke da garin aya ta zuba a ciki cokali uku, sannan ta d'auki wata robar ta bud'e ta zuba garin dabino shi ma cokali uku, juyawa ta yi sosai ya had'e jikin shi sannan ta d'auki kofin ta kafa kai ta shanye, wannan kankanar da ta rage a kofi ta d'auka ta zuba zuma a ciki tare dafasa k'wai d'aya ta kad'a shi sosai sannan ta shanye._


Tashi ta yi ta d'auki komai ta mayar a wajen shi sannan ta dawo gaban fridge d'in ta bud'a, wani kofi ta d'auka wanda dama kullum ya na ciki da karanfani a ciki, ruwan ta shanye wanda su ka jik'a sosai da kanunfari sannan ta rufe ta shiga wanka, da k'yar ta samu ta tsarkake gaban ta saboda ruwan da su ke fitowa, ta na gamawa ta d'auro akwala, ko da ta fito sallah ta fara kabbarawa har ta ida kafin ta zauna gaban madubi, ta jima ta na shafawa ta na gogewa, kwalliya dai ba wata abu ba kam ta yi ta sosai, ta na kammalawa ta mik'e tsaye ta bud'a wata drower ta d'auko wani turare da ba kullum take aiki da shi ba sai Usman ya na gari, a cibiyar ta ta fara fesawa kafin ta fesa a mara, sai bayan kunnuwan ta da wuya da kuma tsakiyar nonuwan ta, haka ma hammata sannan ta fesa a hannu ta shafa a mazaunai, rufewa ta yi ta aje kafin ta d'auko kaya ta saka, wata arniyar doguwar rigar shadda ce ta saka kai kace d'aurin auren shugaban k'asar  garin su ne za ta je, wasu masifaffun takalma ta d'auka masu shegen tsini ta saka sannan ta d'auko kallabin kayan wanda dama ta sa aka d'aura mata shi musamman dan wannan ranar, wani siririn gilashi fari k'al ta sanya ta kalli kanta a madubi, murmushi ta sakarwa kan ta kafin ta dawo ta d'auki had'in ta da ta aje dan ya yi rab'a, kafa kai ta yi bata kuma aje ba sai da ta shanye duka sannan, komawa ta yi gaban madubi ta d'auki turaren ta na yau da kullum da har ya zama jikin ta, feshe kayan ta yi da shi sosai take ta sake d'aukar wani halataccen k'amshi mai kashe jiki, cikin takon isa da k'asaita ta fito daga falon, ta na shirin yin zaune a kujera ta ji mai gadi na wangale k'ofa, murmushi ta yi ta aje wayar ta ta juya ta fita, tsinin takalmanta ya sa dole take tafiyar a hankali mai d'aukar hankali, Usman da ya bud'e k'ofa zai fito ya hangota kasa fita ya yi, zuro k'afa ya yi ya na k'are mata kallo har ta tsaya gaban shi, kallon da ya ke mata ne ya tabbatar mata da wani abu ya ke rayawa a ran shi, saida ta sake narkar da ido tace "Wannan kallon fa?"


Ba tare da ya daina mata wannan kallon ba ya sauke ajiyar zuciya, ganin baice komai ba ya sa ta kamo hannun shi har ya fito ta rufe motar ta kalle shi tace "Sannu da zuwa my *Exelency*."


Murmushi kawai ya yi baice komai ba, matsowa ta yi daf da shi ta shafa fuskar shi tace "Da alama my *world* duk ka wahalar min da kan ka, yanzu muje ciki na baka agajin gaggawa."


Hannun shi ta ja su ka yi ciki shi dai kamar sakarai, sai a uwar d'akin shi suka yada zango, kayan ta fara cire mi shi ta na fad'in "My *sweet angel* ya kasa min magana saboda ya na kallo na kamar wata bak'uwa a gare shi yau, amma ba komai girmanka ne ai."


Za ta sunkuya dan cire mi shi wando ya rik'o ta, wani irin kallo ya watso mata yace "Gaba d'aya na rasa kuzari na, ban san me zan fad'a ba."


Ita mayar masa da kallon ta yi tace "Kar ka damu, zan dawo ma ka da wutar ka." Ta k'arashe da kanne ma sa ido d'aya da d'ata bakin ta har ya yi k'ara, janshi ta yi zuwa ban d'aki har ya shiga ciki, ruwa ta sakar ma sa kafin ta shafa k'irjin shi tace " *My Mine* kasan me zai faru? Yanzu ka fara wankan ina zuwa yanzun nan."


Ba ta jira me zai ce ba ta fice daga d'akin gaba d'aya, kai tsaye madafa ta nufa ta samu ruwan zafi ta saka na'ana'a a ciki tare da cinta d'anya da ganyen lipton, suna dahuwa ta tace a kofi mai kyau sannan ta zuba zuma cokali biyu, ta juyo za ta fita kenan Haseenah ta shigo ciki, kallon kallo su ka yi in da Haseenah ke mamakin irin arniyar kwalliyar da Khadija ta yi kamar za ta biki, ita kuma ta na mamakin abin da ya shigo da ita madafar yanzu, har za ta fita sai kuma ta tsaya tace "Wani abu ki ke buk'ata ne?"


Cike da gatsali tace "Eh, na zo na dafa indomie ne."


Cike da rashin nuna damuwa Khadija tace "Ayya! Ki bari ya fito daga wanka mana sai mu ci abinci, ai yanzu ya shigo bai jima ba."


"A'a nagode." Ta fad'a kai tsaye ta k'arasa shiga madafar, tab'e baki ta yi ta fita ta bar ta, ta na zuwa ta samu ya na ciki bai fito ba, cire takalmin ta yi da d'aurin d'an kwalin ta ta shiga ciki, ba tare da sanin ta shigo ba ta karb'i sabulun hannun shi ta fara goga mi shi a baya, juyowa ya yi ya na ganin ta ya fizgo ta ta fad'a jikin shi, dariya ta yi ta rufe ido saboda ruwan da suka zuba jikin ta, had'e ta ya yi sosai da jikin shi ya cire gilashin ta ya aje gefe, haka ma doguwar rigar cire ta ya yi ya jefar, a tak'aice dai tare su ka yi wankan su ka fito, da gaggawa ta d'auki kofin shayin da ta had'o mi shi ta ba shi ya shanye, cikin sauri su ka shirya su ka fito, ita tebur ta nufa shi kuma ya wuce d'akin Haseenah dan ya kira ta, ya na zuwa ya same ta ta kasa cin indomien da ta dafa saboda rashin dad'i, nan ya lallab'o ta suka fito falon a tare, cike da mamaki ta k'araso ta zauna ta na kallon Khadija ta gefen ido saboda ganin ta canza kayan jikin ta babu kwalliya a fuskar ta, a ran ta kam cewa ta yi "Hum! A nunawa shege shegentaka, wato ki nuna min wani abu ya faru har kinyi wanka, to mu zuba zuwa ni da ke."


Baki Haseenah ta saki ganin abinci har kala kusan hud'u saboda kawai aci yanzu, tunda su ka fara ci take kallon Usman yanda a ke cin abincin, kenan ita ce ya raina ko? Ta tambayi kan ta, Khadija kam daga k'asa take wasa da k'afafun ta ta na shafar Usman da su har su ka kammala, saida ya ma Haseenah saida safe kafin ya dawo d'akin shi, a lokacin Khadija na d'akin ta ta na kama ruwa da ruwan kanunfarin da ta tafasa, saida ta k'ara shfa turare ta yi sassauk'an kwalliya ta saka rigar bacci, doguwar abaya ta d'ora sama sannan ta nufi d'akin. 


Kwance ya ke akan gado babu riga a jikin shi ya rufe ido kamar mai bacci, har ta shigo ta rufe k'ofar ta kashe hasken d'akin ta maye gurbin shi da siririn haske bai bud'a ido ba, cire rigar ta yi ta baccin ta bayyana, kallon shi ta yi har yanzu ido rufe tace " *Mon ange*, ka bud'e idon ka mana."


Bud'ewa ya yi tare da sakin murmushi, ganin yar rigar dake jikin ta ya sa shi waro ido yace "Wayyo Allah, zo Khadija, zo gare ni dan Allah."


Cikin salo da k'warewa ta haura kan gadon ta fad'a jikin shi, rumgume shi ta yi amma saiya k'ara matse ta sosai yace "Ki rik'e ni sosai Khadija."


*To kowa dai ya san me zai faru, dan haka babu kyau shiga rayuwar ma'aurata.*


Haseenah da kishi ya hanata bacci ta kasa samun sukuni, gagara bacci ta yi in da shed'an ke zugata ya na hura mata wutar k'iyayya, a k'arshe ji tayi kawai bara ta lek'a ta ji me ke faru a d'akin, cikin sand'a ta fito ta tsaya k'ofar d'akin ta na saurare, sambatu da surutan da take ji ne su ka sake d'ugunzuma mata tunani, irin yanda taji muryar Usman ya tabbatar mata da kuka ya ke tsabar dad'in abin da ya ke ji, musamman da ya ke fad'in kar ta kashe shi ta yi hak'uri ya bata komai da ya mallaka, ba ta yi bacci ba a daren ko kad'an in da masoyan kam suka kwana k'wak'ume da juna cikin farin ciki, tabbas Usman ya sake yarda aure kawai muk'addari ne daga Allah, amma ba dan haka ba babu abin da zai sa shi k'ara aure ya na da kamar Khadija, da haka asuba ta yi su ka tashi sallah.



              *A gurguje*



Haka rayuwar gidan Usman ke tafiya da dad'i wasu lokutan kuma sai a sannu, sai dai yanzu Haseenah ta d'an shiga taitayin ta ba ta cika shiga harkar Khadija ba bare har ta fad'a mata magana, Khadija kuma dama rayuwar ta take yi babu ruwanta da ita, Bilal ma na wajen kakanin shi hankali kwance ya na zuwa islamiyyar shi, ranar talata da yamma Khadija ta saki aiki Haseenah ta kama, sosai Usman ya yarda Khadija ita ce ta san shi farin sani, bayan kwana biyu ita ma ta saki aiki a ranar alhamis ta saki aiki Khadija ta kama, a ranar kuma ta kama ranar sunan matar Issoufou, tunda rana Usman yace su tafi tare tunda Khadija na da mota, sannan ta san gidan sab'anin Haseenah da zuwan ta d'aya kuma cikin dare.


Tun Khadija na jiran ta kammala aiki su tafi dan ta samu ita ma ta dawo ta kama na ta aikin har ta gaji da jira, ganin ba kowa a gidan da zata aika ya sa ta sallama da kan ta har falon ta, Haseenah da ke uwar d'aka kwance ta amsa sallamar tare da fitowa, ta na ganin Khadija ta ja birki k'ofar d'akin ta na k'are mata kallo, da mamaki Khadija ta kalle ta ganin ko wanka ma ba ta yi ba, cikin dakiya tace "Wai Haseenah ba ki shirya bane?"


A kasalance ta amsa da "Ban shirya ba."


Jin ba ta sake cewa komai ba ya sa tace "To dan Allah ki gaggauta ki shirya mu wuce, wallahi ba dan ke ba ma ni ban tab'a kai wannan lokacin ba ban fita ba, musamman da nasan zanyi aiki."


"To." Haseenah ta fad'a ta juya kawai ta koma ciki, Khadija na ganin haka ta fito ta na mita, a k'alla ta sake b'ata minti talatin ba Haseenah ba labarin ta, ran ta ne ya kai matuk'a wajen b'aci kawai ta d'auki jakar ta ta fita, Haseenah na jin fitar Khadija ta fito ta rufe d'aki dan dama ta shirya tunda ta mata magana, kawai ba ta yi ra'ayin fitowa da wuri bane, har farfajiyar gidan ta fito ta samu mai gadi tace "Wai har ta tafi ne?"


Cikin girmamawa yace "Yanzun nan kam ta fita, dan ga motar can ko titi ba ta hau ba."


Wayar ta ta ciro cikin jaka ta dannawa Usman kira, ya na d'auka ta fad'a mi shi ya zo ya d'auke ta Khadija ta tafiyar ta, da mamaki yace "Wai dama har yanzu ba ki fita daga gidan ba?"


Cikin turo baki tace "Na shirya fa na ke ta jira aunty Khadija ta min magana, tunda ai ba zuwa zanyi ba na tisa ta a gaba har sai ta gama shirin ta, ina falo kawai sai fitar ta na ji."


Ba dan ya yarda da abin da ta fad'a ba yace ta jira shi ya zo ya d'auke ta, dan in dai Khadija za ta fita to bata kaiwa warhaka bata fita ba saboda taje ta dawo da wuri ta kama aikin gaban ta, hanya ya d'auko dan ya zo ya d'aukar ta ya kira Khadija a waya, bayan ta d'auka ne yace "K'anwar ki ta kira ni tace wai kin tafi kin barta, shine na ce ya akayi haka ta faru?"


Khadija da ke tuk'i ne tace "Ba ta fad'a ma ka na kai mak'ura bane wajen jiran ta? Ko kuma kawai ta fad'a ma ka abin da ta ga dama ne?"


Murmushi ya yi daga in da ya ke yace "Ran gimbiya ya huce, kawai dai ina tambaya ne."


Cike da rashin kulawa tace "Ka ga ina tuk'i fa, sai munyi magana."


Kasje wayar ta yi ta ci gaba da abin da take, shima kuma d'auko Haseenah ya yi sai dai bai fad'a mata yanda su ka yi da Khadija ba har suka isa ya sauke ta, da d'ar-d'ar ta shiga gidan bikin ta na sallama wata bayan wata, cikin sa'a ta hango su Hassana da Husseina da duk sauran yan uwan tare da Hajia sarakuwar su zaune, da azama ta isa can ta zauna su ka gaisa, Rabi'a ce ta fara tambayar ta da "...



*Ku yi hak'uri masoya abisa jinkiri na, hakan na faruwa ne sakamakon al'amura da su ke sha min kai na.*👏

04/02/2020 à 21:00 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

(GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA INSHA ALLAH)🤜🤛



*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*



*INA JIGA JIGAN MASOYAN 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S WAD'ANDA BASU DA TAMKA A WAJENMU????? DUK WANDA YAKE TARE DAMU A CIKIN GROUPS D'INMU TO MUN TABBATAR K'AUNARMU CE TASA KUKA KASANCE TARE DAMU, MUNA YABAWA KUMA HAR ABADA BAMU DA KAMARKU WALLAHI,👍 DUK DA HAKA DAI GA LOKACI YAZO, KUMA DAMA TA SAMU NA TABBATAR MANA DA KUMA NUNA MANA HAK'IK'ANIN K'AUNAR DA KUKE MANA,👇*



Kunsan cewa k'ungiyarmu *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* suna cikin gagarumin gasa na samun award Wanda *women24 TV WhatsApp group* suka shirya kuma zasu gudanar?


A wannan gasar ne za'a samu k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan fans da Kuma bin k'a'idar rubutu


Dan ki samu damar zabar k'ungiyarmu *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S ASSOCIATION* zaki iya tuntub'ar wannan lambar 09030159301 Dan su saki a *WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP* anan ne za'ayi zab'en k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan masoya


*Women24 Tv*

Ba zabe kad'ai zakiyi ba


Zaki k'aru da abubuwa da yawa kamar haka


*Yanda ake girke girke*

*yanda zaki gyara jikinki*

*yanda zakiyi makeup*

*yanda zaki daura Dan kwali*


Kuma suna shirye shiryen nan na *arewa24 tv* kamar su


*TARKON KAUNA*

*DADIN KOWA*

*KWANA CHASA'IN*

*JAMAI RAJA*

*SAPNE SUHANE*

*GIDAN BADAMASI*

*RUDIN ZUCIYA*

*BAGHYA LAKSHMI*

*AKUSHI DA RUFI*

*AUDIO NOVEL*

*HAUSA NOVELS*


Kada ki manta da ranar zabe inkin shiga group d'in ki zaba *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* tanan ne zaki iya nuna mana irin sonda kuke ma k'ungiyarmu da littattafammu


Allah yabar zumunci🤝😍🥰💋



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *19*




"Haseenah ke kad'ai ki ka taho ne?"


Da kunya ta kalle ta tace "A'a, shi ya kawo ni ai, da tare da aunty Khadija zamu taho, to kuma bansan tafiyar ta ba."


Ai kuwa abin da ta fad'a ya samu shiga sosai, hakan ya sa Hassana cewa "Amma yasan za ku taho tare?"


"Eh ya sani, shi yace ma mu taho tare tunda safe."


Rabi'a ce tace "Amma kuma dan rashin mutumci shine ta taho ta baro ki? Lallai ma matar nan, kullum iskancin ta k'aruwa ya ke."


Husseina ce tace "To ba ita ke da mota ba, kinga kuwa dole ta yi yanda ta so."


"Hum." Cewar Hassana, cike da wauta Aziza tace "Wallahi kema kar ki yarda ya siya mi ki ko moto ne, dan ba za ki zauna ta na mulkar ki ba."


Hajia ce ta kalli Haseenah tace "Ki shiga wajen mai jegon mana ku gaisa."


"To Mama." Ta fad'a ta na mik'ewa, cike da dattako Hajia ta sake cewa "In ce dai ya baki abin da za ki kaiwa mai jegon?"


'Yar dariya ta yi tace "Eh Mama, tunda safe ma ba bamu dukan mu."


Hajia na ganin wucewar ta ta kalle su dukan su tace "Yanzu mi ye anfanin haka? Wannan yarinyar yaushe ta shigo cikin ahalin ku da har ku ka yarda da ita haka? Mi ye Khadija ba ta mu ku ba a rayuwa da har ku ka butulce ma ta haka? Dukan ku fa mata ne, kuma Rabi'a ce kad'ai ba ta da abokiyar zama a ciki, ke kan ki Aziza da ki ke wata banzar magana na ga saurayin da ki ke so ai mata gare shi, shin idan aka mu ku haka za ku ji dad'i? Nace za ku ji dad'i idan aka mu ku haka? Ba za ku ji ba kenan? Shine kuma ku ke wa wata rashin kunya wacce ta mu ku alkairin da ki shi d'an uwan na ku bai mu ku kamar shi ba, shi d'an uwan na ku kunsan yanda ya ke d'aukar ta da kuma matsayin ta a wajen shi? Ku kan ku da akwai mutumci ai Khadija tafi k'arfin komai a wurin ku, wallahi ta wuce cin mutumci da cin zarafi, ko ba komai mafi soyuwar abu a zuciyar d'an uwan ku shine d'an wannan matar da ku ka raina, sannan ina yak'ini akai ko tamtama babu cewar Khadija ma tafi soyuwa a zuciyar d'an uwan ku, idan kuma kun shirya rasa shi ne to dan Allah ku ci gaba da mata rashin kunya, ni dai na fad'a mu ku gaskiya a matsayi na na uwa, kuma ke Aziza."


Hajia ta fad'a ta na nuna Aziza da hannu kafin ta ci gaba da "Kar na sake jin bakin ki daga yau in har su na maganar su, tunda ke kinfi kowa butulcia cikin su, Aziza matar nan har kashi da fitsarin ki ta ci kamar yanda ni ma na ci, matar nan ta kwantar da ke a gaban k'irjin ta kamar 'yar da ta haifa, matar nan ta mi ki wanka da hannayen ta ta shirya ki, duk lokacin da mijin ta baya nan ke ce abokiyar rayuwar ta, har rayuwa ta canza mu su ta haifi nata yaron ba ta banbanta ki da shi ba, Aziza sai da aka kai k'adamin da ta ware mi ki d'aki a gidan ta, kinfi kowa sanin Khadija a cikin dangin mu, amma kash ke ce farko wajen juya mata baya, Allah ya kyauta."


Ta na fad'a mik'ewa ta yi daga kan kujerar ta koma wajen wasu tsofi ta zauna, su kam tabbas jikin su ya yi sanyi, sai dai a ganin su duk cikin sharrin Khadija ne, Husseina ce tace "Gaskiyar Hajia, wallahi duk ranar da yah Fodio ya ji maganar nan a bakin mu, to fa kashin mu ya bushe."


Aziza ce tace "To ai dole tunda ta gama da shi, in ba kinibibi ba miye ta ke bashi kowane dare ya na sha da sunan shayi? Har da wasu k'ulallen abubuwa kamar kashin shanu kuma bai kai kashin shanu ba na ga ta na sakawa."


"Da gaske ki ke Aziza?" Cewar Rabi'a da duk cikin su tafi tsanar Khadija tun lokacin da ta nemi kud'i wajen d'an uwan ta, ta rik'e abun sosai a zuciyar ta ya na d'awainiya da ita har yanzu, Aziza ce tace "Wallahi kuwa, a madafa ta ke aje abun, kuma ko a gaba na sakawa ta ke."


Cike da makirci Rabi'a tace "Hakan ma wata hujja ce da za ta tona ta, Aziza ya za ayi ki d'auko mana wannan abun?"


Cike da rashin tsoro tace "Abu mai sauk'i, in dai har yanzu ta na aje shi in da ya ke ai zan gan shi."


Hassenah na shiga ta samu Khadija tsakiyar gado da manyan mata sai hira suke ana dariya, cike da fargaba ta yi abin da ya kai ta ta juyo ta fito, wajen su Hassana ta koma su ka ci gaba da hirar su, Khadija kuma na ganin fitar ta ta kalli k'awar ta Hajia Turai Dubaï tace "To kinga amaryar ta wa da har yanzu ki ka kasa zuwa ki gani."


Waro ido Turai ta yi tace "Ita ce kishiyar ki?"


"Eh." Ta fad'a har da dariya, hararan ta ta yi tace "K'arya ki ke wallahi, wannan ce za ta zama amaryar ki? Haba Khadija, ko da dai nasan halin mutanen mu ba kunya ne da su ba, amma taya Usman zai had'a ki da yarinyar can?"


*Umma* Khadija ta kalla tace "Ke da ki ka tabbatar sai ki fad'a mata gaskiya."


Umma ce ta d'ora "Wallahi ita ce kishiyar ta."


"Bala'i." Cewar Hajia Turai  cikin d'aga murya bugu da k'ari Allah ya hore muryar sosai, kasancewar irin mutanen nan ne masu ido bud'e da basu tsoron tashin hankali ko hargowa ya sa ta shiga aibata Haseenah ta na shammace ta, tun Khadija na cewa ta yi shiru dan Allah har ta yi banza da ita, hakan kuma da akayi duk a ido da kuma kunnen 'yar k'anwar mahaifiyar Usman (cousine d'in shi), ba ta b'ata lokaci ba wajen fitowa ta fad'awa Hassana da dama akan maganar Khadija suke, amma sai da ta keb'e ta gefe d'aya, Hassana ba ta tanka ba har lokacin da Mariya ta kira Haseenah wai idan ta na gida za ta zo ta kawo mata sak'on wajen malam, nan Haseenah ta fad'a mata ba ta gida amma za ta zo yanzu ita ta karb'a, sallama ta mu su tace ta tafi gida ba ta jin dad'i, ta na samun adaidaita ta wuce gidan Mariya, magani ta bata kala har uku wanda in dai ta yi aiki da su to ta tabbatar mata Usman zai zama na ta, d'aya za ta shafa a marar ta ne ranar kwanan ta ya sadu da ita, d'aya za ta saka a abin sha da ya danganci koko, fura ko kunu, sai kuma d'aya da za ta zuba a k'ofar d'akin Usman ya tsallaka, cike da farin ciki da jin ta yi nasara ta baro gidan ta nufi gida.


Fitar ta ba jimawa Khadija ita ma ta wuce gida dan kama aiki, nan fa su Hassana suka shirya abin da za su fad'awa Usman tare da shirya yanda za su yi.


Bayan sallah isha'i Usman na zauna a majalisar su ana hirar duniya kiran Hassana ya shigo wayar shi, sun tsara ita ta kira shi ne saboda ita ce babba da ke bi mi shi, ya na d'auka ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa, cikin taushin murya ta d'ora da "Yah Fodio dama ina son yin magana da kai ne, sai dai bansan ta yanda za ka fahimce ni ba."


Kamar ya na gaban ta ya yi murmushi yace "Ki tak'aita mana wahala to, ki fad'a a yanda zan fahimta."


Gaban ta ne ya sake fad'uwa kafin ta dake tace "Yah Fodio dama abin da ya faru d'azu wajen biki ne gaskiya bai ma kowa dad'i ba, Khadija dai ita ce babba kuma za ta iya rik'e ragamar gidan ka ko ba ka nan, amma abin da su ka yi d'azu da k'awayen ta gaskiya bai dace ba, dan wannan salesalen tayar da masifa ne, wallahi saida mu ka iza k'eyar Haseenah ta koma gida saboda ran ta ya sosu."


Kasanvewar ya na cikin mutane ya sa matsa gefe da su yace "Me ya faru? Me Khadija ta yi ita da k'awayen ta? Hassana ba na son masifa da tashin hankali ke kin sanni."


Cike da tabbatarwa tace "Wallahi gaskiya na ke fad'a ma ka, a d'akin *Zaliha* fa su ka zauna suna ta shammatar Haseenah su na zagin ta ta uwa ta uba, idan kuma ba ka yarda ba ka tambayi *Nana* (cousine d'in su) za ta fad'a ma ka gaskiya, musamman ma wannan k'awar ta ta mai ido tsaye Hajia Turai."


Ba wai rantsuwar da ta yi ba ce ya sa ya yarda sai anbaton sunan Hajia Turai da ta yi, matar ba ta da wata d'abi'a da zai ce ba ya son mu'amular ta da matar shi, sai dai irin matan nan ne da masu da kimtsi, komai ya zo bakin ta fad'a ta ke sannan ba ta tsoron bala'i da mace kl namiji, hakan ya sa ma har yanzu ta ke zawarci babu mijin aure sai duniyar ta da ta ke ci da tsinke, nisa da tunanin da ya yi ne ya sa ya kashe wayar bai ma san ya kashe ba, zunbur ya mik'e ya fad'a motar shi ya nufi gida.


Tsaf Khadija ta gama shirya komai ta aje a muhallin shi ta shiga wanka, jin babu motsin ta ne ya sa Haseenah tabbatarwa yanzu ta na wajen shiri, ta falon ta ta shigo na shi falon cikin sand'a da rashin gaskiya, kai tsaye k'ofar uwar d'akin shi ta nufa da k'ullin maganin ta, ta na zuwa ta bud'e ledar tasa yatsu biyu kamar yanda aka fad'a mata, barbad'awa ta yi tare da kiran sunan Usman, sau uku ta zuba kuma a kowane zubawa sai ta kira sunan shi, da sauri ta rufe ledar ta koma falon ta da sauri cikin tsoro, ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke kafin ta dafe k'irji ta yi murmushi, Usman da ke hanyar shi ta zuwa gida ne ya ji wani bala'in sarawar kai kamar an buga mi shi guduma, da k'arfi ya take motar ya tsaya ya dafe kan shi, ya jima a haka sai da ya ji motoci na mi shi odar ya ba su hanya kad'ai ya dawo hayyacin shi ya taka, Khadija na d'aki ta gama duk wani shirin ta ta mik'e ta na d'aura d'an kwali ta ji an bud'e k'ofa da k'arfi, juyowa ta yi dan ganin waye wannan, ganin Usman a wani yanayi da ita dai ba ta tab'a ganin shi a ciki ba ya sa ta d'an kalle shi da mamaki, ganin nufota kawai ya ke ba magana ya sa ta k'ara yin baya da in'i'na tace "A..Abban...Bil."


Ba ta k'arasa ba yace "Khadija akan me ku ka ci zarafin mata ta a gidan biki cikin mutane?"


Mamaki ne fal a idon ta, rarraba ido ta fara yi sai motsa baki ta ke ta na so ta yi magana amma ta kasa, nuna ta ya yi da yatsa yace "To daga yau kar haka ta sake faruwa, idan ba haka ba kuma ran ki zai b'ace, sannan Hajia Turai ba na son ki sake mu'amula da ita, kinji na fad'a mi ki."


Bai jira me za tace ba ya fita daga d'akin ya nufi d'akin Hassenah wacce ta buga tagumi ta na jiran ta jime zai faru, ya na ganin ta da wannan tagumin sai ya ji tausayin ta a tunanin shi akan abin da ya faru ne, ita kuma ba ta ma san me ya faru ba, zaune ya yi kusan ta ya kalle ta yace "Amarya ta, dan Allah ki yi hak'uri kinji akan abin da ya faru, insha Allahu na mi ki alk'awari hakan ba za ta sake faruwa ba."


Cikin rashin fahimta tace "Me kuma ya faru? Akan me ka ke magana?"


Jannyo ta ya yi jikin shi ya na shafawa yace "Idan ke ba ki fad'a min ba ai Hassana ta fad'a min, amma kamar yanda na fad'a mi ki ne ba zai sake faruwa ba in Allah ya yarda."


Shiru ta yi a k'irjin shi ta na tunanin me ye ya faru to? Jin ta yi shiru ya sa ya d'agata daga jikin shi da cewa "Zan shiga wanka, amma ki tabbatar kin fito mun ci abinci ba sai na zo da kai na ba."


Da kai kawai ta ma sa alamar to, fitowa ya yi ya nufi d'akin shi, ya na bud'a k'ofar ya tsallaka ya sake jin gaban shi ya tsinke ya fad'i tare da sarawar kai, hannu d'aya ya saka ya dafe kai ya rintse ido sosai, da k'yar ya iya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."


Gaba d'aya jikin shi ne ya yi sanyi a haka ya cire kayan shi, zai shiga wanka Khadija ta yi sallama a d'akin ta shigo, shiru ya mata kamar bai ji ta ba har ta tsaya gaban shi, wani abu ya ke ji a zuciyar shi da bai tab'a jin irin shi ba tunda ya ke da ita, amma da ya ke sabon abu ne sai ya taushi zuciyar shi, a hankali ta rik'e kunnuwan ta cikin taushin murya tace "Ka yi hak'uri *sadauki na*, na karb'i kuskuren da k'awaye na su ka yi, kuma zanyi yanda ka ce da yardar Allah."


Ba fara'a a fuska yace "Ya wuce." Ban d'aki ya nufa ta yi saurin rik'o hannun shi ya juyo, marairaicewa ta yi tace "Ka tab'a wanka da kan ka idan ban taimaka ma ka ba?"


Wani murmushi ya yi kamar mai ciwon baki kafin ya ja hannun ta zuwa ban d'akin, sosai Khadija ta fahimci akwai sabon al'amari a tare da shi, dan har ta gama mi shi wankan nan ba su yi wata magana ba, kamar yanda sai dai ya mata murmushin yak'e kawai, haka ta gama mi shi shiri su ka fito cin abinci, sun zauna kenan Haseenah ta fito ita ma, tunda ya kafe ta da ido bai d'auke ba har ta zauna, murmushi kawai ya ke sakar mata har Khadija ta gama zuba abinci.


Haka aka ci abinci babu wani nishad'i bare jin dad'i, su na gamawa ya nufi wajen Haseenah dan yi mata saida safe, ita ma Khadija shiga ta yi dan ta yi shirin bacci, amma har ta gama ta dawo bai dawo d'akin shi ba, abun mamaki shine har ta d'auki minti ashirin kwance kafin ya shigo, ya na can Haseenah na zuba shagwab'a wai zai tafi ya bar ta, ya na shigowa kashe wuta ya yi ya kwanta, zunbur Khadija ta mik'e da tafarfasar zuciya ta na kallon k'eyar shi tace "Me zan gani haka Abban Bilal?"


Juyowa ya yi a kasalance yace "Me fa?"


"Baya fa ka juya min, me na ma ka haka da zafi? Akan abin da ya faru ne? Dan Allah ka yi hak'uri in dai abin da ya faru ne zai sa ka juya min baya."


Yanda ta yi maganar cikin muryar kuka ya sa k'wak'walwar shi hasko mi shi wacece ita, tashi ya yi zaune ya rumgumo ta jikin shi yace "Shikenan to ya wuce, ki yi hak'uri kar ki min kuka, ba na yi bane da gangan, kawai ba na jin dad'i ne."


Da kuzari ta kwantar da shi akan gadon tace "Kwanta to na ma ka tausa."


Cire mi shi rigar shi ta yi a hankali ta fara shafar bayan shi, yanda ta gama kashe mi shi jiki ya sa ya juyo ya sauke idon shi akan ta, da k'arfi ya fizgo ta ta fad'a jikin shi ya had'e labb'an su...saida safe.


Kwana biyun da ya yi a wajen Khadija ya zo da al'ajabi, dan sosai ta ke gani bak'in al'amura daga gare shi, shi kan shi ya na jin wannan canji a tare da shi, amma tasirin wani abu ne ya ke mi shi togaciya ga abin da ya ke ji, asabar da yamma Haseenah ta karb'i girki, a daren ranar da ta yi anfani da maganin nan a marar ta ko da Usman ya kusanceta ya ji duk fad'in duniya babu maccen da ya ke son kasancewa da ita sama da ita, ba ma wannan bane yafi d'aga hankali kamar yanda ya ke jin kamar ita ce ma macen da ta fara gamsar da shi a shinfid'a, gaba d'aya ya nemi tasirin wata mace ya rasa, tun a daren ya fara ririta Haseenah kamar yau ya fara ganin ta ko sanin ta.


Washe gari ma bayan ya fita ta sa aka samo mata fura ta dama, sosai ta had'a furar kafin ta zuba maganin na k'arshe a ciki, da kan shi ya zo cin abinci bayan ya kammala ta kawo mi shi furar cikin kofin tangaran mai kyau, kallon ta ya yi yace "Fita na ke so na yi fa, idan kuma na sha furar nan jiki na zai mutu na yu bacci."


Cike da shagwab'a tace "Uhum uhum, wallahi ni dai ban yarda ba sai kasha, saboda kai fa na had'a."


Take ya ji sak'on ya kai zuciyar ya ji ai tafi k'arfin ma ya yi gardama da ita, amsa ya yi tare da kurb'ar furar har ya shanye, mik'ewa ya yi ya shiga wanka ya na fitowa ko riga bai saka ba ya kwanta sai bacci.


Da da magriba ta tashe shi ya yi alwala ya tafi masallaci, bai shigo gidan ba har ya yi sallah isha'i, ya na idawa ya d'auko hanyar dawowa a lokacin kuma Naseer ya dawo da Bilal gida, sun jima a k'ofar gidan su na kafin Naseer ya tafi shi ya shigo ciki, kai tsaye tare da Bilal suka shigo b'angaren Khadija, tunda ya hangi Khadija akan kujera ya ji wani bala'i ya taso mi shi tare da sarawar kan shi, da gudu Bilal ya k'araso ya rumgume ta, rumgume shi ta yi cike da k'aunar d'an na ta tace "Yarima kai da wa?"


D'agowa ya yi ya na cire jakar bayan shi ya na fad'in "Tonton Naseer ne."


Gira ta d'aga sama tace "Uhum! Wato dai kun zama abokai ko?"


Dariya ya yi yace "Mummy bara kiga abin da ya siyo min, kuma Hajia ma ta siyo min wani abu."


Murmushi ta yi ta mayar da hankalin ta kan Usman tace "Sannu da shigowa Babban mutum."


Wani irin amo ya ji muryar ta na mi shi cikin kunne marar dad'in ji da sauti, juyawa kawai ya yi ya fita ta k'ofar da ya shigo ya nufi na shi falon,   ya na fita ya ji wani sak'at a zuciyar shi saboda ba ya ganin Khadija, Khadija kam abun ya bata mamaki sai dai hayaniyar Bilal da kayan da ya ke fito da su ya na nuna mata ya sa ba ta wani saka a kai ba, shi kam ya jima zaune sai ya d'auko tunani kamar akan bak'on al'amarin nan, amma kuma sai ya ji k'walwar shi ta yi wani jugum kamar babu komai a ciki, hakan ya sa ya yi tsaki sama da dubu kafin Haseenah ta shigo ta same shi.


Dare ya yi dare Khadija ta kasa bacci ta na tsammanin jiran shigowar Usman amma babu shi babu labarin shi, tun Bilal na mata hira na abubuwan da suka faru a gida har bacci ya d'auke shi, haka ita ma baccin ya d'auke ta daga wurin ba ta ankara ba, haka har akayi sallaha asuba gari ya waye bai lek'o ba, shi kuma ya na can ko ya ji a ran shi ya zo sai kuma ran shi ya b'ace haka kawai, har Haseenah ta masa magana ya zo ya mu su sallama ya share kawai, dad'i ta ji a zuciyar ta amma a zahiri ta nuna bai dace ba.


Washe gari da safe haka kawai Usman ya ji ba ya son fita ya yi nesa da Haseenah, ko k'ofar gida bai fita ba in ba sallah ya je yi ba, bayan sallah la'asar Aziza ta zo gidan tare da rakiyar k'awar ta, kai tsaye b'angare Khadija suka fara nufa saboda nan kad'ai k'ofar a bud'e, Khadija da a lokacin abun duniya ya isheta na  rashin ganin Usman bayan kuma ta na da tabbacin ya na gidan, amsa sallamar ta yi a dak'ile tare da kallon su a raunane, har su ka zauna babu wanda ya sake magana, kallon Uwani ta yi dake gefe tace "Uwani kawo mu su abun sha ko."


To." Ta fad'a ta na mik'ewa, k'ala Khadija ba ta sake cewa komai ba har Uwani ta dawo da abun sha, sai lokacin Aziza tace "Aunty Khadija wai ina Bilal? Ban gan shi ba."


Kallon ta Khadija ta yi cike da rainin wayo saboda tunawa da ta yi ranar da taji Aziza da bakin ta tana kiran d'an ta shege, a kaikaice ta sake kallon ta tace "...



*Allah ka bawa dukanin musulmi lafiya.*

06/02/2020 à 22:23 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

        *KALLON KITSE*

          _(Ake wa rogo)_         

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑




_SAMIRA HAROUNA_



*Littatafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._



*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



```Fatan alkairi masoya```


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

(GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA INSHA ALLAH)🤜🤛



*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*



*INA JIGA JIGAN MASOYAN 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S WAD'ANDA BASU DA TAMKA A WAJENMU????? DUK WANDA YAKE TARE DAMU A CIKIN GROUPS D'INMU TO MUN TABBATAR K'AUNARMU CE TASA KUKA KASANCE TARE DAMU, MUNA YABAWA KUMA HAR ABADA BAMU DA KAMARKU WALLAHI,👍 DUK DA HAKA DAI GA LOKACI YAZO, KUMA DAMA TA SAMU NA TABBATAR MANA DA KUMA NUNA MANA HAK'IK'ANIN K'AUNAR DA KUKE MANA,👇*






Kunsan cewa k'ungiyarmu *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* suna cikin gagarumin gasa na samun award Wanda *women24 TV WhatsApp group* suka shirya kuma zasu gudanar?


A wannan gasar ne za'a samu k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan fans da Kuma bin k'a'idar rubutu


Dan ki samu damar zabar k'ungiyarmu *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S ASSOCIATION* zaki iya tuntub'ar wannan lambar 09030159301 Dan su saki a *WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP* anan ne za'ayi zab'en k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan masoya


*Women24 Tv*

Ba zabe kad'ai zakiyi ba


Zaki k'aru da abubuwa da yawa kamar haka


*Yanda ake girke girke*

*yanda zaki gyara jikinki*

*yanda zakiyi makeup*

*yanda zaki daura Dan kwali*


Kuma suna shirye shiryen nan na *arewa24 tv* kamar su


*TARKON KAUNA*

*DADIN KOWA*

*KWANA CHASA'IN*

*JAMAI RAJA*

*SAPNE SUHANE*

*GIDAN BADAMASI*

*RUDIN ZUCIYA*

*BAGHYA LAKSHMI*

*AKUSHI DA RUFI*

*AUDIO NOVEL*

*HAUSA NOVELS*


Kada ki manta da ranar zabe inkin shiga group d'in ki zaba *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* tanan ne zaki iya nuna mana irin sonda kuke ma k'ungiyarmu da littattafammu, kuma a ko'ina ko a kowace k'asa masoyanmu suke sunada damar zab'enmu ba sai 'yan nigeria kad'ai ba.


Allah yabar zumunci🤝😍🥰💋


_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *20*



"Bilal ya na nan, kinyi kewar shi ne har haka?"


Wata 'yar dariya ta yi tace "Ban gan shi bane ba ai."


"Uhum." Cewar Khadija can k'asan mak'oshi, jim kad'an Khadija ta kalle su tace "Ku wuce ciki mana ai suna nan, dan nasan wajen su ku ka zo."


Cike da kunya Aziza ta d'anyi jim kamar ba za ta tashi ba, a hankali su ka tashi tace "Bara mu gaishe ta sai mu wuce."


Da ido kawai ta bisu ba tace k'ala ba, saida su ka fita ta gyara zaman ta, su kuma sun jima bakin k'ofa su na bubbugawa tare da sallama amma shiru, da k'yar Haseenah ta fito cikin riga da wando ta bud'e, saida ta saki wani d'an k'aramin tsaki saboda ganin su, washe baki ta yi ta na fad'in "A'a'a'a, su Aziza ne a gidan mu? Sannun ku da zuwa, ku shigo mana, ashe ku ne ke ta bubbugawa, ina wanka wallahi."


Duk ta yi maganar ne lokacin da suke shiga ciki, zaune su ka yi ita ta wuce ciki, da kallo su ka bita kafin su mayar da kallon su kan telebijin, Usman ta samu kwance akan gadon ta kamar mai son yin bacci, da k'yar ta samu ta rabu da shi ta sanyo hijabi ta fito, nan fa su ka shiga hira dan dama Usman yace kar ta gajiyar masa da kan ta za su fita cin abinci tare, dan haka ba ta damu ba har Aziza ta d'an kalle ta dan ita dama madafar ta ke son shiga, cikin taushin murya tace "Auntyn mu yunwa fa na ke d'an ji."


Hararan gefen wutsiyar ido ta wa Aziza amma a zahiri ta yi dariya tace "Ki ke d'an ji ko ki ke ji?"


Dariya su ka yi tace "To na ke ji, akwai indomie?"


"Kinsan ai ba za'a rasa ba, bara na d'ora mu ku" Ta fad'a cike da k'arfin hali, Aziza ce tace "Ah haba dai amaryar mu, ina mu ina saka ki aiki, yayan mu fa na d'aki, dan haka ki bar mana komai ni zan shiga da kai na, ko kin manta gidan nan ba bak'o na bane."


Cikin dariya Haseenah tace "Na sani kam, ai yanzu ma ina jiran ranar da za ki sake kawo mana ziyara ne."


"Zan zo, amma sai an koma makaranta  (school) dan yafi dad'i, saboda yafi kusa kuma nafi jin dad'in zama a lokacin."


K'awar ta ta kalla tace "Ina zuwa *ma chérie.*"


Wucewa ta yi Haseenah ma ta shiga ciki dan ganin mijin ta, Aziza na shiga kai tsaye wata yar drower ta bud'a, cikin sa'a kam ta lalabo abin da ta ke nema, murmushi ta yi tace "Yawwa, na samo shi." Ta na fad'a ta saka a k'asan siket d'in ta kafin ta fara had'a indomie, cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta fito da ita a cikin faranti, su Haseenah na zaune ta aje tace "To to bismillah, ba zan jira kowa ba fa."


Haseenah kallon indomien ta yi sosai yawunta ya tsinke, sai dai kuma a k'oshe take bare ta ci, sai dai ta na mamakin yanda suke dafa indomie haka gwanin kyau da dad'i, ga dukkan alama ma Azizar ta koya ne a wajen Khadija tunda kamar babbar yar ta ce a yanda ta samu labari, ba ta ci ba sai kallon su da take su na hira har su ka kammala, sun tashi tafiya ta shiga ciki ta d'auko kud'i sosai ta basu su hau adaidaita, haka su ka fita cikin jin dad'i da kuma samun nasara wajen Aziza, ko takan Khadija ba su bi ba bare su mata sallama, su na shiga adaidaita aka fara aje k'awar Aziza, daga nan ita kuma gidan Hassana ta wuce, ta na zuwa ba ta yi k'asa a gwiwa ba wajen bata wannan abun, saida ta k'are ma sa kallo sosai ta kalli Aziza jiki a sanyaye tace "Aziza kinsan me ye wannan?"


Kai ta girgiza tace "A'a, amma dai shine ta ke zubawa a shayi, wani lokacin ta daka wani lokacin kuma ta saka a haka."


Tsakin jin haushi Hassana ta yi tace "Wannan fa minana ce, k'wallon ta ne wannan kafin a daka ta zama gari."


"To miye shi d'in?" Cewar Aziza, cikin jin haushi tace "Ana had'a maganin mata da shi, watak'ila akwai wani anfani da ya ke da a jikin namiji ne da ya sa take sakawa."


*Hotiho, ki koma makarantar mata*


Dafe kai ta yi tace "Me ya sa ma banyi tunanin haka ba? Tun farko ya kamata musan ba za ta tab'a aje wani abu muhimmi a madafa ba, bugi da k'ari ita fa k'awar Kaltume ce."


Cikin rashin jin dad'i Aziza ta baro gidan ta koma gida, ta na zuwa gida ta samu malam ba ya jin dad'i zazzab'i mai tsanani, ya sha magani amma har yanzu rawar d'ari ya ke, hakan ya sa aka kira Usman da a lokacin ya ke gida tare da amarsu, cikin gaggawa ya canza kaya ya fita zuwa gidan, ya na zuwa kuma asibiti su ka nufa da shi aka ba shi agajin gaggawa, an bashi taimakon amma kuma ya na buk'atar jini, nan fa yaran su ka shiga layi dan a gwada nasu a k'ara ma sa, gwajin farko aka gane na Usman ya dace da na shi, ba'a b'ata lokaci ba aka kwasa aka k'arawa malam, sun jima a asibitin su na kai da kawowa har dare ya yi sosai.


Ya na zuwa kai tsaye d'akin shi ya wuce, a can Haseenah ta same shi har ya shiga wanka, shiga ta yi su ka yi wankan har su ka fita, cikin shagwab'a ta kalle shi tace "Ni fa yunwa na ke ji."


Kallon ta ya yi sosai, ya na ji kamar ya tuhume ta akan rashin tambayar shi lafiyar mahaifin shi, amma kuma sai ya share yace "Ki yi hak'uri, me ki ke so ki ci yanzu?"


Cikin tiro baki tace "Abu mai dad'i na ke so."


"Kamar me?" Ya sake fad'a ya na d'aukar wayar shi a gaban madubi, "Koma meye." A cewar ta ita ma.


Waya ya yi Bilyamin ya sa ya kawo mi shi duk abun buk'ata, har ya gama shiryawa ita ma haka, suna zaune ya ji ya gagara samun nutsuwa saida yace "Ba ki tambayi jikin Baba ba, kamar abun bai dame ki ba, har da jini fa aka k'ara ma sa, kuma nawa aka d'iba." Ya k'arasa da nuna mata hannun shi da aka d'ibi jinin.


Kallon shi ta yi cikin rashin jin dad'i take ta k'ak'aro hawayen k'arya tace "A ganin ka ban damu da ku bane ko me? Kasan halin da na shiga saboda rashin dawowar ka da wuri? Duk da ana fad'a min wayata babu kud'i amma bai hana ni kiran lambar ka ba saboda tunanin ko za su duba girma da soyayyar da na ke ma ka su aika kira na a wayar ka, amma a haka ka ke cewa ban damu ba? Lallai ma."


Mik'ewa ta yi irin ta yi hushin nan za ta fice, Usman kam sai ya ji kamar ta na zuba ma sa ruwan zafi wannan kukan da take, da sauri ya rik'o ta ta fad'o kan sa ya shiga rarrashi, da k'yar ta yi shiru tace ya wuce, lokacin kuma Bilyamin ya kawo mu su abinci, da kan shi ya fita ya amso tare da bashi kud'i yace ya rik'e canjin, dawowa ya yi ya kawo mata amma kafin ta zuba yace "Bara na shiga na ga yarima, nasan yanzu dai ya yi bacci."


"Amma fa idan ka jima ba zan jira ka ba." Ta fad'a ta na nufa kan teburi ta d'auko faranti, baice komai ba ya fice, ai kuwa a falo ya samu Khadija ita kad'ai zaune, idon ta akan telebijin amma da gani kasan hankalin ta ba nan ya ke ba, da sauri ta zabura ta sauke idon ta akan shi, shi ma ita ya ke kallo amma da wani irin yanayi na tsana da haushi, mik'ewa ta yi ta nufe shi da k'arfi ta fad'a kan jikin shi ta sauke ajiyar zuciya ta na sake rumgume shi sosai, cikin muryar kuka ta furta "Na yi kewar ka Abban Bilal."


A hankali cikin dubara ya raba ta da jikin shi ya na d'an k'aramin tsaki ya kalne ta yace "Me ye na kuka kuma?"


Kamar wacce ya mara sai ta sake fashewa da kuka saboda bak'in cikin da ke zuciyar ta, sunkuyar da kai ta yi k'asa ta na jiran ta ji ya janyo ta jikin shi ya gara rarrashi kamar yanda ya ke, amma sab'anin haka sai cewa ya yi "Wai me ye na kukan dan Allah yanzu cikin daren nan? Wani abu aka mi ki?"


Girgiza kai ta yi cike da mamaki ta na kallon shi, cikin jin haushi ya d'ora da "Shine kuma za ki tasani gaba ki na kuka, ba na son koke-koken nan ni wallahi, haka kawai da girman ki da komai ki tsaya ki na kuka, ke ba duka ba, ba zagi ba, salon jawa mutane magana."


Wani tsaki ya kuma yi kafin yace "Ina Bilal ya ke?"


Khadija da bakin ta ke bud'e kamar k'adangare zai shiga ciki ta nuna mi shi k'ofar d'akin Bilal, cikin hararen ta yace "Ya yi bacci ne?"


Saida ta zura hannu ta cikin gilashin ta ta share hawaye tace "Eh."


Juyawa ya yi rai b'ace yace "Saida safe."


Har ya bud'e k'ofar kuma ya tsaya yace "Baba ba shi da lafiya ya na asibiti,ku yi k'ok'ari da safe ku je ku ga jikin shi."


Fuskar ta kad'ai ta nuna mi shi damuwar da ta shiga a lokacin, saida ta matsa kusan shi tace "Me ya samu Baba? Ya jikin na shi yanzu? Ina fata fai da sauk'i?"


Sharewa kawai ya yi yace "Da sauk'i." Kamar ansa shi dole, zai fita ta sake cewa "Ka tabbatar ya na lafiya? Gaba d'aya ba na jin dad'in jiki na."


Sama da k'asa kawai ya kalle ta ya wuce abin shi, daskarewa ta yi a wajen ta na tunanin abin da ke shirin faruwa da su koma ya faru d'in, ta jima tsaye kafin ta kashe wuta ta wuce d'akin ta, alwala kawai ta d'oro ta zo ta kabbara sallah, tun daga nan ta fara kaiwa Allah kukan ta tana neman agaji da mafita, sai kusan *uku* na dare bacci ya d'auke ta, kuma ana kiran sallah ta farka ta taje ta tashi Bilal shim, Usman da kan shi ya zo ya tafi da shi suka shiga masallaci.


Ko da gari ya yi haske Khadija ta shiiryawa Bilal abun kari ya ci, shiryawa ya yi Baban shi ya tafi kai shi islamiyya, daga nan kuma asibiti ya wuce ya samu jikin malam da sauk'i sosai ya na ta hirar shi akan gado, ya na dawowa ya gida ya sake kwanciyar shi , Khadija kuma ta shirya dan zuwa ganin Baba, ganin shiru babu wanda ya mata magana ya sa ta kira wayar shi, a lokacin Haseenah ta gama soya k'wai da dankalin turawa ta shirya cikin ado mai kyau, ta na ganin kiran amma ta yi banza da ita, ta na ji ta na gani ta hak'ura da tafiyar sai Hajia ta kira ta tambayi mai jikin tace za ta shigo anjima.


Wani abun haushi shine a lokacin Haseenah ta tashi Usman daga bacci wai sai ya kaita asibiti ta ga Baba, tun ya na cewa bacci ya ke jin har ya wartsake ya tashi ya yi wanka ya shirya, wajen tebur suka nufa su ka cika cikin su kafin yace su tafi, *11:00* cif suka fita daga gidan ba tare da sanin Khadija ba, dan lokacin ita ma har bacci ya d'auke ta daga nan haka ma Uwani saboda shirun ya yi yawa.



Da isar su asibiti ta samu su Hassana zaune a bakin wata bishiya akan tabarma su na ta hira, nan ta zauna suka fara gaisawa, Hajia da ke tsaye da buta a hannu ce ta fara cewa "Yo ina Khadija? Ai na d'auka tare za ku taho tunda ta kira ni."


Kalar Haseenah ta sani kam sai cewa ta yi "Aunty ai ta na gida bacci ta ke, watak'ila sai da rana ta taho."


"Uhum." Cewar Hajiar ta wuce sabgar gaban ta, Rabi'a ce ta fara cewa "Hum! 'Yar hutu ce kinsan, kuma shi ba zai iya tashin ta ba saboda gudun b'acin ran ta."


Husseina ce tace "To kinsan da haka ma miye na wahalar da bakin ki wajen fad'a."


Hassana ce ta kalli Haseenah tace "Haseenah dai ki dage sosai kinji ko da addu'a, kar a shantake ayi ta bacci, dan matar nan da ki ke gani ba Allah ne a gaban ta ba, ke ma wallahi watak'ila tsananin rabo ne ya shigo da ke gidan, tunda ba tun yau ake mi shi maganar k'ara aure ba, amma da an mi shi maganar yanda ki ka san ka zagi uwar shi da uban shi haka ya ke kallon ka, mufa har saida ta kai ya daina sakar mana fuska."


Murmushi Haseenah ta yi tace "Insha Allahu su aunty babu abin da zai faru, Allah ai ba azzalumin bayin sa bane."


Husseina ce tace "Allah sarki yar albarka, Allah ya kare ki daga sharrin ta."


"Ameen." Ta fad'a da murmushi, mik'ewa ta yi tace "Bara na shiga na ga jikin Baban."


Ledar bayan ta ta janyo mai d'auke da kayan marmari kala kala ta d'auka ta wuce, da kallo su ka bita kafin Hassana tace "Wallahi yarinyar tausayi ma take bani, sukuku da ita ba kazar kazar."


Rabi'a ce ta yi tsal tace "Ai ba ki ga abun tausayi ba sai randa mu ka je gidan shegiyar nan ta kusa k'ona ta, wallahi inda kinga ta ma bud'e baki ta yi magana kasawa ta yi sai da k'yar."


Haka su ka ci gaba da tattaunawa har suka fito su ka mu su sallama suka koma gida, saida ya wuce ya d'auko Bilal dan lokaci ya yi kafin su ka wuce gida, k'arar bud'a k'ofa ne da mai gadi ke yi ya sa Khadija farkawa, ta ga motar Usman ce sai dai ba ta ga tare da wa yake ba, Bilal na shigowa ya tabbatar mata da shine ya d'auko, d'aki ya wuce dan cire kaya Khadija kuma ta kalli Uwani tace "Bara na shiga madafar da kai na idan bata fara aiki ba na d'ora mi shi ko indomie ce."


"To." Ta fad'a ta bita da kallo, ba ta samu kowa ba dan haka ta shiga abin da ya kawo ta da gaggawa, saida ta kammala ta fito dan d'auko farantin da za ta zuba, Bilal ta gani ya fito daga d'akin da da ledar bredi a hannu da gwangwanin madara, da sauri ta nufe shi ta karb'e madarar ta na fad'in "Sau nawa zan fad'a ma ka ba na son ka na anfani da madarar nan haka kawai idan ba a cikin shayi ba."


Cikin kukan shagwab'a ya biyo bayan ta ya na fad'in "Mummy yunwa na ke ji fa, ki zuba min ko kad'an ce."


Juyowa ta yi ta kalli Uwani tace "Uwani taimaka dan Allah d'auko faranti a d'akin can ki juyo indomien da na dafa."


"To." Dai ta sake fad'a ta nufi d'akin, Khadija dawowa ta yi ta zauna akan kujera tace "Zauna yanzu Uwani za ta kawo ma ka indomien ka ka ci."


Cikin turo baki ya aje bredin ya zauna in da ta nuna masa, Uwani kuma na shiga ta samu Haseenah tsaye ta d'auki indomien nan ta na juyeta wajen da ake zuba ruwan datti, da sauri tace "Kai, aunty amarya Umman Bilal ce ta dafa ta yanzu."


A wani gatsine ta juyo ta kalle ta tace "Wacece hakanan kuma?"


Shiru Uwani ta yi dan ba ta san me za tace ma ta ba, hakan ne ya sa Haseenah zuwa ta shak'i wuyan rigar Uwani tace "Me na fad'a mi ki? Bance ba na son sake ganin ki a madafar nan ba idan ina girki? K'azama da ke kawai ki dinga cud'anya cikin mu sai kace kema wata matar shi ce, dallah fice min daga nan."


Yanda ta tura Uwani da k'arfi sosai ya sa ta yi baya kan ta ya had'u da bango, fitowa ta yi dafe da kan ta ta samu Khadija ta fad'a mata komai, Khadija ta so ta yi magana kan abin da ta yi sai kawai ta share ta sa Uwani ta d'auko gas d'in ta suka kunna, ruwan d'umi ta fara d'orawa Bilal ta had'a mi shi shayi sannan ta sa Uwani ta d'ora tukunya ta je madafar da kan ta ta d'auko duk abin da take buk'ata suka d'ora na su girkin.


Haseenah na ganin haka ta shiga d'akin ta ta samu Usman kwance da waya ya na dannawa, cike da nuna b'acin rai ta yi tsaye tace "A gaskiya abin da ake min ba na jin dad'in shi ko kad'an domin Allah."


Zaune ya mik'e yace "Me ya faru kuma? Waya tab'a min zinariya ta?"


"Ba na son tashin hankali da rigima, ina so na zauna da kowa lafiya, amma aunty Khadija ta na so ta kawo wata b'araka a tsakanin mu ta hanyar raba girkin ta da nawa, saboda Allah ba dan neman magana me zaisa ta d'ora girkin ta bayan ga shi can na d'ora?"


Da d'an mamaki ya kalle ta kafin yace "Amma ai na d'auka na hana ta, me ya sa ba ta ji abin da na fad'a ba."


Hanyar fita ya yi yace "Je ki ci gaba da aikin ki, zan je na gani da kai na."


Kai tsaye b'angaren Khadija ya nufo, ya na zuwa bai same su a wajen ba amma tukunya na saman gas, ai kuwa kamar hauka sabon kamu sai ya sa k'afa ya hanb'are tunkuyar, k'arar dungurawar tukunyar ne ya sa Khadija da ke falo suka taho a guje ita da uwani dan ganin meya faru, ganin Usman tsaye ya na huci ya sa Khadija kallon shi da mamaki tace "Abban Bilal, lafiya? Me ya faru?"


Da yatsa ya nuna ta yace "Ban fad'a mi ki kar ki sake d'ora min girki a gida ba in har ana girki? Ko raina ni ne ki ka yi shi ya sa ba ki d'auki abin da na fad'a da mahimmanci ba."


Cije leb'e Khadija ta yi ta rintse ido lokaci d'aya kuma ta bud'e ta kalle shi tace "Na ji, ka yi hak'uri ba za'a sake ba."


"A sake ma a gani, wallahi ran ki zai b'ace, aikin banza kawai mace ba ka isa ka fad'a mata ta ji ba." Duk ya yi maganar ne ya na komawa in da ya fito, Uwani ta kalla tace "Ki gyara wuri ki mayar da komai muhallinsa."


"To." Uwani ta fad'a jiki a matuk'ar sanyaye dan ba ta yi tunanin shine ba, falo Khadija ta zauna zuciyar ta na suya, wani b'angaren kuma kamar ta fashe da kuka amma ta na tausar zuciyar ta, dan in har abin da take tunani shine ke faruwa a yanzun, to fa zaifi ta adana hawayen ta dan zasu fi mata anfani nan gaba kad'an, haka suka zauna jugum da su Bilal har ya yi bacci ya tashi saboda lokacin islamiyya ya yi, har ya shirya ya yi sallah babu abinci daga wajen Haseenah, Usman kuma tunda ya gama masifa ya bar gidan har yau bai dawo ba, suna zaman jiran shigowar shi sai ga shi ya zo, Bilal ne ya fita ya same shi a farfajiyar gidan yace " Abba na shirya lokaci ya kusa."


Shafa kan shi ya yi yace "Yarima har ka shirya? Gashi kuma yunwa na ke ji yanzun, amma muje na aje ka na dawo."


Shiga su ka yi ya fara baya-baya ya na fad'in "Da alama sai na samar ma ka dreba (driver), dan Bilyamin ma ka ga aure zaiyi, ba za mu dinga takura shi ba wajen kai ka makaranta idan bana nan."


K'ala Bilal baice ba har ya sauke shi a makaranta, juyowa ya yi ya dawo gida, Khadija na ganin mai gadi ya bud'e ma sa k'ofa ta fito, tsaye ta yi har ya fito daga mota ya kalle ta yace "Lafiya dai?"


"Lafiya lau, dama akan maganar duba jikin Baba ne, ka ga har yamma tayi ba mu je ba, shine na ce ka mana izini mana idan na kammala girki sai mu tafi da ita ba sai mun jira ka ba."


Cike da rashin damuwa yace "Kar ki damu, kije kawai idan kin gama, ita ta tafi tunda safe ai, ni na kai ta."


Mamaki ne ya bayyana a fuskar ta tace "Ka kai ta? Amma Abban Bilal kasan tsawon lokacin da na d'auka a d'akin nan ina jiran ta?" Ta k'arashe da nuni da k'ofar falon ta.


Tab'e baki ya yi yace "To sai me? Laifi na yi da na kai ta? Kinga bana son masifa, idan kema ki na so idan kon shirya ki yi magana sai na kai ki da kai na, shikenan?"


Saida ya harare ta sama da k'asa ya ja k'aramin tsaki ya wuce, jiki a sanyaye ta juyo ta dawo, ta na zuwa ta samu Haseenah ta kawo abincin rana bayan sallah la'asar, ko kallon abincin ba ta yi ba tace ma Uwani "Ki ci abincin idan ki na buk'ata."


Juyawa ta sake yi ta nufi madafa, aiki ta fara ba kama hannun yaro, saida Uwani ta gama cin abincin sai dai ba wani mai yawa ba, dan duk yunwar da take ji kasa cin abincin ta yi saboda ba za ta iya cewa ga abin da ya yi yawa ba, sai dai tabbas akwai abin da ya yi yawa a cikin girkin, nan suka shiga aikin su ita da Khadija kafin magriba su ka kammala, kula ya yi daidai da dawowar Bilal daga islamiyya, saida ta aje komai in da ya dace kafin ta shiga wanka ana kiran sallah, Bilal ma ko da ya dawo daga masallaci ta taimaka ma sa ya shirya dan tare za su tafi, Uwani ma saida ta sallame ta kafin suka fita tare ta aje gidan su suka wuce.


Hira sosai ta b'arke tsakanin malam da Bilal, dan jiki ya yi sauk'i sosai, anso sallamar shi amma likitocin sunce su na son jinin shi ya daidaita ne, dan da aka kawo shi jinin shi ya hau kad'an, misalin  takwas da rabi suna shirin tafiya sai ga Usman tare da Haseenah, sam ba ta nuna komai ba haka su ka musu sallama su ka tafiyar su.


Sun koma gida, kuma tun Khadija na zuba idon dawowar Usman har ta gaji, shirin da tayi dan tarbar shi ya wartsake bacci na surarta, su kam suna can sun wuce wajen cin abinci daga nan su ka wuce 'yar kasuwa ya mata siyayya mai yawon gaske, wai ta cancanci fiye da haka ma a cewar shi, haka suka je ya siyo mata ice crime da sauran kayan k'walam da mak'ulashe, *11:56* na dare suka d'auki hanyar komawa gida.


Khadija na jin k'arar bud'a gida ta fito farfajiyar, har saida ya wa mitar mazauni ya fito, da kan shi ya bud'ewa Haseenah ta fito kafin ya d'auko ledojin a hannun shi, tuni ta ankare da Khadija hakan ya sa tace "Beby ka kawo na taya ka d'auka mana."


Kallon ta ya yi yace "Ke lafiyar ki k'alau? Wannan kayan ne zan baki ki d'auka salon ki ja min salalan tsiya, ba dani ba wallahi, to ma miye anfani na idan ban hidimta mi ki ba."


Juyowar da zaiyi da nufin kallon gaban shi ya sauke ido akan Khadija da ta rik'e k'ugu da hannu d'aya, ajiyar zuciya ta sauke shi kam ko a jikin shi, dan har ga Allah ba ya jin wai ya yi ba daidai ba, sai ma d'aure fuska da ya yi yace "Malama ya dai? Har yanzu ba ki kwanta ba kamar ki na jiran mu."


Ganin Haseenah ta nufi b'angaren ta ko a kwalar rigar ta ya sa shima ya bi bayan ta, ita ma wucewa ta yi ta je falon shi ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun teburi ta na jiran shi, ai kam bai jima sosai ba ya shigo falon da alama wanka zai yi, kamar bai ganta ba haka ya wuce uwar d'akin shi ya fara cire kaya, ita ma bayan shi ta bi hannu ta kai da nufin kama mi shi ya yi saurin ja baya sosai yace "Nagode."


Ko wando bai cire ba ya wuce ban d'akin, ta na nan zaune har ya fito ya shirya duk ta na kallon shi ta rasa ma abinyi, juyowa ya yi zai fita yace "Idan kin gama kallon nawa na fita ni, zanyi kallo daga yanzu zuwa lokacin da zan kwanta ba na son takura."


Da sauri har da gudu ta k'arasa gaban shi ta rik'o hannun shi, za ta yi magana sai kuma ta kasa saboda yanda ya raba hannun ta da na shi, shi kam ta na rik'e hannun shi ya ji kamar ta zuba mi shi ruwan zafi a jiki, ba ta yi magana ba ya fice ya bar ta, falon ta biyo shi cikin rawar murya tace "A...a..abincin..ka..."


Da k'arfi ya mik'e daga zaman da ya yi kamar zai had'e ta cikin d'aga murya iya k'arfin shi yace "Ba na ci, nagode, dallah ki fitar min daga d'aki, zuciya ta tafasa take idan ina kallon ki, sam muryar ki babu dad'in ji kuma duk kin bi kin takura ni da zance kamar wata sabuwar rediyo (redio)."


Wani dogon tsaki ya ja yace "Haba, ni na rasa gane wannan jarabar." Kai tsaye d'akin Haseenah ya nufa ya na ci gaba da mita, ragwaf Khadija ta fad'a kan kujera ta fashe da kuka, har za ta d'aga sauti sai kuma ta kame bakin ta ta tashi ta koma na ta d'akin, har ta dasa wani sabon kukan sai kuma ta tuna maganar lahaifiyar ta da take fad'a mu su "Duk abin da ya yi zafi laganin shi Allah, ku rik'e Allah a cikin lamarin ku, ba shakka zai taimake ku dan ya na tare da ku."


Wannan maganar ce ta sa ta d'auro alwala ta shinfid'a sallaya ta d'auki Qur'ani ta fara karatu, saida ta raba dare kafin ta kabbara sallah a kowace sujuda ta na kaiwa ubangiji koken ta.


Usman kuma na shiga ko da ya sauke idon shi akan amaryar shi sai wani irin farin ciki da shauk'i ya rufe shi, sam ya manta da komai a kan shi haka ya so hayake ma haseenah, ita kam sam tsoro ya kamata dan haka ta k'i amince mi shi, da k'yar da sud'in goshi ta lallab'a shi ya koma d'akin shi, amma a ganin shi da ya ga Khadija gwara ya zauna shi kad'ai, haka ya sha baccin shi har kiran sallah asuba.



*Allah ka azurta mu da abokan zama na gari*

08/02/2020 à 23:04 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```


1. Mom teema Hakima

2. Yar baba ( Fatima Zara )

3. Momyn Dady

4. Chappa *Auntyn Khadi*

5. BILKISU Z. YA'U

6. Raheenah m Abbacar

7. Aishan Umma

8. Maman Labyb

9. Aunty Hawwer 

10. Hawwer Jidda

11. Alawiyya

12. Amina

13. Yagana Mousa

14.Rukayya

15. Maman souhailat

16. Ummu sultan

17. Ouma saadou

18. Rahilat

19. Azima *momyn Imane*

20. Mme Jamil

21. Ummi 1

22. Ummi 2

23. Nazeefa

24. Jamila

25. Maijiddah

26. Sadia magaji

27. Phartee shehu

28. Ummu halima

29. Halima Muhammad

30. Maman Tasleem

31. Jawahir Gombe

32. Fareedah Boube

33. Lubabatu Shehu shayi

34. Zeinab mai kano

35. Maman Ahmad

36. Firdaussi Shehu

37. Binta Umar

38. Preettyy Aeeshartyy

39. Rukayya Usman

40. Maryam Abdul Mumin

41. Salma Ibrahim

42. Hussy luv

43. Hafsat A.A

44. Jamila Musa

45. Choukriyya

46. Khadija Isa

47. Matar manya

48. Mamar Soja

49. Momyn Rasil

50. Meeynert

51. Mandiya😁

52. Habiba Bala


_Duk wanda ya ga sunan shi to ya na zuciyar *Samira* ne, sai dai wanda na manta kawai a matsayi na na yar adam ajiza._


_Bismillahir rahamanir rahim_



                   *21*



Abincin jiya ta fara d'aukewa kafin ta d'ora na karin kummalo, ba ta wani d'auki lokaci ba ta k'arasa shirya komai, saida ta shirya ta tashi Bilal shima ta taimaka ma sa ya shirya da sauri, karin kuma ta had'a mi shi ya ci ya k'oshi kafin ya nufi d'akin mahaifin shi, abun mamaki shine a al'adar Usman ba ya komawa bacci bayan sallah asuba, amma sai gashi yanzu rauni da sauyin da aka samu ya sa kasala ta rufe shi ya gagara abin da ya dace, haka ya koma ya kwanta baccin shi, doguwar riga kawai ya zura suka tafi ya kai shi, ko da ya dawo ya samu Khadija zaune a falon shi, da sauri ta mik'e ta kalle shi tace "Ina kwana."


"Lafiya." Ya fad'a ya na shirin wucewa, da ido ta bishi har ya wuce d'akin amarsu, tashin ta ya yi a bacci suka shiga wanka tare su ka fito, sun jima kafin su gama shiryawa su fito tare, Khadija na zaune in da ya barta tun farko, zaune su ka yi akan kujera ita kam sai ta kafe shi da ido da tsananin mamaki, jinkirin ne ya sa yasa Usman kallon ta ganin ba ta da niyyar zuba abincin ya sa yace "Abincin na ki ko na siyarwa ne? Sai ki mana baya ni ai."


Murmushi ta masa ta mik'e ta fara zubawa, shi ta fara zuba ma ta aje a gaban shi sannan ta zubawa Haseenah da ke ta kakkaryewa ta aje mata, ta na shirin zuba ma kan ta Haseenah ta ture faranti gefe ta mik'e tsaye ta kalle shi tace "Baby, zan koma d'aki na na kwanta, ba na jin sha'awar cin abincin nan kwata-kwata."


Kamar mazari haka ya fara tambayar ta "To me za ki ci idan ba ki ci abinci ba? Fad'a min me ki ke so ki ci to? Ai ba kya zauna da yunwa ba ki cutar da kan ki."


Cike da yatsina fuska tace "Umm, da ace zan samu indomie da na ji dad'i."


Kallon Khadija ya yi ya kula kallon ta yace "Abu mai sauk'i, bara yanzu a dafa mi ki, kije ki kwanta to." Kallon Khadija ya yi da ke tsaye yace "Am dan Allah na ce ba, ki taimaka mata ki d'ora mata, ina ganin kamar ba ta da lafiya ne fa, dan gaba d'aya yanayin ta ya canza."


Kallon shi Khadija ta yi ta na wani shegen murmushi mai kama da na mugunta tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, ban raina ka ba, kuma ka isa ka sani komai na yi maka, amma banda hidimar matar ka, gaskiya matsayi na bai taka wannan matakin ba, ka yi hak'uri idan na b'ata maka rai."


Ta na fad'a ta rufe kwanukan ta juya ta bar wajen, komai bai ce ba sai bayan Haseenah da ya bi da abincin ya lallab'a ta har ta ci, saida su ka gama kad'ai ya samu ya fita, saida ya shiga wajen Khadija ya same ta falo zaune, tsaye ya yi a kan ta ya ciro kud'i aljihun shi ya mik'o mata yace "Ba na da tabbacin za ki yi abin da na saka ki, amma dan Allah ki taimaka ki mana abinci mai yawa saboda ba zan dawo ci ba, zan aiko a d'auka saboda akwai bak'in da su ka zo mana."


Karb'a ta yi da hannu biyu tace "Zanyi farin ciki a lokacin da nake aikin nan, saboda hidimar ka ce."


Juyawa ya yi zai fita ta bishi da "Adawo lafiya."


"Allah ya sa." Ya fad'a a tsaurare.


Tun k'arfe d'aya Khadija ta kammala komai kamar ba ta yi ba, sai bayan sallah azahar Usman ya aiko aka d'auki manyan kwanukan tare da lemun da aka had'a na zallar abarba, ba jimawa ta kira shi tace su na so su koma ganin jikin Baba, cike da k'aguwa yace "Kuje, amma ki tabbatar tare ku ka tafi da Haseenah, dan ba na son raba kan nan da ku ke, sannan kar ki manta su na gida an sallame su."


Kafin ta yi magana ya datse kiran, dama a shirye take ita kam, Uwani ta kalla tace "Uwani ki je ki fad'awa Haseenah ta shirya yanzu za mu tafi ganin jikin Baba."


"To." Cewar Uwani ta nufi hanyar fita, jim kad'an ta dawo tace "Na fad'a mata tace ta na zuwa."


Kallo suke su na hira har sama da awa d'aya Haseenah ba ta fito ba, Khadija ta k'agu sosai dan haka ta kalli Uwani tace "Uwani dan Allah koma ki sake fad'a mata ta gaggauta, har uku ta na shirin yi mana a gida ba mu fita ba, ni kuma a wannan lokacin madafa ya kamata ace zan shiga."


Fita Uwani ta sake yi, amma ko da ta dawo sai cewa ta yi "Umman Bilal wallahi da na shiga na same ta kwance akan kujera da d'aurin k'irji, da na fad'a mata sai tace wai da zata shiga wanka, amma kula ba ta jin dad'in jikin ta kawai ki tafi za ta je daga baya."


Saida Khadija ta lumshe ido saboda haushi, mik'ewa ta yi ta kalli Bilal tace "Ka koma d'aki ka sako kayan makarantar ka daga nan saina aje ka, dan banga anfanin dawowar ba tunda mun riga da mun makara."


"To Mummy." Ya fad'a ya na nufa d'akin shi, bayan yan mintuna ya dawo da kayan makarantar shi da jakar shi a hannu, Khadija kuma bawa Uwani makullai tace "Ki rufe ko ina sai ki same ni a mota."


Karb'a ta yi ta kulle ko ina ta fita waje ta same su a k'ofar gida su na jiran ta, shiga ta yi su ka wuce suna tafe su na hira har suka isa, Uwani ce ta fito da kwanukan ita kuma ta na rik'e da jakar ta, haka suka shiga bayan sun gaisa suka zauna aka d'an tab'a hira, ana fara kiran sallah Khadija ta tashi su ka yi alwala su ka yi sallah, suna gamawa kuma suka musu sallama suka tafi saboda kar Bilal ya makara, haka suka aje shi sannan suka wuce gida kai tsaye, da shigar su ta hangi motar Usman, ba ta yi mamaki ba dan tasan wasu lokuta ya kan dawo ya yi wanka, su na shiga falon su suka ja birki ita da Uwani saboda ganin Usman zaune kai da gani kasan babu arziki ko mutunci cikin zaman, gabanta na fad'uwa ta k'arasa kusa da shi tace "Abban Bilal ashe ka dawo? Sannu da zuwa."


Uwani ya ma jan kallo yace "Kira min Haseenah."


Wucewa ta yi ba tace komai ba dan dama tun farko ya na mata kwarjini, Haseenah ta kira suka fito kusan a tare, tsaye duka su ka yi sai Uwani da ta fita farfajiyar gidan, tsaye ya mik'e yace "Nace ku tafi tare, amma me ya sa ki ka tafi ki ka barta?"


K'aramar ajiyar zuciya ta sauke ta kalli Haseenah tace "Na fad'a mata ai, da farko mun jira ta sai tace ba ta jin dad'i mu tafi kawai."


Kallon Haseenah ya yi yace "Ke ya ki ka fad'a min?"


Ko kallon Khadija ba ta yi ba ta kalle shi tace "Bansan za su tafi ba, fitar su kawai na gani daga gida, idan da ta fad'a min ai zan bisu tunda lafiya ta k'alau."


Kallon Khadija ya yi yace "Na d'auka zan iya fad'a mi ki kiji ashe ba haka bane, yanzu ina so naji raina ni ne ki ka yi ko me?"


Da mamaki ta kalli Haseenah ta kalle shi tace "Amma fa wann..."


"Amma me, ki na so ki nuna ba na da mahimmanci ne ko me? Zan fad'i yanda na ke so ayi a cikin gida amma ke kiyi gaban kan ki, wannan ai iskanci ne da d'aukar mutane yan iska, to ban makullin motar."


Da mamaki kawai ta ke kallon shi kafin tace "Makullin mota kuma?"


Zaro ido ya yi yace "Eh, ko taki ce? Ai ba yan uwan ki bane suka siya mi ki bare ki ji dad'in magana, ni ne na siya da kud'i saboda tunanin kin cancanta."


Hannu tasa a jaka ta fito da makullin ta mik'a mi shi, hannu ya zuro zai karb'a ta rik'e tace "Zan baka, amma ina so ka k'ara bincike akan lamarin nan, sanin kan ka ne wannan yarinyar ba ta kai na tsaya na mata k'arya ba, Uwani ita ce na aika ta mata magana, kuma Bilal ya na wajen."


Haseenah ce ta katse da cewa "Uwani? Ita ce tace mi ki ba zanje ba? K'arya take wallahi, wannan yarinyar fa munafuka ce wallahi."


A fysace Khadija ta kalle ta tace "Kar ki sake kiran Uwani munafuka dan ba ita ba ce, Uwani ba yau mu ke tare da ita ba, nafi sanin ta fiye da ke kamar yanda shi kan shi ya fi sanin ta fiya da ke."


Cike da rashin kunya tace "Idan an kira ta munafukar me za ki yi? Me ya sa ki ke son had'a yar aikin gidan nan da mu ne? Da alama wata rana ma cewa za ki yi matar shi ce ita ma."


"Kai." Ya daka musu tsawa, cikin b'acin rai yace "Akan wata banzar yar aiki ne za ku tsaya kuna musayar yawu? Ba na so, kowace ta wuce d'akin ta."


"Banza? Uwani ce banza?" Cewar Khadija ta na kallon shi, "Eh na fad'a, ko nima rashin kunyar za ki min?"


Rumgume hannaye Haseenah ta yi tace "To ai ba ka wuce ta maka ba tunda ka tab'a yar gold d'in ta, wallahi yarinyar can munafuka ce ta gidan gaba, ranar ma ai duk ita ta haddasa masifar da matar ka ta kusan k'ona ni da raina."


"Oho, hakane kenan?" K'ofar fita ya nufa ya na fad'in "To bara ki gani, yau zata bar gidan nan kuma na ga wanda ya isa ya hana tunda gida na ne."


Tun daga k'ofa ya fara kiran sunan Uwani, da sauri ta matso dan ba nisa ta yi sosai ba, Khadija ma bayan shi ta biyo ta na fad'in "Dan girman Allah Abban Bilal kar ka yi haka, ka k'yale yarinyar nan, in Allah ya yarda babu abin da zai sake faruwa da za ka ji sunan Uwani a ciki."


Ko sauraren ta baiyi ba saida ya tsaya gaban Uwani ya kalle ta yace "Ke, na fahimci zaman ki a gidan nan ba zai yiwu ba saboda matsalar da ake samu, dan haka karb'i nan." Ya fad'a ya na fito da kud'i aljihun shi masu yawan gaske da baisan ko nawa ne ba ya mik'a mata yace "Ki je na kore ki, ba na son sake ganin ki a gidan nan, kinji ko?"


Ruwa ne ya cika idon Uwani ta na kallon Khadija, ganin ta k'i amsar kud'in ya sa ya janyo hannun ta ya damk'a mata ya na fad'in "Karb'i na ce ko."


Juyawa ya yi ya koma ciki sai Khadija ta dafa ta tace "Ki yi hak'uri Uwani, wannan ita ce jarabawa ta a game da k'ara auren Usman, kije Uwani, ban ji dad'in korar ki da ya yi ba, amma dai hakan ya sa hankali na ya kwanta, dan a yanda ya ke jin kansa yanzu zai iya wulak'anta ni a gaban koma waye, wanda ni kuma ba zan so hakan ba."


Kuka sosai Uwani keyi da k'yar Khadija ta rarrashe ta ta juya ta tafi, falo ta koma ta same shi tsaye da alama ita yake jira, makullin motar ya nuna mata yace "Daga yau motar nan ta zama ta duka yan gida, zan samo mu ku dreba da zai dinga kai ku duk in da za ku je, sannan daga yau ban yarda wata ta fita ta bar d'aya ba in dai har fita ce ta dangi na data shafe ni, wannan hukunci na ne."


Zai bud'a k'ofar falon shi dake falon ta ya wuce ta tare gaban shi ta na kallon k'wayar idon shi tace "Abban Bilal wane laifi na yi ma ka? Ka fad'a min dan Allah na baka hak'uri, wallahi tallahi ba zan juri wannan sabon yanayin ba, ka sani kai ma ba zan iya ba ko kad'an."


Lumshe ido ya yi saboda ganin fitowar hawayen ta, amma saboda tasirin sihiri sai kawai ya basar yace "Ba zan d'auki hukuncin da ya dace ba dole sai kin min wani laifi? Ba komai to."


Shigewa ya yi ya barta tsaye, da k'yar ta samu ta shiga d'aki ta cire kayan jikin ta ta wuce madafa, yau girki kala d'aya ta yi saboda yanayin da take ciki.


Ba wani shiri ta yi ba kuma tare da Bilal suka ci abinci, sai kusan goma ya shigo gidan, kasancewar Bilal baiyi bacci ba ya sa suka zauna falon shi suna kallo, abinci ya ci kafin ya shiga yi wa Haseenah saida safe, da k'yar ya baro d'akin ta dan baya son rabuwa da ita, Khadija ma d'aki ta raka Bilal ya kwanta kafin ta saka kayan bacci ta nufi d'akin shi, ta na kwance ya shigo ya wuce ban d'aki, ya d'an jima kafin ya fito ta na kallo har ya canza kaya, kashe wuta ya yi kafin ya kwanta gefen ta kuma nesa da ita ya juya mata baya, ta na ganin haka ta d'auki gilashin ta gefen ta saka ta janyo wata ma'ajiya ta d'auki Qur'ani ta fara karatu, Usman na so ya yi bacci amma fitinar sha'awar da ta taso mi shi saboda wasan da su ka yi da Haseenah ya sa ya kasa baccin, a k'alla awa d'aya su na haka ita ta na karatu shi ya na juye juye da matsar mara, a zabure ya juyo gefen Khadija ya rarumota ya danna bakin shi cikin nata, cikin dubara ta samu ta aje Qur'anin hannun ta...


Tabbas sihiri gaskiya ne kuma ya na iya kama kowa, Usman da ke bala'in jin dad'in kasancewa da Khadija a kowane lokaci, matar da take gamsar da shi fiye da tunanin mai tunani, amma yau ya kusanceta ba dan ya na so ba sai dan sauke abin da ke damun shi, da kuma *tsananin rabo*,  da k'yar ya iya hak'ura ya kai bakin gab'a saboda ji ya ke kamar a cikin yaji ne ya ke link'aya da kayan shi, ta wani b'angaren kuma kamar a cikin tab'o ne ya jefa ta haka ya ke ji, babu wani dad'i da ya ji bare ayi maganar gamsuwa, gaba d'aya jin ta ya yi a k'afe babu ruwa kamar tabkin da ya tsotse, wanka ya shiga ya fito ya sake kwantawa ya juya mata baya, tsakin da ya yi ne ya sa Khadija juyawa ta kalle shi, tashi ta yi ita ma ta yi wanka ta dawo ta ci gaba da karatun ta.


Ana kiran sallah farko ya fita, ko Bilal bai waiwaya ba yau ya tafi masallaci, ya na dawowa kuma wajen Haseenah ya wuce, ko tashi ba ta yi ba ita kam ta na bacci, rufe d'akin ya yi ya zame kayan jikin shi a hankali ya shiga cikin zanin rufar, kamar a mafarki Haseenah ta ji wata wawar cakuma da ya wa k'irjin ta d'aya da hannu d'aya a baki, ta so raba kan ta da shi amma bai bata damar hakan ba saboda rik'on gaske ya mata ba kad'an ba, ya na jefa k'wallon sa a raga ya sauke wata arniyar ajiyar zuciya, kwance ya yi akan k'irjin ta ya yi shiru dan abin da ya ke ji ma kamar zai tafi da numfashin shi, saida ya d'auki kusan minti biyu a haka kafin ya fara aiki da gaske, irin sambatu da surutan da ya ke da ihu kamar wani zararre...Hum yau fa suruki na kad'an b'ata min rai gaskiya,😎 ka kiyaye ba na son haka.


Kusan awa d'aya ya d'auka kafin ya rabu da ita ya shiga ya yi wanka ya fito, kayan shi ya mayar a jikin kafin ya kalli Haseenah da ta had'a kai da gwiwa ta na kallon tace "Yanzu abin da ka yi ka kyauta? Yau fa ba kwana ne bane, me ka ke so a kalle mu dan Allah?"


Cike da nuna rashin damuwa yace "Ke ni dallah rabu dani, to zaunawa zanyi na kashe kai na bayan ina da maganin a cikin gida na, can babu abin da ke akwai sai kayan haushi da k'yama, to ya ki ke so na yi?"


Wani kallo ta masa tace "Ka na so ka ce babu abin da ka ke ji acan sai anan?"


Da sauri ya matso kusan ta ya rik'e hannun ta yace "Dan Allah kar ki fad'awa kowa maganar nan, amma wallahi matar can ba ta da dad'i, yanda ki ka san mutum ya fad'a a kwata haka take, ita fa ko miya marar kayan d'and'ano ta fita armashi."


Ba ta san lokacin da ta fashe da dariya ba saboda mugunta, shi kam rufe mata baki ya yi yace "Yanzu fad'a min me ki ke so na baki a matsayin tukuici? Wallahi na ji dad'in kasancewar mu yanzun nan." Ya k'arashe da sumbatar wuyan ta.


Cikin rik'e dariya tace "Ba na son komai miji na, tunda ma ka yi farin ciki hakan ya ishe ni."


Mik'ewa ya yi yace "Nagode matata, ni zan koma can na canza kaya, amma ki tashi ki yi wanka yanzu sai ki fito mu ci abinci."


Cike da makirci tace "Toh."


Ya na fita ta sauka da gaggawa ta shiga ta yi wanka ta fito ta yi sallah, riga ta saka iya gwiwa yar kanti ta fito da ita kai babu d'an kwali, lokacin Bilal har ya shirya Bilyamin ya d'auke shi sun tafi, Usman na zaune akan kujera Khadija na zuba masa abinci, yanda ya d'aure fuska babu annuri ne ya sa ta share shi ita ma, mayar da kallon shi ya yi ga Haseenah da ta fito ta na karkad'e gashin ta cikin takon jan hankali, kallon ta Khadija ta yi har ta zauna akan kujera, da wani shegen murmushi Usman yace mata "Sannu da fitowa."


Turo baki ta yi cikin shagwab'a tace "Ba zan sake ma ka magana ba sai nan da wata d'aya."


"Me?" Ya fad'a da zaro ido, d'orawa ya yi da "Haba amarya rufa min asiri mana, ina zan saka kai na to idan ki ka daina min magana, kinsan fa ke ce haske kuma fitilar zuciya ta dama gidan nan ba ki d'aya."


Sake turo baki ta yi ta kawar da kai tace "Ni ka k'yale ni kawai."


"To wai me na yi ma da za'a min wannan hukuncin?"


Kallon Khadija ya yi saboda aje farantin abinci da ta yi gaban shi, ita ma zubawa ta yi ta zauna ta fara tsakura ta na satar kallon su, amma zuciyar ta ta kai k'arshe wajen k'una, cike da shagwab'a tace "Ka ma manta kenan? Haka kawai ina bacci na za ka zo ka tara min gajiya, yanzu gashi duk jiki na ciwo ya ke, kuma saida na fad'a ma ka kar ka yi amma ka k'i saurara ta."


Hannu ya sa ya na shafa wuyan shi cikin alamun rashin gaskiya, satar kallon Khadija ya yi wacce ta k'i d'ago kai saboda hawayen da ke son taho mata, dan ya kawar da zancen ya sa ya kalle ta yace "Ba ki zuba mata abincin ba ita."


Wani jan kallo ta mi shi tace "Au! Wai ni ce ma zan zuba mata? To ai na ga duka yau kwanan mu ne ni da ita, me zai hana ta zuba da kan ta ko kuma ka zuba mata."


Had'e rai ya yi yace "Ke me ki ke nufi ne? Ba na son maganar banza fa kinji ko, daga k'aramar magana za ki wani tasowa mutane, zuciyar ki ta raya mi ki k'arya da gaskiya kawai sai ki zauna akai."


Zunbur ta mik'e tace "Au! Wai zuciya ta ma ce ta raya min kenan? To kamar yanda ba ka son maganar banza haka nima, wallahi Abban Bilal ka ji tsoron Allah kasan cewa za ka mutu."


Maida kallon ga tayi ga Haseenah tace "Ke kuma ki sani duk rayuwar da aka ginata babu Allah a ciki wallahi k'arshen ta munin ta ya na bayar da mamaki, Allah ma shaida ne ban rik'e ki a zuciya ta ba ko kad'an, na so na zauna lafiya da ke mu taru mu farantawa mijin mu, amma na fahimci kin biyo abun ta bayan gida saboda cimma burin ki a kai na, ki sani Haseenah wallahi tallahi da ace zan yi dan na raba ki da Usman, to ina da bokan da idan har ya shiga tsakanin ki da shi wallahi tallahi ba ke ba duk wanda ya zauna tare da ke ma sai ya tsane shi, amma tuna akwai Allah kuma zan mutu ya sa na d'aga mi ki k'afa, amma muje zuwa."


Ta na fad'a ta juya ta koma falon ta, janyo Haseenah ya yi ya d'ora a cinyar shi ya fara bata abincin ya na fad'in "Ki shirya kayan ki, ina tunanin tafiya da ke Dubai a satin nan, dan ba zan yarda na barki tare da matar nan ba a gidan nan."


Duk da a zuciyar ta akwai abin da taji shed'an na raya mata, amma sai ta nuna ta yi murna ta hanyar cewa "Dubai? Ni? Wayyo Allah yaushe? Da gaske ka ke?"


"Um, ki shirya kawai, ina tunanin tafiya nan da kwana biyu zuwa uku."


Haka suka gama cin abincin ya fita ita kuma ta koma d'aki, ta jima ta na waya da Mariya ta na fad'a mata canjin da aka samu, amma ba ta fad'a mata abin da ta ke shirin aikatawa ba har suka yi sallama, su na gamawa Haseenah ta shirya tsaf ta fito, kai tsayz k'ofar fita ta nufa mai gadi ya bud'e mata k'ofa, a lokacin Khadija na madafa ta tsinkaye ta ta fice, aikin gaban ta ta ci gaba da yi ba tare da tunanin komai ba, har ta gama aiki da duk abin da ta ke yi, ta na zaune falo tare da Bilal Usman ya shigo, ta yi mamakin ganin shi a lokacin sosai, shi ma kuma ya na ta kiran Haseenah ne ta k'i d'aga wayar shi duk abin duniya ya dame shi, hakan ya sa ya zo gidan kuma ya na nufa b'angaren ta ya ga k'ofar rufe alamar ba ta nan, shi ya sa ya shigo wajen Khadija, tsaye ya yi a kan ta yace "Na ga yarinyar nan ba ta nan ko kinsan in da ta tafi?"


Wani murmushin ta yi tace "Ni kuma ina zan san in da ta tafi? Ko gaishe ni ka ga ta na yi bare na samu kimar da za ta fad'a min za ta fita."


Wani dogon tsaki ya yi ya sake kara wayar shi a kunne, ta na kururuwa wayar amma ta k'i d'auka, sake maida kiran ya yi hakan ya sa mahaifin Haseenahr d'auka, dama ko da ta je gida da kuka ta isa, ta na zuwa ta k'ara fashewa da kuka wai ita wallahi ta gama auren gidan Usman, anyi tabbaya amma ta k'i fad'a saida aka kira Baban ta ya zo sannan tace "Ni kawai ba zan koma gidan shi ba, wallahi ba na bacci a cikin dare sai a dinga bani tsoro, yanzu kuma kawai..." Kuma sai ta yi shiru, mahaifin ta ne yace "Kawai me?"


Kallon shi ta yi da ido tsakar kai tace "Ba komai, ni kawai ba zan koma ba."


Ta na ganin kiran Usman a waya sai ta ture wayar wai ko sunan ma ba ta son gani, hakan ya sa iyayen jikin su yin sanyi su ka fara tunanin shiga baga ne na kishiya kawai, shine yanzu da ya kira baban ta ya d'auka, saida su ka gaisa cikin mutumci kafin yace ya zo ya same shi gida ya na son ganin shi, ba musu yace ya na nan tafe yanzun, dan shima idan bai ganta ba ba zai iya salun nutsuwa ba, Khadija na kallo ya fita daga gidan da sauri.



Ya na zuwa kam suka tattauna sosai in da Haseenah ke cewa kawai ya sake ta ba za ta koma ba, shi kam yace ba zai iya rayuwa ba yanzun babu ita, dan haka dai aka sasanta mahaifin ta yace ta je gida zai samar mata magani, haka ya d'auko ta suka dawo gida bayan ya bawa Baban ta kud'i a fara mata magani,  Khadija na kallo suka dawo suka nufi b'angaren ta, ya jima ya na bata magana da rarrashi kafin ya fita, a gida ma suna tafiya mahaifin ta ya fito ya hau moton shi, bai zame ko ina ba sai *pharmacie salfiya* cibiyar magunguna na addini, da ya fad'a mu su matsalar sun zo ya zo da mara lafiyar da suga yanayin jikin ta, amma tunda ya riga ya zo sai suka bashi wanda ya dace da abin da ya fad'a, amma sunce in har ba ta daina ba to su kawo ta wajen su dan su duba ta, ya na barin nan gidan Haseenah ya wuce kai tsaye, dan suna so su d'auki matakin tunda wuri, Khadija na ganin shigowar shi amma ba ta kawo komai a ran ta ba dan bata nufin kowa da sharri, har falon Haseenah ya ke zaune ya na fad'a mata yanda za ta yi anfani da su, saida ya gama kafin ya bar gidan, Haseenah na ganin fitar shi ta kai magungunan d'aki ta aje, d'ibar wasu ta yi daga cikin wanda za ta yi anfani da su yanzun ta zubar.


Usman kuma na barin nan gidan su ya nufa, Hajia ya fad'a ma halin da ake ciki, ta jinjina al'amarin tare da dogon nazari akai, sai dai zuciyar ta ta kasa yarda cewa Khadija za ta iya cutar da ita, dan da za ta hana ta zaman gidan ai da bata ma barta ta shigo ba, amma dai "Allahu a'alam." Cewar Hajiar, ya na fita Aziza ta taso maganar dan ta na waje ta ke jin wasu maganganun, cike da damuwa Hajia ta fad'a mata yanda aka yi, ke Aziza ki na fitowa sai ki ka kira Hassana ki ka fad'a mata, kafin ka ce kwabo maganar ta karad'e yan uwan mata ana ta caccakar Khadija da maganganun b'atanci.


Yamma na yi Haseenah ta shiga madafa ta d'ora girki, sai bayan magriba ta k'arasa ta yi wanka ta shirya, ko da ya shigo ya yi wanka ya sake kaya ya zauna wajen cin abinci, kallon shi ta yi tace "Bara na kira su aunty Khadija su zo mu ci abinci."


Da ido kawai ya bita har ta fita, jim kad'an su ka shigo tare da Bilal, Khadija ba wai ta shigo bane saboda ta na son cin abinci sai dan gudun matsala, akan cinyar sh ya zaunar da Bilal in da Haseenah ta fara zuba abincin, a faranti d'aya suka fara ci shi da Bilal, amma Bilal na kai lomar farko ya kalli Haseenah ba ko k'yabtawa, da k'yar ya samu ya aika lomar ta gangara cikin shi, Khadija da Usman ma na kai wa suka yi saurin furzo shi waje suna goge baki, haka ita ma Haseenah ta na sawa ta firzo ta na ta faman goge baki, Usman ne ya kalle ta yace "Haseenah me ye haka? Kin d'and'ana girkin nan kuwa kinji?"


A marairaice ta kalle shi tace "...


*Yasin na gaji.*

11/02/2020 à 18:31 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


_*H. UMAR*, mahaifin da ya fi na kowa, ina alfahari da kai Baba na, wannan sadaukarwa ce gare ka kai kad'ai, ka cancanci fiye da ita ma, ka huta ka ju dad'in ka, Allah ya k'ara girma da lafiya dattijon arzik'i, *kut.kut.kut.*😉 kaza._



