[8/6, 23:11] +234 814 948 5104: FINI A MIJI IN FIKI A UBAFI NI A UBA👨👧👧👨👧👧👨👧👧IN FIKI A MIJI💑
WRITTEN BY HANNE ADO ABDULLAHI
Yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sanye da kayan makaranta take gudu cin cin cin karfinta.
Duk kokarinta bai wuce n ba ganin ta kamo sabuwar mota kirar seinna mai cike da sauran yara wadanda suka fita da kuma wadanda tafi.
Duk kokarinta ya tafi a banza lokacin da driver motar ya karya kwana wanda hakan ya sa taji hawaye ya zubo a idonta. Ta gama hakkakewa yau ma ta rasa darasin yau.
Zainab ke nan diya a wajen commisioner kudin na jihar watau Dr Abdullahi Zubair.
Asalinsu mutanen Kera ne ta nan kasar garko.
Kwazonsa ya sanya ya fito daga riga ya shiga birni da kafar dama. Tun da kuwa ya shigo bai koma ba.
Hatta ladan nomar da aka auran masa watau mahaifiyar Zainab babbar 'yarsa sai da ya rabu da ita.
Ko da yake ita din ya so zama da ita ko don kyawunta da biyayyarta da kuma yadda take tattalinsa. Amma haduwarsa da Rumaisa sai tayi sanadin da ya kori uwargidansa Khadija.
Ya gama digeen farko zai tafi kasar waje karo ilmi aka aura masa ita. 'Yar aminin mahaifinsa ce amma shi ya ganta yana so iyayen suka bashi.
Kuma da ita yayi jagaltun karatu a England inda yayi degree na biyu dana uku.
Yana dawowa kuwa da babban kwali ya samu matsayi dai dai misali.
A nan ne kuma ya hadu da Rumaisa. Aiki take yi a oficce dinsu.
Ko kyansa ya isa ya ruda mace. Ita ma kuwa haka Rumaisa ta dinga shiga tana fita har sai da ta ja hankalinsa suka fara soyayya.
Tun da kuwa suka hade ya daina karyawa a gida saboda kullum da garar da Rumaisa zata shirya masa.
Kuma itama Khadijan kar ku dauka ko kin wayewa tayi tsaf da ita. Tun da ta gama secondary ta aure shi. Kuma zamansu a turai ta samu ta yi degree a education.
Amma kisisinar Rumaisa sai da ta hana ta zaman gidan nan.
Kun san idan mutum mai son kansa ne kuma yana da shegen wayo tsaf zai yi cinikin ka baka sani ba.
Ita ma Khadija abin da ya faru da zamansu ke nan.
Da farko zaman nasu ba matsala. Samun ciki Rumaisa mai yawan laulayi shi ya bata nasarar korar Khadija.
Wai ita mai abin arziki ganin yadda take fama da laulayi saita dauke mata girki. Ita take komai a gidan.
Kuma duk da hakan ba zata dora tukunya ranar girkin Rumaisa ba tare data tambayeta me za a girka ba.
Idan ta ta shi sai ta sata ta lafta abinci da sunan za a yi baki. Taki kuma fitowa da shi sai ya lalace dai dai sanda taga mijin nasu ya na wajen sai ta fara karya murya a dole ita mai ladabi ce. Ta ringa fadin "yaya ya akayi ki kabar abinci ya baci. Bawan Allah nan yana kokarinsa mu kuma ba sai mu dinga alkintawa ba".
Da ya taso zai tufe Khadija da fada sai ta hana ta ringa fadin bari Dr ba girman ka bane fada da mats ".
Idan kuma shi da ita ne sai ta ringa gaya masa "kara hakuri in samu lafiya. Zan daidaita maka komai na gidanka. Amma in kana mata fada raina ka za tayi".
Ko kuma idan ta dauki albashi haka za a yo masa dinki mai kyan gaske a saya masa su turare. Ko a lafto masa cefane da sunan san a taimaka masa.
Kuma duk randa tayi irin wan nan ta ringa fadin " yaushe ma zan zauna in barka kayi ta wahala kai kadai. In ma banda sakaryar mace wa ke jira sai miji ya dauko ya bata. Kuma idan ban maka ba meye amfanin kudin nawa".
Kan sa kuwa ba karamin fasuwa yake da kalamanta ba. Sabanin Khadija da Allah ya yo ta shiru shiru bata magana.
Sai dai in abin ya isheta ta shiga daki tayi ta kuka.
Ta yaye Zainab ba dadewa, ya gaji saboda da duk hanyar da Rumaisa zatabi ta tabbatar ta fitar da Khadija daga zuciyarsa sai da tayi.
Saboda haka Khadija dai a gida ta yaye Zainab. Ranar sunan 'yar Rumaisa ta fari watau Farida a ranar aka yi ta ta kare.
Dr ne yace idan an gama abincin suna a aika masa da yawa ofis saboda abokanan aikinsa.
Sako dai bai samu Khadija ba da aka turo direban daukar abincin ma wanda ta karbi sakon safe ita ya samu saboda ita tana da waya. Yana iya kiranta yayi magana da ita.
A lokacin kuma waya bata zaga gari haka ba.
Rumaisa ta tura wata daga bakin 'yan suna akan a fadawa direban Dr babu abinci ya kare.
Sun kuwa taru a conference room wan nan sako ya same shi.
Ba karamin bacin rai yayi ba. Ya kuwa dawo gida ya rufe Khadija da fada da bata san na meya ba.
Tayi yunkurin nuna masa bata samu sakon sa ba.
Nan kuwa Rumaisa ta shiga kuka da rantsuwa wacce har sai da ta gigita ita kanta Khadijan. Kuma gaba daya daga ita har mai gidan ta hana su magana sai kuka take tana fadin "kiji tsoron Allah Khadija. Nan na same ki har bakin kicin na fada miki sakon Dr. har kuma na sake fitowa na sake jaddada miki lokacin kina rabon abinci. Ni kam na shiga uku. Me nayi miki kike son sai kin hadani fada da mijina".
Ba karamin mamaki ne ya rufe Khadija da zantuttukan da Rumaisa take yi . Tana yi kuma tana rantsuwar Allah ne shaidarta.
A nan dai shedan ya samu rabonsa. Ba tare da ya saurari jawabin da take kokarin yi masa ba ya yanka mata reciept dinta mai gaba daya. Kuma gudun kar yaje gida a bashi hakurin ya mai da ita ya sanya ya bata saki uku rigis.
Haka ta rungumi 'yarta Zaunab ta koma gida.
Daga baya ta samu miji wani dan uwansu dake malamin makaranta a sakandiren Garko ya aureta. Yayi alkawain rike mata 'ya amma uban Zainab yaki. Ta koma gidan mahaifinta lokacin tana 'yar shekara biyar.
Ta tarar da kannenta mata biyu. Farida da Farisa. Da kuma kannen matar gidan suma su biyu' 'yanmata dasu. Anti Sakina da anti bilki.
[8/6, 23:11] +234 814 948 5104: FINI A UBA IN FIKI A MIJI👨👧👧
BY HANNE ADO ABDULLAHI
PAGE 2
Tun da Allah ya dawo da Zainab gidan nan bata kara sanin menene farin ciki ba.
Da babanta ya je dauko ta daga hannun mahaifiyarta da cin hancin karatu mai nagarta ya rarrashe ta ya kuma dakko ta da alkawarin haka. Amma ga shi nan a sati da kyar take samu ta je sau biyu ko sau uku. Saboda Mammy ta kafa mata dokar ita zata dinga gyara dakinsu bayan sun tashi san nan ta jira kowa yayi wanka ta wanke bandakin su.
Hakan ya sanya ta ke zama ta karshe wajen shiryawa. Kuma da Abbansu zai fara fada a kan cewa me ya hana ta shirwaya da wuri kafin ta bashi amsa , Mummyn zata yi saurin cafewa da fadin "Daddyn Farida kayi hakuri ka san kowa da irin yanayinsa. To ita haka Allah yayi ta bata da hanzari ko kadan".
Yadda take kama da mahaifiyar ta haka halinsu yake iri daya. Ita maba mai azarbabin magana ba ce. Hakan ke bawa Mummy danar cin galaba a kanta.
Bata taba ba ta damar magana da mahaifinta direct ba. Da ya yi yunkurin tambayarta wani abu ko kuma yana niyyar yi mata fada to kuwa caraf zata amshe zancen.
Hakan ya sanya mahaifinta bai san komai dangane da halin da take ciki ba.
A cikn sauran 'yan uwanta Farida duk tafi su kirki. Ita ke kokarin janta a jiki. Amma su anti Sakina sun fi kowa takura mata. Bata da wata daraja sama da wacce za su bawa 'yar aiki.
Ga shi dai itace 'yar gida ,amma ba wata alama da zata nuna maka hakan.
Tun farko da ta zo double bunk biyu ne a dakin. Su anti Sakina na kwana a kasan kowanne yayin da Farida da Farisa suke saman su.
Saboda haka ita bata da makwanci. A kan kafet take kwana. Tun bata fi wata biyu da zuwa gidan ba taji gidan ya gundureta saboda rashin kula da take samu daga wajen mazauna gidan baki daya.
Ita in ba sanda ta zo gidan ba ina ta san wani kula da kanta ko kayanta. Amma yanzu idan tayi wanka ruwanta idan taga dama tayi sallah ita ta sani. Idan ta alkinta kayanta kanta ta yiwa. In ba haka tana ji tana kallo su Farisa zasu mai da mata kaya duster.
Ranan farko da hakan ta faru. Farisa ta zo ta samu ta dauki dankwalin rigarta ta wan nan sallar da aka yi musu tana goge takalmin ta da shi.
Tun ranar salla da ta saka atamfar bata sake sata ba. Haushi ya kamata ta fisge dankwalin tana fadin "saboda wulakanci da kayana zaki yi duster".
"An yi duster da shi. Banza 'yar kauye". Farisa ta amsa cikin rashin kunya. Wai ita takamarta itace babba sai ta dauka tana da 'yancin hukunta kannenta idan sun mata laifi. Saboda haka tana daga hannu ta wankawa Farisa mari. Duka dan hannunta nama guda nawa yake. Marin ma dan kada ne ya samu Farisa.
Amma wai yarinyarnan bata fi shekaru biyar ba amma ta iya kazafi. Sai da ta juta ta kalleta tace "la la la laa! Ni kika mara. Yau kuwa zaki sha mari".
"An mare ki din". Inji Zainab. Nan Farisa ta tafi ta barta tana kunkuni bata mata kaya masu daraja da akayi.
Allah yarinyar nan ba ta fasa kuka ba sai da ta kusa isa dakin Mummy. Ta kuwa dage ta faskara wani irin ihu. Irin wanda baka jinsa sai in tafasasshen mangyada ya zubo a jikin yaro. Da sauri mummy ta fito tana fadin "ke meye ya same ki"?
Ba ta bata amsa ba sai ma wani kukan da ta tsiri yi. Sai da mummy tayi rarrashi sannan ta tsagaita cikin shesshekar kuka tace "ba Zainab ce ba abin da nayi mata ta kamani ta dinga marina. Har taji min targade a kunne....,."
Ai bata jira jin karashen magana ba ta fizge ta suka nufi dakin yaran. Zainab na kokarin ninke kayanta ba zato ba tsammani taji saukar mari zafafa guda hudu biyu ta kowanne bari.
Nan take farar fuskarta ta koma ja.
"Muguwa mai hali irin na uwarta. Dama turo ki tayi ki zo ki nakasta min 'ya'ya. To ki koma ki sanar da ita ni nafi karfin ku daga ke har ita. Annamimiya". Ta fada tana me sake kai mata rankwashi aka.
Saboda azaba kasa kuka tayi yayin da daga gefe Farisa take mata gwalo.
Nan dai Mummy ta kari masifarta ta ja 'yarta suka fice daga dakin.
Sai da suka fita san nAn hawaye ya zubo mata. Nan ta kwanta a tsakiyar daki tana faman kukan ciwon da idonta da kuma kanta ke yi. Ba kuwa ita ta samu relief ba sai da Allah ya dawo da Farida daga lesson ta zo ta tarar da ita a haka.
Falon babansu ta ruga da gudu tana fadin "Abba Mummy ku zo ku ga Zainab ta na kuka bata da lafiya".
Da hanzari duk su biyun suks nufi inda take. Suna zuwa Mummy Rumaisa ta daga ta ta rungume a jikinta tana fadin "ke kuma baki da lafiya ba zakiyi magana a baki magani ba. Yi sauri Farida duba drwaer a dakina ki dauko min panadol".
Tana dago ta da niyyar bata maganin ya hankalta da jinin da ya kwanta a gefen idonta. Cike da tsoro ya tambaya. "Zainab meye haka ma ya samu idonnki"?
Kafin tace komai Mummyn tayi sauri tayi chipping in. "A garin wasan banzan su ta je ta bige. Zainab ki dinga kula. Maza hanzarta Farida akwai chloramphenicol a cupboard din bandaki na ki dauka ki kawo min".
Haka kuwa wan nan zance ya wuce ba tare da Abbansu ya san me ke faruwa ba.
Sa ar Rumaisa Daya ce Abban nasu ya kasance irin mazan wan nan zamani wanda ba ruwansu da sa ido a harkar iyali. Wadanda suka dauka nauyi daya ne a kansu. Su fita su nemo su kawo domin wadata iyali.
To itama wan nan damar ta samu take amfani da ita.
Ba ta fi shekara biyu a gidan ba kuwa Mummy ta sake haihuwa inda ta samu Khalil. Kaf renon Khalifa kan Zainab ya koma.
Hakan ya sa karatun ta ya dada ja baya. Ga mahaifinsu Allazi boko. Shi in ba jarrabawa kaci ba ba abin da zaka yi ka birgeshi.
Na islamiyya ne Allah yasa tana da rabo.
Saboda ana musu shi ne a gida bayan la'asar. Sai tayi sa'a kusan duk fitar Mummy tafi yinta da la'asar din hakan yasa take samun sukunin daukarsa.
Malam Usman shine sunan mijin da mahaifiyarta ta aura. Mutum ne mai yakana da sanin ya kamata. Ga shi dai bata daura super da cotton lace balle getzner, amma kwanciyar hankali ta sanya Khadija ta murmure tayi kyau. Kamar matar wani babban mutum.
Shi tsohon mijinta yana mata dariyar daga England ta koma Garko. Bai san ita kuwa a rayuwar da ta samu kanta, Mecca kawai ta fiye mata zama da malamin mijinta a garkon ba.
Shi ya takura akan tazo taga 'yarta. Ta so taki zuwa saboda sanin halin mutanen gidan data baro,amma sam yaki karbar uzirinta da kokarin nuna mata ba zai yiwu ta fita sabgar 'yarta ba saboda bata tare da mahaifinta. Tun da ai shi kam ya so riketa , suka hana shi.
Sai da ya bari anyi albashi ya hada mata tsaraba rankacakaf ya kuma roki abokinsa mai motar haya golf daya sauke ta. Idan yaso idan ta yini in yayo lodi zai dawo sai ya biya ya dauketa su dawo tare.
[8/6, 23:11] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👨👧👧IN FIKI A MIJI💑
PAGE 3
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Hajiya Khadija ta sauka kofar gidan su Zainab watau gidan tsohon mijinta domin ziyarar 'yar ta wacce ta haura shekara biyu rabo da suga juna.
Ta fito da abincin maigadi za ta kai masa ta hango maigadin yana yiwa tsohuwar uwardakinsa rakiya.
Dauke yake da katon kwando cike da albasa. Yayin da ita kuma ta dauko jarkoki guda biyu irin rabin poster nan.
Dukkansu cike suke da lafiyayyen kindirmo. Ai tana ganinta ta saki flask din abincin maigadin ta ruga a guje ta rungume ta tana fadin "ga ummana ! Ga ummana".
"To sakeni kar ki kada dani " itama ta fada cikin murnar ganin 'yarta ta fari. In ban da tsawo ba abin da ta kara. Sai ma duhu da rama da ta lura ta dan yi.
Ta ki sakin nata saboda gani take idan ta sake ta guduwa zata yi.
Zainab rike da hannun mahaifiyarta suka dumfari kofar shiga gidan.
"Ke dakata. Ina zaki"?
Mamaki wan nan tsawa da ta daka musu ya sanya khadijan tsayawa cikin mamaki.
Ita bata ga lokacin da ta fito zuwa inda suke ba. Saboda ta shagalta da surutun da Zainab ke rangada mata. Bata san cewa karadin murnar ganinta ya fito da Rumaisa ba. Wadda ita kuma mamakin tashin muryar Zainab din ne ya sata fitowa saboda bata taba jin sautin muryarta irin haka ba.
"Uban me kika zo yi. Wacce irin marar zuciya ce ke. Miji ya koreki amma kin nace masa sai bibiyar sa kike".
"Kwantar da hankalinki. Ba wajen Yaya Abdullahi nazo ba. Zainabu na zo gani".
"Zainab kika ce kin zo gani. To itama na haramta miki ita". Rumaisa ta fada tana mai fizgo Zainab da ta makale jikin mahaifiyarta. Bata kuwa tsaya ba sai da ta kaita har cikin dakin ta wurgar da ita. San nan tace "bari in gama da uwarki san nan in dawo kanki". Ta rufe kofar da karfi sannan ta koma tsakar gida inda ta baro Khadija tsaye cikin mamaki.
Tana karasowa tace da ita cike da masifa "ke kuma na dawo gareki. Idan don wan nan jajakuwar 'yar taki kike shigo min gida. To ina son ki sani ke da ita sai dai a lahira idan kuna da rabon ganawa. Kumanayi miki alkawarin wan nan 'yar da kike takama da ita sai na daidaita ta sai na tarwatsa rayuwarta. Sai na maida miki ita abar kwatance saboda munanan halayen da zan tabbatar ta horu da su. Sai kin dawo kina jin kunyar nuna ta a matsayin diyar da kika haifa".
"Allah ya fiki" shine kawai abin da Khadija ta fada ta juya tana kokarin fita daga gidan.
"Dawo ina zaki ban gama magana dake ba".
"Ni ai na gama magana dake" ta fada tana mai kokarin fita daga gidan.
Hijabinta ta janyo har sai da ya yage daga wuya tana fadin "zo ki tafi da wan nan tarkace da kika zo da shi. Ko kinga munyi miki kama da matsiyata irin mijinki da zaki dauko wasu kazaman kayanki ki shigo min da su gida. Idan ma wani asirin kika dibgo kika kawo mana to ni na ci dubu sai ceto."
"Allah ya shirye ki". Shine kawai abin da ta fada ta fizge hijabinta ta nufi gate da niyyar fita.
Bata ankara ba taji wani abu kakkaura kuma mai sanyi na zuba a jikinta. Tana dubawa taga nonon nan jarka guda Rumaisa ta juye mata a kanta. Sai a lokacin ta tuna ashe a freezer ta saka shi ya kwana saboda ya iso ga wadanda ta yiwa tsarabarsa ba tare da yayi tsami ba. Bata gama da wan nan ba taji daya daya jarkar ta doki dunduniyarta. Ashe wurgar ta tayi da ita.
Itam kuwa daya jarkar take ta fashe nonon ya kwaranye a kasa ya kuma hade da jinin da ya zubo daga kafar Khadijan inda jarkar taji mata ciwo.
Shi kansa maigadi yayi mamakin karfin da Rumaisa tayi amfani da shi ta fizge kwandor albasar tayi kokarin jifan Khadija da shi. Shi dai Allah ya bata sa'a ta kauce masa.
Haka nan jakwane jakwane ta fita daga gidan cikin rakiyar zage zagen Rumaisa.
Tana mamakin wan nan kiyayya da take mata. Gida ne ta fita ta bar mar ta. Abin da bata sani ba, tun ranar farko da aka kawo Rumaisa gidan nan ta yaye mayafi suka yi ido hudu da Khadija taji tsanar ta ta zargu a idonta.
Kyawunta ba karamin razana ta yayi ba. Ga shi ita kuma mace ce mai kyayshin tsiya. Bata kaunar kowa ya fita da komai. Tafi son zama star a duk inda ta ratsa.
Amma kyan Khadija ya tsorata ta. Mace kamar ita ta zabi duk wani bangare na jikinta.
Tsayi daidai misali. Kirar jiki abar tinkaho. Kala abar alfahari. Gashi burin 'yanmata. Murya muradin mawaka. Sai kuma uwa uba hali irin na salihan bayi.
Wadan nan qualities din su suka janyo tsanar da Rumaisa tayiwa Khadija. To kuma sai aka dada rashin sa'a. Duk wadan nan martabobi duk da Zainab karama ce, amma sun fara huda a jikinta.
Ai da farko dawowarta gidan , aji daya aka saka su da kannenta. Gashi dai daga local government tazo , amma ba a yi wata guda ba ta zarce kowa a ajin har da kuwa Farida da kuma Farisa. Saboda tsiransu wata goma ne kawai ya saka aka saka su a makaranta tare.
Kwazon ta shine abin da Mummy ta fara attacking ta hanyar tabbatar dabata samu damar zuwa makaranta a kowacce rana ba. Ko hana ta damar yin home work da dai sauransu.
Duk da cin mutuncin da tayi wa Khadija bai ishe taba. Maigidan na shigowa ta tare shi da kukan ta tana rattaba masa wai Khadija tazo ta kare mata zagi da cin mutunci. Akan wai ance tana zaluntar Zainab.
Sai da ta fyace majina san nan cikin muryar kuka tace "yanzu saboda Allah duk yadda nake kokari na akan yarinyar nan amma ba'a gani. Yadda nake tattalata har yafi yadda nake wa su Farida amma duk da haka yarinyar nan da bakinta ta kalle ni a gaban uwarta tace wai ina wahalar da ita. Kuma ni ba wan nan ne yafi bata min rai ba irin gaya mata da tayi wai kana banbanta, ta da sauran yaran gidan nan".
Sai da ta fashe da wani kukan san nan ta sake marairaecewa tana fadin "yaushe aka yi. Me aka yi wa su Farida ba a yi mata ba. Wannan magana ta bata min rai. Amma ai ita Khadijan ta fi kowa data dauki maganar yarinya ba tare da ta binciki
Komai ba".
Tafasa yake ita kuwa tana dada tunzura shi. Habawa ai kuwa da ya tashi a fusace dakin yaran ya nufa. Zainab na kudundune a kasa tana kukan raba ta da mamanta da aka yi,"sai saukar bulala taji. Tayi ihu tayi magiya tayi afi amma bawan Allah nan bai san tana yi ba.
Mummy da mugunta tana karasowa da gudu abu na farko da ta fara yi shine jawo kofar ta rufe ta kuma rike handle din tana fadin "don Allah Abban Farida ka bude kofar nan".
Tabbas ba shi ya kulle kofar ba ita ta rufe amma bacin rai ba zai barshi ya tuna mai ya faru ba.
Sai da yaga Zainab bata motsi san nan ya fice daga dakin yana fadin "don uwarki gobe ki kara. Sai na miki abin da ya fi haka".
[8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👧 IN FIKI A MIJI💑
PAGE 4
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Khadija ta dade tsaye a bakin gate din gidan su Zainab ba tare da ta san abin da zata yi ba. Shi kansa maigadi shock din abin da matar gidan tayi ya hana shi magana.
Ta daure ta bude jakarta ta daiko wayar ta nokia 3310 ta kira mijinta Mallam Usman tana mai sanar da shi cewar ya gayawa abokinsa da ya kawota ba zata tsaya jiran sa ba zata dawo on her own.
Yayi kokarin tambayarta ko wani abu ya faru amma ta katse shi da fadin yayi hakuri sai ta dawo.
Ya buga ya sanar da abokinsa Malam Buba mai golf abin da Khadijan ta fada.
Take kuwa ya fasa lodi ya fita daga layin lodin da ya hau ya dawo gidan Dr Abdullahi Zubairu.
A halin da ya ga Khadija shi kansa hankalinsa ya tashi. Ta na ganinsa sai a lokacin kuka ya kwace mata.
"Shiga mu tafi maman Hafsa" ya fada yana mai bude mata gidan baya. Shi kansa ya rasa kalmar da zai bata hakuri da ita.
A kundila ya tsaya gidan wani abokinsa. Ta shiga tayi wanka matar gidan ta bata wasu kaya ta sa.
Hankali tashe su ka tarar da Malam Usman yana dakon zuwansu. Sai a lokacin shi kansa Mallam Buba ya san abin da ya faru.
Duk kan su sun yi bakin cikin jin wulakancin da aka yi mata saboda kawai ta kaiwa 'yarta ziyara.
Ya bata hakuri wan nan ta wuce. Ba sai kuma ga tsohon miji sun hadu da sabon miji a gidan su Alhaji Abdullahi.
Duk da aurensa da Khadija ya rabu hakan bai raunana zumunci tsakanin mahaifin Khadija da kuma na Abdullahin ba.
Shine ma waliyyin ta a auren ta na biyu da shi Mallam Usman din.
Kanwar Abdullahin ce ta rasu, Allah ya hada su a zaman makoki. Ya riga yaji famfon matarsa ga shi dama kuma yana kullace da shi kansa Usman din.
A cikin gida suka hadu shi da Usman din ya shiga ciki gai da iyayen su mata.
Bai ko lura ya hankalta da jama'ar dake dankare a tsakar gidan ba ko kuma ya na sane niyyar ci masa mutunci yayi oho.
Mallam Usman na kokarin mika masa hannu domin su yi masabiha yaji kalaman Abdullahi mahaifin Zainab sun dake shi kamar bulala. Yana buda baki sai yace "dawa zan gaisa da kai?ai kai kanka ka san nafi karfin gaisawa da matsiyaci irinka".
Kowa ya san Malam Usman, Usman din ne har a sanyi hali. Ga kuma kunyar gidan surukai dake dawainiya da shi. Domin yadda yake mutunta mahaifin Khadija haka yake yiwa tsohon surukinta.
Saboda haka yana budar baki cikin sanyin murya yace "kaga Dr kayi hakuri koma menene mu tattauna cikin fahimtar juna. Ni da kai ai mun zama daya".
"Dawa ka zama data ? Kaga Mallam dakata ka kalle ni da kyau ai ka san ni ba sa'anka bane."
Ya na fadin haka ya cakumo wuyan rigarsa yana fadin cewa "kuma ka gayawa matarka ta kiyayi mata ta. Ranar da duk ta sake taka min gida sai na sa an wulakanta ta yadda bata tsamm........"
"Sakarwa mijina rigarsa ko kuma infasa maka kai da tabarya".
Yaji ihun muryar Khadija ta nufo su kuma dauke da tabaryar. Duk su biyu basu ankara da cewa hayaniyar su ta fito da Khadija da kuma mahaifiyar Dr da ma sauran mutanen da ke cikin dakin ba.
Ta kuwa nufi shi dauke da tabaryar gadan gadan. Da hanzari mahaifiyarta watau kakar Zainab ta wajen uwa ta karbe tabaryar tana fadin "ke Dije baki da hankali ne".
Yayin da shi ma cikin mamaki yace "Khadija ni ki ke son wulakantawa akan wan nam banzan talakan mijin naki"?
"Ga ka nan banza wanda bai san ciwon kansa ba. Kuma ka zauna ka tace haram din da ke cikin kudin da kake ikirarin kana da shi ka gani ko bayan yin hakan halastacciyyar dukiyarka za ta kai tasa"?
Inna mahaifiyarta ta ce " kar in sake jin bakin ki a nan".
"Amma inna kina jin zagin da yake min bayan wulakanci da matarsa tayi min".
"Ke Khadija wuce ki tafi gida. Kar in sake jin kince wani abu". Mallam Usman yace da ita.
Ta yi tsai na dan lokaci ta kalli mijin nata sai taji ba za ta iya yi masa musu ba. Takaicin ya hana ta gayawa Abdullahi bakaken maganganu da ta tanada sai kawai hawaye ya fara zuba a idonta.
Kallon baban Zainab kawai tayi ta saki wani dogon tsaki. Takaici ya kama shi ya daga hannu da niyyar kai mata mari wani irin riko aka yi wa hannun nasa wanda bai taba jin irin sa ba.
Ya juya ya kalli Mallam usman wanda ya rike masa hannu yana fadin "sake ni in koyawa yarinyan nan hankali".
Shi dai bai bashi amsa ba amma kuma bai saki hannun nasa ba.
Innar Khadijan ce ta sake cewa "baban Hafsa kuzo ku wuce gida kai da Dije ba na son rigima".
"Su wuce ina"? Mahaifiyar shi Abdullahin ta fada watau kakar Zainab ke nan ta wajen uba.
Taci gaba da cewa "ita kuwa Dije ai nan gidan ubanta ne ba kuwa wanda ya isa ya sa ta fice daga cikinsa.
Shi dai da yake jin rashin mutunci ya iya ficewa. Shi kuwa baban Hafsa gidan surukansa yazo. Kuma tunanin haka ya sanya ka kuma ci darajar hakan har ka iya shake masa riga bai nuna maka banbancin karfin tuwon dawa da na samanbita ba.
In bai cin haka har kai ka isa ka taba jarumi irin sa. Ka tambaya a kauyen nan kowa ya san irin jarumtarsa."
Ita dai Innar su Khadija sai faman jan ta take tana bata hakuri yayin da shi kuma ya juya yafice daga cikin gidan cike da takaicin abin da mahaifiyarsa tayi masa. Kuma har sai da ya kai kofar gida bai daina jin zafafan kalaman da ta raka shi da su ba. Fadi take "yarinyace ka gaji ka sakota. Kace ba ka so. Wani kuma ya aura. Ka tsaya kanawa mutanen bakin hali. Ai duk wan nan zafin da ka daukan na san na takaicin rashin Khadijan ne".
Ita kanta Khadija da Mallam Usman sai da suka dawo suna bata hakuri saboda ganin yadda ta dauki zafi.
Ta kalli Malam Usman tace "kaga ai gaisuwa kazo min. Koma kofar gida ka zauna ka ci gaba da amsar gaisuwa idan yayi wani yunkuri ka daka min shi a wajen. Ke kuma shiga ki ci gaba da aikin abincin da kuke yi. Ban kuma yarda ki tafi ba sai sanda kuka saba tafiya idan kunzo".
Innar Khadija tace "don Allah ki yi hakuri ki bar zancen nan haka. Da wanne zamu ji da rasuwa ko kuma da shirmen yara"?
"Shi da ya dago fitinar ai bai tuna kanwarsa ce ta jini ta rasu ba. Tun da shi duk abin da matarsa ta dora shi a kai hawa yake ya zauna daram".
Ai kuwa takaicin abin da aka yi masa shi a Kera tsaf akan Zainab ya sauke shi.
Ita bata da masaniya ma na abin da yafaru. Yana cikin mayarwa da Rumaisa irin wulakanci da Khadija ta jawo aka yi masa ita kuwa ta shigo da saurinta tana fadin "Abba kaga da muka je Kera Abba Mallam ya ban....."
Ba ta kai karshen zancenta ba ya kuwa yi mata dukan da Mercy da Ronaldo sukewa Ball. Yarinyar nan sai da ta dangana da bango ta tsaya. Duk da haka bai hakura ba dukanta ya shiga yi kamar Allah ya aiko shi.
Sai da Mummy ta tabbatar ta daku san nan ta tashi ta rike shi tana ba shi hakuri.
[8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👨👧IN FIKI A MIJI 💑 PAGE 4
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Kwanan Zainab uku tana jinyar dukan da mahaifinta yayi mata. Wanda ba komai ne ya hassala shi yayi mata
dukan kawo wuka irin haka ba, sai kyawun da ya ga Khadija tayi.
Ta yi shar da ita kamar ba matar kauye ba. Shi ko zaman su da ita a kasar waje bai ga tayi wan nan kyan da kuma kuruciyaba.
Tafi masa kama da budurwa 'yar shekara ashirin ba uku zuwa da hudu amma ba wai matar malamin makaranta kuma uwar 'ya'ya biyar ba.
Ya dade kwarai bai hadu da ita ba. A tsammani sa tun da talaka take aure zai ganta yarkace yarkace.
Amma sai ya ganta tsaf da ita.
Ga kuma kalaman mahaifiyarsa da ta dinga fadin "mata ce an bashi yace baya so ya sako ta. Wani kuma ya aura shi ne zai zo yana nuna wa mutanen bakin hali".
Ba karamin tunzura yayi da kalaman mahaifiyar ta sa ba.
Yadda ta kwana uku tana jinyar jiki, haka ya debi wannan lokaci yana jinyar zuciyarsa.
A wan nan ma dare sambatunsa ne ya tayar da momi ta jiyoshi yana fadin "sai na wulakanta Khadija. Ita har ta kai matsayin da zan fadi magana ta mayar min da martani".
Momi ta kamo shi ta zaunar da shi a bakin gadon dakin. San nan ta nufi fridge ta debo masa ruwa a kofi ta bashi ya sha.
Sai da ta ga ya dan natsu san nan ta tambaye shi abin da ke damunsa. Take kuwa ya gaya mata niyyarsa ta daukar fansa akan tshuwar matarsa.
Dariyar jin dadi tayi saboda itama tana da burin ta tsawwalawa wa rayuwar Khadija. Saboda a nata tunanin son da dangin Daddy su Farida suke mata ne ya hana ita din su sota a matsayin ta na matar mai kudin dangin.
Ta ki fahimtar cewar su wadan nan fulani da ta ke gani bamasu zalama bane. Kudin ta dana mijinta ba zai sa su dauki raini da wulakancin ta da kuma na 'ya'yanta ba. Hakan ne ya sa suka ja baya da ita.
Ita ma kuwa tayi niyyar ramawa. Take tayi murmushi tace "kana director a finance. Kira na Education kawai ka sa a sallami mijin nata daga aiki. Ai dai dama karyarta ta sa ce. To datse samun nasa muga tsiya".
Jikinsa har kyarma yake saboda jin dadin wan nan gurguwar shawara da matarsa ta ba shi.
Takwas na safe kuwa a gidan Murtala tayi masa. Ya kuwa nemi abokinsa ya kuma nuna masa abin da yake son ayi kuma yama kara da son abata takardunsa kar ya samu damar neman aiki. Summary dismissal yake son abashi.
To shi ma na education din akwai voucher cuwa cuwa da ya ke son ya tura finance din ayi masa approving kuma shine mai sa hannu.
Take suka yi trade by bater.
Voucher a nan office din aka sa masa hannu ba tare da an sha wahalar kaita ba.
Yayin da shi kuma yakira education secretary na zone din ya bada dokar a sallami mijin Khadija daga aiki.
Kafin sha daya na safe kuwa takardar sallamar ta isa ofishin principal din Garko science. Har kuma da sharrin dalilin korar tasa saboda kama shi da akayi yana soyayya da daliba a makarantar.
Shi dai principal na Garko ya samu bakuncin ES na zone din su da kuma bakar takarda korar karen da aka yi wa Mallam Usman.
Ya tambayi dalili ES yace masa "kafar manya ya taka."
"To kuwa ko zan tozarta kowa banda Mallam Usman. Saboda haka ina mai shawartar ka da ka canza lafazin cikin wasikar ka. Kora kuke so to ku sauke shi ba dalili amma banda kazafi". Principal din ya fada.
ES ya tashi zai masa jan ido shi kuwa ya hado masa gangamin sauran malaman .
Take kuwa 'yar karamar zanga zanga ta fara faruwa a makarantar. Shi kuwa Mallam Usman baima san abin da ke faruwa ba saboda ya fita da wasu dalibai kai ziyara kafin ciri dam.
Ya dawo ya tarar da hatsaniyar da ake a cikin makarantar Inda sauran malamai suka dage in dai aka kori Mallam Usman to suma kuwa sai dai su ajiye aiki.
Shi kuma ES YA DAGE IN DAI principal bai sa hannu a takardar sallamar nan ba to kuwa sai dai duk su rasa aikinsu.
Vice ne ya daure ya fahimtar da Mallam Usman abin da ake ciki. Ba shiri kuwa ya gano fada da tsohon mijin matarsa shi ya haddasa masa rasa aikinsa kuma har yana neman ya zamo sanadin da abokan aikinsa zasu rasa nasu.
Ba tare da doguwar shawara ba ya dau takarda ya rubuta shaidar ajiye aiki ya kuma tilasta principal ya sa hannu.
Principal ya karba amma yayi masa alkawarin taya shi neman wani aikin ya kuma umarce shi da ya kawo takardun matarsa su dauke ta temporary tun da shi yana da hurumin daukar irin wadan nan ma'aikatan.
Da wan nan mummunan labari ya isa wajen matarsa. Ya dai shaida mata cewar yana cikin malaman da gwamnati ta rage.
Amma ya nuna mata ta kawo nata takardun za a taimaka masa ita a samo mata aiki.
Ya kuma samu ta yarda da maganarsa. Har kuma ta yarda zata ba da takardun.
Kwana biyu a tsakani ta kaiwa matar principal ziyara saboda ta yi mata barkar matar kaninta da ta haihu.
Anan ta samu labarin abin da ya faru. Da tsananin bacin rai ta dawo gida.
Nan kuwa ta tarar da mijinta. Ba ta bata lokaci yi masa bayani ba tace da shi "abban hafsa aramin wayarka".
Ba tare da tunanin komai ba ya mika mata wayar. Shi dai yaga tayi kira sai kuma yaji ta sake cewa " yi hakuri zamu gaisa an juma. Yanzu nambar yayanki zaki tura min".
Bai ji me akace daga daya bangaren ba amma yaji ta ci gaba da fadin "zan miki bayani ba wani abu bane".
Daga haka ta kashe wayar.
Shigowar sako da kuma kiran data dora shi ya sanyi shi fahimtar me take yi.
Cikin kakkausaurya yaji tana fadin "sannu shugaban ma'aikatan duniya. Zauna ka dawwama aikin gwamnati. Amma ka sani ko ba retire akwai mutuwa. Kuma kai din nan kayi kadan ka iya kuntatawa rayuwarmu. Aiki an bar maka shi. In har kana ji ka isa ka hana mu shakar numfashi san nan zan san ka cika sunanka Abdullahi dan Zubairu. Amma ka sani ......." wuf taji an fixge wayar daga hannunta.
Ta juya takalli mijinta wanda shi ma alamun bacin rai sun bayyana karara a fuskarsa.
"Ashe baki da kunya ban sani ba. Ashe ko ba komai ba zai ci arzikin da ya kasance yaya a wajenki ko kuma ki duba darajar Zainab ba . Amma kika rufe ido kina gaya masa duk abin da ranki ya ayyana miki. Kin je kawai kin jiyo tsegumi a waje kika hau kai kika zauna."
"Ke nan akwai abin da ya faru ka boye min".
"Ni ban san komai ya faru ba. Aiki ne Allah ya kaddara abincina ya kare a kai sai kuma me".
Shiru tayi ta kasa bashi amsa. Maganganu ne dankare a ranta amma ta kasa gaya masa.
Tarbiya yayi mata ta mutuntuwa bata fadi in fada ba. Saboda haka ta kasa mayar masa da martani ko kuma ta ci gaba da yi masa musu.
Sai kawai hawaye da kezuba a fuskarta na takaicin abin da daddy Zainab yayiwa mijinta.
Ganin tana kuka sai kuma ya sassauta muryarsa ya kamo hannunta.
Cikin muryar rarrashi yace da ita "kin ga Khadija ki yi shiru mu zauna mu tattauna yadda zamu shawo kan lamarin. Kuma kin ga principal yayi min alkawarin zai taimaka miki ke ki samu aikin a makarantar".
Haka ya dinga rarrashinta sai da yaga tayi murmushi kuwa san nan shima ya murmusa yace "haba kin bi kin daga min hankali. Sanadin 'ya'yanki su dawo su tarar da ke cikin yanayi na bacin rai su dauka nine ba su san baban su director ne ya jawo ba".
Ranar kuwa kwana tayi tana shawara wadda zata fisshesu ita da mijinta.
Bayan shawarar da zuciyarta ta yanke mata ta dora da nafila domin neman sa'a a wajen Ubangiji.
Washe gare ta nemi izninsa domin zuwa gida.
Da mahaifanta ta tattauna abin da ta ke son yi. Take kuwa suka goya mata baya.
Ta dawo kuwa baifi da awa uku ba sai ga mahaifinta yayi sallama da kudi har dubu dari uku da saba'in.
Kun san mutan kauye ba kamar na birni ba da bamu da abin saya sai kaya da dinki. Su kuwa baka raba su da dan tari.
To haka itama Khadija. Garkenta na manyan shanu biyar bajimai da kuma sanuwa uku da 'yan marakai bakwai ta sa babanta ya kai kasuwa.
Kuma a wan nan lokacin kudin da aka sayar da su makudai ne saboda darajar kudin.
Mallam Usman bai san da duk wan nan shiri nata ba sai bayan da daddare yara duk sun yi barci san nan ta fito da kudin nan ta tura gabansa.
Cike da mamaki yace "wan nan fa "?
"Na yi tunani ne shine naga idan mutum yana tare da azzalumai gwanda ya fita harkarsu kawai. Saboda haka batun ni in kawo kwali na a bani aiki bai taso ba. Aikin gwamnati mu barwa masu takama da gwamnatin mu kuma mu kama Allah mu dogara da kanmu".
"Anya Khadi ba za ki bar zan cen nan ba. Kowa ma ai da Allah ya dogara".
"Na dai ji mu bar wan nan zancen mu koma kan wanda ya dame mu. Noma da kiwo zamu koma. Baffa yace in gaya maka ya baka fadamarsa ta kauyen gurjiya ka kuma san shinkafa ake a wajen. Saboda haka tun da Allah ya hore maka ilmin noman zamani sai ka yi amfanin da ilmin da Allah ya baka ka habaka noman ka. Ni kuma bayan gidan awaki zan zuba. Baffa yace zai hada mu da wadanda suke saye zuwa kudu. Zan kuma ci gaba da saka ta yadda na saba saboda kunji kunjin tsakar gida. Amma aikin daga ni har kai ba mai yinsa".
Shi ma kuwa yayi na'am da wan nan shawara ta ta.
Haka suka tsara rayuwarsu suka dukufa noma da kiwo da kuma 'yan sana'oin da za su rufa musu asiri.
