👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨. ✨✨ ✨ ✨
*Story & written by Rukayya Ibrahim* *Lawal(ummu-inteesar)✨✨*
*Marubuciyar*
*SOYAYYAR MEERAH.*
~DEDICATED TO~
_*HASSAN ATK & HUSSAINI 80K*_
_*SHINFIƊA*_
_Yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata ala,tsira da amici su ƙara tabbata ga shuganmu annani MUHAMMAD (S.A.W) da ahalin gidan sa baki ɗaya._
*GODIYA* _ga_ _mahaliccin bayi wanda ya bani ikon fara rubuta wanan labarin_
_cikin hikimarsa da iyawarsa_
_Allah ya ƙara tsira da amincin ga annabi Muhammad(s.a.w)._
_*GARGAƊI*_
_Ban rubuta wannan labarin dan cin zarafin wani ko wata ba,idan labarina yayi dai-dai da rayuwarka/rayuwarki kiyi hakuri._
_wannan labarin danayiwa take da *YAR GANTALI* (Mai hangen na wani)_
_Wani sashe na labarin true life story ne._
_Na rubutashi ne domin fad'akarwa ga Mata masu irin halayyar yawon GANTALI alhali da aurensu,_
_Yana fad'akarwa ne akan:_
_1:YAWON GANTALI(da wasu matan keyi alhali da aurensu)._
_2:HANGEN ABUN WANI._
_3:KWAD'AYI_
_4: HASSADA_
_5:DARGA(RIGIMA)_
_6:RASHIN GODIYAR ALLAH._
_da Kuma illolinsu._
_Ina fatar Allah ya bani ikon gabatar da wannan labarin yanda ya dace Kuma readers su amfana dashi ameen._
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Bismillahir-Rahmanir-Raheem*
⚡💫⚡ No. 1
Wata matsakaiciyar Mata na hango wacca bazata gaza shekaru 28 ba a duniya, tafiya take cikin hanzari yayin da take goye da y'arta a bayanta.
Wani layi naga tashiga Wanda bai fiye hayaniya ba kasancewar gidajen gurin tsira-ru ne.
Tafiya kad'an tayi acikin layin ta iso bakin wani madai-daicin gate turawa tayi tashige gidan.
Wasu parts nagani guda biyu daga waje parts d'in irinsu d'aya, d'aya part d'in Yana fuskantar d'aya Amma tun daga waje zaka fuskanci akwai banbancin arziki tsakanin part d'in guda biyu.
Cikin sand'a matar tashige part d'in dake bangaren hagu tana waige-waige tana kaiwa tsakiyar gidan kamar daga sama taji ance Sannunki da zuwa FA'IZA.
saurin waigawa tayi inda taji zancen, mijinta ne a tsaye Yana k'are Mata kallo ya d'ora da cewa "yanzu FA'IZA kina ganin abunda kikeyi ya dace? kefa matar aure ce amma kika kai har 9:30pm a waje,ba'a gidan mijinki ba?"
Kallon banza ta watsa Masa tare da cewa " tambaya ma kake?"Ai inaga kafi kowa sanin dacewar abunda nakeyi tunda Kai nake rufawa asiri nake fita nema tunda Kai ka kasa ciyar da iyalanka.
Au nema kikaje kenan? yawon gantalin naki kike Kira da nema?
Kiji tsoron Allah FA'IZA nifa mijinki ne dole ki nemi iznina idan Zaki fita,bawai ki Kama hanya kiyi ficewarki sanda kikaso ba....
Dakata FAWWAD daina ganin na tsaya Ina magana dakai kayi tunanin ko tsoronka nakeji..
Fita ce dai dole sai nayi Kuma yanzu na fara.. ba yawon gantali ba komai zakace shi naje yi.....
Tana Kai nan a zancenta tayi fuu tashige d'akinta ta barshi Nan a tsaye cikin takaici da mamakin hali irin na matarsa fa'iza.
Yaranta guda biyu ta tarar a parlourn nata suna barci a k'asa bako shimfid'a, kasancewar Bata dawo da wuri ba sungaji da jiranta tazo tayi masu shimfid'a kawai sai suka yi kwanciyarsu a k'asa.
Wannan abune dake faruwa kusan kullum Bata dawowa sai sunyi barci da safe ne kawai suke iya ganinta harma su Sami arzikin ta shiryasu suje school koda zasu dawo kuwa tafice gurin sana'arta wato yawo.
Ficewa tayi daga d'akin taje d'akin yaran ta gyara masu shimfid'ar su, sa'annan ta dawo dak'innata ta kwashesu ta mayar dasu nasu d'akin bayan ta gama kwantar dasu ta Koma d'akinta inda ta samu Mai gidan nata har ya shigo ya kwanta akan gado.
Y'arta k'arama data bari akan kujerar parlourn ta d'auke tashiga da ita cikin d'akin ta kwantar da ita a tsakiyar gadon.
Toilet ta shiga tafito a tsaftace kayan barci tasaka tare da fesa turare sa'annan ta kwanta akan gadon.
Lumshe ido FAWWAD yayi Jin yadda d'akin ya garwaye da k'amshin turaren jikinta,
A zahiri FA'IZA macece Mai tsafta duk yawon gantalinta sai ta tsaya ta gyara gidanta da jikinta kafin ta fita. wannan na daga cikin dalilan da yasaka FAWWAD ya kasa rabuwa da ita duk da munanan d'abi'unta da Raina shin da tayi.
Tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna tare da Kiran sunanta FA'IZA! Tashi muyi magana.
Taji shi sarai Amma sai ta Masa banza tare da gyara kwanciyarta.
Pls FA'IZA ki tashi muyi magana nasani cewa kina jina pls.
Tashi zaunen tayi itama tare da tsuke fuska dan tasani zancen bazai wuce Wanda ya sabayi ba a kullum shiyasa ta d'aure mishi fuska Wai Dan k'ar yaga damarta.
Bai damu da hakan da tayi ba yace: FA'IZA ina so muyi magana ta fahimta atsakaninmu, kinsan dai auren soyayya mukayi dake muddin kuwa ina sonki dole nayi kishinki, Dan girman Allah FA'IZA ki tayani kishin kanki ki dinga killace mun kanki a cikin gida bana son wannan yawan fitar da kikeyi.
Jama'a duk sai maganganu suke akan ki,idan na wuce ana nunani da yatsa ana cewa ga mijin Y'AR GANTALI.
Dukda cewa Ni bana zargin ki da yawon banza na yarda dake 💯% amma banajin dad'in wannan yawon bin gidajen k'awaye da y'an uwa da kike kusan kullum.
Dan Allah FA'IZA ki rufamin asiri ki rage wannan yawon naki pls.
Tun da ya fara magana FA'IZA batace komai ba sai K'ara tamke fuska da tayi saida ya dire zancensa kafin tace:
Yanzu FAWWAD maganganun mutane kake kamawa? Kasani fa Dan Ina sonka ne kawai nake zaune dakai, da badan haka ba da tuni na barma gidanka Dan na gaji da wannan rayuwar tsiya da talaucin ta gidanka.
Fita kuwa da kake maganar inayi dan rufin asirinka ne Kai nake taimakawa nake fita nema dan abunda kake kawowa a gidan nan baya wadatar damu ni da yarana shiyasa.
Kai baka ma Jin kunya? "Ga yayanka Nan ba abunda baya yiwa iyalinsa na jindadi Amma Kai ka kasa"
Runtse ido FAWWAD yayi jin maganganun da take fad'a mishi komawa yayi ya kwanta lamo akan gadon Yana tunani
Wai sai yaushe ne FA'IZA zatayi hankali tasan cewa arziki da rashinsa duk na Allah ne? Sai yaushe zata daina mishi gorin talauci?
Shikam yasan Yana iya k'ok'arinsa gurin ganin ya kyautatawa iyalinsa da duk abunda ya mallaka.
Kansa ne ya fara Sara masa hakanne yasa bai Kuma tamkata ba.
Itama kwanciyarta tayi tare da fad'ar dole kayi shiru tunda kasan gaskiya kake k'in ta.
*********
Washe gari tunda sassafe FA'IZA ta tashi tayi duk wani aikace-aikacen ta da zatayi. Saida ta tsaftace gidan ta gaba d'aya ko'ina sai kamshi yake.
Sa'annan ta yiwa yaranta wanka tashirya Aabid da Aa'idah cikin uniform d'insu na makaranta sa'annan ta Basu abincin break-fast d'insu suka ci, suka wuce school.
9:00am FAWWAD ya fice daga gidan zuwa gurin aikin shi.
Fitar sa ke da wuya itama FA'IZA ta fito a shiryen ta tsaf cikin atamfa ja Mai launin fari, ta d'ora hijabinta fari akai.
Ba wata doguwar kwalliya tayi ba, powder kawai ta shafa sai lipstick (man lebe).
Sai kamshi take ta goya y'arta (Simrah) y'ar 2years a baya, ta fito tare da rufe part d'inta.
***********
D'ayan part d'in da ke fuskantar nata tashiga tare da yin sallama.
Daga ciki aka amsa mata, gaisawa sukayi da Fad'ima matar (Fahad) yayan FAWWAD.
Ta mik'a Mata makullin sashen nata tare da cewa.....
#share & comment
Yawan comment d'inku shine zai bani k'warin gwuiwar cigaba.
#Ummu-inteesar ce
❤❤❤❤❤❤❤.
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI (Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by Rukayya Ibrahim Lawal* *(ummu-inteesar)*
*Dedicated to HASSAN ATK& HUSSAIN 80K*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.2
Ta mik'a mata makullin sashen nata tare da cewa" jiya ko da nazo kawo miki makullin kin fita aiki.
Dan Allah idan su Aabid sun dawo ki sammu su abinci su ci ban ajiye musu komai ba.
Ta fad'a tare da juya cikin hanzari za ta bar gidan."
Fad'ima tace Wai Ina zaki kike wannan saurin haka FA'IZA?
D'an dakatawa tayi tare da fad'ar gidan yayar Mansura za ni, ragowar kud'in robobin da ta saka na siyo Mata zan karb'o.
Tana gama fad'a ta cigaba da tafiya har ta kusa k'ofar gidan taci burki tare da cewa ki ajiye mun nawa Koma minene kike dafawa, duk k'amshi ya cika mun hanci.
Dariya Fad'ima tayi tace adawo lafiya.
Ko amsa Mata Bata tsaya yi ba tayi gaba.
Fad'ima tace "Allah ya shirye ki FA'IZA, ace macen aure ta zauna Bata da aiki sai yawo a gari?".
*************
1:30pm aka tashi yara daga makaranta a galabaice yaran suka iso gida.
K'arasawa sukayi bakin k'ofar part d'insu suka ganshi a rufe.
D'ayan part d'in suka nufa Nan ma a rufe maman su Salim(Fad'ima) bata nan.
Kasancewar fitar gaggawar da ta same ta zuwa asibitin su Dan ita nurse ce.
Ta ma Manta cewar yaran su na school.
Dawowa sukayi dai-dai k'ofar part d'insu suka zauna yunwa na damun su sosai.
Aa'idah(Yar 6years) sai kuka take tana rik'e ciki dan yunwa. Aabid(dan 9years) ne ke rarrashin ta. Kiyi hak'uri k'anwata ga biscuit ki ci.
Ya d'auko biscuit a jakarsa ya mik'a mata.
K'arbar biscuit d'in tayi ta fara ci da sauri kamar wacce za'a kwacewa.
Na gode Abie ta fad'a. Sunan da take Kiran Aabid d'in kenan wato(yaya) a yaren turkiyya.
*************
Da misalin k'arfe uku na Rana FAWWAD ya dawo gidan tarar da yaran shi yayi a k'ofar part d'in har Aa'idah tayi barcin wuya a kan cinyar yayan ta.
Ranshi ne yayi mugun b'aci da sauri ya k'arasa gurinsu ya d'urkusa ya tallabo Kan Aabid da ya duk'ar dakai Yana kuka, yace menene boy ?
Yunwa muke ji dady, "idah ma har tayi barci". Yaron ya fad'a.
Kuyi hak'uri yarana ya fad'a Yana k'ok'arin bud'e gidan da makullin shi.
Dawowa yayi ya d'auki idah dake barci ya sab'ata a kafad'ar shi ya shige cikin gidan Aabid na take Masa baya.
**********
FA'IZA kuwa tunda tafi ta bata zame ko'ina ba sai gidan yayar Mansura tayo biyar bashi dak'yar ta samu ta bata rabin kud'in Nan ma sai da taga dagaske tsiya FA'IZAN zata shuka Mata idan Bata bayar ba.
Tana fitowa daga gidan taje gidan Salamatu (Mai dashi) ta ciwo bashin dubu goma. Dak'yar ta Bata kud'in dan tasan FA'IZA mace ce rigimammiya ga iya rik'on bashi.
Daga Nan Kuma ta wuce kasuwa ta siyo turamen atamfa guda biyu na dubu biyar-biyar.
Irin wad'an da tagani ga Fad'ima jiya.
Domin Akwai ta da hangen abun wani, da Kai kanta in da Allah bai kai ta ba.
Ga hassada duk abun da ta gani ajikin Fad'ima ko y'ay'an ta,dole sai ta siye irin shi ko da kuwa da kud'in bashi ne.
Daga kasuwa ta wuce gidan su a can ta bayar da d'inki anan mak'otan su.
***************
Fita FAWWAD yayi ya siyowa yaran shi indomie da y'an kud'in da ya samo yanzu gurin sana'arsa(capenter).
Da kansa ya dafa masu indomien ya tad'a idah dake barci ya basu suna ci.
Yana zaune a gefen su Shi ma yunwar na addabar sa,amma bai ci indomien ba yafi son yaransa su k'oshi.
Tunani kawai yake tare da Allah wadai da hali irin na FA'IZA.
Wai sunan Yana da Mata amma shine har yanzu bai yi lunch ba ga yara Nan ta barsu a yashe.
Gaskiya ba zai yiwu ba dole ya d'au mataki akan ta abun yayi yawa.
************
Sai 4:30pm Fad'ima ta dawo gida sai da tazo zata shige sashen ta ta tuna cewa FA'IZA tace Bata barwa yaran ta komai ba.
Tasani Kuma Yana da wuya idan FA'IZAR ta dawo yanzu.
Cikin hanzari ta shige part d'inta Kai tsaye kitchen ta shiga ta zubo masu abinci a kula ta nufi sashen FA'IZA.
FAWWAD ta tarar shi kad'ai kasancewar ya tura yaran islamiyya.
Gaisawa su kayi sannan ta mik'a Masa kular abincin tare da cewa a bawa yara d'azu fitar gaggawa ce ta taso mun shiyasa na Manta ban ajiye musu ba.
Godiya ya Mata sannan ta fice daga sashen zuwa nata.
Wannan abincin da Fad'ima ta kawo ya samu ya ci ya ragewa yaran.
Sannan ya samu natsuwa ya shirya ya Kuma fita.....
**********
FA'IZA kuwa tana can ta na can tana sana'ar tata wato yawo bata nan bata can har 9:00 sannan ta nufo gida......
Follows me on wattpad@ummu-inteesar.
Share & comment
###ummu-inteesar❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
_Story & written by RUKAYYA Ibrahim Lawal (ummu-inteesar)✨✨_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*MARUBUCIYAR:*
*SOYAYYAR MEERAH.*
*DEDICATED TO HASSAN ATK& HUSSAIN 80K*
_Kamar yanda kuka ji daga farko cewa wani sashe na wannan labarin true life story ne._
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.3
Napep ce ta sauke ta adai-dai Kan layin gidan. Cikin hanzari ta nufi gate din Bayan ta sallami Mai napep d'in.
A ranta tana addu'ar Allah yasa d'an sa'idon nan(FAWWAD) Bai dawo ba har yanzu.
Bawai dan tana tsoron shi ko dan daren da tayi ba, a'a ita bak'in surutun nan nashi ne bata so.
Tasan yanzun Yana ganin ta zai hau yi Mata wa'azi.
Ba ta ma damu da yaran da ta bari ba abinci ba.
A ganin ta tunda Fad'ima na nan basu da matsalar abinci.
Ta sani Fad'ima bata da rowa ko da bata rok'a ba zata ba su.
Ta manta cewar fad'ima ma'aikaciyar jinya ce ko da yaushe za'a iya neman ta ta fita.
*************
Tsaye yake a tsakar gidan yana kai-komo cikin tsananin b'acin Rai da damuwa.
Jira kawai yake yaga ta inda zata b'ullo masa.
Ganin ta yayi kamar an jefo ta ko sallama batayi ba.
Dan a iya zaton ta bai dawo ba, da taga tsohon babur d'nshi a waje.
Turus tayi nadan lokaci a lokacin data ganta a gabanshi kafin ta d'auke kai ta cigaba da tafiya zuwa d'akin ta ba tare data mai magana ba.
Hakan da tayi ba k'aramin harzuk'a shi yayi ba. Wato banda raini ma har da iskanci da wulak'ancin a harkar ta.
Yau ta kaishi bango dole yayi k'ok'arin taka mata burki idan ba haka ba zata mayar dashi mijin tace.
**************
A harzuk'e ya shiga d'akin in da ya tarar tana shirin shiga wanka.
Tsawa ya daka Mata tare da fad'ar ke! FA'IZA iskancin naki ya fara yawa. Ba zan lamunci wannan yawon gantalin na ki ba, a ce ina matsayin mijinki amma banda wata darajar da zaki nemi izini na idan zaki fita?.
To ya isheki haka, daga yau sai yau bana son in k'ara ji ko ganin kin fita daga gidannan idan ba haka ba......
Idan ba haka ba me zakayi? Ta katse mishi zancen.
Ki gwada kika abunda zan iyayi. Ya fad'a yana huci tamkar zaki. Ya d'aura da cewa ba zai yiwu ki din ga barmun yara da yunwa suna b'irari a unguwa ba.
To idan bazaki iya kula dasu ba ki fad'amun na nemo wacce zata iya na aura.
Kin san halin da yaran nan ke shiga bayan bakya nan? Ya zaki dinga yiwa yaranki horon yunwa? Kina so su lalace ne? Wa kika barwa yaran a lokacin da kika fita?. Ya jero mata tambayoyin.
