FUTU A BIRNI hausa novels cmplt

 [8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣3⃣

Fatu bata farka sai 12:23. A hankali take bude idonta har ta fara gani rass. Juyo da kanta tayi gefe inda taji muryan mace na mata sannu, kyakkyawar mata ce mai dan jiki kadan wanda da alama ta danbmanyanta,  "Ya jiki ta qara cewa da fatu, a hankali ta furta da sauqi.  Sannan ta fara qoqarin tashi, matar tayi hanxarin taimaka mata ta zauna. Tace "ki dan huta sai kici abinci. Bari in hada miki tea. Tea ta hada mata mai kauri tasha kadan tayi hamdala. Sannan matar tace meye sunanki, kuma a ina iyayenki suke? "Suna na fateema ana cemin fatu, dangina suna kauye mai suna Garin Modibbo dake karkashin qaramar hukumar Akko. Matar tace "sunana hajia kulsum, nice na buge ki da mota ina sauri zan kai dana makaranta. Kiyi hakuri. Hope yanxu bakya jin ciwo? Daga kai fatu tayi, hajia kulsum tace "gurin wa kika zo nan garin? Ina son in kaiki in bada hakuri. Saurin girgiza kai tayi kanta na qasa tace "a'a hajia hakama ya isa, ba sai kinje ba, nagode. Hajia  kulsum ta tashi ta deba mata abinci da kyar fatu taci rabin plate tace ta koshi tasha ruwa. Hajia na lura da yanayinta, yarinyar tana cikin damuwa. "Hajia ina son zuwa bandaki" hajia kulsum ta taimaka mata taje bandaki, kama ruwa tayi sannan tayi alwala ta fito. Zama ta qara yi  a kan gadon, shiru sukayi na dan lokaci sannan aka fara kiraye kirayen sallah. Sukayi sallah, sannan Doc ta shigo ta duba fatu, ta mata questions game da yadda take ji. Doc ta juya gurin hajia kulsum tace "zaku iya tafiya gida, shes gud now" ta fita. Hajia ta fita taje ta biya kudi ta dawo tace mu tafi. Sun fito harabar hospital dinne fatu tace "hajia ko kun tsinci jakata" hajia tace "eehh, yana gidana manta wa nayi ban dauko miki ba. Amma muje  sai ki karba. Mota suka shiga suka tafi. Unguwar GRA suka shiga, ita dai fatu in banda kalle kalle bbu abunda takeyi, wani layi suka shiga wanda yafi ko ina haduwa don gidaje 20 suna kallon juna sai titi a shimfide a tsakiyarsu. Gaskiya fadin tsaruwar houses din ma bata lokaci ne. Nidai mmn fa'iz nace kamar a turai. Fatu kuma tace Aljannar duniya. A cikin jerin gidajen wata mota hadaddiya ta fito ta hau kan titi, hakan yyi daidai da juyowar fatu wacce take kalle kalle tun shigar ta unguwar mutumin da ta gani a cikin motar shiya sata daskarewa, bakinta a bude tana nuna shi da yatsa, har yazo ya wuce baima san tanayi ba don waya ma yakeyi yana murmushi. Horn hajia tayi a bakin gate din gidanta wanda yake kallon gidan da mutumin ya fito. Aka wangale gate ta kusa hancin motar har ta samu parking space tayi. Sai a sannan ta lura da fatu wacce idanunta na tsiyayar hawaye tana nuna glass da yatsa, fatu" ta kira sunanta amma bata amsa ba, dafa kafadarta tayi ta juyo a firgice sannan ta fashe da matsanancin kuka wanda yasa hajia cikin wasi wasi. Anya yarinyar nan ba aljanu gareta ba? Ace yarinya da ita ta fito daga garinsu ba kowa tare da ita, kuma ba'a mata komai ba tana kuka tana nuna glass. Whats wrong with her? Kodai auren dole za'a mata ta gudu? Ko ko ko? 


Maman Fa'iz👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣2⃣

Hospital:

Tana isa asibiti ta shiga sai gata ta fito da nurses biu hade da gadon tura mara lafiya. Suka ciccibi fatu suka daura akan gadon sukayi ciki da ita cikin sauri. Emergency aka shigar da ita, bayan 15 minutes wata doctor ta fito da sauri matar ta tare ta, tace "ya patient din? Doc tace "da sauqi don bata buge sosai ba, tsoritan da tayi ne yasa ta suma, sai kurjewa da tayi a kafa. Ynxu za'a kaita dakin hutawa zata farka nan da 4-5 hours. Don tana bukatar hutu. Tana gama fadan hka tayi gaba abinta yyinta wata nurse da gangaro fatu a kan gadon marasa lfyn ta kaita dakin hutu matar ba biye da ita. Ta kai minti biu tsaye a kanta sannan ta juya ta koma mota, yaronta dan kimanin 7 yrs yace 'mum ina wanda kika bugen? Sai a sannan ta tuna ashe tare suke, school zata kaishi da yake yau monday tana sauri kar y makara, shine hatsarin ya faru. Shafa kanshi tayi tace 'farouq tana ciki an bata gado, muje in kaika school.

Acan school tayiwa teachers bayanin abunda ya faru don yara sun dde da shiga class. Komawa gida tayi wanda a lokacin 9 da yan mintuna. Ta samu dija mai aiki tana goge a palour, 'sannu da dawowa hajia' hajia ta amsa tace 'kiyi abinci da mutum 1 za'a kai asibiti, na buge wata yarinya a hanya. Bata farfado ba balle in san gidansu, na duba jakanta banga tana da phone ba ko ID card. Cikin jimami dija tace "to hajia Allah ya kiyaye na gaba, taji ciwo sosai ne? Hajia ta mata bayanin da Doc ta mata sannan ta haura sama tana tunanin yarinyar game da tambayoyi cike a kanta wanda bbu wanda zai bata amsan sai yarinyar. Don daga ganin shigar da tayi zaka gane yar kauye ce, amma cikin jakarta kudi dari biyar biyar sabbi wanda yawansu zai kai 25k, kuma jakan nata irin na yara masu zuwa makaranta ne, sai kaya kala uku. Ni kaina mmn Fa'iz sai da zare😳. Duk answers na gurin fatu wacce har ynxu tana gadon asibiti bata san duniyar da take cikiba.


Taku Maman Fa'iz👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣4⃣

Fitowa hajia tayi daga motar ta zagayo inda fatu take, bude murfin kofan tayi ta kamo hannun fatu suka shigo cikin gida ta zaunar sa ita kan kujera a palour. Fatu ta cigaba da kukanta. "Dija dija" dija ta fito dga kitchen ta ce "gani hajia" hajia tace "taimaka min da ruwa pls" komawa kitchen tayi ta fito da tray an daura swan water da cup. Ta ajiye ta koma tana tunanin wace yarinya ce haka hajia ta samu? Daga kafada tayi tace hala yar aiki ce. Hajia ta tsiyayi ruwa ta miqa ma fatu wacce kukanta ya tsaya sai sheshsheka takeyi tace "kisha ruwa" ba musu ta karba ta sha, tayi ajiyar zuciya. Hajia ta numfasa ta fara magana "fatu a yanda na lura da yanayinki kina cikin matsala, kuma kinyi yarinya a barki ki fito daga kauyenku ke kadai ba tare da wani dan uwanki ba. Tambaya nake son miki, ki fadi tsakaninki da Allah, gurin waye kika zo anan garin? Fatu da tunda hajia ta fara magana kanta na qasa tace "gurin dan'uwa na nazo"  " a ina yake?  Fatu tace "na manta sunan unguwan amma yana cikin jakata. "Farouq farouq hajia ta kira shi yana room dinshi yana buga game, tun 12:30 y dawo daga skul. "Gani mummy" "jeka room dina ka dauko min wani skul bag akan bedside drower. Yace "to, amm mummy wannan ba itace ta mutu dazu ba? A cikin motarki. Hajia tayi daria tace a'a suma tayi not mutuwa, now get d bag. Ya juya da gudu ya dauko ya miqawa hajia ita kuma ta miqawa fatu, gurin fatu yaje da take kallonsa tun farkon shigowarsa. Yace daxu mum ta bugeki, kinji ciwone? Tace "a'a tana murmushi, amma kin suma ko? Tace ehh. Zai qara wata tambayar hajia ta katse shi tace " farouq jeka fara shirin islamiyya. In ka dawo she wll answer all ur questions. Ya haura sama da gudu yana cewa to mummy kar ta tafi, ta jirani fa. 

Aljihun gefe na skul bag din fatu ta bude ta ciro wani pic hade da guntun paper ta miqawa hajia kulsum. Mamakine ya bayyana qarara a fuskar hajia data kalli pic din, paper ta bude ta qara gaskata abunda ta gani. Ba komai ta gani ba illa pic din sultan gefenshi kuma fatu ce, a kauye aka dauki pic din,don ga irin bukkan rumbun nan da ake ajiye amfanin gona. A cikin paper kuma adress na gidansu sultan ne,  wato gida mai kallon gidanta. 

Hajia ta dubi fatu tace "wannan dan'uwanki ne? Fatu tace ehhh, "ya dangantakar ku take? Fatu ta numfasa tace hajia zan fada miki ko zaki taimaka min in shiga cikin gidan, don naga kamar sai da mota ake shiga irin gidajenku. 

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆


ASALIN LABARIN

Taku

Maman Fa'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣1⃣

CIKIN TASHA:

Mutanen dake fitowa daga cikin bus din ne na hango wata matashiyar budurwa, wacce inka lura da yadda take waige waige tana zare idanu zaka tabbatar yaune farkon shigowanta garin Gombe, "Gombawa diban fari, ba'a kwana daku ba an tashi daku"😜 Itama FATU haka ya ksance da ita don ynxu misalin karfe 7:20 na safe. Matsawa gefe tayi ta tsaya inda bbu mutane sosai ta cigaba da dube dubenta. Can nesa ta hango wata mai sayar da kosai da dankali a cikin tashan. Nufanta tayi da sauri cikinta na bada wani sauti qululululu don rabon da taci abinci tun jiya da rana sai fura kadan da kakanta ya bata da dare. Sauri take yi har ta isa, sallama tayiwa mata mai sayar da kosai, matar ta amsa, fatu tace a bata kosai da dankali na dari, matar ta sa mata a leda ta miqa mata, kudi ta ciro 500 daga cikin jakarta ta miqawa matar, aka bata canji, gurin wasu yara masu sayarda pure water taje gefe kadan da mai sayar da kosan. Ta sayi guda biu. Anan ta fara tunanin a ina zata zauna taci,  don har masu shaguna sun fara budewa. Bakin wani shago taje inda bbu mutane ta zauna, juya baya tayi yanda baxa a ganta ba ta fara cin kosan tana korawa da pure water. Sauri sauri har ta gama. Alhamdulillah ta furta, sannan ta wanke hannunta ta goge bakinta da zumbulelen hijabinta. Minti biyu da haka ta miqe hade da karkade jikinta ta dauki jakanta ta rataya ta cikin hijabi. Wajen tashar ta fito tana tunani barkatai a cikin zuciyarta. Kuuuuuuuuuuu sai timm. Innalillahi abunta matar dake cikin motar ta fada cikin kidimewa. Kafin ta fito har an fara taruwa akan fatu, tana fitowa tayi kan yarinyar da saurinta tana su taimaka mata su saka ta cikin motar ta. Wasu mata yan sharan titi ne suka taimaka mata suka sata a mota yayin da matar ta shiga driver seat ta cilla kan titi sai hospital.

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣5⃣

ASALIN LABARIN

    Kamar yadda na fada miki sunana fatima. Dangin mahaifina yan asalin garin modibbo ne, fulanine usul. Dangin mahaifiya ta kuma yan dukku ne, suma fulani.     

Kaka na mallam Aminu malami ne sosae wanda yake koyarda almajirai da manya, yana da matarsa binta wacce tun auren saurayi da budurwa suke tare, auren dangi aka hadasu. Yayansu biyar amma biyu ba rai, uku ne suka rayu har girma, goggo innani itace babba, sai sama'ila da kaninshi jamilu sune suka rasu, sai babana mamuda da kaninshi muntari. Tun kafin a haifi muntari goggo innani tayi aure. Tun tasowan babana Allah y yishi mai kokari ta fannin karatu da neman na kanshi, baiyi boko ba amma yyi arabi sosae. Tun yana saurayi ya fara kasuwanci, inda yake bin kasuwannin kauyuka yana sayar da busheshen kubewa. In damina tazo kuma ya taya bbanshi noma. A yawonsa na bin kauyuka ya hadu da mamata a Dukku, tazo siyan kubewa ya ganta yace yana so, itama ta nuna ra'ayin hakan, bai bata lokaci ba ya samu babanta ya masa bayanin inda ya fito da sana'ar sa kuma yaga diyarsa yana so. Babanta yayi murna da jin haka, don akoyaushe addu'arsa bai wuce Rahmatu ta samu miji tayi aure ba, don tun tana karama mahaifiyarta ta rasu anan zamanta ya dawo gurin kishiyar mamanta, ba irin duka zagi da wahala rahmatu bata dandana ba, babanta kuma bashi da bakin magana kamar an asirce shi. Bukatarsa kullum ta samu miji tayi aure ko zata huta. Ya sami yayansa da maganan inda yaqi amincewa, wai tunda gida bai koshi ba baza a bawa bare ba. Kuma ai zatayi nisa da gida. Shi a sonsa a hada ta aure da dansa wanda duk garin bbu wanda baisan yana dauke dauke ba, bashi da takamaimen sana'a. Babanta ya nuna rashin amincewarsa shima, a haka suka tashi ba tare da tsayayyem magana ba. Babana kuma yana komawa gida ya sanar da iyayenshi inda sukayi murna da fatan alkhairi.

Sati daya da maganan babana ya koma dukku don jin amsarsa, Inda ya tafi da kakana wato malam Aminu. mallam sirajo (baban mamana) ya musu iso yasa aka shimfida musu tabarma a zaure, fura da nono aka kawo musu hade da ruwa suka sha sukayi hamdala, sannan aka fara magana. Yayan babana na aka kira yazo, koda aka koro masa bayani yace shi sam bai san zancen ba, fada yakeyi sosai ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba, wai sai da baki suka zo sannan za'a kirashi, kuma sai da sirajo ya amince? To me  zaice? Ai yarsa ce yayi abunda yaga dama. Don anga danshi bashida abun hannu amma da mai kudi yazo shine xa'a bata? Karshe ma cewa yayi bbu ruwansa akanta yayi tafiyarsa. Zuciyar fulani ta tashi na mallam sirajo ya cewa mallam Aminu a yau za'a daura auren, karshen iko kenan. A ranar aka daura auren a masallacin garin bayan an idar da sallahn azahar. Sai shigowa da akayi da goro da cingam cikin gida yara na cewa an daura auren rahmatu da mamuda. Da farko ta aza wasane sai da taga inna haule (kishiyar mamanta) na watso mata kayanta waje tana cewa ta hada ta kulle yau zata tafi gidan mijinta. Tana hawaye tana hada kayanta inna haule bata daina masifa ba da yake bakinta daya da su yayan mallam sirajo da matarsa. Wasu na cewa bakin cikinsu ne ya kashe maman rahmatun. Babanta ya mata nasiha ya miqa amanarta gurin kakana. Tana kuka yana hawaye suka rabu. Basu dawo ba sai bayan isha. Kakata tana jiran isowansu sai kawai taga har da amaryan aka taho. Bayan sun huta sunci abinci mallam Amenu yake sanar da ita komai. Ta jinjina lamarin inda ta tausayawa mamata. Dakin babana aka gyara musu inda ya siyo mata duk kayan daki da ake sayawa amarya na wannan lokacin. 


Hajia kulsum ta numfasa tace fatu ki tsaya anan. Lokacin sallar la'asar yayi. Dakin hajia suka shiga anan ta nuna mata yanda zatayi amfani da toilet din taa barta a ciki ta sauko kasa tana kiran farouq yazo driver ya kaishi islamiyah time yayi. Bayan ta shigo daki ne ta samu fatu har tayi alwala ta fito, sallaya ta miqa mata ta nuna alkiblah sannan ta shiga toilet din don gabatar da alwala. Fatu sake baki tayi tana kallon duniya tun a toilet din take kauyanci taba nan taba can da kyar ta yi alwalan ta fito, a dakin ma sai da taga kamar hajia zata fito ne ta tada kabbara[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣7⃣

Inda sukace jininta ne ya hau sosai, bata jima a asibitin ba ta koma ga mahaliccinta. Damuwa goma da ashirin. 


Anan fatu ta fara hawaye, hajia kulsum cikin tausayawa ta miqa mata tissue paper ta goge fuskarta sannan taci gaba.

Na shaku da kakata sosai, a matsayin mahaifiya na dauke ta. Bana jin rasuwar mahaifiyata kamar nata. Bayan rasuwan kakatace zamana ya dawo gurin goggo asabe, nine wankinta dana 'yayanta da yake duk maza ne sai autar ta zainab yar shekara 4. Shara, wanke wanke da girki ya zama daily work dina, duka zagi da tsangwama kuma har na saba dasu. Duk abunda yake faruwa kakana bai sani ba, da yake baya zaman gida yana can masallaci tare da tsofi irinsa suna karatu. Idan ya ganni ina kuka sai yayita lallashina da inyi hakuri komai zai wuce inyi ta musu addu'a, Tunaninshi mutuwar iyayena yake damuna, bai san harda wahalan da nakesha yanxu bane. Kwatsam ranar wata friday bayan an dawo daga sallahn juma'a goggo ta sameni da duka wai ban gama abincin rana da wuri ba, na tsaya wasa, tace "shegiyar yarinya da ido kamar na mujiya ki gama abincin sannan kixo kiyi wanki, kuma wallahi kika kai la'asar sai naci uwarki. Ta aza mini rankwashi a kaina wanda ya sani sakin wani wahalallen qara, "kina jina ina miki magana kina daga min kai kamar wata kadangaruwa don ubanki" da sauri nace "goggo kiyi hakuri" na cigaba da sheshshekar kuka, na tashi da sauri na fada kitchen. Kakana ne ya shigo da sallamarsa ta amsa tana muzurai, Allah yasa baiji abunda tayiwa fatu ba, don batayi tsammaninsa yanzu ba, baya dawowa a wannan lokacin. Ya shige dakinsa ya jima sannan ya kwala min kira, ina sauri zanje ta yafuto ni, naje, murde min kunne tayi tace "saura ki fada masa wani abu sai na ballaki, bulaliya kawai" ta sake ni hade hankada ni har ina cin tuntube na shiga dakin kakana. Cewa yayi inje inyi wanka zan rakashi unguwa. Na fito na fada mata ta harareni tayi kitchen. Da sauri na watsa ruwa na fito, kaya nasa da hijabi na cewa kakana na shirya muka fita. Maimakon naga mun shiga gari sai naga munyi hanyar gona. A cikin gonarshi a karkashin wata bishiyar dorawa muka zauna. Yace "fatu me asabe take miki a gida? Don yau naji wasu maganganu sabanin hankalina" ban yi jayayyaba na fada mishi komai. Idonshi yayi jawur yace " mahaifiyarki rahmatu amanace a gurina haka kema amanace, bazan bari ta maida ke baiwa ba insha Allah zan nema miki mijin aure kwanan nan inda zaki sami yancinki. Nayi farin ciki da haka sosai. Yayita bani baki hade da nasiha sai yamma liss muka koma gida. Muna zuwa yace in shimfida mishi tabarma a kofar dakinshi ya zauna. Daga ranar ya dawo wuni a gida yana waje tare da mutane, zai aika a kirani sau goma shi ma zai shiga gida sau goma. Abun yana damun goggo asabe sai dai bbu yanda ta iya. Na murmure na fara samun kwanciyan hankali, kaka ya sama min miji dan ladanin garinmu. Hafizu yarone mai hankali da nutsuwa, ga karatun addini baiyi boko ba amma yana da sana'arsa ta dinki, Yana samu ba laifi. Kaka yace "ga zabina wato hafizu dan ladan, idan kin amince inje in sami babansa muyi magana" gaskia bana jin sonshi a raina amma hankali da nitsuwarshi sun kwanta min. Nace "kaka duk wanda ka zaba shine zabina, fatana Allah yasa in samu zaman lafiya da kwanciyar hankali" kaka yaji dadin furucina yace "Allah ya miki albarka uwargidana" daria nayi nace "Ameen tsoho na" carbinsa ya dauka da niyyan min dukan wasa nayi saurin shigewa gida ina daria shima yana daria. Daga kan da zaiyi ya hango wata mota tana tahowa ta layin unguwanmu ga yara rudududu suna binta da gudu, parking tayi a jikin katangar gidanmu. Samari biyu ne suka fito suka nufo kakana da har yanzu yake zaune a kofar gida bai motsa ba. Kallo ya dawo kansu aka manta da mota. Sun fi kama da turawa ko aljanu.