Kuma Alhamdu Lillah asirin nasu ya rufu.
[8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA👪 IN FIKI MIKI💑
Page 6
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Ita dai Khadija da Mallam Usman sun samu nasarar tsara rayuwarsu ba tare da dogaro da aikin gwammnati ba. A yayin da shi kuma Dr Abdullahi yake ta samu nasara a fannin aikin nasa.
Ita ma Hajiya Rumaisa watau matarsa kuma uwar goyon Zainab itan ma tana samun ci gaba a fannin aikin nata.
Zainab ce dai take samun ci gaban me hakan rijiya. Tana dada girma wahala na karuwa a kanta.
A sunan itace babba momi ta dora mata gyaran dakinsu da kuma wankin bandakinsu kafin su tafi makaranta.
Hakan ya sanya kullum sai ta makara. Ai da farkon zuwanta da yake bata makara tana da kokari a makaranta. Amma daga baya da zuwan nata daukar karatu ya fara zama mai dadash dash sai ta ja baya.
Hakan ya faru ne saboda dokar da momi ta bayar ta cewar duk wanda ya haura bakwai da minti ashirin baya cikin school bus to driver yaja ya tafi.
Tun hudu take tashi. Ta sawa kowa abincin lunch box amma ban da ita. Saboda sau daya tayi zawo, Mummy ta yanke hukuncin wai cikin ta ba ya san kayan zaki.
Saboda haka dan lemon makaranta da kuma su biskit da dan chocolate duk a haka tayi wayon haramta mata su.
Uniform din kannenta da kuma na su Anti Sakina da suke manyan 'yan secondary tun dare take fitowa da kowa nasa. Ta dora su singlet da socks da kuma vest akai. Kowa ta jera nasa. Amma idan su Sakina suka ga dama sai sun zo sakawa suce ta sake goge musu da iron.
Ta jira 'yan mantan su yi wanka. San nan tayi wa kananan maza guda biyu ta shirya su.
Ta dawo ta gyara gadajen da bata da ikon hawa. San nan ta wanke toilet. Ta jika inner wears da suka cire da sunan idan ta dawo ta wanke su.
Kuma duk haka ba zai yiwuba sai sun gama shiryawa sun fice daga dakin.
Amma duk hanzarinta kafin ta gama sai dai taji tashin motarsu sun tafi sun barta.
Kafin term biyu kuwa ta koma jakar aji.
Da Momy ta ga ta samu nasara a haka sai kuma ta kirkiro dabarar kyautatawa ga wadanda suka ci jarrabawa.
Ko kayan sallah za'a dinka maka sai kaci jarrabawa.
Ita ta cusawa Daddynsu wan nan akidar. Kuma saboda salon yaudara irin tata sai ta nuna masa saboda Zainab ta kirkiri yin hakan ko zata zuciya ta dago.
Shi kuwa ya yarda da hakan.
A wan nan term din ma sun kawo report dinsu. Farida da Farisa kamar ko yaushe Farida first, Farisa kuma second. Ita kuwa ta dauko ajin gaba daya.
Daddy fada yake yi kamar zai ari baki. Momy tayi saurin tare shi da cewar "ka dinga hakuri daddyn Farida. Ka san kowa da irin yanayinsa".
"Wanne irin yanayi"? Ya fada cikin muryar fadar. Sauran kannenta su kai biyu garesu da suke iya daukar karatu ita bata dauka. Ai in dai haka zaki yi nikuwa ba zamu shirya dake ba". Ya fada yana mai wurga mata report card din ta.
Da yake shi a boko ya samu tasa nasarar gani yake yi idan dai ba boko kayi ba to kuwa baka da wata madafa.
Ya yanke shawarar dauko lesson teacher, amma shima sai dai sauran kannenta su mora. Amma ita sai Momi tace wai Farida ta koya mata. Ita kuma ta kora ta kicin ko kuma ta sata gyaran dakinta ko dai wani aiki na tsakar dare.
Idan kuma Faridan ta dage da niyyar koya mata, uwar ta hana ta. Ta kora ta tace ta je ta ci gaba nata karatun.
A lokacin da Momi ta sake haihuwa ta samu twins dinta. Halim da Hanif shi ke nan abu ya dada jagulewa Zainab. Duka duka a lokacin sherarta goma, amma hatta kwana da jinjirayen nan ita take yi.
Uwar ta dira su kan shan madara. Hakan tasa Zainab ta koma kamar uwarsu.
Ga su da dan banzan kukan dare haka take fama kwana rarrashinsu.
Da safa kuma ta dora da hidimar yayyensu guda uku da kuma ta unties din su guda biyu.
Saboda haka a dan lokutan da ta samu ta leka makarantar ma , bacci take yi a lokacin ajin.
Malaman sun yi punishment har sun gaji. Don ko sata akayi ta tsaya da sunan horo tsaf Zainabun ka zata iya bacci a tsayen da take.
Sau biyu tana reapeating class three da four. Suma kuma kyale ta kawai akayi ta wuce ba don taci ba.
Tana da shekara sha daya da rabi aka yi common entrance ta makarantar gwamnati. Ita din ma faduwa tayi.
Farida Farisa kuwa da kaninsu sai prizes suke amsows a makaranta. Haka nan isalamiyyar itama sai dai sauki.
A gida suke karatun Mallam maigadin su shi yake biya musu. Idan ta tashi zuwa sai Momi ta hado ta da su Halim a zummar basa yadda da kowa sai ita.
Kuma hakan ne tunda ita suka budi ido suka saba gani tana hidima da su.
Uwarsu ko kwana nawa zatayi bata nan bai dame su ba. Amma ita Zainab kullum suna nanike a jikinta.
Fadan wannan term din yafi na kowanne term. Saboda hukumar makaranta dai tace sai dai Zainab ta sake reapeatin class five, amma su ba za su barta ta tafi secondary ba.
Daddy kuma yace ya gaji da asarar kudin makaranta a kanta. Tun da ita kowanne aji sai ta maimaita shi san nan ta wuce.
Ita dai tana tsugunne sai kuka take yi.
Momi na budar baki tace "kaga Daddyn Farida ba fa laifinta bane. Ka san shi kokarin yaron daga nonon uwarsa yake shansa. Ba ka ganin sauran kannenta. Ka yi hakuri its not her fault".
"Yanzu kina nufin haka zan zauna ina asarar kudi na a banza".
"Eh to kaima kana da gaskiya. Amma abin da za a yi. Kaga stantard din makarantar su Farida yayi mata tsauri. Abin da za a yi ka dawo da ita islamic school din kasan unguwar nan. Sai a samo mata lesson teacher. Idan ta dan ware sai a mayar da ita".
Ha kan kuwa akayi. Ta dawo makarantar islamiyya ta gwamnati ta nan bangaren masu karamin karfi a nan unguwarsu.
Ita ta samuta huta da fadan babanta shi kuma ya daina asarar school fees.
Kuma dadinta da makaranta tara ake shiga a taso sha biyu.
Sai hakan yayi mata daidai da schedules dinta.
A hankali ma gyaran gidan gaba daya ya koma kanta tunda bata fita da wuri.
Idan ta dawo kuma ta dora da renon kannenta.
A hankali kuma Momi ta fara dora mata larurar girkin gidan. Shi ma kuwa ba a fi shekara da farawa ba tukunyar gidan ta zama tata.
Baba larai matar Mallam watau mai gadin gidansu ita ke taya ta da wanke wanke da kuma sharar waje.
Itama sai ta fi samun sauki a haka.
Kafin a kai haka ai ta sha bulala a wajen babanta. Amma yanzu kalau suke zaune. Ba ya yi mata fada da yawa balle a kai ga duka.
Balle da ke tayi ma kanta horon yi nayi, bari na bari.
Dama Farisa ita ta fi janyo mata duka. Ita ma kuma da ke ta gano yanda zata zauna da ita sai ta samu lafiya. Duk abin da tayi mata ko zagi ko rashin kunya ko kuma ta bata mata kaya bata kula ta sai dai ta gyara ta kyaleta.
[8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧IN FIKI A MIJI 💑
page 7
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haka nan Zainab ta dinga rayuwa cikin ukubar kannenta da kuma momi wacce ita ke zuga uban.
Da abin da ya isa da wanda bai kai ba sai tayi ta zuga shi yana dukan baiwar Allah nan.
Wani abin tausayi da ya taba faruwa. Sakina ce ta tashi tana holon bata ga dan kunnenta na gwal ba.
Bayan kuma ta ajiye shi a gefen kayanta.
Bayan nan ne kuma Zainab tazo raba kayan guga. Inda ta sa na kowa a inda yake ta kuma hada da gyara musu zaman kayan nasu.
Ita dai tana baya tana malmala tuwon da ta gama kwashewa taji kiran Momi da karfi.
Saboda firgita ba ta san sanda ta saki tuwon da kokon suka zube a kasa ba.
Sauri take kamar zata kifa.
Tana isa ta tarar da Momi da kannenta da kuma 'ya'yanta sun keyawe ta.
"Gani Momi" ta fada tana mai durkusuwa gabanta.
Bata ji amsa ba sai saukar mari tare da karajin muryar Momi tana fadin "shegiya barauniya ina kika kai dankunne Sakina"?
"Wallahi Momi ban ga dankunnenta ba".
Cikin muryar kuka take fada. San nan ta juya wajen sauran kannenta tana fadin "don Allah Farida ki gaya mata. Ai bana sata ko. Don Allah ba kullum idan na tsinci kayanku ina nuna muku ba".
Farida ita ta rike ta tana cewa "anti Sakina muje ki sake dubawa".
"A ina zata sake dubawa? Shegiya barauniya. Uwarki ma haka na sha fama da ita da wan nan sacen sacen. Ashe kin gado ta ban sani ba. Amma idan ni kince karya nake miki ai ubanki zai shigo. Shi ya saki ki fadi gaskiya. Kuma zaki ......."
Karar shigowar mota shi ya tsayar da Momi daga maganar data fara. "Yawwa ga shi nan ma ya shigo. Yanzu kya fadi gaskiya".
Daddy kuwa na shigowa ya tarar da su duk sun taru a falonsa. Momi na ganinsa ta fara magana cikin muryar rarrashi tana fadin "ki lura ki gane abin da nake gaya miki. Gidan wani zaki nan da 'yan shekaru kadan. Idan kika ce halin banza zaki dinga yi na dauke dauke wahala zaki sha. Gaba daya 'yan uwanki zasu hada baki su miki karya ne. Duk kansu sun yadda ke kika dauka."
Daddy jin haka ya sanya shi ya dauko dorinar da ya ajiye domin dukan yara a cewarsa amma fa bata taba shan jinin kowa ba sai na Zainab.
Farida na ganin haka ta yi saurin fita daga falon.
Ita kuwa Farisa sai dada fadin "ai idan kin ji duka kya fada" take yi.
Nan Daddy ya sata ta kwanta rub da ciki ya kuwa kafa mata shaidar zai mata bulala ashirin. Kuma ko ya kai sha tara ta sosa to sauran sun zube.
Haka ya dinga zabgar ta kamar ya samu jaki.
Yana cikinn ta sha takwas sai ga Farida ta shigo a guje tana fadin "Daddy tsaya gashi na tsinto shi a kit din Anti Sakina ashe dama bata da duba da kyau ba".
Momi sai ta shiga salati da tafa hannu tana cewa "yanzu Farida munafuncin da zaki koya ke nan. Ina ce ni da kaina na je na duba kit din ban gan shi ba".
"Mommy kema baki duba da kyau ba. Tun da ni dana je na daga kasan kit na gan shi ya fada ciki".
Bata jira cewar kowa a falon ba ta daga yayarta ta jata zuwa daki. Tsabar azabar dukan da ta sha da kyar ta ke iya daga kafa.
Tayi jinyar ta ta warke. An yi haka da wadansu kwanaki tana baya tana aikin abincin dare. Kar ku dauka ta wani manyanta. A'a duka duka a lokacin shekararta goma sha uku ne kawai.
Kubewa take gurzawa ta miyar daren. Saboda a hankali daga juya min miya zuwa bare min magi ta koma daura kaza ki sauke a gidan.
Su kuwa sauran in ban da karatu ba abin da Momi take barinsu suyi. Shigarta islamiyyar unguwarsu ne ya sanya ta ke kokarin kamo su a na Islama. Amma boko kam ya bi ruwa.
Ko wasikar kirki da kyar zata iya rubuta maka da hausa balle English da sai dai idan tana aiki a falo ta ji a nayi a TV ko kuma sauran mutan gidan idan suna yi a tsakaninsu.
Babu wanda zai ga yanayinta ya dauka ubansu daya da su Farida.
A wan nan ranar ta kusa gama wa ke nan sai ga Farisa ta shawo kwana a guje da kekenta. Ta kasa tsayawa sai kan kwanon kubewar nan.
Da ita da keken da kuma mai gugar kubewar gaba daya suka fadi.
Farisa tana daga hannunta sai taga wajen ya dauje. Da gudu ta harba cikin dadi a lokaci guda kuma ta na tsandara ihun kuka kamar wadda aka cirewa ido.
Ita kuwa boyiboyin gidan ba ta ankara da nata ciwon ba. Hankalinta yayi kan kubewar da ta zube.
Tana kokarin kwashe ta daga kan sumuntin data kife taji muryar babanta da karfi yana kwalla mata kira.
Gaba daya jikinta ya dauki bari. Shi ke nan ta san yau sai ta sake shan wata bulalar.
A firgece ta saki kwanon data kwashe kubewar ta nufi falonsa a guje. Tana zuwa bata yi wata wata ba sai kawai ta zube flat a gabansa ta mikar da hannayenta gaba ta rike su a cikin na juna. Jira kawai take taji saukar bulala. Tun da ta san kira biyu ne a tsakaninta da Momi da kuma Daddy.
Ita momi ko zata sata aiki ko zatayi mata fada. Shi kuma Daddy ko zaimata fada ko kuma zai zane ta.
To yau kuwa tunda ta hado su da shalelen gidan Allah ne zai kwace ta a hannunsa.
Shi kansa yadda yaga ta zo ta zube a gabansa tana sauraren duka daga gareshi sai da tausayin ta ya ka mashi.
A hankali ya ce da ita "ta shi Zainabu ba dukanki zan yi ba. Samo ruwan dumi da gishiri ki gogewa Farisa inda taji ciwo".
Gaba daya jikknta bai dai nabari ba. A haka tayi abin da aka sata.
Ga wata sara da Momin ta dora Daddy a kai. Iya cin jarrabawarka iya kyautar da zaka samu kuma ciki har da dinkin sallah.
Saboda haka kusan ko wacce sallah sai dai Farida ta bata kwancen kayanta da ta saka. Gashi ta fita garin jiki haka zata zumbula su wuyan riga na zamewa ko skirt buhubuhu a jikknta yana jan kasa.
A wan nan sallah Daddinsu ya hada su gaba daya suka je kera domin su gai da 'yan uwa da kuma kakanninsu.
Gaba daya yadda kakannin suka ga Zainab bai musu dadi ba
Ta zama wata 'yar tsurut da ita. Gata kamar ko yaushe a firgice take.
Tun da suka je kakarsu na hankalce da su. Ko kaya zasu saka ita zata fitowa da kowa nasa ta jera musu. Ta kwashe wanda suka cire ta wanke ta shanya . Halem da Hanif kuwa har abada daya na goye a bayanta. Gasu da wata irin kiba kamar mai tallan michelin.
Amma haka nan tutur take fama da su. Ita ba me aure ba amma tafi matar aure hidimar gida da kuma wahalar yara.
Kwana hudu kawai suka yi Momi da Daddy suka zo daukarsu.
Suna falon mahaifiyarsa suna gaisawa inda a anan baban Daddy ya shigo ya iske su.
Mahaifiyarsa ta kalleshi tace "Dacta ina son ka lura da wani abu idan ita Rumaisa ba ita ta haifi Zainabu ba kai kai ne mahaifinta. Amma ka kasa yi mata riko irin wanda kake yiwa sauran 'ya'yanka".
"Hajiya wani abu tace an yi mata"?
"Yo wan nan yarinya sai tace an mata. Ai duk mai hankali idan ya dubi yanayinta zai san a kuntace take rayuwa".
Nan Momi ta shiga matse hawaye tana fadin "ni dai Allah ne shaidata yadda nake rike su Farida haka na ke rike da ita".
"Wayyo Rumaisa share hawayenki ba yan zu ne lokacin yin sa ba. Ki dai tuna zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. Nawa aka yi kafin wan nan kuma duk munga inda suka bulle.
Yarinya gaba daya bayanta a zane kamar jikin alfadari, amma kuce wai ba abin da kuke mata. To wallahi kaji na rantse maka idan ka sake kai hannu da sunan dukan Zainabu ban yafe maka ba".
Daga nan kuwa bata sake magana ba ta shige uwar daki.
Nan dai baban Dr watau Baffan Nene ya saka su a gaba duk su biyun da nasiha. Ita dai Momi har a wan nan lokaci tana ikirarin ba abin da take mata.
Tun da suka dawo kuwa ta dora Daddy akan hana su zuwa kauye saboda a nan ake son lalata masa zaman gidansa a cewarta.
Zainab dai bata samu karatun ta ya hau turba ba sai da Halim da Hanif suka shiga makaranta. Suma kuma ba sa tasowa sai biyar saboda har islamiyya a makarantar suke.
Sai schedule dinta yayi mata daidai. Da safe ta yi breakfast ta shirya 'yan makaranta. Bayan sun fita ta gyara gida. Idan ta taso sha biyu ta wanke kananan kayansu da ta jika ta kuma yi manyan ayyuka.
Abincin rana an soke yinsa a gidan. Saboda iyayen ma'aikata ne suma sai wajen shida suke dawowa.
Daga baya Momi ta tura ta wajen wata kawarta ta koyo yin snacks. Shi ke nan ita momi ta fara sana'ar yin na sayarwa.
Saboda haka tun bayan sallar azahar yarin yar nan zata fara tumurmusar flour.
Ko ta na dani samaosa da spring rolls ko tana murjin meatpie ko kuma tana kwabin cake.
Ga shi Alhamdu Lillah Momi na samun kasuwa ita kuwa Zainab tana ji a jikinta.
Ita zata je kasuwa ta sayo kayan aiki ta murza ta soya ko ta kwaba ta gasa ita kuwa uwar dakin sai dai ta caski kudi.
Amma duk da haka ko ladan aiki bata samu. Saboda ko da sallah ko irin Allah ya isa tallana ba zata samu a dinka mata ba. Sai dai kannenta su bata kwancen nasu.
[8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧IN FIKI A MIJI💑
page 8
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haka nan rayuwar Zainab ta ci gaba da kasancewa. Momi ta rabata da uwarta ta cusa rashin jituwa tsakanin ta da mahaifinta ta kuma raba ta da sauran dangi.
Bata shaku da kowa ba sai dai aikinta da kuma baba Laure matar Mallam mai gadinsu.
Dakuna shida ne a gidan kowanne da bandakinsa ga kuma falo uku. Amma kullum sai ta share na sharewa ta kuma wanke na wankewa. San nan ta bi ko ina ta goge.
Idan Farida ta nuna kokarin taimaka mata yanzu uwar zata kora ta akan maza ta koma kan karatunta.
Saboda haka daga 'yanmatan gidan anti Sakina da anti Bilki zuwa kannenta Farida, Farisa, Khalil, Halim da Hanif ba wanda zai iya rayuwa idan bata taimaka masa ba.
Ko kayan sawarsu ba su iya tsarawa ba sai ta hada musu.
Kusan ko yaushe ka ganta a cikin wata hidima take. Kullum ita ke karshen kwanciya misalin sha dayan dare kuma dole ta tashi hudu.
Jikinta ya saba da wahala. To ita da haka suka kyale ta ma ba kyara da hantara da kuma cin mutunci da ta ji dadi.
Inda kawai take samun sauki wajen Farida da kuma Anti Bilki. Amma sauran sai dai wahala. Su din ma suna sata ayyuka amma ba cin mutunci da wulakanci. Kuma sukan yi hirar arziki da ita.
Inda ta dada tantance matsayinta a gidan wata rana ne tana kwashe tuwon semo. Khalil yana zuwa ya sa cokali ya debo tuwon nan ya bude rigarta ya sakar mata shi a ciki.
Habawa! Ba ta san sanda ta mike cikin jin zafi ba tana ta rawar radadin zafin tuwon da ke kona ta a gadon bayanta.
Haka ta dinga rawa da tsalle saboda zafin da take ji.
Su kuwa sauran yaran sai dariya suke ta tintsira mata. Bayan nan ya dade yayi ja, abinka da farin mutum.
Nan aka mai da abin wasa. Kuma har da Momi a wajen. Itama sai ta kulli aniyar ramawa tun da taga wasane.
Sai ta sayo rayuwar ruwa a makarantarsu. Wasu animals ne da objects na roba. Idan ka siyo shi yana karami. Kana jika shi a ruwa sai ya yi ta shan ruwa yana kumbura.
Ta san shi da tsoron kadangare sai ta sayo mai suffar kadangare ta jika shi wajen kwana uku. Yayi girma sosai kamar kadangaren gaske. Ta lallaba ta wurga masa cikin jakar makarantar sa.
Yana zazzago litattafansa habawa yayi arba da katon jan gwala gwada ya fado.
Tsalle ya daka da ihu a lokaci guda.
Su Momi duk a ka yo kansa. Shi kuwa kamar zai shide sai nuna musu kadangare yake yi.
Zainab tasa hannu ta dauke shi tana fadin "nima na rama"
Wani irin barin makauniya Momi ta rufe ta da shi. Tana dukanta tana fadin "shegiya tsinanniya mayya. Kashe min da zaki yi"?
Tana zaginta tana duka a lokaci daya. Farisa da Khalil kuwa sai dariya suke.
Sai da tayi mata lilis san nan ta tsallake ta ta barta a wajen.
Khalili ya kalle ta ya mata gwalo yana cewa "gobe ma ki kara tabani sai na sa Momi ta yi miki duka banza boyi boyin gidanmu".
Tun daga wan nan lokaci ta dada janye jikinta daga garesu. Saboda kome suke so idan taki yi musu yanzu zaka ji suna fadin "ko yi ta girma da arziki ko yanzu musa kuka . Kin kuma san idan mun digar da hawaye digo daya ko na karya ne sai kin zubar da cikin jug na gaske".
Sai ya zamana bata da wani da take mu'amala daxshi a cikin gidan idan ba baba Laure ba.
Ita ma din kuma Mallam mai gadin su ne ya dora mata nauyin kula da Zainab. Saboda ya lura da taken taken matar gidan so take ta watsa rayuwar yarinyar nan gaba daya.
Ba abin da ya dameta da tarbiyarta. Za ta iya aikenta shago siyo abu komai dare ba abin da ya dameta. Kasuwa kuwa ko wacce iri ce turata takeyi kuma da kashedin lalle ta samo araha.
Mallam sai ya fassara hakan da taken taken lalata rayuwarta. Shi ma kuma sai ya dauki aniyar tsaya wa a kan lamuranta.
Shi ya hana ta fita da daddare. Idan an aiketa ya ja mata kunne kar ya kara ganinta taje shago shi ta ba shi ya sayo mata.
Lokuta da dama kuma da uwar take tura ta kasuwa sai ya tabbatar da matarsa suka tafi. Balle da suka yi sa'a ba yini suke a gida ba.
Haka zalika ya dorawa matarsa larurar kula da tarbiyyar yarinyar tare da nusar da ita harkokin da suka danganci tarbiyarta.
First period dinta ita ta nuna mata yadda zata kula da kanta.
A wata rana mallam yazo wucewa sai ya ganta ta kawowa direban gidan abinci. Shi kuma ya rike hannu ta yana mata wasa. Yana cewa "zo nan matata. Zo ki bani a baki in koya miki wasan masoya. Kin san Momi ta ce ni zaki aura".
Dama kullum haka Momin take gaya mata cewar tun da ta ki karatu sai dai ta auri Sale direban gidan.
Kuma inda zaka san da gaske take. Ita ta dora mata dokar duk sanda ta gama abinci ta kai masa dakinsa.
A wan nan ranar da Mallam yaji kalamansa ba karamin tashin hankali ya shiga ba.
Da fushinsa ya karasa wajensa yace "sakar mata hannu karamin shakiyyi".
Ba shiri ya saki hannunta cikin tsoro. Ko ba komai yana shayin mallam mai gadi saboda yana kallon mai gidan ma ko bukatarsa ta tashi a wajen aiki wajen Mallam yake zuwa ya taimaka masa da addu'a. Gashi kullum ka ganshi da Qur'ani a hannunsa yana karatu ko kuma wani littafin addini. Hakan yasa yake masa kwarjini.
Mallam ya juya ya kalleta ya daka mata tsawa yace "me ya kawoki dakinsa"?
Cikin tsoro da rawar murya tace "momi ce tace in kawo masa abinci".
Ya dan sassauta muryarsa cikin tausayin yarinyar yace "daga yau ki dinga ajiye masa a bakin baranda kar ki sake zuwa dakinsa".
"ToMallam "ta fada da saurinta. San nan ta juya ta wuce cikin gida. Sai da yaga ta shige san nan ya juya wajen Sale yace "kai kuma naga take taken ka. Ta ka saurareni da kyau. Na rantse da girman Ubangiji idan ka kara taba yarinyar nan ni kuma na maka alkawarin kai da mace a duniya har abada. Network naka zan dauke gaba daya. Idan kana ganin karya nake ka gwada ka gani".
Kwarai Sale ya tsorata da barazanar Mallam. Saboda haka ya kashe wan nan boss din.
Ita kuma Baba Laure ta shiga nusar da ita duk abin da ya kamata diya mace ta sani a rayuwarta.
Allah ya basu hahihuwar yara biyu duk maza. Basu samu mace ba, sai suka mai da ita kamar 'yarsu. Ita ma kuma haka ta mai da su makwafin da iyayen da Momi ta hanata ba don Allah ya raba ta da su ba.
Kawarta daya a islamiyya Fatima. A nan bayan layinsu take. Su ba masu sukuni bane domin babanta masinja ne a kotu yayin da babarta take awara. Amma ita take taimaka mata. Ita take bata abincin break.
Ba tare data sanar da ita komai ba ta fahimci halin kuncin da ta ke ciki a gidansu.
Ba ta cika zuwan gidan ba sai ta tabbatar momi da ahalinta ba sa nan.
A haka rayuwarta ta ci gaba har suka fara zama 'yanmata ita da sauran kannenta.
[8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧IN FIKI A MIJI💑
Page 9
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A haka Zainab ta dinga cukurkudar rayuwarta. Ta koma baiwa a gidan ubanta. Ta samawa kanta lafiya ta zama mai hakurin dole. Idan an sakata tayi. Idan ance tayi laifi ta bada hakuri komai gaskiyarta.
Tayi developing wani robotic attitude a rayuwarta. Bata da ra'ayi sai na 'yan gidan. Abin da duk suke so haka take biye musu.
Amma duk da haka bata tsira daga masifa da kuma kyarar Momi ba. Abin da bata sani ba Momi hassada take yi da baiwar kyau da Allah yayi mata.
A yanzu ne ma ta daina aske mata gashin ta. Da bini bini zata dauki almakashi ta mai da mata shi saisaye a sunan wai taga kwarkwata aciki.
Amma gashin nan da yake ba shi da zuciya bashi sati uku zuwa hudu zaka sake ganinsa kwance lamban a gadon bayanta. Gashi baki mailaushi gaske.
A haka kuma ba gyara ya ke samu ba. Da kyar take iya shafa masa vaseline sau daya a wata. Shima Baba Laure ce ta sanya mata dokar duk sanda zata yi wankan tsarkin al'ada ta tabbatar ta tsefe shi ta wanke da sabulu.
Suna fara zama 'yanmata kuwa surar jikinta ta nuna mai kyawu ce lamba daya. Fuskarta kuwa dama tun da ta taso kasan kyakkyawa ce.
Ba abin da ya rabata da mahaifiyarta har hasken fatarsu iri daya ne. Wan nan kyau nata shi ke dada bata ran momi.
Kar kuma ku dauka nata basu da kyan. Suma kyawawa ne bama ya Farisa da ta ke fara kal. Ita ma kuma Farida kamarsu daya sai dai haskenta bai karasa na Farisa ba. Zasuyi kala daya da Zainab. Sai dai ita kuma jikinta ne ba mai kyau ba saboda she is busty.
Amma zamani na gayu. Da yake kuma ta iya parking din su da kyau sai suka zama abin sha'awa.
Ita kuwa borar 'ya'ya ba ma wanda yake tunawa da saya mata undies. Jikin ne Allah ya sanya ya zama mai tsayawa da kansa. Sam bata bukatar sanya bra. Skirt ne da pant idan sun bata ta zubar ta zabi masu dan dama dama.
Shi ma idan Farisa taso wulakanci tayi kararta wajen Momi akan ta satar mata undies. Hakan kuma ba zai sa Momin tayi tunanin sai mata ba sai da ta ci dan banzan duka Farisa kuma ta yi ta dariyar jin dadi.
Tana da shekara sha bakwai Farida na sha shida Farisa kuma bata karasa sha biyar ba suka yi kandi.
Anti sakina da anti Bilki kuwa kannen Momi lokacin suna BUK 300 level. A lokacin ne kuma suka tsayar da samarin da suke so. Anti Bilki ta samu Sulaiman mai aiki da wani attajiri da ke da kamfanin yin atamfofi a China. Yayin da Anti Sakina ta hadu da Kabir. Shi kuma ma'aikaci ne a DPR.
Tun da kuwa suka samu samarin da suke so sai dawainiya ta karar wa Zainabu.
Ga shi yanzu sun shiga ajin sauka a islamiyya. Saboda haka basa tasowa sai uku da rabi. Kuma ya zama dole bayan ta girka abincin dare ta bata lokacin wajen yi wa samarin aunties dinta better na musamman. Ta gyara falon baki inda suke zama. Bayan nan ta kashe lokaci wajen yi musu kwalliya da daurin dan kwali.
Haduwarta da Fatima ya sanya ta koyi abubuwan gayu kamar su make up dauri da kums lalle. Har da gyaran jiki.
Da wajen babar Fatiman suke zuwa lalle da gyaran jiki. Dan raka sun da take yi sai itama ta koya. Shi ke nan kuwa suka daina zuwa ko'ina.
Ita ke musu komai. Amma fa ita bata da lokacin yiwa kanta. Hatta gyaran farce ita take zama tayi musu.
Mahaifinta dai duk yadda Momi zata yi ta sa shi yaga bakin ta ta iya.
Idan har yana gida zata saka Farida ko Farisa wani a cikinsu ya hada masa abincinsa a dining. Wacce ta girka daban amma mai serving ita ake nunawa uban ita ta girka.
A hankali sai da ta sa yayi mata shaidar hatta aikin gida kiwa take masa.
Bari Momi take bayan ta saka ta ta gyara dakinsa da su bandaki ta wanke. Sai an daidaici ya kusa shigowa sai a tura 'yan gata da turaren wuta su saka masa.
Za kuma a tabbatar ya gansu saboda ya yarda su suke hidimarsa. Yayi ta jin dadi yana sa musu slbarka.
Ita kuwa tsakaninsu sai dai zagi da fada.
Kuma ko waye zai ji haushinta.
Ke ba karatu ba kuma ke ba aikin gida ba ai dole uba yaji haushi.
Baba Laure da Mallam sai kuma Mama Hajjo watau mahaifiyar Kawarta Fatima su ka dai ne a tsaye a lamarinta. Ko pad idan wani a cikinsu bai sayamata ba to kuwa sai dai tayi amfani da tsumma.
Ana haka auren Sakina Da Bilki ya tashi. Daddy shi yayi musu komai na 'yan gata.
Zainab ta samu an dinka ankon bikin da ita. Kwatsam sai ga kawar Farisa ta zo daga Lagos ziyarar gidan uncle dinta. Nan kuwa Momi ta karbe ankon Zainab aka bawa bakuwar Farisa.
Kaf snacks din da aka ci a bikin nan da kuma wanda aka kaiwa amare gidansu ita tayi shi.
Duk da bata da anko. Ranar dinner ta ci kwalliyarta da less din da Farida ta bata. A keken Mama Hajjo ta gyara rigar da skirt din suka dawo size dinta. Saboda tsabar karbar kunce kamar sai da takoyi gyara a dole.
Ko ita Fatiman da keken dinkin ke gidansu bata iya dinki kamar Zainab ba.
Ga dai babarta Mama Hajjo mai ciniki goma ce.
Banda awara tana gyaran jiki da lalle tana kuma taba dinki. Amma ita Fatu kamar yadda suka fi kiranta da shi a gidan bata damu da ta koya ba.
Kawancen su da Zainab ta fara tabawa saboda ganin ita Zainab din ta dage tana yi.
To a wan nan rana itama ta ci kwalliyarta da kwancen da aka bata. Tana ta sauri ta biya ma Fatu su tafi tare.
A barandar fita waje Momi ta hadu da ita.
"Ina zaki je"? Ta tambayeta a wulakance.
"Mh gidan party". Itama ta amsa mata a tsorace.
"Idan kin tafi party uwar waye zata gyara gidan "?
Shiru bata amsa mata ba. "Come on juya ki je ki tattare gidan nan kafin in hada miki gajiya".
Kafin ma ta dire maganarta ta juya da sauri ta koma ciki.
Kaf gidan nan sai da share kowanne daki ta goge ta kuma wanke ban dakinsa da falukan gidan.
Ita kanta Baba Laure bata san Momi ta hana ta zuwa ba da kuwa ba za ta tafi a motar farko ba. To ita ta tsaya sai da ta yiwa sauran 'yan matan kwalliya san nan ta shirya.
Bayan ta gama tattaro ciki ta dawo kicin shima ta gyara ko ina nasa san nan ta dumfari wanke wanke.
Ta wanke plate da kofuna sama da dari biyar.
Tun da farko tukwanen da akayi girki ta fara jikawa.
Bayan ta goge plate da kofuna da kuma cokula ta maidasu ma zauninsu, sai ta dawo kan kuloli. Suma sun kai goma runduma runduma kamar za a sata a ciki. Haka ta wanke su ta kife.
Ta dawo kan tukwane suma ta dirje su tas. Tun misali tara na dare tafara aikin nan har shabiyu saura kwata bata gama.
Nan suka dawo suka tarar da ita tana kokarin share wajen da tayi wanke wanke.
Suna shigowa suka ganta jakwane jakwane da ita sai Farisa ta tuntsire da dariya tana fadin "wu kallo ya bar wata yarinya. Mun je dinner mun more boyi boyi tana wanke wanke".
Ita dai bata kula ta ba. Ganin ma zata takura mata data gama sai kawai ta dauki zanin baba laure dake rataye a igiya ta cire kayan jikinta ta shanya su ta lulluba da hijabinta tayi kwanciyarta a sito din kicin din.
[8/6, 23:14] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👨👧IN FIKI A MIJI
Page 10
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Washe garin biki aka kai amare. Bilki matar Sulaiman gidansu yana Ribado road. Yayin da anti Sakina ke karkasara.
A tunanin Zainab raguwar yaran gidan zai sanya aiki ya ragar mata, amma ina sai ma kari data samu.
Ga shi dai kowacce da mai aiki aka kaita, amma hakan bai sa sun rangwantawa Zainab ba.
Kullum tana zaryar hanyar gidajensu. Daga baya ma Momi ta saka mata dokar idan gari ya waye ta yi kokari ta gama gyaran gidansu san nan ta wuce zuwa nasu gidajen ta zauna kar ta dawo sai biyar na yamma.
Tayi kukan takaicin rasa karatun ta na islamiyya gashi sun shiga ajin sauka. Baba Laure ce ta kwantar mata da hankali akan tayi hakuri ta bi yadda aka sata. Allah yana tare da ita. Ta kuma karfafa mata gwuiwa da fadin idan ta dawo sai baba Maigadi ya dora mata.
Allah cikin ikonsa sai ma kuma wani sauki ya billo mata.
Ganin idan taje ma kusan kullum ta kan samu aunts din nata ba su tashi ba. Sai da daina zuwa sai ta tashi daga karatun safe wanda take tashi sha biyu.
Daga nan sai ta hau dan sahu ta wuce karkasara. Za kuma tayi kokari duk abin da zatayi mata zata gama shi kafin karfe biyu.
Tana yi azahar sai ta wuce gidan Bilki.Ita kuma idan tayi la'asar sai ta dawo gida ta fara hidimar abincin dare kafin masu gidan su dawo.
Haka ta koma kullum tana hanya. Shi uncle Sulaiman da ya ke a kamfanin wani babban dan kasuwa yake aiki a matsayin accountant dinsa. Goma na safe ya ke fita ya dawo biyar na yamma. Da safe matar zata lallaba ta sama masa shayi da burodi.
Amma abin mamaki idan ya dawo zai tarar da abinci mai rai da lafiya an ajiye na rana ga kuma na dare shima lafiyayye da shi.
Bai kuma cika haduwa da ita a gidan ba. Saboda ranar jumma 'a ne kawai da yake dawowa zuwa masallaci ya kan hadu da ita.
Shi kuwa mijin Sakina Kabir yana DPR.
Shi ma dai bai san sirrin matarsa ba ya dauka ita ke zankado masa hadaddun delicious din da yake diba.
Domin ko dakunan mazajensu sai ta zo zata gyara ta sa musu turaren wuta ta wanke bandakunan tas.
Ga shi har injin wanki a saya musu amma sai dai ita ta hada wankin ta zuba masa ko kuma idan ta zo ta tafi da kayan gugarsu gida. Idan kuma an goge ta dawo dasu ta shirya kowanne a inda ya dace. Idan kuwa ba ita tayi ba, to kuwa sai dai kayan su zauna haka.
'Yan boko ne na karshe amma fa ba abinda suka iya a domestic responsibilities dinsu.
Su kuwa sauran kannenta ko da sun kaiwa aunties nasu ziyara su tarar aiki kamar zai kasheta to ba abin da zasu kama mata da dashi.
Haka nan ta zama kamar machine kullum cikin hidimar kannen mominta take.
Gwanda ma anti Bilki ita da mijinta suna da kirki. Amma Anti Sakina ba abin da ta rage na wulakanci da
kuma toxarta Zainab. Ga mijin nata wani irin wawa mai barin zance.
Haka nan tana ji tana gani sauran 'yan ajinsu sukayi sauka banda ita.
Saboda tana zuwa normal lesson amma karatun rana na mura'ja ar saukar bata zuwa saboda hidimar amare da ta hau kanta.
Da suka samu ciki kuwa sai komai ya dada kacame mata. Hidimar ta karu mata.
Hakan kuma bai sanya Momi ta rage mata hidimar gidansu ba.
Dole tayi na safe ta kuma gyara gida. San nan ta tafi wajen su Sakina. Suna da masu aiki amma ba za su iya tsayawaa a kansu su yi abin da ya kamata ba.
That is idan ma sun san abin da ya kamata su yi din su da kansu. Sai Zainab tazo. Anti Sakina ce ta fara haihuwa. Saboda haka kacokam Zainab ta koma gidan da zama. Saboda kusan kowa na gidansu a nan yake yini. Amma fa ba abin da suke yi sai dai zaman hira da kuma zan ci kaza zan sha kaza. Ita kuwa tayi ta fama da dafawa da kaiwa da kwashe kayan da aka yi smfsni da su.
Wata rana tana tsaka da wankin toilet din Uncle KB ashe ya shigo gida bata sani ba.
Hijabinta na rataye kan murfin kofa jikinta sanya da skirt da riga sun yi mata das a figure 8 dinta kawai taji an banko kofar tailet din.
A tsorace ta juyo domin ganin waye.
Tana ganin Kb ta dafe kirjinta cikin sakin ajiyar zuciya tace "wai uncle ka bani tsoro".
Wani irin yawu ya hadiya makwat san nan yace "amma an dade ana boye kyawawan kaya a nan. Dama haka kike da kyau shine kike nade jikinki a wan nan yadi marar kyan gani. Bala'i gaskiya an zuba kyau a anan".
Bata rai tayi ta sha kumu. A iya saninta babu wasa tsakaninsu tunda ita ba kanwar matarsa bace. Hannun ta mika zata jawo hijabinta yayi saurin dauke shi yana fadin "kin ci karya yarinya. Ai ba zan sake yarda ki rufe min wan nan blockbusyer din da na samu an yi realeasing dinsa a yau ba".
Kamar zata yi kuka take masa magiyar ya bata hijabinta. Ya nade shi a hannunsa sai ma matarsa da ya shiga kira.
"Sakina zo ki gani".
Da sauri ta karaso inda suke. Ganin su a haka ya sa taji ranta ya baci saboda macece mai tsananin kishi. Ga mijin nata kuma da shegen son mata. Muryarsa ce ta katse ta yana fadin "taimaka min ki bani 'yarki in aura ni kuwa na yi miki alkawarin na daina zuwa ko ina daga wajenki sai nata".
"Kaga Kb bana son irin wadan nan stuid jokes din naka".
"You think iam jocking. Ai ba namiin da zai yi wasa a neman mace irin Zainab. Da gaske na ke yi miki. Kin ga kin huta da yawona ni kuma in huta da mitar ki na ina neman matan banza".
"Ke get out of here kafin in babbalaki" ta fadawa Zainab cike da bacin rai.
Da dan gudunta ta fito daga cikin taoilet tare da rakiyar wani uban fito da Kb ya saki, mai nuna alamun yabawa da abin da ya dada gani.
Bai daddara ba ya sake mai da hankalinsa wajen matarsa yace "yaya do we have a deal? Kara min da ita ni kuma na miki alkawarin na daina yawo".
Bata bashi amsa ba sai ma fizge hijabin da ta yi daga hannunsa ta fita a fusace.
A kicin ta samu Zainab tana tsaye cike da rudani ta wurga mata hijabin ta.
"Don ubanki kama hanya ki bar min gida kafin in canza miki halitta yanzu yanzun nan".
Jiki na bari ta karba ta saka ba tare da tace komai ba.
A kafa ta taka tun daga karkasara har NNDC quarters na Hotoro inda gidansu yake.