Ido ta zuba mishi yayin da yake ta surfa mata masifa kamar bashi ba. Ashe gaskiya ne da akace mai hak'uri Bai iya fushi ba?.
A gaskiya FA'IZA ta tsorata da yanayinsa, da maganarsa ta cewa zai k'aro aure. Amma sai ta dake cikin k'araji tace ka kawo wata mana.
In ka iya ma ka auro matan garin nan baki d'aya.
Ko da yake wacece ma zata iya auren matsiyaci kamar ka?.
Ko ni banda k'addara me zan yi da matalauci irinka?
Kana ganina kasan ni matar manya ce kadd'ara ce kawai ta fad'amin na aure ka.
Ya isa haka FA'IZA! Ya Kuma daka Mata tsawa a karo na biyu.
Ita ma cikin d'aga murya take cewa bai isa ba FAWWAD. Dole sai na dire zance na kamar yanda na k'yale ka ka dire naka.
Ta cigaba da cewa yara da kake magana kasan na fika son su nida nayi nak'uda na haifesu.
Kuma fad'ima na barwa amanar yarana nasan zata kula dasu.
************
Daga haka ta shige toilet ranta na k'una.
D'an sa ido kawai ta fad'a a ranta.
Shi kuwa FAWWAD sulalewa yayi ya zauna a k'asa Yana huci bak'aramin bata masa rai matar sa tayi ba a yau.
Dafe kansa yayi Yana jin yanda yake barazanar tsagewa kalamanta yake tunanowa suna soya masa rai.
A bayyane yace Allah ya ganar dake gaskiya mata ta. Allah ka bani ikon cin wannan jarabawar ka yayemun wannan talaucin.
*************
Washe gari.
Zaune take a kitchen tana girkin rana. Wanda rabon da ta yi shi harma ta Manta.
Tana yi tana tunani gashi tana son fita yau, amma da ta tuna kalaman FAWWAD na jiya da yake cewa zai d'au mataki,Kuma zai k'ara aure dole ta hak'ura.
**********
Fad'ima ce ta fito zata gidan su kasancewar yau Sunday Ba tada duty.
Ganin part d'in FA'IZA a bud'e ya matuk'ar bata mamaki.
A ranta take tunanin ko dai FAWWAD ne ya dawo.
Sai tace dai bari ta shiga ta ganewa idon ta abunda tagani ya Bata mamaki sosai.
Wai yau Fa'iza ce a gida har da su girki? Tab!
Kasa b'oye mamakin ta tayi tace: FA'IZA kece a gida dai-dai wannan lokacin baki fita ba?.
Murmushi kawai FA'IZA tayi tace yau ba inda zani ai.
Jinjina kai fad'ima tayi tace ko kefa FA'IZA? Hakan yafi wallahi ki zauna a gidanki ki tsare mutuncinki ki kula da yaranki.
Amma ace ke kenan kullum kina Kan hanya wai ke ga y'ar kasuwa. Ko ni da nake aikin gwamnati ban fi ki fita ba...
Cikin alamun k'osawa da magan-ganun ta FA'IZA ta katse ta ta cewa fita zaki yi ne?
Eh, tunda bakya son gaskiya ai dole ki katse ni. Ta fad'a tare da juyawa tace gida za ni sai na dawo.
Takaici ya hana FA'IZA amsawa da badan tana cin amfanin fad'ima ba da yau ba abunda zai hana ta ci mata mutunci... K'wafa tayi tace magulmaciya kawai,kifi ruwa gudu ma......
Follow me on Wattpad@ ummu-inteesar
#share &comment.
#ummu-inteesar❤❤❤⚡
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by Rukayya Ibrahim* *lawal(ummu-inteesar)✨✨*
*Dedicated to HASSAN ATK& HUSSAIN 80K*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.4
Yinin ranar dai FA'IZA bata fita yawon gantalin nata ba, saboda tsoron matakin da FAWWAD yay mata barazanar ɗauka.
A haka ta yini ba walwala sai dai a ranar yaranta sun dawo daga makaranta sun sameta ba ƙaramin daɗi suka ji ba.
Idah ce tayi tsalle ta faɗa cinyarta tana cewa Mommy yau baki fita ba?.
Murmushi tayi ta dubi y'arta cikin kulawa tace eh.
Aabid ne ya Kuma jefo Mata wata tambayar, Amma dai Mommy daga yanzu ba zaki ƙara fita ki bar mu ba Koh? Bai jira ta amsa ba ya cigaba da cewa jiya da baki dawo ba har kuka mukayi saboda yunwa dan maman su Salim ma fita tayi.
Dan Allah Mommy kar ki Kuma fita ki barmu ba abinci,mun wahala jiya....
Ya ƙarashe zancen yana ƙoƙarin yin kuka.
Shafa kansa tayi tare da Kuma rungume idah a jikinta.
Tace to yarana kuyi hak'uri zan San yanda za'ayi.
Kuma fitar ma da nake dan na inganta rayuwar ku ne, tunda dadyn naku tsiya ta mai yawa har baya iya kawo abunda zai ishe mu.
"A'a Mommy, dady fa yana ƙoƙari, yana siyo mana duk abunda muke so. Aabid ya bata amsa.
Murmushin yaƙe kawai tayi tace yaro kenan. Simrah ce ta ƙaraso gurin da ɗan gudunta ta ɓoye a bayan maman ta.
Aabid ya janyota jikinsa yace ya akayi sim? Sabiy ne ta faɗa a cikin yarensu na yara tare da nuna k'ofa da yatsa.
Inda sabir (ɗan 3years) yaron faɗima ya biyo bayan ta da gudu shima...(su sim yau an samu zama a gida harda su tsokano faɗa🤔😜).
********************
FAWWAD ma yasha mamaki kuma yayi matuƙar farinciki da ya tarar da matar tasa a gida yau.
Abunda ya daɗe rabonshi da gani.
Abinci ta kawo Masa yaci yana jin daɗi a ransa na wannan nasarar da yafara samu.
Ba shakka barazana ta ce tayi aiki,idan da ba haka ba a yanda nasan FA'IZA ba abunda zai zaunar da ita gida a yanzu.
Idan kuwa har hakane zan cigaba da mata wannan barazanar har ta daina wannan yawon. FAWWAD ne ke wannan tunanin a ransa.
Bayan ya ci ya k'oshi ya ja tsohon babur ɗinsa ya Kuma fita kamar kullum saida ya sauke yaransa a islamiyyar su sannan ya wuce wurin aikinsa.
*************
Zaune take ita kaɗai a ɗaki abun duniya duk ya dame ta.
Zantukkan FAWWAD na jiya sun razana ta sosai,duk da tana ganin faɗa kawai yakeyi da wanne kuɗin zai ƙaro aure? Um! Um! FA'IZA namiji baya da tabbas,tunda kika ji ya faɗa tabbas zai iya aikatawa. Wata zuciyar ta faɗa mata.
Da tunanin yay mata yawa sai kawai ta tashi ta rufe kofar part ɗinta, ta nufi part ɗin faɗima.
A can ne ta tarar da sabon injimin wankin da faɗima ta siye.
Nan da nan fuskar FA'IZA ta bayyanar da hassadarta ƙarara.
Kasa jurewa tayi saida ta tambaye ta kuɗin injimin wankin, ta faɗa mata.
Sai 8:00pm FA'IZA tabar part ɗin faɗima.
Dan su Aabid ma da suka dawo nan suka zauna tare da MOMMYNSU.
Sai da suka ci abincin faɗima sannan suka bar part ɗin.
Dama FA'IZA akwai kwaɗayi haka take zuwa ta yiwa faɗima zaune, duk abunda ta dafa sai sunci ita da yaranta.....
#share & comments.
#follow me on wattpad @ummu-inteesar
##ummu-inteesar ce.
❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
Y'AR GANTALI
(Mai hangen na wani)
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (ummu-inteesar)
DEDICATED TO HASSAN ATK & HUSSAIN 80K
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
BISMILLAHI RAHMANIR-RAHIM
⚡💫⚡ No.5
A ranar dai ko baccin kirki FA'IZA bata samu yi ba.
Kwana tayi tana tufka da warwara,tana tunanin yadda zata fita gobe.
Dan Iya yau kawai da bata fita ba duk sai taji ba daɗi.
FAWWAD kam yau acikin walwala ya kwana bayada damuwar komai a ransa.
WANENE FAWWAD?
Fawwad ɗa ne ga Alhaji Umar Ahmad.
Wanda ya kasance babban ɗan kasuwa A jihar tasu.
Matansa biyu, hajara ce uwar gida sai kuma bilkisu amarya.
Hajara nada yaya uku maza, Hafeez, Fahad da kuma FAWWAD.
Inda bilkisu keda yaya biyu mata,
Ramlah da Nadiya.
Su kaɗai ne y'ay'ansa.
Alhj Umar ne ya sayawa Fahad da FAWWAD wannan gidan a lokacin da zai masu aure, dan Hafeez ya shekara uku da yin aure lokacin.
Mahaifinsu ne ya masu komai na aure daga kan sadaki har lefe,da duk abunda akayi na bikin da kud'insa ne mata kawai suka kawo dakansu.
Aka Daura masu aure Fahad da faɗima,FAWWAD da FA'IZA.
Bayan aurensu da sati biyu mahaifinsu ya tara su yace dasu "bakomai yasa nace kuzo ba sai dan muyi wata muhimmiyar magana."
"Kunga dai yanzu ku magidanta ne, kowanne ku yanada nauyin iyali akansa,shi yasa na tara ku domin inji ra'ayinku akan sana'a."
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa"shin zakuyi kasuwanci irin nawa ko yaya?"
Fahad ya ɗago ya dubi mahaifin nasu yace "Abba Ni dai zan yi kasuwanci irin naka,dama ina da ra'ayi akan haka."
Ya ɗan tsagaita yana duban FAWWAD sannan ya mayar da dubansa ga Abbansu ya ce "sai dai bansan ra'ayin k'anina ba, ko yanada wani ra'ayin saɓanin wannan."
Alhj Umar ya dubi FAWWAD tare da tambayar shi "Meye ra'ayinka? Zaka yi kasuwanci irin nawa?"
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce: "Gaskiya Abba ni bana ra'ayin kasuwanci, nafi son nayi sana'ar hannu kafin aikin gwamnati ya samu."
Shikenan, "yanda kuke so haka za'ayi zan bawa kowannen ku jari yaje yayi irin sana'ar da yake so."
"Sai dai wani hanzari ba gudu ba, bayan na baku jari ina so kowa ya tsayu akan ƙafarsa."
Kada ɗayanku ya dawo mun neman wata bukata tashi ko ta iyalansa daga baya, kun fahimce Ni?. Abbansu ya faɗa.
Cikin gamsuwa kowannen su ya ɗaga kai Alamar eh, suka masa godiya suka tashi.
**************
Bayan ya basu jari kowanne ya fara harkokin shi.
Fahad ya shiga kasuwancin siyar da atamfofi,da yaduka.
Inda FAWWAD yayi amfani da jarinsa ya siye katako da k'usoshi da duk abunda ake bukata dan yin sana'ar capenter.
FAWWAD ya fara sana'arsa inda yake yin saitin kujeru yana siyarwa.
Yana da yara huɗu a lokacin waɗanda ke Aiki k'arkashin sa.
Haka kasuwa ta yita buɗewa FAWWAD.
Yana samu ciniki sosai.
Bayan shekaru huɗu komai ya fara lalacewa kasuwar kujeru ta tsaya cak.
Saboda yawan rigimar da FA'IZA Ke deb'o mai a wajen mutane.
Haka yayi ta siyar da saiti-satin kujerunsa yana biyan bashin da FA'IZA ke d'aukowa.
Dak'yar ya tsira da jarin da zai yi wasu a gaba.
Fahad kuwa kasuwa ta buɗe Allah ya sanya albarka a kasuwancin sa.
Har ya fara fita ƙasashe gurin saro kayan da yake siyarwa.
Hakan yasa arzikin Fahad ya babanta dana FAWWAD cikin lokaci ƙalilan ya kuma gyara waje da cikin part ɗinsa sosai.
Wannan ne yasa daga kallon farko zaka fahimci gidan na mutum biyu ne kuma ɗaya yafi ɗaya arziki.
*************
WACECE FA'IZA?
FA'IZA Yace ga Malam Isma'il sabo wanda ya kasance talaka ne shi,yana sana'arsa ta siyar da itace a wata unguwa dake maƙwabtaka da tasu.
Amma duk da haka yana iya ƙoƙarin sa akan ciyar da iyalansa.
Matarsa ɗaya inna luba,
Yaransa huɗu, Habib⚡💫⚡ No.5
A ranar dai ko baccin kirki FA'IZA bata samu yi ba.
Kwana tayi tana tufka da warwara,tana tunanin yadda zata fita gobe.
Dan Iya yau kawai da bata fita ba duk sai taji ba daɗi.
FAWWAD kam yau acikin walwala ya kwana bayada damuwar komai a ransa.
WANENE FAWWAD?
Fawwad ɗa ne ga Alhaji Umar Ahmad.
Wanda ya kasance babban ɗan kasuwa A jihar tasu.
Matansa biyu, hajara ce uwar gida sai kuma bilkisu amarya.
Hajara nada yaya uku maza, Hafeez, Fahad da kuma FAWWAD.
Inda bilkisu keda yaya biyu mata,
Ramlah da Nadiya.
Su kaɗai ne y'ay'ansa.
Alhj Umar ne ya sayawa Fahad da FAWWAD wannan gidan a lokacin da zai masu aure, dan Hafeez ya shekara uku da yin aure lokacin.
Mahaifinsu ne ya masu komai na aure daga kan sadaki har lefe,da duk abunda akayi na bikin da kud'insa ne mata kawai suka kawo dakansu.
Aka Daura masu aure Fahad da faɗima,FAWWAD da FA'IZA.
Bayan aurensu da sati biyu mahaifinsu ya tara su yace dasu "bakomai yasa nace kuzo ba sai dan muyi wata muhimmiyar magana."
"Kunga dai yanzu ku magidanta ne, kowanne ku yanada nauyin iyali akansa,shi yasa na tara ku domin inji ra'ayinku akan sana'a."
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa"shin zakuyi kasuwanci irin nawa ko yaya?"
Fahad ya ɗago ya dubi mahaifin nasu yace "Abba Ni dai zan yi kasuwanci irin naka,dama ina da ra'ayi akan haka."
Ya ɗan tsagaita yana duban FAWWAD sannan ya mayar da dubansa ga Abbansu ya ce "sai dai bansan ra'ayin k'anina ba, ko yanada wani ra'ayin saɓanin wannan."
Alhj Umar ya dubi FAWWAD tare da tambayar shi "Meye ra'ayinka? Zaka yi kasuwanci irin nawa?"
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce: "Gaskiya Abba ni bana ra'ayin kasuwanci, nafi son nayi sana'ar hannu kafin aikin gwamnati ya samu."
Shikenan, "yanda kuke so haka za'ayi zan bawa kowannen ku jari yaje yayi irin sana'ar da yake so."
"Sai dai wani hanzari ba gudu ba, bayan na baku jari ina so kowa ya tsayu akan ƙafarsa."
Kada ɗayanku ya dawo mun neman wata bukata tashi ko ta iyalansa daga baya, kun fahimce Ni?. Abbansu ya faɗa.
Cikin gamsuwa kowannen su ya ɗaga kai Alamar eh, suka masa godiya suka tashi.
**************
Bayan ya basu jari kowanne ya fara harkokin shi.
Fahad ya shiga kasuwancin siyar da atamfofi,da yaduka.
Inda FAWWAD yayi amfani da jarinsa ya siye katako da k'usoshi da duk abunda ake bukata dan yin sana'ar capenter.
FAWWAD ya fara sana'arsa inda yake yin saitin kujeru yana siyarwa.
Yana da yara huɗu a lokacin waɗanda ke Aiki k'arkashin sa.
Haka kasuwa ta yita buɗewa FAWWAD.
Yana samu ciniki sosai.
Bayan shekaru huɗu komai ya fara lalacewa kasuwar kujeru ta tsaya cak.
Saboda yawan rigimar da FA'IZA Ke deb'o mai a wajen mutane.
Haka yayi ta siyar da saiti-satin kujerunsa yana biyan bashin da FA'IZA ke d'aukowa.
Dak'yar ya tsira da jarin da zai yi wasu a gaba.
Fahad kuwa kasuwa ta buɗe Allah ya sanya albarka a kasuwancin sa.
Har ya fara fita ƙasashe gurin saro kayan da yake siyarwa.
Hakan yasa arzikin Fahad ya babanta dana FAWWAD cikin lokaci ƙalilan ya kuma gyara waje da cikin part ɗinsa sosai.
Wannan ne yasa daga kallon farko zaka fahimci gidan na mutum biyu ne kuma ɗaya yafi ɗaya arziki.
*************
WACECE FA'IZA?
FA'IZA y'a ce ga Malam Isma'il sabo mai itace.
Mahaifinta ya kasance talaka ne shi,wanda ke sana'ar siyar da itace a wata unguwa mai maƙwabtaka da tasu.
Duk da shi bawon Allah ne amma yana tsaye akan duk wata bukatar iyalansa, da tarbiyyar ƴaƴansa.
Matarsa ɗaya lubabatu yaranta na kiranta da Inna.
Ƴaƴansa huɗu,biyu maza biyu mata.
Habib,Fa'iz, FA'IZA da kuma auta Hadiza.
FA'IZA ta kasance yarinya ce rigimammiya mai kwaɗayi,hangen na wani da hassada tun lokacin kuruciya har takai (18years) bata sauya hali ba.
FA'IZA ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance,
Kaf unguwarsu ba budurwar da tayi kyanta.
Hakan yasa k'awayenta ke kiranta da MATAR MANYA.
Ba ƙaramin daɗi FA'IZA jeji ba idan an kirata da hakan,shi yasa ba kowane saurayi take kulawa ba duk da samari da yawa sun taya.
Amma acewarta ita ba matar ƙananun mutane bace.
Ana haka ne ta haɗu da FAWWAD matashin saurayi mai ji da kyau da k'uruciya.
Sai da FA'IZA ta binciki Asalinsa ta gano cewa babansa shahararren ɗan kasuwa ne garin sannan ta fara kulashi.
Har an saka masu ranar Aure ji take kamar tafi kowa ce yarinya a unguwar.
