gidan aurena hausa novels cmt

 8/6/19, 11:17 PM - Messages to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.

3/12/20, 2:41 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            1⃣

Assalamu alaikum makaranta na nadawo muku da wani labari mai dadi  tare da nisha dantarwa da fadakarwa , kuma wannan labari yafaru ne da gaske ,  agurguje dai ku biyoni cikin Shirin don jin yadda zata kasan ce ,, Amma fa ku tana de abun goge hawayen ku agefe.


Tana kwance Kan gadon ta tana bacci , mama tashi go dakin tana ke suhana ki tashi kin San karfe nawa ne kuwa? Kin manta zakije haddan asuba ne  gashi har an kusan fitowa daga masallaci.


Wuf tayi azaman tashi tare da nufan toilet don dauro alwala , mama kuma ta bar dakin , don zuwa tashan sauran yaran .


Agurguje  suhana tashirya ta wuce haddan asuban ta , tayima maman ta sallama , tana cikin tafiya ne ta hango babanta ya fito masallaci  take anan taji gabanta ya  fadi. 


Tazo dab dashi tace baba Ina kwana ya amsa mata da lfy kawai cikin daure fuska inda sabo , ta Saba da halin nasa.


Ta karasa masallaci da suke haddan su, bayan sungama karatu ne , suka fito su uku , Aisha ummi   suhana dayake duk makotan juna ne!!! Aisha ne tace suhana ban baki labari ba , jiya munje   kasuwa nida ummi , Naga kalan dream man din ki  , sai kin gansa  kyakkyawan guy.


Suhana kai haba tawan wlh kuwa, Ina ganin sa ke Kika fado min arai don kalan mijin da kike burin son aura ne.


Suhana tace wayyo ni hafsat suhana Ina  ma Ina wajen, ummi dake gefen su taja tsaki kudai kunshiga uku iskancin naku yakai har ahanyar islamiyama sai kunyi maganar saurayi kuma ma da asuba ,!! To Allah ya shiryeku nikam kunga shigewa ta gida don idan na biye muku , ladan nawa zai tafi abanxa.


Suhana tace kai um kafin takara sa Kiran sunan ummin har tashige gda , Aisha tace kyaleta Dan Allah kin San ustazsncinta ya cika yawa!!!


Suhana tace Aisha nidai arayuwata bani da burin da ya wuce Allah ya bani miji nagari mai Sona tsakani da Allah , kuma fari kyakkyawa mai hanci da idanuwa mai saje mai Dan jiki kadan , indai Allah y bani wannan  , nikam na more arayuwa.


Aisha tayi dariya tace kai suhana ke dai akwaiki da son farin namiji kyakkyawa , baza ki gane bane Aisha , !!!! Aisha tace Allah ya baki, suhana tace amin kawata, kinga bara nashige gda kafin baba ya fito nemana!!!! To sai anjima idan mun hadu a islamiyan yamma "tom.



Yau saura kwana biyu afara azumi , baban su suhana ne yayi musu siyayyan kayan axumi,  yace wa maman suhana za adinga kai nono da kosai sadaqa masallaci dab da Shan ruwa,!!! Suhana da zainab su zasu dinga kaiwa , tace to alhaji.


Yau ankai azumi biyar kuma anfara sallan ( asham) Aisha da ummi ne suka biyo ma suhana , bayan sun gaida mamanta ita kuma ta fito suka tafi.


A hanyar ta tafiya masallaci suhana tace kun San ba karamin jin dadi nayi na zuwan axumin nan ba, ummi tace kai haba wlh , don musamman Zan  Roka Allah da yabani kalan mijin Dana keso,, Aisha tayi dariya tace oh ni indo.


Yanxu suhana  abin naki ya kai da haka , ummi tace kin San ta fara zarewa ne, aikam Naga alama, suhana tace zaku Sha mamaki kuxuba ido ku gani , saima ankai goman karshe   zakuga yadda ake addu'a a tahajjut ,!!! To Allah ya cika Miki burinki tace amin.


Akwana atashi har ankai goman karshe , suhana kullum cikin rokan Allah take daya cika mata burinta Akan mijin aurenta .


Yau da safe bayan sun dawo daga haddan asuba taga kakar Aisha tafito di ban ruwa , sai kuma takasa daukan bukatin , suhana tayi saurin Kara sawa wajenta tana sannu  mama bara na kai Miki gda, tace nagode yarnan.


Suhana ta kai mata ruwan har cikin gda kakar Aisha tace Allah ya saka Miki da alkhairi Allah ya baki miji nagari , suhana tace mama kice Allah y bani miji mai kyanki , tana fadi tana dariya .


Kakar Aisha tayi dariya lallai Yar nan kina da barkwanci, , suhana tace Allah mama da gaske nake , Ina son namiji mai kyau, kakar Aisha tayi dariya tace kodai in baki jika nane Dan larabawa,!!!  Suhana tace wane ni kaka duk Sona da namiji kyakkyawa bazan auri Dan larabawa ba yafi karfina!!! Daidai lokacin daya daga cikin jikokin kaka ya leko ta window don yaga dawa kakar sa ke hira haka har tana dariya.


Idon shine yayi arba da hafsat suhana, yayi saurin kauda kanshi , suhana ma haka , tace kaka kinga natafi gda , to yarnan nagode.


Yau su suhana sun kawo nono masallaci , sai ga jikan kaka yazo shi da abokin sa, abokin sa yace laisu bara na karbo Mana nonon nan Yana da dadi sosai, don na sanka da son nono.


Tare suka karasa wajan suhana babangida ya karba musu , suhana tayi ido hudu da laisu take kirjin ta ya fara bugawa, laisu kura mata manyan idanunsa yayi.



*Kubiyoni* *agaba* *don* *jin* *mezai* *faru*


TAKU HAR KULLUM (UMMU RUMAN) 

Wacce akafi sani da *NUSNIM*

08064481931

3/12/20, 2:41 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

                2⃣

Laisu kura mata manyan idanun sa yayi , Yana so ya tuno aina yataba ganin yarinyar nan, babangida ne yace muje abokina za ashiga sallah !! Sannan ya dawo daga duniyar tunani.


Bayan wuce warsu ta sauke ajiyar xuciya tace ya ilahi wannan wani kalan halittane dashi, kaga mutum da Dan Karan kyau Kamar shi yayi kansa !!! Anya kuwa Dan kasan nan ne. Tabdi nidai wannan guy din ya tafi da hankali na, dama Allah ya bani shi amatsayin mijina, wata bangaren zuciyarta yace mata kul suhana , wannan mutumin ba sa'an aurenki bane"" gaki yarinya kwaila dake,  kin San ko ya wuce tunanin ki, irin su sai manyan mata masu ji da kansu..


Ta sauki ajiyar xuciya tace alhamdulillah ala ni'imatillah.


 Laisu ne ya koma gida Yana tunanin suhana yace wannan yarinyar Kamar itace wacce  ta kawo ma kaka ruwa Gida inbai manta ba, sai yayi Dan guntun murmushi.!!!ya juye nonon  nan akofi ya farasha Yana lumshe idanun sa alamun nonon yamasa dadi, dama kalan nonon daya keso kenan.


Akwana atashi bawuya wajan Allah azumi sai tafiya yake yi, yayin da suhana Kara dantsewa wajan rokan Allah akan mijin da take so , !!! Kuma shakuwa mai karfi yashiga tsakanin ta da laisu , saboda Yana son kindirman nono,  musamman idan mamanta ta burga nonon zata kawo jug daban Wanda za asa mawa laisu nashi ,, tun mama na mita akan shi meyasa baza ya dauka Kamar yadda sauran mutane ke dauka ba?


Suhana sai tace wallahi mama kafin ya dauka mutane sun wawushe ne, shi kuma Dan gayu ne, baya sun irin abunda sauran mutane keyi, shine yace min Dan Allah indinga sama sa nashi daban," mama tace kyaji  dashi.


Yau shene jaji barin sallah , ranar da kuma za agama sallar tahajjut , daran ranar suhana tayi addu'oi ba kadan ba ,!!!  Kuma ayau ne ummi da Aisha da suhana sukaje gidan lalle.


Suna tafiya atare suhana tace hmm kawayena bara na baku labari kuji agarin kai nono masallaci na hadu da wani balaraben mutum kyakkyawan gaske har muka Saba dashi sabida Yana son kindirmo!!! Ummi tace badai cewa zakiyi kina sonshi ba ?  Suhana tace ni asuwa ai duk Sona da farin mutum wannan yafi karfina wlh , irin su sai manyan mata.


Aisha tace kidaina cewa haka Kika sani yace Yana sonki aikema kina da kyau !! Suhana tace tabdi ai duk kyauna wlh ko kwatan kwatan kamo kafar sa banyi va, , Wanda ko hammatan sa nasan tafini kyau wlh!!! Aisha da ummi suka bushe da dariya .


Aisha tace ya sunan sa , suhana tace wai  anji Kamar ana cewa ko laisi ne ko laisu ne, sunan dai da wahalan fadi irin sunan larabawan nan ne!!! Aisha tayi saurin cewa kar dai Ace Yaya laisu ne ya dawo?  Suhana ta kalle ta da mamaki , tace Yaya laisu  kuma,??  Dama kin sanshi ne?


Aisha tace kai ai Yayana ne baban mune daya dashi , Amma awajan kakar mu suka tashi  bayan rasuwan mahaifin mu " kuma shi bai cika zama agarin nan ba , Yana aiki a Abuja ne : shiyasa ba kowa yasan shi ba!!!!  Kuma inkinga Yan matan dake zuwa wajan umman mu akan ta masu hanyar samun soyayyarshi ,"" don sunga suna shiri da ita.


Suhana ta sauke ajiyar xuciya tace tabdi jam , kodai shine Wanda naganshi gdan kakar ki Randa nakai mata ruwa ?


Aisha tace to  kila shine, don kin San su hudu ne mahaifiyar su ta Haifa agidan baban mu, babban su shine abdallah sai na biyun shine nura sai na ukun shine laisu sai autan su umar , dukkan su farare ne""  su suka dauko kyan baban mu asalin larabawan kenan.


Kin San baban mu Dan libiya ne, aikine ya kawo sa Nigeria " sai ya hadu da maman su laisu , ita kuma bafulatanan katsina ce!!!  Har ya aureta suka hafi Yara hudu maxa. 


Daga baya ne ya auri mahaifiyar mu ita kuma Yar nijar ce wato buxuwa ce ,, amma irin bakaken buzayen nan ne , suma aiki ne ya kawo mahaifinta Nigeria , ya aureta ba da dadewa ba ta samu ciki ta haifi yayar mu hadiza, sai aminu sai ni Aisha sai aliyu sai kasim autanmu.


Ummi tace yanxu dama ku Yan libiya ne, shiyasa kyanki yayi yawa kice kyau da kyau ne ya haife ku"" suhana ta bushe da dariya aikuwa dai wlh , shiyasa take wa mutane wulakanci don taga tana da kyau , Aisha ta kaiwa suhana duka eh anji din ke kuma da Kika mutum akan auran miji mai kyau fa""" da alama da Yayana za ayi auran nan " dukkan su suka kwashe da dariya !!! Suhana tace rabani da yayanki dakyar zai soni!! Aisha tace ki daina fadin haka """ sai kiga Allah ya tabbatar da hakan'" suhana tace wlh Danafi kowa murna kuwa wallihi.


Don yayanki ya hadu sosai kuma kalan namijin Dana ke fatan aura ne "" Amma bakomai in Allah yasa zai zama mallakina shikenan.


Yau sallah su suhana ansha kyau za aje masallacin EDI tare da baban su da kannan ta, a hanyar su ta tafiya ce suka hadu da laisu yasha ado ta fitan hankali in ka gansa kace Dan gdan sarkin makka saboda tafiyan kasaitar da yakeyi  " watso mata wani kalan murmushi yayi  mai rikitar da Yan mata'' bata San lokacin da tace ya ilahi   , meke Shirin faruwa dani kar dai Ace na fada tarkon son laisu "" inko hakane na dauko ruwan dafa kaina " shiko laisu ya kura mata ido Kamar mai son karantar Abu a kwayar idanun ta !!! Da sauri ta kawar da idanun ta gefe , tayi saurin Kara sawa wajan da aka tana da don mata .


Washe garin sallah suhana Tara sa gdan wa zataje yawan sallah , gashi kawayenta ummi da Aisha sunyi tafiya !!! Kawai sai mamanta tace kishirya zamuje gdan su mama wato gdan kanwar mamanta "" aiko tare suka tafi sai dare suka Kama hanyar dawowa .


Bayan an sauke su a napep maman su tace taje ta samo canji a shagon ya kubu ta bamawa mai napep ita tashige gda!!!    


Bayan ta sallame shi  tayi hanyar gda sai kawai taji ana cewa mai nono ranta ya bace tasan da ita akeyi , taki tsayawa kawai tayi shigewar ta gda "  tashiga bada dadewa ba yaro yayi sallama yace wai ance ankiran wacce tashi"" maman suhana takalli suhana tace waya biyo ki!!! Ta zumburo baki ni wlh mama ban sani ba kawai naji ana cewa mai nono lokacin da Zan shigo gda  ni kuma naki tsayawa .


Mama tace tashi kije kiji waye kiyi saurin sallaman sa kafin baban ku ya dawo  tace to.


Tana fita tayi ido hudu da laisu da abokinsa babangida   tana kallon su da mamaki, babangida ne ya farayin magana yace afuwan Dan Allah wallahi ban San sunan ki bane shiyasa nace Miki mai nono tace ba komai " yace nagode to Dan Allah ko zamu iya sanin sunan ki"" tace sunana hafsat , Amma anfi kirana da suhana!! Lallai suna mai dadi , tace meke tafe daku bana son babana yazo ya sameni awajen nan.


Babangida yace ok dama abokina ne yace in Masa hanyar da zai ganki domin kin sace mishi zuciya  , da sauri ta dago ido takalli laisu Wanda ke jifanta da murmushi ji tayi Kamar ta nitse kasa Dan kunya "" jinta take tana yawo a sama , Kamar mafarki take"" axuciyar ta cewa take ya Allah kasa ba mafarki nake ba. 


Cikin muryansa mai dadi tace hafsat suhana ko ban Miki bane ido ta daga tana kallon sa ta kasa magana tayi saurin rufe ido da tafin hannunta.


Laisu yace suhana tun lokacin Dana fara ganinki naji araina na samu matar aure , kin  sacen xuciya ta, hafsat ki taimakeni kibani matsugunni azuciyarki wallahi dagaske sonki naki da aure Babu yaudara aciki!!! Tayi saurin dago kanta don ta gasgata maganar sa, ya daga mata gira Yana murmushi """ Zan baki lokaci kije kiyi tunani " bani number ki' tace bani dawaya """ yace ya za ayi kenan tace nima ban sani ba " tace kabani naka Zan kira ka talayin kawata idan ta dawo daga tafiya" ya zaro ido waje.


Yace haba my suhana har sai kawarki ta dawo wlh bazan iya jira ba ta kyalkyale da dariya tace haka ka kamu Ashe , gaba ki dayan su suka saka dariya"" to xankira ka talayin mamana "" ya sauke ajiyar xuciya yace yauwa ko kefa ya( badal)!!  Suhana tace to larabci zakamin " yace no ina nufin masoyiyata!!! To ni Kam Zan wuce sai kajini!!!! Yace to.


Suhana tashiga ta zayya newa mamanta komai" mamanta tace tubdi jam gashi baban ki bazai miki aure yanxu ba sai kingama jami'a , gaskiya akwai matsala Amma Allah y zaba abunda yafi alkhairi"" jikin suhana ne yayi sanyi dajin furucin mamanta """ haka ta kwana tana tunanin laisu " tace yanxu ni laisu yake so da aure !! Kenen yanxu na samu dream man Dina kenan wayyo ni suhana Allah y cikamin burina :: Allah sarki Aisha da ummi baku kusa bantala kusha labari.


Allah yasa babana ya amince ma laisu, donni wlh Babu jami'an da zanje sai na auri laisu na.


*Tirkashi* *kuna* *ganin* *burin* *suhana* *zai* *cika*


Kubiyoni agaba donjin me zai faru.


*TAKU* *ummu* *Ruman* ( *NUSNIM*)

08064481931

3/12/20, 2:42 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

                  3⃣

Bayan kwana biyu da zuwan laisu gdan su suhana ," soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su , batare da sanin kowa ba " ko mahaifiyar ta bata sani ba!!! Kawayenta Basu dawo daga tafiya ba bantala ta gaya musu "" a boye suke tadin su , inzata islamiyan yamma zai biyota ya Rakata" in zataje haddan dare ma , nan ma sai ya biyo ta su sha soyayyar su.


Duk wannan abunda sukeyi mahaifinta bai sani ba " laisu yasha ce mata tabashi dama yaje gun mahaifinta sai tace mashi a'a ya bari tukunna""' laisu yane ma suhana data dau Masa alkwarin zata aureshi bazata juya mashi baya ba , komin rintsi komin wuya suna tare.


Suhana ta amince da hakan kuma ta dauki alkwarin ," da haka zuciyar laisu yayi sanyi.


*Wacece* *suhana*


Suhana yace ga alhaji abubakar da Fatima , mahaifinta Dan asalin kano ne, yayin da mahaifiyarta Yar asalin katsina ce   , Amma suna zaune ne a kaduna  unguwar malali, su bakwai ne awajen iyayen su"" hafsat suhana itace babba sai hajara sai khalifa sai abdallah sai Yasir sai umaima sai umar' sun taso cikin so da kulawa da tarbiya , mahifin su suhana nada tsanani sosai " gashi shi mai son yaran shi suyi karatu mai zurfi, kuma yaransa boarding school sukeyi.


Hafsat suhana queen Amina tayi taga , yanxu shekaranta daya da gamawa '  yanxu haka tana jira jam dinta ya fito , don baban ta yace jami'a zata tafi na jigawa ko jahun nursing school"" suhana kyakkyawar  macece daidai gwargwado, ita ba fara ba kuma ba baka ba, tana da karamin baki, da idanuwa , tana da hanci Amma ba sosai ba  !!! Haka gashi ma tana dashi shima ba sosai ba komai nata daidai, bata cika wani kyau a fuska ba , Amma ajiki dirarriyar macece duk da karancin shekarunta , bai hanasu fitowa ba!! Kuma miskila ce."" Kuma macece mai yawan hakuri da yakana..


Kuma macece mai yawan San addini ,"" bata da ilimin boko sosai akan na islamiya"" kuma mallama ce ita!! Tana koyar da matan aure da Yara . 


Suhana tana da burin son auren nimiji fari kyakkyawa mai kyan hali Dan soyayya "" kullum cikin rokan Allah take daya bata irin wannan mijin"" sai gashi cikin ruwan sanyi Allah ya kawo mata laisu" har tamasa alkawarin aure. Wannan kenan .


Akwana atashi ba wuya awajan ubangiji , kawayen ta sun dawo da tafiyan ta labarta masu komai" Aisha tafi  kowa murnan haka"" tace lallai suhana Amma ke Yar baiwace cikin kankanin lokaci kin sace zuciyar Yayana , Allah y barku tare ' ya baku ikon cikawa junan ku alkawari!! Suka ce amin.


Ummi tace wani hanxari ba gudu ba, suhana kin San mahaifinki baya son kifara kula saurayi ko' tace eh haka ne shiyasa nace Masa ya dakata kar ya tura gdan mu yanxu!! To Allah yayi jagora.


Soyayya tayi nisa Amma mahaifin suhana bai sani ba har sunyi sheka biyu suna soyayya :: kwasam ranar wata jumma'a suhana taje kai gyaran takalmin ta shagon audu " ta tarar bayanan sai wasu samari guda biyu ' daya daga ciki yace tajirashi yanxu zai dawo !! Tace to ta zauna "' dayan saurayin ne yace Yusuf kasan Allah ni baxan iya auran macen da batayi jami'a .


Yusuf yace lallai Kam kana da aiki arayuwar ka ' wlh ba wani aiki , kasan Yan jami'a sunfi wayewa!!! Suhana ta zuba mashi ido tana kallon sa tayi murmushi :::: azuciyarta tace ai sai kaje kayi tayi .



Mai shagon na dawowa ta karba ta Karmin ta wuce. dayan saurayin mai magana ya bita da ido yace Yusuf wancan yarinyar fa ta hadu wlh.


Yusuf ya kwashe da dariya yace kai A B Y baka da dama inace kai kace baka son macen da batayi jami'a ba"" wannan yarinyar ai secondry kawai tagama !!! Kaga kuwa ba sa'arka bace,, A B Y ya furxar da huci , yace Yusuf kasan kauna "" to Inka San kauna to wlh ita tashige ni sosai yanxu!!! Ji nake bazan iya rayuwa in ban mallake wannan yarinyar ba """ Yusuf yace tabdi jam aiko indai wannan yarinyar ne sai dai ko ka mutu .


Don matar manya ce,, daya wan mutane suna son kai mata hari sunka sa sbda mahaifinta da ita kanta don bata fara'a in tafito"'' Amma mutum daya ne Naga yayi nasaran jefa soyayyanshi cikin xuciyarta wato yayan abokina laisu """ shima din soyayyan aboye akeyin sa bama kowa yasani ba.


Tabdi jam nima ko Zan gwada sa'ata wlh don Allah Ina sonta, ya sunanta Yusuf yace sunanta suhana!!! A B y yayi murmushi suna mai dadi , suhana ke tawace da yardan Allah .


Bayan kwana biyu A B Y , ya samu kawar suhana wato ummi yace mata shi Yana son kawarta sosai ta taimaka ta mashi hanya  dayake  yayan ummi abokin sa ne""" ummi tace tabdi jam gaskiya Yaya Abba inda zaka dauki shawarata da karabu da suhana " don suhana tayi nisa batajin Kira !!! Taxama makauniya akan soyayyar laisu.


A.B.Y yace nima Zan gwada sa'ata inaji ajikina zata soni ' nidai kawai ki gaya mata " tace to , yauwa nagode duk yadda kukayi sai ki gaya min "" ok .


Ummi ta samu suhana da maganar Abba "" suhana tayi murmushin takaici "" tace mutumin daya ce shi bazaiyi soyayya da Yar secondry ba sai Yar jami'a"" ko yayi zaton ni Yar jami'a ce...


Ki fada Masa ya makaro laisu na ya rigasa mallaka ta, koda laisu bai zo wajena ba, baxan kula shi ba sbd ni ba Yar jami'a bace .


Ummi ta fada mawa  Abba yayi shiru yarasa ya zaiyi , yace Amma zansan yadda zanyi .


Suhana na kwance akan gadonta tana tunanin laisun ta , ita batajin zata iya  auren wani inba laisu ba, karar Kiran wayarta ce yashigo""  dayake laisu yabata karamin waya tana rikewa awaye batare da baban ta ya sani ba, Amma mamanta ta sani.


Daukan Kiran wayar tayi tana murmushi tare da fadin amincin Allah y tabbata agare ka y habibty nah yanxu nagama tunanin ka"" kai haba gimbiyata , to y kk ya rana hope kina lfy ?lfy lau wlh kana inane haka? Ina daki Ina kallon hoton ki" suhana nakosa in mallake ki " kizamo uwar ya'yana ' gashi gdan mu ankosa aga nayi aure ki taimaka ki bani dama ingana da mahaifinki !!! Na Miki alkwarin Zaki karasa karatunki adakin auranki insha Allah "" duk ya cikata da magiya sai ya bata tausayi,, bakomai na baka izini"" Amma fa karkace ni na turo ka !!! Yayi murmushi yace haba dai ai bazan nuna ba ma kinsan ni!! Yauwa ko kaifa  Allah ya barmu tare ya *badal* amin habibty.


Laisu ya samu abokin baban suhana, dayake shima suna shiri dashi ya Masa magana Dan Allah Yana neman ixini xuwa wajen suhana kuma shi da gaske yake auranta zaiyi .


Mallam yakubu yace laisu ka debo da zafi don alhaji abubakar bai shirya aurad da yarsa ba yanxu Yana da burin tayi karatu"" Amma karka damu zanshawo kansa , kuma na maka sha'awar auran ta !!! To nagode mallam yakubu , yace bakomai.


Suhana ce ke tafiya zataje islamiya, sallama taji an mata cikin murya mai dadi ta amsa sallamar batare da ta dago idanun ta ta kalla mai sallamar ba ""  yace mallama hafsat suhana Dan Allah inba Zaki damu ba Ina son magana dake sai asan nan ta dago ido ta dubeshi " tace au dama Kaine !!! To meke tafe dakai  ya fara kame kame yarasa ta inda zai  fara don ta mashi kwarjini itako ta kura Masa ido" ta danyi murmushi mai Kara mata kyau   tace A.B.Y nasan dalilin ka na tsaidani , akan dai soyayyar ka"" a farko dai Ina baka hakuri donni ba Yar jami'a bace , sannan kuma nayi ma wani alkwarin aure kuma shine Wanda na mallaka mawa zuciya ta" Ina son laisu ba kadan ba kuma Zan iya hada soyayyar shi da wani ba" dafatan zaka min uxuri tunda kasan girman alkwari.


Takama hanya zata wuce cikin sanyin murya yace to shikenan ba damuwa Amma Ina so kimin wani alfarma daya Ina son muxama abokanan juna nida ke in ba damuwa .


Ya bata tausayi   tayi murmushi tace yes I will be your dosti" yayi dariya yace really tace yes "" yace dama are you a Indian lady !!! Ta kyalkyace da dariya  sosai ma kuwa" Ina matukar son India !!! A.B.Y yace lallai Kam munyi anko dake nima haka best film Dina kenan Indian""" suna tafiya suna hira gwanani ban sha'awa har ya Rakata islamiyan nasu.


Ya roketa tabashi number ta dakyar tabashi don bata son soyayya yashiga tsakanin su""illa kawai suyi abota .


Yau mallam yakubu ya samu baban suhana da  maganar laisu " budan bakin alhaji abubakar yace kace inhar zai iya jiranta tagama makaran ta to "" amma nikam yanxu bazan auradda suhana ba don Ina so tasamu ilimi mai zurfi yadda nangaba zata iya rike kanta da Yan uwanta " sbd koda bana raye Yan uwa ba lallai bane su taimake su, mallam yakubu yace hakane to Allah yashige Mana gaba.


Laisu yaji sakon baban suhana ya shiga damuwa sosai  ' nan ya Kira suhana ya gaya mata batasan sanda ta fashe da kuka ba"" don tanajin baza ta iya rabuwa da laisu ba cikin farad daya sonshi ya shigeta !!! Laisu yace kiyi hakuri baza mu rabu ba " karki manta alkawarin mu na nan " Zanciga ba da bibiyan babanki kuma insha allahu zai amince Mana muyi auren mu kiji matas" tayi murmushi Kamar tana gaban sa .


Baban suhana ne ya Kira mamana suhana Yana mata fada akan yaushe ta bari suhana ta fara soyayya da laisu , mama tace Babu mai xuwa wajen suhana da sunan tadi "' ke suhana daga yau na sauke fitan ki konan da kofar gda" suhana tace baba harda islamiyan ma yace eh harda islamiyan"" tafashe da wani irin kuka tare da barin wajen"" mama tace haba alhaji Dan islamiyan dake debe mata kewan zaman gdan shima kahana ta zuwa , kayi hakuri alhaji karkace zakayi mata haka kasan bata zuwa ko Ina sai islamiya!!! Dan Allah saurara  ai duk bakin ku daya kin San da tana tadi don naji a unguwa ance tare suke zuwa islamiyan acan take tadin !!! Mama tace ya subhanallah"" alhaji kar ka dauki maganar mutane ka dakushe farin cikin yarka"" suhana baza tayi haka ba''' Dan Allah dakata ya isheni """ ni yaron ne ma bana son shi kwata kwata.


Tirkashi yata kene 

Wanene mijin suhana.


*Ummu* *ruman*

*NUSNIM*

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

               4⃣

Suhana tashiga tashin hankali 'takira A.B.Y tafada Masa abaunda ake ciki " ya tasauya mata sosai ya bata shawarori akan tabi maganar mahaifinta ' in Allah y yarda zai sauko daga fushin ' kuma insha allahu Zaki auri laisu' taji sanyi sosai azuciyarta.


Bayan sun gama waya da Abba , hawaye ne ya kwararo akan idanun sa " ya dafe zuciyar shi Yana ya ilahi wannan wani kalan so nake mawa suhana Anya kuwa Zan iya hakura da ita kuwa!! Kai gaskiya sai dai mufafata nida laisu .


Awajen laisu kuwa zancen haka take awajen sa shima yashiga tashin hankali"" kuma bazai daina bibiyar suhana ba har sai taxama mallakin sa .


Mallamin su suhana yaga har anyi sati guda Babu suhana amakaranta " takanas yayi yazo gdan su donjin lafiya?


Suhana ta fito ta Masa bayani , yace zai samu mahaifinta ya basa hakuri ya barta ta dinga zuwa"" ilaiko haka ta faru daya ke baban ta najin nauyin mallamin nasu .


Suhana taci gaba da zuwa islamiyan su ' kuma kullum sa Abba ya Rakata dayake ta kofar gdan su take wuce wa " wasa wasa shukuwa tashiga tsakanin su duk Randa daya baiga daya ba baya jin dadi "" adayan bangaren kuma bata da burin daya wuce ta auri laisu.


Laisu ya dinga turawa mawa mahaifin suhana mutane masu kima " wayanda zaiji kunyar su yabashi auran yarsa"" Amma kememe alhaji abbakar yaki.


Kwasam laisu yaje wajen limamin unguwan su na jumma' a yaje ya fada masa daya temakesa yasa baki ' yace insha allahu Zan Masa magana!!! Haka limamin yasa aka Kira Masa baban suhana !!! Dakyar baban suhana yayarda yaba laisu izinin yane mi soyayyar suhana ' inta amince sai asa rana' limamin yaji dadi sosai!!!! Axuciyar alhaji abubakar cewa yake aiko bazan bashi auran yata ba kwanan nan Zan dauke ta in mai data kano tacigaba  da karantu tunda dama saura sati biyu result dinta ya fito.


Laisu dayaji labari yayi murna sosai ya fada mawa iyayen sa " shifa akai gaisuwa da kayan sa rana!!! Baban suhana ya fada mawa mahaifiyar suhana yadda sukayi da liman"" na ba laisu izinin xuwa amma jarabawanta na fitowa zan dauketa gaba daya , ba sai inya sake ganinta ba .


Maman suhana ta kade kai alamun tausaya mawa yarta don tasan suhana na son laisu sosai batajin suhana zata iya rabuwa da laisu.


Suhana da laisu suna cikin farin ciki" labarin soyayyar su ta bazu a unguwa  , dayawan mutane sunyi mamakin yadda alhaji abbakar ya bamawa laisu damar soyayya da yarsa' don ansan mutum ne mai tsanani kuma kaifi daya ' kuma Yana son yayan sa suyi karatu.


Wata sabuwa inji Yan caca shakuwa mai karfi tashiga tsakanin Abba da suhana , Wanda duk Randa daya baiga daya ba bayajin dadi!!!  Abba yaro ne Dan shekara 26 kuma Dan boko ne shi' kuma ma'abocin soyayya ne da son India shiyasa yake birge suhana"" don itama takasan ce Yar soyayya ce da son India """ yayin da shi kuma laisu awajen sa soyayya ta Yara ce don shi gani yake ya wuce wannan level din !!! Shiyasa in yazo hira gun suhana sai dai ita tayi ta suratan ta batare da yace mata uffan ba sai dai murmushi" daga baya data gane shi bai cika son maganganu irin na soyayya ba sai ta kyalesa ' sai dai suyi ta labarin Yan unguwa .


Abba Yana kula da suhana sosai tana tashi bacci da sakon sa zata fara cin karo , zai mata rubutu Kamar haka" gimbiyar mata dafatan kin tashi lafiya kinci abinci ko ' gani zaune Ina tunanin sarauniyan xuciyata ' daure kibani matsugunni koda kadan ne azuciyarki!!! Koda yaushe xuciyata na fada min hafsat suhana tawace nakasa gasgata hakan sbd xuciyar gimbiyar tana gun laisu!! Wayyo ni Allah Ashe ba tawa bace ta aro ce. Suhana bata San lokacin da ta kyalkyale da dariya ba'" tana jin dadin kalaman Abba Amma ba yadda zatayi sbd ta riga da tama laisu alkwarin.


Sau tari takance dama Abba shine keda kyan laisu ' dama Abba tafara sani' data more !! Sbd Abba ya iya tattalin mace  ya iya kalami mai dadi  wayyo ni suhana meke Shirin faruwa dani ,  Anya ban fada tarkon son Abba ba"" inko hakane ban kyauta ma laisu ba!!! Ya Allah ka kawo min dauki.


Bata gama tunanin ta ba sai ga Kiran Abba yashigo tace Dan halas kaki ambato , takara akunnan ta tare da fadin my dosti katashi lfy , yace lfy lau my dosti , dafatan dai kinci abinci ko!! Tace a'a yanxu dai zanci..


Yace kai kai gaskiya jeki ci abinci ban son kina zama da yunwa fa, kar ulcer ta kamaki duk yabi ya rude akanta "" tace karka damu insha allahu yanxu zanci ' Ina fatan kaima dai kaci abinci?


Abba yace ai bazan iya cin abinci dostina bataci ba !! Suhana tayi murmushi tace abbaty please go and eat your food" yace ok my lady " suhana tace kafara ko ' no kai na bisa wuya amaryan laisu.


Suhana tayi dariya tace my dosti baka da dama" yace Amma Ina da dosti suhana!! Tayi saurin kashe wayan don Yana son ya hargitsa mata tunani da kalaman sa!!! Kalaman sa Yana sata cikin shauki Wanda batajin hakan a wajen laisu "" ita dai tasan tana son laisu  kuma tana son auren sa' Amma ta rasa dalilin da yasa takeji wani abu akan A.B.Y.