```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                      *22*



"Wallahi bansan ya akayi gishirin nan ya yi yawa haka ba, ni fa lafiya k'alau na kammala girki na, kuma babu yanda za ayi na yi girki ban d'and'ana na ji yanda ya ke ba, sannan idan ka duba ai haka ba ta tab'a faruwa ba."


Satar kallon Khadija ya yi wacce ta kafe Haseenah da ido ta na murmushi dan ita ta fahimci me take nufi da abin da ta fad'a, girgiza kai ya yi yace "Shikenan kar ki damu, komai ya wuce."


Mik'ewa ta yi duk ta yi kalar tausayi tace "Ku yi hak'uri dan Allah, bara na samo mu ku ko soyayyen k'wai ne ku ci."


Da sauri ya katse ta da "A'a ki barshi kawai, tunda hakane ake so mu zauna, ki kawo mana madara gari da sugar  kawai sai mu had'a da farar shinkafar."


Haka kam akayi taje ta kawo ta zuba a kofofi ta had'a ma kowa, ta mik'owa Khadija ta mik'e tsaye tace "Gaskiya ba na cin wannan had'in da dare, zanje na samu wani abu na ci da zai d'auke ni a wannan daren."


Kai tsaye madafa ta nufa, ba ta ji wahalar d'aukar silallan naman dake cikin masuburbud'ar sanyi ba ta had'a sassauk'an miya mai kyau da dad'i, fitowa ta yi lokacin sai Bilal da Baban shi akan salon suna kallo ta zo gaban tebur d'in ta d'ibo sabuwar shinkafar ta zuba a faranti ta zuba miyar, Bilal ne ya juyo ya kalle ta yace "Mummy ni dai na k'oshi."


"Dama bance ka zo ka ci ba." Ta fad'a ta na kai lomar farko, hankali kwance ta kammala ta tashi tace wa su je su kwanta, kallon Usman ta yi tace "Saida safe."


"Saida safe." Ya amsa ya na shafa bayan Bilal, da ido ya bisu har suka b'acewa ganin shi, ya na ganin fitar su ya taso in da ta ci abinci, ya na bud'a k'aramin kwanon miyar ya lumshe ido, cokali ya sa ya d'auko tsokar nama ya jefa bakin shi, saida ya sake lumshe ido ya na taunawa ya na fad'in "Umm, umm."


Da sauri ya d'ebo shinkafar kad'an a wani faranti ya zuba miyar ya dinga turawa saboda gudun kar Haseenah ta riske shi, har ya gama bata fito ba dan haka ya same ta d'akin ta na ta shirin bacci, nan ya fara lulawa da ita wata duniyar, sunyi nisa sosai ya na neman gangara kawai ta raba kanta da shi ta sauko daga kan gadon, ya na kallon ta kamar wasa ta canza kayan jikin ta ta saka hijab, ba tare da ya taso ba yace "Lafiya dai? sallah za ki yi ne?"


Ko kallon shi ba ta yi ba ta nufi k'ofar fita, zaune ya tashi yace "Wai lafiya? Ina za ki je haka?"


"Gidan mu." Ta fad'a ta na fita daga d'akin, da sauri ya sauko shi ma ya zura doguwar riga ya fito, ko da ya fito har ta kai farfajiyar gidan, rik'o ta ya yi yace "Haba Haseenah, ina za ki je da daran nan haka?"


Kallon shi ta yi kamar za ta yi kuka tace "Ka yi hak'uri dan Allah ka barni na tafi gidan mu, wallahi ba zan iya kai safe gidan nan ba, ni kad'ai na san me na ke ji."


A tak'aice dai haka Usman ya yi juyin duniya Haseenah tace ba za ta kwana gidan nan ba, shi kuma a ganin shi abun kunya ne ya kai ta gidan su, a cikin daren nan ya kai ta gidan su wajen Hajia, sam abun bai wa iyayen dad'i ba haka su ka kwana suna jimami, shi ma da k'yar ya dawo gidan ya kwanta, sai dai ba wani bacci ya yi ba saboda Haseenah na nesa da shi, saida asuba da yaje ya tashi Bilal sun dawo daga masallaci ya ke ce ma Khadija "Kinsan yer uwar ki ba ta kwana gidan nan ba?"


Da mamaki ta kalle shi tace "Subhanallah, me ya faru da ita? Ta na ina to?"


Wani murmushin gefen labb'a ya yi yace "Kar ki damu, gari na k'arasa wayewa zanje na d'auko ta, Haseenah za ta zauna gidan nan kamar yanda ke ma ki ke zaune."


K'ala ba tace ba har ya fita, da kan ta ta had'a mu su abin kari suka karya kafin ya fita, daga nan gida ya yi lokacin magana ta gama kewaye dangi Haseenah ta kwana gidan surukanta saboda ba ta son kwana gidan mijin, wannan kuma ba komai bane sai sharrin Khadija da ke son korarta a gidan.


Ko da Usman ya je gidan ya samu iyayen Haseenah har sun zo suma, nan fa mahaifin ta ya nuna ba zai yarda a illata mi shi yarinya ba akan namiji, dab haka yace dole sai an kewaya Qur'ani a gidan, duk wanda ya cutar da wani to Qur'ani ne zai ci shi,😂 (tirk'sahi, Haseenah kin jawo bala'i), da k'yar mahaifin Usman ya rarrashe su ya basu hak'uri yace su bar komai a hannu shi zai d'auki mataki, saboda baya so cin zarafi ko mutumci ya fara shigowa lamarin, sun hak'ura amma sun ce dole a binciki gidan dan ga dukkan alama wani kafi ne a ciki da zai hana ta zama, sun yarda da hakan sosai dan haka ma suka ce zasu tura 'yan uwan Haseenah mata su je su duba.


Hassana da Husseina aka kira suka zo gidan, nan aka fad'a mu su abin da ya faru da wanda zai faru a gaba, gidan Usman suka nufa tare da Haseenah da ta yi shiru ta kasa magana.


Khadija na girkin rana a lokacin ta ga Mariya da kuma *Razina* sun shigo duk da ba ita ce aikin ba, cikin sakin fuska da mutumtawa suka gaisa sosai, ganin za su wuce ciki tace "Ina ga fa ba ta nan, ta fita ina jin."


Mariya ce tace "Eh mun sani, ta na nan ma zuwa yanzu."


"Ahan." Cewar Khadija ta ci gaba da aikin ta, ta na kusan gamawa kuma sai ga Haseenah tare da su Hassana, suma saida su ka gaisa kafin Khadija ta kalli Haseenah tace "Ke haka ake sai ku fita cikin dare babu wanda ya sani, saida safe ya ke fad'a min wai ba kya nan."


Kamar za ta yi kuka tace "Ki yi hak'uri dan Allah." Ta na fad'a ta wuce falon ta.


Kallon su Hassana ta yi tace "Ba ta da lafiya ne na ganta wani iri haka? Ko daga asibiti ku ke?"


Cikin d'age kai Hassana tace "Lafiyar ta lau." Ta na fad'a ita ma ta yi gaba sai Huseeina da ta bi bayan ta, su na shiga Hassana ta zauna kusa da Haseenah ta dafa ta tace "Haseenah, ki fad'a mana gaskiyar abin da matar nan take mi ki kinji?"


Girgiza kai ta yi tace "Ba komai."


"Kin tabbatar?" Cewar Mariya da suka zagaye su, shiru ta yi sai Hassana ce ta kalle su dukan su tace "Ku na ji ko, gaskiya dole a d'auki matakin kare yarinyar nan kafin ta cutar da ita, kunga fa yanzu nuna mana ta yi kamar ba ta san me ke faruwa ba, har da tambayar ko ba ta da lafiya ne kuma daga asibiti mu ke, dan haka Haseenah sai kinyi taka tsantsan sosai."


Husseina ce tace "Gaskiya wannan rashin tausayi da imani ya yi yawa, ace yarinya ko sati biyu ba ta cika ba amma ki na so ki fitar da ita daga gidan, wannan ai zalinci ne, shikenan fa so ta ke ta mayar da ita k'aramar bazawara."


"Haseenah ki na da ciki ne?" Da sauri ta kalli Razina da ta jefo mata tambayar, cikin rashin sani tace "Ban sani ba ni ma."


Hassana ce tace "To ko kin sani kar ki yarda ki bari ita ma ta sani, ko ki na ganin alamu kar ki bari ta gane tunda kinga ta fiki wayo, dan wallahi tasan da ciki jikin ki sai ta kusa kashe ki."


Mariya ce tace "Kisa fa ki ka ce?"


Cike da tabbatarwa tace "K'warai kuwa, ki na ganin ba ta iya wa ne? Wacce suka kwashe shekaru kullum da d'a k'waya d'aya, samun cikin Haseenah fa alama ce ta za ta fara hayayyafa gidan Usman, kinga kuwa dole a d'auki tsatsauran mataki."


"To Allah ya raba mu da sharrin wannan mata mu dai." Cewar Razina.


"Ameen." Su ka ji an amsa daga bakin k'ofa, wa za su gani in ba Khadija ba da kwanukan abinci tsaye, fik'i-fik'i su ka kama da ido cike da rashin gaskiya, cikin takon izza da isa ta k'araso in da suke ta aje kwanukan ta d'ago ta kalle su d'aya bayan d'aya, murmushi ta yi da ya k'ara mata kyau kafin tace "Ina rok'on Allah ya kare ku daga sharrin na kamar yanda ku ka yi fata, wani abu d'aya da na ke so ku gane shine, da ace ina kishi da Haseenah kuma haukan kishi, to wallahi tallahi da miji na bai ma kula ta ba bare har ta had'a kafad'a da ni, da ace za fitar da ita daga gidan nan bayan ma ta shigo wallahi da ba ma zan bari ta shigo ba, dan in ta shigo ai za ta iya yin alfahari da hakan, sannan za ta ga abin da yafi komai daraja a jikin miji na, za ta kwanta akan shinfid'a shi kamar yanda zan kwanta, to miye anfanin barin sai ta shigo sannan na fitar da ita? Ai ba ma za ta shigo ba wallahi da na so hakan, ku ji da kyau."


Ta fad'a ta na kallon su dukan su, ci gaba ta yi da cewa "Idan na yi niyyar mallakar Usman ta hanyar asiri ku sani ina da kud'in da zan iya biyan boka ko da na k'asar india ne, idan har na tashi mallakar Usman wallahi zan mi shi mallakar da har mahaifiyar shi ba za ta anfane shi bane, idan mallakar Usman zan mallake shi cikin awa d'aya tak, kuma na hargitsa duk wani lissafi na shi, idan har na mallake shi to sai ya kai matakin da ko bayan gida zai zaga sai ya nemi izini na kafin yaje ga buk'atar shi, ku a matsayin ku na 'yan uwan shi wallahi sai ku zubar da hawaye kafin Allah ya had'a ku da shi akan hanyar har ku gaisa, dan haka ku daina kallo na a matsayin wacce ta mallake shi har take k'ok'arin fitar da wannan yarinyar, ba alfahari ba, amma zan iya cewa Haseenah ba ta kai macen da zan iya kishi da ita ba har na had'a ta da boka ko malam, ko ke ba ki kai matsayin ba." Ta fad'a da nuna Mariya da yatsa, gyara tsayuwa ta yi ta na murmushi tace "Wannan." Ta nuna labb'an ta da yatsa, "Da kuma wannan." Ta kama duka nonuwan ta a hannu, "Sai kuma wannan." Ta k'arashe da nuna k'asan ta da yatsa sannan tace "Su kad'ai ne su ka mallaka min zuciyar Usman a hannu na, tabbas sihiri zai iya anfani a kan shi ta hanyar saka shi ya ci zarafi na, amma idan ki ka ce ya rufe idon shi sannan ya saurari zuciyar shi, to ko shakka ba na yi cewa sunan *Khadija* ne za ki ji ya fito a bakin shi."


Hannu tasa ta ciro gilashin ta ta bushe shi da baki kafin ta mayar ta kalle su Hassana da Husseina tace " *Ku daina wa kitse kallon rogo* idan ku ka aika shi baki zai fahimtar da ku asalin me ye shi."


Juyawa ta yi ta fice abinta ta na jujjuya k'ugu cikin k'arewa tafiyar da sai oga ake wa ita amma yau sun saka ta gwada mu su, har saida ta b'acewa ganin su Hassana ta sa k'afa ta ture kwanon tace "Kar wanda ya ci abincin, dan ba mu san me ta saka ba."


Husseina ce tace "Kinji shegiya, wai so take ta nuna babu abin da take, to ai ko da ki ka ganmu da hak'oran mu talatin ki ka gan mu, dan haka sai ki fad'awa kaji amma zabbi hira suke."


D'akin Haseenah suka shiga in da suka duba lungu da sak'o ba su ga wani abu ba, layar da mahaifin ta ya bayar Mariya ta taka kujera ta jefata bayan ma'ajiyar kaya (drower) ta kalli Haseenah tace "Ko da kin canza zaman kayan d'akin kar ki jefar da abin can ki sake mayar da shi, Baba ne yace a aje na tsari ne."


K'ala ba tace ba har Mariya ta sake d'aga katifar fa a b'angaren hannun dama ta aje wata layar tace "Duk halin da ake ciki kar ki sake ki aza kan ki ba b'angaren da layar nan take ba, kinji ko?"


Da kai kawai ta nuna ta ji, har suka gama aiki su na hira akan Khadija da abin da ya faru, haka suka gama ko sanin tafiyar su Khadija ba ta yi ba, Haseenah na ganin tafiyar su ta d'auke dula layoyin ta nasa su cikin shara, ana haka yamma ta yi ta karb'i girkin ta a hannun Khadija, yau ma saida ta kammala girkin ta d'auki d'an banza gishiri ta zuba ciki, ta gama shiryawa tsaf ta aje komai a muhallin shi.


Kamar jiya yau ma ba su iya cin abincin ba, haka su ka yi 'yan dubaru kowa ya bar wajen, sai dai ran Usman ya b'ace sosai, hakan ne ya sa lokacin da ya shiga yi mu su saida safe, Haseenah kuma da ke son sanin me zai faru ya sa ta biyo bayan shi, ya na shiga d'akin ta tsaya bakin k'ofa ta na sauraren su, ya samu Khadija d'akin ta kwance, fuska ba fara'a yace "Dan Allah zan rok'i alfarma a wajen ki."


Tashi ta yi zaune ta d'auki gilashin ta ta saka kafin tace "Alfarma kuma Abban Bilal, sanin kan ka ne kafi k'arfin kowace irin alfarma a waje na, fad'i kan ka tsaye insha Allahu zan ma ka idan da hali."


Saiwa ya gyara tsayuwa yace "Ba na son sake jin wani abu a cikin abinci idan 'yer uwar ki ta dafa, tunda na lura abun akwai almubazzaranci a ciki, kar fa ki manta kud'i na ke sawa ina siyo abincin nan, kar ku ganshi a zube kamar kayan banza dan an zube mu ku na shekara, ba ku tunanin akwai wanda na safe ma sai sun nemo? To ba na so daga yau, kar a sake kinji na fad'a mi ki."


Juyawa ya yi da fad'in "Saida safe." Da gudu Haseenah ta juya ta koma d'akin ta ta kwanta ta na haki, ya na fita Khadija ma shiru ta yi ta na tunani kafin daga bisani zuciyar ta ta hasko mata mafita ita ma, murmushi ta yi ta kwanta abinta bayan ta sake shafe jikinta da addu'a. 



Da safe ma haka Haseenah ta gama shirya abin kari sai dai a k'urarren lokaci, hakan ne ya janyo ta manta ba ta zuba komai a abincin ba, ba dan ta ji abinda ya fad'a ba sai dan ta manta, ta gama shiri za ta fito ya shigo d'akin cikin tsadaddiyar shadda bla (bleue) sai k'amshi ya ke, rumgume ta ya yi ya sumbace ta kafin ya d'ago ta daga jikin shi, hannu ya sa aljihu ya kamo hannun ta ya d'ora mata wani matashin akwati na sark'a, da mamaki ta ke kallon abun har ta bud'a, da kan shi ya d'auki sark'ar ya mak'ala mata a wuya, sannan ya cire mata yan kunnan da ta saka ya saka mata na sark'ar, hannu ta sa ta shafa tace "Kai, amma na ji dad'i sosai da kyautar nan, nagode." Ta fad'a ta na kallon shi, murmushi ya yi yace "Ba komai bane wannan, irin faranta min da ki ke ai kin wuce karb'ar sark'ar zinare."


Zaro ido ta yi dan sai yanzu tasan sark'ar dake wuyanta, murna fa ba'a magana wajen Haseenah ta dangwala sark'ar zinare a wuya, haka su ka fito ta na karairaya kamar ta karye, da kan ta ta zuba mu su abincin dan tuni Bilal ya na islamiyya, Khadija da ta fahimci takunta kamar dariya ma ta bata, dan ga dukkan alama yau ta fara saka sark'a mai tsada, tab'e baki ta yi a ran ta tace "Da alama ba ki san sark'a mai tsada ba ko a ido, dan da kin sani da yanzu kin kashe kan ki da ganin kusan kullum sune a wuya na."


Lafiya lau suka ci abinci su ka kammala, saida ya mik'e zai fita ya kalli Khadija yace "Nagode da alfarmar da ki ka min, sannan ki min message d'in abubuwan da ku ke buk'ata, anjima zan turo Bilyamin ya kawo mu ku."


Ita kam dariya ma ya bata dan haka ta mi shi wani murmushi mai shiga rai tace "Angama ranka shi dad'e."


Ya na fita ta mik'e zata koma d'akin ta, kallon Haseenah ta yi ta na murmushi tace "Sai kuma gashi yau gishiri bai shiga abincinki ba, ko ya akayi haka ta faru oho?"


Kafin ta yi magana ta shige ta barta nan, ta na shiga falon ta ta tura mi shi sak'on abubuwan da suka kusan k'arewa da wanda ma suka k'are, lokacin har Haseenah ta shiga girkin rana aka kawo kayan, Usman ma gida ya dawo cin abinci dan har ga Allah ba ya so ana kai mi shi abinci waje in dai girkin Haseenah, dan ya gama fahimta tafi k'warewa wajen iya dafa shinkafa da jar miya, yamma na yi kuma Khadija ta karb'i girki, ita ma saida ta gama girkin ta lafiyayye sai kawai ta d'auki sukari (sugar) ta zuba a ciki, tsaf ta kawo shi ta jera kamar abun k'warai, sai dai yau a shirye take duk wacce za ayi ayi a gidan, dan ta lura Haseenah ba zaman lafiya take nema da ita ba.


Zaune suke wajen cin abinci Khadija na zuba ma kowa abincin, k'amshin abincin ne ya sa Usman had'iyar yawu har ya riga kowa kaiwa a baki, rufe ido ya yi ya tauna ya kuma had'e, bud'e ido ya yi ya sauke akan Khadija da ke shirin kai loma a bakin ta, shiru ya yi ya na kallon kowa har suka kai bakin su suma, kasa had'ewa su ka yi suka furzar dan haka Khadija ta d'ago ta kalli Haseenah, murmushi ta mata cike da makirci tace "Ramawa ki ka yi kenan?"


Zazzare ido Haseenah ta yi ta kalli Usman da ya kafe ta da ido ya na kallo, cikin in'i'na tace "...



*Maganin biri karen maguzawa, waya fad'a mi ki barno gabas take.*

12/02/2020 à 21:57 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *23*



"Wallahi ba ni bace, babu abin da na saka a abincin nan."


Had'e fuska Khadija ta yi tace "Kinga Haseenah, ni da ke yanzu duk d'aya ne, tunda kin rama to komai ya wuce, kin fahimta."


Cikin b'acin rai Usman yace "Yanzu miye haka? Me ku ke son mayar da ni to? Ke koma miye ai laifin ki ne tunda ke ki ka fara, ki na babba amma ko tsaya d'aukar raini ga k'aramar k'anwar ki, mtssss."


Tsaye ta mik'e ta na kallon shi tace "Dakata Abban Bilal, ni nafi k'arfin na tsaya jawa kai na raini wajen wannan mutsitsiyar yarinyar, gata ka tambaye ta tsakani da Allah uban waye ya fara zuba gishiri ko sugar a abinci? Ita ce da kan ta, har ni za ta wa makirci, saboda ta baka ka kurb'a shine za ta dinga ja min magana a wajen ka ta hanyar lalata abincin da ta girka, me ta ke nufi da hakan? Tasan dole ni za'a zarga dama ba ita ba, shine ni ma na nuna mata mace ce ni kuma gaba na ke da ita ko a haihuwa."


Zata fice ya mik'e tsaye yace "Dawo nan."


Dawowa ta yi ta tsaya sai Haseenah da ta mik'e ta kalle shi tace "Wallahi k'arya ta ke min babu abin da na saka, kawai sharri ne ta ke so ta ja min, taya ma zan lalata abin da na girka da hannu na?"


Kusanta Khadija ta matso cikin b'acin rai ta nuna ta da hannu tace "Wallahi ki ka sake cewa ina mi ki k'arya sai na fitar mi ki da jini a baki, marar kunya kawai fitsararriya, ke har ni za ki kalla ki ce ina mi ki k'arya? Wace ce ke dan Allah da zan mi ki k'arya?"


Usman ma matsowa ya yi yace "Ta fad'a d'in k'arya ne, ko k'aryar ta mi ki ne ba ki aikata ba? To gata nan ki fitar mata jinin dan Allah, wallahi da na gaggauta d'aukar mataki a kan ki, kiji mace kai ki yi laifi kuma ki ce ba za'a mi ki magana ba, ke wace ce?"


Cikin tafasar zuci ta kalle shi tace "Ni ce ma macen? To ta mace maka k'ofar d'aki, kuma na fad'a wallahi ta sake cewa na mata k'arya sai na kife ta da mari kuma a gaban ka."


Ai fa abu ya yi k'amari, sai kawai Usman ya jawo Haseenah da k'arfi ya dawo da ita gaban Khadija yace "Ke fad'a mata ta yi k'arya na ga me za ta yi, kiji iskanci kai ki yi laifi kuma ki ce ba za'a mi ki magana ba, wacece ke da ki ka fi k'arfin a mi ki magana?"


Idon ta ne suka rufe ta kalli Haseenah tace "Ki fad'a idan ke yar halak ce."


Haseenah ta tabbatar babu abin da zai hana Khadija ta dake ta, dan haka ta koma gefen Usman ta na fad'in "Abban Bilal kaga, ni fa ba na son matsala, laifi ne ta aika ta kuma na yafe, dan haka kawai abar..."


Ba ta k'arasa maganar ba Khadija ta kife ta da mari, cikin hargagi ta shak'o wuyan ta tana fad'in "Wa ki ka yafewa? Ni wai ki ke cewa kin yafe wa? To bari ki gani idan na ci uban ki gobe ko kud'i aka baki ba za ki sake shiga harka ta ba."


Tuni Khadija ta yi fatali da ita a k'asa warwas, sosai ta shak'e wuyanta ta na jijjigata ta na fad'in "Za ki sake shiga harka ta, daga yau za ki sake rai na ni?"


Duk abin nan da ake Usman na ta k'ok'arin raba su amma Khadija ta rik'e ta sosai, saida ya sa k'arfi sosai ya rumgumo Khadija ya d'aga ta daga jikin Haseenah, jefar da ita ya yi gefe in da ya kaiwa Haseenah d'auki ya kamota ta tashi, kallonta ya ke duk ta fita hayyacinta ido sunyi waje saboda wahala, ganin haka ne ya sa Usman juyowa cikin b'acin rai ya kashe Khadija da mari, gilashin ta ne ya k'arasa fita ya fad'i, dafe kunci ta yi ta d'ago ta kalle shi, cikin tsananin hushi ya nuna ta da hannu yace "Wallahi yau sai kin tafi gidan ku, ba zan d'auki wannan iskancin ba, haka kawai saboda kifi yarinya k'arfi sai ki dinga mata cin kashin da ki ka ga dama, to ba zai yiwu ba, kawai kije gida sai na nemi ki."


Za ta yi magana Bilal ya sakaya hannun shi ta k'ugun ta ya na kallon Usman da ke rarrashin Haseenah ya nufi d'akin shi da ita, Bilal kam hannun ta ya kama yace "Mummy ki zo mu tafi, mu tafi gidan su Hajia kawai."


Sunkuyawa ya yi ya d'auko mata gilashin ta ya d'aga hannayen shi da nufin saka mata, b'acin rai ne ya saka ta fizgar gilashin ta karya shi gida biyu ta jefar, hanya ta kama da nufin komawa d'akin ta amma sai ta yi karo da kujera, hannun ta Bilal ya kama bai saki ba har saida ya kai ta d'akin ta, su na Bilal ya sake d'auko mata wani gilashin ya saka mata kafin yace "Mummy, meya sa Abba ya daina son ki yanzu?"


Kallon shi kawai ta yi ta mik'e ta d'auko akwatin ta ta zuba kaya, d'akin Bilal ta koma can ma ta had'o mi shi kayan shi kafin ta saka mayafi ta d'auki jakunkunan suka nufi k'ofar fita, a lokacin Haseenah ma sai kuka take ita wallahi gidan su za ta tafi kafin Khadija ta kashe ta, hakan ya sa lokacin da suka iso falon shi suka hangi Khadija da Bilal za su fita, da hanzari ya fito ya tare ta yace "Bilal d'ana ne, kuma ba da shi ki ka zo gidan nan ba, dan haka ki bar min yaro na."


Fuska a had'e tace "Ni ma zan tafi da shi ne saboda ko da na zo gidan tare na same ku."


Duk ya gane magana ce ta fad'a mi shi amma haka ya fizgo Bilal yace "Yana nan tare da ni, idan kuma da wanda ya isa ki aiko shi ya k'watar mi ki shi na gani."


Tab'e baki ta yi tace "Hum! Wa ma zan aiko ya k'watar min shi? Ai sai marar kunya irin ka."


Da yatsanshi ya nuna kan shi yace "Ni ne marar kunyar? Ni ki ke fad'awa haka Khadija?"


"An fad'a, da abin da za ka yi ne? Mugu azzalumi, ni dama nasan tunda ka ce za ka k'ara aure nasan abin da za ayi kenan, aikin banza kawai."


Da sauri Bilal ya tsaya tsakiyar su cikin d'aga murya yace "Abba."


Kallon shi ya yi ya d'an shafa kan shi, kamar zaiyi kuka yace "Abba nasha ganin ku kuna rigima akan abubuwa dayawa, amma ban tab'a ganin ku a irin wannan yanayin ba."


Hannun shi ya kama su ka nufi komawa cikin gidan, juyowa yaron ya yi ya na kallon mahaifiyar shi haka ita ma shi ta ke kallo, saida ta ga shigewar su ta juya ita ma dan ba zata tsaya rok'on shi akan Bilal ba, tunda ta haiho shi dai ai ta san ba zai raba ta da shi ba, mai gadi ta barwa kayan Bilal ta fice daga gidan ta hau adaidaita, kai tsaye kuma gida aka aje ta ta shiga ciki cike da kunya da kuma tafasar zuci, kamar yanda har yanzu gidan su ba su daina al'adarsu ba ta taruwa falon mahaifiyar su haka ma yau, da sallama ta shiga duk da taji hayaniyar su ba lallai ta bari su ji ba, ai kuwa ba su ji ba har saida ta shigo d'akin ta aje jakar ta k'ofar d'akin, kowa mamaki ne ya kama shi in da ake fad'in "Khadija, ke ce a wannan daren?"


Ashir ne ya d'ora da "Lafiya dai ko auta? Daga ina ki ke haka k'arfe goman dare?"


Saida ta k'are kallonsu duka taga yan uwan ta ne kafin ta k'arasa shiga ta je gaban Mama ta zauna kanta k'asa, Mama ce ta fara dafa ta tace "Khadija, lafiya na gan ki haka? Wani abu ne ya faru?"


Cikin k'unar zuci tace "Usman ne yace na zo gida sai ya neme ni, Bilal ma na tare da shi."


Mansur ne yace "To me ya sa? Me ki ka mi shi haka da ya d'auki wannan matakin."


Kallon shi ta yi tace "Saboda amaryar shi mana, saboda munyi fad'a da amaryar shi shine yace na taho gida, kuma wallahi ba zan koma gidan shi ba tunda abun shi akwai rashin mutumci, gwara su zauna shi da ita har duniya ta tashi."


A hankali Habeeb ya sa hannun shi ya shafi fuskar ta yace "Yatsu ne fa akan kumatunta, marin ki ya yi?" Ya tambaye ta, saboda idon ta sun rufe ya sa tace "Eh mana, bayan mari ma wace magana ce bai fad'a min ba."


"Mari kuma?" Cewar Ashir ya na sake juyo da fuskar ta, Naseer ne ya katse shi da cewa "Ai kuwa Usman bai nemi zaman lafiya ba, yanzu saboda wata shegiyar yarinya zai mare ki, bari su ga yanda ake rashin mutumci kam."


Mama ce ta katse shi da cewa "Kai miye haka? Wai me ya sa ku ke haka? Me ya sa kuke son mantawa da baya?"


Shirun da su ka yi ne ya sa Mama cewa "Shikenan ita tafi k'arfin a b'ata ran ta kenan? Karfa ku manta shekaru suka yi a tare, shine yanzu daga yar k'aramar matsala za ku wani fara maganar rashin mutumci, to ba na so kunji na fad'a mu ku, kuma ma ita ta fad'a mu ku gaskiyar abin da ya faru? Ita ba babba bace ba? Meya hana ta yi hak'uri da duk abin da ta gani ko ta ji? Ai dama na fad'a mi ki dole sai kin kau da kai musamman yanzu da suke kan ganiyar cin amarcin su, zai iya yin komai saboda giyar da ya ke kurb'a."


Cikin rashin jin dad'i Bashir yace "Amma kuma Hajia har da duka? Koma me ya faru ai ya nutsu ya san me yake, amma tab'a lafiyar ta gaskiya fa ba abin da za mu iya jura bane."


Cikin hushi Habeeb yace "To ni abin da yafi k'ona min rai shine wai akan wata amarya, to k'ara aure hauka ne da zai kwance mi shi kai, gaskiya har da iskanci."


Naseer ne yace " Wallahi magana zan masa, dan ba zai mare ta a banza ba, in ba haka ba kuma to fa abubuwa marasa dad'i ne za su fara faruwa tsakani wanda basu faru ba a baya."


Cikin nutsuwa Ashir yace "Kunga ku kwantar da hankalin ku, yanzu dai ba yace ta zo ba har saiya neme ta? To ai sai mu jira shi har ya neme ta kamar yanda yace, kunga sai muyi magana yanda ya kamata."


"Ni ko ya zo ma ba zan koma ba, Usman ya gama tozartani a gaban d'ana da matar shi, gaba d'aya nunawa ya ke kamar ba mu tab'a zaman mutumci da shi ba, dan haka ko ya zo ma babu in da zanje."


Ta na gama maganar ta ta mik'e ta nufi tsohon d'akin ta da tasan dama nan za ta sauka, Mama ma mik'ewa ta yi ta lek'o k'ofar d'akin ta d'auki jakar ta ta kai mata d'akin kafin ta fito, yan uwan kam sun jima su na tattaunawa dan ransu ya b'ace sosai, in da Khadija ma sam kasa bacci ta yi a daren saboda tunanin sauyin rayuwa, mutumin da ko tafiya zaiyi wacce ta zama dole da k'yar ya ke iya rabuwa da ita, wasu lokuta kuma idan da sarari tare sukan tafi duk in da zaije, ko suje da yaron su ko kuma su bar shi su tafi, amma yau shine ya kore ta daga gidan shi wai saiya neme ta, k'wafa ta yi tare da gyara kwanciya a ran ta tace "Wallahi ba zan koma ba sai ya gane kurensa, har ni nayi kama da macen da zai ce jeki saina neme ki." Wata k'wafar ta sake yi cikin b'acin rai.



A wajen.su Usman kuma da k'yar ya rarrashi Haseenah ta hak'ura da taga Khadija ta tafi, ko da ya kwantar da Bilal ya dawo ya dinga mata abubuwa kamar tsohon bazawari, ita kam har kunya ma ya fara bata, haka dai suka kasance har gari ya waye.


Kasancewar babu karatu a ranar ya sa Bilal shiryawa ya yi zaune a falon mahaifiyar shi ya na kallo, haka yake zaune wurin nan yunwa na gwagwuyar mi shi ciki amma babu yanda zaiyi, d'akin mahaifiyar shine ke da abubuwan ci kuma a rufe yake, har saida ya kai ya fito wajen mai gadi ya zauna ya na kallon hanya, lokacin ne Usman ya gamo shiriritar sa ya fito neman Bilal, ganin shi tare da mai gadi ya sa ya kira shi suka koma ciki, tare suka karya kumallo ya tashi zai fita, kallon shi Bilal ya yi yace "Abba dan Allah ka tafi da ni wajen Mummy."


Cikin d'aure fuska yace "Ni na fad'a ma ka wajen ta zanje?"


A hankali ya girgiza kai, ganin ya juya zai fita ya sa shi k'ara cewa "To Abba ka tafi da ni sai ka aje ni wajen Hajia."


Cikin hassala ya juyo yace "Wai me ya sa dole sai na tafi da kai? Kai ba za ka iya zama gida ba idan ba karatu? To ba can wajen zanyi ba ka zauna tare da Mamar ka."


Kallon Haseenah Bilal ya yi kamar yanda Baban shi ya nuna mi shi ita da hannu, idon shi ne suka cika da hawaye ya sunne kai k'asa, Haseenah ce tace "Kaga dan Allah, ba na son neman magana ni, in har ba zai zauna ba saboda ya na ganin cinye shi zanyi dan Allah ka tafi da shi, dan ba zai yiwu yaro da gidan ubanshi ba a same ni daga ni sai shi a gida ya zama kamar wani maraya, dan gashi tun yanzu ya na nunawa a gaban ka, in ba ma iskanci ba ni d'in bak'uwar ka ce?"


Duk da hararan shi da take amma baisa Usman jin wani abu ba ko kad'an, hakan ne ya sa ma ya nuna Bilal da yatsa yace "Kar ma kace za ka fara min wannan nunkufarcin a gida wallahi, dan ba za ka ji dad'i ba, kuma a gidan za ka zauna kai da ita naga wanda ya isa ya hana."


Hannu ya sa aljihu ya matso kusan shi yace "Ka saki ranka kaji ko, idan zan dawo zan siyo maka abun mamaki."


Kai kawai ya d'an d'aga mi shi alamar to, fita ya yi Haseenah na ganin haka ta kalle shi tace "To d'an masu gida, maza tashi ka d'auke kwanukan nan ka wanke su, dan na lura kai ba'a morar ka a gidan nan."


Hawayen da yaron ke rik'ewa ne suka taho mi shi, mik'ewa ya yi ya d'auki farantan ya nufi madafa da su, ya kai madafar zai bud'a k'ofar ya rasa ya zaiyi, cikin dubara ya zura hannu zai bud'e sai kuwa wani faranti ya fad'o k'asa ji kake "tatssssssss."


Da gudu gudu Haseenah ta taso ta fito waje ta na fad'in "Ka zubar halan? Saboda bak'in hali, dan na saka aiki shine za ka fasa min kaya."


Ta na zuwa ta kalli farantin da ke k'asa ta kalli Bilal da ya kafe ta da ido cike da tsoro, cikin jin haushi da mugunta ta d'aga hannu ta d'auke da mari ta na fad'in "Dan uban ka kai musakin ina ne? Uban ka ne ya siya min da za ka fasa min kaya?"


Kamar saukar aradu taji daga bayan ta ance "Sai dai uban ki wallahi ba na shi uban ba, 'yar matsiyata da ba ki gaji arzik'i ba, talaka 'yar talakawa, wato an samu wuri ko?"


😂😂😂😂 _Bala'i da d'umi d'umin shi, ni kam waye wannan? A cikin yan biyar wa ya fi zafin zuciya? Ku tayani tunani mana mutane na._😉

13/02/2020 à 13:10 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *24*




Tunda Haseenah ta ga Hajia Turai gaban ta ya fad'i, hak'ik'a ta tsorata sosai dan Hajia Turai irin mutanen nan ne da kana ganinsu kaga zubin rashin mutumci da masifa a tare da su, riga da siket ne jikin ta na atamfa sun kamata sosai, sai siririn gyalen da ta d'ora a kafad'a d'aya ta k'araso wajen su Bilal d'in, ido waje ta kalle ta tace "Ke yanzu akan wannan banzan farantin ne har za ki tsaya ki na zagin shi, miye wannan d'in? Ke yanzu in ba halin tsiya ba me akayi akayi wannan banzan farantin da ake siyarwa dala tamanin, shine da ba ki da mutumci har za ki tsaya ki na wani zagin shi, ke kinsan waye wannan yaron kuwa? To Bilal da ki ke gani kamar d'an ciki na haka na d'auke shi, domin kuwa uwar shi ta min abin da ba zan tab'a mantawa ba har abada, kar ki ce za ki saka k'afar wando d'aya da Khadija, dan wallahi ki na sakawa fatar jikin ki ce zata yaye ta bar ki da kunya, Bilal kuma ya zama dole ki zauna da shi dan gidan uban shine nan d'in, yarima ne a fadar mahaifin shi dan haka ya zama dole mai son ya zauna da sarki ya so yarima."


Gyara tsayuwa ta yi har da wani jijjiga ta nuna ta da yatsa tace "Wallahi tun ranar da na ganki nasan sai an samu munafurci a k'ugun ki, bansan irin zaman da ku ke ba dan har yanzu ba mu zauna da Khadija ba, amma dai tabbas nasan akwai matsala a gidan nan, to ki shirya da kyau yarinya dan zuwa na na gaba gidan nan ba lallai ya mi ki kyau ba, wallahi tallahi kinci sa'a akwai in da zanje yanzu cikin gaggawa, ba dan haka ba da sai na kwab'e rigata na yi zigidir kafin in ci ubanki, dan na lura ke 'yar marasa mutumci ce."