Yanda FAWWAD ke kyautata mata da dukiyar mahaifinsa yasa ta sakankance ta samu irin miji da take mafarki wato mai kuɗi.
Lefen da aka kawo Mata naji da faɗa yasa tafara wulak'ancin a unguwa a dole ita ga matar manya.
Hmmmmm readers yakuke gani?
Anyah FAWWAD shine irin mijin da FA'IZA ke mafarki kuwa?🤔🤔🤔
Taka a sannu FA'IZA kar reshe ya juye da mujiya.
# follow me on Wattpad@ummu-inteesar.
#share & comments.
UMMU INTEESAR CE.❤❤❤❤❤❤❤❤
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL* *(Ummu-inteesar)*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO HASSAN ATK & HUSSAIN 80K*
*30 jan.2020*
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.6
Haka dai FA'IZA tayi ta wulakanta k'awayen ta.
A bangaren inna Luba(maman fa'iza)
Itama ba ƙaramin farin ciki tayi ba y'ar lelenta ta samu miji mai kuɗi.
Dama can duk acikin ƴaƴanta ta fison FA'IZA wannan dalilin ne yasa komai FA'IZA zatayi dai-dai ne a gurin Inna,kuma ba wanda ya isa ya hana.
Inna ta taka muhimmiyar rawa gurin ɓata tarbiyyar FA'IZA ta hanyar ɗaure mata gindi tayi duk abunda take so. Duk da namijin ƙoƙarin da babansu ke yi kan tarbiyyar su.
Taka kowa take a gidan son ranta ba wanda ya isa ya nuna mata ko ɗan yatsa matukar inna na gidan.
Shi yasa FA'IZA bata ganin kan kowa da gashi har yayunta ta raina su.
Duk rashin mutunci da munanan dabi'un FA'IZA ba ta nunawa FAWWAD ko ɗaya daga cikin halinta ba.
Kwantar dakai tayi dan tasamu ta shiga gidan arziki.
A haka akayi auren FA'IZA da FAWWAD
Tun daga lokacin da FA'IZA ta gano cewa FAWWAD da dukiyar mahaifinsa ne ya auro ta, ta raina shi a lokacin ne kuma ta fara fito mai da halayenta da ta ɓoye mai a baya.
Haka dai FAWWAD yayi ta hak'uri da ita.
Bayan shekara ɗaya da auren su ta haifi santalelen ɗan ta mai kama da mahaifinsa sak ranar suna yaro yaci sunan Aabid.
Bayan shekaru biyu da haihuwar Aabid FA'IZA taje gidan yayanta Habib, ta nemi ya taimaka mata da kuɗi taja jari ta fara sana'a.
Cikin mamaki Habib ya ce da ita"FA'IZA wane irin rashin godiyar Allah ne dake?" "Yanzu duk dukiyar mijinki bata isheki ba sai kinyi wata sana'a?"
Tab'e baki tayi kafin tace" ashe fa yaudarar mu yayi dukiyar ta mahaifinsa ce kuma yanzu ya cire su daga cikinta,jari kawai ya basu shikenan fa"
Ba yanda Habib ya iya haka ya ciro dubu ashirin ya bata.
Ya bata dan Allah da zumunci ne kawai,dan da halinta zai bi baya jin zai iya bata ko k'wandalar sa.
****************
Wata rana FA'IZA ta nemi izini a gurin mijinta akan ta na so ta fara sana'a.
Ya nuna mata ba wata matsala kuɗin jarin da zai bata ne kawai ba shi da. Domin shi ma nasa jarin yana neman karyewa.
Ta gaya masa ta na da kuɗin jarin, izni kawai take nema zata je kasuwa ta saro abunda ya kamata.
Kai tsaye FAWWAD ya amince dan aganin sa cigaban su ne duka.
FAWWAD bai san cewa wannan shi ne kuskurensa mafi girma da yayi a rayuwar aurensu ba.
Domin wannan amincewar tasa ita ce mafarin rushewar farin cikinsa.
Ita ce silar fara yawon gantalin da FA'IZA keyi.
************
Daga wannan ranar
Kullum sai ta fita wai ita ga yar kasuwa.
A lokacin kuma ta samu cikin Na biyu,
Duk da ƙaramin cikin dake jikinta mai laulayi ne, hakan bai hana ta yawon gantalin ta ba.
**********
Wata rana idan ta fita sai an rako ta gidan ta saboda laulayin da take yi.
Watarana har akan hanya take amai amma bazata fasa zuwa inda zata ba.
FAWWAD ya rasa yanda zaiyi da ita haka za ta janyo mai kashin kuɗin magani ga rigimar da take ɗebowa a waje.
A takaice har ranar da FA'IZA zata haihu bata zauna a gida ba saida ta fita.
A can nak'uda ta kamata sai da matar gidan da taje ta rako ta gidanta.
Allah dai ya kare bata haihu a hanya ba, suna shiga gidan haihuwa tazo gadan-gadan....
Hmmmmm!
Anyah fa'iza? Ina tsoron wata rana ki haihu kan hanya fa.🤔🤔
FAWWAD kana ban tausayi.
Follow me on wattpad@ ummu-inteesar.
Share & comment
#Ummu inteesar❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
_*Story & written RUKAYYA IBRAHIM LAWAL*_ _*(Ummu-inteesar)*_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
_*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*_
_*DEDICATED TO ATK PALACE GROUP*_
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.7
Hindatu matar da ta rako FA'IZA gida ita ce ta shiga sashen faɗima ta sanar da ita halin da ake ciki.
Wayarta kawai ta ɗauka suka nufi sashen FA'IZA ita da hindatu.
Fahad ta kira ta sanar mai shi kuma ya kira FAWWAD ya sanar dashi abunda ke faruwa.
*************
Yana zaune akan bencin da suke ajiyewa dan zama shi da yaransa yana tunani tare da juyayin halin da matarsa ta saka sa aciki.
Kiran Fahad ya shigo wayarsa dagawa yayi tare da sallama yana cewa "yaya ina wuni?"..
Fahad bai tsaya amsawa ba ya ce "ka je gida da sauri ga matar ka can an maido tana nak'uda"
Cike da ruɗewa FAWWAD yaja tsohon babur ɗin sa ya nufi gida, yana tunanin da ya saba.
Salati faɗima tayi (a lokacin da ta suka tarar da FA'IZA har ta haihu a bakin k'ofa dakinta) tare da faɗar" Allah Nagode ma,wace irin mata ce ke FA'IZA?" "Da kin haihu a titi fa? Me zaki faɗa wa mijinki?.
Gaskiya ki canja hali tun kan lokaci ya k'ure miki FA'IZA"
Yanzu da badan wannan baiwar Allah ba da tuni kin haihu a titi..........
**********
Sai da suka tattare komai suka gyara gurin sannan suka gyara baby girl ɗin tare da taimakawa FA'IZA ta gyara jikinta.
Sa'annan hindatu tayiwa faɗima sallama zata tafi.
Godiya faɗima ta mata,taje part ɗin ta ta ɗauko turmin atamfa da kuɗi ta bawa matar.
Itama matar godiyar ta yima faɗima sannan ta tafi.
*****************
Tun a hanya FAWWAD ya kira iyayen FA'IZA ya sanar masu halin da ake ciki.
***********
Sai bayan shekara huɗu sa'annan FA'IZA ta kuma haihuwa.
Wannan karon kam, FAWWAD bai bari tayi wannan shegen yawon ba domin kuwa yarjejeniya sukayi akan zata zauna gida har ta haihu tayi arba'in ba tare data fita ko'ina ba shi kuwa zai bata 50,000 Naira,
Da tayi arba'in.
Hakan ne yasa ta hak'ura domin tana matuƙar son k'udi dama su take fita nema a faɗar ta to gasu har gida.
**************
Shi yasa aka haifi simrah cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.....
Har tayi kwana hamsin da haihuwa bata je ko'ina ba,
Ba ƙaramin daɗi FAWWAD yaji ba, ganin ta hak'ura da gantalin na dogon lokaci yasa yayi tunanin ko ta daina ne gaba ɗaya.
Bai san cewa yanzu ne ma zata fara ba kuɗinta kawai take jira ya bata har ta gama kirga abunda zatayi dasu.
A ranar da ya bata kudinta a ranar ta koma bakin sana'ar ta sai dawowa yayi ya tarar da part ɗin a rufe.
Simrah dai ba'ayi renon Cikinta a titi ba,kuma ba'a haife ta a titi ba, saidai anyi renon ta da shayar da ita a titi....😜
Dawowa daga labari.
Washe garin ranar FA'IZA taje neman aron kuɗin da zata siye injimin wanki.
Babban na faɗima takeso ta siya, dan faɗimar tasan cewa fa ba ita kaɗai ce mai arziki ba.....
Gun (Hashim) abokin FAWWAD wanda suke mutunci sosai, ta tafi ta ce dashi FAWWAD ne ya ce tazo ta aro mai dubu Saba'in a hannunsa domin shi yana jin nauyinsa ne bazai iya zuwa ba, kuma yana buk'atar kuɗi ne da gaggawa.
Bai kawo komai a ransa ba ya ɗauki dubu saba'in ɗin ya bata, ya ce "amma dan Allah ki sanar dashi ƙarshen wata nakeson kuɗin,dama nasan yanada alkawari ne na bashi."
Murmushin cin nasara FA'IZA tayi tare da cewa "to ngd malam Hashim."
Juyawa tayi tabar gurin tana k'issima abubuwa da yawa a ranta, wanda ita kaɗai tasan ko menene.....
To readers komai FA'IZA ke k'issima wa a ranta???🤔🤔🤔🤔🤔
Follow me on wattpad@ ummu-inteesar
Share & comment
Ummu inteesar❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL* *(ummu-inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
_*DEDICATED TO ATK PALACE GROUP*_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡No.8
Kai tsaye gidansu ta nufa, dan ta nunawa Inna kuɗin. Dama duk abinda take yi da sanin innar, dan kullum sai taje gida.
Amma bata zuwa sai lokacin da ta tabbatar babansu yana wurin sana'ar sa, gudun kar ya mata faɗa.
Cikin rashin sa'a suka yi kicibis da baba a lokacin da zata fito daga gidan shi kuma zai shiga.
"Sannu da dawowa baba, ina wuni?"
Amsa wa yayi tare da cewa "me ya fito dake gidan mijin ki da Wannan lokacin"
"Dama baba uhmm, amm dama..." Ta soma magana a diririce.
"Dama me?" Baban ya tambaya.
Fa'iz dake kokarin fitowa daga gidan ya gansu a tsaye,ya tsaya.
Sai a lokacin ya ce "Ai bata da amsar da zata baka ne baba, domin kullum sai tazo gidan nan, idan nayi magana Inna ta ce ba ruwan."
Kullum? Baba ya tambaya tare da fiddo ido waje alamar mamaki.
Kwarai kuwa Fa'iz ya faɗa.
Kallon zaki gane kuranki baba yayi mata tare da cewa "daga yau kar in sake jin kin zo gidan nan ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba, kin jini?" Idan ba haka ba zan haɗu dake ne.
Ya juya ga fa'iz "idan ka kuma ganin ta gidan nan ba dalili ka sanar dani."
"Insha'allah" fa'iz ya ce.
Baba ya mayar da duban sa gare ta tare da daka mata tsawa "mekike jira da ba zaki fice mun daga gida ba? mutuniyar kawai.
Cikin hanzari ta rab'a ta gefensa ta fice adai-dai lokacin da yake cewa "ita ma wacce ke ɗaure miki gindin zamu haɗu da ita ne ai."
****************
Tana barin gidan taje ta samu wata k'awarta bazawara ta rakata ta siyo injimin wankin na dubu saba'in, kana ta wuce gida dan ajiye shi.
Gun faɗima ta shiga (bayan ta yiwa injimin mazauni adai-dai inda faɗima ta ajiye nata a part ɗinta).
Da sallama ta shiga suna gaisawa ta ce" maman salim zo muje sashena kiga wani abu."
Ba musu faɗima tabi bayanta tana tunanin menene?
Gun injimin wankin ta kaita ta nuna mata tare da ce wa "ki tayani murna nima dai yau nayi injimin wanki.
Cikin mamakin inda FA'IZA ta samo kuɗi haka ta ce: "Ai kuwa yayi kyau kamar dai irin nawa na jiya."
Cikin gadara FA'IZA ta ce sake dubawa dai, wannan babban naki ne ko kamfanin su ma ba ɗaya bane, haka kuɗin ma da banbanci."
Ƙara cika da mamaki faɗima tayi me matar nan take nufi,kodai tana hassada ta ne?.
Amma sai ta haɗiye mamakin ta ce "eh kuma fa hakane sai yanzu na lura, nawa ne kuɗin sa halam?.
Murmushi FA'IZA tayi ta ce "dubu 80,000 na siye shi, kinga naki kuwa jiya kince mun 50,000 ne, kinga da bambanci ko agun girma ma."
Sai a yanzu faɗima ta tabbatar da cewa magana ce FA'IZA ke gaya mata, ta tabbata kenan FA'IZA na hassadar ta. A zuci tayi zancen.
*****************
Bayan wasu kwanaki FAWWAD yana gun sana'arsa suna ta faman aiki shida yaransa, sai ga Hashim ya zo gurinsa.
Bayan sun gaisa Hashim ya ce "dama nazo karɓar kuɗi na ne, banso zuwa ba domin ina jin nauyin ka,sai dai inada uzurin da zanyi da kuɗi na ne na ga kamar ka manta ne shiyasa nazo"
"Wanne kuɗi kuma malam Hashim bangane ba?" FAWWAD ya tambaya a mamakince.
Murmushi Hashim yayi yace "inaga ka manta ne kuɗi na daka aiki Matarka FA'IZA ta arar maka gurina nake nufi."
Na kuwa gaya mata ta sanar da kai ƙarshen wata nake son kuɗina, sai naga har an shiga sabon wata yau kwana goma kenan shiru shiyasa na biyo sahu."
"Kuɗi kuma FA'IZA ta aro? Yaushe na aike ta?" Ya faɗa ciki-ciki.
Ashe Hashim ɗin ya ɗan ji kadan.
"Me kake cewa Malam FAWWAD bakai ne ka aiko ta ba?"
"A'a nine na aika ta,kayi hak'uri mantawa nayi ban mayar ma kuɗin ka ba. Amma ta sanar dani."
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin dubi Hashim da ke tsaye yana jiran ya bashi kuɗin sa.
Ya ce "dan Allah kayi hak'uri Hashim yanzu dai banida kuɗi, amma zan baka ko zuwa nan da sati ɗaya ne."
"Shikenan bakomai amma dan Allah malam FAWWAD kayimin alƙawarin bani kuɗin nan kafin sati ɗayan." Hashim ya faɗa.
"Insha'allah" FAWWAD ya faɗa.
Hashim yamai sallama yabar gurin.
Komawa FAWWAD yayi ya zauna dabas akan benci ya dafe kansa da hannunsa biyu, Allah na gode maka da wannan jarabawar, sai yaushe ne zaki daina ɗebomin rigima?. A ɗan bayyane ya faɗa haka.
Sai a lokacin ya tuna yaga injimin wanki a gida daya tambaye ta ina ta samu kuɗin sayensa, sai ta ce mai kuɗin sana'arta ne da take tarawa.
Kasa zama yayi ya tashi ya ja babur din shi ya nufi gida.
***************
Ko da ya shiga gidan bata nan ta fice wurin yawon gantalin nata da ta sama yi.
Sai dai me tun a kofar part ɗin yake ganin hayak'i tare da jin ihun yaransa.
Da gudu ya ƙarasa ciki Aabid yagani a bakin kofar ɗaki ya ɗora hannu akai yana ihu, yana ganin daddyn su ya shigo ya faɗa jikinsa yana kuka tare da nuna mai kitchen da ya fara kamawa da wuta ya ce dady idah na ciki......
Ai bai tsaya ƙarasa jin zancen ba kawai ya faɗa kitchen ɗin da gudu domin ceto rayuwar yar sa da take ta ihun neman taimako.....
Hmmm! To fa readers, garin yawon FA'IZA Tana neman jefa rayuwar ƴaƴanta a halaka.
Follow me on wattpad @ ummu-inteesar
Share & comment
#ummu-inteesar
❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu-inteesar)*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO ATK PALACE GROUP*
Fans ku tayani da addu'a Allah ya bani lafiya.
Kafata ke ciwo sosai shiyasa,kuyi maleji da wannan.
Ina alfahari daku
Members na yar gantali fans group.
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.9
Yana shiga ya nufi gurin Aa'idah dake kwance tana ihu wuta naci a jikinta.
Ƙarasawa yayi cikin rikicewa da ruɗewa ya rasa ta ina zai fara taimakon ta, handkerchief ɗin dake aljihunsa ya zaro ya shiga kakkab'e mata wutar dake ci a jikinta. Anan wuta tayi nasarar laso hannayensa duka biyu.
Bai ko lura da hakan ba saboda ruɗewa,ya tallabo ta ya rungume bayan yayi nasarar kashe wutar jikinta, aguje ya fito da ita ya nufi hanyar gate inda Aabid ya biyo bayansa da gudu yana kuka.
Fitowar sa tayi dai-dai da shigowar motar Fahad cikin gate ɗin.
Cikin hanzari Fahad ya ƙara saurin motarsa ya nufo inda ɗan uwansa ke tahowa riƙe da yarsa a hannu duk fatarta ta sab'ule.
A firgice Fahad da faɗima suka fito a motar suka nufo shi, hannu faɗima ta mik'o dan ta karbi idah, ƙara ƙanƙame ta yayi ajikinsa yana kallonta hawaye na bin kumatunsa.
Sai a lokacin Fahad ya lura da wutar dake cin gidan.
A ruɗe yace faɗima ke ja motar ki kaisu asibiti Ni zan tsaya anan nakira yan kwana-kwana.
*************
Gidan baya ta buɗewa FAWWAD ya shiga rungume da idah.
Aabid ma ya shiga ya zauna kusa da dadynsa tare da kifa kansa cinyar dadyn nasa ya na cigaba da kuka.
Zagayawa faɗima tayi ta shiga mazaunin driver ta tada motar asibiti mafi kusa da su ta nufa.