Jarabawan su suhana ya fito ta samu jahun dake cikin garin jigawa state " ba karamin murna babanta yaji ba ' aiko nan yake fada mawa mamanta suhana ta samu makaranta a jigawa ' sannan kuma ta samu na nan kaduna wato kasu""" Amma baza tayi na kasu ba jigawa zata tafi !!!


Maman tace haba alhaji yanxu saboda baka sonta da laisu shine zaka kaita izuwa wata garin mai nisa " kar ka manta ya macece fa ba namiji ba daza ka kaita wani garin " ana son ya mace ta kasance kusa da iyayenta !! Sai aure ne kawai zai rabata dasu!!


Kuma ma menene aibun wannan yaron' Dan gdan mutunci ne fa kasan wanene shi fa " kabarshi ya aureta inyaso saita cigaba da karatun ta adakinta tunda shima yasan darajan karatu Yan gdan su sunayi!!' 


Ya isheki Fatima sai yanxu nagane kece kike hure ma hafsat kunne wato Ina tufka kina warwara to bari kiji ingaya Miki aure ne dai hafsat baxa ta auri laisu ba ' ni ne ubanta zanga Wanda zai aura mata shi. Fuuuu ya wuce '' suhana dake labe tana jinsu ' duk fuskanta ya jike da hawaye ' tanajin alamun fitowan sa tayi saurin barin wajen""" dakin su tanufa ta fada Kan gado tana kuka mai cin rai .


Mamanta ne tashigo dakin taganta tana kuka tasan taji abunda suke fada"" cikin muryan damuwa maman tace suhana hakuri zakiyi kibi umarnin mahaifin ki ' kin sanshi kaifi daya ne in yace Abu baya canxawa inba wani ikon Allah ba!!! Ki koyi cire laisu aranki kila ba alkhairi bane agareki ..



Suhana tace mama yaxanyi da raina Ina son laisu sosai mama kuma zai barni incigaba da karatuna ' Amma baba yaki"" narasa meyasa bai son laisu ' takara fashewa da kuka "" mamanta na Shafa bayanta tace kici gaba da addu'a insha allahu Allah zai kawo Miki mafita .



Bayan mamanta ta fita ta janyo wayarta ta shiga Kiran laisu ringing daya ya dauka " yace ya dai matas sai ta fashe mashi da kuka tuni hankalin sa ya tashi "" Yana suhana lfy? me ya faru? dan Allah kiyi sHiru ki gaya min meke faruwa?


Da kyar ta samu ta mishi bayani nan take jikin sa ya mutu ' da kyar ya iya hada kalmomi kina nufin yanxu daukeki baba zaiyi ya kaiki jigawa "" meyasa baba zai Mana haka "" sai da ya bari mun shaku da juna zai rabamu "" suhana wani laifi nayi wa babanki haka da bai Sona ?


Wlh nima ban sani ba bakomai mudai haka tamu kaddarar tazo Mana " to suhana lokacin rabuwan mu yaxo dama haka Allah yake Al'amarin sa  kuma matar mutum kabarin sa  . Nan takara fashewa da kuka tace laisu kana nufin karabu Dani kenan, Ina alkawarin da mukayi wa juna, komin rintsi komin wuya baxa mu rabu ba.  To suhana yakike son inyi yanxu!! Kuka ne ya kawo mai yayi saurin kashe wayan nasa don bai son tasan kuka zaiyi sai hankalinta ya Kara tashi.


Wasasa Abu yayi kamari suhana inta Kira laisu baya daukan wayarta duk tabi tashiga damuwa ta rame abbaty ne kadai ke iya kwantar mata hankali da kalamai masu dadi "" babanta sai shirye shiryen kaita kano take!!! Mamanta data ga da gaske yake kuma taga yarta sai lala cewa take ' kawai ta yanke shawaran Kiran mahaifin sa ta fada Masa ' ba karamin fada yayi ba "" ya kuma ce mata ta kwantar da hankalin ta insha allahu za ayi auren nan " tayi Masa godiya sannan ta kashe wayan ' sai taji wani sanyi azuciyarta!! Don tasan yarta zata samu farin ciki.


Mahaifin alhaji abbakar ne ya Kira shi ' ya dinga Masa fada kuma tare da bashi umarnin ya auradda suhana ga Wanda take so ' inyaso sai taci gaba da karatunta adakin sa"" zaiyi magana mahaifin sa ya katseshi" ban San jin komai kayi abunda nace kawai.


Ran alhaji abbakar ya baci sosai ' yaje yasamu Fatima yace Fatima nagode da abunda Kika min shine Zaki hadani da mahaifina ko"" burin ku in auradda hafsat ga laisu ko to shikenan Zan auradda ita din !!! Amma ki sani duk abunda ya faru *a* *gidan* *auren* *ta*  ba ruwana ke da ita ku karata'' kafin tayi magana yayi ficewar sa .


Alhaji abbakar yasamu mallam yakubu yace mai kacewa laisu ya turo da magabatan sa azo asa ranar aure kuma bana son bidi'a aciki ko kayan sa rana bana so sadaki kawai nake so.


Tirkashi ana wata ga wata.


Labari yaje kunnan laisu Kamar ya zuba ruwa akasa yasha don murna yayin da ita suhana labarin daya xo mata' haka kawai taji batayi murna sosai ba "" iyayen laisu sun kawo sadaki dubu sittin  ansa lokacin biki Nanda wata uku' laisu ba haka yaso ba ' yaso Ace wata daya ne.


Ita kuwa suhana  sai taji auren ya fitan mata arai ' Abba dayaji labari yafi kowa shiga damuwa yayi kuka har ya godewa Allah ' suhana tayi ta lallashin shi tana bashi baki ' insha allahu dosti zaka samu wacce ta fini komai da komai pls kayi hakuri nayima laisu alkawarin aure, kuma kasan Babu kyau Saba alkawari "  to shikenan my dosti .



Yau garin antashi ana ruwan sama ga iska na kadawa suhana ce ta fito barandan gdan samun su da alamun yau tana jin nishadi kanta ba Dan kwali iska sai hura ta yakeyi da feshin ruwa""  tace kalan wannan yanayi daidai kadai cewa da masoyin ka kenan sai tayi murmushi data tuno da angonta laisu tace bara ta Kira sa ringing daya ya dauka"" tare da fadin ..


Assalamu alaikum zaujaty '  ta amsa Masa sallamar , yace lfy dai ko Naga kiranki da safen nan, tace dama nakira ne muyi hiran soyayya '"" yayi dariya yace soyayya ai sai Yara ' kinga nikam yanxuma aiki nake ki bari sai anjuma zan kiraki mugaisa "" kit ya kashe wayar kafin tace wani abu inda sabo tasaba da halinsa nakin sonyin soyayya.



Sai ga Kiran A .B.Y yashigo wayarta ta daga tana hello namaste my dosti ' kesiho yace mata saptiho, ma'ana yakake yace mata lafiya lau, that is good yanxu haka mekakeyi " yace Ina kallon wani India film ne na( ye sil sila ye pyari kya ) tace woow wacece aciki yace mutuniyar kice (Kajol) woow so romantic " tace how I wish we are together ' batasan sanda tayi subul da baki ba" shi Karan kanshi Abba yasan tana cikin shaukin so ne" kawai sai ya biye mata .


Cikin murya mai dadi yace my suhana kinga yadda garin nan ya kasance cikin ni'imah dai dai zama da masoyi kenan " ji nake kamar Ina yawo a kogin samaniya shaukin sonki shike yawo Dani"" dama dama ' Amma ba tawa bace ta aro ce ' taka a sannu Yar budurwa yarinya Yar kwalisa  " mai tafiya Kamar hawainiya  " Ina matukar sonki my dosti suhana , I really love you.



Hmmmmmmmm 

Inba comment Babu cigaba wallo


*Ummu* *ruman* 

08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

                5⃣

Suhana ta lumshe idanun ta tana jin wani kalan farin cikin da bata taba ji ba" abbaty yace dostina kina jina kuwa " cikin katsalan lan murya tace eh Ina jinka ' yace suhana Ina kaunar ki banta ba son wata ya mace ba bayan ke " kuma bazan taba son wata ya mace ba bayanke!!! Suhana karkiga laifina Allah ne ya jarabce ni da sonki narasa ya zanyi da raina gashi kin min nisa .


' suhana ta fashe da kuka don itama son abbaty ne ya kamata " son da bata tabayiwa laisu irin sa ba ' abbaty yace why are you crying suhana feel free to tell me your hrt , I will help you.


Tace abbaty kayi hakuri da da yanda zanyi, da kai Zan aura Amma aikin gama ya gama " nayima laisu alkawarin auren sa  ' nima yanxu Ina Dana sanin yin alkwarin nan !! Kuma iyaye sunshiga lamarin kaga ko bayadda zanyi !! Gaba ki dayan su sai kuka sukeyi  abun tausayi.



Lokaci sai tafiya ya keyi biki  na matsowa saura wata biyu" suhana da laisu sun rage yawan haduwa kamar Basu damu da junan su ba"" ta bangaren abbaty kuma soyayya sukeyi da suhana sosai" sai kace ba ita bace zatayi aure.


Mutanen unguwa  sun fara tsegumi akan abbaty Yana soyayya da yarinyar da laisu zai aura"" labari yaje kunnan laisu ransa inyayi dubu ya bace sbd abun kunya ne ace ya hada neman budurwa da karamin yaro Wanda bai kamo ajinsa ba . Abokanan sa suka dinga zugashi yaci uwar abbaty.


Aiko suhana na zaune sai ga Kiran laisu ya shigo wayarta tana dauka ya rufe ta da masifa" yanxu kin kyauta suhana abun ma yaudara ce   " kin San da kudin aure na akanki yaxaki je kina soyayya da Dan iskan yaron' nan San salin girmana ya fadi  " angaya Miki ni irin mazan nan ne da ake hada soyayya da wasu mazan " Ina alkawarin dakike ikirarin kin dauka min "" dama karya ce  '" dama munafunta ta kike son yi ko" kawai ki fito fili kice baki Son aure na sai in sani.


Bawai kije kina hada soyayyata da Dan iskan ____ kafin ya karasa tace ya ishe ka laisu ya Isa. so ba hauka bane daza kadinga gaya min wayannan munanan maganganun"" har kana ikirarin girma zai zube to dama wani girma ne da kai inba najiki ba" karamin yaron da kaki ikirarin Dan iska ' ai yafi ka komai " ya fika iya soyayya ya fika tattali ya fika iya kula da mace " arana abbaty zai kirani sau biyar ko fiye da hakan ' don kawai yaji ya lafiyata take "" kai kuma fa sau nawa kake kirana arana" dakyar kake Kira sau daya arana.


Shima din in kakira baifi ayi magana sau biyu ba sai ka kashe wayar ka" innayi maganar soyayya sai kace Yara ke soyayya ba irin kuba " nasha fada maka ni Yar soyayya ce  Amma sai ka basar "" tace laisu wlh da badan nasan girman alkawari kuma da ba dan mahaifina yasaka ranar aure na ba da sai ince Allah ya hada kowa da rabonsa """ takashe wayan tare da sakin kuka mai cin rai.


Laisu ya tsaya Yana kallon wayar hannun sa " Yana mamakin suhana yadda ta canxa cikin farad daya har shi take kashe mawa waya " kuma take fada Masa wayannan munanan maganganun!!! Lallai Kam ya kamata yatashi tsaye don yaga alama abbaty yagama da suhana " in baiyi wasa ba zai rasa suhana " ya buga kansa ajikin bango Yana surutai!!! Wlh baka Isa ba  A.B.Y kake ko wa !! Angaya maka ana shiga gonata ne.


Suhana kwance tana kuka ummi kawarta tayi sallama tashigo ta ganta a haka '" tace subhanallah lafiyanki kuwa suhana kike kuka" suhana ta fada jikin ummi  tana fadin ummi nashiga uku narasa yaxanyi da raina son abbaty yakamani " gashi da kudin auren laisu akaina kuma na Masa alkwarin auren sa " yaxanyi ummi yanxu laisu ya kirani yaci mutunci na wai yaji agari Ina soyayya da abbaty " nan dai ta fada wa ummi haduwanta da abbaty da yadada suka fara abota da yadda suke da laisu har xuwa wannan ranar daya kirata.


Ummi tace tabdi jam lallai suhana ban taba sanin baki da hankali ba sai yau  " Ina, Ina Kika yiwa laisu alkawari sbd baki daukeni da muhimmanci ba Zaki yanke hukunci cikin rashin tunani" sbd son miji Mai kyau Zaki jefa kanki cikin halaka, sbd son miji Mai kyau Zaki bijirewa mahaifinki akan karatun ki '" ki bata Masa rai"" kina da tabbacin laisu zai barki ki cigaba da karatu "" kin San kalan rayuwar auren da zakiyi agdan laisu? To tun bakuyi auren ba gashi ya fara fito Miki da mugayen halayen sa"" Allah ne kadai yasan dalilin dayasa baba baya son bashi auren ki!!! Ni dama tun asali laisu din nan bai min ba mutum sai uban girman kai " kamar wani Dan gdan sarauta don yaga Yana da kyau da rufin asiri.


To wlh inbacci kike ki farka "" ni wlh nafi sonki da abbaty sbd inajin Yayana Yana fadin kalan son da abbaty yake Miki " ni nayi zaton ma tun lokacin Dana xo Miki da maganar sa dayace Yana sonki ke kuma ki kace baki son sa nayi zatan maganar ya wuce "" Ashe kun hade kuna soyayya.


To menene aibun abbaty in kyau kike mawa to shima Yana da kyau dai dai " in hancin ne Yana dashi idon ma Yana dashi haske ne da shekaru da wadata kawai laisu zai nuna mawa abbaty !!! Amma shima abbaty nangaba ba acire Masa tsammanin hakan ba tunda karatu yake yanxu.


Nida zakiji ta shawarata da kin rabu da kyalkyal banxa kin Kama hasken farin ciki ba hasken bakin ciki ba"" suhana ta dago ido tana kallon ummi !! Tace ummi kiyi hakuri ba naki shawaran ki bane laisu shine kalan mijin Dana dage gun Allah ya bani" kin manta kuma mutum bai cika goma Tara yake""  bama wannan ba naji Ina son abbaty Amma abbaty yamin yaro shekaran sa fa 26 Babu wani tazara mai nisa tsakanin mu , shiko laisu shekaran sa 36 kinga ko laisu ya girmemin sosai " kuma shi abbaty baza abarsa yayi aure yanxu ba sbd bai gama karatun sa ba bantala yasamu aiki"' shima ciyar dashi ake agdan su " shiko laisu da kafafun sa yake tsaye " kuma mahaifina bazai yada inje Masa da wani zance ba " tunda shi kaifi daya ne baya magana biyu .


Ummi tazuba mawa kawarta ido tana karantar ta sosai tace suhana lallai kina son laisu sosai dakyar Zaki iya rabuwa dashi" ana nuna Miki hanya daidai ke kuma kina kaucewa "" eh anji shi abbatyn yaro ne Amma kuma ya miki abunda shi babban bai Miki ba"" kinga ki farfado daga baccin da kikeyi wlh" idan baki yi a hankali ba zakiyi dakin sani daga baya lokacin kuma lokacin ya kure.


Bayan tafiyan ummi suhana tana ta tunani tunani tarasa mafita " kawai ta dauki wayanta takira abbaty ringing daya ya dauka tare da sallam tana jin muryan sa ta sauke ajiyar xuciya   yace lfy kike dosti naji kina ajiyar xuciya " sai ta fashe da kuka " yace oh my God kyahuwa dosti it means meke faruwa " nan ta labarta masa komai .


Yayi guntun murmushi mai hade da takaici " yace kiyi hakuri suhana ki kwantar da hankalin ki ba abunda laisu ya Isa yamin " dazun nan ma ya kirani abokina awaya wai Yana son ganina a dakinsa anjuma da magrib .


Suhana tace ya ilahi to me zaima ka duk ta rude yace karki damu bai Isa yamin komai ba anjuma Zan gaya Miki komai idan mun dawo ok tom " bara naje masallaci yanxu pls dosti ki tabbatar kinci abinci kuma karki sake kuka don karki zayyi ciwo kinji my dosti tace toh dosti na .


After magrib abbaty da abokin sa sukaje gun laisu ya amshe su da hannu bibbiyu"  suka gaisa abbaty yace lafiya kake nema na" laisu yace ba lafiya ba Kam!!! Dama akan maganar suhana ce naji ance kuna soyayya tare " kuma Naga da sadakina akanta  " kuma Naga ka hure mata kunne hankalinta ya karkata akan ka shine abun bai min dadi ba "" sbd matar da Zan aurace kuma da akwai alkhari tsakanina da ita !! Kasan kafin kafara tadi nafara inaga ma an haife ka kuwa " to inne man matane bawanda banyi ba har kwana dasu nashayi kai ni nafi karfin ince Ina son mace sai dai ita tace tana Sona ta biyoni " sbda haka nawuce sa'an mune mace daya dakai akarshe Ina rokan ka da kabarmin suhana wlh nashirya aure ne yanxu " duk cikin matan Dana nema Babu wacce ta dace in aura sai suhana" gashi kuma yanxu hankalinta Yana karkata gareka pls ka kyale min ita .


Abbaty yayi murmushi mai Kama da ciwo yace ka godewa Allah suhana na sonka kuma ta rike maka alkwari da badan alkawarin data maka ba Ina tabbatar maka da nine nan Zan auri suhana  afusace laisu ya tashi.


Hmmmmmmmmm


*Ummu* *ruman*

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

                 6⃣

A fusace laisu ya tashi Yana huci yace baka isaba wlh nafi karfin ka aurin yarinyar da Zan aura kuma nafi karfin muhada neman Abu daya da kai' ka dai San wannan yarinyar matar manya ce " ba kanana irin kuba.


Abbaty yayi murmushin takaici yace laisu kenan tunda haka kace kafi karfin mu hada nema da kai to ni kuma nace yanxu mu zuba bazan fasa neman suhana ba har sai Randa Naga tayi aure " kuma nida Kai zamuga wazata aura.


Abbaty zai fita daga dakin laisu yace dakata," don yasan inbai lallabi abbaty to ba shakka zaiji kunya don Yana ganin zai sace zuciyan suhana.


Abbaty yace lafiya katsaida ni," cikin taushin murya laisu yace yi hakuri abbaty Dan Allah ka kyale suhana badonni ba wlh aurenta zanyi kataimaka min"" cikin murya mai rawa abbaty  yace bakomai Allah ya baku zaman lfy.


Bai jira abunda laisu zai ce ba suka fita daga gdan su laisu ' hayena ke kwarara a idanun abbaty ' abokin sane ya dafa kafadan sa yace kayi hakuri abbaty Allah zai musanya maka da wata" abbaty yace baza ka gane bane  abokina mace kamilalliya irin suhana bata dace da auren miji irin laisu ba' bakaji Yana cewa har neman mata yayi.


Amma bakomai Allah ya zaba abunda yafi alkhairi sukace amin!!! Bayan ya dawo ba da dadewa ba suhana takira abbaty donjin yadda sukayi da laisu yace mata bakomai kawai ya rokeni ne inbar  Masa ke , ya boye sauran munana abunda yakeyi bai son taji daga bakinsa don kartayi zaton sharri yake masa' suhana tace shikenan dostina kayi hakuri nasan yadda kake Sona to ba yadda zanyi ne shiyasa " da ace banyiwa laisu alkawari ba to Ina tabbatar maka dakai Zan zaba!! Abbaty yayi murmushi yace bakomai "" kinga bara naje babana yasani wani Dan aiki ' tace ok sai anjuma .


Karya ya mata ya fada ne kawai don yasamu yayi kukan dake damun sa axuciya.


Laisu ya Kira suhana yabata hakurin abunda ya mata da kyar ta hakura suka dawo daidai ' biki sai Kara towa yakeyi  saura sati biyu biki " laisu ya tattara kayansa don ya koma makaranta  don ba zai tsaya ayi  bikin Yana nan ba ana gobe zai tafi ya Kira suhana awaya yace inba damuwa su hadu agdan su ummi ' tace mishi tana ma gdan yanxu yace to ganin zuwa" ta Dan gaggyara jikin ta  abbaty ya kirata awaya yace gashi akofar gda tace to gani nan' cikin takunta Mai Jan hankali ta fito sai kamshin turaren amaren da ake mata takeyi .


Sallama tayi ya amsa Yana jifanta da murmushin kauna " yace amarsu kenan sai wani kamshi kike Mai dadi " suhana tayi murmushi tace ai kaima kana kamshi " yace Amma bana irinki ba  " laidan dake hannun sa ya Mika mata yace ga gift dinki na aure , sbd ni gobe Zan koma skull " tace what dosti yanxu gobe zaka tafi ka barni shine ko ka fada min kukane ya kufce mata ' yace ya Salam kin San bana son kukanki don Allah kiyi shiru" to ba Kai bane zaka tafi tun ba adaura aure ba ..


Abbaty yace suhana  kiyi hakuri yaxama Dole in tafi bazan iya tsayawa adaura aurenki ba Ina gani sbd Nina San yadda xuciyata take min " kiyi hakuri kimin uxuri karki hanani tafiya pls my dosti wlh xuciyata na xafi dostina ,    Amma kiyi hakuri " Allah ya baku zaman lfy " Ina Miki fatan alkhairi dosti!!


Kisa azuciyarki bazan taba son wata macen ba Kamar yadda na soki" na soki sosai suhana xuciyata gangan jikina gaba ki daya tana wajenki " zai yi wuya sonki yafita azuciya ta, tare da sonki za abirne mu"  


shadi hai mubarak suhana


Mere yaar ki shadi hai 


I will miss you alot dosti na


Bye sai watarana


Yayi saurin barin wajen tsugunnawa tayi tana ta kuka tare da rungume ledar daya bata" ta Dade awajen da kyar ta tashi tashiga gdan su ummin tana zuwa tafada jikin ummin tana kuka sosai ummi nabata hakuri " suhana tace shikenan ummi mun rabu da abbaty gobe zai bar garin bazan sake ganin sa ba ya tafi kenan" kinga ledan daya bani .


Ummi ta karba ta bude wani hadaddan kayan bacci ne da turare sai   zanin gado mai kyau sai zobe da agogo shima Mai kyau " ummi tace woow gsky abbaty ya iya siyayya allah yasaka Masa da gdan aljanna Allah yabashi hakurin rashinki amin summa amin.


Bayan suhana ta koma gda tayi ta Kiran layin abbaty Amma Ina akashe ' shiko abbaty Kamar yasan zata kirasa ya kashe wayarsa  don bai son yaji muryanta hankalin sa tashi yakeyi. Washe gari ya Kama hanyar kano dayake a b.u.k yake karatu ..


Ana gobe daurin aure Yan uwa Dana nesa da kusa duk sun xo " laisu yaso a yi party a bikin Amma suhana tace bazata ba sbd bata son bidi'a " ita bikin ma kwata kwata bata sonshi xuciyarta zafi yake duk tabi ta rame  sbd tunanin abbaty gashi tunda ya tafi wayarshi akashi, ta rasa ta Ina zatayi magana dashi.


An daura auren laisu da da hafsat suhana ' anci ansha laisu kamar Wanda akasashi a gdan aljanna don dadin ya mallaki suhana yanxu tana karkashin ikon sa . Suhana kuma sai kuka takeyi" da daddare aka kaita gdan mijinta dake kabala " kawayenta anan zasu kwana.


Washe gari kowa ya watse anbar amarya da angonta ' sunci sunsha , sungabatar da sallan su" daga nan kuma zance ya canxa salo sunshiga duniyar ma'aurata laisu yasamu amaryasa a yadda yake so sai dai muce Allah y bada zaman lfy!!!


Yanxu ne zamu ga menene a gidan auren suhanar. 


Kumin hakuri Dan Allah kanwata ke aure shiyasa banyi dayawa ba .


TAKU *ummu* *ruman*

*NUSNIM* 08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

               7⃣

Laisu ne ya taimaka mawa suhana tayi wanka  tashirya' rayuwa sukeyi cikin nishadi suhana na son laisu sosai  kuma tana godewa Allah daya mallaka mata shi  amatsayin mijin aurenta" kasan xuciyarta kuma tausayin dostin tane ' ko awani hali yake batasa sani sai dai tana Masa fatan dangana da juriya .


A bangaran abbaty kuwa Randa aka Kai suhana gdan mijinta yayi kuka ba kadan ba har ya godema. Yana rokan Allah daya sama sa dangana da juriya akan hafsat suhana .


Akwana atashi ba wuya awajen Allah har suhana tayi wata uku gdan laisu' tayi kyau abinta ga kwanciyan hankali .alokacin kuma daga wajen aikin su laisu sun turosa ya dawo ya karo karatun degree ' don diploma ne dashi' ya dawo kaduna da zama ya nemi kasu ;; Amma yanxu anrage Masa albashi , yanxu samun sa Babu yawa  !! Kuma duk wannan kyalkyal din daya keyi yanxu Babu shi haka sukaci gaba da rayuwa da dadi ba dadi""  har sukayi wata shida da aure Amma har yanxu suhana ba ciki " wata auntyn laisu dake aure a Minna ta kirasa sun Dade suna hira tace yanxu nasan amarya nada ciki ko" yace a'a wlh !! Tace toh aiko kayi gaggawan kaita asibiti a dubata, sannan kuma ka cewa su mama tayi bari inba hakaba yanxu sai asa mata ido ayi tunani bata haihuwa" yace to shikenan.


Washe gari laisu ya Kai suhana hospital aka dubata" likitan yace za a wanke mahaifarta insha allahu za adace, ran suhana ya bace don me za ace mata za amata wankin mahaifa wlh bazan yarda ba ' bayan sun dawo gda tace wa laisu itafa baza ta yarda ataba lfyar jikinta ba" mutane nawa ke aure sukai shekara goma Basu haihuba sai daga baya Allah ya Basu haihuwan su suce mene" mu wata shidane kacal sai ace mun kasa hakuri to Ina badani ba.


Laisu ya Kira maman sa da Yan uwansa yace musu suhana tayi bari , suko sai tausaya mata suke , sunxu har gda suna mata sannu da mamaki Suhana ke kallon su ,  " tana fadin azuciyarta wato kenan in Allah baibani haihuwa da wuri ba Zan zama abun tsangwama tab ni kuma da irin wannan dangin mijin na hadu dasu kenan, to Allah ya kyauta.


Awata na bakwai da auren su suhana ta samu ciki zokaga murna gun Yan uwa bare ma uban gayyan , alokacin ne kuma aka saka bikin yayan laisu din , matar da zai aura a kano take " lokacin daxa akai lefe surikar suhana tace da ita za atafi!!! Dama alokacin suhana Dan uwanta zaiyi aure sai ta hada tafiyan duka sunje gdan amaryan  Dan uwan laisu din Yar gdan masu kudi ce !!


An musu tarba Mai kyau tare da kayan ciye ciye , anci ansha suka fito zasu tafi aka sauke suhana a hoto road gdan innarta .


Lokacin bikin abdallah ya matso su suhana ne zasuje da yan'uwan mijin ta su hudu " lokacin da suka Isa kano gdan amaryan abdallah duk Yan gdan sun watse sun tafi kamu " amarya ce kawai ta rage da kawayen ta ana shiryata" daya daga cikin dangin su laisu tashiga cikin gdan taga Yan tsirran mutane tayi musu sallama tace mu baki ne daga kaduna mune dangin mijin zainab amarya" kanwar baban amaryan tace ayya sannun ku da zuwa kuxo muje innuna muku inda zaku sauka , don yanxu kamu zamu je .


Suka ce to , aka ijye su suhana ba akawo musu komai ba sbd kan mutan gdan yayi zafi kuma a kurarran lokaci suka zo . Shiru shiru ba awaiwaye suba, sai daya daga cikin dangin mijin tace kunga ku mu shirya mubar gdan da alama Yan gdan Basu da mutunci ' sai ga amaryan abdallah tashigo dakin ita da kawayenta suna kallon madubi don agyara mata daurin dankwalin.


Kanwar maman su laisu ne tace Dan kunga kuyi saurin kushirya tunda ba asan damu ba anyasar damu ' amarya zainab ne ta juyo tana mallamai ku kuma dawa kuke kunxo gdan mu kuna kananan maganganu" .


Suhana ce tayi magana tace baiwar Allah maida wukan inba yazama Dole ba bazaki ganmu ba muma bikin amaaryan abdallah muka zo " zainab tace kuna nufin kune dangin mijina ' dayar dake zaune kusa da suhana tace eh mune!! Kema kece amaryan abdallah din tace nice" zainab taja tsaki tawuce !!


Kanwar maman su laisu tace tabdi jam gskya bamuyi sa'an suruka ba , suhana Allah y Miki albarka ke Yar gdan tarbiyace lokacin da muka je naki ba haka aka Mana ba" Amma abdallah bayyi sa'ar mata ba.


Anyi biki an watse amarya ta tare  a gdanta .


Cikin suhana sai girma yakeyi yayin da laisu na tarairayenta " ita abunda ke damunta' bata son yawan damunta da yake .


Yau saura kwana 5 babban sallah  cikin suhana kuma watan sa goma " Amma haryanxu bata haihu ba , ana cikin haka suka ambaliyan ruwa ya shigar musu daki dakyar suka samu suka tsira lokacin karfe daya na dare " haka suhana tayi ta kwashe kayan haihuwarta tana fita dashi da kuma takardun mijinta na makaranta "  sunsha wahala sosai ba kadan ba " gadon da mahaifinta ya mata ya narke aruwa dayake na kamfanine" dayan gadon ne baiyi komai ba sbd shi na Jan katako ne. Yawancin kayan dakinta ruwa ya tafi dashi dakayan sawanta .abun tausayi.


Ta dawo gdan su da zama kafin su sami wani gdan mahaifinta ya dinga fada don Mai yasa laisu zai Kama gda inda fadaman ruwa yake " mutum na Abu ba tunani kalli kayanki duk sun lalace sai kace ba kudi nasa na saya ba.


Ta dawo gda da dadewa labour yazo mata bata iya bacci sunyi jigilan asibitin gwamnati Amma sai suce musu ba haihuwa bace" gashi tana bleading din bakin jini" mamanta tace takira laisu yazo ya kaisu asibitin kudi ita tagaji da wulakancin da asibitin gwamnati ke musu ' shi kuma laisu yace shi kam baida kudin zuwa hospital din kudi ran maman suhana ya baci tana ta fada " ana haka sai ga yayar mamanta tazo.


Taga halin da ake ciki tace maza su taso suje asibitin formwan na kudi aiko suka tafi a motarta  !!! Suna zuwa doctor Yusuf yace akaita labour room yaje ya dubata ya dinga fada yace babyn baya cikin ruwa kuma ruwan mahaifan ya tsiyayi " suna wasa da rayuwar ta da babyn " yace operation kawai za amata don baza ajira aga zata haihu da kanta ko baza ta haihu da kanta ba .


Aiko aka Kira laisu  yazo aiki za ayi , laisu yayi ta fada shi bashi da kudi yayansa abdallah yaxo yace amaida ta asibitin gwamnati zata haihu acan nan suncika gaggawan yiwa mutane aiki don suci kudin su" .


Maman suhana tace baku Isa ba wlh ya zaku dinga min wasa da rayuwar yata ce muku akayi bani sonta kunsan ciwon nakuda kuwa " to wlh ba inda zamuje anan asibitin zata haihu in kunga dama ku biya inba kuga dama ba kar ku biya " abdallah ne yabada hakuri sannan sukaje suka biya.


Anyi c.s lfy suhana ta haifi namiji mai Kama da babansa  yaro kyakkyawa" duk dangi anxo ganin yaro!! Bayan kwana hudu aka sallame su " laisu yace baza ayi suna ba shi baida kudi rago kawai ya siya shima Dan karami " dai dai da kayan yaro laisu bai siyaba abun ya fara ba mawa maman suhana haushi tana Allah wadai da halin laisu " suhana Tasha kuka sosai" ya za ayi ace haihuwan fari ba abunda laisu ya musu sai dai kullum yace baida kudi.


Da surikarta tazo barka ta xo da kayan dangin miji ke yi a kwalle a dankwali  atamfa guda 6 kayan yaro guda biyu ranar maman suhana batanan " da maman ta dawo daga irin wannan wulakanci shima saida suhana tayi kuka .


Takira kawarta ummi tana fada mata komai ummi tace tabdi jam ai wannan wulakanci ne, akawo maka kaya a kulle a Dan kwali kuma kayan yaro  kala biyu   " suhana tace ummi wani kayan haushin ma tunda na haihu ko irin naman nan mutumin bai saya min ba" kayan tea ma tunda ya siya sau biyu bai kuma siya ba" sai dai fa agdan mu amun komai..


Ummi wlh nayi Dana sanin auren laisu haihuwa daya Amma ya canxa Ina kuma Dana sake wani haihuwan , ummi tace kema hakuri ya ganki" suhana tace kin San wani abu wai lokacin bikina ba akai musu gara na dangin miji ba * " shima sukayi tayin suratai akai  "" kuma kafin bikina babana yace musu baya son irin wayannan bidi an" kuma sun amince!!! Sai vayan biki suka canxa suna kananan magana .


Harda fadin matan abdallah iyayenta sun kawo musu buhun shinkafa buhu biyu babba katan din su taliya biyar biyar " shine suke yadawa .


Ummi tace am srry to say suhana Anya dangin mijinki ba Yan auren jari bane .



Hmmm gidan aure na kenan kuci gaba da bini


Dan Allah kudinga comment akai 


*Ummu* *ruman* 

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: Q🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

                 8⃣

Ummi tace I am srry suhana Anya dangin mijinki  ba Yan auren jari bane" wlh ban sani ba ummi !! Ni wlh duniyar ma tamin zafi ' narasa Ina Zan sa kaina inji dadi !! Allah sarki sai kici gaba da addu'a tunda dama kin kware gunyin addu'a akan Abu.