[8/6, 23:14] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👨👧👨👧👨👧
IN FIKI A MIJI💑💑💑💑
Page 11
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A gajiye tikis Zainab ta iso gidansu saboda ga gajiyar aiki ga kuma ta hanya da ta sharo ta a kan takalminta.
Amma ganin motar Sakina a gidan ya sanya taji gajiyar tata ta wartsake.
Ta kofar baya ta zaga tana kokarin sulalewa ta gudu dakinsu saboda bata san abin da ya kawo Sakinan gidan ba.
Tana kokarin hawa benen karaf Farisa ta hango ta.
"Momi ga munafuka ta dawo. Na kamata tana kokarin gudu ta buya".
Farisa ta fada cikin daga murya.
Kafin ta gama hada da kuma fassara maganar Farisa sai kawai taji Momi ta rufe ta da duka tana cewa "shegiya tsinanniyar karuwa. Idan tambadewa kike sha'awar yi ba sai kin je kin nemi mijin Sakina ba ki shiga kasuwa da gaske har da kudi zaki samu".
Ranar ta sha duka da zagi. Sabo da daga kafar bene Momi ta jata har falon gidan inda suka zauna ita da 'ya'yanta suka kare mata cin mutunci bana wasa ba.
Ita dai in ban da kuka ba abinda take yi.
Shigowar Halim da baby Amra 'yar wajen Sakinan shi ya katse taratsin masifar da ke saukarwa Zainab.
Sai kuka yarinyar take tsandarawa kamar za a cire mata ido.
"Kai Halim ina ka dauko Amra"?momi ta tambaye shi.
"Uncle KB ne ya kawota yanzun nan yana waje ".
Momi tabayar da umarni a shigo da shi.
Daidai zai shigo Sakina ta dada narkewa ita als dole an cuce ta a bi mata hakkinta. Cikin gatsali ya gai da momin san nan ya juya wajen matarsa yace "ke kuma da kika fito ki ka barta yaya kike son in yi da ita".
Itama cikin tsiwatace "ai na dauka ka samu inda zaka kaita".
Dariya yayi san nan yace "aiwai ke nan yaji kika yo. Wan nan kuma ya rage nake. Dama alfarma zan yi miki saboda korafin da kike min na yawo amma tun da kin fi son haka sai mu ci gaba".
Momi ta katse shi da fadin "yanzu Kabiru a gabana kake fadin irin wadan nan maganganun"?
"Ah to Momi ni meye laifina. Idan dai macen bata kai ta rikeni ba ai ni kuwa zan nemawa kaina mafita. Na ga wanda zata iya rikeni tace ba haka ba sai kuwa tayi hakuri da yadda ta sameni".
Kafin Momi ta gama hadiye mamakinta ya mike yana fadin idan kin sauko kya iya karasawa gida idan kuma kin san ba zaki koma yau ba nima in nemi wajen kwana".
Daga nan bai kara cewa komai ba ya mike yayi tafiyarsa.
Da farko Sakina taso itama ta dan ja ajinta amma Momin ta nuna mata shi wan nan gabon mijin nata sai dai su bi shi a hankali. Saboda ko ba komai akwai shi da sakin hannu. Mutunci ne kawai ba shi da shi.
Haka ta dauki borin kunyarta ta koma. Wan nan abu da ya faru bai kuma sa ta ragewa Zainab duk wata hidima tata ba. Sai dai fa akwai close marking. Duk yadda zata hana Zainab haduwa da Kabiru tana kokarin yi.
Ita ma kuma Zainab din ba son haduwa da shi take ba. Saboda indai zai ganta sai ya yaba wani abu a jikinta.
Ga shi dai a lullube take amma hakan bai hana shi rike memory da ya gani ba.
Ana haka Farida ta samu tafiya Sudan ita da Farisa. Ita Farida ta samu medicine yayin da aka bawa Farisa computer scince. Ita kuwa jakar gidan tana nan.
Shekarar farko da zasuyi sauka zaman gidan Sakinna ya hanata. Bayan wata shida aka sake yaye wasu daliban da suka fadi screening na farko aka basu damar sake maimatawa aka saka da ita shi kuma daddy ya hana ta kudin sauka a dalilin Momi ta ce masa yasayyadin ne saurayinta shi yasa ya saka sunanta amma ba abin data sani.
Haka tana ji tana gani ta sake maimaita wata shekarar.
Ga kawarta Fatu ita har ta samu shiga Legal ita kuwa tana nan tana fama da hidimar Momi da ta su Sakina.
Raguwar 'yan gidan ya dan rage mata aiki balle da su Halim ma sun girma suma ba sa tasowa sai biyar na yamma.
Hakan ya sa Momi ta dada habaka sana'arta ta snacks.
Shekarar su Farida daya a sudan, Momi ta debe duk yarsn gidan suka kai musu ziyara daga nan ta dauke suka karasa Saudiyya suka yi Ummara san nan suka je Turkey da England yawo.
Saboda Momi ta kwashe wajen wata bata gida sai hakan ya bawa Zainab dama shiga wajen Mama Hajjo watau mahaifiyar kawarta Fatima.
A nan ta dada karuwa da darussan rayuwa. Saboda Mama Hajjo macece mai hikima cikin wasa da dariya take nusar da su abin da ya dace da rayuwarsu kamar irin su mu'amala da iyaye da kuma dangin miji da shi kansa saurayin idan an same shi har kuma ya zuwa lokacin da zai zama miji.
Ha ka zalika nan ta sake kwarewa da gyara irin su lalle da halawa da dilka.
Ita kanta ba ta san ta tana da talent na zane ba sai da ta zanawa Fatu lallen rasma idan kagani sai ka dauka a saudiyya aka zani shi.
Haka nan ta ci gaba da kasancewa lokaco lokaci Momi zata debi sauran yaranta har su Bilki dake gidajen mazajensu su kaiwa 'yan sudan ziyara daga nan su wuce yawo kasashen duniya, amma banda Zainab.
Saboda idan ta tafi da ita harkar cinikinta zata tsaya.
Kuma yadda ake cinikin snacks tana nan haka ake yinsa ma in bata nan.
Kusan in bata nan ma kudi sun fi taruwa saboda babu mai ci sabanin idan yaran gidan suna nan.
Sai da su Farida suka dauki tsawon shekara uku a Sudan san nan suka zo hutu saboda IT da za suyi a kasar nan.
Biliki ce ta sake haihuwa ta biyu ke nan. Dukkan su suna gidan. Yan boko na kwance a kujerun falon suna ta latse latsen wayoyinsu yayin da ita kuma take ta kai da kawowa na ganin tsaftar gidan da kuma abincin da za a ci ya kammalu.
Uncle Sulaiman ne ya fito daga dakinsa da hanzari rike da waya yana amsawa a dan firgice yana fadin "gani nan zuwa yallabai".
Sai da ya kashe wayar san nan ya ya juya wajen Bilki yace mata "mai gida na ne ya zo mana barka".
San nan ya fice da hanzarinsa ya shigo da shi.
Yadda suke kwance a kujera ko zaman su ba su gyara ba.
Haka zalika rawar jikin da Sulaiman yakeyi ta kokarin martabar bakon bai shalle su ba.
A yangace kowacce ta dago kai ta kallashi.
San nan aka yi masa gaisuwar ya kake. Shi ma da lafiya kawai ya amsa musu san nan ya mai da hankalinsa wajen gaisuwar ban girman da Bilki da Sulaiman suke masa.
Ita Bilkin ce ta sake mikewa ta shiga kitchen Farida da Farisa su na nan a yadda suke. Sai faman latse latsen waya suke ta faman yi.
Ba ta fi minti biyu da shiga ba Zainab ta shigo falon dauke da dan madaidaici tray wanda ta dora jug da kananan kofuna guda biyu da kuma robar ruwan swan. Sai daga gefe dan side plate ne data rufe da foil paper. Kamar ko da yaushe sanye cikin dogon hijabinta wanda ya kusa rufe idon sawunta.
Cike da natsuwa ta karasa kusa da shi ta jawo side table ta dora tray a kai san nan ta russuna daga gefensa tace "barka da yamma".
Sautin muryarta kawai ya sanya yaji duk wata jijiya ta jikinsa ta amsa. Take adduar da yake korawa baby Musty ta makale a bakinsa.
Da kyar ya daure ya amsa mata da cewa "barka kadai".
Bata lura da yanayinsa ba ta jawo tray gabansa ta zuba masa ruwa a kofi daya dayan kuma ta zuba masa matsattsen lemon zaki san nan ta dan kware gefen side plate din da ta rufe da foil samosa da meat pie suka bayyana.
Wai tas Mallam Al bashir ya manta da azumin litinin da alhamis da yake yi ya kaiwa abincin nan attack saboda kawai ya manta da komai in ban da kyakkyawar fuskar Zainab.
Yatsun hannuta zara zara su suka dada mantar da shi komai sai kokarin shan lemu da ta zuba da su.
Ba tare da ta lura da yanayinsa ba ta mike ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta.
Sai da ya cinye meatpie biyu da samosa uku ya kuma sha lemu kofi biyu san nan ya tuna yau ya dau azumi.
Yaran nan suna kallo tunda bakon nan ya shigo maigidan yake mazari a gabansa amma hakan bai san sun gane darajar da bakon yake da ita ba.
Shi dai Albashir yayi musu barka. Amma fa rabin hankalinsa na ga son sake ganin baiwar Allah nan da ta shayar da shi lemon da bai taba jin mai dadinsa ba a rayuwarsa.
A lokacin da ya shigo masu gidan basu dade da yin lunch ba saboda lokaci ya nuna wajen karfe biyu da rabi.
Zainab tana shiga kitchen tayi sauri ta dora nama da busasshen kifi da stock fish a pressure pot.
Ta dauko kazar gidan gona guda daya ta wanke ta mutssuke ta da kayan kamshi da su maggi ta dora mai ta hau suya ba tare data tafasa ta ba.
Da ta gama da jar suyar ta kwashe ta zuba a food flask.
Zuwa lokacin abin da ta dora a pressure pot ta san ya nuna ta bude ta zuba jajjagen attarugu kadan da tumaturin leda sai da ta bari ya dan bararraka san nan ta wsnke ganye ugu da bitter leaf kadan ta zuba a kai ta kuma watsa agushi a ciki ta rufe tukunyar.
Ta dauko guntuwar doya. Miya na sauka doya ta dahu ta buga masa sakwara.
Duka duka bata fi 40 minutes a kitchen ba sai gata da wani tray din da su plate da serving spoon ta dora kan dining.
San nan cikin san yin murya ta juya wajen Bilki tace "Anti na gama".
Nan dai maigidan ya ja bakonsa dinning. Shi kuwa bakon yayi wa abincin nan ci mara algus.
Da kyar bayan la'asar shi ma don kar masu gidan su kosa ya hakura ya bar gidan.
Ya kuwa tafi zuciyarsa cike da tunani 'yar kyakkyawar budurwar da ya gani wadda ta sa shi karya azumi da kuma yin abin da ba dabi'arsa ba watau cin abinci a gidan mutane.
[8/6, 23:15] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👨👧👨👧
IN FIKI A MIKI💑💑💑💑
Page 12
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Al bashir Usman matashi ne dan kimani shekaru ashirin da bakwai. Kyakkyawan saurayi dogo wanka tarwada mai kyakkyawar kira.
Irin dan nan ne da ko wadan ne iyaye suke burin samun irinsa. Ga ilmi addini dana boko san nan ya kawata rayuwarsa da kyawawan dabi'u.
Da ne ga Hajiya Rakiya da hamshakin mai kudin nan wanda ya kasance daya daga cikin masu kudin garin nan watau Alhaji Usman Ahmad Babba.
Bayan gama karatun AlBashir sai ya dauki wani layi sabanin irin business din da ya tashi ya samu mahaifinsa yana yi watau harkar sufuri na jiragen ruwa.
Textile company ya bude a China shi da wani abokin karatun sa dan asalin kasar mai suna Kim Suen. Lokaci daya ya zama mamallakin rabin hannun jari a kamfani buga kaya me suna KIMBASH.
Kusan a kasuwar garin nan babu wasu kananan kaya da suke samun kasuwar nasu.
Su kan saka kananan lesuka da kuma atamfofi da yadudduka na maza da mata.
Komai tsadar zaninsu ba ya wuce dubu hudu a hannun masu saye daidai. Amma ingancinsu sai mai goyo sai ta shekara hudu tana amfani da shi ba abin da yayi.
Hakan ya sa suka samu kasuwa sosai. Karamar riba suke bi. A wata atamfar bai fi a samu naira goma kan kowanne turmi ba amma fa a rana za a iya sayar da turmin miliyan.
Bai fi shekara biyu da fara wan nan harka ba ya biya mahaifinsa baashin kudin da ya bashi ya fara kasuwancin da su.
Da a kasuwar duniya za a tallata shi darrajarsa zata kai naira biliyan hudu.
Ga shi dan gata na kin karawa saboda shi ne suta a gidansu. Yayyensa mata hudu.
Yaya Ai. Yaya Rabi . Yaya maryam sai kuma wacce yake bi Yaya Bilkisu.
Dukkasu kowacce tayi aure da nata iyali. Amma yaya Ai wacce suke kira da Maama, ta bar mata rikon babbar 'yarta mai suna Meena.
Wata irin rayuwa suke ta tsananin kauna da kuma mutunta juna. Idan ka gansu tare da mahaifansu sai ka dauka abokan juna ne.
Amma hakan ba zai hana Bilkisu da take karama ta saka Al Bashir ya canza wa danta pampers ba.
To wan nan rikakken dan gata gaba da baya da kuma tsananin wayewa da yayyensa suka ci buri a kan auren sa shi ne ya gama zaga duniya ya kasa gano kowacce irin mace sai Zainab diyar dana dade ban ga yarinya marar gata irin nata ba.
Tun da ya yi ido biyu da ita a gidan chief accountant dinsa watau Sulaiman gaba daya ya rasa sukuni.
Da kyar ya daure ranar da ya fara ganinta ya bar gidan. Saboda gaba daya tagama ruda shi.
Ga shi dai bai gama sanin ko wacece ita ba saboda ko sunanta bai sani ba. Amma 'yar zirzirgar da tayi na kimanin awa biyu, yana hankalce da ita.
Hakan ya sa ta dasu a ransa kamar dashen tsohuwar bishiyar kuka.
Su dai masu gida alkhairin da ya kai musu shi ya sanya su tsananin farin ciki.
Yan mata dubu dari cas ya ajiye musu da sunan su sa kati. A zuciyarsa kuwa niyyarsa sakon ya kai ga sabuwar masoyiyarsa. Ba shi da masaniyar ba ta ma da masaniyar anbada wata kyauta. Ita kuwa maijego dala dubu ya bata da sunan a sayawa jariri pampers.
A wan nan rana tunanin Khadija bai barshi yayi bacci ba. Saboda haka kamar yadda ya saba kwana yayi yana sallah da karatun AlQurani mai girma domin neman dauki a wajen shugaban halitta.
Washegari kuwa daga masallaci dakin ummansa ya shigo kamar yadda ya saba duk safiya.
Duk kudinsa ya kasa tashi daga cikinsu. Dakinsa ciki da falo yana daga gefen babban falon gidan.
Da sallama ya shiga dakin Ummansa.
Kamar yadda zata lazumi ya sameta ta na yi kamar kullum.
Amma yau sabanin lokutan baya da zai zauna ya jira ta ta gama shi ma kuma yayi nasa a gefenta. Yau kam kasa hakurin haka yayi.
"Ummana barka da asuba " ya fada yana mai dora kan sa a kan cinyarta kamar wani karamin yaro.
"Barka ka dai" itama ta amsa tana mai shafa kansa.
Ba sai ya gaya mata ba shakuwa irin tasu, tasa ta gano tabbas yau da matsala.
Tana kokarin tambayarsa taji sallamar Abbansu ya shigo.
Shima bayan gaisuwa a tsakaninsu ya juya ya kalli dan nasa, yace "yau kuwa kalau dan uwan Ummansa yake na ga yau autancin ya motsa"?
Tashi yayi daga cinyar mahaifiyarsa ya koma ya rabu da uban kamar marar lafiya, san nan cike da kaskantar da murya kuma cikin ladabi ya shaida musu halin da ya tsinci kansa .
An tambayi sunanta yace bai sani ba. Yar gidan waye bai sani ba. Abu daya ya sani a kanta gidan da ya hadu daita.
Abbansu ne ya ba shi shawarar ya koma ta inda aka hau ta nan ake sauka. Saboda haka ya umarce shi da ya koma gidan Sulaiman ya yi duk binciken da zai yi daga wajensa
[8/6, 23:18] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👨👧👨👧👨👧
IN FIKI A MIJI💑💑💑💑
Page 13
BY HANNE ADO ABDULLAHI
KimBash textiles ba sa budewa sai wajen tara. Shi kuwa oga ya kan kai goma bai shigo ba.
Amma ran nan masinja da mai shara ne kawai suka riga shi zuwa. Oficce din accountant Sulaiman Bello ya fara kaiwa ziyara saboda shine makasudin zuwan sa da wan nan sanyin safiya, sai dai fa ya daki gurbi, domin kuwa bai shigo ba.
Ya buga wayarsa a kulle. Ya aika kiransa yafi sau bakwai ana dawo ma sa da sakon bai zo ba. Shi da kansa masinjan hankalinsa ya tashi ganin wan nan sako na duk bayan minti biyar da ake aikawa accountant.
Bai san cewa shi mai sakon ba ya ganin sakon a kai a kai ba. Wanda yake aiken gani ya na yi yana ba da ratar wajen minti talatin.
Hankali a tashe ya nufi gidan accontant. Saboda bai san kiran na menene ba.
A round din Obasanjo suka yi clear da shi. Saboda haka ya juyo da mashinsa ya dawo office.
Yana parking shi ma Tasi'u masinja yana karasowa. Da hanzari ya nufi inda yake kokarin kulle motarsa.
Yana kokarin gai da shi shi kuwa da sauri yake fadin "yi sauri ofishin chairman. Aiken sa takwas oficce dinka yana nemanka".
Shi ma kiran ya ruda shi. A tunaninsa ba laifin da ya aikata. Haka zalika jiya ogan nasa ya kai masa ziyara har gida. Kuma yadda ya saba mutunta ma'aikatansa shima a haka suka rabu da shi. Me ya kawo irin wan nan sammaci haka?
A rikice ya karasa wajensa cikin hanzari. Ya na shiga kuwa ya tarar da shi yana safa da marwa a office din.
Yana ganinsa ya saki ajiyar zuciya.
Kafin ya karasa shigowa ya isa wajensa shi da kansa ya kamo shi. A kujerar bakin table din sa ya zaunar da shi. Shi ma ya ja daya ya zauna suna fuskantar kujerar AlBashir ta asali.
"Lafiya yallabai naji ance kana ta aiken nema na. Bari in dauko laptop dina da ga mota sai muji dadin discussing koma meye".
"Manta ba aikin office ya sa ni kiran ka ba? Wacce yarinya ce jiya na hadu da ita a gidanta".
Ya dan daga kansa alamun tunani. San nan yace "Jiya yallabai 'yanmata uku ne a gida na. Farida dake karanta medicine a Sudan. Sai kanwarta Farisa itama a sudan take sai kuma kanwata Aisha. Su ke nan su ukun a falon".
Da wani irin shauki, Albashir yace masa
"Ta nan wata doguwa light skinned tana tafiya kamar amaryar dawa. So humble yet classy and well mannered. Wata data kawo min ruwa da abinci".
Damamaki a fuskarsa yaga ga haddadun 'yanmata da suka ci kwalliya ta birgewa amma sai nannadaddiya ce ta burge oga.
Cikin mamaki yace "yallabai ba dai Zainab kake nufi ba".
"ZAINAB"! AlBashir yaja sunan cikin makogaransa mai dauke da wani irin shauki.
"Beautiful name. Itace wata mai wadansu itin xarazaram fingers looking so beutiful in her Hijab".
Cikin dariya Sulaiman yace "yallabai i have never notice her beuty.amma dai she is the only one wearing hijab a cikinsu".
"To ita din nake magana a kai. Yaya kuke da ita?."
"Dukkansu 'ya'yan sister Bilkisu ne. Kuma a gidansu ta girma. Babansu shine commisioner of finance na garin nan. I know their family very well.
Ya dan dada rankwafowa kusa da shi san nan yace "ka san ni da kyau. Ka san family background dina . Zainab ma kuma na fahimci ka san su very well tun da kayi aure from the family".
Sai da Sulaiman yaja numfashi san nan yace "amma yallabai iam very suprise by your choice. Naga ga more sophisticated girls around but you chose the most backward. Na ga maza yanzu sun fi son polished 'yan mata amma kuma kai naga......." sai kuma ya kasa karasa maganarsa.
"Bad choice". In ji AlBashir. San nan ya ci gaba da cewa "ka san ni 'yan uwana mata ne. I know a real lady and a fake one. Look at the respect she gives. How well mannered she is as well as her caring nature. That is what makes a good wife".
"Haka ne yallabai. Amma akwai matsala daya. Kaga dai kasa dai dai ce a duniyar nan baka zaga ba. So akwai banbancin exposure a tsakanin ku".
"Duk ka manta da wan nan. Ni zan bata irin exposure da nake bukata ta samu. Ai ba kowacce exposure namiji yake bukatar matarsa ta samu ba. Ni dai ka yi min jagora zuwa gidan in samu shiga. In ka min haka ka gamamin komai".
Nan dai suka daidaita a kan da la'asar zasu kaiwa Zainab ziyara.
Ana fitowa daga masallaci kuwa Albashir ya aika fagge wajen telansa aka karbo masa sabuwar shaddarsa president bugun switzerland ba chinaba. Cream colour da ita ta sha wani irin dinki irin na manyan kekunan nan na computer. Ya karya hula da tayi matching da kayan ya kuma bude jikinsa da turaren cool water.
Idan ka ganshi sai ka dauka sabon ango ne ba mai shirin zuwa nema ba.
A motar ma Sulaiman ne mai tuki shi kuwa marriage candidate sai dada gyara hula yake yi yana dada duba kansa a madubi ya tabbatar kwalliyar sa tayi.
A kofar gidan Dr Abdullahi suka yi parking bayan sun yi horn maigadi ya bude musu gate. A wajen parking suka yi parking. Momi na zaune a falo ta ji shigowarsu.
Nan suka yi shawara akan shi Sulaiman tunda kusan dan gida ne ya shiga yayi masa iso.
Shi ma kuwa Sulaiman ganin ya zabowa Zainab zakaran gwajin dafi ya dage wajen karantawa momi uban gidan nasa.
Tun da ya fara bata labarin AlAbashir zuciyar Momi take tafasa. A zuciyarta take ayyana irin azabar da zata gana mata saboda bakin ciki.
Sai da ya gama tacee "to kai Sulaiman ga kanwarka a gidan ga kuma su Farida amma duk bai gansu ba sai wan nan kucakar yarinya"?
"Su ma ai kin san halinsu Momi. Gaisuwar arziki bai samu daga wajensu ba suna zuba dan banzan girman kai. Ita ma ai ladabinta ne ya jahankalinsa da kuma ...,.."
"To kaga ya isa haka. Duk wani bayaninka ba zai yi tasiriba. Ka koma ka sanar da shi Zainab an mata miji. Idan har a gidan nan yake son aure yazo ga Farida nan ko Farisa duk wacce yake so zan bashi.
A bakin gate ya samu AlBashir suna hira da Mallam mai gadi. Saboda kowa ya san shi dabi'arsa ce sakewa da kana nan ma'aikata na gidansu da kuma na office.
To a haka ya same shi da Mallam suna 'yar hira yau da kullum. Saboda rashin sanin halin da zai shiga idan yaji batun da ya zo da shi a nan ya fara kora masa bayanin da Momi ta zayyana masa a kan Zainab.
Nan take kuwa ya shiga rudani. Amma sai ya daure yayi ajiyar zuciya yace "allah yasa haka shi yafi alkhairi".
[8/6, 23:21] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI👨❤👨👨❤👨
Page 14
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Lokacin da Mallam mai gadi ya dawo wanda shi kuma Sulaiman yaje daukko mota domin su tafi, yayi mamakin ganin bakon a wani yanayi. Yanayin sa ya banbanta da farkon shigowarsa gidan. Farkon da ya shigo gidan cikin fara’a ya shigo. Amma yanzu bayan dan bayanin da Sulaiman yayi masa, da ka kalle shi kasan cikin tashin hankali yake.
“yallabai lafiya dai? Naga kamar wani abu ya daga maka hankali”? mallam ya tambayeshi.
Sai da ya shafi fuskarsa da tafukan hannunsa. San nan ya dan yi tsai da dubansa akan fuskar Mallam yace “ka san dan adam idan ya kallafawa ransa samun abu, ya kuma gaza samun wan nan abu to ya kan shiga damuwa. To nima abin da ya faru da ni ke nan. Na kallafa raina akan samun Zainab a matsayin matar aure to kuma ashe ba rabona bace. Ashe an bayar da ita. Shine naji duk hankalina ya tashi”.
Cike da tsananin mamaki Mallam ya dago ya kalleshi. Amma jin kugin mota na kusanto su ya sanya ya kasa yi masa bayani. A iya saninsa ya wuce matsayin maigadi a gidan, saboda amfanin da yake yiwa mai gidan.
Duk wata harkarsa ta office ko kuma abin da ya shafi yaran gidan shi ya kan sanya yayi masa addu”a da kuma sauka. Wanda shine ma babban dalilin da ya sanya yake zaune da shi. Gadin nasa carmouflage ne. ya kuma san babu yadda za ayi a bayar da auren Zainab bai sani ba. Amma ya yi niyyar yin bincike akai. Saboda haka cikin hanzari yace masa “ka bani lokaci ina son ganawa da kai akan wata muhimmiyar Magana wacce bazata yiwu yanzu ba. Amma idan har ka amince zan maka dan wani bincike idan har na gano gaskiyar lamarin zan zo maka da bayani nagartacce akan wan nan yarinya”.
Take kuwa yanayinsa ya canza ya koma wata sabuwar murnar. Cike da godiya ya dakko katinsa ya mika masa shi ma kuma ya karbi lambar wayarsa.
Bai fi minti biyu da bawa Mallam katin nasa ba, Sulaiman ya karaso da motar. Nan ya shiga suka tafi da Sulaiman wanda bai yi kasa a gwuwa ba wajen sanar da shi sakon Momi akan cewa suna da burin hada zuri’a da shi saboda haka zata bashi auren ko Farida ko kuma Farisa duk wadda ya ke so a ciki. Shi ma kuma kokarin tura tasa kanwar yake yi watau Aishan da ya same su tare a gidan.
Saboda kawai baya son yaci fuskarsa ya kasa gaya masa a inda ya jiye kannen nasa. Yaran da ganinsu zasu yi girman kai sabanin ita wadda ya gani ko ba a gaya masa ba, ya san zata kasance mai sanyin hali da kuma mutunta mutane. Tsaf tsarinta yayi na irin matar da yake so.
Bai tanka masa ba, sai da shi Sulaiman din yace masa “kuma yallabai you are not on the same level da ita. Exposure dinta is quite minimal”.
Ya katse shi da fadin “Iam looking for a wife not a colleague. So ni iya yadda nagan ta yai mina a haka”.
“Na sani yallabai amma ka duba sauran ‘yan uwanka. Kaga Yaya Ai is a qualified pediatrician while Yaya Rabi na san director ce a CBN. Tun da ka sha aikena wajenta. While Yaya Maryam although bata aiki na san business take yi ga kuma mijinta ambassador ne.
Kai ko Anti Bilki da take matar ambassador tayi mata nisa. Ba ka ganin kamar Zainab ba zata iya mingling da su yadda ya kamata ba”?
“Sai kuma ka manta ko kuma ban taba gaya maka ba, wacce ta haifo duk wadan nan succeful matan bata taba zuwa makarantar boko ba. But yet hakan bai hana su bata respect din da she deserve ba. Haka zalika mazansu irin matan da suke so ke nan. Ni kuwa I want a homely person for my wife. That is what I saw in Zainab ban kuma ganshi a wajen sauran da kake nuna min sun fi dacewa da niba”.
Zai sake yi masa bayani ya ce “ kaga manta kawai. Allah ya sa haka shi yafi alkhairi.
Amma a can gida kuwa ba a bin da ya faru da Zainab ba ke nan. Momi ta zageta ta kuma yi mata tijara. Ta kira ta da karuwa. Yadda ta nuna mata, ita ta ke neman Al Bashir, ba shi yace yana sonta ba. Bayan ta lakada mata dan banza duka wanda ta dan kwana biyu rabon da a yi mata shi tace mata “kuma idan ina numfashi aure iri na uwarki zaki yi sai dai kema ki koma kauye kiyi auren daka da sussuka. Amma ke da jin dadi a rayuwa har abada”.
Ku san ko da yaushe ta na da ‘yar masaniya na dalilin duka ko kuma fadan da aka yi mata amma na yau bata da idea na dalilin fadan da zagin cin mutunci da aka yi mata.
Allah sarki duniya. Momi bata san cewa ita ma Khadija mahaifiyar Zainab Allah ya yassare mata ba. Noma da suka sa a gaba da kuma kiwo ita da mijinta, Allah ya tallafa musu. Saboda ba zuwa take ba, da ta ga gidan da ya kera mata a Garkon. Noma da kiwo Allah ya sa musu albarka, ya zama hanshakin mai kudi. Kullum yana China domin shigo da sabbin na’urorin noma da injuna irin na su busar da kifi.
Hatta kifin da yake kiwo, busar da shi yake yi ana fita da shi wajen kasar nan container container. Shinkafa kuwa, ya samu hadin gwuiwa da wani babban dan kasuwa wanda ya bude ma’aikatar zazzabar shinkafa a nan garin. Da yake ya san kan noma shinkafar da aka fi sani da kilaki saboda kyawunta ya sanya kusan shine babban supplier na shansherar shinkafa ga wan nan kamfanin. Ga ‘yar kyakkyawar matarsa da kyawawan ‘ya’yansa guda biyar. Hafsa ce babba sai Sadam sai kuma tagwayen mazan su biyu da suke bi musu Ahmad da Aliyu. Sai kuma auta Anisa.
Zama ne kawai ace suna Garko. Amma gata da sutura sun kerewa Zainab sosai. Ko ba komai su har turanci suna ji sosai, saboda tsayuwar iyayensu akan haka. Sabanin ita da ta dai yi sa’ar samun karatun addini amma na boko sai a hankali. Sa’a daya tayi islamiyar tasu tana da kyau sosai, saboda haka ba’a yadda dalibai suyi Magana da wani harshe ba a harabar makaranta sai dai larabci kawai. Hakan ya sanya ta iya larabci matuka.
Sun dan samu turanci sama sama, saboda policy da ministry ta saka na cewar manyan isalamiyoyi su dinga koyar da dalibai karatu da rubutu na turanci da kuma lissafi. Ta dai dan samu abin da ba a rasa ba. Amma lissafin kam ta iya shi ko don cinikin Momi.
Ita fa ko ‘yar wayar nan ta zamani da matasa su kan rike ita bata da ita. Yar Nokia ce mai torchlight irin wadda samarin kan kira talk to me sharp sharp. Ita ma din taji jiki sai da kyauro take riketa.
Mu dawo asalin labarin. A ranar da Al Bashir ya je neman auren Zainab, a wan nan rana duk dauriya irin ta Baba Laure sai da ta suke. Bayan ta koma wajen ta ta ke cewa da Mallam maigadi watau mijinta, “anya kuwa Mallam ba zamu hakura da zaman gidan nan ba”
“Saboda me kika fadi haka “? Shima ya tambayeta.
“Wallahi Mallam na gaji da ganin azabar da matar nan take yiwa Zainab. Kullum yarinya a cikin tashin hankali zaka ganta. Ko wata baiwar tafi ‘yar nan gata”.
Cike da mamaki yace “yau kuma me ya hada su”?
“Yo ni ina na sani. Ita kanta yarinyar ba ta san me tayi ba yau tayi mata wan nan dan banzan duka. Ni dai naji tana banbanmin wai ta ga wani mai kudi tace yazo ya aureta. Har tana ikirarin in dai tana numfashi aure irin na uwarta zatayi. Shashasha ko an gaya mata auren uwar Zainab abin assha ne. ita in banda zaman birni akwai abin da zata gwada mata. Ina ce ko ni da kai zaman da muke yi ke nan a gidan nan. Ba mijin uwar ne ya roki arzikin mu zauna saboda mu dinga sa ido akan ita Zainab din ba tun lokacin da ya zo ya tambaye ka akan yadda take rayuwa ka sanar da shi rikon sakainar kashin da ake yi wa tarbiyyarta. Ya roki arzikin ka kula da ita. Akwai kaunar da ta fi wannan. Ni in ba don Zainab ba da tuni na dade da bar musu gidansu. Mata kwata kwata ba Allah a ranki”
Jin bai ce mata komai ba ta sake kallonsa tace “mallam kana ji ina ta fada ka zuba min ido kawai ba ka ce komai ba”
Sai da ya nisa san nan yace “a iya saninki kina da labarin anyi mata miji”
“Ina take da niyyar aurar da ita. Ta fi son ta ajiye ta, tana mata bauta” .
Duk da haka yayi karambani da suka hadu a masallaci da mai gidan ya kebe shi yake sanar da shi wani yaro ya ga Zainab ya kuma nemi da ya yi masa hanyar nemanta. Da baban ya tambayeshi sana’ar me yake yi, bai san ya akayi ba, sai ji ya yi bakinsa yayi subul da baka yace “gwanjo yake sayarwa a kofar wambai”.
Bayan sun tattauna da Momi shi da kansa ya nemi ganawa da yaron.
Washe gari kuwa bai yi sanya ba, ya nufi ofishin Alhaji Al Bashir. Bai samu matsala ba ya samu ganinsa. Daga yadda yaga ma’aikatar da kuma yanayin hadahadar da ake a wajen hakan ya tabbatar masa da lalle babban mutuum ne.
Conference room ya sanya aka kaishi. Shi ma kuma a can ya same shi. Bayan sun gaisa. Ya ce da shi “yallabai kana ganin zaka iyan auren Zainab a duk yanayin da ka sameta”?
“Kwarai zan iya”. Shi ma ya amsa masa.
“To zan gaya maka kadan daga cikin irin rayuwar da take yi a gidan. Idan har kana ganin zaka iya aurenta a haka to shi ke nan”.
“Mallam kaunar da na ke yiwa yarinyar nan ba karama bace. Saboda haka kar ka dauka wani batanci zai sa in ji son da nake mata ya ragu. Shi kan sa Sulaiman yayi kokarin nuna min matsayin mu ba daya ne da ita ba. Amma hakan bai girgiza ni ba. Abin da ya sani janyewa fada min da aka yi cewa an mata miji”.
“Idan nace ba ayi mata mijin ba zaka dawo ke nan”?
“Da gudu ma kuwa”?
“To kuwa akwai matsala. Saboda idan dai zaka je neman aurenta da duk wata baiwa da Allah yayi maka, matar ubanta ba zata taba yarda ta barta ta aureka ba. Amma da zan ka dan yi basaja ka ragewa kanka daraja da aji da kamar kasha casa’in da tara ka bar daya kawai daga darin da Allah ya baka, to ka iya nasara”.
Bakinsa har rawa yake yi. Yace “fada min me kake son inyi. Ko meye zan iya yinsa a kan Zainab”.
“Da kyau yanzu haka kafin in fito nayi Magana da mahaifinta kuma shi da kansa ya sanar da ni cewar ba wani miji da aka yi mata. Na kuma sanar da shi cewar wani yaro yana neman iznin aurenta. Amma fa nayi baranbarama. Domin ya tambayeni sana’ar ka nace gwanjo kake sayarwa a kofar Wambai. Idan kuma har kana son auren ta to kuwa a wan nan siga zaka je neman aure. Amma matsayinka na gota haka, ban ga yiwuwar matar uban zata bar ka, ka mallaketa ba”.
Yana fadar haka ya mike da niyyar tafiya. Shi da kansa ya rako shi yana kokarin debo kudi ya bashi, “yace masa Alhaji kar muyi haka da kai. Burina in ga Zainabu ta samu rayuwa mai kyau”. Bai jira yaji amsar sa ba ya buga mashin dinsa ya ja ya tafi.
[8/6, 23:20] +234 814 948 5104: FINI A UBA I👪👪
IN FIKI A Miji💏💏
PAGE 15
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A wan nan rana Al Bashir ya zayyana wa iyayensa duk abin da ake ciki game da yarinyar da yake son aura. Hajiya Rakiya watau ummansu tace “to yanzu ta ina za a bullo da wan nan Magana. Dan uwana ko dai hakura zaka yi. Ka nemi wata”. Ta kan kira shi da dan uwana saboda sunan yayanta yaci wanda kuma shidin aboki ne ga mijinta watau Alhaji Usman. Haka zalika ta sanadinsa aure ya kullu a tsakaninsu.
Cike da rauni Al Bashir yace “don Allah Umma kar kice in hakura. Addu’a zaki tayani da ita”.
Sai da suka kwashe da dariya ita da Abbansa san nan ya fuskanci zolayarsa suke. Suna haka babban amininsa yayi sallama ya shigo. Mujib abokinsa ne tun suna yara. Tare suka yi karatunsu da komai. Bayan gaisuwa iyayen suka shaida masa aikin da ya tunkaro abokinsa. Cikin tsokana yace “ai ina ga Abba abin da za ayi rumfa zaka sama mana a kasuwar mu zauna mu koyi irin nasu kasuwanci saboda kar muje wajen intabiyu a kure mu”.
“very good ka kawo shawara mai kyau. Saboda haka gobe ka fito da sassafe ni da kai zamu fara zuwa wambai. Kuma zamuyi haka na tsawon sati guda saboda mu samu experience”.
“You must be kidding me”. Mujib ya amsawa Al Bashir cike da mamaki. Su dai iyayen dariya kawai suke musu.
Al Bashir cikin dakewa yace “nayi maka alamar ina wasa a cikin wan nan lamarin. So get ready my friend gobe zamu shiga kasuwa”.
A haka suka sallami iyayen nasu. Washegari kuwa takwas na safe a kasuwar ‘yan gwanjo ta wambai ta same su. Ita kanta kasuwar da tambaya suka samo ta. San da suka shiga kusan da yawa basu fito ba. Amma yadda suka ga yanayin kasuwar abin ba Magana. Ga shi dama an kwana ana lafta ruwan sama. Ga kasar wajen baka kirin ta dame da ruwa ta koma wata kwata kwata.
Site din kawai ya isa yayi discouraging din su. Mujib ya kalli wajen ya ga yadda yake yace “is she worth this wahala’?”
“she is worth more than this”. Take ya manta da scenario da ke keyawe da shi ya fara wassafa masa Zainab. Fadi yake “you need to see her long slim fingers. Ga ta da wani irin skin mai wata irin creamy colour. The eyes Subahanallah. Idan ta kalle ka da su, sai ka ji gaba daya ka rasa sukuni…..”
“Dakata Mallam sau nawa ka ganta har kake wan nan artist description din”.
“Once my friend. Only once but it seems like I met her a thousand times. And the voice. When she speaks mallam the voice is so melodious like that of a trained singer”.
Sai da Mujib ya kaiwa wani katon sauro da ke kokarin shan jininsa duka san nan ya sake cewa “just use the conventional way mu saki kudi kawai a bamu aurenta”.
Ya shafi fuskarsa cikin damuwa san nan yace “this time around it wont work. Saboda akwai adversaries da ba sa son ta a luxurious life. In ba haka ba ai mahaifinta ma is well off. Saboda shine commisioner of finance na state din nan gabaki daya. I jut don’t know what is wrong wih her step mpther. She is the problem a yadda na samu labari”.
“Ina ga the stepping in the mothering is the problem. Amma we will get more details idan muka hadu da ita yarinyar “
Wani saurayi ne ya katse musu hirar tasu a lokacin da yake kokarin bude shagon da suka zauna a bakin rumfar. Nan dai suka nuna masa kaya suke son sara suma su fara sai dawa. Shi kuwa sai murna yake yana fadin “ai bari mai gida ya zo kayan mu giredi ne”.
Abin dariya sai da aka bude shagon suka ma fuskanci wadanne irin kaya ake sayar wa a shagon. Su ba su taba sanin wani yana saka kaya idan ya gaji da ita ya cire ya sayar wani ya saya ya saka ba sai a wan nan ranar. Da kuwa warin gwanjon nan ya buge su, sai atishawa tuk tuk.
Shi kuwa saurayin sai fadi yake “ai in gaya maka baaba wan nan karon sabulun maganin kwarin da suka saka mai karfi ne. saboda wancan karon da muka dauko kaya da yake sabulun ba shi da kyau har da beraye muka samu a ciki”.
Mujib na jin haka ya mike tsaye da sauri jin an ambanci bera yace “please lets get out of here kafin mu samu wani infection”.
Jawo shi Al Bashir yayi ya zaunar da shi a gefensa san nan ya ci gaba da tambayar sabon abokin nasu wanda suka fahimci sunan sa Ahmad amman an fi sanin sa da swaggedeen. Nan dai ya shiga gaya musu irin alkhairin da ake samu idan an sai kaya a shagonsu. Yace “ka ga duk kasuwan nan ba wanda ya kai Alhajina sauke kaya giredi. In dai ana maganar shirt shirt to kuwa tamu tafi ta kowa kyau. Idan ka gansu sai ka dauka sabbi ne. gashi dealer ana yanka ta akan dubu sabain mu kuwa tamu sittin da tara ce. Kuma in gaya maka a kowacce dealer idan dai kai ka yanka ta da kanka, baka samu riga ba ka samu dari da ashirin. Kuma in gaya maka ko wacce riga zaka iya sayar da ita a kan dari shida zuwa bakwai.
Kuma in gaya maka ranar da kasuwa tayi kyau zaka iya samun ribar dubu daya zuwa biyu. Ga wanka da zaka dinga dauka mallam. Shi ma duk a cikin ribar ne”.
Gaskiya Al Bashir ya yaba da iya marketing na bawan Allah nan. Ba su gane kurensu ba, sai da kasuwa ta cika ta batse wajen misali sha daya na rana. Nan suka dada fuskantar yadda cinikin kasuwar ke gudana. Sun kuma yaba da kokarin bayin Allah dake neman halal din su. Amma fa situation report din su, ba dadi. Yanayin kasuwar kadai ya isa yayi discouraging dinka daka shiga saye ma balle sayarwa.