Kallon Bilal ta yi ta fito da chocolat daga jakar ta ta hannu da murmushi ta mik'a mi shi tace "Saboda kai kawai na zo gidan nan, ga wannan nasan ka na son ta sosai."


Karb'a ya yi da hannu biyu yace "Nagode aunty."


Shafa kan shi ta yi tace "Ba komai d'an auntyn shi." D'orawa ta yi da "Maman ka na ciki ne?"


Saida ya kalli Haseenah da ta juya ta shiga madafa yace "Bata nan, tun jiya ta tafi gida, ni ma ina so naje wajen ta."


Shiru ta yi ta na nazartar wani abu kafin ta sake shafa kan shi tace "Ka yi hak'uri kaji yarima, yanzu ni ina sauri zanje wani wuri ne duba wasu kaya, kuma kaga banda ikon da zai fitar da kai daga gidan nan dan bansan me ya faru ba, amma ka yi hak'uri kji ko."


Kai kawai ya d'aga mata, murmushi ta sake mi shi tace "Yawwa, to yanzu ka shiga ciki ka zauna kaji ko, ni na tafi sai anjima."


"To aunty." Ya fad'a ya na shiga ta falon mahaifin shi dan sada shi da falon maman shi dan k'ofar waje rufe take, Turai na ganin haka ta lek'a madafar ta ga Haseenah ta yi tsaye jugum ta na jiran Turai ta tafi ko ta samu ta koma falon ta, wani murmushi ta mata tace "Amarya ni zan wuce." Hannu ta sa aljihu ta fito da 'yer jaka goma ko karyawa babu ta cilla mata tace "Wannan zai isheki ki siyi sabbin farantai har dozin dozin, amma ki sani yarima da iyayen shi ba matsiyata bane irin ki."


Har ta juya zata fita ta kuma sake tsayawa ta juyo tace "Idan Usee d'in ya zo ki fad'a ma sa Hajia Turai Dubaï ta zo, sannan ki ce ya fad'a mi ki wacece ni, za ki ji baya ni daga bakin shi."


Juyawa ta yi ta fice ta bar Haseenah duk ta yi gumi saboda tsoro, dan har ga Allah har zuciyar ta tsoron matar ya d'arsu a zuciyarta, dan kana ganin kasan ta take Khadija ta shanye wajen masifa da ma k'arfi, amma da ta samu nutsuwa ta dawo jikinta saita shirya sake wani makircin da tugu, d'aukar kud'in ta yi ta saka a cikin rigar nonon ta, kiran Usman ta yi a waya ya na d'auka ta fashe da kuka tace "Abban Bilal dan Allah duk in da ka ke ka zo gidan nan ka sake ni, wallahi na gaji da abin da ake min kullum ace na yi hak'uri, na gaji Abban Bilal."


Usman da tuni ya zabura ya tashi tsaye cikin tashin hankali yace "Haseenah! lafiya? Me ya faru ki ke kuka?"


"Ni dai kawai ka zo ka bani takardata, ba na so saina tafi gidan mu ka sake tafiya ka dawo da ni, Allah na gaji da zaman gidan ka."


Usman kamar zai fashe da kuka sai kuwa cewa ya yi "Haba Haseenah, ya za ki fad'i haka? Kinsan ke ce rayuwa ta fa, idan ki kace na rabu da ke to ni ina zan saka kai na? Kinsan fa ke ce fitilar gidan nan, ke ce sukuni da walwala na gidan nan, ke ce farin ciki da kwanciyar hankali na, idan ki ka ce za ki bar gidan ya ki ke so na yi to? Dan Allah ki fad'a min miye ya faru ni kuma na mi ki alk'awarin d'aukar mataki da gaggawa."


Tunda Murtala ya lura ya kuma ji abin da yake fad'a kan shi ya d'aure, shi dai a sanin shi har ya auri Haseenah ba wani zazzafan so yake mata ba, hasalima kullum cewa yake auren su Allah ne ya k'addara shi kawai, amma da zai iya hanawa da ya hana dan ya zauna da matar shi, ci gaba ya yi da kallon shi yayin da Haseenah tace "Haka kawai dan ka kori matar ka shine k'awar ta za ta zo har gidan nan ta ci mutumci na ta uwa ta uba, ba irin zagin da baiwar Allahr nan bata min ba, ta kira ni da matsiyaciya yar matsiyata, talaka yar talakawa, duk saboda ka kori matar ka, saboda Allah Abban ni ina da hannu cikin korar matar ka da ka yi? Ba kai ne ka yanke hukuncin ba? Amma shine za ta turo min 'yer iska gida har tana neman duka na, to ba zan iya ba wallahi, dan kalaman da ta fad'a ni sun tsorata ni sosai, dan ko ban bar gidanka ba yau to zan barshi gobe, tunda sun ci alhwashin ba za su barni ba nima na rayu da kai, kawai ni ka zo ka sake ni ko na samu naje gidan mu lafiya."


Cikin wani irin yanayi yace "Wacece ita? Fad'a min sunan ta kawai."


Kamar mai nazari tace "Wata wai ko Hajia Turai, har da cewa na tambaye ka wai kai za ka fad'a min wacece ita."


Daga in da Usman ya ke ya nufi wajen motar shi zai shiga ya na fad'in "Kar ki damu ba sai kince komai ba, ba dai haka tace ba? To barni da ita, nasan sosai, marar mutumci ce ta gidan gaba, amma zan wa tubkar hanci."


Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam har da tsalle duk da bata san me zaiyi ba tasan dai ta sake gogawa Khadija bak'in panti, zai shiga mota Murtala ya rik'o hannun shi ya na kallon k'wayar idon shi yace "Wannan kamar ba Usman d'ina ba, ya naga ka canza haka, me ya faru ne?"


K'ara had'e rai ya yi yace "Ka bari dan Allah ina zuwa yanzu, akwai abin da ya faru ne da gaggawa a gida."


Ya na fad'a ya janye hannun shi ya rufe motar ya wuce zuciya sai tafasa take an tab'a mi shi Haseenah, *Abu azimun inji wata k'awata*, aifa abu ya girmama fiye da yanda ma su karatu suke tunani, dan Usman baiyi k'asa a gwiwa ba wajen zuwa ofishin 'yan sanda akai k'arar Hajia Turai akan taje gidan shi ta ci mutumcin matar shi har da mata barazana, zai iya d'aukar mataki amma dan kar ace ya d'auki doka a hannun shine ya sa ya garzayo nan, amma a mata kashedi ba ita ba gidan shi ko da kuwa me ya ke faruwa a gidan.


Nan fa aka kaiwa Hajia Turai takardar sammaci har gida, lokacin zuwan ta kenan tare da wasu samari da suka d'auko mata kaya sai ga motar 'yan sanda, ana bata takardar ta shiga motar ta fara bala'i tun daga cikin motar, fad'in take "Ai Usman k'aramin d'an hau ne, baisan ni d'in nan babu gidan kason (magark'ama) da ban kwana ba, wani jami'i ne da ya kwana ya tashi a garin nan bai sanni ba, ko ya d'auka duk bala'in nawa iya baki ne, to muje na nuna mi shi yanda ake rawar...kalmar data fad'a ba dad'in ji, amma dai kamar wannan abar ce ta anbata mai kama da ayaba."😎


Su na isa kad'an ne ya rage ofishin ya kama da wuta saboda yanda Hajia Turai ta d'aga murya take masifa, haka Usman bawan Allah ya zama kamar mahaukaci saboda shegiyar Haseenah shima ya biye mata, mutumin da ko da matanshi ba ya son hayaniya amma sai gashi ya zage damste a waje tare da k'awar matar shi suna musayar yawu, ita tana fad'in ita zai ci wa mutumci saboda yar iskar matar shi, shi kuma ya na fad'in akan me za ta je gidan shi ta yiwa matar shi wulak'anci, cikin masifa take fad'in "Kai in banda ma sususu ne kai, wannan tsomalalliyar yarinyar har yaushe ta zo gidan, yaushe ka fara cin gindin ta da har ka mance kalar gindin Khadija 😎, kenan ita wajen bokaye ta kai ka, banza kawai lusari marar kunya, kai har ka isa ka manta hallacin da Khadija ta ma ka, tun ba ka da komai take tare da kai, kusan ma ita ce silar arzik'in ka, amma shine yanzu ka samu sabon..."


Da k'yar dai wanda ke mu su shari'a yace kar ta sake zuwa gidan shi, kuma kar wani abu ya samu matar shi, in ba haka ba za ta shiga hushin hukuma, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Wallahi kunji na rantse ko, da ace nasan in da ake siyar da k'ank'arar mayu to da na siyo ba dan komai ba sai dan na lashe matar ka, ka sani ba zan sake zuwa gidan ka ba, amma wallahi tallahi na had'u da matar ko sai na ci kakan..., tunda tace ma ka na yi abin da banyi ba kuma ta lak'awa k'awa ta sharri ko, to ba makawa sai ta samu shaidar sanin Hajia Turai, ka dube ni da kyau Usman kai ka sanni, wallahi k'aramin aiki na ne na keta yarinyar nan da wuk'a, kuma a shirye nake da na je duk kotun da aka kira ni dan shari'a akan ta, banzaye kawai daga kai har ita."


😂 _Allah ya kyauta._


Nan aka raba su kowa ya kama gaban shi, amma fa Hajia Turai ta zuba ido da kunne ta na jiran ta ji wani sabga da zai taso wanda zaisa ta had'u da amaryar Usman, Usman kam tunda ya shiga mota ya kifa kan shi yake jin zuciyar shi babu dad'i haka ma yanayin shi, wai me ya faru da shi da har ya aikata wannan abun kunyar? Gashi ya ja bala'in da yafi k'arfin na shi ta ci mutumcin shi son ran ta, Me ya sa ya yi haka to? Me ya sa baiyi bincike ba ko ya duba al'amarin? Amma kuma ya na tunawa da Haseenah sai zuciyar shi ta yi sakayau da ita, domin ya bata hak'uri ya sa ya k'arasa bakin titin da ke ofishin wajen masu siyar da waya, nan fa ya siya mata tsandareriyar waya ta ban hak'uri haka Bilal, dan ya jima ya na si ya siya mi shi dan ya dinga game, saida ya tsaya ya yi sallah azahar kafin ya wuce gidan, har madafa ya same ta ya bata wayar, ta yi murna sosai ta masa godiya, kallon ta ya yi yace "Ina Bilal?"


"Ya na falon maman shi, ba irin lallab'ar da ban masa ba ya fito ya k'i."


Fita ya yi ya na fad'in "Ina zuwa." Ganin ya sa ta bi bayan shi dan kar azo tambayar Bilal wani abu zaiyi, tare su ka shiga ya na kwance da alama ma bacci ya ke ji, zaune ya tashi yace "Abba sannu da zuwa."


Shafa kan shi ya yi ya na zama kusan shi yace "Yarima hutawa ake?"


"Um." Kawai ya fad'a yayin da Haseenah ta harare su ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "Hum! Yarima dai yarima, ku ba ku gaji sarauta ba amma ku lak'abawa yaro sunan yarima, haba dai." Ta k'arshe da yin k'wafa. 


Ledar hannun shi ya mik'a mi shi yace "Duba ka ga tsarabar ka."


A hankali Bilal ya ciro kwalin ciki, ya na ganin waya ce ya yi sauri budewaya fito da ita sai shek'i take, dariya ya yi ya rumgume mahaifin na shi yace "Abba nagode, na ji dad'i sosai."


Rumgume shi ya yi cike da so da k'auna yace "Hakan na ke son ji dama."


Karb'ar wayar ya yi ya had'a mi shi da kan shi in da ya janyo mi shi mega (data) daga na shi ma'ajiyin sannan ya nuna mi shi yanda zaiyi ya dinga janyowa duk lokacin da ya ke so, nan fa suka zauna su na ta danne danne a wayar ya na nuna mi shi abubuwa da dama, Haseenah kam in ranta ya yi dubu tabbas ya b'ace, musamman da ya nunawa Bilal yanda zai iya janyo data amma ita saida ya amshi wayar ya jawo mata, haka ta gamo girkin ta kawo tare su ka ci da yaro kamar yanda suke ci a baya a faranti guda, har la'asar ya na gida tare da Bilal saida su ka yi sallah a masallaci kad'ai ya fita yace zaije gidan, dan da safe bai je ya gaishe su ba.



*Hajia Turai* ta na zuwa gida ta'aniya zazzaga bala'i, k'arshe dai shiryawa ta yi a motar ta taje gidansu Khadija, Khadija na falo sun gama girkin rana suna cin abinci ta zo gidan, nan fa ta tashi duk wani mai baccin rana a gidan ta na fad'a mu su wulak'ancin da Usman ya mata, Khadija da ta iya k'awar ta ta shiru ta yi saida ta kalle ta tace "Ke kuma sai magana na ke amma kin min banza, ko har yanzu ki na son mijin na ki?"


Tasan in ba ta bita sannu ba sai sunyi baran-baran, dan haka tace "Haba kema dai bari fad'in haka mana, ai ni tuni na yi wuri na aje shi tunda ya tab'a min ke k'awa ta, kwantar da hankali kinji tawa ki manta da lamarinsu kawai."


"Yawwa yanzu na ji magana, ai na d'aukar har yanzu ki na son komawa gidan shi." Ta fad'a ta na saka hannu cikin kwanon abincin, murmushi Khadija ta yi tace "Haba ina, ai sai a aljanna kuma idan da rabo mun had'u."


Saida ta cika baki da abinci tace "Shegiyar yunwa na damu na, amma wannan mijin na ki ya k'i bari na ci abinci ya aika min da yan sanda gida na, ke kinga bala'i da zafin shi ni da Usman a ofishin yan sanda."


Yanda Khadija ta santa tasan yanzu ma saita sake dawo da labarin baya, hakan ya sa Khadija cewa "Haba k'awa ta rabu da su kinji, ci abinci dai yanzu muje d'aki akwai hira."


Wata dariya ta yi "Hahahaha, haka na ke son ji k'awa ta, ki barsu kawai wallahi lokaci na zuwa da saiya dawo da k'afafun shi ya neme ki, wallahi saiya durk'usa har k'asa ya na neman afuwarki, ita kuma wannan tsinannar ko, haba, yo an fad'a mi shi mu na wasa ne, ai iskancin ma ba haka kawai mu ke yin shi ba, wallahi ko uban..."


Tabbas Khadija tasan cewa za ta yi uban shi dan ita ba damuwa bane gare ta, dan haka ta rufe mata baki tace "A'a k'awata, surukina ne fa, dattijon arzik'i ne babu ruwan shi."


"Hakane kuma, ai da ina so na mi ki misali da gyatumin shine."


Duk abin da suke fad'a mamar Khadija na gefe na saurarn su, dariya kawai take ba tare da sanin su ba, haka suka gama sun shiga d'aki nan ma kuma Salamatu ta zo wacce Khadija ta fad'a mata a waya tana gida, aifa d'akin Khadija kamar zai tsage saboda hargowar da suke yi, har k'arfe biyar na yamma suna gidan nan kafin suka tafi.


A wajen Usman kuma ko da ya je gida bayan sun gaisa da Hajia ta tambaye shi ya iyali, nan fa ya kora mata bayanin abin da ya faru daren jiya,   Malam da shigowar shi kenan ya rabka salati ya na fad'in "Fodio, me na ke ji kana fad'a haka? Ka ce ta tafi gidan su sai ka neme ta? Me ka ke nufi da haka? Fodio ba ka ji kunyar fad'in maganar nan ba dan Allah?"


K'asa ya yi da kan shi baice k'ala ba, malam ne ya d'ora da "To tashi ka fita, kuma da anyi sallah isha'i ka zo ka d'auke ni k'afar ka k'afa ta muje mu dawo da ita, ni ba za ayi wannan haukan da ni ba kaji na fad'a ma ka."


A hankali ya mik'e ya saka takalmin shi zai wuce ta gaban malam ya kalle shi da kyau har ya fita, kallon Hajia ya yi yace "Anya kuwa yaron nan lafiyar shi k'alau?"


"Ni ma dai abin da na ke tunani kenan, ya na wasu abubuwa kamar ba'a hayyacin shi ba." Cewar Hajia da ke k'ok'arin d'auke tabarmar da ya tashi akai.


"Ai kuwa sai a d'auki mataki tun kafin abu ya yi nisa, amma in ba haka ba taya ma zai ce Khadija ta tafi gida saiya neme ta."


"Gaskiya kam."


K'arasa shiga d'aki malam ya yi ya na fad'in "Allah ya sawak'e."


Kamar yanda ya fad'a ana sallah isha'i ya dawo gidan ya d'auki malam, basu zame ko ina ba sai gidan su Dijeh wajen biko, karo na farko a rayuwar su da haka ta faru, sallama su ka yi tun farfajiyar gidan aka amsa, Ashir da kan shine ya mu su iso falon Mama, dan dama suna nan zaune dukan su, matansu ne suka fito tare da yara aka bar mazan tare da Mama sai Khadija da ke d'aki ta kan iya jiyo maganganun da suke.



*'Yata kawai ki koma*😉

14/02/2020 à 16:55 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *25*



Saida ya gama fad'in abin da ya faru kafin ya d'ora da "Wallahi Mama Khadija ta bani mamaki, wai ni Khadija zata kalla ta dinga fad'awa duk abin da ya zo bakin ta, saboda kawai na mata kishiya saita raina ni, ko kuma dan na mata magana akan abin da tayi bata kyauta bane, wannan abu ya b'ata min rai sosai, shine dalilin da ya sa nacr ta zo gida saina neme ta, banyi haka dan cin mutumcin ta ko cin zarafinku ba, sai dai nasan dole anan akwai wanda za su fad'a mata kuma ta saurare su, dan naga yanzu kishi ya rufe mata ido gaba d'aya."


Malam ne yace "Kai dallah rufewa mutane baki, koma menene ai sai kayi hak'uri, duniyar nan uban waye baisan halin mace ba akan kishi, ko kai kana ganin kamar uwarka ba ta da kishin ne, ita kan ta mahaifiyar ta ta da ka ke magana akai ai tasan zafin shi, kenan sai ka yi hak'uri ka d'auke kan ka dukansu na d'an lokaci ne za su yi, in banda rashin hankali irin na ka da can farko ta ma ka haka kafin zuwan amaryar?"


Murmushi Mama ta yi tace "Alhaji ka k'yale shi haka, to idan yace ya saka mu su ido suyi yanda su ka dama suna fakewa bayan kishi, ai kuwa kullum da tsiyar da za su b'ullu da ita a gidan, hakan zaisa ba za'a zauna lafiya ba, ni banga laifin shi ba dan hakan shine daidai, ka na ji ko." Mama ta fad'a ta na kallon shi cike da kulawa, kallonta ya yi take kuma ya sunkuyar da kan shi k'asa, d'orawa ta yi da "Ka yi hak'uri dan Allah akan abin da ya faru, insha Allahu zan ja mata kunne hakan ba zai sake faruwa ba, abinka ne da d'an yau ka haife shi baka haifi halinshi ba, babu irin tausar zuciyar da ban mata ba, amma ba ta ji ba ko kad'an, amma ka yi hak'uri kaji, insha Allah za ta kiyaye a gaba."


Kallon malam ta yi tace "Bara na kira mu ku ita sai ku tafi ko." Cike da dattako malam yace "Shikenan Hajia mun gode sosai da karamci, Allah ya bar zumunci."


Mama na wucewa d'akin Khadija dake ta cika ta na batsewa Usman ya d'ago kai a hankali ya kalli su Ashir da duk su ka hakimce su na kallon shi, d'auke kan shi ya yi dan gani yake kamar za su rufe shi da duka, dan ko basu fad'a ba kasan ba haka su ka so ba, musamman Naseer da Habeeb da bakin su ke ta motsi😂, a d'aki kam tuburewa Khadija ta yi wai babu in da za ta je, saida Mama ta fara nuna b'acin ran ta kad'ai ta fito ta na kumburo baki, wajen yan uwan ta ta tsaya ta ja birki ta na kallon su, Naseer ne yace "Ki yi hak'uri kinji auta, Hajia tace ba ta yarda mu ce komai ba."


Kallon Usman ta yi da shima yake kallon ta, har ga Allah kafin ta fito ya ji ya na son ya koma tare da matar shi, amma ya na ganin ta yanzu sai ya ji kamar yace ta yi zamanta ko kuma ya rufe ta da duka, haka kawai ya ji ranshi ya b'ace ko da ya ganta, amma sai ya dake ya mayar da hankalin shi kan Mama da tace "Maza ki bawa mijin ki hak'uri yanzun nan, sannan ki mi shi alk'awarin hakan ba za ta sake faruwa ba, in kuma ki ka sake to fad'an ni da ke ne ba da shi ba."


Kamar za ta yi kuka ta kalli Mama tace "Mama, wai ni ce ma zan ba shi hak'uri? Har fa mari na ya yi mama, kuma dama duk na ji abin da ka fad'a ina d'aki." Ta fad'a ta na mayar da hankalinta kanshi, ci gaba ta yi da cewa "Bansan me ya sa za ku yi tunanin na lalata abincin yarinyar nan ba, domin Allah ku dube ni da kyau ku dubi Haseenah, ace na rasa ta yanda zanyi na yi maganinta akan kishi saita hanyar zuba gishiri a abincin ta, haba dai kuma, wannan ai abune da hankali ba zai d'auka ba, kenan ma ta gagare ni?"


"Khadija." Mama ta fad'a cikin tsawa, shiru ta yi ta kalli Mama, cikin b'acin rai tace "Rashin kunyar da ya fad'a mana ki na masa ita ce za ki nuna mana sanfurin da ki ke ma sa?"


A hankali ta durk'usa duka gwiwoyinta biyu tace "Ki yi hak'uri Mama."


"Ba ni za ki bawa hak'uri ba, mijin ki ne gashi nan."


Saida ta had'e hawayen ta kad'ai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri." Yanda ta turo baki ne ya sa Mama cewa "Anya kuwa Khadija ke ce? Ke ce Khadija auta ta da na sani."


Kallon maman ta tayi ta sake kallon Usman ta saisaita murya tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, insha Allah ba zan sake ba."


Da k'yar ya iya k'arfin halin k'ak'aro mata murmushi yace "Ba komai ai ya wuce, ni ma ki yi hak'uri abisa marin ki da na yi, kuskure ne da b'acin rai."


'Anzo wajen." Cewar Naseer, d'agowa ya yi daga jinginar da ya yi a bayan kujera yace "D'an uwa Usman dan Allah a dinga kiyayewa, shi duka a fuska ya na da had'ari sosai, mari kan iya jayo makanta, mari ya kan iya sanadin rasa ji, mari zai iya sakawa haure ya fita, mari kan saka kai ya yi ciwo, dama wasu matsaloli da dama, ka ga sai a dinga sanin me za ayi idan rai ya b'ace."


Yasan ba lallai Mama ta yi shiru ba, dan haka ya na fad'a ya tashi ya bar falon ya nufi b'angaren shi, da murmushi Usman ya bishi ya kalli sauran yace "In Allah ya yarda ma ba za ta sake faruwa ba, wannan ma tsautsayi ne."


"Allah ya kiyaye gaba." Cewar Ashir, haka suka tashi su ka koma gida, saida ya ajeta gida kafin ya wuce ya kai malam, Bilal ya yi farin cikin ganin mahaifiyar shi, Haseenah kam ba ta ji dad'i ba ko kad'an, sai dai tasan nan ba da jimawa ba za ta koma tunda yanzu sai yanda ta yi da Usman.


A matsayin kwanan Khadija ne yau ta shirya ta kuma je har d'akin shi kamar yanda ta saba, tabbas ya kwana d'akin, amma da kwanan shi da rashin kwanan duk d'aya, dan kuwa baya ya juya mata ko uhum ba ta ji daga bakin shi ba har ya yi bacci, amma ita ba ta yi baccin ba sai nafila da ta kwana ta na yi ta na kaiwa Allah kukanta, har asuba tana nan kafin ya tafi masallaci ita kuma tayi sallah, bayan ta kammala ta shiga madafa ta d'ora girki.


Usman kuma na dawowa daga masallaci d'akin Haseenah ya nufa su ka gaisa, daga nan ya fad'a mata gobe fa zai yi tafiyar nan ta shirya in tana zuwa, amma bayan tunani da tayi sai taga za'a zargeta idan suka tafi tare, dan haka ta marairaice tace "Um,um gaskiya ni na fasa tafiyar ma, ka ga kai kasuwancin ka ne zai kai ka, bai kamata muje tare ba kuma na hana ka sabgar gaban ka, kawai kaje Allah ya tsare mana kai, ranar da na haihu sai mu tafi tare da yaronmu mushak'ata."


Saida ya rumgume ta yace "Gaskiya ban ji dad'i ba, Haseenah ba zan iya farin ciki ba ki na nesa da ni, me ya sa ba za ki je ba? Zan iya yin wata d'aya fa ko sati uku ban dawo ba, ki na ganin zan iya rik'e kai na bayan na saba da ke a d'an lokacin nan."


Cike da gatsali tace "To ba ga aunty Khadija ba, ku je tare mana, ni kuma sai mu zauna abunmu ni da yarona Bilal, ko ya ka ce?"


Tunda ta ambaci sunan ya ji kamar ta jefe shi da mashi akan tsohon ciwon shi, b'ata rai ya yi yace "Ya ina magana da ke za ki kawo min maganar matar can? Gaskiya ba na so kar ki sake."


Saida ta shafi fuskar shi tace "To shikenan yi hak'uri ba zan sake ba."


"To yanzu fad'a min za ki je ne?" Ya fad'a ya na k'ara cukuikuyeta, ba alamar wasa tace "Gaskiya ba zan je ba, kawai ka tafi kai kad'ai."


"Shikenan, amma taya zan barki ki zauna tare da matar can? Na ga fa ba wani sakin jiki ki ke da ita ba."


Shiru ta yi ta na tunanin abinyi ita ma, da sauri yace "Ko na kira Hajia ta turo mi ki Aziza? Tunda kinga dama ita ce ke zuwa nan idan zanyi tafiya."


Wani murmushi ta yi da bai kai ciki ba tace "To shikenan ba damuwa, hakan ma ya yi ai."


Da haka ya fito ya shiga d'akin shi ya yi wanka ya shirya ya fito kan teburi, saida Haseenah ta fito kafin su ka fara cin abincin, tabbas daga yanda ya ke cin abincin za ka san ya masa dad'i, amma da zaran ya had'a ido da wacce ta dafa abincin saiya d'aure fuska, haka su ka gama ya tashi ya fita su ka bishi da addu'a, Khadija da ta bi bayan shi har wajen mota sannan ya juyo ya kalle ta yace "Ya dai malama ki ke bina haka?"


Murmushi ta yi tace "Abban Bilal hushi ka ke dani har yanzu akan abin da ya faru?"


Wani d'auke kai ya yi yace "Mtsss, ba komai kawai, kawai dai ki na ba ni mamaki ne."


A hankali ta janyo hannun shi ta na shafawa, in da shi kuma ya ke jin kamar hannun wuta ne da ita, cikin taushin muryar da tasan ta na tasiri akan mijin ta ta fara magana "Dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, insha Allah ba zan sake b'ata ma ka rai ba, ka ji? Ka yafe min, kasan hankali na ba ya kwanciya idan ina ganin ka haka."


Saida ya raba hannunshi da na ta yace "Shikenan ba komai, Allah ya sa haka."


Juyawa ya yi zai shiga mota tace "Shikenan kuma ba komai za ka tafi."


"Kamar me fa?" 


Cikin yanayin jan hankali tace "Ba rumgumewa, ba sumbata, abun ba armashi."


Kasak'e ya yi ya na kallon ta da tunanin abinyi, matsawa ta yi kusan shi ta shafo fuskar shi, a hankali ta kai bakin ta kan na shi ta zura harshenta cikin bakin shi,  harshenshi ta kama tana wasa da shi in da ta kai d'aya hannun ta cikin rigar shi ta na murza k'irjin shi, d'aya hannun kuma shafar sumar kan shi take ta na yamutsata, tunda ya lumshe ido ya rasa kuzarinshi, hak'ik'a ya na son abin da take ma sa sosai d'in nan, amma ya na jin ba zai iya biye mata ba, amma da ya ke Khadija bala'i ce saida ta watsa mi shi duk wani lissafin shi da nutsuwa ya ma manta ina ne ya ke yanzun, me kuma zaiyi ko ya ke yi, saida ta ji jikinshi ya saki sosai sai wani gurnani da yake ya na k'ok'arin kai hannayen shi cikin rigar ta kawai ta raba kan ta da shi, wani arnan kallo ta masa da manyan idon ta a cikin gilashi kafin ta kashe mi shi ido d'aya, wata yar mik'a ta yi tare da fad'in "Ashhhh."


Bye bye ta mi shi ta juya da nufin komawa ciki, wata karairaya ta dinga yi wanda ya sa hankalin Usman k'ara tashi saboda yanda take juya jikinta, wata zabura ya yi saboda wani zirrrrr da ya ji tun daga k'asa har sama, fitowa ya yi daga motar ko rufewa baiyi ba ya bi bayan ta har da gudu ya na so ya kamo ta, ta na shiga falon ta ga Bilal zaune sai kawai ta wuce d'akin ta, Bilal na ganin baban shi ya bi bayan maman shi sai kawai ya mik'e ya fita, wajen mai gadi ya zauna su na hira ya na kallon hanya, Usman na shiga wani k'arfi ne ya zo mi shi cikin sauri ya ke son aika sak'on shi, haka dai al'amari ya yi nisa sosai suka gangara, tabbas tun bakin k'ofar za ka ji abubuwa kala kala masu rikatar da mutum, amma ya na k'arasa shiga ciki sai ya ji wani b'acin rai da rashin ma'ana da...abubuwan ma dayawa, da k'yar ya k'arasa abin da ya fara cikin d'an lokaci ya samu nutsuwa ya tashi ya yi wanka ya saka kayan shi, ko kallon ta baiyi ba ya wuce abin shi ya na jan tsaki ya na gunguni.


              *A gurguje*


Bayan ya fita gida ya nufa in da ya aje mu su duk wani abun buk'ata, sannan ya fad'awa Hajia ta tura Aziza can ta taya Haseenah kwana, tunda yamma ko da Haseenah ta karb'i girki Usman ya zo gidan, bai bari ta yi aikin ba ya zura ta d'aki ya na ta huce haushin shi na safe, har saida ta kai ita kan ta Haseenah ta fara nadamar kan ta dan ba k'aramar wahalar da ita ya yi ba, hakan ya sa ko da dare ya yi yace ta shirya suje cin abinci, saida su ka shirya za su tafi ya shigo falon Khadija yace Bilal ya zo su fita unguwa, sam ba ta yi tunanin har da Haseenah ba, har su ka fita sune sai sha d'aya da rabi na dare suka dawo, kai tsaye kowa falon shi ya nufa, sai lokacin ne Bilal ya fad'a mata har da auntyn shi su ka tafi, ba ta nuna mi shi komai ba, amma ta na shiga d'aki ta yi yan dabaru ta ci abinda ya sawak'a saida ta zubar da hawaye, har ta yi bacci ba ta ga Usman ba da sunan zai mu su saida safe.



Misalin *08:10* ya shigo falon ta cikin shirin da gani ba tambaya kasan tafiya zaiyi, tare suke da Haseenah dan Bilal na d'aki har yanzu ya na shiri, kud'i ya mik'o mata yace "Ga wannan kya yi anfani da shi, ni yanzu zan wuce Niamey zuwa asuba kuma jirgin mu zai tashi, nasan akwai komai babu wani abin da za'a buk'ata, sannan maganar kai Bilal makaranta na barwa amarya ta duka makullan motar da tawa da taki, idan za ku yi anfani da su sai ki mata magana, saina dawo."


Ya na fad'in haka ya juya rumgume da Haseenah a jikin shi, suna fita saida ya gama shinshine ta da lalabe lalabe kafin ya fito da enveloppe ta kud'i har jaka d'ari biyu ya bata, zo kaga murna ga yar matsiyata an bawa Khadija jaka talatin an bata d'ari biyu, 😂 da k'yar ya fita Murtala ya d'auke shi ya tafi cike da kewar amaryarshi.



Sai da rana Aziza ta zo gidan da kayan ta, lokacin Khadija na zaune ta na waya da wata yer uwar ta (cousine) ta na mata k'orafin ta daina zuwa wajen ta, *Aishatu* ce tace "Aunty Khadija na zo Allah ko, ba dai ni nace mi ki na zo ba."


"Hum, yaushe to?"


Daga d'aya b'angaren ne Aishatu tace "Idan na sa lokaci na sanar da ke."


"To ina jiran ki." Ta fad'a su ka yi sallama tace ta gaishe da su aunty (k'anwar maman ta).


Ta ga shigar Aziza b'angaren Haseenah amma ko a jikin ta, ta na jin su suna aiki a madafa amma bata kula da tsiyar su ba, har lokacin d'auko Bilal ya yi daga islamiyya, Ashir ta kira a waya bayan sun gaisa ne tace "Yah Ashir wata alfarma a gurin ka dan Allah?"


Saida ya yi murmushi yace "Auta ai babu alfarma tsakanin mu, fad'i me ki ke so yanzun nan a mi ki shi?"


Cikin sanyin murya tace "Al'amarin Abban Bilal ya na buk'atar addu'a, na sani mijina ba ya hayyacin shi, yanzu haka ya yi tafiya, amma ni saida safen nan na sani, kuma ya tattara makullan mitar shi da tawa ya bawa yarinyar nan, yace sai dai idan ina buk'ata na karb'aa wurin ta, a gaskiya yah Ashir hakan zubar min da mutumci ne, na tabbata sai mun samu matsala da ita akan haka, yanzu haka Bilal na ismaliyya ba'a d'auko shi ba, shine na ke so ka samar min wanda zai dinga kai shi ya na d'auko shi har lokacin da zai dawo, tunda ka ga ma nan da kwana kad'an za'a koma makaranta (school)."


Duk da ya ji ba dad'i amma cewa ya yi "Kinga kar ki damu da wannan, barta da makullan ta had'iye su in za ta iya, yanzu zanje na d'auko Bilal d'in na kawo shi gida, ba buk'atar sai an d'aukar mi shi dreba, ba wai dan ba za'a iya biyan kud'in ba, sai dan darajar Bilal ta wuce haka a wajen mu, kamar yanda na ke kai yara na da kai na haka zan dinga biyowa ina d'aukar shi shima, ko da babu mazauninshi a motar shi to za'a siyi sabuwar mota ne saboda shi kawai, motar tsiyar me da har za'a mi ki iko da ita."


Ya na fad'a ya kashe wayar bin wayar ta yi da kallo tasan ranshi a b'ace ya ke, amma ta ji dad'i kuma da Allah ya bata yan uwa masu huce takaici, baifi minti sha biyar ba saiga Bilal ya shigo gidan da k'atuwar leda da kayan mak'ukashe a ciki, Haseenah da kallo ta bi shi har ya shiga tana mamakin waya kawo shi, ya na shiga ya aje ledar gaban Khadija ya shiga dan sauya kaya, ba jimawa ya dawo da wayar shi a hannu ya shiga latse latse ya na korawa da kayan mak'ulashen shi, sai daf da la'asar Aziza ta shigo wajen Khadija kawo mu su abinci, ko kallon Allah ya isa ba ta ishi Khadija ba har ta aje ta fita, ta na fita Khadija ta d'auki wayar ta kira *Hafsatu* Mak'wabciyar ta tace ta aiko yara ya amshi abinci, ba jimawa yarta ta zo Khadija ta juye mata shi a kwano d'aya ta tafi da shi, dan ita dai ba za ta ci abincin Haseenah ba in dai har za ta fitar mata da na ta da d'an ta a had'e, sai dai kome zai faru ya faru.



*Tun daga wannan rana* Ashir ne ke zuwa ya d'auki Bilal da kan shi tare da yaran shi da na yan uwan shi, dama shi ya d'orawa kan shi alhakin kai yaran, sai dai ba kullum yake zuwa d'aukar su ba sai dai ya sa a d'auko su, amma yanzu da ya zamana akwai Bilal a cikin tawagar da kan shi ya ke d'auko su, hakan ya sa har yanzu bakin Khadija da na Haseenah bai had'u ba da sunan magana, ta yi shiru ta rik'e makullai ta na jiran ace kawo ta yi rashin kunya, Khadija kuma ta nuna mata ita ba bak'uwar mota ba ce, ana cikin haka hutun k'arshe ya k'are na makaranta, yara da manya aka fara hada hadar komawa, Ashir ne ya wa Bilal komai kama daga sababin kaya da abin da zai buk'ata a sabon ajin shi, har zuwa kud'in makarantar shi ya biya ba tare da sanin ma Khadija ba, saida aka kawo kayan kad'ai ta ji kuma ta gani, Usman kuma dama ba kiran ta ya ke ba, idan ma ta kira shi zai ce ta kashe zai sake kiran ta yana cikin mutane ko wani abu, sai in ya kira Bilal ne kad'ai yace ina maman ka yace gata nan, to lokacin zai ce bata waya kuma har su jima suna magana ya na tambayar ta abubuwa.


Zaman Aziza da Haseenah ma ba laifi, a fuska faran-faran take mata, amma da ta bada baya za ta bita da harara dan duk ta gundureta, sai dai kuma har yanzu ba ta bar yiwa Khadija bita da k'ulli ba, duk ranar girkin Khadija idan ta aiko mu su da shi bata nunawa, dan dama Aziza sai ta tafi islamiyyar su ta dawo wacce Haseenah ce ke bata kud'in adaidaita dan ta yi nisa daga nan, kullum sai kusan k'arfe d'aya take dawowa, Khadija kuma na gama abinci da wuri tun kafin Bilal ma ya dawo, hakan ya sa da an kawo mata zata zauna ta ci ta k'oshi tasha ruwa, sauran kuma komai yawanshi da kyawunshi sai dai ta shek'a mi shi ruwa ta zuba wajen wanke wanke, da Aziza ta dawo za ta nuna ba'a basu abinci ba, haka za ta aikata ta siyo mu su awara ko soyayyan dankalin hausa, wata rana kuma su dafa indomie ko suyi taiba, kullum a takarce suke hakan ya sa Aziza da taje gida ta fad'awa Hajia, a wannan karan kam Hajia ta yarda tunda Aziza ce ta rantse ta fad'a mata, da farko ta so ta kira Usman ta fad'a ma sa dan ya mata magana, amma sai tayi tunanin ja mata matsala, dan haka saita shirya taje gidan da kan ta da nufin yi mata magana cikin ruwan sanyi, amma abun mamaki a gabanta ta zubawa su Haseenah na su abinci kwanon miya da na tuwo ta bawa Bilal ya kai, ita ma saida aka zubo mata ta ci ba wani sosai ba kafin ta mata sallama za ta tafi, saida ta shiga da nufin yi wa Haseenah sallama ta samu Aziza sun ware sai shigar tuwo suke kamar 'ya'yan yunwa, nan fa Aziza ta shiga cewa wallahi dan ta ga Hajia e ta zo ta zubo mu su, kuma d'ari bisa d'ari Hajia ta yarda, haka ta tafi gida ranta ba dad'i ta na ji a ranta Khadija ta bata kunya, *Khadija baiwar Allah* ba ta san ma tsiyar da suke ba, dan ita abincin Haseenah ma idan ta aiko kullum saidai ta kira mak'wabtanta azo a d'auka, ita kuma haka za su yi ta yan dubaru ita da d'an ta.


*Yau sati biyu* kenan da tafiyar Usman, kuma jibi ne komawa makaranta, hakan ya sa Usman kiran Khadija a wayar ta, ta yi mamaki dan abu ne da bata tab'a gani ba tunda ya tafi, ta na d'auka suka gaisa a gajarce ya d'ora da "Na ga yara na ta shirin komawa makaranta, amma saboda banda girma da mutumci a idon ki ban isa ki fad'a min ba ko da wani abu da ku ke buk'ata."


Murmushi kawai ta yi tace "Allah huci zuciyar ka ranka shi dad'e, ai akwai hikima sosai a cikin hallitar kowane bawa da iyaye biyu, naga ba ka gari ne kuma kullum cikin aiki ka ke, ba ka da lokacin waya dani bare har mu yi magana da ta shafi d'an ka, shi ya sa ni kuma na mi shi duk wani abin da zai buk'ata, har kud'in makarantar ma na biya."


Duk da ya ji wani abu a zuciyar shi a game da ita, amma basarwa ya yi yace "Uhum." Kashe wayar kawai ya yi, take ya durmiya cikin tunani, Khadija kud'in da ya bata babu abin da za su mata, amma da su take buk'atunta har ta biyawa yaro kud'in makaranta, amma kuma Haseenah daya lodawa masu yawa yanzu haka zaije ya tura mata kud'i ne dan tace suna buk'atar kud'i, dan haka  ya kasa nutsuwa ya kira Aziza ya tambaye ta da gaske Haseenah ta na bata kud'in adaidaita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh yah Fodio, ta na bani na zuwa da dawowa, har da ma d'an na kashewa, kuma kullum fa sai mun siyi abinci in dai ranar girkin Khadija ne, kuma jiya masu karb'ar kud'in ruwa sun zo dole sai aunty Haseenah ce ta basu."


Duk da ya yarda da Aziza dan abu d'aya suka fad'a amma Haseenah ba ta fad'a mi shi suna siyen abinci ba, haka dai ya sa Nura ya kawo mata kud'in sannan ya kira ya tambaye ta K'arin haske akan abin da Aziza ta fad'a, cikin marairaicewa tace "Kawai ba na so ne wani abu ya faru kuma ace ni ce sila."


"Shikenan to ya yi kyau." Ya fad'a ya na kashe wayar, wayar Khadija ya kira dan jin dalili, amma suna gama waya ta farko Aishatu ta kira ta tace ga ta k'ofar gida mai gadi na mata iskanci, dariya Khadija ta yi kafin tace ta na zuwa, Bilal ta aika sai gasu sun shigo tare, Aishatu budurwace da ke da larura ta iska, hakan ya sa komai nata daban ne, fad'a da masifa kamar shan ruwa ne a wajen ta, tunda su ka shigo tare da Bilal ta ke zagin mai adaidaitar da ya kawota wai yace sai dai ta bashi arba'in ita kuma ishirin ta bashi, hakan ne ma ya sa sam Khadija ba ta ji kiran Usman ba saboda wayar na (vibration) ne, aifa nan hira ta b'arke suna ta yi kamar wanda aka jonawa lantarki, tunda wuri kamar yanda ta saba suka shiga girkin yamma, kuma yau ta yi niyyar yin waina dan akwai wa abokanan mahaifin ta, saboda sabo ya sa ba wani wahala tasha ba musamman kuma ga mai kamawa, sai salade da shima aka siyo mata suka gyara abinsu, Bilyamin ta kira ya kai wainar in da ta zubawa Haseenah na su tace ya kaii, da sauri Aishatu tace ya jirata su tafi tare ta ga amarya, nan fa gaban Khadija ya shiga dukan uku uku, dan ba lallai ta shiga lafiya ta fito lafiya ba, k'aramin aikinta ne ta k'arewa Haseenah kallo tace au dama wannan ce amaryar? Saida Khadija ta rik'e hannunta tace "Dan Allah idan ki ka je ku gaisa kawai ki juyo ki dawo, ba na son tashin hankali ko kad'an."


"Wai amaryar 'yar akuya ce kenan? To ai sai ki fad'a mata ki na da irin mu 'ya'yan busurai, mu za ta wa iskanci?" Cewar Aishatu har tana gaggawar tafiya, rik'e ta Khadija tayi tace "Ni fa ban fad'a mi ki haka ba, kawai dai ku gaisa ki juyo ki dawo, kar ki ce za ki tsaya wani abun da bai shafe ki ba."


Saida ta fizge hannunta tace "Naji dallah."


"Kinyi alk'awari?" Cewar Khadija ta na binta da kallo, k'ala ba tace ba ta bi bayan Bilal su ka shiga, Bilal ne ya yi sallama amma shiru, bubbuga k'ofar ya yi ya sake jin shiru, sai Aziza ce ta lek'o daga sama ta hangeshi tace "Bilal ga auntyn ka nan sama."


Daga nan yace "Abinci ne na kawo mu ku."


"Kawo nan." Cewar Aziza, kallon Aishatu ya yi tace "Muje saman na ganta, ai ko saman bakwai take sai na ganta yau."


Can suka nufa, Bilal na isa ya aje abincin sai aishatu da ke k'arewa Haseenah kallo ta hakimce akan kujera ta na latsa waya, kallon Aziza ta yi tace "Ke na ganeki k'anwar Usman ce ko?"


"Eh, ina wuni." Cewar Aziza wacce ba tun yau ba tasan Aishatu farin sani, mayar da kallonta ta yi ga Haseenah ta na wani murmushi tace "...



*Allah fidda A'i daga rogo.*

15/02/2020 à 13:58 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *26*



"Wai ke ce dama amaryar da ya yi? Kai, amma dai wallahi maza ba su da tabbas, yanzu shi dan Allah rufe mi shi ido ki ke kayi? Ko kuma tallarki aka mi shi?"


Bilal ne ya kalle ta yace "Aunty Aishatu mu tafi ko."


Bushewa ta yi da dariya tace "Bilal barni na k'are kallon amaryar Baban ka, wannan mace haka sai kace kaza ta ga wuk'ar yankanta."


Wata dariyar ta saka mik'ewa Haseenah ta yi da nufin magana sai Aziza ta rik'e hannun ta, girgiza mata kai ta yi alamar a'a ta rabu da ita, ganin hakane ya sa Aishatu cewa "Da kin barta ta fad'i abin da ke ran ta ai kar ta zama ajalin ta, ni ma saboda ba zan iya yin gulmarki bane ya sa na fad'i abin da ke raina tun a gaban ki."


Iza k'eyar Bilal ta yi tace "Mu tafi kai yaro ka ji, Allah ya tsigewa Babanka rigar wahala, wannan mata kafin ya sa k'asusuwanta su cika ai sai mai kampanin gidan shinkafa na *oriba* ya san da zaman shi."


Ta na wucewa Haseenah tace "Ita kuma wannan mahaukaciyar fa? Wacece ita?"


Ajiyar zuciya Aziza ta sauke tace "Hum! Cousine d'in Khadija ce, mahaukaciya ta sawa a gidan gaba, wallahi da kin biye mata ina tabbatar mi ki yau a gidan nan sai kinga motar masu kashe gobara."


Tab'e baki ta yi tace "Kin dai gani Aziza da idon ki, duk wanda ya zo gidan nan wajen ta sai ya zo ya ci mutumci na, ba na shiga sabgarta amma ita sai ta san yanda ta yi ta tsokane ni, yanzu wannan da me ya yi kama?"


"Ki yi hak'uri dan Allah ki rabu da ita, can aniyarta ta koma mata." Cewar Aziza, Haseenah ce tace "Mu sauka k'asa kawai dan magriba ta gabato."


"Gaskiya kam." Aziza ta fad'a ta na d'aukar kwanon abinci ta na fad'in "Ta mayar da mu mabarata k'arfi da yaji, in dai ta yi abinci ran alhamis da juma'a to ranar za mu samu abinci, saboda ta na yin abincin da take rabawa mutanen ta, shi ma fa ba kullum ba sai taga dama."


Kallon ta Haseenah ta yi ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "To ai saboda ki na gidan a wannan ranakun shi ya sa ba na iya zubar da shi, sai kin fita kad'ai na ke samun wannan damar."


Tunda Aishatu ta koma take mita akan amaryar Usman, har akayi sallah magrib da isha'i su ka ci abinci, anan take tambayar Khadija za ta je bikin *Saratu* (kamar jikanya take ga mahaifiyar Khadija), zaro ido ta yi tace "Wai yaushe ne bikin Saratu?"


"Jibi mana." Cewar Aishatu tana shirgar wainar ta, cike da mamaki Khadija tace "Wallahi na manta, kuma Mama ba ta sake tuna min ba, amma dai bara na kira Abban Bilal na fad'a mi shi yanzun nan, dan zan iya mantawa, kuma tafiya ce da ba nan cikin gari ba akwai buk'atar ya sani da wuri."


Saida ta d'auki wayar ta ga kiran shi har uku ba ta d'aga ba, maida kiran ta yi kamar kuma jira ya ke sai kuwa ya d'auka dan ya zazzage kwandon bala'i, cikin sa'a sai Aishatu ta d'aga murya tace "Gaida min shi, ki ce na ga amaryar shi ina taya shi murna."


Dariya Khadija ta yi tace " bara na baki sai ki fad'a mi shi." Bata wayar ta yi, kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu ya sa su ka dinga hira ta na tsokanar shi shima haka kafin Khadija ta karb'i wayar, ta na d'orawa a kunne tace "An wuni lafiya saraki."


"Lafiya lau, anga damar d'aukar wayar?" 


Murmushi ta yi tace "Ka yi hak'uri, ina aiki ne a lokacin ban lura ba, yanzu ma na d'auko wayar ne zan nemi izinin ka sai na ga kiran."


"Izinin me kuma?"


"In ba ka manta ba wata biyu da ya wuce na baka goron Saratu? To bikin ne ya taso yanzu ni har na manta ma saida Aishatu ta tuna min."


"Yaushe ne?"


Ta na wasa da yatsunta tace "Jibi, ranar da su Bilal za su koma makaranta."


"Amma ai ba cikin gari bane?"


"Eh hakane."


"Shikenan, Allah ya tsare, zan kira Mama na tambaye ta shirye shiryen tafiyar." Ya na fad'in haka ya datse kiran, ita kam bata wani damu ba tunda dai ya barta, sai wajen tara na dare Khadija ta ma Aishatu kyautar fitar hankali kafin ta bar gidan.



B'angaren Haseenah kam tunda ta ci wainar nan dayawa sai ta tayar mata da zuciya ta dinga kelaya amai, sosai ta galabaita har Aziza ta tashi hankalin ta, dare na sake yi kuma sai zazzab'i da ciwon kai, Hajia su ka kira aka fad'a mata tace su shirya su fad'awa Khadija tunda ita ta iya mota saita kai ta asibiti, ira kuma za ta same su asibitin yanzu, har Aziza za ta tafi wajen Khadija kawai Haseenah ta rik'e hannunta tace kar taje, "Me ya sa to?" Ita ce tambayar da ta mata.


Cikin galabaita tace "Kawai ba na so tasan halin da na ke ciki, ko ta taimaka min ba dan Allah bane, dan ta samu mafakar da za ta yak'eni ne."


Da mamaki tace "Amma Haseenah dan ta kai mu asibiti miye a ciki?"


Kallonta ta yi tace "Aziza in za ki samo mai adaidaita ki samo, in ba za ki sami ba ki bar shi, yanzu haka da yan uwa na za su san ina cin abincin ta wallahi da sun tofa min yawu, mutum fa ba abun yarda bane, kuma ke kinfi kowa sanin ta ai."


"Gaskiya ne kuma." Cewar Aziza jiki a sanyaye, haka suka shirya suka fita a hanya suka yi sa'ar samun adaidaita su ka hau, asibitin kud'i aka kai da ke nan kusa da su ta *Clinique Alheri*, tun kafin su ka likitan Hajia ta k'araso ta na waya da Usman da ta sa aka kira shi take fad'a mi shi, aifa kamar ya taso ya zo ya ke ji ance amarsu ba lafiya, ko da su ka ga likita ya mu su albishir da ta na da ciki amma k'arami, nan dai aka mata allura tare da bata magunguna, bayan sun biya kud'i tsagaga su ka dawo gida da rankiyar Hajia, kwance Haseenah ta yi Hajia ta kalli Aziza tace "Da na ce ku fad'awa Khadija ta kai ku me ya sa ba ku mata magana ba ku ka hau adaidaita?"


Aziza ce "Hajia zan..." Da sauri Haseenah ta mata alama da hannu kan ta yi shiru, duk da Hajia ta gani amma da tace "Me ye ta yi shiru?"


Cike da tausayi tace "Hajia kawai ku bar maganar, tunda dai gashi mun tafi kuma mun dawo lafiya."


Shiru Hajia ta yi da mamaki, kallon ta tayi tace "Kun ci abinci?"


Kallon juna su ka yi sai Haseenah ce tace "Wallahi wata waina ce aunty Khadija ta aiko mana, ko gama ci banyi ba zuciyata ta tashi sai amai."


"Yanzu ta na aiko mu ku da abincin kenan?" Cewar Hajia ta na kafesu da ido, Aziza ce tace "Hajia bata aikowa fa, sai kamar irin wannan ranakun alhamis ko juma'a, shi ma sai in ya na girkin ta ne."


Kallon Haseenah ta yi tace "Ki fad'awa Aziza idan za ki ci wani abu mai sauk'i saita d'ora mi ki kafin ki sha magani, ni yanzu gida zan tafi dare ya yi."


"To." Ta fad'a ta na yamutsa fuska, Hajia na fita tasa Aziza ta d'ora mata zallar shayi tasha kafin tasha magana, kiran ta Usman ya yi suka dinga hira har saida tace za ta yi bacci, Hajia kuma na fita ko kallon b'angaren Khadija ba ta yi ba saboda ran ta ya sake b'acewa a game da ita, adaidaita ta hau ta koma gida, ba ta yi nauyin baki ba wajen fad'awa malam abin da ake ciki, sai dai shi baiji komai ba a zuciyar shi, sai dai yafi mayar da hankalin shi kan Usman da ya ke d'an ganin canji a tare da shi yanzun, da haka suka kwanta da fatan ganin wayewar gari lafiya.



Tunda safe Hajia ta had'a abin kari ta bawa Nura ya tafi ya kai ma su Haseenah, a lokacin Khadija na madafa da doguwar rigar bacci a jikinta Nura ya shigo, da kallo ta bishi har ya wuce b'angaren Haseenah kai tsaye kamar yanda Hajia ta fad'a mi shi, amma bai jima ba ya dawo dan gaisawa kad'ai ya yi da Haseenah ko jiki bai tambaye ta, falon Khadija ya lek'a sai Bilal kwance akan kujera, baisan da shigowar shi ba yace "Yarima barka da safiya."


Juyowa ya yi yace "Tonton Nura, ina kwana?"


"Lafiya lau, ka tashi lafiya?"


"Lafiya lau."


Ba tare da ya shigo ba daga k'ofar yace "Ina maman ka?"


"Ta na madafa." Ya fad'a da ma sa nuni da yatsarshi, hannu ya d'aga ma sa yace "Ina zuwa to." Madafar ya nufa da sallama, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata, kowa ya shigo gida ke ya tarar, ko mai gida sai kin lamunce ya shigo, sannu da aiki."


Da wuk'ar hannunta ta nuna shi tace "Bansan dad'in baki, fad'i abin da ka ke so na ma ka."


Cikin had'e rai yace "Kamar ya? Ban gane me ki ke nufi ba?"


Kallon shi ta yi tace "Ai dana gan ka gidan ka to da dalili, bugu da k'ari kuma gashi har da min wani kirari kamar marok'i."


Dariya ya yi yace "Lallai uwar gida daban ki ke da kowace mace, cikin sakan biyar har kin fahimci akwai abin da na ke buk'ata ki min ko?"


Hararan wasa ta mi shi tace "Yau da gobe ai bata bar komai ba, karfa ka manta a hannu na ka k'arasa girma."


B'ata rai ya yi yace "Haba kema, basar mana."


"To naji, me ka ke so."


Saida ya matso kusan ta yasa hannu ya na cakurar dankalin da take soyawa ya na jefawa baki yace "Aunty Khadija maganar fa mai mahimmanci ce."


"Uhum, ina jinka."


Saida ya saci kallon ta yace "Aure na ke so."


Da sauri ta dakata daga abin da take ta kalle shi tace "Me? Aure fa ka ce Nura?"


"Eh mana, ko ban isa ba?"


Zaro ido ta yi tace "Ni bance ba, amma dai me zai hana ka bari kad'an k'ara mallakar hankalin kan ka, Nura aure fa ba iya abin da kawai ka ke tunani bane."


Kamar zaiyi kuka yace "To ni me na ce mi ki ina tunani?"


Mirmushin gefen labb'a ta yi tace "Ba ma irin wannan hirar da kai, amma na tabbatar ba zai wuce wutar balaga ce ke fizgarka ba."


"Kinsan me?" Ya fad'a ya na rik'e k'ugu, "A'a sai ka fad'a."


"Mijin ki ma haka yace da na masa magana, wai na bari har nan da ko shekara biyu, a gaskiya kuma ni ba zan iya ba, aunty Khadija wallahi gaskiya na ke fad'a mi ki, na fad'awa su Baba sunce ba ruwansu na fad'awa Usman tunda shine zai min auren, shi kuma yace ba yanzu ba."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu me ka ke so na ma ka?"


Cikin sigar rarrashi yace "Ki daure dan Allah ki taimaka min ki ma sa magana, wallahi nasan zai saurare ki, ni fa har mun gama magana da iyayen yarinyar ma, sunce kawai na turo manya na."


"Babbar magana." Cewar Khadija, "Haba wannan k'arama ce, yanda na san ki da Abban yarima ai sha yanzu mgani yanzu ne."


"Sanin da ka yi mana ada ne wannan." Cewar Khadija a zuciyar ta.


Basarwa ta yi tace "Shikenan kar ka damu, zan jaraba na gani, amma ba lallai ya amince ba tunda har ya nuna bai yarda ba tun farko."


"Zai ma amince in dai ki ka masa magana wallahi." Da haka ya bar gidan ita kuma ta shiga tunanin yanda za ta fara tunkarar sabon Usman d'in ta da maganar nan, ba ma lallai ya saurare ta ba bare har ya amince da abin da Nura ke tsammani.


Ta na gama abin karin ta bawa Bilal na su Haseenah ya kai mu su, suma ko da su ka kammala suka fito farfajiyar gida, Bilal na yawo da moton shi a tsakar gidan Khadija zaune da waya ta na tunanin ta kira ko karta kira, ta na haka sai kiran shiya shigo wayar ta, yau ma mamaki ta yi ganin kiran shi, hakan ya sa ta d'auka ta aza a kunne, ba sallama bare gaisawa yace "Na kira Hajia akan maganar tafiyar nan, sai ki shirya da wuri ki same su can gida dan sun ce Naseer ne zai kai su."


"H...hello." Ta fad'a da sauri saboda jin zai katse kiran, cike da k'aguwa yace "Ina ji? Lafiya?"


Cikin fad'uwar gaba tace "Lafiya lau, dama ina son yin magana da kai ne."


"Magana akan me kuma?"


Murya k'asan mak'oshi tace "Nura ne dama ya same ni akan maganar aure da ya ke so, amma yace ka ce ba yanzu ba, shine..."


"Shine za ki sani na yarda na mi shi auren ko me?" Ya fad'a cike gatsali, kamar ta kashe wayar sai kuma ta daure tace "A'a ba haka bane, ya fad'a min ne saboda shi a  tunanin shi Khadija tafi k'arfin komai a gurin Abban Bilal, ya zo da buk'atar shine gare ni saboda sanin da ya mana ina iya shawartarka akan al'amura har na cikin gida ma kuma ka yi aiki da ita, ya fad'a min ne ba dan tunanin zan saka ka dole ba, sai dan cewa kamar ina da mahimmanci da kima a wajen ka da zan iya nemawa wani alfarma a wajen ka, sannan ni a gani na ba wani abu bane idan an mi shi auren, matashi kamar Nura ya kalli iyayen shi yace ya na son aure, ina ga a mi shi auren shi yafi kwanciyar hankali."


Har k'asan zuciyar shi maganganunta sun ratsashi, amma saiya dake yace "Me Nura ya sani a game da aure da za ayi mi shi? dan ya na da abinyi ba shi ke nuna zai iya rik'e mace ba."


"Amma ai ko neman auren ya tafi daga cikin tambayoyin da za'a masa akwai son sanin abin da yake, hakan kuma nasara ga d'an uwan mu da ya zamana ya na da aikin yi, ko ba komai zai ciyar da ita, zai shayar da ita da tufatar da ita, sannan ina da yak'inin zai kula da ilimin ta ko wane iri ne, sannan zai iya biya mata buk'atar ta."


Saida taji sautin sauke ajiyar zuciyar shi a kunnenta kafin yace "Bansan me ya fad'a mi ki haka ba da ki ka yarda da shi, gashi har kinsa nima na ji banda wata hujjar hana shi auren, ki fad'a ma sa na amince, amma dole ya jira ni na dawo sai ayi duk wacce za ayi, idan kuma ba zai iya jira ba sai ya turaki ki nemo masa auren."


Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam dad'i ne ya sata bushewa da dariya saboda abin da ya fad'a a k'arshe, wayar Nura ta kira ta fad'a ma sa yanda su ka yi da shi, sosai ya yi murna tare da binta da addu'a Allah ya barta da yayan su, suna gama waya ta ji wayar Bilal na k'ara, hannu ya sa a aljihu ya fito da ita ya d'auka, take ta fahimci Abban shi ne ya kira shi, suna nan zaune Hajia ta shigo gidan da sallama saboda ganin su, da farin ciki Khadija ta mik'e ta tarbe ta tana mata sannu da zuwa su na gaisawa, Bilal ma saida su ka tab'a hira irin ta kaka da jika kafin ta kalli Khadija tace "Ina yer uwar ta ki ta na ciki?"


"Eh Hajia su na ciki."


Nufa b'angaren ta yi ta na fad'in "Bara mu gaisa."


"A fito lafiya." Cewar Khadija, ta na shiga su ka gaisa kafin ta tambaye ta sun ci abinci ai? Eh, shine amsa da su ka bata, kallon Aziza ta yi tace "Ke ki zauna gidan to, ke sai ki tashi mu koma asibitin."


Dama a shirye take, hijabi kawai ta saka suka fito tare da Hajia da ke rik'e da katin likita a hannu, "Hajia har kun fito? Gida za ku tafi ne?"


"A'a." Ta fad'a kai tsaye, ganin Haseenah tare da ita ya bata mamaki, musamman da taga ta na gaba ta na binta, "Hajia lafiya kuwa? Ko ba ta da lafiya ne?"


Sai kawai Hajia ta ji haushin wannan tambayar, bud'ar bakinta cewa ta yi "A'a lafiyar ta k'alau, akwai in da za mu ne."


Da ido kawai ta bisu ta na mamakin kamuwar Hajia ita ma da wannan cuta ta 'ya'yan ta, ido kawai ta zuba mu su har suka dawo lokacin ta na madafa ta na girki, lokacin ne kuma 'yan uwan Haseenah da ma 'yan uwan Usman d'in suka fara zuwa ganin ta, ita dai ta na kammala girki ta fitar mu su ta bayar aka kai, sai dai ta yi niyyar ko ciwon ajali ne Haseenah keyi ba za ta je ta duba ta cikin mutane, tunda ta lura b'oyewa ake ba asa ta sani saboda tunanin wani abu.


Da yamma Haseenah ta karb'i girki, amma 'yan uwan ta ne suka shigar madafar suka yi yanda su ke so, sai dare su ka bar gidan Khadija ta shiga dan samun abin da za su ci, yanda ta ga madafar abin ya bata mamaki da dariya, saida ta gyara ta sosai kafin ta samu abin da za su ci, ko da su ka kammala suka kwanta abin su.



*Hummmmmmmmmm.*


Tunda asuba Khadija ta shirya tare da Bilal suka yi karin kumallo, sai da ta kira Usman tace ta na si ta aje Bilal a gida, amma sai yace "Me ye haka Khadija? Gidan nan fa akwai mutane, ya ki ke so ki nunawa yaron banbanci a zahirance."


"Shikenan ka yi hak'uri." Ta na fad'a ta kashe wayar ita ma, zuwa k'arfe *07:15* suka fito, saida su ka shiga d'akin Haseenah da sallama suna falo ita da Aziza ita ma ta na shiri, "Antashi lafiya?"


"K'alau." Cewar Haseenah, Aziza ce tace "Ina kwana."


"Lau." Cewar Khadija, kallon su ta yi tace "Dama zan tafi Tessaoua ne wajen biki, na kulle d'aki na, ga kayan Bilal idan an dawo da shi sai ya canza wannan, sai na dawo."


Hannun shi ta kama su ka fita, Aziza kam cewa ta yi "Ka ji matar nan sai ka ce akwai bawanta anan d'in."


"Ke kuwa miye a ciki? Bilal ai d'an mu duka, Allah dai ya kaita lafiya."


Saida ta gama shiri suka karya tace"Idan na tafi zan tsaya gida na wuni, na san dai saida dare ko na dawo gida."


Da haka su ka yi sallama ita ma ta tafi makaranta, Khadija ma ko da suka isa Ashir ne ya kai su makarantar duka, su kuma zuwa tara Naseer ya d'auke su suka tunkari *Tessaoua*.



*Me kuma zai faru yanzun?*

16/02/2020 à 13:20 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *27*



Sha biyu Ashir ya d'auko su Bilal, suna hanya Khadija ta kira shi su ka gaisa, gida aka aje shi kafin suka wuce, k'ofa mai gadi ya bud'e masa ya na fad'in "K'aramin Alhaji har an taso?"


"Eh, ya aiki?" Ya fad'a da fara'a, shi ma da fara'a ya mayar masa da "Alhamdulillah."


Ciki ya shiga kai tsaye kuma b'angaren Haseenah ya wuce tunda yau ita ce maman shi, sallama ya dinga rabkawa amma ya ji shiru, saida ya bud'a k'ofar falon ya shiga kad'ai ya ga takalma alamar bak'i amma kuma ba kowa a falon, kujera ya samu ya zauna ya ciro wayar shi ya na dannawa da chocolat a hannu ya na sha, minti talatin ya d'auka a falon sai dariya da shewar su Haseenah ita da Zeinab wacce daga makaranta take ita ma ta ratse nan, tashi ta yi ya nufi d'akin na ta ya k'wank'wasa k'ofa duk da bud'e take, shiru su ka yi kafin tace "Waye?"


A hankali ya yaye labulen ya kalle ta yace "Aunty sannu, ni ne."


Fuska a d'aure tace "To, yaushe ka shigo gidan?"


"Na jima zaune a falo, yanzu ma dan na ce ku bani kaya na ne zan canza wannan."


"Ka je idan na fito zan baka kayan." Ta fad'a ta na mayar da hankalin ta kan Zeinab, har ya juya zai fita tace "Kai zo nan."


Dawowa ya yi jiki a sanyaye ya tsaya gaban ta, kud'i ta mik'o mi shi tace "Ka wuce maza kaje ka siyo min katin waya na airtel."


"To." Ya fad'a ya na karb'ar kud'in ya fice, ta k'aramar k'ofa ya bi zai fice mai gadi yace "K'aramin Alhaji fita za ayi?"


"Eh." Kawai ya fad'a a tak'aice ya na zura duka hannayen shi biyu cikin aljihun doguwar rigar shaddar shi wacce ka na gani kasan ta ji kud'i, a k'afa ya taka har ya iso bakin titi, ya jima tsaye kafin ya samu ya tsallaka saboda akwai ababen hawa sosai a wajen musamman da ya zama ranar farko ta komawa makaranta, siyowa ya yi ya dawo gidan ya kawo mata, falo ya dawo ya zauna amma bai jima ba aka fara kiran sallah, tashi ya yi ya fita a panpo na daf da shigowa gidan ya yi alwala ya tafi masallaci, daya dawo wajen mai gadi ya zauna shi ya na sauraren redio shi kuma ya na kallon hanya, tsawon lokaci ya d'auka nan zaune kafin ya ji cikin shi na neman agaji, cikin gidan ya koma ya samu su Haseenah har yanzu a d'aki amma su na cin soyayyen k'wai da indomie, ga lemu a gefe suna korawa mai sanyi, cikin muryar tausayi yace "Aunty abi..."


Kallon da ta ma sa ne ya sa ya yi shiru, Bilal yaro ne miskili da bai cika magana ba, in kaji yawan maganar sa to da iyayen sa ne idan suka had'u, jin ya yi shiru ya sa tace "Me ye kuma? Kayan ka na ce ka jira ni na tashi sai na d'auko ma ka, ka gansu can gefen gado, banyi niyyar tashi ba yanzun."