Yaron suhana yaci sunan mahaifin laisu Amma ana Kiran sa da Asad  haka rayuwa taci ga ban mawa suhana sai datayi wata uku agda sannan laisu ya sa marmu su gda.


Gidan gadon su dake malali suka saida , shine suka siya wani a kadaure , karamar gdana Anba mawa laisu daki biyu parlo daya sai kicin " sai sauran dakunan yayyan laisu biyu suka dauki daki daya , sai dayan dakin kannan sa biyu maza suka dauka .


Laisu yazo gdan su suhana yace mata sun siya gda a kadaure " tace a kadaure kuma kasan fa bana son zaman kadaure yacika kauye kauye "" yace to ya za ayi yazama Dole ne'" kuma layin gdan su mamana ne" tare da Yan"uwana maza zamu zauna.


Suhana ta zaro ido tace kace tare da maza zamu zauna gauraye wayanda Basu da aure tabdi jam wlh baxai yuba , cikin lallashi yace ai baza ma zamuyi din din dinba kafin insamu kudi ne in Kama Mana wani hayan da kyar suhana ta amince" don bayadda zatayi , .


Suhana tafada mawa babanta yace mata asauka lfy * tace baba Dan Allah ko xaka gyara min gadona da kujeru duk sun Dan lalace!! Ya wurga mata wani uwar harara baki da hankali shi mijin naki me yasa bazai gyaraba" aishi keda hakkin ya gyara Miki  bani ba" ni nasan darajan kudi.


Haka suhana ta kakkabe kayanta ummi kawarta tazo ta taya ta wankesu komai yayi tsaftsaf"" ranar sati ta tare agdan da suka siya gdan baida wani kyau gashi fenti ne kawai aka shashshafa sama sama " da kyar laisu ya siyi ledan daki aka saka " ummi tace lallai suhana rayuwa juyi juyi ke kuma yanxu haka rayuwarki ta dawo abun tausayi kalli dakin ki fa , Wanda ko dakin Mai aikin gdan ku yafi naki kyau . Tabdi rayuwarki ta isheni darasi !! Suhana dake zubar da kwalla tace ummi bantaba tunanin zanyi rayuwa irin wannan ba .


Nikam tawa kaddaran kenan Allah kadai yasan abunda yake nufi Dani ummi ta fashe da kuka" tana kiyi hakuri suhana komai yay faro zaiyo karshe !! Hakane kam.


Suhana tace kin San menene ummi "' ummi tace sai kin fada !! Abunda nakeji shine mun dawo layi daya da surikata " gashi kin San baba bai min garan haihuwa ba sbd kin San shi baya wannan bidi'an " gashi har laisu Yana cemin yanxu babana bai min gara ba ? Nace Masa ka manta gdan mu ba a bidi'a. Da haka na rufe zancen.!! Ummi kin San daidai da riga daya babana bai siyama Asad ba.


Ummi tace karkisa wannan aranki suhana " duk da babanki Yana fushi akan aurenki ya miki hidima tunda duk wani nama da Mai jego keci mahaifinki ke siya Miki da kayan tea har izuwa yau da Kika bar gdan sa" so kar wannan abun ya dameki uban yaron ma bai siyawa dansa riga ba bantala kuma baba.


Suhana tace haka ne Allah ya shige Mana gaba  !!ummi ce ta janyo wani Dan karamin akwati sabo Mai kyau " suhana tace yauwa ummi wannan akwatin wanene haka Mai kyau tun tuni Ina son tambayar ki sai kuma na sha'afa!! Ummi tayi murmushi tace nakine sakone akace inbaki.


Suhana ta zaro ido waje tace what waye yabani wannan kuma " ummi tace bude ki gani , suhana tayi saurin budewa   atamface guda uku masu kyau sai lace guda biyu sai Dan kunne da sarka ' sai kayan baby guda goma da takalmi da su turare " duka masu kyau!! Suhana tana duddubawa tana ya ilahi yanxu duka wannan nawa ne ummi ".


Ummi tace eh naki ne , ummi tace kiduba cikin aljihun akwai wani sako aciki ' suhana tayi saurin ss hannu tana lalube kawai tazaro kudi sabobbi masu kamshi yan dari biyar biyar , har dubu ashirin data iriga!! Tace ummi yanxu wannan shima nawa ne " ummi tace eh naki ne.


Suhana tayi saurin saukowa kasa ta dafa gyuwowin ummi tace ummi Dan Allah fada min wanene ya min wannan gatan , na tabbata ko wanene Yana da muhimmanci arayuwata" ummi tace tabbas kuwa " ba kowa bane ya Miki wannan abun face abbaty !! Suhana ta zaro ido tare da dafa kirjinta tace ummi yanxu dosti nane yamin wannan abun, Wanda yakamata ace miji nane yamin .


Innalillahi wainnailaihi raji'un ta fashe da wani irin kuka Mara sauti tana Kiran ya Allah " Allah kasa ka mawa bawanka da gdan aljanna kasa ya gama da duniya lfy gaskiya abbati yayi na mijin kokari .


Ummi tace tabbas kuwa suhana abbaty yayi kokari" suhana tace tayaya yasan na haihu ummi tace mijin kine ya tura masa da sakon kin haihu " wai inyana tunanin Zaki dawo garesa to yacire raida ke don yanxu kinzama mama mama ' haka ya tura masa.


Suhana tayi murmushin dayafi komai ciwo tace lallai laisu bashi da mutunci Amma yaje ya cigaba dayi watarana in ance yayi bazaiyi ba. Ummi tace aikuwa , shine fa laisu ya kirani yake fada min " yace amiki barka sosai Yana gaisheki ashafa Masa Kan babyn sa suhana tayi godiya sosai" ta zare dubu biyar ta bama wa ummi tace bazata karba "" itama ya bata dubu 7 kyauta suhana tace ayya Allah y biyasa.


Rayuwa kenan " suhana ta dawo kadaure da sati daya yayyan mijinta maza suma suka dawo daga Mai shekara 40 sai Mai shekara 45  sai Mai 33 " duk wai dasu suhana zata zauna kuma Basu da aure"" kuma dakin su Babu tazara, sbd karamin gda ne.


Suhana tace yanxu da wannan Zan zauna tuxurai  ,   gda daya " bayan sun dawo gdan laisu' yace girki gaba daya zata dingayi  , sai ta dinga zuba musu" Suhana bayadda ta iya haka  take girki gaba daya .


 Dawowanta gdan rayuwar ta ta canxa " suhana ta lalace tayi baki tayi rama sosai " dai dai da girki bata da ikon dafa abunda takeso sai abunda surikarta da yayyan mijinta suka ce zasu ci shine zata dafa dai dai da cefeni surikarta keyi ta kawo    .


Hmm yanxu akafara .

 


*Ummu* *ruman*

*By* *NUSNIM*

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            9⃣

Dai dai da cefeni surikarta keyi ta kawo kuma baza akawo ishashshe ba " kuma idan suha ta gama girkin laisu shi zaizo ya raba abincin ya cika mawa Yan uwansa kuma abinci sau daya akeyi  arana, kuma ahaka suhana ke rayuwa watarana ta zauna tayi kuka mai cin rai .


Dai dai da kawayen suhana suka zo wajenta bata da ikon daza ta Basu abincin gdan , sai dai ita ta saya musu da kudinta "" ko shimfida Basu hadawa ita da laisu ' a shekara baifi sau biyu yayi kwanciyar aure da ita , shima adaddafe sbd laisu ba cikakken namiji bane " ahaka kuma suhana ke rayuwa agdan " kullum maganar sa kenan kudi yake jira yayi magani.


Suhana taga naira biyar na gagararta tazo tafara saida su Jinja da xobo da kankaran kuka ' ta haka take Dan samu tana magance matsalolin gabanta , kuma taki ta fada mawa iyayenta halinda ta ke ciki.


Laisu yanxu yasamu wata Sara idan yaga kawayen suhana sunxo ya dinga mata ihu kenan Yana daka mata tsawa wulakanci dai kalala'. Sai dai suhana tayi kuka tayi shiru Dan kanta , tun mutane na zuwa gdanta har suka daina xuwa sbd baza su iya ganin ana wulakanta suhana ba.  Ummi ma sai da taja baya da zuwa gdan suhana .



Kullum suhana nacikin kunci ita kadai ba me debe mata kewa sai yaronta adil ' don shi laisu koda yaushe Yana dakinsa Yana danne dannen waya charting da Yan mata gashi bai da aiki sai Hawa Facebook ana maganar banxa" daga suhana tashigo dakin sai yafara fadan !!! Lafiya Mai ya kawo ki dakina nifa bana son takura " Dan Allah kifiti kifita " irin Kamar yaga wani dodo" haka suhana zata fita tana kuka ta kulle kanta adaki ita da yaronta adil Mai shegen wayau" don yanxu shekaransa biyu da rabi " Inga mamanshi na kuka sai yace momi ki daina kuka daddy ne ko' momi Inna girma zansiya Miki gda inbaki kudi" suhana ta Kara fashewa da kuka ta janyo danta ta rungume abunta .


Haka wataran suhana ta dauko wani book da abbaty ya cika mata lokacin tana budurwa , ba abuda ke cikin takardan sai kalamomin soyayyane da yadda yake nuna kulawar sa akanta , da yadda sonta ya mamaye zuciyarsa ta kankame takardan a kirjinta tana ya Allah ya Allah" Allah ka sassauta min wannan jarabawan.


Akwai wata rana suhana ta fita kofar gdan su ita da adil zata saya mashi biskit' kawai sai taci karo da wata Yar matashiya kyakkyawa da ita baza ta wuce shekara ashirin da takwas ba 28 ba" tana kallon suhana taje feta da murmushi itama suhana ta maida mata da martani , tayiwa suhana sallama ta amsa " tace ni sunana Khadija mu makwabtan junane ga gdan iyayena can " koda yaushe Ina ganinki inxaki fita inba damuwa zamu iya zama abokai.


Suhana tace ayya badamuwa  sannu Khadija ni kuma sunana hafsat suhana " Khadija tace suna mai dadi , bara na wuce insha allahu Zaki dinga ganina Ina kawo Miki ziyara.


Khadija makociyar su suhana ce Amma tana zaune gdan iyayen tane" bazawara ce ita , kuma irin wayayyun Yan barikin nanne ' zata ba mawa suhana shekaru hudu Amma kuma tana da kirki.


Khadija na xuwa gun suhana susha hira ' yau da gobe sai Allah Khadija taxo tagane kalan zaman hakurin da suhana keyi agdan mijinta ta tausaya mata sosai ' sannan kuma ta fara bata shawarwari ' suhana tana jin dadin zama Khadija " Khadija ta tsani taga namiji na wulakanta mace ""watarana  agaban Khadija laisu yayi ta dakama suhana tsawa Yana mata masifa tare da sababi ita kuma suhana jiki na rawa ta tashi ta Masa abunda yakeso " bayan laisu ya bar gdan " Khadija ta kalli suhana tace banta ba sanin baki da hankali ba sai yau " duk wani iskanci da laisu ke Miki ke Kika bashi kofa  don yaga kina kyalesa sa shiyasa yake juyaki duk yadda yaso " Dan wulakanci har agaban mutane yake nuna mulkin sa" to kibude kunnan ki kijini da kyau daga karki kuskura ki Kara barinsa Yana Miki tijara gaban mutane" ki sa Mesa ki fada Masa idan yaki ya bari ,  Yana Miki kema ki mayar Masa " idan Kika Masa haka zai daina "" sannan kuma kidaina sa damuwa aranki " kiba mawa damuwa inba haka ba sai damuwa ta Miki illa shiko ko ajikinsa .


Nan dai Khadija tayi ta nunawa suhana hanyar daza ta kwaci kanta ' " Khadija ita ke xuwa ma suhana tun safe sukai dare tana tayata hira " anan ne Khadija ta fada mawa suhana wacece ita " tace ita Yar lesbian ce sannan kuma ita tana bin maza " suhana ta girgixa da jin haka don kalan siffan Khadija baza kace tana aikata wayannan munanan aikin ba" acikin zuciyar suhana tace Allah ya shiryeki Khadija"" sai Khadija tace amin tana kallon suhana 


Suhana ta zaro ido tace tayaya kijaji abunda nace " Khadija tayi murmushi tace ainasan abunda Zaki fada kenan kuma naji dadin haka "" kuci gaba damin fatan shiriya nima Ina son haka !!! .


Koda wasa Khadija bata taba Jan ra'ayin suhana akan munanan ayyukan datakeyi ba"" zama da Khadija yasa idanun suhana ya bude , kwata kwata laisu baya son tarayyan su tare da khadijan don ya fara ganin suhanan idonta ya fara budewa " yanxu suhana ta daina cin girkin gdan ta kawai idan tayi zata ba dangin mijinta da mijin nata!!! Ita kuma zatayi nata Mai dadi dayake Khadija na bata kudi" dai dai da Dunkin sallah Khadija keyiwa suhana.


Kanwar suhana ce ta dawo daga hutu sai tace gdan yayarta suhana zataje tayi hutun ta acan"" da kyar babanta ya barta , suhana da ganin kanwarta tazo hutu wajenta ba karamin dadi taji ba" sunata murnan ganin juna" laisu ya dawo yaga Maryam kanwar suhana yafara washe bakin karya yana fadin sister munyi fushi dake tunda kinki xuwa wajen mu " Maryam tace amin afwan Yaya laisu baxan sake ba insha allahu yace to shikenan "!!


Bayan fitan laisu Maryam ta kalli yayarta tace Yaya suhana ya Naga kinrame ciwo kikayi ** suhana tace aikuwa ciwo nayi Maryam "' ayya sannu ko " tace Ina baby adil ne? Suhana tace sun fita da auntynsa Khadija makociyata.


Khadija ta dawo taga kanwar suhana nanfa tashiga hidima asiyo wancan adafa wannan a soya wannan harsaida Maryam ta dinga rokonta tana tabari Dan Allah sannan ta bari dakyar.


Zuwan Maryam gdan laisu' baisa ya canxa halinsa ba sai abunda ya cigaba " har Maryam tazo ta gane zaman da Yar uwarta takeyi agdan tayi kuka har ta godema Allah' " kuma ta dau aniyar baxa ta sake gaisheshi ba tunda cinkashin dayake ma Yar uwarta kenan"" taso ta fada mawa iyayen su Amma suhana ta roketa karta fada .


Laisu zai wuce Maryam ma ta wuce ko sannu bata ce Mai" Ashe abun na damun sa " daya gaji da hakan !!! Ranar da daddare Maryam ta fita tadi suhana na zaune a falo tana kallo laisu yazo yacewa suhana " idan Maryam ta dawo kice ta tattara kayanta ta koma gda ubanta !!! Suhana ta jiyo da mamaki tana kallon sa " tace me kace ya Kara maimaitawa " tayi murmushin daya fi komai ciwo tace kabari intadawo kafada mata da bakin ka yace to.


Maryam ta dawo tana murna saurayinta ya bata 10k da kuma sabuwar waya" cikin murna tazo tana nunawa yayarta tace" kinga Kamal ya bani" ke ki rike kudin duk don kinfini bukatarsu " ni kuma sai in rike wayar , suhana tayi mata godiya duk suna cikin murna !!! Suna cikin hakane laisu yazo daga shi sai gajeren wando da vest , yace Maryam suhana ta fada Miki sakona " tace Bata fada ba "" yace to kice ta fada Miki " Maryam ta tambayeta tace ita ba abata sako ba " sai dai shi ya gaya Miki.


Laisu yace cewa nayi ki tattara kayanki ki koma gdan ubanki " suhana bata taba tunanin laisu zayyi haka ba.


Maryam tayi murmushi tace alhamdulillahi nagodema Allah dayasa Ina da gdan ubana" laisu yace kin San da kina da gdan uban kikazo Kika tare min agda banxan yarinya kawai Mara tarbiya Yar iska" kalmar daya dake xuciyar Maryam kenan " cikin harxuka tace sai dai Kaine karamin Dan iska Wanda bai San darajar iyalinsa ba .


Cikin harxuka laisu yace nice  Dan iska " Maryam tace eh kaine, Ashe ba dadi daza ka cemin Yar iska aiko ya yunkura ya biyota har daki yashake mata wuya har Kan gado suhana na rabawa ya tureta ta buge da durowa , Yan uwansa na kallo basuce komai ba sunki rabawa aiko suhana taje ta dauko kwalba zata rotsa Masa akai sai ga kaninsa ya kwace ya raba fadan dayaga xa akashe Masa Dan uwa.


Maryam tafita daga gdan tana zazzaginsa shima Yana ramawa  " suhana tarasa abunyi xuciyarta ne taji kamar zai fito " laisu yace duk ku barmin gdana wajen 12 nadare kenan !!! Khadija ne ta fado gdan tana masifa ta janye suhana suka tafi gdansu " Nanda nan Maryam takira mahaifin su ta fada Masa " ransa ya baci sosai yace ni laisu zai Koran min da yara mata da daddare nan 12 dare !!! Yace zai turo adauki Maryam ita kuma suhana ta kwana a makota da safe ta wuce unguwar dosa gdan madaurin aurenta.


Hmmmm ya ilahi wannan kenan kar ku manta labarin nan ya faru ne da gaske inkece haka ta faru dake ya zakiyi 


Kubiyo agaba donji


*Ummu* *ruman*

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM* 

              🔟

Da sassafe suhana ta wuce unguwan dosa gidan madaurin aurenta nan ta zayyane musu komai " basuji dadin abun bayan gari ya waye mahaifin suhana yaxo gdan " aka Kira suhana aka tambayeta " nan shima takwashe komai tafadawa mahaifinta " mahaifinta yace meyasa daya ce Miki  kifada mawa Maryam ta tafi gda baki fada Mata ba..



Alhaji Ibrahim wato wan baban suhana yace kaiko abubakar tayaya zata iya bude bakinta ta cewa yar'uwarta ta bar Mata gda " baban ta yayi kwafa sosai yace harni za awulakanta akoro min ya'ya da daddare kuma 12 na dare.


Aka Kira wan laisu wato abdallah  da mallam yakubu Wanda laisu ya aikosa lokacin dayake son auren suhana' sai kuma suhana da madaurin aurenta "" aka tambayi suhana ta fadi abunda ke faruwa ta kwashe komai ta fada " akace laisu shima ya fada nasa" laisu yace '' wai Maryam bata basa girma Bata gaisheshi ' sannan kuma ana Tara Masa kawaye Yan iska agda sannan kuma ana Masa albazaranci da abinci ana kaiwa makota " suhana tasake baki tana ganin yadda ake sharri"" yaci gaba da cewa sannan kuma akwai wata Yar iska makociyar mu kullum agdana take tarewa .


Kuma take hurema suhana kunne ban Isa ince suhana Yi kaza ba sai Taki haka abincina sai akwashe aba mawa mutane " suhana ta fashe da kuka tace wlh karya  yake min wan babansu ya daka Mata tsawa datayi shi.


Budan bakin abdallah yace shi yake siyan kayan  abinci agdan sbda haka baiga dalilin daxaisa ana Masa albazaranci da abinci ba tunda ba laisu yake siyaba' duk dai aka taru aka bamawa suhana rashin gaskiya" .


Tace ita baza ta koma gdan ba ' aka tilasta Mata ta koma gdan laisu Amma tadau alwashin sai sungane Goran abincin da nura ya Mata.


Bayan ta dawo yayarta ta lallasheta , bayan sun juya Khadija ta shigo suhana ta fada Mata komai Amma Bata fada Mata ba ason tana shigowa gdan ba don bazata iya rabuwa da Khadija ba sbd tana taimakonta, nan dai Khadija ta bata hakuri tare da cewa kici gaba da addu'a Allah zai Miki maganin sa"" can da magrib sai ga laisu da nura anshigo da karamin buhun shinkafa da taliya dasu  manja Maggi da dai sauransu " laisu yazo Yana washe baki yace ga kayan abinci can mezaki dafa Mana Yana murmushi 


Suhana tace bazan Kara cin abinda Dan uwanka ke siya ba na gwamma ce in zauna da yunwa da dai inci abincin sa tunda Kai baka da karfin daza ka iya ciyar da iyalinka   " to duk Randa ka samo naka halaliyar sai muci.   Laisu ya kalleta da mamakin jin kalamanta baiyi tunani zata iya irin wannan maganar ba"" yace wannan maganar saki akayi kifadesa tace bawanda ya sani kayi zaton bani da zuciya ne." Ta tashi tabar Masa parlon 

Tashige daki tana tunanin Yar uwarta Maryam tayi missing dinta dama ita da Khadija ke debe Mata kewa.


Laisu yaje ya dafa musu abincin yasama Yan uwansa nasu yace ma suhana ga abinci tayi banxa dashi " ankira sallah yashiga masallaci " sai ga kanwar Khadija da abincin da Khadija tace ta kamawa suhana don karta zauna da yunwa shinkafa da miyan kaza ga kuma su salat da drinks "" suhana tayi godiya sosai dama tana tunanin me zataci !!! Bayan tafiyan kanwar Khadija sai ga laisu ya dawo  yaga suhana tana cin abinci yace yabaki abincin nan?


Suhana tace makotan Dana ke Kai musu abincin kune shine suka fara dawo min dashi ' maganar ta tsaya masa arai yayi kwafa yashige dakinsa " suhana tace banxa kawai me siffar aljanu !!! Ni NUSNIM nace kyal kyal kyal yau wace Rana ankushe mutum Mai kyau.


Ahaka rayuwa yaci gaba da tafiya suhana tana Dan sana'arta kuma Khadija ke taimakon ta " yanxu kwata kwata suhana ta daina cin abincin da abdallah ke kawowa ' da safe dai laisu zai Bata kudin Kari dari biyu shi take ka cancanawa " Khadija ta rage shigowa gdan sbd Bata son tana ganin  suhana cikin damuwa," Amma jefi jefi takan Dan shigo, kuma tana Mata Aiken kudi  .


Ana hakan laisu ya gama makarantarsa , ya koma gun aikin sa' bai damu daya kirasu awaya ba sai yayi kwana biyu har yakai da suhana tana mantawa wai tana da miji" gashi a wata baifi ya turo Mata da kudin abinci 10k a awata daya " ahaka take maneji wataran haka suke xama da yunwa ita da danta sai kuma in makota sun aiko Mata sai suce !! Wasa Wasa laisu sai yakai wata hudu Bai dawo ba tun anasa ranar dawowan sa har agaji .


Suhana    intashiga cikin kawayenta sai taji Mata na hirin mazajen su ' wannan tace ni mijina gaza ni ni nayi dacen miji nagari wannan tace aini sai godiyan Allah" suhana sai dai tayi murmushi tace axuciyar Ina itace yaushe rabon datasa laisu a idonta harta manta .


Saida laisu yayi wata shida da  a Abuja sannan ya dawo " suhana sai murna takeyi irin ita Mai miji din nan ' daya dawo ta tareshi da murna " ya basar ya nuna alamun ko in kula"" sai kawai dansa daya jawo jikin sa Yana Masa Wasa ' ta gaishesa tamasa ya hanya ya amsa .


Tunda laisu ya dawo baidamu ya hada gado da suhana ba , har yayi sati daya yakama yin shirin komawa abun yakona ma suhana Rai !!! Ace mijinka yayi wata shida baya tare da iyalinsa , sannan kuma ya dawo   yanuna Bai damu da Kai ba ' dazai tafi ya bata dari biyar yace inyaje daga baya  zai turo musu kudin abinci.


Haka ya kada kansa ya tafi Basu da ko wake  daya ' abun ya Dame suhana" tace yanxu laisu haka ya kada kansa ya tafi ko abinci Bai ijyemun ba sai dari biyar me Zan siya da dari biyar ta fashe da kuka!!! .


Tunda laisu ya koma ya kashe wayarsa don kar suhana takirasa tamasa maganar abinci"" kullum suhana sai takira   laisu Amma layinsa akashe " gashi Basu da abinci tarasa waxata tunkara yataimaka Mata . 


Yau suna zaune Adil Yana kuka yace mummy yunwa nakeji " Dan Allah mummy kiban abinci ta jawoshi ta rungumesa tace Adil kayi hakuri wlh ban San Ina Zan samomaka abinci ba gashi Khadija batanan "" yacigaba dayin kuka !!! Kawai tace Bari taje gun surikarta ta taimaka Mata da abinci ta bamawa Adil ".


Tayi sallama tashiga shashin surikarta  ta gaisheta da kyar take amsa mata' nan suhana ta fada Mata bukatar ta"" maman laisu tace Allah ya kyauta intaimaka  Miki mai mugan hali da bakar kafa " tashi  ki fita kibani waje mutuniyar banxa" Adil yace Kaka  yunwa mukeji " kaci ubanka fitarmin daga gda .


Suhana ta fita tana share kwalla ' suka koma gda Adil ya kwanta Kan jikin ta Yana wayyo mummy cikina Yana murdawa' hankalinta yatashi tana cikin tunanin ya zatayi kawai ta tashi taje ta Nemo nikab dinta da safa sai dogon hijabi tasaka ta dauki Adil suka fita dayake darene!! Basu zarce ko Ina ba sai wajen da ake gasa kaji dayake manyan mutane masu motoci ke zuwa wajan , suhana takarasa wajen wani mota tace mawa Mai motan Dan Allah mallam kataimaka min da kudi Zan siya mawa yarona abinci yaci Adil dake goye abayanta yace wayyo mumy cikina ' suhana ta fashe da kuka ''" Mai motan yaji tausayin su " aiko ya siya masu gasheshshen Kazan nan guda biyu" awajen akwai wani shagon provision shima yashiga ya siya masu kayan tea da  bread ' ya kawo musu ya bata ledojin tare da 20k """ jiki na rawa suhana ta karba tana gode Masa    yace bakomai duk Wanda ya taimaki wani Allah na taimakonsa.


Bayan sun dawo gda suhana ta bude ledojin daga kayan daya siyo musu masu yawa  ' nan ta hada musu tea ta juye musu kaza daya Adil nagani yacika da murna .


Yana yeee mummy yau zamuci dadi tayi Masa murmushi"


Washegari tashiga kasuwa tasiyo musu kayan abinci " saida laisu yayi wata daya da tafiya yakirata da kamar baza ta daga ba" Amma kawai sai wani zuciyar Tata tace tadauka taji me  zai cemata ' tana dauka taji yafara Dan Allah kuyi hakuri wlh waya tace ya fadi nandai yayi ta Mata dadin baki" yace yabada 5k atura maku kafin insamu  wani" suhana tace to kawai takashe wayarta.



Suhana ce ta shirya zataje m.t.n office don zatayi wellcome back din wayarta kawai sai ta hadu da abbaty yazo bank din dake kusa da wajen wato U.B.A bank numfashin sune ya kusan daukewa yayin da sabuwar soyayya ta taso gab gab gab " abbaty be yayi karfin cewa dosti kece nake gani kuwa suhana ta girgixa kanta yes nice dosti dukkan su suka fara dariya suhana harda hawaye" abbaty yace ga waje can muje muxauna mugaisa .


Sun karasa wajen bayan sungaisa abbaty yace dosti lfy Naga duk kin rame ki canxa kamanni " suhana tace ba Dole ba dosti " tace dosti nayi marking big mistake   arayuwata " nan suhana tashiga bashi labarin rayuwarta sai ga abbaty na kuka " suhana ta tayasa.


Yace kiyi hakuri dosti watarana zakiji Dadi , Zaki manta kunyi wannan rayuwar insha allahu Zan dinga taimaka Miki " yace kinyi wellcome back din " tace no yanxu zanyi ok je kiyi nima bara na cirewa baba kudi " bayan sungama  suka kuma haduwa "" abbaty ya yaba mawa Adil kudi a dunkule da kyar suhana suka karba tace zata kirasa kamar karsu rabu  .


Bayan ta dawo gda ta karbi kudin a hannun Adil dubu goma ne tayi murna sosai" wata sabuwa inji Yan caca   suhana waya take da abbaty kuma soyayya ta dawo sabuwa ta manta tana da miji kwata kwata .



*Ummu* *ruman*

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

              1⃣1⃣

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya babu ranar da suhana da abbaty basuyi waya ba " tsakanin ta da laisu inayini Ina gajiya kawai Bai ciki Kiran su ba' har yakai suhana zasu hadu da abbaty awani waje suyi hiran su ta dawo gdanta .


Yau watan laisu biyar suhana ce zaune tana tunani" tace wayyo ni Allah nikuma haka rayuwata zata kasance  da aurena Ina soyayya da wani namijin ' Ina Zan Kai wannan zunuban ya Allah sai ga hawaye a idonta'' wayyo ni suhana yazanyi Ina neman jefa kaina ga halaka'  laisu ka cuci rayuwata karabani da farin cikina kasa min bakin ciki azuciyata ' ka dakushe min rayuwata.


 Ka banxarta damu " wallahi sai Allah ya saka min gashi kasa nadawo da soyayyata ga abbaty Wanda ayanxu ji nake Zan iya mallakawa abbaty kaina sbd shaukin so da kauna .


Cikin tane yafara murdawa' ta durkushe tana wayyo Allah ' suhana ta Dade tana fama da ciwon ciki sbd sha'awa dake yawan damunta macece mabukaciya " gashi Babu miji akusa da ita '' ashekara sau biyu sukeyin kwanciyar aure da laisu Wanda shima a daddafe' sbd laisu ba cikakken lafiya garesa ba " kuma yaki ya nemi magani.


Sai yace in ya fita waje Yana jin sha'awar mace Amma in agdane Sam baya jin sha'awa!!! Suhana takance ko dai iskane ke damun ka yace shima Bai sani ba .


Wani zubin in sha'awar ta tashima suhana ta dinga kuka kenan sai kawai tasamu ruwan Lipton Tasha da zafin sa " sannan take samun sa'ida' . Tana cikin haka kawarta  ummi tashigo ' tace lfy   suhana naganki haka"" tace wallahi ummi cikina ke ciwo narasa yaxanyi da wannan ciwon cikin .


Ummi tace agaskiya suhana bazan boye Miki ba kin fara bani haushi ban taba ganin mahaukaciya irinki ba kina neman  kashe kanki da kanki Dole ne sai kin rayuwa da laisu " mutumin da Yana can ya manta da ku ' Allah kadai yasan abunda ya keyi a abujan kullum baida aiki sai faman  Kiran baida kudi to uban me yakeyi da albashin sa kuma Yana aiki a Federal.


Kai akwai alaman tambaya a alamarinsa' sannan kuma shi dutse ne da baida sha'awa yakai watahar takwas ace ba matar ka a kusa da kai' suhana tace tabbas maganar ki gskya ne ummi nima nakanyi tunani haka ace wata takwas baka tare da matar ka sannan kuma in kadawo gda baza ka taba neman taba har ka koma " gsky impossible ' laisu na tare da Mata laisu na bin Mata inba haka ba banga dalili ba' ummi tace kul karkisa wannan aranki bantala ma ya Dame ki' kibishi da kyakkyawan zato.


Suhana tayi murmushi tace ummi Babu abinda xai dameni akan laisu bakin cikina daya " baya biya Mana bukatun mu' ga Adil nan dai dai da kayan arxiki baidashi'' haka last week naje gda gun babana daya taimaka min da kudi "" kinga fada daya dinga min ' yace ba naki karatu ba nazabi laisu amatsayin karatu"" to kadan nagani daga cikin matsalan dana ke ciki sannan kuma yace kar in Kara zuwa wajensa da matsalata yamin tatas yace inje gun mahaifiyata tamin magani.


Ummi tace ya ilahi wai haryanxu baba bazai sakko ba  " sai kiciga ba da hakuri " suhana tace bakin cikina daya ummi daya daga cikin wan laisu wlh Shaye Shaye yakeyi su taba wiwi giya sannan kuma Adil na xuwa dakin su Yana ganin abunda sukeyi " haka kwanaki Ina hada wuta sai ga Adil ya zo da taba Yana cukano wuta wai zaiyi irin abun kawun sa" bakaramin duka na Masa ba. 


Ummi tace innalillahi wainnailaihi raji'un yanxu tsakani da Allah Shaye Shaye a gda sannan ga matan aure" suhana tace to Bari kiji kin San har BF kwanaki yanuna mawa adil' sai ga Adil nafadin mummyna Naga wawu wawu awayan kawunsa  , sannan kuma duk yasace min kayan kicin Dina daidai da bokati mutumin nan yasace min ban Isa in ijye Abu ba agdan nan sai ya dauke min ' nafa da mawa laisu Amma yaki daukan mataki to yazanyi da raina ummi.


Ummi dake Kan kujera ta zamo kasa tana nashiga uku ni ummulkhairi wlh suhana naji natsani maza yanxu basai a lalata Miki tarbiyan yaronki ba " Amma laisu Dan iskan mutum ne ' irin sune kesa matayen su sufada harkan karuwanci" suhana tace tabbas kuwa ummi dabadan Ina kai xuciyata nesa ba wlh daban San wani kalan rayuwa zanyi ba" kin San Allah ummi idan ciwon cikina yatashi ji nake kamar in fita waje inbi maza' ummi tace ya Allah ya Allah " ""  sai ta fashe da kuka suhana tace ummi ki ga haka kwana ki da kawun Adil yasha giyansa ya bugu kawai ya fado min daki Yana surutai na daka Masa tsawa da sauri yafice min adaki na rufe na jawo wayata na fada mawa laisu yace inyi hakuri kawai .


To kinji fa wai mijina kenan ko kishina bayayi ya barni cikin wannan banxan gdan ' me cike da kayan haushi " Amma bakomai yaje shida Allah ..


Ummi tace Anya kuwa lamarinki Babu sihiri kuwa suhana don abun yayi yawa" inba Zaki damu ba kixo muje gun wani mallamin islamiyan mu Yana taimako sosai wlh kin San Yan darika sunada baiwa " suhana tace nifa bana son bin mallamai wlh don karkayi shirka " ummi tace to wannan mallamin bahaka yake ba ' suhana tace to shikenan gobe sai muje.