****************
FA'IZA kuwa tana can gurin sana'ar Tata tun 9:30am da tabar gidan, ta shiga wannan gidan ta fita wancan riƙe da ƙatuwar ledar dake ɗauke da kayan sana'arta aciki.
Yau dai hijabai,wandunan yara,hulunan yan mata da makamantan su, sune ta ɗauko.
Kasancewar su customers ɗin ta ke buƙata a yau.
Ba ita ta nufo gida ba sai 8:30pm, aganinta ma ta dawo da wuri,domin yau bata je gida ba saboda gargaɗin da baba ya mata.
Tun da ta shigo layin gidan taji gabanta na faɗuwa.
Ƙara saurin tafiyarta ta,tana tura gate ɗin ta ji shi a rufe, hankalin ta ya tashi gabanta na tsananta faɗuwa.
"Hakan na nufin ba kowa a gidan kenan? Meyafaru? Ina Faɗima ko tana asibiti ne gun aikinta? meyasa FAWWAD bai dawo ba har yanzu?"
Ta tambayi kanta tambayar da bata da mai amsa mata ita.
Dam! K'irjinta ya buga da ƙarfi da ta tuna yaranta, "ina yarana?" Ta faɗa a bayyane.
Juyo wa tayi ta shiga mak'otansu tana tambaya.
Suka sanar mata cewa "gobara akayi a bangaren ta."
Cikin tsananin tashin hankali ta ce "ina mijina da yarana? Badai abinda ya same su ko?"
**************
Suna shiga asibitin kai tsaye emergency suka nufa, aka kawo gadon ɗora mara lafiya, miƙa masu ita yayi.
Idanun nurse ɗin suka sauka a kan hannun FAWWAD dake a k'one, nurse ɗin ya ce "kaima fa Kanada buƙatar taimako."
Sai a lokacin faɗima ta lura da hannun FAWWAD dake a sab'ule.
Kukan da take ƙoƙarin riƙewa ne ya k'wace mata, cikin kuka ta ce "Wannan wace irin masifa ce? Wace irin shed'aniyar mata ce ke FA'IZA? Gashi ran y'arki na neman salwanta, lafiyar mijinki ta tab'u saboda yawon gantalin ki......
**************
Suka sanar mata cewa su dai ko da suka fito Fahad kawai suka gani da motar yan kwana-kwana amma suna kyautata zaton cewa suna asibiti."
Hannu ta ɗora a kai ta saka ihu tare da yada ledar hannunta a gurin tana faɗar "na shiga uku ni FA'IZA, me ya sami yarana?.
A rikice tabar gidan tare da daga waya ta kira faɗima tana tambayar ta yaranta da kuma mijinta suna ina?.
Dogon tsaki faɗima ta ja,sannan ta sanar mata sunan asibitin a tak'aice.
Napep ta tara zuwa asibitin.
***************
FAWWAD ne a kishingid'e kan gadon marasa lafiya inda yarsa ke kwance rai a hannun Allah duk an naɗe jikinta da bandage kwayar idonta kaɗai kake iya gani.
Saboda azabar da take ji ko kuka ta kasa yi sai hawaye da ke bin gefen idonta.
Tunani kawai yake tare da nadamar damar da ya bawa FA'IZA ta yin sana'a,
Bayan ta janyo masa asara mai yawa a rayuwarsa, gashi a dalilin yawon gantalin ta tana neman salwantar masa da rayuwar ƴaƴansa.
Abinda yafi damunsa shine yanzu a'ina zai samo kuɗin jinyar y'arsa? Ga bashi da ta ciyo mai na kuɗi masu yawa, wanda idan ma ya siyar da kujerunsa har jarin ba zai tsira da shi ba wurin biyan bashin.
Ga abbansu ya gargad'e su akan zuwa gunsa da buƙatar iyalansu bayan ya basu jari....
**************
Ya na cikin wannan tunanin ne FA'IZA ta shigo ɗakin tare da sallama.
Kallo ɗaya ya mata ya kauda kanshi gefe daya.......
😱😱 Allah Sarki FAWWAD ka haɗu da jarabawar rayuwa..😭😭😭
Follow me on wattpad@ Ummu inteesar.
Share & comment
Ummu inteesar
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (ummu-inteesar)*
*DEDICATED TO ATK PALACE GROUP*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.10
Tun daga bakin kofar ta hango y'arta a kwance duk an nad'e ta da bandage da gudu ta ƙarasa bakin gadon tana ƙarewa y'ar ta kallo.
Kuka ta fashe dashi ganin yanda kyakkyawar yarta ta dawo a yau.
Dogon tsaki FAWWAD ya ja kana ya miƙe yabar ɗakin zuciyarsa cike da tsanar FA'IZA.
Faɗima ma dogon tsaki tayi haɗe da miƙe wa zata bar ɗakin, saurin riƙe mata hijab FA'IZA tayi haɗe da tambayar ta "meyafaru da ƴaƴa na faɗima?" "Ina Aabid ɗina? Saboda ruɗewa ma ko Aabid ɗin bata gani ba Alhali yana kwance kan tabarma kusa da ita.
Wani uban tsaki Faɗima ta kuma ja sannan ta fuzge hijab ɗin ta da FA'IZA ta riƙe, tayi gaba abin ta ba tare da ta ce mata ci kanki ba.
A waje ta sami FAWWAD a tsaye ta mishi sallama tare da ƙara bashi hak'uri da kwantar mai hankali akan abinda ya faru.
"Kayi haƙuri FAWWAD kai kuma irin taka jarrabawa kenan ta samun gantalalliyar mata,nasan abun da ciwo amma ka jure Allah na tare da mai hak'uri, karka sakawa zuciyarka damuwar da zata illata lafiyarka kayi hak'uri." Faɗima ce ke gayawa FAWWAD haka
Godiya ya mata sa'annan ta mai sallama akan zata gida sai gobe tare da addu'ar Allah ya basu lafiya shida y'arsa.
****************
FA'IZA kuwa tun da kowa ya watse aka barta ita kaɗai a dakin sai yara, take ta kuka gashi ta rasa mai mata bayanin abunda ya faru da ƴaƴan ta.
Har ta fara tunanin kodai Aabid ɗin ya mutu ne, cike da tashin hankali ta d'ago idanun ta suka sauka akan Aabid dake barci sai ajiyar zuciya yake sauke wa Alamun yasha kuka.
Sai a yanzu ta samu y'ar nutsuwa,amma ba ta daina kukan ba. Domin kuwa FA'IZA tana matuƙar son ƴaƴanta, dan kawai yawon gantalin ya shiga jininta ne kawai kuma ba yanda zata yi yasa take barin su gida.
********************
Tun 8:00am mutanen gidansu FAWWAD suka zo dubiya har da Abbansa, domin ajiya sai 9:00pm Fahad yaje gidan ya sanar masu,da har sun shirya za su zo Abba ya ce su bari har da safe sai su je gaba ɗaya.
Bayan yin gaishe-gaishe tsakanin su dasu FAWWAD suka nemi guri suka zauna kowa na jimamin abinda ya faru.
Anan ne mama bilki ke tambayar FAWWAD yan da abun ya faru. Ya bata amsa da cewa nima bansani ba, dawowa ta kenan daga gun sana'ata na tarar da gobarar.
Mama Hajara ta ce bakowa a gidan ne lokacin da abun ya faru?.
Ya bata amsa da cewa "nidai bai tarar da kowa ba face yaran biyu."
Aabid da farkawarsa kenan ya rugo da gudu zuwa inda nadiya ke zaune ya faɗa cinyarta yana kuka.
A daidai lokacin da Abba ya karb'e zan cen da cewa "ita kuma maman tasu fa tana ina lokacin da abun ya faru?"
Kowa yayi tsit tare da duban FA'IZA da tunda aka fara zancen ta kifa kanta akan cinya tayi shiru.
***********
Sallamar da akayi ne ya sa kowa juyowa dan ganin su waye.
Fahad da faɗima ne suka shigo ɗauke da kayan abinci.
Sai ga Baba mai itace(baban fa'iza) da Fa'iz da Habib abayansu su ma sunzo dubiya.
Shigowarsu tayi dai-dai da lokacin da Nadiya ke rarrashin Aabid tana cewa "yi hak'uri yarona,yanzu ka gayamun meyafaru?"
Goge hawayen idonshi yayi tare da faɗar "idah ce ta ƙone saida nace ta jirani na zo amma bata ji ba ta kunna ashanar."
Kowa ya maida hankalinsa ga yaron dan son jin abinda ya faru.
Nadiya ta kuma tambayar sa "menene ya faru?, Gayamun me kukayi wutar ta tashi?.
Yaron ya soma basu labari kamar haka:
"Bayan mun dawo daga makaranta sai muka tarar mama bata nan kamar kullum, gashi muna jin yunwa sosai.
Indomien da dady ya siya mana da dare na dauko zan dafa, harna murd'a abun gas ɗin naga ba ashana a kitchen ɗin naje dakin mama dan na dauko inda na bar idah a kitchen ɗin........."
Follow me on wattpad @ummu inteesar
#share& comment
Ummu-inteesar❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO ANTY HAUWA ADMIN*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
_⚡💫⚡ No.11
Ina daga ɗaki naji ta na cewa "Abie kazo ga ashanar nagani, bari na kunna."
Daga ɗakin na ce "karta kunna tabari na zo amma kafin na fito sai ihunta najiyo tana wayyo! Wuta,Abie! Abie!! Ka taimake ni."
Yana kainan a labarinsa ya kuma fashewa da kuka.
Yayin da Nadiya taci gaba da rarrashin sa.
Ɗakin yayi tsit kamar ba masu rai a ciki banda sautin kukan Aabid ba abunda akeji.
***************
FA'iza da sai a lokacin taji meya faru ta fashe da matsanancin kuka.
Kukan ta ya ƙarawa mutanen ɗakin jin haushin ta, mussanman babanta.
A hasale ya isa gurin da take zaune, har ya ɗaga hannu zai mare ta,Abban su FAWWAD ya riƙe mai hannu tare da Faɗar "kayi hak'uri Malam idan rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba."
"Alhj. Da ka barni na maretan watak'ila ko tayi hankali." "Da aurenki zaki zauna kina yawon gantali a gari?" "Itama mai ɗaure mikin sai nayi mummunan saɓa mata gashi a dalilin ɗaure mikin da take kina shirin kashe mun jikoki."
"Kayi hak'uri malam tunda Allah ya tak'aita wahalar anan."
Kukan kawai FA'IZA ke yi da taga yanda kowa ita yake ɗora wa laifi, sun kasa gane cewa ƙaddara ce,ba laifin ta bane koda tananan bazai hana Faruwar k'addarar ba in an hukunto.
D'ago kai tayi ta kalli FAWWAD taga ko motsawa bai yi ba,bare tasa ran zai bawa baba hak'uri.
A haka taron ya watse, ran kowa a b'ace, ba wanda yakuma yiwa FA'IZA magana.
Ran babanta a matuƙar b'ace yabar gurin.
**************
FAWWAD ya kira babban yaronsa(na wurin sana'ar) ya sanar mai da cewa idan sun ƙarasa aikin da ya bari,ya siyar da kujerun duka ya kawo mashi kuɗin Sa'annan ya faɗawa sauran za su je hutun wata ɗaya, kafin yaji sauk'i.
****************
Bayan kwana uku Har asibitin yaron yazo ya duba su, sa'annan ya bawa FAWWAD kuɗin kujerun ya tafi.
FAWWAD ya kira Hashim ya tambaye shi nawa ne kuɗin, dan nuna masa yayi ya manta ne,Alhali bai ma sani ba.
Sai da hankalinshi ya tashi da yaji kuɗin har 80,000 ne,
Ya ɗauka irin dubu goma ɗin nan ne, har yayi planning idan yabawa Hashim kuɗinshi sauran sai yayi jinyar y'arsa dasu.
Gashi duka kuɗin dubu ɗari ne.
Jiki ba k'wari ya je gun hashim ya ciri kuɗin sa ya ba shi.
Hashim ya masa godiya ya tafi.
****************
FA'IZA kam abun duniya duk ya taru yayi mata yawa, yanzu kowa yabar kula ta,ba mai yi mata magana.
Aabid kaɗai ne a abokin hirarta, FAWWAD baya shiga shirgin ta ko abinci ta je gida tayi ta kawo baya ci,sai dai idan Faɗima ta kawo ko aka kawo daga gidansu yake ci.
Yau tsawon sati Uku kenan baya kula ta,duk ta shiga damuwa domin tana matuƙar son FAWWAD.
******************
Tsawon wata ɗaya kenan FAWWAD na zaune a gida bayada wata sana'a har idah taji sauki aka sallamo su.
Abbansa ne ma ya biya kuɗin jinyar Tata gaba ɗaya,magani kawai FAWWAD ke siya da kuɗin sa.
A yau ne kuma a ka k'ira shi daga gidan rediyon da ya nemi aiki a watannin baya(dama yayi diploma a mass communication)
Cewar yazo aiki ya samu.
Yayi matuƙar farin ciki da samun wannan aikin duk da a ƙaramin matsayi aka ɗauke shi.
Ya fara aikinsa cikin nasara,inda har a lokacin baya kula FA'IZA sai dai ayanzu idan ta kawo masa abinci yana ci.
*****************
FA'IZA kam ta gama rikicewa gashi ranar ta je gida dan bawa baba hak'uri Amma sai ya koro ta.
Ko da ya fara aikin bai sanar mata ba sai gani tayi ya daina dawowa da karfe 3:00 na rana kamar yanda yakeyi,A bakin Aabid taji cewar ya fara aiki a gidan rediyon VISION FM na garin.
Tun ranar da idah ta ƙone FA'IZA bata kuma fita yawon gantali ba tana gida tana kula da yaranta.
Iyakacin ta sashen Faɗima.
Ranar ta je gun Faɗima suna hira (domin a yanzu ta sauko daga fushin da take da FA'IZA).
Faɗimar ke cewa "yanzu dai abinda ya faru ya zama izina agareki,kinga yanda kowa ya juya miki baya a dalilin haka, yanzu ne lokacin da ya kamata ki nutsu ki cire wannan gantalin a ranki, dan watarana zaki iya rasa ɗaya daga cikin yayanki a dalilin haka."
Numfasa FA'IZA tayi kafin ta ce "wallahi nima ba a son raina nake fita kullum ba, kawai dan abinda yake bamu baya isar mune."
Wani numfashin taja ta sauke kafin ta ci gaba da cewa "ki duba kiga Yayansa ba abunda baya kawo maku najin daɗin rayuwa amma shi baya haka,iya kacin sa ya siye abinci ya ajiye shi ɗin ma baifi ya ajiye na sati biyu ba...."
Murmusawa Faɗima tayi kafin ta ce "Habah! FA'IZA bakya ganin arzikin su ba ɗaya bane?" "Sannan Fahad ma dakike bada misali dashi kina da tabbacin komai da kike gani agidan nan shi ya kawo?"
Wani murmushin ta kuma yi tare da Faɗar"Fallasa sirri tsakanin ma'aurata biyu bai dace ba,amma zan sanar dake wani abu ayau ko kya fahimta ki gane cewar FAWWAD yana k'ok'ari.."
Gyara zama tayi tana sauraren Faɗima.
Fad'iman ta ci gaba da cewa "Fahad da kike gani...............
Follow me on Wattpad@ Ummu inteesar
Share& comment
Ummu inteesar❤❤❤❤❤❤❤❤❤___"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(Ummu inteesar)*
____________________
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO ANTY HAUWA ADMIN*
ina godiya da soyayyar ku agareni READERS NA WANNAN BOOK hakika kuna nunamin soyayya ta hanyar yawan yin comment ɗinku ya nunamin cewa wannan littafin yanada farin jini sosai a gareku,idan hakane kuci gaba da bibiyata dan jin ƙarshen labarin yar gantali.
*Masoya ina godiya da yawan addu'oinku gareni,ngd sosai Allah bar zumunci da k'auna*
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.12
Faɗima ta ci gaba da cewa "Fahad da kike gani ba shi ne ke siyen komai da kika gani a gidan nan ba,iyakacin shi duk wata ya ajiye mana kayan abinci da cefane,sai sutura da a shekara baifi yayiwa yaran nan ɗinki uku ba sai na sallah da yake."
"Ni ma haka baifi yamun kala uku ashekara ba,duk sauran abubuwan da kike gani agidan nan kama daga kan injimin wanki,iron,pridge da duk wani kaya na more rayuwa da kika gani a gidan nan ni nake siyen su da kuɗin albashina a hankali ina tarawa."
Da wannan Albashin nawa dakike gani dashi nake rufawa mijina asiri,ba a gane yayi mana ko bai mana ba."
Mamaki ne ya cika FA'IZA ace duk kuɗin da Fahad keda shi amma a shekara baifi yayiwa iyalansa kala uku-uku ba?.
Ashe ma FAWWAD yafi shi tunda shi duk abinda ya samu iyalansa yake kashewa,yana kula da su dai-dai gwargwadon iyawarsa.
Dan kawai shi talaka ne abunda yake kawowar ba isarsu yake ba.
*******************
A ranar FAWWAD na dawowa daga gurin aiki ta sameshi dan ta bashi hak'uri.
Zama tayi kusa dashi bayan takai masa abinci yana ci,sai rarraba ido take abunka da mai laifi.
Yi yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da cin abincinsa,ya na kammalawa ya mik'e zai bar gun,
"FAWWAD" ta kira sunan shi, cigaba da tafiya yayi yana nufar bedroom kai tsaye batare da ya waigo ba.
"MIJINAH dan Allah ka saurare ni" nan ma banza yayi mata yaci gaba da tafiyarsa, har ya kai kofar bedroom ɗin ta taso da ɗan gudunta ta ƙaraso inda yake, sai ji yayi ta riƙe masa riga ta baya.
Waigowa yayi fuskar nan a haɗe babu annuri,ya galla mata harara ba tare ya tamkata ba.
Saurin sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da fara rokon shi "dan Allah mijina kayi hak'uri ka gafarta mun,nasan na maka laifi mai girma da na cancanci hukuncin da yafi wannan ma, Amma dan Allah ka yafemin masoyina."
Tana kainan a zancen ta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Kukan ta ya taɓa zuciyar FAWWAD sosai,(domin ya tsani yaji kukan mace ko wacce iri bare ma matarsa Abar k'aunarsa.)