Juyowa ya yi ya sake fitowa daga d'akin, Zeinab ce tace "Kin bashi abincin shi?"


"Wannan d'in?" Ta nuna Bilal da ya fita da yatsa, d'orawa ta yi da "Ai munafiki ne da ki ke ganin shi kamar uwar shi, ba sa cin abinci na fa, yanzu in d'auka in bashi wani abu ya faru ace ni ce, yanda duk na ke k'ok'arin jingina mata laifukan nan ai kinga kashina ya bushe, kuma wallahi ni har ga Allah ma na manta da ya na gidan."


Da haka su ka ci gaba da hirar su Bilal kuma na fita ya samu mai gadi shi ma ya gaji da jira ya siyo wake da shinkafa, a hallitar Bilal bai tab'a cin wake da shinkafa ba, amma yau da ya ke jin yunwa sosai kuma mai gadi yace su ci, sai kawai ya sa hannu su ka ci abincin tare, saida su ka gama su ka sha ruwa, sun d'an fara tab'a hira Bilal ya ji cikin shi ya fara k'ullewa, a hankali ya fara dafe ciki ya na d'an matsa shi, amma sai abun ya fara k'amari sosai, mik'ewa ya yi kawai ya koma cikin gida kai tsaye madafa ya nufa, jar kanwa ya samu ya samu kofi ya sa ruwa ya jik'a yasha kamar yanda wani lokacin idan cikin shi na ciwo maman shi ke bashi, har zai fito sai ya ji ciwon ya fi na baya ma, dafe ciki ya yi sosai ya na murd'awa har ya sulale k'asa, jin azabar ciwon na k'aruwa ya sa shi tafiya wajen Haseenah, falo ya same su wannan karan su na kallo ana hira, a dafe da ciki ya tsaya gaban ta yace "Aunty ciki na ke ciwo, dan Allah ki bani magani idan ki na da?"


A wulak'ance ta kalle shi tace "Cikin ka kuma? To miye a ciki ya wuce kayan zak'in da kullum uwayen ka ke siyo ma ka ne ka na had'iya, sune kawai za su tambaye ka, ni ba na da magani."


Ganin idon shi cike da hawaye ne ya sa ta d'auki kud'i ta mik'a mi shi tace "Je ka siyo maganin bakin titi sai ka sha."


Karb'a ya yi ya fita ya na duk'e-duk'e, mai gadi na ganin haka yace "K'aramin Alhaji lafiya ka ke, ya na ga ka na dafe ciki? Ko ciwo ya ke ma ka."


Cike da k'aguwa yace "Ba komai." Ya wuce abinshi, da k'yar ya kai kan shi shago ya siyo maganin ya juyo ya dawo, madafa ya zarce ya samu ya sha maganin sannan ya wuce d'akin Haseenah, kwance ya yi bawan Allah akan kujera sai Haseenah tace ai ya sauko daga kan kujera ko ubanshi bai tab'a kwance anan ba, k'asa ya kwanta babu ko tapi (carpet) shinfid'e in da ya ke.


Ko dare Haseenah ba ta yi girki ba ta na hutawar ta, Bilal na gefen ta kwance ya galabaita dan babu abin da ya yi sauk'i daga ciwon cikin, sai ma kumbura da cikin shi ya yi kamar zai fashe, hakan ya sa zazzab'i sauko mi shi mai zafin gaske, yamma lis ta kalli Bilal da ke ta rawar d'ari tace "Kai zo amshi nan ka karb'o mana salade wajen mutumin can na tsallaken titi."


Da k'yar ma ya iya bud'a idon shi ya kalle ta sunyi jawur, rarrafawa ya yi ya zura mata hannu ya karb'i kud'in da take mik'o mi shi, da wuya ya iya mik'ewa tsaye ya fita sai rangaji ya ke, k'wafa ta yi tace "Munafiki, ciwon k'arya ne ka ke k'irk'irowa saboda kawai ka jaza min masifa."


An fara kiran sallah magriba kenan sai ga Khadija ta sallamo gidan, daga jakar ta sai ledar da tayowa d'an gudaliyar ta tsaraba, kai tsaye  b'angaren ta ta fara bud'awa ta shiga, uwar d'aki ta shige ta cire kayan jikin ta ta saka doguwar riga ta atamfa, lokacin kuma Aziza ita ma ta sallamo gidan dan Hajia tace ta zo ko aiki ta kama ma Haseenah, zaune ma ta same ta tace ba ta d'ora komai ba, amma ta bada a siyo mu su salade su ci, Khadija kuma jin shiru ba motsin d'an gudaliya ya sa ta sallamo falon Haseenah, "Sannun ku da hutawa."


Haseenah da gabanta ya shiga fad'uwa dan ta d'auka ma can za ta kwana, Aziza ce kad'ai tace "Sannu aunty Khadija, har kin dawo?"


"Na dawo yanzun nan, ya gida?" Ta tambaya ta na kai kallon ta kowace kusurwa na falon, kallon Aziza ta yi tace "Wai ina Bilal? Ko ba'a dawo da shi ba."


Cikin rashin sani Aziza tace "Eh...to, ban dai..."


Jin kakarin amai a k'ofar d'akin ne ya sa Aziza yin shiru yayin da Khadija ta fita da sauri dan ta gane ko muryar waye, da sauri ta rumgumo shi jikin ta duk da aman da ya ke bulalowa, take idon ta suka kawo ruwa ta kalle shi tace "Bilal, me ya same ka? Me ka ci ka ke amai haka? Lafiya?"


Da k'yar ya iya kallon ta da ido dishi-dishi cikin muryar galabaita yace "Mummy, ke ce? Ki kai ni likita Mummy, ciki na ciwo ya ke."


Kuka ta fashe da shi ta manna kan shi a k'irji kamar za ta bashi nono tace "Bilal me ya same ka? Halan ka ci wani abu da ya b'ata ma ka ciki?"


Shiru ya yi sai numfashi da ya ke saukewa na wahala, fitowar su Aziza da Haseenah ne ya sa ta kalle su tace "Na d'auka za ku kula da shi ba sai na ce na bar amanarshi a hannun ku ba, amma shine ku na kallon shi a wannan halin, ya yi kyau, ki bani makullin mota na kai shi asibiti." Ta fad'a ta na kallon Haseenah.


Cike da gadara Haseenah tace "Ki yi hak'uri, gaskiya ba zan iya baki makulli ba, ko da ya bar shi a hannu na baice na ba ki ba, cewa ya yi idan buk'atar aiki ta tashi da mota sai ayi, kuma akwai wanda zai dinga fita da su."


D'auke kan Bilal ta yi daga k'irjin ta cikin hushi ta mik'e tsaye tace "Ina tunanin na jima da fad'a mi ki ba na so ana min wasa da d'ana, wallahi ba ke ba ko Usman ne ba zan lamunci ya min wasa da lafiyar shi ba bare ke, domin kuwa har yanzu shine kad'ai gare ni, shi kad'ai na mallaka a duniya sab'anin Usman da zai iya haifar wasu yaran da wasu mata, misali ke, dan haka ki ban makullin mota yanzun nan kafin kisa hankali na ya bar jiki na miki dukan mutuwa a gidan nan, kinga sai ayi biyu kenan dan na fahimci so ki ke ki kashe min d'an nawa."


Jin haka ya sa Haseenah juyawa ta koma falo, da sauri Khadija ta biyo bayan ta tasha gabanta ta shak'i wuyan rigar ta, janta ta yi har saida ta kai ta d'akin ta ta wurga ta kan gado tace "Maza tashi ki d'auko makullin ki bani."


Haseenah da ta ji mararta ta d'aure kasa tashi ta yi sai dafe mara, hakan ne ya sa Khadija cire d'an kwalin atamfar dake kan ta ta d'aure k'ugu da shi tace "Na rantse mi ki da Allah idan ba ki tashi kin d'auko min ba ko, wallahi gidan nan sai dai ya kama da wuta amma banga wanda ya isa ya shiga tsakani na da ke ba, Haseenah yaro na ne fa kwance babu lafiya, ga abin hawa a cikin gida kuma na iya sarrafa shi amma ki ce ba za'a hau ba, ba dan larura ce ba ma ni ko kallon motar na sake yi bare har na yi sha'awar hawan ta, dallah ki tashi ki d'auko min."


Jiki na rawa Haseenah ta mik'e da k'yar saboda sosai ta ke jin ciwo a marar ta, d'aukowa ta yi ta mik'a mata ta fizga ta juya za ta fita tace "Lokaci zai zo da za ki gane mahimmancin d'a da kuma zafin haihuwa."


Ta na fitowa k'ofar d'akin ta yi karo da Aziza da ta k'i shiga saboda tsoro, saida ta kwance d'an kwalin ta ta d'aura akai ta kalli Aziza da kyau tace "Aziza ba ni ki ka cutar ba, kan ki kika cutar, ba ni ki ka azabtar ba, d'an ki kika azabtar, hak'ik'a na ji ba dad'i a zuciya ta, amma ki sani bai kai wanda d'an d'an uwan ki ya ji ba, wannan yaron ko d'an mak'wabta ne ina tunanin zai iya samun tausayin ku a matsayin ku na 'yan adam kuma mata masu d'aukar ciki da haihuwa, amma kash an rasa wannan tausayin daga gare ku ba dan komai ba sai dan kawai ku na so wai ala dole sai kun cuzguna min, to bari na tuna mi ki wani abu, Bilal d'an ki ne domin kuwa ciki d'aya ku ka fito ke da mahaifin shi, Aziza rayuwa ba ta da tabbas, watak'ila wannan yaron da ki ke nunawa k'iyayya yanzun sai kin fini cin moriyar shi ni da na haife shi, idan ki na ganin kamar zanji zafi saboda kun cuta mi shi, to ki sani fa ku sai kun fini cutuwa, domin wannan yaron d'an uwanku ya na son shi fiye da komai a rayuwar shi, sannan abu d'aya da ku ka manta shine, ko a makaranta ana kiran shine da sunan *Bilal Usman Ali* ba wai *Bilal Khadija*, da yau mahaifin shi zai fad'i ya mutu, to ko shakka babu ke d'in nan Aziza zaki fini iko da shi ta wani b'angaren, da ace yau zanje nemawa Bilal aure a wani gidan, daga cikin tambayar da za'a mana ita ce *ina dangin mahaifin shi*? Domin kuwa kune shak'ik'an shi, kuma wallahi ina tabbatar mi ki ke d'in nan kawai idan na nuna a matsayin k'anwar mahaifin shi zai iya sawa a bamu aure, dan haka ku farka daga baccin da ku ke, duk abin da kukawa Bilal zai koma kan ku ne da d'an uwanku, ke ma kuma mace ce, nan da wani lokaci za ki yi aure kije gidan miji, ba zan mi ki fatan samun matsala a gidan auren ki ba, amma zan so ko na wuni d'aya ne ki fuskanci irin rayuwar da na fuskanta a dalilin ku, kinsan me Aziza? Na fi jin zafin juyawar bayan ki a kai na fiye da sauren 'yan uwan ki, kinsan me ya sa? Saboda ke ba baya kad'ai ki ka juya min ba, har da cin amana da yaudara, Allah ya ganar da ku gaskiya, za ku gane waye ya mallake d'an uwan ku."


Da sauri ta juya ta koma kan Bilal da ke kwance k'asa har yanzu, da gudu ta d'auko mayafin ta ta d'auke shi tasa mota suka bar gidan, asibitin da aka kai Haseenah ta kai shi, saida suka ciri tikitin ganin likita kafin suka samu aiki, bawan Allah saida aka saka mi shi k'arin ruwa sannan ya sabu bacci, kan shi na kan k'afafun Khadija ta na shafa kan shi, hawaye ta ke saboda tunanin irin halin da d'an ta ya shiga saboda wata tsinanniya a cewar ta, Habeeb dake ta faman kiran wayar Bilal dan su gaisa ne amma ba'a d'agawa, hakan ya sa ya kira Khadija sai lokacin suka san abin da ke faruwa, kafin ki ce kwabo asibitin ta samu hallarar 'yan biyar da mahaifiyar su, iya abin da ta sani kawai ta fad'a mu su, saida Bilal ya farka a bacci ne ya kora mu su jawabin duk abin da ya faru tun daga zuwan shi gidan har wannan lokacin, kuka Khadija ta yi sai Mama ke bata hak'uri, haka dai dare ya yi ko da ruwan suka k'are aka sallame su suka koma gida.


*Bayan fitar* Khadija sosai Aziza taji ba dad'i tare da jin nadama, amma bata gama gane halin da take ciki ba taji ihun Haseenah daga d'aki, sosai Haseenah ke murk'ususu tana kiran cikin da marar ta, waya Aziza ta d'auka ta kira Hajia ta fad'a mata, ana sallah isha'i Hajia ta zo gidan dan ganin lafiya, amma ganin irin azabar da take sha ya sa ta tambayi dalilin abun, Aziza ba ta yi magana ba sai Haseenah ce tace Khadija ce ta yi niyyar kashe ta yau a gidan, saboda kawai tace ta bata makullin mota tace Usman bai yarda ba haka kawai, ran Hajia ne ya b'ace saida Aziza tace " Amma fa likita tace za ta kai Bilal da ba shi da lafiya."


Cikin b'acin rai Hajia tace "Daga haka kuma sai tace saita nemi kashe ta, yanzu dubi ta'asar da take shirin yi."


Kama Haseenah ta yi suka tashi aka tafi asibiti,  adaidaita na aje su suka shiga ciki, Aziza kad'ai ta lura da motar Khadija a k'ofar shiga amma banda su da basa hankalin su, saida akawa Haseenah éco aka duba cikin na ta, a cewar likitan "Cikin ta lafiyar shi k'alau, amma fa a kiyaye dan yanzu haka jijjiga ce ta sa take jin wannan ciwon, ayi hankali sosai in ba haka ba cikin biyu za ayi d'aya, ko dai cikin ya zube ko kuma ya bar mahaifarta ya koma bayan mahaifa, dan haka a kiyaye sosai."


Nan aka rubuta mu su magani za su  koma gida Aziza tace "Hajia kinga motar aunty Khadija har yanzu su na nan, mu shiga mu ga jikin Bilal mana." 


A tak'aice Hajia tace "In ke za ki shiga ban hana ki ba, ni ma ai marar lafiyar na kawo."


Ba dan ta ji dad'i ba suka wuce gida bayan sun siye maganin a pharmacie, Hajia da kan ta ta fad'awa Usman halin da ake ciki, kuma yanda take magana zai nuna ma ka cikin hushi take, shi ma dai tunzura ya yi har yace "Zan shigo garin gobe, ba zan yarda da wannan iskancin ba dan naga abun nata rashin mutumci ne."


"Ai kam dai gwara ka yi ka dawo, dan nima na fara gajiya da wannan al'amarin." Aziza da jikin ta ya yi laushi ce ta kalli Hajia tace "Amma Hajia fa makullin mota kawai ta amsa ta kai yaro asibiti, me ye laifi a ciki?"


"Yarinya ce ke Aziza, ba wai makullin kawai ta amsa ba, ta so ace tsotsayi ya gifta cikin jikin ta ya zube, dan haka gwara ya zo ya wa tubkar hanci."


Saida su Ashir suka rankosu har gida, canzawa Bilal kaya ta yi sannan ta kwantar da shi akan gadon ta, ita ma shirin baccin ta yi su ka kwanta bayan ta jima tana tofesu da addu'a.


*Washe gari da safe* Gidan kamar ana wani sabga, dangin Khadija sun hallara dan ganin jikin Bilal, dangin Haseenah ma da dangin Usman sun hallara dan ganin jikin ta, duk da kowa na b'angaren da ya kawo shi amma ka kan iya jiyo hayaniya ta ko ina, a lokacin ne kuma Usman ya diro garin ba dan ya shirya zuwa ba sai dan amaryar shi na wani hali.


*Allah kare k'aramin yak'i.*

17/02/2020 à 21:31 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *28*



Saida ya fara ganin Haseenah ya tabbatar komai lafiya kafin ya nufo wajen Khadija da nufin bala'i, ya na shigowa falon sai ya yi sanyi ganin mutanen dake d'akin, a hankali yake takawa ya na kallon Bilal dake k'afafun Mama ta na bashi magani, Khadija ma da mamaki take kallon shi kamar ba ta tab'a ganin shi ba, da sauri ya k'arasa ya zauna gefen Khadija ya na fad'in "Yarima, bashi da lafiya ne? Me ya same shi?"


Shiru Khadija ta yi sai Mama ce tace "Bashi da lafiya ai tun jiya, amma da sauk'i sosai."


Hannu ya zura ya kamo shi kamar d'an shekara biyar haka ya rumgume shi a k'afafun shi ya na shafa shi yace "Yarima ba ka da lafiya? Ya jikin na ka da sauk'i ko?"


Da kai kawai ya ma sa alamar eh, rumgume shi ya yi a jikin shi ya kalli Khadija yace "Amma ya akayi ba ki kira ni kin fad'a min ba?"


Cikin hushi tace "Saboda kai ne silar shigarshi wannan halin, kuma ma naga me za ki yi mana idan na fad'a ma ka? Tunda ba damuwa ka yi damu..." Da sauri Mama ta kalle ta tace "Khadija."


Kallon Mama ta yi ta na kumburo baki, Mama ce ta d'ora da "Subhanallah, Khadija haka ki ka koma magana da mijin ki? Ki na hauka ne?"


Shiru ta yi sai Usman da ke murmushi ya kalle ta yace "Me ya sa ki ka yi tunanin haka? Taya zan zama sila baya bana nan."


Shiru kawai ta yi saboda Mama ta mata magana, mik'ewa Mama ta yi ta d'auki gyalenta ta yafa ta d'auki jaka ta kalli su Naseer dake gefe kamar sun zo neman aure tace "To sai ku tashi mu tafi ko, ko kuma nan za ku tabbata?"


Mik'ewa su ka yi a tare da d'ai d'ai suka bawa Usman hannu su ka yi sallama kafin su ka fita, ta na ganin fitar su ta kalle shi tace "Dama na bar Bilal gida ne saboda umarnin ka, amma ka sani ba zan sake wannan kuskuren ba wallahi, tunda dai na gama lura matarka ba imani ne da ita ba, sannan daga yau wallahi ba zan sake d'agawa kowa k'afa ba, duk wanda yace zai min kan kara to tabbas sai nai masa na itace."


Mik'ewa ta yi saida ta zo gaban shi ta karb'i Bilal ta d'ora a kafad'a saboda k'arfin halin kafin ta nuna shi da yatsa tace "Da nace kowa ina nufin kowa ma, ba sauk'i a al'amarin."


Za ta juya ne taji sallamar su Hajia da sauren yaranta mata biye da ita, tsaye ta yi ta na kallon su har su ka k'araso su ka zauna, Hajia ce ta kalli Bilal da ke kafad'ar ta tace "Kai namijin duniya ya jikin na ka?"


Wani irin mamaki ne ya bayyana a fuskar Khadija ta sunkuya ta aje Bilal ta kalle ta da kyau tace "Hajia, ya jikin shi fa ki ke tambaya? Hakan na nufin dama kinsan ba ya da lafiya amma shine bai samu kimar da za ku zo ku duba shi ba tunda ku ka shigo gidan nan, tunda rana fa na ke iya jiyo hayaniyar ku a gidan nan, amma sai yanzu za ku zo ku tambaye ni lafiyar shi, hum, to ba ni ku ka wa ba, kan ku kuka wa."


Juyowa ta yi ta d'auki Bilal za ta wuce d'aki Aziza tace "Aunty Khadija ga kayan shi in ji Haseenah."


Juyowa ta yi fuska a had'e tace "Bilal na da kayan da a shekara baya saka su, ku mayar mata ta mayarwa da bokan nata tace ba ma so."


"Khadija, wai baki da hankali ne? Ke kad'ai ki ka fi kowa baki anan da za ki zaunar da mu ki na fad'a mana magana, so ko ke kice dole ke ce akawa laifi kenan bayan duk abin da ki ka aikata, me ki ka d'auke ni ne da har za ki tsaya ki na fad'awa 'yan uwa na magana kuma daga ciki har da mahaifiya ta, ko kinsan da hushin ki na dawo garin nan? Amma shine za ki nuna ke ce ma akawa laifi, to ya isheki haka, maza wuce ciki zan zo na same ki." 


Yanda ya ke maganar ne ya sa ta yi dariya tace "To ka had'iye ni mana kaga shikenan sai ka huta."


Ta na fad'a ba ta tsaya sauraren shi ba ta shige ciki da Bilal a hannu, tana shigewa Hajia tace "Haka kuma abin nata ya zama? Lallai mutum bashi da kama, yanzu waye zai iya cewa Khadija za ta yi abin da ta yi."


Rabi'a ce tace "Hum, dama ai sai anyi yunwa halin kowa ke fitowa."


"Gaskiya ne, yau na tabbatar da hakan." Cewar Hajia, Usman ne ya kalle su yace "Hajia ku yi hak'uri dan Allah, kar ku damu da abin da ya faru."


"Ya kar a damu, ba ka ji maganganun da ta fad'a mana bane, nan gaba mu ka san me za ta fad'a ko ta yi mana, za ta iya cewa ma Bilal d'an ta ne ita kad'ai."


Mik'ewa su ka yi su na fad'in "Sai anjiman ku."


Tafiya su ka yi Aziza ta koma wajen Haseenah, shi kuma d'akin Khadija ya koma, ya na zuwa ta kwantar da Bilal yace "Ya kamata kisan ina d'aga mi ki k'afa ne saboda abubuwa dayawa, amma naga sam kin kasa fahimta sai ma son wuce gona da iri, Khadija wannan fa mahaifiya ta da ki ka tsaya ki ka fad'a mata magana son ran ki, me ki ke ji da shi? Rashin kunya ko fitsara?"


Tsaye ta mik'e tace "Kalle ni da kyau kaga da me ya kamata ka kira ni."


Da yatsa ya nuna ta yace "Na zo ne dan na fad'a mi ki wani abu, wannan ya zama na k'arshe da hannun ki zai sake tab'a jikin Haseenah, in kuma ba haka ba wallahi zan d'auki matakin da ba lallai ya mi ki dad'i ba, kinji na fad'a mi ki."


"Haseenah? Haseenah fa ka ce? To in har kaga hannu na bai tab'a jikin ta ba ka tabbatar ba ta min rashin kunya ba, wallahi ko yanzu tace za ta min abinda ba zan d'auka ba ni kuma can ci uwar ta a gidan nan kuma a gaban ka."


Daf da ita ya matso cikin d'aga murya yace "Saboda ki nuna min kin rainani? Ban isa na fad'a mi ki kiji ba kenan?"


Kafin ta yi magana ya sake k'ure ta da fad'in "Bak'in ciki ki ke da ta samu ciki za ta haifa min wasu yaran? Shi ya sa ki ka yi k'ok'arin zubar mata da ciki, wallahi Allah ne ya ceceki cikin nan bai zube ba, da sai na sa kinyi aman duk wani abu da ke cikin ki kema."


Rasa abin fad'a ta yi saboda kukan da ke son taho mata, rab'awa ta yi da nufin shiga ban d'aki ya rik'o hannun ta ya nufi k'ofar fita da ita yace "Muke ki bata hak'uri, 'yan uwan ta ma na nan suna tsammanin jin hukunci daga gare ni, ba zan barki haka ba, amma da farko ki ba su hak'uri."


Jin wani sabon rainin hankali ya sa Khadija fizgo hannun ta da k'arfi tace "In kuma ka ga haka ta faru to tabbas ba ta hanyar aure aka haife ni ba."


Juyowa ya yi ya na kallon ta ita kuma ta gyara tsayuwa tace "Wallahi na rantse da sarkin daya busa min numafshi ko za ka kashe ni ba zan bawa uban kowa hak'uri ba, Usman." Ta kira sunan shi cikin d'aga murya ta d'ora da "Karfa ka yi tunanin sanin da ka min da, wallahi yanzu walkice ni daidai na ke da k'ugun ko wace shegiyyy..."


 Marin da ya zabga mata ne ya sa ta fad'i gefe har gilashin ta na fita daga idon ta, dafe kunci ta yi ta d'ago kai ta kalle shi, cikin fitar hayyaci ya shak'o wuyan rigar ta ya mik'ar da ita tsaye yace "Wuce muje na ce."


Ba tate da tayi yunk'urin k'watar kan ta ba tace "Ba zan je ba wallahi, banga laifin da na yi ba da zan bawa wani hak'uri."


Wani marin ya sake kifa mata da k'arfi da ya sa Bilal zabura ya tashi zaune, sake dafe kunci ta yi ta na kallon shi dishi-dishi, da hannu ya nuna mata k'ofa yace "Wuce muje."


"Ba zan je ba." Ta fad'a ta na k'ok'arin tashi tsaye, a karo na uku ya sake gwab'a mata wani marin ya na fad'in "Ai kuwa za ki mutu kamar yanda ki ka ce, tunda taurin kai ne da ke."


*Lovely sister kin tuna ko? Ki ci gaba da hak'uri komai zai wuce da ikon mai kowa mai komai.*


Bilal na ganin haka ya sauko daga kan gado ya rik'e hannun mahaifin shi ya na hawaye yace "Abba dan Allah ka daina, ka bar dukan ta."


Ture shi ya yi gefe d'aya ya na fad'in "Kai bar ni na nuna mata na fita taurin kai, zuciya ai ba ki fini ba." Ya k'arashe da kifa mata wani marin, a tak'aice saida Usman ya mata lafiyayyun mari har guda takwas a kumatu kamar ya samu jaka, da ta kasa tashi ne gashi ba ta iya jin komai ba ta ganin komai ya sa take zaune har yanzu k'asa, cikin hargagi ya ke fad'in "Wai ba za ki tashi ba?" Ya fad'a ya na zura k'afa ya na kai mata hanb'ara, Bilal ne ya rik'e shi ta baya ya na kuka sosai ya na fad'in ya k'yale mi shi Mummyn shi, Usman kam ido sun rufe rai ya b'ace bai ma san me yake yi ba sai harbinta ya ke da k'afa ya na had'awa da hannu ya na nausarta, da sauri Bilal ya zo ya rumgume ta ya juyo da kan shi ya kalli Usman yace "Abba na tsane ka, ba na son ka, ka fita ka ba mu wuri, Allah saiya sakawa Mummy na."


Cak ya tsaya da hannun shi sama daga d'agawar da ya yi zai dake ta, duk da ya ji kalmar tsanar har k'asan zuciyar shi amma saiya basar ya nuna ta da yatsa yace "Yanzu hankalin ki ya kwanta da ki ka ji d'ana ya na fad'in ya tsane ni? To ki zuba ruwa k'asa kisha dan farin ciki, ni ma kuma Allah ne zai saka min da har ki ka yi sanadiyar da d'ana ya furta min kalmar tsana, munafuka kawai shed'aniya, kuma ki sani wallahi in har ki ka ce wannan halin za ki ci gaba da nunawa a gidan nan kenan, to ki na tare da wahala wallahi."


Juyawa ya yi ya fita, d'auko gilashinta Bilal ya yi ya saka mata, mik'ewa ta yi ta shige ban d'aki ba dan tasan in da take saka k'afar ta ba, zaune ta yi bakin bahon wanka ta kunna ruwa suna zuba ta fashe da kuka, tabbas yau tabbatar da Usman baya hayyacin shi tunda har zai iya mata wannan dukan a gaban d'an su, mutumin da magana marar dad'i ba ta tab'a shiga tsakaninsu ba amma yau har da kiran ta munafuka, ta jima zaune ta ci kukan ta kafin ta mik'e ta wanke idon ta ta kashe ruwan ta fito, lokacin fuskar ta har ta kumbura kamar an hura balam-balam, jakunkunanta ta d'auko ta d'ura duk wani abun buk'atar ta a ciki Bilal na kallo, hijabi ta saka ta kalli Bilal tace "Bilal."


Cikin muryar kuka yaron ya amsa da "Na'am Mummy."


Cikin muryar da tasha kuka tace "Tafiya zanyi Bilal, ka zauna gidan mahaifin ka dan ba na jin zan iya dawowa gidan nan, amma ka sani ina tare da kai kaji ko."


Da sauri ya taso yace "A'a Mummy, ni dai dan Allah ki tafi da ni, wallahi ba zan zauna nan ba, yanzu Abba ba ya so na, aunty amarya ma ba so na take yi ba, ni dai wallahi binki zanyi."


"Bilal ba zan iya tafiya da kai ba, ba wai dan ba na so na tafi da kai d'in ba, sai dai nasan mahaifin ka ba zai bari ba, ka tuna ranar ma da zan tafi shi ya hana na tafi da kai? To ka yi hak'uri ka zauna kaji, idan ba ka jin dad'in zaman nan sai ka ce ya kai ka gidan su Hajia."


Cikin kula yace "Ni dai ba na so Mummy, idan kuma ki ka tafi ki ka bar ni wallahi guduwa zanyi daga gidan nan."


Cikin sanyin jiki tace "Shikenan je ka had'o kayan ka."


Ya na fita ta zauna bakin gado ta zuba tagumi ta na fitar da wasu hawaye masu zafin gaske, ba wani jimawa Bilal ya dawo da k'atuwar jakar shi shima ya sanyo duk wani abun buk'atar shi, kallon shi ta yi tace "Ka d'auko kayan makarantar ka?"


"Eh, suna ciki." Mik'ewa ta yi ta kashe duk wutar d'akin ta kile da makulli suka fita, a hankali cikin sand'a ta isa ga k'ofar da za ta shigo da mutum falonta da falonshi ta kulleta kafin suka fita ta d'aya k'ofar, nan ma rufewa ta yi kafin tace Bilal ya kira mai gadi k'ofar gida sannan ya tsayar mu su da adaidaita sahu, ba wahala kam mai gadi ya shigo har in da take ya tsaya yace "Mai adaidaitar na k'ofar gida Hajia."


"Yawwa karb'i nan." Ta fad'a da bashi jakunkunan tace "Ka fitar mana da su muna zuwa yanzun."


"To Hajia." Ya fad'a ya na d'aukar jakunkunan ya jasu Bilal ma ya ja tashi jakar, saida ta lek'o ta hangi motar Usman alamar ya na gidan, saida taga ficewar mai gadi kad'ai ta fito ita ma ta fita, har an yiwa kayan nasu wuri dan haka za ta shiga mai gadi yace "Hajia, lafiya dai ko? Ko tafiya za ku yi ne?"


Juyowa ta yi ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri Baba mai gadi, duk da dai abin da ya faru yanzun sirrine na gida na, amma kai ba yau muke tare ba, tunda na dawo sabon gidan nan na tarar da kai, tun Bilal na jinjiri, matsala ce ta faru da tasa dole sai na bar gidan nan na wani lokaci, ku yi hak'uri, na bar ka lafiya."


Ta na gama fad'a ta shiga adaidaitar suka wuce, da kallo ya bisu ya na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, ita kuma amaryar da abin da ta zo da shi kenan? Wannan wace irin jaraba ce, mata da mijin ta kullum cikin farin ciki, idan ka ji hayaniya to suna wasa ne kamar yanda su ka saba, amma yau gashi su na shirin rabuwa dalilin wata, kai Allah ya kyauta."


Usman na ciki shi da Haseenah bai san tsiyar da ake ba, ba jimawa kam adaidaita ya sada Khadija da gidan su, Mama na ganin su da kaya ta fara salati da sallalami, kai tsaye d'aki ta nufa ta aje kayan ta ta wuce d'akin ta, tashi Mama ta yi tabi bayan ta sai matan yan uwan ta ne su ka bisu da ido, matar Habeeb ce kad'ai ta iya cewa "Aifa lokacin ya yi."


Shiru sauran su ka yi dan suma kawunan nasu a rarrabe suke, kowa da b'angaren da yake saboda suma akwai uwayen gida akwai kuma amare.


Babu abin da Khadija ta b'oyewa maman ta duka ta fad'a mata, duk da taji ba dad'i sosai amma sai bata nuna mata ba, kallon maman ta tayi tace "Dan Allah Mama taimaka min da maganin ciwon kai."


Tashi kawai Mama ta yi ta d'auko ta kawo mata tasha ta kwanta, matar Mansur ta shigo d'akin dan su kwashi labari sai dai ta samu Khadija har ta fara baccin wahala da fuska har yanzu a sumtume, sam Mama ba ta fad'awa 'yan uwan ta ba ko a waya sai dare da suka dawo su ka tarar da wannan abin takaici, lokacin Khadija zazzab'i ya sake rufe ta, Naseer har da k'walla ya yi da ya kalle ta, yanda ya sunkuyar da kai ne ya sa Habeeb dafa shi, goge fuskar da ya yi ne ya tabbatar musu kuka yake, Bashir ne yace "Kai haba dai maza, kuka fa? Ai ba kai ya kamata ka yi kuka shi ya kamata ya zubar da hawaye."


Wasu hawayen ne suka sake taho mi shi yace "Yanzu domin Allah me ya sa Usman ya yi haka? Mufa mun bashi ita ne da tunanin zai kula da ita, me ya sa zai mana haka yanzu? Saboda kawai ana ganin ita marainiya ce mahaifin ta ya rasu."


Sun jima d'akin ta suna tattaunawa in da take kwance ta dunk'ule, saida dare ya yi suka tashi suka koma nasu dak'unan, saida tasha magani kafin ta sake kwantawa, sai dai ba ta yi bacci ba har aka kira sallah asuba, sallah ta yi ta sake komawa ta kwanta ta na istigfari tasbihi da hailala da hannun ta na dama.


Ko da Usman ya fahimci basa gidan haka kawai yaji bai wani damu ba, hakan ya sa ma da safe ko da ya je gida ya samu su Hajia da maganar ya kuma fad'a mu su kar suce za su je su dawo da ita, harda had'a su da Allah akan su barta harta shiga hankalin ta, Bilal kuma d'an shi ne ba ta isa ta raba shi da shi ba, amma malam yace sam ba da shi za ayi haka ba, a k'arshe ma tambayar su dalilin faruwar haka akayi, fad'an Hajia shine "Makulli Usman ya bawa Haseenah ta aje na mota da zai tafi, ita kuma ta tashi fita tace ta bata, shi kuma yace kar aba kowa idan za'a fita a fad'a mi shi zai aiko da wani ya kaisu duk in da za su je, shine ta turmushe yarinya da k'aramin ciki ta karb'i makullin, dalilin hka fa ya kusa sawa ta yi b'ari."


Duk da jin haka yace zaije ya dawo da ita gidan ta, kuma kamar yanda ya fad'a ya cika maganar shi, amma maganganu mabanbanta ya ci karo da su, musamman da suka fad'a mi shi har da duka, har d'akin Khadija aka mi shi jagora ya ganta kwance da k'arin ruwa a hannu, dan tunda ta yi sallah asuba zazzab'i ya sake rufe ta, hakan ya sa Naseer ya d'auko likita har gida aka dubata, sosai suka nuna mi shi b'acin rai da cewa ba za ta koma ba har sai Usman ya dawo hankalin shi, baiga laifin su ba kam dan ya sa dole wata rana zai neme ta, haka malam ya juya rai b'ace da kuma kunyar abin da ya aikata, tun a hanya yace Usman ya same shi gida za su yi magana, da "To Baba." Ya amsa.


*Ku na ganin zaije? Yanzu fa Haseenah ita kad'ai ce.*


Saida ya sake wanka ya shirya yace "Amarya ta zanje gida na dawo, amma ba zan jima ba kinji, ki kula da kan ki."


Kallon shi ta yi ta na k'ara rufe jikin ta da zanin gado tace "Gida kuma? Na d'auka d'azu ka ce min gida ka tafi, ya da wuri haka za ka koma."


Ya na gyara zaman hular sa yace "Eh wallahi Baba ne wai ya ke son gani na, amma na san ba zan jima ba ai zan dawo."


Shiru ta yi a zuciyar ta tace "To idan fa yanzu ma dawo da Khadija za su tafi? Dole na yi wani abu."


Shagwab'e fuska ta yi tace "Yanzu tafiya za ka yi ka barni a haka? Ba ka da matsala kenan tunda ka samu biyan buk'atar ka ko?" K'ok'arin saukowa ta fara daga kan gadon ta na fad'in "Shikenan ai ka tafi."


Matsowa ya yi kusan ta zai kamo hannun ta ta kubce ta shige ban d'aki, bakin k'ofar ya tsaya yace "Haba ke kuwa, kar ki yi hushi mana, kinfa san ba na son b'acin ran ki ko kad'an."


"Ahhhhhhh, wayyo Allah ciki na, marata." Fad'in Haseenah daga cikin ban d'aki, bai tsaya tunanin komai ba ya kutsa ciki ya same ta zaune dafe da ciki alamar fad'uwa ta yi, bai tsaya komai ba ya d'auko ta sai kan gado ya dire ta, kallon ta yake ciki da damuwa ya na rik'e da hannayen ta yace "Garin yaya ki ka fad'i haka? Haseenah karfa ki mana asarar kyautar nan da Allah ya bamu, kinfi kowa sanin lokacin da na d'auka ina fatan Allah ya sake bamu haihuwa, ina son na ga gidan nan ya cika da yara kuma ya zamana ke ce uwar su."


Yanda ya k'arashe maganar kamar zaiyi kuka ne yasa tace "Ka yi hak'uri dan Allah, ni ma santsi ne kawai ya kwashe ni, ban kula ba sai ji na yi na fad'i saboda rai na a b'ace yake."


Kallon ta ya yi yace "To me ya b'ata mi ki rai haka da har ki ke neman ja mana babbar asara."


Cikin turo baki tace "To ba kai ne ka ce zaka fita ka bar ni ba, ni kuma wallahi ba na so ka tafi, satin ka biyu fa baka gari, kasan dai dole munyi kewar ka mu na buk'atar ka a kusa da mu, shine kawai daga ka samu yanda ka ke so sai ka ce za ka fita."


Da rawar jiki yace "Ai dai fitar ce ba kya so ko? To na fasa, kin gani ma? Zan kira Baba na fad'a mi shi ya yi hak'uri zan je anjima, shikenan kinji dad'i?"


Dariya ta yi ganin ya cire hular shi da takalma ya fasa tafiyar, ko farfajiyar gida babu wanda ya lek'a a cikin su suna d'aki suna soyayyar su, hatta abinci sai dai ya kira Bilyamin ya siyo ya kawo mu su, haka dare ya yi amma Haseenah na jikin Usman, da ya yi maganar tafiya wajen Baba za ta fara shagwab'a wai zai barta ita kad'ai, haka ya k'arar da wunin na shi bai je kiran Baba ba kuma bai kira shi a waya ba.


Tunda malam ya ga shiru ya tabbatar da zargin shi na cewa akwai abin da ke damun Fodio, ganin har dare ya yi anyi shirin bacci ya sa malam samun Hajia a d'aki har ta fara bacci ya tashe ta, saida ta wartsake yace "Bacci fa bai kama ki ba, tashi ya kamata ki yi mu duk'ufa da addu'a, dan shakka babu Fodio ba kan shi d'aya ba."


Saida ta k'ara murza ido tace "Malam, ban gane ba, me ya ke faruwa da Fodio kuma?"


"Shiga gaba." Ya bata amsa kai tsaye kafin ya d'ora da "Na yi mamakin da ku ka kasa fad'a min gaskiyar abin da ya faru a gidan shi, kun fad'a min ta karb'i makulli da k'arfi, amma ba ku fad'a min ta karb'a bane saboda za ta kai Bilal asibiti, yaron da aka barwa Haseenah ya wahala saboda babu mahaifiyar shi nan, sannan shi kuma Fodio bai fad'a min ya daki Khadija ba, ke ma kuma ba ki fad'a min ba."


"Duka malam?" Ta fad'a da dafe k'irji, d'orawa ta yi da "Wallahi ban sani ba ni ma, bai fad'a min ba ko alama."


Gyara tsayuwa ya yi yace "Har da duka, kinga yanda ya kumburawa yarinyar nan fuska da kin tausaya mata, tun jiya ta na kwance babu lafiya har zuwa safiyar nan da na je gidan ana k'ara mata ruwa, wannan abun kunya da me ya yi kama? Kinga yanda ran 'yan uwanta ya b'ace su na cewa ba za ta koma ba si in ya zo ya nemi ta koma tare da alk'awarin ba zai sake tab'a lafiyar jikin ta ba, kuma ni banga laifin su ba ko kad'an dan su na da gaskiya."


Shiru Hajia ta kasa magana saida malam ya sake cewa "Na fahimci yarinyar nan ta na biyar shi da sharri, ba kuma alkairi bane ya kawota gidan nan, dan haka k'arya take tace za ta cutar da ahalina wallahi, ko da boka take yawo ni nan zanyi maganin ta, Allah ya fi k'arfin ta wallahi."


Kallon Hajia ya yi da zufa ta rufe ta yace "Ke ma ki taya d'an ki da addu'a."


Fita ya yi daga d'akin ita kuma ta k'ara gudun masuburbud'ar sanyin dake d'akin, ta jima bacci bai sake d'aukar ta ba ta na tunani akan abin da malam d'in ya fad'a, anya kuwa Haseenah za ta iya yin haka? Yarinyar da a zahirance ita ake cutawa, taya za ace kuma ta cutar da wani? Kai da kamar wuya gaskiya.



*Da kamar wuyar zata kassara ku.*

21/02/2020 à 19:15 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *29*




Sai k'arfe *10:25* suka tashi daga bacci, Usman ne ya fara shiga wanka da tunanin ya gaggauta shiryawa dan ya fiya kiran malam, ya sakarwa kan sa ruwa kenan Haseenah ta shigo ban d'akin, bahon wanka ta cika da ruwa ta had'a sabulu a ciki ta cire d'aurin k'irjin ta, da k'arfi ta jashi su ka famtsama cikin bahon su biyu, dama abin da take so kenan, shi ya sa ma ta yi anfani da damar wajen b'ata lokaci suna wanka da 'yar shiriritarsu irin ta amare, sun d'auki lokaci kafin su ka fito haka nan ma wajen shiryawa saida su ka jima, suna fitowa falo cikin shiri ya kalle ta yace "Mummyn beby yau ma ba ki dafa mana komai ba fa, ya za mu yi kenan?"


Zaune ta yi akan kujera tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki masarrafar telebijin (remonte) ta kunna tace "To ai ina ganin ba sai na yi girki ba, tunda kaga amarci mu ke ci, ko ba haka ba?"


Zaune ya yi kusan ta ya na fad'in "Kuma fa da gaskiyar ki, dan mafiya yawancin lokuta idan na dawo daga tafiya sai dai muje cin abinci kawai."


Cike da izza ta na karkad'a k'afa ta kalle shi tace "Oho, kenan aka ake yi, amma shine ni ba za ka iya d'auka ta ba muje?"


Waya ya ciro daga aljihu yace "Yanzu dai bara na fara kiran Bilayamin ya kawo mana na karin kumallo, anjima da dare sai muje mu ci ko, hakan ya mi ki?"


"Ba damuwa." Ta fad'a cike da k'asaita, ta na ji ya bawa Bilyamin sallahun abin da suke buk'ata su ci, bayan d'an lokaci Bilyamin ya iso da abincin, ya na karb'owa kai tsaye kan teburi ya nufa da shi ya d'auki faranti ya zuba ya kalle ta daga in da ta ke zaune yace "Madame ki taso abinci na jiran ki."


Tashi ta yi cikin tako d'aya bayan d'aya ta isa, zaune ta yi akan cinyar shi ya dinga saka mata abincin a baki, saida su ka gama ya tashi zai fita tace "Babban mutum ni fa gida na ke so ka aje ni, idan za ka shigo da dare sai ka biya mu taho tare."


"Gida kuma?" Ya tambaya da mamaki, "Eh, gida." Jim ya d'anyi dan gaskiya a tsarin shi ba'a mi shi haka ko kad'an, ace sai yanzu ne kawai za ta fad'a masa ta na so ta fita kuma yanzu yanzu saboda raini, had'e fuska ya d'anyi yace "Ki yi hak'uri mana Mummyn beby, ki bari har gobe sai kije."


Yamutsa fuska ta yi tace "Gaskiya yanzu na shirya tafiya, in kuma ka hana ni wallahi kuka zan kwana ina yi a gidan nan." Ta na gama fad'a ta mik'e ta nufi hanyar falon ta, ganin fa da gaske ranta zai b'ace ya sa ya yi saurin rik'o ta ya had'a da jikin shi yace "Shikenan to naji, ran gimbiya ya huce, je ki d'auko hijabin ki sai mu tafi."


Cikin farin ciki tace "Da gaske kake?" Cike da tabbatarwa yace "Sosai ma, ai ba na da wani abu da ya fi min ke mahimmanci, zanyi hidimar ki kafin na yi tawa, ki yi sauri ki je."


Cikin d'an lokaci ta d'auko hijabi da jaka da takalma duk kala d'aya suka tafi, ba jimawa ya sauke ta gida tare da bata kud'i kafin su ka yi sallama, mahaifiyar ta kad'ai ce a gidan a farfajiyar gida zaune, bayan sun gaisa sosai suka fara tab'a hira, anan ne mahaifiyar ta tambaye ta ko ta na anfani da magungunan ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh, ina sha Mama, amma fa akwai matsala."


 "Matsala kuma? Tame?"


Cikin sanyin jiki tace "Mama wannan layun da aka aje na duba su ban gansu ba, kuma gashi har yanzu ana tsorata ni a cikin dare."


Da al'ajabi dattijuwar tace "Toh! Amma abun da mamaki, to ina suke? Kuma kin tabbatar an aje su in da ki ka duba?"


"Wallahi Mama wajen ne, su aunty Mariya fa da kan su su ka aje su, amma da na duba babu komai a wajen."


"Toh." Ta fad'a ta na girgiza kai kafin tace "Lallai wannan abu ya wuce duk in da ake tunanin shi, amma bari Baban ku ya shigo sai na fad'a mi shi komai."


Sosai ta ji dad'in wannan wunin da ta yi a gida, gashi ana ta bata kulawa a matsayin ta na mai k'aramin ciki, sai abin da take so ake bata ta ci, har mahaifin ta ya zo aka fad'a mi shi abin da ke faruwa, a cewar shi ta kwantar da hankalin ta zai sake karb'o mata wasu, sannan ta ci gaba da addu'a komai zai wuce.


A b'angaren Khadija kam ganin jikin ya k'i kyau ya sa Mama cewa "Khadija."


"Umm." Ta fad'a ta na d'an gyara kwanciyar ta, "Khadija ba ki da ciki kuwa?"


Murmushi ta yi tace "Ciki Mama? A'a, ba na da komai wallahi, kawai dai zazzab'in wahala ne."


"To Allah ya tabbatar da alkairi." Cewar Mama, Bilal ne ya shigo da sallama ya na cire jakar makarantar shi, kusan maman shi ya je ya sumbace ta da fad'in "Mummy ya jiki? Kinji sauk'i?"


"Na ji sauk'i yarima, har kun taso?" Saida ya fara cire rigar shi yace "Eh Mummy, kawu Ashir yace na mi ki sannu da jiki ba zai shigo ba ya na sauri."


Mama ce ta katse shi da cewa "Kai d'auki tarkacan kayanka ka wuce da su d'akin ka, kar ka kuskura ka min tsirara a tsakiyar falo."


Matsowa ya yi kusan ta ya yi tsaye yace "K'arasa cire min kayan ma in ki na son samun lada."


Rufe fuska ta yi tace "Kai b'ace min da gani kaji ko."


Fad'awa ya yi jikin ta ya sumbaci kumcinta ya na fad'in "Ina son ki Hajia ta."


Rumgume shi ta yi ita ma tace "Ni kuma ba na son ka yau, dan nasan akwai abin da ka ke so waje na."


Kallon ta ya yi yace "Me ki ka dafa yau?" Hararan shi ta yi tace "Uhum, nifa na san za'a rina dama, ina ka fito ci ina zaka ci, to wake na dafa."


Dariya Khadija ta yi tace "Mama ta na so ta sake kumbura ma ka ciki ne."


Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Kema kin zama aunty amarya muguwa?"


Daruya suka saka sai Mama ce tace "Ai ni mugunta ta ma sai tafi ta ta, dan kuwa idan ka gama ci ba ruwa zan baka kasha ba, sai dai na ba ka kwanan nan fura ka kora da ita."


D'aukar kayan shi ya yi ya nufi d'aki ya na fad'in "Kuma idan na mutu ke ce za ki fara zubar da hawaye."


"To ba dole ba, na rasa miji na uban 'ya'ya na, idan kai ma na rasa ka ai zan shiga cakwakiya."


Usman ya je gida bayan ya aje Haseenah, Hajia kad'ai ya samu dan rana ta take sosai zaiyi wuya ka samu namiji gida a wannan lokacin, bayan sun gaisa ne Hajia tace "Amma me ya hana ka zuwa tun jiya da aka kira ka?"


Cikin rashin gaskiya yace "Wallahi Hajia wani d'an aiki ne ya taso min, kuma yarinyar nan ba ta ji dad'i ba, saida ma na kai ta asibiti aka rubuto mana magani."


_Daga cikin bala'in da asiri ke iya jawa mutum akwai k'arya, zai iya k'arya dan ya kare kan sa ko kuma wanda ya ke so, akwai rashin kunya ga wanda baya hayyacin shi, abune mai sauk'i miji ya tub'ewa mata kayan ta ya mata wulak'anci a gaban 'ya'yansu, kad'an ne daga aiki sihiri daina ganin girman wanda ka ke ganin girman shi, akwai wasa da addini wanda za ka ga wani ya na sakaci da shi, illolin fa dayawa yan uwa, fatan mu Allah ya k'ara tsarkake mana zuk'atanmu._


Take Hajia ta fahimci k'arya ya fad'a, amma saboda kunya ta dake tsakanin uwa d'an fari sai kawai ta share tace"Allah ya sawak'e, gashi kuma yanzu malam d'in har ya fita, sai dai in za ka same shi can shagon."


Cikin sunne kai yace "Ba damuwa sai na je can d'in ai."


Ba tare da ta kalle shi ba tace "To ya maganar Nura, ya fad'a min sunyi magana da Khadija kuma tace ka amince, amma a bari sai ka dawo, gashi kuma ka zo ba ka ce komai ba."


"Eh Hajia, ya na ina ne Nuran?"


"Ya na shago mana."


"Shikenan zan kira idan na fita saiya same ni ko can shagon Murtala ne."


Cikin had'e tafukan hannayenta tace "Hakan ma ya yi."


Kallon ta ya yi yace"Hajia me zai hana ku je ku d'auko Bilal?"


Sai lokacin ta kalle shi tace "Ban gane na je ba? Kai me zai hana ka tafiya? Kuma ma ka na nufin ba za ka je ka dawo da mahaifiyar shi ba kenan?"


Cikin b'acin ran an ambaci sunan Khadija yace "Hajia ni babu in da zanje, ita ta tafi saboda ta na so, dan haka taje can ta k'arata, ni yaro na ne kawai matsala ta."


Karo na farko a rayuwa da Hajia ta iya d'agawa Fodio murya, cikin jin haushi tace "To ba zan je ba, ranar da ka shirya ganin d'an na ka sai kaje ka d'auko shi da kan ka."


Kallon ta ya yi shima, amma saboda ran shi a b'ace ya ke da maganar Khadija sai kawai ya mik'e cikin kumburo baki yace "Ni zan wuce, sai anjima."


Da kallo kawai ta bi shi har ya fita daga gidan, girgiza kai ta yi ta na mamakin wannan canjin daga Fodio, mik'ewa ta yi ta shiga d'aki ta na fad'in "Ai kuwa da alama gaskiya malam ya fad'a, amma koma menene zan wa tubkar hanci."


Daga nan wajen malam ya zame, k'ofar shagon ya samu malam zaune akan bacci shi da wani suna hira, har k'asa ya durk'usa ya gaishe su kafin malam ya sallami waccen, mayar da kallon sa ya yi kan Usman da ke durk'ushe yace "Fodio sai yanzu ka zo kiran nawa? To nagode."


"Wallahi Baba..." D'aga mi shi hannu ya yi alamar ba ya son ji kafin ya d'ora da "Jiya na je gidan su Khadija, kuma naji duk abin da ya faru, Fodio ka bani mamaki sosai da na ji ance wai ka d'aga hannu ka daki Khadija, wannan abun kunyar har yaushe da irin shi, duka! Kai a matsayin ka na mai hankali da ilimi, a shekarun ku na k'uruciya haka ba ta faru ba sai yanzu da girma ya fara riskar ku, wanda ya kamata ace yanzu ne soyayya take da tausayin juna, amma ace ka dake ta akan abin da ma k'arya ake mata da sharri, kawai rud'in zuciyar ka ne  ka biyewa da kuma wata banzar hud'uba da wasu sakarkari suka ma ka, kasan me ya sa ta karb'i makullin motar? To saboda ta kai yaron ka asibiti ne, yaron da ya wuni da yunwa alhalin ya na gidan uban shi wanda ke wadace da kayan abinci sama da na shekara d'aya, amma wai akan hakane har ka d'orawa baiwar Allah laifi har ka iya dukan ta, ni ko a gani na ko taka Haseenah ta yi ta mayar da gabanta gabas ta yanka ta da wuk'a za ka iya mata uzuri, uzurin kuwa shine za ka duba dalilin da ya sa ta yi haka tunda ita uwa ce, amma ba komai, ka je gidan ka gani yanda ka lalata mata fuska da rashin hankalin ka, tace ba za ta dawo ba kuma na yarda da abin da ta fad'a, dan haka kaje kai da amaryar taka ku cinye kan ku, amma ka sani wallahi Fodio ina jin tsoron ranar da za ka yi nadama, dan alamu sun nuna *kallon kitse ne ka ke wa rogo*, tashi ka bani wuri."


A hankali Usman ya d'ago kai ya kalle shi tabbas ran shi ya b'ace sosai, cikin taushin murya yace "Dan Allah Ba..."


"Nace ka tashi ka bani wuri ko." Cewar Baba, mik'ewa ya yi ya juya zai shiga mota malam yace "Ji nan." Juyowa ya yi ya matso ya sake zubewa durk'ushe, d'orawa ya yi da "Har yanzu ita matar ka ce, kuma d'an ka ya na tare da ita, ban kuma yarda ka ce za ka d'auko yaron nan ba saboda banga alamar zai samu kulawa ba, dan haka umarni ne daga gare ni ya zama wajibi a wajen ka kai mu su kayan abinci da basu kud'in da za su yi sauran buk'atun su, ka ji da kyau?" Ya fad'a da kama kunnen shi.


Cikin sunkuyar da kai Usman yace "Na ji Baba."


"Tashi ka b'ace min da gani." Cewar malam ya na gyara zaman shi, tashi ya yi ya shiga mota ya wuce kamar zai fasa ihu saboda sharudd'an malam, amma kuma ba yanda zaiyi dole ne ya yi hakan d'in.


Yamma sosai Haseenah na kwance d'aki ita kad'ai Mariya ta kira ta, bayan sun gaisa ne take tambayar "Wai ni kam ya ku ka kare da rigimar ku da matar nan? In ce dai Usman ya d'auki mataki?"


Wata shak'iyar dariya ta yi tace "Ai tuni ta kama gaban ta, yanzu haka ni kad'ai ce a gidan, kwananta biyu yau ba ta gidan."


Daga d'aya b'angaren Mariya tace "Ke Haseenah! Da gaske ki ke?"


"Eh mana, zan mi ki k'arya ne?"


"A'a, amma Haseenah ki na ganin abun baiyi yawa ace ta bar gidan?"


"Baiyi ba, tunda ba ni na fitar da ita ba, bansan akan me su ka tattauna ba da har ta bar gidan, kuma shi ma ba na tunanin shi ya kore ta tunda har na ji yace tunda haka ta zab'a matsalar ta ce."


Cikin sanyin jiki Mariya tace "Toh, yanzu me ye abunyi? Ba za ki bashi hak'uri ba ya dawo da ita tunda ya na jin maganar ki yanzu."


Ba tare da tunanin komai ba tace "Abin da na ke so yanzun bai wuce ki zo gida ki same ni ba na baki kud'i ki kaiwa malamin nan ya sake mana wani aikin."


"Wani aiki kuma?" Ta fad'a da k'arfi, cikin sassauta murya tace "Idan fa ta dawo da matsala, so na ke kawai ta ci gaba da zama acan har mala'ikan mutuwa ya same ta."


Cike da gargad'i Mariya tace "Ke Haseenah ba ruwa gaskiya, me ya sa za ki yi haka? Me ya yi zafi? Na ga dai Usman ne kuma kin same shi, ina ganin ai zafi idan ta na gidan za ki fi k'unsa mata bak'in ciki, amma a dawwamar da ita a gidan su gaskiya abun ba dad'i."


Cikin gaggawa tace "Kinga, kedai idan kin samu dama ki zo gidan ki same ni sai muyi magana."


Shirun da Mariya ta yi ne ya sa Haseenah cewa "Ki na ji na?"


Abin da ta lura a lamarin na Haseenah shine akwai alamun rashin kunya, amma saita dake tace "Shikenan na ji, idan na fita gobe siyan kaya zan biyo."


"Ok." Kawai ta fad'a ta kashe wayar, nan ta ci gaba da zama har saida aka kira sallah magrib ta fito, kuma kamar yanda su ka yi da Usman bai dawo sai bayan isha'i, lokacin ta shirya sosai dan dama da kayan kwalliyar ta a cikin jaka, daga nan restaurent *Kebab* suka nufa cin abinci, rayuwa kenan, rayuwa ta juyowa Haseenah kam yanda ta ke so, gashi kuma ta na garata son ran ta, daga nan ma *plaza* su ka wuce suka siyi ice crime da sauran kayan mak'ulashe kafin su ka wuce gida, wangale k'ofa mai gadi ya yi amma ko kallo bai ishi dukan cikin su duk da gaisuwar da ya ke mu su, girgiza kai ya yi cike da takaici kafin ya rufe k'ofar. 



*Washe gari* bayan fitar Usman Mariya ta zo gidan, bayan Haseenah ta bata kud'in ta mik'e za ta fita, gwangwanin madara ta gani na *lacstar* aje, kallon ta ta yi tace "'Yar k'anwar tsakura min mana ko a leda ne na d'an kaiwa 'ya'yan ki."


Cikin b'acin rai tace "Ba fa na san haka gaskiya, jiya ne fa na fasa madarar nan, idan na ce na dinga rabarwa ai ba za ta min ko sati ba."


Waro ido ta yi tace "Sati fa? Yanzu wannan sai ki shanye ta a sati ke kad'ai?"


Wata irin dariya ta yi kafin tace "Ai kamar kunu haka nake damata ina sha, kuma shine yace ta zama abinci na saboda ya na son ganin yaron da zan haifa kamar d'an turawa." Ta k'arashe da shafa cikin ta, tab'e baki Mariya ta yi tace "Yanzu ni dai sammin na tafiya ta."


Saida taja tsaki kafin ta samo 'yar leda ta zuba mata cokali uku ta mik'a mata ta na fad'in "Karb'i nan ta isheki, ba na so yace ina almubazzaranci da kaya wallahi."


Ganin 'yar madarar da ta zuba mata ya sa ranta b'acewa ta aje tace "Ki had'a kawai kisha, Allah ya raba lafiya."


Ko a jikin ta ita kam har suka fito farfajiyar gidan Mariya tace "To ai kya bani ko na adaidaita ko?"


'Yar k'aramar jakar hannun ta ta nuna mata tace "Kin ganta wallahi k'ananan kud'i a ciki ita ce jaka biyu (maybe dubu d'aya yanzun, dan farashin kud'in ya sauya), amma ki bari idan ki ka dawo daga wajen malam d'in saina baki."


Saida ta kalle ta sama da k'asa ta fice ko sallama ba ta mata ba, tun a hanya Mariya ta yanke hukuncin ba za ta je wajen malam d'in ba tunda ta lura iskanci ne abun na Haseenah, dan haka ma ta wuce gida kai tsaye ta fara tunanin abinyi da kud'in wanda zai anfane ta, a k'arshe ma dai jarin ta ta k'arawa yawa wajen k'ara siyo wasu kayan gwanjo.


Yamma lik'is saiga Bilyamin ya sallama gidan su Khadija nik'i-nik'i da kayan abinci da na masarufi, hakan baiwa mutanen gidan dad'i ba saboda a ganin su za su iya ciyar da kamar Khadija d'ari ma bare ita kad'ai, amma da Mama ta fahimtar da su sai suka mayar da wuk'ak'en na su, in da Khadija kuma tunanin ta kenan ba zai zo ba ya na nufin na yi ta zama a gida.


Gida Usman ya koma dan sanar da su ya tattauna da Nura kuma za su je neman masa aure, har d'aki ya samu iyayen na shi ya sanar da su yanda ake ciki, ya d'an jima suna tattaunawa akan lamarin kafin ya fara yunk'urin tafiya, "Karb'i nan."


Cewar malam, kallon malam ya yi ya kalli kofin hannun shi, ruwa ne dai fari k'al da su, kallon malam ya yi yace "Baba wannan fa? Na miye?"


"Karb'i kasha, na tsari ne." Ya fad'a ba alamar wasa, hannu ya sa ya karb'a ya yi bismillah ya kifa kai ya shanye, aje kofin ya yi ya musu sallama ya fita, bayan shi Hajia ta biyo saida ya zi gaf da d'akin ta tace "Bismillah nan." Saboda ba za ta kira sunan shi ba, bayan ta kawai ya bi suka shiga, ya na shiga ta mik'o mi shi roba da nono a ciki da abun magani tace "Shanye ka bani roban, kuma ka hi bismillah, sannan kasha zuciyar ka d'aya ba tare da tunanin cutar da wani ba ko wata."


A raunane ya kalle ta yace "Hajia shi kuma wannan na miye?"


Wani kallo ta watso masa amma ba tace komai ba, sanin ma'anar kallon ya sa ya kifa kai nan ma saida ya shanye kad'ai ya mik'a mata robar ya mata saida safe ya fito, haka ya d'auki hanya ya na tunanin abin da iyayen shi ke nufi da shi, da haka ya isa gida ya samu Haseenah yau dai ta yi girki kam, amma badan ranshi na so ba ya ci abin da ta dafa d'in har suka kwanta.


Bayan tafiyar shine Hajia ta ji kamar ta yi kuskuren rashin sanar da shi wani abu, amma ta yi niyyar fad'a mi shi gobe da safe idan ya zo, sai dai kuma ta makara kam, dan Usman ya jima baiyi bacci ba ya na dafe da cikin shi, da Haseenah ta tambaye shi kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "...



_Mu tara a shafi na gaba insha Allah._


*Ku yi hak'uri da ni mutane na abisa jinkira na, hakan na faruwa ne saboda sauyawar yanayi na.*



~*LUVE U ALL*~🥰😘

23/02/2020 à 13:03 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_*Lubabatu Shehu shayi*, ina ganin sak'onninki sosai, lallai ke masoyiya ce ta hak'ik'a, tun a gidan Raheenat muke tare, kuma gashi har yanzu kina tare dani a gida na na kallon kitse, Allah ya bar k'auna._


*KALLON KITSE FAN'S 1&2*


💑 _Wannan sadaukarwar taku ce, kuyi yanda kuke so da ita._💑



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *30*



"Wallahi kawai wani kindirmu ne Hajia ta bani nasha, gaba d'aya ya na neman lalata min ciki ma." K'aramin tsaki ya yi, ita kam da mamaki tace "Kindirmu kuma? Haka kawai?"


Kamar wanda aka takura dole yace "Ina jin ko magani aka saka a ciki kome, ban dai sani ba ni dai kawai ya lalata min ciki sai tayar min da zuciya yake."


Cike da kissa ta shafo shi tace "To in hakane kar ka sake sha mana, tunda ya na tayar maka da zuciya, zai iya saka ka amai ma fa."


"Ina tunanin haka nima." Ya fad'a ido rufe, kallon shi ta yi tace "To wai ma maganin meye aka baka? Ba ka da lafiya ne dama ban sani ba."


Bud'e ido ya yi ya kalle ta yace "Ke kar ki tsora ta, lafiya ta k'alau mana ke shaida ce, tace dai ko maganin tsarin jiki ne da kuma...mtss na manta dai, kawai share."


Tashi tayi zaune ta na kallon shi idon shi rufe, tabbas in dai har hakane to iyayen shi sun fara hango wani abu kenan, d'aukar mataki shine abin da ya kamace ta kawai, dan haka tace "To beby in hakane me zai hana ka karb'o maganin, kaga sai ka rik'a sha anan zaifi da sai kaje can, koya ka gani."


Cike da damuwa yace "Kar ki damu kan ki, ni fa ba wani shan shi zan dinga yi ba, ina addu'a na tsarin jiki hakan ma ya isa, kawai ki rabu da su, kinsan tsofaffin nan da tame-tame."


Murmushi ta yi tace "Duk daha beby, idan ma ba za ka sha ba ai sai ka karb'o shi, dan in har ya na wajen su to ba fashi sai ka sha shi ko da za ka mutu ne."


Shiru ya yi ya na tuna lokacin da ya tambayi Hajia amma ta yi banza da shi, hakan na nufin dole dai ya sha ba makawa, dan haka yace "Ba tabbacin za su k'ara bani, amma in har sun bani na sha to zan karb'o shi daga wajen su na taho da shi."


"Gaskiya kam, da ba zan so wani abu ya samar min miji ba uban 'ya'ya." Ta fad'a ta na gyara kwanciyar ta, daga haka babu wanda ya sake magana har bacci ya d'auki dukan su.



*Yau kam* Alhamdulillah Khadija ta tashi jiki da sauk'i sosai, da kan ta ta gyara d'akin ta da na Bilal da ma na Mama, zuwa k'arfe goma kuma ta fita madafar da matan gidan ke aiki, da kan ta ta fara girkin rana kafin matan yan uwan ta suka fito su ka kama aka k'arasa, *12:10* yaran su ka fara shigowa da sallama wasu kuma da gudu, kowa wajen tashi uwa ya nufa kafin suka wuce d'aki dan cire kaya, lokacin ne Khadija ita ma ta shiga d'aki dan ta yi wanka ta yi alwala, ta na d'aure da k'irji za ta shiga ban d'aki wayar ta tayi k'ara, dawowa ta yi dan d'auka amma har ta tsinke, d'aukar wayar ta yi ta duba mai kiran, sunan k'awar ta ne Kaltume, aje wayar ta yi da niyyar idan ta fito ta kammala za ta kira ta, har ta aje ta yi sauri ta sake d'auka saboda idon ta da ya sauka kan kwanan (date) wata, dubawa ta yi da kyau taga tabbas yau wata na da kwana *21*, kai da kawowa ta fara yi tsakiyar d'akin ta na tunanin yanda ta kasa ankara da lokacin al'adarta har wata ya ja haka, sai lokacin kuma ta iya tunawa fa tunda Usman ya yi aure ma bata sake ganin jinin ta ba, to me hakan ke nufi? Ta tambayi kan ta.


"Kenan ciki gare ki kamar yanda Mama ta tambaya?" Da sauri ta zo gaban madubi ta janye d'aurin k'irjin ta tana shafa marar ta, tabbas sai lokacin kad'ai ta iya fahimtar tudun da mararta ta yi, a hankali ya fad'a kan gado ta yi zaune ta rufe ido, wasu hawayen farin ciki ne suka zubo mata ba tare da sanin ta ba, hannu ta sa ta share ta d'aga hannu sama ta furta "Alhamdulillah Allah, Allah kaine Allah, kuma kai ka ce mu rok'e ka za ka amsa mana, Allah nagode ma ka abisa wannan baiwar da ka min, Allah ka tabbatar min da alkairi."