Amma su yinin ranar haka suka kashe shi wajen koyon cinikin gwanjo. Da kuwa aka zo yadda ake bend down and pick din proper Mujib yana birkita kaya yana zagin Al Bashir saboda bai ga dalilin da zai basu wan nan wahala haka ba. Daga baya suka ga aikin bana wasa bane suka yi cinikin dealer biyu aka sayar musu da ita. Shi kuwa swaggedeen sai murna yake yi. Har da musayar lambar waya saboda gaba.
Sun sai kayan da sunan bari suje su dawo. Kuma har kudin sun biya. San nan suka fita daga kasuwar. Suna isa gida wanka kawai suka shiga kafin suka isa wajen ummansu domin su sanar da ita yadda ta kaya.
Yaya Ai da ta shigo ta tarar da abin da ake ciki ta kwashi dariya kamar cikin masaki saboda yadda Mujib ya dinga kuranta irin wahalar da suka sha. Cikin dariya tace “kaga ai kun shiga shadin ‘yan kasuwa”.
Shi kuwa Abba da yaji yace “ina fatan zaku dada appreciating talaka da wahalar da yake ta neman halal din sa”.
Plan b da suka aiwatar shine na nisanta Sulaiman da campaign headquarters dinsu saboda kar a hadu wata rana ruwa ya balle. Take kuwa Mujib ya bada shawara a tura shi branch office din su na China saboda yayi nisa da su, sai komai ya kankanma.
A cikin sati kuwa komai na tafiyarsa shi da iyalinsa ya kankama da sunan zai yi shekara daya a wajen. Shi kuwa Mallam mai gadi da ya ga an dauki tsawon kwana takwas ba Al Bashir ba dalilinsa sai ransa ya baci. Saboda tun da ya ba shi shawarar nan shi kuwa bai tsaya da addu’a ba. Rokon Allah yake ya hada kawunansu ya kuma tabbatar da alkahiria akai.
Sulaiman na barin kasar suka shirya da la’asar shi da Mujib zasu zance. Umma na kallonsu kowa ya sha gogaggiyar shadda ta gani ta fada wacce da gani kudin ta ba za su kasa dubu dari ba yadi biyar kawai. Ga uban turare designer da suka bulbula, tace “zancen za’a ne haka”?
“Eh Umma” Mujib ya amsa mata”.
“Ashe kuwa da kun tonawa kanku asiri. Yanzu ku kuma ai sai dai ku nemi kayan gwanjo ku saka. Kuma a wacce motar zaku”?
“Wai da a final din da ake kai Meena makaranta zamuje tun da it’s the cheapest car a gidan nan”.
Sai da tayi dariya san na tce da su “shi mai sai da gwanjon ne ya ke da mota kuma final discussion? Ai sai dai ku ari babur din Sale mai guga”.
Suka shiga suka canja shiga inda suka saka kananan kaya. Ko ba komai su ana samun irinsu a gwanjo duk da dai nasu sun so su tona musu asiri, amma dai sun dan badda kama.
Tun da suka hau mashin din nan suka tafi Mujib yake masifa a hanya. Saboda ko sanda suka yi yayin hawa mashin din nasu bike ne irin dirkeken nan. Fadi yake muna zuwa naga bata kai yadda kake fada ba, I will call off the deal sai dai ka nemi wata”.
Shi ma kuwa with full confidence yace “na yarda. Idan har ka ga she is not worth the trouble zan kyaleta in nemi wata”.
Wajen Mallam mai gadi suka fara isa. Ba karamar murna yayi ba lokacin da ya gansu. Shi yayi musu iso wajen Dr Abbdullah Zubair watau mahaifin Zainab. Daga falon suka tabbatar da cewar gidan masu shine suma. Momi na gefensa ta hakince. Tun daga amsar gaisuwar da yayi Momi bata sake barinsa yayi Magana da bakin nasa ba.
Ita ta sake tambaya inda yake sana’a yace a kasuwar wambai. Tace “rumfa gareka ko kuma rabuwa kake da wani”?
Mujib ne “yace gaskiya Momi bamu da rumfa a nan dai muke tsayawa bakin hanya”.
“kuma a rana ku kan samu kamar nawa”.
Cikin wani irin ladabi na karya yace “a rana mukan samu ribar wajen dubu daya randa kasuwa ta yi kyau har da dari biyu ko uku”.
“yama kace sunan ka”?
“ni sunana Balarabe Usman”. Al Bashir ya amsa mata saboda shine sunan da kakkarsa ta wajen uwa take kiransa da shi saboda sunan danta na fari ke gareshi. Ba abin da ya basu mamaki irin yadda tunda suka gaya wa Momi cewa cirani iyayen su suka zo daga katsina, bata sake bibiya taji asalinsu da kuma irin binciken da addini ya sa a yi a kan masu neman aure ba. Nan take kuwa ta gano cewa ta samu inda zata kai Zainab inda zata kaskanta ta wahala.
Saboda haka ta juya wajen miji tace “ina ga Daddyn Farida ka ba shi dama ya fara neman aurenta tun da dai yana da sana’ar da zai riketa, kar mutane su dauka ko don kana Commisiner ni kuma ina director ‘yarmu tafi karfin auren talaka”.
Ta sake mai da hanakalinta wajen su Mujib tace “ka iya ci gaba da neman aurenta. Amma duk abin da za a yi ka tabbatar nan da wata uku za a aurar da ita. Idan ka kasa zuwa neman aurenta nan da wan nan lokaci zamu aurar da ‘yarmu. Kuje ku jira ta a waje zan turo muku ita yanzun nan”.
Sukayi mata sallama suka fita. Mujib bai san sanda ya saki wani irin zagin ba. Yace “matar nan she is a real evil. Gaskiya ko da ban ga Zainab ba I will want you to take her away from this wicked woman”.
Momi kuwa da murnar ta ta shiga gida. Zainab na kwashe kayan Kwando ta same ta a kicin. Sai da ta rangada mata guda a ka san nan tace “uwar neman maza sai ki godewa Allah. Neman ya kare miki kije ubanki ya fitar miki da miji kafin ki fitar masa da abin kunya. Ga shi kuma mai sana’a mai riba. ‘yar garaugarau dai da kuma riga da wando ko skirt na gwanjo ba sa gagare ki ba”. Ta sake fashewa da dariya “san nan tace ki wuce kije yana jiranki. Amma ki tabbatar kin shigo gida nan da minti ashirin saboda bar ganin zaki wajen saurayi ba uban da zai dora miki abinci dare. Su Farida karatu ya sha musu kai, saboda haka idan kika haura hakan zaki hadu da ni”.
Ita dai saroro tayi tana kallonta saboda tama kasa fahimtar abin da Momi take nufi. Sai da ta fita san nan Baba Laure tace “wuce kije kin ji uwata”.
Sanye cikin hijabinta wanda ya kusa rufe dunduniyar kafarta ta nufi wajen bakon da bata san shi ba.“
[8/6, 23:22] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 17
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A nan wajen Mallam ta same su tsaye. Tun da ta dosu su suka tsaya da zancen da suke yi. shi dai Mujib mamakinsa ya tafi ne akan yadda take spreading wata irin aura even though ko ina na jikinta a lullube yake. shi kuwa sarkin masoyan duniya nurnar ganinta ce ta saka shi ya kasa ci gaba da zancen da su ke yi.
cikin zazzakr muryarta ta durkusa har kasa tace "barkanku da yamma"
"barka kadai gimbiya" inji Mujib. "Da fatan mun same ki lafiya kalau"?
"lafiya kalau ". kunma har a wannan lokaci tana durkushe bata mike ba.Mujib ne ya sake cewa "to gimbiya Zainab mike mana ai mun gama gaisawa".
"a'a ba komai hakan ma yayi" ta sake fada. A tare bakin nata suka hada ido sai kawai suka zube a gabanta suma suka durkusa. cike da mamaki tace "lah ya haka kuma"?
"Tun da gimbiya na durkushe ai kuwa ba mu ga ta tsayuwa ba". Bata san sanda wata 'yar gajeriyar dariya ta subuce mata ba. san nan ta mike tsaye. mikewar tata yayi dai dai da zuwan Mallam wanda ya karaso wajensu dauke da kujerun roba guda biyu. hakan ya sanya su suka zauna a kujerun yayin da ita kuma ta zauna a dan dakalin dake bakin varender gate din.
Bayan nan suka sake sabuwar gaisuwa. mujib ne ya nuna mata Al Bashir ya ce "kin gane shi"?
ta dan dago ta saci kallansa sai kuma ta girgiza kanta alamun a'a. cike da zolaya yace "da gaske Zainab baki gane ni ba. ni kuwa tun randa na fara ganinki na yi printing din fuskar ki a zuciyarta". murmushi ta sake yi cike da jin kunya san nan tace "Allah da gaske nake kayi hakuri ban gane ka ba”.
“Amma dai ina fatan daga wan nan haduwar zaki gane ni ba tare da na sake introducing kai na ba”.
“In sha Allahu” ta amsa masa tana mai nuna jina kunya.
Mujib ne ya sake gyaran muryar tare da cewa “to malama zainab ni dai suna na Mujib Sani shi kuma wanda kika kase ganewa sunan sa Bash. …” mintsinin da ya kai masa shi ya hana shi karasa sunan da ya fara fada.
Nan take ya gane me yake kokarin shaida masa. Take kuwa ya gyara kuskurensa yace “shi kuma sunansa balarabe. Kuma shi ya ganki yaji kuma yana da ra’ayin ki zamo abokiyar rayuwarsa idan har kin aminta da shi”.
Shiru ita dai bata yi Magana ba sai wasa da take da hannayenta ta cikin hijabinta.
Kiran sunanta da Mujib yayi shi ya sanya ta sake dago kanta. Tana dagowa kuwa suka hada ido da AlBashir wanda ya kura mata ido. Itama ta dan yi tsai da idanuwanta cikin nasa san nan ta yi kokarin kau da nata idanuwan.
Nan dai Mujib ya yi ta kokarin ganin ya dasa bishiyar kaunar Al Bashir a cikin ranta. Duk da dai basu sami tartibiyar amsa ba, amma sun gamsu da yadda ta yi musu.
Shi kuwa AL Bashir duk da ba wata Magana mai yawa ya samu yayi da ita ba, Amma tsayuwar ta kawai kusa da shi ya sanya shi jin wani nishadi.
Khalil ne ya karaso inda suke tsaye cikin gatsali yace “ke kizo momi tace ki zo ki dora abincin dare”.
Bata jin dadin yadda ya tsinka ta a gaban bakinta ba. Kuma tabbas suma sun gane bata ji dadin hakan ba. Da yaji shiru bata bashi amsa ba ya sake cewa “ko in je ince ba zaki zo ba. In kuma na fada kin san sauran jikinki ne zai gaya miki”.
Ya juya zai tafi, Mujib ya yi sauri janyo shi yana fadin “yi hakuri abokina. Yanzu zata zo kaji kar ka gaya wa Momi komai”.
Ya kalleta cike da tsiwa. Yace “kin yi sa’a. da yau na kalli kukan yaya babba tana shan duka”. Yana fadin haka ya juya ya bar wajen.
Al Bashir ya lura da kwallar da ta ke kokarin sharewa cikin dabara tana kokarin kar su ganta.
Yayi ajiyar zuciyar na takaicin abin da aka yiwa Zainab dinsa. San nan yace “waye wannan”?
“kanina ne” ta amsa masa a takaice.
Ya sake ajiyar zuciya y ace “shi ke nan Zainab shiga gida. Sai gobe idan na sake dawowa”.
Ta sake durkusawa har kasa tace “na gode ku gai da gida”. San nan ta juya ta bar su tsaye a wajen su kuma suka rakata da kallon tausayi. Ba su tafi ba sai da suka yiwa mallam sallama. Shi kuma ya sanar da shi lambar wayar Zainab, wacce itama Baba laure ya sa ta dauko masa wayar. Ba ko kbo a cikinta saboda haka sai please call me yayi zuwa wayarsa san nan ya samu damar kwafar lambar tata.
Suka fita mashin kuma yaki tashi haka suka hakura suka tura shi suna tafe suna tattauna yadda suka samu Zainab.
Albashir ne ya fara tambayar Mujib yace “yaya is she worth the trouble”?
“She is worth more than that. Ta bani tausayi matuka. And from yadda kaninta yayi embrassing dinta a gabanmu is a clear indication na bata da wani galihu a gidan. Amma fa gaskiya abokina tayi. Such rare beauty is very scarce”.
“Ok fine kaima daga yau bazan kara zuwa da kai ba. Dama ai zancen farko ne kawai aboki yake rakiya. Daga yau kagama”.
Dariya ya saka san nan yace “ai kaima ka san ko ba serious relationship bane once ka furta ni kuwa na haramta kaina zuwa wajen. So just trust me. Kuma kasan na gaya maka ni Meena nake jira ta gama secondary ka bani ita”.
“au wai da gaske akan wan nan small girl din”.
“shi yasa na ga wadda muka baro wajenta is over thirty five. Ita ma wan nan ta girmi Meenan ne”?
“Fine kaje neman auren Meena. Amma bani zan raka ba. Don bazan je gaban ‘yata ina wage baki da sunan na rako abokina zance wajenta ba”.
“Ai tunda na shigar maka kasuwar gwanjo zaka iya yi min duk wulakancin da kaga dama. Nima bance zan kiraka rakiya ba”.
Haka suna hira suna tura mashin din nan basu yi realising ba sai ganin su suka yi daga Hotoro NNDC gidan su Zainab har sun iso round din Ahmadu Bello Way. Wanda su kuma Alu Avenue zasu shiga inda gidansu yake.
Sule mai mashin dai Allah ya taimake shi, saboda suna isa gida aka bashi kudi ya sayo sabon mashin su kuma ya gyaro musu wan nan saboda zuwa wajen Zainab.
[8/6, 23:24] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 18
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Da misalin sha daya na dare, zainab zaune a kicin din gidansu. Kowa yayi bacci banda ita. Yini tayi ta na murjin meat pie guda dari biyar da Momi ta samu odar sa. Da karfe bakwai na safiyar washe gari tayi alkawarin masu shi su zo su dauka. Kunnenta sanye take da ear piece tana sauraron radio ta cikin wayarta.
Duk wanda ya santa, ya san ta da wan nan dabi’ar. In dai tana aiki to kuwa sauraron radio take yi. Da haka take saurare direct daga radion, sai ranar da Farisa ta ringa yi mata masifa akan tana damunsu da jiye jiyen radion ta, wanda ita kuma itace abokiyar hirar ta. Hakan ya sanya take manna ear piece a kunnenta.
Ta san programmes din kusan kowacce tasha da kuma lokutan yada su. Amma yau abin da ya bata mamaki, ringin taji a wayarta ta, wanda ya katse mata shirin duniya labari da take sauraro a tashar freedom.
Da sauri ta matsa amsawa a tunaninta Momi ce zata bata wani sakon.amma tana sallama kamar yadda ta saba sai taji bakuwar murya ta amsa mata sallamar da tayi.
“me kike yi har yanzu baki yi bacci ba”? aka tambaya daga daya bangaren. Sai da ta dago wayar daga inda take ajiye a kasa saboda ta ga waye mai kira da wan nan tsohon dare. Bata ga suna ba sai bakuwar lamba da ta gani.
Ba shiri ta maida hankalinta kan wayar tace “yi hakuri wa kake nema ne”?
“wacce nake nema na samu. Ko ba Zainab ce nake Magana da ita ba”?
“itace ,amma don Allah kayi hakuri ban gane wa ke Magana ba”.
“Allah ya sani Zainab zaki sa zuciyata ta buga, ina nan na kasa sukuni da tunaninki amma ke har kin manta da ni”.
Ta dan yi ajiyar zuciya san nan tace “ka yi hakuri da gaske ban gano waye ba”.
“na yarda Zainab. To bakon dazu ne Balarabe”.
Murmushi tayi mai sauti wanda har sai da yaji sautin sa ta cikin waya, san nan tace “kayi hakuri ban dauki muryarka ba. Barka da war haka”.
“barka kadai Zainab” shi ma ya fada cikin jin dadin yadda yaji alamun murna da jin sautin muryarsa.
San nan ya ci gaba da cewa “mu dawo maganar mu ta dazu. Me ya hana ki bacci har wan nan lokaci”?
Tabbas tayi murna da jinsa , saboda tsayuwarsu yau daya taji shi a cikin ranta. Ta kuma kasa daurewa har sai da ta sanar da baba laure bakon da ya zo mata da la’asar. Ita ma kuwa ta taya ta murna, ta kuma nuna mata cewar kar taji komai in dai har tana sonsa, saboda ta kan Mallam suka biyo.
Ta fada mata haka saboda shi ma Mallam din iya abin da ya sanar da matarsa ke nan. Take kuwa ba ta san yadda akayi ba sai jin muryarta tayi tana cewa “idan na mayar da wan nan tambayar kanka zan samu amsa”?
“Me kuwa zai hana Zainab”?
“To na tambayi abin da ka tambaya’
Kai tsaye yace “tunanin santaleliyar yarinyar dana hadu da ita shi ya hanani bacci. Kin ji amsa ta ni ma kuma ina sauraron taki amsar”.
“Ni labarai nake ji”.
“kai Zainab. Ni nan na rasa sukuni saboda ke amma ke kin ma saka ni a kwandon shara. Kin ma manta da ni gaba daya”.
Ba ta san san da ta dada kasa da sautin muryar ta ba, tace “kayi hakuri ba haka bane. Amma idan kaji ba dadi kayi hakuri. Ka san komai sai a hankali”.
Kwarai ya yaba da hikimarta. Ga shi dai bata fito kiri kiri ta nuna tana ra’ayinsa ba. Amma kuma yaji dadin yadda ta karbe shi.
Saboda haka yayi ‘yar karamar dariya yace “hakane Zainab. Na yarda da maganar ki. Amma yanzu duk da haka ki taimaka mini inji kwakkwarar bayani. Shin kin amince dani kokuwa. Ki taimaka min Zainab inji Magana daya daga bakinki”.
Kunya ce ta kamata kamar yana ganin ta. Ya ji alamun haka saboda haka yace please Zainab ki taimaka min ko na samu kwanciyar hankali idan naji Magana mai dadi daga wajenki”.
Cike da kunya tace “Allah ya tabbatar mana da Alkhairi”.
Daga inda take tana jin alamun murna a sautin muryarsa in da ya ci gaba da cewa “na gode Zainab. Hakika yau kin faranta min raina yadda ba kya tsammani. Allah ya tabbatar mana da alkahiri”.
Kwarai ta shagala da jin dadin hirar da suke yi shi da ita. Gaba daya taji nishadi na shigarta. Aiki take yi amma bata taba jin dadin aiki irin yau ba. Kafin kiransa a gajiye take matuka, saboda Allah Allah take ta karasa ta kwanta. Amma sam tun da ya bugo wayar ta gane wake Magana taji gajiya ta bar jikinta. Cike da nishadi taci gaba da danne meat pie din da ta zubawa nama. Tana yi tanajera shi a cikin kwalin da zata sanya a freezer kafin masu shi su zo dauka washegari.
Cikin sassauta murya yace “bani labarin abin da kikaji a cikin radion”. Nan kuwa ta shiga bashi labarin duniya dalla dalla.
Ya yaba da knowledge dinta a a current affairs. Ku san duk abin da yaji a tashar CNN da BBc world shi ta maimaita masa.
Sai da ya nisa san nan yace “you are very current. Ina ga alamar jourrnalist zaki zama . sam bata gane me yake nufi ba saboda haka tayi shiru bata bashi amsa ba.
Nan dai ya dinga janta da hira, har ta gama aikinta ta karasa gyaran kicin din. Ba shi ya daure yayi sallama da ita ba sai wajen sha biyu da rabi. Ya rabu da ita da alkawarin washe gari zai kawo mata ziyara.
Momi na barin gida washegari tayi sauri ta shirya ta shiga gidan su Fatu da kokarin ta sameta kafin ta wuce makaranta. Ta kuwa sameta ranar bata da lecture sai bayan goma. Cike da zumudi ta zayyana mata labarin dan kyakkywan bakon da ya kawo mata ziyara jiya da kuma wayar da suka kwashe lokaci mai tsawo suna yi da shi.
Feelings da ta ke ji a tare da ita bata taba jin makamancinsa ba. Ji take yi kamar ta janyo lokacin da yace zai sake zuwa wajenta. Ranar dai a anan ta lalace bata je islamiyyar safe ba haka nan bata bar Fatu taje tata makarantar ba. Domin suna ta tattauna batun Balarabe sai dubawa suka yi su kaga sha biyu tayi.
Da sauri tayi wa mama hajjo sallama ta koma gida.
Kamar yadda yayi alkawari. Ta na kokarin karasa hada abincin dare bayan sallar isha Mallam da kansa ya zagayo inda take a kicin tana aiki ya shaida mata cewar Balarabe ya zo.
Da sauri ta karasa abin da ta keyi. Ta canza hijabin jikinta san nan ta nufi wajensa. Sai da ta dauki jug ta zuba matsattsen lemon zaki a ciki, san nan ta nufi bakin gate wajensa.
Yau shi kadai ne. tun kan ta karaso daddaan kamshin turarensa ya bigi hancinta. Ba tare da saninta ba ta ja numfashi ta shaki kamshinsa sosai. Tun da ya hangota fitilar gidan ta haske ta ya kura mata ido. Bai taba ganin macen da ta iya taku irin na Zainab ba. Ga shi dai da dan hanzari take tafiya, amma sai ka rantse rawa take.
Sai da ta iso gabansa san nan ya saki ajiyar zuciya. Shi ya sa hannun ya karbi jug din yana fadin “barka da fitowa gimbiya”.
A kunyace ta dago ido suka hada nata da nashi. Dan duster da ta riko ta cikin hijabinta, ta saka ta goge bakin verander tace “Bissimmillah zauna”.
“ni in zauna ke kina tsaye, ai kuwa haka bazata yiwu ba”. Tana kokarin zama gefen verender da sauri yace “kai kai dakata”.
Da dan firgice ta juya tana kokarin tambayarsa abin da ya faru. Kafin tayi Magana sai gani tayi ya sanya gefen shaddarsa wacce da ace ta san kudinta to ta haura dubu dari. Amma haka ya sanya bakin rigarsa ya goge mata gefen da ta goge masa.yace “kema zauna my putri”.
Ba ta san me yace da ita ba amma dai ta fahimce wani suna ne na jin dadi ya kira ta da shi. A wajen da ya goge mata ta zauna. Shima ya zauna a dan nesa kadan da ita suka saka tray da ta zubo masa lemo a ciki a tsakiya. Ta dan rankwafa ta gaishe shi kamar yadda tayi masa farkon zuwanta, san nan ta zuba lemon a cup ta mika masa.
Cike da jin dadin abin da ta yimasa ya dauki lemon nan. Ya sha rabi ya na kokarin ajiye sauran, kawai bata Ankara ba sai jin muryar Khalil tayi yana cewa “eyeh lallai. Zainab kin rika. Jug din da Momi ta ware wa bakinta shi kika dauko kika kawo wa Bala mai gwanjo saboda kin raina Momi. Yau kuwa zaki gane kurenki”.
Gaba daya ji tayi wutar kanta ta dauke saboda takaicin wulakancin da Khalili ya yiwa bakonta da ita kanta. Amma ta san babban ganganci ne ta nuna masa hakan. Kafin ta yi Magana yace “kin ga save your breath. Momi ce ta ce ki zo ki hadawa bakinta abinci, saboda su Farida da Farisa are very tired kin san su ba NFAs bane sun dawo daga IT sun gaji.
A jiya Zainab tsakannin shabiyun rana zuwa na dare sai da ta dana samosa 500, spring rolls ma haka, da kuma meatpie shi ma same quantity, hakan kuma bai sanya ta ragi aikin gidan da take da komai ba, amma wai masu zuwa IT ten na safe su dawo 1 na rana sune suka fita gajiya.
Khalili kuwa sauri yake yaje ya gayawa Momi labarin jug din data dauko, saboda haka ya na gama fadin haka ya yi gaba abinsa. Ganin haka ya sa ita ma ta mike da sauri ta ce da Al Bashir “yi hakuri ina zuwa”.
Kafin ma ya amsa mata ta bi Khalil da sauri. Shi dai mamakin wan nan yaro yake. Ji yake kamar ya tashi ya rufe shi da duka, saboda wannan ne second time yana wulakanta masa Zainab dinsa.
Tana jiyo sautin muryarshi yana sanarwa Momi labarin jug dinta na acrylic da ta kaiwa bakonta waje. Tana kuwa kokarin hada musu abinci Momi na caccakar ta tana masifar jug din da aka kaiwa bako ruwa a ciki. Bata tanka mata ba ita dai kokarin hada abincin take yi a dinning. Sai da ta gama komai su kuma suka zauna suka fara ci wanda ta dauki minti ashirin, san nan ta koma a tunaninta ma zata tarar ya tafi, amma ga mamakinta tarar da shi tayi zaune suna hira da Mallam.
Ta zauna sun dan fara hira bai fi da minti goma ba, sai ga Farida ta iso wajensu. Ita kam sun yi gaisuwar mutunci don har ta yi introducing kanta a matsayin kanwar Zainab. Ya dan ji dadin ganin yadda ta mutunta ta. Amma shi ma abin takaice ta kalleshi tace “sorry to intrupt you. Amma Momi tace kizo ki kwashe plates a dining ki gyara kitchen”.
Tana fadar haka tayi masa sallama ta koma ciki. Daga ido tayi tana kallonsa, kafin ma tace komai yace “kar ki damu Putri jeki zan kira ki anjima”.
Tayi masa sallama ta dauki jug dinta ta shiga gida. Tana bada baya, AlBashir yace “mallam haka Zainab take fama da ku a gidan nan”?
“Ai kuwa haka take fama kullum”, ya amsa masa. Sallama suka yi ya karasa bakin mashin din Sule ya dauko leda mai dan girma ya mikawa Mallam yace “don Allah mallam kar ki karba. Kayi hakuri”.
Sai bayan ya tafi Mallam ya bude yaga kykkyawan yadi mai laushin gaske da kuma turmin atamfa duk da bai san kudin su ba, amma tabbas ya san masu dan tsauri ne.
[8/6, 23:25] +234 814 948 5104: FINI A UBA I👪👪
N FIKI A MIJI💏💏
PAGE 19
BY HANNE ADO ABDULLAHI
kusan tun da suka rabu da Al Bashir cikin tunanin sa take. Da ta tuna wata Magana da suka yi shi da ita sai ta saki murmushi kamar wata sakarya. Ita Kanta bata san sanda murmushin yake kwace mata ba.
Baba Laure na hankalce da ita, har ta kasa daurewa tace “uwata yau wane irin nishadi kike ciki ne. ni dai ina ga Balaraben nan ne sanadin wan nan farinciki naki”.
Kunya taji matuka na yadda ta bari har baba Laure ta gano yanayin shaukin da ta ke ciki. Ba ta dai amasa mata ba. Amma fa duk da haka yanayin fuskarta bai canza ba.
Yau bata da aikin snacks, amma Momi ta sanar da ita da safe da waina da ganda zasu karya a gidan. Kuma ta tabbatar sun dahu kafin bakwai da rabi na safe. Ganin ba pressure pot garesu ba, ya sanya ta hada gawayi a makubur din su, ta hada gandar ta dora ta barta tana dahuwa a hankali.
Niyyarta data gama hada kullin masa, sai ta kwanta. In yaso ta samu bacci ko na awa hudu, san nan ta tashi tayi kokarin yin nafilar da ta saba, sai ta hau danin wainar.
Kirrrrr karar waya ta katse mata tunani. Tsayawa tayi tana kallon fuskar wayar kamar fuskar mai kiran zata gani a ciki. Sai da tayi ringing uku san nan ta sa hannu ta latsa kiran.
Sansanyar muryarta ce ta doki kunnensa wanda ta aika masa sallama da ita.
Shima cikin shauki ya amsa mata. San nan cike da zolaya yace “ina fatan yau tunani nane ya hana ki bacci”.
“idan yin hakan laifi ne ayi min afuwa, zan daina”.
“haba putri salju. Abin da nake addu’a ya kasance sai kuma ince an yi min laifi. Ai fatana in shiga zuciyarki in yi kane kane, yadda ba wanda zai samu shiga, wanda yake cike kuma in hankido shi waje ya fada kwata”.
Dariya kawai tayi san nan tace “kar ka wahalar da kanka. Barka da dare”.
“barka kadai putri salju”.
“sai dai ka san ban san ma’anar sunan da kake kira na da shi ba. Kar ko ce min kake zainab mai katon baki”.
“Akwai madubi a tare da ke”?
“a’a me kake so ayi da shi”?
“So nake kije ki tsaya ki karewa kanki kallo. Ki gaya min meye bashi da kyau a fuskarki, kama daga goshinki mai kyalli kamar watan dan dare sha hudu. Wanda ya fito da kyawawan dara dara kuma fararen idanunwanki. Su kuma suka hadu suka kara fitar da kyakkyawa siririn hanci , wanda da ya taso bai tsaya a ko ina ba sai da ya iso inda kyakkyawa bakin ki mai dauke da siraran labba, wanda cikin sa yake cike da kanana, hakora farare tas da su. Af nayi mantuwa akwai wata siririyar wushirya da ta dada kawata su. Kamar yadda fuskarki ta kawatu da dimples.
So ki duba a madubi kiga ina na kuskere ban fasalta ba. Ko kuma ina kike jin na fadi da daidai ba”.
Murmushi kawai tayi ta kasa bashi amsa. Sai shine ya sake cewa putri salju yana nufin coolprincess, kuma wani yare ne na wani gari dana taba zaman ci rani”.
Bata gane me cool proncess din ke nufi ba, amma dai ta daure bata nuna masa ba. Ya sake ci gaba da tambayarta. “mu dawo maganar dazu, me kike yi baki yi barci ba”?
“waina nake kokarin hadawa. Ko zaka ci”?
“idan an bani mai zai hana. Ko yanzu sai in biyo in karaba”.
Sai da ta sake dariya mai cike da nishadi san nan tace “a’a ba zaka samu yanzu ba, sai dai da safe idan zaka iya zuwa”.
“wanda yace zai zo da tsakar dare ta ina kika ga safiya zata wahalar da shi? Karfe nawa ki ke son in zo in karba”?
“Idan zaka iya zuwa takwas zuwa tara zaka same ni. Idan ka wuce haka kuwa zaka daki gurbi”.
“in sha Allahu kuwa zan zo. Ke dai tanadar min waina ta. Yau ba kya jin labarai ne, ko dai hira dani tafi labaran dadi”?
“kai yaya b………” bata san yadda akayi ba taji ta kasa kiran sunansa. Nan dai hira ta barke a tsakaninsu, duk da shi ke fiye da rabin zancen. Amma ga mamakin ita kanta zainab din kusan shine bakon mutum na farko da ta ji tana iya sakewa da shi har tayi musayar Magana da shi din.
Washe gari kuwa zainab tayi abin da bata taba yi ba. Tana sauke naman nan ta debi parts masu kyau guda hudu, ta samu dan karamin flask ta zuba a ciki. Kafin takwas da rabi ta gama gyara ko’ina.
Al Bashir na ganin motar Momi data dadi sun fita daga gidan, ya karasa ya shiga ciki. Kamar ko yaushe mallam ne yayi sallama da ita. Sanye cikin shudin uniform wando da riga da kuma cream colour hijabi na yadin makarantarsu ta fito. Hannunta dauke da flasai guda biyu.
Bayan sun gaisa ta gabatar masa da wainar da tayi masa alkawari. Lomar farko da ya kai bakinsa sai da ya lumshe idanuwansa saboda dadin abincin nan. Bai taba cin waina mai laushin ta ba, haka zalika shima dahuwar jelar san tayi dadi matuka. Ga kamshin kayan kanshi yana tashi wanda daka bude kwanon shi zai maka sallama.
A wajen Mama Hajjo ta koyi dabarar sa spices sau biyu a girki. Ta zuba kadan domin fitar da karnin daga farko san nan idan girkin ya dauko dahuwa ta kara kadan saboda ya fitar da kamshi. Haka zalika bata daka spices ta ajiye. San da zata yi girki san nan take daka su, saboda sun fi kamshi a haka.
Yana ci suna hira yake tambayarta wacce makaranta take zuwa.
“umar bin Khattab, ta’alimul Qur’an” ta amsa masa.
“iyeh ashe mutuniyar tawa ya sayyada ce. Yanzu izunku nawa”?
“mun yi sauka da biye shekara uku da suka wuce. Yanzu kuma saura mana bai fi izu goma ma mu gama da hadda ba. Wanda muna san ran nan da wata uku zamu hattama, saboda kasa ne. kuma tun lokacin muna biye mun samu haddar sama da izu talatin ku san yanzu maimaitawa ake”.
“ma sha Allah. Ni kawai kice in sayo allo ga malama har gida. Ba bulala ba kudin laraba”.
Dariya kawai tayi bata bashi amsa ba. Sai da ya gama cin abincinsa wanda ya cinye tas duk da yawan sa, san nan yace “thank you putri salju for a wonderful meal. Na san abin da naci will carry me for most of the day”.
Tana jin yana tsaro turanci taga ya kamata ta sanar da shi cewa ita ba ‘yar boko bace, saboda kar yazo ko mai jin turanci yake so ita kuma ta yaudare shi.
Sai da ta dan saci kallonsa san nan cikin sanyin murya tace masa “kayi hakuri ni bana jin turanci”?
Shima cikin sanyin murya yace “Me yasa ba kya jin turanci”?
“Saboda bani da kokari aka cire ni a makarntar boko daga primary na tsaya. Sai aka mayar da ni islamiyya”.
“shekararki nawa Zainab”?
“ashirin’ ta amsa masa a sanyaye.
“kar ki sake cewa kanki baki da kokari. Haddar Qur’ani tafi ko wane karatu wahala. Duk kuwa wanda ya same ta, to ba wani karatu da zai gagare shi a duniya. Turanci kuma ba lalle ne kowa sai ya iya shi ba. Idan kikaje kasashe da yawa musamman yankin Asia da Europe duk da yaransu suke karatu da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
A nan kasar ne kawai idan baka iya turanci ba mutane suke ganin ka koma bayan al’umma”.
“ai kuwa ba dadi kowa ya iya abu ya zamana kai kadai ne baka iya ba”.
“fine and good. In dai turanci ne mastalarki ni kuwa nayi miki alkawarin koyar da ke”.
Take kuwa fuskarta ta kasa boye farin cikin da take ciki. Sai da ta shiga ta mayar da kwanukan da ya ci abinci san nan ta fito dauke da school bag dinta. Tare suka fita, shi yana tura mashin dinsa ita kuma tana gefensa suna tafe suna hira. A nan ya samu ya sanar da ita asalinsa da na iyayensa da kuma labarin yayyensa da family dinsu. Duk da dai ya rufe mata level of affluence dinsu, da kuma shi matakin karatun sa.
Ya nuna mata shima iyakarsa secondry school daga nan ya shiga kasuwa. Tsoron kar ya kwafsa ya saka shi bai bata detail story na kasuwar ta sa ba.
Sun fi minti arbain suna tafiya, kafin suka iso makarantar tasu . tabbas ya jinjina mata nisan makarantar da gidansu, amma ya lura yaga ita ko a jikinta hakan ke nuna ta saba da nisan.
A bakin kofar makaranta ya sa hannunsa a aljihu ya dakko wrapper daya ta dubu goma sababbi ya mika mata. Bata amsa ba tsayawa kawai ta yi tana yi kallonsa.
“Don Allah kar kice min bazaki karba”.
“don Allah kar kace sai na karba. Kudin sun yi yawa”.
“ba abin da yake da yawan da zan kasa baki shi. Kuma trust me kasuwar tamu yanzu akwai alkhairi. Please ki karba ko kudin break kya yi da su”.
“Duk da haka mu bi komai a sannu. Kar mu durkusar da kanmu”.
Yana kokarin yi mata magiya ta karbi kudin daga hannunsa ta zari guda biyar daga wrapper ta bude aljihusa na gabar rigarsa ta zura sauran a ciki. Yana kokarin yin Magana, tace “Please nima na roke ka mu bar maganar haka.in dai kyautar ce wan nan ta ishe ni. Shima dan kar kace naki karba ne”.
Tana yi masa sallama ta shige gate din makarantarsu. Ta bar shi yana kallonta cikin tsan tsan tausayi. Yarinyar is so humble yet classy. Ita bata san da kyar ya daure ya bata dubu goman da ya dauko ba, saboda ko driversa ya kan bashi haka a kyauta kawai,balle ita da yake jin zai iya mallaka mata duk abin daya mallaka a rayuwarsa,
[8/6, 23:26] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 20
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Kusan kullum sai AlBashir ya kaiwa Zainab ziyara da safe kafin yaje office.
Wahalar mashin dai yana fama da ita, amma sam ko ajikinsa. Idan Mujib yayi masa tsiya sai yace masa “muna bata lokaci ne kawai zuwa gym, but this is a better exrcise”.
Shi dai Mujib tun zuwan su na farko sau daya ya kara rakiyar zance, saboda ya koma portharcourt in da yake aiki a kamfanin SHELL. Shi kuwa kullum sai ya kai ziyara gidansu saboda haka fahimtar juna na dada wanzuwa a tsakaninsu.
Ya kuma fi son zuwa wajenta da safen saboda ya lura ba a interrupting dinsu sabanin zuwan yamma da kuma na dare, da bata minti biyar a tare da shi wani bai zo yakirata ba. Haka suke hirar a tsintsinke, har dai ya hakura ya tafi.
Amma yau da yazo da safe lokacin da ya saba sai ya ganta tare da su Momi da duk sauran yaran gidan ana ta loda kaya a mota. Guri daya ya samu ya labe ya kuma yi sa’a ba wanda ya lura da shi.
Tas suka loda kaya cike da but, mota biyu. Daddy da Momi a daya, yayin da yaran gidan suka shiga Venza. Gaba daya suka tafi. Shi har ya tsorata ya dauka ko tafiya suka yi zuwa wani gari, Zainab bata shaida masa ba. Amma Mallam na kokarin kulle gate sai ya hango ta cikin uniform dinta.
Wani irin farin ciki yaji ya lullube shi. Domin kuwa ya san da tayi tafiya, zai yi kewarta ba kadan ba. Tana kokarin shiga gida sai muryarsa suna gaisawa da mallam ta tsai da ita. Shi ma kuwa da hanzari ya karaso in da take, ya bar mallam na kokarin kullo gate din.
“ai yau hawan jini ya kusa kamani”.
“don Allah yayi hakuri kar ya kamaka, ko don ya tausawa min”.
“Ashe har kina tsorona da ciwo, amma ni ban kai ga gane hakan ba. Kin barni sai rara gefe na ke yi”.
“Hm kai baka da dama”. Ta durkusa sosai tare da fadin “barka da safiya”.
Ba karamin nishadi yake ji idan tayi masa irin wan nan gaisuwar ba. Sai yaji shi kamar wani basarake. “Barka kadai” shi ma ya amsa mata. Ya karasa ya zauna a wajen da ya saba zama. Itama ta karaso ta zauna a gefensa.
“Mu dawo maganar dazu. Ki na tsorona da hawan jini, amma ba kya kareni daga shi”.
“Gaya min abin da zan maka in hana hawan jinin kamaka”.
Sai da ya dan nisa san nan yace “Idan na fada kin yi alkawarin yi min abin da nake so”.
“In har bai fi karfi na ba, nayi maka alkawarin yi maka duk abin da ka ke so”
“Ki kwalli cikin idona kice min I love you my sweet heart.yin haka zai saka ni inji sanyi a cikin raina. In kuma daina kokwanton matsayi na a zuciyarki”.
Kasa tayi da idonta san nan cikin sanyin murya tace “ba kullum baki kan furta asalin abin da ke cikin zuciya ba, amma idan mutum ya lura halayyar dan Adam kan iya yi masa nuni da abin da ke cikin zuciyar”.
Sai da ya dan yi tafi san nan yace “yarinyar nan ashe wayo gareta ban sani ba. Amma hakan ma ya gamsar da ni. Tun da kullum cikin kykkyawan yanayi na ke ganin ki. To amma ina mutan gidanku suka tafi dukkansu kika yi saura sai ke kadai, ko da sauran mutane a gidan”?
“Su farida ne zasu koma makaranta shine duk suka yi musu rakiya”.
“A wane gari suke karatun”?
“A sudan”.
Cike da mamaki yace “Sudan? To ke me ya hanaki tafiya Sudan din”?
Fuskarta ta dan nuna damuwa, san nan tace “Tun farko na sanar da kai bani da kokarin boko. Kaga Farida Medicine take yi. Farisa kuma computer”.
Cike da haushi yace “and they left you to be their maid”.
Ta dago ta kalle shi san nan tayi murmushi tace “ina ga kana mantawa na gaya maka ban iya turanci ba”.
“aikuwa in sha Allahu zaki koye shi. Yaushe zasu dawo”?
Ta daga kanta alamar tunani. Ta tuno da lissafin da Momi tayi mata, in da ta bata dubu goma a kan ta dinga sayen abinci a ciki. Amma fa ta hada da gargadin idan anyi ciniki kar ta taba mata ko kwabo, ta kuma lissafa mata yadda tafiyarsu zata kasance, san nan tace “eh to watakila suyi wata biyu, saboda sunce idan sun je Sudan suka gama ko ragisrarashin, sai su wuce Saudiyya suyi ummara. Daga nan kuma su kaiwa anti Bilki ziyaraa can kasar sin”.
“yanzu ke da waye a gidan”.
“daga ni sai Baba laure ko da yake ita tana wajenta a baskwata”.
Sai da ya daga kai ya kalli girman gidan san nan yace “kuma ke ba kya tsoron kwana ke kadai a cikin gidan nan”?
Ta dan yi murmushi san nan tace “ni bana wani jin tsoro.kuma ma na saba suyi tafiya su barni ni kadai”.