Rumtse idonsa yayi da ƙarfi yayin da take cigaba da rera kukan da ke ƙara narkar masa da zuciya.
Muryarta ya tsinto tana cewa " ka gafarce Ni mijina na tuba, bazan iya jurar fushinka a gareni ba zuciyata zata iya tarwatsewa a dalilin haka,na tuba.....maganar ta ta katse yayin da wani sabon kukan yazo mata.
Cike da mamaki FAWWAD ya buɗe idonsa ya zuba mata su har yanzu tana sunkuye riƙe da rigarsa.
Bakomai ne ya bashi mamaki ba kamar hak'urin da take bashi cike da k'ank'antar dakai,har da kuka, kamar ba FA'IZAR sa ba mai tsiwa da ɗaukar kai.
Allah ya sa ma su Aabid basa nan yau su na gidan su FAWWAD sai simrah dake part ɗin faɗima tana wasa da sabir. Yaji daɗin haka sosai.
Sunkuyowa yayi ya kama kafad'unta ya miƙar da ita tare da kallon cikin idonta, ya ce "shikenan matata daina kukan ai kinsan ina sonki, dan haka na yafe miki." "Amma dan Allah inaso daga yau kar ki kuma fita gidan nan ba tare da izinina ba da kin mun haka shikenan."
Wani killer smile ta sakar masa tare da cewa "insha'allah, bazan kuma ba "
Duk da a'iya fatar baki zancen nata ya tsaya, zuciyarta cike ta ke da son fita.
"Nagode sosai uwar y'ay'anah" ya faɗa.
Murmushi kawai tayi A ranta ta ke cewa ba dai ka yafe Wannan ba? Zan san duk yadda zanyi na koma bakin sana'a ta ba tare da ka sani ba, dan wallahi nagaji da zaman gida.
****************
Yanzu sun shirya sosai ita da mijinta zamansu gwanin ban sha'awa, tana mai biyayya sosai komai ya samu ya kawo za ta karb'a ta masa godiya saɓanin da........
Amma ta ciki na ciki dama kawai take nema ta fita.
FAWWAD ya gama sakankancewa yanzu matarsa ta shiryu ta bar gantali.
Watarana bayan ya tafi aiki ta fito ta lek'a sashen Faɗima taga bata nan ta fita, sai ta dawo ta je ta shirya ta fito tana jin d'ar d'ar a ranta.
Rufe sashenta tayi tare da fice wa a gidan, da zimmar zata dawo kafin lokacin dawowar FAWWAD da Faɗima a gidan.
******************
Hakan kuwa ta faru can zuwa ƙarfe uku ta dawo gidan ta tarar har su Aa'idah sun dawo daga makaranta.
Agurguje ta dafa masu abinci suka ci tare da lallab'a su akan cewa kar su yarda su faɗawa dadynsu ko wani tana fita, ita kuwa zata siyo masu duk abinda suke so.
Yaran suka ce "to mommy ba zamu faɗa ma kowa ba, har maman salim"
Kayan tea da bread da su bescuit ta siya masu,ta nunawa Aabid inda ta ɓoye ta ce masa "idan kun dawo daga school bana nan saika haɗa maku kusha, kaji yaron kirki?"
Saida ta nuna masa yanda ake haɗa tea ɗin sa'annan ta bar gun.
*****************
Haka FA'IZA ta ci gaba da satar hanya tana fita ba tare da mijinta ko Faɗima sun sani ba.
Dan kafin su dawo ta dawo gidan, sai murna FAWWAD ke yi matarsa ta shiryu.
Da misalin ƙarfe goma na safe FA'IZA ta gama shirin ta na fita tsaf,ta fito sanye da doguwar rigar yadi brown mai ratsin milk aciki ta saka hula milk colour tayi kyau sosai.
Hijabi ta ɗora kalar milk shi ma ta rufe part ɗinta ta fita goye da simrah a bayanta duk da cewa yanzu yarinyar t
cika 3years, amma kullum sai ta goya ta idan zata fita dan ba tada mai ajiye mata yarinyar.
Tafiya ta ke cikin hanzari kamar za ta wuce ƙafar ta,sauri take sosai dan har 4:30pm tayi ga shi ta na sauri ta isa gida kafin ɗaya daga cikin mutane biyun nan su dawo.
Ta na hawa tsakiyar wani babban titi da zimmar k'etarawa sai ji tayi kif! Mota ta ɗauke ta sama...
Tun daga lokacin bata kuma sanin inda kanta yake ba............
Hmmm! Tofah readers garin yawon FA'IZA ta haɗu da hatsari......kome zai sameta bayan haka mu haɗu a page na gaba.
Follow me on wattpad@ UMMU INTEESAR
SHARE & COMMENT
UMMU INTEESAR
❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO: ANTY HAUWA ADMIN*
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.13
Jama'ar gurin suka yo kanta da gudu suna faɗar"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Simrah kam ko minti biyu bata ƙara ba,rai yayi halinsa.
Gashi mai motar da ya kad'e ta ya gudu ko tsayawa baiyi ba.
Wani Alhj. Ne da yazo wuce wa a motarsa,faruwar hatsarin ce yasa ya tsaya,shi ne ya taimaka aka saka FA'IZA( da take a sume) a motarsa ya kaita asibiti.
****************
A bangaren FAWWAD kuwa tun 4:00pm da ya fita sallar la'asar, ya ji gabansa na faɗuwa a hankali.
Bai kawo komai a ransa ba,ya cigaba da aikin gabansa.
Har bayan shud'ewar awa ɗaya gabansa bai daina faɗuwa ba, sai ma tsananta bugawa da k'irjinsa ya ke.
Haka kawai yaji hankalinsa yaƙi kwanciya, 6:00 pm nayi ya fito akan sabon babur ɗin shi da ya sake kwanan nan.
A ƙagauce ya nufi gida, ya na zuwa ya k'ofar part ɗin ya tarar da shi a rufe.
Nan fa hankalinsa ya kuma tashi,ransa ya ɓaci sosai.
A ransa yake cewa "Anyah FA'IZA wannan hanyar da kika biyo zata ɓulle dake kuwa?" Kenan satar hanya kika yi yau?.
Wata zuciyar ta ce mashi "waya sani ko haka take yi kullum?"
Buɗe gidan ya yi ya shiga ya zauna ya na jiran ta.
Aabid da Aa'idah kuwa suna gidan Ramlah (k'anwar fawwad)
An kai su su yi mata kwana biyu.
********************
A gurin da hatsarin ya faru kuwa anyi ta neman wanda yasan wannan matar dan kai rahoto ga ahalinta,amma ba a samu wanda ya santa ba, kasancewar unguwar nesa dasu ne sosai-sosai.
Gashi bata taɓa zuwa unguwar ba sai ranar.
Da yake tsautsayi ne ke kiranta. Gashi ba a samu waya atare da ita ba, dan tunda hatsarin ya afku wani ya lalabe wayarta kirar camon cx ɗin da ke jakarta da kuɗinta duka.
Wannan Alhjn. Daya kaita asibiti shine yad'auki nauyin kuɗin aikin da za a mata da komai.
Domin kuwa likita ya tabbatar masa da cewa karaya ce, karayar ma ba ɗaya ba.
Ta sami karaya biyu a k'afar dama, ɗaya a cinya ɗaya a gwabri. Sai k'afar hagu da ta karye a gwabri itama, sai kukkujewar da fuskarta da hannayenta su kayi.
*******************
Ba ita ta farfaɗo daga dogon suman da tayi ba,sai ƙarfe 11:30 na dare, buɗe idonta ta yi a hankali tana ƙarewa dakin kallo ,har ta yunk'ura zata tashi zaune ta ji ƙafafuwan ta kamar a ɗaure.
Saurin duban kafafun nata tayi inda ta gansu a nannad'e da p o p da wasu k'arafa a ciki.
Sai a lokacin ta tunano lokacin da ta fito da lokacin da ta hau titi ta ji wata ƙara gif! Tun a lokacin ne kuma bata kuma sanin komai ba sai yanzu.
Hakan na nufin kenan hatsari tayi? Kuma kafafuwanta sun sami matsala?
Wani uban ihu ta kurma,wanda ya janyo hankalin nurses ɗin dake kusa da gun, zumbur ladi(matar da Alhj. Ya ajiye dan kula da FA'IZA) ta farka daga barcin da take.
Rarrashin ta ladi ta shiga yi, FA'IZA kuwa sai kuka take "Ina y'ata simrah?" ta tambaya acikin kukan,duk ta firgice.
A dai-dai lokacin ne kuma wasu nurses guda biyu mace da namiji suka shigo.
Cakumar nurse ɗin FA'IZA tayi a gigice ta na faɗin "ina y'ata simrah?" Duk sai ta bawa nurses ɗin tausayi.
Suna ganin kamar zafin ciwo ne ya haukata ta.
Fita namijin yayi ya d'aga waya ya kira Alhj. Ya sanar mai halin da ake ciki.
*****************
A lokacin har Alhj. Ya kwanta amma sai ya tashi dan dole ya hawo motarsa ya zo asibitin.
*****************
FAWWAD kuwa hankalinsa ya dugunzuma da ya ga har sha biyu na dare tayi ba FA'IZA ba alamarta.
Duk yawon gantalin FA'IZA bata taɓa kai koda 10:00pm a waje ba,gashi yau har 12 ba ita ba alamarta.
"Wani mummunan abu ya faru da ita" zuciyarsa ta faɗa masa.
Hankali a matuƙar tashe ya nufi kofar fita part ɗin, har zai fita kuma ya dawo da ya tuna dare yayi yanzu ina zai nufa idan ma ya ce zai je nemanta.
"Y'ata simrah fa?" Dam! K'irjinsa ya buga da k'arfi da ya tuna da ita FA'IZA ke fita.
"Allah ya kare mun ke y'ata ya sa kina cikin k'oshin lafiya."
A haka yayi ta sambatun kiran sunan y'arsa.
A tak'aice dai ranar barci bai ga idon FAWWAD ba.
*****************
A asibitin kuwa Alhj. Khamis ne ya shigo ɗakin da FA'IZA ke ciki tana ihu haɗe da kiran sunan y'arta.
Guri ya samu ya zauna cikin tsananin tausayin ta,ya fara ba ta hak'uri.
"Ga wanda zai baki labarin y'arki" nurse ɗin ta faɗa.
Aikuwa kamar ta duro ta cakume kwalarsa ya faɗa mata inda yakai y'arta take ji.
Cikin raunanniyar murya Alhj. Ya sanar da ita komai da ya faru, ya ƙara da cewa "y'ar dake goye a bayanki ko mintuna biyu ba ta ƙara ba a duniya, kasancewar kanta ya rabe gida biyu,harma........."
Ai FA'IZA ba ta tsaya jin ƙarshen zancensa ba, ta tsandara wani gigitaccen ihu,sai ta kuma suma a karo na biyu......
Share& comment
Follow me on wattpad@ Ummu inteesar
UMMU INTEESAR
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
____________________
_*DEDICATED TO ANTY HAUWA (maman uswan)*_
*Ina yinki over my Anty Allah ya raya miki zuri'arki, yasa kifi haka.*
_*Gaisuwa ta musamman agareku MEMBERS NA AREWA WRITERS ASSOCIATION.*_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.14
FAWWAD kuwa dak'yar yaga safiya tayi, domin ganin yayi duk daren ranar yafi kowanne dare tsawo a rayuwarshi.
Dak'yar ya bari 7:00am tayi sa'annan ya fita ba tare da ya yi break ba,hankali a tashe ya nufi gidan rediyon da yake aiki.
Ya kai rahoton b'atar matarsa da y'arsa.
Nan da nan aka saka sanarwar neman Matar FAWWAD da y'arsa.
******************
A can asibitin kuwa FA'IZA bata farfaɗo ba sai 7:30am, da ta farfaɗo ma ba abunda take sai kuka da sambatun kiran sunan y'arta.
Duk ta hargitse sai faman kiran simrah ta ke.
Adai-dai lokacin ne kuma Alhj. Khamis da matarsa safiya su ka shigo ɗakin,dan sai a yau matar tashi tazo duba jikin patient d'in da ya bata labari.
Kwando abincin dake hannunta ta ajiye,sannan suka gaisa da Inna ladi tare da tambayar ta "ya mai jiki?" Inna ladi ta amsa "dasauki alhamdulillah,sai damuwa dake tattare da ita."
"Bata fi mintuna biyar da farfaɗowa ba,ku ka shigo."
Guri suka samu suka zauna tare da yiwa FA'IZA ya jiki, da ido kawai ta ke bin su ta na cigaba da sambatun ta.
"Kaicona Ni FA'IZA me wannan kasuwancin nawa ya ƙare ni dashi?, Gashi na rasa y'ata simrah har abada ko gawarta banganiba."
"Kaicona! Kaicona!!."
Tausayin ta ne ya lullub'e zuciyar mutanen dake ɗakin.
Alhj. Ya ce "baiwar Allah da zaki bamu labarin ki da zamu so hakan,kuma hakan zai taimaka mana wurin gano yan uwanki da mijinki mu sanar dasu halin da kike ciki."
********************
A can gida kuwa faɗima ce ta fito around 7:30 zata je ta sauke yara makaranta,da mamaki a fuskar ta take kallon part d'in FA'IZA da ya ke a k'ulle, "toh! Ina FA'IZAR ta je ne da sassafe haka?,ai ko FAWWAD lokacin fitarshi baiyi ba yanzu." Ko sanda FA'IZA ke fita yawon ta bata fita tunda sassafe haka,kuma idan ma zata fita sai ta lek'o mun gaisa muddin ina nan."
A ranta take wannan zancen haka kawai ta ji hankalinta bai kwanta ba, a bayyane ta ce "Allah ya sa dai lafiya."
Da haka ta ja yaranta uku ta saka a mota ta fice daga gidan.
*******************
Can asibitin kuwa FA'IZA ce ke kuka har yanzu ya kasa faɗa masu ko wacece ita.
Ta sani wannan karon ba ƙaramin tashin hankali FAWWAD da iyayensu za su shiga ba,kuma yana da wuya su yafe mata,shiyasa taƙi Faɗa.
******************
Tun 10:00am aka fara yaɗa sanarwar nemanta a gidan rediyon VISION FM amma shiru ka ke ji har dare.
Da FAWWAD yaga haka sai ya sanar da iyayenta da nashi iyayen dan su taya shi addu'a, Allah ya bayyanar masa da ita.
Faɗima ta ruɗe matuƙa sanda taji sanarwar batar FA'IZA da ake,a lokacin tana asibiti gurin aikinta.
Da yake faɗima tana son FA'IZA sosai jin ta ta ke kamar yar uwarta ta jini.
Hakan ya sa duk wata idan ta karb'o Albashinta ta ke ba wa FA'IZA dubu uku aciki.
Rashin karɓar shawara da rashin ji kaɗai ke haɗa ta da FA'IZA.
*******************
Ranar ma haka FAWWAD ya kwana ido biyu ba barci,kasancewar har zuwa lokacin ba'a samu labarin FA'IZA.
*****************
Washe gari da misalin ƙarfe 11 na safe hjy.safiya(matar Alhj.khamis) ta shiga sashen Hajiya Inna surukarta(mahaifiyar Alhjn.) Dan ta gaida ta anan ta tarar hjy Inna na sauraren redio,aikuwa sai ga sanarwa an fara.
"Ana neman wata mata mai suna FA'IZA matar FAWWAD Wacce ta bata a ranar Assabar,kuma tana da goyo"
Saurin kwashe numbobin da aka karanto waɗan da za'a tuntuba idan anganta hjy safiya tayi.
Kana ta kira Alhj. Ta sanar mai,ya ce ta kira number ta sanar masu asibitin dan yana kyautata zaton patient d'in shi ake nema.
Ai kuwa kai tsaye ta kira ɗaya daga cikin numbobin cikin Sa'a kiran ya faɗa wayar FAWWAD.
********************
Ya na zaune ofis cikin jimami sai jaje ake zo mishi, kiran ya shigo wayarsa, ya na d'agawa sai ji nayi ya ce "wanne asibitin?"
Ta na gama faɗa ya zari makulin babur d'insa ya nufi asibitin da aka kwatanta masa.
******************
Alhj.khamis ma daga ofis ɗin sa ya wuce asibitin kai tsaye dan tarbon mijin wannan baiwar Allah.
A birkice FAWWAD ya shigo ɗakin da aka kwatanta ma sa.
Turus! ya tsaya yana ƙare mata kallo hankali a tashe.
Share& comment
Follow me on Wattpad@ummu inteesar
UMMU-INTEESAR❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: Soyayyar meerah*
*DEDICATED TO: ANTY HAUWA (maman uswan)*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.15
Ɗauke idonshi yayi daga duban ta,ya koma ya na ƙarewa ɗakin kallo, da ganin yanda ya ke yi kasan wani abu yake nema.
Bakomai ya ke nema ba face yarsa simrah,amma ga mamakinsa har ya gama rarraba idonsa amma bai ganta ko'ina ba.
A sukwane ya nufi inda FA'IZAN ke zaune akan gadon majinyata, "Ina y'ata simrah?" Ya tambaya.
Kuka kawai FA'IZA ta saka mishi ba tare da ta iya ba shi amsa ba.
Hakan da tayi ne ya dad'a rud'ar da FAWWAD, girgiza kafad'unta ya shiga yi yana faɗar "ki gayamun FA'IZA ina kika kai mun y'ata."
Har lokacin FA'IZA bata iya tamka shi ba sai kuka take zuciyarta na k'una.
Alhj.khamis da yaga haka,cikin matuƙar tausayawa ya dubi FAWWAD ya ce: "bawan Allah kayi hak'uri sake ta ni zan gayama komai"
Sakin ta FAWWAD yayi ya nufo inda Alhjn. Ya ke tsaye,ya ja ya tsaya kikam akan Alhjn kamar zai kai masa duka,bai dai ce komai ba.
Alhj.khamis ya shiga zayyanowa FAWWAD duk abinda ya faru tun daga farkon abinda ya sani.
Sai dai ganin yanayin FAWWAD ɗin yasa ya kasa gaya masa y'arsa ta mutu, FAWWAD da ya riga ya k'agara yaji ina y'arsa ya ce "ina y'ata banji kayi zancenta ba duk a labarinka."