Saukowa ta yi daga kan gadon ta shiga wanka, da sauri ta k'arasa ta fito ta saka kaya ta yi sallah, gyalen ta ta saka ta d'auki jaka tasa takalma ta fito, da kallo Mama ta biyota tace "Ke kuma ina zuwa haka da rana patsal-patsal haka?"


Kasancewar duk matan gidan na d'akin ya sa ta matsa kusan amaryar Ashir tace "Duk cikin nan ke ce babba, dan haka ke ce zan iya fad'awa dan ba na jin kunyar ki."


Rad'a ta mata a kunne kafin ta fice daga d'akin da sauri, dariya amaryar Ashir ta yi ta kalli Mama tace "Mama wai kinsan me?"


"Sai kin fad'a mana zan sani." Cewar Mama, saida ta jinjina kai tace "Ai Mama sai kin bani goron albishir kafin na fad'a."


"Ita goron ki ka bata kafin ta fad'a mi ki? Ai naga kyauta ta fad'a mi ki."


Dariya matar Bashir ta yi tace "To ai Mama shugaban k'asa ya hana aikin banza."


Tab'e baki Mama ta yi tace "To can ku k'arata ku da shugaban k'asar na ku, ku rik'e sirrin ku ba na son ji."


Dariya amaryar Ashir ta yi tace "Mama Khadija fa cewa ta yi ta na zargin ta na da juna biyu, yanzu ma za ta je asibiti ne a tabbatar mata da gaskiya."


Waro ido Mama ta yi tace "Ke *Safiya* ba na son k'arya, da gaske ki ke?"


"Wallahi kuwa Mama haka ta fad'a."


Wani murmushin farin ciki Mama ta yi kafin tace "Allah ya tabbatar da alkairi, *wani hanin ga Allah baiwa ne*."


"Hakane Mama." Suka amsa da shi.


Khadija na fita cikin sauk'i ta samu adaidaita sahu ta kai ta *Clinique tattali*, kamar yanda ta yi tunanin kam hakane ta faru, dan kuwa ta samu k'awar ta ce akan aiki mai sunan *Maryama*, kasancewar babu mutane a asibitin ya sa suka fara tab'a hira kafin ta fad'a mata abin da ya kawo ta, nan ma saida aka sha wata hirar kafin ta mata gwajin fitsari, ko da ta duba dan ta ga sakamakon Khadija tace"Dakata." 


Kallon ta ta yi ita kuma tace "Kawai ki min murmushi idan har gaskiya ne tunani na, in kuma babu to ki had'e rai."


Dariya Maryama ta yi tace"Kaga wani sabon gwajin ciki kuma, to bara na gani." Ta na dubawa kam ta ga ciki dai ya tabbata, haba wa ai sai ta washe mata hak'ora tace "Ke kiyi farin ciki, wallahi ciki ya tabbata, kai Khadija na miki murna wallahi."


Rumgume juna su ka yi cikin farin ciki, ba ta jima ba ta mata sallama ta bar asibitin, daga nan kuma gidan k'awar ta ta wuce Kaltume dan sanar da ita, da shigarta gidan ta ji sun k'ara birge ta abun sha'awa, dan farko *Madina* kishiyar Kaltume ta so ita ma ta yi kalar nata iskancin, sai dai ina tuni Kaltume ta nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, sannan shi kan shi mijin na su *Alhaji Ibrahim* yasan da ya fad'a tarkon Kaltume da babu mai k'watar shi idan ba ubangiji shi ba, a k'arshe dai Madina ta fahimci tazara mai tsayi ce tsakanin su da ita dole ta hak'ura, musamman da ya zama babu mai iya bata shawara ga yanda za ta mu'amulanci rayuwar gidan ta, cikin sauk'i sai suka zauna lafiya kamar ba kishiyoyi ba, yanzun ma saida suka gaisa sosai ita da Khadija har suka fara tab'a hira kafin Kaltume tace su je daga ciki, nan fa ta fad'a mata ta na da ciki kar kuso suji bud'ar da Kaltume ta rabka har k'ofar gida, tsabar nuna farin cikin ta ya sa nan take ta bawa yara kud'i tace su siyo alawa mai tsada su rabawa yara, anjima kuma da yamma za ta yi fanke na sadaka da godiya ga Allah, Khadija dai kallonta kawai tale ta na k'ara k'aunar Kaltume, tabbas a rayuwa bata da yar uwa mace amma Kaltume ta zame mata komai, har kusan yamma kafin ta bar gidan saboda kiran ta da Mama ta yi, haka ta koma gida nan ma Mama da aka k'ara tabbatar mata gaba d'aya gida ya d'auka Bilal zai samu k'ane ko k'anwa, in da Mama ke binshi da gwalo ta na fad'in "Tuzurun wofi, yanzu dai sai naga k'afafun uban wa za ka hawa ko kuma wanda zaka wa shagwab'a, dama can rashin ganin wani ne a gaban ka ya sa ka wannan iskancin."


Shi kam cewa ya ke to sai me, ai k'ane za'a mi shi dan haka bai damu ba, kuma idan ya na son hawan k'afafu ga nata nan zai hau, da haka har 'yan biyar su ka zo suma suka d'ora nasu farin cikin ana addu'ar Allah ya sauketa lafiya.


*Mu ma dai munce ameen.*


Kamar kullum Usman ya je gaishe da iyayen sa, kuma kamar yanda ya saba riska yau ma malam baya nan, sai dai ya bar sak'on wannan ruwan addu'ar a bashi ya sha, saida ya shanye Hajia ta fito daga ban d'aki tace "Tashi kaje ka yi wanka ruwa na nan na had'a ma ka."


Kasa magana ya yi saboda mamaki da kuma rashin sanin abin da zai fad'a, saida ta maimaita da "Ko ba ka ji ba ina magana?"


Saida ya gyara zama ya kalli jikin shi da kyau yace "Amma Hajia na yi wanka fa, wane irin wanka ne zanyi yanzu kuma?"


"Ka tashi ka shiga lokaci tafiya yake." Marairaicewa ya sake yi yace "Amma Hajia wai dan..." Katse shi ta yi da "In za ka tashi ka tashi kafin ka b'ata min rai."


Tashi ya yi kamar zai k'urma ihu saboda haushi, ya rasa irin wannan sabon al'amari na iyayen shi, haka ya tub'e kayan da ya sanyo yanzun ya yi wanka da wannan hakukuwan na magani, haka ya sanyo kayan ya fito duk ruwan jikin shi sun tsaya a kayan, ya na fitowa Hajia kuma ta bashi damammiyar fura da maganin jiya a ciki, saida ta masa jan ido yasha dan cewa ya yi jiya baiyi bacci ba, hakan ya sa ta bud'e mi shi ido sosai sannan ya sha, wata 'yar kwalba ta d'auko bak'a mai d'auke da maganin *jibda* a ciki, da kan ta ta lak'ato a hannu ta shafa mi shi a wuya zuwa kai da hannuwan shi har zuwa damatsenshi, bashi ta yi tace ya d'iba ya shafa a cikin shi har zuwa k'irji, kamar zaiyi kuka ya kalle ta yace "Hajia wai duk wannan na miye haka? Wannan abun nan amai zai saka ni, sam warin shi babu dad'i."


Shiru kawai ta yi ba tace komai ba dole ya shafa yanda take so, mik'ewa ya yi yace "Hajia ko za ki bani magungunan sai ki nuna min yanda ake sha, ina ga kamar hakan zaifi ko?"


Kallon shi ta yi tace "Alhaji, kai ka haife ni ko ni na haife ka?"


Cike da ladabi ya rusuna yace "A'a Hajia ki yi hak'uri, ban fad'i haka dan b'ata ran ki ba."


"To ka wuce ka tafi in da za ka je kawai, sannan ba na so ka fad'a wa wani ko wata batun magungunan nan, ko da kuwa matan ka ne ban yarda ba, kaji ni ko?"


"Naji Hajia, amma wallahi da gaske na le idan ki ka bani zanyi aiki da su, Hajia ki duba kiga hakan zaifi a gani na, misali yanzu na wankan nan, idan da a waje na yake da haka ba za ta faru ba, amma idan ya na nan zai zamana kullum sai na yi wanka anan kenan, sannan idan na yi tafiya za'a dakatar da maganin kenan har sai na dawo, sannan Hajia..."


"Dakata dallah." Ta katse shi tare da d'aga hannu, shiru ta yi ta jima ta na tunanin abin da ya fad'a kafin ta gamsu ta d'auko duka magungunan ta bashi, saida ya karb'a ta nuna mi shi yanda zaiyi aiki da su kafin ta sake jadadda mi shi bata so ko matar shi ta sani, alk'awari ya mata babu wanda zaiji dan haka ta bashi ya tafi, aljihu ya saka su ya fita daga gidan ya shiga harkokin gaban shi, sai yamma ya dawo gida cin abinci, zai shiga wanka ne ya fito da komai na aljihun shi ya na ajewa akan gaban madubi, ya na aje ledar maganin Haseenah ta kalle shi tace "Oga wannan fa na miye haka?"


Ba tare da wani damuwa ba yace "Um, ba na fad'a mi ki zan karb'o wannan maganin ba a wajen Hajia? To ai sune na karb'o d'in, da k'yar ta bani su bayan na mata alk'awarin ba zan bari kowa ya sani ba."


Ya na fad'a ya shige wanka, zaune ta yi tana kallon magungunan har ya fito, cikin taushin murya tace "To yanzu ya za ka yi da su kenan? Za ka ci gaba da sha ne?"


Da k'arfi yace "Wa? Ni! Haba dai Hajia, kinga kawai d'auke su ma daga nan ki zuba su shara danni ko d'aya ba zanyi anfani da su ba."


Mik'ewa ta yi da wani mirmushin mugunta a fuskar ta ta kalle shi tace "Haka na ke son ji dama, dan ba na son namiji mai tsirfa kamar mace."



*Da dare* Usman da malam da kuma rakiyar Murtala da d'aya abokin nashi mijin Hajia Salamatu wato *Alhaji Salisu* suka je aka nemowa Nura auren sahibar shi *Choukra*, cikin girmamawa aka yi abin da za ayi aka gama kafin abin da zai biyo baya, ko da su ka dawo har gida suka fara aje malam in da ya umarci Usman da ya shigo su yi magana, suna shiga ya bashi ruwan addu'a yasha, ganin Nura a gidan ne ya sa yace ya je gida gobe da safe ya same shi kafin ya fita, da "To yah Fodio." Ya amsa kafin ya fito suka wuce. 



*Washe gari* da safe Hajia Sadija ce ta yi sallama gidan surukan Khadija in da Mansur ke binta a baya, tarba ta musamman suka samun daga wajen Hajia da malam d'in kafin su ka nutsu, cikin dattako Mama tace "Nasan za ku yi mamakin gani na da sanyin safiyar nan, to ba wani abu bane dama face wani alkairi da ya tunkaro mu, shine na ce ba za mu yi farin cikin mu kad'ai ba, kuma da kuma Usman d'in ku na da hakk'in ku san me ke faruwa."


Malam ne yace "To gaskiya dai ba mu yi mamaki ba, abu d'aya da na ji shine fargaba, kuma bai wuce fargaban tunanin makomar auren yaran mu ba."


Murmushi ta yi tace "Malam kenan, kamar yanda na fad'a ne a farko alkairi ne ke tafe damu, kuma insha Allahu babu abin da zai shafi makomar auren yaran nan, yanzun ma k'addara ce kawai ta gifta a tsakanin su, amma komai zai daidaita da yardar Allah."


"Allah yasa haka Hajia." Cewar malam yayin da Hajia kuma tace "Allah ya yarda, ya kuma kawo mana k'arshen matsalar."


"Ameen ya Rabbi."  Mama ce ta d'ora da "Dama dai ba wani abu bane Bilal ne za'a wa k'ane ko k'anwa idan Allah ya amince."


Da sauri duka suka kafe ta da ido kowa da mamaki, Mansur ma da kallo ya bita da mamaki, dan sam bai d'auka abin da zai kawosu ba kenan, amma ya zaiyi shiru ya yi ya na sauraren ikon Allah, Hajia ce tace "Wai Hajia ki na nufin Khadija juna biyu ne da ita?"


Dariya mama ta yi tace "K'warai kuwa."


Da tsantsar farin ciki tace "Kai Alhamdulillah, Allah abin godiya, Allah mun gode ma ka, gashi bayan shekaru goma sha uku za ka k'ara azurta baiwar ka da ni'imar ka wacce babu wanda ya isa ya bawa wani sai kai, baiwar da kud'i basa sayanta kuma alfarma bata bayar da ita."


Malam da hak'oran shi ke waje ya na faffad'an murmushi ne yace "Tabbas hakane, arzik'i ne da imanin ka ko kafircin ka bai isa ya baka shi ba, sai mai bayarwa ya ga damar baka."


"To wannan dai shine dama na ce bara mu zo mu fad'a mu ku, dan bai kamata ku kasa sani ba."


Malam ne yace "Gaskiya ne Hajia, kuma mun gode da wannan girmama mu da ku ke yi, Allah ya saka da alkairi."


"Ba komai wallahi." Mama ta fad'a ta na mik'ewa ta na gyara mayafin ta tana ci gaba da fad'in "Mu zamu wuce, dama zanje 'yar kasuwa ne na ce mu fara biyowa ta nan d'in."


Mansur mik'ewa ya yi suka mu su sallama, har k'ofar gida malam ya rakaso in da ya sake jadadda ba su hak'uri akan abubuwan da suka faru, sannan yace a gaishe mi shi da su sosai, da haka su ka wuce shi ma ya dawo gida suka k'ara jinjina al'amarin, suna haka Nura ya sallamo d'akin tare da Aziza cikin shiri, har k'asa suka gaishe da iyayen su kafin Nura yace "Zan aje Aziza makaranta ne daga nan na biyo gidan yah Fodio, jiya yace na je gida na same shi."


Malam ne yace "To shikenan Allah ya tsare, Allah ya mu ku albarka."


"Ameen Baba." Su ka amsa suna mik'ewa, Hajia ma d'orawa ta yi da "Allah ya tsare, sai kun dawo."


"Ameen Hajia." Cewar Aziza suna ficewa.


Mansur na d'aukar hanya ya kalli Mama yace "Hajia ta, dama abin da ki ka zo fad'a mu su? Wallahi ko kad'an banyi tunanin haka ba."


Ba tare da ta kalle shi ba tace "Kenan da ka sani da ba zaka kawo ni ba?"


Dariya ya yi yace "Wane ni, ni d'in banza na kasa kai ku in da ku ke so."


"Dan haka ka ja min bakin ka kayi shiru, in kuma ranka ya b'ace to rufe ni da duka." Ta fad'a ba alamar wasa, dariya ya sake yi shi dai yace "Allah ya huci ranku Hajia ta, ban fad'i haka dan b'ata ran ku ba wallahi, amma a gafarce ni."


Shiru ta yi basu sake magana ba har ya kawo ta yar kasuwa wajen *Nasruminallah* ta fita ta lek'o tace "Zan d'auki lokaci anan, saboda akwai atamfofin da zan duba, idan ka na da aikin ke ka wuce kaje in da za ka."


"To Hajia ta ame za ku koma kenan?" Kai tsaye tace "A adaidaita mana."


Waro ido ya yi yace "Ah haba dai, Hajia ki na da mu a cikin garin nan mu barku ku hau adaidaita sahu, haba dai wuce nan ai wallahi, Hajia ta shiga kusha zaman ki, zan jira ku har  lokacin da ku ka gama."


Sai lokacin ta masa murmushi mai tsada cike da so da k'auna tace "Allah ya bar min kai."


Cikin jin dad'i shi ma yace "Ameen Hajia ta, ai wannan addu'ar kad'ai ma ta isa tasa na kwana wajen nan ina jiran ku."


Dariya kawai ta yi ta shiga shagon da ya kawo ta, shi kam gyara zama ya yi ya k'ara sautin wa'azin da ya ke saurara, ya na haka Bashir ya kira dan tambayar in da ya kai mu su uwa su, nan ya fad'a mi shi komai ai sai Bashir ya fara zazzaga fad'a wai akan me Hajia za ta mu su haka, ai sai su d'auka ko wani abu suke so a gurin su ko kuma su na son amayar da yar uwar su ne, Mansur kam da ya ji ya cika mi shi kunne kuma ya na gaba da shi babu rashin kunya tsakanin su sai raha, hakan ya sa yace "To yallab'ai Bashari ni zan kashe wayar sai ka kira wayar Hajiar ka fad'a mata haka."


"Wallahi zan wulak'ance idan ka sake kira ni da Bashari, fitsararre kawai, shine ma har za ka ce na kira Hajiar, wato so ka ke kaga ta yi hushi da ni ko? To ba zan kira ba."


Cikin dariya Mansur yace "Dan haka ni ma sai ka shafa min lafiya da surutun nan naka." Ya na fad'a ya kashe wayar ya na ci gaba da dariya, dan ya san in ya koma gida sai su sake wata badak'alar akan kashe mi shi waya da ya yi, shi kam Bashir jefar da wayar ya yi ya na ci gaba da mita, Aisha dai na saurarn shi dan yau ya na d'akin ta har ya shirya ya fita su ka gaosa da Khadija bai daina mita ba.


Nura na aje Aziza ya wuce gidan dan dama babu nisa sosai daga nan, saida sula gaisa sosai da mai gadi kafin ya wuce ciki, Haseenah na madafa ta na soya dankali saboda wuyar da take ji, Usman kuma na d'aki ya na bacvi dan lokacin tashin shi baiyi ba, har saida Nura ya tsaya k'ofar shiga falon Usman ya tsaya ya d'an fara bubbugawa, Haseenah dake kallon shi tana ta fad'a wai miya kawo shi da safiyar nan, sai lokacin ta lek'o ba tare da tunanin rigar baccin da ke jikin ta ba tace "Sannu ko?"


Juyawa Nura ya yi ya sauke idon shi a kan ta, d'auke idon shi ya yi lokaci d'aya sai dai ya na shakku ko ita ce amaryar ma ko ba ita bace, dan shi dai dama ba wani saninta sosai ya gama yi ba har yanzu, musamman kuma yanzu da yake ta taso daga bacci ne duk a hargitse take, hakan ya sa ya ga ta masa wani irin muni kamar tsohuwar akuya,😂 Nura bala'i, a tak'aice shi ma yace "Sannu, mai gidan fa?"


Cikin yamutsa fuska tace "Alhaji ya na bacci, kuma lokacin tashin shi baiyi ba, sai dai ko za ka dawo wani lokaci."


Wani kallo ya mata sama da k'asa yace "Da alama ba ki gane wane ne ni ba, amma ko Khadija dake gaba da ke na zo gidan nan tana taso min in har ina son ganin shi, amma bara ki gani."


Wayar shi ya ciro daga aljihu ya danna lambar Usman ya doka masa kira, murmushi ta yi tace "Ni Hassenah suna na, ita kuma Khadija sunan ta, kaga dole hallayar mu da d'abi'ar mu za ta banbanta, ba lallai abin da ta maka ba ni ma shi zan maka, dan haka na fad'a maka Alhaji na bacci."


Ta na fad'a ta fito daga madafar ta bud'a k'ofar falon ta shiga, ta na shiga Usman kam bacci yake hankali kwance, kai tsaye wajen wayar shi ta nufa dan ta na nesa da shi kuma ta na vibration, d'auka ta yi ta kashe wayar gaba d'aya sannan ta aje ta fito, ta gaban Nura ta sake wucewa ta koma madafa ta ci gaba da aikin ta, shi kam ko da ya kira ba'a d'aga ba kuma da ya sake kira ya ji a kashe yasan ita ce, rai b'ace ya juya ya fita dan a cewar shi in ya tsaya ya na kallon ta to tabbas zai d'auki man da take suya da shine ya k'ona mata fuska da shi, dan haka ya fita daga gidan.


Ko da ta kammala abin da take wanka ta yi ta shirya ta taso Usman, taya shi ta yi ya yi wanka ya shirya ya fito suka fara kari, cike da kasala ya kalle ta yace "Wai ina waya ta ne ban ganta ba?"


"Ta na d'aki." Ta fad'a a tak'aice, wata hamma ya yi ya kalle ta yace "Wallahi gaba d'aya jiki ba dad'i, ba na da ra'ayin fita yau kam."


Murmushi ta yi tace "Zan so kasancewa tare da kai na tsawon wunin nan, idan haka ta faru zan ji dad'i sosai."


"To shikenan, yanzu kije ki fito min da k'ananan kaya na canza wannan manyan da na ji dad'in zaman gidan."


"To." Ta fad'a da azama ta nufi d'akin shi, d'orawa ya yi da "Ki biyo min da waya ta dan Allah."


"Ok." Ta fad'a ba wani fargaba a tare da ita, ba jimawa ta dawo da kayan da wayar, da ka ta ta saka mi shi kayan ta ninke waccen ta mayar d'aki, ta na shiga d'akin ya kunna wayar ya fara kiran wayar Bilal, ya yi mamaki da yaron ya kasa d'aukar wayar shi, dole ya hak'ura ya barshi sai lokacin ya ga sak'o da ke nuna Nura ya kira shi bai samu ba, kiran Nuran ya yi wanda har yanzu yake cika ya na batsewa cike da haushin Haseenah, a kakkauce suka gaisa kafin Usman yace "Jiya na ce ka zo ka same ni gida, akan wani dalili ne ba ka zo ba, ko ka na so ka nuna ban isa bane?"


Cikin b'acin rai Nura yace "Kuma yaya, ka tambayi wannan shed'aniyar amaryar ta ka mana, tunda safe na zo amma tace ka na bacci wai ba za'a tashe ka ba, ni kuma naga ko shugaban k'asa ne kai tunda har kai ka ce na zo ai dole a barni na ganka, amma ta rufe ido wai ita mai miji." Ya k'arashe maganar da k'wafa, Usman da ya yi shiru ya na sauraren shi zuciyar shi na tafasa saboda ya tab'o masoyiyar shi, tabbas da ya na tsaye gaban shi wallahi da ya sai ya mare shi, dan haka ya gyara zama daidai lokacin kuma Haseenah ta fito daga d'akin, cikin b'acin rai Usman ya fara fad'in "...



*Yan uwa ku taya ni da addu'a, bébé Abdul Latif ba lafiya, Allah ya bashi lafiya.*

24/02/2020 à 21:49 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *31*



"Yanzu Nura ni ka ke kallo ka ke fad'a ma haka? Ko dan ka na ganin a waya ne shine ya ba ka damar fad'a min abin da ka ga dama? Lallai wuyan ka ya isa yanka Nura, har ni za ka bud'a baki ka aibata matata a gaba na a dodon kunnuwa na, to nagode, kuma ka yi hak'uri idan ran ka ya b'ace saboda kiran da na ma ka, ni dama ba aikin ka zanyi ba, na ce ka zo ne dan na baka kud'in da za ka fara shirye-shiryen bikin ka tunda an riga da an gama magana, amma tunda har ka ci mutuncin matata a gaba na ba tare da fargaba ba, to na fasa sai ka je ka samu malam saiya ma ka komai, ko kuma ka je ka fad'awa wacce ta sanya aka nemo ma ka auren ka ga saita d'auki nauyin komai."


Ya na fad'a ya kashe wayar ya jefa kan kujera, zaune ta yi ta na kallon shi tace "Ya dai babban mutum na ji ka na waya haka kamar ka na fad'a? Kai da wa ne haka?"


Cikin fusata yace "Ni da wannan banzan Nura fa, wai har ni zai kalli tsabar ido na ya na fad'a min magana har ya na ci mi ki mutunci, amma ba laifin shi bane laifi na ne da na sakar mu su fuska har su ke samun damar fad'a min abin da duk ya fito bakin su."


Cikin ladabi tace "To me yace ma ka?"


"Ki barshi kawai, ban san tunawa." Matsowa ta yi kusa da shi ta b'alle mab'allin rigar shi ta sa hannu ta na shafa k'irjin shi ta na fad'in "Na fi ka sanin cewa yan uwan ka ba sa so na, musamman yanzu da aunty Khadija ba ta gidan nan, wallahi gaba d'aya haushi na suke ji, gani su ke kawai laifi na ne ni ce silar barin ta gidan, amma ka sani ba zan tab'a damuwa da hakan ba in dai har ka na tare da ni."


Rumgume ta ya yi yace "Kar ki damu Mummyn beby, babu abin da zai raba ni da ke saboda ina bala'in son ki sosai."


Nura kam shi ma cikin hushi ya aje wayar shi ya ci gaba da aikin da ke gaban shi ya na balbala masifa shima, bai damu ba dan yace ba zai bashi gudummuwa ba, dan dama a shirye ya ke kafin ma ya fara maganar auren, dan haka ya yi niyyar yi wa kan shi komai ba tare da jiran taimakon wani ba, sunyi mai wuyar tunda sun nemo mi shi auren.


Har ya gama abin da ya ke ya dawo gida kowa bai fad'awa abin da ya faru ba, dan Nura mutum ne mai zuciya da kuma rik'o sosai, wannan abun da ya faru ko da an yafi juna zaiyi wuya ya d'ora idon shi akan Usman ba tare da ya tuna wannan ranar ba, uwa uba kuma Haseenah da ya ke da tabbacin ita ce silar faruwar komai, har ya yi wanka ya ci abinci zai fita Hajia tace "Wai kai ya ku ka yi da Fodio da ka je gidan?"


Fuska a had'e yace "Ba komai Hajia, dama wani sak'o ne zai bani na kai wani wurin."


"To ai ni na d'auka ko maganar auren ta ka ce za ku tattauna." Hanyar fita ya nufa ya na fad'in "A'a ba ita bace."


Har ya kusa kaiwa k'ofar fita ta sake cewa "Zo ka kira min shi a waya, ni tun yamma na ke kira ba na gane me ake fad'a, kuma har yanzu bai shigo gidan ba har dare ya yi." Dawowa ya yi ya karb'i wayar ya danna kiran lambar Usman ba tare da yace komai ba, wayar na k'ara a lokacin amma ba'a d'auka ba.



Manne suke da juna basu rabu ba, sai dai ta samo mu su abu su tab'a kawai su yi sallah idan lokacin ya yi, mai gadi bawan Allah sam sun ma manta da a al'amarin shi bare a aika mi shi da abinci, sai dai ya siyo kawai ya ci amma ran shi bai mi shi dad'i ba, a haka har dare ya riske su Usman sai amsa waya ya ke musamman abokan shi na rashin ganin shi yau da ba ayi ba a waje, wani ikon Allah kuma saida su ka yi shirin kwanciya sai ciwon mara ya hana Haseenah sukuni, cikin rud'ewa ya d'auke ta su ka nufi asibitin da aka fara duba ta tun farkon rashin lafiyar ta, suna gaban likita lokacin kiran Hajia ya shigo wayar shi, kasa d'auka ya yi ya mayar da hankali kan abin da likitan ke fad'a cewa ta daina duk wani aikin wahala, in fa ba haka ba zata iya yin b'arin cikin nan, haka aka sallamo su suka dawo aka ce ta ci gaba da shan magungunan da aka bata na farko, tun cikin mota yake fad'in "Wallahi ba za ki k'ara dafa ko ruwan zafi ba a gidan nan, ke baki san yanda na ke son abin da ke cikin nan naki ba, amma bari cikin ki ya k'ara k'wari wallahi k'asar waje zan fita da ke ki haihu acan, dan ni ban ma gamsu da likitocin nan d'in ba, daga yanzu kuma zuwa lokacin zan samo mi ki yar aiki ko kuma Aziza ta dawo nan ta dinga aikin gidan."


Ita dai ta na sauraren shi dafe da marar ta har suka isa gida, da kan shi ya canza mata kaya ya kwantar da ita ya bata magani tasha sannan ya rufe ta da zanin rufa, k'ura mata ido ya yi ya na kallo har bacci ya d'auke ta, wani bala'in tausayinta da kuma son ta ne ke k'ara gyauraya da jinin shi, ta yanda yake jin kamar ya mayar da cikin jikin shi saboda ta samu sauk'i, ya jima zaune kafin ya fito da wayar shi ya ga kiran Hajia, fita ya yi falo ya sake maida kira cikin sa'a kuma Hajia ta d'auka, a d'an kakkauce suka gaisa kafin ta tambaye shi ya yi aiki da magungunan nan, "Sosai ma Hajia, ai duk na yi aikin da su." Cewar Usman fa, tambayar shi ta kuma yi me ya hana shi zuwa yau? Malam ma ya bayar da ruwan addu'a a abashi amma bai zo ba, haka kawai ya tsinci kanshi ya sharara k'arya ta hanyar fad'i "Hajia ai wani abu ne ya d'an taso da ya sa dole sai da na je *katsina*, kuma sai bayan isha'i na dawo ina zuwa na gaji sosai kawai na d'an kwanta, yanzu ma ina bacci ne na farka sai kuma na ga kiran ku."


Cike da gamsuwa Hajia tace "Ah to shikenan, saida safe, Allah hutar da gajiya."


"Ameen Hajia, nagode, saida safen ku." Ya na fad'a ya kashe wayar ya shiga uwar d'akin shi ya canza kaya kafin ya dawo d'akin Haseenah.


Washe gari da safe kafin malam ya fita saida ya sake bayar da ruwan addu'a, Hajia dai ba ta ma fad'a mi shi na jiya na nan ba kawai ta amsa, sai kuma akayi sa'a Usman ya zo gidan, shi ma kuma ya zo ne da maganar Aziza ta koma can da zama ta na taya ta aiki, kasancewar ba sabon abu bane ya sa Hajia cewa idan malam ya zo za ta fad'a mi shi, idan ya amince saita kira a fad'a mi shi, nan ta d'auko ruwan duka biyu ta bashi ya shanye kafin ya fita, daga nan wajen Murtala ya nufa su ka d'an tab'a hira har ya na tsokanar shi wai amarya da uwar gida sun hana shi fita ko ina, nan ya kalle shi ya tab'e baki yace "Wace uwar gida kuma da ba ta nan?"


Da mamaki Murtala yace "Ban gane ba ta nan ba, to ta na ina?"


K'ara tab'e baki ya yi yace "Ta na gidan su mana."


"Gi me?! Murtala ya fad'a da k'arfi har da dafe k'irji, a wulak'ance ya kalle shi yace "Gida na ce, gidan iyayen ta, ko tafi k'arfin zuwa gida ne?"


Kai tsaye ba tare da fargaba ba Murtala yace "Ta fi k'arfi, wallahi in dai Khadija ce tafi k'arfin haka aboki na."


Sake tab'e baki dai ya yi yace "Sai kuma ka yi kan ka ake ji." Dafa shi Murtala ya yi yace "Wai dan Allah in tambaye ka mana? Ka na nufin ta tafi gidan su saboda ganin damar ta? Ko kuma kai ka kora ta gida? Ko kuma ma dai wasa ka ke min?"


Cikin hassala yace "Ya zan ma ka wasa da wannan maganar, wai ita Khadijar nan me ku ke d'aukar ta ne da ba za'a hukunta ta ba?"


Wani kallo Murtala ya ma sa yace " Mun d'auki Khadija a matsayin rayuwar Usman, sannan Khadija ita ce sirrin duk wata nasara ta Usman, kar ka manta da haka aboki na, duk abin da ka zama yau Khadija ta taka muhummiyar rawa a zuwan ka wannan matakin, amma gaskiya abin da ka yi yanzun kasa ni kai na na fara jin kunyar had'uwar da ita da iyayen ta da kuma 'yan uwan ta, shin aboki na yanzu da wane irin ido za ka iya kallon Ashir idan kun had'u ko da bisa hanya ne?"


Cikin b'acin rai ya kalle shi yace "Da wane ido fa, da idon da ya ke kallon na shi 'yan uwan matar wacce ya saka lokacin da zai k'ara aure, Rahama ba, ka tuna da ita? To ai gwara ma ni tunda ba sakin ta na yi ba, kuma ita ce ta d'auki kayan ta ta tafi ba ni nace ta tafi ba."


Murmushi Murtala ya yi yace "Kafi kowa sanin dalilin da ya sa Ashir ya rabu da Rahama, ta yi ikrarin in har ya k'ara aure to ba shi ba kwanciyar hankali, sannan daga lokacin ta dinga nuna raini akan mutanen da suka fi komai daraja a wurin shi, mahaifiyar shi da kuma Khadija, wulak'anta su da ta fara yi ta na kallon su kamar sune ke zugashi ya sa ya kasa jura ya sallame ta, amma kai kuma fa? Fad'a min tayar ma ka da hankalin da ta yi."


Tsaki ya yi yace "Kaga, ni ban zo nan ba saboda jin wannan maganganun, kawai..."


Dafa shi ya yi cikin nutsuwa yace "Me ya ke damunka aboki na? Fad'a min miye matsalar mana? Khadija ce fa, matar nan da ba ka son komai sama da ita, ina wannan soyayyar? Ina wannan k'aunar? Ko da yake ma bai kamata na tambaya ba, nasan har yanzu ka na son ta."


"Ba gaskiya bane, ni yanzu ba na son ta." Ya fad'a ba alamar wasa, murmushi Murtala ya yi yace "Ka rufe idon ka, sannan ka saurari zuciyar ka ita kad'ai, kar ka bari wani tunani ya shiga tsakanin ka da zuciyar ka, ina tabbatar ma ka hoton Khadija za ta gani."


Ya na fad'a ya mik'e ya shiga cikin shagon shi dan ya ba shi dama, Usman kuma na ganin haka saiya mik'e ya tashi ya shiga motar shi shima ya bar wajen, gida ya koma ya na zuwa mai gadi ya bud'e masa k'ofa ya shiga, har ya aje motar a muhallin ta kalaman Murtala na masa yawo, hakan ne ya tilasta masa dafe sitiyari ya rufe ido ya na mayar da nutsuwar sa gare sa, ya jima a haka kafin ya zuba ya bud'e ido saboda ganin Khadija da ya yi cikin doguwar riga bak'a, gefen ta Bilal sai dariya suke suna kallon wani abu da ya birge su, amma ko da ya bud'e ido ya na tuna fuskar ta saiya k'ara had'e fuska, tsaki ya yi kawai ya fito daga motar ya wuce wajen amarya.


Da shigar shi ya samu Haseenah na waya da Mariya akan maganar su, kasancewar a shirye take ya sa tace ta karb'o sak'on ta zo ta amsa ko ta aiko a karb'ar mata, a cewar Haseenah "Zan kira yah Mubarak ya je ya amso min." Da "Sai ya zo." Mariya ta amsa su ka datse wayoyin.


Wanka ya fara shiga ya yi ya fito d'aure da abin tsane ruwa a k'ugu (towel), wayar shi ya d'auka gaban madubi ya danna kiran lambar Bilal, a daidai lokacin Bilal na zaune gaban Khadija su na karatu, ya na fito da wayar daga aljihu ya datse kiran saboda ganin mai kira, irin shi ma wai an tab'a mi shi mahaifiya d'in nan, ganin hakane ya sa Khadija kallon shi tace "Bilal, ba kiran ka ake ba na ga ka na katsewa? Waye haka?"


Turo baki ya yi gaba baice komai ba, dariya Khadija ta yi tace "Ko dai surukata ce ta ke kiran shi ya sa ba ka so ka d'auka gaba na?"


Kamar zai fashe da kuka yace "Mummy."


"To waye ke kira?" Ta fad'a ta na d'aukar wayar da ya aje saman gado, tana dubawa ta ga mahaifin shine ya kira ya katse, da mamaki ta d'ago ta kalle shi tace "Bilal! Mahaifin ka ne dama ya kira ka ke katse shi?"


Kafe ta ya yi da ido, cikin tsawa tace "Da kai na ke magana ka na jina ka yi shiru, ina so na ji hujjar da tasa ka ke datse kiran shi ba ka d'auka."


Cikin turo baki yace "To Mummy ba Abba ne ya daina son mu ba, kuma a gaba na fa ya dakkk..." Kashe shi ta yi da marin da ya sashi saurin dafe kumci ya fashe da kuka, cikin zafin rai ta d'ora yatsanta akan bakin ta tace "Shiiii, kar ka bari na ji sautin muryar ka har zuwa lokacin da zan gama magana."


Gimtse kukan shi ya yi ya na kallon idon ta tace "Bilal matsala ta ce fa da mahaifin ka, kai miye na ka a ciki? Me ya shafe ka da har za ka juyawa mahaifin ka baya a kai na? Kasan me ya faru ne a tsakanin mu? Ko kuma na fad'a ma ka ba na son mahaifin ka ne? To maza kafin na k'irga uku ka kira mahaifin ka ka bashi hak'uri sannan ka nemi gafararsa."


Da sauri ya d'auki wayar ya mayar da kira, Usman da ke cikin saka kaya ne ya ga kiran Bilal, d'auka ya yi kafin yace wani abu Bilal yace "Assalama alaikum, Abba ina wuni."


Wani murmushi Usman ya saki tare da sak'awa a ran shi tabbas Khadija ce ta sashi ya kira shi, dan ya na da yak'ini akan Khadija wajen tarbiyar Bilal, bai iya amsa sallamar sai cewa ya yi "Yariman hushi ka ke da Abban ka?"


Jiki na rawa Bilal yace "A'a Abba ba hushi na ke da kai ba, dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, ba zan k'ara ba insha Allah."


Murmushi ya yi yace "Ba komai yarima ya wuce, ya ka ke? Ya karatu?"


"Lafiya lau Abba." Ya yi maganar ya na kallon Khadija da ta kafe shi da ido, ta na ji su na wayar su kafin daga bisani Usman yace "Yarima yaushe za ka zo mana gida? Kasan fa mu na kewar ka."


Cikin turo baki yace "Gaskiya Abba ba zan je gida ba ba tare da Mummy ba, kawai kai ka zo nan."


Ba tare da damuwa ba yace "Shikenan to, amma idan naje makaranta zan gan ka?"


Cike da k'aguwa yaron yace "Abba! Me ya sa ba za ka zo gida ba?"


"To to shikenan, na ji zan shigo gidan zuwa gobe."


"Wane lokaci?"


Saida ya d'anyi tunani kafin yace "Umm, ina ga zuwa dare zan shigo."


"To Abba." A hankali Usman yace "Saida safe ko, ka yi bacci lafiya."


"To Abba, ga Mumm..." Bai k'arasa fad'a ba ya ji ya datse kiran, kallon maman shi ya yi yace "Mummy ki yi hak'uri to, Abba ya hak'ura."


Janyo shi ta yi ta rumgume hawaye na fita a idon ta tana fad'in "Bilal ba na so ne abin da ke tsakani na da mahaifin ka ya shafe ka, idan ba ka manta ba a baya haka bata faru ba tsakanin mu, yanzu ne haka ta fara faruwa saboda dama ita rayuwa ta gaji haka, ba lallai mutum ya tabbata cikin farin ciki ba, zan iya cewa a rayuwa ta ban tab'a fuskantar matsalar da ta sani bak'in ciki ba kamar wannan, dan haka zanyi hak'uri da jarabawar da Allah ya d'ora min har na cinye ta, ko da kuwa hakan na nufin k'arshen zama na kenan a gidan mahaifin ka."


Da sauri ya d'ago yace "A'a Mummy, gaskiya ba za ku rabu ba, ni dai wallahi idan ku ka rabu to ba za ki sake wani aure ba." Zaro ido Khadija ta yi ta na kallon shi da mamaki tace "Kai kuma a ina ka samu wannan tunanin?"


Cikin shagwab'a yace "To ba *Beby* (d'iyar Ashir ta farko mai sunan maman su) ce tace mana Maman su za ta yi aure ba."


Girgiza kai ta yi tace "Kenan idan ban koma gidan sa ba saina tabbata a cikin d'akin nan? Kai ba ka kishi na ne? Ko ba kaga shi mahaifin naka ya k'ara aure ba, me ya sa ba ka hana shi?"


"To Mummy ai shi namiji, ni kuma ba na so ki sake min wani Abba, na fi so ku zauna ku biyu abunku yafi dad'i." Shiru ta yi tunda shekarun shi basu kai tace dole saita fahimtar da shi ba, sannan ita kan ta tana wa Usman kishin kan ta ta yanda take fatan ya zama mijinta har abada, da haka suka ci gaba da karatun su har dare ya yi su ka kwanta.


*Washe gari* da safe gidan ya yi shiru sosai aka amshi bak'uncin Murtala, dan gaskiya abun bai masa dad'i ba sosai, a falon Hajia suka zauna tare da Khadija da Hajia ya na basu hak'uri da nuna mu su rashin jin dad'in sa, sannan ya d'ora mu su da sam bai sani ba sai jiya, cikin fara'a suka nuna mi shi babu komai haka Allah ya hukunta, kuma ai da sauk'i tunda ba saki bane Allah zai iya daidaita lamarin, haka dai ya tafi abun ba dad'i sai hak'uri kawai.


Yau Usman ya samu malam a gida bai fita ba saboda jiki da jini, saida ya sha ruwan shi kafin ya mik'e zai bar gidan Hajia ta tambaye shi ko yaje ganin Khadija? A cewar shi dai "A'a ban je ba, amma na ce yau zanje anjima."


"To aiko gwara ka tafi dan kasan halin da take ciki." Da mamaki ya kalli Hajia yace "Hajia wani abun ne ke faruwa da ita?"


Cikin murmushi tace "Ai Khadija Allah ya..." Da sauri malam ya d'aga mata hannu alamar ta yi shiru, girgiza mata kai ya yi kawai bai ce komai ba, jin ba tace komai ba ya sake mu su sallama ya fita, Hajia kuma malam ta kalla tace "Me ya sa ba ka so ya sani? Ya na da hakk'in sani fa."


"Ki barshi kawai, idan ya je saita fad'a ma sa idan ta so ya sani, idan kuma ba ta so ba saiya gano da kan sa." Har ya mik'e zai fita Hajia tace "To amma ni banga anfanin b'oyewar ba."


Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Ni kuma na gani, in dai ina fad'a aji to ban yarda ki fad'a ma sa da bakin ki ba, dan halin da Fodio yake ciki yanzu ba ya iya rik'e sirrin kan shi ma bare na wani, a gaskiya ni ban yarda da amaryar nan tasa ba."


Da *yamma* Khadija su na farfajiyar gida yara duk sun cika gidan da hayaniya suka ji sallama, amsawa akayi tare da masa izinin shigowa, Bilal na ganin shi da gudu yaje ya rumgumr shi, Khadija ma na juyowa ta mik'e ta na dariya saboda farin cikin ganin shi ta na fad'in "...



*Addu'ar ku tamkar takobi ce a gare ni mafi kaifi a duniya, ina k'aunar ku masoya.*

25/02/2020 à 21:16 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *32*



"Ango kai ne a gidan namu, lallai babban bak'o, amma dai da alama hanya ce ta d'auka ka ya sa ka biyo nan, ba dan haka ba ni dai na san ka da tsoron bayar da kud'in cefanai."


Dariya ake in da ta nufi falon Mama ta na fad'in "Bismillah Nura shigo." Bayan ta ya bi ya na rik'e da hannu Bilal, saida ya gaisa da mutanen da ke nan kafin ya k'arasa shiga ciki, zaune ya yi akan kujera ita ma ta zauna bayan ta aje ma sa ruwa da lemu, kallon ta ya yi yace "Ke haka ake sai ki tarfani a gaban manyan mutane, sai kisa su d'auka gaske ne abin da ki ka fad'a."


"Au! Ba gaske bane kenan? To ka na bayarwa ne? Yanzu fad'a min yaushe rabon da ka zo gidan nan?" Sosa kai ya yi yace "Gaskiya na kwana biyu, yanzu kuma da na samu labarin ki na nan wallahi kunya ce ta hanani zuwa."


Murmushi ta yi tace "Ba na son ku na fad'in haka wallahi, kenan idan k'addara tace za mu rabu da Usman ba da shi kad'ai zan rabu ba har da ku?"


"Ah haba dai, ai ba za mu tab'a bari ki fita a cikin dangin mu ba wallahi, ke fa alkairi ce a cikin mu, shima yasan da haka, wannan mai k'afafun angulun ce ta sauya mi shi tunanin shi."


Bilal ne ya bushe da dariya yace "Aunty amaryar ce haka?" Kallon Bilal ya yi ba alamar wasa yace "Kai k'yale shegiya mai suffar kwad'o, ai fata na ke Allah ya had'a ni da ita wata rana ta nuna min rashin kunya, wallahi ko kallon da raina bai so ba ta min sai na karya mata k'afa, yar banza hanci kamar bakin sahani (buta) amma sai iya shege a k'ugun ta."


Khadija in banda dariya ba abin da take kafin ta yi shiru tace "Kenan ni ma haka ka ke shammace ni bayan ido na?" Kallon ta ya yi yace "Ah haba dai, ke ai ko mutuwa ta na kunyar idon mahaifi, kin wuce nan wallahi."


Nan fa Nura ya kwashe duk abin da ya faru ya fad'awa Khadija tare da d'orawa da "Kin ganta fa da kod'add'iyar fuska kamar an tafasa kabewa, wai Alhaji ya na bacci, kuma lokacin tashin shi baiyi ba, sai dai ko za ka dawo wani lokaci, ke kinji bak'in cikin da ya taso min a lokacin, kamar na d'auki man da takr suyar da shi na bad'a mata a fuska ta k'arasa sulala."


Rik'e ciki Khadija ta yi tace "Dan Allah bar maganar nan kafin ciki na ya k'ulle, wallahi ba zan iya da masifar nan ta ka ba."


Gyara zaman sa ya yi ya saita nutsuwar sa yace "Kinga ba wannan ba, ni fa dama na zo ne na fad'a mi ki jibi za'a kai kaya na, kuma ke ce wacce na ke so ta shige gaba a komai, dan ni a wuri na kamar ke ce ki ka min auren nan wallahi."


"Ba damuwa Nura, insha Allah zan kasance a duk wata hidima ta auren ka." Sun jima su na hira cikin d'aki kafin ya tashi tafiya bayan ya mata alk'awarin kawo mata amaryar shi bayan an kai kaya, haka ya tafi ya bar Khadija da Bilal da dariya duk sanda su ka tuna iskancin da ya sokawa Haseenah.


Da yamma Usman da kan shi yaje ya d'auko Aziza ya kawota gidan, suna zuwa sun tarar da Mubarak ya kawowa Haseenah maganin ta, Mariya kuma dama maganin mata ne da take anfani da shi ta bado a kawo mata, d'ayan tace ta had'a da madara tasha zai k'ara mata haiba ne da kwarjini a wajen shi, d'aya kuma tace ta binne a cikin gidan, hakan zaisa Khadija ko ta dawo ba za ta iya zama ba saita koma, dan ta k'ara rubtawa da ita kuma tace kafin ta binne ta samu takardar da alk'alami ta rubuta sunan Khadija akai,😂 *yaro man kaza*, Mubarak na tafiya bayan Usman ya gwangwaje shi da kud'i wai ya sa mai a moto, a lokacin anata kiran sallah magriba, Aziza ma alwala ta yi ta kabbara sallah hakan ya bawa Haseenah damar fitowa da maganin ta je wajen wata pliwa mai kyau mai bayar da sanyi wacce ke kusada panpon dake farfajiyar gida, nan ta durk'usa ta sa wuk'a ta tona rame ta binne ledar maganin, duk abinda take a idon mai gadi da yake fitowa daga ban d'aki da buta a hannu ya na kurkure baki, da sauri ya sake komawa ban d'akin ya na lek'owa dan tabbatar da abin da ya ke gani, ya na kallo har ta tashi ta koma d'aki ta yi alwala ta yi sallah, mai gadi ma alwala ya yi a gaggauce ya wuce masallaci, bayan magriba Usman ya shigo saboda zaije ganin Bilal, tun a bakin k'ofa mai gadi ya tsayar da shi ya fad'a mi shi fa da matsala a gidan nan, ya ga wani abun da bai yarda da shi ba, Usman da ya nuna kamar bai yarda ba sai ya ja shi har in da aka binne abun ya kuma sa hannun shi ya tone ya nuna mi shi, warware takardar ya yi duk da baisan me aka rubuta ba, nunawa Usman ya yi yace "Kune yan boko, ko za ka iya gane me aka rubuta anan?"


Da wani yamutsa fuska yace "khadija aka rubuta, sai me?"


Abu dai ya tumbatsa hakan ya sa Usman k'walla kiran Haseenah yace ta zo, nan ta same su tsaye gaban ta na tsananta bugawa tace "Gani."


Nuna mata takardar ya yi da ramin yace "Ke ki ka aje abin nan a ciki?" Da mamaki ta kalle shi tace "Ni kuma? Inji wa?"


Nuna mata mai gadi ya yi, nan fa Haseenah ta shiga rantsuwa ba ita bace Garba ma ya rantse yace da idon shi ya gani, k'arshe dai makirci ne ya yi aiki saboda kuwa kuka Haseenah ta saka ta na fad'in dama kowa ba k'aunarta ya ke ba, kowa bayan Khadija yake kuma ana d'ora mata laifin fitar Khadija daga gidan, dan haka ita ma barin gidan za ta yi in ya so saiya zauna shi kad'ai, hakan zai sa ba za'a zargi kowa ba, haba wa ai sai hankalin maza ya watse ya rasa nutsuwarsa amarsu tace za ta tafi, take a wajen yace mai gadi ya bar mi shi gida tunda dai shima ba k'aunar shi yake ba kuma munafiki ne, sam Garba baiji wani zafin korarshi da akayi ba, dan ya na da yak'inin akwai abin da ke damun ogan shi, dan haka ya kalli Haseenah yace "Kibi a sannu duniya ce ba matabbata ba, tabbas ni ina b'angaren Hajia uwar yarima, kuma wallahi d'an halak ne ni, dan haka zan mata hallaci a lokacin da babu wanda ya yi tsammani."


Juyawa ya yi ya bar gidan bayan ya tattare nashi ya nashi, shi kuma ciki suka shiga saida ya k'ara rarrashin ta ya nuna mata babu fa wanda ya isa ya b'ata ran ta kuma ya yi shiru, saida ya ga murmushin ta kad'ai ya shirya ya kama hanya, anyi sallah isha'i kenan ba jimawa Usman ya zo, k'ofa ya aje mota ya sallamo farfajiyar, yara ne ke ta wasa abinsu kasancewar gobe ba makaranta kamar sallah ce a gurin su, yaran na ganinshi su ka rumtuma wajen shi su ka rufe shi suna gaishe shi, farar ledar hannun shi ya fito da ita ya bawa kowa rabon sa mai alawa da mai chocolat, bawa Bilal sauran ya yi ya shafa kan shi yace "Kawunan ka na nan?"


"Kawu Ashir da kawu Habeeb ne su ka shigo, kuma su na b'angaren su." Wata ajiyar zuciya ya sauke dan ba ya son ganin su ko kad'an, cikin rad'a yace "Hajia fa?" Nuna masa ya yi yace "Ta na falon ta."


Hannun shi ya kama yace "To muje ka rakani na gaishe ta saina koma, sauri na ke." Falon Hajia su ka nufa da sallama su ka shiga ta amsa ta mu su izinin shigowa, zaune ta ke kan kujera cikin riga da zani mai kama da siket, kallo d'aya Usman ya mata ya d'auke kan shi saboda kwarjinin da matar ke ma sa baya iya had'a ido da ita a baya ma bare yanzu da ya san shi mai laifi ne, duk da dai dattakon matar na birge shi matuk'a, dan mace ce mai kamar maza wacce kusan gaba d'aya tarbiyar yaran ita ce ta yi ta, a kunyace su ka gaisa ita kam ganin haka ya sa ta saki fuska sosai fiye da ma farko su na gaisawa, mik'ewa ya yi cike da kunya ya na fad'in "To Hajia ni zan koma, dama ina sauri ne nace dai bara na biyo."


Gyara zama ta yi tace "Maman shi ai ta na ciki, ka wuce ku gaisa sai ka wuce ko." Da wutsiyar ido ya d'an saci kallon ta ya na sosa kai, kama hannun shi Bilal ya yi sai cukuikuyeshi ya ke, kallon shi Mama ta yi ta harare shi tace "Kai dallah miye haka malam sai wani cakumar shi ka ke kamar wani wutsiyar shi, dawo nan ka zauna har ya fito."


Ta nuna mi shi kusa da ita, mak'ale kafad'a ya yi yace "Wai ke ina ruwan ki, ba Abba na bane, karfa ki ga idon Abba na ki b'ata min rai, sai na ce na fasa dawo da ke d'akin ki."


Rufe baki Mama ta yi tace "Ka ji masharranci kuma, to yaushe ka kore ni da har yanzu ba ka dawo dani ba?"


Dariya Bilal ya yi yace "Ka ji ko tsohuwar nan, wato so ki ke Abba ya bani hak'uri na dawo da ke, to na k'i d'in sai kinyi sati d'aya babu kud'in cefanai."


Usman da ke dariya shi dai cewa ya yi "Ka na manta wani abu yarima, na fad'a ma ka kafin ma Mama ta san da kai mu ta fara haihuwa, shin ka na ganin duk yawan mu za mu iya barin ta da yunwa? Abu ne da ba zai yiwu ba ai."


"Ah to fad'a mi shi dai, kuma da ka gan shi nan cika bakin ne kawai, gishiri wannan na dala biyar bai tab'a bayarwa aka siya ba, watak'ila ma ko sabon bebe da zai zo yanzu na yi miji idan na ga ya fika k'ok'arin cefanai."


Dariya Bilal ya yi yace "To ai dai sai na sake ki sannan za ki koma gare shi, kuma idan fa aka haifo min mace ya za ki yi?"


Shiru kawai Mama ta yi sai murmushi da take ta na kallon shi, gwalo ya mata yace "Yeeeehooo, na rufe mata baki, ai ba'a aure akan aure, kuma nasan ke kishi ya mi ki yawa."


Sai lokacin Usman ya juya ya nufi d'akin Khadija, Bilal kuma zaune ya yi kusan Mama ya d'ora kan shi akan k'irjin ta, ture shi ta yi tace "Kai d'aga min nono malam, k'walelen kare da hantar kura fa, tom."


Saida ya sa hannu ya tab'a nonon yace "To me zanyi da wannan tsohon nono, abin duk ya yamutse, ga na Mummy ta nan sabo dal a leda."


Bushewa su ka yi da dariya dukansu ta janyo shi jikin shi su ka rumgume juna, tabbas kamar yanda ta ke matuk'ar k'aunar Khadija matsayin ta na mace, haka a cikin jikokin ta ma take matuk'ar k'aunar Bilal saboda wayon shi, yaro ne mai shiga rai dan shi ko irin mahaukaciyar k'uruciyar nan baiyi ba, hasalima cikin yara za ka ga shi wasan shi ta dabance, sannan bai cika son hayaniya ba kuma baida yawon surutu, idan kaji bakinshi cacaca to sun had'u ita da shi ne.


Tun kafin Usman ya shiga ya ke tunanin abin da suka fad'a na maganar bébé da haihuwa, me su ke nufi? Khadija ciki gare ta kenan? Dama k'ofar a bud'e ta ke dan haka k'arasa tura ta kawai ya yi ya shiga, zaune take akan gado da littafin *hisnul muslum* ta na karantawa, ta na kallon shi ta d'auke kai ta mayar kan littafin tace "Me ya sa ba za ka nemi izini ba kafin ka shigo?"


Saida ya k'arasa shigowa har ya zo daf da gadon yace "Saboda da kai da kaya duk mallakar wuya ne."


Kallon shi ta yi fuska ba annuri tace "Kan na iya zama na ka amma banda kayan saman shi."


Murmushi kawai ya yi yace "Haka ake tarban bak'o a garin ku?"


"Duk bak'on zai iya shiga kowane lungu da sak'o na gida ba bak'o bane, musamman ma irin ka da ba sa neman izini kafin su shiga, kuma ina da tabbaci ba waje na ka zo ba, dan haka me zai sa na damu kai na?"


Kafe ta ya yo da ido ya na kallo kamar ya na karatun wani abu, jin shirun ya yi yawa ne ya sa tace "Bilal fa ya na farfajiyar gida."


"Na gan shi ai." Kallon shi ta yi tace "Hajia kuma ai ta na falo." Saida ya zura hannayen shi aljihu yace "Ita ma mun gaisa."


Mayar da hankalin ta tayi kan littafin ta tace "Da kyau." Ci gaba ta yi da karatun ta shi kuma yace "Ya beby ya ke?"


Cak ta tsaya amma ba ta kalle shi ba sai rarraba ido da ta fara yi, tambayar da take wa kan ta ita ce ya aka yi ya sani? Dan ba ta san Mama ta je ta fad'awa su Hajia ba, rasa abin fad'a ya sa Usman zaune kusan ta ya na k'are mata kallo yace "Kenan da gaske ne? To amma me ya sa ba'a fad'a min ba?"


Kallon shi ta yi cikin dagiya tace "Waya fad'a ma ka ina da ciki? Ko kuma ka na so ka b'ata min rai ne?"


"Ban gane ba? Bayan da kunnuwa na naji Mama ta na fad'a, gashi kuma na tambaye ki amma duk alamu sun nuna gaskiya ne."


Murmushi ta yi tace "Ka taya ni addu'a Allah ya bani nawa nima, amma yanzu ai amaryar ka ce ke da shi, duk da ka ce ina mata bak'in ciki."



Kafe ta ya yi da ido yace "Ki rantse da Allah ba kya da ciki." Cikin mamaki tace "Rantsuwa kuma? To miye na rantsuwar? Abin da na ke nema ido bud'e zan samu kuma na kasa fad'a ma ka."


"Ba ki ke nema ba dai, mu ke nema, kar ki manta da haka, har yanzu ina son sake ganin abin da zai fito daga tsatsonki." Kallon shi kawai ta yi shi kuma ya mik'e yace "Kin dai tabbatar ba ki da komai?"


"Eh." Ta fad'a, sake jajjadawa ya yi "Kin tabbatar babu?" Cikin k'osawa tace "To! Na ce babu, babu, idan ba ka yarda ba ka je ka tambayi su Maman ka ji, su a zatonsu ne ciki gare ni saboda rashin lafiyar da na yi, ni kuma wahala ce ta sani wannan rashin lafiyar na dukan da ka min."


Murmushin gefen labb'a kawai ya yi ya sunkuyo da kan shi kusan fuskar ta yace "Kin tabbatar dai ba kya tare da ciki na ko?"


K'asa ta sauke idon ta hakan ya sa yace "Sai kin kalli ido na." Kallon shi kam ta yi tace "Eh, babu komai." Tsaye ya mik'e yace "Shikenan, amma ki tabbatar duk ranar da na ji labari yasha bambam wallahi sai kin gane kurenki."


Saida ta sake kallon idon shi tace "Na yarda." Jinjina kai ya yi yace "Shikenan, saida safe."


Juyawa ya yi ya fice daga d'akin ta bishi da kallo, saida ta tabbatar ya bar gidan ta fito ta samu Mama ta tambaye ta, ba ta b'oye mata komai ba hakan ya sa tace dan Allah kar su sake ya san ta na da ciki, dalili Mama ta tambaya saita nuna mata kawai ba ta so ya sani yanzu, dan ta na tsoron rashin imanin yarinyar nan matar shi.



*Bayan kwana biyu* an kai kayan Nura, kuma kamar yanda ya fad'a Khadija ma saida ta halarci kai kayan, kuma da yake a dangi ma ba kowa bane yasan abin da ya faru, Haseenah dama ba ta je ba dan haka ma ba su had'u ba, anje lafiya kuma ayi duk abin da ya dace, lokaci kawai za'a jira *wata uku* mai zuwa lokacin hutun farko na yan makaranta, duk lokacin da biki ya taso irin haka akwai wanda Khadija ce ta ke mu su d'inkin anko, yanzun ma ba ta gaza ba ba ta kuma duba abin da ya faru ba, haka ta d'inka kaya kala takwas ta aikawa kowa na shi daga ciki har da Hajia da kuma k'annan ta guda uku, k'annan Baban Usman biyu sai wasu tsofaffi biyu suma, kamar yanda Nura ya yi alk'awari ya kawo Choukra ta wuni gidan su Khadija, sai dare ya zo ya d'auke ta su ka koma bayan tasha goma ta arzik'i. 


*Haka* abubuwan suka ci gaba da tafiya da dad'i ba dad'i, Khadija na kula da cikin ta cikin kulawa sosai, Bilal na karatun shi hankali kwance ba tare da matsala ba, ranar da babu karatu kuma Khadija na kiran Nura ya zo ya d'auke shi ya kai shi wajen su Hajia, amma basu tab'a katarin had'uwa da mahaifin shi saboda yanzu gida sai su yi sati kwana shida ko biyar basu gan shi da idon su ba, wayar ma sai da k'yar ake iya samun shi wani lokacin, kuma har yanzu bai san Khadija na da ciki ba, dan malam yace ba ya so ya sani sai in Khadija ce ta fad'a mi shi ko kuma ya gani da kan shi, a haka har aka cinye wata *uku* wanda ya yi daidai da fara shagulgulan bikin Nura, a lokacin Khadija har ta fara zuwa awo dan cikin ta na wata *biyar* ne har ya fito ta yanda duk wani mai ido zai iya ganin shi, tun kwana biyu saura Khadija ta turo Bilal ya kwana nan har zuwa ranar bikin tare da gudummuwarta da na Mama da kuma ta su Ashir, gudummuwar da suka bayar ko yan uwanshi babu wanda ya mi shi wannan bajin ta.


Wajen Haseenah ma haka abin yake, abin da ranta ya so ta ke ci tasha wanda ya mata, Aziza tuni ta jima da gane kurenta, dan kuwa duk aikin gidan ne ita ce ba dare ba rana, idan ba ta yi ba Usman ya balbale ta da jaraba, Haseenah na zaune ta na gatsar 'ya'yan itatuwa, sa'a d'aya shine ba'a cika yin girki a gidan ba kusan kullum saida a siyo daga waje, wani lokacin Aziza ta ci idan an siyo ko kuma ta d'ora wani abu ta ci, duk wannan bai cika damunta ba kamar yanda ta ga Usman ya zama kamar karan farautar Haseenah, in dai ya na gari to ya na gida nanak'e da ita ko gajiya ba ya yi, duk bak'on da zai zo wajen ta to fa haka zai dinga rawar jiki ya na aikawa ana siyo musu abin tab'awa, idan sun tashi tafiya kuma ya wadata su da kud'i da sunan kud'in taxi, haka ita kan ta Haseenah kud'i yake kashe mata kamar ba gobe, a wata *ukun* nan sai Haseenah ta shirga wata murgujejiyar k'iba, masha Allah ko fa kai mak'iyinta ne ka ganta dole k'ibar da ta yi ta burge ka dan ta mata kyau, hakan kuma ya sa Usman sake narke mata dan abun har kusan haukata shi take, ga magunguna da take aiki da su, ga k'iba (wanda kowa yasan akwai sirrin dake tattare da k'iba ba) ga kuma ciki, duk tsiyar nan da ake tsulawa Aziza ta kasa fad'awa kowa saboda kunya, to idan ita ma tace ta mallake shi kenan tsakanin ita da Khadija wacece ta mallake shi? Hakan ya sa ta yi shiru, ko gida taje idan aka tambaye ta wai ya na nan sai dai tace eh, idan ya na nan d'in, dan yanzu ko balaguro ya yi da k'yar yake iya sati d'aya zuwa kwana goma ya dawo, shiru take yi ba ta fad'a mu su komai inda su kuma su ka damu sosai su ka fara maganganu akai.


*Yau* Alhamis ya rage nan da kwana biyu za'a d'aura auren Nura, su Rabi'a sun hallara ana ta kujuba-kujuba Aziza ta shigo gidan, dukan su kallon ta su ka yi da mamakin ganin ta ita kad'ai, Husseina ce tace "Aziza ke kad'ai ki ka taho?"


Saida ta nemi gurin zama tace "Ni kad'ai na taho."


"Ina Haseenah?" Cewar Rabi'a, tab'e baki ta yi tace "Ta na gida, wai ba ta jin dad'in jikin ta."


Hajia da ita ba wannan ne damuwar ta ba cewa ta yi "Ina shi Alhajin ya ke?"


"Ya na gida na baro shi, na ji ya na cewa ko zai kai ta asibiti." Girgiza kai Hajia ta yi tace "Allah ya kyauta, gaba d'aya ta mayar da shi wani sha-katafi, ko motsi taji a cikin ta sai ta fad'a mi shi shi kuma sai yace aje asibiti."


Tab'e baki Aziza ta yi tace "Ai kam ba shi da maraba da shanyayye."


"To ai ba kama bace, duk alamu sun nuna shegiyar yarinyar nan ita ce mai laifi, wallahi sai yanzu ne nake na tabbatar da tun farko *kallon kitse mu ka yi wa rogo*."


Nura da ke fitowa daga d'akin shi cikin sauri ne ya kalle su dukansu yace "Ku sai yanzu ma ku ka sani kenan? To mu zuba zuwa mu ga mu da ku waye zaiyi nasara, 'yan bayan Khadija ko 'yan bayan wannan mai kama da agwagwar."


Hajia ce tace "Abun bak'in cikin ma wallahi ta yanda gaba d'aya ta raba shi da mutane, d'an taimakon da muke san mu mi shi bamu ma gan shi ba bare mu taimaka d'in, amma ba dan haka ba da yanzu nasan komai ya wuce, kuma kinga shi malam ya ma bar maganar kamar baisan me ke faruwa ba."


Nura dai ficewa ya yi ya kama sabgar gaban shi sai Rabi'a da tace "Ai kuwa ba za mu yarda ba wallahi, ni zanje gidan na ga me ke faruwa, wallahi saina fad'a mata magana."


"Ai kuwa in ban cire ki a cikin dangin shi ba to tabbas zaki sha dukan tsiya." Cewar Aziza, da mamaki Rabi'a tace "Kamar ya duka? Ba shi da lafiya?"


Aziza ce tace "Lafiyar shi lau, amma babu mai tab'a ta ya yi shiru, akan haka fa ya kori Garba mai gadi."


Hajia ce tace "Ni kai na da zan ganshi da sai ran shi ya b'ace, tunda aka fara hidimar nan har yanzu banga k'eyar shi gidan nan ba, kuma ni har yanzu daga Nura har malam banji wanda yace ya bashi gudummuwar bikin nan ba, akwai abubuwa dayawa wanda da shi ne mu ka dogara, ba dan Allah ya rufa mana asiri ba yanzu yarinyar nan sun aiko da wannan gudummuwar ta su da ya za mu yi."


Hassana ce tace "Bai fa bayar da komai ba hajia?"


"Ni dai bai bani ba, kuma Nura da malam ba su fad'a min ba, kinga ko abune mai wuya ace sun kasa fad'a min."


Husseina ce tace "Ah ba ma ta yiwu ai, in har ya bayar dole sai ki sani Hajia."


"To me ya ke nufi? Ba zai bayar ba ko ta hana shi?" Cewar Rabi'a, Hajia ce tace "Gidan fa da za akai amarya ma Murtala ne ya bashi gidan, da ina jin har yanzu ba mu san ina za su zauna ba."


"Wallahi sai naje, sai dai ya kashe ni." Cewar Rabi'a cikin b'acin rai ta na mik'ewa ta yi kam ba b'ata lokaci ta saka hijabin ta, Hassana ce tace ita ma za ta je ta jira ta, Husseina dai cewa ta yi "Allah ya kad'e hau." Ko amsata ba su yi ba su ka tafi, cikin k'ank'anin lokaci su ka isa gidan, sunyi nasarar samun falon Haseenah bud'e, shiga su ka yi da sallama amma ba kowa sai telebijin ita kad'ai, zaune su ka yi sai Rabi'a da ke ci gaba da rumtuma sallama dan suji su fito.



*Alhamdulillah Ala ni'imatul islam.*

27/02/2020 à 13:42 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *33*



Tun su na sallama har su kai su ka yi shiru babu wanda ya amsa, suna magana k'asa kasa su ka ji an bud'a k'ofa, mayar da kallon su su ka yi ga mai fitowa, wa za su gani in ba Usman ba da doguwar riga kamar wanda ya taso daga bacci, da kallo su ka bishi har ya k'araso ya zauna ba su daina kallon shi ba, cikin wani cijewa yace "Ashe kune? Daga ina haka?"