Take yaji ransa ya baci. Tabbas matar nan is wicked, ba abin da ya dameta da safety ko tarbiyyar yarinyar nan. Amma ya danne bacin ransa yace “me ye ragisrarashin”.
Abin da dalibai suke yi idan zasu koma sabon zangon karatu”.
“OK you mean registration”.
“Eh shi”.
“ok repeat after me re-gis-tra-tion”
Sai da ta maimaita wajen sau uku kafin ta samu ta fade shi daidai.
Sai da yaga ta samo wan nan yace “to daga yau idan nazo zamu yi English lesson na atleast one hour”.
Ta gyada kanta alamar ta gane. Amma duk da haka sai da ya saka ta ta fahimci ma’anar kowacce kalma da ya fada.
Ganin gidan bakowa sai suka samu sake. Washegari da zai zo ya taho mata da wayar TECHNO irin ‘yar dubu hamsin din nan. Da yake ba sanin darajar waya tayi ba, bata fahimci mai tsada bace. Haka zalika ya jibgo mata tarin litattafan koyon turanci da kuma spelling. Kullum kuwa yazo haka zai kashe lokaci yana koyar da ita turanci. Bayan nan ya dauki sarar yawaita Magana da turancin a tsakaninsu, kuma zai bata lokaci ya bata dama tayi ta canka har sai ta gano ma;anar abin da yake nufi.
Haka zalika yana yawaita encouraging dinta data yi simple sentences da turancin. San nan ya bata lokaci wajen koya mata amfani da wayarta ta yadda zata shiga dictionary ko kuma google ta gano ma’anar kalmomi da kanta.
Haka nan kullum idan yazo zai sakata, ta koyi spelling at least 10 new words da kuma meaning dinsu. Ba shi ba ni kaina na yaba da kokarin Zainab. Saboda dai simple sentences ta iya constructing din su da kyau. Haka nan ta na fahimtar zancen da ya kan yi mata da turancin.
Haka kuma dan chatting din da ya koya mata suke yi lokuta masu yawa shi ma ya taimka mata wajen fahimtar yaren turancin. Abin ya so bani mamaki amma sai na tuna zancen wani malami da ya ce duk wanda ya iya harshen larabci, koyon ko wan ne irin yaren a duniya ba ya masa wahala.
To itama advantage din data samu ke nan. Zainab dai na samun attention amma aikinsa Allah ya sa yana da mataiamaka na kwarai da an samu matsala. Amma Alhamdu Lillah kwalliya tana biyan kudin sabulu, saboda kuwa dan dai turanci daya biyu na kare yawa yana samuwa. Haka zalika rubutu ma ana samun ci gaba. Ga kuma jajircaccen malami ga kuma daliba maikwazo sai komai ya tafi daidai.
Yau su Momi sun dauki sama da sati hudu basa gida. Ba abin da ke hada su illa idan an kira Momi a waya ana bukatar snacks ta yi wa Zainab waya ta bata instruction din abin da ake nema.
Damuwarta kadan ce saboda da dama ko suna gidan ba wata mu’amala da ke hada su in dai ba wani abu za a sakata ta yi ba. Farida ce kawai dama dama, domin ita har hira tana zama tayi da ita. Ga kuma yawan alkhairin da ta ke mata. Domin ko wan nan shopping din da suka je sai da ta sayo mata roll on na sure guda biyu da kuma body spray din su. Ta hado mata da turaren splash na VICTORIA SECRET GAEDEN.
Da zata tafi kuma ta bata kayan sawa wadan da ta cire zata bayar saiti shida kuma duk masu kyau da tsada, haka nan ba su ji jiki sosai ba. Da kuma wasu designer turararruka da kadan suka yi kasa da rabin kwalbar, guda biyu.
Ita ma kuwa haka ta dage da kanta ta tambayi Momi kaji aka sayo tayi musu dambun nama mai dan Karen dadi. Ta yi mata fura wacce baba Laure ta koya mata ta shanya ta bushe. Ga su tankwa da busasshen attarugu duk ta hada musu. Har da yajin daddawa aka sayo kayin hadi Mama hajjo ta hada mata. Ita kuma ta kai inji nika ta tankade musu shi.
Saboda haka ba wani kewar su tayi ba da ba sa nan. Balle kuma yanzu da take cloud seven watau duniyar masoya. Ba karamar kewa Balan ta mai gwanjo yake dauke mata ba.
Kullum sai ya kawo mata ziyar da safe da kuma yamma, san nan da dare su sha waya da shi. Ita ba sayen katin waya take ba, saboda haka bata san tsadarsa ko arahar sa ba. Sai kuma ya kara da yi mata wayo, inda ya sanya mata dubu hamsin a wayarta, yace da ita tayi ta waya ko yaushe MTN ne suka bata bonus na dubu hamsin din. Haka kuwa ta yarda.
A wan nan rana da ya shigo da safe ya sanar da ita zai kawo abokanan sa su gaisa da ita. Bayan ya gama koyar da ita karatu yayi sallama ya tafi da alkawarin zuwa shi da abokansa bayan la’asar.
Nan take ta shiga tunanin me zata basu idan sun zo. Kudin da Momi ta bata ta dinga sayen abinci tana ci ta duba taga saura dubu biyar da dari shida. Saboda dama tun da ta duba taga lissafin kudin sai ta daukarwa kanta, da safe ta sha ruwan bunu. Da rana ta ci a gidan su Fatu ko kuma ta karbi tuwon BabaLaure. Da daddare kuwa sai ta ci bread na sittin ta sha ruwa. Balle kuma dama ita gwanar azumin litinin da alhamis ce. Idan tayi bude baki sai ta sayo indomie super pack guda daya. Taci da magariba, sai ta rage kadan tayi sahur ta sha bakin shayi. Shike nan.
Saboda ta fitar da shi kunya tayi abin da samari kance ‘a wajen gayu da girma ya fadi gara jari ya karye’. Itama haka tayi kuddumus mutuwar kazar kuku, ta dauki kudin nan. Ta sayo kazar ta guda daya ta dubu daya. Ta sayo mince meat rabin kilo da flour rabin kwano da kuma sauran kayan meatpie da samosa.
Ta sayo lemon bawo na dari uku, sai man gyada rabin kwalba. Sai da ta kashe dubu uku da dari takwas. Ta duba taga abin da yai saura mata baifi dubu daya da dan wani abu ba. Amma a yau ba abin da ya dameta irin ta farantawa Al Bashir rai.
Ta zauna ta murza meatpie.ga shi kwaben yayi kyau, sai da ta samu guda goma sha hudu. Samosa guda ashirin. Da ta ga man ba zai ishe ta suya ba. Sai ta gasa meatpie din a murhun gawayi saboda dan guntun gas din dake gidan kwanan su Momi biyar da tafiya ya kare.
Itama kazar tayi musu gashi mai kyau da kuma dadi. Lemon kuwa barewa tayi ta nika ablender ta mai da shi juice.
Kafin la’asar ta kammala komai. Ta samu plates masu kyau ta saka a ciki. Kazar kuma ta zuba aflask. Ta samu jug mai kyau ta zuba lemon. San nan ta debo ruwan sha a dispenser gidan ta sa a wani jug din. Komai dai can a can. Balle dake ta samu sake ba wanda zai hana ta daukar komai.
Ta share verender bakin falon babansu. Ta dauko carpet ta shimfida. Bayan ta idar da sallar la’asar ta rangada wanka. Acikin kayan da Farida ta bata wadanda ta gyara, ta dauko riga da skirt na wani cotton lace mai kyau ta saka. Kayan suka yi mata cif kamar dama daidai jikinta aka dinka. Ita kanta ta yaba da kyan da tayi.san nan tabi jikinta ta feshe da turare. Tana jinkiran wayarsa ta yi murmushi ta saka hijabinta mai hannu ta nufi waje.
Su hudu ta gani, har da shi. Har kasa ta durkusa yadda ta saba gaishe shi haka tayi musu. Suma cikin fara’a suka amsa mata. Tayi musu jagora har bakin falon. Sai da suka zauna ita kuma ta shiga cikin gida domin hado dan entertaimaent din da tayi musu.
“where did you find this clean item” ? daya daga cikin su ya tambaya.
“kyauta daga Allah” in ji AlBashir.
“Amma fa mun wahala. “inji Mujib. “can you imagine we had to spend the whole day a kasuwar gwanjo. Ai I promise duk sai na kai ku kun ga wajen. It was just awful”.
“For such classy babe I can spend ten years in prison”. Shi ma dayan ya fada.
“Ina ga gwara in sallame ku, ba wani amfani da zaku yi mun anan” Al Bashir ya fada.
Gaba daya dariya suka saka ganin kishinsa kiri kiri. Dayan zai bashi amsa Zainab ta fito hannunta dauke da katon tray. Shi ya tashi da hanzari ya karbeta yana fadin “putri salju ba sai ki kirani in dauka ba”.
Ba ta bashi amsa ba sai dan murmushi da tayi. Sai da ta zuba musu ruwa da lemo kowanne san na aka sake sabuwar gaisuwa. Ya kuma nuna mata abokansa tare da introducing dinsu. Ya nuna na kusa da shi yace “wan nan shine Mustapah,ga kuma Sa’ad. Sai kuma”.
Ta katse shi da fadin da cewa “ai shi na gane shi. Ba Ya Mujib bane”?
“shine ashe kin gane shi”?
Ba tayi Magana ba sai murmushi da ta dada yi. Mustapah na gutsirar meatpie yaji wani irin dadi ya ratsa shi. Bai sanda yace "Amma dai wan nan daga Madina aka kawo shi ko”?
Gaba daya suka tuntsire da dariya. Ita dai bata shiga cikin zancen zolayar da sukewa junansu ba. Sun taba hira kadan duk da dai ita bata cika sa musu baki ba. Balle lokuta da dama da turanci suke Magana. Duk da bata ji duka ba, amma tana fahimtar wasu zantukan nasu.
Da ace tana da exposure, to da kuwa ta lura da yanayi jikinsu da kuma suturar da ke sanye a jikinsu da ta gane masu kudi ne na gaske. Amma bata da wan nan ilmin. Sai da sukaci suka koshi domin kuwa sun cinye kusan komai data kawo musu.
Mustapha ne ya sanya hannu a aljihunsa da niyyar debo kudi. Idon Al Bashir kir a kan aljihunsa ya ganshi yana kokarin zaro dollars daga aljihunsa. Da sauri yace
“chill bro. the case is low profile”.
“but the object is classy and worth it. It is supposed to be a high profile case”. Inji Sa’ad.
“forget it it’s a long story. Thats why we had to spend a day at bend down and pick boutique”.
Duk iya kokarinta bata fahimci zancensu ba. Ta dai dauki sabbin kalmomi a kanta da niyyar idan sun kebe ta tambaye shi fassararrsu. Ita tana tunaninta su kuma suka ci gaba da tattauna maganganansu.
“amma duk da haka we cant leave with out giving any percuma for her”
“Yeh a I agree but make it kacik”.
Sa’ad ne ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye mata. Suka mike tare da yi mata sallama.shima ya mike domin rakasu.
“Putri ina zuwa”.
Tare suka fita. Sai da sukaje yaga wata katuwar thundra a fake a kofar gidan kusa da mashin dinsa. Yace dasu. “Amma you guys almost flop my plan. Data fito ta gan ku da wan nan motar fa. Me zaku ce “?
“very simple sai ince ni driver ne a wani gida na dauko motar gidan na fito raka abokina zance.” Mustafa ya amsa musu.
Dariya suka saka duk kansu. Sai da suka shiga zasu tafi Sa’ad ya leko yace “When you are done, call us so that we can come and pick you”.
“kar ku damu. Sai na dawo I will call you back”.
Inda ya tafi anan ya tarar da ita zaune a gefen verender. Shima gefenta ya zauna a gefen carpet din da ta shimfida. Suna hada ido dukkansu murmushi ya subuce a fuskarsu. Shi yasa hannu inda kudin suke ajiye ya dauko yace “ga sakonki, ko kin bani”.
“da kai kaya duk mallakar wuya ne”.
“Kin san me ina jin dadin duk sanda kika nuna min I have right over you dadi nake ji”.
“Ni kuma yin hakan shine babban burina a rayuwa”.
Zai yi magana tace me ake nufi da profile. Na san dai high sama ke nan. Amma ban san fassarar case da profile ba”.
A dan firgice ya juya ya kalleta. Amma sai ya dake yace “forget it. Amma a ina kika sayo snacks din nan ba karamin dadi suka yi ba. Kina ganin mun yi abin kunya, sude kwano a gidan surukai harda tauna kashi”.
“Na ji dadi da kunyi enjoying abin da na kawo muku. Amma ai snacks a gidan nan ake yinsu, saboda Momi tana na sayarwa. Kusan kullum sai nayi”.
“amma naga bata nan” ya fada cikin dan bacin rai”.
“Eh ai ko bata nan ana placing order kuma tun da dama ni nake yi, duk da haka anayi tun da dama……” sai kuma ta kasa karasa abin data fara fada.
“Tun da dama ke kike yi. Ke ba kya gajiya ne na lura kullum cikin hidima kike”.
“Lah a ai bashi da wuya. Don dai in yi samosa da spring rolls guda five hundred kowanne in a day”.
Bai ce mata komai, saboda ji yake ransa na suya. Ita ‘ya’yanta na karatu ta maida ta wata baiwa. Bai dai ce komai ba, sai ma kudin ta da ya mika mata. Fir taki karba, sai da ya nace san nan ta zari guda biyu daga ciki, san nan tace “rike sauran a wajenka”.
“Kyauta ko ajiya”
“kayan Allah ai na Annabi ne ko kuwa”.
“naji na yarda,amma please ki karbi kudin nan”.
“kayi hakuri ba na son in na maka musu, amma ka taimaka ka ajiye su a wajenka.
Washe gari kuwa wani mutum yazo akan yana sallama da ita. Bayan sun gaisa ya fada mata cewa maigidansa ne ya aiko shi sayen snacks a wajenta. Da sauri ta gaya masa kudin ko wane. Tana jin sa yabuga waya yake fada. Bayan yayi sallama ya ajiye ya juya wajenta yace “maigida yace shi ga yadda yake saye kuma haka zai saya amma in har zaki sayar”.
Tayi mamakin price din da ya ambata saboda abin da zai saya sai da ya ninka kudin kowanne sau uku. Baba Laure ce ta sanya ta ta karba. Ta kuma nuna mata tayi wan nan order kanta ce bata Momi ba. Tun daga ranar kuwa kusan kullum za a zo sayen snack. Kuma kullum tayi ciniki bata samun kasa da ribar dubu ashirin.
Ita dai bata san me saye ba. Sai dai saboda kudin da ya kara sai ta kara masa girma da kuma yawan fillings din ciki. Amma duk da haka kudi take caska ba na wasa ba. Sai ta shiga tarasu a wajen mama Hajjo saboda saukar da take burin yi wan nan shekarar. Da kuma tunanin saka kanta a LEGal kamar yadda kawarta tayi. Haka zalika tana burin idan sun yi aure sai ta taimakawa Bala ya kara jari.
Shi kuwa Bala mai gwanjo /AL Bashir, shi ke dibga mata wan nan ciniki ba tare da sanin ta ba. Kuma da yazo bata boye masa komai ba na sabon customer da tayi da kuma cinikin da yayi mata.
Shi kuwa a bangarensa, idan ya sayi snacks ya kan kaiwa Ummansa da kuma sisters din shi. Kuma ko bai saya ya kai musu ba zasu tambaya, saboda a cewarsu ba su taba cin mai dadin wanda yake sayowa ba. Shi dai bai sanar da su daga ina yake sayowa ba.
[8/7, 21:33] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 21
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haushi bai kara kama Al Bashir ba sai da ya ga irin garar abincin da Zainab ke shirya mishi. Abin da ya faru, wata rana ne ya je wajenta suna hira. Ta lura da hamma da yake ta dokawa. ta kalle shi ta ce “kamar kana jin yunwa”?
“wallahi kuwa” ya amsa mata. San nan ya ci gaba da cewa “kin san sana’ar tamu. Yau da ciniki gobe sai godiyar Allah. So nake ma in fara daukar dealer tawa ta kaina, in daina tsinta, saboda yin haka yafi riba. Hmmm” wata hammar ta sake katse shi.
“ina zuwa “ kawai tace da shi. Ta juya ta shiga gida. Dama ta dan tsinto kayan abinci da ribar cinikin da ta ke yi. Tana shiga cikin sauri ta dafa masa jollof din taliya wadda ta wadata da busasshen kifi da kuma alabasa. Sai da ta dakko dahuwa, san nan ta nika dan attarugu ta da sweet pepper ta zuba a ciki. Ta kara kayan kamshi kadan ta rage wuta ta barta ta karasa a hankali.
Ta yanka gwanda kanana, ta hado ta doro komai a tray. Nan dai bakin vereander Mallam inda suka saba zama ta kai masa. Tana bude flask din wani daddadan kamshi ya bugi hancinsa. Sai da ya shaki kamshin abincin nan san nan ya hadiye yawu.
Nan kuwa ta zauna tana zuba masa yana ci tana dada wata daga gefen plate din domin tayi sanyi. Kafin ya gama da ta gabansa ta sake tura masa wadda ta fifita masa. Yaci abincin nan sosai. Sai da ya gama ta zuba masa ruwa ya sha.
Ta tura masa plate din gwanda, yana sha sannan tace “kuma dealer da kake son dauka da tsada”?
“Kai tsadar ma. Tana kaiwa dubu saba’in zuwa da biyar”.
“idan nayi wani abu kayi alkawarin ba za kayi min musu ba”
“come on don’t trick me ki sani yin abin da yafi karfina”.
“Allah nayi alkawarin ba zai fi karfin kaba”.
“To shi ke nan nayi”?
Kudi ta ciro daga cikin hijabinta kashi kashi. Tace “taya ni kirga wan nan”.
Ya dinga ware su yana hadawa. Sai da ya gama hada su tsaf san nan ya kirga. Dubu dari da sittin da shida da dari biyar ya samu. Ya gaya mata san nan ya mika mata.
“barsu dai a wajenka. Lissafi zamuyi. Bani twenty daga ciki”.
Ya kirga ya mika mata. San nan ta sake cewa. “ka sake ware min sha biyar din ka bani”. Ya sake yin yadda tace.
Yana bata yana fadin
“lallai hajiyata ashe kudi gareki haka. Shine baki aika an kawo miki security ba”?
“meye security”.
“sorry tsaro nake nufi. Ko da yake kina da masu tayaki zama a gida saboda haka ba wani tsoro ma da zaki ji.
“Ka manta ne amma tun farko na sanar maka ni bana jin tsoron zama ni kadai. Na saba zama ni kadai a gidan nan, ba tare da kowa ba”.
Da hanazari ya maida kallonsa wajenta. “ban gane kin saba zama ke kadai ba. Kina nufin da su Momi suka yi tafiya ba wanda ya zo tayaki zama? Da ki ka gaya min hakada farko na dauka tsokanata ki ke yi, ko kuma za a turo masu tayaki zama daga baya".
Ba tare da nuna damuwa ba tace
“Mh mh ni kadai ce”.
Sai da ya daga ido ya kalli gidan san nan yace “yanzu duk girman gidan nan ke kadai ce, ba kowa a cikinsa”?
“lah to meye ai na saba. In dai nayi addu’a ba tsoron da nake ji”
Muryarsa can kasa yayi zagin da bai san sanda ya kubuce ya fito daga bakinsa ba. “bloody awful people” ya furta.
“Sorry Magana kake ban ji me kake cewa ba”.
Nan da nan ya waske yace “mh mh ina mamaki ne kawai saboda ni har yanzu na kasa rabuwa da mamana. Ga dakina ga nata. In fita kofar gida ma na kasa, saboda tsoro”.
Dariya tayi tace “wan nan kuma ba tsoro bane shakuwa ce”.
“eh amma ni kin yi min laifi. Tun da nake zuwa baki taba bani ummanmu a waya mun gaisa ba”.
Nan da nan yanayin ta ya canza alamun damuwa kadan ya bayyana a fuskarta. Ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun ta. Tace “kayi hakuri nima bani da numberta shi yasa”.
“yaya zaki ce baki da number mahaifiyarki”?
“eh to dalilin ne ya faru. Rabona da ita na kai ten years. Ba ita ba rabona da inje Kera ma haka”.
Wani irin tausayinta ne ya tsirga masa. Nan ya dinga bugar cikinta cikin wayo har ta sanar da shi inda kakanninta da kuma Umman ta suke.
Sai da ya gama digesting wan nan information din san nan yace “kin barni da tulin kudi a hannu baki ce min komai ba”.
Ba ta ce komai ba sai da tattare kwanukan da ya ci abinci. Ta mike da niyyar shiga gida, san na tace “ashirin ta ishe ni biyan kudin sauka. Sauran kuma sun ishe ni in saro kayan snacks dina. Saboda haka kayi amfani da sauran ka dauko mana dealer da kake Magana akai. Amma please ka ware dubu daya da dari biyar na kai, kayi mana sadaka saboda samun sa’a”.
“A’ a ba za ayi haka ba”.
“gaba kawai yai abinta tana fadin “kace ina gai da Umma da su Yaya Ai”.
Bata bashi damar amsa komai ba tayi shigewarta gida. Tun daga wan ana rana kuwa ta daukarwa kanta ciyar da shi da safe da kuma yamma da yake zuwa wajenta. Kullum kuwa ya zauna ta kwashi dariyar santi.
Ya gwada kawo mata dan cefane wai ya tallafa mata. Kaji hudu ya saya ya kawo mata. Yadda ya kawo su haka ta gashe masa su ta saka a foil ta ba shi. Sai da ta zo raka shi yaga ta saka leda a kwandon gaban babur din. Kafin ya tambayeta meye ta shiga gida.
Sai da ya isa gida ya tarar da yayyensa biyu da kuma ummansa da kuma kanneta maza guda biyu. Ya shiga da kullin a tunaninsa ma ko snacks ta zuba masa. Amma ana budewa wani kamshi ya doke su dukkansu. Nan kuwa suka dinga ci suna santi. Uncle Sani har da tambayar ina ya sayo shi ma ya bi ya sai ma iyalinsa. Ya ce masa bashi akayi.
Ba tare da saninta ba yayi kokari ya nemi inda mahaifiyarta take aure a garko. Yana tsammanin yaga gidan talakawa. Yayi mamakin ganin irin arzikin mijin mahaifiyarta ta. Gida ne bulo da bulo. Ga rufin kwanon jinin talaka an shimfida shi. Da ya shiga cikin gidan kuwa ko ina marbles ne a shimfide banda wajen harabar gidan da ya sha interlocks.
Mallam Usman yayi murnar ganinsu matuka. Su hudu su ka je shi da abokansa. Duk da a Bala mai gwanjo da kuma abokansa suka je ya mutunta su kwarai da gaske. Babban falonsa ya sauke su yana ta murna diyarsa ta samu miji.
Nan kuma masu aikin gidan suka shiga hidimar kawo entertainment. Ba a san da zuwansu ba, amma hidimar kabakin abincin da aka sauke su da shi sai kace wadanda suka halarci hadaddaen party.
Sai da su kan dan huta san nan akayi musu sallama da Maman Khadija domin su gaisa. Da ganin kyakkyawar suturar dake jikinta da kuma yanayinta ka san matar da ake so ce kuma ake kula da ita. Babu alamun hustling a tare da ita.
Duk da dai cikin hijabi tazo amma hakan bai hana su ganin kyawunta da kuma tsananin kamar da suka yi da Zainab ba. Tana fita kuwa Sa’ad yace “Allah ya sani wan nan mata tana da kyau mai tsanani”. Dariya suka saka. Mujib tace “bari mai gidan yaji kana yaba matarsa. Kaga sai kasa muyi asarar wadda muka zo nema. Mukoma da kai an yi mana rotse”.
Sai da ya daidaici sun gama san nan ya dawo falon. Sabanin mahaifin Zainab, shi kam MallamUsman ya tsaya tambayar yar kure na son sanin asalinsu da kuma sana’ar su.
Har Mustafa ya fara bayanin gwanjo, Mujib ya dakatar da shi da fadin “Mallam kayi hakuri cikar kamalarka ba zata bari muyi maka karya ba. Mun boye asalin mu da kuma sana’ar mu saboda da farko da muka nuna kanmu a zahiri an so hana mu Zainab, amma da muka dan yi basaja sai kuma muka samu sa’a."
Nanya zauna ya gaya masa asalin ko su su waye. Kusan duk wanda ke nahiyar Kano ya san sunan mahaifin ALBashir. Take Mallam Usman yace “kai kanin Aisha Usman ne”?
“mallam ashe ka san yaya Ai”? ya amsa a cikin ladabi.
“kwarai na santa mun yi BUK tare. Duk da dai ba fannin mu daya ba. Amma harkar student union ta sa muka san juna sosai. Kuma maigidanta abokin wani yayana ne. domin shi ko kwanaki da sukaje Ummara mun hadu dasu”.
Take murna ta kamasu na ganin akwai sanayya a tsakaninsu. Ya kuma gamsu da nasabar su duk da dai bai san halayyar yaron ba. Amma yaji dadin ganin akwai ta inda zai bincikin halayyar yaron. Duk da ya san bada aure ko hanawa ba nashi bane, amma hakan bai hana shi binceken ba.
Kannenta ne suka shigo da driver wanda ya kai su kano sukayo shopping din su a Shoprite. Sun yi murna kwarai da bakin da suka gani. Nan kuma hira ta koma sabuwa da kannen nata. Ganin wanda zai aureta ya sanya sukaji kamar ita suka gani. Saboda in ban da Hafasa da kuma kaninta mai binta Faruk sauran duk ba za su iya shaida ta ba. Sai dai labarinta da suke ji a wajen Abbansu.
Su Albashir sun yi mamakin ganin yadda kannen nata suke wayayyu. Kamar ba girman kauye ba. Ga kanwarta hafsa da ya tambayeta inda take karatu ta sanar da shi ta gama Turkish. Yanzu NTI university zata. Da ta dauko wayarta kuwa domin karbar number Zainab yayi mamakin ganin IPhone ce a hannunta.
Kannenta ma guda hudu duk a nan suke boarding section dinsu. Shi kuwa mallam Usman yayi mamakin irin arzikin da ya same shi da shi. Motar hawa ma TACOMA 2014 yake hawa, yayin da ummanta Venza take hawa. Yayi mamakin dalilin zaman su a kauye.
Sai kusan la’asar ya sanya su, su fito ya karasa da su kauyen kera domin gai sawa da kakanin Zainab. Har sun fito zasu shiga motarsu honda accord 2016 sports version yace “a’a gwanda mu hau mai dan tudu saboda yanayin hanyoyi namu”.
Tafiyar da bata fi ta dauke su minti talatin ba amma sai da suka dauki kusan awa daya. Can ma Mallam Usman ne yayi hidimar gabatar da su a wajen su Baffa.sun dai sha tsokana. Domin shi Baffa Abdullahi yace a kwai bashin bulalar shadi guda dari a kanta, saboda haka sai Al Bashir ya shirya ya karba,
Cike da farin ciki suka baro garin bayan dimbin alkhairin da suka ajiye musu, wanda su Baffa suka yi fada akai. Amma cikin wasa Mustafa yace “cin hanci muka baku saboda ku saki auren Zainab mu mu samu mu aura”.
Haka suma su Nenne kakaninta su kuma suka ce musu sadakin su ne suka biya saboda su yiwa kawarsu zaman daki. Cike da farin ciki suka baro garin. A gidan Mallam Usman ne dai ba su basu kudi ba, amma sun bawa yaran gidan kyautar dubu dari da sunan su sha ice cream.
[8/7, 21:39] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 22
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Hajiya Rumaisa kuwa da ta debi yara da sunan mai da su makaranta sai da ta yi yawon shakatawa da su san nan ta mai da su. Ni kaina ban sani ba dama hutun nasu bai kare ba ko kuwa tsabar gata ne ban san abin da ya faru ba.
Da farko sun shiga Sudan suka dau tsawon kwana hudu. Nan suka ce tun da karatu bai yi zafi ba,za su bi Momi da Daddy yawo. Inda zaka san da plan dinsu duk visa su iri daya ce. Bayan sun bar Sudan, China suka wuce direct, anan ne Momi ta karbi makudan kudade a wajen Daddy da sunan zata yiwa yara sayayyar kayan aure. Komai na mutum uku ta saya. Daddy yaji dadi matuka ganin yadda ta hada Zainab da yaranta ta sai musu komai iri daya.
Bilkisu taji dadin wan nan ziyara ta su. Ga Momi ga Daddy ga Farida ga Farisa ga kuma ‘yar uwarta Sakina. Sosai tayi murna da ganinsu. Anan ne kuma aka ragargaji sayayya.
Daga nan suka yi tunanin shiga makka domin Ummara, amma ita ma tun da sukaje harami sau daya, basu sake komawa ba. Sai yawan mall mall da suka dinga yi. Malam Usman ma, ya debi nasa iyalan sun je ummara saboda alkawarin da ya yayi wa Hafsa na cewar idan jarrabawarta tayi kyau zai kaita ummara. Ya kuma cika mata alkawari har kannenta ma suka samu albarkancinta.
Ya san kwana biyu kafin tahowarsu Al bashir ya kai musu ziyara. Kuma tabbas bayan nan ko ranar da zasu taho sun yi waya da Hafsa kuma ba wanda yaji labarin za su zo kasa mai tsarki. Saboda tun da Albashir yaje zuwan farko zumunci na waya kullu tsakanin ta da mutan gidan da mahaifiyarta ta ke aure.
Gaskiya daga Dr Abdalla har hajiya Rumaisa ba su ji dadin yanayin da suka ga Khadija da mijinita a ciki ba.
Ga kyawawan ‘ya’yansu masu dimbin ladabi da biyayya. A wulakance su Rumaisa da nasu 'ya'yan suka gaishe su kamar yadda suka saba gai da dangin mahaifinsu.
Shi kuwa Mallam Usman bA wan nan ne a gabansa ba. Rashin ganin Zainab tare da su shi ya daga masa hankali.
Ya san kawaicin matarsa. Ko meye zai faru ba za ta taba nunawa ko a fuska rashin ganin su da Zainab ya sosa ranta ba.
Saboda haka suna shiga masauki, da hanzari yace “Hafsa nemo min wayar yayarku”.
Da sauri ta buga. Ringing daya na biyu ana uku ta dauka. Cike da murna tace “’yar kanwata kina lafiya”?
“lafiya kalua Zainabu. Ba ita ba ce Abban kune”.
Cikin dariya mai nuna ladabi tace “Lah Abba ban san kai bane. Abba barka da war haka”. Ta gaishe shi tare da dan rusunuwa kamar tana gabansa. Wan nan kuma al’adar ta ce. Domin ko shi Al Bashir idan zata gaishe shi a waya sai ta dan rusuna kamar yana kallonta.
Shi ya ci gaba da Magana, yace “zainab ina mutan gidan ku”.
“Abba sun yi tafiya. Sun je kai su Farida makaranta”.
“Tun yaushe ke nan sukayi tafiyar”?
Ta dan daga kanta alamar lissafa wani abu. San nan tace “Abba yau satinsu shida da kwana hudu”.
Kamar zai ce wani abu sai kuma yayi controlling kanshi. Yace “shike nan ba damuwa. Abin da nake so dake ki kiyaye mutuncin kanki ki kuma tuna komai ki ka yi Allah na kallonki. Kar ki yi san ranki don ganin ba idon dan Adam a kanki”.
“In sha Allahu Abba zan kiyaye. A dai ci gaba da samu a addu’a”.
“ba komai Zainab. Me kike so na sayo miki in zamu dawo”.
“Nan take ta tuna ankon bakar after dress da zasu yi naa sauka. Saboda haka da hanzari tace “Abba in so samu ne ina son bakar after dress”.
“Bayan nan fa”?
Ta sake cewa” Abba ita kadai nake so”.
Ba yadda bai yi da ita ba ta fadi wani abun, amma sam taki. Daga bisani ya mika mata ummanta da sauran kannen suka gaisa. Hafasat ce ta fita da wayar domin su dan sha hira da yayarta. Gashi dai dan kwanaki ne da fara mu’amalar ta su amma kai kace sun dade da juna yadda suka shaku. Sukan iya kashe sama da awa daya suna hira a waya.
Sai da ta shiga daki. San nan tace “Yaya Zee ina ya Bala”? nan dai suka dinke da hira. Sai da za suyi sallama ita ma ta bata sakon turare mai dadi saboda lura da tayi Balan ta mai son kamshi ne.
Tsaftar sa da kuma iya gayunsa yasa ya ke dada birgeta. Ba wanda zai kalle shi yace talaka ne a tunaninta. Sai da ma Fatu ta gaya mata ai masu san’ar gwanjo haka suke da gayu saboda suna samun kaya masu kyau kuma da sauki.
Da suka dawo kuwa driver ya dauko su a airport sai da suka fara zuwa wajen Zainab, saboda sanin da suka yi na cewa ita kadai ce a gidan. Tayi murna matuka da ganin mahaifiyarta da kuma sauran ‘yan uwanta da kuma Abbansu Hafsa. Rabonta dasu tun ran da taje Garko wajenta babanta yayi mata dukan kawo wuka. Ba yadda bata yi da su ba su shiga sam suka ki. Anan cikin mota suka gaisa. Akwati guda Abban ya mika mata a matsayin tsaraba. Ita ma Hafsa ta bata wata ledar mai dauke da turarrruka har shida duk kuma designer. Na mata uku na maza uku.
Anan ne kuma ta san ashe Mallam ya san Abbanta. Ya kawo kudi ya bashi,san nan sukayi sallama suka tafi.
Da AlBashir kuwa ya kawo mata ziyara da la’asar ta debo kayan da Abbanta ya sayo mata, wanda ya kasance after dress masu kyau da tsada guda goma da kuma wasu rin dogayen riguna na Morocco masu dan veil a kansu suma kala kala guda goma. Ta dai dauki after dress guda biyu da kuma doguwar riga daya. After din da doguwar rigar ta bawa Fatu. Ta bawa mama Hajjo turare guda daya. Daya kuwa ta bawa Baba laure.
Sauran kayan nan haka ta hada su sai ga AlBashir ya kawo mata ziyara. Nan dai inda suka saba tsayawa da shi bakin verender Mallam nan suka tsaya. Bayan sun gaisa. Ta debo tsarabar nan baki daya ta bashi. Tace “ka sayar da kayan na dauki daya na kuma bawa Fatu daya. Ga kuma turare Hafsa ta kawo maka”.
Ya dauki turaren Giogio for men ya bude shi sai da ya shaki kamshinsa san nan ya bude kwalbar yana fesawa. Wani dadin kamshi ya baibaiye su. Sai da ya lumshe idonsa domin dadin turaren, san nan yace turare dai na dauka, amma banda kayanki. Idan na dauka inyi me dasu. Ki ajiye mana ki dinga yi min kwalliya ina ganinki ina jin dadi. Da ace ina da hali ai da kin ga kayan kwalli…….”
Ita kanta bata san sanda ta kai hannunta ta rufe bakinsa ba alamun bata son maganar da yake yi. “Please na roke ka kar ka kuma yi min makamanciyar maganar nan. In ba haka ba zamu bata. Haka na ganka kuma haka nake son…..”
Sai a lokacin kuma taji kunya ta kamata na abin da tayi da wanda ta fada.
Shi kuwa he kind of froze saboda dadin kalamanta. Ya san tana son sa amma bata taba fitowa ta fada kuru kuru ba sai yau. Akwai dai alamun kauna da kyautatawa da ta ke nuna masa.
Ba shiri ya yi wani dana tsalle tare da juyin 360. Ya bude kwalbar turaren ya ci gaba da fesa musu shi da ita yana fadin “bari kawai yau ayi kamun amarya da ango, tun da yau amarya da kanta ta furta asirin zuciyarta”.
Kunya ce ta kamata ba shiri ta tashi da saurin tana kokarin guduwa. Take ya gano wayon da take son yi. Ba shiri shi ma kuwa ya cafki gefen hijabinta ya rike yana fadin “please kar ki kashe min tsananin farin cikin da nake ji a a yau din nan. Na san ki na kaunata, amma nayi ta mafarki ki furta sai yau kuma na samu amma ki na neman ki guje min. haba Putri salju na”.
Da kyar ya rarrashe ta ta tsaya, amma fa still yana rike da hijabinta. Tace to ka sakar min hijab mana ai na fasa guduwa”.
“tab di jan naki wayon. In saki kigudu ki barni” ya fada da maganar yara, wacce ta sa ta dariya. Haka ta saki jiki suka ci gaba da hirarasu.
Su Momi ba su dawo ba sai bayan kwana hudu da dawowar su Mallam Usman. Saboda daga Saudiyya sai suka nemi long transit VISA suka kwana uku a a Dubai. Na ma dai wasu kudin aka sake murkushewa. Wan da daga nan ne suka yi sallama su yaran suka hau jirgin komawa Sudan har da Khalil da yayi joining dinsu wan nan shekarar. Su kuma suka dawo da Halim da Hanif da kuma Sakina da yaranta guda biyu.
Ba zata suka yi mata saboda Momi ta so kamata da laifi, amma batayi sa’ar yin haka ba. Saboda ita dai yadda ta saba haka taci gaba da kula da gidan. Bai dameta ba da aka zo ana rabon tsaraba ita ba a bata komai ba, saboda ta saba da haka ranta bai baci ba. Ita kuwa yanzu ba abin da ke damunta in dai zata samu damar ganin rabin ranta to kuwa ba abin da zai bata ranta.
Kusan duk abin da Momi ta nunawa Dadi da sunan zainab ta sayawa, ashe karya take ‘yan gidansu ta rabarwa. Ba abin da ta bata. Da suka zauna da Dadi tace masa “waini Zaunab tazo tayi maka godiyar tsarabar da aka kawo mata”?
“Ni bata zo tace min komai”.
“kai ni na rasa bakin halin irin na wan nan yarinya. Yanzu duk abin da aka saya mata amma bata yi appreciating ba saboda kawai ba ayi tafiya da ita ba”. A dan hasale Daddy ya amsa wa Momi da cewar "tafiya ba ita jawo wa kanta ba. Itama da ta yi karatu ai da da ita za a dinga zuwa ko ina. Amma tunda haka ta zaba, sai ta zauna tayi ta sakarcinta. Ai tun da ma ta samu mai sonta, gwara kawai a aurar da ita”.
Yana fadar haka Momi taji faduwar gaba, saboda kuwa ba ta tsammaci jin haka daga gun daddy ba. Idan ta tafi wa zai ci gaba da yi mata bautar da Zainab ke mata. Ai kuwa zata san yadda zata lalata zancen auren nan.
[8/7, 21:39] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 23
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Tun da mutan gidan nan suka dawo, Zainab bata huta ba. Allah ya taimake ta ko ina na gidan a share yake kal kal da shi. Da farko suna shigowa aka bawa driver kudi yaje ya sayo kayan abinci. Ba ita kuwa ta samu ta gama sorting din su out ba sai bayan isha. Ta sa food stuff a store a cikin robobin da suke arranging kayan abinci.
San nan ta dawo kan perishables ta wanke condiments ta barsu suka tsane san nan ta bi ta duddura su a cikin zip lock, yanda zasuyi saukin dauka idan za ayi amafani da su. Ta saka su a freezer su wacce take daban data nama.
Sannan ta dawo kan nama da su kaza da kifi da dai sauran su irin su kayan ciki da su ganda. Suma haka kowanne ta wanke shi ta barshi ya tsane, san nan shima ta duddura tasa a zip lock din. Suma ta zuba a tasu freezer.
Hatta fruits da vegetables sai da ta gyara. Su kuma kowanne da fridge dinsa. Ta debo ruwa da drinks masu yawa ta zuba a fridge din wajen dinning inda nan ne ya kasance nasu wurin zaman. Sauran kuma tayi arranging din su a kantar store din gidan. Hatta su tuna da su salad cream sai da ta zuba su a pantry cupboard dake kitchen san nan ta dawo dora abincin dare.
Ana tamabayar me za adora Anti Sakina da bata wuce gidan ta ba tukunna tace sakwara. Su Halim sukace wake da shinkafa. Ita Momi tace ferfesun kayan ciki da soyayyen dankalin hausa take sha’awa. Haka ta zage ta bata lokaci wajen sallamar kowa.
Ba dai ita ta samu kwanciya ba sai bayan sha biyu na dare saboda sai da ta jira suka gama san nan ta gyara ko’ina. Ga shi kuma an bata dokar da safe tayi doya da kwai da ferfesun naman kai. Daddy kuma ayi masa kosai. A kuma dama kunun gyada.
Saboda haka tanayin sallar asuba ta dora daga inda ta tsaya jiya.
Misalin tara na safe taji wayar Balanta yana kira, alamar yazo ke nan. Baba Laure ta bawa sako ta kai masa. Doyar data soya ta zuba a foil paper ta kuma hada masa da dahuwar da tayi ta zuba a ‘dan wani karamin flask da ta sayo musamman domin haka, tace ta mika masa zata kirashi a waya.
Tayi hakane gudun abu biyu. Ta san da taje zai shagaltar da ita har su Momi su tashi ba ta kammala abin da ta sa ta ba. Ko kuma a fito a same shi a gidan da safe bata san yadda zasu dauki al’amarin ba.
Mallam mijinta ta bawa ya mika masa sakon. Yana jin abin da ta fada ya kalle shi yace “hala mutan gidan sun dawo”. Shirun Mallam din shi ya dada tabbatar masa da cewa sun dawo. Ya sake cewa Mallam “kar ka damu In sha Allahu komai ya kusa zuwa karshe”. San nan yayi masa sallama ya nufi mashin dinsa da abin Karin da masoyiyarsa ta bashi.
To ita fa tana wan nan kujiba kujiba ne kuma Momi ta kai saranta wajen mahaifinta na kinyi masa godiyar tsarabar da tayi karyar ta bata. Duk suna zaune kuwa a dinning suna karyawa ya kira ta. Ta tsugunna da ga gefe kamar yadda ta saba. Nan kuwa ya rufe ta da fadan da ba ta san dalilinsa ba. Fadi yake yi “ni kin raina ni kin dau bakin cikin ‘yan uwanki da sukaci gaba kin dorawa ranki. Kuma na fada miki in dai ni kina son mu shirya dake karatu na so kiyi kika yi. Saboda haka banga dalilin da dan anyi musu abu saboda kwazon su za ki dinga bakin ciki akai ba”.