Washe gari sukaje gun mutumin nan suka fada Masa matsalolin duka yace da karfe biyu sukirashi bayan in andawo sallar jumma'a sukace to " da lokacin yayi suka Kira shi yace musu gskya laisu Yana bin Mata acan Abuja sannan kuma yarinyar daya ke tare da ita ta dafa ta  bashi yaci sai yadda tayi dashi '' in kuna so za aiya karkato kansa gare ki Amma kudin aikin dubu shabiyar' suhana tace azuciyarta Ina Naga wannan kudin' ummi tace to kinji


Haka suka Kara zuwa wajen wani shima yace laisu yayi aure acan Abuja kuma matan tarabaku dashi ta mallake sa ' kuma duk kudinsa ita takeci' kuma kwanan nan zai sayi wata sabuwar mota Mai kyau " suhana dai duk xuciyarta adagule shima kudin aiki dubu goma .


Haka suka dawo gda suna tattaunawa akan in sun Sami kudi zasu koma .


Suhana na zaune tana tunani abbaty ya Kira ta" yace gimbiyar Mata y kike yau na wuni da tunanin ki tace kai haba .


Yace yeah na tashi kalau beastie cinyar sa maganin Mai hadama, samun ki arxiki ne, don ke din duukiyace kinfi komai don kece komai. Ina godiya allahu swt ya jaddada rahmar sa agare ki, ya kuma sa kifi haka ya daukaka ki ya Kara basira. Don ke din ikon Allah ce.



Amin my sugar Ina begen ka my everything.


Abbaty yace kin rikitani duk kin sa na rude na mimmike narasa nutsuwa kada fa na tabu Amma Zan amince da tabuwa Dan samunki . Don ke duniya ce *absun* ikon Allah ce I luv u with all my hrt suhanaty .


Ina cigiyar novels Dina


Aljana ce ko mutum

Shahrazad labarin sharrin zuciya 


*Ummmu* *ruman*

NUSNIM

08064481931


Pls kudinga sharhi da comment if not Allah zandaina typing

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

          1⃣3⃣

Iyayen da abokanan arxiki hankulan su atashe da batar suhana' sai ayanxu baban suhana yake daya sanin abunda yayima Yar tasa naki sauraronta dajin damuwanta' ummi ne taga letter da suhana ta ijye tayi saurin dauka tana nuna mawa su mama tace da alamun suhana ce ta ijye' mama tace karanta muji kowa na wajen Yana so yaji.


Ummi ta fara karantawa kamar haka, da farko Ina baku hakuri yan'uwa na ' bazan iya cigaba da rayuwa cikin kuba ' naso ace ma Allah ya dauki Raina ' sbd xuciyata tagaji da daukan bakin ciki dab take data fashe,  mama ki Kara rokan min gafara gun babana hakkin sane ke Bina yau Dana bi abunda yace akan zabin daya min"  bazan fuskanci wannan rayuwan ba '" nayi Dana sani arayuwata Amma ba laifina ne ba" duk so ne yaja min da alkwari " Wanda ayanxu ya gushe azuciyata.


Laisu ya wahalar Dani ya cutar Dani Yan uwansa ma sun cutar Dani ' na fuskanta kalu bale agdan aurena "" mamana kiyi hakuri naki fada Miki kalan rayuwar da nakeyi agdan aure na gudun kar kisa damuwa azuciyarki " mama Ina rokanki da ki rike min Dana Adil awajen ki don Babu Wanda ya cancanta ya rikesa sai ke ' sbd uban sa ma baida mu da shi ba" sannan ummi kawata Ina Kara gode Miki kinyi namijin kokari akaina wajen nuna min kuskuren danayi na amincewa laisu" alokacin duk so ya rufe min ido .


Kai kuma laisu kaje kaida Allah nabarka dashi kuma baza ka Kara samun macen daxa ta taba zama da kaiba Kamar ni" sai kabi umurnin mahaifiyarka nason Kara auren Yar gdan masu kudi' kuma Ina so ka gaggauta ijye min takardan sakina gun iyayena.


Maryam kanwata ga Adil danki ki kulan min dashi kibashi hakurin rashina.


Saduwan alkhairi Yan uwana. Gaba ki dayan su kuka sukeyi harda laisu Wanda nadama ta lullubesa da tausayin hafsat suhana ' haka mama ta tsuguna tana kuka kamar karamar yarinya tana fadi hafsat Dan Allah ki dawo garemu rashinki babban illane agare mu, mama ta kalli laisu tace mugu azzalumi kawai sai ka girba abunda ka shuka wlh kuma ga gaggauta sakar min ya in ba hakaba koto ce zata rabamu da Kai.


Ana cikin haka sai ga baban suhana yashigo asibitin shida abokin sa a mota ' ya karaso da sauri ganin mama a durkushe tana kuka' yace badai hafsat ta mutu ba " mama tace ai har gara ta mutu mu Burne ta da hannun mu akan bamu San inda take ba.


Yace banga ne maganar ki ba nan tafara bashi lbrin komai tare da Mika Masa wasikar ya karanta " sai ga hawaye a idanun baba jikin sa sai rawa yakeyi ya tashi afusace yaje gaban laisu ya cakomoshi  ya wanka Masa Mari har uku lafiyayyu " Yana fadin wlh kafito min da yata inba haka ba koto ce zata rabamu da Kai " Yana gama fadin haka baba ya fadi kasa sumamme wajen ya dauka da salati doctor ya Kara so da sauri aka daukesa akasa shi agado aka basa taimakon gaggawa.


Laisu yace nashiga uku yazanyi da hakkin mutanan nan ya Allah na tuba kaya femin.


Suhana ce ta farka daga baccin datayi Mai nauyi ' tana bude ido taganta acikin wani daki sai kalle kalle takeyi alamun tayaya tazo nan ' sai ta danyi tunani ' hajiyar shaxee ce tashigo dakin ganin suhana ta tashi sai ta Mata murmushi tace har kin tashi Yan Mata" suhana ta kafeta da ido don tuno inda tasan ta ' hajiyar shaxee tace kin manta nine" nice wacce na daukoki amotata don in kaiki inda Zaki sai kuma Naga kinyi bacci shine na kawo ki gdana.


Yanxu dai tashi kiyi wanka kici abinci suhana ta daga Mata Kai tace to ' hajiya ta nuna Mata toilet tashiga ita kuma ta fita don dauko Mata kayan shazee dayake yanayin jikin su daya " bayan ta fito daga wankan ta wuce wajan data ga an ajye kayan Shafa taje ta shafa " hajiya r shazee tashigo dauke da kayan da abinci  ta Mika mata kayan ta sannan tace in kin saka kayan sai kice abinci bare naje na dawo suhana tace to nagode!!! .


Suhana tana cin abincin tana fadin wacece wannan matar menene dalilinta na kawo ni gdan ta nida naso kawai mota ta bigeni in mutu in huta sai ga hawaye nabin fuskarta "  hajiya ce tashigo shazee na biye da ita abaya " hajiya tace subhanallah kukan me kikeyi Yan Mata ' shazee tace Dan Allah ki bar kukan nan zaisa kanki ciwo .


Suhana tace to " cikin sanyin murya tace ku suwaye , hajiya tace to nidai sunana hajiya ni'ima Amma Yara nace min hajiyar shaxee ' inada Yara biyar babban Dana sunan sa abdulrahman na biyun sunan sa abdulrazak na ukun sunan sa abdulmalik ' na hudun sunan ta hafsat na biyar kuma auta ta kingan ta sunanta shahrazad.


Shahrazad tayima suhana murmushi " suhana sai taji tana son shazee haka itama shazeen" hajiya tace zan so in San ke wacece da kuma asalinki don tun a asibiti Dana ganki kin ban tausayi sai naji kin shiga Raina ' kuma insha allahu zantaima keki ' suhana sai tafashe da kuka da ta tuno da lbrinta ' shazee ta rude tace Yi hakuri Yar uwa kidaina kuka in Allah ya yarda karshen damuwar kice taxo .


Suhana tayi shi tace sunana hafsat suhana ' shazee tace woow suna Mai dadi kuma sunan kudaya da adda hafsatu yayata kenan, suhana tayi murmushi ' nan ta kwashe lbrinta tunda ga farko har karshe  , har zuwa asibiti .


Me hajiya zatayi inba salati da sallallami itako shazee kuka takeyi bil hakki " yayin da suhana ma kuka takeyi ' hjya tace kiyi hakuri suhana komai yay farko Dole zaiyi karshe insha allahu karshen zamanki yazo da laisu ' kuma zakiyi karatu Zaki cika burin mahaifinki kuma' zakiyi auren gata Wanda ko wata mace zata so tasami haka' sai anan suhana ta girgixa Kai tace hajiya nagama aure arayuwata sbd duk mazan haka suke .


Hajiya tayi murmushi tace suhana ba haka suke ba suna kawai suka Tara ' Amma kowa da halin sa ' Zaki zauna awajena har sai kinyi karatu ' kuma Zan dinga bibiyar iyayenki da danki " Zan tabbatar kuma laisu ya baki takardan ki insha allahu don su laisu irin mazajen nan ne da suke Kai matayen su ga halaka ' oh Allah ' shazee tace Allah hajiya ji nake kamar naje na bindige laisu wlh ' suhana tayi murmushi tace shazee kenan " sai yanxu na lura duk Abu Mai kyau Yana da dafi me zafi .


Hajiya tace Ina bako wani abu me kyau keda illa ba inkin ce haka muma kenan muna da illa hadda ke kema tunda kema kina da kyau dukan su suka kwashe da dariya.


Rayuwa kenan suhana ta saki jikinta sosai sbd taga suna da kirki gashi duk dukiyar su Basu da girman Kai don Allah ya wadata su' sauran yaran hajya basa nan suna karatu a kasar waje ' adda hafsatu ce tayi aure sai kuma shazee dake karatu a Jami ar kasu  , ita da suhana sa'annin juna ne.


An sallame mahaifin suhana daga asibiti sun dawo gda ' gdan Basu ya zama shiru ba dadi sbd batan suhana anyi cigiyar har angaji an zuba mawa sarautan Allah ido  ' Adil yayi neman mahaifiyar sa har yagaji tun Yana kuka har ya daina koda yaushe Yana jinkin Maryam ko baban suhana sune suka maye Masa gurbin mahaifiyar sa' dama bawai yashaku da abban sa bane.


Laisu kuwa abun duniya ya dameshi yarasa Ina zai tsoma kanshi yaji dadi ' gashi matarsa na abuja ta matsa sai ya dawo " ga kuma mahaifiyarsa itama da ta Masa akan Dole sai ya aure Fatima Yar kanin ta ' ita abinda ya dameta da batan suhana!!! Ga iyayen suhana su kuma sun hura wuta sai ya Basu takardan sakin suhana . Laisu haukane ya rage bayyi ba.


Abbaty bawan Allah shima dayaji batan suhana saida yayi sati baisan inda hankalin sa yake ba  " yayan ummi shike lallashin sa ' sai sumbatu yake' Yana dostina dostina Ina Kika shiga baida aiki sai Kiran dosti ' ummi kuwa duk tawani susu ce Kamar ba itaba kullum cikin hawaye tana tunanin a Ina kawarta take .


Wasa Wasa suhana tayi wata biyu da barin gda ta Dan murje kyanta ya dawo ' ita kanta tana mamakin canxawar ta" wanka ta fito zata Shafa Mai sai ga shazee ta shigo tace ummu Adil sai yanxu kike wankan suhana tace aikuwa wlh yau kasala ke damuna  ' bayan ta shafa Mai tasaka wata doguwar riga Mai kyau' batayi kwalliya ba " shazee ta kalleta da kyau tace ummu Adil kin San Allah ba Wanda xaice kinyi aure kin haihu  " suhana tace kai haba !!! Shazee tace Allah da gaske nake ' duk Wanda ya ganki bazai su ya Kara dauke ido akanki ba sbd ke matar manya ce ' suhana tayi dariya tace kekam shazee baki rabuwa da zolaya wlh ' yau  fa muna da babbar bakuwa fa tace wacece' me sunan kice adda hafsatu ' Kai haba Allah kuwa.


To maza tashi muje kicin muhada Mata abun ci " shazee tace tab nidai bazani ba wlh don nagaji ga masu aiki can Bari asa su , suhana tace a'a kyalesu bara ni zanyi da kaina ""' shazee tace kekam baki rabuwa da aiki " to menene acikin Dan aikin bawuya fa.


Suhana ta shiga kicin ta dafa shin kafa da. Miyar kifi ga salat sannan kuma ga farfesu da ta Mata sai kuma  drinks din cocumber , gda ya gauraye da kamshi hajiya ta dawo daga aiki ta tadda gdan na kamshi " tace wake girki haka" suhana ta hango tana jera  kayan abincin ' shazee  kuma na sakkowa da sama ganin hajiya tace oyoyo hajiyar shazee kin dawo .


Suhana ma ta karaso ta Mata sannu da zuwa dukkan su ta rungume tana murmushi " ta kalli suhana tace Yan matana nasan ke kikayi wannan girkin Mai dadi ba wannan  Yar kauyen ba tana nuna shazee" sukayi dariya!! Sallamar adda hafsatu ce ya tsaida su ' da gudu shazee ta rungumeta ' tana oyoyo addata nayi kewarki , suhana ta kura masu ido tace lallai gsky kyawawa ne yaran hajiya.


Ta karaso suka zauna aka gaggaisa adda hafsatu ta Mika mawa suhana hannu tazo inda take dayake hajiya ta fada Mata komai' suhana ta karasa ta rungumeta " tace Allah y kawo Miki sauyin rayuwa kanwata natayi ki bakin ciki' kuma insha Allah bazakiyi Dana sanin zaman ki tare damu ba ' Zan tafi dake Dubai acan nake so kiyi karatun ki" shazee tace what adda Zaki dauki min ummu Adil Dina sai ta fara kukan shagwaba.



*Ummu* *ruman*

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

 *BY* *NUSNIM*

               1⃣2⃣

Haka rayuwa yaci gaba da tafiyarwa suhana da dadi Babu Dadi ' laisu yaki canxa halinsa ' har yakai rabon da suhada shimfida daya da laisu shekara biyu kenan shiko ko ajikin sa " itako kullum cikin ciwon ciki sai dai Tasha lipton da lemon tsami .


Akwai wani dawowa da laisu yayi sai Yana zaune adakin sa wajejen shida da rabi na tsafe yayin da suhana ke bicci adaki " mahaifiyar laisu tazo gdan tasa mi laisu adakin sa sai kanin sa ma yashigo ' tace laisu bara kaji nifa bani son matar ka Sam gashi Bata da kunya ga bakar kafa ' tunda ka aureta ka talauce' kanin sama yace wlh kuwa mama nima natsane ta Sam " 


Duk maganganun da sukeyi suhana na labe tana ji, shiko laisu maganganun su yabata Masa rai Ina ruwan su da matarsa " matar sa Mai hakuri da juriya .


Mahaifiyar shi taci gaba da cewa wani abun alheri ne yasa memu" laisu yace menene wannan kuma tace Ina Fatima Yar gdan kanina itace jiya harda kukan ta wai Kai take so zata aura ka kalli duk dukiyar gdansu ka kalli manyan masu kudi dake zuwa neman aurenta Amma fur yarinyar nan tace Bata son su sai Kai su kansu abun ya Basu mamaki.


Kaga kuwa idan ka aureta kamar kayi arxiki ne sbd tun ba aje ko inaba har an mallaka min gda nawa nakaina  , da makodan kudi" Ina kuma daka aureta , laisu ya kalli mahaifiyarsa yace ni gsky ummu bani da ra'ayin Kara aure har Mata uku fa ' umman sa tace mene kace " Ina ce matar ka daya  laisu yace matana biyu dayan tana Abuja acan na aureta batare da sanin kowa ba .


Suhana dake labe ta Danna wani uban Kara ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya " da gudu suka fito daga dakin Dan ganin abunda ke faruwa kwance take ko alamun numfashi Babu ajikinta ga jini dake malala ta kasanta " laisu duk yabi ya rude Yana jijjigata suhana suhana suhana Dan Allah karki mutu kibarni pls kitashi nasan bana kyauta Miki insha allahu nadaina pls kitashi ' Ina batasan ma yanayi ba .


Ya kinki meta sai hospital da sauri aka karbeta  don ceton Rai shiko laisu sai safa da marwa yakeyi' da kyar suka samu numfashinta ' Amma cikin jikinta ya xube  Wanda batasan ma tana dashi ba' likitan ya musu bayani yace gsky tana cikin matsala sosai sakama damuwa daya Yi Mata yawa ta kamu da ciwon xuciya ' sannan kuma munyi bincike sosai macece mabukaciya sbd haka sprm ya Mata illa aciki sbd Bata samun tana fitar dashi shiya haifar Mata da ciwo aciki' Wanda Allah yayi da sauran kwanan ta aduniya ' ni Karan kaina amatsayina na likita Naga jarumtan baiwan Allah nan" don amatakin data ke ciki yanxu haka bakowa ke iya rayuwa ba.


Laisu yace innalillahi wainnailaihi raji'un shikenan nakashe Yar mutane ya zanyi da hakkin suhana akaina Allah ma baxai taba barni ba' mahaifiyar laisu ita takasa magana ma sbd tunanin daya Yi Mata yawa akai ga na auren da laisu yace yayi ga kuma wannan na suhanar " dukan su sunyi tagumi sai ga mahaifiyar suhana ita da Maryam duk a rude, dayake laisu yakirasu .


Suka nufi dakin da take kwance an samata oxygen abun numfashin nan sai tayi wani irin haske alamun tazubar da jini sosai.


Maryam ta duka tana kuka tana me ya faru da adda suhana mama kalli yadda takoma " mama yakamata araba auren nan inba so muke murasa ta gaba daya ba" maman tace Maryam kenan ni Karan kaina natsani auren nan " naso arabashi Amma suhana Taki 'ni ban San wani irin so ne take ma  laisu ba,  kowa dai da tasa kalan kaddaran' Maryam ta fita afusace taje gun laisu da mahaifiyarsa " tana fadin mekayiwa Yar uwata da har akasa Mata oxygen ' kasheta kaso kayi ne" to wlh in kuka kashe min Yar uwa kuma baku da kwanciyar hankali" mugu kawai azzalumi Mai kyan Dan maciji " ta durkushe kasa tana kuka ' shiko laisu daya San Basu da gsky baice kala ba sai wuki wuki yake da idanu'.


Ummi ne tashigo asibitin cikin sauri taci karo da Maryam akasa tana kuka ga laisu tsaye shi kuma ya dafa bango' ummi tace Maryam lfy karki cemin suhana ta rasu' Maryam ta rungume ummi tana kuka itama ummi sai ta fashe da kuka ' duk abunda ke faruwa akan idon wata Mata duk tana kallon su  kuma tana jin abunda suke fada har lokacin da mama ta fito daga dakin da aka kwantar da suhana ta karaso kusa dasu Maryam .


Tana fadin menene haka kuma kuna so kutara mana jama'a ne addu ah yakamata muyi har Allah ya bata lfy " suka tashi suka shiga dakin da aka kwantar da ita suna zaune suna kallon ta likita ne yashigo dubata yace sannun ku ya Mai jiki sukace da sauki.


Mama tace likita shin me ke damun Yata ne , nan likita ya Mata bayani Kamar yadda yayi wa su laisu   mama ta fara salati tana sallallami kawai sai tafashe da kuka" ummi tace wallahi mama haka suhana take fama da ciwon cikin nan ga damuwa da yayi mata, gata da zurfin ciki bakomai zata fada maka ba" nima don Ina xuwa gdanta ne shiyasa nagane halin datake ciki. 


Suhana dake kwance ido arufe duk taji abunda likita ya fada ta runtse idanunta tana tuno dalilin xuwanta asibiti ' kawai sai ta tuno maganganun da laisu sukeyi da mamar sa . Ta rintse idanuwan ta hawaye na fita ta gefe.


 Mama tace insha allahu suhana daga yau kinbar xama gdan laisu bazai yuba da gatanki" shi kuma babanki dolensa ma ya sakko akan fushin dayake dake ' duk da Yana jin xafin kalan rayuwar da kikeyi" dama Allah y kaddara sai kin auri laisu ' dama rabon dil ne ke tsakanin ku.


Mama tace maryam ummi ku xauna ku lura da ita ni kuma bara naje gda in hada abinci suka ce to mama' bayan tafiyan mama, da jimawa kadan sai Maryam tace mawa ummi su tashi suje masallaci suyi sallah tunda tana bacci bata farka ba .


Bayan fitan su suhana ta tashi tasamu biro da takarda awajen tayi rubutu ta ajye tadauki mayafi akusa da gadon ta yafa akanta ta fito tana Dan dingishi " acan nesa ta hango laisu zaune yayi tagumi , tabi ta dayan hanyar har tafita haraban asibiti ta jingina jikin wani mota tana maida numfashi  " dai dai lokacin da wannan matar taxo wajenta' don akan idonta ta fito waje shine ta biyo bayanta don taga Ina zata' sai gashi ta tsaya jikin motan matan.


Matar ta dafatan suhana ta dago a Dan firgice sai matar tayi Mata murmushi ' tace Ina xakije Naga kin fito alhalin baki da lfy , suhana tace bako Ina tana saurin barin wajen , matar ta bita da ido , har suhana tabar asibitin , wani tunani matar tayi kawai ta shige cikin motar tabi bayanta ' ta taddata tana tafiya da kyar shine ta Mata horn tare da bude kofa " suhana taga wannan matan ne dai.


Azuciyarta tace to lfy take Bina matar tace in baza ki damu ba kishigo mota ta in kaiki inda Zaki , da Kamar baza ta shiga ba " sai ta hango mamanta tana xuwa zata shiga asibitin ," batasan lokacin datayi saurin afkawa cikin motan ba  ' matar taja motar ta suka wuce.


Bayan su Maryam sun dawo masallaci suka tarar da Babu suhana suka shiga nemanta Amma Ina Basu ganta hankalin su ya tashi sosai harda shi laisu din sai kuka suke tayi sai ga mama tashigo ta tarar da abunda ke faruwa itama nan da Yan asibitin aka shiga dubata tako'ina Amma Babu suhana , aibashiri aka Kira baban suhana dayake yayi tafiya Bai San da abunda ke faruwa ba" shima hankalinsa yatashi.


Yana son yarsa' bawai Bai sonta ba idan ya tuno da abinda ta Masa sai ransa ya baci " shima ba shiri ya gaggauta abinda ya keyi don ya dawo gda  


Nanfa gda ya rude da bacewar suhana  mama da kanta taje gaban laisu tana kuka tana me kayiwa yata har yakaita da kwanciya asibiti kuma harta bace nan nadama abunda yake Mata ya fara yawo a kwakwalwarsa "" mama tace baza ka fada min ba' idanun laisu yayi jazur mallam ya kubune yace bada Kai ake magana ' nan laisu ya fada masu hirar da sukayi da mahaifiyarsa bayan idon suhana , " shine yace Ashe suhana ta tashi daga bacci tana jin mu " sai kawai mukaji ihunta!! Nan mutanan dake wajen suka fara salati ummi tace Amma kayi asara laisu , bakasan darajan alkwari ba yadda    suhana ke son ka, kara sa abunda zaka saka Mata dashi sai aure bayan idon ta dama dalilin  dayasa kenan kake cusguna Mata ka banxatar da ita  ' to wallahi Allah bazai taba kyale ka ba " sai Allah ya saka Mata wlh Kai kuma daga yau kafara kuka da idanun ka daga yau bakai ba kwanciyar hankali .


Suhana na cikin motar matan sai tafiya suke tayi har tayi bacci matar Bata sani ba juyawan daza tayi don ta tambayeta Ina zata' kaita" sai taga tayi bacci , kawai sai ta juya Kan motan ta zuwa gdan ta dake unguwar sarki " tayi horn me gadi ya bude mata tashiga tayi parking din motarta : ta fito tabude kofan baya ta janyo suhana dayake bata da nauyi duk tabi ta bushe' sai ga wata Yar budurwa tace laa mummy yanxu Kika shigo ' .


Tace yauwa  shahrazad zo ki Dan taimaka min mufito da ita, " tayi sauri ta karaso don taga waye taga suhana ita da mummyn ta suka kamata suka shiga cikin gdan a dakin mummy aka kwantar da ita aka rufa Mata bargo " sannan suka bar dakin.


Shaxee ne ta ishe mummyn da tambaya wacece wannan mummyn tace nima ban santa ba wlh nan da i ta kwashe lbrin da tasani Wanda akayi agabanta ta fada Mata ' shaxee tace Allah sarki duk yadda akayi tana cikin matsala sosai Amma bara ta farfado sai muji ita wacece.


Kumin hakuri dawainiyar Yara ne yamin yawa bantala ga twins shiyasa 


Pls kudinga comment yin hakan shizaisa inji Dadi kuna fahimtata


*Ummu* *ruman*

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:43 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

             1⃣4⃣

Hajiya tace haba auta ' in kina son ganinta basai ki dinga zuwa can din ba ' tafiyanta can din shi yafi muna so tasamu ilimi ne ' kema din Aida badan naki karatun ba da sai kibisu ' Amma bazai yuba sbda kin kusa gamawa" shazee tace to abarta anan asata a skull din mu.


Adda hafsatu tace Ina bazan so zaman anan ba sbd watarana wani zai ganta " gwara mutafi da ita can din haka dai akayi ta lallashin shazee " bayadda ta iya hakanan ta hakura don tana son ta ummu Adil ta samu sauyin rayuwa  .


Anyima suhana passport an gama Mata komai nan da sati biyu jirgin su zai daga " suna zaune a parlo suna hira shazee tace hajy nikam wai su hamman abduls ba zasu dawo ba sunyi zaman su a u.s " hajiya tace ai abdulrahman shi Yana India yace bayan zu zai dawo ba sbd ayyuka , shi kuma abdulrazaq da  Abdul Malik sune suke u.s sunce sai sungama masters din su zasu dawo !!! Shaxee tace tabdi nikam bazan iya nesa dake ba hajiya ta.


Suhana tayi dariya tace ranar daza kiyi nesa tana nan zuwa ai" shazee tace Kamar ya bangane ba " suhana tayi dariya ganin ta Dan tsorata " ranar da zamu kaiki gdan mijin ki" shazee tace tabdi niba zanyi aure ba !! Da hajiya da suhana suka hada baki sukace dalili ?


Tace ni bana son inyi nesa da hajiyata " hajiya tace shazee Dole kiyi aure domin  aure sunna ce ta ma'aiki""" sukayi Mata nasiha domin shazee Bata son kula maza hasalima Bata da saurayi " hjy tayi fadan har tagaji .


Suhana tace sister kefa ba yarinya bace ' yanxu nida ke muna 25 yrs so ya Isa ace kifitar da mijin aure fa shaxee tace indai zanyi aure to tare dake za ahada ayi Mana , suhana tace tabdi Ashe Zaki Dade bakiyi aure ba , suhana ta tashi tabar wajen alamun ta tuno wani abu sai ga hawaye.


Kafin su suhana su tafi sai da shazee da hajya da suhana sukaje suka dauki hotuna kala kala masu kyau' suhana tayi kyau Kamar wata Yar hamshakiya ita ba fara ba ita ba baka ba " yayinda su shazee da hajiya farare ne sosai sbd su fulanin chadi ne gaba da baya , mahaifin su shazee ya rasu sanadiyan jinya dayayi ' kuma Dan kasuwa ne da kwangiloli daya ke samu ta haka arxikin sa ya bunkasa hajiya kuma likitan Mata ce a asibitin garkuwa take aiki wato inda aka kwantar da suhana" babban danta abdulrahman shi ya gado mahaifin su ta wajen kasuwan ci ' da shigo da kaya Nigeria " yayinda abdulrazaq likita ne shima abdulmalik kuma low ne shi kuma ' dukan su kyawawa don Allah ya Basu baiwan kyau ba kadan ba.



Jirgin su suhana ya daga zuwa Dubai ,ta tafi da kewar kasarta da Yan uwanta da abun kwaunarta wato Adil danta .


Bari muwaiwaya gdan su suhana muga wata wainar ake toyawa.


Mama ne ke zaune tayi ta gumi Maryam ne tace mama lfy kikayi shiru kinyi tagumi tace Maryam baza ki gane ba har yanxu ba aga suhana ba bamu sani ba tana Raye ko Bata raye" Maryam tace ki daina damuwa haka mama insha allahu aunty suhana tana lfy kuma in Allah ya yarda zata dawo garemu tana bukata addu'ar mu" baban su ne yashigo yace tabbas kuwa watarana zata dawo garemu kawai muci gaba da Mata addu'a bana fata in mutu ban saka hafsat a idona sannan in roketa gafara " Maryam tace baba kaima karka damu suhana ta Dade da yafe maka .


Maryam taci gaba da cewa baba ya zancen maganar sakin suhana da laisu har yanxu shiru" baba yace idan naje bana samun sa ko aike nayi shima bana samun sa ' mama tace nida kaina zanje wajen mahaifiyarsa don tasa danta yasaki yata" don suhana baza tayi yawo da igiyar aure ba.


Laisu ne zaune a office dinsa yayi tagumi Yana tunanin suhana Ina zaiga suhana ya roketa gafara ko ya Sami sukuni' ga matarsa ta Abuja jarababbiya ce Banda masifa ga  yawan bukatan namiji akusa da ita ko Yana office zata Kira sa sai yazo yabiya Mata bukatarta kuma dolen sa inbaizo ba ta biyo shi office din  tace anan zai biya Mata bukatar ta abun kunya abokanan sa suyi tamai dariya" gashi shi ba cikakken lfy garesa ba.


Watarana Yana zaune Yana aiki office mahaifiyarsa ta kirasa tace laisu Ina baka umurni daka sake suhana ga mahaifiyar ta agdan sunce Inna Isa da Kai insaka kasa kar musu Yar su.


Ya numfasa badan ranshi ya so ba yace  yace ya saketa saki daya" mama tace alhamdulillah tace sai ka rubuta Mata a takarda sbd shaida ' akwai kanina dake abujan zai zo ya karbi takardan " Bata jira Mai zaice ba ta tashi ta fita daga gdan .



Suhana dake kwance adakinta sai kawai taji gabanta ya fadi , sai kuma taji kamar ancire Mata wani nauyi akanta.


Laisu yashiga tashin hankali tunda ya saki suhana sai yaji ma Kamar Ankara mashi wani sonta ne sai Kiran sunan ta yakeyi " Allah sarki rayuwa kenan sai mutum baya wajen ake gane amfanin sa.


Fatima ta hura mawa iyayenta wuta akan inba a daura Mata aure da laisu ba zata iya mutuwa" iyayenta sun shiga damuwa mahaifinta ya Ciro waya ya Kira yayarshi wato mahaifiyar laisu' yayi Mata bayani !!  Cikin mintina kalilan sai gata tazo arude tana Fatima Dan Allah ki daina damuwa haka insha allahu kamar kin auri laisu ' barima kiji nasaka bikin nan" nan da wata daya sai ki fara shiri Fatima tayi saurin rungume goggonta tana murna tana godiya.


Bayan sun dawo asibiti baban Fatima yasa aka fara gyara dayan gdan sa inda zasu zauna " ita kuma maman laisu takira laisu tace Masa tana son ganin sa  yazo gda" yace lafiya mama tace inkazo zakaji.


Bari mu waiwaya *DUBAI* suhana ce zaune ita da adda hafsatu suna hira ' adda hafsatu tace ranar Monday Zaki fara zuwa skull din ' angama komai " suhana tace Amma nagode sosai adda ba abinda Zan biya ku dashi sai fatan alkhairi " adda hafsatu tace ba komai suhana burin mu kiyi karatu kisamu  sauyin rayuwa ' oh waya ga  doctor suhana " suhana tayi dariya aikuwa adda kin San burin mahaifina kenan Yana so yaga acikin ya' yansa akwai likita ' yaso Maryam kanwata tayi Amma takasa sai low ta karanta " tace ayya kin San karatun likita Yana da wahala kuma nutsuwa yake so shiyasa bakowa zai iyayi ba.


Suhana ta fara karatunta lfy' Amma nikaf take sawa sbd Bata son yin mu Amala da mutane' Yan makarantar suyi ta kallon ta " itako ko ajikinta .


Laisu ya dawo gda sakamakon matsa mashi da mahaifiyar sa tayi' Yana zaune gaban mahaifiyar sa  ' ta kallesa da kyau tace laisu dama zancen auren kune da Fatima an saka ranar aure karshen watan nan" yace what gsky mama ni bana son auren nan ' abarni inji da matsalan dake gabana" kina ga har yau ba aga suhana ba " kuma ina son matata bazan iya Kara wani auren ba " dakata laisu lokacin dakaje kayi aurenka a Abuja bamu sani ba " sbd haka ni kallon mara Mata nake maka.


Kuma kamar ka auri Fatima angama shasha kawai arxiki na binka Kai kuma kana guduwa   " dai dai da lefe an dauke maka ' kuma Bari kaji umurni ne nabaka Dole ka aure ta .zaka tsaya har ayi bikin ko kuma zaka koma daga baya sai kadawo in lokacin ya kusa" Zanyi tunani akai yayi ficewar sa Yana  share kwalla ' wannan wace kalan rayuwace take bibiyata"  ace Kamar ni za ayiwa auren Dole" Allah ka wargaza auren nan.


Suhana ce kwance tana waya da Yar uwata shazee " shaxee tace ummu Adil Dina nayi kewar ki sosai wlh " suhana tace wlh nima nayi kewar ki ' Dan Allah yaushe Zaki zo Nigeria hutu" suhana tace nida Nigeria sai nan da shekara hudu Inna Gama karatuna.


Shazee tace tabdi har sai kin gama nikam bazan iya jure rashin ganin ki ba " Zan dinga zuwa  hutu " suhana tace to ai shikenan" yauwa ummu Adil lbari Mai dadi Zan baki Amma sai kin biya " suhana tace please sister tell me Dame Zan biyaki"  Ina so ki bani Adil kyauta ' suhana tayi dariya indai Adil ne nabaki shi !! Toh nagode ingaya maki daxu da safe naje skull din su Adil nagansa har mukayi Hira dashi " suhana tace Dan Allah sister dagaske?