Taku a kullum


Maman fa'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣6⃣

Sunyi sallah inda fatu taci gaba da labarinta..

   Zaman lafiya akeyi tsakanin mamata da surkunanta, abu daya ya ke damun mahaifiyata rashin haihuwa. Duk lokacin da goggo innani tazo sai ta samu bakar magana ta yaba mata, nan ma kakata na mata fada. Ta shekara biyu ne ta shirya zuwa ganin gida. Tana isa ta tarar babanta ba lafiya sosai sai dai a kwantar a tayar, tayi kukan halin da yake ciki shi kuma yayi murnar ganinta, don tayi kyau tayi kiba. Ta bawa kowa tsarabar sa bbu wanda ta manta, bayan kwana biu tace a kaishi asibiti, mallam jauro (yayan babanta) yace ba za'a kaishi ba, ai rubutu da maganin gargajiyan da ta raina shi ya kawo shi har yau, yayi ta mita. Satin ta uku tana jinyarsa Allah ya amshi abunsa. Tayi kuka sosai bbu wanda bai tausaya mata ba. Bayan sadakan arba'insa akace azo ayi rabiyan gado, aka raba da yake ita mace ce bata tashi da komai ba sai budurwar akuya. Tun suna bata abinci har rannan mallam jauro yace shi ya gaji da ciyar da ita, hala wani mugun abun tayi acan mijin ya korota shine zata zo tace wai tazo ganin gida, ai wata biun ya cika mijin baizo ba, tana kuka tana bashi hakuri amma ko a jikinsa, hasalima inna haule da matarsa ce suke zugashi, a cewarsu zata cinyesu in suna bata abinci, Akuyarta ta sayar take cin abinci. Ranar sai ga babana ya zo inda ya tarar da rasuwan surikinsa, ya musu ta'aziyya yace zai dauki matarsa su tafi. Budan bakin mallam jauro cewa yayi kar rahmatu ta sake zuwa garin don wanda ya hada ya raba, (kuji rashin tunani da imani) in kuma tazo ta nemi inda zata sauka badai gidansa ba. Mamata tayi kuka kamar ranta zai fita haka babana ya jata suka tafi. Anan yake tambayanta yan'uwan mahaifiyarta. Tace fulani masu yawo ne, sunzo dukku babanta  mallam sirajo ya ga  mahaifiyar ta wacce ta taba aure a cikin yan'uwansu amma zaman baiyi dadi ba, 'yarsu daya suka rabu da mijin, aka daura musu aure, bayan wata 2 sauran kuma suka kara gaba. Daga nan basu kara yowa ta dukku ba. Sun dawo gida ta samu muntari yayi amarya.  Shekararsu 9 Allah bai basu haihuwa ba, inda amarya asabe ta haifi 'yaya 4, goggo innani ta hada kai da asaben muntari suna kuntata wa mamata kakata na tsawatar musu. Ana haka har ta samu cikina sunyi murna sosai amma cikin yazo da laulayi ta wahala sosai inda tana haihuwata tace ga garinku. Babana yayi kukan rashin matarsa mai hakuri da juriya ga sanin dattako. Ran suna naci sunan kakata (mamar babana) wato Fatima inda ake ce mini fatu. Na taso cikin kulawan mutum uku, kakannina da babana. Don yanzu kawu muntari ya fara bin hudubar su goggo innani wai an fi sona akan yayansu. Na yi primary anan kauyen mu. Inda duk garinmu bbu wanda ya kaini kokari, sannan na shiga secondry ina jss 2 babana ya hadu da accident akan hanyarshi ta zuwa kasuwanci. Bamu da labari sai gawarsa da aka kawo. Fadin irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne. Nayi kuka har na rasa inda zan tsoma raina. Anan nake tunanin kodai gaskiansu goggo asabe cewa dangin mu akwai mayu masu cinye duk wanda suka rabe su. Kakata kuma tun daga lokacin ta fara kananun rashin lafiya. Na cigaba da karatuna inda kakana ya jajirce sai na gama secondry skul, duk sa'annina sunyi aure daga mai 'ya'ya biu sai mai uku. Na kuma faranta masa nayi candy daga nan kuma samari suka min caaa! Don duk wanda yazo gurina kakana kance mishi sai na gama karatu. A cikinsu kuwa harda dan kawu muntari da dan goggo innani. Ni kuma wallahi duk cikinsu bbu wanda nake so. 

Rannan ina bacci da dare naji ana shafani, bude idon da zanyi naga babangida dan kawu muntari ne. Zan yi ihu ya toshe bakina, na takarkare na dankara mushi cizo sannan nayi ihu. Mutanen gida suka fito ana haskawa. Fitowa nayi da gudu cikin gida ina haki, kaka yace "mene fatu me ya sameki? Nace "babangida ne ya shiga dakina kuma yana tabani" na fada ina matsar kwalla wanda har lokacin jikina bai daina rawa ba. Inna asabe ta cabe "munafuka, sharri zaki yiwa yayan naki? Me zaiyi da ke jiki kamar na aljanu" kaka ya dakatar da ita yace "ina babangidan? Ya ce gani nan, "kaji abunda fatu  tace? Yace "wallahi karya take min, na fito zaga bayan gida ne naji kamar nishin mutum a daki, nayi zaton batada lafiya ne da na haskata sai naga mafarki takeyi tana wannan nishin. Shine na bugi hannunta tana tashi tasa ihu. Salallamai goggo asabe tasa wai nayiwa danta sharri. Shi kuma ya fita zaure inda dakinsu yake yana mita wai dama ba'a sonsu a gidan. Ni kuma sai rantse rantse nake, kakanina da kawu muntari sun yarda don zai aikata. Kakatace ta jawoni dakinta na karasa kwana anan. Daga ranan na dawo dakinta kwana. Sati da faruwar lamarin kakata ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzabi ga jiri da yake dibanta, anyi magani na gida har asibiti aka je inda suka ce [truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣8⃣


Sallama sukayi ya amsa, kana ya dubi yaran da sukayi dandazo suna kallon samarin yace su tafi wasan su, kan kace me kowa ya watse don basu da rashin kunya. daya daga cikin samarin  yace

"Don Allah baba nan ne gidan mallam mahmudu? Duk'ar da kai kaka yayi sannan yace "ehh" still wanda yayi tambaya na farkon yace "gurinshi muka zo shi da matarshi, daga gombe muke" kaka yayi dan jimm sannan yace "Allah ya musu rasuwa dukansu" "sun rasu" saurayi na biyu ya fada cikin firgici, sannan ya nemi guri ya tsuguna yana "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya jikanku".

Saurayi na farkon ya dubi kaka da tarin damuwa a fuskarsa yace "Allah ya jikansu yasa sun huta" "Amin Amin" kaka ya furta yana goge hawayen da ya zubo mishi ba shiri. Saurayi na tsugunne yace "jameel mu tafi" ya miqe jikinshi a sanyaye ya nufi mota. Kaka ne yace "zaku tafi baku sanar dani alakar ku ba" jameel yace "wancan abokina nane, sunanshi sultan, matar mallam mamudu wato aunty rahmatu qanwar mamanshi ce, uwarsu daya. "Allahu Akbar Alhamdulillah" kaka ya fada cikin tsananin mamaki don baiyi tsammanin za'a ga dangin mahaifiyar rahmatu ba cikin ruwan sanyi haka. "ai akwai rabo tsakaninsu sun sami 'ya mace fatu, tana nan, ni mahaifin mahmudu ne" farinciki ne kwance a fuskar kaka yana murmushi. Jameel ne ya kwalawa sultan kira ya fito daga mota still jikinshi a sanyaye, jameel yace "akwai cousin dinka fatu, 'yar aunty rahmatun ce" cikin doki yace "ina take? Yana kallon zauren gidan. Kaka yace "tana ciki, amma in bazaku damu ba ina son magana daku. 

Tabarma kaka ya shimfida musu a zaure suka zauna, shiga gida yayi ya sameni  tsakar gida ina karanta wani  littafi, yace "uwargida ki samin ruwa a kofi nayi baki" nace "to". Miqa mishi kofin nayi ya karba ya wuce cikin zauren. Bayan sun qara gaisawa ne kaka ya fara basu labarin mamata har zuwa kaina, bai rage komai ba harda wahalan da nake sha gurin asabe idan taga kaka baya nan. Kaka ya qarasa magananshi da cewa "idan baza ka damu ba kai sultanu ka auri qanwarka zata fi jin dadi cikin ku, nasan dana fadi na mutu fatu bata da gata sai Allah, don wadannan ba riqeta da gaskia zasuyi ba" kaka ya cigaba da maganarsa duk akan sultan ya aureni ya taimaka min. Kan sultan ne yadau zafi yayi dana sanin nemo su, gaskia bazata sabu ba. Shiru yayi kansa a qasa ko motsi mai kyau bayayi, ya bude baki zaiyi magana kenan Jameel yayi caraf yace "hakan yayi kyau, Allah ya tabbatar da alheri" Amin. Kallon mamaki sultan yake bin jameel dashi don ya wargaza mishi plan, wata dabara ce tazo mishi in akayi sa'a zai fita.

Yace "mallam zamu koma gida sai daga baya inshaAllah magabata su zo. Kaka yace "mutum bai san ranar mutuwanshi ba, watakila bazan kai zuwa gobe ba har zuwa lokacin da zaka turo magabatanka, kamar yadda na fada maka nine ke riqe da fatu, ayau nabar dunia zasu iya aura mata wanda ransu yake so, inda zata cigaba da shan wahala. Nafi aminta dakai shiyasa nake so ayau a daura muku aure, "Shikenan" abunda sultan ya iya fadi kenan don tsohon ya cika kwarjini bazai iya mishi musu ba.


An daura aurena da sultan a masallaci bayan an idar da sallah. Inda kaka ya zame min waliyyi liman kuma waliyyin sultan. (Tarihi ya maimaita kansa). Gida suka dawo inda kaka yace ya tafi dani, amma sultan yace zai tafi wani course na wata biyu inya dawo zaizo ya daukeni, kaka bai kawo komai ransa ba ya yarda. Shiga cikin gida yayi ya barsu a zaure inda ya aika in kai musu abinci don ranar ni nayi girki. Har lokacin banida labari don kawu muntari yayi tafiya, asabe kuma taje ganin gida. 'yayansu kuma ba zuwa masallaci suke ba. Na fita na kai musu, durkusawa har kasa nayi na gaishesu mutum daya ne ya amsa yana min murmushi, amma dayan ko dago kai baiyi ba. Mai murmushin yace "me sunanki" nace "fatu" yace "masha Allah abokina yayi sa'ar mata" fita nayi ina mamakin maganarsa, to a ina hafizu ya sami abokai yan birni haka. 

Shiga na keda wuya kaka ya kirani dakinsa, da farko nasiha ya fara min kan ya bani labarin abunda ya faru. Babu abinda na iyacewa illah hawaye da ya dinga bin fuskata, na rasa hawayen menene, ta wani gurin ina farincikin samun dangin mamata, while ta wani gurin ina tausayawa kaina don wanda aka aura min ko kallona bai yi ba. Na dade a dakin kaka sanna ya fita dubo bakinshi ko sun gama cin abinci. Ya fita ya samu jameel yaci amma sultan ko ruwa bai sha ba, jameel ne yake cewa wai sultan din azumi yakeyi. 

Kaka ya musu iso cikin gida aka shimfida musu tabarma ta bayan dakunan mu gurin akwai bishiiya gefenta kuma rumbun ajiye abinci ne. Kaka ya wuce yana cewa bari ya kira fatun. Gefen su kadan na zauna akan wani dutse na sunkuyar dakai ina wasa da yatsuna. Mijin nawa dai har yanzu kansa na kasa bazaka game yanayin da yake ciki ba. Ja[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


0⃣9⃣


Jameel ne ya fara magana "Amaryanmu kina lafiya" nace "lafiya kalau" ya kara cewa "sai kika ji an daura aure babu wani taro babu al'adu irinsu zance, bayarwa, kayan aure da sauransu. "Uhmm" na iya cewa. "Komai da kika gani muqaddari ne daga Allah, wannan aure naku insha Allah baza kuyi dana sani ba. Ya cigaba da maganan shi inda yake nuna mana mu riqe junan mu cikin amana duk da ba auren soyayya bane, ya karasa magananshi cikin nasiha. Duk abunda yake cewa sultan bai ce uffan ba, don wayarsa ya dauka yana dannawa. Mikewa yayi sannan yace "bari in barku kuyi magana, kar in takuraku da yawa" ya fada cikin tsokana. Mun fi minti biyar b wanda yayi magana can yace "kinyi makaranta? Nace "ehh" "ina kika tsaya" "secondry" yace "shekarunki nawa? Nace "17" sai lokacin ya dago kai ya kalleni 4 d first time nayi saurin sunkuyar da kaina. Can ya kara cewa "kin taba shiga birni" nace "Aa'aa" yace cikin bata rai "kin min yarinta da yawa, kuma karatunki baiyi zurfi ba, bana jin zan iya rayuwa da irinki" dai dai nan jameel ya dawo yace "times up, kar muyi yamma a hanya" hope kun daidata? Ya fada yana murmushi. Babu wanda ya kula shi don ni ina kokarin mayar da hawayen da yake son zubo min ne, jameel ne yace in matso kusa da sultan zai daukemu hoto. Shiru nayi sai da ya kara maimaitawa na taso na tsaya nesa dashi, turo sultan yayi gurina wanda yake aika masa harara ta ko'ina, baya yayi yace mu dago fuskokin mu, still kowa kansa na qasa, yace to bari in kira kaka, may be zaku fi jin  magiyarsa. Saurin dago da kanmu mukayi yace "smile" sannan ya daukemu a hoto. Abun mamaki yana daukan hoton wani abu ya fito daga cikin camera, ya kara daukan mu abun ya qara fitowa. Miqa min na farkon yayi na karba ban duba ba. Sultan har ya fita waje, ciro kati yayi daga aljihunshi ya bani, yace "wannan shine address na gidansu sultan, abokina yana da wuyar sha'ani amma in kika yi hakuri komai zaiyi karshe, ki ajiye address din don bamusan gaba me zata haifar ba" ya karashe maganarsa cikin tausayawa. Nace "Nagode Allah ya kiyaye hanya" shima fitan yayi inda ya iske kaka da sultan suna hira kamar bashi ne yake bata rai dazu ba. Tafiya sukayi kaka ya shigo cikin gida yana mai farincikin fatu tayi sa'ar miji. Ni kuma tun tafiyan jameel na nade tabarman na shige dakina ina kuka mai tsuma zuciya, daa kaka yasan wa ya aura min da bazaiyi farin ciki ba. Kiran da kaka yake min yasa nayi saurin goge fuskata na fita ina murmushi yace in sameshi a dakinsa. A dakinsa na samu guri na zauna ya miqo min kudi yace "sadakin ki ne dubu ashirin" nace ya dauka ni bana so, yace ai hakkina ne maza in karba. Na karba na wuce dakina na cigaba da kukana har bacci ya daukeni. Bugun kafa na naji anayi na tashi ya firgice goggo asabe na gani tsaye a kaina fuskar nan a tamke, tace "wani jita-jita nake ji a gari wai an daura miki aure hka ne? Nace "ehh" nan ta fara masifa ai dama dangin mu haka suke sai sunga mai kudi suke aura, ga babangida yana sona amma kaka ya hana shi. Allah yasa mijin nawa ma dan yankan kai ne, kallonta nayi ido cikin ido nace "ba kudin shi muka bi ba, sultan dan'uwana ne, mahaifiyarsa addar mamata ce" cikin mamaki tace 'eeeyeee' nace  "kwarai" fita tayi daga dakin tana jin bakin cikin auren, don yadda aka fada musu mijin nawa dan birni ne kuma ga kudi akace da mota irin ta sarkin Kumo yazo. Sadakina na boye don nasan ko ita ki 'yayanta wani zai biyo dare. An koma baya don goggo asabe tana ganin kaka ya fita zata fara cin zalina, girki kuma da shara wanke wanke nice keyi da kaka yayi maganan a rage min koda daya  ne cewa tayi horar dani takeyi, gidan wani zanje don haka ya kamata in saba da aiki, kaka kuwa ya yarda da magananta.  Bayan wata da daurin aure na wani mutum yazo da envelope ya bani yace aikoshi akayi daga gombe. Na aza wasika ce amma sai naga kudi ne 30k. Kakana na kaiwa yayi godia yana cewa sultan bai mance dani ba tunda har yana kokarin sauke wasu hakkina. Bayan wata daya muna tsammaninshi sai muka ga dan aikan rannan. Yace sultan yace a fada mana zai qara yin wata uku. Kowanne karshen wata sai dan aiken yazo da envelope kudine a ciki wataran 50k watarana 30k. Koyaushe aka kawo zanyi tsammanin akwai wasiqar sultan a ciki amma babu. Har wata 3 ya wuce babu labarinsa daga nan su goggo asabe suka fara habaici "ai nasan za'a rina, hala kakaba mishi ita akayi, yoo dama me zaiyi da kucakar yarinyar nan; shi dan birni. A haka zakiyi ta zama har ki tsufe, dama kudi kuke so to ai gashi ana turo muku" idan ta fara maganganun nan nakan shiga daki inyi ta kuka ina kallon hoton[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣1⃣

Dawowa na gida na iske kaka na yana masallaci, don haka kai tsaye dakina na fada na ajiye kayan na fito nayi alwala nayi sallah. Ina idar wa naji kakana ya dawo, goggo asabe ta kirani in kai mishi abinci, naje na karba, har zan juya ta kirani na jiyo, "amm fatu yau ba'a kawo miki saqo bane, wallahi rance nake so ki bani na dubu uku, masifaffiyar goggon kin nan innani na ara a gurinta, don tsiya jiya har da aiko sadiqa tayi tamin rashin mutunci" nan ta fara matsar kwalla, kar ki manta hajia duk randa aka aiko kudi rabashi akeyi duk abunda aka bani ita ke amshe wa da wayo, wani tace zata biya bashi wani kuma tace zata karbo min maganin bakin mutane, Wani kashin na abincin gida, don wani abincin da muke ci ba'a cinsa a gidan maigari, kinga kamar taliya da dan waken fulawa, wallahi wataran harda macaro  muke ci (inji jawaheer😂😂). Hajia tace "Macaroni kike nufi? Fatu tace "ehh, sauran a ajiye saboda bukatun yau da kullum. Nace "an kawo in kaka ya bani zan kawo miki" na fita a zuciyana ina cewa anji kanku. Dakina na fara bi na dauko envelope din na wuce dakin kaka. A daki na iske shi yana kishingide, na masa sallama ya amsa, ajiye abincin na miqa mishi saqon nace a hanya na hadu dashi ya bani. Ya karba jikinshi a sanyaye yace zai kirani anjima. Ina fita naga goggo asabe a kofar dakinta tana jirana, sai da na isa tace ina kudin? Nace " sai yaci abinci sannan zai bani. Shiga dakinta tayi bata kulani ba ni kuma nayi shigewata daki ina jiran kiran kaka don karanta wasiqa. Bayan Minti sha biyar lamido dan goggo asabe ya zo ya kirani hijabi nasa na fita. Shiga nayi na samu guri na zauna nace "kaka gani" yace "takarda na gani a cikin kudin Allah yasa ba abunda nake zato bane, ya fada yana mai girgixa kai cikin damuwa. Nace "ba komai kaka Allah ya zaba mana mafi alkairi. Yace "ameen" hade da mikomin paper. "Hajia kinsan abunda na rubuta? Hajia tace "a'aa" fatu tacigaba "rubuta ban hakuri nayi na jimawan da sultan yayi bai zo ba, hakan ya samu asali ne ga riqeshin da akayi a kasar wajen, kuma kaka ya bari inzo gombe gidansu yana so yayi wa mamarsa suprise"

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍


1⃣0⃣


Idan na gaji inyi alwala inyi sallah in kai kukana gurin Allah. 