Nan dai ya dinga fada. Ya dauki kusan miti ashirin yana tsattsagar Zainab a wajen.ita dai in ban da sharar hawaye ba abin da ta ke yi. Sai da yayi iya yinsa, san nan ya sallameta ta tafi. Sai da ta gama hidimar abincin rana wajen karfe uku ta shiga daki domin ta kimtsa ta tafi islamiyya, san nan taga miss call din Bala guda goma sha hudu, sai a lokacin ta tuna tayi alkawarin kiransa.
Kafin wayar tayi ringing ya dauka. Irin daukan nan in flashing ka so yi sai an ci katinka. Ta yi sallama ya amsa mata muryarsa can kasa alamun rauni. “yaya na ke jin kamar baka da lafiya”?
“Ina zan yi lafiya Putri Salju? Kwata kwata yau ban ganki ba banji muryarki ba”?
“Subahana Lillahi. Me yayi zafi haka? Kai dai kawai ragwanta ke damunka”
“A kan soyayyarki Zainab ni rago ne na karshe ma kuwa. Kina ganin na shigo wajen aiki na kasa komai. Ga Mujib nan ya sakani a gaba sai tsokanata yake yi. Please Zainab kiyi min izni in zo in ganki ko na ji dadi da sanyi a cikin raina”.
“kayi hakuri aiki ne ya dan sha kaina har na sha’afa da kiran ka da nace zan yi. Wayar kuma na sata a caji a daki saboda haka ban ji tana ringing ba. Yanzu kaci abinci”?
“Ina na kasa shan ko ruwa ne tunda banji muryarki ba”?
Ta yi kasa da muryarata alamar rarrashi, san na tace “yi hakuri Ya Balarabe daure ka tashi kaci abinci. Ka samu ko paracetamol ne ka sha. Duk da dai sauran kwana goma bikin saukar mu, amma yau zan ki zuwa makaranta in jira zuwan ka, in har zaka iya zuwa”.
“Invitiation din da kika bani ya sanya naji na wartsake gaba daya. Nan da la’asar zaki ganni”.
“yawwa jarumi na. ai na san kai jajirtaccen mutum ne. Ina ya Mujib din bashi mu gaisa”.
Yana karabar wayar yace “ranki dade yau kin kada ‘yan maza har kasa warwas”.
“ ni kuma ba zan amsa gaisuwar kaba, saboda naga kamar kana sakaci da amanar da na baka. Kana kusa zaka bari har yaya na ya wuni bai ci komai ba”.
Dariya ya yi, san na yce “gaskiya kin so dora min laifi ne kwai. Amma ina ce ko ciwo ne ya kamaka ai akwai liktan kowanne irin ciwo. Shi nasa ciwon ke kadai ce maganinsa”.
Murmushi tayi san na ta ce “Yanzu dai na baka aiki ka tabbatar ya ci abinci sosai ya sha magani. Nan da awa daya da zaku zo in ganshi garas. In ba haka ba, tarar da zan dora maka bankin duniya ma ba zai iya biya maka ba”.
“tuba nake gimbiyar Balarabe. Yanzu za ki ga aiki da cikawa”.
Ya ajiye wayar ya juya wajen sa ya ga yadda ya takarkare yana cin doyar data zuba masa tun safe. Dauke kwanon yayi yana fadin yanzu saboda Allah dama akwai wan nan better dish din in this office kana jina ina ta kirarin yunwa nake ji, amma kayi min shiru”.
Shi ma ya fisgo flask din yana fadin “let go ka jira yanzu zan tura gidan yaya A’I a aiko mana da abinci this is for me alone”.
La’asar kuwa a masallacin layin su Zainab suka yi sallah. Tun da suka hau mashin nan zuwa gidan Mujib yake mitar shi fa ya gaji da hawa mashin, saboda haka yau idan sun je su nemi turo iyaye saboda ayi mai kankat.
Kafin isowarsu ta salla wanka ta feshe jikinta da turaren Tommy hilfigre da kuma splash dinta na Victoria secret garden. Ta sa atamfar ta mai dan kyau daga cikin kayan da Farida ke bata. Ta dakko dogon hijabinta da yayi matching da kayan ta saka.
Tana gama azkar kiran wayarsa na shigowa. Ta kofar baya ta bude ta nufi wajensa a inda suka saba haduwa. Yana ganita ya saki murmushi. Bayan sun gaisa kafin suce wani abu, aka turo kofar gate din. Daddy ne ya shigo ga dukkan alamu daga masallaci yake. Su duka su biyun suka karasa in da yake suka durkusa har kasa suka gai da shi.
Shi kansa ya yaba da yadda ya gansu. Saboda da duk wanda ya gansu ya san ba mutanen banza bane. Amma kuma hudubar Momi ta yau da safen nan na yawo a kansa, in da tace masa “da gasken Dadin Farida aure zaka yiwa Zainab”?
“to ba gwara ayi mata auren ba. Ita ba karatu take yi ba balle ace wani abu take jira. Yanzu fa idan zaki tuna shekararta ashirin”. Ya amsa mata.
“Eh ni ban ce kar ayi mata aure ba. Amma ina fatan ba wan nan mai tallan gwanjon zaka dauki santaleliyar yarinya kamar Zainab kabashi ba. Ai an san arziki na Allah ne, amma a dinga duba komai ya zama dai dai ruwa dai dai tsaki”. Daga nan sai ta fara sharben hawayen karya tana fadin “kuma ni idan kayi haka ni zaka jawa zagi, sai aga don bani na haifeta ba na tura ta inda zata wahala. Tun da kaga yaron dake neman Farisa babansa senator ne. su Sakina ka duba kaga irin mazan da suka aura. Kuma ita a aura mata mai tallan gwanjo”.
“to ya kike son in yimata ba ita ta kawo shi tace shi ta ke so ba. Kin san yaran yanzu da kallafa rai a kan abu. Idan naki bata shi sai ki ga an zo ana samun matsala. Kuma idan shi an ki bashi aurenta, tana da wani manemin ne”.
“manema kai Daddy. Kaga akwai kanin wata kawata. Au nama tuna ka san ta Maman Aziza. Ya dawo daga London ya samu aiki a chevron. Tun da yazo gidan nan ya ganta ya ke ta nacin in bashi ita. Idan har ka yadda a rushe maganar waccan yaron, sai a hada ta da shi. Ka tuna daddy hustling din nan shi ma ba dadi gareshi ba”.
Allaha ya sani ba wai son Zainab ne ba yayi ba, haushinta kawai yake ji na yadda taki ta zama kamar sauran yaransa a zatonsa, tun da shi bai san ya akayi karatunta ya gurgunce ba.
Amma yadda yaga yaran a tsaye da alamun akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu. Bayan sun gaisa ya shiga gida. Nan kuwa ya sanar da ita abin da ake ciki batun ganinsu da yayi yanzun nan.
Take ita ma kuwa ta bashi shawarar yadda za a yada kwallon mangoro a huta da kuda. Su dai suna tsakiya da zancensu su uku cikin jin dadi da annashuwa sai ga Halim yazo ya ce suje dukkan su uku Daddy na neman su.
Cike da tsoro suka bi shi zuwa falon Daddyn. Nan suka same shi zaune tare da hakimarsa. Cikin ladabi suka sake gaishe shi san nan ita ma suka mika mata tata gaisuwar.
Daddy yayi gyaran murya. Ya kalli Zainab, yace “Zainab wan nan shine yaron da kika zaba ki ke son ya zama abokin rayuwarki?”
Shiru ta kasa Magana. Sai Momi ta ce “ki buda baki kiyi Magana mana. Duk kanmu nan akwai wani bakonki”. Cikin jin kunya ta daga kanta alamun eh.
San nan ya juya ya maida hankalinsa inda su Al Bashir ke zaune duk murna ta cika musu ciki, na ganin nesa zata zo kusa. San nan ya sake cewa “mallam Balarabe ina son in sanar da kai na shirya aurar da Zainab nan da lokacin kankanni, saboda haka idan har da gaske kake yi ka turo da iyayenka nan da kwana goma. In aka wuce wanan lokacin zan bayar da ita ga wani”.
Da sauri Mujib ya amsa da cewar “da iznin Allah ba zamu haura hakan ba, yanzu zamu je mu sanar da su sakon da kabamu”.
Nan take Momi ta sake samo wata dabarar tace “kuma Dadi ina ga abin da za ayi a saukaka komai. Kaga dai idan ma kayan daki akayi mata, bai fi ya samo musu daki falle daya ba. Saboda haka kar ka karbi komai ya biya sadaki kawai idan yaso shi yayi mata kayan daki daidai da su shi da kansa. Kaga an sauke msa wahalar lefe. Tun da kuma sana’ar gwanjo kake na san ka san inda zaka samo furniture second hand”.
Ba su san sanda suka hada ido tsakanin Mujib da Al Bashir ba, na ganin yanayin cin mutuncin da Momi ta dauko yi musu. Al Bashir ya sake kai idonsa inda Zainab ke tsugunne. Yana kallon yadda take kokarin sharen hawayen da suka zubo daga idonta. Shi ma Mujib ya hango yanayin da take ciki.Take ya mai da hankalinsa wajen daddy yace “ba komai Allah Raini. Akwai abokin mu daya kafinta ne. idan muka sayi kayan aiki na san zai mana kayan gadon da sauki. Sai a gaya mana sadakin yadda idan munje gida sai mu sanar su taho da shi gaba daya”.
“Dubu dari biyar” suka ji muryar Momi ta furta. Da su da Zainab din duk ba su san sanda suka dago suka kalleta a firgice ba. Zainab ta maida kanta kasa kawai taci gaba da kuka. Shi kam kukan nata yafi komai daga masa hankali. Ji yake kamar ya tashi ya naushe bakin Momi da ta sanya rabin ransa kuka.
Mujib ne yayi saving situation din yana neman a dan rage musu, saboda su masu karamin karfin ne.
“Ashe da ma ba auren kuke so ba wasa kawai kuka zo yi da hankalin ‘yata. Ni dai iya abin da muka ga zamu bukata na sadakin ta ke nan. Idan zaku iya biya BisMillah. Idan kuma kun ga ya fi karfin ku to ku tafi Allah hada kowa da rabonsa”. Momi ta sake fada.
Daga haka kuwa ta mike shima Dady ya mike suka shiga gida. Suna barin falon Zainab ta saki wani kuka mai shessheka, wanda ke nuna alamun rike shi tayi.
Tashi yayi ya koma kusa da ita. San nan cikin muryar rarrashi yace “Putri Salju dago ki kalle ni”. Ta dago ta kalle shi. Yana ganin yadda fusakrat ta koma shi ma ya shiga tashin hankali. A lokacin yayi niyyar tonawa kansa asiri ya juya ya kalli Mujib yace “lets quit this game”.
“Not now is like there is a hidden agenda behind it. Roll the dice to the end”.
Mujib yace da Zainab “kin ga mufa wan nan ba wani abin daga hanakali ne a wajenmu ba. Zamuje mu ga yadda za’a yi”.
“Amma ya Mujib 500. Ta ina zamu samo su”. Sai kawai ta sake sakin wani kukan mainuna alamun karaya.
Hannunta yaja ya rike cikin nasa, yace “kin ga Putri daina damun kanki. Ga mashin dina na san idan na sashi a kasuwa zan samu dubu hamsin. Ina da dashin da na shiga na dubu goma. Kuma an bani. Ni na dauki na karshe na dauki dubu sittin. Idan an juya zan samu na farko kin ga ai an samu dari da saba’in. na kuma san Abbana zai tallafa min da ko yayane”.
Yana fadar haka ta mike da sauri tace “ina zuwa”. Tana fita kuwa bata jima ba ta dawo, hannunta dauke da bakar leda. Ta mika masa.
Sai da ya sa hannu ya warware kullin ya ga ashe kudi ne a ciki. Suka kirga suka ga dubu saba’ain da biyar. Yace “me za yi da su”?
“ka hada ka kawo sadakin da Momi ta tambaya”.
Sai da yaji kamar zaiyi kwalla saboda tausayin ta. Tabbasa tana son sa bilhakki da gaskiya, saboda duk kokarinta na kar araba su ne. ya karba yace “ko dai in hada da wadan can da kikabani a yi miki kayan dakin”.
“ni dai ban ce ba. Kayan daki ba su zasu bani farin cikiba. Sadaki nake so ka kawo shine kawai muradina”.
Shi kansa Mujib sai da ta burgeshi da kuma tausaya mata da yayi na ganin yadda ta mato akan kaunar abokinsa. Nan take yace “kar kuji komai. Nima ina da dan tanadi na, na san kuma ba zasu gaza dubu dari ba. Idan muka hada na san zamu samu wani abu substantial”.
Momi bata basu damar ci gaba da Magana ba ta aiko Hanif ya kirata akan tazo ta dafawa Daddy tea kuma ta dora abincin dare.
Mikewa tayi yayin da suma suka mike Mujib yace “dan Allah kar ki sawa kanki damuwa. Mu dai goyon bayanki kawai muke bukata. Idan muka samu wan nan to mu kuwa mun yi niyyar tunkarar ko wane kalubale ne ya fuskanto mu’.
Nan dai suka yi sallama. Ta shiga gida su kuma suka tafi
[8/8, 21:42] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI 💏💏
PAGE 24
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Tun da su Al Bashir suka fita yake cikin bacin rai, na ganin abin da Momi tayi musu. Har wata karkarwa yake ta bacin rai. Mujib ne yayi karfin kiran mallam Usman. Bayan ya gaishe shi ya sanar da shi duk abin da ake ciki. Ya basu shawara suje su sanar a gida. Idan yaso duk abin da mahaifansu suka yanke shi za su bi. Shi kuma ya dada kwantar musu da hankali akan su yi tawakkali komai zai faru. Su dauka haka Allah ya kaddara.
Ba suyi kasa a gwuiwa ba kuwa suka je. Sun kuwa yi sa’ar samun Abban su tare da yayan ummansu watau takwaran shi Al Bashir wanda shine dalilin da take kiransa da dan uwana.
Nan Mujib ya zayyane musu komai. Shi kam bacin rai ya hana shi Magana. Nan Ummansu ta shigo aka kira yaya A’i. Ita ma ta karaso aka sanar da ita abin da ake ciki. Nan dai suka yanke shawara zuwa gidan su Zainab ranar jumma’a wanda ya kasance dai dai da kwana tara da wa’adin da aka diba musu.
Umma ce ta tuntsire da dariya tace “wai zan so inga wan nan zarar mata da ta saka dan uwana a kwana har ta kaishi da zuwa kasuwar gwanjo da kuma hawa mashin”.
Yaya A’I ma dariyar da take ke nan. Ita kuwa tun da abin nan ya faru ta rasa natsuwarta. Gani take yi ta rasa Al Bashir. Bata san haka ya shiga ran ta ba sai yanzu da ta ga tana neman rasa shi. Ta rasa dalili wanda ke sayen snacks a wajenta tun da su Momi suka dawo bai kara zuwa ba, balle ta samu kudin shiga. Ba tare da sanin ta ba Al Bashir ya daina zuwa saye saboda tunanin aiki zai yi mata yawa
Fatu ta nema su ka kwashi rigunan da Abbanta ya kawo mata daga Saudi. Ba wanda ya sani suka tafi Camp. Tayin farko ma rigunan ‘yan Morocco a sha biyar aka taya su. Su kuwa after din dubu ashirin da biyar. Take suka yanke shawarar yi musu kudin goro. Kowacce dubu ashirin. Ita ba ta san ma masu tsada bane sai a lokacin.
Fatu ce ta bata shawarar ta dauki riga biyu daga ciki da kuma after daya, don ta samu na kwalliya. Ita kam da an bi ta tata ta fi son ta sayar duka ta bawa Balan ta kudin.
Suka sayar da after guda bakwai da rigunan suma guda bakwai. Kudin su dari biyu da tamanin haka suka dawo da su cas.
Fatu ta sake saka ta ta dauki tamanin daga cikin kudin. Suka shiga kofar wambai ta sayi zannuwan gado guda biyu na gwanjo ‘yan dubu bibiyu. San nan suka shiga wajen masu kayan kicin ta tsintsinci ‘yan kayan kicin dai dai na dubu hamsin har da risho ta saya.
Daga nan suka tsaya shagon mudassir a filin parking. Nan ma ta sai atamfa ‘yar 4500 guda hudu. Ta sai wata shadda barauniyar bazin ta dubu hudu. Ta sai leshi guda biyu na dubu biyar biyar..
kwarai ta haura budjet din ta da dubu biyu, amma haka ta dada daurewa ta sai masa shadda ‘yar dubu goma yadi goma da zummar ta sai masa ta daurin aure. Ta kuma saya masa guda biyu ‘yan dubu biyar biyar yadi biyar. Ta fito bakin shagon ta sai masa hula guda biyu ‘yan 2500.
Suna sauka daga adaidaita a kofar gidan su Fatu, shi kuma yana karasowa a kafa. Suna ta kakabin sauke kaya ta bayansu suka ji ance “yan mata adon gari inzo in yi dako ne”?
Da hanzari suka juya. Suna ganin shine duk suka saki dariya. Bayan sun gama sauke kaya. Fatu ta shiga gida ta fito masa da ruwan pure water da mamanta take sayarwa da kuma kunun zaki. Sai da suka shiga suka yi sallah duk yana jiransu a dakin yayan Fatu, san na suka sake fitowa.
“wai daga ina kuke ne haka na ganku a gajiye”?
Daga wajen mai magani muke ta isheni da kuka za a raba ta da masoyinta, shine na kaita wajen wani mai magani yace mu samu hawayen kuda da kwan sauro sabuwar kyankyasa da kuma kafar kiyashi ta hagu zai hada mana lakanin da ruwa da iska ba mai rabaku”.
“saboda Allah Fatu kina ganin halin da muke ciki amma zolayar mu ma kike yi”.
Cikin dariya ta ci gaba da cewa “ina kuwa zolaya kana ganin yadda na dage taya ku neman magani” ta fada tare da mikewa don kokarin fita daga dakin. Sai da ta fita yace “Putri Salju ina labari”?
“lafiya kalau. Amma ya na ganka a kafa ina mashin dinka”?
“Ba jiya na sanar da ke zan sayar ba ai har anci kasuwarsa”.
“amma ban so ka sayar da shi ba. Ka ga ai zai taimaka maka zuwa kasuwa da yana nan”.
“kasuwar ba sai a je a kafa ba in dai za a sameki”.
“Allah yayi mana jagora”.
Fatu ce ta shigo da tray din abinci. Tana ajiye wa ta fita ta barsu a dakin. Ita ta bude food flask din. Birabiskon gero ne da miyar yakuwa.
“Allah ya sa ka iya cin abincin bare bari” ta fada tana mai zuba masa a plate.
Yana ci suna hira. Ya kuma ci da yawa, ko don dadin zancen da take masa. Sai da taga ya ci sosai, san nan ta fito da kudi daga cikin zaninta ta mika masa dari da sittin. Cike da mamaki ya kalleta yace “inaa kuma kika samo kudi masu yawa haka. Na fa lura hajiyata kudi gareki. Wadan nan kuma daga ina”?
“kudin kayan da kaki karba ne wannda Abba ya kawo min tsaraba daga Mecca”.
Nan ta shiga lissafa masa yadda ta sayar da su da kuma abin da ta saiwa kanta. Cike da tausayin irin son da take masa ya ke sauraron bajintar ta. Bata lura da yanayin sa ba, cike da zumudi ta shiga fitaar da kayan da suka sayo tana nuna masa. Ta kuma dauko shaddar da ta saya masa da hulunansa guda biyu ta mika masa.
Har wata kwalla ce ta subuce masa na tsananin tausayinta. Yanzu ya lura ashe ba mace ta tsara maka kalaman soyayya ne zai nuna son da take maka ba. A’a sadaukarwarta da kuma kula da kai shine hakikanin soyayya ta gaskiya. Ji ya ke kamar ya tashi ya rungumeta saboda tsananin murna.
Ya dago ya kalleta cike da wani irin shauki a ransa. San nan yace “Zainab na gode da irin son da kike min. ni kuma nayi miki alkawari da iznin Allah ba zaki taba kuka da aure na ba. Zan nuna miki kauna. Zan baki farin ciki da baki taba tsammanin samun irin sa ba. Yanzu a ina kika ga ya kamata mu nemi dan gida da zamu zauna”.
“tace ka san ni ba sanin gari nayi sosai ba. Amma duk inda zaka nema ka nemi inda ba zaka sha wahalar zuwa kasuwa ba”
“Ni da ce ma zaki yarda sai mu ci gaba da zama a gidan mu kusa da Ummata. Ina da daki ciki da falo daga waje da kuma dan bandaki na. In yaso ko daga verender sai an rufa miki kitchen”.
“Amma lalle kuma ina gidan sai Umma ta yi girki, sai kace ban san ciwon kai na ba. Kabar mana kitchen daya ya ishe mu. Wadan nan kaya kuma ka tafi dasu. Tun da Momi tace kai za ka yi komai, sai ka tafi dasu wajenka. Amma kayan sawar ka barmin zan dinka da kaina a keken mama Hajjo”.
“Sana’a nawa kika iya. Ban da snacks da kike yi har dinki kin iya”.
“lah aihar zanen lalle da gyaran jiki na amarya na iya. Dama zance idan zaka amince min sai nima in dan dinga sana’a a cikin gida. Ko dinkin ko gyaran jikin ko kuma snacks din duk wanda ka zabar min”.
“To putri Salju ni da nake burin mai da ke sarauniya kuma kina debowa kanki aikin wahala”.
A shagabe tace “ni dai kayi min izzni in gwada wata sana’ar kaji mi……”
Bai san sanda ya sa hannu ya lakace mata kumatu ba yace “da wanan muryar taki ai ko duka na kika nemi iznin zan barki kiyi balle sana’a. amma dai ni complain dina daya kar neman kudi ya hana a kula da ni.
“Zan maka alkawari daya. Matso kana gida zan ajiye komai in maida hankali na da duk wata kulawa ta gareka”.
“da gaske matata”.
“Da saura tukun na”.
“A’a wai da na ji kin kira ni mijin ki sai na zama convince of my status”.
Kunya ta kamata ta kasa amsa masa sai ta basar da zance. Ganin haka shima ya kyale maganar yace “Amma ki bani har kayan sawar taki in tafi dasu. Zan nuna wa Ummana gobe zan dawo miki da su”.
Nan kuwa taa hada masa har da kayan kicin din data saya. Su kam da niyyar ya barsu a a gidansu kawai.
Yana shiga ya jibgewa Ummansa kaya a gabanta, yana fadin “Umma kuna tsokana ta na shiga gwanjo saboda Zainab. Ita ku duba irin abin da take yi sabo da ni”.
Yaya Maryam da ta shigo taji labarin abin da Zainab tayi na kokarin ganin ta taimakawa Albashir ya aureta, ita ta ba da shawarar a bata duk atamfofin sai da kuwa ta samo original super kowacce haka ma shaddar ta sayyo ‘yar 40k dinta. Leshi ne aka kasa samun manyan su irin wadan nan.
Zainab ganin ta hada da wan nan ta mai da hankalinta kan saukar da za suyi hankalinta kwance. Ta san dai kudin nan ko ba su cika dari biyar ba sun kusa. Shi kuwa shi da Mujib duk abin da aka yi sai sun bugawa mallam Usman watau Abban Hafsa sun sanar da shi.
Ranar jumma’a da misalin goma na safe su Alhaji Usman da kuma ‘yan uwansa suka tunkari gidan Dr Abdallah Zubair domin nemar wa dansu aure. Ga shi dama suna da daurin auren ‘yar wajen Alhaji Bashir saboda haka suka nufi gidan da niyyar daga nan sai su wuce daurin auren wanda ita ma kuma dan wani aminin Alhajin ne zai aureta.
[8/8, 21:55] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 25BY HANNE ADO ABDULLAHI
Zainab bata da masaniyar abin dake faruwa, saboda tana gidan su Fatu suna aikin snacks din da zasu yi sauka gobe. Tabbas Bala ya sanar da ita ko yau da safen nan akan cewa iyayensa zasu shigo washegari da yamma. Da kanta taje tana kokarin sanar da momi. A dakinta, ta same ta ce “Mh Momi dama Ya Bala ne yace…..”
Bata barta ta karasa ba ta fara sauke mata bala’i. “ya Bala a gidan uban wa. Ke har kin isa ki aurar da kanki banyi niyyar kiyi aure ba. Shashashar banza marar hankali. Ta shi ki bani wuri ko in yi ball dake”.
Hakanan ta mike tana mai zubar da hawayen takaici. Ta rasa me zata yi a duniyar nan Momi ta sota. Laddabi biyayya da kuma hidimar da take mata, ‘ya’yan da ta haifa a cikinta basa yi mata 2% dinta. Amma duk da haka ita ce a hantare ko da yaushe.
Ita dai bata samu sanar da iyayenta zuwan iyayen Bala ba. Ta dai fawwala wa Allah lamuranta ta kuma yarda idan har mijinta ne shi ba wanda ya isa ya raba su.
Shi ma dai Mallm Usman haka suka yi kundunbala su da kakannin Zaina na wajen uwa da kuma na uba. Da kuma kannen kakanin nata guda biyu. Shi ya tuko so zuwa gidan Dr Abdullahi, saboda information din da su Mujib suka bashi akan zuwan iyayensu yau.
Su kuma daga bangaren iyayen Al Bashir sun shirya ke nan saiga gwamna jiha ya iso saboda halartar daurin auren da za ayi, wanda ya hada dangi da duk wasu abokan arziki. Shi ma Al Bashir kusan duk abokansa sun zo daurin auren cousin dinsa saboda angon abokinsu ne.
Jiniyar gwamna ita ta tsaida su daga shiga mota domin zuwa wajen iyayen Zainab. Bayan sun gaisa suke shaida masa inda suke da niyyar zuwa, amma tun da yazo zasu fasa zuwa, su tsaya a daura auren da dama shi ya tara su.
Allah ya sani His Excellency yana ganin mutuncin Alhaji Usman, watau shi mahaifin Al Bashir, saboda su suka tsaya masa ya hau kujerar da yake kai saboda sun ganshi a matsayin mutum mai gaskiya.
Tashin farko ma da zai fara campaing. Naira million 500 ya bashi gudummowa. Kuma da aka ci zabe ya nuna san ya saka masa da alkhairin ya ki yarda, saboda ko kwangila yaki karab. Ya nuna masa saboda talakawa suka yi kuma talaka suke so ya ci moriyar dashin da suka zuba.
Ai kuwa His Excellency najin auren Al Bashir za a je nema, yace da shi za aje. Nan kuwa suka runguda zuwa Hotoro NNDC inda gidan su Zainab yake. Dr bashi da masaniyar kommai sai gani yayi security sun zagaye gidansa. Kafin chief protocol officer ya gama yi masa bayani, baki sun iso.
Bayan an gaggisa suka sanar da Dr Abdullahi uzirin da ya kawo su. Ka hango ta yadda zai yiwa governer musu yana matsayin COMMISIONER dinsa? Cike da murna ya karbi abin. Nan kuwa suka FITO da sadakin da aka yankawa dansu suka mika.
Saboda tsabar rashin gata bai damu da ya tambayi Zainab ko ta na son sa ba ko bata so.
Tun da ai yana sane da cewar Bala mai gwanjo ke neman aurenta ba Albashir Usman Ahmad Babba ba.
Su dai su Baffa dasuka zo daga Kera sai mamakin wan an abu suke. Shi kuwa Mallam Usman bai yi mamki ba saboda ya san matsayin Al Bashir. Ana kokarin tashi sai Baffan Nene yace “to ni kam ranki shi dade da ayi aje a dawo, ga sadaki ga waliyyan ango gana amarya ga kuma liman na unguwar nan, a daura aure mana kawai shi ke nan”.
“haka ne kuwa” da yawa daga falon suka amsa.
Jin haka Alhaji Bashir kawun Al Bashir ya dau waya, ya bugawa babban dansa yace maza a yi diverting jama’ar da suka taru domin daurin auren ‘yarsa da kuma dan abokinsu shi da Alhaji Usman zuwa gidan su Zainab, ga wani daurin auren na gagawa ya taso.
Kafin minti talatin kuwa muatane sun cika kofar gidan. Ba shiri mallam ya bude store da aka jibge tabarmi wadanda aka saya lokacin auren su sakina ya shiga baza su a haraba da kuma wajen gidan.
Momi na daga cikin gida saboda kasancewar wannan jumma’ar ta kama public holiday ba su je aiki ba. Kafin ta Ankara kawai sai gani ta yi mutane na ta tududdowa cikin gidan. Baba laure ce, ke shaida mata ai wadanda suka kawo sadakin Zainab ne suka bukaci a daura aure yau din nan.
Ta lailayo wata ashar da bazan iya rubuta muku ita ba, tace “uban waye mijin, saboda da dai na san ba wan nan dan iskan mai gwanjon bane’.
Baba Laure dake mata dariya kasa kasa tace “na dai ji kamar ana ko dan gidan gwamna garin nan, don shi ma ya zo na dauka ma kin ji jiniyarsa”.
“naji jiniya amma ban dauka nan gidan bane, na dauka wucewa su kayi”.
“ai kuwa dai nan suka tsaya”.
Kwasa tayi a guje ta shiga ciki, kamar tababbabiya. Ta buga wayar mijin hayaniyar falon nasa bata barshi yji ba. Jikinta gabadaya sai rawa yake yi. Ta ce "Yi sauri Hanif falon Daddy ku ka kira min shi kace masa na fadi bani da lafiya”.
Da sauri kuwa ya nufi falon dadin nasu ya isar da sakon Momi ga Dr Abdullahi. Jin haka kuwa ya mike da hanzari yana fadin “ina zuwa wani abu ya faru a cikin gida”.
Da sauri Baffan Nene ya riko shi yana fadin “kaga kar ka shiga ciki ko uziri maitsawo ne wakilta wani kawai ya dauran auren ai kaga ba a bar su mai girma .Gwmana suna jiraba”?
Nan takewa kuwa ya wakilta mahaifin sa a kan ya daura auren Zainba, shi kuma ya shiga yaji uzurin da ya faru a ciki. Yanda ya ganta shi kansa hankalinsa ya tashi sai sambatu take tana fadin an munafunceta.
“Kayi sauri ka tsaida auren nan. Ba zai yiwu ba”. Sune kalaman da ke fita daga bakinta. Kokari yake ya fahimci abin da yake nufi, amam duk ta rude sai Magana daya take maimaitawa.
Kafin su Ankara sai jin sanarwa suka yi an daura auren Zainab Abdullahi Zubairu da kuma Alhaji AlBashir Usman akan sadakin naira dubu dari biyar, wanda Baffa Nene ya wakilci amarya His excellency ya zama wakilin ango.
Da Momi da Zainab tare suka shide wacce itama sanarwar ta same ta ta sanadin wan Fatu da aka daura auren tare da shi.shi kansa Al Bashir bai zaci durin auren a haka ba, a bazata yazo masa.
Zainab na jin an daura aurenta ba da Balrabe ba, ta kalli yayan Fatu watau Ya Baanaa cikin firgici da kuma tsoro. Tace “Ya Baana me kake nufi? Da wa aka daura aure na? na shiga uku”. Tana fadar haka tayi luu ta sume a wajen.
Shi ma daga can kofar gida jin sanarwar daurin aurensa ya san yi shi luu din kamar zai fadi. Su mujib suka taro shi suna tsoknar sa. Allah ya taimake shi da zai je daurin aure babbar riga ya saka, ba don haka ba, da hoton daurin aurensa ya fito da karamar riga.
Suna cikin farin ciki shi da abokan sa wadan da ba nashi dauri auren suka zo ba, na Sagir Inuwa suka zo wanda ya kasance shi ma abokinsu ne sai ga Ya Baana ya nufo su da sauri daga cikin gida yana neman taimako wai Zainab ta suma.
A miliyan ya zumbuda yafada gidan su Fatu wanda yake bayan na su Zainab. A tsakar gida ya tarar da ita rungume jikin mama Haajjo tana kokarin shafa mata ruwa. Bai san sanda ya durkusa ya kamota jikin sa ya rungume ba, sai fadi yake “kar kiyi min haka Zainab. Don Allah ki tashi idan kika barni bansan yadda rayuwata zata kasance ba”
Da kaga yanayin da yake Magana ka san a rude yake. Tana farkowa kuwa ta ganta manne a kirjinsa yana kuka. Ita ma ba shiri ta saki kuka tana fadin “wayyo Ya Balarabe Momi tayi nasarar raba mu. Na shiga uku dawa aka daura min aure da shi. Wallahi ban sonsa kai nake so.
Jin kalamanta ya sanya shi dada rungumota jikinsa ya ma mata da wasu mutane a tsakar gidan. Mama Hajjo ce tasa Fatu ta shiga dasu dakin Ya Baana saboda idon mutane.
Bai ji kunyar kowa ba haka ya daga ta cak ya shiga da ita dakin. Kan katifar dakin ya kwantar da ita, san nan ya tura kananan kitson da suka zubo har gadon bayanta wanda suka barbazu a fuskaarta lokacin da aka yaye mata hijabin da ke jikinta lokacin data suma.
Tana kallonsa sai ta sake fashewa da wani sabon kukan. Ya sake rungomata jikinsa kanta na karkashin habarsa fadi yake “come on Putri is alright. Ki yi shiru ki daina kukan I will explain things to you”.
“Ya Balarabe ba abin da za kayi min explaining. Ka barni kawai in karashe rayuwata cikin bakin nciki”.
“in sha Allahu cikin Farin ciki mai tsawo da alkhairi da kuma yakana zaki kare raywarki”?
“Ta ina? Kaine farin cikina, na kuma rasaka saboda haka bani da wani sauran farin ciki”. Ta sake fashewa da wani sabon kukan.
A cikinn hannuwan sa ya saka fuskarta. San na yace “Putri look at me”.
Ta dago ta kalle shi kamar yau ta fara ganinsa. “kin taba tambayata suna na na asali”?
Gigiza kai tayi alamar a’a. “Putri nine Al Bashir da ni aka daura miki aure. Nine mijinki nine zan kasance farin cikin ki”.
Take taji wata irin kunya ta kamata. Nan ta ringa tariyo boren da ta yi saboda a zaton ta ba shi ta aura ba. Hannu ta sanya ta rufe fuskarta cikin jin kunya.
Sake rungomata jikinsa yayi yana fadin “a’a kar muyi haka dake kunya kuma ta ina. Yanzu ki ka gama suma kina farfadowa akan ba abaki ni ba. Yanzu kuma kin samu sai kuma ki fara yiwa abin da kike so damage”.
“Ta ina nayi maka damage”?
Yana kokarin bata amsa Fatu tayi sallama. Sai da suka amasa san nan ta shiga tana fadin “ai na gaya maka lakanin da malamin nan ya bani kamar yankan wuka yake. Amma ba yanzu zan karbi ladan aiki na ba sai nan gaba, da kuma tarar kin sanar da mu sunanka na asali har kana sakamu suma”.
Hararar wasa ta sakar mata. Ita kuma ta ci gaba da fadin “ai yanzu ka gano matsayin da kake mitar an ki a nuna maka. Tun da yau dai ka tabbatar in ba kai ba sai kabari. Tun da rijiya ma idan an shiga a iya fito da mutum da rai”.
“Ni dai bani da abin cewa sai godiya”.
“za dai kazo godiyar amma ba yanzu ba. Ku zo daddy ya aiko a kira ku”.
Hijabin ta ta mika mata suka fito suka nufi gidan su Zainab cike da farin ciki.
Anan kuma suka tarad da iyayensu da kuma Alhaji Bashir da Alhaji Usman, wadanda sakon kiran uban amarya ya same su lokacin da suka fita za su raka his excellency, wanda zai wuce wajen dayan daurin aren wanda shine ya fito da su dukkansu.
Sai da motarsa ta tashi san nan suka koma cikin falon, inda suka samu hajiya Rumaisa tana ta gursheken kuka da ikirin dole a raba wan nan aure. Baffan Nene ji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka. Shi Alhaji Bashir ne yace a bata damar ta fadi dalilin ta na son raba auren
Tace ba zata fada ba sai an kira Al Bashir yazo. Ana wan nan takaddama shine aka tura kiransu. Suka shigo cikin farin ciki wanda ya gaza boyuwa a fusakarsu duk su biyun.
Alhaji Usman ne yace “hajiya gasu sunzo fada mana dalilin da kike son sai an raba su”.
A razane duk suka dago idonsu su ka kalleta watau ango da amaryar da ba su san kiran na meye ba. Allah ya sa tare suka shigo shi da Mujib. Kamar daga sama yaji muryar Momi na fadin “saboda ya yaudari ‘yata, shi yasa nake son a rabasu”.
“Wacce yaudara yayi mata”? nan kuma Baffan Nene ne ya fada cikin bacin rai.
“Ya san shi ba namiji bane ya yaudareta ya aureta”.
Dukkan su na falon haka suka ji saukar zancen Momi kamar dukan guduma
[8/8, 21:57] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 26 BY HANNE ADO ABDULLAHI
Dakin ya dauki shiru na dan wani lokaci. An rasa mai abin cewa. Shi kuwa Al Bashir sai kwankwasar daben kasa yake yi da knuckles din shi. Mujib da ya san shi tun suna yara, ya san alamun kurewar bacin ransa ke nan. A hankali ya dora hannayensa a kan nasa ya dan matsa.
Ya dago ya kalle shi idanuwansa jawur kamar an zuba masa gauta a ciki. Girgiza masa kai yayi alamar yayi hakuri. Ga wani uban gumi da ya wanke shi sharkaf duk da sanyin falon.
Ita kuwa amarya dago kanta tayi ta kai kallonta zuwa angon, tana mamakin furucin Momi. Tunani ta ke a zuciyarta “to in ba namiji ne ba shi menene? Mutum ga saje ga kira irin ta maza murya irin ta maza sutura irin ta maza kuma ace ba namiji bane”?
Wan nan shine tunanin da zuciyarta ke wassafa mata. Bata san sanda wata karamar dariya ta subuce mata ba, saboda sakarcin Momi da take gani. Tayi saurin kunshe dariyarta kar iyayenta da kakanninta su jiyo ta. Amma tabbas bata ga ta inda za a ce ya balarabenta ba namiji bane.
Dogo mai kyakkyawar kira ta mazan kwarai, kuma momi ta kalle shi tace ba namiji bane. Shine abin da zuciyarta ta ci gaba da wassafa mata. Tana cikin wan nan tunani taji muryar Baffan nene yana cewa “Rumaisa kiji tsoron Allah. Ta yaya kika san wan nan maganar”?
“Baffa tsoron Allah ne yasa na furta wan nan maganar a gabanku sabo da bana son cutar da Zainab”.
Muryar Al Bashir can kasa yace “na nawa kuma”?
Mujib ne ya yi saurin sakin gyaran murya wadda ta dakushe kalaman Al Bashir ba wanda yaji mai yace sai shi kadai. Hanakalinsa bai dada tashi ba sai da yaji muryar mahaifin sa yana fadin “Balarabe kaji tsoron Allah. Idan har ka san ba ka da lafiyar sauke hakkin auren yarinyar nan ka shaida mana tun da wuri kar ka cuce ta”?
Dago idonsa yayi ya sauke su akan mahaifinsa, wanda shima ya hango tsananin bacin ran da ke tare da shi, amma ba ya son ya zama mai son kai a tsakanin ma’auratan yafi son kowa a bashi hakkinsa.
Baffa ne ya sake cewa “Rumaisa ke muke jira muji dalilin ki na cewa shi din ba namiji bane”
“Mh ai Baffa zancen ya zaga garin nan, tun da ba wanda ya taba ganinsa da wata yarinya ya nuna yana sonta, shi ne nima na samu labari”.
“ita ke nan iya hujjar da kika dogara da ita”?
“ka ga baffa bari muji daga bakin yaron, kar a cuci yarinya” Alhaji Usman ya dada fada.
“Haba Alhaji saboda kawai yaro ya kame kansa baya shiririta sai a dau kazafi a lankaya masa. Kai AlBashir ka kare kanka mana. Tun da ita bataji kunyar zargin ka ba, kai ma kar kaji kunyar maida mata martini”.
Ya dago kansa ya galla mata harara kamar zai tashi ya rufe ta da duka saboda tsabar takaici. San nan murya can kasa yace “Baffa ni bani da abin cewa sai dai a bani lokaci shi zai tabbatar da gaskiyata ko karyata”.
“Wan nan hakane” in ji Baffan Khadija.
“ai kuwa wallahi ba zai yiwu ba. Ba zan zauna ina gani a cuci yarinya ba. Dole ne ya sake ta”. Ta fada cikin muryar kukan da ban san ko na karya bane kona gaskiya.
Baffa Nene ne ya sake harzuka ya mike tare da fadin “Allah ya sa kin gane ba wanda ya isa sakin auren sai mai shi da kansa ba. Bani ba. Ba ke ba, ba kuma shi kansa mahaifin yarinyar da ya zuba miki ido kina ciwa mutane mutunci ba”.
“Don Allah Baffa kayi hakuri. Duk maganar bata bacin rai bace kayi hakuri”. Alhaji usman ya fada.
Take ya juya harshe cikin fulatanci yake fadin “kin so nakasa yarinya Allah ya kareta shine kika bullo ta nan”. Ya juya inda AlBashir ke tsugunne yace da shi “kai mike kadauki matarka ku bar gidan nan. Aure ni na baka shi, ba kuma wanda ya isa ya karbe shi daga wajenka. Wuce ku tafi”.
Yana fadin haka ya nufi hanyar fita. Har ya kai kofa ya dawo inda Zainab ke tsugunne ya daga ta ya fita da ita ya dago hannuta ya hada dana Al Bashir yace ban yarda ka tafi ka barta a nan gidan ba. Yanzu ku kama hanya. Kaje duk inda Allah ya hore maka ka ajiye matarka”.