Wallahi kuwa , pls y Kika ganshi ya Kara wayau ko shazee tace eh gashi so cute har mukayi hotuna ma pls sister turo min hoton shi"" Amma tayaya kika gane skull din daya ke' wlh driver dinmu natura gdan ku da safe ya bi min bayan Mai kaishi makaranta" Ashe baban kine  ke Kaishi a motarshi shine ya bisu abaya yaga school kaduna science academic, shine yaxo ya fada min dayake me school din maman kawa tace shiya sa ganin sa bakmin wahala ba" suhana tace Allah sarki my Adil nayi kewarsa daya ' pls bara nashiga Whatsapp sai ki tura min.


Shazee ta turo hotunan suhana Allah Allah take ta bude taga adil dinta ' fuskan Adil ne ya bayyana Yana murmushi hannun sa rike da alawa ' taga Wanda suka dauka da shazee ka rantse da Allah ita tahaifeshi sbd hasken su daya ga hanci da idanuwa ' kawai sai ta fashe da kuka " tace Allah ya rayaka Adil Dina ya Kare min Kai ta sumbaci wayar . A haka bacci ya dauketa' har ta makara zuwa skull sauri sauri tayi ko karyawa batayi ba.


 Driver  ya ijyeta ta fito daga mota Bata Ankara ba ta bige wani mutum takardun hannun sa ya fadi ' jikinta na rawa tace I am sorry sir ya bita da idanu Yana kallon baice komai ba ' shi tsoro ma ta bashi sbd nikab din fuskarta ' ta wuce da sauri .



Maman arfat

Harney

Aunty rabi

Yayar cool

Aunty saudat

Ummy

Shona 

Zainab g.g 

Hajara b muhmd

Zahida Abdul 


Da sauran su 


Wallo kuturo kudin data fa 


*Ummu* *ruman*

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

              1⃣5⃣

Ta wuce da sauri still dai ya kura Mata ido sai murmushi yake' suhana nashiga abokiyar zamanta me suna Aisha itama Yar Nigeria ne tace hafsat kin makara fa ' suhana tace Bari kawai ' wlh ban kwanta da wuri bane 'ayya.


Bayan kwana biyu sai ga su shazee da hajiya sun kawowa su adda hafsatu ziyara batare da sanin su ba' ba karamin murna suhana tayi ba da ganin shazee  " hjy tace lallai suhana Dubai ta karbeki sosai kinga yadda Kika dawo kuwa ' suhana tace kai hjya ' ai kasar ce ma akwai Dadi yadda Kika San kar in koma Nigeria' shazee tace Kika sani ki hadu da Dan Dubai kiyi aurenki.


Gaban suhana ce yafadi ta dafa kirjin ta tace innalillahi' hjy tace lfy kuwa!! Shazee tazo ba mata ido tace ummu Adil Dina badai maganar danayi shi ya canxaki yanxu ba .


Suhana tace karki damu na tuna ne har yanxu akwai auren laisu akaina' hjya tayi murmushi ' tace Babu auren laisu akanki sai ma idda da kikeyi' ta waro ido waje tace kina nufin laisu ya sakeni hajiya tace tabbas kuwa , suhana tayi ajiyar xuciya.


Adda hafsatu tace hajiya tayaya Kika sani ' suhana ta maida kallonta gun hajiya don jin Mai zatace""  hajiya tace ranan nan Ina hospital a office Dina sai ga maman suhana tazo wajena kasan cewa ni likitan Mata ne taxo Akan daukewar al'adanta ' kallo daya na Mata na gane mamar suhana ce shine nake tambayarta anganki kuwa tace min ba aganki ba" nabata shawarori kuma taji Dadi sosai sannan ta fada min mijinki ya sakeki ' sai nace alhamdulillah.


To kinji yadda akayi suhana tayi murmushin yake taji wani iri da sakin nan,yanxu fa ita bazawara ce ko ' shazee tace shikenan kinga yanxu u are free ' Zaki iyayin wani saurayin" suhana ta kalli shazee ' sannan ta tashi ta shige daki jiki a sanyaye.


Shazee tace Anya kuwa Babu abunda ke damun suhana ?

Adda hafsatu tace kila maganar sakin nan ne ya dameta " hjya tace tabbas kuwa kin San kowa ce mace tana dandana dacin saki koda ita ta bukata a saketa to Dole sai taji Babu Dadi alokacin da aka saketa" Amma karku damu zata ware.


Shazee ta tashi tabi bayanta tasami suhana tayi tagumi tana hawaye ' da sauri ta karasa wajenta ta cire Mata hannun ta fara goge Mata hawayen tana pls sister stop cry ' suhana tace shazee yanxu na rabu da laisu na dawo bazawara ' shazee tace are you  not happy ? Suhana tace no kawai ina tunanin yanxu ya rayuwata zata kasan ce.


Shazee tace kidaina sa damuwa aranki zai iya janyo Miki wani cuta' pls ki saki ranki muci gaba da harkokin mu ' suka yi Dariya "" tare suka dawo parlo suna tsokanar juna .


Adda hafsatu tace yauwa ko kefa takwara Dan Allah ki saki ranki ' suka shiga Hira suhana ta gaya musu yadda karatun ta ke tafiya  sunji Dadi sosai don sunga tadage " hajiya tace au na manta in gaya muku my 3 sons za su dawo next week ' shazee ne tashiga ihun murna tana jin dadi" adda tace lallai su Bros abduls za adawo kenan ' hajiya tace aikuwa kinga zuwa Nigeria taka maku ko" suhana tace Allah ya dawo dasu lfy Amma nikam bazan Sami zuwa Nigeria ba sai nagama karatu na.


 Shazee tace kai suhana haka Kika tsani kasar mu ' suhana tayi murmushi tace baza ki gane bane shazee bana son intuna abubuwan da suka faru Dani arayuwata shiyasa bani son zuwa sai nagama " ki Mika min gaisuwata wajen Bros ' kice wata sabuwar sister dinsu nagaishe su' insha allahu watarana zamu hadu dasu.


Shazee tace to shikenan bazan takura ki ba ' adda hafsatu tace kenan takwara ke kadai zamu Bari agda ' Zaki iya zama" suhana tace eh adda ga masu aiki Zan iya zama " to shikenan. Kinga ma tunda baki da skull jibi' saki rakani India zanje dubo kanwar baban Yara da aka kwantar da ita acan ' ba Dan taso ba tace to shikenan adda!!! Shaxee tace laa Adda hafsatu inkinje ku nemi Bros abdulrahman Mana ' tunda Yana can " Adda  tace kayya nikam bazan Sha wahalan neman miskilin nan ba ' tunda zamu hadu a Nigeria ai shikenan .


Washe gari su shazee suka koma Nigeria "" the next day kuma su suhana suka tafi india suna sauka a airport din India sai ga motan da zai Kai su asibiti ya karaso ' Adda na gaba suhana na biye da ita abaya ' Adda har tashiga motan suhana zata shiga sai ta manta ta Yar da Yar karaman jakanta" ta juya sai ko ta hangosa acan Dan nesa " tace oh ni suhana wai Mai ke damu nane .


Tace Adda bara ta je ta dauki Jakarta ta jefar " Adda tace ok kiyi sauri " da sauri ta karasa wajen ta dauka ta dago zata wuce bata Ankara ba ta bige wani mutum da takardu a hannun sa suka zube" tace ya ilahi waini Kam lfy ta, shiko da mamaki yake kallonta ' still ya tsorata yace axuciyar sa wai meke hadasa da masu nikab din nan shifa tsoron su yakeji " dayake nikab tasa !! 


Yana tsaye ya kasa kwashewa tayi sauri ta kwashe Masa ta Mika Masa batare da ta kalli fuskarsa ba tace I am sorry sir ' ya Kara kallonta inbai manta ba yataba jin muryan nan kafin ya gama tunanin sa har ta bace Masa.


Bari mu waiwaya Nigeria gdan laisu " laisu da amaryar sa Fatima ranar da aka kaimashi Mata yasha mamakin ganin mace ita ke sarrafa namiji a gadon auren su " sannan kuma yayi mamakin dayaji amaryan bataxo da budurcinta ba " sai ya tuno lokacin daya Sami suhana ," sai ga hawaye a fuskar sa" yace axuciyar sa shi kam bayyi sa'an mataye ba sai suhana " gashi yanxu anrabashi da ita " kuka ne ke kokarin kufce Masa yayi saurin tashi ya shige toilet " yayin da ita kuma Fatima sai baccinta take tare da munshari tunda ta samu abunda ta keso.


Yayi alwala ya fito ya tada sallah : bayan ya idar   ne ya fara rokan allah days bayyana  masa suhanar shi" ya dawo mashi da ita amatsayin   matarsa  ya gama ya Shafa adduz',oin sa' sannan ya fito parlo Yana karema gdan kallo gdan mekyau da ciki da abubuwan more rayuwa don haduwa Kam ba amagana " yayi tsaki shi har ga Allah kudi yanxu baya birgesa Sam suhanar sa ce agaban sa.



Su Maryam angama degree dinsu ' Amma ba mijin aure duk masu zuwa wajenta ' Yan soyayya ne kawai daga ta musu maganar aure to sai su gudu' maman ta tace ai duk laifin baban kune gashi yanxu kingama karatun Amma Babu mijin aure' da tun lokacin da mijin ke zuwa ya barki kinyi auren da yanxu shikenan " Amma Ina yaki amincewa Yana ce sai kingama boko'' gashi yanxun Yana so kiyi aure Amma Babu mijin.


Maryam da tayi tagumi tana hawaye mama tace yanxu yaron nan mansur Dan gdan mutunci ' lokacin kina level one yaso aurenki Amma babanki kememe babanki yaki ' to gashi yanxu Babu mijin kin dawo zaman gda " Maryam tace mama kowa da tasa kaddaran " nikuma tawa kenan na rashin mijin aure " Allah sarki aunty suhana ita gata tayi auren da wuri Amma bataji dadin saba' yanxu gashinan shekara daya kenan Babu ita tana araye ko Bata raye Allah kadai ya sani " mama dake gefe itama tana hawaye!! Tace Maryam daina yimin maganar hafsat bana jin dadi idan na tuno ta" karki damu insha Allah miji zai zo Miki  nagari .suna cikin magana ummi tayi sallama tashigo mama tace kara so ummi' ta zauna kusa da Maryam ta gaida mama ta amsa ' mama tace ya na ganki haka ummi tace ' mama wlh agdane aka min maganar aure' ni kuma Babu mijin sai mutum daya kuma shi din ya haramta aguna " kuma ni tsoron aure ma nake idan natuno mazan Yan iska ne" mama tayi murmushi .


Tace  ummi kenan ai ba duka mazan suka zama daya ba " hakane mama Amma kafin kasamu na kwarai sai ansha wuya.


Maryam tace hakane aunty ummi " nima bagashiba ba mijin auren ' ummi tace aike da sauki Maryam tunda bawai kin wuce shekarunki ba " hakane Amma duk da hakan tunda nagama skull"


Mama tace ummi wanene Wanda kikace yace Yana son aurenki Amma ke bazaki auresa ba ' mama wlh abbty ne ' ni kuma bazan iya auren mijin da kawata keso ban mata halacci ba " bazan iya cin amanarsa" Maryam ne tace aunty ummi karkiyi wasa da damarki abbaty yazo ya same ni akan Dan Allah inne ma Masa matar aure sbd agdan su an hura masa ya fito da mata shi kuma suhana yaje jira" shine na bashi shawaran ya aure ki aunty ummi" karki damu koda sister ta bayyana baza tayi komai ba sai ma taji Dadi don Allah ki auresa " kinga kishiyar maman sa tana so ta Masa mugunta a hadashi aure da kanwarta kuma gashi kanwar Tata Bata da tarbiya" shine baban sa yace inhar Yana da wacce yakeso ya fito da ita inko Babu shi zai aura Masa kanwar matarsa.


Kinga ko idan kin auresa kintaimakesa sister ma zataji dadin haka sbda kin ceto abbaty da hada zuri"a mara kyau,.


Mama ma ta Mata nasiha da Bata shawarwari kuma taji dadin hakan.


*Dubai*


Adda hafsatu sunshirya " suhana ta musu rakiya zuwa Nigeria ' sai da suka shiga jirgi driver ya dawo da ita' 


Adda hafsatu sun Isa lfy " shazee tace Allah sarki my ummu Adil yanxu ita kadai aka Bari acan hafsatu tace aikuwa nima bazan Jima ba Zan koma don bana son suhana na zama ita kadai sbd ta cika tunani' hakane kam Adda ' yanxu gobe Mai gyaran gdan zasu zo ko hajiya tace eh " motocin ma gasunan duk ansiyo su sbda kin San yaran nan suncika kaidoji' Adda tace Amma dai an Sami farin motan Nan ko hajiya .


Shazee tace kai aunty ai tun ana saura sati daya aka kawo motan hamma abdulrahman " kin San  hamma inba farin mota ba bazai hauba ' sai kace Dan sarkin novel din *kutausaya*  *min* wato *king* *laisu*   *10* *white* *car*  Wanda NUSNIM ta rubuta labarin" suka kwashe da dariya.


Anshirya ko Ina na gdan yadda ku kasan za akawo wata Yar gwamna ko Ina yayi kyau" washe gari motocin driver din abdulrahman yashiga cikin farin motarsa don taro uban gidan sa' haka driver din abdulrazaq  shima yashiga motansa Mai kalan blue"" sai driver din abdulmalik  shima yashiga motarsa me kalan red ' sai kuma  su hjya  da suka shiga motar su  sai airport taro zaratan mazaje ' suna tsaye jirginsu ya sauka.


Daga nesa na hango wasu larabawan samari guda biyu suna tahowa hannun su rike da juna suna murmushi " fadan kyawunsa Bata lokaci ne' shazee ne tasaka ihu tana laa hajiya gasu hamma abdulrazaq da hamma abdulmalik" tayi saurin karasawa ta rungume su' sukace oyoyo autar hajya tace I really miss you Bros   sukayi dariya suka karaso kusa dasu hajya suka rungume junan su " Adda hafsatu tace Bros Ina big bro  yake " abdulmalik yace ku kalli can ' gabaki dayan su suka juya don kallon sa ' shazee ne da adda hafsatu suka bude baki suna kallon sa Kamar basarake ' idon sa rufe da bakin glass Yana Jan trolly dinsa " woow what a wonderful guy.


*Comment

*Ummu* *ruman*

NUSNIM

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            1⃣6⃣

Idonsa rufe da bakin glass Yana Jan trolly dinsa" shazee tayi saurin Kara sowa wajensa tana murna zata rungumesa yanuna Mata hannu alamun ta dakata " dayake tasan halin sa bakamar su Abdul Malik ba" sai yayi Mata murmushi yasa hannun sa akan kafadarta ya zagaye " itama tayi murmushi tace u are welcome bro' yace tanx my sis" har yau baki San kin girma ba ko" kina nan da rawan kannan naki " da haka suka Kara so wajen su hajiya " ya saki shazee yaje ya rungume hajya Yana  fadin nayi kewar ku hajiyata!!  Adda hafsatu tace hamman nice baka kauna shiyasa ko ka kalleni.


Yaja hancin ta yace fushi nake da Yar kanwata sbd ko nemana bakiyi awaya" tace srry big bro wlh nayi loosing phone Dina ne" but I am sorry bro' yace ok" hajya tace oya kushiga mu tafi gda kowa ya shiga motar sa .


Suna Isa gda kowa ya wuce part din sa, su hajiya kuma suka wuce cikin gda shazee tace hjya kinga  yadda su hamman suka dawo kuwa ' gsky hajiya ya kamata suyi aure ' karaf akunnan su Abdul Malik ya karaso da sauri ya buge Mata baki tace wayyo Allah' ta kallesa ya galla mata harara abdulrazaq yace lallai ma yarinyar nan mu Zaki fada mawa muyi aure angaya Miki munshirya yin aure yanxu ne.


Hajya tace aiko baku isaba wlh ya kamata kufito da Mata kuyi aure duk sa'annin ku daga me Yara biyu sai Mai uku' shiko abdulrahman sa'annin sa sai Mai Yara biyar " dukkan ku ko daya baku dashi' to bazaiyuba nima Ina son Inga kunyi aure " in kuma baku da Mata ne' sai anemo muku cikin yan'uwa.



Abdulrahman dake Kara sowa yace tabdi jam Allah ni hajiya kar a hadani danni Ina jin azuciyata matana na kusa Dani Ina son in Kara haduwa da kwayar da nuwanta ' magana yake Yana lumshe idanun!! 


Dukkan su binshi suke da mamakin ganin yafada kogin soyayya ' abdulrazaq ne ya dafa shi yace bro ba dai ka fada tarkon kauna ba' in ko hakane lallai yarinyar nan Mai babbar sa'ace aduniya nan" kawai yayi murmushi ya tashi ya wuce wajen cin abinci' hajiya sai washe baki take tana alhamdulillah' wacece wannan tace to min Dana 'abdulrahman din da Bai son yaji ana maganar mace yau shine yake fadin wacce yake so' lallai Kam Allah maji rokon bayinsa.


Dukkan su suna cikin murna dama dama sbd abdulrahman yakiyin aure shiyasa su abdulmalik sukaki yin aure " Adda hafsatu tace kai Amma naji Dadi wlh ,' saura ku Bros karaf idanun abdulmalik da abdulrazaq yakai Kan hoton suhana dake manne jikin bango ita da shazee ta bazo gashinta ta gefe tana murmushi beauty point dinta ya lutsa ta gefe wushiryar ta ya fito.


Dukkan su atare suka wacece wannan Mai kyau din su hajya suka kalli wajen ' tayi murmushi tace yata kenan hafsat suhana ' karaf akunnan abdulrahman dake cin abinci' aranshi yace suhana suhana wannan wani irin sunane Mai dadi .


Abdulmalik yace woow what a beautiful name suhana ',abdulrazaq yace Amma hajya naji kince yarki' tace

Eh suhana yata ce' abdulmalik yace to agaskya hajya nikam kakata ta yanke sa'a wlh nayi Mata" abdulrazaq ya daka tsalle yace wlh baka isaba Dani tafi dacewa' Nike sonta" sai rigima ya kaure  tsakaninsu kowa nacewa dashi ta dace"   abdulrahman na jin su" su shazee zuba musu ido sukayi suna kallon ikon Allah" hajiya tayi murmushi tace azuciyarta lallai Kam suhana tun yarana Basu  ganki ba Amma son shiga sonki gashi ba mutum daya har su biyu' Zan so, ace na hada jini dake Amma tayaya' shazee ne tazo gaban su tana dariya tace kai Bros akan mace kuke wannan cacar bakin'  sai ta Kara tuntsirewa da dariya tace garama kubari don matar aure ce,' dukkan su sukayi tsit tare da hadiye mugun yawon bakin ci"" nan ma ta kwashe da dariya abdulmalik yace pls sister da gaske kike ya marairaice fuska Kamar Mai Shirin yin kuka .


Adda hafsatu tace tabdi jam yanxu bros akan wannan kake Dan murya Kamar zakayi kuka'  yace wlh intakama ma zanyi kuka abdulrazaq yace konima wlh. don kalar matan Dana keso kenan " shiko abdulrahman ko kallon hoton baiyi ba.


Adda hafsatu tace suhana ba matar aure bace bazawara ce  tana da yaro daya";suka ce what yanxu wannan har tayi aure tana da yaro tabdi jam to gsky tana da jiki Mai kyau " Amma mijinta rasuwa yayi ko? Don bana mijin da zai samu wannan yace ya saketa' tace aikuwa mijinta Yana nan da ransa!!! Abdulrazaq yace to wlh wawan namijine Wanda bai San komaiba .


Hajya tace kunga kutashi kuje kuci abincin ku kunga abdulraham har yagama cin nashi" sai a lokacin suka tuna basuci abinci ba' dukkan su suka tafin Kan daining table don cin abinci.


Abdulrahman yace nikam bara naje na kwanta na huta tace to shikenan' ya kalli su abdulrazaq yace ku kuma kuxauna kuna fada Kan macen da Bata San daku ba illa ta raba  kanku " Yana gama fadin haka yayi wucewar sa""" abdulrazaq yace wlh hajya sonta nake kuma aurenta zanyi abdulmalik ma yace tabdi hajya ni nariga cewa Ina sonta ' kuma nikam Naga Mata ' suna cikin hakane suhana takira shazee ' sunanta ke yawo Kan screen din wayan shazee tace Yar halas Taki ambato  ta daga tare da fadin my sister suhana my ummu Adil ' queen of our house suhana ta kyalkyale da dariya tace yau kuma wani irin sabon salo ne" naji ki cikin farin ciki ne, menene sirrin.


Tace ba Dole kijini cikin farin ciki ba zaratan samarin gdan mu sun dawo yanxu haka muna tare dasu " abdulmalik Yana nuna mawa shazee hannu data sa wayan a speaker yaji muryanta itako Taki saima dariya da takeyi.


Suhana tace pls shazee my regards to them ok I will my sis" Amma zanso ku gaisa da su" abdulrazaq Yana jin ta fadi haka ya fara murna Yana ce Mata shi zata ba mawa shima abdulmalik Yana fadin haka " suhana tace I am sorry  sister wlh sauri nake inada lectures " next time zamu gaisa ki gaidan min da hajiyata da adda kicewa Adda nayi missing dinta' sannan ta kashe wayarta.


Abdulmalik yace meyasa Zaki hanani wayan mugaisa' tace wlh Bros tace wai sauri take tana da lectures zata Kira wani lokacin ' ta Miki sakon gaisuwa gun hajiya da adda " tace Adda wai tayi missing dinki "" Adda tayi dariya tace suhana kenan yarinya Mai shiga Rai insha allahu jibi' xan koma wajen ta don nima nayi missing dinta  " abdulrazaq yace shin wai wacece wannan suhanar Naga alama kuna tare da ita waje days.


Hajiya tace karku damu zakuji ko wacece.' bayan kwana biyu da dawowar su Adda hafsatu ta koma Dubai wajen " suhana tayi murna sosai ta Bata tsarabarta .


Haka rayuwa ya cigaba da tafiya yayin da suhana ke karatunta cikin kwanciyar hankali takara murjewa.



Anyi auren abbaty da ummi dukkan su sunsha kuka sbd tuno da suhana da sukayi suna ganin sunci amanarta' Maryam ne ke nuna musu basuyi laifi ba. ankai ummi gdan mijinta dake badarawa gdsne hadadde Mai kyau da tsari " dakina hudu de sai parlo biyu ko wani daki da toilet aciki gdan ya tsaru yawancin kayan gdan shiyayi" lokacin da aka kaita ummi data ga gidan kawai ta fashe da kuka tace wannan gdan da suhana ya Dace an Gina sa akan tane'  Bai kamata ni ummi inshigo gdan suhana ba Maryam.


Maryam tace kiyi hakuri aunty ummi dama Allah ya rubuta suhana ba matar abbaty bace" kuma matar mutum kabarin sa " nandai ta lallashe ta sannan kowa ya watse akabar amarya ita kadai tana kuka' har abbaty ya shigo dauke da laida a hannunsa ya ijye Mata yace gashi kici kiyi hakuri ki daina kukan nan sai kanki yayi ciwo ' sai da safe na wuce dakina yaja Mata kofa ya fice tayi ajiyar xuciya" don fitan sa dakin yafi mata Dadi don bata don hada shimfida dashi tana kunyar suhana.


Rayuwa tayima laisu zafi yanxu baya aiki ya dawo gda matarsa ta can ta biyo sa ' ya sakata agdan da suhana ta zauna' don dakyar ta zauna sbd bala'i taitayi ita baza ta iya zama a irin wannan gdan ba kuma da maxa aciki ' bayan anshawo kanta akan kudi ake jira  za acanxa mata " laisu yace Allah sarki suhana Allah ya baki hakurin zama agdan nan sai ga hawaye' wayar shi ce tayi Kara amaryar sa ce Fatima ta Kira ya daga wayan tace laisu kana inane gsky ka dawo gda Ina bukatarka don amatse nake bazan iya kaiwa anjima ba' ya cire wayan akunnan sa Yana kallon wayar haushi takaici , kawai ya kashe wayar yace wlh bazani ba sai dai ki mutu" Fatima kuwa da tajishi shiru kawai ta dauko abunda take biya ma kanta bukata lokacin tana gda ' wato gaban namiji da akayi na roba " tayi amfani da kayanta.


Baban suhana ne yakira Maryam taxo ta' yace Maryam nikam haryanxu ba Wanda yazo wajenki da son ya aureki?  Tace wlh baba Babu ko daya ni yanxo ko saurayi bani dashi : baban yayi shiru yace tashi kije Allah ya zaba abunda yafi alkhairi mama dake gefe tace amin  ' suna zaune sai ga Adil ya shigo cikin sallama ' Kamar yadda mahaifiyarsa keyi duk wani halayyan sa irin na mummyn sa ya dauko  yashigo yace. Sitti nah kina lfy wato kakarshi mace ita yake cewa sitti' mummynsa ta koya masa haka" kakan sa namiji kuma jaddi nah kana lfy duk suka amsa mashi lfy lau adil y karatu yace lfy.


DUBAI


Yau week end suna na zaune tana cin fruit sai taji kawai tana son shiga kasuwa tayi siyayya' ta tambayi Adda ta Bata kudi tasa kayanta tare da nikaf dinta ta dauki Hanan yarinyar Adda don ta rakata' sun shiga kasuwa sunyi siyayyar su zasu tafi suhana tayi tuntube zata fadi wani guy yayi saurin taro ta ta fado jikin sa idon ta a rufe don tsoro " xuba Mata ido yayi Yana kallonta yadan tsorata yace you again tayi saurin bude ido suka shiga kallo kallon yace  kike bibiyata duk inda naje sai naganki ' kinjefa xuciyata cikin tunani Anya ke mutum ce tayi gaggawan kwace jikinta dake jikinsa Bata ce mashi komai ba saima kallon sa da takeyi tana Mai kallon sani' ya daga Mata gira yace kin jefa xuciyata cikin tunani Randa nafara ganin ki ranar sonki ya darsu araina pls ke wacece ' tayi tsaki ta kwashe kayanta ' tajuya Bata ga Hanan ba sai can ta hangota taje siyan ice cream.



Kumin hakuri rasuwa aka Mana


UMMU RUMAN

*NUSNIM*

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            1⃣7⃣

Taje ta jawo hannun ta suka wuce gida ' Adda tace har kun dawo eh adda .


Suhana ta shige dakin ta ta fada Kan gado kawai fuskar mutumin nan ya fado Mata arai tace wanene wannan mutumin ' da alama Yana son ya shiga rayuwata " ni kuma ban shirya hakan ba ' to Amma yace muna yawan haduwa to aina?.


Kawai taja wani dogon tsaki ' akwana atashi Babu wuya awajen Allah saura shekara daya suhana ta gama karatun likitan ta ' yauma ta fito don zuwa kasuwa siyan kayan Shafa" kawai sukayi kicibis da wannan mutumin .


Yace ya Allah cikin harshen turanci yace wai meyasa kike son xuwa duk inda zanje ? Suhana ta kallesa da mamaki tace kai dama Kaine ?


Kai Zan tambaya meyasa kake bibiyata ? Sai yayi murmushi yace wata kila alkhairi ne ke tattare tsakanina dake shiyasa muke haduwa ' gashi kin ki kibani Daman insan ke wacece yau shekara uku kenan xuciyata tana dawainiya da sonki " a kullum addu'ata Allah ya nuna min ke, suhana taja guntun tsaki tace kashiga hankalin ka fa mallam .indai soyayyace ka makaro don xuciyata cike take da kayoyi masu suka' idan kace zaka shiga ciki Dan Dole to Ina tabbatar maka zata maka illa sosai kuma ta caccake ka .


Yayi guntun murmushi yace indai Zan samu shiga ciki ai da sauki bazan damu da caccakata daza tayi ba" sbda Kota jimin ciwo ita da kanta zatamin magani' suhana ta Kara Jan tsuki  ta nemi hanya don ta wuce  ya tare hanyan yace koda baxa ki amsa soyayyata ba pls ki bude min fuskarki nagani don Allah ' ta wurga masa uwar harara ' ya kalli kwayar idanunta da kyau yace shikenan nasan watara fuskan nan sai taxama tawa da yardan Allah.


Ta wuci tana jin haushin mutumin nan ' xuciyarta na harbawa tace wai wani irin mutumi ne wannan meyasa nake haduwa dashi ? Meyasa nake kasa sukuni idan nagansa ? Ina Mai kallon sani' Kai wanene?


Ta daura pilo akanta tana wayyo Allah wannan mutumin Yana so ya tarwatsa rayuwata ' haka ta wuni tunani sai taji kasar Dubai ta fita ranta dama tana hutu ne' tasamu Adda hafsatu tace Mata Adda Zan biki India din ' Adda tayi murna tace ko kefa dama bana son zamanki agda ke daya.


Bikine zasuje Adda tace da suhana zataje ita kuma taki shine kuma yanxu tace zata .


Washe gari suka tafi India a hotel din daza ayi bikin suka sauka amaryan kanwar kawar Adda ce tare sukayi karatu a India da adda " amaryan sunanta Priya ' anyiwa su Adda tarba ta musamman kuma ankarramasu sosai.


Amarya ce da kawayen ta uku suka xo wajen su Adda gaishesu sai sukaga suhana ' amaryan take tambayen Adda shin wannan me kyau din nan kanwar kice ?


Adda tayi murmushi tace eh kanwata ce' gsky ta birgeni abani ita taxama daya daga cikin kawayene" Adda ta kalli suhana Wanda kanta ke kasa tana zancen xuci tace Kash me ya kawoni nida ban San shiga mutane gashi banxo da nikaf Dina ba Adda ta hanani.


Adda tace suhana kinji abinda Priya tace ko tashi kibita ' Priya sai murmushi takeyi ta Kama hannun suhana suka wuce kawayen ta sai murna sukeyi don suma ta birgesu" Priya tace ki saki jikinki  tsakani da Allah muke sonki nida kasar kuma za akaini zaman aure.


Suhana ta zaro ido tace yanxu Nigeria Zaki mijinki acan yake aiki ne?


Meyasa xaki bar kasarki Mai kyau kitafi wata kasa" Priya tace sbd son Dana kema Yan Nigeria shiyasa na auri miji Dan Nigeria"


Suhana ta zaro ido waje tace you mean  Dan nigeria shine mijinki? Priya ta daga Kai alamu eh shine" sai kawai taji Priya ta Kama magana da hausa tace ' shiyasa Dana ganki naji Ina son muyi abota dake Koda naje kasar ku kixama friend Dina tunda Banda kowa sai dangin miji da kuma sister dinki .


Suhana ta hadiye miyau da kyar don mamakin jin Priya na hausa kace dashi aka haifeta" suhana tace gsky kinyi kokari kamar ba ke keyin hausan ba" Priya yace Yusuf angona shi ya koya min' .


Nan akayima suhana kwalliyan India bakaramin kyau tayiba su kansu sai data birgesu " suhana ko dadine yacika ta ganin yadda ta canxa gashi dama tana son India " aiko aka shiga shagulan biki da ita Adda hafsatu na Mata video ' wajen da aka tana da don rawa akasa ka waka *meeri* *yaar* *ki* *shadi* *hai* aiko suhana ta tashi tashiga filin rawa don tayi nata rawan aiko tayi kokari sosai abunka ga Mai so dama .


Har ango da abukanan sa suka zo Bata sani ba tana ta rawar ta' aminin angon ne ya kura Mata ido don ta burgesa da nesa yaga fuskarta ya gane ba Yar India bace Amma kuma shigar da tayi sai ka rantse ita tafi dacewa' da taxama ba India ' sai yayi murmushi' suhana da ta gaji ta dawo wajen zamanta Priya tace sannu friend Ashe kin iya rawan kasarmu ango yace angaya Miki kuka dai kuka iya rawa ' sukayi dariya ango yace sannu Yar kasar mu ya sunanki tace sunana hafsat woow sunana Mai dadi ' yakira aminin sa don su gaisa da hafsat ' Yusuf yace *A* *A* zokaga Yar kasarmu da ta birge Yan indiyawa arawa suhana tayi murmushi tare da sunkuyar da kanta kasa " A A ya karaso Yana murmushi yace aikuwa bara na ganta daga Kan da zatayi sukayi ido hudu" dashi  !!! .


Yana Mata murmushi ita kuwa ta zaro ido waje shima ya daina murmushin Yana kallon kwayar idanunta ' atake ya ganeta ita kuma ta nuna sa da Dan yatsa tace you again how comes " sai kuma ya fashe da dariya yace alhamdulillahi Kai Amma nafi kowa farin ciki ayau tunda Naga fuskar da na Dade Ina son gani" suhana ta murguda baki tare da hararansa " yace kiyi a hankali da wannan hararan kar idon  naki ya fadi.


Priya da Yusuf sukace kunsan junane' AA yace eh toh bamu sani ba Amma muna yawan haduwa nan ya Basu lbarin haduwarsu" Priya tace laa ai irin huduwar da muka dingayi da Yusuf kenan" gashi har ya kaimu gayin aure""" kuma haka zata kasan ce daku" suhana ta zaro ido waje tace  ba amin ba bana fatan haka arayuwata nagama aure har abada na tsani namiji Mai kyau mugayene bana fatan in Kara auren namiji Mai kyau nan suhana tashiga sumbatu tana hawaye " suko kallon ta suke da mamaki duk tafita hayyacinta " Priya ne ta girgizata" tace hafsat kina cikin hankalin ki kuwa meke damunki?