Sati daya daya wuce na cika shekara daya da aure, a cikin shekaran kuma dan aika yana kan zuwa kowanne month. Idan muka tambayeshi labarin sultan sai yace bai dawo bane. Hankalin kaka ya fara tashi ya fara dana sanin daura auren, akwai lokacin da ya kirani ya ke cemin ko zamuje kotu a raba auren? Nace mishi a'a, don nasan gwanda zamana da igiyar sultan akaina akan in zama bazawara hankalin kaka zai fi tashi. A ranar da zan cika shekara da aure muke tsammanin zuwan dan aika, a ranar na shirya plan dina don sanin matsayina. Yawanci bayan azahar dan aika yake kawo kudi, kaka na samu a kofar gida karfe 12:30 nace zan shiga jeji debo ganyen lalle, yace in aika yara mana, nace ina son zuwa da kaina ne, bai kawo komai a ransa ba ya mini izini. Already na gama shiri na fito, hanya kawai na yanka na shiga jeji inda nan ne hanyar shigowa cikin gari. Sai da na debo ganyen lallen na fito bakin hanya na tsaya a gindin bishiya ina jiran dan aika.

Nafi minti 30 na hangoshi yana tahowa kamar kullum a kan machine dinshi. Fitowa nayi ina tafiya nayi kamar ban ganshi ba, yazo dab dani na juya ya ganni ya ce ahh fatu me kikeyi anan? Yana kokarin tsayar da machine din, nace laa nazo tsinkar ganyen lalle ne yanxuma gida na nufa. Yace in hau ya isar dani, nace a'a nagode. Yace to ga aikan tunda na hadu dake a hanya, ki gaishe min da mallam Ameenu. Na karba nayi godia ya juya ya koma. Sai dana tabbatar yayi nisa sannan na bude envelope din, yau ma kamar kullum kudine babu wasiqa. Na fito da yar takarda daga cikin ledan da tun fitowana daga gida yana cikin hijabi na, hade da dan kunu a farar leda takardan na tura cikin envelope din na shapa kunu na liqe kamar ba'a budeba nayi hanyar gida ina mai farin cikin hukuncin dana yanke. 


Jama'a menene fatu ta rubuta? 😳😳😳😳

Ina mai bawa masoya hakuri na rashin jina kwana biyu, phone dina ne ya samu matsala. 

Luv u ol


Taku a kullum 

Maman Fa'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣3⃣

Sun idar da sallah suka ci abinci, dija mai aiki ta tattare gurin fatu ta taya ta suka kai kitchen ta fito palour, farouq sai zuba surutu yakeyi fatu tana biye mishi har aka kira sallan isha ya tafi mosque suma suka tashi don yin sallah. Bayan sun idar da sallah ne suka dawo palour hajia ke tambayar fatu "sultan din bai baku number wayarshi ba? Fatu tace "hajia ai address din ma ya jameel ne ya bani bashi ba" kuma ni ban taba yin waya bama, to da waye zanyi? Ta karasa tana daria. "Babangida da kawu muntari ne kadai masu waya a gidanmu sai goggo asabe da ta taba siya tayi wata hudu ba'a kirata ba shine ta sayar😂😂. Murmushi hajia tayi tace "to yanxu fatu ya za'ayi ki tunkari sultan har kice ya sauwaqe miki? Fatu tayi dan jimm sannan tace "hajia tunda innar tawa qawarki ce sai ki fada mata ita tayi mishi magana" hajia tace "ke bakya dokin ganin innar taki ce"? Fatu tace "hajia inaga abunda sultan ya mini itama shi zata min, mahaifiyata suka zo nema bani ba, kinga ko baza su damu dani ba, nima kuma bazan tura kaina cikinsu ba" Haajia tace "fatu mahaifiyar sultan zata so ki sosai, don tun muna jeka da fari ta je dukku gurin mamanta wato kakarki, sunje aka ce musu ta rasu, 'yarta rahmatu kuma tayi aure a wani gari. Hajia sadiya (maman sultan) ba yanda ba tayi su fada mata sunan garin ba amma suka ce sun manta, zuwanta na biyu bana mantawa bamu dade da dawowa nan gidan ba ta qara zuwa, wannan karon  Cewa sukayi karta qara zuwa gurinsu, don basu hada dangi da ita ba, wacce suka hadan ma sun yafe ta. Duk maganganun nan daga bakin yayan kakan ki yake fitowa, wai sunan shi mal jauro, ina mamakin yanda akayi sultan ya nemo ku". Fatu tayi shiru tana tunanin ya auntyn ta hajia sadiya zata karbeta, taji dadin jin ance tana son su. Hajia ta cigaba da cewa "ni a nawa shawaran ki zauna anan har lokacin da kike tunanin zaki iya samunshi ki masa magana, batun hajia sadiya kuma baza ta taba yarda sultan ya sake ki ba, don haka ki zauna anan ki fara makaranta har zuwa lokacin da naga ya dace ki tunkareshi. Fatu tayi shiru tana tunanin maganan hajia, hala in taje gurinshi yanzu yace bazai saketa ba ya korata kauye, amma in ta zama 'YAR BIRNI bazai wulakanta ta ba zai bata abunda take nema cikin salama tunda yasan tana da ilimi.

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣6⃣


A guje fatu ta shigo palour, hajia dake qoqarin haurawa sama ta dakata tace "lafiya fatu? Fatu tace "mummy wallahi mal usman na gani, mai kawo min saqo din nan, yana tura gate" hajia tace "mal usman ne yake kai miki saqo dama? No wonder kowanne month yakance zaije kumo kai saqo, kuma ban taba tambayarshi ba, da yake shi dan garin kumon ne" fatu dai bata ce komai ba sai zare eyes da take yi. Hajia tace "karki damu, nasan abun yi, kije ki shirya ki sauqo muyi breakfast" fatu tace "to" kana ta miqe ta haura zuwa dakinta. 

Hajia kuma hijabinta ta saka ta nufi bakin gate gurin mal usman. Yana ganinta ya taso da sauri har yana duqawa ya gaishe ta, ta amsa masa cikin fara'a kana tace "mal usman saqo da kake kaiwa kumo gurin waye kake kaiwa" mal usman yace "gurin wata yarinya da kakanta ne, shekara kenan ina kaiwa, inaga na taimako ne ko kuma yar uwarsu yallabai sultanun ne" harda abunda ba'a tambayeshi ba ya fada. Hajia ta nisa tace "Yarinyar tana nan gidana amma shi sultan bai sani ba, idan ya baka saqon next month ka kai can garin modibbon, idan kakan ya tambayeka labarin fatu kace tana nan lafiya kalau, kar ka nuna masa ba'a gidan su sultan din take ba, zaka min wannan alfarmar? Kai tsaye mal usman yace "hajia duk yanda kika ce haka za'ayi" hajia tace "nagode kuma shima sultan din kar ka nuna mishi komai" hajia ta fada sannan ta shige cikin gida. Shi kuma ya koma bakin aikinsa don ta daure masa kai, amma dai yasan duk rintsi hajia baza ta taba cutan wani ba, kuma in ba kwanan nan ba basu san cewa Iyalai biyun ba dangin juna bane.

Sake curtain din window fatu tayi bayan taga hajia ta koma palour tayi ajiyar zuciya ta fada toilet tana mai addu'an Allah yasa mal usman ya bada hadin kai.

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍  

1⃣4⃣

Da wannan tunanin tace "hajia na amince in har zaki yarda ki dauke ni, wanke wanke da shara ko girki zan dinga yi? Hajia tace "ban gane ba" fatu tace "kince zan zauna anan inyi karatu to kuma banida kudi kuma ai bazan zauna hakanan ba tareda ina muku aiki ba" murmushi hajia tayi sannan tace "ni babu abunda zaki min, kudin makaranta kuma nice zan biya, dake dasu jameel duk daya na dauke ku" fatu harda hawayen farinciki tana kwararawa hajia kulsum addu'a sai da ta dakatar da ita. Fatu tace "hajia to kakana fa? Don yace in sanar dasu in na isa" hajia tace "karki damu nasan abunyi" farouq ne ya shigo da sallaman shi ya nemi guri kusa da fatu ya zauna hajia tace " farouq a ina ka zauna tun tafiyanka sallah isha? Yanzu gashi har 8:42" yace "mummy gurin baba mai gadi na tsaya, yana bani labarin sojoji ne, kinsan ina son zama soja" hajia tace "kai kam da son soja, shima mal amadu da yake biye maka kana sa shi surutu" daria sukayi dukansu, farouq yaje ya dauko home work dinshi ya kaiwa fatu wai ta tayashi. Yanda take nuna mai komai dalla dallah yasa hajia cikin mamaki, don ta english take masa bayanin wanda in bai gane ba sai ta masa da hausa, sun gama ya dauki bag dinshi ya musu sai da safe ya wuce dakinshi. Hajia ta dubi fatu wacce tafiyan farouq bai mata dadi ba, don har ta fara takura kana tace "fatu kince a kauyenku kikayi primary, to sec fa? Fatu tace " a garin kumo nayi scndry skul dina, abokin babana ne wanda ya kawo ni tasha yake zuwa da sassafe ya kaini, in an tashi ni kuma in hau acaba ya mayar dani kauye, anan na fara tun daga jss1 har nayi waec da neco, na samu kyautuka da dama ranar speech and prize giving day din mu. After months result ya fito na samu both waec and neco, sai dai banyi jamb a shekarar ba. Bayan aure na ne nayi jamb ina tunanin in sultan ya yarda sai inyi university dina. To da yake bai zo ba sai abun ya mulmulce" hajia tace "kinci jamb dinne? Fatu tace "eeh naci, ina da 220 points" hajia tace "ahh lalle kinyi kokari, last year ne kikayi ko this year? Fatu tace "nayi last year kuma nayi this year" hajia tace "ashe bazamu sha wahalan sama miki admission ba, yanzu dare yayi muje ki kwanta ki huta, gobe in Allah ya kaimu zamu qarasa magana" kashe komai na wuta sukayi suka haura sama hajia ta kaita wani daki kusa da na farouq, daki ne madaidaici da toilet dinshi a ciki, komai na dakin pink nd white ne, gadon Mai dan girma, sai wardrobe dinshi da mirrow duka pink, can gefe kuma gurin karatu ne desk da chair white, labulayen pink nd white sai paint na dakin sky blue mai oily sai sheqi yakeyi. Sana'ar dai fatu ta sake yi wato sake baki, hajia tace "nan dakin aisha ne yanzu kuma ya dawo naki" fatu tace "hajia duka wannan, nikam ko da mai aikin ki zan dinga kwana" hajia tace "a'a anan zaki zauna na fada miki bana son kina banbanta kanki dasu farouq, duk daya kuke, ki saki jikinki tamkar nan ne gidanku, abunda nake bukata daga gareki kenan in har zan samu" fatu tayi saurin riqo hannun hajia tace "kinfi karfin bukatar abu a gurina sai dai ki bani umarni, insha Allah zaki sameni mai miki biyayya, wallahi ban taba tsammanin akwai masu kudi da son jama'a irinku ba hajia. Nagode Allah ya biyaki da Aljannah ya kuma raya miki 'yayanki" "Ameen Ameen" hajia ta fada sannan ta mata sai da safe ta wuce dakinta, rufe kofar fatu tayi ta ajiye jakanta a gado, ta hau kan gadon tana daddannawa, can ta miqe ta shiga toilet din sai da ta gama qare masa kallo tana daria sannan ta fito ta cire hijabinta ta bude jakanta ta dauko soso da sabulu hade da brush da tootpaste ta ajiye a gefe. Cire kayanta tayi ta dauki Wani extra zani da alama na wankanta ne tasa ta shiga wanka, bata dade ba ta fito ta sane jikinta ta shafa mai, tazo daukan wani kaya ne taga wasu night wears riga da wando orange colour masu laushi akan gadon, taga kuma an saka bedsheet an lailaye gadon wahoho fatu tace "Alhamdulillah" tasa kayan ta jera kayanta kala uku a cikin wadrobe din jakan ma tasa shi a ciki wanda akwai kudinta a ciki. Ta kashe wuta ta haye kan gadon tayi addua ta rufe idonta tana tunani har bacci ya dauketa.


Taku a k[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣2⃣

Tunda na fara kaka murmushi yakeyi cikin jindadi, har bansan lokacin da hawaye ya zubo min ba, na share ba tareda ya gani ba. Sai dana gama yace " fatu Allah ya amsa addu'a na, kullum burina mijinki yazo ya dauke ki, ayau Allah ya nuna min ranar" kwalla taff a idon kaka na farinciki. Hajia nayi dana sanin rubuta wannan wasiqar don bawai inason zuwa gurin sultan don ya karbe ni a matsayin matarsa bane, a'a don ya sauwaqe min ne nima in samu dai dai ni in aura. Kuma hakan zaisa kaka ya samu kwanciyar hankali. To amma tsananin farincikin dana hango shimfide fuskarsa sai tausayinsa ya kamani, ban kyauta masa ba. Kaka yace in shirya gobe in tafi. Kuka na fara Nace a'a sai shi sultan din yazo, zanyi ta zama da igiyarsa a kaina har ranar da Allah ya kawo shi. Ban taba yiwa kaka musu ba sai ranar. Bai ce min komai ba har na tashi na tafi dakina na cigaba da kukana, ina tausayin kaina da kaka. Da kawu muntari ya dawo aka fada masa abunda mijina ya rubuta shima ya bada goyon baya in tafi, goggo asabe kuwa hankalinta ne ya tashi don bata son taga abu mai kyau ya rabe ni. Ana gobe zan taho  na fara shirin tafiya gombe don inje ayita ta qare, na kasance koyaushe ina tunani da addu'ar Allah yasa zuwana ya kasance alkhairi. Hajia har abinci nake kasa ci, ace an daura mini aure yau shekara amma mijin bai ko waiwayeni ba. Abunda kaka ya fada min ne ya girgiza ni, wai da kawu muntari zanyi tafiyan!!! Tirkashi😳😳

Nace masa ai a wasiqar sultan yace inzo ni daya, na nuna masa tunda nayi karatun boko ai bazan bata ba koda a kano ne😜, Kaka ya amince. Da dare kasa cin abinci nayi don ina da tabbacin in naje sultan zai sake ni kamar yadda zan bukata. Da kyar kaka yasa na sha fura da daddare a dakinsa, mun kusan kai karfe goma yana min nasiha gameda inda zan koma wato gidan mijina, jinshi kawai nake yi ina mai tausaya mana. 

Tun da asuba na gama shiri kaka yana dawowa daga masallaci naje na gaishe shi, ya miqo min 15k wai in riqe zai min amfani a can din. 5 din saman na dauka nace zai ishe ni, ya qara min nasiha ya bani addu'o'I. A lokacin gari ya fara haske, machine din abokin baba ne mukaji yana diri a kofar gida. Har daki na sami goggo asabe na Mata sallama, duk 'yan gida aka fito domin ganin tafiyana. Ban dauki komai ba sai 'yar jakana na skull da kudin sadakina 20k sai kayana kala 3 don nasan ba jimawa zanyi ba. Kudin kuma bashi kayanshi zanyi. Na haye machine din ina hawaye haka muka kama hanya suna daga min hannu. 6:22 muka iso kumo, direct tasha muka isa ya sakani a motar gombe, shi ya biyamin kudin motan ma, yayi tafiyarsa don anan kumon yake aiki. Bakwai saura motar mu ta tashi mune bamu shigo garin gombe ba sai 7:30. Anan na sauka na sayi abinci, fitowana kuwa tsautsayi ya afka dani. Wannan shine takaitaccen tarihina. 


Shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa a ransa, farouq ne ya dawo yana mummy oyoyo, hajia ta shafa kanshi tace "Ka dawo" yace "ehh, yauwa mummy kika ce dama baza ta tafi ba, to yanzu in mata questions din? Hajia tace "gata a gabanka ai" zuwa gurin fatu yayi yace "dama tambaya daya ya rage, ina ne gidanku? Kai tsaye fatu tace "a kauyen kumo, ka taba zuwa kumo? Yace "aa'aa" tace "kana kama min da wani sunan shi jameel" yayi caraf yace " ya jameel yayi aure rannan ya tafi da matarsa south africa wai yana aiki, amma naji dady na cewa ya kusa dawowa" kafin ya qara bude baki hajia ta katse shi tace "aje a canja kaya ayi shirin zuwa sallah magrib" ba musu ya haura sama da gudu. Hajia ta juyo ta kalli fatu da kanta na qasa tace " jameel dana ne yana da kanne 4, mahmud ne mai binsa sai khadija da Aisha da autana umar farouq. Mahmud yana karatu a cyprus lawyer ne, insha Allah nan da 4 months zai kammala ya dawo gida. Khadija da Aisha sunyi aure inda khadija ke Abuja Aisha ke kano. Jameel abokin sultan ne tun suna yara, daa ba'a unguwan nan muke ba, muna jeka da fari ne, Allah cikin ikonsa ya budawa mahaifansu inda suka sayi fili anan GRA, In kin lura yanayin ginin gidajen iri daya ne amma kowanne da design dinshi. Skul daya sukayi tun daga primary har sec, inda a university kowa da zabinsa, don sultan fita waje yayi ya karanci Business ad, while jameel yana gwags karantan likita. Alhamdulillah sun kammala with flying colors. 8months da suka wuce jameel yayi aure ya tafi da matarsa south africa akan karatunsa. Mahaifiyar sultan qawatace sosai, hakama dads dinsu suke abokai. 

Kiran sallah da aka fara ya tsayar da hajia, sai da aka idar tacewa fatu ta isa daki tayi sallah, ita kuma hajia ta nufi kitchen don duba me aka girka.



 Nima na fita daga gidan don inje in daura nawa sanwar kar oga ya dawo babu abinci, kunsan bature yace "Hungry man is an Angry man"🏃🏽🏃🏽🏃🏽🏃🏽🏃🏽 

Taku a[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣5⃣


Bangaren hajia kuwa wautan fatu take gani, ace miji kamar sultan kaso rabuwa dashi? Ita dai bazata bari hakan ta faru ba shiyasa take son fatun tayi karatu ta kuma waye yanda shi sultan bazai so koda kuda ya gifta tsakaninsu ba. Duk da sultan bai kyauta ba amma ba taga laifin shi sosai ba don rayuwar turai yayi, ya saba ganin mata masu class da wayewa zai so matar sa ta kasance kamar su. 

Don haka hajia tayiwa kanta alkawarin kai fatu gidan sultan cikin so da kaunar junansu. 