Numfawa Alhj. Yayi kafin ya ce "kayi hak'uri bawan Allah y'ar dake goye a bayanta ko mintuna biyu bata ƙara ba a duniya,rai yayi halinsa kasancewar kanta da ya rabe....."
Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, tashin hankali wanda ba'a sakawa rana.
Abinda zai riƙe ya shiga lalabe, amma kasancewar a tsakiyar ɗakin suke bai samu komai da zai riƙe ba hakan ya saka shi yin fad'uwar yan bori a gurin.
Banda hawaye ba abunda ke fita a idonshi, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, Allah ya jikanki y'ata." "Ba kiyi dacen uwa tagari ba, mahaifiya da kowanne d'a ke saka ran samun ceto daga gare ta duk lokacin da ya shiga wani hali,yau ta ki mahaifiyar ita tai silar mutuwar ki."
Ya kusan minti goma a gurin kafin ya tashi ya fice daga asibitin ba tare da ya kalli side ɗin da take ba,Alhjn. Kawai yayi wa godiya yayi gaba abinsa.
********************
Bayan ya ƙarasa gida cikin ƙarfin hali ya d'aga waya ya kira mahaifinta ya sanar masa anganta ga halin da ake ciki.
Hak'uri baban ya bashi tare da Faɗar" Allah ya sawwake mata,amma Ni ba inda zani da sunan dubiya."
Hak'uri FAWWAD ya bawa baba kafin ya katse wayar.
Ran baba idan yayi dubu ya ɓaci, a ranar bai ko tsaya lokacin tashinsa daga gun sana'ar tasa yayi ba ya fice zuwa gida.
Bayan yaje gidan ya tara duka iyalansa maza da mata, (anyi sa'a yayansa mata na gida ranar sunzo yini)
ya sanar masu abinda ke faruwa da FA'IZA, tare da bada umurnin "karku sake naji labarin ɗaya daga cikinku yaje duba wannan shed'aniyar yarinya koda wasa,wanda yaƙi ji kuwa baya ƙi gani ba,dan sai nayi mummunan saɓa wa mutum." Cike da ɓacin rai yake zancen.
Inna Luba ce tace "haba malam saboda Allah ya zaka ce kar wanda yaje duba ta ƙaddara ce fa,kuma fa karaya akace ta samu fa."
Tsawa baba ya daka mata tare da Faɗar "ko menene ita ta jawa kanta,ban hana maki yiwa y'arki addu'ar samun lfy ba,amma ba wanda zai je duba wannan gantalalliyar yarinyar da ta kashe y'arta gun yawo." "Umurnina ne wannan.
Daga haka ya tashi yayi waje a fusace.
*******************
A gidansu FAWWAD ma labari ya isar masu, ran iyayensa mata ba ƙaramin ɓaci yayi ba.
Akan haka mama Hajara ta ce "ba wanda zai je duba FA'IZA a familynsu," Alhj (baban FAWWAD) ne ya tsawatar,tare da masu nasiha kuma ya basu umurnin zuwa duba ta ko sau ɗaya ne, saboda FAWWAD ba dan ita ba,dan duk yanda ta lalace dai matarsa ce.
*****************
Ramlah ta shirya ita da nadiya suka ɗauki su Aabid da Aa'idah suka tafi asibiti dan su kai yaran su duba jikin mamansu.
Suna shiga ɗakin,Aabid da Aa'idah suka je da gudu gun momynsu,.
Har suna haɗa baki gun tambayar ta "mommy me ya sami kafarki? Ina sim? Munyi missing ɗinku kwana biyu.....
Share & comment
Follow me on wattpad @ummu inteesar
UMMU-INTEESAR ce
❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(Ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*GODIYA*: ina miƙa Godiya ta mai tarin yawa a gareka *YAYA IBRAHIM MU'AZZAM INDABAWA*, hak'ik'a dukkanin kalamai sunyi kad'an su bayyana irin godiyar da nake agareka.
Sai dai ince Allah ya saka maka da Alkhairi ya raya zuri'a.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.16
Shafa kansu kawai take tana hawaye ba tare da ta ce komai ba, taya zata fara faɗa masu k'anwarsu ta mutu?.
********************
FAWWAD kuwa tunda ya bar asibitin k'ashin bai zame ko ina ba sai gidansa.
Yana shiga kai tsaye ya shiga bedroom ya faɗa kan gado,ya na ta tunani gami da zubar da zafafan hawaye.
Tun sanda FA'IZA ke fita yawon ta bai taɓa zargin ta da yawon banza ba,sai yau.
Ganin Alhj.khamis a matsayin mai kula da ita tun lokacin da lalurar ta sameta ne ya saka shi yin wannan mummunan zargin akanta.
Yana zargin kodai tana tare da Alhjn ne lokacin da abun ya faru?, Idan bahaka ba meyasa sai shi kaɗai ne zai taimake ta a lokacin da hatsarin ya afku?
Ba ma wannan ba haka kawai zai ɗauki nauyin jinyarta Alhali bai santa ba? Kai gsky da lauje acikin nad'i.
Haka nan zuciyar FAWWAD tayita mishi sak'e-sak'e akan FA'IZA da Alhj.
"Kin cutar dani FA'IZA." Ya furta a hankali.
Nan take wata zuciyar ta kwab'eshi " a'a FAWWAD banda zargi, zato fa zunubi ne koda ya zamo gaskiya."
A haka dai ya wanzu cikin tsananin damuwa da tunani har zuwa wani lokaci mai tsawo.
***************
Faɗima ma da taji labarin rasuwar simrah hankalinta ya tashi sosai, kuma ranta ya ɓaci,hakan yasa ta gudurce a ranta cewar har FA'IZA ta gama zaman asibiti ba zata ce duba ta ba.
*****************
Har mako uku suka shud'e FA'IZA bata kuma ganin wani daga cikin ahalinta ko na FAWWAD sun zo duba ta ba, ballantana shi uban gayyar da tun ranar farko da ya zo aka tabbatar mai da mutuwar y'arsa bai koma waiwayota ba.
Hakan ya d'aga mata hankali sosai,kowa ya guje ta,banda Alhj.khamis da matarsa da Inna ladi da suke hidima da ita, ba wanda ke zuwa wajen ta.
Sau ɗaya aka kuma kawo mata su Aabid sai innarta da ta sato hanya ba tare da sanin baba ba tazo duba ta.
Hak'ik'a FA'IZA tayi nadamar abinda tayi ta ci kuka har ta gode Allah, ta kuma k'udurcewa ranta cewar koda ta sami lafiya ta tashi ba zata kuma yin sana'ar fita ba.
******************
Bawan Allah FAWWAD sai da ya ɗauki hutu a gurin aikinsa ya zauna a gida yana jimami,duk ya bushe ya lalace abincin kirki ma baya ci,Gidan duk yayi masa k'unci.
Sai mutane ke zuwa masa Gaisuwa,duk ya zama abin tausayi.
Idan ya na zaune a gidan duk inda ya waiga wulgawar Y'arsa simrah yake gani tana dariya tare da guje-gujenta acikin gidan.
Yana matuƙar son ƴaƴansa,amma bai san haka yake matuƙar son simrah ba sai da ya rasa ta.
Yana yawan furta "kin cutar dani FA'IZA,na tsane ki."
*****************
Bayan wata uku aka sallami FA'IZA daga asibiti,yanzu ta warke sarai sai dai tafiyarta ce har yanzu bata daidaita ba.
Alhj.khamis da matarsa ne suka yi mata rakiya zuwa gidan mijinta.
Duk da zuciyarta cike take da fargaba amma tasan bata da wurin zuwa da ya wuce nan.
A kofar gida Alhj. Yayi parking motarsa, hjy safiya ce ta rakata har cikin gidan lokacin FAWWAD baya nan yana gun aiki.
Makullin da ke cikin jakarta tun watannin baya ta zaro ta buɗe part ɗin suka shiga.
Lokacin da hjy safiya zata tafi ta kawo kuɗi masu dama ta bawa FA'IZA, ta ce ta riƙe saboda ko zata buk'aci wani abun.
Godiya FA'IZA ta mata, ta ce ai ba komai mun zama ɗaya yanzu,wani kati ta mik'awa FA'IZA mai ɗauke da address ɗin gidanta da number waya.
Ta ce "idan kin samu lokaci sai ki kawo mana ziyara koh?.
Murmushi FA'IZA tayi suka yi sallama Hajiya ta tafi.
********************
Tun daga bakin gate yake hango kamar part ɗinsa abud'e bayan yasan ba kowa aciki tunda su Aabid na gun Ramlah har yanzu.
Shanye mamakinsa yayi ya nufi part ɗin, ya na shiga ciki ya tarar da FA'IZA a parlour ta hakimce.
Amma fa hankalinta a tashe yake dan tun da ta ji kukan babur ɗinsa zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri dan bata san ya za su kwashe ba.
Nan da nan fuskarsa ta sauya, haɗe girar sama da ta ƙasa yayi.
"Sannu da zuwa." Ta faɗa a daburce.
D'aga mata hannu yayi Alamar ya isa, tare da Faɗar "me kika zo yi a gidana?"
Dagowa ta yi ta kalleshi da mamaki a fuskarta.
"Da ke nake magana fa,me ya kawo ki gidana?."
A cikin daga murya yake zancen.
Bai jira amsarta ba ya ɗora da cewa:
"A tunani na da kina da hankali ba zaki nufo gidana ba, kai tsaye za ki wuce gidanku. dan ayanzu baki da muhalli a gidana."
Kallon shi take a daburce ta ma kasa magana dan ba ƙaramin mamaki tayi ba jin kalaman mijinta gareta ayau,.
"Ki fice min daga gida yanzun nan tun kafin ranki ya b'aci,ki je..........."
To fah🤔 readers me ke shirin faruwa da FA'IZA?
ME FAWWAD KE SHIRIN AIKATAWA?
MUJE ZUWA.
Share & comment
Follow me on wattpad @ Ummu inteesar
❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
____________________
_*Masoyana ina yinku over Allah ya bar k'auna, members ɗin yar gantali fans group ina yinku sosai Allah ya bar k'auna.*_
_Maman sultee my kishiya kema ina ɗan yinki ba sosai ba.🤣🤣🤣_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.17
"Ki fice min daga gida yanzun nan tun kafin ranki ya ɓaci, ki je gidanku sai na nemeki."
Durk'usawa tayi ta fara bashi hak'uri jikinta na kakkarwa, amma ko kallonta baiyi ba ya ce" ki tafi kawai na tsaneki FA'IZA,ba na son ganin fuskarki a tattare dani."
Tashi tayi jiki a sab'ule sai hawaye take ta shiga Cikin bedroom ɗin ta ta ɗauko ƙaramin akwatinta tare da hijabin ta ta fito.
Cike da k'uncin zuciya ta tari napep sai gidansu, tayi sa'a kuwa koda ta ƙarasa gidan baba bai dawo ba.
Da sallama ta shiga gidan Inna dake cikin d'aki jin Muryar shalelenta yasa ta fito, da sauri ta yi kan FA'IZA ta rungume ta dan murna.
"Ah ah yaushe aka sallamo ki daga asibiti? K'afa ta mik'e kai Alhamdulillah." Inna ta faɗa yayin da ta sake FA'IZA tana dudduba kafarta, a lokacin ne kuma ta lura da akwatin da FA'IZA ke riƙe dashi.
Da mamaki a fuskarta ta ce "ya na ganki da akwati a hannu? daga ina kike haka?."
Hawayen da take ƙoƙarin riƙewa ne suka zubo mata,hannu ta saka ta share su tare da Faɗar "ɗazun nan aka sallamo ni daga asibiti,yana dawowa ya ce naje gida sai ya neme ni."
Jan hannun ta Inna tayi suka shiga d'aki tana famar rarrashin ta, habah shalele na daina zubda hawayenki akan wannan matsiyacin mijin naki da bai san ƙaddara ba,ke fa matar manya ce ko sakinki yayi zaki samu wani mai arzikin ki aura."
*****************
Sai bayan la'asar baba ya shigo gidan (ya dawo cin abinci)
Kawai sai ya tarar da FA'IZA a gidan,
"Ke meya kawo ki gidana yanzu?,ashe ban ce maki karki ƙara zuwa gidan nan ba dalili ba?."
Cikin in ina ta ce "shi... shine ya ce na tafi gida sai ya neme ni.
Baba ya ce yamun dai-dai ai dama sakinki yayi ya huta,kinga sai kiji daɗin yawo da kyau." A zafafe yake maganar,
Ya cigaba da cewa "ki zo ki fice min daga gida yanzun nan, banida mazaunin ki a gidana."
"Ina kake so ta je yanzu malam?" Inna ta faɗa.
"Duk ma inda zata tafi Ni sani,da sanda take yawon ta Ni nake nuna mata inda take zuwa?" A fusace yayi zancen.
Ganin ran baba ya ɓaci matuƙa yasa FA'IZA ta d'auki a kwatinta ta bar gidan jiki a sanyaye.
Inna bata yi yunk'urin hanata ba haka kuma bata koma magana ba,dan ta san komai zai iya faruwa idan ta tamka.
**************
Tafiya take janye da akwatinta cike da tashin hankali da k'uncin zuciya,sai tunani take faman yi.
******************
FAWWAD kuwa tun bayan fitarta yake kwance akan kujera ya na cin zafi a zuciyarsa,ya ma rasa tunanin me zai yi.
Da yaga yana neman sakawa kanshi ciwon zuciya akan wata shashasha kawai sai ya tashi yayi wanka ya fita.
*******************
Yanzu ina zata? Tun da baba ya kore ta.
Gidan k'awarta Laure ya fad'o mata arai,kawai sai ta kudiri zuwa can.
Cigaba da tafiya tayi a ƙafa, tayi nisa a tunaninta kawai sai taji hon. ɗin mota a bayanta.
Ko waigowa bata yi ba taci gaba da tafiyar shan gabanta mai motar yayi tare da taka burki.
Tsayawa ta yi cak a gun, buɗe motarsa yayi ya fito yana yi mata sallama, d'agowa tayi ta kalleshi, kirjinta ya buga da ƙarfi dam!,
A ranta take cewa mutumin nan ne na watannin baya da yake bibiya ta, to me yake nema agareni bayan na faɗa mai ni matar aure ce?."
Katse mata tunani yayi da cewa.
"Magana fa nake baiwar Allah"
"Bawan Allah na gayama Ni matar aure ce,har da y'ay'ana uku, meyasa kake bibiyata?." FA'IZA ta faɗa.
Murmushi Alhj. Yayi kana ya ce "da farko dai sunana Alhj. Dauda Nera, abinda yasa nake bibiyarki shine, ina so na aure ki ne,domin ban yarda cewa kina da aure ba, don ganinki da nake yi kusan kullum kaɗai ya isa ya tabbatar mun da cewa ke ba matar aure bace saidai bazawara."
***************
Kallonshi kawai FA'IZA tayi, taji ciwon maganarsa,amma sai ta Basar kawai ta ce "to shikenan naji yanzu ina kan hanya ne sauri nake."
Ya ce mata to muje na sauke ki inda zaki in yaso sai mu ƙarasa zancen a mota koh?.
****************
A kofar gidan Laure ya sauke ta sai fara'a take sukayi sallama ta shiga gidan.
Ranta fal murna tuni ta manta k'uncin da take ciki,sai murna take tayi sabon kamu ta samu mai arziki, aranta take ji ko da ma ace FAWWAD ya saketa yanzu bata da baƙin ciki...........
Anyah! FA'IZA kin biyo hanya mai ɓullewa kuwa?🤔🤔🤔
Meye makomar auren FA'IZA da FAWWAD?
MUJE ZUWA.
FOLLOW ME ON WATTPAD@UMMU INTEESAR
SHARE & COMMENT
UMMU INTEESAR CE❤❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu inteesar)*
*Marubuciyar: Soyayyar meerah*
________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.18
Da sallama ta shiga gidan ɗauke da fara'a a fuskarta.
Laure dake wanki a tsakar gidan ta taso da murnar ta tana yiwa FA'IZA oyoyo.
Tabarma ta ɗauko ta shimfid'a a tsakar gidan tare da Faɗar "bismillah k'awata."
zama tayi bayan sun gaisa, Laure ke tambayar ta labarin da taji a gari cewa FA'IZAR tayi hatsari harma simrah ta mutu.
"Ke kuwa A'ina kikaji Wannan labarin?" FA'IZA ta tambaya tare da kama hab'a alamar mamaki.
Murmushi Laure tayi ta ce "ai k'awata zancen duniya baya b'oyuwa a unguwar nan naji ana faɗa wai garin yawon gantalin ki kin kashe y'arki."
Turb'une fuska FA'IZA tayi tare da Faɗar "mutanen duniya dai anyi munafukai,wato har an baza Ni agari daga ƙaddara ta faɗa mun."
Laure da taga ran ƙawarta ya ɓaci, ta ce yi hakuri k'awata ban faɗa dan na b'ata miki rai ba yanzu meye labari? Ya na ganki da akwati?.
Tab'e baki tayi kamar ba za ta yi magana ba,sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta faɗa wa Laure.
Jinjina kai Laure tayi ta ma kasa cewa komai.
FA'IZA ta ɗora da cewa "shiyasa na zo gunki don ba ni da ƙawar da ta fiki kaf garin nan,kuma kinga ke bazawara ce mijinki ya rasu daga ke sai yara a gidan."
"Ba damuwa karki ji komai ai nan gidanki ne, amma ni dai shawarar da zan baki ita ce ki je ki bawa mijinki hak'uri ya bar ki ki zauna dakinki shine mutuncinki." Laure ta faɗa.
******************
A can gidansu FA'IZA kuwa abin duniya ya dame Inna sai tunani take ina fa'iza ta shiga yanzu?.
Gashi ta na tsoron tarar baba da zancen dan a yanda ranshi ya ɓaci ita kanta zai iya korarta daga gidan idan tayi magana. Dole ta hak'ura ta dinga yiwa y'ar Tata addu'a.
Duk sai Inna ta ji ta tsani FAWWAD dan shine silar faruwar wannan abu.
*******************
A gidan laure kuwa FA'IZA ce zaune akan tabarma har yanzu bayan ta gama cin abincin da laure ta kawo mata.