Sai alokacin ta dawo hayyacinta ta tashi tace ma Priya tana zuwa " tayi saurin barin wajen ta wuce dakin da aka Basu tana budewa ta fada Kan gado sai kuka mai tsuma xuciya" !!! Suko su Priya mamakin hafsat sukeyi " Yusuf yace kodai ta taba aure ne ? AA yace nima haka nake tunani Priya tace Anya kuwa donni batayi Kama da wacce ta tabayin aure ba " Amma koma menene Zan tambayi yayarta AA yace good don Allah ki tambayeta don wlh son ta nake sosai  " tace karka damu insha allahu za adace.


Haka aci gaba da gudanar da biki tundaga wannan ranar suhana ta kulle kanta adaki don bata son ganin AA Yana sata shiga wani kalan yanayi" Priya ba yadda batayi ba Amma suhana fafir Taki fitowa haka ta hakura ta kyaleta.


Shima AA ya kasa sukuni na rashin ganin hafsat din sai bikin ya fitan Masa arai ' a haka akayi biki aka watse su hafsat sun koma Dubai Bata Bari sun Kara haduwa da Priya ba sbd kar ta Mata maganar AA.


Wasa Wasa suhana ta rasa gane kanta ' sbd kullum sai tayi mafarkin ga AA Yana rokanta da ta amshi soyayyar sa ' sai kuma tunanin sa da ya addabi xuciyarta " duk dare sai tayi kuka tarasa gane kanta" yanxu hankalinta ya karkata ga iyayenta da kuma tilon danta Adil yaron da yanxu Bai wuce shekara biyar ba " sbd shazee tana yawan turo Mata hotan Adil din.


Bara mu leka Nigeria mugani'


Har yau Maryam ba mijin aure abun duniya ya dameta kasan cewa ita kadai ta rage cikin kawayenta kullum mama na Bata hakuri'' baban suma tausayinta yakeyi ' tare da kin kunyarta sbd yasan duk shi yajawo Mata wannan abun .


Ummi kuwa da mijin ta abbaty sun gaji da zaman jiran suhana " don su awawtarsu zasu jirata in ta baiyana sa abbaty ya saki ummi ya aure suhana" shiyasa ma Basu kwana daki daya" Maryam ne data fahimci haka lokacin data zo gdan ta musu kwana biyu shine tasa ka musu kwaya a lemo " sannan tabar gdan ' dalilin daya sa kenan abbaty ya kusanci ummi amatsayin matarsa' tundaga lokacin so kauna da shakuwa ya shige su ," abbaty Yana tarairayan ummi "" tun ummi najin kunya har tadainaji ta sake abunta yanxu ma haka ciki gare ta.


Laisu kuma Yana nan da jarababbun matansa sun kodar dashi har yafita hayyacin sa sbd jaraban su da masifa " don arana kowacce tana so yayi having sex da ita sau 5 5 " shi kuma ba cikakken lfy ba hakanan suke jagwalgwala shi" har ya kwanta ciwo sosai duk Kan matan ba Mai kula dashi' mahaifiyar sa ce tazo taga halin daya ke ciki sai ta saki kuka tana laisu lfya haka" Ashe haka ka koma ban sani ba' uwar gdan tasa tace yauwa baba ki tattarashi ki kaishi gdan amaryarshi tayi jinyarsa ni baida amfani awajene !!! .


Maman laisu tace mijin naki kike ma haka" tace eh mana ni nagaji dashima wlh don bai cika lfy ba gsky kije kine mama sandar girmansa lfy inba hakaba bazai Babu macen daza ta iya zama da danki' ta ja tsaki zata wuce"" laisu ya zubar da kwalla bakin cinkin abunda take fadawa mahaifiyar sa!!! Yace kije na sakeki saki uku""' tace ko ajikina Dama nagaji wlh.


Haka maman ta Kira Dan uwansa aka samo napep sukaje dayan gdan matansa " sunyi gamo da katar don matane da samari Yan iska suna holewa yayin da Fatima ke rungume jikin wani namiji tana kissing dinsa shima Yana Shafa Kan bombom din ta" karaf a idon laisu da mahaifiyar su"'' maman laisu ta fara salati tana Fatima yanxu abinda kikeyi kenan? Ashe ke Yar iskace wacce bata San darajan aure ba to wlh sai na fada mawa ubanki shiko laisu rufe idanun sa yayi ji yake Kamar ya hadiye zuciya ya mutu" Fatima tace kindade baki Kira ubana ba goggo " sbd iyayena sunsan harkan danakeyi * so ba abinda zai damesu" maman laisu ta saki baki tana kallon ikon Allah laisu ya bude idanunsa yace Fatima banyi mamakin haka ba " sbd ban samiki a budurwa ba tunda ga lokacin nagane ke wacece" dama umurnin mahaifiyata ce yasa na ke zaune dake Wanda da badan haka ba bazan zo inda kike ba" amma kije kiyi tayi duniyace ta ishi kowa riga da wando kije na sake ki saki uku ' tayi shewa don kasake ni sai Mai.


Ko kayi zaton zanyi ihu ne Kamar yadda nayi na aure ka,' to karya kake Koda can don ina son kadaicewa da Kaine narasa tayaya zanyi shiyasa na bullu da wannan hanyar " kuma tunda na sameka sai Naga Kai ba cikakken namiji bane" kawai hakuri nake dakai' to  yanxu alaka da Kai ya Kare sai abarmin gda tunda gda nane kawai sai ta Kara manna bakinta cikin na saurayinta' maman laisu zatayi magana laisu yace muje mama kawai ' maman laisu sai xubar da kwallan da ta sani takeyi a haka suka dawo gdan ta " takira abdallah take fada Masa duk abunda ke faruwa shima sai da yayi kwalla" yace kaidama laisu baka da cikakken lafiya yace eh bani dashi " maman shi tace ikon Allah shine baza ka fada amaka magani ba.


Abdallah yace nima gashi yanxu Ina fama da matsalan aure matana kullum sai tamin Gori wai iyayenta me Basu Mana ba " wai dangin mu makwadaita ne mun fi son masu kudi " abubuwa kala kala motar da babanta ya bani ta kwace kayanta harda gorin abinci take min"" anan wajen laisu yayi murmushi yace inba ka manta ba munyiwa suhana haka" duk matsalolin nan da muke ciki duk alhakin suhana ce ' abdallah yace tabbas kuwa gsky mun cuci yarinyar nan "" maman laisu ta fashe da kuka tace innalillahi hakkin ta bazai kyalemu ba inbamu nemi ya fiyar ta ba.


Suna cikin hakane sai ga iyayen Fatima  sunxo sunyi cirko cirko akansu mahaifinta ya yafara masifa anci  mashi mutunci " an wulakanta Masa yarsa' har laisu yasa hannu ya dakan Masa yarinyar sa " to wlh bazeiyu ba ga duka ga saki " maman laisu da laisu suka dinga salati ganin sharrin da Fatima ta musu zatayi magana laisu ya hanata yace kawo kaje ka bincika yarka da kyau bazan fada maka komai ba " Amma ka kasance mutum Mai adalci " ya wanka Masa Mari ' mamanshi tace dakata karka kuskura ka Kara Marin sa akan wannan mazinaciyar Yar taka' " nan fa fada ya kaure har yakai mahaifin Fatima ya kori tayarsa daga gdan data ke " dama gdan sa ne.


Maman laisu taci kuka sosai haka suka kwashe kayan mahaifiyarsa aka dawo dashi gdan su laisu na gado inda suhana ta zauna'.


Hmm rayuwa kenan wlh mubi a hankali


Hajiya ta bamawa su abdulrazaq da abdulmalik labarin wacece suhana " sun tausaya mata' sosai gashi dukkan su so suke su aureta don su nuna Mata gata da tarairaya" hajiya tace daya yayi hakuri ya barma daya Amma kowannan su yaki " shine tace to sai ku gwada sa'arku duk wanda yaci nasaran samun soyayyata to dashi za ayi wannan yace nasan ni zata zaba' wannan Ma yace nasan ni zata zaba.


Shirye shiryen dawowan suhana ake wayaga murna gun abdulrazaq da abdulmalik " yadda kuka San wata saurauniyar ingland zata zo sai shirya ko Ina akeyi duk wannan bidirin Banda abdulrahman shi dariyama suke bashi shi aganin sa hauka ce.


Suhana ana can za ayibikin yaye su shazee ne kawai ta samu damar zuwa ' anshirya komai tsaf ' angabatar da su suhana amatsayin manyan likitoci wayanda suka San aikin su sosai tare da Basu shedar zama likita " suhana ta kasance mafi kwaxo acikin su " ta samu kyaututtuka da dama " su Adda sa murna ake ' suhana tsugunnawa tayi tana  kuka yayin da ta tuno mahaifin ta " shazee tazo ta dagata suka rungeme juna ana murna suna kuka " da haka taro ya watse suka dawo gda da kyaututtukanta harda kyautar mota gida kudi duk anbata " sbd ta burge mutane.


Washe gari kuma jirginsu ya tashi zuwa Nigeria " yayin dasu abdulmalik ke jiran isowan su.



Duk Wanda baiyi comment akan shafin nan ba  to zanyi fushi



*Ummu* *ruman* 

NUSNIM

08064481931

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENAH* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            1⃣8⃣

Shazee ce tafar saukowa cikin doguwar riga hannunta rike da jakarta yayin da suhana ke biye da ita abaya itama after dress ne ajikinta tayi rolling da jan gyale 'idon ta sanye da glass hannunt rike da jaka' sai murmushi take .


su abdulrazaq duk sun sake baki suna kallon ta' ashe a hoto ba kyau gareta ba " tafi haka afili" da sauri suhana tazo ta rungume hajiya   "tana oyoyo hajiyata nayi missing dinki ' shazee ma ta rungume su abdulmalik.


Suhana ta juya tace ina yinin ku bros  baki na rawa dukkan suka ce lfy lau " zasu kara magana hajiya tace kunga muwuce gda tukunnan sai a gaggaisa" suka shaga mota suka wuce gda


Suhana sai kalle kalle takeyi tana goge guntun hawayen dake xuba a idanunta har suka isa gda ' suna shig haraban gdan suhana taga gdan yayi kyau kamar ana biki   " shazee ne  takasa danne tambayarta tace   waini hjiya biki za ayi agdnnan ne naga gdan ya canxa min.


Adda tace aikuwa nima abunda nagani kenan " hajiya tayi murmushi tace wlh yayyan kune  suka shiryawa suhana walima anjuma da daddare.


Suhana tayi murmushin jin dadi wai duk ita ake mawa wannan tarban shazee tace lalle bros tun yanxu za afara nuna bajintan " adda tace ke din nan ko   !!! suhana bata gane me take nufi ba .


Suka shiga  cikin gdan hajiya tace kuje kushirya zakuje wnke kai mai kwalliya zata zo ta muku sbd time na tafiya .


Ashe su hajiya taro suka shirya ma suhana sun gayyaci yan uwa da abokan arxiki  don su faranta mata rai " bayan su suhana  sundawo sunshirya cikin wani tsadaddan lace mai kyau ' suhana tazama wata tauraruwan Mata duk inda tabi awajen taron idon su abdulmalik Yana kanta ko wannan su Yana so ya bayyana sonshi zuwa gare ta Amma sun kasa.


Suhana tasamu kyaututtuka da dama kuma sun dauki hotona da dama' harda Wanda abdulrazaq da abdulmalik suka sata a tsakiya suka dauka .


Bayan kwana biyu da dawowan suhana hajya ta tarasu a parlo don suyi magana akan haduwan suhana da iyayen ta.


Hajiya tace to alhamdulillah tunda yanxu kingama karatun ki ' burin mahaifinki yacika zakije Masa da kwalinki nazama cikakkiyar likita ' Amma naso ace da auren ki akanki zakije ga iyayenki " take anan gaban suhana ya fadi ita ta manta ma ana wani aure ' hajiya tace Adda duk zaman ku acan Dubai suhana Bata samu miji ba?


Adda tace wlh nikam iya sanina ba Wanda yazo wajenta Amma ban sani ba ko a skull din su tana dashi.


Hajiya tace suhana kina da Wanda kike so  Acan Dubai ? Suhana ta danyi shiru" hajiya tace karki damu ki gaya min ' suhana tace hajiya nikam aure baya cikin tsarin rayuwata ayanxu " bana son abunda zai Kara ruguza min rayuwata .


Abdulrazaq ne ya amshe maganar dacewa' suhana wannan ba hujja bace " ba duk mazan aka taru aka zamo daya ba karkiyi la akari da abunda laisu ya Miki  dama  haka halinsa yake ' akuma Bai kamata kici gaba daxama ba aure ba iyayenki baza su so haka ba" mutuncin ya mace dakin mijinta so kiyi hakuri ki manta da abunda ya wuce ki bude zuciyarki kiyi sabuwar rayuwa " insha allahu Zaki Dace da miji nakwarai kuma abun alfahari.


Suhana taji dadin maganganun sa sosai harda su hajiya ma " abdulmalik yace to yausheni kike so musada ki da iyayenki tace Ina son Nanda 1month ' hajiya tace shikenan Allah ya kaimu lokaci.


Bayan wani lokaci  Abdul Malik ne yaje dakin Dan uwansa abdulrazaq ' ya ganshi kwance Yana tunanin ta Ina zai bulluwa suhana cewan Yana sonta da aure" kuma ga kanin sa ma na sonta' abdulmalik ne ya dafashi yace Bros lfy kake tunani ' yace ba komai " abdulmalik yayi murmushi yace bawani nan Bros nasan kana tunanin suhana ce .


Dama nazo in fada maka na hakura da son suhana ' nima jiya nayi gamo da matar aurena wacce atake naji sonta ' har naje gdan su mungaisa da iyayenta"" aiko abdulrazaq ya rungume Dan uwansa Yana murna Yana Masa godiya .


Yace ka fada mawa hajiya yace ban fada Mata ba nabari ne in fara fada maka tukunna" yace tanx Bros tashi muje gun su hajiya "


Abdulrazaq ya fayyace masu komai su hajiya sunyi murna sosai shazee tace hamma  abdulrazaq sai ka bayyana mawa suhana kana sonta kafin lokaci ya kure maka wani ya maka shigan sauri " hajya tace aikuwa.


Yau da yamma suhana tace ado tana zaune a parlo ita kadai don su hajiya sun fita ita da shazee abdulmalik ne ya kaisu '  abdulrazaq yayi Mata sallama ta amsa  tana mashi murmushi' yasami waje ya zauna suka gaisa yace Mata Ina abokiyar hiran Taki ce " tace wlh sun fita da hajya """ yace ok " yace dama magana nazo muyi dake inbaza ki damu ba.


Tace ok Ina jinka hamma Abdul " yace suhana tun Randa nafara karo da hoton ki naji kin mallake xuciyata " narasa sukuni har sai da na tambaya wacece ke aka fada min " Amma sbd kwarjininki nakasa xuwa in bayyana Miki irin son Dana ke Miki  kuma da aure nake sonki " kitaimakeni kibani matsugunni azuciyarki insha allahu baza kiyi Dana sani ba " ni Mai kaunar kice har abada suhana.


Suhana taja dogon numfashi ji take Kamar xuciyarta zata tarwatse ' gashi ya kafa Mata idanuwa tarasa me zata ce mashi " ita yanxu ta tsani namiji Mai kyau don gani take duk Mai kyau mugu ne"  gashi kuma baza ta iya ce mishi Bata son Shiba don sun Mata halicci sun gyara Mata rayuwarta  " kuma sun taka rawar gani gun dawo Mata da farin cikinta".


Abdulrazaq ne yace bazan matsa Miki ki soni ba kije kiyi shawara da zuciyanki " nabarki lfy,. Bayan ya wuce itama ta tashi ta ta wuce dakinta ta fada Kan gado tare da sakin kuka " tace nashiga uku ya zanyi da raina " bazan iya cewa abdulrazaq bana sonshi ba" !! Ina jin kunyarsa kuma bazan iya auren sa sbd bana sonshi.


Duk da na Hana xuciyata yin soyayya Amma sai da takumu da son wannan mutumin mai Kama da walkiya " gashi tun haduwa ta dashi a India ban sake ganin Shiba " Anya ba aljani bane Ina son sa Ina Zan gansa .


Ji tayi ance Mata wanene shi ya sunan sa tayi saurin dagowa shazee ce ta gani a tsaye tana hawaye" suhana ta fashe da kuka ' shazee tayi saurin Kara sowa  wajenta ta rungumeta tana rarrashinta.


Tace suhana ita so daya ce tal kifada mawa Yaya Abdul baki son sa akwai Wanda kike so" bazai zargeki da komai ba kuma wlh bazaiji haushi ba sbd Yaya abdulrazaq Yana saukin Kai da fahimta" sannan kuma hajiya baza ta kullace kiba ' sbd muna kiyi rayuwa Mai dadi bamu so ki koma gdan jiya " wanene wannan dakike so Kika ki fada Mana?


Nan suhana ta kwashe labarin komai ta fada Mata har haduwar su na karshe" tace ni ban San Ina son sa na sai da nadawo Nigeria nagane hakan " shazee tayi dariya tace suhana kinyi kuskuren kin bashi dama shima Allah kadai yasan halin da yake ciki don na tabbata Yana sonki sosai.


Suhana tace shazee bazan iya fada mawa abdulrazaq bana sonshi ba don wlh da kunya Zan daure in auresa a haka kila daga baya na soshi" ji sukayi ance baki isaba wlh " aiko baxan zauna da macen da Bata Sona ba .


Abdulrazaq ne ya karaso Yana murmushi suhana tazaro idanu'" shazee tace kai Yaya Ashe labe kake Mana " yace no sis wlh nazo ne ince ma suhana ta Dan dafa min indomi yunwa nakeji  naji kuna hiran shine na tsaya naji" kuma karki damu wlh


Don baki Sona bashi zaisa muji haushinki ba ni atake ma naji Allah ya cire min sonki"" sai naji nima Ina son ki dawancan mutumin " kamar yadda shazee tace kinyi wawta da baki bashi dama ba" nima nace haka.


Yanxu tayaya zamu gano sa" shazee tace to ko sunan sa baki sani ba? Suhana tayi shiru Kamar tana tunani tace na tuna ranar awajen biki naji Yusuf mijin Priya Yana ce mashi A A..


Suka Nana ta sunan da cewa A.A tofa wanene shi Amma Bari mu tambayi Adda hafsatu ta hadamu da Priya kila ita zata fada Mana wanene shi' karki damu ke mun dauke ki tamkar Yar uwan mu na jini" suhana tace nagode muku sosai sosai.


Su shazee sun fadawa hajiya komai tace Allah sarki to Kai Abdul sai ka dauki dangana " baxanyi fushi da suhana ba wai don Taki auren ka" nima bazan so shazee ta auri Wanda Bata so ba' kaga kuwa kaso mawa Dan uwanka abunda kake Soma kanka ' hakane hajiya to Allah yayi muku albarka" amin.


Abdulrazaq yaje Dubai gun Adda hafsatu ya gaya Mata komai  " taci ka da mamakin zurfin ciki irin na suhana gashi ko zurfin cikin zai hallakata kuwa" nandai takira yayar Priya ta Bata number dinta " ita kuma ta bamawa abdulrazaq din.


Bayan kwana biyu ya dawo nigeria ya Kira Priya sunyi magana tace mishi suna Nigeria " a Abuja 'amma next week zasu dawo kaduna daxama don anyiwa mijin ta canjin aiki " Abdul yace ok to Zan Bari in kun dawo sai inxo Amma ki hadani da Yusuf din " tace bara na turo maka number shi yace nagode.


Priya ta turo da number mijinta Abdul ya Kira shi yayi masa  bayani Yusuf yaji Dadi sosai ' yace magana ta waya bazai yiba kabari sai kazo wajena" yace ok.


Abdulrazaq ya dawo gda agajiye suhana da shazee a zaune suna ganin sa suka fara oyoyo hamma Abdul yace ku Kam baku girma ne oyoyo sai kace Yara " bare ma ke suhana da fa yaronki kina biye ma wannan shazee suka kyalkyale da dariya " shazee tace we are equal Yaya " bayan ya zauna suka mamayeshi suna hamma Abdul shin da akwai alamun nasara" yace insha allahu " ya  fayyace musu komai sunyi murna sosai.



Bayan sati Abdul sukayi waya da Yusuf ' yace yazo ranar gobe Yana jiransa" yace Priya tace yazo Mata da kawarta taganta " yace zaixo da ita.


Washe gari tare suka tafi harda shazee " sunyi murnan  ganin juna" " nan Yusuf yace tun ranar bikin mu abokina AA yashiga damuwa narashin ganin hafsat " har ya kwanta a asibiti baida abun fada sai hafsat naso inkira gda in fada mawa iyayensa Amma yaki bani number su" sbd bantaba zuwa gdan su ba " nima din ta dalilin kasuwanci muka hadu " bayan yaji sauki yadaina shiga mutane da abokanai " na Masa fadan yaki ji magana daya hafsat har Yana sunbatu " daya ga Ina takura Masa  ,' ya tattara kayansa ya bar kasan ban San inda yaje ba kuma yakashe layinsa ' har izuwa yanxu ban San inda AA yake ba" kullum cikin addu"ata Allah yasa Yana lfy.


Suhana da shazee sai kuka sukeyi don tausaya mawa AA" suka ce Allah y bayya na masu inda A.A yake suka ce amin .


Bayan kwana biyu hajiya tace Bari mushiga kasuwa muyi sayayyan komawar ki gda " tunda saura kwana biyu" su hajiya sunyi bajinta sosai " suhana taga tsaraban da akayiwa iyayenta tayi murna sosai harda hawayenta.


Shazee ne ta matso  kusa da suhana tace suhana inkin koma gda pls karki manta mu kinga nasha ku dake," kuma kin min promise Zaki bani Adil" suhana tayi murmushi tace my sister tayaya Zan manta ku hasalima muna tare Koda yaushe bazan iya rabuwa daku ba " pls karki damu yar'uwa Rabin jiki suka rungume juna " hajiya na kallon su gwanin Sha"awa tace aranta suhana naso in hada jini dake Amma hakan bayyi ba ,' Amma ba komai ana tare ai.


Washe gari suka  Kama hanyar zuwa gdan su   suhana abdulmalik da abdulrazaq da hajiya dasu suhana " suhana ta masu kwatan cen gdan har suka iso kofar gate din sukayi horn Mai gadi ya bude " suhana taga gdan ya canxa Mata .


Me gadi ne ya Kara so kusa da motar  su* abdulrazaq yace  Dan Allah mallam ko xaka Mana sallama da Mai gdan yace eh" aiko yashiga " yafada sakon bakin" baban suhana yace su Kara so.


Mai gadin ya masu jagora ha parlon gdan ' su Abdul  ne agaba sai hajiya abayan su sai suhana dake baya rungume da shazee don jikinta rawa yakeyi " " alhaji da yace bismillan ku suka Kara so ciki mama na ganin hajiya tace doctor yau kece a gdan mu hajiya tayi murmushi tace eh nice .


To Allah yasa lafiya " tace sai alkhairi hajiya tace hafsat ga iyayenki ki bude fuskarki " don tsoro ya hanata zuwa ta rungume iyayenta gani take babanta zai koreta" mama ta zabura wacce hafsat din ba dai suhana ta ba shazee tace mama itace.


Suhana ta fashe da kuka taje da sauri ta rungume mamanta dukkan su suka sa kuka" baban suhana Kam kasa motsi yayi akan kujera sai zufa yakeyi Yana murxa idanunsa Yana ganin Kamar mafarki yakeyi" abdulmalik dayaga haka ya karasa wajen sa ya dafa sa yace baba ba mafarki kake ba diyar kuce ta dawo gare ka " sai ya fashe da kuka yace yaki suhana cikin murna suhana ta karasa gun babanta tana murna suna kuka atare " Maryam ne da Adil sukayi sallama suka shigo ganin mutane a parlo abdulrazaq ne kawai ya amsa sallamar  ya bita da ido Yana murmushi " taga mamanta na kuka kuma taga wata ajikin babanta Yana rungume da ita suna kuka' mamane tace Maryam ga Yar uwarki can suhana ta dawo gare mu.


Maryam tasaka ihun murna tana aunty suhana aunty suhana " suhana ta dago ta rungumeta suna kuka ' Adil ne ya karasa gun sittin sa wato maman suhana Yana share Mata hawaye yace sitti na waya sa min ke kuka " tayi murmushi tace Adil din suhana yau ga mahaifiyarka nan ta dawo gare mu ' Adil yace ni mamana itace aunty Maryam " Banda maman da ya wuce ita" karaf akunnan suhana ta saki Maryam ta juya garesa tace my boy ka manta mummy dinka wacce take maka wasan Doki" Adil ya kura Mata ido baice komai ba ta karasa ta rungumesa shiko Bai rungumeta ba" don bayyadda da ita ba" suhana tace pls karkace ka mantani Adil ta sakesa sai kuma ta rushe da kuka shazee dazo tana rarrashinta pls sister is ok stop crying " da kyar ta daina kuka " Adil yayi ido hudu da shazee yace laa auntyn  chocolate ya rungumeta yace nayi missing dinki shine kika gudu kika barni don nace ki kaini gdan ku" tayi murmushi my Adil karka damu yau zaka bini gdan mu yace yes Zan biki ya hai murna don ya Saba da shazee sosai kallo ya dawo kansu da mamaki suke kallon su Amma Banda suhana dayake ita tasan alakan su' hajiya tace ikon Allah yanxu shazee Ashe kin San yaron nan ko ki fada min.


Baban suhana yace Bari mugaggaisa dai tukunna kafin muji komai' bayan sun gaisa hajiya ta fara warware musu komai tun haduwarta da suhana a asibiti har izuwa yau .


Baban suhana ya fashe da kuka da fadin nayi Dana sani arayuwata " yata kiyafe min Dan Allah ' nayi kuskure ' mama tace agaskya doctor kinyi namijin kokari ba abinda zamu ce Miki Allah ya albarkaci zuri'ar ki baki daya ya kuma Kare ki yashiga tsakanin ki da makiyan ki ' ' baban suhana tace baba na Dade da yafe maka nice ma ya kamata inne mi gafaranka ' nakin bin umurnin ka inda ace nabi umurnin ka inaga da ban fuskanci wayannan matsalolin ba ' a'a suhana komai mukaddari ne daga Allah ," haka Allah ya rubuta gashi sanadiyan hakan kinzama babban likita najinjina Miki hafsatul suhana" Allah ya baki miji nagari ' ke kuma hajiya Allah yasaka Miki da gdan aljanna ya jikan mijinki ya Kai haske kabarin sa ya albarkaci zuri'arki', hajiya taji dadin addu'oin' tace amin duk anxama daya' suhana ta hadamu munxama family.


Baban suhana ya jawo abdulrazaq da abdulmalik yace yanxu kune abokaina ko ' Ina gode muku da kuka kulan da ya'ta' dukkan ku kuna da aure? Yaranku nawa" suka Sadda kansu akasa ' hajiya tace Basu dashi wlh Allah Bai kawo Mata b " Amma yanxu abdulmalik ya samu Mata saura abdulrazaq ' baba yace ayya Allah ya Sanya alheri Kai kuma Allah ya baka Mata" budan bakin abdulrazaq yace baba wlh nima na samu Mata yanxun nan"" suka bishi da kallo suka ce a Ina kamar sun hada baki.


Ya nuna Maryam Wanda jikinta yayi sanyi da alamun itama ta amince dashi ' hajiya tayi murmushi tace alhamdulillahi yau Zan hada jini da suhana" mama ko sai washe baki take ita da baba yayin da abdulrazaq yayi saurin barin parlon Yana jin kunyar tabargaxan dayayi agaban iyaye.


Hajiya tace Allah yasa ba amata miji ba' baba yayi saurin cewa 'aiko ba amata ba' hajiya tace alhamdulillah ' suhana ta rungume Maryam tana jin Dadi tace gaskiya Maryam kinyi Dace da miji adali natayaki murna " Maryam Kam sai hawayen murna take" shazee ma ta Kara so ta rungumeta tana wellcome to our family sister ' Nandai akayi ta maida maganganu tare da nuna farin cikin juna' .


Dasu hajiya zasu tafi Adil ya makale mawa shazee Dole tare suka tafi dashi ' akabar suhana da iyayenta sun sata a tsakiya anata labarai " mama tace Maryam lallai Kam kin Dace ace duk dadewan nan da kikayi baki samu miji ba ' Ashe alkhairi ne' Ashe suhana ce zata zo Miki da miji" suhana tace wlh Maryam kinyi Dace da miji da dangin miji na Miki murna sosai nan tabasu lbarin alkhairan mutan gdan .


Anan Suma suka Bata lbarin abubuwan daya faru harda auren ummi da abbaty suhana tayi murnan sosai tace Allah sarki ummi ta cika aminiya ta kwarai wlh banji haushi don ta auri abbaty ba saima murna danayi da tserar dashi daga fadawa halaka ' gobe sai muje gdan ta ki rakani' , Maryam tace tana nan da yarta guda daya Mai suna hafsat suhana" "" suna tace woow kenan sunana akasa gsky naji Dadi wayyo dadi' '


Nan ma Maryam ta Bata labarin abunda ya faru da laisu ' suhana ta tausaya mashi kuma tace nayafe Masa duniya da lahira "" washe gari suka shirya sukaje kasuwa  " sukayi ma babyn ummi akwati daya itama ummin hakan ' sannan driver ya kaisu gdan su ummin suna shiga sukayi sallama lokacin abbaty zai tafi office ummi da small suhana sun rakoshi suna Mai bye bye " kawai sukayi ido hudu da su.



Ummu ruman


NUSNIM

08964481931

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            1⃣9⃣

Ummi ce ta kwalla Kara tace suhana shin kece ko ko mafarki nake ta shiga murxa ido shiko abbaty kasa motsi yayi " suhana ta Kara so da sauri suka rungume juna ita da ummi nan kuma kuka ya biyo baya ' Maryam ne tace mukara sa ciki don karku fadi anan garin murna.


Gaba ki dayan su suka shiga cikin parlon harda abbaty Wanda yake jin kansa wani iri sabuwar soyayyar suhana ce ta taso Masa  duk aka zazzauna ummi Kamar zata maida suhana ciki don murna ""  ummi ta tashi taje tahado kayan motsa baki ' a lokacin ne suhana tasa mu bakin magana ta kalli abbaty dake kallon ta ' tayi murmushi tace su dosti ango ya bayan saduwa ya kuma nasa me ku?


Yayi shiru Bai ce mata komai ba sai kallonta daya keyi ' can kuma yace su dosti manya shine Kika boye Mana kikasa muka shiga tashin hankali  Ashe ke ko kina can kina jin dadin ki""" kalli yadda Kika dawo Kamar ba keba' Maryam tace aikuwa kaima dai kafada da alamun tana cikin kwanciyar hankali mu ta manta mu.


Ummi ne ta amshe zancen lokacin da take Kara sowa tace bawani nan suhana baza ta taba manta damu ba muna cikin ranta bayyadda zatayi ne shiyasa" suhana tace yawa aminiya nasan ke Zaki fi fahimtata" suka kwashe da dariya .


Abbaty yace kibamu lbarin rayuwar da kikayi bayan barinki gda.


Nan suhana ta kwashe komai ta fada masu' ummi tayi kuka Maryam ma sai da takarayin  kuka ' abbaty yace nataya ki murna zama likita ' kuma ki rike su hajiya Amana don samun irin su a yanxu Yana da wahala wlh " don ba karamin taimako suka Miki sai dai Allah kadai zai saka masu.


Ummi tace suhana na Miki laifi ' zata karasa maganarta suhana tace ummi kiyi shiru ba abin da Kika min don kin auri abbaty shine kike tunanin zanji haushi' Ina kinyi kuskuren tunanin haka' Dani dake duk daya muke kuma matan mutum kabarin sa"" kuma dama Allah ya rubuta ni ba matar abbaty bace' ummi tace karki fadi haka suhana.


Zan so ki auri abbaty muxauna tare "" suhana tayi murmushi tace Allah ya tsareni inyi zaman kishi da ke ' to  Bari intakai ce Miki karkiyi tunanin har yanxu Ina son dosti" abbaty ya tsura Mata ido Yana kallonta Yana jin dacin maganar ta" ummi tace haba daddyn small suha kasa baki a maganar nan Mana ' abbaty yace nifa ba abinda Zan iya cewa kin San dai wannan tafi karfina a yanxu don wannan ba suhanar da bace " matar manya ce"" abarni da matata ummi ta isheni rayuwa tunda har an iya fadin ba a Sona" suka kwashe da dariya.


Suhana tace ban canxa ba hasalima akwai Wanda xuciyata ta mutu akan sa na rasa ya zanyi ingansa" shima nan ta Basu labarin AA "" abbaty yace gsky kinyi sakaci dosti Amma insha allahu zamu tayaki da addu'a ummi tace gskya suhana kinyi wawta yanxu ta Ina zamu fara neman AA abbaty yace ta addu'oi . Nan dai suka ci gaba da hiran su sai yamma suka bar gdan. 


Laisu yasami labarin dawowar suhana Amma ba halin yazo gareta domin kuwa Yana kwance a asibiti bashi da lfya.


Adil yanxu ya fahimci mahaifiyar sa sosai ' Amma Yana gdan su shazee " don shazee ta shagwabashi sosai yazama Dan Lele agdan" ' soyayya Mai karfi akeyi tsakanin Maryam da doctor abdulrazaq',, suhana tasamu aiki a   hospital din su abdulrazaq ' amatsayin babban likita " Amma tana zuwa hospital din barau dikko ' ranar laraba'  .



Suhana ne suke waya da shazee tace sister nayi miji fa ' suhana tace don't tell me sis " tace wlh naje dauko Adil a school   na hadu dashi shima yazo daukan yaran yayanshi'" sis kin San guy din nan ya tafi da xuciyata , yanxu so yake ya turo Amma nace Masa ya tsaya sai kin samo dream man dinki. Suhana tayi murmushi tace sis kar kice Zaki jirani gara kiyi aurenki musha biki" Kika San zanga shi ko bazan ganshi ba .