Hassana ce tace "Ina wuni?" Bai amsa ba sai shafa kan shi da ya fara yi, Rabi'a ce tace "Dama Hajia ce tace mu zo mu ga ko kuna lafiya, daga kai har Hassenah ta jima ba ta gan ku ba."


Kamar wanda aka takura wajen maganar ya ke fad'in "Tsohin nan matsala ce da su wallahi, ko shekaran jiya fa na je gidan mun gaisa, lafiya k'alau na ke ni, ita ce ma dai ba ta jin dad'i, yau lafiya gobe ba lafiya."


Hassana ce tace "Shi ya sa har an fara shagulgulan bikin nan amma har yanzu babu wanda ya gan ta? Yah Fodio ka na ganin hakan ya yi daidai domin Allah, akwai fa abubu..."


"Ke dakata." Ya katse ta ya na mik'ewa tsaye, da yatsa ya nuna ta yace "Ke ma 'yar hassadar ta ce kenan? To da alama ba Hajia ce ta turo ku ba kun zo ne ku min rashin kunya, to ba na da lokacin ku, idan kun gama ku rufe mana k'ofar."


Ai kuwa ya na gama fad'a ya koma in da ya fito ya bar su nan, kallon juna su ka yi Rabi'a tace "Kutumar bala'i, yanzu haka abin ya zama dama? Lallai."


Mik'ewa Hassana ta yi tace "To ai sai mu tafi ko? Tunda ba gidan uban mu bane."


Fita su ka yi su ka bar gidan ba yanda su ka iya,  ko da su ka je gida nan fa aka bud'a sabon shafin hira akan abubuwan da ke faruwa, duk da haka kuma Aziza babu abin da tace dan ita dai kam kunya ma take ji, ana sallah magrib Usman ya dokowa Aziza kira wai ta zo gida ya na son ganin ta, gabanta ne ya dinga fad'uwa tunanin ta kar ace ya yi tunanin ita ta fad'a mu su wani abu, da k'yar ta kimtsa ta fito jiki na rawa ta zo bakin titi kuma ta kasa samun adaidaita da wuri, hakan ya sa ta sake b'ata lokaci kafin ta je, ta na zuwa gidan ran Usman ya gama b'aci saboda Haseenah ce ke neman ta amma ta b'ata lokaci, dan haka ta na shigowa falon saukar mari ne ya mata maraba, bai tsaya iya nan ba saida ya dinga masifa wai ta na can ta samu gulma ta bar aikin gida anan, Haseenah na zaune kan kukera ta kalle su tace "Kai ba ka yi mamakin zuwan su Hassana ba? Ai bayan fitarta ne su ka zo ma'ana ta fad'a mu su wani abu, suna can gidan ku sun baza tabarmar gulmata su na yi da ni, dan nasan dama babu mai so na kafatanin ahalin ka."


Ido ya rufe ya dinga zagin Aziza kamar ba ciki d'aya su ka fito ba, kafin daga bisani yace ta wuce ta gyarawa Haseenah d'akin ta, da "To." Ta amsa, ta na kallo ya kama hannun Haseenah suka nufi falon shi, ta na ganin haka ta shiga d'akin da take kwana ta gama had'a kayanta ta fito ta bar gidan, tunda ba za ta iya rama marin ta ba amma kuma in ba ta bar gidan ba tasan dole wata rana za ta jiwa Haseenah ciwo, dan haka ta bar gidan ba tare da sanin su ba ta koma gida.



Bayan sallah la'asar aka ce ana sallama da Khadija, da mamaki ta fita amma wa za ta gani sai Baba Garba mai gadi, da fara'a kamar za ta had'e shi ta mi shi izinin shiga ciki, har falon Mama ta saule shi in da Mama ke zaune ita ma, gaisawa su ka yi sosai kafin ya fara da "Hajiar yarima bayan barin ki gidan nan abubuwa da dama sun faru, tabbas mijin ki ba'a hayyacin shi ya ke ba, shiga baga ne kawai, amma insha Allahu komai ya k'are tunda har na je gida lafiya na dawo lafiya, kin gan shi nan abin da ya tsayar da ni." Ya fad'a ya na mik'o ma Khadija wani k'ullin magani k'arami, karb'a ta yi ta na kallo kafin ya d'ora da "Wannan maganin na karya sihiri ne, wani kaka na ne ya ke bayar da shi, maganin ya na da wuyar samu sosai, hakan ya sa ya ke da tsada ga wanda zai siya duk da dai ba ya da farashi, amma ke kyauta na karb'o mi ki shi saboda girman ki, Hajiar yarima wannan maganin da ki ka ji da ganin shi wallahi na rantse mi ki ko da bokan india mutum ke tink'aho to anfani da shi saiya karya komai, ba na da tamtama akan shi, tabbas na ke da, ki jaraba shi ki gani da yardar Allah za'a dace."


Ba tare da ta daina kallon shi ba tace "To amma ya ake anfani da shi?"


Da yatsa ya ke mata alama cewa "A buta za'a zuba maganin sai a saka ruwa ya yi wanka da shi, idan ya fito ya tsane jikinshi sai a samu garwashin wuta kuma a zuba maganin ciki a turara, ba dole sai ya shak'a ba ko yaje kusa da wutar, jikin shi ne kawai ake so hayak'in ya shafa lokacin da babu sutura a jikin shi, sai kuma wannan." Ya fad'a ya na sake mik'o mata wata ledar yace "Wanna kuma a tabbatar ya shak'a a hanci sau uku, insha Allahu idan ya shak'e shi zaiyi atshawa, to da izinin Allah duk wani bala'i dake kansa zai bar shi ko ba'a so."


Daga Khadija har Hajia godiya su ke masa amma ya na cewa ba komai, haka ya tashi tafiya su ka bashi kud'in mota ma amma ya k'i karb'a yace ya yi ne saboda Allah kawai, sai lambar shi kawai sabuwa da Khadija ta karb'a ta na ci gaba da k'ara masa godiya, nan su ka shiga tattauna yanda za su saka Usman yin wanka da maganin nan, gaba d'aya kan su ne ya kulle dan haka Mama tace kawai ta bari har bayan bikin Nura in ya so sai su san abinyi, haka akayi Khadija ta kai maganin ta nasa a cikin jakar ta da ke kusa da gado, bayan sallah magrib kuma su ka yi waya da Bilal har ya na fad'a mata shi gaba d'aya surutun gidan ya dame shi, tunda yamma ake ta maganar Abban shi da matar shi har ya fara jin haushin mutanen, hak'uri ta bashi tare da cewa ya fita waje yanzu ai da malam ya shigo zai zauna k'ofar gida, haka akayi kam sai k'ofar gidan kad'ai ya samu nutsuwa.


Ko da Aziza ta zo ana sallah isha'i lokacin malam da Bilal na masallaci, da kuka ta shigo gidan aka tarbe da tambayar lafiya? Nan ta fad'a ma Hajia abin da ya faru kuma ran ta ya b'ace sosai, wannan karan an tab'a mata autar ta dan haka dole rai ya b'ace, ji ta yi ba za ta hak'ura ba dan haka ta kira shi a waya, ya na d'auka ita ma ta zazzage shi da masifa har ta na fad'in ya zama lusari yarinya k'arama na juya shi, shi dai k'ala bai ce ba har ta gama ta kashe wayar, sai lokacin ne su ka san Aziza ba ta gidan, ko a jikin su kam dad'i ma su ka ji da ta tafi d'in. 


*Washe gari* ta kama juma'a, malam na sallah asuba ya dawo gida ya canza kaya ya fita, a k'asa ya ke tafiya cikin nutsuwa ya na zikiri har ya yi doguwar tafiya, tashar mota ya isa da ke *'yar sonita*, mota ya samu da babu komai a ciki ya fad'i garin da za shi, saboda biyan buk'ata yace shata ya ke so a kai shi a dawo da shi, dama garin ba wani nisa ne da shi ba, nan ya shiga tare da dreba su ka d'auki hanyar da zai sada su da wani k'auye da ake kira garin *Bamo*, har k'ofar gida aka aje shi ya kusa yi sa'ar samun wani tsoho da ba za su gaza wari ba a k'ofar gidan akan tabarmar kaba, daga yanda suka gaisa suke dariya zai nuna ma ka ba sanin yau bane ko kuma ma abokai ne, zaune su ka yi daga cikin wata runfa dake gefe akan wata tabarmar da ke d'auke da buzun akuya, nan ne har tsohon ya ke fad'in "Mu muna shirin tafiya garin auwa yamma kuma kai sai ka ga, lafiya kuwa?"


Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "Lafiya ba lafiya ba *Lawali*, halin da gidan nan ke ciki ne ma ya sa na kasa hak'ura har yamma ta yi ka zo ni na zo da kai na."


Cikin nutsuwa yace "Toh, me ya ke faruwa ne haka malam Ali?"


Nan dai bai tsaya b'ata lokaci ba ya fad'awa tsohon abin da ke faruwa a gidan na shi, malam Lawali ne yace "Amma yanzu har wannan iskancin na faruwa amma ka kasa sanar da ni, wannan shegentakar har ta bar kan wasu ta dawo kan yaran mu, gaskiya banji dad'i ba da sai yanzu ka ke fad'a min."


"Da farko na d'auka abun na ta ba zaiyi k'amari haka ba, amma daga yanda ta raba shi da kowa na shi ne ya nuna min ita d'in dama ba mai son shi da arzik'i ba ce, na fara bashi taimako da kai na wanda na san zai warware komai cikin sauk'i, to matsalar da aka samu baya ma zuwa gidan akai akai bare har maganin ya karb'i jikin shi, shi ya sa na ce to bari na sada matsalar nan da kai."


Cikin b'acin rai Lawali ya mik'e ya nufi cikin gidan shi ya na fad'in "Ina zuwa bani minti biyu, wannan ai maganar banza ce da wofi, mu za'a kawowa iskanci har gida, yo badan ma yaran sun zama 'yan zamani ba basa son shan saiwa na tsarin jiki yo da ko kusa da shi ta isa ta zo ma, kuma kai ma da ka fad'a min da wuri da ko kwana d'aya ya yi a cikin tarkon ta, ga dukkan alama ba ta san wata aura ba shi ya sa, mu da ake baro k'asa mai tsarki azo neman taimako wajen kuma a dace da yardar ubangiji shine har d'an mu zai shiga wannan halin kuma ya kwashe watanni a kasa fito da shi, aikin banza aikin wofi." Haka ya shiga gidan ya na ci gaba da bambami har ya shiga d'akin shi ya d'auko wasu sayun magani fari dogaye ya fito da shi, kawo mi shi ya yi yasa a leda ya zauna kan kujera ya juya bayan shi ya d'auko robar lemu sai dai ruwa ne a ciki fari tas ya bashi yace "Da wannan ruwan za'a jik'a magani, ruwan da ya yi alwalan sallah magriba da su sai ka cire maganin a zuba ruwan alwalar, idan ya yi sallah sai ya yi wanda da su amma a buta za'a zuba ruwa."


"Na fahimta, nago..." Katse shi ya yi da cewa "Kar ka fara min godiya, in ba haka ba maganin ba zaiyi ba ma, ko ka manta wanene kai a wuri na?"


Dariya malam Ali ya yi ya mik'e, saida ya shiga cikin gidan su ka gaisa da matan kafin ya fito ya samu dreban nan su ka wuce da cewa sai sun zo suma wajen bikin Nura, kamar bai je ko ina ba sai gashi ya dawo ko rana bata gama haska duka gari ba, jika maganin ya yi da wannan ruwan  kafin ya shiga wata sabgar ba tare da ya fad'awa kowa ba.



*Yamma* lik'is Khadija ta fito bayan ta biya ta karb'owa Bilal sabon d'inkin shi sannan ta zo gidan, ta na sallama kam gida dama ya samu hallarar dangi har an fara d'ora tukunyar abincin d'aurin aure, nan fa kowa Hajia Khadija Hajia Khadija, sosai ta gaisa da mutane kafin ta wuce d'akin Hajia, abun mamaki sam Hajia kasa had'a ido ta yi da ita sai haka suka gaisa cikin kunya, su Hassana ma da Rabi'a haka, sai ma wani sabon al'amari daga gare su na kowa ya na son ya mata magana, wurin zama suka samar mata tare da kawo mata ruwan sha da lemu, sai dai suma ba kowa ke kallon ta ba, ita kam ko a jikin ta sai dai ba ta sakar mu su fuska ba, kuma ta zo gidan nan dan ta ga malam ta bashi wannan maganin, dan ita bata san yanda za ta sa shi ya yi wanka da shi ba, ganin sun baibaiye ta ya sa ta fito tace su yi aiki, sai lokacin Bilal ya shigo Khadija ta tambaye shi ina malam? A cewar shi ya na k'ofar gida tare suke da shi ma, aika shi ta yi ya yo ma sa magana, a soron gidan su ka had'u da malam in da ta bashi magungunan ta fad'a mi shi duk yanda akayi, murmushi malam ya yi ya mata godiya tare da fatan alkairi, ciki ta koma ta yi zaune su na b'are tafarnuwa, malam kuma na fita ya kira Usman a waya ya na d'auka yace "Duk abin da ka ke ka zo gida yanzu ka same ni."


Usman da ke tsaye gaban gado ya na kallon Haseenah ta na shiri zai kai ta can ne yace "To malam, dama yanzu za mu taho gidan."


Datse kiran kawai malam ya yi yayin da ya bi wayar da kallo, kallon Haseenah ya yi da ta mik'e ta saka hijabin da ya dace da kayan ta haka ma jaka da takalmi, a gaskiya ta yi kyau sosai cikin wani bak'in leshi mai ji da kud'i da kyau, kwalliyar da ta yi kai kace yau ne bikin kuma ba aiki ne za ta tafi kamawa ba, wayoyinta biyu ta d'auka duka a hannu ta rik'e suka fito, da kan shi ya bud'e mata k'ofa ta shiga kafin ya ja suka bar gidan yamma ta k'ara yi sosai.


Daga nesa ne aka fara kiran sallah hakan ya sa Khadija tashi ta yi alwala ta shiga d'aki dan yin sallah, ta na shiga d'aki ta kabbara sallah ta ji sallamar Usman, saida gaban ta ya fad'i kafin ta saita nutsuwar ta ta ci gaba da sallar ta, gaisawa ya yi sosai da mutanen da ke wajen in da Haseenah ke gaishe da mutane ciki-ciki, fita ya yi tare da malam ysu ka yi alwala in da malam ya tara ruwan shi ya aje suka nufi masallaci, mata ma alwala suke su na sallah, Khadija na fitowa daga d'aki Haseenah za ta shiga, dukansu gadara su ka nuna in da Haseenah ta had'a da girman kai da raini, babu wacce ta matsawa wata dan ta wuce hakanne ya sa su ka bangaji kafad'un juna su ka wuce, tsaki Haseenah ta k'ara da shi wanda ya sa Khadija jawo hijabin ta ta kalli fuskarta tace "Kamar tsaki na ji kinyi ko? Da ni ki ke?"


Cikin nuna isa tace "Sake min hijabi malama." Dawowa Khadija ta yi cikin d'akin yanda ta ke fuskantar ta da kyau, k'ara shak'o hijabinta ta yi za ta yi magana Hassana ce ta shiga tsakani tace ma Khadija "Dan Allah yi harkar gaban ki, kinsan sai ka kula kashi ka ke jin warin shi, kare kuma ai ba ya haushi shi kad'ai."


Kallon ta Khadija ta yi tace "Ta ci albarkacin ma su albarkaci." Ta na fad'a ta fito daga d'akin ta na mu su sallama, Haseenah kam kallon Hassana ta yi wato ma ita ce karyar? K'wafa ta yi a ran ta ta zauna ko sallah ba ta yi ba, ta na kaiwa k'ofar fita malam ya tiso k'eyar Usman zuwa d'akin shi, tsaye ta yi su ka yi sallama da malam Usman kuma idon shi na kan cikin ta dake cikin hijabi ya ke ganin kamar gizo, shigewa malam ya yi Usman kuma ya tsaya bakin k'ofar k'ik'am, rab'awa Khadija ta yi za ta wuce sai kawai ya had'a ta da bango ya rufe kamar zai rumgume ta, kallon fuskar ta ya ke cikin wata irin murya yace "Me na ke gani a jikin ki ne haka?"


Fuska a had'e ta kalle shi ta na sake gyara hijabinta tace "Me ka gani?" Hannu ya zuro zai tab'a cikin ta yi saurin bige hannun shi ta ture shi ta kalle shi tace "Ka zama mai d'a'a mana, haka kawai sai ka tab'a jiki na."


Za ta fita ya rik'o hijabin ta yace "D'a'a? Ni ne marar d'a'ar?" Kafin ta yi magana ya fizgo ta ya had'a da bango, saida ta rintse ido tace "Ashhhhh." Saboda zafin da taji, hannu ya sa cikin hijabin ta ya na fad'in "Bara kiga rashin d'a'a, ke da kinsan ba na da d'a'ar kuma ki ka aure ni? Yanzun ma fitsara za ki min kenan." Da sauri ta rik'e hannun shi da ke shirin shafa cikin ta, kallon idon ta ya yi yace "Ban sani ba ko gizo ne ido na ke yi min, amma sai na ke gani kamar ciki ne a jikin ki."


Shiru ta yi ta kasa d'ago kai ta kalle shi, hannunta da ta rik'e na shi hannun ya kama yatsunta sosai ya na murzawa tare da juyasu son ran shi, tun ta na jurewa har ta fara matse ido saboda mugunta ce yake mata, jin idon ta na neman kawo ruwa ne ya sa ta kalli cikin gidan tace mi shi "Malam fa na jiran ka." 


Da sauri ya saki yatsunta ya d'an ja baya ya juya ya kalli cikin gidan shi ma, ta na ganin haka ba ta b'ata lokaci ba wajen takawa da sauri ta bar soron gidan, juyowa ya yi dan ya kalle ta sai ya ga wayam, cije leb'e ya yi tare da k'wafa yace "Wato ni za ki rainawa hankali ko, ki na d'auke da ciki na amma ki na b'oye min, wallahi na tabbatar da gaskiya sai ran ki ya yi mugun b'aci, sai kin gane ba'a min haka a zauna lafiya."


Ciki ya shiga ya samu malam a d'akin shi, abun mamaki shine izini da malam ya masa ya shiga ban d'akin shi ya yi wanka da ruwan da ke cikin bokiti, idan ya gama sai ya d'auki wanda ke cikin buta suma ya yi wankan da su, yanda fuskar malam ke had'e ya sa dole bai iya tambayar komai ba face shiga ya yi abin da aka ce, tunda ya yi wanka da ruwan cikin bokitin nan ya ji kan shi ya masa bala'in nauyi, jiri ne ya dinga d'ibar sa har saida ya rik'e kan panpo kafin ya ji ya fara masa sauk'i, butar ya d'auka ita ma ya kwararo ruwan daga sama har k'asa, rawa ya ji jikin shi ya d'auka kamar mazari, bala'in da yake ciki ne ya sa ya kasa sako kayan shi sai towel d'in malam da ke rataye ya d'auro ya fito, malam na zaune ya na jiran shi da kaskon garwashin wuta, har zaiyi zaune saboda abin da yake ji sai malam yace "Dakata."


Tsaye ya yi malam yasa maganin nan ya na kewara shi da shi, Usman da hatta numfashin shi ya fara canzawa kasa tsayuwa ya yi sai kawai ya fad'i k'asa kwance ya na rawar d'ari, k'amk'amewa ya yi sosai ya na rawar d'ari, sunkuyawa malam ya yi yace "Fodio lafiya ko? Me ka ke ji?"


Cikin hard'ewa da hak'oran sa keyi ya iya had'a kalmar "S...ss..an..yi...na..ke.ji." Aje kaskon malam ya yi ya shiga uwar d'aki ya d'auko mi shi bargo ya na zuwa ya rufa ma sa, d'auko wannan garin maganin ya yi ya zauna k'asa kusa da shi ya bud'e ledar ya dangwalo da yatsunshi biyu ya kara masa a hanci yace "Shak'a, shak'a Fodio kaji."


Shak'awa ya yi duka hudar hancin shi kafin yaja zanin rufar ya sake rufe kan shi, mik'ewa malam ya yi amma shi kan shi saida ya yi atshawa guda hud'u, Usman kam da ya kama atshawa tun ya na yi daga zaune har saida ya bud'e rufar ya tashi zaune, atshawar da ya yi ba iya ka kafin ta tsagaita mi shi, jingina ya yi da kujerar da ke bayan shi ya na dafe da kan shi, da k'yar ya fara furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, la'ilaha illalah, Muhammadur- rasulillahi sallalahu alaihi wassalam."


Matsowa malam ya yi kusan shi yace "Fodio ya ka ke ji yanzu?" Ya na dafe da kan shi cikin yamutsa fuska yace "Gaba d'aya ji na ke kamar ba ni ba, kamar na farka daga wani mummunan bacci na ke ji."


"Alhamdulillah, Allah kai ne abin godiya." Cewar malam kafin ya mayar da kallon sa ga Fodio yace "Ka tashi ka saka kayan ka sai ka samu ka je gida ka kwanta ka huta ko, amma dan Fodio a daina wasa da addu'a, ba zance sakaci da addu'a bane ya ja abin da ya faru, saboda kuwa na sanka sosai ba ka wasa da ibada, amma dai ka sake zage damtse ka ji."


Mik'ewa ya fara yi da k'yar yace "Insha Allahu Baba, amma wai me ya faru da ni ne?"


"Idan ka je gida ka huta mayi magana wani lokacin."


Jiki a matuk'ar sanyaye ya sanya kayan shi ya fito daga d'akin wanda ya yi daidai da fara kiran sallah isha'i, haka ya wuce ba tare da ya kula kowa ba saboda abin da ya ke ji, a k'ofar gida ya samu Bilal zaune akan tabarmar malam ya yi alwala, shi ma alwalar ya yi suka nufi masallaci tare, bayan sun fito ne Usman ke tambayar shi "Wai ina sarauniya ne ban gan ta ba?"


D'aga kai Bilal ya yi ya kalle shi kafin yace "Mummy na na gida ba ta jima da tafiya ba." Ji ya yi sam babu wani abun da ya ke iya tunawa ma a kan shi a halin yanzu, kallon Bilal ya yi yace "To ni yanzu gidan zan tafi, za ka je ne ko kuma na barka?"


"Um um, Mummy tace na zauna nan sai an gama bikin kawu Nura." Shafa kan shi ya yi yace "To shikenan ni zan tafi, ka kula da kan ka kaji ko."


Saida ya sunkuya ya sumbace shi kafin ya shiga motar shi ya wuce gidan shi saboda tunanin shi Khadija na can,😂 tsohon zance, ai kuwa da ya je dai bai samu samu kowa a gidan ba, kiran Khadija ya yi yace "Ki na ina ne?"


Da mamaki Khadija tace "...


*Lokacin Haseenah fa ya fara fan's, yanzu nasan za ku ji dad'i.*



_Ma chérie *Hakeema* barka da samun k'aruwar 'ya mace, Allah ubangiji ya raya mana ita akan sunna, zafa musha shoki yan uwa😎 nasan baku tab'a gani na ina kwaso shoki ba._

01/03/2020 à 14:18 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```


_Wannan page ta ki ce ke kad'ai mahaifiya kuma maman mu da tafi kowa, my sweet and lovely ki bayar da wannan page ga *Momy na*, Allah ya k'ara girma da lafiya mai anfani._


_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *34*



"Ban gane ina ina ba?"


Cikin tausasawa yace" To ranki shi dad'e Hajia uwar yarima ina aka je ne?


Saida ta furzar da iska tace "Ka fad'a min abin da ya sa ka kira ni amma ba wannan ba."


A hankali yace "Nana Khadija ina k'ofar gida yanzu haka kuma babu kowa a ciki, sannan daga gidan su Hajia na ke ba kya can, yarima yace min kin zo gida amma kuma ban same ki ba, ina ki ka je ki fad'a min?"


"To me za ka min da ka damu da sai ka ganni?" Ta fad'i hakane saboda tasan in har cikin jikin ta to fa ta shiga uku, dan sai ya yi mata abin da yace zaiyi, shi kam a cewar shi "Ina son ganin ki ne, ki fad'a min ina ki ka na je na d'auko ki tunda na ga motar ki aje."


Haushi ne ya kamata tace "Kaga malam ina d'an wani aiki, sai anjima." Datse kiran ta yi ya bi wayar da kallo, a hankali ya furta "Me ya samu Khadija ta ne haka? Ba ta min irin haka fa."


Shawara ya yanke ya kira wayar Hajia, ta na d'auka yace "Hajia Khadija na ce ko ta na nan gidan?"


Da mamaki Hajia tace "Khadija kuma, ai ko da ta yi sallahn magriba ta tafi gida."


"To Hajia kuma gani a k'ofar gidan ba ta nan, na kira ta kuma ta k'i fad'a min in da take."


Yanda ya ke maganar cikin damuwa ya sa Hajia cewa "To ka shiga cikin gidan mana sai ka tambayi Hajiar ta, ita ai ba za ta kasa fad'a ma ka ba, ita ma nasan ba ta fad'a ba ne saboda ta na jin haushin ka."


Da mamaki fal a fuskar shi yace "Hushi da ni kuma? Hajiar ta? Hajia wai me ki ke fad'a ne? Ban gane ba sam wallahi."


Fahimta da Hajia ta yi akwai abin da ya faru ne ya sa tace "Yanzu dai in ganin ta ka ke so ka yi ka je gidan su, ni kaga ina wasu harkokin."


"Hajia wai me ta ke yi a gidan su? Dan Allah ki fad'a min ko na ji sauk'i, wallahi ji na ke kamar na tashi a bacci." 


Shiru Hajia ta yi ta na tunanin abin da za ta fad'a ma sa, kamar zaiyi kuka yace "Hajia ki taimaka ki fad'a min mana, dan Allah ki ce ba wani mugun abu na yi wa Khadija da har ya sa ta tafi gidan su, Hajia kinfi kowa sanin Nana ita ce rayuwa ta, dan Allah ki cire ni a duhun nan."


Cike da k'aguwa Hajia tace"Fodio, na ce ka je godan nasu ka same ta ko."


Ikon Allah sai kawai Usman ya ji hawaye a fuskar shi, cikin rawar murya yace "Hajia sakin ta na yi?"


Jin muryarshi ya sa Hajia jikinta yin sanyi, tabbas sunyi kuskure a baya da su ka nunawa Khadija k'iyayya, gashi alamu na nuna cewa Khadija dai ita ce rayuwar d'an su, jin shiru ya sa yace "Hajia na shiga uku idan sakin ta na yi, Hajia tun yaushe ta ke gida?"


Kashe wayar kawai Hajia ta yi ta aje gefe ta fito waje su ka ci gaba da harkokin gaban su, sai dai kuma hankalin ta ya koma kan Usman da abin da ke faruwa, Haseenah na d'aki zaune ba aikin fari bare na bak'i sai kallon mai bisa ruwa takewa kowa, Usman kam daga nan baiyi k'asa a gwiwa ba wajen wucewa gidan su Khadija ya na addu'a a zuciyar shi "Allah ka sa ba wani abu nayi wa Khadija ba, Allah na rok'e ka kasa ba fad'a mu ka yi ba." Wani lokacin kuma mamakin kasa tuna komai ne ke damunshi, da haka ya isa gidan ya paka mota a k'ofar gidan, zai sallama sai ga Bashir zai fito daga ciki, gaisawa su ka yi cikin mutumta juna kafin yace ya wuce ciki Hajia na nan shi zai fita ne, ba musu ya wuce dan dama ba tsayawa zaiyi ba, Hajia na zaune tsakiyar less da atampopi ya sallama tace ya shigo, zaune ya yi k'asa kamar yanda ya same ta a k'asa ita ma, gaisawa su ka yi kamar kullum kafin ya d'anyi shiru ya na tunanin ta'inda zai fara, shiru ne ya ratsa d'akin kamar ba kowa a ciki, a hankali Hajia ta kalle shi da murmushi tace "Komai lafiya dai ko?"


Saida ya rarraba ido kafin yace "Mama, wani abu ne ya ke faruwa da ni da na ke so na samu amsar tambayoyi na anan, dan Hajia ta ma k'i saurara ta bare ta fad'a min me ke faruwa, dan Allah Mama ki taimaka ki fad'a min ina Khadija take? Sannan meya faru tsakani na da ita da har ya sa take zaune gida?"


Jim Mama ta yi ta na tunanin to in har iyayen shi ba su fad'a mi shi ba me zaisa ita ta fad'a, murmushi kawai ta yi ta kalle shi tace "Ba komai Usman, ka wuce ta na ciki yanzu mu ke zaune tare da ita ta shiga ta yi sallah."


Damuwar kan fuskar shi ce ta k'aru yace "Mama, dan girman Allah ki fad'a min meya faru tsakanin mu, Mama idan ma sakin ta na yi wallahi tallahi bansan na yi ba, shi ya sa na ce mu ku wani abu ne ke faruwa, gaba d'aya na kasa tuna komai ji na ke kamar daga dogon bacci na tashi."


Ganin kamar zai mata kuka ya sa ta saki fuska tace "Kar ka damu Usman, ba wata babbar matsala ba ce, ka shiga ka same ta a ciki ku yi magana, idan har ka na so ma za ka iya tafiya da matar ka gida yanzun."


Sai lokacin murmushi ya bayyana a fuskar shi yace "Mama da gaske zan iya tafiya da ita? Kai Alhamdulillah Allah na gode ma ka."


Dariya Mama ta yi ta na kallo ya shiga ciki, dama k'ofar ba rufe ta ke ba kamar yanda tafi barinta mafi yawan lokuta, ya na tura k'ofar ya shiga ya yi daidai da Khadija ta idar da sallah ta mik'e tare da cire hijabin ta, riga ce jikinta ruwan madara mai k'ananan hannuwa wacce ta kama ta, sai bak'in siket da ya bud'e sosai bai kama jikin ta ba, saida gabanta ya fad'i ganin mutum kawai a d'akin, amma kuma saita kasa motsawa saboda tasan yau ta ta kam ta k'are dan idon shi na kan cikin ta, Usman da tunda ya d'ora idon shi akan cikin ta yaji k'wak'walwar shi ta fara tuna ma sa da wasu abubuwan, mamaki ne fal a fuskar shi har ya fara matsowa kusan ta, ta na ganin haka ta fara ja da baya a hankali shi ma ya na bin ta, daf da ban d'aki ta juya da sauri za ta shige ciki da azama ya rik'o hannun ta.


Janyo hannun ta ya yi har saida ya zaunar da ita bakin gadon ya tsaya gabanta sank'am kamar zai fad'a mata ya na kallo, kan ta k'asa ta kasa had'a ido da shi kafin yace "Ya mu ka yi da ke?"


D'agowa ta yi tace "Akan me fa?"


Had'e rai ya yi yace "Kar ki raina min wayo mana, Khadija me ye hujjar ki na b'oye min ki na da ciki? Akan me za ki min haka?"


Mik'ewa ta yi tace "Kaga malam dan Allah kar ka d'aga min hankali, ni babu wani ciki da na ke da, ko kai ka ga na yi ma ka kama da masu ciki ne?"


Wani bala'in haushi ne ya taso mi shi amma sai ya share yace "Tashi wuce muje gida sai mu yi maganar acan."


"Wane gidan kuma?" Ta fad'a ta na kallon shi, kai tsaye yace "Gidan ki mana."


Wani murmushi ta yi tace "Ni ai duk filaye ne gare ni har yanzu ban gina gida ko d'aya ba."


Cile da k'aguwa yace "Haba uwar yarima, gidan mu fa na ke nufi, ki tashi mu tafi mana."


Cikin nuna rashin damuwa tace "Au! Ai wannan gidan ka ne ba nawa ba, idan da nawa ne ma ai da ba ka yi abin da ka yi ba har na baro ma ka gidan."


A hankali ya durk'usa kan gwiwoyinshi ya rik'o hannayen ta yana murzawa yace "Khadija fad'a min me na mi ki in ba ki hak'uri? Ke kinsan ba zan iya cutar da ke ba, tunda mu ke da ke ba mu tab'a samun sab'anin da yasa mu ka raba shinfid'a ba bare gida, dan Allah ki fad'a min sai na baki hak'uri yanzu kuma mu koma gida tare, sanin kan ki ne ba zan iya bacci ba alhalin ke ki na nan."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ka na nufin ka ce ba ka san ma me ka min ba?"


Kamar zaiyi kuka yace "Wallahi na manta Khadija, komai ya dawo min kamar sabo a rayuwa ta." Tab'e baki ta yi tace "To kaga ka tashi dai yanzu ka koma gidan ka kafin amaryar ka ta fara neman ka."


Tsaki yaja yace "Ina mi ki magana mai mahimmanci ke ki na magana akan wata, dallah malama ki tashi ki wuce mu tafi gida."


Waro ido ta yi irin mamakin nan tace "Eyee! Lallai ma mutumin nan, to ba zan je ba ina nan gidan mu."


Ba alamar wasa yace "Haka ki ka ce?" Ita ma ba tsoro tace "Eh, haka na fad'a."


Yatsunshi ya sa biyu ya kama agarar (jijiyar da ke bayan k'afa kusa da diga-digi) ya dinga murzawa da zafi, da sauri ta janye k'afar ta sai kuwa ya rik'e k'afar ya na fad'in "Ba dai kinfi son na mi ki hukunci a gidan ba? To ai sai mu zuba ni da ke, na ga wanda ya isa ya k'wace a hannu na yau."


K'ok'arin k'watar k'afar ta ta shiga yi amma ya hanata dama, idon ta ne suka cika fal da ruwa ta na so ta bashi hak'uri amma ta k'i magana, shi kam ko a jikin shi har cije leb'e yake ya na fad'in "Uhum! Da dad'i ko? To yaya yanzu za ki fad'a min dalilin ki na k'in fad'a min ki na da ciki?"


Jin zafi ya kai mata ya sa ta bud'a baki da k'arfi tace "Mamaaaaa, ki zo ki taimake ni."


Bushewa ya yi da dariya yace "Kuma a zaton ki za ta zo? Kar ki wahalar dani a banza ki fad'a min abin da na ke son sani."


Jin bala'in na k'aruwa ya sa Khadija fashewa da kuka irin na sangartattun yaran nan ta na fad'in "Dan Allah ka yi hak'uri zan fad'a ma ka, wallahi zafi ke akwai, dan Allah ka daina zan fad'a."


D'an tsagaitawa ya yi yace "To ina jinki." Saida ta fara goge hawaye tace "To d'anyi baya mana ka matse ni sosai."


Kallon da ya mata ya sa ta d'an matsa baya amma sai ya sake binta ba tare da ya mik'e tsaye ba, shiru ta yi shi kuma ya sake kamo k'afar ta yace "Ke fa na ke saurare, muguwa kawai, da meye nufin ki to? Ban cancanci zama uban d'an ba ko kuma ke kad'ai ke da shi? Allah sai kin fad'a min dalilin ki ko na rabu da ke."


Tangale kanta ta yi da hannayen ta ta rufe fuska ta na tunani, a hankali taji ya d'an d'ago ya zauna bakin gadon ya rumgumota jikin shi, cikin taushin murya yace "Nana, ki fad'a min komai da ya faru mana, meye ake b'oye min haka da ba'a so na sani? Kowa na tambaya sai ya yi shiru ba ya son fad'a min komai."


D'agowa ta yi daga jikinshi tace "Kaje ka tambayi Hajia ko Baba su za su fad'a ma ka komai."


"Ban damu da sanin komai ba Khadija, na fi damuwa da sanin abin da ya sa ki ke zaune gida."


Tallabo fuskarta ya yi yasa idonta cikin na shi yace "Khadija me nai mi ki da zafi haka?"


Kamar za ta fashe da kuka tace "Mun samu sab'ani ne da kai akan amaryar ka, sab'anin da ya sa ka yi abin da ba ka tab'a yi ba a rayuwar ka, shine ni kuma na dawo gida gaba d'aya a lokacin ba ka buk'ata ta a gidan ka."


Da tsantsar mamaki yace "Sab'ani? Amma me na yi to?"


"Duka, duka na ka yi." Ta k'arashe da sunkuyar da kan ta k'asa tana hawaye, dafe kan shi ya yi yace "Duka? Ni da hannu na?"


Tsaye ya mik'e jiki a sanyaye ya sake sunkuyawa gabanta ya d'ago fuskarta yace "Ki yi hak'uri Khadija, wallahi Allah bansan na yi ba sai yanzu da ki ke fad'a min, ki gafarce ni dan Allah kar ki hukuntani da laifin da bansan na aikata ba, yanzu haka kunyar had'a ido na ke da ke da ahalin ki."


Ya na fad'a ya tashi ya fita ko juyowa baiyi ba, Mama ya samu a in da ya barta da alama kan ta ya d'au zafi, sunkuyawa ya yi yace "Mama, Khadija ta fad'a min abin da ya faru, Mama ina mai baku hak'uri da gaba d'aya zuciya ta, ku yafe min dan Allah, ba dagangan na yi ba, kuma banyi dan cin zarafin ku ba, hasalima abu ne da sam banyi tsammani ko tunanin faruwar shi ba."


Mik'ewa ya yi tare da cewa "Saida safe Mama." Ya fad'a ya na barin falon ba tare da jiran me za ta ce ba, Mama kam sai taji tausayin shi ya kamata sosai, watak'ila har ya yi anfani da maganin da Garba ya kawo cewar Mama a zuciyar ta, Khadija ma tausayin mijin ta ne ya sa ko fitowa ba ta yi ba ta kwanta daga nan kuma bacci ma ya d'auke ta.


Kai tsaye gida ya sake komawa ya samu malam zaune k'ofar gida sai Bilal gefen shi da wayar shi a hannu, zaune ya yi akan tabarmar ganin haka ya sa malam cewa "Fodio lafiya dai na gan ka haka?"


Idon shi cikin na malam yace "Ba lafiya Baba, Baba ka fad'a min dan Allah me ya faru da ni ne? Sannan me na aikata a lokacin da na rasa tunani na? Kawai ganin abubuwa na ke kamar sabi kuma kamar a almara."


Tank'washe k'afafu malam ya yi yace "Fodio, abubuwa sun faru da dama, idan da ka nutsu kai da kan ka za ka iya tuna komai, amma ka kasa kwantar da hankalin ka ma bare har ka samu nutsuwar."


Cike da damuwa yace "Baba ina maganar nutsuwa ga wanda ya na kallo rayuwar shi ke barazanar fita daga gangar jikin shi, a yanzu haka fa Khadija na gidan iyauen ta zaune da kuma ciki na a jikin ta, Baba ban ma san tsawon lokacin da ta d'auka acan d'in ba."


Murmushi sosai malam ya yi yace "Watan ta uku yanzu."


"Wata uku?" Ya fad'a da k'arfi da zaro ido kafin ya d'ora da "Baba da sakin ta na yi fa da yanzu ta kammala idda kenan? Kutumar bala'i, Allah ya ceceni."


Dariya malam ya yi kafin yace "Ai kam dai, dan ni dai ka ganni nan ba zan tashi zuwa yi ma ka biko ba da girman ka da komai."


"Yanzu dai malam ku fad'a min abin da ke faruwa da ni, ina so na sani."


Gyara zama malam ya sake yi bayan dogon tunani da ya yi kafin yace "Abin da ya faru da kai ba zamu dangana shi da kowa ba, dan har yanzu ba mu san mai wannan alhakin ba, dan haka kai ma ba na so ka d'auki laifin ka d'ora kan wani ko wata, ka barwa Allah kawai shine zai ma ka sakayya." Jinjina kai Usman ya yi alamar gamsuwa kafin malam ya ci gaba da bashi labarin iya abin da ya sani kawai daga barin Khadija gida zuwa yau d'in nan, sosai al'amarin ya girgiza Usman tare da bashi mamaki, to shi kam waye abokin gabar shi da har zai mi shi haka? Kasa tunawa ya yi sai kuma zuciyar shi tafi ta'allak'a mi shi komai da Haseenah, dan a ganin shi ita ce za ta iya sawa ya manta da Khadija dan ta bar gidan ita ta zauna, to amma kuma malam yace kar ya d'orawa kowa laifi, ya barwa Allah zai ma sa sakayya dan haka ya ja baki ya yi shiru, amma kuma abin da ya ji yanzun ya sa ya tuna da abubuwa dayawa da su ka faru, sai dai ba duka ba, saida safe ya mi shi dan lokacin har bacci ya d'auki Bilal daga nan, ganin zai shiga mota ya sa malam cewa "To matar ta ka fa wa ka barwa ita anan? Ko nan za ta kwana ne?"


Zaune ya yi cikin motar ya kira ta a waya yace ta fito, ba wani jimawa ta fito cikin takun k'asaita da izza dan dama zaman gidan ya isheta, kafe fuskata ya yi da ido har ta k'araso, tabbas ba munin fuska ba ko munin halitta, sai dai wani abun al'ajabi wani irin haushin ta ne yake ji na taso mi shi, wanda ko farko duk da ba wani son ta yake sosai ba amma dai ba ya mata irin wannan k'iyayyar, zagayawa ta yi ta shiga suka d'auki hanya ba tare da sunwa juna magana ba, jin shirun ya yi yawa kuma ya d'auki hanyar gida ya sa tace "Kasan fa ba mu da abin da za mu ci a gida, ka siya mana kafin mu wuce ko."


Cikin isa da gadara ya juyo ya kalle ta, a hankali kuma ya d'auke kan shi daga kallon ta cikin mak'oshi yace "Uhum."


Saida ya tsaya ya siya mata iya cikin ta kafin suka wuce gida, suna shiga ya nufi k'ofar na shi falon, da sauri tace "Beby, ina kuma za ka je?"


Juyowa ya yi yace "...



*Gidan uban da ki ka aike shi mana.*🙊🙈

04/03/2020 à 19:43 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *35*



"Zan d'an shiga ciki na kwanta ne saboda na gaji, ki ci abincin kawai dama ni na k'oshi." 


Sake juyawa ya yi zai wuce tace "Amma yau d'akin ka za ka kwana ne?"


"Eh." Ya fad'a a hassale tare da juyowa ya na kallon ta ya ci gaba da cewa "Kuma ke ma ina so ki kwanta d'akin ki dan ba na son takura."


Da mamaki tace "Takura kuma? Ni ce ma zan zama takura a gare ka? Babban mutum wai lafiyar ka k'alau."


Ajiyar zuciya ya sauke irin ta takura masa d'in nan kafin yace "Lafiya k'alau, na yau kawai na ke so ki bar ni na kwanta ni kad'ai, ki yi hak'uri." Ya fad'a ya na wucewa ciki ya barta nan, mamaki ne ya kama ta sosai da tunanin ko lafiyar shi? Ita dai a saninta lafiya lau suka je gida, amma daga lokacin da ya shiga d'akin malam ba ta ma san da tafiyar shi ba sai da taji kamar su na waya da Hajia duk da dai ba ta da tabbacin da shi su ka yi wayar, ita ma d'akin ta ta nufa ta cire kaya ta yi wanka kafin ta ci abinci ta kwanta, sam ba ta samu wata damuwa ba wajen baccin ta, dan kuwa ba jimawa baccin ya d'auke ta.


A wajen Usman kuma kasa bacci ya yi ya na tunanin abin duniya, da farko dai da kunya ce ke neman sa shi yin k'asa a gwiwa, amma kuma saiya duba ya ga ai ba a sanin shi bane komai ya faru, sannan bai saki matar shi ba bugu da k'ari ta na d'auke da cikin shi, da haka kuma sai ya ji ya ma k'agu gari ya waye ko ya sake komawa wajen Dije, ba kuma zai gushe ba har sai ta dawo gare shi, saboda fatan dacewa ya sa ya d'auro alwala ya shiga fad'awa Allah kukan shi tare da neman taimakon ubangiji.


*Washe gari* da safe d'aurin aure, sammako sosai Usman ya yi ya hallara d'aurin auren bayan yace wa Haseenah ta yi k'ok'ari taje da wuri ita ma, haka ya fita kamar shine angon cikin babbar riga da 'yar ciki farare, ya na isa a k'ofar gida ya tsaya saboda mutanen da ya samu a wajen, nan su ka shiga gaisawa da mutane har lokacin da motar Naseer ta kutso cikin taron jama'ar, mazauni aka samarwa da motar kafin Mama ta bud'e ta fito daga ciki, Usman na ganinta ya tafi da azama dan kwasar gaisuwa sai ya ga Khadija ta fito a matsayin dreban da ta tuk'o motar, tsaye ya yi ya kasa k'arasawa saboda haushi, tabbas yasan ta na fita da gyale sai dai yau ne ya fara jin haushin haka, domin kuwa ta na fitowa gyalen ma a kafad'ar ta yake, duk da doguwar rigar shadda ce jikinta wacce ta fito da d'an cikin ta na wata biyar, amma dai baiji dad'i ba duk da ya ga sai gyara gyalen take, har saida su ka zo daf da shi kafin ya sunkuya ya gaishe da Mama ta amsa cikin sakin fuska, wucewa Mama ta yi shi kuma ya mayar da kallon sa kan Khadija da ita ma shi take kallo yace "Ke ba ka iya gaisuwa ba ne ko me?"


Cikin tsiwa tace "Um ban iya ba, ko ka koya min ne?"


Gyara tsayuwa ya yi ya na k'ara sab'a rigar shi a kafad'a yace "Uwar yarima wai yaushe ki ka raina ni ne haka?"


Ta na kallon idon shi tace "Tun ranar da ka fara wulak'anta ni saboda ka yi amarya."


Wani kallo ya mata kafin ya d'an saci kallon mutanen da ke wajen yace "Yanzu ko albarkacin mutanen nan ba zan ci ba na ga murmushin nan na ki mai saka ni bacci."


'Yar siririyar dariya ta yi tace "Toh fa Alhaji mai babbar riga, kai da za ka je d'aurin aure kuma me ya had'a ka da bacci? To ka farka idan mafarki ka ke, kai da sake ganin murmushin Nana Khadija kuma sai dai ko a lahira, a lokacin da aka min umarni da na shiga aljanna, to zan iya juyowa na kalle ka dan na ma ka bye bye, to fa zai iya yiwuwa a lokacin ne za ka ga murmushin."


Shi maganar ta dariya ma ta bashi, da sauri ya rik'o hannunta ya matso daf da ita yace "Ki na so ki ce ni kuma zan zauna har sai kin riga ni shiga? Ko kuma nufin ki ni ba ma zan shiga ba?, ai k'afar ki k'afa ta insha Allahu, in kuma ba haka ba to sai dai ki same ni a ciki kewaye da sabbin mata na."


Fizge hannunta ta yi tace "Ka na dukan nawa ne kuma ka ke tunanin za ka shiga aljanna."


Wucewa ta yi ta bar shi nan tsaye ya na ta dariya shi kad'ai, Murtala ne ya k'araso wajen shi yace "Mijin Khadija lafiya ka ke dariya kai kad'ai?"


Hararan shi ya yi yace "Ni kad'ai ka gani a wurin? Ba ka ga wacce na gani ba."


"Na gani kam, ince dai kun sasanta za ta koma?" Kallon shi ya yi sosai yace "Da alama fa sai ka tayani bata hak'uri, ran 'yar aljanna ya b'ace sosai."


Zaro ido Murtala ya yi yace"Wa? Ni! Sam ba dani ba, kai dai da ka mata laifi ka bata hak'uri amma banda ni."


"Au! Yanzu ka na nufin ba za ka tayani ba kenan? To nagode, ai na d'auka zan iya yin zaune gida ma kai kaje har sai ka dawo min da ita, ashe ba haka bane."


"A'a ni ba haka na ke nufi ba, kasan dai maganar nan ta manya ce ba iri na ba, kuma tsakanin ka da Khadija ma ai ba ta b'aci."


Ba jimawa da shigar Khadija mutane aka fito dan tafiya wajen d'aurin auren, daga ciki har da Mama dan dama d'aurin auren take son samu, nan aka shiga motoci aka wuce d'aurin auren, Khadija na zaune d'akin Hajia Nura ya shigo da sauri ya na kiran sunan Hajia, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida yane, ke ba ki je d'aurin auren ba?"


Hararan shi ta yi tace "Wa? Allah ya sawak'e, me zanje na yi a d'aurin auren kishiya, ai ina daga nan ina aika mu ku da addu'a."


"Yawwa hakan ma ya yi ai, addu'ar ita mu ke buk'ata ai." Cewar Nura ya na kallon Hajia da ta fito daga d'aki, cikin k'aguwa yace "Hajia takalma na da na baki jiya na ke nema."


Ledar hannun Hajia ta mik'o mi shi tace "Dama nasan su za ka nema ka ke min wannan kiran."


Bud'ewa ya yi ya saka takalman kafin ya juya zai fita yace "Hajia ku fara tausar min k'irjin ta kafin na dawo." 


Haka suka wuce wajen d'aurin aure gidan waliyin Choukra, kuma ba'a b'ata lokaci ba waken yin abin da ya kai kowa wurin, nan aka d'aura auren *Nura Ali* da amaryarshi *Choukra Sabi'u*, bayan taya juya murna da farin ciki ne abokan ango su ka nufi inda za su ci su sha, manyan mutane kuma suka dawo gidan su ango dan cin abinci suma.


Bayan tafiyar 'yan d'aurin aure ne ba jimawa kuma Haseenah ta zo ita ma kamar yanda Usman yace ta zo da wuri, a d'akin Hajia suke zaune nesa da juna amma babu mai kula wani, haka suke zaune Khadija na hira da mutanen da ba su je d'aurin auren ba, Hajia ce ta fito daga uwar d'aki ta kalli Khadija tace "Nana wai kinga Bilal kuwa?"


"A'a Hajia, ya na ina ne?"


"Ai tare da malam su ka shirya su ka fita, kin ganshi kamar shine angon sai rawar k'afa ya ke, saida na gargad'e shi dai kan karya kuskura ya kalli wasu mata."


Dariya kawai ta yi ba tace komai ba har mutane su ka fara shigowa aka fara hayaniya, nan su Hassana da sauran mutane suka fara raba abinci ana kaiwa mutane.


Bilal ne ya shigo tare da malam kai tsaye wajen mahaifiyar shi ya nufa ya zauna kan k'afafun ta, wanda hakan ya yi daidai da shigowar Usman da kwalbar lemu a hannun sai malam a biye da shi, kwantar da kan Bilal ta yi a k'irjin ta tana sumbatar shi tace "Yarima na yi kewar ka fa, kwana uku ka na nesa da ni."


Bilal kenan d'an gata sai kuwa ya sake wani cakume ta kamar zai sa nonon ta a baki yace "Mummy yunwa na ke ji fa."


Lek'a fuskar shi ta yi tace "Ban gane ba, ba ka ci abinci ba ne a waje?"


Cikin shagwab'a yace "Ban ci ba, to duka fa manya ne a wajen."


Murmushi ta yi tace "To yarima na k'arami ne? Yaro ana bikin kawun ka ace ka na rasa abin da za ka ci, to ba ka had'u da Abban ka bane?"


K'ara tusa kanshi ya yi cikin jikin ta yace "Um um."


D'ago kan ta tayi za ta yi magana sai ga Usman tsaye gaban ta ya na fad'in "Yarima yanzu da girman ka za ka hau k'afafu haka?"


Da sauri Bilal ya d'ago ya na ganin Abban shi ne ya yi tsaye ya mak'ale mi shi a wuya, rumgume shi ya yi shima yace "Me ya ke faruwa ne na ga ka na ta zuba shagwab'a haka?"


Khadija ce tace "Bai ci abincin bane, amma kuma kai ga hannun ka nan har da lemu ma ka ke korawa."


Kallon ta ya yi yace "To yanzu shan lemun nawa ya zama haramun ne ko me?"


"Ya zama mana, taya za ka jefa loma bakin ka ba ka san gudan jinin ka ya ci ko bai ci ba." Yanda ta had'e fuska ne ya sa ya ga ko ya fad'a mata shi ma bai ci abinci ba ba yarda za ta yi ba, dan haka ya juya da Bilal d'auke da shi yace "Yarima muje ka zab'i abin da ka ke so ka ci, rabu da mahaifiyar nan ta ka yau tunda safiya ta waye ta tashi da masifa, can ta k'arata da masifarta."


Shiru ta yi sai kallon k'eyar shi da take, shi kam jin ta yi shiru ya sa ya juyo dan ya san ta na nan ta na kumbura, wata irin harara ta dalla masa da tasa shi b'arkewa da dariya yace "Yi hak'uri Hajia, nasan me ye matsalar ki, ki ba ni hak'uri sannan ki lallab'a ni sai na mi ki magani."


Yanda ta motsa bakin ta ya sa ya fahimci me take nufi, dan haka ya mata gwalo yace "Idan kin kamani ki mayar da gabana gabas ki yankani."


Da haka ya fita su ka bar gidan, tun lokacin ba ta sake ganin Bilal ba har biki ya yi biki ana ta bayar da zafi, Haseenah na d'akin Aziza kwance sai narkewa ta ke, sai dai kuma abin ya d'an dameta na yanda kowa baya ma kula ta, sai wanda ya ganta ne dole ya ke iya gaisawa da ita, amma har Aziza sai ta shigo d'akin ta fita ko kallon in da take ba ta yi ba, haka yamma ta yi aka raba abinci, kasancewar a d'aki take ita kad'ai ya sa aka rabe abinci ba'a ma san da ita ba, babu wanda ya damu da hakan sai ma ran su Hassana da ke k'ara b'aci.


Da dare mutane duk sun tafi gidan amarya da ango, Khadija ce d'aki ke gaggauta shirya dan tafiya tare da masu jiranta a waje tunda ta zo da mota, sai Haseenah da tun sallah magriba ta tafiyar ta gida, Hajia na zaune kan katifa gyangyad'i na neman fizgar ta Khadija tace "Hajia bacci ne?"


Kallon ta tayi tace "To tukuna dai."


Saida ta gyara jakarta a kafad'a tace "To ni zan tafi, kuma ina ga daga can gida zan wuce, sai dai gobe idan Allah ya kaimu."


"To Allah ya yarda Khadija, Allah hutar da gajiya, angode sosai Allah ya saka da alkairi, saida safe." Duk ta na maganar ne saboda Khadija har ta kai bakin k'ofa ta na amsa mata, za ta bud'a labulen d'akin Usman ya sallamo, kaucewa ta yi da tunanin ya wuce amma saiya wani tsare ta da ido yace "Hajia ke kuma wannan kwalliyar fa? Duk ta zuwa kallon ango da amaryar ce?"


Kallon Hajia ta yi sai ta ga ita ma su take kallo dan haka ta share shi kawai, hannu ya sa aljihu ya ciro da hankici (hankiciep) ya kai a bakin ta zai goge mata jan baki, da sauri ta ja baya ta na rufe bakin tace "Ya za ka goge min? Yanzu fa na saka shi, kuma ina da bak'o ne a gida."


Wani kallo ya mata yace "Bak'o kuma? Wane irin bak'o?"


Ba alamar wasa tace "Bazawari nn..." Bugun da ya kai mata a baki ne ya sa ta saki k'ara ba ta shirya ba tare da rufe bakin ta durk'ushe kan gwiwanta, Hajia da ta zabura ne ta kalle shi tace "Alhaji meye haka? Me tai ma ka?"


Zaune ya yi akan kujerar da ke iya fuskantar Khadijar ya na hararan ta, cikin d'aga murya Hajia tace "Fin k'arfi ne ko me? Dallah malam ka bata hak'uri ko."


Rai b'ace ya kalli Hajia yace "Hajia ba ki ji me yarinyar nan ta ke fad'a ba ne, ina matsayin mijin ta za tace wani wai bak'o na jiran ta, har da cewa wai bazawarinta." K'wafa ya yi hakan ya sa Hajia kallon Khadija da har yanzu ba ta motsa ba tace "Yi hak'uri kinji Khadija tashi ki tafi abinki, ba zan iya tashi bane saboda k'afafu na amma da na rama mi ki dukan ki, ki yi hak'uri kinji."


D'agowa ta yi a hankali ta sauke ido a kan shi sun mata jawur, murmushi ta yi ta kalli Hajia tace "Saida safe."


Mik'ewa ta yi ta fice daga gidan, ta yi k'ok'ari ta sauke ma su jiran ta a waje gidan amarya amma ita ba ta tsaya ba ta wuce gida.



              *A gurguje*



A kwana biyu zuwa lokacin da aka kammala sabgar bikin Nura Usman ya shiga taitayin shi, dan ko wayar shi Khadija ba ta d'auka bare ta saurare shi idan ya zo, hakan  ya tab'a shi sosai dan ya damu, haka ma Haseenah ta fara damuwa sosai akan lamarin na shi, dan har yanzu ba su kwana d'aki d'aya ba, gari na wayewa kuma zai buga sammako yaje gida ya na lallab'ar malam ya je ya dawo da Khadija, sam ba ya da lokacin wata Haseenah yanzun, abinci ma idan ta dafa sai dai ta ci ita kad'ai amma ban da shi, ba ya son zuwa gidan saboda ba ya son ganin Haseenah da idon shi, ya na iya k'ok'arin shi sosai wajen b'oye k'iyayyar da yake mata, ya rasa dalilin da ya sa ya ke sake jin tsanar ta a kullum idan ya ganta, ba ya son jin muryar ta ko ganin giftawarta a gidan, duk da ba ya da kokwanto akan cikin da ke jikin ta cewa na shi ne amma dai ba ya jin ya na k'aunar abin da ke cikin ta kamar yanda ya ke k'aunar wanda ke cikin Khadija, a haka har aka kwashe *sati biyu* babu abin da ya sauya.


A sati biyun nan ne Usman ya yi tattaki har k'auyen su Baba Garba mai gadi ya je ya bashi hak'uri akan abin da ya farusannan ya nemi da ya dawo bakin aikin shi, ya hak'ura ya kuma nuna masa komai ya wuce shi dama bai rik'e ba saboda ya san ba laifin shi bane, amma dai ba zai iya komawa aiki ba saboda jiki da jini, amma idan ya amince akwai d'an shi da ke neman kangarewa zai iya had'a shi da shi saiya zauna a mazaunin shi, ya amince ya taho da yaron mai sunan *Rabe*, tabbas ya fara aiki yanda ya kamata sai dai burin Usman akan yaron ba wai ya zama mai kula da pliwoyin (flawers) gidan shi bane da k'ofa, ya na so a gama wannan zagon na karatu sannan ya d'ora shi ya ci gaba da karatun shi tunda ya na yi ya dakatar saboda shirme, duk da haka kuma Usman bai daina bibiyar Khadija ba, yanzu haka har ya gaji da sawa Bilal na rok'on ta akan ta dawo, Hajia da malam dama sun ce ba ruwan su, a k'arshe ya samu da k'yar ya lallab'a Murtala ya je ya mata magana, nuna masa ta yi ba komai za ta koma, amma ya na barin gidan tace ba yanzu sai ya sake shiga hankalin sa, jin shiru shiru ya sa saida ta kai ga Usman ya turo Nura da Kabir da kuma Mannir su ka je bata hak'uri, sai lokacin Mama tasan da irin tsiyar da Khadija ke tsulawa, dan sam babu wanda ya tab'a ce mata ya zo bata hak'uri dan ta koma, Usman kuma idan ya zo ta kan basu wuri ne dan su tattauna, kuma ba ta nuna mata wasu alamu na rashin jituwa, hakan ya sa ba ta san me ke faruwa ba, shi ma Usman ya so ya b'oye mata ne dan yasan za ta iya tirsasata akan ta dawo, duk da ya na matuk'ar so ta koma amma ya fi so ta koma dan ganin damar ta, kuma har yau ba ya ganin laifin ta akan hukuncin da take masa, dan kuwa babu abin da ta rage shi da shi a rayuwa amma ya mata kishiya, sannan ya rasa meya shiga kan shi da ya dinga cin mutuncin ta, dan wasu abubuwan sai yanzu ne idan ya na rarrashin ta take iya fad'a mi shi irin abin da ya mata, bugu da k'ari kuma bata gama hucewa ba ya zo ya bugar mata baki har saida ya kumbura, wanda kullum mitar hakan take masa, nan Mama tace su koma Khadija za ta dawo gidan ta ba jimawa, sun tafi da farin cikin samun nasara amma sam Khadija tace ba yanzu zata koma ba, da Mama ta fara fad'a kuma sai 'yan biyar suka tausheta suka ce tunda ba yarinya ba ce kawai a rabu da ita, hakan ya sa a ranar Usman ke ta zuba idon ganin Dije amma shiru, ko bacci baiyi ba a ranar ya na sak'awa ya na warwarewa, washe gari da dare ya je gidan da kan sa, a falo ya samu duk 'yan biyar d'in da wasu daga cikin yaransu, Mama na d'aki hakan ne ya sa ya zauna suka gaisa sosai, Naseer ne yace "Auta kam ta na ciki, amma kafin ka shiga ciki ka kawo kud'in ganin ta."


"To in dai hakane me zai hana ka fad'a min gaba d'aya farashin da zan biya, kaga sai ka d'auke ta da kan ka ka kai min ita gida na." Cewar Usman cikin raha, dariya su ka yi sai Habeeb ne yace "K'anwa ta fa tsada ne da ita, farashin ta baya fad'uwa."


Cikin zolaya yace "To kunga, duk cikin kun nan naga babu wanda zai iya taimaka min, dan haka ni zanje na yi yak'i na ni kad'ai, in har k'anwar ku bata koma gida na zuwa gobe ba to ku canza min suna."


Cike da cika baki ya mik'e zai nufi d'akin Khadija Naseer ya bushe da dariya yace "Wane sunan za mu saka ma ka to?"


Juyowa ya yi ya harare shi yace "Ka zab'a da kan ka mana."


Bashir ne ya yi saurin cewa " sai mu saka mi shi *Mani*."


Komai baice ba ya wuce d'akin, ko sallama baiyi ba yau dan al'amarin ba sauk'i,  kuma cikin sa'a saiya samu Khadija tana ban d'aki, murmushi ya yi kafin ya cire hular kan shi ya aje gefe ya kwanta kan gadon ya yi d'a-id'ai, kusan minti biyu ya d'auka kafin Khadija ta fito daga ciki d'aure da k'irji, kasancewar cikin ta ya sa ya d'age sosai daga sama har ya kan iya hango cinyoyinta, ita kam gilashin ta ne take gogewa ta na k'ok'arin sakawa, ta na sawa ta ja ta tsaya da tsoro fal a idon ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim, innahu min Suleimana wa innahu bismillahir-rahamanir-rahim."


Ba tare da damuwa ba Usman yace "A kan ki, wato na ma zama shaid'an ko?"


Wata ajiyar zuciya ta sauke ta matso kusan shi tace "...



*Ina k'aunar ku.*

06/03/2020 à 12:54 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *36*



"Malam lafiyar shigo min d'aki haka kawai, wa ma ya baka izinin shigowa nan?"


Kamar ba dashi take magana ba ma saiya share ta, ta jima tsaye ta na kallon shi ganin bai damu da tsiyar da take ba ya sa ta juya ta isa gaban madubi ta fara shafe shafe kamar yanda ta saba, lokaci lokaci takan juyo ta kalle shi amma abun mamaki shi kuma hankalin na ga waya ya na dannawa, saida ta gama ta nufi wajen kaya ta d'auko riga, ba tare da ta cire d'aurin k'irjin ba ta saka wando da rigar nono kafin ta saka doguwar rigar, juyowa ta yi ta kalle shi tace "To malam, idan ka gama da d'akin sai ka rufe min ko, ni zan fita."


Gyale ta d'auka ta fesa turare ta juya zata fice, da sauri ya duro daga kan gadon yace "Ina za ki je?"


Ta na kallon idon shi tace "Bak'o..." Sai kuma ta yi shiru saboda tuna ranar da ya kwamtse mata baki, rik'e k'ugu ta yi tace "Ka ban hanya mana zan wuce."


Rumgumo ta ya yi jikin shi ya dawo da ita ya zaunar akan gado, ture shi ta yi tace "Malam ka daina tab'a ni mana."


Sosai ya kalle ta yace "Khadija, har yanzu fa ni mijin ki ne, a labarin da ki ka bani ba ni ne na kore ki ba, amma Khadija ki na hukuntani abisa laifin da na ke tunanin ko da na aikata shi ne dadangan za ki yafe min, me ya sa haka Khadija? Kin daina so na ne yanzu? Ko kuma ba kya son ki tsufa a gida na ne yanzu kamar yanda ki ke fad'a min."


Mik'ewa ta yi tsaye tace "Ni dai kawai ka fitar min daga d'aki, so ka ke mutane su d'auka wani abun ne ke faruwa anan? Dan Allah ka tashi ka fita."


Yau fa ya yi niyyar ba zai bar gidan nan ba babu wani sakamako mai kyau, dan haka ya haye gadon ya gyara kwanciya ya kalle ta yace "Ba zan fita d'in ba, idan kuma ki na ganin za ki saka k'artin 'yan uwan ki ne su fitar da ni to bismillah."


Mamaki ne ya sa ta zaro ido tace "Abban Bilal, yan uwan nawa ne ma k'arti? To ai ko ba k'artin banza bane tunda su na ciyar da duka girman gidan nan dama wasu dake kewayen shi."


Hararan ta ya yi yace "Ni kuma na gaza ko? To ki jaraba kiran su ki gani mana idan za su iya."


Rumgume hannaye ta yi tace "Amma dai kasan tsaf zan iya saka su kefa min kai cikin kwalbatin unguwar nan ko?"


Wata irin dariya ya bushe da ita yace "To ki kira su mana, na fad'a mi ki ina tsoro ne."


Fitowa kam ta yi daga d'akin amma abun mamaki ba kowa a falon har telebijin ma an kashe, mayar da d'akin ta yi ta rufe ta dawo ta zauna kan kujerar da ke gaban madubi, kallon ta ya yi yace "Hajia ko za ki iya samo min kayan bacci a gidan nan?"


A harzuk'e ta kalle shi tace "A ina zan samo ma ka kayan bacci? Na wa zan d'auko ma ka?"


Har ta yi shiru shi kuma ya fara dariya sai kuma ta kalle shi tace "Wai ma tsaya, idan na d'auko ma ka kayan baccin me za ka yi da su?"


Ba alamar wasa yace "Nan zan kwana yau, tunda na fahimci ba za ki koma gidan ki ba, kinga saina raba mu ku kwana, biyu a nan biyu a can."


Tasowa ta yi ta kamo hannun shi ta na fad'in "A'a wallahi, akan me? Haka kawai kasa a kafa min hak'ora, kwana a nan saboda me?"


Fizge hannun shi ya yi yace "In dai ba kya son na kwana nan to ya zamar mi ki dole ki had'a kayan ki yanzun nan mu tafi na mu gidan."


Cikin b'acin rai tace "Wallahi babu in da zanje, haka ake kawai ka b'ullo min ta wannan hanyar."


A nutse ya kalle ta yace "Na fad'a miki ki bani hak'uri tare da lallab'a ni dan na mi ki maganin matsalar ki, amma girman kai ya hana ki ko? To ba damuwa mu ci gaba da zama a hakan tunda haka ki ke so, yarinya sai taurin kai."


"Ni na fad'a ma ka wani abu na damu na?" Ta fad'a ta na nuna kan ta da yatsa, saida ya tashi zaune yace "Ke kuwa ke da damuwa, gata nan b'aro-b'aro ina gani a idon ki."


Duk da idon na ta na cikin gilashi amma saida ta mitsika idon ta kafin tace "Ban gane ba fa."


Kashe mata ido ya yi yace "Yaushe rabon ki da ni? Yaushe rabon da na yi wasa da ke? Hajia Dije yaushe rabon da ki ji zallar ingantacciyar madara a jikin ki?"