Ta shiga bata labarin Alhj. Dauda Nera da alƙawarin auren da ta masa,kana ta ɗauko sabuwar waya keypad da ya bata ɗauke da layinsa a ciki dan su riƙa gaisawa kafin ya sai mata babba.
Zaro ido laure ta yi tare da Faɗar "ba ki da hankali ne FA'IZA da aurenki za ki yiwa wani alƙawarin aure?, Kin ban mamaki wallahi."
Dariya sosai ta yi kafin ta tsagaita da dariyar tare da cewa "ai na gaya mashi Ni matar aure ce amma da alama bai yarda ba,sai cewa yayi to ya ji duk da haka yanda nake da dirin nan gaskiya bazai iya hak'ura dani ba na je na kashe aure na,na na aureshi yay mun Alƙawarin mallaka mun duk abinda nake so, kama daga kan gidaje gonaki da sauransu."
Laure da ta gama tsinkewa da lamarin kawar tata,harma tana tunanin kodai hatsarin da ta yi ya taɓa mata ƙwaƙwalwa ba a sani ba. Ta ce "to na ji yanzu ya za kiyi da auren FAWWAD dake kanki?"
Wata dariyar ta Kuma shek'ewa da ita tare da Faɗar "Ni nasan me zanyi akai,ba ruwan ki."
"Ki bi a hankali dai don motar kwaɗayi bata saukeka ko'ina Sai a tashar wulak'anci." Laure ta faɗa tare da tashi tabar gurin dan abun na k'awarta sai dai addu'a kawai.
****************
Bayan kwana biyu FAWWAD ya dawo gida da marece ya na zaune,ya na kallon yanda duk gidan ya sauya duk gidan ya yi ƙura ga datti nan ko'ina ba kyan gani.
Ga shi baida lokacin gyarawa, FA'IZA ce ta fad'o mai arai lumshe ido yayi yasan da tana gidan da yanzu gidan ya d'au k'amshi don FA'IZA akwai tsafta.
Amma ba yanda ya iya dole ya ɗauki kyakkyawan mataki akanta,idan bahaka ba zata cigaba da janyo mai masifa a rayuwa.
Har ya fara tunanin maidata bayan sati biyu.....
***************
Sallamar da akayi a kofar part d'in ne ya katse mai tunanin da ya ke.
Cike da mamaki yake kallonta har ta ƙaraso ciki.
Shanye mamakinsa yayi ya haɗe rai tare da Faɗar "Me ya dawo da ke gidana a daidai wannan lokacin?,ban ce ki zauna a gida sai na neme ki ba."
Wani shu'umin murmushi ta sakar mai wanda ya kasa gane fassarar shi.
Ta ce "dad'ina da kai gajin hak'uri, da kayi hak'uri koda ba ka tambaya ba zan sanar ma da kai meke tafe dani dan ba zama na zo yi ba.
Ƙura mata ido ya yi yana jiran jawabinta, Har ya faɗa wata duniyar.
Muryarta ya jiyo ta na faɗar "zuwa na yi ka bani takarda ta,shine kaɗai abinda ya kawo ni."
Sororo yayi ya na kallonta har sai da ta maimaita sannan ya ce "kina nufin so kike na sake ki?.
"Ƙwarai kuwa dan banga amfanin zama da igiyar aurenka akaina ba tunda ka tsane ni.
Share ta kawai yayi ya koma ya zauna.
To matso kusa dashi ta na cewa "idan har ka haihu ga iyayenka kuma kai ɗan halas ne to ka bani takarda.
Cike da tsanar ta ya d'ago ya kalle ta tare da Faɗar "tabbas zan nuna maki Ni dan halas ne gaba da baya,duk da cewa saki baya cikin tsari na amma tunda kin nema da kanki ki je na sakeki saki ɗaya.
Sai da kirjinta ya buga da ƙarfi amma tsabar rufe mata ido da abin duniya yayi sai ta dake tayi shewa tare da Faɗar "godiya na ke malam FAWWAD, da ka taimaka ka raba ni da igiyar aurenka ta tsiya.
Da hannu kawai ya nuna mata k'ofa.
Dariya ta koma shek'ewa da ita ta ce "idan kayi hak'uri yanzun nan zan barma matsiyacin gidanka tunda na samu abinda nazo nema."
"Yaya kuma ka riƙe na bar maka a shekarar nan zan haifi ɗan gata."
Daga haka ta fice daga gidan tana murmushi amma akasan zuciyar ta tana jin zafi da rad'adin sakin duk da ita ta nema.
*******************
Gidan laure ta koma tana jiran dare yayi alhjnta ya zo su sha hira.
Da dare kuwa ya zo ya kawo mata sabbin turamen atamfa biyu na dubu goma-goma tare da babbar waya touch da kud'i Naira dubu goma.
Amma ya gaya mata ta tattala wayar shi baya son sakaci.
Sannan ya gaya ma ta baya son ad'auki dogon lokaci tunda Dukan su ba yara bane.
Alhjn. Zai kai kimanin shekaru 60 a duniya, wani tsamurarrare dashi marar k'iba. Yafi kama da irin kamun yunwa ɗin nan.
FA'IZA kuwa bata damu da shekarunsa ko yanayin jikinsa ba, murna kawai take zata aure mai kuɗi.
Har bakin mota ta raka shi, motar da yazo da ita yau tafi ta shekaranjiya kyau da tsada, Abin da ya ƙara rikita FA'IZA kenan duk sanda zata kuma ganinshi wata kalar motar da wasu kalar kayan na dabam take gani baya maimaita mota ko kaya..
Shiga motar yayi ya wuce ita kuma ta koma ciki sai tsaga murmushi ta ke.
Hmmmmm! Niko nace anyah Fa'iza kinyi da ce kuwa?
Abun da kika aikata zai barki kuwa?
Zanso nga ƙarshen wannan gantalalliyar.
Follow me on Wattpad@ummu inteesar
Share & comment
UMMU-INTEESAR CE❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu-inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*ina yinku over sister Maryam, sister Nana khadija, sis Amatullah,sister Rahanatu comment ɗin yana ɗora ni a gajimare💭💭 Allah ya bar k'auna*
*GODIYA TA MUSAMMAN: A GAREKI ANTY HAUWA MAMAN USWAN ALLAH YA KARE MANA KE DA ZURI'ARKI ADUK INDA KUKE.*
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.19
Daga shigar ta ta soma bawa laure labarin cewa Alhj. Dauda ya ce ba ya so a ɗauki dogon lokaci ba a yi auren ba, kwanan nan yake so.
Laure ta dube ta a mamakince ta ce "to ke wace amsa kika bashi?"
"Cewa na yi to sai ya turo." FA'IZA ta faɗa.
Ƙara cika da mamaki laure ta yi, "tabbas k'awata ta samu matsalar ƙwaƙwalwa." Ta faɗa a ranta, a fili kuwa cewa ta yi "Anyah! Kina qlau kuwa FA'IZA? Aure cikin aure zaki yi?"
Dariya FA'IZA ta sa ka sai da ta yi mai isarta sannan ta ce, "au ashe fa na manta ban sanar da ke cewar FAWWAD ya sake ni ba,ki yi hak'uri na so faɗa miki ɗazu d'aukin zuwan alhj. Ne ya mantar da ni.
Zaro ido laure ta yi tare da dafe k'irjin "yaushe ya sake kin?," Ta tambaya cike da kad'uwa.
Murmushi FA'IZA ta yi tare da Faɗar "ɗazu na je na saka shi agaba sai da ya sake ni, dama ba kina tambaya ta yaya zan yi aure ba? To yanzu fa? Ince dai zan iya yin aurena?.
Cike da tsoro laure ta ke kallon ƙawar tata aranta ta ke tunanin ko da a ce FA'IZA ba tada tabin hankali to lallai tana da aljanu.
********************
A gidan Alhj.umar kuwa, FAWWAD ne a zaune gaban mahaifinsa,ya na yi masa fad'an meyasa ya kori matarsa?. " Ka je ka dawo da ita yanzun nan, ai hak'uri zaka yi ka cigaba da addu'a tare da mata nasiha." Abbansa ya faɗa.
Sunkuyar da kansa ya yi cike da ladabi ya ce " Ai Abba mun rabu da ita shekaranjiya."
"Ka na nufin ka sake ta kenan?. Abban ya tambaya
Shiru ya yi yana sosa k'eya kamar mara gaskiya.
"Ka ban mamaki FAWWAD ina tunanin ka na da hankali ashe baka da shi?, Kaf danginmu wa ka tab'a jin yayi saki? Sai akanka aka fara." Cikin faɗa-faɗa ya ke zancen.
"Yi hak'uri Abba wallahi ita ce ta nema, har da cewa idan ni ɗalas ne na sake ta fa Abba." FAWWAD ya faɗa a marairaice.
jiki a sanyaye Abba ya ce "Shikenan ta shi ka je Allah ya maka Albarka, Allah ya kyauta."
FAWWAD ya ta shi ya Kinapa sashen iyayensa mata.
********************
Bayan kwana biyu laure taga al'amarin k'awarta sai addu'a,sai cigaba FA'IZA keyi da shirye-shiryen aurenta.
Laure ta ce "FA'IZA na ji kina zancen aure da
i,iddar fa? Ko ba zaki yi ba ne?
"Au kinga wallahi nama manta ashe fa sai na yi iddah bari Alhjn. Ya zo na sanar mai,duk da na ga har yanzu bai yarda ina da aure ba.....
Follow me on wattpad@ Ummu-inteesar
Share & comment
UMMU INTEESAR CE
❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu-inteesar)*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO: MARYAM D/DAJI (MAMAN RAMADAN)*
*Ƙawata ta kaina ina inki over ALLAH ya raya mana Abdul da Ramadan akan sunna ameen.*
*Much love dear*
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡No.20
Alhjn. Na zuwa kuwa ta sanar mai cewa dole fa sai ya jira tayi iddah sannan su yi aure.
Sai a lokacin ya yadda ta taɓa aure amma yana mamakin yawo irin nata,aransa ya ce wani abu wanda bansan ko menene ba,yayi k'wafa tare da jinjina kai Alamar zaki shigo hannu ne.
******************
Sai da ta kwatanci lokacin da baba ba ya gida sannan ta je, ta sanarwa Inna ta samu miji mai kuɗi harma FAWWAD ya sake ta tana gama iddah zatayi aure.
Zo kaga murna agun inna,sai da ta rangad'a gud'a sau uku kafin ta ce "dama na gayamaki ke matar manya ce ko sakinki ya yi shi ke da asara dawuri zaki samu miji ba gashi ba kuwa zance na ya tabbata."
Murmushi kawai FA'IZA ke tsabgawa ta ɗauko kuɗi tare da kayan da Alhjn. Ya bata ta nunawa Inna kana ta bata Dubu biyar da turmin atamfa ɗaya, Inna kuwa baki har kunne sai albarka take sakawa FA'IZA tare da bata gwarin gwuiwar ta yi aurenta ta bar mishi yaran a gunshi.
Kafin baba ya dawo FA'IZA tabar gidan.
******************
FAWWAD kuwa ya na nan ya na cigaba da aikinsa a hankali yana tara kuɗin albashinsa abinci kawai ya ke ci aciki sai ya yi sutura ya saka.
Yanzu baya da nauyin kowa akansa yaran na gidan y'an uwansa.
A tsakanin watanni uku ya tara kuɗinsa ya tayar da tsohuwar sana'arsa yaransa na kula da wajen shi ko ya na zuwa aikinsa,idan ya ta so daga gun aiki ya kan biya ta gunsu yaga yanda aikin ke gudana.
A cikin k'ank'anin lokaci ya fara samun riba mai yawa fiye da da ma.
******************
FA'IZA kuwa bayan ta kammala iddar ta, ta je gidansu ta cewa Inna ta sanar da baba iyayen angon za su zo gunsa dan ai maganar aure.
Inna ta ce ta jira a mok'ota idan ya dawo za ta sanar mai ko me ya ce idan ya fita za ta aika kiranta.
Bayan baba ya dawo Inna ta sanar mai da bukatar FA'IZA.
Rufe idonsa ya yi ya ce shi sam baisan wannan maganar ba, ba zai tsayawa FA'IZA ta kuma auren wani ba bayan FAWWAD, dan haka tun wuri ta je ta nemi wani uban da zai mata wakilci a aurenta, shi ba ruwansa da aurenta.
Bayan ya fita ta aika aka kira mata FA'IZAR ta sanar mata yadda suka yi da baba.
Cike da k'uncin zuciya ta bar gidan tana tunanin mecece mafita a yanzu? Dole dai iyayen ango sai sun haɗu da iyayenta kafin ayi aure.
*****************
Da ta koma gidan laure ta sanar da ita komai, saboda haka ta nemi taimakon ƙawar tata,akan haka laure ta ja ta zuwa gidansu gun babanta, suka rok'e shi akan ya je ya lallab'a baban FA'IZA ya yarda ya mata wakilci a aurenta.
Baban laure ya ce "badamuwa zai je"
Suka mai sallama suka koma gida suna jiran sakamako.
Washe gari baban laure ya je ya samu baba mai itace da zancen,amma fir baban ya ce shi bai san zancen ba.
Baban laure ya yi ta lallab'a shi amma yaƙi,haka ba yanda ya iya ya dawo gida jiki a sanyaye,ya aika aka kira masa laure ya sanar da ita.
****************
FA'IZA ta shiga damuwa sosai gashi Alhjn. Ya matsa da zancen auren nan.
Shi kuwa Alhj Dauda Nera bakomai ne yasa ya matsa ba sai dan auren da ya ke so ayi kafin asirinsa ya tonu.
*****************
Alhjn ya sanar da ita cewa ranar ASSABAR mai zuwa ya ke so akawo Goro da sadaki tare da ɗaurin auren duka.
Da taga bata da wata mafita dole ta Kuma lallab'a laure suka je gidan suka rok'i babanta akan yayi wa FA'IZA wakilci a aurenta.
Cikin sa'a kuwa baban ya amince ya ce "ai d'a na kowa ne Allah ya nuna mana lokaci,ni zan zama uba agareki."
Cike da murna suka dawo gida FA'IZA ta cigaba da shirye-shiryen shiga amarci.
******************
A na saura kwana uku a d'aura aure Dauda mai gadi duk ya ruɗe ya rasa yanda zai yi ga shi tusa na neman k'urewa buddari tunda ya san ba shi da gida a garin nan da zai sa ka amarya.
A cikin wannan yanayin ne ya je gun ALHJ. tasi'u Nera (wani uban gidansa da suke mutunci sosai) ya rok'e shi akan ya taimaka ya ara masa ɗaya daga cikin gidajensa koda kwana ɗaya ne jal zai saka amarya.
Alhjn. Ya dubi Dauda yayi murmushi ya ce "Dauda sai yaushe za ka daina ɗebo rigima,idan ba rigima ba mai za ka yi da wata mata yanzu,tunda ko na gidan basu k'oshi ba."
Sukunyar da kai kasa Dauda yayi yana rokon Alfarma tare da Faɗar" ka min rai Alhj. Matar da zan aura ce son abin duniya yayi mata yawa, yanzu da ta gano bani da kuɗi za ta gujeni ne,kuma wlh ina matuƙar bukatar ta Alhj."
Murmushi Alhj tasi'u yayi aransa yana tausayawa wannan kwaɗayayyar, ga shi ta debo ruwan dafa kanta garin kwaɗayi.
" Shikenan ta shi mu je na kai ka gidajena da ba kowa aciki ka zaɓi ɗaya na ara maka,amma fa kwana biyu kawai."
Godiya ya masa suka shiga motar Alhjn su ka tafi.
Sai da ya zaɓa ya darje sannan Alhj. Ya sauke shi gun y'an wankin mota, ya ari ɗaya ya bawa mai wankin Naira dubu,sannan ya hawo sai gun FA'IZA....
Hmmm to fah readers kunji fa?
Fa'iza na shirin ɗebo ruwan dafa kanta.....
Alhj Dauda Nera dai ashe mai gadi ne🤣🤣🤣🤣wayyo fa'iza kin ban tausayi.
Fallow me on wattpad@ummu inteesar
Share & comment
UMMU-INTEESAR CE❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰
✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (Ummu-inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*DEDICATED TO: FIDDAUSI SANI (DAMSEL FEEDORH)* *marubuciyar sahibul kalbi*
up up up my feedorh Allah k'ara miki basira ya kawo miji nagari musha biki💋💋❤
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.21
Ranar Assabar da misalin ƙarfe goma na safe mutane suka shedi ɗaure auren FA'IZA da Alhj Dauda Nera akan sadaki dubu hamsin.
FA'IZA ta shirya wata kwarya-kwaryar walima a gidan ƙawarta laure, wannan karon kam sai da Hadiza (k'anwar FA'IZA) Ta zo walimar ba tare da sanin baba ba,duk da ya masu iyaka da ita.
Ƙarfe huɗu na yamma aka fara gudanar da walimar inda aka kirawo babbar malama *ANTY Saratu munzali*🤪 da ta shahara akan harkar wa'azin mata,dan ta yiwa FA'IZAR nasihar zaman aure.
Can na hango *UMMU AFFAN* marubuciyar *cikin waye* ita da members na *Y'AR GANTALI FANS GROUP* Sun zo gulma 🤪dan su ga irin shigar da hjy FA'IZA za ta yi a ranar.
Aikuwa Amarya ta haɗe cikin wani tsadadden material golden colour,(wanda alhjn. Ya kawo mata na fitar buki.) fuskar nan tasha make up sai k'yalli take, murmushi kawai take tsabgawa.
Taro yayi taro anci ansha sai fatar Allah ya maida kowa gida lfy.
*******************
Bayan an kammala walimar da dare aka ɗauki amarya zuwa gidan Angonta.
Dama Alhjn. Ya faɗa mata baya buk"atar ko tsinkenta da sunan kayan d'aki,domin akwai komai a gidansa na more rayuwa amarya kawai yake buƙata.
Ba ƙaramin daɗi FA'IZA ta ji ba da taji wannan zancen,don haka ta sakankance tabbas ta samu mijin nunawa tsara.
Tuni ta manta da ƴaƴanta bare wani FAWWAD,harkokin gabanta kawai ta ke.