Shazee tace insha allahu Zaki ganshi kuma atare zamuyi aure to amin yar'uwa ' kinga bara naje nayi shiri Zan shiga hospital din barau dikko zanga wasu patient Dina " daga nan Zan biyu musha Hira nayi missing hajiya" shazee tace ok" suhana tace ki ijye mun Abu Mai dadi tace ok sai kinxo.


Suhana ta karasa hospital din ta shiga ward din maza tana duba su har tazo Kan wani gado sai ji tayi ance suhana ce wannan dagowan daxa tayi sai taga laisu ne ba lfy duk yabi ya lalace Babu wannan kyan daya ke dashi  " ta tsura Mai ido har ga Allah ya bata tausayi ' yace suhana Dan Allah Kiya fe min" cikin tausayin sa tace bana son wannan maganar " na riga na yafe maka Allah yafe mu gaba daya 'bata tsaya ta Kara jin maganar sa ba ta bar dakin da sauri' ta wuce office dinta sai kuka kawai takeyi domin yabata tausayi sosai sbd yadda halittansa ya canxa' Bata San lokacin da ta dauki waya ba ta Kira asibitin su abdulrazaq tace aturo da motan daukan Mara lfy zuwa barau dikko don daukan laisu!!! Ilaiko haka akayi  akazo aka tafi da laisu can ta fadawa abdulrazaq akula dashi don ciwon xuciya ke damunsa .


Su abdallah da mamansu sai mamaki sukeyi waye wannan yayi musu wannan taimako " shi Karan kanshi laisu Bai sani ba .


Da kyar suhana ta kai kanta gda don tagaji gashi Bata jin dadin jikinta " Adil ne yaxo da gudu Yana  oyoyo mummyna ' ta dagashi sama tana jujjugashi ' sannan suka zauna Kan kujera zai fara Mata Hira ' tace dakata sarkin surutu' Ina hajiya da sister yace suna sama" suhana ta wuce dakinta don tayi wanka ko taji dadin jikinta .


Bayan ta gama ta fito ta samu su hjya a parlo suna kallon taxo da saurinta ta fada Kan jikin hajiya tana hajiya nayi missing dinki ' yau two month banganki ba "; hajiya tayi murmushi tace nima haka my daugther.


Shazee tace my sis namiki mutumin ki fa tace mene shi pepper chicken da arish na Miki tace woow sis kamar kin San ko shi nake son ci " pls ki kawo min nan inci yanxu ' tace ba damuwa.


Tana cin abinci tana Basu labarin ganin laisu da tayi a asibiti ' hajiya tace kin kyauta ko bakomai mahaifin tilon danki ne' Allah ya biya ki ya saka da alkhairi anjima zamuje gaishe shi ' Adil yaga mahaifinsa.


Mutuniyar Taki ta fada Miki tayi miji kuwa eh wlh hajya' gsky nayi murna kinga yanxu sai a hada bikinta Dana hamman abdulrazaq da hamma abdulmalik.


Hajiya tace Ina aiko ba Wanda zaiyi aure sai sunjira ki sai mun gano inda AA yake  suhana tace hajiya kar ayi haka kila AA nan bazan ganshi ba nan kusa .


Kidaina fadin hakan insha allahu tare za a hada aurenku gaba daya" gobe ma Adda hafsatu zasu dawo nigeria da zama ita da mijinta' sannan gobe abdulrahman zai dawo ' shima yazo ayita da wajewa " nagaji da ganinsa haka ba aure wlh.


Suhana tace gsky Kam ya kamata Kam yayi auren nan hajiya ' .


Washe gari su Adda sun iso hakama abdulrahma: nan aka zauna ana ta Hira hajiya take bashi labari samun mijin shazee da kuma su abdulrazaq shima yayi murna hajiya tace saura Kai ' yayi murmushi yace nima saura kiris hajiya 'tace na baka nada wata daya wlh inba fito da Mata ba Zan aura maka ko wacece" .


Bayan kwana biyu da dawowan su suhana itama tazo gdan don tayi kwana biyu" ga iyayenta sun ce yakamata tayi aure yanxu" shine abubuwa ya dagule Mata lissafi.


Da misalin karfe 1 na dare   suhana ta fito parlo don Tasha ruwa kawai sai taga inuwan mutum ' sai da ta firgita tace innalillahi ' shima sai da ya firgita cikin tsawa yace wacece " suhana ta tsora ta gashi parlon ba aganin fuskar mutum duk duhu" gani yayi tayi banxa dashi kawai ya Karasa cikin xuciya ya finciko ta saura kiris ta fada jikin sa yayi saurin ja da Dan baya ' sannan ya kunna wutan parlon haske ya gauraye ' aiko sukayi 4 eyes ' cikin wata irin murya Kamar sun hada baki jiki narawa ko wanne na nuna Dan uwansa da yatsa suka ce you again ' sai ga hawaye me tattare da murmushi a fuskar suhana shi kuma ya daure fuska' yace me ya kawo ki gdan mu ' ta kasa ce mishi komai sai kawai hawaye ke fita a idanun ta "" yace ba tambayar ki nake ba ' ko kin xone ki ruguxa min Dan ragowan rayuwata da ya rage?  Shin menene alakarki da Yan gdan mu " sai anan ta bashi amsa tace alaka ta jini sosai, atsakanin mu' yayi murmushin daya fi komai ciwo.


Yace Ina rokonki da ki gaggauta barin gdan mu kafin ki tar  watsa Mana don gdan mu an Gina sa akan tafarkin soyayya Mai daurewa so you better get out' ya juya da sauri zai wuce dakinsa '" yaci karo da abdulrazaq Yana Masa kallon tuhuma.


Shi ko ya banka Masa harara ya Kara so wajen suhana sai kuka take tana nashiga uku ni hafsat abdulrazak yace shin kin sanshi ne" ta daga Kai alamun eh " yace ko shine AA din?.tace tabbas kuwa ' yace tabdi jam akwai aiki Kam.


Ummu ruman kumin uzuri abubuwa ne sun min yawa that is why 

.

*NUSNIM*

08064481931

Pls adinga sharhi.


Shamsiya nagode da data Allah ya biyaki .


Cigiyar novels Dina


*Shahrazad*

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            2⃣0⃣

Suhana tace hamma abdulrazaq meyasa bazai tsaya yaji uxurina ba " sai ta Kara fashewa da kuka ' yace kiyi hakuri ki koma daki gobe zamuyi magana da safe" tace to.


Abdulrahman Yana shiga dakin sa ya fara safa da marwa' yace shin wannan wacece ita ? Menene alakanta da da gdan nan? Ya zauna ya dafe kansa dake tsara Masa" yace ya Allah.


Suhana batayi bacci ba sbd damuwa yayiwa xuciyarta yawa " haka ma abdulrahman yaka sa bacci Yana so a amsa Masa tambayoyin sa . Amma ya rasa wa zai amsa Masa.


Shazee ne tayi sallama ta shigo dakin suhana don taga har 10 na safe Bata fito ita data Saba fitowa da wuri ' suhana ta hango tayi tagumi  da alama ma Bata San shazee ta fito ba  ' shazee ta karasa wajenta tare da dafata tana sister lfy ' suhana tayi figigit ta dawo hayyacinta tare da sauke ajiyar xuciya .


Shaxee tace sister tell me meke damun ki kinga yadda idonki yayi zuru zuru sai kace wacce ta tashi daga ciwo" suhana tace sister wlh dama ciwon na tashi da yafi min akan damuwar nan dake Shirin ruguxa min rayuwa .


Pls tell sai ta fashe da kuka tace sis naga AA " shazee ta zabura tace what sai ta fara murna " tana aina sister" duk farin ciki ya baibayeta "" suhana ta kalleta tace sis kidaina murnan nan kuka kawai xaki tayani" don AA ba Wanda ya tsana irin ni baya son ganina hasalima yace inbar musu gidan su ".


Cikin daurewan Kai shaxee tace Mata dakata sis bangane mekike nufi ba tayaya gdan nan yazama gdan su AA bamu sani ba """ suhana tace tabbas  AA yayan kine nima ban sani ba sai a Daren jiya.


Shazee ta zaro ido tace wani yayan nawa aciki kin San su ukune " suhana tayi murmushi tace babban Bros dinki" shazee tazaro ido waje tace jar uban nan" yanxu dama hamma abdulrahman dinnan ne ? Tabdi Jan " sis inda zakiji ta shawarata wlh da kin rabu dashi me zakiyi da wannan miskilin me fadin xuciya " yanxu akanshi Kika shiga wannan halin " lallai so Bai Miki adalci ba" wlh har kin ban tausayi don ko dariya hamma abdulrahman bayayi to tayaya zakiyi zaman aure dashi ?


Suhana tayi murmushin takaici tace kin bani mamaki sister nayi zaton Zaki Taya ni fighting abunda nake so " to Bari kiji duk wani miskilancin abdulrahman da rashin dariyar sa da fadin ransa duk zai daina idan Allah ya mallaka min shi Zan canxa shi" Zaki Sha mamaki ' Bari kiji nabiyun haduwata dashi  adubai lokacin daya ke son number ta na hanashi dariya yake mun wlh .


Shazee tace to shikenan zanyi murna inkin auresa Amma halinsa ne natsana" wlh" suhana tace karki damu zai canxa' shazee tace Amma abin mamaki Ina ce da Adda hafsatu kukaje bikin Priya a India " suhana tace eh wlh' shazee tace ko irin su hadu da Adda hafsatun basuyi ba' nasan da sun hadu awajen bikin dayasan tare kuke da ita" tace tabbas kuwa.


Kuma kin San menene lokacin da mukaje kasuwan Dubai nida yarinyar Adda hafsatu ai mun hadu dashi shima Amma baiga yarinyar Adda ba lokacin taje siyan ice cream " ikon Allah "  kin San da sun hadu zata shaidashi tunda sun sanshi ' , haka kukayi ta samun sabani kenan" sai gashi akaran banxa yau kun hadu Amma ba cikin farinciki ba.


 Yanxu daya ce kibar kidan nan " shi a tunanin sa ya Isa ya Kore ki ne? Suhana tace tabbas ya Isa tunda babban wa uba ne' kinga ko Yana da iko' shazee tace kanbu to wlh Bai Isa ba bara na fadawa hajiya ' suhana tace karki kuskura ki fada Mata don Allah " bana son taji zafin shi ko ta mishi fada Raina ba xai so ba' kimin alkwarin baxa ki fada ba shazee da mamaki take kallon suhana tace shikenan .


Suhana tace ko kefa ' bara nayi wanka na shirya don zani hospital " tace ok bara naje gun my boy don muma  zamu fita yawo.


Suhana tayi wanka ta shirya ta Yi break fast dinta , ta gaida hajiya ta  Mata sallama ta fito zata hau motan ta kawai suka bige juna ita da abdulrahman ' tayi saurin ja da baya" shiko ya tsaya Yana kallon ta don ya rasa abin cewa," tayi saurin cewa I am sorry " yace srry 4 your self . Bata ce kala ba ta wuce ta bude motar ta zata zauna yace dakata ' ta Dan tsaya Amma Bata juyo ba " yace Mata Ina fatan fitannan da kikayi kin tafi kenan baza ki dawo ba.


Suhana tayi murmushi mai birge masoya  ' tace Masa ban tafi ba sbd nan gdan mune  kuma Ina nan daram daam. Ta ja motan ta wuce


Kalamanta sun bashi mamaki sai yayi murmushi' ya shige ciki duk wannan abunda sukeyi abdulrazaq na kallon su ' yace Bros Naga alama suhana zata canxa ka .da naso insa baki a lamarin Amma baxan sa ba Zan xuba ido.


Taje ta duba jikin laisu da alamun Yana samun sauki abdallah da maman laisu sun nemi gafaranta Taya fe musu' sukan Dan taba hiri kadan kadan ita da laisu.


Shazee ta je gdan adda hafsatu ta fada Mata komai game da suhana da hamma abdulrahman " ta cika da mamaki" Babu inda ya bata mamaki sai a auren Priya  da  Basu hadu dashi ba tace Allah Mai iko' insha allahu zasu daidai ta' .


Bayan kwana biyu baban suhana ya Kira ta akan zancen aure' yace suhana bazan Miki Dole ba shawara Zan baki amatsayinki na Mai hankali shekaru sai tafiya kikeyi " mane man auren ki sai zuwa sukeyi akan suna neman aurenki ni kuma  nace sune mi soyayyarki tukunna shine nace bara na fada Miki tace to baba insha Allah Zan duba' baba yace in kuma Zaki koma mawa laisu ne to ' don Naga ya shiryu ba kaman daba' suhana Bata ce komai ba" ta wuce.


Ta Isa gdan su shazee xuciyarta a jagule akan maganar auren nan gashi ana so a hada auren ta da Maryam ga shazee ma tace baza tayi aure ba sai da ita'  ' ta dafe kanta akan motan ta " idonta yayi jawur.


Abdulrahman ta hango Yana zaune Yana Shan lemo yana daddanna wayansa sai murmushi yakeyi shi kadai, ta karatso wajen a fusace taja kujeran dake kallon sa ta zauna tana kallon sa ' shiko ko kallonta bayyi ba' Amma ta gefen ido Yana kallonta.


Tace AA Ina son magana da Kai sai anan ne ya dago yaga yanayin ta Kamar Bata cikin hayyacinta ' ya damu da ya ganta cikin Yana yin nan" Amma a fili ya nuna I don't care " tace Ina son in San matsayina awajen kane ' yace matsayi kuma dama kina da matsayi ne awajena ' tace kwarai kuwa ' kadaina wani boye boye  don baida amfani" .


Ya kalleta yace hafsat suhana kike ko' to Bari kiji baki da wani matsayi awajena " yanxu ba da bane' Ada na soki da zuciya daya na bibiye ki Amma kin kine ' ki jefa rayuwata cikin masifa adalilin sonki  Wanda ke awajanki ko a jikin ki' bakin menene so ba "" bakisan ya halin da mutum yake shiga idan Bai samu abunda ya ke soba' tunda daga haduwata dake a India nace na rabu dake ko kece autar Mata" so yanxu baki da wata matsayi awajena'" hasalima abunda nake so in tambaye ki me kike yi agdan mu" domin muntashi da kaunar juna mun San menene so mun San darajan so ' shiyasa zamanki agdan nan Bai kamata ba sbd ke baki San darajan so ba " ina rokanki da ki bar Mana gda" .


Duk maganganun da ya keyi a kunnan shazee' yayin da suhana sai hawaye ke fita a idanun ta' shazee ne ta Kara so itama tana hawaye' zatayi magana suhana ta dakatar da ita. Tace sis pls karki ce komai.


Sannan ta kalli AA tace AA naji kalaman ka " nagode da ka fada min menene matsayi na awajen ka' Amma Ina so ka dinga ba mawa Dan Adam uxuri kuma ka dinga bashi dama don kaji dalilin sa " da kake cewa ban San so ba" to Kaine baka San so" sbd sanin menene so naki sauraranka abaya" sbd sanin bakin cikin da so ya sani shiyasa naki sauraran ka abaya ' "" kuma bazan taba ruguxa muku gda ba insha allahu yanxu xan bar muku gdan ku "" kuma sai kayi daka sanin furta min wayannan kalaman naka' alokacin da bakin alkalami ya bushe '  ta share hawayenta' yace ba wani Dana sanin da zanyi tayi murmushi ' Adil ne yazo da gudu yace oyoyo uncle abdulrahman' dayake sun Saba dashi Yana son ya ron' ya daga sa sama yace my boy ka dawo yace yes my uncle.


Cikin tsawa suhana tace Adil zonan " sai alokacin yaga mummyn sa ' yayi saurin sauka daga jikin AA  ' ya karasa wajen mummyn Yana mumyna waya dameki Naga kina kuka' sai taji tausayin Dan ta rungumesa tace zo muje gun sitti tace tana son ganin ka' yace to mummy muje ta Kama hannun sa suka wuce " shiko sai kallonta yake da mamaki Mai ya hadata da yaron nan?


Har ta Kai wajen motan ta ta dawo baya ta dubi shazee dake hawaye " tace sister kimin alkwarin bawanda zaiji abunda ya faru pls kitaimaka kar su hajya su sani harda abdulrazaq pls na rokeki "" shazee takasa magana ta daga Mata Kai alamun ta amince " ' tace nagode sai munyi waya. Ta wuce abunta.


Shazee ta tashi ta kalli AA ta gallamasa harara ta wuce don yin magana dashi Bata baki ne. Shiko zuciyarsa sai zafi take Masa " gashi cike take da tambayoyi Amma ya rasa ya zayyi !!! .


Suhana gdan ummi ta wuce don bata so taje gda aganta cikin Yana yin nan , ummi tayi mamakin ganinta haka " tace suhana lfy kuwa ' suhana ta kwanta Kan kujeran tace ummi ki Kai Adil wajen small suhana yayi Wasa don bana son nayi magana agaban sa"" tace to ta kaishi ta dawo nan suhana ta gayama ummi komai " ummi tace suhana karkiyi saurin karaya  AA Yana sonki  karki ga laifinsa yayi ne don ya gano kina sonsa ko baki sonsa " suhana tace ummi Allah da gaske yake furta kalamansa AA baya Sona yanxu " kuma hakan nagani a kwayar idanunsa.



Ni yanxu kawai xance mawa laisu ya fito tunda yanxu ya shiryu" sbd mutum daya bazan zauna intoyewa Maryam da shazee hakkin su ba " suna so suyi aure Amma sbd ni ' sukace sai atare zamuyi kuma iyayen mu ma haka suka ce" ummi tace tabbas kuwa bare ma Maryam wlh" to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.


Da yamma suhana ta koma gdan su" mama tace yau kuma nan Kika gudo ' suhana tayi dariya tace yau Ina son inyi Hira dake mamana.


Suhana ta fada mawa mamanta ta fitar da miji Maryam tace kai haba wanene sis tace laisu Maryam ta hade fuska tace haba aunty suhana meyasa Zaki koma gdan sa" tace bakomai ra'ayina ne hakan .


Mama ta kalli yarta yace kin tabbata suhana " ba tare data kalli mamanta ba tace eh mama' sai ta tashi ta wuce daki ta rufe tana kuka' ' Maryam ta biyota taji dakin arufe.


Mama ta fada mawa baba yace Allah yasa shine mafi alkhairi '., Suhana ta Kira laisu ta fada Masa" Bata jira amsar saba ta kashe wayarta" .


Suhana na zaune adakinta mama tace Mata tayi bakuwa tana parlo tace to ganinan zuwa " aiko da ta fito sukaci karo da Khadija kawarta " suhana tayi ihun murna ta rungumeta " tace Khadija na Ina Kika boye nayi kewar ki sosai wlh naje gdan ku mamanki take cemun kina katsina wajen kanwarta" Khadija tace hmm suhana akwai labari.



Bayan sun gaggaisa suka ci abinci " suhana tajata dakinta" nan Khadija ta shiga Bata labarin rayuwarta" wlh suhana wani saurayina na damfara kudi '  " wajen miliyan daya da rabi bayan nabar hotel din da ya ka ma min naci karo da barayi suka kwace jakar kudin " shine nadawo gdan kanwar mamana hankalina atashe narasa ya zanyi" bayan kwana biyu saiga saurayina ya kawomin manyan sojojiji aka kamani sai gdan yari " saida  nayi shekara biyu a kulle Ina Agana min azaba " iyayena sunshiga kunci da damuwa Anki saki na " da taimakon wani soja aka sakeni sbd ya tausaya min " tundaga lokacin nagane duniyar nan ba komai bace ' kudi zai iya kaika ga halaka" yanxu na shiryu ' duk abubuwan da Kika San inayi ada na daina yanxuma islamiya nake zuwa" " Ina fatan Allah y fito min da miji na gari"" suhana ta tausaya mata' tace amin .


Khadija tace duk da naji labarin abunda ya faru dake Amma zanso inji abakin ki don kin San ance Waka abakin maishi tafi Dadi " tace hakane" nan suhana ta Bata labarin komai 


Har saida Khadija ta xubar da kwalla  tace da kin ba mawa AA uxiri kinji Kamar yadda ummi ta fada Miki" tace Amma Allah yasa auren laisun shine mafi alkhai agare ki tace amin.


Maman suhana taje ta fada mawa hajiya yarta suhana laisu ta fitar amatsayin miji " sannan tace itafa tana ganin ba ason ranta ta fitar dashi ba" Amma ita suhanar ta jajirce shine take so' " hajiya tace ki kwantar da hankalin ki"" ki mata addu' fatan zama lfy ' tace to shikenan ' mama tace sai a hada bikin lokaci daya don a huta " hajiya tace hakane  gobe kawunsu zasuje neman auren abdulmalik sai asa bikin nan da wata uku " itama shazee next week zasu turo "" ok Allah ya Basu zama lfy gabaki dayan su"" amin.


Hajiya tace ammafa mama kin kwace min yata kwana biyu Bata zuwa " mama tace Yar takice Kamar Mai aljanu kin zaune Zaki ga ta dawo duk suka kwashe da dariya.


Abdulrahman tun sanda abun nan ya faru ya bar kasan ".


An tsaida ranar auresu Nanda wata uku " su laisu sai murna akeyi yaso Ace wata daya akasa Amma ba yadda zaiyi " don lallaba suhana yakeyi " ko Hira Bata bashi dama yaxo wajenta ba ko awaya ma haka.


Da kyar suhana ta dawo gdan su shazee " shima din saida shazee tace inba ta dawo ba zata fada mawa hajiya dalili kuma abdulrahman din ya bar kasan ." 


Musamman hajiya ta Kira Mai gyara don gyara amare Amma na suhana daban ne ' Maryam ma ta dawo gdan suku kenan!! Lokaci sai tafiya yakeyi.


Abdulrazaq da abdulmalik da Adda hafsatu suka cewa suhana yanxu ta hakura da AA din ne " tace eh gun tsohon mijinta zata koma' Basu takura Mata ba" Amma abdulrazaq " ya sawa maganar ta ? Akwai Abu akasa kuma taki fada Masa komai"" kuma ba halin ya tambaya yayanshi' " sai kawai yace Allah yasa shine mafi alkhairi.


Yau saura wata daya biki " anata shirshirye harda Priya " haryanxu Yusuf Bai San AA wan Abdulrazaq bane " hajiya ne takira abdulrahman dake India "" tace to me bakin hali tunda kaki fitar da Mata" ga kannan ka nan zasuyi aure " ansa  ranar auren ma bakazo ba' gashi yau saura wata daya biki shima kana can " ko kayi wasu iyayen ne acan ba musani Sam baka San zaman kasar ka " ka ware kanka kaman wani Mara gaskiya to Bari gaji kayi gaggawan da wowa " inba hakaba zaka ga fushina" duk hidiman bikin yakamata ace da Kai za ayi amatsayin ka na babba Amma ka ware kanka !!! To wlh ka dawo acikin satin nan . Yace Yi hakuri hajiya Zan dawo ' ta kashe wayanta.


Washe gari ya hada kayansa sai airport ' Yana zaune suna jiran jirgi ' wani mutum yaxo ya zauna kusa dashi ' ' Kamar ance ya waiga yaga Yusuf abokin sa " yace yusuf' yausuf ya juyo yace AA cikin zaro idanu' Kaine kuwa?


AA yayi murmushi yace nine " Yusuf yace tabdi jam Amma wlh baka da kirki " daga fadan gsky sai ka gujeni AA yace Yi hakuri abokina baza ka gane bane" yanxu Ina zaka wlh Nigeria zani kannaina zasuyi aure yace ok nima can zani kasan nakoma can da zama da matana " yace ayya.


Yusuf yace yauwa Amma naji dadin ganin ka' wlh " Ina hafsat dakake so to wlh Tasha wahalan nemanka har gdana suka xo da Yan uwanta tana kuka' Ina zata' ganka "" ba irin neman da bamuyi ba "" Amma ba muganka ba" gskya hafsat suhana na sonka " AA yayi shiru azuciyarsa yace dama hafsat ta nemeni kenan tana Sona"" Anya kuwa"" Yusuf yace Amma yanxu lokaci ya kure ka bayyana alokacin da Bai Dace ba " AA yace bangane ba Yusuf yace Bari ka gani' wayar sa ya ciru yashiga wajen hotona' hoton suhana da laisu ya bayyana yace kaganta zatayi aure zata koma' gun tsohon mijinta " yashiga nuna Masa hotonan harda Wanda sukayi Maryam da abdulrazaq da shazee da nata angon Umar sai abdulmalik da amaryarsa shima " duk sunyi kyau ' haka AA ya San dare a zaune zuciyarsa na bugawa yace aure fa kace kuma da tsohon mijinta?


Yusuf yace tabbas kuwa ' sbda rashinka ta zabi ta ko mamawa mijin" AA yace dama ta tabayin aure ne??


Yusuf yace sosai ma ai yaga rayuwa suhana " " maganganunta ne ya fado Masa arai lokacin da take cewa sai kayi da kasanin abunda kamin a lokacin bakin alkalami ya bushe" Kaine baka San so ba" a dalilin wahalan so baki kula ka abaya"   gumine ya fara karyo Masa sai cewa yake innalillahi " Ina bazan yarda ba wlh.



Ni kuma NUSNIM nace da tsohuwar Zuma ake magani" me zamuyi da Kai AA tuxuru ma da Kai hahhh 


Ina son sharhi akai


*Ummu* *ruman*

NUSNIM


08064481931

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: '🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

           2⃣1⃣

Gumi ne ya fara karyo  Masa sai cewa yaake innalillahi " Ina bazan yarda ba wlh. Yusuf yace lafiyanka kuwa AA duk hankalin ka ya tashi " sai kawai AA ya fashe da kuka yace Yusuf na tafka babban kuskuren da bazan iya gyarawa ba " ya zanyi da raina pls Yusuf ayau Ina neman taimakon ka amatsayinka na abokina ' Dan Allah karka Bari suhana ta auri wani bani ba don adalilinta nayanke aure arayuwata adalilinta  nashiga tashin hankali ba kadan ba" nandai yayta surutai ' Yusuf Bai gane me yake nufi ba.


Yace AA dakata ka fahimtar dani ' Nana AA ya kwashe komai abunda yayiwa suhana' Yusuf ya kwashe shi da mari' AA ya dafa kuncin sa Yana kallon Yusuf alamun mamaki" Yusuf  yace wannan Marin da na maka na tabbata kaji zafinsa "" to haka suhana takeji aranta idan ta tuno baza ta same ka ba" kullum cikin kuka take tana rokan Allah ya bayyana Mata Kai.


Bayan ta ganka shine kamata wannan rashin mutuncin Ashe baka sonta da gaske " Ashe duk yaudara ce " AA ya matse hawayen idanun sa " yace Yusuf kaji na rantse da Allah wlh Ina sonta Randa nafara ganin ta agdan mu nayi mamaki ' ban San menene alakanta da Yan gdan mu ba' sbd karta Kara tarwatsa min rayuwata shiyasa nace ta bar gdan bawai don bani sonta ba" itace dai nake ganin Bata sona' don bayadda banyi da ita ta amince mun a Dubai Taki ' karka manta fa adalilinta na rabu da kowa nawa har Yan uwana naje na kebe a Germany don Ina son kadai cewa ni kadai' '' adalilinta na kamu da Hawan jini ' sbd bani son in bude idona inganta agdan mu saboda ciwona ' ganinta Yana Yana sa inshiga tashin hankali"" 


Randa na Mata abun nan ba ason Raina bane kawai bayadda zanyi ne gani nake Bata son" shiyasa the next day na bar kasan don nakasa sukuni.' ya fashe da kuka ya ba mawa Yusuf tausayi kayi hakuri in Allah ya yarda sai ka aureta ""AA yace tayaya matar da zatayi aure yanxu kuma kuma tsohon mijinta ' suna cikin hakane aka kirasu jirginsu zai tashi ' yace tashi muje in muje gda zamu San abunda za ayi.


Suhana ce kwance ta rasa meke Mata Dadi kwata kwata Bata son auren nan bayadda ta iya ne " shazee ne ta shigo tace sis lfy kikayi shiru alamun kina tunani " suhana ta kakalo murmushi tace bakomai' don bata son shazee ta dagota '. Shazee tayi murmushi tace sis bansan yaushe Kika canxa ba da baki son insan damuwar ki' baki dawa ta fa akusa dake sai ni" nasan baki son auren laisu kawai don ki faranta Mana ne Kika auresa " nasan zuciyarki na wajan Yaya abdulrahman " shine baki son ki dawwama cikin farin ciki ne ' karki manta Mai hali baya fasa halinsa.


Suhana tace nasani shazee ya kike so inyi " shazee tace ki amince in fadawa hajiya tsakaninki da abdulrahman " suhana tayi saurin cewa a'a shazee karki min haka baki gani agabanki yace baya suna ' idan Kika fada mawa hajiya zata sashi Dole ya aure ni" ni kuma bazan auri namijin da baya Sona ba wl"" shazee tace ai shikenan .


Su ummi ne da Priya suka shigo ' Priya tace me kuke tattaunawa kun wani kunshe a daki " sukayi dariya shazee tace sis ce ke koya min yadda Zan tarairaye angona Umar " ummi tace lallai ku amaren zamanin na baku da kunya fa " suka karayin dariya"" Priya tace kunga bara na wuce gda jirgin su Yusuf ya kusan sauka zanje in tarairayi nawa mijin sai anjima zamu dawo dashi"" suka sa shewa suna fadin Yee indiyawa sun San wani abu wai tarairayan miji' ' Priya tace ai mune muka iya soyayya ' kuma muke koya muku"" mu har a fada Mana soyayya " kun manta sharukhan ne"" Nan suka sa ihu suna shewa.


Wajejen la asar AA yashigo gdan su " lokacin su hajiya da kanwar ta rakiya da su shazee da Adda hafsatu da ummi da Maryam duk suna zaune a parlo suna kallon akwatin shazee da aka kawo masu kyau  set 6 ne kayan  cikin ya hadu sosai don Umar yayi bajinta .


Adda hafsatu ce  tace laa hamma dama kana hanya shine baka fada ba" hajiya ta zuba mashi ido taga yadda danta ya rame sosai sai ya Kare haske ' kuma ga damuwa a fuskar sa" azuciya hajiya tace innalillahi wai meke damun yaron nan ne " Anya ba mayu suka kamasa ba " shi ga zurfin ciki ga rashin son mutane ban tala kaji matsalan shi. Rakiyace tace anshiga uku abdulrahman haka ka dawo Kamar Mai ciwon kanjamau " wai baka da lfya ne' sai alokacin kowa na wajen ya kura da Raman da yayi" .


Abdulrahman yayi murmushin da yafi komai ciwo yace yafendo ai baku damu Dani ba shiyasa baza kusan meke damuna ba kunfi damuwa dasu abdulmalik ' yanxu ko mutuwa nayi bawanda zai sani" rakiya tace " toh ' Kai da kake kullum fuska a daure baka dariya ka shegen zurfin ciki ga rashin son mutane " to tayaya za ashiga sha'aninka" suku sauran Yan uwan ka suna son mutane Basu da matsala" ni gani nake ma Anya aljana Bata aure ka ba kuwa tunda haryanxu baka fito da Mata ba" sai alokacin hajiya tayi magana tace wata macece zata so wannan Mai murdadan halin "" Adda hafsatu ce tace kai yafendo da ga dawowan sa kuntasa sa agaba kuna Masa tijar ko hutawa fa baiyi ba" shazee ne taja tsaki tabar wajen ' hajya tace wannan ita dawa kuma " ummi ne tayi saurin cewa " wai don na tsunguleta ne"" shiko abdulrahman yasan dashi takeyi"" don ba karamin haushin shi takeji ba"" yanxu ta daina ganin girman sa.



Abdulrahman ya tashi ya shiga ciki yayi wanka ya fito Adda hafsatu ta hada Masa abinci yaci da kyar don bakinsa ba test' bayan ' Yana cikin cin abinci ne suhana ta shigo ta fada Kan kujera lokacin bakowa a falon sai AA dake Kan daining table Yana cin abinci ' tace wash Allah na nagaji tacire gyalen dake kanta harda Dan kwalin ta ta girgixa gashin nan" tace wash nikam gashin nan ya isheni wlh Anya baxan rage ba kuwa" sai ji tayi ance karki rage Yana Miki kyau" tayi saurin dagowa don taga waye don baza ta taba manta muryan nan ba ' ganinsa tayi Kan daining table yayi facing dinta ' gabanta ne ya fadi " azuciyarta tana innalillahi'wa'innalillahi" Bata taba tunanin zai dawo ba sbd ya Saba dadewa baixo ba.


Ya sauko ya Kara so kusa da da'ita Yana jifanta da wani irin murmushi ' itako ji tayi kamar an kafeta awajen " sai alokacin taga muguwar ramar da yayi' yace hafsat suhana amaryan AA " sai alokacin tasamu bakin magana tace excuse me  point of correction amaryan laisu zakace' ' kawai AA ya tsugunna agabanta yace suhana ki taimakeni kitaimaki rayuwata ki taimaki Yan uwana daga fadawa maraici na wlh Inna rasaki Kamar na rasa rayuwa tace' ki manta da abunda ya faru abaya " wlh Ina sonki Ina kaunar ki' sharrin zuciya ce yasa namiki haka alokacin shima din bawai don bani sonki bane  , sai gani nake har lokacin baki Sona .


Suhana tayi murmushin takaici tace bakin alkalami ya bushe AA nikam bani Sonka tsohonmijina Zan ko mama wa" dama shi yafi da cewa da rayuwata " sai daga baya nagane hakan. Batajira amsarsa ba tawucewarta ta tana share hawaye kuma tana tausayinta.


Hakika AA ta hango tsananin sonta a kwayar idanun sa " Amma kuma bakin alkalami ya bushe. Shazee duk tana kallon su batace komai ba.


AA ya dafa kansa dake ciwo Yana innalillahi yazanyi da raina na Dana mawa kaina wuka da kaina " ji yayi an dafasa " ya dago kansa abdulrazaq ne yace hamma kabani mamaki zaka kashe kanka da kanka baka dauke mu Yan uwanka ba" shiyasa baza ka iya fada Mana matsalarka ba kana ganin baza mu iya taimaka maka bane?