Tun asuba fatu ta tashi tayi sallah ta dan jima tana addu'o'inta sannan ta shafa. Ta kusan minti 30 a zaune tana tunanin ko ta fita ne ta taya mutanen gidan aiki ko ta zauna ne oho. A haka har gari ya fara haske Knocking kofarta taji anayi da sauri ta tashi ta bude. Hajia ta gani ta durkusa har kasa ta gaisheta, hajia ta amsa tana murmushi tace "ya kwanan baqunta" fatu tace "Alhamdulillah" hajia ta miqo mata wata doguwar riga tace "idan kinyi wanka ki saka, sai ki sauqo kasa breakfast ni zan je in shirya farouq zuwa skul" fatu ta karba tayi godia ta ajiye kan gado Sannan tayi hanyar fita daga dakin hajia tace "ina zaki je" fatu tace "zanje in shirya farouq dinne" bata jira me hajia zata ce ba ta fita ta shiga dakin farouq don kusa da nata yake, tattausan murmushi hajia tayi sannan itama ta fice zuwa dakinta. Fatu tana shiga dakin ta samu shi baccinshi ma yakeyi, a hankali da wayo ta tashe shi ya shiga wanka bayan ta hada mishi ruwan wankan. Da ya fito ta tsane mishi jikinshi ta shafa mishi mai hade da sanya mishi uniform dinshi, gurin sa neck tie ne suka kai ruwa rana, don daga ita har farouq din babu wanda ya iya. Daria yake ta mata yace "mummy ta iya, muje ta saka min" daukan skul bag dinshi tayi suka sauqo zuwa palour anan suka sami hajia tana rufe lunch box din farouq. Tace "iyee har kun gama ne?" Cikin daria farouq yake bata labarin yanda fatu ta rinqa kokawa da neck tie wai bata iya ba, hajia ta dara kadan ta kirashi tana saka masa duk fatu tana gani. Dinning hajia ta kaishi aka hada mishi tea ga hadedden indomie dinshi a gefe, cikin nitsuwa ya cinye ba tareda ya bata kayansa ba, kana ya tashi yace "mum yau ma kece zaki kaini skul" hajia tace "noo, driver zai kaika, jiya ma don yayi asubancin tafiya garinsu ne" Farouq ya hade rai hajia na lallashinshi don kar ya makara. Fatu ce ta jawo shi jikinta ta rada masa magana a kunne,  duk iya gulma na banji me ta fada masa ba, kawai naga suna daria ta riqo hannunshi tace "muje in raka ka mota" hajia da ta tsaya kallonsu tace "ohh wariya za'a min kenan? Farouq yayi saurin hugging dinta tace "a'a mummy kema zan fada miki in na dawo, bye" har mota fatu ta rakashi ya shiga suna dagawa juna hannu, baba maigadi ne ya bude gate suka fita, yana kokarin rufe gate din fatu ta kalleshi da kyau. 

O M G 😳 mai kawo mata aika ne. Da gudu ta koma palour shi bai ma ganta ba.


Taku a kullum


Maman Fai'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣9⃣


Hajia tace yaje yayi wanka ya sauqo yin lunch, fatu ta riqe hannunsa suka tafi dakinsa tana tambayarshi labarin skul. Yayi wanka fatu ta wuce dakinta don gabatar da sallah, shima farouq wucewa mosque yayi. Bayan ya dawo ne suka hallara a dinning don cin abinci, suna kan ci fatu ta dauko musu zobo, ta tsiyayawa kowa kana ta zauna. Farouq ne ya fara tabawa yace "mummy wannan Ribena ne? Mummy tace " kamar zobo ne lemme taste it" hajia ta dan kurba tace "natural" kana ta kira dija tazo "haba dija, dama kin iya irin wannan zobon amma baki taba mana ba? Dija tace "hajia bani bane fa, fatu ce tayi" nan hajia ta maida dubanta ga fatu wacce cin abincinta take hankali kwance, tace "fateema a ina kika koyi wannan zobon? Fatu tace "mummy a skul ne, nayi food nd nut ai" fatu ta fada mata yanda sukayi. hajia tayi smile tace "zaki koya min nima, gashi babu wani flavour ko color, komai natural sai qarin lafiya ba abun cutarwa" duk sukayi daria, in banyi qarya ba kowa yasha zobo cup 5😜. 


Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, yau fatu ta cika 3 weeks a gidan, tayi fresh tayi kyau abunta, hajia tana nuna mata gata ba qarya, don kaya kala kala naga fatu na sawa ita da tazo da kala 3, shoes and bags ma gasu nan kamar na wata yar gwamna, make up kuwa takanas hajia ta kaita PRETTY AYSHA PALOUR ta koya mata kwalliya na zamani. 


Sanye take cikin wani swiss lace mai pink nd blue, tayi simple make up amma tayi matuqar kyau, kayan sun amshe ta kamar ka sace ka gudu, gyalenta ta dauka ta yafa a kafada ta fito palour ta samu hajia na kallo manara tv. "Sannu da hutawa mummy" hajia ta juyo tace "yauwa yar mummy, gurin mal usman zaki je kice kafin ya wuce kumo ina son ganinsa" fatu tace "to mummy" ta fita daga palourn ta nufi bakin gate. Turuss ta tsaya ganin sultan na magana da mal usman din. Rabon da ta ganshi tun ranar shigowanta gombe. Zuciyarta ne yake dukan uku uku, kar fa ya ganeta ya korata kauye ko kuma yaci mutuncinta, wayyo Allah! A zuciyarta tana ina ma bata fito yanzu ba. Yana gama maganansa ya miqa wa mal usman envelope yana cewa "bari in gaisa da mummy" juyowan da zaiyi yayi arba da ita, dumm gabansa ya fadi, "tsarki ya tabbata ga Allah da ya tsara wannan halitta" sultan ya fada a zuciyarsa yana mai qarewa fatu kallo ita ma din shi take kallo, sunfi 1 min a haka, fatu ce tayi qarfin halin fara tafiya ta nufi gurinsa.


Taku a kullum

Maman Fa'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [3:15PM, 7/11/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣2⃣


Kwanaki sun shude yau watan fatu biyar da barin garinsu tayi nisa a karatunta kuma tana fahimta, qawarta daya sunanta itama ma fatima. Qawancen su ya samu asali ne ranan wata monday fatu tayi latti sosai gashi har an shiga  lecture kuma lecturer baya barin a shiga, fatu sai safa da marwa takeyi a bakin hall din, fatima da take ciki ta hango ta sai ta bata tausayi, don tana lura da fatu, irin dodging lecture da students sukeyi ita sam bata yi ga kokari kamar me! Tana cikin tunaninta taji an jefe ta da abu; dumm gabanta ya fadi don tasan lalle yau zai korata waje, maimakon taji ance yi waje sai taji yace "Me kike kallo a waje? Bata san lokacin da tace "qawata ce" "u can join her" abunda ya fada kenan. Zare ido ta fara yi tace "sir bata da lafiya ne, ko dazu she called me tace bazata samu zuwa ba, so ganinta da nayi ne ya ban mamaki" sai da yayi dan jimm sannan ya mawa fatu hannu da take waje ta sake baki tana kallon ikon Allah. (Sana'ar ta ne dama sake baki😂). Sai da ta shigo yace "get well dear" tana in ina tace "thank you sir" guri ta samu ta zauna aka cigaba da lecture. Bayan ya fita ne ta samu fatima ta miqa mata hannu hade da sallama ta amsa hade da shaking hannunta. Fatu tace "amma kin taimakeni nagode sosai, gashi ya bamu light akan abunda zai fito a exams. Fatima tayi murmushi tace "ai kuwa, me sunanki? Fatu ta amsa "Fateema Mahmud" tayi carab tace "sunan mu daya amma ana kira na xahra levels" fatu tace "I like it" xahra tace "tnks namesey"

Haka qawancen su ya cigaba cikin aminci. Suna ziyaran junansu lokaci lokaci, hajia ta yaba da hankalin xahra shiyasa take barin fatu tana ziyartar ta. Bangaren sultan kuma soyayyar fateema ta gama narkewa a zuciyansa, sukan gaisa amma daga nan yake tsayawa, dan gaisuwan da yake yawan shigowan ma ya rage, don akwai ranar da yazo fatu tana ganinshi ta haura sama, yazo ya zauna suka gaisa da mummy, hajia tace "nikam sai kora min 'ya kakeyi, da ta ganka sai ta tafi" yayi murmushi yace "afuwa mummy" Haka suka cigaba da hiransu har yake tambayanta daddy tace yana Abuja, don shi bai cika zama a gida ba, lokacin zuwan fatu ma baya gida, da ya dawo hajia ta bashi labarin ta bai yi comment akai ba, illa cewa da yayi Allah ya taimaka. Yasa hajia ta kira masa ita ya mata questions akan rayuwarta ta bashi amsa,  kana ya mata nasiha yace ta dauki gidan kamar gidansu, kuma ta maida hankali akan karatu.

Yau shirye shirye akeyi a gidan don tarban manyan baki, mahmud ne zai dawo daga cyprus sai jameel da matarsa suma zasu dawo daga south Africa. Hajia ta kasa zaune ko tsaye haka fatu, duk wani shiri da girke girke an kammala sai isowan su kadai ake jira, karfe 2 na rana sukayi waya sun sauqo, nan da nan hajia ta aika driver a dauko su, farouq yaso a je tarbansu hajia tace nooo. Bayan tafiyan driver fatu tace wa hajia zata je tayi wanka kafin su dawo, hajia tace to. Fatu ansha aiki, tana shiga daki tace bari ta dan miqe a gado kadan, bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba.

Jameel sun dawo cikin dokin ganin gida, hajia tayi murnan ganinsu harda kwallanta, farouq murna kamar ranar ne sallah. Bayan an gama gaishe gaishe aka nufi dinning cin abinci, amaryan jameel, lubna mai dauke da qaramin ciki tafi kowa kwasan girki, sai santi take zubawa, mahmud da yake qanin mijinta yana ta tsokananta kota kulashi, mummy dai dadi ya hanata magana. Can hajia tace "mahmud kai kuma maimakon kana gama karatunka kayo gida shine ka biya can south africa ko, wato ko missin din gida baka yi?  Riqe hannunta yayi yace "wlh mummy jameel ne ya dameni wai in biya can tunda suma sun kusa dawowa wa, mummy 3 wiks kawai nayi a can din fa" ya qarasa maganarsa cikin shagwaba, daria sukayi lubna tace "ji shi kamar wani yaro" "yaro nake tunda ban kusa ajiye baby ba" mahmud ya bata amsan da ya saka ta kunya, don haka tayi shiru. Murmushi Jameel yace "mummy nafi son mu dawo rana daya ne thats why nace ya biya can, nd he enjoyed staying there" hajia tace "Alhamdulillah tunda kun dawo lafiya all, sai shirye shirye walima da party na taya murna, in da next 1 week" murmushin jindadi mahmud yayi yace "thanks mum, Allah ya biyaku dawainiyan da kukeyi akan mu" dukansu suka amsa da Ameen.

Bayan kammala cin abinci kowa ya nufi part dinshi, jameel ya dauki matarsa suka tafi gidansu da yake basu da nisa da gidan iyayen nashi.

[3:19PM, 7/11/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣3⃣


Fatu bata farka ba sai bayan la'asar, kallon agogo tayi ta saka salati ta shige bathroom. Wanka tayo da alwala ta bada farali kana tasa kaya hade da light make up. Palour ta fito taji shiru tace ba dai har sun kammala ba. Kitchen ta shiga ta samu dija na aikin girkin dare ta tsaya tambayanta hajia dasu jameel, dija tace "ai tun dazu su lubna suka tafi, mahmud kuma inaga ya shiga cikin gari. Fatu tace "mmn isya yanda kika san an mini duka haka nake jin jikina dazu, ina shiga daki kawai na kwanta in huta ashe bacci ya kwashe ni" Dija tace "kinyi kokari ai" fita daga kitchen din tayi dakin hajia, sai da ta knockin tayi sallama aka amsa ta shiga. Hajia ta samu zaune a bakin gado tana waya da aunty sadiya (maman sultan). Kujera na dressin mirrow taja ta zauna Sai da hajia tayi hangin fatu tace "mummy ya gajiyan yau? Hajia tayi mrmshi tace "ai ke za'a cewa ya gajiyan yau, kikayi ta bacci abunki" daria fatu tayi tace "Allah mummy nima bansan tym din da bacci ya debe ni ba, kuma farouq ma ko yazo ya tasheni" mummy tace "ni nace ya barki ki huta. Ki dauki wancan jakan ki kaiwa hajia sadia tsaraban su ne, naki kuma sai kin dawo ki gani" fatu tace "tooo" daukan jakan tayi ta fito, room dinta ta shiga ta dauko hijabi iya gwuiwa tasa ta fito. 

A palour ta tarar da qanwarsa Amrah tana danne danne a waya, zata kai 13 yrs, "anty fateema oyoyo" amrah tace da fatu yayinda take zuwa gurinta ta karbi ledan hannunta suka zauna, fatu tace "washhh, Ina mammi" amrah tace "tana dakinta, bari in kirata" bata jima da shiga ba suka fito tare, hajia sadia na cewa "amrah bi kitchen ki daukowa fateema ruwa" zama tayi akan kujera fuskarta dauke da murmushi tace "sannunki da zuwa fateeman mummy" murmushin fatu ma takeyi amma fuskarta a qasa, ta zamo daga kan kujeran ta gaisheta kana ta koma ta zauna. "Mummy ne tace in kawo muku tsarabanku" ta fada yayin da take miqawa hajia ledan. Amrah ta kawo wa fatu ruwa ta tsiyaya mata ta koma kusa da hajia sadia ta zauna tana cewa "mammi ina nawa" hajia sadia tace "gashi nan, kinga na kowa Anyi wrapping dinshi da suna" ta karba tace "anty fateema kice nagode sosai" fatu tace "to amrah" amrah ta wuce dakinta don ganin tsarabanta. Fatu ta miqe tace "mammi sai anjima" hajia sadia tace "daga zuwa? Ko ruwa baki sha ba" fatu tace "mammi na sha" sultan ne ya shigo a dai dai inda hajia sadia ke cewa "ki gaishe min da mummyn naki" sultan yace "muje in raka ki" saurin dago da kanta tayi ganin ita yake kallo yasa ta fara tafiya tana cewa "to mammi" hajia sadia kuma ta koma ciki tana jindadi, don tun ba yau ba take son sultan da fateema, don yarinyar ta mata, ga nitsuwa da hankali, har cikin ranta take son fatu. A bakin gate ya cim mata, wani sauri takeyi bata son wani abu ya hada su, gudun kar ta kopsa ya ganeta. Sultan yace "madam ba haka tafiyanki yake ba" dolenta ta fara tafiya yanda ta saba, hakan ya bashi daman jerawa da ita. "Ina wuni" fatu tace dashi, yace "lafiya kalau fateey, kina lafiya" a gajarce tace "lafiya" dai dai nan suka iso bakin gate ta shige abunta, shi kuma ya juya ya fara tafiya, tana shiga taga bai biyota ba, sai taga sam bata kyauta ba, ko godia babu, leqawa tayi tace "hey" ya juyo ta sakar masa murmushin da ya saka shi jin sansanyar iska na bin jinin jikinshi. Yace "yess" tace "thanks" bata jira amsar sa ba ta shige. Samun kansa yayi da tsayawa a gurin yana doka uban murmushi da yasa hakoransa shan iska yana kallon kofar, yafi 5mins a gurin wucewar wata mota ce ta sa shi dawowa hayyacinsa ya koma gidansu. Ita kuma tana shiga a farfajiyan gidan ta hadu da mahmud zaune a irin kujerun shan iska nan yana karanta newspaper tazo ta gurinshi tace "sannu da hutawa" ya sauqe jaridan yace "yauwa" tayi wucewarta. A ranshi yace wacece wannan? May be dangin su sultan ce don tana kama dasu, amma dai ta hadu ba laifi, tashi yayi ya shiga cikin gidan shima, mummy ne ta fara ganinshi tace "mahmud har ka dawo? Yace "ehh" ya nemi guri ya zauna. Fatu tace "mummy shine ya mahmud? Mummy tace "shine" fatu ta gaishe shi ta masa sannu da dawowa ya amsa. Tace "na hadu dashi a waje ban zata shi bane ai" mummy tace "ayya, kina bacci suka dawo shiyasa" mahmud yace "mummy banganeta ba" mummy tace "yar uwarku ce daga bauchi tazo karatu ne" tana fadan haka ta tashi ta shige kitchen. Kallon fatu yayi yace "a gidan wa kike a bauchin, don ban taba ganinki ba duk zuwa na" shiru tayi ta rasa me zata ce can ta qakalo murmushi ta ce "ko na fada ma baza ka gane ba" zai qara magana mummy ta fito da basket a hannun ta tace "fateema ko zaki kai abincin gidan jameel? Ta nan sai ki musu sannu da dawowa" da dokin ta tace "ai kuwa mummy" "amma ki jira yanzu farouq zai dawo daga islamiyya sai ku tafi tare driver ya kai ku" yamma liss farouq ya dawo driver ya kaisu gidan jameel da amarya lubna.


Afuwan fans, sai yau Allah yayi na turo FATU A BIRNI. Ba jan ranku nayi ba, lokaci ne ban samu ba. Barka Da Sallah. Allah ya maimaita mana. Ameen


Taku a[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣7⃣


Wankanta ta tsala ta fito ta shafa mai da dan pop powder dinta na 100, sai kwallinta data sawa idonta, ta lakuti vaseline ta shafawa lips dinta. Doguwar rigan da hajia ta bata ta saka black ne mai adon sky blue a gaban rigan, kana ta dauki gyalensa shima sky blue ta yane kanta Wahoho jama'a sai yau na qarewa fatu kallo. Fara ce amma ba tass ba, tana da matsakaicin tsayi, figure 8 ce don rigan anyi shaping dinta, idanunta ba manya bane kuma ba kanana ba, tana da dogon hanci ba laifi, bakinta dan tsurut kamar bakin bottle, tana da gashin gira dai dai, fuskarta mai yawan murmushi. Itama kallon kanta ta tsaya yi a jikin mirrow tana smilling, sannan ta nufi kofa ta fita. Tun daga kan steps hajia ta ganta a ranta tace "masha Allah" don sultan yayi sa'ar mata, ga kyau ga ilimi both arabi da boko ga nutsuwa ga kuma ladabi da biyayya. Fatu ta iso ta dan duqa tace "mummy sannu da aiki" har ranta hajia taji dadin yanda fatu ta saki jikinta tana kiranta da mummy. Dinning suka nufa fatu tayi serving dinsu indomie da dankali da kwai sai tea. Suna ci suna hira duk akan yanda skul din fatu zai kasance. Bayan sun gama ne hajia tace zata yi bacci kadan kana ta haura sama. Fatu ta tattare gurin ta kai kitchen ta samu dija na wanke wanke,;ta tayata suka qarisa cikin tadi da raha, suka gyara kitchen din. Anan ne dija take tambayar fatu dangantakarta da hajia fatu tace "zan fada miki amma ba yanzu ba" dija tayi daria tace "to Allah ya kaimu ranar" fatu tace ameen ta haura sama itama ko zata runtsa.