*****************
Yan kai amarya sai sontin gidan FAIZA su ke yi, aljanar duniya haka suka yiwa gidan lak'abi da shi.
Hadiza kuwa tana barin gidan bata zame ko'ina ba sai gidansu ta bawa Inna labarin daular da aka kai FA'IZA ciki.
Inna Kam Dan murna harda rawa sai da ta taka ranar,bayan sun gama murnarsu Hadiza ta koma gidan mijinta.
******************
FA'IZA kuwa bayan kowa ya watse kafin angon ya shigo ta tashi ta fara kewaya gidan ta na kallon irin tsari da had'uwar gidan ranta fari k'al kamar takarda,wani irin nishad'i ta ke ji ayau.
Gidan da aka kai FA'IZA ya tsaru iya tsaruwa,wani irin tank'amemen gida ne, ire-iren gidajen masu kuɗin nan ne da FA'IZA ke gani a turkish series, parlourn gidan ma ya haɗu sosai ga wasu lausasan kujeru ma su taushi da santsi komai na parlourn purple& pink ne, kai tsayawa kwatanta yanda gidan ya tsaru ma bata lokaci ne,sai dai kuyi imagining kawai.
****************
FA'IZA kuwa ta zauna wannan kujerar ta ta shi ta lek'a nan ta lek'a can tamkar wata y'ar ƙauye.
A haka Alhjn ya shigo ya same ta.
Ƙarasawa ta yi ta tarbo sa ta na masa murmushi "sannu da shigowa angona." Ta faɗa.
Shima murmushin ya mayar mata tare da cewa "Barka da hutawa Amaryata,kina ta kallon gidanki ne?,gidan ya maki ko a sake?."
"A'a wallahi Alhj ai gidan ya haɗu sosai,Ni nan ma ya isheni rayuwa." Ta mayar mai fuskarta ɗauke da murmushi.
Murmushin mugunta ya mata a ransa yake Faɗar "sakarya gobe ne kaɗai zaki wuni a gidan nan zan maidaki ƙauye,nima da zan samu na rayu anan dana ji daɗi." A fili cewa yayi muje ciki Amaryata ya ja hannunta suka shige ɗaya daga cikin manyan bedroom ɗin gidan.
***************
FAWWAD kuwa yana nan yana rayuwarsa shi kaɗai,sosai ya shiga damuwa rashin mata a tare dashi,sai dai ya jure saboda shi yanzu tsoron yin aure ma yake,idan ya tuna FA'IZA da Soyayyar da su ka sha abaya da kuma yanda rabuwar su ta kasance sai ya tsinke da lamarin mata.
****************
Gashi Mama Hajara(mahaifiyarsa) ta takura shi da maganar aure, ya nuna mata shi baida abin yin aure yanzu, ta ce ita zata masa amma ba zai yiwu ya zauna ba aure ba tunda yana da yara. Kawai ya nemo mata idan kuma bai gano wacce ta masa ba, ita ta na da wacce za ta bashi.
Abba ma yayi ma sa magana.
Ganin iyayensa sun damu sosai ya saka ya amince cewar zai yi aure,mahaifiyarsa tayi murna sosai akan haka ta tura shi gidan ƙawarta dan su dai-daita da y'ar Amina k'awarta.
********************
Washe garin ranar Amarci Amarya FA'IZA ce zaune a dinning ita da Angonta su na break fast,su na hirarsu abin gwanin sha'awa.
Acikin hirar ne Alhjn. Ke sanar mata gobe za suyi tafiya.
Nan da nan annurin fuskarta ya k'aru jin ya ambaci tafiya a zaton ta ko honey moon za su je ƙasar waje, Aranta ta ce "ƙasar turkey zance da ya ba ni zaɓi,zan je in ga k'asarsu erkan meric(Omar) da hazal subasi(zehra) dama ina son series d'in tarkon k'auna, Ashe da rabon zanje ƙasar su." Ita kaɗai ta ke wannan tunanin shi ko Dauda mai gadi da ya ga ta yi nisa a tunaninta kawai sai ya ɗinga mata dariyar mugunta aransa,ya ci gaba da kwasar Gara dama bai saba cin irin wannan abincin ba sai yau, dan haka ya buɗe tumbi ya na ta ci..🤣🤣🤣🤣(ɗan baka saba ba).
🤣🤣🤣wayyo FA'IZA za'aje turkey Dan Allah idan zaki ki zo ki wuce da Ummu Affan da Nana khadija member ta yar gantali fans Suma suna son zuwa🤣🤣🤣
Follow me on Wattpad@ ummu inteesar
Share & comment
UMMU INTEESAR CE.
❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.22
A ranar kuwa Inna ta sato jiki tazo ganin gidan FA'IZA,Hadiza ce ta rako ta,jin yanda Hadiza ta kod'a mata gidan ya saka ta kasa hak'uri har Amarya ta kwana biyu sannan ta je.
Ai kuwa Inna tasha kallo agidan ma sai da ta taka rawa agaban y'ar Tata don murna,sai da FA'IZA ta cika ma su cikinsu da dad'ad'an girke-girke na zamani (wanda yar aikin gidan ta dafa) kafin su ka bar gidan.
********************
Yana zaune kan kujerar parlourn baƙin zuciyarsa cike da wasi-wasi da tunani kala-kala,ta shigo parlourn da sallama.
Sai da ta yi sallama sau biyu sannan FAWWAD ya jiyo ta,ya amsa mata.
Samun guri tayi ta zauna su ka gaisa.
Gabatar mata da kansa ya yi,da kuma buƙatar dake tafe dashi.
Cike da kunya Salima ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na murmushi,kafin ita ma ta gabatar masa da kanta.
Tun daga kallon farko ya fahimci cewa yarinyar tana da nutsuwa sosai,ga kunya ga kamun kai, ga dukkan alamu yarinyar ta k'oshi da tarbiyya irin ta addinin Islama gata kyakkyawa kuma.
Nan take zuciyar FAWWAD ta samu nutsuwa tare da amincewa da zaɓin mahaifiyar tashi.
Exchanging number suka yi shida ita sannan ya ma ta sallama ya tafi.
*****************
Washe gari ya kama ranar monday,A ranar ne kuma tafiyarsu, saboda haka tun da sassafe FA'IZA ta shirya,ita ce ma ta tashi Alhjn daga barci, sai zumud'i take.
Tashi ya yi yayi wanka ya shirya shima.
Ganin FA'IZA ta janyo ɗaya daga cikin trolley da ke ajiye a ɗakin,ya sa ka shi Faɗar
"A'a Amaryata bakya buƙatar ɗaukar wasu kaya anan Jakar hannunki kawai za ki ɗauka,akwai komai da zakiyi amfani da shi acan."
Laullausan murmushi ta sakar mai kana ta ajiye trolleyn tare da Faɗar "ai shikenan Alhjna muje kawai karmu ma kara, kasan jirgi baya jira sai dai ajira shi."
Cike da mugunta yayi dariya aransa yana Faɗar zaki ga jirgi ba dai tak'amarki kwaɗayi ba? Zaki gane ne."
Fitowa su ka yi ya rufe gidan ko'ina sannan yaja motarsa su ka fita daga gidan.
Sai da ya biya ta gidan Alhj tasi'u Nera yayi parking a d'an nesa kaɗan ya kashe motar, ya dube ta ya ce "Amaryata dan Allah ko za ki ba ni minti biyu? da akwai wanda nake son gani ne anan kafin mu wuce."
Hjy FA'IZA murmushi kawai ta masa tare da Faɗar" an baka."
Fita ya yi daga motar ya ƙarasa a ƙafa har kofar gidan,su ka gaisa da mai gadi sannan ya masa iso gun mai gida.
Bayan Alhjn. Ya fito suka gaisa Dauda mai gadi ya masa godiya tare da miƙa masa makullin gidansa kamar yanda ya yi alƙawarin,sannan ya masa bankwana akan shi zai koma ƙauyensu.
*******************
Jan motar ya yi suka ƙarasa gun y'an wankin mota, ya yi parking.
Cike da mamaki FA'IZA ke dubansa kasa jurewa ta yi ta ce "Angona me yasa katsaya anan mu da zamu airport?."
Murmushin mugunta ya mata ya ce "Ayyah Amaryata motar ce duk ta yi datti,kuma na sanki da tsabta ba za ki juri tafiya aciki ba,shiyasa nayi tunanin bar masu ita anan idan sun wanke na aiko akarbar man a mayar gida."
Yar dariya ta yi ta fito daga motar, dauda ya ja wanda ya ara masa motar gefe ya masa godiya tare da bashi hak'urin kwanan da motar ta yi a hannunsa,ka na ya dawo inda ta ke.
Napep suka shiga sai tasha, ita dai da ido kawai take binsa, layin motocin da ke zuwa local government ɗin da ƙauyen su ke ciki ya nufa.
Nan ma da ta tambaye shi ina kuma zasu,ya ce k'auyensu zai kaita ta gaisa da yan uwansa kafin su wuce.
Ba ta kawo komai a ranta ba ta hau motar suka hau hanya.
********************
FAWWAD kuwa gidansu ya je ya sanar da umma sun daidaita da Salima dan haka aka saka ranar aurensu,ba a wani saka dogon lokaci ba sati biyu kacal aka saka kasancewar iyayen yarinyar suma suna da abin hannunsu dan haka a shirye suke.
Ba ƙaramin daɗi iyayensa su ka ji ba,Albarka kawai su ke sa ka masa.
Shi ma ayanzu ya manta da wata FA'IZA ya na matuƙar jin Salimah a ransa domin yarinyar tana da biyayya gashi ta k'ware a Soyayya,bugu da ƙari ta na matuƙar son ƴaƴansa,don tun a satin farkon da suka haɗu ta takurashi sai da ya kai mata yaran gidansu su ka yi kwana biyu.
******************
Bayan sun isa local government ɗin suka fita daga wannan motar suka hau wata wacce zata kaisu ainihin ƙauyensu Dauda.
FA'IZA dai tun da aka sauke su a tashar kauyen har suka hau babura zuwa k'ofar gidanshi ba tace k'ala ba,kallon yanayin garin kawai ta ke.
Tun daga yanayin garin za ka gane cewa akwai matsala,wani ɗan
ƙaramin ƙauye ne,wanda baya da wadatar gida je,tsilli-tsilli kake ganin bukkokin garin waɗan da wasu ke kewaye da darni,wasu kuwa babu bukkar ce kawai.
*****************
"Ikon Allah wannan wane irin gari ne haka?,ashe acikin duniyar nan akwai irin ƙauyukan nan?,kai Allah mun gode maka da ka yi mu a birni." Tana cikin wannan tunanin ne ta tsinto muryarsa ya na faɗar" bismillah Amaryata mu shiga koh?."
Jiki a sanyaye ta d'aga ƙafa dak'yar ta shiga gidan.
Ba ko sallama ya faɗa gidan tare da tamke fuska,ita kuwa ta na biye dashi a baya.
Yara(maza da mata) kusan guda bakwai ƙananu da ke ta wasa a tsakar gidan suna ganinshi suka watse kowa ya gudu zuwa ɗakin da tafi zaton shine na iyayensu............
Hmm! Toh! Fah wad'an Nan yaran fa?🤔 ƴaƴan waye?🤔🤔
Follow me on Wattpad@ Ummu inteesar
Share & comment
UMMU INTEESAR CE❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Y'AR GANTALI*
*(Mai hangen na wani)*
👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰👩🏻🦰✨✨ ✨✨ ✨✨
*Story & written by: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (ummu inteesar)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*
⚡💫⚡ No.22
A ranar kuwa Inna ta sato jiki tazo ganin gidan FA'IZA,Hadiza ce ta rako ta,jin yanda Hadiza ta kod'a mata gidan ya saka ta kasa hak'uri har Amarya ta kwana biyu sannan ta je.
Ai kuwa Inna tasha kallo agidan ma sai da ta taka rawa agaban y'ar Tata don murna,sai da FA'IZA ta cika ma su cikinsu da dad'ad'an girke-girke na zamani (wanda yar aikin gidan ta dafa) kafin su ka bar gidan.
********************
Yana zaune kan kujerar parlourn baƙin zuciyarsa cike da wasi-wasi da tunani kala-kala,ta shigo parlourn da sallama.
Sai da ta yi sallama sau biyu sannan FAWWAD ya jiyo ta,ya amsa mata.
Samun guri tayi ta zauna su ka gaisa.
Gabatar mata da kansa ya yi,da kuma buƙatar dake tafe dashi.
Cike da kunya Salima ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na murmushi,kafin ita ma ta gabatar masa da kanta.
Tun daga kallon farko ya fahimci cewa yarinyar tana da nutsuwa sosai,ga kunya ga kamun kai, ga dukkan alamu yarinyar ta k'oshi da tarbiyya irin ta addinin Islama gata kyakkyawa kuma.
Nan take zuciyar FAWWAD ta samu nutsuwa tare da amincewa da zaɓin mahaifiyar tashi.
Exchanging number suka yi shida ita sannan ya ma ta sallama ya tafi.
*****************
Washe gari ya kama ranar monday,A ranar ne kuma tafiyarsu, saboda haka tun da sassafe FA'IZA ta shirya,ita ce ma ta tashi Alhjn daga barci, sai zumud'i take.
Tashi ya yi yayi wanka ya shirya shima.
Ganin FA'IZA ta janyo ɗaya daga cikin trolley da ke ajiye a ɗakin,ya sa ka shi Faɗar
"A'a Amaryata bakya buƙatar ɗaukar wasu kaya anan Jakar hannunki kawai za ki ɗauka,akwai komai da zakiyi amfani da shi acan."
Laullausan murmushi ta sakar mai kana ta ajiye trolleyn tare da Faɗar "ai shikenan Alhjna muje kawai karmu ma kara, kasan jirgi baya jira sai dai ajira shi."
Cike da mugunta yayi dariya aransa yana Faɗar zaki ga jirgi ba dai tak'amarki kwaɗayi ba? Zaki gane ne."
Fitowa su ka yi ya rufe gidan ko'ina sannan yaja motarsa su ka fita daga gidan.
Sai da ya biya ta gidan Alhj tasi'u Nera yayi parking a d'an nesa kaɗan ya kashe motar, ya dube ta ya ce "Amaryata dan Allah ko za ki ba ni minti biyu? da akwai wanda nake son gani ne anan kafin mu wuce."
Hjy FA'IZA murmushi kawai ta masa tare da Faɗar" an baka."
Fita ya yi daga motar ya ƙarasa a ƙafa har kofar gidan,su ka gaisa da mai gadi sannan ya masa iso gun mai gida.
Bayan Alhjn. Ya fito suka gaisa Dauda mai gadi ya masa godiya tare da miƙa masa makullin gidansa kamar yanda ya yi alƙawarin,sannan ya masa bankwana akan shi zai koma ƙauyensu.
*******************
Jan motar ya yi suka ƙarasa gun y'an wankin mota, ya yi parking.
Cike da mamaki FA'IZA ke dubansa kasa jurewa ta yi ta ce "Angona me yasa katsaya anan mu da zamu airport?."
Murmushin mugunta ya mata ya ce "Ayyah Amaryata motar ce duk ta yi datti,kuma na sanki da tsabta ba za ki juri tafiya aciki ba,shiyasa nayi tunanin bar masu ita anan idan sun wanke na aiko akarbar man a mayar gida."
Yar dariya ta yi ta fito daga motar, dauda ya ja wanda ya ara masa motar gefe ya masa godiya tare da bashi hak'urin kwanan da motar ta yi a hannunsa,ka na ya dawo inda ta ke.
Napep suka shiga sai tasha, ita dai da ido kawai take binsa, layin motocin da ke zuwa local government ɗin da ƙauyen su ke ciki ya nufa.
Nan ma da ta tambaye shi ina kuma zasu,ya ce k'auyensu zai kaita ta gaisa da yan uwansa kafin su wuce.
Ba ta kawo komai a ranta ba ta hau motar suka hau hanya.
********************
FAWWAD kuwa gidansu ya je ya sanar da umma sun daidaita da Salima dan haka aka saka ranar aurensu,ba a wani saka dogon lokaci ba sati biyu kacal aka saka kasancewar iyayen yarinyar suma suna da abin hannunsu dan haka a shirye suke.
Ba ƙaramin daɗi iyayensa su ka ji ba,Albarka kawai su ke sa ka masa.
Shi ma ayanzu ya manta da wata FA'IZA ya na matuƙar jin Salimah a ransa domin yarinyar tana da biyayya gashi ta k'ware a Soyayya,bugu da ƙari ta na matuƙar son ƴaƴansa,don tun a satin farkon da suka haɗu ta takurashi sai da ya kai mata yaran gidansu su ka yi kwana biyu.
******************
Bayan sun isa local government ɗin suka fita daga wannan motar suka hau wata wacce zata kaisu ainihin ƙauyensu Dauda.
FA'IZA dai tun da aka sauke su a tashar kauyen har suka hau babura zuwa k'ofar gidanshi ba tace k'ala ba,kallon yanayin garin kawai ta ke.
Tun daga yanayin garin za ka gane cewa akwai matsala,wani ɗan
ƙaramin ƙauye ne,wanda baya da wadatar gida je,tsilli-tsilli kake ganin bukkokin garin waɗan da wasu ke kewaye da darni,wasu kuwa babu bukkar ce kawai.
*****************
"Ikon Allah wannan wane irin gari ne haka?,ashe acikin duniyar nan akwai irin ƙauyukan nan?,kai Allah mun gode maka da ka yi mu a birni." Tana cikin wannan tunanin ne ta tsinto muryarsa ya na faɗar" bismillah Amaryata mu shiga koh?."
Jiki a sanyaye ta d'aga ƙafa dak'yar ta shiga gidan.
Ba ko sallama ya faɗa gidan tare da tamke fuska,ita kuwa ta na biye dashi a baya.
Yara(maza da mata) kusan guda bakwai ƙananu da ke ta wasa a tsakar gidan suna ganinshi suka watse kowa ya gudu zuwa ɗakin da tafi zaton shine na iyayensu............
Hmm! Toh! Fah wad'an Nan yaran fa?🤔 ƴaƴan waye?🤔🤔
Follow me on Wattpad@ Ummu inteesar
Share & comment
UMMU INTEESAR CE❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
_____"
0 Comments