AA yace kuyi hakuri nayi kuskure  ' ya fashe da kuka yace abdulrazaq Dan Allah Ina son in San wacece suhana wani alaka muka hada da ita Dan Allah" abdulrazaq yace yanxu Zan fada maka wacece ita kuwa.


Nan yashiga bashi labarin suhana tundaga farko harkarshe " AA ne ya zauna sai kuka yake Kamar karamin yaro abun ba karamin tausayi ya bamawa abdulrazaq ba "" Yana fadin Allah sarki baiwar Allah " cikin zafin nama yace suhana baza ta auri laisu ba "" dama arashi nane zata auresa "" shazee ce ta karaso itama kukan take .


Tace harda mu Kan mu don muyi aure ta amince zata auresa" na tabbata da badan ni da hamma abdulrazaq da Maryam ba" da kuma iyayenta  na tabbata suhana baza tayi aure ba" suhana tana son farin cikin mutane ' shiyasa take dakushe nata farin cikin don ta faranta na mutane.


Nayi bakin ciki nayi kuka duk a son da Sona take maka" ban taba mantawa muna Hira da suhana ta ke fada min in ta aure ka sai ta canxa ka sai sai tasa ka rabu da wannan halin naka da muke korafi akai " nace Mata da ko munyi murna da tacika jaruma "" sai kuma wannan abun ya faru daka koreta daga gdan nan kuma ta hana mu fadawa hajiya don karta kullace ka.


Shazee ta tsugunna tana kuka' tace hamma na don Allah ka auri suhana kajiyar da ita dadin da akeji agdan aure ' kasata farin ciki dawwa mamme "" ka rabata da auren laisu "" kullum cikin dare Ina kallon ta tana kuka' Amma Taki Bari mu sani " sbd Bata San hankalin mu ya tashi ' gaba ki dayan su hawaye sukeyi.


AA yace insha allahu sai na aureta sai na canxa Mata rayuwa"" sai ji sukayi ance aiko baza ka taba auren yata ba' baka cancanta kazama mijinta ba" hajya ce ta bayyana aga bansu' duk fa awannan Daren ake wannan draman.  Hajya na Kara sowa tace kun bani mamaki wlh bare ma ke shazee yanxu kina ganin suhana zata auri laisu inace sai inda karfin ki ya Kare  gun hanawa Amma kin biye na suhana kun boye mun Kai kuma abdulrazaq kaima  amatsayinka na babba baza ka iya bincike da kaji suhana zata auri laisu " Kai kuma abdulrahman Banda abunda Zan ce maka illa ince maka baka auri suhana ba" sbd na Mata miji Wanda ya Dace da ita ba kaiba.



Sannan kuma baza ta auri laisu ba " bashi bane mijin daza ta aura duk no na hada wannan plan din " ni nace laisu yace zai aureta"  duk wani motsin ku na sani har koranta da kayi agdannan duk na sani na zuba ido ne Inga iya gudun ruwan ku" sai Naga Ashe dukkan ku baku da hankali har kunyi girman daza ku boye min komai." Shazee ne tayi karfin hali tace yanxu hajiya da gaske dama ba laisu xata aura ba kuma babanta ya sani " hajiya tace tabbas kuwa nida iyayenta muka shirya wannan plan din " sauran plan din kuma baza kuji ba" shi laisu ma na sa mar Masa da Mata kuma Yana sonta tana sonshi " cikin hukuncin Allah ya cire mashi son suhana tare da dangana"" na saya Masa gda inda zai zauna da matarsa dai dai da akwati ni namasa  " sai dai in Masa fatan zama lfy " insha allahu next week za adaura aurenku ku duka " alokacin zaku ga mijin suhana " ai tuni AA ya Suma don jin abunda hajyar su tace don yasan Bata magana biyu sai daya.


Shazee ne ta Ankara da hakan tasaka ihu abdulrazaq shima ya gani Yana hamma abdulrahman pls katashi wlh sai ka aureta nasan hajya Wasa takeyi"" itama hjya ta rude ai sai asibiti da gaggawa aka karbe su  da kyar aka samu numfashin sa ' aka sa Masa oxygen su shazee sai kuka sukeyi " shazee tace hajiya Dan Allah ki taimakesa ki bashi suhana" hjya tace karki sake mun magana bazai taba aurenta ba.


Doctor yazo yace da sauki jikin NASA gsky damuwa ta Mai yawa adinga kulawa sbd zai iya jawo Masa babban matsala.  Hajya tace abdulrazaq Kai ka kwana dashi mu zamu wuce' Zan turo driver ya kawo muku komai' suka wuce amota hjya take gargadin shazee karta fada mawa suhana komai" taja Mata kunne sosai " " 


Suhana na daki da kyar ta iya bacci don tunani AA take' washe gari da safe su hajya sun wuce asibiti kuma ta fada mawa iyayen suhana " since zasu zo dubashi " Amma tace kar su fada mawa suhanar  " sunce to " jikin dai da Dan sauki ba laifi" bayan kwana biyu suhana Bata Kara sa abdulrahman a idanunta ba" tace kila ya kuma barin kasan ne" sai shirye shiryen biki ake tayi yau saura kwana biyu a daura aure" har yanxu AA na hospital baya magana sai suhana kawai yake fada" itako suhana ji take Kamar Bata da lfy ga kirjinta da ke Mata zafi ' .


Yau ne mother's day da kyar akayi mother's day din don suhana da shazee kamar ba lfy " shima din hjya ce ta shirya hakan " " don sunce baza suyi party ba sai walima .


Yan uwa da abokan arxiki sun hallara gda  ya cika ' amare sunyi kyau Kamar ka sace su , da daddare shazee tasami hjya tace hjya pls ki rushe auren suhana ki aura mawa hamma pls" tace shahrazad wai Ina Wasa dake ne ki fita idona baza ta aure sa ba .


Haka shazee ta fita dakin hjya tana kuka' " da daddaren hajiya taje asibiti dubashi " Yana ganin hjya yace hajiya ki taimaka ki aura min suhana " Ina ban aure ta ba Zan mutu wlh"" tace karka damu baza ka mutu ba sannan kuma baza ka aure ta ba"  zaka samu macen da ta fita" ya runtse idanu' Yana hawaye shi yasan yadda yakeji axuciyar sa.


Washe gari mutane sun hallara wajen daurin aure ' ya'yan su " tun safe suhana ke kuka gashi Taki kwalliya sai fama ake da ita Adda hafsatu ta rasa ya zatayi ' sai ji sukayi andaura aure " su abdulmalik sai murna akeyi yayin da gaban suhana ya fadi ' itako shazee ga bakin ciki ga farin ciki ta rasa wanne zatayi " su laisu ne suka shigo gdan su shazee akace suhana ta fito a dauki hoto " ta kulle kanta a daki Taki fitowa" abdulrazaq yaje asibiti yaga hamman sai Nishi yakeyi kadan kadan yama abdulrazaq nuni da hannu ya xo wajensa" ya karasa yace Abdul andaura auren bada niba ko" Abdul ya runtse ido Yana hawaye' yace hamman kayi hakuri'' ai Bai karasa ba yaji hamman Yana salati atake numfashin sa ya dauke " ai ganin haka abdulrazaq yafara jujjugashi Yana hamman pls katashi karka Mana haka " doctor ya karaso da sauri ya dubashi yace innalillahi me aka Masa yanxu zuciyar sa tabuga atake" sai hakuri Allah ya dauki abunsa .



*Ummu* *ruman* 

NUSNIM

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

*BY* *NUSNIM*

            2⃣2⃣

Sai hakuri Allah ya dauki abunsa " abdulrazaq yace innalillahi wa'innailaihi raji'un tare da fashewa da kuka Yana hamman pls karka mutu ka kyale mu'  doctor ya rike shi Yana bashi hakuri Amma Ina Kamar zugashi akeyi  ' abdulrazaq yasa hannu a aljihunsa ya Ciro waya ya fara Kiran hajiya " wayan nata ringing Bata dauka ba " sbd hayaniyar mutane shazee ne ta hango Kiran" tace hjya ana Kiran ki fa" ta dauki wayan tare dasawa akunnan ta," .


Sai ji tayi ance hjya ya rasu ' cikin tashin hankali hajiya tace what badai hamman ba " kukan da abdulrazaq keyi ya tabbatar Mata da haka " hajiya tasa salati tana innalillahi'wa'innalillahi Allah yayiwa abdulrahman rasuwa " shazee ne ta saka ihu Wanda ya karkato hankalin Yan biki wajen su " " ta banka aguje tana suhana suhana suhana ki fito abdulrahman ya rasu adalilin rasaki.


Ita kuwa tana zaune dafe da kirjinta dake Mata zafi " sai kawai taji wannan batun Kamar a mafarki"  dai dai lokacin da shazee yazo gabanta kenan tana haki tana kuka' " suhana tana girgizata " tana shazee karki min haka" meyasa Zaki dinga yimin irin wannan wasan wlh abdulrahman bazai mutu ya kyaleni ba " Sam bazaiyuba " Nan suhana ta fita hayyacinta " tarasa meke Mata Dadi tace Yana Ina ne shazee tace Yana asibitin ku.


Da gudu ta wawuri key din motan ta " ta antaya aguje haraban gdan ko mayafi Babu" daidai lokacin su hajiya sunfito zasuje kenan".


Abun tausayi hjya tana ganin suhana sai ta fashe da kuka " suna tashiga mota abdulmalik Yana ce Mata ta tsaya Amma Ina batajin Kira " da gudu taja motar ta Tata sai abiti tana parking ta fito ko rufe motan batayi ba" Yan asibitin sun tsorata  sosai.


Karo tace da abdulrazaq dake bakin kofa ya dafa Yana hawaye" sai kawai ganinta yayi ta cakumo sa tana ina yake Ina yake' ya tsorata dayanayinta' ya nuna Mata dakin ta shiga da sauri hangosa tayi Yana kwance ' ta fashe da kuka ta karasa ta kifakanta a kansa tana kuka'" tana why Abdul karka barni AA wlh Ina sonka ' Kai ne mijina " pls katashi kataimaka min araba aurena da laisu " wlh Sam bani sonshi" arashinka na auresa " pls katashi tana Yi tana jijjigashi ' har muryanta ya dashe"  su hjy ne suka karaso sai kuka suke tayi shazee Kam ta Suma sai ta farfado' hajya ta karasa dakin ta tsaya abakin kofa.


Tana ji suhana tana cewa AA Kai kadai nake son aura ' pls katashi ka raba aurena da laisu da aka daura yanxu' cikin kuka hajya tace ba da laisu aka daura Miki aure ba 'da abdulrahman aka daura aurenki suhana ta tsaya cak da kukanta ta tashi tsaye tana kallon hajy" wani irin murmushine ya kubuce Mata da kuka tana fadin yanxu AA ne mijina hjya ta daga kanta alamun eh" sai ga laisu ya shiga yace tabbas shine mijinki" tace tayaya hakan ta faru ban sani ba" ji sukayi computer din dake jikin gadon AA ya fara din din din din alamun numfashin mutum na tsintsinkewa" abdulrazaq ne ya karasa wajen da sauri Yana fadin Yana Raye Bai mutu ba ku bani kayan aiki .


Da sauri sauran ma'aikan suka shiga akace su hajiya su fita ' kowannan su bakinsa cike da addu"a barema suhana Wanda farin ciki tare da tambayoyi sun Mata yawa.


Cikin kankanin lokaci numfashin AA ya dawo daidai ya bude idon sa Yana kallon saman dakin hawaye nabin kuncin sa ido biyu sukayi da abdulrazaq " a hankali ya furta abdulrazaq narasa ta ko " abdulrazaq yace baka rasata hasalima Kaine mijinta " murmushi ya kubce masa yace karya kake abdulrazaq so kake ka kwantar min da hankali kafada min gskya kawai .


Ganin AA baiyarda da maganar abdulrazaq ba " yasa abdulrazaq Kiran hajiya da suhana ' don sutabbatar mashi da haka"AA yayi ido biyu da mahaifiyarsa  ya kaudar da kansa Yana hawaye don Yana ganin duk itace silan rasa masoyiyar shi' hajiya tace my son karkayi fushi dani baxanji Dadi ba" daidai da second ban taba tunanin raba ka da suhana ba" sai ma in Kara hada ka da ita" abunda ya bani haushi kaida ita baku bani muhimmanci arayuwa ba ' kun kasa gaya mun matsalan ku" Wanda ni na Dade Ina so Inga na hada ku aure Amma na rasa tayaya ' sai daga baya nahada plan din auren suhana' da laisu' iyayen suhana suka bani goyon bayan haka' shima din don intabbatar kuna son junan ku ko bakusan junan ku ' shiyasa. Na muku haka" kuya feni Dana jefaku cikin wani hali' ayanxu suhana matar kace ' dama tun asali da Kai aka daura Mata aure' " nima nayi kuskure da ban fito ta wannan hanyar ba " da yanxu nayi asaran tilon Dana kuma angon suhana" wani irin farin cikine ya mamaye AA basan sanda ya tashi daga kwancen ba ya rungume hjyarsa " tare da cewa " agsky kincika uwa Mai son farin cikin ya'yanta Ina alfahari dake hjyata"" nima nayi kuskure ki yafemin " duk laifi nane " suhana ta karaso ta durkusa gaban hjya" tana hakika hjya bani da bakin godiya kin min komai arayuwa" sai dai ince Allah ubangiji yasaka Miki da gdan aljanna ya raya Miki zuri'arki' baki daya" kuma Kiya fe min kuskuren danayi" hajiya ta dagata ta.



Tace bakomai suhana zurfin cikin kune keda abdulrahman zai halaka ku" yanxu kunga sai kudena zurfin cikin " tunda ya koya muku hankali" duk suka sa dariya" mama tace Banda abun ya'yan zamani su wayannan ma da ban suke acikin yaran zamani"" suna Abu Kamar na mutanan da" da Maryam ne da tuni kowa ya San da soyayyata" nan ma aka kwashe da dariya " hjya tace Kai mama Zaki fara tsokanar suhana ko " aikin San ta da kunya da Kara" Amma Ina fatan za adaina wannan zurfin cikin" don kar watarana ana da cikin jikana ' ba asan ba ashan gishiri ba aje asha Amin atsaran jika " duk adalilin xurfin ciki"" suhana ta ji kunya ta boye fuskarta jikin Adda hafsatu""AA ne yayi karaf yace aini daga yau na Dena zurfin ciki ' yafendo rakiya tace ja'iri ya hango mutuwa shiyasa yace ya daina " yanxun ma inkayi Wasa sai in raba auren "" AA yayi saurin cewa tabdi jam aiko Naga alama zamu  raba hanya dake yafendo" aure ko na hannuna ba Mai iya kwacewa.


Likitane suka shigo shida abdulrazaq " yace Bari ya duba jikin NASA" ya tambayesa Ina da Ina ke Masa ciwo yace babu ko Ina " sai Dan ciwon jiki shima din in andan na min zai daina"" doctor yayi dariya yace wannan aikin matar kace" nan ma akayi dariya" doctor yace wai nikam kallon india film din sharukan ne" don Naga ka kware a iya soyayya don Kai soyayyarta taka daban take, me cike da salo kala kala'" sai anan Adda hafsatu tace ba Dole ya iyaba" yaje India ya tare ko kasan shi baiso.


Doctor yace yanxu dai an sallameku sai aje gda a huta hajiya" akai maka amarya" nan akasa dariya" wajajen karfe 2:30 suka wuce gda' anata murna " su ummi sai tsiya sukema suhana " .



AA yayi wanka yaci abinci" Yusuf ya karaso da abokanan AA duk sunsha malinmalin AA ya kalle su da mamaki yace Ashe duk kunsan da auren " Yusuf yace nida abdulrazaq muka gayyaci abokanan ka batare da sanin ka ba " angwayen sun hadu abdulrahman abdulrazaq abdulmalik  ba karamin kyau sukayi sai samusu allbarka akeyi ' hjya dadine ya rufeta harda hawayenta yau ta aurar da zaratan mazanta da autarta mace shazee. 


Suma su suhana sunyi kyau ba kadan ba " don duk gdan su shazee suka tare don hjy tace anxama daya Maryam shazee suhana "  nan kowacce ta matsa kusa da angonta ' angon shaxee yazo wato Umar farouq aboki ga abdulmalik. ' nan sukayi ta daukan hotuna:.


Suhana da Maryam

Sun koma gdan baban su don Yi musu nasiha sosai" ita suhana sai dai akara tuna Mata Maryam ce sabuwa .


Da daddare motocin daukan amare sukazo gdan su suhana suna kuka aka rabasu da maman su Priya da ummi sukayi rakiyan shazee gdan ta dake u/dosa kusa dasu hjyan ne' ita kuma Maryam aka kaita nan Urban shelter hanyan kadaure .


Ita kuma shazee malali aka kaita Basu da nisa da gdan su suhana' kowaccen su Tasha kuka" yayin da kuma aka kawo amaryan abdulmalik  cikin gdan su hjya ' don akwai flat dinshi daya gyara ' don Basu son suyi nisa da hjyan su.


Abbaty Yana daya daga cikin abokanan abdulmalik kasan cewa sunyi karatu atare"  .


Abbaty da laisu sunji kewar suhana Amma kuma sun dangana " hjya ita ta siyawa laisu gda Mai kyau inda ya ijye matar sa Aisha yarinya ce baza ta wuce17 years ba" kuma Yana sonta .


Kubiyo ni ashafin gaba kuma na karshe taku har kullum NUSNIM .

Amarya agun Lamin 4ever hahhhhhhh.



Idan kunji dadin shafin nan inji ' kawai katin waya ya shigo layina .


Ina gode muku grop din hausa novels na ummu yahaya (sisin mamanta?

Da grp din  hausa novel na Mrs mubeen . Sai kuma grp Dina *all* *dostis*  *of* *nusfulhayat*



08064481931

3/12/20, 2:44 PM - Nusaiba Sulman: 🍒 *GIDAN* *AURENA* 🍒

 *BY* *NUSNIM*

         2⃣3⃣

Ankai kowa gdan aurenta' hajya da mama sukace alhamdulillah sun godewa Allah daya nuna masu wannan ranar.


Suhana ce zaune bakin gado kawayenta sun tafi sunbarta ' AA ne yayi sallama ya shigo daki ta amsa mashi ciki ciki" ya karaso ya tsugunna gabanta " yace my life yanxu kinzama tawa " Ina godewa Allah da ya mallaka min ke" suna ta Kara dukar da kanta kasa tana murmushi yace tashi muje muyi sallahh sai muci abinci" ba musu ta tashi tayi alwala suka gabatar da sallah yayi musu addu'oi.


Sannan yace kece angon fa yau tunda ni ban San komai ba sbd haka akwai ledoji a parlo ki dauko Mana kixo muci naman mu" yanayi Yana dariya" suhana tace kai hamma Abdul ' ranar da aka kawo maka amarya ma sai ka sata aiki" yace ai lada xaki samu .


Tayi murmushi sunci sunsha sai zance ya canxa salo sbd kowannan su kokari take ya nuna mawa Dan uwansa soyayyar sa" amarya fa ta Dan Sha wuya' shiko AA yau cikin farin ciki yake.


Haka shazee da Maryam ba amagana sun gane ruwa ba sa'an kwando bane" don sukam sun Lodi kayan Mata ba adadi suhana ta Hana su Amma sunki "su aganin su suna son su daga totar Mata"" sai gashi kowaccen su ta dannana waja waja.


Haka wajen lai yatafiyar da amaryar shi yadda yake so" sai kuma akayi dacen taso tazo daya da amaryan. 


Asuba ta gari AA ya tashi yaje sallah da kyar suhana ma ta tashi ta tsaftace jikinta ta gabatar da sallah sannan ta shiga kitchen don yin abun breakfast shiko AA Yana masallaci Yana karato " sai karfe bakwai yashigo gdan" yaji gdan sai daukan kamshi yakeyi ko'ina gashi har ancanxa tsarin zaman kujerun " yayi kyau sosai.


Ya wuce dakin sa don shima ya shirya' bayan ya gama ne ya fito ya wuce dakin suhana ita kuma lokacin ta gama tsara adonta ta fito fes da ita " tana ganinsa ta sunkuyar da Kai kasa " tta sugunna tace hamma Ina kwana' yayi saurin dagata ya jawota jikinsa yace daga yau inxaki gaisheni zuwa zakiyi ki rungume ni kimin kiss a kumatu da baki' sannan kuma kidaina cemin hamma kisa min wani sunan soyayya tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannun ta " tace to .


Yace nifa kidaina jin kunyata domin munxama daya " kibari musha soyayyarmu " kuma insha alluhu Zaki sameni ayadda kikeso fatana ki rikeni da Amana kuma ki kaunace ni sosai" Inna Saba Miki rashin sani ki fada min karki rikeni aranki " Ina so muyi zama na dindin din " sbd ke rayuwa tace suhana cikin kwana daya kin canxani" Ina kuma da in munyi sati " I love you my Zindagi (rayuwata)" suhana tace I so much love you hayatee ya rungumeta sosai" suhana tana ganin zai wuce gona da iri tace hayatee pls muje kayi breakfast .


Yace woow harkinyi breakfast kina amarya baki tsaya akawo Mana daga gdaba tace "a'a ai hakkina ne indafa nawa mijina domin insamu lada .


Yace nagode suhanty na Allah yayi Miki albarka tace amin suka nufi parlo sukayi break din su' bayan sun gama yace zumuje innuna Miki gdanki da kyau " suka tashi sukaje " ko Ina nagdan ya tsaru " gawajen Wasa da wajen buga basketball da waje flowers' suhana taji Dadi sosai' bayan sun zagane suka koma ciki domin su kwanta wajejen karfe 10:30 AA yaji a kwankwasa misu  kofa ya tashi yaje yaga me aikin gdan su hajiya ce ta kawo muci break ya karba ya rufe kofa ' ya ijye basket din a daining ya wuce ya kwanta tare da janyo suhana jikinsa Yana shakar kamshinta.


Basu suka tashi ba sai 1saura ' itacema tafara tashima shima ya tashi yayi wanka sannan ya wuce masallaci' ita tashirya tayi sallah ' ya dawo yaganta tana karatun alkur'ani sai yaji takara shiga ranshi fiye da da " azuciyarsa yanama Allah godiya daya basa hafsat suhana ' tagama tashafa addu'oi yace allahu Akbar Ashe matata hafeezace ' tayi murmushi.


Tace bara naje na daura Mana girki yayi saurin jawota jikin sa yace ke wacce irin amarya ce daga kawota sai tayi ta aiki' saka hannun ta awuyansa' dayan hannun taja hancinsa tace bana son hayatee nah ya dinga zama da yunwa kuma kasan ance aljannar mace tana karkashin kafan mijinta' yace kinga na daga kafan kin ma shiga aljannar insha allahu sukayi dariya su duka" yace au na manta daxu  da safe hjya ta aiko da break ' suhana tace muje mugani'  to.


Su fito Yana hannun su na tsakale da juna suka wuce daining ' suka bubbude waina ce da miyan taushe taji nama ta ko Ina, sai kuma farfesun kaza sai soyayyan doya da kwai ,. AA yace agaida hjya gskya tana son mu sosai" suhana tace aikuwa " AA yace kinga basai kinyi girki ba wannan ma ya Isa .


Nan suka zauna suka ci abincin su a plate daya .


Bara mu waiwaya gdan shazee da Maryam


Shazee ana can anacin amarci ita da ummar dinta sai nan nan yake da ita don yasan yayi aika aika' haka Maryam ma doctor abdulrazaq shima haka yakeji danasa Kamar zai lashe Maryam don so da kauna " dukkan su suna godewa Allah da samun abokin rayuwa na kwarai" shima abdulmalik Yana can da amaryasa ana shan love " saidai fatan alkhari, 


hjya ita tadau dawainiyan kawo musu abinci Amma Banda shazee,  shaxee dangin mijinta da kuma maman suhana suke Kai Mata kasan cewa suna unguwa daya' ita ko suhana musamman ta Kira hajiya tace Dan Allah ta daina turo musu abinci ta hutar da ita ' zatayi da kanta don ta Sami lada"" ba karamin dadi hajya taji ba" tana Kara godewa Allah daya Bata suhana amatsayin surikarta.


Bayan wata biyu da aure amare duk sunyi kyau abunsu gwananin ban sha'awa dukkan su sun hadu agdan su hajyan shazee, suhana da Maryam da shazee sai amaryan abdulmalik dake gdan Amma bangarenta daban itama tashigo don gaida hajya' ga mazajen nasu' su " Adda hafsatu ma tazo ' nanfa akayita Hira"" hjya ba kunya tsakaninta da surukanta don surikar zamani ce ita Bata yadda da wannan kunya kunyan ba don duk ta daukesu kamar ita tahaife su .


Abdulrahman ne harda Hira da su dariya sosai " shazee tace a lallaikam sis suhana nayarda hamma abdulrahman zai iya canxawa gskya kinyi kokari " hjya tace nima wlh nayi mamakin ganin abdul ya canxa.


Abdulrahman ya Shafa kansa ya janyo suhana yace habibty muje kimin tausa" hajya tace tashin hankali lallai Abdul wuyanka ya Isa yanka " suhana kuwa sai taji wani kunya ya lullubeta " ganin haka hjya tabar parlon cikin dabara alamun tana wayan karya" suhana naganin tabar parlo tace habibtee tashi muje shazee tace munafuka dama kunyar karya ne" Adda hafsatu tace to ke Ina ruwanki .


Nan ma sunje sungaida iyayen su suhana " sunyi murna da ganin cazawar yaransu kuma sun musu addu'a .


Bayan kwana biyu Khadija da ummi da Priya suka kawo wa suhana ziyara " sunsha Hira sosai ummi tace aminiya wai menene sirrin Naga duk kincanxa Kamar ba keba'  khadij tace aikuwa wlh " suhana tace ummi nayi dacen samun miji nagari akullum fatana Allah yasaka mawa AA da gdan aljanna" yacika namiji tamkar goma " AA Bai son bacin Raina duk wani tarairaya da akewa mace nikam nasamu agun AA sai dai mugodewa Allah ''.


Khadija tace Allah ya samu adanshin ku suhana tace amin" Khadija tace next week za asaka ranar aurena" suhana tace da gaske " tace eh wlh' cikin jin Dadi suhana da ummi suka ce muntayaki murna Allah yasanya alheri " Ashe zamusha biki .


Khadija tace Allah yasa laulayin cikin ki yabarki ki kaini dakin mijina" suhana ta zaro ido waje ' tace aini bani da ciki " ummi ta bushe da dariya tace lallai suhana a hakane baki da ciki" Khadija itama tayi dariya tace sai kace wannan cikin shine nafari" amatsayinki na likita baki ma San kina da ciki ba" Priya tace gsky AA ya iya ijyan da likita bokan turai baisan dashi ba " dukkan su ukun suka fashe da dariya suhana ta jefa masu kanana pilolin Kan kujera " tana wani shagwama Kamar zatayi kuka " ummi tace ke bafa AA bane awajen da kike Mana shagwaba  "" tace wlh kubar tsokanata .


Rayuwa kenan komai ya daidaita su laisu fa anshiryu ya zama kamili sosai kuma Yana iya bakin kokarinsa akan iyalinsa sai dai hamdala, dansa Adil Yana zuwa hutu gdan babansa don da dakinsa agdan " aunty amarya na sonshi shima Yana sonta ,, kuma Yana zuwa gdan suhana hutu ' bayi can bashi can suhana taso daukansa mamanta ta Hana tace awajensu zai zauna.


Akwana atashi Babu wuya anyi auren Khadija ta auri me mata da Yara biyu kuma suna zaune lfy '' yayin da suhana cikinta nada wata bakwai ba karamin girma yayi ba don sai da aka nemoma ta me tayata zama don bata iyayin komai.


Maryam ma nada cikin wata hudu ita da shazee .


Hajya da mama Basu da aiki sai kaiwa masu ciki kayan kwadayi na gargajiya daga macewa danwake zataci sai Mai cewa dambu sai Mai cewa wainar fulawa haka dai ake tayi' cikin suhana nada wata Tara ta haifo ya'yan ta 4 Mata biyu maza biyu kyawawa Amma taji jiki" zoku ga murna gun yan'uwa ba amagana " AA Kam Kamar ya zuba ruwa akasa yasha don murna " bayan ta huta aka wuce da ita gdanta ' hajya tarewa tarewa taje tayi agdan da kanwar maman suhana " Yan uwa kuwa kullum cikin zuwa sukeyi .


 Suhana na samun kulawa ta ko Ina" sai dai godiyan Allah ' yaran sunci suna Kamar haka AYMAN da AYMANA

Sai AYAN da AYANA.

Anyi suna dai dai gwargwado batare da karya ba .sai dai muce Allah y raya Yan hudu 


AA ya budewa suhana asibitin daya Gina Mata batare da sanin ta ba ga kuma ma'aikata kwararru daya zuba Mata" sbd farin ciki saida tayi kuka " yace ta daina gode Masa " don bai Mata komai ba " don duk wacce ta baka ya'ya to tagama maka komai " shiyasa take Kara son ta aranshi bare ma inyaga su Ayman sai yaji Dadi Yana murnan yanxu duk wayannan nasa ne.


Maryam da shazee sun haihu " Maryam na miji ta Haifa ita kuma shazee mace ' tazaran su kwana biyu ne "" " sai matar abdulmalik itama ta haihu mace '' murna gun hjya ba amagana ' sai dai mu musu fatan alkhairi.


Bayan wasu shekaru" wani dankareren motane ya shigo cikin gdan su suhana lokacin suhana na zaune ita da AA da Yara , a haraban gdan wajen hutawa,' saurayin ya fito daga cikin mota idon sa sanye da glass " Allah ya Masa kwarjini da baiwan kyau, fuskarsa dauke da murmuhi.


Yaran na hangosa suka taho da gudu suna oyoyo Yaya Adil ya rungumesu Yana dariya suka karasa wajen su AA .


Ya sake yaran AA ya tashi suka rungume juna Yana my son wellcome back " Adil yace daddy nayi missing dinka " nan sukayi dariya Kamar wasu abokanan juna suhana tace lallai Adil haka turai ta karbeka jibi' yadda ka dawo kana wani kumbo sai kace irin Mai shekara 30 din nan alhalin baka wuce ,23  ba "" Adil Kamar zaiyi kuka yace mummy kin fara ko Dama nasan baki Sona daddy yafi Sona da kannaina"" suhana tace kaji dashi jibeka fa ai sai ace Kai Yaya nane.


Daddy yace habibtee kidaina maida min son tsohofa baki San irin mazajen da akeyayi bane yanxu tace  tace tabdi  wannan mejiki Kamar Zaki ' shiyasa bazan baka auren yata asiya ba Yar wajen shazee " gara in samomaka Mata a kauye"" sai sukaji murya ance ai dayake bakece Zaki auraddashi ba ma ' so baki da right din za ki bashi Mata Yar kauye" shazee ce ke magana.


Suhana tace oyoyo  sister  " ni ki kyaleni tunda tsiya kike ma Dana Adil yace  aunty shazee kyale mummy tsofa ne ya fara Mata yawa daga gani" AA yayi karaf yace Kai son aiko yanxu h tafi budurwar ka kyau ba "" Adil yace tofa daddy yanxu juya min baya zakayi" sai sukaji murya ance indai akan habibty din sane to zai juya maka baya "" abdulrazaq ne shida  Maryam da dansu suka karaso suna dariya " ...


AA yace Ina ruwanka' sa ido " sai ga laisu da matarsa da yaransa biyu Kamar hadin baki ko kuma ma ince hadin bakin ne sunxo su taya suhana murnan zama babban likita ta kasa baki daya likitan da tayi suna akowani gari" can kuma sai ga abdulmalik da matarsa " da Adda hafsatu sai kuma Khadija da ummi " abun ya bamawa AA da suhana mamaki" nan fa aka shiga cikin gda "  AA da suhana sukaje suka shirya sukayi anko sun fito hannun su rike da juna ' parlon ya dauki tafi don masoyan sunyi kyau sosai " anyi order su abinci abunsha kala kala " ga Mai hoto na aka shiga daukan hotona'  harda su laisu zuciyar sa ba komai sbd duk anxama daya " ana xumunci" suhana tayi jawabi tace Ina gode muku Allah yasaka da alkhairi Allah ya bar xumunci " Ina kuma godewa gwarzan mijin abun alfahari Wanda bazarshi na Kai wannan matsayin Dana fuskanci kaina aciki" sannan Ina godewa hajiyata da adda hafsatu sun taka wani matsayi arayuwata " iyayena wayanda suka kawo ni duniyan nan Ina masu fatan gamawa lfy Allah yasaka masu" Yan"uwa da abokan arxiki Suma Allah yasaka masu da alkhairi ya'yana abun alfaharina Allah ya raya min ku . " Tana share hawayenta' AA ya rungumeta "Adil yace woow so romantic " yace aunty shazee Zaki aura min asiya ta" laisu yace " Kai Adil gskya turai yasa ka koyo rashin kunya " AA yace bashi yayi lokacin sa ne ko my son . Akasa dariya happy family 4ever.


TAMMAT 

Anan na kawo karshen wannan labarin nawa Mai suna *gidan* *auren* .


Ina fatan makarantana su ilimantu da wannan novel din " .


Bin iyaye shine komai arayuwa. Mu kiyaye pls 


Ina son duk Wanda yaji dadin novel din nan yayi sharhi akai .


Innayi kuskure akai kumin afwan  , sai kunjini a next novel Dina Amma na kudine.


Ina cigiya wannan novel din nawa

*shahrazad* *labarin* *sharrin* *zuciya*


Dan Allah duk Wanda ya iya documents na novel Ina son ayi mun Dan Allah.


Na barku lfy 


*Ummu* *ruman*

NUSNIM

08064481931



Post a Comment

0 Comments