Taku a kullum


Maman Fa'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣0⃣


Tafiya take yi a hankali zuwa gurinsa don ita duk a tunaninta ya ganeta, tazo dab dashi ya aika mata da murmushi yace "sannu yan mata" tsayawa tayi cakk, a ranta tace ashe bai ganeta ba, don haka ta fuske tace "sannunka" kana ta cigaba da tafiyanta zuwa gurin mal usman. Ta gaishe shi tace "mummy tace tana son ganinka kafin ka tafi" yace "to" kana yayi qasa da muryansa yace "fatu yallabai ya ganeki kuwa? (Mal usman gulma😂) shiru tayi tana kallon gefe, sannan tace "ka manta abunda hajia tace ne? Duqawa yayi kamar me neman gafara yace cikin karamin murya "ahh yi hakuri, wallahi mantawa nayi fateema, bakin nawa ne ba sakata" murmushi tayi tace "ba komai" wuce wa tazo ta sake yi ta gaban sultan wanda tun tafiyanta gurin mal usman ya tsaya ya zuba musu ido, sai dai bai san me suke cewa ba. Tana shiga palour ta isar wa hajia saqonta tayi saurin haurawa sama, hakan yayi dai dai da shigowan sultan ya zuba ma bayanta ido, sai yake ganin duk duniya babu wanda hawan step ya masa kyau irin wannan babe din. Sai da ta shige ya juyo da kallonsa palourn ganin idon👀 mummy qurrr a kansa yasa yaji kunya. Daya daga cikin kujeran ya samu ya zauna yace "sannu mummy" tace "kaima sannunka" dariya yayi don duk a tsarge yake kamashi da mummy tayi yana kalla mata baquwa. Suka gaisa, mummy ke jajensa tace "wato don jameel baya nan shine ko kafanka ba'a gani ko" murmushi yayi yana sosa qeya yace "wallahi mummy ban zauna bane, last wik ma dawowana daga china, kuma nazo farouq yace kina bacci" hajia tace "ba komai in abokin naka ya dawo ai zamu na ganinka, Kaga shikam yayi iyali, kai kuma naga alama so kake azumin nan a fara kada maka gangan tuzuru" daria yayi sosai yace "mummy ki shirya bayan sallah zakuyi bikina, na samu mata sai dai bamu daidaita ba" Mummy ta kallesa tace "a ina" sultan yace "kin santa ma mummy, ki tayani addu'a kawai" da jin haka mummy ta gane fateeman ta yake nufi, sai ta fuske tace "nidai ban gane wacece ba, Allah ya baka sa'a" ganin bai samu fuska ba yasa ya maida kallonshi kan tv, yafi kusan 30 mins xaune da hajia suna hira sai dai ko kadan bata kawo masa tadin baquwarta ba, fatu kuwa qin fitowa tayi. Ya gaji da jiran fitowan ta yayiwa hajia sallama ya fita.


Taku a kullum


Maman Fa'iz👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣8⃣


Shigan fatu daki ta kwanta a gado tana tunanin rayuwarta, ita kanta mamakin yanda ta sake a gidan takeyi, amma da ta tuna da yanda hajia ta karramata sai take ganin ko me hajia tace tayi zatayi in dai bai kauce shari'a ba.  Duba agogo tayi 8:34, kakanta ne ya fado mata a rai, yanzu haka yana can yana kewanta, Allah sarki, hawaye ne ya fara sintiri a beautifull face dinta idonta a rufe, a haka har bacci ya dauketa.

11:00 ta farka, bandaki ta shiga ta kama ruwa sannan ta sauqo palour, babu kowa sai kamshin girki da yake tashi a kitchen, ta shiga kitchen din ta samu dija tana girka abincin rana, fatu ta mata sannu da aiki ta kama sunayi tare. Fatu tace "maman isya (dija) mummy bata fito bane? Dija tace "ta fito dazu ta fadi abinda za'a girka" Fried rice wanda yaji hanta da kayan lambu sukayi sai coslow, fatu tace "akwai zobo ne?" Dija ta kawo mata, tace "mman isya a ina zan samu bawon abarba? Dija tace "sai dai a aika habu driver ya karbo, akwai masu sayar da fruits a bakin hanya" dija ta fita ta bawa habu driver aika, minti goma ya dawo da bawon abarba mai yawa, fatu ta karba ta daura akan wuta tasa ginger, kanunfari da zobon, suka ci gaba da hiransu suna gyara inda suka bata har zobon yayi, ta sauke dija ta tace shi a wani bokitin roba ya dan huce suka sa sugar sukayi blending cucumber suka saka. Dija ne ta fara tabawa tace "zuwaiiitt kenan, hajia zata ji dadin wannan zobo dama bata cika son na kwalin nan ba" fatu tayi murmushi itama ta taba tabbas yayi dadi don bata taba yi ba, time din da take secondary tayi food and nutrition to anan ta dan iya wasu girke girken sai dai ba kowanne ta gwada saboda yanayin gidansu. Freezer suka kai don yayi sanyi da wuri, barin dija tayi a kitchen Din ta fito palour, hakan yayi dai dai da shigowan farouq 12:40 da sauri ta rungumeshi tana masa oyoyo, peck ya mata a kumatu tayi murmushi itama ta masa duk suka sa daria, wa yaga FATU A BIRNI har an fara wayewa😜. Duk abunda sukeyi hajia na kallonsu tana jindadin shakuwarsu na kwana 1. Da gudu yaje gurin hajia itama ya mata peck ta masa oyoyo.

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣7⃣


Jameel yace "I am sorry to say bazan iya raka ka ba, I cnt face da dattijo" yana gama fadan haka ya fice daga palourn, sultan ya bi bayansa amma yana fita jameel already yaja motarsa ya bar gidan, shima ya fita.

Lubna dake kitchen ta fito jiki a sanyaye da alama taji duk hiransu, jameel ya bata labarin fatu tun ba yau ba, haka kawai itama take kaunar sultan da fatu, ko ba komai 'yar uwarsa ce, marainiya mai neman taimako, kuma a yanda taji jameel ya fada fatun tayi karatu har zuwa secondary, so why not ya maida ta skul in educated wife din yake so, tunani barkatai lubna tayi akan fatu, tana tausayawa yarinyar. Tashi tayi ta shige dakin jameel ta bude drawer da yake ajiye pictures, da kyar ta samo pic din sultan da matarsa fatu. *WHAT*? naji ta furta da karfi hade da miqewa tsaye harta manta cikin 6months da yake jikinta.


Fatu na isa gida tayiwa mummy kunun aya tasa mata a fridge, fitowanta daga kitchen din yayi dai dai da shigowan mummy gidan, fatu tace "sannu da dawowa mummy" tace "yauwa fateema" fatu tace "farouq daya dawo daga skul yace zai biki gidan mammi, yaje ne" hajia tace "dan rigima yaje, ynxuma na barsu zasu je unguwa da amrah ne" fatu tace "ayya, nima inason zuwa gidan anty lubna anjima" mummy tace "Allah ya kaimu" fatu tace "Ameen, na gama kunun ayan, yana fridge" da murmushi a fuskar hajia tace "nagode 'yata Allah ya miki albarka" "Ameen mummy" fatu tace ta bar mummy a palour ta shige dakinta don tadan huta zuwa yamma, ko meyasa sultan yake nemanta oho. Wayarta ta dauka don tayi chattin amma sai taga missed calls din lubna 4, da sauri ta kirata don ita ta dauka ma ba lafiya ne. Ringing daya biyu ta dauka tace "Hello fateema kina gidana ne? Tace "ina gida, naga missed calls dinki ne, lafiya kam? Lubna tace "sai alkhairi, don Allah ina son ganinki yanzu yanzu" fatu tace "ai anjima ina zuwa da yamma" lubna tace "a'a its urgent pls ko minti biyar karki qara" fatu tace "to pls bari inyi wanka" "ohhh fateema kiyi hakuri ki dauko kayan da zakisa in kinzo kiyi anan" fatu tace "to gani nan zuwa" kashe wayan tayi zuciyarta na dukan uku uku. Anya ba ganeta sultan da jameel sukayi ba? Saisaita kanta tayi ta dauki abubuwan da take bukata taje dakin mummy tace "mummy bari inje yanxu anty lubna ta kirani" mummy tace "to shykenan Allah ya kiyaye hanya, ki dauka mata kunun ayan nan naga itama tana so" murmushi fatu tayi tace "to mummy" bayan ta dauka ne ta fita mal habu ya drivin dinta sai gidan jameel.


Maman Fateey👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣6⃣


Yau kimanin wata biu da sati biu kenan da haduwan sultan da fatu a a gidan jameel, shakuwa mai tsanani ya shiga tsakaninsu, wanda yawanci in sultan na qasar shi yake kaita school, waya kuma kowanne dare sai sunyi b4 bacci, no love jst qanwa da yaya. Chattin babu wanda fatu batayi da taimakon qawarta xahra levels. fatu har sunyi exams na second semester suna hutu. Yau saturday sunyi da levels zasu je saloon, Karfe 11 na safe tana gidansu levels daga nan suka rankaya gurin saloon din da yake ba nisa tsakaninsu.


A gidan jameel naga sultan da abokin nashi a palour suna magana, jameel yace "its time ka furtawa fateema cewa kana sonta, don kun saba wanda nasan lokacin da kuka dauka kuna tare itama ta fara sonka" sosa kai sultan yayi yace "kana ganin ta fara sona? "Kwarai insha Allah" Jameel ya bashi amsa. Sunkuyar da kai sultan yayi kana ya dago yana kallon gefe. Muryan jameel yaji yace "FATU FA?? Da sauri sultan ya juyo da kanshi gurin jameel zuciyarsa na dukan uku uku, don shi ya manta ma da wata fatu, yau kimanin wata uku kenan ko aika da yake mata ya daina, fateema ta mantar dashi cewa yana da mata ajiyayya. Jameel ya qura masa ido yana jiran yaji mai zai ce, shi dai fatu ta masa tun ranan har yanxu kuma yana tausaya mata a matsayinta na marainiya abar tausayi, "baka yi magana ba" jameel yace dashi, sultan da har yanzu bai gama saita kanshi ba yace "ni fateema nake so, bani da ra'ayin zama da mata biu kuma. Inaga its time itama da zan furta mata abunda ya dace da ita" jameel zaiyi magana sultan yace "jameel u knw yanda aka hada auren, sam babu yarda ta. I cnt live with her" Shiru jameel yayi, sultan sai da ji hankalinshi ya dawo jikinshi ya dauki wayarsa yayi dialing numbern fatu.

Bayan an gama musu suka rankayo gida. Fatu ne da xahra ke hira kan sultan levels na cewa "wallahi qawa har yanzu ina mamakin wai sultan mijinki ne amma kuma bai ganeki ba, kuma wai he's in love with new fateema" murmushin daya fi kuka ciwo fatu tayi tace "labarin rayuwata kamar a movie, bansan nan gaba ya zaya kasance ba, zan rabu dashi ne ko zamu kasance a inuwa daya a matsayin mata da miji, levels ki tayani addu'a kawai. Allah ne kadai abun dogaro na" siririn hawaye ta goge hakan yayi dai dai da ringing din da wayarta ya fara "dan halal, yaqi ambato" cewar fatu yayin da murmushi ya bayyana a fuskarta, xahra ta bita da kallon tausayi. "Assalam alaika yayan fateey" "wa'alaiku mussalam qanwata, ya kike? Tace "lafiya lau, ya aiki? Yace "da godia, jiya kince zaki je saloon kinje ne? Tace "ehh, yanzu muka dawo ina gidansu levels ne" Yace "ok, in baza ki damuba anjima da yamma inason ganinki" tace "ok yayana, zaka zo gidane? Yace "noo, mu hadu a gidan jameel" sukayi sallama sukayi hanging. Fatu ta kalli levels tace "I gotta go, zanyi wa mummy kunun aya nd sultan yana son ganina" levels kada kai tayi kawai ta rakata haraban gidansu tasa drivernsu ya maida fatu gida.

Sultan na ajiye waya yace "jameel insha Allah nan da 1 week zamu je Garin Modibbo gurin FATU"


Maman Fateey👯👯

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣5⃣


Tun shiganta motan kamshin jikinsu ya gauraya ya bada wani ni'imantaccen scent mai kwantar da hankali, ga a'c ya sanyaya ko ina. Ba sultan kadai ba har fatu taso inama suyi ta zama haka har abada *what? Fatu ar u in love?* tsohuwar cool music na celin dion mai taken _TITANIC_ ya saka musu (in d nyt in my dreams I see u, I feel u....) yana bi a hankali, fatu da ta gama narkewa ta juya kanta gurin window tana jin kalaman waqar har cikin zuciyarta yana ratsa ta. Maimakon taga anyi hanyar gida sai ya biya wani guri, basu tsaya a ko"ina ba sai katafaren gurin sayar da phones. Ya juya zaiyiwa farouq magana yaga yayi bacci. Fatu ta juyo tace "baka ce zaka yi branching ba, srry mun takuraka" yace "no wahala, abu zan saya kuma gashi farouq yayi bacci banida dan rakiya, muje ki rakani" tace "no, in kai alone ne zaka fi sauri" Yace "noo, to ki biyani rakiyan dana miki dazu" yanda yyi maganar kamar yaro yasa fatu daria tace "muje to". Suka shiga tana binshi a baya,  yace "pls ki tayani zabe, amrah nake son sayawa waya" tasan dai amrah nada waya koda yake abunka da masu shi, tara wayoyi a hannu qaramin aikinsu ne. Iphone latest ta nuna tace "wannan yayi" Yace "irin nawa" tace "sai kuyi anko" yace "hakan za'ayi" Qaramin Nokia ya qara dauka ya biya kudinsu, anan ya qara sayan sim cards 2 dfffrnt layi suka fita. Har komawansu mota farouq na baccinsa, basu zame ko ina ba sai *eman* ya saya musu ice cream da snacks, daga nan suka yoo gida wajen tara saura. Har cikin gidan ya shiga yayi parking suka fito daga motan, fatu na qoqarin daukan farouq yace "lemme help" ba musu ta matsa masa ya dauke sa suka shige gidan, a palour ya kwantar dashi mummy kuma da alama tana dakinta, Fatu tace "thanks" yace kinyi mantuwa a mota, tace "ni? Ok tsaraban da anty lubna ta bani" fita sukayi ya bude motar ya dauko ledojin da sukayi shoppin ya miqa mata, tace "wannan ne nawa" ta karba yace "dan tsaya pls" tayi juyi irin ta gajin nan, yace "srry" bude ledan wayoyin yayi ya saka musu layi duk tana tsaye ya kunna ya miqa mata, yace "bari in gwada kira" ita duk bata dauka wani abu ba ta karba, wayarshi ya ciro sak irin na hannunta ya kira sai ga numbern shi ya bayyana a screen din, miqa mishi tayi tace "yayi" yace "kip it, naki ne" cikin zaro ido tace "what? Noo kayi hakuri.... kafin ta qara magana ya rufe motarsa yayi reverse tana tsaye har aka wangale masa gate ya fita, ta jima kana ta koma gida jiki a sanyaye, a palour ta tarar har mummy ta shigar da farouq dakinsa, tana sauqowa qasa, fatu tace "mummy mun dawo" hajia tace "sai yanzu kenan? Jameel din ne yadawo daku? Fatu tace "a'a amm.... yayan amrah ne" sarai hajia tasan sultan ne ya dawo dasu don tana ganin shigowarsu duka, tace "bari in duba kullin masan nan, gobe da safe dadynku zai sauqo yace shi yake sha'awa" har hajia ta dubo ta fito fatu na tsaye a gun, hajia tace "auu baki haura bane? Kaman zatayi kuka tace "mummy wayoyi ya bani fa" da fara'a hajia tace "a ina" fatu ta labarta mata komai, hajia taga wayoyin tace "amma sunyi kyau Allah ya amfana" fatu da mamaki ya gama lullubeta tace "mummy gobe zan mayar masa dai ko? bata fuska hajia tayi tace "maganar gaskia fateema ki nemi soyayyar mijinki, abunda zan iya fada miki kenan, kibi komai a hankali da nutsuwa" har zata juya fatu tace "mummy ga tsaraba anty lubna ta bani" mummy ta gani tayi Allah ya amfana tayi upstairs. Zama jugum fatu tayi tana aukin tunani, ita ta rasa a wani yanayi take, shin tana son mijinta ne ko bata sonshi? Kodai kawai son yan'uwantaka ne? Amma deep inside her heart tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba. Da taga tunani bazai fishhe ta ba tace "Allah ka shige min gaba" tashi tayi ta dauki roban ice cream daya da snack iya wanda zata ci sauran tasa a fridge, kashe wuta tayi ta kulle kofa tayi dakinta, bayan ta gama ci ne tayi wanka ta fito taga leda akan mirrow nata, murmushi tayi tace tsaraban mummy ne. Ta duba takalma ne yan ubansu guda uku kowanne da jakansa, na lubna kuma turaruka ne da cosmetics, adana su tayi ta kwanta. Qarar wayanta ne yasa ta tashi zaune a tsorice (sabon shiga😂🤓) a hankali tasa hannu ta dauka, number ta gani wanda tasan na sultan ne tace "hello" can gefe akace "hii" shiru ya biyo baya, can a gefe yace "sultan ne ya gajia? Tace "lafiya, nagode fa Allah ya saka" har cikin ranshi yaji dadin addu'anta yace "ameen, sai da safe, karki shanye ice cream din ki ragewa farouq nashi" daria dukansu sukayi kana sukayi hanging, daga ita har shi da murmushi a fuskarsu bacci ya dauke su. Hmm _lovebird[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣1⃣


Sultan na fita ya hadu da farouq ya dawo daga skul, tafawa sukayi yace "big boy, ka dawo? Ya skul" yace "lafiya kalau, yau muka yi games, mukayi gudu muna waqan soldiers" sultan yace "Ai ana ganinka anga sojaa, give me five" suka qara tafawa, kana sultan yace "amm sojaa, nikam wacece baquwar mummyn nan? Farouq yace "anty fateema ce, tazo karatu ne" da yake hajia ta gargade shi kan duk wanda ya tambayeshi fateema ya fadi haka nan. Yace "ok good boy, maza in ka shiga gida kace ina gaisheta" yace to. "Fateema" sunan ta mai dadi, murmushi yyi ya shafi face dinsa kana ya dan bugi kirjinsa saitin heart dinsa, (ko me hakan ke nufi oho😜) fita yayi daga gidan, a bakin gate ya hango mal ahmadu yazo karban mal usman guard tunda zaije aika. Suka gaisa ya wuce gidansu. 

Dawowan farouq yasa fatu sauqowa kasa ta masa oyoyo, yace "bro sultan yace yana gaisheki" kallon mummy tayi taga hankalinta na kan tv don haka tace "yaushe" yace "yanzu na hadu dashi a bakin gate, kin ganeshi? Shine wanda nake baki labarin ya kawo min tsaraba zuwansa china, muje in qara nuna miki tsaraban" fatu tace "awww yanzu na tuna, kaje kayi wanka kayi sallah sai muci abinci, akwai labarin da zan baka" ya tafi dakinsa. Mal usman ne ya shigo ya gaishe da hajia ya tsaya a bakin kofa, hajia tace "sultan ya baka aika ne? Yace "ehh" tace "ka bawa fateema ta dubamin, miqa ma fatu yayi ta bude kudi ne dai har yanzu, har zata rufe taga wata karamar paper da dauka ta miqa wa hajia. Hajia tace "a'a letter dinki ne" rufe envelope din tayi ta bawa mal usman yasa a aljihu. Hajia tace wa fatu shikenan kije dakinki. Ta wuce. Hajia tace "mal usman kamar yadda na fada maka fateema tana nan amma kakanta bai sani ba, haka sultan, inaso a dauka a gidansu sultan take, kakanta kan iya tambayarka fatu, kace masa tana lafiya, kuma a baka takardun karatun ta duka, sultan zai saka ta a makaranta" da saurinsa yace "hajia an gama" kudi ta bashi ya karba yana godia kana ya fita.

Fatu kuwa tana shiga dakinta ta fada kan gado tana tariyo yanda sultan ya mata murmushi, karo na biyu kenan da taga smillin dinshi. Ya qara mata kyau da kwarjini, dazu tayi matuqar yin qoqarin ganin bata kwapsa ba balle ya ganota. Papern tayi saurin budewa, ta fara karantawa


Hii


""Ki cewa mal Ameenu na gaishe shi, ki kuma bashi hakurin rashin ganina, may be bayan sallah zanzo""


Samun kanta tayi tana nanata wasiqar, duk da ba ita akayiwa ba amma taji dadin sa. Murmushi naga ya subuce a fuskarta can kuma ta fara hawaye, tana tausayin kanta, yanzu zata rabu da mijinta, duk da ba sonshi takeyi ba amma zata so ta zauna da dan'uwanta. Kuma taga yana mata murmushi. Wata zuciya tace fateema yake yiwa ba fatu ba. Kar ma kisa shi a ranki, a duk lokacin da ya gano kece fatu bazai qara kulaki ba. Wasu zafafan hawaye ne suka qara gangaro mata tayi saurin gogewa, farouq ne ya shigo dakinta wai ta sauko yin lunch, goge fuskarta tayi suka fita tare da yake tana fashin sallah. 