Shiru ta yi kawai sai kallon bangon d'akin da take, murmushi ya yi yace "Shi ya sa yanzu zuciyar ki ta cika saurin hawa, ki ka cika masifa da jaraba, sannan ba kya da kuzari kamar yanda ki ke a baya, sannan hakan zai shafi lafiyar abin da ke cikin ki, saboda ni d'in nan da kika raina to lafiyayyen abincin shi na jiki na, za ki iya haifar yaron ki babu kazar-kazar a jikin shi da walwala kamar sauran yara, saboda ya rasa wani muhimmin abu da ya kamata ya samu amma kin hana shi saboda ki na bak'in ciki."


Juyawa ta yi ta kalli agogo ta ga har k'arfe goma ta soma wucewa, dan dama shi ma tara ta wuce ya shigo, kallon shi ta yi tace "Dan Allah babban mutum ka tashi ka tafi dare ya yi, ni kai na bacci na ke so na yi."


"Wasa ki ke ko Khadija? Yanzu ki na nufin ba ki yarda da abin da na fad'a mi ki ba kenan? To shikenan, ni dai na yi niyyar kwana anan, idan ke ki na jin kunyar kar mu wayi gari mu fito a d'aki d'aya to ki je d'akin Bilal ki kwanta."


Dafe goshi ta yi tace "Na shiga uku na, Abban Bilal ya ka ke so na yi ne?"


Wani kallon mamaki ya bita da shi, saukowa ya yi daga kan gadon ya tsaya daf da ita yace "Khadija, ke da kan ki, ke ce yau saboda takura da gundurar da na mi ki har ki ke iya fad'a a cikin ido na cewa kin shiga uku, Khadija me nai mi ki da zafi har haka? A gaskiya ban yi tsammanin jin wannan maganar daga bakin ki ba."


Juyawa ya yi cikin sanyin jiki ya d'auki hular shi yasa ya kalle ta yace "Shikenan uwar yarima, ni zan tafi, bana iya ce mi ki ga ranar da zan dawo ba, dan gaskiya kin kashe min k'warin gwiwa na, tunda ba kya son komawa zan rabu da ke, idan kin haihu kuma sai ki min magana idan ki na buk'atar takardar ki."


Kama hanya ya yi zai bar d'akin  Khadija da idon ta su ka cika taf da hawaye ji ta yi kamar ta k'urma ihu, saida ya kama hannun k'ofar zai murd'a ta yi k'arfin halin janyo rigar shi da k'arfi, baya ya yo kamar zai fad'i tare da kallon ta, kafin ya ankare ta hankad'a shi kan gadon ya fad'a da k'arfi, da iya k'arfin ta ta fad'a kan shi ba tare da tunanin cikin jikin ta ba, rufe shi ta yi da duka tako ina kamar Allah ne ya aiko ta, kallon ta kawai yake bai hana ta ba sai murmushi da yake dokawa, ita kam kuka take ta na fad'in "Aikin banza kawai, ashe dama ba so na ka ke ba shi ya sa har za ka iya saki na, so ka ke kaje kai da amaryar ka ku ci amarcin ku."


Ganin sosai ta ke kukan da gaskiyar ta ya sa ya kwantar da ita a k'irjin shi ya na shafa bayan ta ya na fad'in "Kinji yanda zuciya ta kuwa ta buga lokacin da na ambaci kalmar takardar nan, dan Allah Khadija ki daina azabtar da ni haka, gaba d'aya kinsa na zama kamar mahaukaci saboda k'ok'arin ganin kin dawo gare ni, ki tausayawa uban yaran ki mana."


Luf ta yi a k'irjin ta na share hawayen ta, sun jima a haka kafin yace "To ya ake ciki yanzu? Za ki koma ne ko ko sai na aiko mi ki da takardar har gida?"


Wani naushi ta kai mi shi a ciki wanda ya sa shi bushewa da dariya ya dafe ciki, tashi ta yi zaune kafin ta kalle shi tace "A gaskiya ba zan iya binka ba a daren nan, kawai ka je gobe na dawo da kaina."


Dariya ya yi ya kamo kunnen ta ya rad'a mata "Ashe yarinya ta na so na mata b'arin madara."


Murmushi ta yi tace "Matsala ta da kai rashin kunya."


"Um hakane, amma ai ke ki ka koya min."


Tashi ya yi yace "Da gaske za ki dawo gobe?"


"Zan dawo mana, ba ni na fad'a ba."


"Idan ma ba ki dawo ba wannan karan su Hajia Kaltume da Turai zan aiko su d'auke ki su kai min ke."


Kallon shi ta yi tace "Turai dai? Lallai."


Tsaye ya mik'e yace "Yanzu kira min Bilal da shi zan tafi, dan nasan dole ma ki dawo idan na tafi da shi ai."


Ita kam saboda ta yi niyyar komawa ya sa ta mik'e tace "Muje idan ka d'auke shi sai ka wuce."


Tare suka fita daga d'akin su ka nufi d'akin Bilal, idon shi biyu ya na rik'e da wayar shi a hannu, nan ta canza mi shi kaya su ka tafi da niuyar za ta zo mi shi da sauran kayan, saida ya shiga d'akin Mama da ta jima da bacci ya tsokane ta yace ya tafiyar shi, idan ta damu da shi ta je ta yi bikon shi ita ma, saida ta rako su har k'ofar gida Bilal ya bud'e motar ya shiga, Usman na ganin haka ya damk'i Khadija da wata wawar sumbata da ta rikita su dukansu, da k'yar ya sarara mata kafin ya kalle ta da jajayen ido yace "Ki yi sauri ki zo da wuri, ina buk'atar ki kusa da ni Hajia ta."


Motsa bakin da ta yi ya sa ya yi murmushi yace "Na ji dai idan kin kama ni ki yankanin amma fa bayan kin shayar da ni ruwan ki."


Dungure mi shi kai ta yi tace "Wai kai ka manta da ka tsufa ne, watanni kad'an fa su ka rage ma ka ka cika shekara *arba'in da biyar* cif a duniya, amma ka na abu kamar wani tsohon bazawari."


Saida ya sa hannu ya na shafar k'irjin ta yace "Kafin na cika hamsin da biyar kuma sai kun haifa min yara goma, kin ga ai ba na mayar da kai na tsoho ba, kuma ma ai ba daga nan abun yake ba, k'arfi da mazantakar na nan." Ya mata nuni da zuciyar shi.


Da haka suka rabu ya tafi da Bilal, yau kam Khadija ta yi bacci cikin nutsuwa saboda burin ta ya cika, ta juya Usman son ran ta ta hakane ma har ta gano yanzun Haseenah ba ta da wani girma a idon shi, dan haka ta yi bacci da zumud'in gari ya waye ta fara shirin komawa.


A wajen Usman kam Haseenah ba ta san da shigowar shi ba saboda har ta yi bacci ita ma, saida ya shinfid'e Bilal a gadon shi kafin ya wuce d'akin ta ba dan komai ba sai dan ganin halin da take ciki kamar yanda yake yi kullum, bud'a k'ofar da ya yi ne ya sa ta tashi ta na murza ido, kallon ta ya ke sosai ya na jin wata sha'awar na sake fizgar shi, sai dai kuma ba ya so ya neme ta saboda ba ita ta taso shi ba dama, da k'yar ya iya cewa "Ki yi hak'uri na tashe shi ko? Ashe hr kin kwanta ma, yau kam ban shigo da wuri ba."


Gyara zama ta yi tace "Sannu da shigowa."


"Yawwa sannu, ya ki ke?"


Kallon shi kawai ta yi ba tace komai ba, juyawa ya yi zai fita yace "Saida safe ko, yau ma zan kwana a d'aki na saboda muna tare da yarima ne."


Da mamaki tace "Yarima kuma?"


Juyowa ya yi yace "Eh, Bilal ba."


Wani haushi ne taji ya kamata, saukowa ta yi daga kan gadon tace "Kenan a gidan na su ka yi dare haka? Babban mutum ka na ganin abin da ka ke yi ya dace kenan? Wannan fa ba adalci bane, ka daina kula ni, ka daina min magana, ba ka cin abinci na, sannan ba ka kwana a d'aki na, me nai ma ka hakane da ka ke min irin wannan hukuncin? Ni ba wani abu bane a gare ni dan na durk'usa har k'asa na ba ka hak'uri, ka fad'a min dan Allah."


Gyara tsayuwa ya yi ya na kallon ta, hak'ik'a komai gaskiya ta fad'a, sai dai baisan me zaice ba domin kuwa ba zai iya fad'a mata haka kawai ya ke jin tsanar ta ba, cikin taushin murya yace "Kinga ki yi hak'uri da duk abin da ke faruwa, kawai harkoki ne su ka d'anyi tsamari, amma insha Allahu komai ya kusan zuwa k'arshe, ki k'ara hak'uri kinji ko, saida safe."


Ya fad'a ya juya kenan ta sake cewa "Shikenan ka je ka kwana da Bilal, dad'inta dai ba ya da abin da ni ke da shi, komai daren dad'ewa nasan dole ka neme ni a duk in da na ke."


Juyowa ya yi ya kalle ta da mamaki yace "Da Bilal d'in za ki yi kishi? D'ana ne fa shi, kinsan mahimmancin shi a gare ni kuwa? To shi d'in kamar rayuwa ta ne, ina k'aunar sa fiye da komai, ki iya bakin ki in dai akan iyali na ne, ba na juran b'acin ran su ko kad'an."


Idon ta cike da ruwa tace "Usman ba ka adalci wallahi, kullum nunawa ka ke Khadija da d'an ta sune rayuwar ka, kullum sune ma su mahimmanci a wajen ka amma ni ko oho, to kasan ba ka so na me ya sa ka aure ni?"


Girgiza kai ya yi yace "Ni bance ba na son ki ba, sai dai abin da na sani kawai shine ina son iyali na, idan ki na son zama da ni ki so su kema, kuma kar ki d'auka Khadija kishiyar ki ce ki yi kishi da ita, maganar gaskiya ta wuce nan a wuri na, Bilal d'ana ne da ya fito daga jiki na tsatsona, amma ina wa mahaifiyar shi son da bana ma sa, kinsan me ya sa?"


*Ita rayuwa dama haka take, da kin zauna da su lafiya da wannan ranar ba ta zo ba, kuskuren da mu mata keyi wani lokaci shine, ba ma fahimtar abin da mazajenmu suke so, idan har ki ka fahimci mijinki na bala'in son mahaifiyarsa ko yan uwansa ko yayansa, sai ke ma ki bishi ki nuna musu so na gaskiya, ba dan komai ba dan kawai ki faranta mi shi, hakan zaisa ya dinga kallonki da daraja da kima, saboda kina son abin da yake so, amma kishi da hauka da wauta sai ta saka mu rufe idonmu mu nuna k'iyayya da kishi kan abinda suke so, yanzu dai gashi kalaman da a baya bai iya fad'a mata yanzu gashi ya na kallonta ya fad'a mata, kenan ta jima ba ta mutu ba, Allah kasa mufi k'arfin zuciyarmu.*


D'orawa ya yi da "Saboda da ita na fara had'uwa, ita Allah ya fara bani kafin ya bani Bilal, ita ce wacce Bilal d'in ya fito daga jikin ta, shi ya sa na ke mata k'aunar da ko shi Bilal ba na masa, zanji zafi matuk'a idan aka ce yau na rasa Bilal, amma kuma zanyi farin ciki idan na waiga naga Khadija a gefe na, ba dan komai ba saidan nasan za ta sake bani wani Bilal d'in."


Ya na gama fad'a ya juya ya bar d'akin ya koma na shi ya kwanta ya rumgume Bilal kamar zai had'e shi, ya na shafa shi har bacci ya d'auke shi shima, Haseenah kam kuka ta fashe da shi mai tsanani, wai abin da a baya yake ma sayawa baya fad'a yau gashi ya fad'a, kai lallai abin nan bana lafiya bane, tunaninta ne ya bata duk wani shiri da tayi a kan shi ya wargaje, dan haka dole ta sake sabo, da haka ita ma ta yi bacci da tunanin kiran Mariya idan gari ya waye. 



*Luv u all.*😘

09/03/2020 à 15:01 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```


_💕 Masoya wannan littafi wannan kyautar ku ce, nagode da soyayyar da kuke nuna min ni da kaya na😚, Allah ya barmu tare._💞



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *37*



Ko da gari ya waye Bilal ya shirya cikin k'ananan kaya dan yau alhamis ce ba karatu, Usman ma kamar kullum cikin shadda ruwan madara ya shirya, tare suka fito falon Haseenah sun same ta zaune tana waya da Mariya, bayan ta fad'a mata akwai matsala ne Mariya tace ta sake fito da kud'i kawai a mata aiki, kafin ta yi magana ta ji fitowar su hakan ya tilasta mata aje wayar, juyowa ta yi ta na kallon su, duk da cikin hushi take amma tabbas tasan an samo Bilal ne daga Usman, dan zubin hallitarsu ma iri d'aya ce, duk da ba ta zauna da yaron sosai ba amma ta fahimci ya na da miskilanci fiye da ubansa, kai tsaye teburin cin abinci su ka nufa dan ba su ma lura da ita a zaune ba, saida ta ga sun zauna ta taso ta nufo su dan zuba mu su abinci, sai dai ta na mamaki yanda yau Usman zai ci abincin ta tunda ya jima baici ba, shi kuma zai ci ne kawai saboda Bilal na gidan yau, amma sam baya sha'awar cin abincin ta tunda ya lura kullum abinci kala d'aya ta iya sarrafawa, tun kafin ta tsaya wajen Bilal yace "Aunty ina kwana?"


Cike da makirci ta shafo kan shi tace "Yarima, ashe gidan mu ka kwana jiya, lokacin da ku ka shigo har na yi bacci, ya ka ke?"


Shi kam yaron fuskar shi ba fara'a yace "Lafiya lau."


Kallon Usman ta yi wanda ke kallon cikin ta shi ma tace "Ina kwana babban mutum?"


Ba walwala a tare da shi yace "Lafiya lau, ya jikin na ki?"


Da murmushi ta amsa da "Da sauk'i sosai." Shayi ta fara had'awa Bilal ta aje ma sa kafin Usman d'in, tare su ka karya dukan su bayan sun gama Usman ya mik'e zai fita, hannun Bilal ya kamo yace "Muje ko yarima, yau da kai za mu fita."


Da zumud'i ya mik'e tsaye dan bin mahaifin shi amma sai Haseenah tace "Haba dai babban mutum, wannan ma ai son kai ne wallahi, yaushe rabon da na ga Bilal, yau ya zo kuma shine za ka fice da shi, gaskiya ni dai ban yarda ba."


Kallon ta ya yi yace "To ya ki ke so ayi?" Kallon Bilal ta yi tace "Ka bar min shi mana, anjima idan ka dawo sai ku fita tare."


Duk da ya samu labarin dalilin da yanzun mahaifiyar shi ke gida, amma kuma ba ya jin akwai wani abu da za ta iya yi wa Bilal tunda ya na gari, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Bilal yace "Yarima, ka zauna tare da auntyn ka kaji, zan fita amma ba zan jima ba zan dawo, idan kuma ka gaji da zaman gidan ka na iya fita k'ofar gida wajen Rabe sai kuyi hira."


Saida Bilal ya kalli Haseenah kafin ya kalli Usman yace "To Abba, amma fa kar ka jima sosai."


Dafa kan shi ya yi yace "Ba zan jima ba insha Allahu."


Saida ya sumbace shi kafin ya kalli Haseenah yace "Ba wani abin da ki ke buk'ata?"


Sosa kai ta yi irin na kunyar nan ta kasa magana, hannu kawai ya sa aljihu ya fito da kud'i ya bata, karb'a ta yi ta mi shi godiya kafin tabi bayan shi har ya shiga mota, Rabe da ke zaune da littafin karatu (dan tunda aka ce za'a maidashi makaranta abun ya sake shiga ran shi) ya taso suka gaisa kafin ya bud'e mi shi k'ofa ya fice ya na binshi da addu'a, rufewa ya yi har ya zauna Haseenah ta k'wala mi shi kira ya zo, tsaye ya ke kamar yanda take su na kallon juna tace "Wannan pliwoyin ka basu ruwa mana, ya ka ke abu kamar ba ka san aikin ba ne."


Wani kallon raini ya mata dan babu abin da bai wani ba game da ita kafin yace "Tofa, to na ji zan ba su ruwan, shikenan?" Ya na fad'a ya juya ya bar mata wajen, ciki ta koma ba ta damu da shi ba dan a cewar ta k'aramin arne ne shi ba ta shi take ba, yau dai ba wata matsala tsakanin ta da Bilal, ya na zaune gefe ta na zaune ita ma sai dai su kalli juna, dan dama ba tace ya bar shi bane saboda ta na da wani nufi akan hakan, kawai ta fahimci ta b'ata mi shi rai ne jiya saboda abin da ta fad'a, ana hakane ta shiga madafa d'ora girkin rana, ba jimawa da fara aikin Bilal ya shigo da sallama, amsawa ta yi tace "Ya dai?"


Cikin ladabi yace "Aunty dama zanje gidan aboki na *Abdallah* yanzu zan dawo."


"To shikenan sai ka dawo, amma kar ka jima kuma uban ka ya dawo ya min tijara." Ta fad'a ta na ci gaba da aikin ta, da sauri ya fita ko amsa ta biyi ba, ashe Bilal moton shi ya d'auka ya fita da shi Haseenah ba ta ma sani ba, Rabe kuma tunda bai san ba'a barin shi fita da shi ba shima bai hana shi ba sai ma bin moton da kallo da ya yi har ya daina ganin Bilal kafin yace "Kai, Allah ka bamu kud'i mu ma muji dad'in rayuwa."


Wannan addu'a fa bana bari ta wuce ba ni kai na, dan haka na amsa da *ameen*, Bilal ya je gidan su Abdallah da babu nisa sosai da nan d'in, sunyi farin cikin ganin juna dan sun jima basu had'u ba, amm bai yarda ya jima ba ya mu su sallama ya juyo ya dawo, *tsautsayi fa ance idan ya wuni baya kwana*, rabon ayi Bilal su ka had'e shi da wani mai mota a lokacin da zai shigo kwana, mutanen dake wajen ne da su ka ankara wasu kuma akayi gaban idon su ya sa suka rabka salati tare da sallalami, tuni aka rufe wajen ana jimami tare da taimakawa Bilal da tuni baisan in da kan shi yake ba, a daidai lokacin motar Usman ta shigo layin, dan gaba d'aya hankalin shi ya kasa kwanciya, yanzun ma ya taho ne da nufi ya d'auke shi ya tafi da shi duk in da ya saka k'afar shi, ganin wannan taro yasan had'ari ne dan haka ya tsaya tunda dai a unguwar su ne abun ya faru, tashin hankali da ba'a saka mi shi rana, sai ga Usman ya ga Bilal hannun mutumin da ya bige shi jina-jina kamar babu rai a tare da shi, kallon shi ya kai kan moton shi daya wargaje abinka da dama roba tafi yawa a jiki, wani irin duka ne gaban shi ya fara yi yayin da zuciyar shi kamar za ta fito, a hankali ya ke kutsowa cikin mutanen wanda ke ta hayaniya kowa da abin da yake fad'a, wasu na fad'in sun san shi za su je su fad'a a gidan su, in da wasu suka dakatar da su da cewa kar aje babu namiji a gidan mata ba lallai su rik'e kan su ba idan su ka ji irin wannan labarin, hannu Usman ya zura ya karb'o Bilal daga hannun mutumin da ke kallon shi da mamaki, yana amsar shi wayar Bilal ta fad'o daga aljihun shi ta fad'i k'asa,  d'aya daga cikin mutanen wurin ne yace "Mahaifin shi ne."


Motar shi mutumin ya bud'e da nufin a saka Bilal ciki amma sai Usman ya nufi tashi motar da shi, amma daga ganin yanda ya ke takawa jikin shi sai b'ari yake haka ma hannayen shi, dan yanda ya ke kallon Bilal baya jin zaiyi rai, sosai jikin shi ke rawa har ya na neman fad'uwa da Bilal d'in, da sauri wani mutum da shi ma anan unguwar yake ya karb'e shi a hannun shi ya na fad'in "Ayi hak'uri Alhaji, ayi hak'uri, insha Allahu zai tashi."


Zagayawa mutumin ya yi ya kwantar da Bilal sai Usman da ya shiga ya tayar da mota, wanda ya bige shi ne ya bi bayan shi har suka isa asibitin da tafi kusa da su, amma ganin halin da Bilal ke ciki ya sa suka tura su babban gida (Hôpital), nan aka karb'e shi da taimakon ubangiji aka bashi taimakon daya dace.


Usman na zaune akan wani banci amma da simitin aka yi shi ya na tunani, shin dama Haseenah na da burin kashe ma sa d'an sa ne kome? Yanzu taya zan fara fad'awa Khadija maganar nan? Sai ta ga kamar da ni aka had'a baki ma aka cutar da shi, wata zuciyar ce tace mi shi, haba dai, ba ma za ta yi tunanin haka ba, nauyayyar ajiyar zuciyar da ya sauke ce ta sa wanda ya bankr Bilal d'in kallon shi, dafa kafad'ar shi ya yi yace "Dan Allah ka yi hak'uri, abun ya faru ne a bazata, bansan..."


Kallon shi ya yi yace "Ba komai malam, tsautsayi ne da baya wuce ranar shi, nima ina da abin hawan nan, kuma hakan na faruwa sosai."


Jinjina kai ya yi yace "Allah ya tashi kafad'un shi."


Da k'yar Usman ya iya cewa "Ameen." Likita ne ya fito daga d'akin ya na cire abin da ke rufe a hanci shi, hannu ya ba Usman da ya mik'e yace "Mu gode Allah, ya na samun lafiya in Allah ya yarda, ya na bacci yanzu."


Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah, nagode sosai likita, Allah ya saka da alkairi."


"Ba komai." Cewar likitan ya na shirin shiga ofishinshi, Usman d'in ne yace "Likita za mu iya ganin shi kuwa?"


Juyowa ya yi yace "Eh, za ku iya." Da sauri Usman ya nufi d'akin, Bilal ne kad'ai a ciki kwance jiki duk bandeji, k'arasawa su ka yi kusan shi suna kallon yanda Allah ya canza hallitar shi cikin k'ank'anin lokaci, mutumin ne ya mi shi sallama tare da cewa saiya dawo, ya na tafiya ya kira malam ya fad'a mi shi, zuwa bayan sallah azahar d'akin da Bilal ke ciki ya cika da yan uwa, sai dai wajen su Khadija har yanzu ba su san me ke faruwa ba, duk suna zaune jugum har yanzu Bilal bai farka ba wayar Usman ta shiga kururuwa, cikin sanyin jiki ya fito da ita ya duba, take gaban shi ya tsinke ya fad'i saboda ganin sunan *uwar yarima*, kallon Hajia ya yi da ke fuskantar shi, har wayar ta tsinke bai d'aga ba saida tace "Ka d'auka mana, wa ya ke kira ne?"


Cike da damuwa yace "Khadija ce." Malam ne yace "Ka d'auka mana sai ka fad'a mata wani abun, inyaso sai kaje gidan ka fad'a musu a nutse."


Khadija da ke tare da k'anwar Mama da kuma Kaltume zaune kasa hak'ura ta yi ta sake aika wani kiran, dan gabanta ne taji ya tsananta fad'uwa haka kawai, ta kira Bilal kuma ba ta samu ba shi ya sa ta kira Abban shi, d'auka ya yi cike da son b'oye halin da ake ciki yace "Uwar yarima ya ake ciki? Har kinyi kewata ko?"


Hajia dake kallon shi mik'ewa ta yi ta fita saboda kunya, inda Khadija ta amsa da "Na yi kewar ka mana, kai fa?"


"Kema kinsan na yu kewar ai, yanzu fad'a min kin shirya ne na zo na d'auke ki?"


Dariya ta yi tace "Haba dai, da rana haka patsal-patsal, ai ko zan shigo saida dare."


"Kamar wata marar gaskiya, to me ya sa?"


"Saboda lokacin da za'a kaini gidan ma da daddare aka kai ni, dan haka yanzu ma sai da dare zan koma."


Murmushi ya yi yace "To da da d'in da yanzu d'aya ne? A lokacin fa kina sabuwa ne fil a leda, yanzu kuma na bi ta ciki na fito, sannan Bilal ya fito ta nan ga kuma k'annan shi ma na shirin fitowa."


Duk da ya sassauta murya saida Hassana taji me ya fad'a, kallon shi ta yi ta kuma sunne kanta k'asa ta rufe baki cike da kunya, Khadija kam cewa ta yi "Matsala ta da kai fa kenan, yanzu dai ba wannan ba, ina yaro na yake? Ina kiran shi amma ba a samu."


Wani tsam yaji a jikin shi kafin ya daure yace "Bilal ya d'an fita tare da Murtala, mu na shago ne, watak'ila cajin wayar ne ya k'are, amma zan..." Kasa k'arasawa ya yi saboda rawar da muryar shi ke yi, da k'yar yace "Zan kira ki saina baki shi."


Ba tare da damuwa ba tace "Shikenan sai na jika, sai anjima."


Cike da zolaya yace "Au! dama muryar d'an ki kawai ki ka kira kiji? To ya yi kyau."


Dariya ta yi tace "To meye a muryar ta ka da za ta dame ni? Bayan anjima kad'an za mu kasance tare da kai."


Da haka sukayi sallama bai nuna mata komai ba, sai lokacin ne malam yace ya kamata su san halin da ake ciki, fita ya yi da niyyar zaije ya samu Ashir ya fad'a masa, hakan kuwa akayi dan ba jimawa ya isa in da Ashir ke harkokinshi, bayan sun gaisa ne ya fad'a masa abin da ke faruwa, ya jinjina al'amarin tare da tashin hankali, amma sai Usman yace "Idan dai har kai za ka d'aga hankalin ka to ya mahaifiyar shi kenan? Na zab'i na fad'a ma ka saboda ka san ta hanyr d za ka kwantar mata da hankali."


Shiru Ashir yayi kafin daga bisani yace "Hakane Usee, insha Allahu zan fad'a mata yanda za ta fahimta, kar ka damu."


Hannu ya bashi su ka yi sallama yace zai wuce gida ne, shi ma Ashir d'in gidan ya nufa daga nan dan fad'a musu, Mama ya fara fad'a ma tasan halin da ake ciki, ita kanta Mama da k'yar ta iya fad'awa Khadija, cikin tashin hankali tace Ashir ya kaita asibitin taga d'an ta, a hanya ma kuka take ta na fad'in kawai laifinta ne da ta yarda ta bashi yaron, Mama ce ta dinga tausarta da kalamai masu kwantar da hankali da k'arfafa gwiwa, suna isa asibitin aka nuna musu d'akin, da sallama su ka shiga amma Khadija na ganin Bilal kamar ba shi ba sai ta yi shiru, da k'yar ta isa ga gadon ta zauna ta na shafa fuskar shi, hawayen da suka taho mata ne ya sa malam cewa "A'a Khadija dan Allah, kar ki masa kuka mana, k'addara ce da kuma tsautsayi, ki masa addu'a Allah ya tashi kafad'un shi."


Hassana ce ta yi tsaye kanta tana shafa bayan ta tana bata hak'uri ita ma, sun jima a haka kafin ta kalli Nura tace "Har yanzu bai farka ba?"


Cikin sanyin jiki yace "Bai farka ba har yanzu, amma dai likitan yace an masa allura ne."


Cikin zubo da wasu hawayen tace "Ko dai ya mutu ne? Dan Allah ku fad'a min idan ya mutu, wallahi zan d'auki dangana."


Hajia ce tace "Haba Khadija, idan ya mutu za mu saka shi gaba ne haka, da ran shi mana gashi ma ya na numfashi."


Haka suka zauna jugum sai wasu dake tafiya wasu na zuwa, sai yamma kad'ai Bilal ya farka idon shi har sun kumbura, bud'ar bakin shi da "Mummy, Mummy." Ya fara, dama ta na kusa kam ta rik'o hannun shi tace "Gani nan Bilal, bud'a idon ka."


Bud'a ido ya yi ya kalle ta sosai, hawaye ne suka taho mi shi yace "Mummy ina Abba na?"


Saida ta mayar da na ta hawayen tace "Ya tafi gida yanzu zai dawo."


Da k'yar yace "Mummy, ciwo na, ki bani ruwa na sha." Ruwa ta d'auka ta bashi, komawa ya yi ya kwanta yanda ya ke har bacci ya sake d'aukar shi.


*B'angaren* Usman kuma tun a hanya yake tunani dama Haseenah ta shirya raba shi da yaron shi, in ba haka ba me ya sa ta hana shi ya fita da shi? Kawai makirci ne ta shirya mi shi dan ta raba shi da Bilal d'in shi, tunda ai tasan baya bari Bilal ya fita da moton shi, ko a k'afa bai cika son ana aikan shi ba wajen ti-ti, da wannan tunanin ya k'araso gida dan d'aukar mataki akan amarsu.


_Ita dama rayuwa haka take tafiya, ka shuka alkairi saika girbi alkairi, a baya mutane suna ganin laifin Khadija saboda makircin Haseenah, wanda ita Khadija a kan gaskiyarta take, yau kuma gashi Haseenah ita ma bata da niyyar cutar da Bilal, amma sakkayar Allah dama haka take, gashi ita ma yanzu za'a hukunta ta akan laifin da bata san hawa ba bata san sauka ba, Allah ka mana agaji da kan ka._


Haseenah da ke madafa a lokacin da waya a kunne ta kira Mariya ta na tambayar ko za ta zo? Cewar Mariya "Haseenah ba zan samu damar zuwa ba wallahi, saboda kwana biyun nan munyi hidimar biki, ko na tambayi Abban Fadila ma ba zai bar ni ba, amma ke ki zo ki kawo kud'in, idan na samu dama sai naje wajen malam d'in."


Cikin damuwa tace "Haba aunty Mariya, na fad'a mi ki fa halin da nake ciki, wallahi Usman ko magana ba ya son yi min, ina ga fa Khadija wani asiri ta masa ya juya min baya, kuma yace za ta dawo gidan, jiya ma kar ko so kiji maganar da ya fad'a min akan Bilal, to ina ga ta dawo gidan? Ai sai dai ya sake ni."


Mariya ce tace "To ya za ayi? Ni dai yanzu na fad'a mi ki uziri na ai, kinga kuwa dan na gyara aurenki ai bana b'algace nawa ba."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "To shikenan, bara ya shigo saina tambaye shi naji idan zai bar ni, ko zuwa gobe sai naje na kai mi ki kud'in, amma fa aunty Mariya wannan karan so na ke gaba d'aya a zautar da shi ya zama ba komai a gabansa sai ni, sannan ba shi kad'ai ba har iyayen shi da yan uwan shi ina so a rufe bakin su, su zama babu ruwansu da harkar shi bare har wani ya yi tunanin taimaka masa da ko da addu'a ce."


Da matuk'ar mamaki Mariya tace "Ke Haseenah, a ina ki ka koyi mugunta haka? Yaushe zuciyar ki ta zama marar imani haka? To kinga gaskiya no ba zan iya wannan aikin ba, dan in na biye mi ki mu ka yi haka to kashin mu zai bushe wallahi."


Cikin rashin nuna damuwa tace "Me ki ke nufi? Kamar ya banda imani?"


Muryar Usman ce ta bata amsa da "To ki na da shine imanin?"


Bata san lokacin da ta saki wayar ba ta juyo da k'arfi, hannu tasa ta rufe bakinta matuk'ar tsoro a fuskarta, tabb', lallai yanda ta ga alamunshi ta san yau babu tsumi ba dabara, amma duk da haka bara ta jaraba lallab'a shi ko Allah zaisa a dace, a cewar ta fa, durk'ushewa ta yi ta had'e hannayenta ta kalle shi tana hawaye tace "Dan Allah dan girman Allah Abban Bilal ka yi hak'uri, wallahi tallahi sharrin shaid'an ne da zugar aunty Mariya, ka yi hak'uri ka yafe min dan Allah ko dan cikin nan dake jiki na, wallahi na ma ka alk'awarin haka ba za ta sake faruwa ba."


Takowa ya yi har kusanta ya sa hannu ya kashe wutar gas d'in, tsayawa ya yi ya na k'are mata kallo, wai yarinyar da ya aura saboda nutsuwarta da hankalinta, ita ce ta yi sanadiyar faruwar abubuwa marasa dad'i irin haka a rayuwar shi, ita kam kallon da yake mata ne ya sa ta sake cewa "Dan Allah babban mutum ka yi hak'uri, wallahi ba laifi na bane, wall..."


Marin da ya zuba mata ne ya sa ta kwamtsa wata k'ara ta fad'i kwance, duk'awa ya yi ya d'ago ta cikin zafin rai ido jawur yace "Haseenah me nai mi ki a rayuwa? Me ya sa ki ka cutar dani? Me ya sa Haseenah?"


Cikin duburburcewa tace "Wallahi ba ni bace, ka yi hak'uri dan Allah, ba zan.." Shak'e mata wuyan da ya yi ne yasa komai nata tsayawa idon ta fitowa waje, cikin fitar hayyaci Usman ke fad'in "Haseenah ke annoba ce, jaraba ce kuma masifa ce ke da bala'i, barin irin ki a doron duniya wallahi japa'i ne, wallahi da zan kashe ki amma ba zan iya ba saboda cikin da ke jikin ki, Haseenah banga anfanin zama da ke ba a rayuwa ta, kin raba ni da hankali na da ubangiji na, kin raba ni da iyaye na da 'yan uwa na, kin raba ni da matar da nafi so a rayuwa ta, sannan kin raba ni da d'ana da ya fito daga ciki na, Haseenah ni kam ya zanyi dake? Wane irin hukuncin ma zan mi ki ne da zai sa na huce abin da ki ka min."


Haseenah dake ta fafutukar neman rayuwa ya na sakin ta ta samu ta sauke wasu numfarfashi,  mik'ewa ya yi tsaye ya juya baya ya cire hular kan shi yana shafa sumar shi kamar zai cire kan, sake juyowa ya yi ya nuna ta da hannu yace "A dalilin ki yanzu haka Bilal na kwance asibiti, bansan ko zai rayu ba saboda yanda jikin shi yake, dan haka Haseenah ba zan iya ci gaba da zama dake ba, kije gidanku kawai na sake ki saki biyu."


Wata k'ara Haseenah ta yi ta d'ora hannu akai tace "Ahhhhhhh, na shiga uku na lalace, dan Allah Usman ka rufa min asiri ka yi hak'uri ka yafe min, wallahi ba zan sake ba na rantse ma ka, ka taimaka min mana ka dubi cikin nan dake jikina, kar ka mayar dani bazawara tun yanzu Usman ko haihuwar fari banyi ba."


Girgiza kai yayi ya tab'e baki yace "Hum, ai ko meya faru ke kika jawa kan ki, dan haka ki tattara naki ya naki ki bar min gida na, idan ki ka bari na dawo gidan nan na same ki wallahi saina lahira ya fiki jin dad'i."


Yana fad'a ya fice daga madafar ya shiga b'angaren shi, rage kayan jikinshi ya yi ya shiga ya watsa ruwa saboda yaji sanyi, yana fitowa maganin ciwon kai yasha kafin ya canza kaya ya bar gidan ko kallon b'angaren Haseenah baiyi ba, a tunanin shi ma tana barin gidan zai ruguza wannan b'angaren dan ya zauna lafiya, dan ba zaisake bari zuciyarshi ta raya mi shi sake k'ara wani aure nan gaba, lokacin har an fara kiran sallah la'asar sai kawai ya tsaya ya yi sallah kafin ya isa asibiti.



*Ana tare*🤝

11/03/2020 à 19:36 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *38*



Bai samu ganin Khadija ba saboda a lokacin suna sallah, kuma an rufe d'akin da Bilal ke kwance saboda hayaniyar da tayi yawa aka barshi shi kad'ai kafin wani lokaci, fita Usman d'in ya yi yace zai dawo anjima.


A wajen Haseenah ba yanda ta iya dole ta d'an d'auki abin da ta d'auka ta fito ta na kuka ta bar gidan, amma da taje gida kasa fad'an komai ta yi sai tace kawai ta na girki ya same ta yace ta taho gida ya sake ta saki biyu, su kam iyayen take su ka d'ora laifin kan Khadija cewa ita ta shiga ta fita aka sake ta, Haseenah dai komai ba tace ba sai sauraren su, mahaifin ta ne yace zai je ya samu mahaifin Usman d'in dan ba zai d'auki wannan wulak'ancin ba a sako masa 'ya da tsohon ciki, ba ta yi yunk'urin hanawa ba tunda ita kan ta za ta so ta koma d'in, haka ko akayi bayan sallah magriba anyi katari malam ya na gidan mahaifin Haseenah ya sallama ya fito, da ganin shi malam ya tarbe shi yanda ya kamata ya shinfid'a mu su tabarma a waje su ka zauna, nan fa malam *Mussa* ya fad'awa malam abin da ke faruwa, sosai malam ya jinjina ya kuma fad'a mi shi baisan me ke faruwa ba sai yanzu, amma ya yi alk'awarin tuntub'ar Fodio yaji dalilin yin hakan, nan dai ya kwantar masa da hankali suka rabu lafiya, malam kam baiyi k'asa a gwiwa ba wajen kiran Usman yace ya same shi gida, ana idar da sallah isha'i ya k'araso ya samu malam, a cikin gida suka samu waje tare da Hajia suka tattauna sosai sosai, anan ya fad'a mu su cewa "A gaskiya Baba ba zan iya zama da yarinyar nan ba, domin kuwa duk ita ce silar abubuwan da suka dinga faruwa da ni, kawai ku rabu da ita can ta haihu, idan ta haihu zanje na d'auko abinda ta haifa bayan ta shayar da shi dan ba zan iya barin abin da ta haifa a hannunta ba saboda mugun halin ta."


Malam ne yace "Amma duk abin da tayi Fodio bai kamata ka sake ta a wannan halin ba."


Shirun da ya yi yasa Hajia cewa "Koma dai menene ita taja, a gaskiya Hassenah ta bamu mamaki, yarinya sumi-sumi ashe lunbu-lunbu ce macijin k'yaik'ayi, muna ta wa Khadija kallon mai laifi ashe ita ce muguwar."


Murmushin gefen labb'a malam ya yi yace "Ai ni na sani dama *kallon kitse ne ku ke wa rogo*, kawai na zura mu ku ido ne har ita yarinyar ta mu ku ido, in banda hauka irin na ku ma ko gaske ne Khadija ta mallake Usman ai ni a gani na daidai ta yi, domin kuwa in har za mu iya yin magana irin ta jahilai to za mu iya cewa k'ashin arzik'in shi a jikin ta yake, shi ba kyau ba, shi ba hasken fata ba, shi ba kud'i ba a lokacin da ta aure shi, kuga kuwa tana da damar da za ta iya d'aukar kowane mataki dan ya zama na ta."


Cikin sanyin jiki Hajia tace "Gaskiya ne, wallahi sai yanzu na ke jin kunyar ta akan abubuwan da suka faru, daurewa kawai nake ina kallon ta."


Murmushi Usman yayi yace "Hajia ku kwantar da hankalinku in dai Khadija ce na tabbata ba ta kallon ku da wannan abun."


Nan dai suka gama tattaunawarsu kafin ya mu su sallama yace zai tafi asibiti, su kuma dama acan su ka yi sallah magriba, ba su jima da dawowa ba Abban Haseenah ya zo, daga nan asibiti ya nufa ya samu kam kamar ana wata sabga d'akin taf da mutane, Khadija dake zaune kusan Bilal muryar shi ce ta fallasa mi shi yanayin da yake ciki, duk sai taji ba dad'i tausayin shi ya kamata, gaisawa ya yi da mutanen dake d'akin kafin ya isa a gadon Bilal, kafe Khadija ya yi da ido yace "Nana ya mai jikin?"


Saida ta had'e abin da ya tokare mata mak'oshi ta kalle shi da murmushi ta sa hannu ta karb'i k'atuwar ledar hannun shi ta aje gefe tace "Mai jiki gashi nan da sauk'i."


"To Allah ya bashi lafiya." Ya fad'a ya gyara tsayuwarsa, sake d'agowa ta yi ta kalle shi, saida ta k'are masa kallo tace "Babban mutum ka ci abinci kuwa?"


Wani murmushin gefen labb'a kawai ya yi bai bata amsa ba, duk da zuciyarta na raya mata wani abun amma kuma k'wak'walwarta na hasko mata wani abun, kawai anfani tayi da abin da k'walwarta ke hasko mata ta kalle shi ta mik'e tsaye tace "Ina ga mu tafi gida kawai, ga Mama nan za su kwana a wajen shi."


Da mamaki ya kalle ta ya kuma juya ya kalli Mama, mama ce tace "Kuje kawai zan zauna wajen shi, ai ni ce ke daidai dama na tsaya tare da shi tunda d'an gudaliyar mijin ne."


Murmushi su ka yi kafin Usman ya fara fita ita kuma ta had'a kayanta ta same shi a mota, kallonta ya yi yace "Wane gidan zan kai ki?"


Dariya ta yi tana kallon shi tace "Gidan miji na mana, ko ka manta yau ne zan dawo dama?"


Lumshe ido ya yi ya kwantar da kanshi jikin kujerar motar, d'agowa ya yi ya kalle ta yace "Khadija Allah ya miki albarka, kamar kinsan ina buk'atar kulawar ki, Khadija duk duniyar nan ke kad'ai ce macen da ta iyani."


Da murmushi a fuskarta tace "Muje to ka min wanka ka canza min kaya, sannan na sama mana abun da za mu ci sai muyi bacci."


Wata harara ya dallo mata yace "Baccin lafiya? Yau fa kamar amarya ki ke."


Dariya ta sake yi tace "To mu samu muje gidan ko." Tayar da motar ya yi su ka d'auki hanya, saida ya tsaya ya siya musu sandwichs a hanya kafin suka wuce gida, tare suka shiga wanka suka shirya cikin kayan bacci kafin suka d'an sama cikin su sandwich d'in nan, sam Khadija ta manta ma da maganar wata wai Haseenah, hakan yasa ba ta tambaye ta, shiru d'akin ya d'auka saida Khadija ta juyo in da Usman ke kwance, zaune ya ke akan gadon ya tangale bayan shi da pilow damuwa b'aro-b'aro a fuskar shi, tashi ta yi zaune ta matsa kusan shi ta d'ora hannun ta akan k'irjin shi tare da d'ora kanta a kafad'ar shi, gyara mata zaman ya yi ta yanda yake shafar kanta a hankali, cikin taushin murya tace "Bilal ka ke tunani ko?"


Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace "Hakane, muna kwana nesa da Bilal a lokacin da ya kwana gidan su Hajia ko gidan su Mama, amma ban tab'a tunanin akwai ranar da za ta zo ba ina kwance kan gado na cikin sanyi shi kuma ya na kwance a gadon asibiti, ban tab'a tunanin haka ba ko kad'an."


Zunbur ta tashi zaune tana kallon shi tace "Ba ka tab'a tunanin wannan ranar ba? Amma me ya sa? Ko ka manta da mutuwa ne?"


Shiru ya yi ya tsareta da ido, d'orawa tayi da "Abban Bilal, mu gode Allah daya kasance ya na raye mana, da fa ta Allah ta kasance da yanzu ka na kwance akan gadon nan ne shi kuma ya na kwance cikin rami, zanin rufar shi shine k'asa, kaga kuwa sai mu gode Allah a hakan ma."


Murmushi kawai ya yi bai ce mata komai sai kallon ta da yake, matsawa ta yi ta sake lafewa a jikin shi tace "Yau fa dare na ne na farko, kar ka bari tunani da damuwa suyi tasirin hana ka kula da ni da kuma wannan bawan da baisan ma asalin yana da mahaifi ba har yanzu, ka bamu kulawar ka mana na wannan dare, karka damu da Bilal insha Allahu ya na cikin kariyar ubangiji tare da kulawar Mama, zaiji sauk'i."


Dariya ya yi ya matse ta sosai a jikin shi yace "To yanzu me kuke so na fara mu ku, dan dole zansa wannan d'an baban farin ciki yasan cewa yau fa ya shigo hannun shi, amma ina fatan dai kin shirya karb'ar uk'ubata?"


Da mamaki ta kalle shi tace "Ban gane uk'ubar ka ba?" Murmushin mugunta ya mata yace "Nasha wahala sosai kafin ki yarda ki dawo gida na, kin whalar da ni sosai, kin azabtar da ni fiye da tunanin ki, dan haka nima yanzu zan rama a daren nan tunda kin shigo hannu na."


Zabura ta yi ta na neman durkuwo daga kan gadon ya yi saurin rik'o ta yana fad'in "Ai ba ki isa wallahi, ina ki ke tunanin za ki je a daren nan? Daga ni sai ke fa a gidan."


Kukan shagwab'a ta saka mi shi tana zillewa tana fad'in "Allah bar ma gidan ka zanyi, ciki na fa k'arami ne, so ka ke min asarar shi bayan 'yan uwan ka har tsegumi suka fara min saboda ban k'ara haihuwa ba, Allah ni dai ka rabu da ni."


Sosai ya rumgume ta yace "Mak'aryaciya kawai, na fa san komai, cikin ki ya kusa shiga wata shida, a hakanne zan zubar da shi?"


"Ni dai ka sake ni na koma d'aki na kawai tunda mugunta za ka min." Ta fad'a ta na son raba kanta da shi, ya rik'e ta sosai ya rad'a mata a kunne "Na mi ki alk'awarin tafiyar da ke a hankali, abinci kawai zan baku cike da k'aunar ku."


D'ago kai ta yi ta kalle shi tace "Na ga idon ka idan gaskiya ka ke fad'a." Da sauri ya sa tafukan hannayen shi ya rufe fuska ya juya mata baya yace "Um um, ban yarda ba gaskiya."


Cakulkuli ta fara masa ta na fad'in "Ashe ba gaskiya ka fad'a ba, yeee Allah ya tona min kai."


Da irin haka suka tafiyar da daren su cike da kewar juna, bayan komai ya kammala ma alwala su ka yi Usman na gaba ita a bayan shi su ka yi k'iyamun-laili, ana kiran sallah farko ya nufi masallaci ita kuma ta mayar da sallahnta, daga nan kan darduma bacci ya d'auke ta, ko da ya dawo ya ganta d'aukar ta ya yi ya kwantar akan gado, makullin mota ya d'auka ya fita ya samo mu su abin karyawa ya aje kafin ya shirya ya fita zuwa asibiti, duk lokacin Dije na bacci bata farka ba, ya jima a asibiti tare da Mama da malam da Hajia suna ta hira kafin ya baro asibitin, gida ya dawo kai tsaye ya samu Khadija zaune akan teburin cin abinci ta na zubawa za ta ci, k'arasowa ya yi ya zauna yace "Dijangala tame gari, Dije sarkin hutu har an tashi kenan?"


Murmushi kawai ta yi tace "Na tashi, amma kuma saina nemi mijina na rasa in da ya shiga, kad'an ya rage na bayar da sanarwa a gidan radio sau kuma ga ka."


Cikin dariya yace "Allah ya na son ki da rahama shi ya sa ba ki yi asarar kud'in ki ba."


Zaune ta yi ta na aje farantin abincin gaban shi tace "Kuma na yi sa'a miji na ya na iya jiyo bugun zuciya ta daga duk in da yake, hakan ma ya taimaka wajen dawowar ka kusa da ni."


Hannu suka saka tare, kafin ta kai loma bakin ta tace "Wai ina Haseenah ne? Ba za ta fito cin abincin ba?"


Jim ya d'anyi kafin yace "Bata nan." Ba tare da damuwa ba tace "Ok, ko ta tafi asibiti ne awo?"


Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma yace "Ta na gidan su." Kallon shi ta yi tace "Gidan su kuma? Lafiya dai ko?"


Cike da jin an takura shi yace "Kai Khadija, ta na gidan su na ce mana, sakin ta na yi."


Dam, taji gaban ta ya fad'i, tabbas tasan ba su yi zaman lafiya da Haseenah ba, kuma ta na kishinta sosai ta na kuma ji haushin irin cutar da ta mata, amma hakan ba shi zaisa ta yi farin ciki da mutuwar auren ta ba, abu d'aya da ta sani shine ita ma mace ce kamar ita, tasan dole wannan kalmar ta girgiza tunanin ta, abun duba kuma anan shine cikin da ke jikin ta, in har za ta iya fad'an gaskiya to duk abin da ta yi ya kamata ace an mata uzuri, dan ko ita ce ba ta san irin damuwar da za ta shiga ba idan aka ce haka ta faru da ita, bare Haseenah da ko wata takwas ba ta yi ba a gidan miji amma ace an sake ta da cikin fari a jiki, a hankali ta kalle shi tace "Amma Abban Bilal zan iya cewa wani abu?"


Ba tare da ya kalle ta ba yace "In dai akan wannan yarinyar ce ba buk'ata, hukunci ne kuma na yanke, zan kula da komai daga yanzu har lokacin da za ta haihu, idan ta haihu kuma ta gama shayar da abin da ta haifa zan d'auko shi na dawo da shi kusa da ni, nasan banda matsala wajen samun wanda zai rik'e shi, ko ke za ki yi min wannan karamcin."


Wani mamakin ne ya sake bayyana a fuskar ta ta na kallon shi, ganin haka ya sa ya mik'e yace "Ni zan fita waje, idan kin gama ki same ni saina aje ki asibiti."


Da kallo kawai ta bishi har ya fita, ji ta yi abincin ya fita a ran ta ita ma sai kawai ta tattara ta shiga da shi madafa, juyewa ta yi a kwano ta fito da shi ta bawa Rabe, godiya ya mata kafin ta samu Usman suka wuce, babu mai magana har suka isa asibiti ya aje ta a bakin k'ofar, saida ta fito ta rufe k'ofar ta kalle shi tace "Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo."


Kallon ta ya yi yace "Ameen, Allah ya sa." Da haka ta shiga ciki shi la ya wuce, sosai ta yi farin cikin ganin Bilal a zaune ya na shan koko mai d'umi, godiya ta yi ga Allah da ya sa yaron ta ya rayu kula har za ka iya cewa ma jikin shi da sauk'i fiy da jiya da ba za ka ce ya na raye ba, sai dai fatan Allah ya k'ara mi shi lafiya mai anfani.


Haka su ka ci gaba da jinyar Bilal cike da kulawa, in da aka d'auke shi daga gidan gaggawa aka mayar da shi cikin asibitin, kullum 'yan uwa su na zirganiya a hanyar asibiti ganin Bilal, Khadija kuma da Usee suna farin ciki idan suka koma gida, har yanzu ba ta sake mi shi maganar Haseenah ba amma abun na damunta sosai, kullum tana auna hakan da kanta ta na ganin idan ita ce ya za ta yi? Ta na so ta sake mi shi magana amma da ta yi magana da Hajia sai tace kawai ta share ta kar ma tasa ran shi ya b'ace akan wata, shi ya sa ta d'anyi shiru amma ba wai ta hak'ura bane, dan abin da take tunani ba kowa bane ke tunanin shi, a haka suka kwashe *sati d'aya* a asibiti.


*Kwana goma sha d'aya* aka sallami Bilal saboda jikin shi ya yi sauk'i sosai cikin hukuncin ubangiji, a lokacin kuma Haseenah rayuwa ta fara gara ta yanda take so...



*Allah ka sa mu dace.*

13/03/2020 à 14:14 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


```Fatan alkairi masoya```



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *39*



Sabo da jar miya da cin abin da rai ke so ya sa Haseenah ba ta iya cin abincin gidan su, da yake ta na da 'yan kud'in da ta samu hannun Usman sai take anfani da su wajen siyan abin da take so, sannu-sannu kuma sai k'annan ta suka fara d'ora mata raini ta yanda ko aikensu ta yi ba sa zuwa, da k'yar wani lokacin za ta basu kud'i su tafi, wani lokacin kuma sai dai ta tafi da kanta ta siyo dan abu mai galmi da yaji, gaba d'aya a takure take jin kanta a zaman gidan nan, d'akin da suke kwana ita da k'annan su ga zafi ga rashin sarari, yau dai data tashi ta d'auko jakar yan kud'in ta da nufin siyo abin kari sai kud'i suka ce nemi in da ki ka aje, nan ta yi haukan nema amma ba ta gani ba, ta tambaya maman ta kuma tace to ita ina za ta sani, kuma ba kowa gidan sai su duk sauran su na makaranta, dole d'umamen tuwon da aka yi shi ta dank'ara tasha ruwa, ruwa ta kai ta d'auki kwandon sabulu dan yin wanka, amma sabulun sai kad'an ya rage wanda ba zai mata komai ba, cikin jin haushi ta kalli maman ta tace "Mama, wai yanzu shi ma sabulun da na saka saida wani ya d'auka?"


Cikin sanyin hali tsohuwar tace "To Haseenah ba sai ki yi hak'uri ba, da kina gidan ki nan kowa ke wadace da sabulun, sun d'an saba ne da wanka da mai k'amshin shi ya sa da su ka ga naki su ka d'auke."


"To amma Mama ni fa kad'an ne na taho da shi sabulun, yanzu haka ina ga bai wuce uku ba wanda ya yi saura, idan ya k'are sai mu yi ya kenan?" Duk ta yi maganar ne kamar za ta fashe da kuka, a tak'aice tace "Sai ku taru ku hak'ura."


Tsaki ta yi ta shiga d'aki ta d'auko wani ta saka ta shiga ban d'akin, wanka ta yi ta fito ta shirya cikin doguwar riga, tsakar gidan ta fito ta d'auki waya da nufin shiga yanar gizo, sai dai ina babu sadarwar ta k'are kuma babu kud'i a wayar, kallon ta maman ta tayi tace "Haseenah, wai har yanzu mijin ki bai kira ba?"


Cikin takaici tace "Mama bai kira ba, dama ai ba kira na zaiyi ba."


"Kuma ke ba ki tab'a jaraba kiran shi ba ko?" Kallon maman ta tayi tace "Mama taya ni zan kira shi, ai ba d'auka zaiyi ba." Shiru kawai tsohuwar ta yi sai Haseenah da ta shiga duniyar tunani, sai lokacin ma ta tuna da waccen ranar da ya sake ta yace Bilal na asibiti kwance a dalilin ta, to me ya samu Bilal d'in? Ta tambayi kanta, kallon maman ta tayi tace "Mama."


"Um." Ta fad'a ta na kallon ta, cikin taushin murya tace "Mama me zai hana ke da Baba kuje ku dibo jikin Bilal?"


Sake kafe ta da ido ta yi tace " Bilal kuma? D'an Usman d'in?" Ita ma ta na kallon ta tace "Eh mama."


"Dama ba shi da lafiya amma ba ki fad'a ba sai yanzu?" Shiru ta yi ta na sosa kai, tsaki ta yi tace "Allah ya kyauta, Haseenah ko ba ku yi zaman mutumci da matar shi ba ai ina ga dai kya fad'a aje a duba shi ko dan awa Usman kara, ke da shi fa yanzu wata alak'a ce mai k'arfi ta shiga tsakanin ku, ki daina ganin ya sake ki hakan ba shi zai ruguza alak'ar ba."


Da rana bayan Baban su ya shigo mahaifiyar su ta fad'a mi shi ta na so taje ta duba jikin Bilal, da yake dama matar ta fi shi hankali da hangen nesa shi ya sa yaran ma suka fi shakkar uwar akan uban, sai kawai yace ai babu mutumci tsakanin su da Khadija, 'yar su na gida ne saboda ita dan haka babu in da za ta je, nan ta nuna mi shi ba saboda Khadija zata je ba saboda Usman za su je, d'an shi na asibiti kwance ya na da kyau suje ganin shi, ai kuwa bai bari ta tafi ba dan sosai ya rufe ido shi bai yarda ba, haka ta hak'ura ba dan ranta ya mata dad'i ba.


A wajen su Khadija kuma jikin Bilal da dama sosai, suna zaune tare da shi ya d'ora kan shi a k'afafun Mama su na hira, Mama ce tace "Wai ni kam banji motsin abokiyar zaman taki ba, ko bata nan ne?"


Sai lokacin Khadija ta iya tuna bata fad'awa Mama ba, da sauri tace "Kai, Mama ashe baki sani ba ko? Wallahi bata nan gidan tunda na dawo."


Mamaki fa a fuskar Mama tace "Bata gidan, to meya faru? In ce dai lafiya?"


Cike da damuwa Khadija tace "Mama yace sakin ta ya yi, kuma na so yi masa magana amma ya nuna kawai babu ruwa na, sannan na yi magana da Hajia ita ma tace wai na fita harkar ta, sai dai ni gaskiya banji dad'i ba mama saboda ganin halin da take ciki abar a tausaya mata ce."


Cike da jimami Mama tace "Ah sosai ma, komai ai hak'uri ake yi ba a yanke hukunci cikin hushi ba."


Tab'e baki Khadija ta yi tace "Mama kullum tunani na shine idan ni ce ya zanyi? Abun baya min dad'i ko kad'an, amma tunda ya nuna baya so na rabu da sh."


"A'a Khadija." Cewar Mama ta katseta kafin ta d'ora da "Duk da baya so ke ya mata kisan hanyar da za ki shawo kan shi cikin hikima, na sani Khadija kishiya babu dad'i, kuma burin kowace mace ta zauna ita kad'ai a gidan mijin ta, amma ina so ke ki zama ta daban a cikin mata, Khadija idan kika zama silar dawowar ta to kin saka mata alkairi da sharrin da ta mi ki, wannan kuma shine nagarcin addinin ki, yafiya, mantawa, kyautatawa, kinji ko Nana Khadija, ki yi wannan jarumtar ko da baya so, amma idan kinga abun zai zama matsala to sai ki barshi kawai."


Da murmushi tace "Insha Allahu Mama zanyi, nima dama na so tun farko na yi hakan, amma yanzu kin k'ara k'arfafa min gwiwa, tunda ko ba komai sun ruga da sun zama d'aya shi da ita tunda ta na d'auke da cikin shi, rabuwar kuma ba dad'i musamman ita da k'ananan shekaru."


"Gaskiya kam, dan hakan zai iya zama tozarci gare ta da b'ata mata suna."


Cikin nutsuwa Khadija tace "Mama ba lallai ma a kalle ta da laifi ba, ni ba zan fita daga zargi ba tunda dama ana ganin na mallake shi, kinga yanzu za'a ce ni ce na fitar da ita daga gidan, babu wanda zai tuna lokacin da ni na d'auka a na mu gidan gaban iyaye na, nata ne yanzu zai fito fili kowa ya ji."


Cike da gamsuwa mama tace "Gaskiya ne kam, dan ko ansan kin zauna a gidan ma za'a d'auka kishin ki ne ya tura ki gidan, mutum, mutum ai sai Allah." 


Murmushi Khadija ta yi tace " *Mutum mugun ice, ya mutu ma fa sai an d'aure shi Mama.*"Dariya Mama ta yi kafin suka ci gaba da tattaunawa.


Washe gari da safe ma daga Haseenah sai maman ta a gidan duk kowa ya tafi harkar gaban shi, rana ta fito sosai Mariya ta shigo d'auke da kaya da alaman sabuwar d'auka ce ta yi, gaisawa su ka yi sosai har ta fara hira da maman ta akan kasuwancin na ta, sun jima nan kafin maman su ta tashi ta shiga d'akin su dan yin wani abun, Haseenah na ganin haka tace "Aunty Mariya, muje d'aki ina son magana da ke."


Cikin rad'a tace "To lafiya dai ko?" Saida ta mik'e ta nufi d'akin tace "Ki zo kiji ke dai."


Mik'ewa ta yi ta na fad'in "To na ji alkairi." Suna shiga bakin katifa suka zauna Haseenah ta tsareta da ido tace "Aunty Mariya, na d'auka abin da ya faru da ni za ki taimaka min wajen ganin na koma gidan Usman, amma ke ko a jikin ki ma sai harkokin gaban ki kike."


Cewar Mariya "To me zanyi in ba harkokin gabana ba, sannan wane irin taimako ki ke buk'ata daga gare ni yanzun?"


A daidai lokacin da Haseenah za ta yi magana a lokacin mahaifiyar su ta fito daga nata d'akin, za ta wuce ne taji Haseenah tace "Ki yi wani abu mana na koma gidan shi, Ko so ki ke na haihu gida?"


Kallonta Mariya ta yi tace "Na yi me? Me ki ke nufi? Wai na sake komawa wajen malam? Sam wallahi ba da ni ba, ai na fad'a mi ki tun ranar Haseenah gaskiya ba zan iya binki mu tsunduma kogin da ki ke neman jefa mu a ciki ba, idan na yi haka to fa nan gaba ba naki auren bane zai mutu har da nawa."


Wani kallo Haseenah ke mata amma ba tace komai ba, d'orawa ta yi da "Kinga k'anwa ta, ki yi hak'uri da abin da ya sameki ki rugumi k'addara, sakin aure ba'a kan ki aka fara ba bare ya k'are kan ki, yanzu idan mu ka ce zamu matsanta sosai to wallahi abubuwa ba za su yi kyau ba, dan ko da an sake juyar mi shi da tunani ya dawo kan ki wallahi ranar da ya sake dawowa hankalin shi a karo na biyu to fa zai sake koroki ne, dan haka abin da yafi kawai ki tuba ga Allah tare da rainon cikin ki har ki haihu, domin Allah fa kin cutar da su sosai, kin raba shi da matar shi, kinsa dangi suna mata kallon marar imani kuma mai laifi, alhalin kuma ke ce mai laifin, ke ba ma dangin shi ba kad'ai har dangin har yanzu suna kallon Khadija a matsayin wacce tasa aka sake ki, alhalin kuma duka mutane *kallon kitse su ke wa rogo*, ke da ake gani ba ruwanki ke ce kuma gubar."


Cikin jin haushi Haseenah tace "Ni ce ma gubar? To idan ni guba ce ke kuma fa? Ai ke ce babbar guba tunda ke ki ka haddasa komai, ina zamana lafiya ban tab'a tunanin wacece matar shi ba, amma ke ki ka zo min da labarin cewa matar shi yar duniya ce ta mallake shi, sannan waya kai ni wajen malam in ba ke ba, wa yake zuwa har gida na ya na karb'o kud'in da ake kaiwa malam d'in? Ai ke ce da kan ki, amma   shine yanzu za ki kira ni da guba, to ke ce babbar guba ba ni ba wallahi."


Tab'e baki Mariya ta yi a ran ta tace "Sakarya kawai." A fili kuma cewa ta yi "Wannan kuma ke ta shafa, ni kinga tafiya ta sai anjima." Ta na fad'a ta mik'e za ta fita sai ga mahaifiyar su ta shigo d'akin dan kaf babu abin da bata ji ba, baya ta rumgume hannaye ta na kallonsu cike da haushi kafin tace "Abin da ku ka aikata kenan? Mariya, Haseenah, wannan ita ce tarbiyyar da mu ka baku a gidan nan? Wannan wane irin zubar da mutumci ne? Kenan mutuwar auren ki ba ya da nasaba da kishiyar ki? Haka kawai kinsa muna kallon ta a matsayin mai laifi, to rashin lafiyar da muke tunanin ki na fama da ita fa har da nemo mi ki magani? Ko dai duk k'arya ce ki ke? Dan babu yanda za ayi mata biyu a gidan miji d'aya su zama mushrikai." 


Sosa kai Haseenah take cikin rashin abin fad'a sai tsohuwar ce ta k'ara da "Ko ba ki fad'a ba ya nuna ba ki da gaskiya, amma Haseenah taya ki ka iya shirya makirci irin haka? Ko ni da na haife ki ba zanyi abin da ki kai ba."


Kallon Mariya ta yi sama da k'asa tace "Babbar banza, yanzu idan akwai wanda ya kashe mata aure ai bayanki ya ke."


K'asa ta yi da kanta sosai hakan ya sa tsohuwar juyawa ta fita ta barsu, cikin sanyin jiki Mariya ta fita sai Haseenah da ta fashe da kuka, *Asiya* kuma d'akin ta ta koma ta shirya saida ta fito za ta fita ta lek'a d'akin Haseenah tace "Zan fita yanzu, babu kowa a gidan ki fito ki d'ora girkin rana kafin yaran nan su dawo, daga yau kin bar kwanciya a d'aki da sunan wai ki na da ciki a tausaya mi ki, girki da wanke-wanke ya zama na ki."


Ta na fad'a ta fice abin da har zuwa bakin ti-ti ta samu adaidaita ta hau, kai tsaye gidan Khadija ta isa, duk da ba sosai Khadija tasan ba amma dai ta gane ta, sosai ta tarbe ta kamar za ta had'e ta cikin girmamawa, dama kuma in dai ta wannan fannin ne Khadija gwana ce, hakan ya sa ma take da farin jinin al'uma, har d'akin Bilal ta rakata taga jikin shi kafin su ka dawo falo ta zauna, cike da dattako tsohuwar ta kalli Khadija tace " 'Yata Khadija, na zo ne ganin jikin yaron ki da sai jiya na ke jin bai da lafiya, sai kuma abu na biyu na zo na baki hak'uri akan abin da ya faru, 'yar nan wallahi ba mu tab'a tunanin Haseenah za ta iya cutar da wani ba, amma sai yau kuma yanzu na ke jin irin ta'asar da su ka yi ita da 'yar uwar ta daga bakin su, hak'ik'a yau Allah ya wanke ki daga zargin da mu ke mi ki, muna kallon ki a matsayin wacce take hana 'yar mu zaman gidan aure, ashe ba haka bane komai makircin su ne, ashe har zuwa gidan da take ta nuna bata lafiya ba ta son zaman gidan duk k'arya ne, kawai d'ora mi ki laifi ne suke son yi, dan Allah ki yi hak'uri ki yafe mana kinji 'yar albarka."


Khadija da ta yi jim ta na jinjina al'amarin Haseenah, sai yanzu ne take sanin wannan labarin na rashin lafiya, kenan ita ake kallo da wannan laifin ma, murmushi ta yi ta rik'o hannun Asiya tace "Mama, ke fa uwar ce a gare ni, yanda Mama na bata neman gafara na akan duk abin da za ta min to haka ke ma, wallahi na yafe mu ku dukan ku, ni dama ban tab'a rik'e kowa a zuciya ta ba saboda ina so nima Allah ya kalle ni da idon rahama, dan haka ku kwantar da hankalin ku yanzu mun zama d'aya ni da ku, kuma ita rayuwa dama haka take, wanda wautar shi ta fito fili shi ake kamawa da laifi, wanda kuma ya iya takon shi to ko shine mai laifin sai kaga babu mai gani bare ayi magana, kuma ita dama ance *fahimta fuska* ce."


"Hakane kam, Allah ya mi ki albarka, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya, Allah ya kare ki daga sharrin abokan zama irin su Haseenah." Sakin hannun ta Khadija ta yi ta mik'e tace "Ni zan tafi, dama ko mahaifinsu bai san na zo ba."


D'aki Khadija ta shiga ta tarkato kaya sabulu da turaruka da turmin atamfa mai kyau, sannan ta had'o da wani k'aton mayafi da ita bai birge ta ba tunda mama ta siyo mata shi daga Dubai, haka ta had'a tsohuwar nan da su ta rakata har k'ofar gida, Rabe da ke zaune tace ya d'aukar mata kayan har saida ta samu adaidaita, Asiya kam a adaidaita har kuka ta yi ganin irin alherin da Khadija ta yi mata, ta na komawa gida ta samu mahaifinsu ya dawo zaune a tsakar gidan, tun bata gama shigowa ba yace "Daga ina ki ke Asiya?"


Kai tsaye tace "Daga gidan Usman."


Da sauri ya kalle ta haka ma Haseenah da ke bakin murhu ta na girki duk ta yi gumi, cikin hushi yace "Yanzu da na ce kar ki jr shine ki ka wanke k'afa ki ka tafi ba da izini na ba? Asiya yaushe ki ka fara yin watsi da maganata? Akan matar da ta kashe ma yar ki aure ne za ki wulak'anta ni haka?"


Abun da bai tab'a faruwa ba shine yau ya faru, cikin d'aga murya tace "A'a malam, kar ka sake ganin laifin ta akan zunubin da 'yarka ce ta aikata shi, wannan yarinyar babu abin da ta aikata, kaga mai laifin nan gaban ka." Ta fad'a ta na nuna Haseenah wacce ta yi k'asa da kan ta, a tausashe yace "Me ki ke nufi da ba ita ce mai laifi ba Haseenah ce?"


Kujerar katako ta janyo ta zauna kusa da shi ta aje jakar hannunta gaban shi, nan ta zayyane mi shi duk abin da taji sun tattauna da kuma zuwanta gidan Khadija yanzu, cikin b'acin rai ya d'auki takalman shi ya tilk'awa Haseenah a baya gashi kam ba ta san da saukar takalman ba, ji ka ke timmm a bayan ta, k'ara ta saki ta dafe baya ganin ya d'auki d'aya takalman ya sa ta shura a guje d'aki, masifa ya dinga zazzagawa takaicin shi kud'in da ya kashe wajen amso mata magani, zagi ya dinga aika mata a d'akin ya na yi ya na kallon kayan da Khadija ta bado.


*Daga ranar* komai ya k'ara canzawa Haseenah, kaf gidan yanzu babu mai kallon ta da mutumci, girki da wanke-wanke ko ga yara a gidan ita ce ke yi, wani lokacin ma mahaifin su har kayan shi ya ke bata ta wanke mi shi, duk a ganinsu horon da za su iya yi mata kenan da zaisa ta shiga hankalinta,  wani abu dake damun Haseenah sosai shine rainin da duka k'annan ta suka aza mata, ko kallon su ta yi sai ka ga wata ta kwad'a mata harara, haka kullum take cikin fad'a ita da k'annan ta, ga ciki na ta girma sosai ga kuma rashin kud'i, idan ta tafi awo kad'ai take jin dad'i duk da rashin kud'i ya sa ta canza asibiti, yanzu haka ta na awo ne a asibitin da ke kusa da su asibitin *Ali Chaibu*, a haka ta yi laushi sosai take k'ara nadamar abin da ta yi, gashi Usman ko kiran ta bai tab'a yi ba bai kuma tab'a zuwa ba da sunan ya ganta, ya je sau biyu amma wajen mahaifin ta ya tambayi komai lafiya suka gaisa ya tafi, sai dai duk sati biyu yakan aiko Bilyamin ya kawo mu su kayan abinci da kud'i saboda bebyn shi, har yanzu babu abin da ya rage daga jikin ta na k'iba da ta yi, sai dai fatar ta ta canza sosai ba kamar da ta na gidan ta ba, dan kuwa duk kayan da zai aiko iyayen ta sukan zama na anfanin duka gidan ne, kud'i kuma sai in za ta tafi asibiti ake bata wanda basu taka kara sun karya ba.


Duk lokacin nan da aka d'auka a wajen Khadija ita ma ta matsa lamba sosai kullum maganar Haseenah take wa Usman, ta yi rarrashin duniya ta yi kissar ta yi nisihar amma ya mayar da ita kamar mahaukaciya, akan maganar nan har fad'a su ka yi suka daina magana tsawon kwana uku, saida Bilal ya shirya su kad'ai suka koma magana, amma fa ba ta daina mi shi maganar ba, har tsawa ya mata ya zare mata ido yace idan ta na da zuciya ta daina mi shi maganar Haseenah amma tace ba ta da zuciya in dai akan maganar nan ne, haka kawai take jin zuciyar ta na yin sanyi kullum take son ganin ta dawo gidan ta, ta fad'a mi shi ya sake bata dama ta biyu mana tunda 'yar adam ce ita, amma abun baiyi tasiri ba, har Bilal ta sa ya rok'e shi take yace ya fita a harkar manya ba ruwan shi, izuwa yanzu kanta ya yi zafi akan maganar, hakan ya sa ta samu malam ta kalallame shi sosai, kuma ta yi sa'a ya gamsu da abin da ta fad'a sosai, alk'awari ya mata zan mi shi magana, kuma kamar yanda ya fad'a ya wa Usman magana, amma sai yace shi fa in aka sake matsa mi shi to zai bar mu su garin ita ma Khadijar ta koma gidan su, wannan magana ita tasa malam cewa "A'a Fodio, me ya yi zafi haka, Allah ya huci zuciyar ka, shikenan tunda ba ka so ai."


Cikin b'acin rai yace "Baba Khadija hankali ne bai ishe ta ba, in ba haka ba yarinyar da ta cutar da ita da ni da ku ma amma wai ta dage kai da fata sai an dawo da ita, to tsiyar me za ta mana idan ta dawo?"


Malam dai cewa ya yi "Yi hak'uri to shikenan, zam fad'a mata ta yi hak'uri kawai a bar maganar, Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi."


Malam da kan shi yaje har gidan ya fad'awa Khadija dan Allah ta manta da maganar Haseenah ta kula da mijin ta kawai, ba dan haka ta so ba ta nuna shikenan ya wuce, saida malam ya fad'a mata yace idan an sake takura shi fa zai bar gari ne, kai kawai ta gyad'a alamar taji, da dare ko da Usman ya shigo ya na zaune a falon ta tare da Bilal suna kallo Khadija ta fito da kinkimemiyar akwati da cikin ta masha Allah ya fito sosai, saida ta zo gaban shi ta tsaya tace "Malam ni zan tafi gidan mu tunda ka kasa min alfarma d'aya, idan na haihu nima ka zo ka d'auki abin da aka haifa."


D'auke kan shi ya yi daga kallon ta ya na kallon telebijin kamar bai san ta na yi ba, juyawa ta yi da jakar Bilal ya zabura zai tashi Usman ya rik'e shi ya fad'a jikin shi, cikin kunne ya rad'a mi shi "Bari kaga yanda zanyi da ita, ko k'ofar gida ba za ta je ba."


Har ta kai bakin k'ofa amma ba ta ji ana tsayar da ita ba, juyowa ta yi ta kalle shi ta tsaya cak, cikin d'aure fuska ya sa hannu aljihu yace "Kai na manta, zo karb'i kud'in adaidaita mana."


Lalaba aljihu ya ke kafin yace "Hajia banda canji, karb'i makullin mota ta ki tafi da ita gobe zan je na d'auko."


Ya k'arashe maganar da jefa mata makullin gabanta, haushi ne ya kamata sosai ta d'auki makullin ta juya ta fita, a hankali take tafiya da tunanin ko zai zo ya hanata amma shiru, k'wafa ta yi ta juyo da sauri cikin jin haushi ta dawo falon, zaune ta same shi yanda suke hankali kwance suke kallo, da sauri ta k'araso wajen shi ta  d'auki akwatin dama ba komai ciki ta jefa mi shi a jiki tana fad'in "Hamago kawai, kenan dama so ka ke na tafi na bar ma ka gidan saboda ka gaji da ni ko? To babu in da zanje wallahi mutu ka raba ni da kai, sai na yi takabarka da yardar Allah."


Tunda ta fara magana Usman ke dariya har da d'aga k'afafu ya na rik'e ciki, d'auke akwarin Bilal ya yi ya shiga d'akin ta da shi, Usman na ganin haka ya fizgota ta fad'a jikin shi ya rumgume ta yace "Ke a haukanki kin d'auka zan zauna hakane har ki bar gidan nan? Ai kafin ki isa gida zansa a sato min ke a dawo da ke."


Cikin kukan shagwab'a ta kalke shi tace "Abban Bilal dan Allah kayi hak'uri ka dawo da ita, wallahi tausayi take bani sosai inna tuna rayuwar da take, wannan ita kad'ai ce alfarmar da na ke nema a gurin ka, ka taimaka ka dawo da ita gidan nan mana ta haihu gidan mijin ta, kullum ina aunata da kaina sai naga idan ni ce ya zanyi ace zan haihu gidan mu, babu dad'i ko kad'an wallahi, dan Allah babban mutum ka taimaka mata kaji, na maka alk'awarin za mu zauna lafiya da yardar Allah."


Tun tana magana ya mayar da kallon shi ga telbijin, saida ta gama ya kalle ta yace "Khadija me ya sa ki ke son takura min akan magana d'aya? Me zaisa ba za ki bar maganar ba tunda har na ce ba na so? Me ta mi ki a rayuwa na alkairi da har ki ke son dawo da ita cikin rayuwar mu?"


Cikin muryar tausayi tace "Wallahi babu komai, na dai fad'a ma ka dalili na kawai, Abban Bilal shekara nawa mu ka d'auka muna neman haihuwa, amma zuwan Haseenah gidan nan sai gashi Allah ya azurtani da nawa cikin nima, watak'ila hakan ya faru ne saboda hak'urin da mu ka yi da kuma tsarkake zuciya ta da na yi wajen zama da ita, ba ka tunanin yanzu idan na sa ka dawo da ita Allah ya sake mana wata rahamar ta hanyar da ba mu yi tsammani ba?"


Ganin ya yi shiru alamun maganganunta na ratsa shi ya sa tace "Za ka iya tuna a cikin karatun da ka ke koya mana kai ka bamu labarin abin da ya faru tsakanin *sayyidi na Abbakar* da *musd'ahu* mai hidima gare su kuma wanda su ke d'aukar nauyin shi, Musd'ahu na d'aya daga cikin wanda suke yayata k'azafin da akawa *Nana Aisha (RA)* cewa ta yi zina, a lokacin da ran sayyidi na Abbakar ya b'aci ya kori Musd'ahu daga gidan shi tare da cewa ba zai sake d'aukar nauyin shi ba, me Allah yace akan haka, Allah ya na son masu yafiya, idan ka yafe kuma sai ka manta da komai, sannan ka k'ara da kyautatawa, to hakanne ya kamata ya faru a yanzu, ka yafe mata gaba d'aya, sannan ka manta da abin da ya faru ka daina tunawa, kyautatawar da za ka mata kuma bai wuce ka dawo da ita d'akin ka ba ta haifi abin da ke cikin ta ba ta kuma raine shi gaban ka, kar kaga ka na keyawa da masoyan ka za su kula maka da d'an da za ta haifa, rik'on yaro sai uwar shi, duk wanda kaga bai rayu da mahaifiyar shi ba dan hakan na mi shi dad'i bane, dan Allah miji na, Usman na Nana, ka saurari matarka mana ka tuna had'uwar ku ta farko da ita da kuma yanda zaman ku ya kasance, saika yanke hukunci."


Shafa kumatun shi ta yi ta d'aga shi zata koma d'aki dan ta bashi damar yin tunani, sumbatar kumatunshi ta yi ta rad'a mi shi a kunne cewa "Kar ka manta Khadija na matuk'ar son ka sosai, kai ne rayuwa ta babban mutum."


Da murmushi kawai ya bita da kallo harta shige d'aki, ya jima nan zaune ya na tunanin abin da ta fad'a mi shi, har ga Allah babu ko k'aunar Haseenah a zuciyar shi bare soyayyarta, amma zai dawo da uta saboda farin cikin Khadija kawai, amma kuma ba yanzu sai ta shiga watan haihuwar ta kad'ai zai dawo da ita, kamar yanda ta sa Khadija zama a gidan su ita ma saita d'and'ana zaman gidan sosai ya ratsata kafin, tashi ya yi ya shiga d'aki saida su ka yi shirin kwanciya kafin ya fad'awa Khadija ya ji zai dawo da ita amma da sharad'i, da sauri tace "Sharad'in me?"


"Zan dawo da ita amma ba yanzu ba, idan hakan ya mi ki to, in kuma bai mi ki ba to abar maganar, sannan zan dawo da ita ne ba dan ina buk'atar zamanta a gida na ba sai dan kin matsa."


Kallonta ya yi yace "Kin yarda?" Da sauri tace "Na yarda Abban Bilal, duk da haka na san ba zaka tauye hakk'in ta ba."


Daga ranar ya samu zaman lafiya Khadija ta daina mi shi magana, haka aka kwashe wasu watannin a lokacin cikin Haseenah ya shiga watan haihuwa, taje asibiti aka bata sati biyu idan bata haihu ba ta koma, a lokacin Khadija da Hajia da Usman da malam suka je gidan su Haseenah biko, abun ya bawa Haseenah kunya sosai ta yanda ta dinga kuka ta na neman gafarar Usman da Khadija, nan iyayen ta ma suka basu hak'uri kafin aka k'ara mata fad'a da nasiha, Khadija da kanta ta tayata had'a kaya dan da tace ma su bari har gobe Khadija tace a'a, tsaf suka had'a kayan suka fito tare da ciki kowace ta na turawa, kayan Usman ya karb'a ya kai mota kafin suka tafi, gida ma saida malam ya sake mu su jan kunne tare da tunatarwa akan zaman aure ibada ne kafin Usman ya mayar da su gida, suna fita Haseenah ta sake fashewa da kuka ta rik'e k'afar Khadija tace "Aunty Khadija ki yi hak'uri ki yafe min dan Allah, wallahi na yi nadamar abin da na aikata."


Kamata Khadija ta yi tace "Haseenah na fad'a mi ki ba komai wallahi, na hak'ura har abada kuma, Allah dai ya k'ara had'a kan mu."


Bilal ne ya fito daga d'aki da riga a hannu ya mik'owa Khadija yace "Mummy taimaka saka min rigar nan, wuyanta matse ni yake."


Da sauri Haseenah ta tara mi shi hannu tace "Kawo na saka ma ka yarima." Bata ya yi ya na kallon mummyn shi a d'ard'ar ya matsa kusa da ita, saida ta saka mi shi ta kalle shi tace "Yarima ka yi hak'uri ka yafewa auntynka kaji, na yi nadamar abin da na yi."


Kallon mummyn shi ya sake yi ta sakar mi shi murmushi hakan ya sa ya rumgume Haseenah yace "Aunty amarya, uwa fa ba ta neman yafiyar 'ya'yan ta."


Kallon shi ta yi tace "To in dai uwa ce ni ai ba aunty ya kamata ka kira ni ba."


Murmushi ya yi sosai ya kalle ta da kunya yace "Mummy." Har zuciya Haseenah taji muryar Bilal ya kira ta da sunan uwa, rumgume shi ta yi take taji wata soyayyar shi ta d'arsu a zuciyar ta, sun jima nan har Usman ya shigo kafin kowa ya nufi na shi d'akin, wani irin sanyi Haseenah taji sai take ji ashe zaman lafiya da wanda Allah ya had'a ka zama da shi dad'i ne da shi, sai taji kamar yau ne aka fara kawota gidan tare da k'udurawa a ranta zata wa Khadija biyayya ko da kuwa za ta zama baiwarta ne hakan ba zai dame ta ba, har ta yi shirin kwanciya Usman ya shigo da doguwar riga yace ta same shi falon Khadija, da to ta amsa mi shi ya fice ko kallon ta baiyi ba, haka ta fito jiki a sanyaye dan tasan yanzu ba mutumcin ta Usman zai gani ba, kuma kamar yanda ya fad'a a gidansu cewa ya fa zo ne saboda Khadija ce ta matsa, to tabbas tasan dawowar nan da ta yi zaman Khadija ne za ta yi, sun samu Khadija zaune da alama su take jira, zaune ya yi kusan Khadija Haseenah kuma cike da kunya ta zauna k'asa, Khadija ce tace ta zauna sama amma tace a'a tafi jin dad'in nan, Usman ne ya gyara murya ya fara magana kamar haka.


"...

15/03/2020 à 23:06 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

           *KALLON KITSE*

            _(Ake wa rogo)_

💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



_SAMIRA HAROUNA_



*Litattafan marubuciyar*



*1* _KAUSSAR_

*2* _D'AUKAR FANSA_

*3* _BA SO BANE_

*4* _AUREN HAD'I_

*5* _SANIN MASOYI_

*6* _JIHADI_

*7* _K'ANGIN RAYUWA_

*8* _ITACE K'ADDARARMU_

*9* _KAWU NA NE_

*10* _MAATA_

*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*

_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛



🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚



```Fatan alkairi masoya```



*ALHAMDULILLAH ALA NI'IMATUL ISLAM*



_Bismillahir rahamanir rahim_



                       *40*



"Haseenah, Allah ya nufa dai akwai sauran zama tsakani na dake, ina fatan abubuwan da suka faru a baya sun koya mi ki wa'azi, Haseenah zan fad'a mi ki wata magana wacce a baya na ke fargaba da shakkun fad'a mi ki, ki yi hak'uri ko da hakan zai b'ata mi ki rai, kinga Khadija da ki ke gani?" Ya fad'a ya na nuna Khadija dake gefen shi, Haseenah dai ta baza kunne ta na saurare, d'orawa da "Ba iya matata ba ce kad'ai, rayuwa ta ce, kuma kin dawo gidan nan ne a dalilin ta, ita ta dage har saida ta ga kin dawo gidan nan, ke na tak'aice mi ki ma har saida ta kai munyi fad'a da ita ko magana ba ma yi saboda ke kawai, Haseenah dan Allah ki tsarkake zuciyarki ku zauna lafiya, Allah kuma ya bani ikon yin adalci a tsakanin ku."


Khadija ce tace "Ameen mijin mu, Abban Bilal da kuma k'annan shi ma su zuwa, mun yarda ka ci gaba da jagorancin mu har zuwa gidan aljanna, mu na da yak'inin ba za mu tab'a yin nadama saboda kai *adalin miji* ne da mu ka yi sa'ar samun shi a wannan zamanin."


Fuskar nan ta Usman kamar gonar audiga haka yake mata murmushi, saida ta kai aya yace "Allah yasa matata, Allah kuma ya sa ba zigani ki ke yi ba dan naga ki na neman fasa min kai."


Dariya ta yi sosai ta mi shi fari da ido tace "A haba dai alaji, ai kasan ba ma haka da kai, duk abin da zai fito daga baki na akan ka gaskiya ne, saima saya wani abun da na ke saboda tsaro."


Kashe mata ido ya yi ita ma kuma haka, Haseenah ta saki baki ta na kallon su, wani zafi taji ya na taso mata a zuciya tare da jin mugun kishi, amma a take ta lumshe ido ta furta a ranta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allah kasa na fi k'arfin zuciya ta."


Ta na bud'a ido ta kalle su sai taji sanyi tare da jin sauk'in abin da ke ran ta, murmushi ta yi ta na ci gaba da kallon su ta ayyana a ranta in har ta na son zama da Usman dole ta girmama matar shi, sannan ya zama dole ta iya zama da su ta durmiya cikin rayuwar da suke, da k'yar ta mik'e tsaye saboda nauyin da ta yi tace "To sarakan soyayya, ni zan shiga na kwanta, kunsa fa na yi kewar gado na."


Ba Khadija ba har Usman saida ya dara kafin yace "Kenan rayuwar gida babu dad'i ko?"


Turo baki ta d'anyi tace "Babu kam." Jingina ya yi a kujera yace "Dan haka sai kowace ta kama kanta ta, in ba haka ba zan dinga yanka mu ku kati ne ku na tafiya gida ku na hutu."


Kallon shi Khadija ta yi ta kalli Haseenah tace "Idan mutum ya shirya siyan abinci da kwanan kad'aici to ai ko yanzu a shirye muke, dan idan zamu shekara  gida ma kaga lafiya lau mu ke kum hankali kwance."


Haseenah ce ta juy tace "Saida safen ku aunty." Da murmushi tace "Allah tashe mu lafiya."


Mik'ewa Usman ya yi yace "Bara na raka ki mai ciki, kar ki je ki zame." Hannun ta ya kama har suk isa falon ta, suna shiga ya saki hannunta har ta shiga uwar d'aka ta kwanta, juyawa ya yi zai fita yace "Ina zuwa."


D'akin Khadija ya je ya mata saida safe kafin ya koma d'akin Haseenah, sam bai wani sakar mata fuska ba har bacci ya d'auke su, dan har ga Allah har yanzu ya na jin haushin ta idan ya tuna baya, kawai babu yanda zaiyi ne Khadija ta tilasta mata ya dawo da ita, kuma tunda ya dawo da ita dole ya sauke hakk'ok'in ta ko kuma ya had'u da fushin ubangiji, Haseenah kuma sam ba ta yi bacci ba saboda sabon ciwon bayan da ya taso mata, tun tana shiru ta na addu'a har ta daddab'a Usman ya farka, nan fa ya rikice saboda ba'a tab'a nak'uda a gaban shi ba, haihuwar Bilal ma baya garin, Khadija ya taso daga bacci ta taimaka mi shi, kayan haihuwar Haseenah na gida ba'a d'auko ba sai Khadija ce ta d'auko nata su ka tafi asibiti da su, saida aka karb'e ta an shiga d'akin haihuwa kad'ai Usman ya kira Hajia ya fad'a mu su, kafin Hajia ta iso Khadija ma ta fara jin bayan ta na d'aurewa tare da rik'ewar mara, a hankali taja baya ta zauna kan bancin da ke wajen, da sauri Usman ya sunkuya ya na kallon ta yace "Ya dai Nana, ko dai kema jikin ne?"


Wani iska ta furzar ta girgiza kai tace "Um um." Sake kafeta ya yi da ido yace "Kin tab'a ba komai?"


"Babu." Ta fad'a ta na huci, kallon tuhuma ya mata yace "Khadija ko dai kema a shigar da ke ciki ne?"


"Ka bar shi kawai, ba buk'ata." Ta fad'a a wahalce, "Kin tabbata?"


Da k'yar tace "Na tabbata." Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, amma dan Allah da kinji wani abu ki yi magana tun da wuri."


Komai ba tace ma sa ba har Hajia ta same su tare da malam da ya kawota, kamar dama jiran zuwan Hajia ake sai ko ga wata likita ta fito ta kalli Usman tace "Alhamdulillah ta haihu lafiya, an samu d'iya mace."


"Alhamdulillah." Suka fad'a kusan a tare, nan akayi duk abin da ya kamata wanda suke buk'ata, lokacin dare ya yi sosai Hajia tace Usman ya koma gida da Khadija ita za ta zauna wajen su, ba b'ata lokaci suka kama hanyar gida Khadija sai gyangyad'i take, kallon ta ya yi ya na murmushi yace "Hajia wane suna ki ka zab'a da za'a sawa 'yar ta ki?"


Cikin doguwar hamma tace "Ka tambayi maman ta mana, watak'ila ta na da sunan da take sha'awa ita ma."


Wani kallo ya mata yace "Ta na da wata uwa ce da ta wuce ki a duniyar nan?" Cike da kasala tace "To idan da hali a saka mata *Nana Aisha* kaga idan na haihu nan kusa nima munyi 'yan biyu kenan sai a saka mata *Humaira*."


Cikin murmushi yace "Idan kuma namiji ki ka sake sunkuto min fa." Cikin zolaya tace "Sai ka saka masa *Humair*."


"To amma..." Da sauri ta katse shi tace "Dan Allah ka rabu da ni bacci na ke ji." Dariya ya yi yace "To idan ki ka yi bacci a motar fa?"


Kai tsaye tace "Saika d'auke ni ka kwantar da ni akan gadon ka."


Wani kallo ya mata yace "Me ya sa sai a kan gado na?"


"Saboda ina so haihuwa ta same ni akan gadon." Marairaicewa ya yi yace "Yanzu ku saboda Allah haka za ku had'e min kai ku haihu lokaci d'aya, kenan dole nima sai na yi jego kamar ku."


Dariya Khadija ta dinga shek'awa har da rik'e ciki kafin tace "Ai daidai kenan, kaga kai ma sai ka nemi k'unzugu ka aje saboda tarban jinin bik'i."


Kamar zaiyi kuka yace "Allah ni dai ban yarda ba, babu wani jego da zanyi haka kawai da raina da lafiya ta, dole kisan dubarar da za ki dinga min saboda na gujewa abkawa jego."


Hararan shi ta yi tace "Saboda ni kad'ai ce ke da kai?"


Saida ya kashe mata ido yace "Amma ai ke dabance, ke kad'ai ce ki ka iyani yanda ya kamata, ke ki ka fi kowa sanin abin da na ke so da abin da na ke da buk'ata."


Ba tace komai ba har suka isa gida rabe ya bud'e mu su k'ofa suka shiga, sun samu Bilal na baccin shi kamar yanda suka bar shi, nan suka kwanta suma bacci cike da gajiya, sam Khadija ba ta yi tsammanin gari zai waye ba ta haihu ba saboda abin da take ji, amma sai gashi ta tashi cikin k'arfin jiki, tunda asuba ta had'a kyakyawan abin karin kumallo sannan ta shirya, haka Bilal ma ya shirya Usman ma kafin suka karya na su kumallo abin da basu saba ba kari tunda safiya, asibiti suka tafi sun samu iyayen Haseenah da kuma Mariya, bayan sun gaisa suke mata godiya akan kayan ta da ta bayar Haseenah ta yi aiki da su, nan Usman ya zauna kuda da Haseenah ya kalle ta yace "Mai jego wai wane suna ki ka zab'awa 'yar ta ki ne?"


Kunya ce ta kama Haseenah ta rufe fuska da hijabi, dariya ya yi yace "Ki fad'a mana, dan ni zan iya saka mi ki sunan tsofaffi kamar sunan su Hajia."


Hajia ce tace "Sunan na mu ne na tsofi kenan? To aiko in ka yi wasa sunan Hajiar (mahaifiyar Haseenah) za'a saka mata."


Dariya ya yi ya kalli Hajia a ran shi kuma yace "Asiya." Mahaifiyar Haseenahr ce tace "Ko kuma sunan ki ba, ai yafi nawa."


Na kuma Haseenah ce ta kalli Hajia a ran ta ita ma tace "Allah ya sa kar ya sawa 'yata sunan mahaifiyar shi, *Hawa'u* ai sunan da ne."


Jin dai su na ta cecekuce ya sa tace "Kawai tambayi mahaifiyar ta wane suna ta ke so?" Ta fad'a da nuna Khadija, kallon ta Khadija ta yi tace "Ni kuma?"


"K'warai aunty Khadija, babu wanda ya dace ya saka mata suna bayan ke, a sanadiyar ki ta samu gatan da aka haifeta gidan mahaifin ta, dan haka kawai ki zab'a mata sunan da ya mi ki."


Murmushi Khadija ta yi tace "To shikenan a saka mata Aisha, sai ku tayani addu'a Allah ya sa na haifi mace sai a saka mata Humaira, kunga sun zama 'yan biyu kenan, Aisha da Humaira."


Kowa ya ji dad'in abin da ya faru, haka aka sawa yarinya Aisha tare da sa mata albarka, su kuma aka bisu da addu'a k'ara had'a kan su, nan Usman ya wuce da Bilal makaranta, zuwa k'arfe takwas ko da aka kama aiki aka sallame su, amma ba su bar asibitin ba har sai kusan k'arfe tara kafin Usman ya aiko Bilyamin ya d'auke su, tunda Bilal ya dawo ya ke b'angaren Haseenah ya na lagudar yarinyar, wani iko na ubangiji sai yarinyar ta yi kama da Bilal d'in kamar ciki d'aya suka fito, duk mutanen da ke zuwa wajen Bilal bai bar wajen ba, Khadija ta yi mamaki sosai yaron da ba ya son hayaniya da taron jama'a, amma sai gashi ya wuni zigidir wajen Haseenah har saida yamma lokacin islamiyya ya yi kad'ai ya bar wajen.


Sosai yan uwan Khadija da abokan ta suka mata kara wajen zuwa yi wa Haseenah barka, sai dai Hajia Turai ta rantse ta maya kan ba za ta zo ba sai in Khadija ta haihu, to fa ranar za ta zo gidan ko me zai faru sai dai ya faru, a lokacin kuma Khadija ta nemi da Usman ya mata izini taje ta dawo da Uwani ko dan aikin da ke tunkaro su ta na buk'atar mai taimako, ba musu ya mata izini ta tafi tare da Bilal, ba ta sha wahalar shawo kan su ba saboda dama ba laifin ta bane, nan suka dawo tare da su aka d'ora daga in da aka tsaya.


Sosai Khadija ke kama girmanta wajen ganin ta sauke nauyin da Usman ya d'ora mata, kowace safiya kafin Haseenah ta fito daga wanka za ta samu abin karyawarta yana jiran ta, da rana kuma idan su Mariya su ka zo tare suke aikin rana cikin raha da annashuwa, haka za su dinga cewa ta zauna ta huta za su yi amma sai tace a'a, haka suke girkin rana da na dare tare, kuma sosai suke k'aruwa wajen koyan girkin, dan kwana uku da akayi da haihuwar kullum akwai abin da ake girkawa, a haka aka shiga kwana na hud'u, a lokacin sosai Khadija take jin jikin ta fa ba dad'i amma ta na daurewa ne, yau dai ko da suka gama girkin rana ta shiga d'akin ta ba ta fito ba, saida Uwani taga abin ya fara tsananta ta fito ta nemi taimakon mutane dan su tafi asibiti, Hassana da su Rabi'a na gidan a lokacin su ka taho dan ganin lafiya, d'aki suka same ta kwance sai nishi take ta na ware k'afafun ta saboda tasan haihuwarta kusa take, nan suka duk'ufa aka taimaka mata, leda aka shinfid'a akan gadon suka fara karb'ar haihuwa, ai kuwa ba jimawa sai kan yarinya ya lek'o duniya, suna k'arasa jawo ta sai ta fashe da kukan da ya sa Usman da ya taho hankali tashe lokacin da Bilal ya kira shi ya tsaya cak, rufe fuska ya yi kafin ya bud'e ya na dariya mai kama da kuka, d'aukar Bilal ya yi ya na juyawa da shi cikin farin ciki.


Nan su Hassana su ka fito da yarinyar suka bashi ya karb'a, ya na kallon ta ya ji wata muguwar k'aunar yarinyar saboda sak Khadija ya ke ganin fuskarta, yan uwa fad'an irin bidirin da ake ma b'ata lokaci ne, Khadija dai ga farin jinin mutane gashi haihuwar ta zama biyu, hakan ya sa kullum gidan kamar ranar ake biki, kuma an mayar da bikin rana d'aya ma'ana ranar da Khadija ta haihu,  a k'alla mutanen da ke zuwa gidan basa irguwa kuma mafi aksari mutanen Khadija ne, shirye shirye ake sosai in da k'awayen Khadija su ka yi anko har kala biyar saboda farin ciki, kuma babu wanda Usman baiwa Khadija da Haseenah ba, dan ma Khadija ta yi wa kan ta dayawa da bai sani ba, a lokacin kuma Khadija ta tuna da ranar bikin ya yi daidai da zagayowar ranar haihuwar Usman, wanda shekarun su ka kama *arba'in da biyar*, dan haka ta fad'awa k'awayen ta su kaltume cewa ta na so ta mi shi bazata, nan aka fara wani sabon shirin dan bashi mamaki, in da ba kowa ya sani ba daga yan uwan Usman maza da mata, sai yan uwan Khadija da na Haseenah, sai kuma abokan Usman d'in wanda aka gayyata.


*Rana bata k'arya* sai dai uwar d'iya ta ji kunya, yau akayi suna kuma yara sun ci sunan da uwarsu ta zab'a musu wato *Aisha* da *Humaira*, duk girman gidan Usman sai gashi ya kasa d'aukar  mutanen da ke wajen har saida aka had'a da wasu runfa har biyu a k'ofar gida, duk wanda ya zo sai yace masha Allah saboda taron jama'ar, kuma kashi uku a cikin hud'u duk na Khadija ne, ita ma kuma hakan ya faru ne sakamakon jimawa da tayi ba ta haihu ba, Usman yayi iya k'ok'arin shi wajen samarwa mutanen abinci da abin sha, inda aka yanka manyan shanu har guda biyu, a b'angaren Khadija kuma shiga kawai take ta na sakewa, duk da Usman ya musu d'inki iri d'aya kuma yawa d'aya amma saida kaltume da Hajia Turai suka sake mata wani d'inki, ita kanta ba ta sani ba sai ana gobe bikin kad'ai suka kawo mata su, yawan taron jama'a ya sa muryar Khadija  dishewa ta shak'e ba'a ji saidai ta d'aga hannu kawai.


B'angare d'aya kuma su Kaltume na sama suna gyara wajen da za'a gabatar da walimar dare wacce su ka shirya ma Usee, a haka har dare ya riske su lokacin mutane sun watse sai masu aiki da aka samu suna share gidan, nan fa aka sake sabon shiri in da Khadija ta sake d'aukar wata sabuwar kwalliya wacce ta ci kud'i sosai, Aisha da Humaira ma shiryasu akayi cikin kaya iri d'aya kuma kalar na iyayen su da Bilal, Haseenah da Khadija ma cikin wanda Usman ya d'inka mu su suka saka kala d'aya, nan suka kira Usman a waya wai ya zo gida ba lafiya, a gigice ya tambayi me ya faru? Sai kawai su ka kashe wayar suna dariya, Usman dama walima ya yi sosai shima haka ya tsallako abokan shi ya taho gidan a sukwane, d'akin shi ya nufa ya na shiga ya same su zaune sai hira suke, matsowa ya yi ya na fad'in "Lafiya? me ya faru ne?"


Tare su ka taso Haseenah na cire mi shi hula Khadija kuma riga tace "Ba komai, wanka za ka yi ka yi sabuwar kwalliya."


Duka da mamaki ya kalle su yace "Kwalliya kuma, kamar wata mace? Kwalliyar me?"


Khadija ce ta d'ora mi shi hannu a yatsa tace "Shiiiii, ba magana."


Iska ya furzar yace "Wallahi kun d'auki alhaki na, haka kawai kun tayar min da hankali."


Kallon shi Khadija ta yi cike da shagwab'a tace "Ka yafe mana to." Turo baki ya yi gaba yace "Na k'i d'in."


B'ata rai ta yi ta tisa k'eyar shi ta kalli Haseenah tace "Shiga da shi ciki ki wanke min shi tas, kafin ku fito zan fito mi shi da kaya."


Ba musu suka shiga ban d'aki ta taya shi wanka, ita kuma kaya ta fito mi shi da su kalar na su sai dai ba iri d'aya ba, haka suka fito suka shirya shi kamar wani sarki ko kuma yaro, tsaf su ka yi da su kafin suka fito dan hallara wajen taron wanda a wannan lokacin ya samu halartar manyan bak'in da aka gayyata har daga mak'ota *nigeria* ma, Humaira na hannun Aishatu in da Aisha ke hannun Mariya, haka suka haura sama cikin shiga ta alfarma gwanin birgewa, sai lokacin Usman ya saki baki ya na kallon ikon Allah, tuni hankalin shi ya koma kan wani rubutu da akayi da manyan bak'i aka saka *HAPPY BIRHTDAY GARKUWAR MU*, sunkuyawa ya yi wajen Khadija yace "Aikin ki ne ko?"


Ita ma matso da kanta ta yi tace "Ba ruwa na ni, nima gani kawai na yi."


Tun kafin su isa wajen zamansu Khadija ta hango manyan bak'in da ta gayyata, nima dai baza ido na yi sosai saboda ganin wurin ya cika da mazan hajiyoyi sosai, mamaki ne ya kamani ganin wasu manyan mutane a gefe, haba ai saina bar bin bayan su Khadija na tafi da sauri wani tebur, domin tabbatarwa kaina da gaskiyar abin da na ke gani yasa na k'arasa na tsaya na ce " *Kaussar*." (jarumar littafin *Kaussar*).


Ai kam da sauri ta juyo ta kalle ni, da farin ciki ta mik'e tsaye ta rumgume ni tace "Aunty Meera, ke ce? Me kika zo yi anan?"


Kafin na yi magana daga bayan Kaussar aka ce "Me fa ta zo yi daya wuce d'aukar shegen rahoton nan nata da ta saba yi na jaraba, ko gajiya ba ta yi ta na bi gida-gida ta na wa ma'aurata bin k'wak'waffi."


Wa zan gani in ba *Ahmad* ba, k'ara waro ido na yi saboda ganin ya k'ara k'iba, sai dai ya k'ara haske sosai abinka ga jan buzu kuma balarabe, sai uban k'asumbar nan sai walk'iya take bak'i k'irin, tab'e baki na yi na dalla mi shi harara na ce "Can ta matse ma ka dai, kuma in da ba na d'auko labarin ai da ban d'auko na ku ba."


Shima cikin hararan ta yace "To kin d'auka gata ne ki ka mana, bayan kin gama kalle min mata."


Sama da k'asa na harare shi na ce "Ikon Allah." Kallon Kaussar na yi na ce "Wai yaushe bagwarin mijin nan naki ma ya iya haussa ne haka?"


Dariya Kaussar ta yi ta koma ta zauna kafin tace wani abu yace "Ranar da ki ka zaunar da ni ki ka koya min."


Nuna shi na yi da hannu na ce "Allah ka kiyaye ni ko na sa a k'wace matar ta ka sannan ka koma inda ka fito."


Dariya ya yi wacce ta k'ara bayyanar da tsantsar kyawun shi yace "Bismillah idan kin isa, ke ki na ganin kin isa ki datse wannan auren? To yanzu haka yaro ta baro gida wanda take bawa nono, kinga kuwa ni da ita ba rabuwa sai mutuwa."


Sama da k'asa na sake hararan shi na yi gaba ina kallon Kaussar na ce "Za mu yi magana idan mijin nan na ki ya yi bacci."


Da dariya ya bini da kallo ya na fad'in "Sakaran ina ne ni zanyi bacci a wannan taron, bayan akwai irin su *Najib* (jarumin littafin *D'aukar fansa*)a wurin nan."


Da sauri Kaussar ta rufe mi shi baki saboda su na kusa da su Najib, ni kuma sake ware ido na yi dan naga ina ya ke, ai kam baifi tako hud'u ba na iso ga teburin shi, kallon shi na ke sosai tare da kyawawan matan da su ka saka shi tsakiya su biyu, da murmushi a fuska na ce "Alhaji Najib barka da dare."


Wani mummunan fad'uwa gaba na ya yi saboda kallon da ya watso min kamar kumurci, d'auke kan shi ya yi k'ala baice min ba dan haka na kalli *zarah* na ce "My Zarah sannu ko?"


Da murmushi sosai tace "Sannu aunty Meera, ya ki ke? Me ki ke anan? Ke ma aunty Khadija ta gayyace ki ne?"


"Eh...t..." Ban k'arasa ba Najib yace "Har sai kin tambaye ta me ta ke anan? Gulma mana ta kawo ta, ko kin manta anyi drima a gidan Usee watannin baya da su ka wuce?"


Murmushi kawai Zarah ta yi sai *Yasmine* da tace "Ko da gulma ce ta kawo ta ai kam ta yi anfani, dan nasan akwai dayawa masu irin halin Haseenah wanda za su gyara."


Kashe mata ido na yi na ce "Da kyau tawaje na kin gane, ba zan tsaya b'ata lokaci da wannan mijin na ku ba mai k'aton ciki kamar kun aza mi shi randa."


Da k'arfi ya juyo zaiyi magana Zarah ta rik'e tace "Haba beby ya isa mana, rabu da ita dan Allah."


K'wafa ya yi ya zauna ya na huci, ni kam ko a jiki na sai ma gaba da na yi na bar shi da masifar shi,  kamar daga sama na ji na yi karo da k'afar wani, da sauri naja baya ina fad'in "Ayyah sannu ko, yi hak'uri dan Allah ban..."


Bai k'arasa ba saboda ganin *Saif* (jarumin littafin *Ba so bane*) sai dokan uban murmushi yake ya na kallo na, ajiyar zuciya na sauke dan nasan ba matsala, da dai sauran mazan hajjajan ne da ban san me zai faru ba, kafin ya yi magana *Zeinab* tace "Lah aunty Meera ke ce? Me ki ke anan?"


Izuwa yanzu kam na fara gajiya wannan tambayar da kowa ke min ta me ya kawo ni, amma sai na dake na ce "Ni ma na zo bikin Khadija ne."


Da wannan murmushi Saif yace "Ko kuma suma idon ki ka saka mu su ba kamar yanda ki ke wa kowa."


Kallon shi na yi na ce "Haba Saif ya za ka ce haka, kaine fa na ke gani mai hankali a cikin sauran."


Waro ido ya yi yace "Au! Wai ki na nufin sauran duk mahaukata ne?"


Kau da kai na yi na ce "Ka ga ni dai bance ba kar ka ja min sharri."


Juyawa ya yi bayan shi yace " Bara na ga ina zanga aboki na na fad'a mi shi kin ce mahaukata ne su."


Da sauri na bar wajen ina fad'in "Shi ma dai ya lalace kamar sauran, nasan kuma ba zai rasa nasaba da wannan bigaggen *Salman* (jarumin littafin *Auren had'i*) d'..."


Ai dole naja birki domin kuwa karo na yi da Salman d'in, wani kallo ya min yace "Ni ne ma bigaggen?"


Murmushin dole na yi na ce "Ah haba dai, ni na isa na kira ka da bigagge, dama da Saif na ke."


Dafe k'irji ya yi yace "Abokin nawa ne bigagge kenan?"


Zanyi magana naji andafa ni ta baya ance "Aunty Meranmu dan Allah rabu da su, wahalar da ke kawai za su yi."


Baki na.saki saboda ganin *Ummi* ta zama wata babba kuma hamshak'iyar mace, kallon Salman na yi a raina ina raya koya yake ya na iya d'aukar ta ma yanzu? Hum, kallon ta na yi na ce "Ummi na ina 'yan biyu?"


Da murmushi a fuskarta tace "Yan biyu su na wajen su lamama, amma ya na gan ki anan? Me ki ke yi?"


Salman ne ya juya ya zauna kan kujerar da suka tashi ya na fad'in "Me fa zai kawota da ya wuce d'aukar rahoton da ta saba, ta na nan kullum ta k'i canzawa sai tsukewa take, Allah ya sa wayar taki ta fad'i sai mu ga ta tsiya."


Wata dariyar rainin hankali na mi shi na ce "Ka ji malam Salmanu, wato so ka ke na zuma b'ukekiya kamar matar ka, to ni mijina ba ya buk'atar na yi k'iba haka yake son gani na, sannan da ka ke fatan wayata ta fad'i to in fad'a ma ka ta na fad'uwa wallahi sai ka biya ni, in kuma ba haka ba zansa Ummi ta ma bore har sai an sake ma ka tiyata, ai dai ka gane tiyatar da na ke nufi ko?"


Ta fad'a ta na kashe mi shi ido d'aya, baki ya saki ya na kallo na har na wuce na bar shi, saida na b'acewa ganin shi ya kalli Ummi yace "Kuma ke sai kiyi idan ta saki?"


Cike da tabbatarwa tace "Sosai kuwa, me zai hana ni?" Gyad'a kai kawai ya yi ya cije leb'en k'asa, har na wuce na yi saurin dawowa baya cike da tsoro, murza ido na yi ina so na ga wai tabbas shine wanda na ke zato ko kuma dai gizo ne, da mamaki na ce " *Abbas* (jarumin littafin *Sanin masoyi*), ai kam da sauri ya juyo, amma abun mamaki ya na gani na saiya had'e rai ya sake juya min baya, har zan shiga tunanin dalilin da ya sa ya min haka sai kawai na ji andafa ni, juyowa na yi sai kuwa na ga takwarata, cike da farin ciki mu ka rumgume juna ta na fad'in "Takwarata me ki ke anan?"


Raba jikina na yi da nata na sake kallonta ta yi kyau sosai, murmushi na yi na ce "Na zo biki ne ni ma."


Tsaki naji Abbas yaja hakan ya sa mu ka kalle shi a tare, *Sameera* ce tace "Jarumi na lafiya ka ke tsaki?"


Da k'yar yake maganar saboda miskilanci yace "Kinsan ba na son hayaniya, wannan kuma ta tsaya min a kai ta na zuba kamar 'ya'yan kurna."


Tabbas raina ya b'ace yanda Abbas ya nuna ni kamar ya nuna kashi, tab'e baki na yi na ce "Da ace banga lokacin da ka ke wa takwarata 'yar murya ba da sai ka zare min ido, amma tunda har na ga komai to magana ta k'are, wannan shan kunun duk birga ce wallahi."


Kallon Sameera na yi na ce "Takwara idan kun koma gida lafiya ki gaishe min da su Bashir da su Abba da Mama." Da murmushi a fuskar ta tace "Za su ji aunty Meera."


Har zan wuce na ji Abbas yace "Ta na nan har yanzu yanda take kamar za ta fad'i ta na fama da bibiyar rayuwar mutane."


Wucewa na yi na barshi da takwarata tace mi shi "Ba fa na son haka uban yara, duk abin da za ka fad'a mata kamar ni ka ke fad'awa."


Wani kallo kawai ya bita da shi kamar zaiyi bacci, ni kam ina barin nan na shiga neman mutuniya ta, ai kam bansha wahalar ganin ta ba, da gudu na k'arasa na rumgumeta ta baya ina fad'in "Ohhh, my Hajiata."


D'ago kai ta yi ta kalle ni tace "Lah! aunty Meera, ke ce anan? Me ki ka zo yi wurin nan?"


Saida na taushe zuciya ta kafin na ce wani abu *Umar Faruk* (jarumin littafin *Jihadi*) ya fizgoni na yi baya ya na fad'in " Dallah malam sake ta, me ye haka kin wani zo sai kin karya ta."


Ba dan Umar ne ba da sai na mi shi rashin mutumci, amma saina k'yale na ce "To cinye ta zanyi da ka wani taso min haka?"


A tsaurare yace "Ki yi baya ki daina tab'a jikin matata shine kawai abin da na sani."


Rik'e hab'a na yi na ce "Ikon Allah, beby mijin beby, wato wai kai mai kishi ko? To Allah ya kyauta."


"Ya ma kyauta." Ya fad'a ya na kallo na, *Khairat* na kalla na ce "Hajiata ina *Zubaida* ne? kinsan fa fan's sunyi kewarta."


Murmushi ta yi tace "Ta na gida bata jin dad'i ne, kuma ga tsohon ciki da ke jikinta, shi ya sa ta zauna gida tunda tafiya ce mai nisa."


Juyawa na yi na kalli Umar ina dariya, shi kam sai ya had'e rai ya na harare na, saida na fara takawa na ce "Lallai Umar ba dama, wato har yanzu ka na nan ka na tsula tsiyarka, daga wannan ta sauke wannan za ta d'auka, humm."


Juyawa na yi zan wa Khairat magana amma sai Umar ya ciro takalman shi zai jefe ni, da gudu na bar wajen ina dariyar mugunta, kujera na samu na zauna ina sauke numfashi kamar saukar aradu daga gefena aka ce "Aunty Meera ya ki ke?"


Da murmushi na juyo dan na gane mai muryar, da farin ciki na d'aga mu su hannu na ce " *Falmata* (d'aya daga jaruman littafin *Itace k'addarar mu*), lafiya lau, ya ki ke kema?"


"Lafiya lau, me ki ke anan?" Saida na b'ata rai na ce "Abin da ki ke yi."


*Adam* ne yace "Daga tambayar arzik'i malama sai abu ya zama na tsiya."


Hararan shi na yi na ce "Kai ni rufe min baki dallah ban sa da kai ba."


"Ke ni ki ke fad'awa haka?" Ya fad'a a hassale, ni ma a hassalen na fad'a "Eh anyi d'in, me za ka yi?"


Tasowa ya yi ya nufo kaina amma ban gusa daga in da na ke ba, saida ya tsaya gaba na ya nuna ni da yatsa zaiyi magana na ga an rik'e hannunshi daga baya ance "Haba kai kuwa Adam, aunty Meera ce fa, ba ka gae ta bane?"


Sai lokacin na ga mai magana ashe *Marwan* (jarumin littafin *Kawu na ne*) ne, huci ya yi ya sauke hannun shi ya koma mazaunin shi, har ya zauna a kalli Falmata na ce "Fati wai ina d'an uwan ku mahaukaci?"


Cike da jimami tace "Ki bari kawai aunty Meera, har yanzu ya na can babu sauk'i, wallahi duk ya sauya ya zama mahaukacin gaske."


Tab'e baki na yi karo na farko da na ce "Allah ya yaye mi shi, *Fadjimata* kuma Allah ya mata rahama."


"Ameen." Ta fad'a ta na mayar da kallonta gaban ta, sai lokacin na kalli Marwan na ce "Marwan ina aunty na take?"


Da yatsa kawai ya min ishara zuwa bayana, ina juyawa na ga *Wafa'atu* bayana da tulelen cikinta masha Allah, da farin ciki na mik'e na rumgume ta na ce "Aunty Wafa'atu ashe Allah ya nufa."


Ita ma da farin ciki tace " allah ya nufa Meera, addu'ar ki data fan's d'in ki ta same mu har inda muke, gashi yanzu Allah ya sa nima ina d'auke da cikin wata bakwai."


"Kai to Allah ya raba lafiya aunty wafa'atu."


Da "Ameen." Suka amsa su dukan su, sai lokacin Wafa'atu tace min "Amma me ki ke yi anan? Ke ma Khadija ce ta gayyace ki."


Raina ne ya b'ace da tambayar sai kawai na yi gaba na bar su tsaye, ina cikin tafiya naji anyi magana cikin shagwab'a ance "Aunty Meera shine ko ganin mu ma ba kya yi."


Juyowa na yi sai kuwa naga *Raheenat* (jarumar littafin *K'angin rayuwa*) ce, saida na gama kallon mutanen da ke tare da ita, ita da *Sameera* suna manne da juna haka ma *Abdul hakeem* da *Sadiq* suna jone sai tattaunawa suke, matsawa na yi dan mu gaisa amma Abdul hakeem sai cewa ya yi "Ke me ya kawo ki nan?"


Baki bud'e na ce "Abdul hakeem yaushe ka zama haka kuma? A sani na dai ka na da taushin zuciya."


"Sanin baya ki ka min, ai yanzu abin ba sauk'i, dan haka b'ace min da gani kafin ran ki ya b'ace." Yanda ya ke maganar ya sa na tsora ta na juya zan tafi Sameera tace "Haba takwarata, yaushe ki ka zama mai tsoro ne haka har da wannan zai tsorata ki."


Abdul hakeem ne ya kalli Sadiq yace " aboki na ka sa matar nan taka ta yi shiru kafin na fitar mata da jini a baki."


Kallon Sadiq Sameera ta yi tace "To sa na yi shiru d'in, ina jira."


Wuk'i-wuk'i Sadiq ya yi da ido kafin ya kalli Abdul yace "Aboki na ka yi hak'uri, ba zan iya ma ka komai ba gaskiya, wannan matar da ka ke gani ina tsoron bala'in ta."


Wata dariya Sameera da Raheenah su ka yi harda tapa hannu, ni kam dariya na yi na yi kafin na ce "Wai ina yara na ne?"


"Suna gida." Cewar Raheenat, juyawa na yi na ce "Sai anjiman ku."


Kallon Sadiq na yi na ce "Ka gaishe min da bazawarar nan taka."


Waro ido ya yi ya kalle ni ya kalli Sameera, tasowa yayi zai min magana sai kawai takwara ta jawo rigarshi ya koma ya zauna tace "Dan Allah ya toni asirinka shine za ka bud'e mata ido."


Abdul ne ya kalle ni yace "Kedai anyi guba wallahi, to yanzu dad'in me ki ka ji?"


Kallonshi na yi na ce "Ka mantabi guba ce lokacik da ka ke sawa ina rubuta labarin soyayyarka da sabuwar budurwarka."


Kallon shi Raheenat ta yi ,dariya na yi na wuce gaba ina ganin bala'i ya b'arke tsakanin Sadiq da Sameera, Raheenah da Abdul dan fa ita ta yarda bazawara yake nema tunda a ganinta ina bibiyar rayuwar mutane, ta teburin da Adam ke zaune na wuce nan ma cewa na yi ya gaishe da budurwar shi, a tak'aice saida na bi duka ma'auratan d'aya bayan d'aya ina hura mu su wuta, kuma babu wacce ba ta yarda ba saboda ganin ba zan fad'a mu su abinda ba haka bane, kafin ka ce me wajen taron ya fara d'aukar gumi saboda muryoyin dake tashi sama, musamman Kaussar da Khairat da Sameera ta Abbbas, sosai suka rufe ido wai ana cin amanarsu, da dai abin ya k'i sauk'i sai gashi ina niyyar sulalewa na bar wurin na ji ance "Aunty Meera barka."


Ina juyowa da sauri naga teburin cike da jaruman littafin *Aure*, da farin ciki na k'arasa muka gaisa kafin na kalli matan na ce "Ina yaran?"


*Fatima* ce tace "Suna gida aunty Meera."


Sai *Rauda* da tace "Ai sun fara wayo yanzu." Kallon Laure nayi da kanta ke k'asa duk take jin ta a takure, murmushi nayi na ce "Lauratu sarauniyar kunya, to Allah ya mayar da ku gida lafiya, ni na yi gaba wajen nan ba zai zaunu gare ni ba."


"Me ya sa?" Cewar *Iro*, kallon shi na yi kafin na ce wani abu *Siryanu* yace "Akwai bala'in data had'a tunda kaji haka."


*Imam* ne yace "Ko kuma tsokana ba, kasan Meeran mu da tsokana fa, watak'ila akwai wanda ta harzuk'a."


Ban tsaya saurarensu ba na fece ba su ma san da tafiya ta ba sai gani sukayi bana wajen.


😂😂😂😂😂


Ina shirin hawa adaidaita sahu na ji an shak'o hijabina na dawo baya, wazan gani in ba Umar faruk ba da hijabi na a hannu, Saif da Marwan sune masu sanyin ciki sune suka ce ya sake min hijabi tunda ni ma fa ba kara zube ni ke ba ina da aure, saki na ya yi amma Abbas yace "Wallahi ko kije ki fad'a mu su k'arya ki ke ko kuma mu kwana anan mu da ke."


Ahmad ne yace "Ai ba maganar mu kwana anan bane, magana ce ta muje gidanta a matsayin samarinta ma su son ta."


😂  *Ahmad ko bala'i*


Jin haka ya sa na ce su yi hak'uri mu tafi na fad'a mu su gaskiya dan ina son *beby na* ni ma, haka suka tasoni a gaba na zo na fad'a mu su kawai dan raha ne, saida magana ta fara lafawa sai kawai muryar Usman naji yace "Abokai ku taimaka ku tafar min da matar nan dan Allah, dan nima ta d'an fara damu na, sam bata bari mutum ya yi sirri da matarsa."


Murgud'a masa baki na yi na ce " To babu in da zanje sai na k'arashe labarin har k'arshe sannan."


Cikin fad'a Usman yace "To zan gani idan gidanki ne ko nawa."


"Gidanka ne amma babu in da zata je har sai ta k'arasa abin da ta fara." Cewar Khadija, turo baki yayi kamar zaiyi kuka amma bai ce komai ba, nima cewa na yi "Zan tafi yanzu dai saboda na gaji, amma zanyi sammakon zuwa gobe da safe."


Dukansu hannu suka d'aga min suna min bye bye da cewa "Saida safe Meranmu."


Haka na bar wurin cike da kewar *jarumai na* ko ba komai ina jin dad'in zama tare da su, da haka suma su ka ci gaba da walimar su har aka yanka panke dare ya yi sosai kafin Usman ya samawa kowa makwanci mai rai da lafiya ya kwanta dan huta gajiya, haka duka ma'auratan suka kwanta suna soyayyarsu dan har yanzu akwai wanda basu san sun girma ba.


*Asuba ta gari*


Daga lokacin suka fara jego cike da gata da kulawa, a yanzu idan kaga zaman na gidan Usman saiya baka mamaki, duk da har yanzu suna jin kishi amma dai ba kamar baya ba, haka suke tasa Usman gaba su dinga masa k'iriniya shi kuma yana biye musu, rayuwar ta musu dad'i yanzu kuma sun fahimci zama lafiya yafi zama d'an sarki, a haka rayuwa da lokaci ke tafiya girma na k'ara zuwa musu, Haseenah k'iba take tayi abinta saboda kwanciyar hankali da hutu, amma Khadija har yanzu tana nan yanda take bata rage ba bata k'ara ba, a haka sherau su ka je sosai har shekara *goma sha biyar*.


A wannan shekarun abubuwa da dama sun faru masu dad'i da marasa dad'i, daga ciki akwai rasuwar su malam da Hajia, haka ma mamar Khadija ta rasu sakamakon rashin lafiya, haka mahaifin Haseenah ma ya rasu sai maman su wacce tsufa yasa ko yayanta bata ganewa, da haka kusan dukansu suka zama marayu suna kuma kula da junansu sosai, abun farin ciki kuma akwai haihuwa har biyar da Haseenah ta k'ara bayan Aisha, kuma dukansu mata ne sai auta shi kad'ai ne namiji wanda ya ci sunan *Ali* amma suna kiranshi *Khalifa*, kuma wacce yake biwa ita aka wa Khadija kara aka sawa sunan mahaifiyarta *Sadiya* ita ma suna kiranta da *Nawwal*, hakama hajia an mata takwara *Hawa'u* wacce akewa alkunya da *Noor*, sannan daga ciki akwai kammala karatu da bilal ya yi a k'asar *Canada*, amma har yanzu Khadija bata sake haihuwa ba daga Humaira, amma kaf yaran Haseenah ita ke kula da su kamar ita ta haifesu, a haka Bilal ya dawo ya zama cikakken saurayi son kowa k'in wanda rasa, matashin saurayi kyakyawa kuma miskilin yaro mai d'auke da shekaru *ashirin da bakwai*, hakan yasa Usman damka duk ragamar gidan hannu Bilal, a cewar shi aure zai mi shi nan da d'an lokaci kad'an, wannan damar da Bilal ya samu tasa yake juya komai na gidan har iyayen mata, shi ya sa yanzu kullum gidan cikin hayaniya suke saboda Bilal dai baisan yawan surutu, yau ma kamar kusan kullum Aisha da Humaira ne suka shirya dan auwa bikin k'awar su, masha Allah yan matan Khadija kenan, tabbas shak'uwa dake tsakaninsu tasa har suke kama sosai ta fuska da yanayi, sai dai Humaira tafi haske sosai da dogon hanci sannan tafi cikar hallita da kumari, kayan jikinsu ma iri d'aya ne haka suka nufi d'akin Bilal dake sama dan karb'o makullin mota su bawa drebansu ya kaisu, da sallama suka tura k'ofar Humaira ce gaba.


Kwance yake ruf da ciki babu riga a jikinshi sai dogon wando dake d'aure da d'amara (belt), saida suka tsaya kanshi Humaira tace "Yah Bilal makullin mota za ka bamu mun shirya."


Shiru kamar baiji ba, Aisha ce ta kama hannun Humaira tace "Kinga mu fita wallahi bana so ya tashi ya mana tsinannan duka."


Fizge hannunta tayi tace "Ke wallahi kin cika tsoro, kawai saiya doke mu daga wannan maganar."


Kallonshi tayi ta sake cewa "Ya Bilal magana muke fa."


A hankali ya juyo tare da tashi zaune yana kallonsu, saida ya gama kallonsu yace "Ku rufe k'ofar d'akin sai ku zo ku karb'i makullin."


Kallon juna su ka yi saboda sun san me ya ke nufi da abin da ya fad'a, zare ido su ka fara yi kafin ya sake daka musu tsawa yace "Na ce ku rufe k'ofar ko."


Haba wa ai da gufu suka fita suna rige-rige, Allah ne ya saukesu k'asa lafiya basu zama ko ina ba sai falon Usman, kamar an turosu haka suka fad'a d'akin, kowace wajen ta ta uwar ta nufa wacce tasan zata tsaya mata, Humaira wajen Haseenah Aisha wajen Khadija, wata cakuma da Aisha tawa Khadija yasa d'an kwalinta fad'uwa kan kujera hakan ya bayyanar da yar furfurar dake kan ta wacce ba'a ganinta sosai ma, Khadija ce tace "Kai Aisha ho, wannan ba sai ki karyani ba, lafiya me ya faru?"


Haseenah da sai wani k'ara rumgume Humaira take ne tace "Ai da gani ba tambaya kinsan su da wannan yariman mai gida."


Khadija ce tace "Wallahi al'amarin nan ya fara isata fa, gaba d'aya yaron nan ya hana min yarinya sakewa a gida."


"Ai ba laifinshi bane, laifin wanda ya bashi muk'amin ne a gidan." Cewar Usman daya fito daga d'akin shi tare da sauran yaran sunata gurgurar chocolat, hakan ma yayi daidai da shigowar Bilal ya sanyo farar riga wacce ta kamashi, tabbas ko kad'an Bilal baiyi kama da mahaifinshi ba saboda k'irar jikinshi ma ta k'akk'arfan maza ce kusan zaka iya cewa ma kawunshi ne yayi Habeeb, saidai kyawun mahaifiyarshi da yayi kawai da manyan idanunta, belt d'in dake hannunshi ya nad'e ya yo kan Aisha zai tsala mata ta sake shigewa jikin Khadija, Khadija ce tace "Allah ka daketa sai ranka ya b'ace, kaji marar kunya kai, kai baka ji ance ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi ba."


Juyawa yayi ya kalli Humaira hakan yasa Haseenah cewa "Karma ka fara matsowa nan kaji na fad'a maka."


Usman ne yace "Yarima meya faru? Laifin me su ka yi?" Cikin b'acin rai yace "Abba nasha fad'awa yaran nan su daina shigar min d'aki idan ban musu izinin shiga ba,yanzu fa haka kawai suka suka fad'a min d'aki ina kwance ba riga a jiki na."


Khadija ce ta katse da cewa "To shine zaka dake su? Ba sai ka sake musu nasiha ba, kaji sai kace wani gudan babban mutum, yaushe ne aka daina saka maka kaya."


Usman ne yace "Koma yau ne aka daina saka mi shi ai dai an daina saka mi shi saboda ya wuce munzalin, dan haka dole ya hukuntasu tunda sun k'i su san daidai da ba daidai ba."


Kallonshi Khadija tayi ta motsa bakinta hakan yasa Usman yace "Naji ki kamani amma bayan na mik'awa yarima na wannan yaran nan na bayanku."


Wata dariya Haseenah ta yi tace "Kana ganin zaka iya k'watar su a hannun mu ne?"


Wani kallo ya mata yace "Kin manta da k'ashi d'aya ne gareni, bugu d'aya zan mu ku kuji ku a makara."


Dariya Khadija tayi tace "To ina zaka zauna kai kuma?"


"A duniya mana." Ya fad'a ya na zama kusa da su, Haseenah ce tace "Kenan ka fara soyayya a waje bamu sani ba."


Shafa kanshi yayi da ya kusan cika da furfura yace "Ai wasu kyawawan yan mata na samu suka mak'ale min wai ni suke so, kuma na yi alk'awarin aurensu, ai yarima ma zai zama waliyi na."


Dariya suka saka a tare sai Khadija da tace "Komawa baya kenan, to idan zaka je d'aurin auren dai ka shafa gawayi a kanka danka rufe wannan farin abun na kan ka."


Sake shafa kan yayi yace "Alamar arzik'i ne ai, kuma naga kema akwaita a kanki."


Cike da k'aguwa Bilal yace "wai yanzu na zo da matsalata amma ku manta kun shiga sabgar gabanku, Allah ya shirya min ku iyayena, banda kamarku a duniyar nan."


Harya juya zai fita ya tsaya ya nuna su Humaira da yatsa yace "Kuma wallahi babu inda za ku je, na gaji da wannan yawan na ku kullum."


Khadija ce tace "To ni ka ban makullin tawa motar zan fita, ai dai kasan aro ne na baka jiya ko."


Kallon Usman yayi yace "Idan sarki ya bayar da izinin fita sai ku fad'a min zan kawo mu ku."


Cike da jin dad'i Usman ya aika mishi da sumbata yace "Allah ya maka albarka yarona, shi ya sa banda matsala da gidan nan ko bana nan nasan akwai original Usman a gidan, da ni ne da yanzu sun min fari da ido na basu makullan."


Fita yayi daga d'akin sai Usman daya kalli su Aisha yace "Ku kuma ki fito daga nan munafukai kawai, dama da kinga suna raba ido kinsan basu da gaskiya, kuma wallahi ku ka sake shigar masa d'aki ba neman izini da kaina zan hukuntaku."


Cikin turo baki suka sauko suka fita daga d'akin suna kumbura, dan tunda su ka ji Bilal ya rantse sun sa babu inda za su je, suna fita Usman ya kalli tsofaffin nashi yace "Ku shirya da kyau, wannan hutun na k'arshe zan had'a yaran nan da Bilal na aurar da su."


Wata sanyayyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace "Alhamdulillah, wallahi naji dad'i da wannan maganar, dan duk sanda na kalli yaran sai naji fargaba ya ziyarceni, gashi k'awayen su sun fara aure, sai kaga an fara sakawa yaranka wani tunani na daban alhalin kana tsaye kan tarbiyarsu tsawon lokaci."


Haseenah ce tace "Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, amma ka fitar musu da maza ne?"


"Eh to, a tunani na dai da zan had'a Aisha da *Kamal* (babban d'an Murtala) ne."


Humaira kuma sai a had'a ta da *Mujahid* (d'an Issoufou d'an uwan Usman), amma fa sai in basu da wanda suke so, dan ba zamu had'a su da wanda ba sa so ba tunda zamaninmu da nasu ba d'aya ba, da a lokacin yanzu ne aka mana auren da aka yi mana ni da *Dijangala* to na tabbatar ba za su zauna ba."


"Ai ko ni da ga yanzu ne aka had'a ni da kai to da babu abin da zanyi da tsoho." Cewar Khadija kafin ta d'ora da "A gaskiya dukansu sun fad'a min suna da samarinsu har shi Bilal d'in."


Kallonta Usman yayi yace "Kenan duk sun fad'a mi ki nine suka mayar bare."


Gwalo ta mi shi tace "Nifa uwa ce."


Haseenah ce tace "Aunty su wa suka fad'a mi ki suna so?"


Cike da k'asaita tace "Sirri ne tsakani na da yara na."


Tasowa Usman yayi ya bata kunnanshi yace "To fad'a min a kunne naji."


Ai kuwa rad'a mi shi tayi cewa "Bilal ya fad'a min suna soyayya ne da *Ikram* (yar Kaltume), sai Humaira tace suna soyayya da *Kamal* d'in da ka ke son had'a Aisha da shi, sai kuma Aisha tace wani yaro ne mai sunan *Jabir*, d'ane ga Alhaji Abbakar, amma kuma da wata yar matsala."


Kallonta ya yi yace "Matsalar me?" D'orawa ta yi da "Domin kuwa *Miemie* (yar Ashir) tana mutuwar son Bilal, dan har ta fad'a masa ma, kuma yace ba zai iya cewa baya sonta ba saboda tana birge shi sosai."


Dariya usman ya yi sosai kafin yace "Dan haka saiku shirya, yaronku da mata biyu zai fara insha Allah, na yarda da mazantakarshi."


_Tofa fan's wata sabuwa, ga Usman na shirin lak'abawa Bilal mata biyu a lokaci daya, tabbas akwai wasu darussa a cikin labarin rayuwar gidan Bilal, sai dai Meeranku yanzu ta zama lazy wrriter, da zan zo na kawo mu ku d'orawar shi amma ba zan iya ba saboda na gaji yasin._


*Alhamdulillah*


*Alhamdulillah*


*Alhamdulillah*


*Ina godiya ga Allah da ya nuna min na kammala littafi lafiya kamar yanda na fara, Allah ubangiji kasa a anfana da darasin dake ciki, Allah ka sa mu tsarkake zuciyoyinmu wajen yin kishi mai tsafta, duk wanda suke da abokan zama Allah ka k'ara had'a kansu, wanda basu da kuma Allah ka had'a su da na gari, Allah ka k'ara sanyaya mana zuk'atanmu.*👏👏👏



Post a Comment

0 Comments