Aikuiwa yana mika ta, caraf ya sa hannu ya damke nata. Shi kuwa yayi ficewarsa daga falon yana fadin “ina Mallam Usmanu yazo ya mayar dani in rabu da ganin wanan bakin cikin”.
A tare duk suka fice daga falon, suna jiyo muryar Momi tana tashin hankali. Su dai suka fita suka barta da mijinta wanda tun da aka fara Magana bai ce komai ba, saboda tsoron kar Baffansa ya tsinka shi idan har ya goyi bayan matarsa. Shi ma kuma wannan lokacin ba zai goyi bayan nata ba. Saboda ko banza His Excellency ne madaurin aure. Wanda hakan ya sa zai dada samun kusanci da shi.
Shi wannan aure na Zainab ai an taki sa’a. wadan nan dalilai suka sa shi yaki siding da kowa. Shi ma a nan ya tafi ya bar Momi tana ta hargowarta.
AlBashir rike da hannun Zainab cikin rakiyar Mujib suka nufi motarsa Mercedes benz G63. Sai da ya zaunar da ita a kujerar baya san nan ya zaga daya gefen ya zauna, yayin da Mujib ya shiga mazaunin direba.
Ba wanda yace da kowa komai a cikin motar sai sauke zazzafar ajiyar zuciya da Al Bashir yake yi. Zainab ta saci kallonsa sai kawai zuciyarta ta raya mata wai gashi nan daure da dankwali da zani da riga irin na mata. Picture in her mind is so funny saboda haka ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba.
Sai a san na shi ma ya saki ransa ya shako wuyan ta cikin wasa yana fada “dariyar me kike min”?
Muryarta can kasa cike da dariya take fadin kayi hakuri, hotonka na hasko da gwaggwaro da high heel shine dariya ta kamani”.
Tare suka dago ido suka kalli juna shi da Mujib sai a nan suka fahimce Zainab ba ma ta san accusation da Momi tayi masa ba. Ita kallon physical halittarsa kawai ta ke and not something else. Dariya suka bushe da ita a tare.
Mujib yace “yaya ina zan kaiku for your honey moon ko mayi saurin proving Momi wrong”.
Kafin ya bashi amsa, wayarsa tayi ringing sai da ya daga wayar san nan ya tuna da appointment din da yake da shi da wanda ya kira. Ya na dagawa yace “yi hakuri ranka dade. Shaf na manta I was coming to see you, wani lamari ne ya sha kai na”.
Ya dan yi jim alamar sauraro san nan ya sake cewa “a’a gani nan zuwa yanzun ma kuwa”.
Ya kashe wayar ya maida cikin aljihunsa. Yana murza hannun Zainab dake rike a hannunsa ya ce da Mujib “please lets go to immigration office I need to get a passport done”
“Amma na dauka yau public holiday they wont be around”?
“no suna nan because of hajj operation they work round the clock”.
Mujib zai sake Magana ya hango Al Bashir ta cikin madubi yana rada wa matar sa wata Magana wadda ta sata dariya, sai kawai ya fara waka yana kida, da steering motar. Yana fadin “ranar muke jira yau
'nima da tamburana gani na zo’
'ango muke yiwa shi
'Muyo rawa da murna anyi aure’
Gaba daya dariya suke masa na ganin ya daddage ya na ta zuba waka. A haka suka isa farm center inda passport office yake. Duk da wajen a cike amma an kaisu VIP room dinsu. Ita dai biye take da su tana mamakin yanzu hoton passport kawai sai an zo wani waje. Da sun yi Magana da ko a nan unguwarsu an dauka.
Amma sabanin yadda tayi tunanin wannan hoton daban ne, saboda har su yatsun hannu aka dinga daukar hotonsu. Bayan an gama sun fita sun shiga mota Mujib yace “ango har yanzu baka sanar da ni inda zan kaiku ba. Kaga dai auren da muka taru domin sa kayi hijacking, tun da dai ni da kai ba za mu iya attending ba”.
“You know what, da nayi niyyar mu wuce gida, but on second thought why should I deny may deer and her mother the right to enjoy and cherish this moment. So I think mu wuce Garko kawai’”.
“kaga idan kai da Zainab murnar angwancewa ta sa kun mance komai. Ni yunwa nake ji, saboda haka kafin mu wuce find me some thing to eat please”.
A wani haddaden restaurant suka tsaya. Nan fa ya sha daga da Zainab akan taci abinci amma ganin sa da kuma idon Mujib ya sa ta kasa ci. Ya juya ya kalli Mujib yace “please dan bamu privacy mana”.”
"yanzu kuwa” ya fada yana mai mikewa domin kuwa shi dama ya gama .
Yana fita ya jawo kujerarsa daf da tata wadda har kafadarsu tana gogar juna. Ya debo abinci a spoon yace “Ha’ ta so ta noke,amma bai bata damar yin haka ba, sai dai ma threat din dura da yayi mata. Sai da ya tabbatar ta ci yadda ya kamata san nan ya kyaleta. Kuma har ya tabbatar ta koshi bai daina bata da hannunsa ba. Ita kam kunya ce ta lullube ta na ganin wani Balan da bata san da shi ba.
Suna shiga mota taga sun dauki hanyar Maiduguri. Da sauri ta kale shi tace “ba gida zaka mai da ni ba”.
“a’a garko zan kai ki wajen umman Hafsa”.
“Wai gashi ban taho da kaya ko daya ba. Da zaka yi hakuri kayana da na dinka suna gidan su Hafsa da naje na dauko”.
Wani irin kallo ya watsa mata. San na yce “saboda ni kuma bani da wayo. In koma filin dagar yakin da na sha da kyar. Yau dai kiyi managing da na Hafsa, gobe in sha Allahu zan kawo miki.
Haka nan suna hirar su cikin annashuwa suka isa gidan mallam Usman. Nan kuwa suka shaida masa akan cewa kawo Zainab suka yi wajen mahaifiyarta ta yi mata irin bikin da ta ke so.
Kwarai daga shi har hajiya Khadija sun ji dadin abin da suka yi musu. Nan dai suka yi sallama suka juya saboda suna son halartar bikin da dama shi suka taru domin sa.
Washe gari kuwa sai gashi da kayanta da Fatu da Kuma Mama Hajjo wacce ta hado kayan gyaran jiki rankatakaf da turarurruka masu kamshi domin gyaran amarya. Anan kuma mallam Usman ya sanar da shi shawarar da suka yanke ta kai biki kera.
A gida kuwa Momi kamar wata zautacciya ta koma saboda tsabar bakin ciki. Balle data gano waye mijin asalinsa da matsayinsa sai da taji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. Su dai masu aure sun samu an zarga musu shi ita kuwa mai bakin ciki sun barta da abinta.
[8/8, 21:58] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKIN A MIJI💏💏
PAGE 27
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Zainab na ganin Fatu da mama Hajjo ta taso ta rungume su cike da murna. Sun tsaya zasu fara kaudi Hafsa ta shigo da sakon Al Bashir yana son ganin Zainab. A babban falon Abbansu ta same shi, ya zuba kwalliya sai tashin kamshin yake.
Da sallama ta shiga, yana jin sallamarta ya dago suka kalli juna. Bai sani ba ko idanunsa ke masa gizo amma sai yaga ta kara wani kyau na fitar hankali ga kuma wa ni irin serenity in her face da ba zai iya describing ko na meye ba. But to him she look more at peace.
Abin da bai sani ba, kwanciyar hankali yanzun nan take bayyana a yanayin mutum kamar yadda tashin hankali yake bayyana. Duk da kunya ta dan fari dake tsakanin Khadija da Zainab, amma tabbas sun ji dadin dan kankanin lokacin da suka samu sakewa da juna.
Ajiyar zuciya ya saki, san nan ya mika mata hannunsa alamun suyi masabiha yana fadin “assalamu alaikum”.
Ita ma nata hannu ta mika masa alamun amsar musabihar tasa tare kuma da amsar sallamar da yayi mata. Yana damkar hannunta ya jawo ta jikinsa ya rungumeta tsan tsan a kirjinsa. Duk da dai Zainab na da tsayi dai dai misali, amma tsayuwar su tare sai ya mai da ita wata gajera a gabansa.
Ta fara kokarin zare jikinta daga gare shi ya kara rike ta tsam, yadda ba za ta iya kwacewa ba. Yace “haba amaryar Bala Mai gwanjo, ina zaki gudu ki bar Balanki”?
Ita ma muryarta can kasa kamar mai rada kuma cike da jin kunya tace “wan nan ba Ya Balarabe na be. Ni nawa kawaici gareshi da kunya”.
Dada rungumeta yayi yana dariya, san nan yace “ahaf manta da shi shi a lokacin ba a halasta masa yin hakan bane shi yasa ki ka ga yana wani kamewa wai shi ala dole ga mai kiyayen hududullah”.
“amma ai dai ya tsaya inda aka umarce shi din ko”?
“ni kuma ina ne iyakata”? ya tambaya tare da tsare ta da idanun bayan ya dan sassauta rikon da yayi mata. Shiru ta kasa ba shi amsa.
“ba ki da amsar hakan to ni ina da ita”. Ya sa dan yatsansa dan ali ya shafo tun daga goshinta zuwa hancinta ya dangane da bakinta zuwa habarta wadda ya dago ta da yatsansa ta kalle shi sosai ciki idonsa. Sai da ya dan yi kissing bakinta, san nan yace “Putri Salju Al Bashir da aka aura miki bashi da iyaka a kan ki”.
Kunya ce ta kamata sai kawai ta boye kanta a cikin kirjinsa. “a’a kar muyi haka mana, daga na kawoki garin Fulani sai kuma ki kama al’adarsu”.
Ta samu ta dan zame kadan san nan tace “dama nima tawa ce ala’adar”.
Tafi yayi mata yace “eyeh Putri saya. That’s more like it. Na fi son duk maganar da nayi ki bani amsa”.
Take ta canza topic tace “yaya gajiyar bikin da kuke yi”? “gajiya tabi lafiya zamuje mu kai amarya Kaduna an jima kadan. Na dai bar su Sa’ad sun dauko wani choreographer wai ya koyar da su rawar Fulani, saboda sun rantse biki zasu yi da gaske a Kera”.
Dariya ta saka a hankali tace “haba wasa dai suke yi. Ina su ina bikin kauye:?
“ashe kuwa zaki sha mamaki. Baki san friends dina da son challenge ba. Already har sun yi oder costume da zasu yi amfani da shi. So gwanda ma ki sanar da su Fatu they should get ready for a duel”.
Nan dai ya zauna har kusan azahar suna ta hirarsu cikin annashuwa da jin dadi. Kuma duk abin nan da ake hannunta na cikin nasa bai saki ba. Ita kanta yanayin da ta ji na wani nishadin da bata taba jin irinsa ba, sai ya sanya ta daina kokarin kwace hannu ta bar shi yana wasa da shi.
Da kyar ya iya mikewa bayan 12.30 shi ma sabo da nacin wayar su sa’ad ne da su Mujib ya hakura. Har bakin mota ta raka shi, anan ne kuma wata wayar ta sake shigowa. Ganin angon ne da kansa ya sa a speaker. Daga can banagaren aka ce “wai kana ina ne. ka san so muke by 1.30 latest mu bar garin nan, amma kai an neme ka an rasa”?
“kai jiya da aka neme ka aka rasa waye ya dame ka da cigiya? Ba kyale ka aka yi ba. I beg give my space. You know the feelings that iam experiencing so why are whining like a wounded cat”.
“yi hakuri mutumina. Da zaka yi dabara ma kawai ka dauko abin da ke saka feelings din mu wuce tare kawai da ya fi sauki”.
Kallonta yayi yace “kina jin su wai in dauke ki ki raka ni. Taimake ni muje amaryar Bala Mai gwanjo”.
“Bala mai gwanjo ai ka kasa shi wan nan dai ta Ya Al Bashir ce. Kuma ma …..”dariya suka ji ansaki daga cikin waya ta mutane da dama wadda ke nuna alamar can ma a speaker suka saka shi. Muryar Mujib taji yana cewa “taimaka ki sake shi ya taho ko ki biyo shi ku taho tare Allah I promise ba zan gaya wa kowa ba, kin san hanyar kaduna idan dare yayi ba kyau gareta ba”.
Dariya kawai tayi ba ta ce komai ba. Da kyar dai ta samu ta lallaba shi ya bar garin. Tun da ya tafi kuwa yake waya da ita har ya isa Kano.
A Kaduna suka kwana saboda dinner da aka yi a can, amma washegari karfe 8.30 a garko tayi masa. Nan fa Hafsa da Fatu suka shiga hidima da shi. Aka ajiye masa kayan breakfast, amma shiru bai ga wacce yazo wajenta ba. Can dai hakurinsa ya kare yace “wai ke Hafsa ina kika boye min mata ne”?
“ai matar ka sai dai hakuri. Mama Hajjo ta fara mata gyaran jiki ta ce kai da sake ganinta sai an kawo ta gidanka”.
A firgice ya dago yace “you must be kidding me”?
“Sorry I am not” ta amsa masa.
Ya juya wajen Fatu da ke masa dariya saboda firgicewar da yayi. Yace. “Fatu wai da gaske ne? amma in ki ka ka yi min haka kin kayuta ke nan, har da ke za a hada baki a hana ni ganin rabin raina”?
“Kayi hakuri ba hadin baki bane. Sun dai ce wai idan ana biki ba a cika son ango yaga amarya ba, wai hakan na kara dankon soyayya a tsakaninsu”.
“And whose theory is this”?
Hafsa ce ta ce “absent makes the heart fonder”.
“Kin ganki nan ba za a iya kada ki a magana ba. Zan hadu dake ne. akwai ran da zan rama”.
Haka dai suka taya shi hira suka samu ya karya, saboda from all indicationsa asubanci ya yiwo daga Kaduna. Amma sai yai wa Mama Hajjo ta dan Zamani. Bata hana shi ganin amarya ba, sai ya fara engaging dinta a video call. Kusan kullum zasu dauki sama da awa uku sun hira, ido da ido ta cikin waya.
Ranar laraba aka sa amarya a lalle, a nan garin kera. Kanwar Kakar Zainab ce ta kama amarya da kwaryar nono sabuwar tatsa. Kuma kaf yayyen Albashir da kuma da yawa daga cikin danginsa sun samu halarta. Momi Rumaisa ma da ‘yar tata gayyar taje saboda fadan da mijinta ya yi. A wannan lokaci ya samu nasarar nuna mata bacin ransa na abin da tayi.
Ranar jumma kuwa tun da safe sai ga wasu mutane da tantuna da kujeru cikin motocin daukar kaya guda biyu. Baffa da ya san da zuwansu ya sa an share makeken filin da ke kofar gidansa wanda ke daura dana amininsa kuma kakan Zainab na wajen uwa.
Suka jere kujerun nan gwanin ban sha’awa, a karkashin tantin nan. Suka yi traditional decoration da zai nuna maka Fulani heritage. Aka tanadi guri na musamman domin zaman ango da amarya. Kafin magariba kuwa motoci suka dinga shigowa garin dauke da ‘yan biki kamar masu zuwa hajji saboda yawansu.
Nan fa aka shiga fito da gasassun raguna da danyar madara da soyayyun zabbi, ana kawo wa baki. Haka suma matan da aka sauke su a cikin gida.
Sai bayan an yi sallar isha, san nan aka fito zuwa harabar da aka tanada domin wan nan sha’ani. Filin yayi tar da haske saboda fitulun da aka kakkafa. Aka yi wa mutanen kauyen da suka zo kallo wurinsu daban na baki daban.
Mai kida kuwa sai dukan kayan kidan sa yake yana busa sarewa tare da waka mai dadin gaske da fillanci, saboda speeker da aka saka masa kana jiyo sautin kidan nasa da ga nesa.
Can ana tsaka sai ga amarya ta shigo cikin shudin saki buba da zani da kuma dankwali san nan aka yafa mata wani a kanta, amma ba lullubi ba. A kan kawai aka yafa shi aka barshi ya sauka ta bayan wuyanta. Ga wani kyakkywan murjani da ke rataye a wuyanta.
Tayi kyau bana wasa ba. Kwalliyar so simple but classy and elegant. Shi ma angon yana gefenta sanye da nasa sakin shudi kamar nata, wan da shi kuma riga da wando ya dinka, san nan ya dora babbar riga ta shadda light blue a kai.
Abokan nan ango kuwa idan ka gansu zaka rantse ba su taba shiga birni ba. Sun sha kwalliya da riga da ake kira lauje waje, wando kafi shanun wuya da kuma hula habar kada.
Suka shigo cikin wata rawar Fulani mai birgewa kowa rataye da sanda a wuyansa. Haba kan kace meye wan nan filin ya kacame, sai ruwan kudi ake yi musu. Suka yi da’iar suka saka ango da amarya a tsakiyarsu. Su dai basa rawa da tsalle yadda abokan suke yi, amma suna dan rausayawa.
Gaskiya lilisco Choreogrpher da suka dauko yayi kokari, domin kuwa ko samarin kauyen ba za su iya irin rawar da suka diba ba.
Kuma wani abin birgewa sun daga rawar tasu to another level. Innovation din da suka yi shi ya kara mata armashi. Can ana tsalle rawar Fulani da kafa daya sai kaga gaba dayansu sun tsuguna sun debo shoki, ko su shagide su fara sekem, ko su fara wani karkada kafar su suna azanto ko shaku shaku.
Ana nan ana ta shan dabdala, kawai ba sai mai kida ya canza salo ba. Ba a ankara ba, sai gani Baffan Nene akayi a tsakiyar fili, yana tsuma. Ya wulwula sanda sama ya café habawa sai wuri ya dau tafi da ihu. Ashe wai taken su ne suna samari shi da amininsa baffan Khadija.
Shi kuma Baffan Khadija ya taso ya shigo ya daga sanda kamar zai kwala masa, sai kuma ya shafa ta a jikinsa kawai. Nan fa tsoffin nan suka shiga wani takun rawa da matasan kauyen kaf ba su san da irin ta ba. Ai kuwa shi kansa AlBashir da ya dauko wrapper ta dubu ya dauki daya ya mikawa Zainab daya sai da kudin nan suka kare.
Na dade banje bikin da naji dadin sa irin wan nan ba. Kusan kowa had fun a wajen. Biki dai bai tashi ba, sai kusan hudu na asuba. Momi na gefe zuciyarta in ban da tafasa ba abin da take yi. Wai wan nan shegiyar Zainab din ce ta samu wan nan daukakar. Sai wani gumi take yi. Najuya naga sansanyar iskar da ke kadawa ba ta sa ko masu rawar sun yi gumi ba sai ita. Nace to ina ga jininta ne ya hau.
Bayan an yi sallar asuba da yawa suka samu suka dan runtsa. Daga nan aka fara shiryen shiryen daukar amarya. Da azahar suka bar garin tare da dangin Zainab masu yawan gaske saboda yaya A’I ta sanar da cewar suma can yinin biki ne ke jiran su, shi ne ma dalilin da aka tafi da wuri.
Tana shiga gidan su Albashir aka zarce da ita sashensa mai dauke da daki da falo da kuma bandaki. Sallah kawai ta yi, wata mai make up ta fara aikinta. Ta tsantsara mata kwalliya cikin wani leshi da ina kyautata zaton bai yi kudi ba a saye shi 150k.
Aka dora mata gwaggwaro mai stones da kuma mayafinsa. Idan ka ganta kamar wata bakuwar balarabiya. Bayan ta gama kintsawa sai taga kowa ya na ficewa daga dakin, aka barta ita kadai.
Kamshin turarensa ta fara ji kafin ta jiyo takunsa. Shima ya bayyana cikin wani danyen voil mai tsananin kyau. Sai wani walai walai yake. A gabanta ya durkusa ya rike hannayenta duka biyu. Ido kawai ta dago ta kalle shi. Ganin yadda ya kura mata ido ya sanya taji kunya ta sauke nata.
Hannayensa ya sa ya tallabo fuskarta ya kissing din goshinta. San nan yace “welcome home my Putri”.
Ba ta iya magana ba sai murmushi kawai da ta aika masa. Shi ya dago ta daga zaman da tayi ya rike hannuwanta, ita kuwa ta bishi kamar rakumi da akala. A haka suka fito daga falonsa zuwa bakin verender dakin nasa. Daga kasan matattakala guda biyar da zaka taka kafin zuwa dakinsu ‘yan uwa ne damkan.
Suna fitowa sai guda yiyiyiyi, kamar Gidan bikin larabawa. Inda kuwa kasan irin celebrities din na sun fito paparazzi na daukar su hoto haka aka dinga yi musu. Sun dauki kusan minti biyar tsaye a wajen, kafin Ya Maryam ta samu ta sa mutane suka basu hanyar wucewa wajen zamansu.
Suna tafiya wakar shimfida fuskar ta wuce ta tabarma na tashi daga speaker DJ. Saboda haka sai yaya A’I ta hana su karasawa wajen zamansu. Nan suka tsaya suna wata rausaya mai daukar hankali, kafin kace kwabo dangi sun yanyame su ana ta ruwan kudi.
Nan ma an ci an sha an raba souvenier, inda aka raba kyautar atamfar buyers batik da kuma sallaya mai laushin gaske ‘yar Turkey da hijabi dinkin Indonesia mai dauke da hijab da burmemen skirt a cikin wata jaka mai kyawun gaske. Sai goshin magariba taro ya waste. Inda kuma akai kaita wajen Umma da nata ‘yan uwa suka sa mata albarka.
Tana idar da sallar isha sai gashi ya shigo da alama shima daga masallaci yake. Yana zama a bakin gadon dakin, yaya Ai tayi sallama tana mai ajiye musu kwandon abinci. Shi ta juya ta kalla tace “maza ku ci abinci, kar ku Makara saboda nine za’a fara checking in”.
Bata jira amsar sa ba ta juya ta fice. Shi ya tilasta mata ta dan ci abinci ba laifi, san nan ta canza kayan jikinta zuwa atamfa super wadda ta dora hijabin da ya dace a kai. Cikin kayan da mamanta ta dinka mata ne.
Shima ya canza kaya zuwa riga da wando kawai na shadda ba babbar riga. Hafsa ce tayi sallama janye da trolley tana fadin “Umma tace kuyi sauri kar ku Makara”.
San na ta juya wajen yayarta tace Ya Zainab ga kayanki na gama hadawa”.
“na gode budurwar kauye “ya fada yana mai karbar trolley daga hannunta. Shi ya dauki nasa da nata. Ita dai ta rataya jaka kawai ta bishi ba tare da sanin ina zai kaita ba. A haka suka shiga mota cikin rakiyar ‘yan uwa bayan sun yiwa Umma sallama suka nufi airport.
[8/8, 22:16] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 28
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Tun da suka kama hanya bata yi Magana ba. Sai shine ya matso kusa da ita. Hannayenta ya kama yana wasa dasu a cikin nasa. Ta dago a kunyace ta kalle shi. Kamar zata yi Magana, sai kuma ta fasa ta saukar da kanta kasa cike da jin kunya. Kallon da yake mata shi ke dada sa ta jin nauyinsa.
He pierced her with his eyes yarda tana jin kallonsa har cikin jininta. Hakan ke hanata yi masa Magana, saboda tsoron bude bakinta take yi kar ta tona wa kanta asirin zuciyarta. Ko sanda suke video call da shi, ba ta san yadda ake ta ke biyewa kalaman soyayyar da yake tsarata ba ita ma kuma ta kan dan mayar da martini.
Sai call ya kare idan ta zauna ta tariyo abin da ta ringa fada sai kuma ita da kanta taji kunyar kanta. To yanzu ma shi ke hanata Magana. Kar asirin zuciya ya fito ta lebe .
Shi ya katse mata tunanin da ta ke yi ta hanyar dan matsa hannunta da ke rike cikin nasa. “me amaryar Bala Mai gwanjo take tunani ne”?
Ta dago ta kalle shi amman irin kallon da ya ke mata shi ya sanya ta kasa fadin abin da tayi niyya, ta saukar da kanta kasa.
“Okey I get it you are wondering ina zan kaiki. Kar ki damu na tabbatar zaki ji dadin surprise din dana shirya miki”.
Sai da suka shiga airport ta gane abin da zai faru. Tafiya zasu yi. Allah ya sa ba a jirgi zai dora ta ba. Ita tsoron shiga jirgi ta ke yi tun da bata taba hawa ba. Kuma ta kan ji labarai cewar wasu suna amai har da gudawa idan suka hau jirgi.
Take kuwa tsoro ya bayyana a fuskarta har ya gano hakan. Yace "Putri ba dai tsoron hawa jirgi kike ba, naga yadda fusakar ki ta canza da ganin mu a airport”.
“na dauka duk abin da ya zama na farko a rayuwa ka kan tsorata da shi”. Itama ta bashi amsa a sanyaye.
Sai da ya dada lankwasa muryarsa san nan yace " ke nan kina tsoron aure na da ke”?
“A’a sam bana tsoro because kai na au……” ta kasa karasa Kalmar da tayi niyyar fada saboda kumya.
Dada rungomata jikinsa yayi cikin dariyar jin dadi yadda take kokarin nuna kaunar ta a gare shi duk da kunya kan mata handbreak.
“thank you for trusting me. Haka zalika kar kiji tsoron komai in dai kina tare dani. Zan yi iyawata in tabbatar ba abin da ya gagare ki”.
Take kuwa taji ta yarda da hakan sai ta sakar masa murmushi me nuna ta yarda da shi da kuma duk abin da yace. Departure lounge suka dosa. Kwarai tayi mamakin ganin yadda ma’aikatan wajen suka sanshi suke kuma yi masa gaisuwar ban girma. Wani babban ma’aikaci ne ya karaso suka gaisa san nan ya karbi passport din su yace da wani staff din wajen “maza a kammalawa KIM BASH checking dinsa”.
VIP section na departure lounge din suka je ya nema musu wajen zama. Suna zama kuwa attendant din wajen yayi approaching dinsu yana tambayar me zasu sha. Sun nuna basu bukatar komai, amma ya nemi da ya sayo masa peppermint. Ba su fi minti biyar da zama ba aka kawo musu passport din su tare da boarding pass. Haka nan mai sayen peppermint shi ma ya dawo.
“ga dukkan alamun kai sananne ne a wajen nan”?
“in ban da neman aurenki ba abin da ya taba ajiye ni a kasar nan for more than a month ban yi tafiya ba”.
Da alamun damuwa wadda ke nuna bata kaunar rabuwa da shi haka zalika ba ta san sanda bakinta ya yi subutar fadar “Ke nan yanzu haka zaka ci gaba da tafiye tafiyen”?
“kwarai kuwa but with you by my side, gorgeous”.
A nan kuma taji sanarwa ta loud speaker. Ba dai san ta meye ba, amma taga ya mike tare da dago ta daga inda take zaune. A cikin jirgin ma a VIP suka zauna. Har da wani dan labule da ya raba cabin din su da na wasu, san nan ga kujeru idan kaso ka kwantar da su kamar gado.
Shi ya daura mata seat belt dinta bayan sun zauna. Sai da aka fara sanarwa a cikin jirgin ta gane ashe jirgin Saudi air suka shiga zuwa kasa mai tsarki. Murna ce ta kamata. Idan bata manta ba, yau 24 ga watan dhulkida. Hakan ya sa ta gane zata samu damar sauke aikin hajji.
Da su Farida sukayi candy daddy ya kai su. Aka ce ba za a je da ita ba, saboda bata ci jarrabawa ba. Haka nan da auren su anti Sakina sun sake zuwa har da su Sakinan nan ma ba a je da ita ba akan ba wanda zai kula da su Halim.
Shi kansa ya lura da farin cikin da take cike. Shi ma kuma yaji dadi matuka. Balle da ya tuna maganar yayyensa inda suke tsokanrsa da cewar wa yake zuwa macca honey moon.
Hannunsa ya sanya ta cikin hijabinta ya dada rungomata jikinsa, yana mata hira mai dadi. Nan kuwa ya tafi da hankalinta har jirgi ya daidaita a sama ba ta masan an tashi ba. Sigh of relief ya saki lokacin da ya ga ba tayi reacting to take off din su ba.
Ita ce a zaune bakin taga saboda haka ya rankwafo ta gefenta yana mata explaining wasu abubuwa har kuma suka shiga gajimare sosai suka daina ganin komai. Haka nan da aka kawo abinci shi ya dinga bata a baki. Sosai taji dadin abincin. Shauki ya hana su baccin duk su biyun duk da kashe fitila da a kayi saboda dare ko wasu na bukatar yin bacci a cikin jirgin.
Tana rungume a jikinsa suna hirar su kasa kasa. Awa biyar cur suka sauka a airport din birnin Ma’aiki SAW. Hotel din su daf da shabbaki yake. Tsananin murna tun a lokacin taso shiga. Ya lallabe ta sai da suka yi wanka san nan suka shiga anan kuwa suka yi sallar asuba.
Tana dosar masallacin ba ta san lokacin da hawaye ya zubo mata ba saboda wani shauki da ya shige ta na murnar ganin abin da tafi muradi yau ta samu. Kullum idan su Farida suka dawo daga ummara ko aikin hajji suna bata labari ta kan ji ta kawatu da son zuwa inda suka je. Nan ne kadai idan sun bata labari take jin son zuwa, amma sauran kasashen da suke zuwa suna bata labari ba su taba dada ta da kasa ba.
A ranar dai bayan sallar asuba, baccin gajiya suka yi. Ko karyawa basu samu yi ba sai kusan azahar. Bayan sun idar da sallah ya shiga da ita Raudha. Wayyo kukan dadi kawai take yi. Ya dade yana tsimayin fitowarta har ya fara tsammanin bata tayi tun da wajen shigar mata daban dana maza. Sai bayan kusan awa daya ta fito.
Tun daga wan nan lokacin ba abin da suka sa a gaba sai ibada. Kullum karfe biyu na sulusin dare suke zuwa masallaci. Bayan sun gama nafilolin da suka sawwaka, zai dakko Qur’ani mai girma ya bata izu biyar shima ya dauki biyar. Kwana shida cif suka sauke shi.
A kawan na takwas suka nufi garin macca domin aikin hajj. Ta ga gata matuka a wajensa. Duk in da zata tana makale a jikinsa kamar za a sace ta. Haka lokacin da za a fita zuwa Minna a karamar motar suka tafi kuma ta wani titin daban wan da duk travelling agency su ne ya yi musu organizing as part of their VIP package.
A nan din ma a Camp A ya kama musu tent su biyu kawai sai kananan gadaje guda biyu a ciki da kuma dan karamin bandakinsu attache to the room. Babu wata wahala data fuskanta, saboda ba kananan miliyoyi Al Bashir ya saki ba domin ta samu easy and comfortable Hajj.
Ranar da suka yi jifa na farko ranar babbar sallah ke nan ranar suka shiga Macca domin yin dawafin aikin Hajj da kuma sa’ayi. Bayan sun kamalla jifa na biyu da na uku suka dawo hotel din su dake daf da harami a Zam Zam towers.
Da magariba suka shiga ka’aba suka yi sallah. Sai da suka yi isha da shafa’I da wuturi. Ya kuma kara da wata nafila da ita dai ba ta san ta meye ba. Ya dade yana addu’a wacce ta fuskanci rayuwarsu da ita yake tayi wa wan nan addu’ar a gaban dakin Allah. Bayan sun fito suka nufi inda zasu ci abinci. Abu daya ta lura dashi yau wata irin annshuwa yake ji a cikin ransa.
Bayan sun koma masaukinsu, ita ta fara shiga tayi wanka san nan shi ma ya shiga. Sabanin lokutan baya yau wata irin silk negligee ya ajiye mata a kan gado. Ita data daga ma ta dauka shimi ce. Ba ta san ta meye ba ta mayar da ita ta jiye, ta dauko zulumbuwar rigar da ta saba sakawa ta saka. Tana gyara gashinta ya fito daga wanka.
“ya haka”? ya tambaye tare da kai kallonsa wajen rigar da ya ajiye mata.
Bata kula shi ba ta ci gaba da abin da take yi na kokarin gyara inda zata kwanta, wanda tun da suka zo Saudiyya kullum a kan couch din dakin yake kwana ya bar mata gadon.
Ta ci gaba da kokarin shimfida masa quilt da kuma pillow domin yaji dadin kwanciya. Ya dan daure muryarsa alamun ba wasa yace “ke ba dake nake Magana bane kin yi banza da ni”.
Ta dan tsorata jin yayi mata Magana da muryar da bata taba jin yayi zance da ita ba.
“Wai da shimfida nake kokarin yi maka”.
“ban saki ba, ba kuma naso. And kafin raina ya baci ki cire wan nan buhun da kika zuba ajikinki ki dau kayan da na ajiye miki ki saka”.
Ta kai kallonta kan rigar amma ta kasa dauka. Tsawa ya sake daka mata “wai ba Magana nake miki ba”.
A firgice ta dau rigar ta shiga bandaki a guje. Dariya ya saki kasa kasa ganin yadda ta tsorata, amma ba ya son bata fuskar yi masa musu sai ya dada shan kunu. Ta sa riga amma ta kasa fitowa, saboda haka da taji alamar murda kofar yana fadin “ba zaki fito bane” a tsorace ta dau bath robe din data cire ta zurma ta dora a kan night gown din data saka, wacce ta bi ta lafe a jikinta ta fitar da duk wani asirin kyau da ta boye cikin hijabinta.
Yana ganinta haka bai san sanda dariya ta so kubuce masa ba. Shi ya karasa inda ta tsaya yan fadin “to karaso mana, na rasa wan nan sanyin naki na yau na menene. Ni ne fa Balarabenki ba wani ba”.
Ta bayan ta ya tsaya ya rankwafo ta bayanta. Hannayensa ya saka ya cire nata daga rikon rigar wankan da tayi. Ya salube ta, san nan ya tsaya ya na kare mata kallo, wanda bai taba yi mata irinsa ba sai yau din nan.
Allah ya sani da kyar ya iya karasa alkawarin bakacen da yayi wa ubangiji na cewar idan har Allah ya sa ya auri Zainab zai daurewa zalamarsa har sai ya kawota gaban dakin Allah san nan komai zai kasance tsakaninsu.
Haka ya faru ne sakamakon wata hira da suka taba yi shi da ita. Tambayarta yayi yace “Putri a duniya wacce kasa kike da burin zuwa a rayuwarki”?
Da wani irn excitement a fusakar ta tace “ai ni ba inda nake son zuwa irin kasa mai tsarki. Ranar da duk na ganni a garin macca da Madina ban san irin farin cikin da zan yi ba. Kullum idan su Farida suka je suka dawo suna bani labara sai in ji kamar in yi tsuntsuwa in je”.
“Amma ya akayi suka je ke ba ki samu zuwa ba bayan kece babba”.
Kasa tayi da murnarta and all the excitement left her voice. Cike da rauni tace “saboda ni bani da kokari bana cin jarrabawa”.
Ya tausaya mata matuka. Ganin yadda take da ilmin addini da kuma yadda take jin larabci ya san kawai muguntar matar gidan ce ta hana ta zuwa. Wan nan shine dalilinsa na yin wan nan bakace.
Ni da na ga shiru ba a fara honey moon ba, har na tsorata na dauka ko maganar MomI ce ke son tabbata, ashe shi baka ce ne kansa. Ya kai minti uku yana kare mata kallo. Wata irin kirar jiki gareta da shi dai a iya yawonsa bai taba ganin perfection irin nata ba.
Da yake ganinta cikin hijabi, ya dauka flat take, ashe all the curves are in the right places. Jikinta so beautiful. Da ya kai hannunsa kuwa ya taba skin din jikinta, sai da ya saki wani irin numfashi. So soft and silky. Taushin hannunta ya dade yana bashi mamaki. Ga shi kullum cikin aiki take, amma hakan bai sa hannayenta tauri ba, saboda bata rabo da shafa man kadanya a hannu nata.
Ya saba da jin kamshin jikinta, amma hakan bai sa yana jin ya gaji da shaker sa ba. Wajen wuyanta ya tsaya yana shinshinarta. Ya kuwa shaki kamshin ta sosai, kafin ya sauke labbansa akan nata. Take jikinta ya dauki rawa na abin da taji da bata taba jin irinsa ba.
Ta saba da dan light kiss da yake mata, amma wannan French kiss din is different. Take jikinta ya dauki rawa. Kafafunta suka kasa daukarta. Jin zata zube a wajen ya dauke ta kamar karamar yarinya, ya shimfideta a kan gadon, shima ya bita .
To alhamdu Lillah kazafin Momi ya tabbata karya, saboda a wan nan rana ya tabbatarwa da Zainab cewa shi lafiyayyen namiji ne mai tsananin kwazo kuwa. Saboda asuba ita dai ta kasa ko motsi, amma shi ya daure a gaggauce ya samu raka’a daya a masallaci.
Sai da ya dawo san nan ya taimaka mata ta gyara jikinta tayi wanka. Sallah dai bata samu ba sai bayan shida na safe. Ita dai duka tayi sanyi saboda bata tsammaci haka daga gareshi ba. Yayin da shi kuwa murna kamar ta zautar da shi. Gaba daya ya rude mata sai rawar jiki yake. Ga shi ya hana ta matsawa ko nan da can kamar za a sace ta.
Kwana biyu kawai suka kara a Macca suka shiga Riyadh wajen wani abokinsa da suke kasuwanci tare a nan kasar. Na ma dai amarcin da suke ragargaza ya fi komai. Da zasu tafi kuwa kyautar sarka babba da awarwaron gwal guda shida suka bata.
Daga nan suka wuce China saboda shi kansa ya san yayi neglecting aikinsa. Gidansa na zhoungou anan suka sauka. Bilkisu taji dadin ganinta. Shima dai nan din aiki rabi da rabi ne. saboda baya sama da awa uku a factory bai zo inda take ba. Ta dai sha tsokana wajen Bilkisu.
[8/8, 22:27] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 29
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Soyayya dai ana rangada ta tsakanin Al Bashir da Zainab. Ga karatun ta na koyon turanci da suka dage dashi. Kullum kafin ya fita zai koya mata newa words da spelling da pronunciation dinsu. Haka zalika zai bata example yadda zata yi constructing sentence da su.
San nan zai ba da dokar lallai kafin ya dawo ya tarar ta haddace su. Kuma hakan take yi. Ba ta shara bata wanke wanke ba wanki ba guga. Saboda haka sai ta samu enough time to face her studies. Tana kuma da wani web site wanda ita ta lalubo shi da kanta, bai ma san ta kai wayon haka ba. Duk abin da ya kakare mata a wajen za ta duba ta ga yadda zata gyara.
A yau da ya fita bai dade ba ya dawo, saboda yana son suje shopping. Tare suka shiga mall din suka nufi wajen kayan mata. Bawan Allah nan ya sai mata kayan mutunci , yaki sai su dogon wando da su three quarter and other revealing out fits yake zabar mata.
Da kyar ta samu a wani shagon larabawa ya saya mata dogayen riguna masu kayan gaske. Suka shiga wajen undies. Kunya ce ta kamata ganin shi da kansa yake duba inner wears. Ya gane yanayin data shiga amma sai ya share kamar bai gani ba.
“Putri wane size zamu dauka”? ya tambayeta lokacin da ya dakko wata shudiyar rigar ciki mai dan banzan kyau kamar ka saka ta a saman riga. Kudinta ba zai kasa dubu ashirin ba kudin Nigeria.
“putri I am talking to you tell me your size”.
Ringin din wayarta ne yayi saving din ta daga embarrassing situation data shiga. Tana dubawa taga number Fatu. Wata ajiyar zuciyar ta saki da ta tuno mastalar da take ciki. Ta fara mata zolaya, ta tsai da ita ta kuma juya harshenta cikin larabci tace “ke ki tsaya akwai matsala”.
Daga can ta amsa mata “wacce irin matsala me ya faru ina fatan ba ke da bala bane”.
“ni da shine mana. Ya kawo ni sayen kaya yanzu muna shagon undies yake tambayata size din na. Kin san kuma kullum kwance ake bani saboda haka lambar duk ta koke ban san size din ta ba. Ni kuma kunya nake ji in sanar da shi hakan. Kuma kin ga na gwanjo ma da muke saye suma ba lamba a jikinsu. Ban san yadda zan yi ba”.
Dariya tayi sosai san nan tace “na tuna size dinki kin tuna a lefen kawarmu Salma da aka baki. Ki ka ce baki taba jin dadin saka ta irin ranar ba saboda kin samu perfect size dinki”.
“Wai Allah na gode maka. Size nawa ne”?
“kice masa 38B’.
“Shi ke nan na gode zan kira ki idan na koma gida”.
Tana juyowa suka hada ido da shi ta saki murmushin wanda ya katse lokacin da ta ji muryarsa cikin larabci yana fadin “da ma baki tona mana asiri wajen Fatu ba. Mu shiga fitting room in gwada miki da kaina”.
Da sauri ta juya zata fita daga shagon saboda tsananin kunya data kamata. Dankota yayi yana kokarin tura ta cikin fitting room din wanda ke kusa da su.
“ka yi hakuri zan fada da kaina”.
Yana mata cakulkulin wasa yake fadin “zaki kara gulmata da wani yare”?
Ita kuma tana dariya tana fadin “a’a kayi hakuri ba zan kara ba”.
Haka dai a shiririce kamar wasu kananan yara suna tafe suna wasa a haka aka gama shopping din. A wajen sayen takalmi kuwa shi ya tsuguna a kasa kusa da ita. Duk takalamin da aka kawo ya dora kafarta akan cinyarsa ya gwada idan ya ga yayi masa su saya.
Amma fa sun saya da yawa. Domin yadda take da karuwan jiki haka take da karuwar kafa. Duk wanda aka sa sai kaga yayi mata kyau. Har mai shagon ya tambaye shi da turanci saboda ya naji akan wai ita din model ce.
“yeh a very expensive one. But only I get to see her in her modelling outfit”. Ya amsa masa. Farkon zuwanta har mamaki take ita kanta da yadda mutane ke tanka kyawunta. Ga shi dai a cikin after dress take, amma hakan bai hana kyawun ta fitowa ba.