Acan garin modibbo kuwa mal usman ya kai saqo kamar kullum. Mal aminu ke tambayarsa? Ina uwargidan nawa, da fatan tana lafiya? Mal usman yace "tana lafiya kalau, tace a gaisheka ma. Kuma a bata takardun makarantar ta zata cigaba da karatu. Cikin jin dadi kaka ya dauko komai da komai ya bashi, da yake duk takardun nata a gurin kaka yake.

Bayan mal usman ya dawo ya bawa hajia, nan da nan tasa a nema wa fatu admission a GSU cikin qanqanin lokaci aka sama mata, aka gama komai ta fara zuwa lectures.



Anan zamu tsaya a FATU A BIRNI insha Allah bayan sallah zamu cigaba.

Kuyi hakuri na rashin post da wuri hakan ya samo asaline na rashin charge.

FATU NA MUKU HAPPY RAMADAN🍉🍏🍎🍐🍊🍉

Allah ya bamu ladan dake cikin wannan wata ta Ramadan. Ameeen

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [10:38PM, 7/22/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣0⃣


Fatu ta kalli lubna tace "he's on his way" jinjina kai lubna tayi ta fara magana "ki kula kiyi duk abunda ya dace, zan fita in nemo mijina nima" daria suka sanya dukansu, hijabi ta sanya ta fice a gidan a yar qaramar motarta, a waje ta hadu da sultan sukayi gaisuwan light ta harba titi shi kuma ya shige gidan maigadi ya rufe gate. 

Da sallamansa ya shigo falon fatu data bashi keya ta juyo a kasalance ta amsa sallaman, daskarewa yayi a gurin yayinda ita kuma take jefanshi da malalacin murmushi tace "ka shigo mana" samun kanshi yayi da bin umarninta, a 1sitter ya zauna yayinda ita kuma take 2sitter suna fuskantar juna, bai taba ganinta haka ba gyale ko hijab ba sai yau,  manyan idanunshi sexy ya zuba mata kamar yau ya taba kallonta, kunya ce ta rufe ta ta dago ido tace "kai yayana wannan kallon" bai sani ba bakinshi ya furta "u luk gorgeous" "tnx" ta furta mishi. Tashi tayi tace "mutanen gidan basa nan bari in dauko maka ruwa" a hankali take tafiya wanda ya bawa sultan daman kare ma bayanta kallo, tana shigewa kitchen ya jijjiga kanshi yace "control sultan, control" saisaita kanshi yayi ya gyara zama yana tunanin ta ina zai fara mata magana, bai gama shawara ba ta fito da tire a hannunta ruwa ne da cups sai juice, nan dinma kura mata ido yayi har ta iso ta jawo centre table kusa dashi ta ajiye kana ta sunkuyo yanda dole ya shaqi kamshin jikinta, tace "wanne za'a zuba maka? Sultan da ya lula shaqar kamshinta ya kuma shagala da kallon kirjinta yace "na'am" sarai tasan abunda yake kallo amma ta nuna bata ganeba cikin ranta kuma tace ka kalla halalinka ne. Miqewa tayi tsaye ta qara maimaita masa tambayar da sauri yace "juice" don yasan dole ta tsaya shaking dinsa kafin ta zuba masa hakan kuma na nufin shaking din abunda yake son kallo Murmushi tayi ta dauki juice din ta shaking dinsa daga tsaye ta sunkuya tana saka masa a cup, tana gama sawa ta koma gurin zamanta shi kuma ji yayi inama tayita tsiyaya masa har gobe, kodai yace ta saka mishi ruwa ne? "Control sultan" ya fada a sanyaye ya dauki kofin yasha kadan ya ajiye. "As u said kana son ganina" fatu tace dashi yayinda take harde  kafuwanta, yace "ehh" tace "gani to".


Maman Fateey👯👯

[10:38PM, 7/22/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣1⃣


Sunanta ya kira "Fateema" tsikar jikinta ne ya tashi tace "na'am" yace "magana ce tafe dani very important" yayi shiru tace "ehen i'm ol ears" yace "fateey tun ranar da na fara ganinki nake jinki cikin raina _love at first sight_ da tunaninki nake kwana dashi nake tashi, nayi amfani da lokacin da muka dauka tare don mu shaqu nd to knw more about each other" fatu da tun daya fara magana kanta na qasa naga murmushi ya subuce a fuskarta, "fateey" ya kira sunanta a hnkali, dago idanunta tayi suka sarqe cikin nashi "I'm really madly deeply in love with you fateema" Da sauri ta sauqe kwayar idonta yayinda wani siririn hawaye ya biyo kuncinta, na rasa gane na farinciki ne ko ko! Shiru tayi, zufa ne ya fara keto masa ba dai tana da wanda take so ba! "Fateema ko kinada wanda kike so ne? Ya fada cikin tashin hankali. Kada mishi kai tayi alamar a'a. "Bakya so na ne? Talk to me fateema, idan bakya sona zan iya jiran har lokacin da kikaji kin fara sona, shirunki kan iya sa jinina ya hau pls talk to me" ya qarasa maganar yana dafe kanshi da yaji yana barazanar tsagewa. Lura da yanayinsa yasa tace "Ina buqatar time nayi tunani" yace "zuwa yaushe? Tace "ko nan da 2 weeks" yaqe yyi 'wanda masu iya magana suka ce mugun kuka' yace "kiyi hakuri na baki 5 hours, zan kiraki anjima in d nyt" zatayi magana ya tari numfashinta yace "kiji tausayina please" ya langabar da kai kaman qaramin yaro dolenta yasa tace "to Allah ya kaimu" yace "Ameen matata" daria tayi tace "tun kafin inyi tunanin? Kana gaggawa" shima darian yayi ya mance ciwon kan daya fara damunshi dazu yace "I knw tunaninki zai kasance positively" daga nan suka bige da hira yana sako maganan soyayyarshi tana basarwa. Kiran sallan da aka fara ne yayi daidai da shigowan lubna da jameel sai darawa sukeyi, ganin fatu ta sultan yasa sukayi kasaqe suna kallonsu, sultan tadi yayi tadi ya dawo 2sitter inda fatu take sai hiransu suke. Gyaran muryan jameel yasa suka farga yace "sannunku" fatu tayi saurin daukan gyalenta ta yane jikinta sultan kuma ya miqe yace "ai sai muje sallah ko, tunda kaji ana kira" bai kula darian da jameel ke mishi ba ya fita daga falon shima jameel ya bishi suka wuce masallaci yana tsokanarshi wai akan yarinya ya dawo parrot.

Suna fita lubna tace "mutumiyata ya akayi" labarin yanda akayi fatu ta bata duka. Kallon sama lubna tayi tana murmushi tace "sai nan da 4 days zamuyi move din mu na biyu" fatu tace "na fara tsoro anty lubna, anya bazai..... "noo insha Allah babu abunda zai faru sai alkhairi, mu hada da addu'a" Daga nan suka shiga daki sukayi sallah suka girka simple abinci mara nauyi, ana kiran isha sukayi sallah bayan sun idar ne su sultan suka dawo. Lubna tasa fatu ta qara gyara fuskarta sai dai wannan karon da gyalenta suka fito falo, abinci suka fara ci wanda fatu duk a takure take yayinda lubna, Jameel da sultan ko a jikinsu, suna qare cin abincin Jameel da lubna suka rako su bakin mota, inka gansu sai sun burge ka, a gaba ta zauna suka tafi.

Suna isowa gida tana kokarin budewa ya sa lock tayi tayi ta bude ta kasa, kallonshi tayi ya zuba mata sexy eyes dinshi yana murmushi,  anan ta gane shi yasa lock, da shagwaba tace "amma ka wahalar dani, Allah na dauka yaqi buduwa ne" kwaikwayanta yayi yace "ai ban gaji da kallonki bane" daria tayi tace "kai ko? Bude mata yayi yace "sai na kiraki, kar kiyi bacci" "ok" tace yayinda ta fita ta maida marfin motar, daga mishi hannu tayi alamar bye amma bawan Allah yaqi tafiya, har cikin zuciyarta take jinjina irin son da sultan ke yiwa fateema. "Allah ka barmin mijina" ta furta a hankali ta shige cikin gida, shima sai daya ga kulewarta yayi ajiyan zuciya yace "Allah ka taimakeni" kana ya wuce gid[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣4⃣

Gefen sultan kuma yana komawa gida ya wuce dakinsa ya kwanta yana tunanin fateema, wayarshi ce ta katse masa tunaninsa, ganin number jameel yasa shi miqewa tare da amsa wayar "ka shigo ne?........ ok bari in fito. A haraban gidan ya ga jameel bayan sun gaisa ne kai tsaye suka shige cikin palourn gidan, mammi ce kadai zaune tana rubutu a wani memo, sallaman da sukayi yasa ta cire tabarau idonta "lale marhabin da mutanen S Africa" zama sukayi, bayan sun gaisa da mammi ne suka fito haraban gidan, sultan yace "dude yau ma tazo gidan nan wallahi, har rakata bakin gidanku nayi" ya fada yana shafa sajensa daya kwanta luff a fuskar sa, jameel dai kallon mamaki yake binshi dashi, tunda suke sultan bai taba cewa yana son wata ba, shi har ya fara tunanin ko yana da matsala ne, mata sunsha warce kansu a gurinshi amma ko kallonsu baya yi, amma akan wata wai fateema ya gama rudewa. Koyaushe sukayi waya sai sultan yayi maganar ta, jameel yana so yaga  wacece fateeyn nan da take qoqarin zautar masa aboki. "Wai dama haka love din yake? Da ita nake bacci da ita nake tashi, jameel na rasa yadda zanyi" Jameel da ya tsaya kallonshi sai yanzu ya samu bakin magana "why not ka tunkareta? Ajiyar zuciya mai qarfi sultan ya sauke yace "I cant! Tana min kwarjini da yawa, to me zan ce mata ma? Kuma I asked farouq bata riqe waya nd tura wasiqa ka gane yayi yawa" Jameel yace "amma ka taba sanin tana da saurayi? Sultan yace "ko a skul bata kula kowa qawarta ma daya ce, a gida ma babu wanda yake zuwa mata, all I know shine ita TAWA CE! "Bravo alaika" jameel ya fada yana tafa masa, "ka iya yanda zakayi ka samu details akanta amma baka san yanda zakayi ka mata magana ba" sultan yace "kai dai ka taimakeni" "yanzu dai muje gidana ma qarasa maganar acan" shiga cars dinsu sukayi suka fita.

Gidan jameel ya hadu shima ba laifi, dai dai zaman mace daya. Driver na ajiyesu farouq ya fito da gudu ya shige cikin gidan, fatu ma ta fito tacewa mal habu ya jirasu yanzu zasu fito. Tana shiga motocin su jameel suka shigo. Bayan sun fito ne jameel yake tambayan mal habu ko aika ne ya kawo, yace masa ya kawo farouq da fateema ne, sultan dake gefe yayiwa jameel ido, jameel yace "ok kaje zan dawo dasu anjima" ba musu habu ya tafi. Su kuma suka tsaya anan suka cigaba da maganansu. Farouq a daki ya tarar da lubna tana gyara cikin wardrobe dinta, tace "farouq yaushe kazo" yace "yanzun nan, ni da anty fateema ne" tace waye kuma anty fateema" yayinda ta riqo hannunshi suka fito palour inda fatu tayi wa kanta masauqi a daya daga cikin kujerun da suka qawata palour.

Sannu da zuwa lubna tayi wa fatu tace bari in dauko miki ruwa, fatu tace "a'a nagode, ban jima da sha ba" suka gaisa anan lubna tace "sai dai ban ganeki ba" farouq yace "nace miki sunanta anty fateema kuma tazo karatu ne gurin mummy" daria sukayi lubna tace "to uban yan surutu, kai na tambaya? Bai kulata ba don ya danno tashan cartoon. Maida hankalinta tayi kan fatu tace "ke yar uwarsu ce kenan, kamar na taba ganinki, daga bauchi kike ko? Fatu tace "ehh, mummy tace a kawo muku abinci, kun dawo lafiya? "Lafiya kalau" lubna ta bata amsa. Fatu ta kalli farouq tace "my sojaa lets go" ba musu ya miqe yace "bye anty lubna, kuma sai na fadawa mummy kince nine uban yan surutu" zaro ido lubna tayi tace "kaji dashi" fita yayi zuwa inda sukayi parking amma wayam ba mota, sai motoci biu da ya gani, zai juya ya koma ya hango sultan da jameel da bayan cars din. Gurinsu ya nufa dai dai nan su fatu suka fito suma. Fatu tana ganin ba motan su tace "ba dai mal habu tafiya yayi ya barmu ba? Sai dana ce ya jiramu fa" ta karisa maganan kamar zatayi kuka. "DJ" lubna ta kwalawa jameel kira suka taho dukansu sultan n Nna cewa "oyoyo uwargida, don yanzu kin tsufa wata sabuwa zamu kawo" lubna ta harareshi na wasa tace "hurul ain kenan? Suna can suna jiransa insha Allah" gaisawa sukayi tsakaninsu fatu na gefe riqe da hannun farouq tana wasa dashi, can tace "ya jameel sannu da dawowa" yace "yauwa, fateema ko? Tace "ehh" gaisawa sukayi tace sai anjiman ku. Da sauri sultan yace "ina zaki je" bata kalle shi ba taja hannun farouq tace "gida" jameel yace "ni nacewa mal habu ya tafi zan maida ku in munyi sallah" ba yanda ta iya dole ta koma, su kuma suka wuce masallaci da farouq. Lubna taja fatu dakinta sukayi sallah, sai tadi sukeyi kamar sun jima da sanin juna, anan ta tayata qarisa gyaran wardrobe din, suka share dakin duk da kafin su dawo an share da gyara ko ina na gidan. Su sultan basu dawo ba sai bayan sunyi sallah isha. A palour suka tarar da su lubna da fatu suna ta tadinsu, sallama sukayi suka shigo, Lubna tace "ba dai har anyi sallah isha ba? Jameel ya zauna kusa da ita yace "ina zaki sani tunda kin samu abokiar hira" lubna ne ta canja tasha zuwa cartoon wa farouq tace  "fateema ki shiga daki kiyi sallah, bari inyi serving dinsu abinci" shigan fatu keda wuya suma suka wuce kan dinning jameel yace "mutumina ka tafi da yawa fa, irin wannan kallon haka" cike da tsokana ya karasa maganar. Lubna tace "ba dai fateema yake kallo ba? Sultan yace "dadina dake yawan tambaya, ni kawai ki tayani campaign" Jameel yace "ni dai kaman na taba ganinta a bauchi, amma inaga mahmud zai fi saninta don ya fini shiga ziyara, ko hutu yazo sai yaje bauchi ya zaga dangi" nan dai sukayi ta tattaunawa har suka samu solution, fitowan fatu yasa sukayi shiru, ganin haka ta gane maganarta sukeyi kawai ta wayance ta zauna kusa da farouq. Bata dade da zama ba suka kammala jameel yace "muje ko fateey" sun fito haraban gidan jameel yace "ohh ashee ba mai da yawa a mota na, pls sultan ka sauqesu mana" sai da yayi dan jimm kana yace "ok" jameel ya tura farouq baya, lubna kuma ta budewa fatu gaba tace "ki zauna a gaba ke" ba musu ta shiga, lubna ta miqo mata leda tace "ga tsaraba ba yawa" godia fatu tayi sultan yaja su suka tafi.


Taku a [truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [4:05PM, 7/26/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣2⃣


Fatu na shiga gida ta samu farouq na kallo ya mata oyoyo tace "har yanzu bakayi bacci ba? Yace "yau saturday,  remember? Ba skul gobe" tace "yess hakane, ina mummy? Yace "tana falon daddy" tace "ok, bari in shiga in watsa ruwa".

Wanka tayi ta sa sleeping dress ta dora hijab kana ta fito palour, ganin mahmud a zaune kusa da farouq wanda har yayi bacci yasa kirjinta dukan uku uku! Tun dawowan shi yake tsare ta da tambayoyi yana so yasan daga cikin wani gida take a familyn nasu, answers da take bashi basa gamsar dashi kuma akwai alamun rashin gaskia a tattare a ita, _real lawyer_ 😄. Rufin asirinta daya shine after walima na gama karatunshi ya fara aiki a abuja, ba kowanne weekend yake dawowa ba, duk randa ya dawo kuma bata bari su zauna su kadai, in kuma suka zauna zai fara tambayoyi, in mummy na kusa sai tace "mamuda nan fa ba kotu bane da zaka dame yarinya da questions, distant relative ce baza ka ganeta ba" To yau kam qaryanta ya qare tunda ba mummy mai rufe bakinsa. Murmushi ta qaqalo tace "ahh mutan abuja sauqar yaushe" murmushin shima yayi yace "dazu da yamma, kina fita na shigo, naje gidan jameel din ma na samu kuna maganarku ke da matarsa, so bana son katse muku sai na tsaya, da naji bamai qarewa bane yasa na tafi" cikinta ne ya bada sautin qulululu... kirjinta na bugawa da sauri da sauri tace "m..me..me.. kaji? Murmushin cin nasara yayi ya qara narkewa a cikin kujeran yace "abunda kuka gama magana akai" Shiru tayi fuskarta na qasa tace "can u kip a secret?" bai motsa daga kwanciyar ba yace "yess, amma ina son details" briefly ta fada masa abunda ya dace, ta qarisa maganar da cewa "promise me babu wanda zaka fada wa" daria yayi yace "ni banida gulma, bincike na iya" daria sukayi dukansu hkan yayi daidai da shigowan mummy tana cewa "oya farouq kallon ya isa haka kaje ka kwanta" ganin su fatu yasa ta yin shiru Tace "fateema kin dawo? Fatu tace "eeh mummy, anty lubna tace a gaisheki kuma tana godia da kunun aya" da murmushi a fuskar hajia tace "madallah, mahmud dauki farouq ka kaishi dakinsa" Mahmud na haurawa tace "fateema akwai matsala ne? Naga mahmuda yana damunki da tambayoyi" murmushi fatu tayi tace "babu komai mummy, munyi magana dashi" hakan yayi daidai da dawowan mahmud mummy tace "to asuba ta gari, fateema ki locking kofa ki kashe wuta, na tafi" suka mata sai da safe ta wuce side din daddy.

5mins ya qara shima ya mata sai da safe, kopa ta kulle ta kashe wuta ta wuce dakinta. Tana hawa gado ta lalubo wayarta ta kira xahra "badai kinyi bacci ba? Fatu tace da ita xahra wacce da alama tayi nisa da baccinta tace "8:30 ma ina kan gado" fatu tace "ok dama labari zan baki amma tunda kin fara bacci sai da safe" da sauri xahra ta miqe zaune harda kunne bedside lamp tace "bani in sha, wallahi na tashi" daria sosai fatu tayi tace "shegen son labari"


Maman Fateey👯👯

[9:37PM, 7/26/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣3⃣


Labarta mata yanda akayi duka tayi. Shiruu xahra tayi can tace "anya wannan plan din babu hatsari a ciki, kar garin neman gira a rasa ido fa" itama fatun shiru tayi xahra ce tace "are you there? "Yess" fatu ta bata amsa ta cigaba da cewa "insha Allah ba matsala, ki tayani da addu'a, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" "Ameen" xahra tace suka cigaba da tattaunawa daga baya sukayi hanging.

Missed calls din sultan ta gani kusan goma a screen din wayarta tace yaushe ya kirani? (Har yanzu dai sabin shiga ne) Wani kiran ne ya qara shigowa ta dauka tace "hello" bai amsa ba ya watso mata tambaya "da waye kike waya? Ina kiranki ana cewa call waiting" murmushi tayi kaman yana kusa da ita tace "levels ne fa, ka koma lafiya? Shima murmushin yayi yace "lafiya lau, ya maganar mu? Tace "wacce kenan? Shiru yayi kaman bazaiyi magana ba, a kalla babes sun kai goma shima yana musu irin tambayan nan cikin jin kai, amma reshe ya juye da mujiya yau shi ake yiwa! "Answer na dazu, u said zakiyi tunani" fatu tace "ok, na tuna" yace "ina jinki" shiru tayi yayinda shi kuma ya qagu yaji matsayinsa a gurinta, gani yakeyi in ya rasa fateema duk matar da ya aura baza ta samu soyayyar da yake yiwa fateema ba. Sunanta ya kira "fateey, kinyi shiru" sai da ta dauki 5seconds kana tace "yess, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" farinciki fal a fuskarsa yace "u mean kin amince? Tace "yeah". Hira suka yi cikin wayewa da natsuwa, sai da sukayi 30mins yace "ya kamata in barki haka kiyi bacci, amma ban gaji da jin sweet voice naki ba" qanqame wayar tayi a kunnenta tana lumshe ido ta qara qasa da murya tace "okay, gud nyt" yace "nyt dear, karki manta kiyi addu'an bacci" tace "ok tnx" sallama sukayi. Suna kashe wayan fatu ta tashi ta dauko pic dinsu tare da kudin sadakinta ta qura musu ido, kuka ne ya kwace mata tayi mai isarta har bacci ya dauketa. Sultan kuma yana ajiye wayan yace "saura fatu" murmushi yayi ya fara danne dannen laptop akan business dinshi. Yau kimanin 4days da fara soyayyarsu, in kaga yanda suke love sai ka aza sun shekara, wani zazzafan soyayya sultan yake nunawa fatu, yayinda itama take nuna masa bata da kowa like him. Haka da yamma zaizo ya dauketa suje yawon shaqatawa su sha hiransu ya dawo da ita, ga shopping niki niki. Wata rana kuma a gidan jameel zasu yi hiran, sai dare ya dawo da ita, nan ma sai an qara bata time kafin ta shiga gida. *love kenan* Mummy ta lura da hakan ta kira fatu tace "meke faruwa tsakaninki da sultan? Cikin jin kunya tace "wai mummy sona yakeyi" murmushi mummy tayi tace "kefa? Kina sonshi? Rufe fuska fatu tayi hakan yasa mummy ta gano answer dinta, "Alhamdulillah" mummy ta furta a hankali, tace "kin fada mishi matsayinki a gurinshi? Da sauri fatu tace "a'a mummy ba yanzu ba, kuma zan fada mishi da kaina in lokaci yayi" mummy taso ta gane wani abu amma ta basar a cewarta tunda suna son junansu shykenan. Ranar da suka cika 5 days suka hadu a gidan jameel. Hiransu sukeyi gwanin ban sha'awa, lubna ne ta fito da pics ta rarraba musu suna kallo, na daria suyi daria, na a bada labari a labarta, caraf a cikin pics din dake hannun fatu taga hotonsu itada sultan, turo baki tayi tace "honey wacece kusa da kai haka? Ta wani manne maka! Ta qarisa maganan tana miqawa lubna pic din, lubna na karba tace "laa fatu ce, uwargidan sultan" sultan da tunda fatu ta fara magana notinan kanshi ya sunce, ji yakeyi kaman ya rusa ihu, shikam fatu ta cuce shi, a 'yan kwanakin da yayi da fateema ya lura tana da kishi, yanzu in tasan fatu matarsa ce ya zaiyi. "Innalillahi" yayinda fatu ta miqe tsaye tana dafe kirji "lubna matarsa fa kika ce"..[truncated by WhatsApp]

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [9:45PM, 7/19/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣8⃣


Sultan na fita gidansu ya nufa, kai tsaye room dinsa ya nufa ya zauna akan daya daga cikin kujerun da suke room din. Shi gabadaya jin haushin fatu yakeyi, ta bata mishi plan din rayuwarsa, gashi akanta har sun sami matsala da abokinshi wanda tun suna yara rabon da hakan ya faru, shi fa bazai iya ba, never!! Zai saketa ya kawota gurin mammi ya kuma gargadeta tayi kipp da bakinta. Laifinshi ne ma daya qarfafa bincike wajen nemo innar tashi. Tunani ya fara shekara biyu da suka wuce yana tare da mammin shi a dakinta suna hira lokaci daya tayi shiru yace "mammi lafiya" tace "tunanin 'yar uwata nakeyi, ko ya take? A ina take? ita kadai ce 'yar uwata da muke uwa daya, sai kannena da muke uba daya, shekarana 6 a lokacin aurensu ya mutu, ba yanda ba'ayiba a maida auren abun ya faskara, a haka aka barsu amma kuma ana tare don rabuwansu bai raba zumuncin dake tsakanin babanta da babanshi wanda suke yan uwan juna ba. Ina shekara 7 muka je dukku anan wani da ake cewa mal sirajo ya ganta yace yana so, a lokacin yana da mata da 'yayansa 4, da kyar aka bashi aurenta don ma tace itama tana sonshi ne, saboda bakin cikin hakan dangin mu suka tattara suka bar garin a cewarsu ta zabi bare akan dan'uwanta, duk da shi din ma bafulatanin ne, amma wai su fulanin yawo ne. Na sha kuka dana rabu da ita, bamu wuce ko ina ba sai yola dama can ne asalin garin mu, anan muka zauna har babana ya fara shiga birni yana kasuwanci anan yaga yara na zuwa skul ya saka ni, har Allah ya buda masa sosai yayi aure, kamar yanda ka sani kannena biu, rufa'I da musa. Mahaifinka shima auren dangi aka hada ni dashi, a can na haifeku duka muka dawo nan gombe lokacin ina goyon amrah. Na tashi cikin dangi amma ina kewar mahaifiyata Muna dawowa gombe na je dukku ganin mahaifiyata amma aka ce ta rasu, kanwata kuma tayi aure, nayi nayi su fada min inda tayi auren amma suka ce sun manta, sultan ina kaunar naga wani tsatso daga mahaifiyata" kwallan daya taru a idonta ne ya saurin zubowa ta share. Tun daga wannan lokacin sultan ya qudura aniyar nemowa mahaifiyarsa 'yar uwarta, yaje sau daya shima suka fada masa haka, zuwansa na biyu shigan dare yayi da wasu soldiers da yayi hayansu, tsoro sosai suka bawa mal jauro wanda ya fadi inda take aure har da sunan mijin nata. Yanzu a dalilin haka ya jawo wa kanshi damuwa.

[11:06PM, 7/20/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣9⃣


Fatu na isa gidan jameel ta shiga gabanta na dukan uku uku, a palour ta tarar da lubna na zaune "kin iso? Tace da ita, sai da ta zauna tukun tace "ehh, Allah yasa lafiya" hoton ta ajiye akan cinyar fatu wanda lokaci qanqane dan walwalar da yake fuskarta ya bace ya koma matsanancin damuwa, ido ta kurawa hoton kamar yau taba kallon irinsa, lubna da ta kafe ta da ido tana nazarinta tace "explain please" hawaye naga yana zarya a kumatun fatu tana girgiza kai tace "its over, d charade" lubna ta matso kusa da ita ta dafa kafadunta tace "its not over yet, yanxu aka fara, trust me" tiryan tiryan fatu ta fara bata labarin har zuwanta gombe da yanda hajia ta taimaketa ta sakata a skul ta maida ita *FATUN BIRNI* ta kuma dauketa tamkar 'yar cikinta da ta haifa. Ajiyar zuciya lubna tayi tace "one last question, do u love sultan" dago idonta tayi da sukayi dan jaa don kuka tace "anty lubna......a life without sultan, even an immortal life would be empty, I wish to stay on earth with him" murmushi mai bayyana 32 lubna tayi tace "kamar yanda na fada miki its not over, to hakan ne" magana suka fara wanda nayi nayi inji amma fateey na ta dameni da kuka, naga dai lubna na zazzago magana yayinda fatu ke ta maida hankali 100% tana ji, can naji tace "he'll love her too" fatu da ta kasa boye farincikinta ta ruqunqume lubna tana daria kamar ance yau za'a kaita gidan sultan. Sai da suka natsa tace "anty lubna tnx alot Allah ya bar mini ke" "Ameen" ta bata amsa tana murmushi. Kiran sallah la'asar yasa suka farga dat its time. Lubna ta shiga bandakinta ta hadawa fatu ruwa a bathtub turarukan wanka naga ta diga a ciki, tayi alwala ta fito, ta bawa fatu towel ta shiga bathroom din yayinda ita kuma ta fara sallah. 15mins ta dauka tana dirja jikinta kamar yau aka haifeta😉 kana tayi alwala ta fito, zani da hijab lubna ta bata tasa tayi sallah, daga nan ta feshe jikinta da body spray ta shafa humra da kulacca duk na lubna, nan da nan dakin ya dau asirtaccen kamshin da komin gulmanka bazaka gane me da me aka hada ba. Wani swiss lace red nd black naga lubna ta dauko ta bawa fatu ta saka, fatu tace "na taho da kayana fa" "ban taba saka shiba, ko DJ bai san da zaman shiba, jst ki saka" ba musu ta karba ta saka, kamar a jikinta aka dinka, figure 8 dinta ya fito tarr, zaunar da ita lubna tayi akan kujera ta fara tsara mata make up, dauri ta kafa mata wanda yasa gashinta ya fito ta tsakiya ya kwanta a bayanta, Qara feshe ta tayi da wani turare mai sanyin kamshi, tace "done! Kallon kanta tayi a mirrow, ita kanta tasan tayi kyau bana wasa ba, kamar wata amaryan da za'aje dinner, qaran phone dinta ya katse kallon qurilla da take yiwa kanta, sultan nagani a screen din, dauka tayi ta kashe murya tace "Hello" sultan da yake kusa da motarsa yayin saurin dafawa don yanda muryan ya kashe masa jijiyoyin jikinsa, "hey" ya fada a sanyaye, ya cigaba "gani zan fito yanzu, kina gida ne in biya mu tafi tare? Sai data ja aji tace "nop, ina gidan yanzu haka" yace "ok gani zuwa" ya kashe wayan. Tsayawa nayi na qare masa kallo yau, dogo ne amma ba can ba, kuma da alama yana motsa jiki, fuskarsa irin na fulani sak, dogon fuska, manyan idanuwa, dogon hanci da bakinsa dan daidai, ga saje daya zagaye fuskar da quarter million suka qara qawata shi, gashin kansa kamar na fulani Aww ashe fulanin ne, black ga santsi a kwance. Fatar jikinsa Brownie ne kuma ba chocolate ba, daka ganshi kasan hutu da kudi sun zauna hade da kwanciyar hankali. Half jumfa ne a jikinsa na dakakkiyar shadda mai launin blue, takalmin shi da agogon shi black, ya hadu ne iya haduwa Dan Fulanin. Motarsa ya shige sai gidan ja[truncated by WhatsApp]

[8:50pm, 8/5/2016] Dara: [10:51AM, 7/31/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣4⃣


Fatu ta juyo da kallonta gurin sultan tace "matarka? Pls kace wasa ne" bai dago ya kalleta ba zuciyarsa na tafarfasa, ya dafe kanshi yayi shiru, lubna ta miqe tayi daki dama jameel yana gurin aiki. "alama ya nuna gaskia ne kenan, ya Allah" juyi tayi ta cigaba "ashe yaudarata kakeyi? Na dauka kai mutumin kirki ne ashe ba haka ba ne, why me sultan? Jin muryanta kaman tana kuka yasa ya dago da kanshi, hawaye ne ke sintiri a fuskarta, ji yyi bazai iya ganin su suna zuba ba, kamo hannunta yyi ya zaunar da ita a 2sitter shima ya zauna, still hannun su na cikin na juna, yace "aure aka min amma bada son raina ba, ke kanki kinsan ke kadai nake so, ki fahimceni" juya masa baya tayi tana share hawaye tace "na fahimta amma ka sani ni bazan zauna da kishiya ba, kaje ka zauna da matarka, Allah ya baku zaman lafiya" cikin kidimewa ya juyo da fuskarta yace "what? Yanzu fateema zaki iya rabuwa dani? Wallahi bana sonta ko kadan kuma nakusa zuwa in bata takardar ta, nima bazan iya zama da villager irinta ba" wasu zafafan hawayene suka sauqo wa fatu yayinda wani baqin ciki ya turnuqe ta, wato itace villagern!!!  daukan hoton tayi ta yayyaga kuci kuci, ta zubar a palourn tace "maza duk halinku daya, jiki da kwalliyan mace kuke bi, baku damu da kamala ba, karka qara taka inda nake" ficewa tayi a gidan ta barshi zaune a gun yana jin radadin maganarta. Shi a iya saninshi mace bata taba hararansa balle ta gaya masa magana. Me take nufi da kalamanta? Tattara pieces na pic din yyi yasa a small dustbin din da yake falon, shima ya fita daga gidan. 

Fatu kuma tana fita ta tari keke napep ya kaita gida, tana shigowa palour Allah yaso ba kowa ta haura upstairs zuwa dakin ta, zaman yan bori tayi a tsakiyar room din tacigaba da kukanta. Meyasa mazan ynzu basu damu da addinin mace da kamun kanta ba? Sunfi son wayayya yar boko wacce ta dace ta zauna a gaban mota kuma ta nunawa duniya? Meyasa taimako da tausayi yayi qaranci wanda har ana raba zumunci don son zuciya da kyale kyalen duniya? Tayi alqawari muddin ya saki fatu to bashi ba ita har abada, kallon kanta tayi a mirrow, me ya qaru a jikinta kuma me ya ragu? Gayu da gogewan da tayi yake so ba ba ita ba. "Villager" ta furta ta qara rushewa da kuka, ita tayi setting din draman amma ya dawo mata real life, a tunaninta zai so matarsa fatu ita kuma ta fada masa gaskian wacece ita! But sai hakan bai faru ba, miqewa tayi kaman wanda aka tsikara tace "yanzu inya sakeni ya zanyi? Ni fatu ya zanyi" zuciyar ta taji na mata quna, hakan yasa ta kwanciya akan gado tana aukin zubar da hawaye har bacci yayi gaba da ita.


Maman Fateey👯👯

[10:54AM, 7/31/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣5⃣


Sultan gidansu ya nufa kai tsaye yayi hanyar garden a can ya zauna. Maganar gaskia yana son fateema amma wani gefe guda kuma yana jin bazai iya sakin fatu ba, don da zai iya da tuntuni ya aikata hakan tun bayan aurensu da 1month, a lokacin ya fara mata aika mata kudi, yaso ya rubuta amma zuciyarsa ta haneshi da aikata hakan, a baki kawai yake fada amma shi kanshi yasan ko yaya zaiyi bazai iya ba. "Shes quit nd innocent" daukan wayarsa yayi ya turawa fateema text....


_ban yaudareki ba kuma bana fatan hakan ya taba faruwa, duk da bana sonta 'yar uwata ce kuma marainiya, I dunno what to do, bana jin zan iya sakinta, amma please ki daina batun rabuwa dani, I cnt take it fateema_


Tsawon minti goma da turawa ba'a masa reply ba, hakan yasa yace "bata huce ba har yanzu, ya kamata na bata lokaci"

Fatu na tashi daga bacci kusan bayan la'asar tayi wanka da sallah, yanzu kam ta daina jin qunar da zuciyarta yake mata, wayoyinta ta dauko ta fito palour, ba kowa kamar mummy ta fita unguwa farouq kuma yana islamiyya, a kitchen ta tarar da dija na yankan kayan miya suka gaisa dija tace "ya na ganki kamar bakida lafiya? Fatu tace "kaina ke ciwo, ina mummy? Tace "tana gidan hajia sadia, a zubo miki abinci ne?  Fatu tace "a'a kiyi aikinki zan zuba" daukan plate tayi ta zuba tuwon shinkafa ne miyar ugwu yasha kifi da nama sai kamshi yakeyi, spoon ta dauka ta fito daga kitchen din, a dinning ta zauna tafara cin abicinta, wayarta ta dauka sai a sannan taga text din sultan, fuskarta ba yabo ba fallasa ta ajiye, tana gama cin abinci takai kitchen ta dawo falo ta kunna data wayarta, mssgs na sultan ta gani duk na ban hakuri, ta karancesu tsaf ta kashe data ta kunna kallo amma hankalinta baya kai sai tunani, a haka mummy ta shigo tayi sallama bata jita ba, sai da ta taba ta sannan ta juyo a dan tsorice, ganin mummy ne ya sata fara'a tace "sannu da dawowa mummy" Mummy ta kalle ta fuskarta da damuwa, zama tayi tace "fateema lafiyanki kuwa? Idan akwai abunda ke damunki ki fada min, karki boyemin komai I'm ur mum" kanta ta kwantar akan kafadan mummy yayinda hawaye masu dumi suka biyo fuskarta tace "mummy nayi missing din gida ne, tunda nazo banje ba haka kuma banji daga garesu ba" shafa kanta mummy tayi tace "karki damu, in kin kusa komawa skul zakije musu, saboda akwai abunda nake so in aiwatar kafin kije" 


Maman Fateey👯👯

[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣7⃣


Basu sha wahalan gane gidan ba duk da dan sauyin da aka samu kusan shekara da rabi, yau ma a kofar gida suka samu mal Ameenu yana zaune da wani mutum suna magana. Tun dosowar motar mal Ameenu yake kallonta duk da bashi sultan ya taba zuwa da ita ba amma yana kyautata zaton yau fatu tazo da mijinta. Nesa dasu kadan suka parking yayinda suka fito kowa da dan murmushi a fuskarsa, ganinsu yasa mal Ameenu fadada fara'arsa kaman an mishi bushara, yana leqen bayansu yaga ta inda zaiga *FATUN BIRNI* Kawu muntari da yake gefen mal Aminu yace "baba, ko dai maigidan fatu ne yazo? Gyada masa kai yayi saboda sun iso, sallama sukayi aka amsa musu suka sami guri akan babban tabarman suka zauna, kaka yace "muntari shiga gida ka samo musu ruwa" kawu muntari ya tashi da sauri ya shiga gida. Gaggaisawa sukayi cikin mutunci kaka bakinshi yaqi rufuwa sai hamdala yakeyi yace "ai na aza da ita zaku zo, ashe ku kadai ne" Jameel yace "na'am baba" don bai fahimci maganar ba sultan ma haka. Kaka ya cigaba da cewa "bbu abunda zance maka sultanu sai Allah ya maka albarka, yasa ka gama da duniya lafiya, wato naji dadin wasiqarka, shekara da auranku baka zo ba, nayi tsammanin ko baka son hadin da aka maka ne, har na fara maganan raba auren ganin yanda aka fara surutu a kauyen nan, mutane sunyi gaskia da suka ce 'mai hakuri shi kan dafa dutse har yasha romonsa' nan din ma hakan ya faru, ranar da kayi aika ta hadu da mal usman a hanya ya bata saqon kamar kullum" kallonsu kaka yayi da fara'ar da har ynzu bata bar fuskarsa ba, daga jameel har sultan sun zuba mishi ido, ya cigaba "wasiqan da na gani a ciki yasa na dauka ko ka sauwaqe mata ne, data karanta muka gane" daria kaka yayi amma babu wanda ya tayashi don gabadaya kansu ya daure, sun rasa inda maganarshi ya dosa, fitowan muntari yasa jameel cewa "me ya rubuta" muntari yace "rubutawa sultanun yayi cewa fatu ta bishi gombe zai yiwa mamarsa bazata, ko ba haka kace min ba baba? Kaka ya amshe "ehh" muntari yace "ai naso inje aga gurin da kuke din saboda ziyara, amma fatun tace ita kadai kace taje" tari ne ya sarqe sultan yanayi ba kakkautawa ruwa aka miqa mishi yasha sannan ya tsaya idonshi har yayi jaa, Jameel ne yayi qarfin halin qaqaro murmushi yace "haka fa, abun zai kai wata nawa ma? Daga kanshi yayi kamar mai son tunowa muntari yayi caraf yace "wata takwas ai ko" kiran sallah azahar da aka fara yasa sukayi shiru kowa da abunda yake saqawa a ransa, sai da aka idar mal Ameenu yace bari a kawo muku buta kuyi alwala, shiga gidan kaka yayi da kawu muntari aka barsu su kadai, a sannan ne sultan ya dubi jameel da tsananin damuwa a fuskarsa don a yanzu sun gane komai daya faru yace "ina cikin duhu jameel" girgiza kai jameel yayi yace "ita ta rubuta wasiqa kace taje, tun wata takwas da suka wuce kuma da alama har yau bata dawo ba, sultan, fatu ta bata" shiru sukayi sultan ji yakeyi kamar ya kurma ihu ko zaiji sassauci a zuciyarsa, _FATU TA BATA! IDAN MAL AMEENU YA GANE BATA TARE DASHI YA ZAIYI? IDAN MAHAIFIYARSHI TAJI ABUNDA YA AIKATA HAR HAKAN YA JANYO BACEWAR YAR QANWARTA YA ZAIYI? SHIN FATU TANA RAYE? IDAN TANA RAYE TA INA ZAI FARA NEMANTA? TA INA?_  Tambayoyin da suka cika brain din sultan wanda  babu wanda zai iya amsa mishi, ji yayi zuciyarshi na zafi yana ganin duhu duhu, hakan yayi daidai da fitowan kaka da muntari suka ajiye buta miqewan da sultan zaiyi yaji kanshi yayi nauyi ya zube a qasa.


Maman Fateey👯👯

[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣6⃣


Yau saturday ya kama ranar da sultan zaije garin modibbo, da kyar da lallami yasa jameel ya shirya ya rakashi, wayarsa ya dauka ya turawa fatu text,


_yau zan tafi garin modibbo, pray for me_


Sai daya tura kuma yaji haushin kansa, yau kusan kwana uku bata daukan wayarshi bata amsa text dinshi, ko yazo ya aika ta fito bata zuwa, rabon daya ganta tun ranar da lubna ta kopsa masa, amma hala kawai ko abinci zaici sai ya mata text, zuwa unguwa da sauransu, amma bata kula shi. Shiga mota yayi ya zauna yana jiran jameel ya fito daga gidansa. Fitowa jameel yyi tare da lubna sai wani mannewa juna sukeyi suna I miss u, I miss u, haushi ne ya cika sultan ya danna horn da karfi wanda yasa suka dawo cikin hayyacinsu, tsaki jameel yaja yace "mallam zaka kashe min kunnen yaro" ko kulashi baiyiba, yanashiga yaja motar suka fara tafiya. Tittitititi alamar shigowan saqo da sauri sultan yaja birki wanda yasa jameel tsorita shi ya aza ma sun buge wani ne, da sauri Ya dauki wayan ya duba saqone daga fatu


_ka gaisheta_


 Shine abunda ya gani, wato duk mssgs dinshi tana gani wannan ne kawai taji zata amsa? Jameel wanda har yanzu zuciyarsa bai daina bugu ba yace "amma kai dan iska ne sultan, wannan wani irin ganganci ne zaka tsayar da mota cikin sauri haka? Kuma akan wata kake qoqarin kashe mu duka? Da mamakin shi sultan murmushi yake yi yace "srry dude, na love" jameel bai iya qara cewa komai ba don tsananin mamaki, shi ko ada da yake cewa in soyayya ya kama sultan zaisha wahala to bai taba zaton abun zai kai haka ba. "This is madness" sultan ya kunna motar yace "indeed". A haka suka kama hanyan kumo, jefi jefi sultan na bude saqon yana dubawa, da jameel yaga abun yayi yawa yasa ya karbi driving din, sultan yayi ta gwada calling fatu ko zata dauka amma taqi dauka, daya gaji ya hakura. Fatu kuma yau levels ta kawo mata ziyara, a daki na gansu suna zaune akan gado, fatu tayi wani _silent_ kamar marainiya xahra na bata baki "bai kamata kisa damuwa a ranki, duk da nasan its hardly ace baki damun ba amma gaskia ki sassautawa zuciyanki, addu'a zaki cigaba dayi, ki barwa Allah komai, kinji kam? Fatu da alama bata jin abunda xahra k fadi don wayarta take dannawa a hankali, kwace wayar xahra tayi pics din sultan take kallo, ido xahra ta bita dashi yayinda fatu ta gyara kwanciyarta ta bawa xahra baya, "ehh lallai babyn nan wato ni na zauna ina baki shawara kin maida ni bi ta can ko? Kinata kallon mijinki" tashi xahra tayi ta dauko laptop din fatu da sultan ya saya mata wai na karatu tace "me ma pasaword din? Sarai tasani amma ta tambaya _"SULTAN"_  fatu ta bata amsa, daria xahra tayi tace "soyayya ko wahala" ta cigaba da danne dannen ta har ta samu film din da take so ta fara kallo. Fatu kuma tunani ne fall a ranta na abunda zai faru in sultan ya isa ya tarar fatu ta fita nemansa months back!!!


Maman Fateey👯👯

[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣9⃣


Ba fatu kadai ba har lubna da xahra mamakine a fuskarsu, tsintan  pieces na pic din sultan ya fara yana ajiyewa a gefe, jameel ne ya shigo ya tsaya a kanshi yayinda su fatu ma suka matso suna ganin ikon Allah. Sai daya gama tarawa ya kwashe, yazo zai wuce ta kusa da fatu, tsayawa yayi yana kallonta itama ta tsura masa ido, har ta fara tausaya masa ganin a yini daya har ya fara susucewa, kawar da kanta tayi shima ya wuce bai ce mata komai ba, zama yayi a kujera ya jawo centre table ya baza pieces din ya fara jerawa, jameel ne ya zauna kusa dashi ya dafa kafadarshi yace "sultan" bai kalleshi ba yaci gaba da jerawa amma ko kadan basu jeru ba don kuci kuci suke, gumin da yake hadawa ya diga akan wani piece yayi saurin gogewa hakan yasa abunda yayi qoqarin hadawa kusan minti 10 ya wargaje, watsa nakan table din yayi a qasa ya dafe kanshi, ya kwantar da kanshi akan kujera, jameel da yake gefenshi yace "kayi addu'a sultan" addu'o'I ya fara idonshi a rufe yana dafe da kanshi. Jameel ne ya fara basu labarin abunda ya faru tun zuwansu, yana qarisawa sultan ya tashi zai fita, jameel ya tareshi yace "ina zaka je? Ka huta tukun" girgiza kanshi yayi yace "zanje gida ne, ka kai hoton gidan tv a fara cikiyanta don Allah, da gidan radio please" yana gama maganarshi ya fice, jameel yabi bayanshi. Lubna ta juyo da dubanta gurin fatu wacce take danna wayarta alamar bata da matsala tace "fateey ya kamata ki fada mishi kece, kiga fa yanda yake qoqarin zaucewa" tsayawa tayi da danne dannen tace "dadina daya da basu bayyana wa kakana ba" xahra tace "u have to talk to him" tashi tayi ta tsaya tace "a'a ba yanzu ba" murmushi tayi tacigaba "na zauna tsawon shekara daya cikin zullumin inda mijina yake, nayi kuka, nayi addu'a, duk inda nabi mutane magana sukeyi anacewa ga bazar bazar, wato mace mai aure amma ba miji, kaka ya hana ni fita, haka na zama tamkar mujiya, cikin gidan ma ba'a barni ba, goggo asabe cikin gaya min baqaqen maganganu take" juyo da dubanta tayi kan su xahra tacigaba "duk akan waye na sha wannan bakin ciki? Akan sultan, dalilin cewa ni baqauyiya ce, wacce bata waye ba, ban dace dashi ba" lubna tayi ajiyar xuciya tace "bawai na raina halin dakika shiga bane, a'a kinaji yanda DJ ya fadi abunda ya faru, har suma fa yayi" murmushi fatu tayi tace "babu abunda zai sameshi, xahra mu tafi" sallama sukayi wa lubna suka wuce gida, ita lubna har ta fara tausayawa sultan, fatun ma ta tausaya mishi amma tayi alqawarin saiya horu tukun, tana son nuna mushi dan adam ba abun wulakantawa bane, kuma cewa "kare ma yanada rana, balle mutum dan adam mai tunani da hankali"


Maman Fateey👯👯

[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣8⃣


"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" abunda kowannensu yake furtawa kenan sukayo kanshi, jameel ne ya shiga jijjiga shi yana "sultan, sultan ka tashi" yama manta cewa shi doctor ne, ruwan buta yasa aka miqo masa ya yayyafa masa, ajiyar zuciya mai qarfi ya sauqe kafin ya bude idonshi a hankali yace "ina fatu? Ganin zai qara magana yasa jameel saurin cewa "mu daga shi mu kaishi mota, dole sai an kaishi asibiti" mal Ameenu da yake da salallamai a gefe yace "muntari tayashi ku dauke shi, maza maza" hannayensa suka saka a kafadunsu suka kaishi mota kaka na "ashsha Allah ya bashi lafiya" yana girgiza kai. Suna sakashi a mota yana cewa "ina fatu? Ina fatu? Jameel yayi saurin shiga driver sit ya kunna motar, yana tunanin yanda zasu fara nemo fatu, tunawa da yayi cewa fateema ta yaga pic din fatu da suke dashi yasa yayi saurin fitowa daga motar ya samu kaka fuskar shi gwanin tausayi muntari na cewa "baba, sai cewa yakeyi ina fatu fa" alamar akwai matsala kenan, kaka na ganin jameel bai ko saurari muntari ba yace "jikin ne? Ko dai a qira madam nasi (nurse daya da suke dashi a qauyen) ta dubashi? Jameel yace "a'a nima doctor ne, fatu yake son gani, in akwai hotonta a bani" kaka cikin jimami yace "kayya wannan wani irin cuta ce? Fatu bata daukan hoto sai hoton ta daya da aka dauketa tana shekaru uku" da azama jameel yace "a bamu" kaka yayi saurin shiga gida muntari ya mara masa baya, shi kuma jameel ya koma gurin sultan a mota. Yana isa ya samu sultan ya fara dawowa hayyacinsa yace "yarinyar nan tana son kashe ni, tana jawomin matsala a rayuwata ta koyaushe, ina take? Bubbuga bayanshi jameel yakeyi yana cewa "be strong, be strong dude, zamu nemota insha Allah, I'm with u" jameel kaman ya fadawa kaka batan fatu amma yana hango tsananin tashin hankalin da zasu shiga in suka ji labari shiyasa ya shirya qaryan cewa sultan nason ganin hoton ta ne, fitowa kaka yayi muntari na binshi a baya kamar jela, da sauri jameel ya isa gurinsu ya karbi hoton tare da cewa "mungode, amma dole sai mun dangana da asibiti" muntari yace "to wani irin cuta ce wannan da zaisa mutum suma ya tashi da son kallon matarsa? Kaka ne ya harare shi kana ya maida kallonshi kan jameel yace "ai ya kamata ku hanzarta tafiya kafin wata matsala ta kunno" sallama sukayi jameel ya koma mota, ya samu sultan ya dafe kanshi yace "ka rage tunani sultan don kar ka jawowa kanka matsala, zamu nemota duk inda take" motar yaja suka tafi suka bar kaka cikin daurewan kai, meke faruwa ne?


Fatu na kwance kamar wacce aka tsikara ta tashi tace "xahra akwai matsala" xahra tasa pause ta juyo tace "a ina? "Yanzu idan suka je suka fadawa kaka bana tare dasu wallahi hankalinshi zai mugun tashi dama gashi da hawan jini, yanzu ya zanyi? Ido xahra ta qura mata tana tuna maganar fatu da take cewa rayuwarta kamar a film, wannan shine asalin film. Kafin xahra ta bude baki fatu ta sauqo daga kan gado ta dauki gyalen dogon rigan da yake jikinta ta yafa kawai tace "tashi muje gidan lubna, kaina ya daure, ban san me zanyi ba, zata fini sanin ya za'ayi" daukan gyalenta xahra ma tayi suka fito a palour suka tarar da mummy sukace zasu je gidan lubna, tace Allah ya kiyaye a gaisheta.

Suna fita daga garin sultan yace "taya zamu nemota bayan bamu san inda ta nufa ba, kuma ko hotonta bamu dashi" Jameel ya miqa mishi pic din da kaka ya bashi ya qurawa hoton ido kaman tana kama mishi da wata daya sani, tunawa da cewa ya taba ganin fatun yasa yabar tunanin, yace "wannan fa tana yarinya ce, ina wanda ka dauke mu? Jameel bai masa magana ba, tunowa da cewa fateema ta yaga yasa yayi zugum yana kallon dajin Allah. Suna shigowa gombe yace "jameel muyi gidanka" haka suka iso kowa da tunanin da yakeyi, ko gama parking jameel baiyi ba sultan ya bude ya fita da sauri jameel ya qarisa parking din ya biyo bayanshi "whats wrong sultan? Ina!! Already ya shige. Ko tsayawa kallon wadanda suke palourn baiyiba ya wuce gurin da dustbin yake ya juye a qasa.


Maman Fateey👯👯




Zaharaddeen shomar

Whatsapp  08168575100




[4:13PM, 8/5/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣0⃣


Fitansu suka wuce gidan tv bayar da cikiyan, ba qaramin daru sultan ya tayar musu ba kan sunce bazasu karbi hoton a matsayin wanda zasuyi cikiyar ba, A cewarsu suna buqatan hoton ta na yanzu, yanda jama'a zasu ganeta, da kyar suka karba ganin yana neman daga musu hankali, suka ce zasu saka amma ba dole bane jama'a su gane ba. A gidan radio ma hakan ya faru sun buqaci a fada musu kamanninta da shekarunta, kamannin Jameel ne yayi guessing ya fada shekaru kuma sultan yace "17 noo 18" kallon mamaki ma'aikatan suke binsu dashi, ace yazo a masa cikiya amma bashida  cikekken details. 

A hanyansu ta dawowa sultan yayi shiru yana tunanin abunda zai faru gaba, don shi gani yakeyi fatu ta mutu ko kuma an sace ta, gani yakeyi baza a taba ganinta badon wata takwas ba wasa ba, yanzu me zai cewa mammin sa, yanda take muradin ganin qanwarta da zuriyarta, akan son kai irin nashi ya saka mafarkin mahaifiyarshi bazai taba zama gaskia ba. Hawaye naga ya gangaro a fuskar sa, yayi saurin gogewa don kar jameel ya gani, Yace "jameel nayi kuskure kuma nayi nadama, daa na yarda da qaddaran auren yarinyar nan daa haka sam bai faru ba, nayi wa mammi alqawarin nemo mata qanwarta, amma sai gashi ta dalilina da selfish mind dina nayi sanadiyyar bacewar the one nd only blood din aunty na. Ban san a wani hali yarinyar take ciki ba, ko tana raye ko ta fada hannu mara kyau I dunno, jameel Allah zai kamani akan hakkin fatu, tana matsayin matata shekara da wata takwas ban waiwayeta ba" muryan shi ya fara rawa hawayen da yake qoqarin boyewa ne ya silalo, jameel ya kalleshi ya girgiza kai cikin tausayawa, sultan ya cigaba da magana bayan ya share hawayen "jameel da na dauki shawararka tun bayan auren da ban shiga matsala yanzu ba, yarinya ce fa, she's just 17 a lokacin, tana kuka ina fada mata maganganu marasa dadi, kamar qanwata take fa, qanwata ce kuma matata" gyara zamanshi yayi idonshi na hawaye yacigaba "ban san wani hali kakanta da mummy zasu shiga ba in har ba'a samu yarinyar nan ba, ban san da wani ido zan kalle su in musu bayani ba" Zai qara magana jameel ya dafa kafadarshi yace "its ok, ka rage damuwa sultan, za'a sameta da yardar Allah"

[9:17PM, 8/5/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

🌻🌻🌻FATU A BIRNI👜👠 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻          

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣1⃣


Sun shigo unguwan jameel yace "mu wuce gidana muci abinci ne? Sultan yace "ka kaini gida kawai, nikam na koshi" gidan su sultan ya nufa, a haraban gidan yayi parking ya fito amma sultan yaqi fitowa, gani yake yana shiga mammi zata karanci abunda ya faru! Jameel ya bude masa kofa ya jawo hannunshi ya fito dashi kamar mara lafiya, a palour gidan ya zaunar dashi ya fara kwalawa amrah kira, amrah da take dakinta ta amsa ta fito ta gaishe shi ta dubi sultan da ya wani sanyi dashi kamar maraya tace "ya sultan bashida lafiya ne? "Ehh, ki kawo mishi abinci" tace "too" ta wuce kitchen, dai dai nan mammi ta fito daga dakinta tana waya, ganin sultan cikin wani yanayi da bata saba ganinshi ciki ba yasa tace da wanda take wayan "zan kiraki anjima" ta kashe, jameel ya gaisheta hankalinta na kan sultan da yake binta da ido kamar yau ya taba kallonta (yayi laifi yana tsoron duka😆) Tace "meya sameka _manga_? Runtse idonshi yayi, ji yakeyi kamar ya fada mata laifin daya aikata na wasa da rayuwar abunda take muradin gani. Jameel ya ari bakinshi yace "kanshi ke ciwo mammi kuma bai ci abinciba, a bashi paracetamol in yaci" amrah ta fito da tray a hannunta ta ajiye a qasa tace "inyi serving ne? Mammi tayi saurin cewa "ehh" jameel ya musu sallama ya tafi gidanshi cike da tausayin halin da abokinshi yake ciki, Amrah ta zuba masa a plate jalof na spaghetti da irish potato yaji kifi, da kyar ya yadda yaci don sai da mammi ta bata rai tukun, magani ta ballo masa ta bashi dolenshi yasha ba don zai yaye mishi matsalan da yake ciki ba. Yana gamawa mammi tace ya tafi dakinshi ya kwanta ko na 30mins ne. 

Su fatu na isa gida suka wuce dakinta, tunanin fatu daya yanzu kuma, kar magana ta fito mummy taga laifinta, shiru tayi tana tunano halin da tabar mijin nata ciki, xahra ta buge ta tace "kinyi abu yana damunki, ko a yanzu sultan ya jijjiga, abeg karki sashi kwanciyar asibiti, kinsan ajeebo ne bai saba da damuwa ba" harara fatu ta watsa mata tace "eeyee tunda ni kuma ajeebako ce na saba da damuwa sai in tausaya mishi ba? Levels tace "ba haka bane qawas, lamarin duniyan nan in kowa yace zai rama abunda aka masa fa baza'a zauna lafiya ba, kuma hakuri yana da kyau, ko yanzu ya gane kuskurenshi kuma yayi nadama, shawara nake baki" tana gama fada ta shige toilet. Kogin tunani fatu ta fada  'tana son mijinta sosai, tana son kasancewa tare dashi, amma yini daya yayi kadan a cikin horon laifin daya aikata' ajiyar zuciya ta sauqe ta rafka uban tagumi, alamar an bude kofa yasa tayi saurin sauqe tagumin, xahra na fitow tace "ni zan tafi gida" rakata tayi mal habu ya maida ita, fatu ta dawo gida cikin damuwa, kitchen ta nufa tana taya dija aiki don rage yawan tunani.


Maman Fateey👯👯



Zaharaddeen Shomar

Whatsapp  08168575100



Post a Comment

0 Comments