Shi da kansa in ya zauna ya dinga mata kirari ke nan. Ya kalleta ya ce “my beautiful princess. Elegant while covered, appealing idan ta sauke abaya, idan kuwa a ka zarce haka, you drive me crazy”.
Sai da suka huta suna cin abinci tace “yanzu sabo da Allah ashe ka iya larabci amma kana jin mu ni da Fatu kaki nuna mana. Da ma zaginka muka yi fa ai da ka bar mu da jin kunya”.
“haba putri kin kasa gaya min kina sona, sai kuma na yi sa’a kin iya gayawa wata da harshen da kike tsammani banji, and you expect me to disclose my secret no way. Yau ma sa’a kika ci. Maza ku canja wani yare mu gani ke da ita”.
“a’ai an gama wan nan game din”.
Bayan sun kwanta da daddare yake shaida mata gobe zai fita da wuri kuma zai dade a factory. Bayan ya fita ta dauki sugar da lemon tsamin ta ta dafa ta saka a fridge yayi sanyi, saboda tana son yin halawa.
Sai da ta shiga sauna bath din da ke bandakin gidan ta turara kanta san nan ta fito bayan ta goge danshin turiri ta fara dana wa jikinta halawa nan tana fizgewa. Sai da kuwa ta dauke duk wani gashi dake jikinta banda na gira da kai. Bayan nan ta dauko dilka cream da ta sayo a shagon larabawan nan ta muttsike jikinta da shi.
Duk bata fi tara na safe ba ta gama da wan nan. Sai ta dakko sole tape din data yanka jiya da daddare akan chopping bord dinta. Sai da ta saki murmushi da ta tuna yadda ya dameta da tambayar me zata yi da razor da sole tape da ya ga tana masa wani yanka kamar bille.
Murmushi kawai tayi bata ba shi amsa ba. Na kafarta ta fara sakawa san na ta dawo hannu ta saka wanda tayi wa yankan hula daidai saman faratunta na hannu, da ga nan kuma ta nada shi siri siri kamar spring. Shi ma ta yabe da lalle
Ta sa leda tadaure ko ina saboda kar yayi saurin bushewa. Barcci tayi ba ta farka ba sai bayan uku. Ta cire lallen wanda tun daga saudiyya tayi dakonsa shi da mahallabiyar da ta sa masa.
Dau kuwa ya kama. Hakan ya dada fito da asirin kyawun hannaye da kafafun nata. Lokacin data shiga wanka kuwa saboda santsi da jikinta yake yi, haka nan ruwa ya dinga gangarewa daga jikinta.
Tana idar da sallah ta tsantsara kwalliya da daya daga cikin kayan da suka sayo. Dogon wando jeans da kuma T-Shirt wacce ta dada kawata mata figure dinta. Bai shigo ba sai bayan magariba, tana zauna a kujera ta dora kafarta kan center table tana kallon TV.
Yana bude kofar cike da gajiya yaji ya wattsake saboda arba da yayi da wata jar kafa da aka yi wa wani rodi rodi kamar kwale. Sakin jakarsa yayi ya dumfare ta. Dagota yayi tana rike a hannunsa yana juyata saboda ya karewa kwalliyarta kallo.
“woh! My putri gaskiya kin biya ni. Nawa za a caji wan nan kwalliya haka”?
“idan ka bani kyautar zuciyarka, ka biya ni”.
“kin dade da samun wan nan putri, nemi wani abu daban”.
Da kyar ta lallaba shi yayi wanka sukaci abinci. Ko shi abincin akan kafarsa ya dora ta yana feeding dinta. Lokacin da suka je bacci kuwa sai da ya kusa zaucewa saboda santsin jikinta kawai.
Allah ya sani zainab tana tsananin alfahari da kaunar da Al Bashir ke nuna mata. Bata taba sanin somebody can give so much love ba sai a wajensa. Sai da suka dauki wata biyua China ya samu ya rage ayyukan gabansa, san nan suka biya ta England can ma dai dan wani abin na sana’arsa ya dai daita. Suka shiga Turkey suka kwana biyu, san nan suka yada Zango a Dubai. Wanda suka yi kwana goma kacal.
Sama da wata uku ba sa Nigeria, san nan suka dawo gida. Ba wani ba ita kanta idan ta kalli madubi bata yarda itace saboda wani irin beuty data kara, balle shi uban gayyar da ko barci take birge shi take yi.
Driver ne ya dauko su daga airport inda bai ajiye su ko ina ba sai gidan su Al Bashir. Amma maimakon su shiga gate din main house sai taga sun shiga a smaller version of the main house.
Duk da bata kwana a gidan ba, amma she has a good memory of the environment. Inda gidan yake yayi kama da filin da aka yi yinin bikinta. Ganin kamar tana tunani, ya saka shi cewa “sorry putri I remember cewa kin ce zaki iya zama da mamana shi yasa na gina gida gefenta, because having the two of you very close to me zai sani in kasance cikin farin ciki, amma ba zan takura ki if you have any reservation sai mu canza waje”?
A dage ta juyo ta kalleshi. San nan tace “ashe kai har zaka ga darajar matar da zata ki zama da mahaifiyarka. Ni Ya Bala ne alkawari muka yi zai ajiye ni kusa da ummansa. Idan nayi laifi tayi min fada. Idan na kuskure ta gyara min. ni kuma in dinga binta sau da kafa ina mata ladabi da kuma koyon lamuran rayuwa a wajenta, saboda ko ba komai ta zama role model a idona ko don Haifa min mijin mai cike da tarbiyya da halin kwarai da tayi”.
Ganin driver ne kawai ya hana shi rungomata jikinsa.
Itace ta ce da driver “mu fara shiga main haouse tukunna”.
Ai kuwa su Umma na jin takun motarsu duk suka fito ita da yayyensa gaba daya cikn murna, sai fadi take “ga bakin China sun dawo. Kuma dan uwana ba sai ku karasa da ita gida ba ta huta tukunna”.
“umma is not my fault ita ta fada akan sai tashigo nan san nan zata gida”.
Nan dai aka zauna gaisuwa ta musamman. Ruwa kawai umma ta barsu suka sha a wajenta ta kora su gida.
Sai da hawaye ya zubo a fuskar Zainab da taga dankareren gidan da wai nata ne.
Dan wani zaure suka shiga daga tsakiya, wanda ta nan kofa biyu ce daya ta shiga dakin baki da toilet dinsa, mai kallonta kuma ta shiga wargajejen falon da ke hade da dining dinsa, wanda daga karshensa katon kitchen dinta yake.
Shi kuma a gefensa faffadar staircase ne wanda zai kai ka saman gidan, yayin da a bangaren hagu kuma ta sake ganin wata kofa a rufe, sannan suka hau inda ta samu manya dakuna guda uku da falo dan madaidaici da kuma dan wani ofis na aiki a cikin gida da yayiwa kansa.
Daga dakunan har falon ni dai na san ko Rakiyan Jagi da Amina ba zasu hada gida ya fi haka kyau ba. Labulayen nan har sheki suke yi kamar da silk aka yi su. Haka carpets din dake shimfede suma abin kallo ne.
Da ta shiga dakin daya ya nuna mata a matsayin nata, kawai hawaye ne ya zubo mata. Closet ta samu dankare da kayan sawa sun fi kala dari. Kuma a cikin kayan nan Holland ce mai karamin kudi. Ga takalma da jakunkuna birjik da su. Fiye da rabin kayan a dinke suke.
Ga turarurrka designer fal kan dressing table dinta. Haka nan toilet shima an kawata shi da copboards masu dauke da towels da kuma kayan shafa daga wani lungu.
Ko a mafarki bata taba haskowa kanta irin wan nan rayuwa ba. Meena ce da ta zo kawo musu abinci take shaida mata ga lefenta inji su Maama. Ta gane Yaya A’I take nufi da wan nan suna.
Ita ta kama mata suka dan dada gyara abin da ba a rasa ba, san na tayi musu sallama ta shiga main house.
Washegari bayan sun dan taba kailula, suka zauna ware tsaraba. Shi ya sa ta ware na mutan garko daban na mutan kera daban san nan na ‘yan gidansu. Suma kuma nan gidan haka ta dauki tasu tsarabar rankatakaf ta kai musu. Fatu kuwa da mama Hajjo da ‘yan gidansu akwatin su daban.
Bayan nan ya bude mata daya kofar da ke rufe a kasa. Wani irin industrial kitchen ta gane mai dauke da injuna yin snacks da katon oven da zaka iya gasa cake dari biyar a lokaci daya. Shi kuwa samosa makinga machine din sai dai ta hada fillings idan ta kwaba flour a mixer wacce a lokaci daya zata yi kwaben flour na kwano uku.
Asa dough din a wani waje a sa fillings a wani waje, sai dai ka dainga daukar finished samosa din ka ko spring rolls ko meat pie daga karshe depending on mould din da ka saka. Ita ma kuma a cikin awa daya tana nada maka samosa ko spring rolls ko meat pie dari biyar.
Ga su chopper da meat mincer da dai duk wani abu da zata bukata to enhance her business. Abu daya zata iya tunawa suna China aka nuno irin wan nan kitchen din da yadda ake operating dinsa. Cike da exicitement tace “how I wsih I could get some thing like this”. Bai ce mata komai ba bai ma nuna ya na da interest a kan abin data fadi ba.
Juyowa ta yi ta rungume shi ba tare da sanin tayin hakan ba. Sai godiya take zuba masa. “Hold on. The kitchen is your wish, idan kin so kiyi sana’a idan baki so just let it be, because you don’t need to”. Albashir yace da ita.
Ba ta samu shiga gidansu ba sai wata washegarin da la’asar ta nufi gidan ba tare da ta san irin tarbar da momi zata yi mata ba.
[8/9, 13:58] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 30
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A motar ta Rav 4 yayin wan nan lokacin kalar maroon mai ruwan hanta, direbanta mai suna mallam Yunusa yana tukata, ta doshi gidan su. Horn ya danna, mallam ya leko ta ‘yar tagar da ke manne da dakinsa. Tayi saurin sauke gilashin gefenta, tace “mallam Barka da yamma” .
Da murna ya wangale kofar gate din. Kusan tare da motar suka nufi wajen da za ta tsaya. Da kansa ya bude kofar bangarenta, yana fadin “barka da zuwa uwata. Yau ke ce a gidan nan”?
“nice mallam”. San nan ta rusuna yadda ta saba gaishe shi. Bayan sun gaisa take tambayarsa baba Laure.
“Ai Laure tana gida. Kin san bayan aurenki da sati guda Alhaji ya aiko wani mutum da sako, gida ne sukutum ya saya mana shi a nan unguwar badawa, baki ganshi ba kato da shi”.
Cike da murna tace “kai amma madalla, an gode ni bai ma sanar da ni ba”.
Nan dai suna ta dan tattaunawa, hango Halim da ta yi shi ya katse tattaunawar tasu. Da gudu yaron ya karaso ya rungumeta. Ko ba komai akwai shakuwa a tsakaninsu. Dukkan su su biyu suna kaunarta kwarai da gaske ko don wahalar kuruciya da ta sha dasu.
Hannunsa rike a cikin nata ya jata suka shiga gidan. Ita kuwa hankalinta yafi karkarta kan yanayin da ta ga gidan. Sam ba haka ta tafi ta bar shi ba. Da gani kulawar da ya saba samu tayi karanci kwarai da gaske..
Harabar dai a share take ba laifi ko don dama Mallam ne ke gyara ta. Amma fa tun da suka fara shiga cikin gidan ranta ya baci matuka. Kai kace gidan ya dau shekara bai ga shara da mopin ba.
A kofar baya kuwa tarin wanke wanke ta tarar da wata ‘yar mitisitisyar yarinya ta tasa su a gaba tana kuka.Ta kalli kayan tsibi guda ga kuma yarinyar duk ba ta fi shekara tara ba. Kayan nan kuwa sun fi kama da an ci abincin biki an waste.
Shi kuwa bai kula da yanayin ta ba sai kaudi yake zuba mata yana bata labarin makaranta. A hanyar shiga falon suka yi kicibis da Hakim. Shima kamar dan uwanta haka ya rungumeta a haka suka shiga wajen Momi. Duk sun dafe mata kamar zasu ka da ita.
Fadi suke “Momi ga Ya Zainab ta zo”.
“kai da Allah can ka cika mana kunne da surutu sai kace wanda yaga bako daga gidan aljanna”. Tana daga ido taga ashe anti Sakina ce mai wan nan bala’in. a haka dai ta durkusa kusa da Momi cike da ladabi tace “momi barka da war haka”?
A wulakance ta dago ta kalleta. Take kuma tsadaddar after dress din dake sake a jikinta ta tsone mata ido. Da gani kasan ba zata kasa dubu hamsin ba. Ga kuma awarwaro gwal guda hudu ma su dan karan kyau sanye a hannunta.
Da ta dago kuwa wani daddadan kamshiun turaren ne ya daki hancinta wanda tassan tabbas bakuwar da ta shigo ita ta zo da tsarabarsa. A wulakance ta ce “sai yau ki ka ga damar zuwa ki gai da mutane? Ki dai yi a hankali shi gidan miji ba matabbata bace. Idan ta kubuce gidan dai da ake gudu nan za adawo”.
Murmushi tayi saboda a yanzu kaunar da Al Bashir ke nuna mata ta bata wani irn confidence da ya sanya bata jin shakkar kowa da kuma komai a rayuwarta.
“Momi kiyi hakuri ba na nan ne sai jiya na dawo”.
“marar kunya ai ba sai kin sanar dani kinje yawon shakatawa da miji ba. Idan ba kya nan ko waya ba za ki iya yi ba”.
“Momi kiyi hakuri a gida na bar wayata ban tafi da ita ba. Kuma ban rike number kowa ba a kaina. Shi yasa”.
“ke dai kika sani.in dai auren zamani ne kiyi mu gani. Wadanda suka mutunta iyayensu ma, suka rabu dasu lafiya yaya suka kare, balle ke mai auren yaudara”.
Ba ta bata amsa ba ta mai da hanakalinta wajen Anti sakina tace “Anti sakina barka da yamma”. Sai da ta maimaita sau biyu san nan ta yi firgigit daga kallon leshin da ya bullo ta gefen rigar zainab wanda ita bama ta san ya bullo din ba. Ba kunya kuwa ta kai hannunta ta taba domin ta tabbatar da original din ne ko kuwa barawon sane. Amma laushinsa ya sa ta gane dan dubu dari da hamsin din ne.
Bata amsa mata gaisuwa ba sai ta bita da cewar, “saboda zaki zo gida yau kika yi wan nan kuren adakan saboda ki zo ki birge mu. Ta baki burge din ba”. Ta yi tsaki ta sake cewa “aikin banza ga riga ba mutum. Kayan ma sam basu hau jikin ki ba saboda rashin sabo. Sabon shiga arziki”.
Har ranta ya dan so ya baci, amma da ta tuna sanda ta san kayan yadda meena ta dinga koda kyan da su kayi a jikinta, sai taji komai ya yaye. Shi kuwa uban gayyar sai da ya sata ta yi posing ya dau hotonta saboda tsabar kyawun da ta yi.
Da kuma ta sake tuna kalaman umman AlBashir da tan kace matar dan uwana mai kyau da kyawun hali. Saboda duk jin kunya na Zainab, matar nan taki surukanta da ita. Jan ta ta ke yi a jiki kamar yadda zata ja sauran ‘ya’yanta a jiki.
Muryar Dadi ce, ta katse mata tunanin da ta ke da tsaka da yi, wanda ya tarbe ta da murna yana fadin “a’a yau Zainab ce a gidan”?
Da sauri ta mike ta nufi inda yake a tsaye, ta durkusa dai dai kafafunsa tace “Dadi barka da war haka”.
“Barka kadai Zainabu” ya amsa mata cike da sakin fuska, wan da ba ta jin ta taba ganinsa ya yi mata Magana cikin fara’a irin ta yau. Amma idan bata manta ba babu wata mua’amla da ke hada su illa a kai karararta ya kira yayi mata fada.
Amma yau irin fara’ar da ya tarbe ta da ita ta faranta mata nata ran matuka.
Kujera ya samu ya zauna kusa da inda take tsugunne a gefensa. “yaushe kuka dawo ne”?
“Jiya Dadi”?
“Kai madalla. Allah yasa an samo hajj mabaruk”.
“Amin Dadi. Na shiga wajen Anti Bilki ta na gai she ku da kyau”.
“kai madalla muna amsawa”.
Dai dai nan Momi ta kasa daurewa ta mike tare da buga wani uban tsaki ta yi shigewarta daki. Allah sarki Zainab, bata san dadi ya iya hira ba sai wan nan ranar. Shi yake mata tambayoyi tana bashi amsa yana kuma hadawa da comment. Zan cen nasu duk ya danganci wuraren da ta ziyarta. Inda kuma shi yayi ta encouraging dinta tana bashi labari.
Ko ba a gaya maka zaka fahimce cewar yayi matukar farin cikin da yanayin ‘yar tasa. Sun kai kusan awa dawa suna hira, san nan shi da kansa yace “tashi ki koma gida kin san ba a son magariba ta ringa samun mutum musamman mace a waje”.
Da kansa ya shiga dakinsa yayi dubi dubi ya rasa mai zai bata, sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya damko kudi wanda bai san yawansu ba ya mika mata yace “ungo karbi ki sayi wani abu ki shiga gidan naku da shi”.
Saboda murna ba ta san sanda hawayen dadi ya zubo mata ba. Wai ita Zainab Dadi yake mikawa kudi da hannunsa ba tare da ta tambaya ba. Ta sa hannun biyu ta karba cike da murna.
Halim da hanif da suka raka ta mota su ta bawa tsarabar akwati biyu suka shigo da ita gidan. Bata bawa Mallam tsaraba ba sai dai ta tambayi kwatancen gidansa ya yi mata. Mallam Yunusa ya ce ya gane wajen. Nan suka rabu da alkawarin za ta kai musu ziyara.
Daga nan kuwa bata yi birki a ko ina ba sai gidan aminiyarta watau Fatu. An sha murna da tsalle na jin dadi. Mama Hajjo sai dariya take yi musu. Da kyar ta samu ta sake ta suka gaisa da maman.
A nan taci tuwon dare saboda magariba a nan ta same ta. Ita kanta sai kallon mamaki take binta da shi na ganin yadda ta canza ‘yan kwanakin kadan da basu hadu ba. Ba ta boye musu ba ta nuna damuwa da yadda taga gidansu duka ya kazance.
Mama Hajjo da Fatu suka kalli juna suka tuntsire da dariya. Maman tace “ya kuwa ba zaki ga gida ya koma haka ba. Injin shara da wanke wanke da kuma goge bata nan. Ai watan tonon asirin Momin ku ya kama. A dan wata biyu nan tayi masu aiki sun kai ashirin. An dakko nufawa, an dau kabilun kaduna, ke har an dawo ana daukar na madobi.
Kowa yazo ya zauna kwana biyu sai su gudu akan ba za su iya ba. Me kawo mata ‘yan aiki ta ce ta gaji da debo ;’ya’yan mutane tana kawowa ana wulakanta su. Ita Sakina ai Allah ne ya cece ta. Wata gansamemeiyar banufiya ta tashi yiwa rashin mutuncin data saba. Tana marinta, ita kuwa ta kai mata naushi. Allah ya taimaka ba ta samu idonta ba. Sai da tayi sati kusan biyu tana jinyar raunin da tayi mata”.
Da mamaki tace “amma ita da take zuwa lokaci lokaci me zai hada ta fada da masu aiki, duk da dai nasan tana zuwa sosai”.
Fatu ce tace “au baki da labari. Wan nan sokon mijin nata ta kama da mai aikinta a dakinta. Ta kama yarinyar da duka, ta turo ta waje tsirara, shi kuwa ya fizge zaninta ya lullube mai aikin da shi. Ya kuma rattaba mata saki uku a lokaci daya. Sai a makota aka bata aron zani ta daura.
Tana isowa gida ya biyota da yaranta ya tattara ya nemi transfer ya bar garin”.
Cike da mamamki tace “ba sai ta kaiwa ‘yan uwansa yaran ba”?
“ta ina zata kai su bayan ba saninsu tayi ba. Sai da wan nan abun ya faru ashe ba su yi bincike a kan asalinsa ba. Suna gani dan canji a tare da shi suka bashi ‘ya. Waliyyin ma ashe limamin masallacin ofis din su ne. sai da gumu ta gumu aka gano cewa ashe Ibira ne. Yanzu haka bata san inda yake ba”.
“Allah ya kyauta”.
“Amin. Ai ke ta so da irin wan nan auren sai kuma Allah ya kare ki komai ya koma kanta”.
Kiran sallar isha ya tashe su daga hirar. Tana idarwa kuwa, ta tarar da miss call sun kai goma na habibiy kamar yadda tayi saving number sa a wayarta. Tana kokarin kiransa taji wayar Fatu ta dau kara. Fatun na ganin shine ta danna speaker, tare da yin sallama.
Sai da ya amsa san nan yace “saboda Allah Fatu kin yi min adalci ke nan. Da rana da ruwa da iska duk suka kare a kaina, a kasuwar gwanjo da kuma turin mashin, amma matata tazo ki tsare min ita ki hana ta dawo wa gida”.
“Ni na isa in tsayar da matar bala Mai gwanjo. Wai yawo na raka ta gidan sauran kawayenmu su gaisa”.
“Don Allah kiyi min rai. Matar tawa kika dauka zuwa yawo. Kice yau duk tsoffin samarinta sun gama kalle min ita”.
“Ai sai dai suyi kallon amma ka sha gabansu. Ka tuna fa suma akayi saboda an dauka an rasa ka”.
“Kuma fa da wan nan da wanan. Amma yanzu taimaka ki fito min da ita. A gajiye na dawo gida, amma rashin ganinta ya sa na kasa zama a gidan na biyo sawu”.
“ai kuwa komawa zaka yi don sai ta kwana biyu zata dawo”.
“ba matsala, ai dakin Baana ya na nan sai mu zauna a ciki”.
Dariya suka tuntsere da ita dukkan su biyu. Fatu ce tayi masa iso ya shigo ya gaida Mama Hajjo. Da ya tashi fita kuwa ya ajiye mata dunkulen dubu dari a wajen. Ita kuma ta sakko da akwatin tsarabar su daga mota ta mika mata.
Tun da Fatu ta rako su soron gidan yake makale da ita a hannunsa kamar zata gudu. A motarsa range Rover suka shiga domin komawa gida, shi kuma driver ya wuce da motar da ta zo da ita.
Washe gari ma kuwa ta kaiwa Baba Laure ziyara a gidan da suka koma. Ta yaba kwarai da girman gidan, saboda bangare guda suka zuba kiwon kaji wajen dari biyar ga kuma wani kango da suka zuba tunaki a ciki. San nan ga wani sashe inda ‘ya’yan mallam maza guda biyu suka dawo da zama. Kowa da sashensa mai dauke da dakuna uku da falo da kici da bandaki biyu.
Dama su ke nan yaransa maza.
Nan ma dai ta dada jinjina samun tabarbarewar da gidan nasu ya dada yi. Nan baba Lauren ta sanar da ita sak abin da Mama Hajjo da Fatu suka gaya mata jiya. Ta kuma shaida mata cewar, sana’a ta tsaya cik. Tun tana karbowa ta jagwalgwala ta kasa yi har abin ya soma zama rigima da customers ta hakura. Baba laure ta ci gaba da fadin “ai ni ta so ta jibgawa wan na wahalar, ni kuwa Alhaji Yana bawa Mallam kyautar gidan nan na tattara na gudo. Ba irin masifar da bata yi ba ni kuwa na kekesa kasa na ki komawa.
Ai ko shi mallam saboda Dadi yake zaune. Kin san yanzu lafiya ta yi masa karanci”.
A dan firgice ta tamabayeta abin da ya samu Dadin. Ta amsa mata da cewa ciwon suga ne ke damunsa. Sai da ta gaya mata san nan ta tuna da ramar da taga ya dan yi.
Ita ma dai nan ta bar mata tata tsarabar ta dawo gida.
[8/9, 13:59] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 31
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Zainab dai ta zama ‘yar gata gaba da baya. Ba wurin miji ba, ba wurin yayyensa ba. Ga kuma dangin ta na wajen uwa da uba wadan da suka mai da ita kamr kwai domin laillaya. Ita kuwa Umman su Al Bashir yadda take ji da autanta haka take ji da matar sa.
Kuma hausawa kance halin mutum jarinsa. Ko baki ta samu labarin Umman tayi gaisuwa ce kawai zata hada ta dasu. Tana fita kuwa ta shiga kitchen dinta ko na Umma sai dai kaga masu aiki na shigo da kabakan abinci kamar dama an san da zuwansu.
Haka wata rana umman ta dan hadu da tsautsayi. Accidenta tayi amma bata ji ciwo sosai ba. Ta dai dan kukkuje. Kun san mutan garinmu da zurfin tunani da kuma son zumunci haka suka ciko bus biyu manya. Daya cike da mata sama da goma daya kuma maza.
Babu kuma wanda ya san da zuwansu. Duk iya kokarin mutum ba zai iya wadata mutum sama da ashirin da abincin da bai san da zuwansu ba. Ita dai tana ganinsu ta zare jikinta ta koma gida. Industrial kitchen dinta ta shiga. Allah yasa tana da ajiyayyun snacks wanda tayi wa yaya A’I ba ta zo ta dauka ba.
Shi aka fara soyawa aka gabarta musu da ruwan lemon kanakana. Ko ba komai ta san zai iya rike su kafin dai awa daya ta gama abinci. Kafin awar nan kuwa ta cika, ita da masu aikinta guda biyu sun sauke tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa wacce ta sha naman rago.
Gefe guda kuma ga ferfesun kayan ciki da aka hada da shi. Ba su gama ba sai gata ta shigo da katon tray dauke da yankakkun kayan itatuwa. Nan ta zauna aka fara gaisawa. Caraf kuwa facalar Umman matar wan Abbansu ke nan mai suna baba kulu ta ce “hm sannu isasshiyya sai yanzu kika ga damar zuwa gai da mutane”?
To dama kowa ya san ta da neman Magana da kuma sa ido. Umman ma sai da suka kwashi adashin tsiya taga ba abin da zata dauka a wajenta san nan ta samu lafiya.
Ita dai ba tayi magana ba ta sunkuyar da kanta kawai. Bata hakura ba ta sake cewa da umman “dama haka surukar taki bata san darajar mutane ba aka ishe mu da matar auta mai hankali. Ina hanakalin yake iyayen mijinki suzo sama da awa biyu amma ki kasa shiga ki gaishe su”.
Ta sake juyawa ta kalli Zainab ta ci gaba da cewa “ki bar ganin daga kauye muka zo, mune dai asalinsa”. Ita Zainab tun da tazo gidan ba wanda ya taba yi mata ko da kallon banza balle a kai ga fada. Rabonta da jin fada tun a gidan momi, sai kuma yau da wan nan azababbiyar baba Kulun ta dasa nata.
Umman Al Bashir na kai kallonta wajen Zainab taga yadda take share hawaye. Mikewa tayi daga inda take zaune ta karasa wajenta. Ba ta ji kunyar kowa ba ta jawo ta jikinta tana goge mata hawaye tana fadin “yi shiru matar auta. Kar ki bari wani abu ya bata ranki har dan uwana ya shigo ya tarar da ke a yanayi na bacin rai. Kin san ko yaya ranki ya baci shi ma kasa sukuni yake”.
San nan ta maida hankalinta wajen baba kulun tace “kin san mutane kowa da irin tunaninsa. To ita Zainab nata tunanai na in taga baki sun iso ta yi iya iyawarta ta wadata su da abin da su ci su sha, kafin ta zauna luguden lebe. Ai kema dan kin koshi ne da kabakin data kawo miki shi yasa har kika samu damar aibata ta”.
“au Allah akan matar danki kike nema ki gayan min bakar Magana. In dai surukan zamani ne gaki ga su. Idan kin dawo kina kukan an janye miki da ke kika jawo wa kanki. Ko da yake naki ma sunan sa janyayye kamar yadda kika janye dan wata dole kema sai an janye naki”.
Dariya Umman tayi saboda ta gane abin da take son fada Kenan. Ta ce “ai ni kowa a dangi ya shaida tsakanin na da surukuta mutuntuwa ce da kyautatawa. Kuma yadda ta rike ni haka kuwa zan rike wacce aka kawo min”.
“aikin banza kamar ba mu san komai ba. Ba asiri kikayi musu ba ita da dan nata suke fifita ki sama da kowa”.
“kash yaya Kulu kin sha fadar maganar nan na kuma ce ki shirya in raka ki wajen malamin da yayi min aiki a akansu ko kema kya samu yayi miki”.
Wata ce a cikin matan dake zaune a wajen tace “Don Allah Hajiya kyaleta. Shi zaman duniya ai kowa da halinsa yake yinsa. A danbatta gaya min gidan da bakiyi fada da su ba. shi yayanmu ai don mai hakuri ne da kuma Dadan data hana shi sakinki shi yasa kike ganin kamar kin fi karfin kowa. Kin fi so yadda kike sa in sa da naki surukan itama ta dinga yi da tata”.
Ita dai Zainab jiki a sanyaye ta miki daga wajen ta koma sama wajen Meena.Wan nan kuma shine abu na farko da ya taba mata rai a gidan mijinta daga shi kuma bata sake haduwa da wani ba. Yadda suke son Al Bashir kusan itama haka suke nuna mata.
Amma fa gidan Dr Abdullahi Zubair ba haka abin yake ba. Saboda dai dadi ya gaji da kazantar da kuma kwaben abinci da ake yi a gidansa. Ashe itama Momin ko ta manta ne ko kuma dama can girkin da sauki oho. Amma ko ita da kanta tayi abinci ba dadi yake yi ba.
Baki kuwa ya daina gayyato su, saboda idan ya kawo su kunya yake ji. Gida kaca kaca ba gyara. Ransa bai kara baci ba, sai ranar da ya fito daga masallaci suna gaisawa da malamin islamiyyar su Zainab, yake masa godiyar abin arzikin da mijin Zainab ya aika masa. Shima yana murna ya ke ce masa “ai mallam zainab kam abin na ta akwai albarka a ciki. Kaga dai da uwar ta so taki auren saboda wata jita jita da taji amma yanzu ga shi nan Alhamdu Lillah komai nata yana tafiya daidai”.
Shi ma yasayyadin ya dora da fadin “biyayyar Zainab da kuma kwazonta ba zai tashi a banza ba”.
“kayya mallam Auwwalu. Allah dai ya shiga cikin lamarin. Amma Zainab ai na sha wuya da ita a gidan nan. Kullum sai an kawo min kararta, ga kuma dakikanci da ta dorawa kanta. Ba yadda ban yi da ita ba tayi karatu amma sam yarinyar nan taki”.
Da mamaki yasayyadi yace “ita Zainab din”?
“Ita kuwa wallahi. Sam bata son karatu ba kuma ta son taimakawa a gidan. Kullum tana dakin a kwance”.
Mallam Awwalun ne yace
“ai mu kuma abin mamaki kusan tun kafuwar makarantar nan ba mu taba samun daliba mai kwazo da hazaka da kuma ladabin ta ba”.
“Ahaf a makaranta take muku haka. Amam mu a gida ai wahalar ta muke sha. Kullum a cikin fada take da uwar goyonta. Ga bakin cikin kannenta da take yi. Allah dai ya sa ta samu mijin kwarai”
Yasayyadi ya dan yi tsai san nan yace “Alhaji kayi hakuri da wata Magana da zan sanar da kai. Ka san kannena dukkansu biyu kawayen ta ne. haka zalika mahaifiyata tana shiga wajen hajiya. Amma labarin da ke fitowa daga gidan ka akan zainab ba mai dadin ji bane. Ka san su al’amarin mata akwai daure kai a ciki. Amma zan sanar da kai abin da na lura baka sani ba.
Kaf aikin gidan ka har ma da sana’ar matarka Zainab ce mai yin su. Makaranta kuma ba kokari ne bata da shi ba. Amma hajiya da kanta, ta rantse sai ta lalata rayuwar Zainab saboda bakin cikin mahaifiyar ta da ta ke yi.
Zainab na iya diban kawan uku na kowanne sati bata samu zuwa makaranta ba. Ko tana hidimar gidan ka ko kuma ta kannen matarka, wacce har gidajen su ake turata taje tayi musu boyi boyi.
Ba aje makaranta ba ta yaya za a samu karatu ya tsaya. Ai rufar ka akayi. Abin da take yi wa Zainab shi ya hada su da mahaifiyata saboda tayi mata nasiha. Zani wan nan sai dai idan sauran ‘ya’yanka sun ga dama sun bata kwancen nasu. Shin ko ka san a gidan ka Alhaji, Zainab bata taba kwanciya a kan katifa ba. A kasa take kwana.
Zainab ai ta sha wahala. Kuma ni Wallahi da na san bada sanin ka abubuwan nan suke faruwa ba da na yi karambani sanar da kai, saboda zagi dai kam ka sha shi a unguwar nan a kan Zainab”.
Dr in ban da zufa ba abin da yake sharewa daga fuskarsa saboda bacin rai. Sai yanzu ya gano dalilin da ya sa tun da Zainab ta bar gidan komai ya daina tafiya daidai. Ashe dama ita ke aiwatar da komai. Shi yasa momi ta fito da dabarar yin kyauta idan kaci jarrabawa kawai, saboda ta san ta toshe duk wata hanya da zata sa Zainab ta samu wan nan kyautar.
Yasayyadi ne ya katse masa tunanin da fadin “kayi hakuri Alhaji na san azarbabi na ya zarce misali. Amma a musulunci an fi son idan kaga dan uwanka na aikata kuskure to ka yi kokarin sanar da shi ya gyara, ba ka tafi kana gulmar sa ba. Ni ma kuma nayi ta neman sanadin da zan gaya maka naka kuskuren amma na rasa. Kasan yadda muke da hakki a kan ‘ya’yan mu haka suma suna da hakkki a kanmu”.
“ba komai mallam Auwalu. Na gode da wan nan nasiha taka da kuma fahimtar dani da kuskure na da kayi. Na gode kwarai da gaske”. Ya fada yana mai mika masa hannu domin suyi sallama.
A fusace ya shiga gidan sa nan kuma ya tarar da momi ta ci kwalliya za ta kamu. Dama kuma ita aladarta tana tsananin son buki. Saboda dinner ko ta waye sai ka gan ta a garin kano. Akawi randa ta kasa samun katin halartar wata dinner saboda jarabar son zuwa saboda ta hadu da haddaun mata, satar katin tayi ta kai sabon gari aka buga mata irinsa.
A falo suka yi kicibis da shi tana fadin “dama kai nake jira ka shigo sauri nake yi fita zan yi”.
“ba inda zaki je azzaluma macuciya mayaudariya”.
“dr ni kake zagi? Ko dai ka sha wani abu ne”?
“ba abin da na sha ido na ne ya bude daga nannauyan bacci da kika sakani. Ashe yarinyar nan zaluntar ta kika dinga yi ban sani ba”.
“wai wacce yarinya kake magana akai ni ban ma gane me kake nufi ba”?
“maganar Zainabu nake yi. Ashe ke kika cuce ta kika hana ta makaranta ban sani ba. Ashe baiwa kika mai da ita a gidan ubanta./ ashe kas kantar da ita kikayi a gaban ‘yan uwanta data girma. Amma ba komai ai kinga yadda Allah ya mai da ita”.
“Oho sai yanzu na gano inda zamcen naka ya dosa. Kace dai yarinya ta auri mai kudi kaima zaka shiga ayi da kai. Shi yasa kake ta wan nan rara gefen. Yo kuma in ban da abinka kwantar da hanaklinka. Auren masu kudi ai yanzu aka fara shi a gidan nan. Farisa da zata auri dan senator ashe ita goya ta a baya zaka yi saboda nuna kauna da kuma soyay…….”
Bai san sanda ya wanke ta da wani zazzafan mari ba wanda tun da take ba a taba yi mata irinsa ba.
“Dr ni ka mara”?
“An mare ki din idan kina da abin yi ki zo kiyi”.
Har zata ci gab da zazzaga masa masifa, take sai tunanin ya shigar mata na cewar duk yadda akayi asirin karya tambaya data yi masa ya karye ke nan. Saboda malamin da yayi mata aikin ya tabbatar mata ba zai taba tantamar abin da ta gaya masa ko yayi shakku akan duk abin data fada.
Tuna haka yasa tayi shiru kar zancen ya dada kwabe mata. Amma fa wata irin tsanar Zainab ce ta dada shiga cikin ranta. Shi kuwa bai ma kula da yanayin da take ciki ba, ya fita da sauri ya shiga motarsa. Har ya sanya ribas zai fita sai kuma ya fito ya tambayi mallam ko ya san gidan Zainab.
Ya dai kwatanta masa. Kuma da yake ma ba boyayye bane mai gidan bai sha wahalar samun gidan ba. A baking gate suka yi kicibis da Al Bashir yana yiwa maigadi bayani wajen wacce yazo. Da hanzarinsa ya karasa wajensa. Har kasa cike da girmamawa ya tsugunna ya gaishe shi.
Shi da kansa ya wangale masa gate ya karaso ciki da motar sa. Tun daga harabar gidan ya san cewa Allah yayiwa Zainab sakayyar kuntatawar da sukayi mata shi da matarsa. Da kyar ya daurewa kwallar dake barazanar zubo masa.
Shi kuwa AlBashir kamar zai kwanta a kasa ya takashi saboda ladabin da ya ke a gabansa. Babban falonsa ya shiga da shi. Shi da kansa kuma ya bude fridge ya dauko ruwa da wani lemo na cucumber ya hada ya doro a jug. Ya kuma shiga kitchen da kansa ya debo danbun nama da kyar ma ya gano shi sai da shamsiya mai aikinta ta nuna masa inda yake.
Yana jiyewa ya tuna da wani dabinon ajwa da basa rabuwa da shi. Ya sake zabura ya dauko ya dire masa. A gefen kafarsa ya zauna aka sake sabuwar gaisuwa. Sai sa masa alabarka ya ke yi yana amshewa.
“dadi Bisimillah sha ruwa bari in kirawo zainab din”. Ya fada yana mai mikewa domin haurawa sama.
‘yar hutu kuwa tana zaune ta tsala ado da wani dan Karen leshi mai laushi da kuma tsadar gaske. Ita dai ta san sun yi sallama da shi akan zai fita sai kuma gashi ya shigo. Cak ya daga ta daga kishingidar da tayi ya mikar da ita tsaye.
“Putri yau idan na baki wani albishir wanne goror zaki bani”?
“sai da ta dan sumbance shi san nan tace “kai da ka mallakeni kuma ai komai nawa naka ne, sai dai in tayi maka salatin Annabi in yi tawassali da shi Allah ya yafe maka kura kuranka.
“Godiya nake Putri. Muje innuna miki albishir din”?
“Allah ya sa ba mota ka sake sayo min”?
“Wan nan yafi duka wani kyalkyalin duniya da kika sani daraja”.
Tare suka sauka saka. Hango Dadi da tayi ya sanya ta karasa sauka matattakalar benen da sauri cike da ihun “dadiiiii”.
Sai dariya yake ya na fadin “yi a hankali Zainabu”.
Sufa tayi a gabansa ta tsugunna tare da damke hannayensa duk biyu a cikin nata.
“Dadi da gaske kaine”?
Shi ma cike da dariyar murna ya fara tsokanarta yana fadin “ke kuma haka akeyi, saiki gudu sama ki bar mijinki da hidimar saukar baki”.
Shi ne yayi saurin cafewa lokacin da ya zauna a gefenta yana fadin “Dadi ba laifin ta bane. Ka san akwai bakon da ya zarce saukar matar gida sai ta maigidan kansa”.
Dariya suka saka dukkansu. Sai lokacin Zainab ta samu sukunin gaishe da mahaifin nata amma har a wan nan lokaci tana rike da hannunsa taki saki, kamar yace guduwa zai yi ya barta.
Al bashir ne ya mike tare da fadin “let me see if Umma is around”.
“da ka barta sai mu shiga”.
Bai bata amsa ba ya mike yace da Daddy yana zuwa. Yana fita ya mai da hankalinsa kan Zainab. Muryarsa kamar zai yi kuka yace “ashe har turanci kina ji yanzu”.
“gaskiya Dady ba laifi. Although it is not that fluent amma dai i can converse effectively”.
Cike da murna yace “da kyau Zainab. Ga kuwa turancin nan radau”. Sai kuma ya dada marairaice fuska, yace “zainab”. Ta dago ta kale shi ba tare da ta amsa ba saboda jin seriousness din dake muryarshi. Tana sauraron kalaman da zasu fito daga bakinsa sai kawai taji muryarsa tana cewa “Zainab rokon gafarar ki na zo nayi akan irin wulakantanciyyar rayuwar da na barki ki ka yi a gidana. Ni da kaina na nakasa ki saboda haukan kishin mahaifiyarki da ya rufe mini do, da kuma wan nan munafakar uwar taku da ta ringa ingiza ni ina zaluntarki”.
“Don Allah Daddi kar ka sake cewa in maka gafara. Bani da wata afuwa da zan maka illa kai ne ma zan dawwama neman yafiyarka ko na kuskure maka”.
“sam Zainab baki taba bata min ba. Tun da nake dake ko musu baki taba yi dani ba komai gaskiyarki. Nine dai na dinga take hakkuwanki da suka wajaba a kaina”.
“Don Allah Daddy kayi min afuwa ka daina maimaita Kalmar cuta da ka ke ganin kayi min. har abada bani da wani mahaifi sama da kai. Abubuwan da suka gifta na kuskure sun wuce har abada”.
“Kin san Allah ba da sanina na dinga yi miki abin da nayi ba. Wan nan uwar taku ita ta ringa ingiza ni. Kuma na miki alakwarin sai na dau mummunan mataki akanta”.
“Don Allah Daddy itama kayi mata afuwa. Duk duniya bani da ‘yan uwa da suka wauce su Farida. Tabbas kuma idan ka bata wa Momi zasu ji ba dadi. Ni kuma rashin jin nasu dadin zai saka ni nima inji ba dadi. Saboda haka afuwa ga kowa ita ta kamance mu”.
“Madalla na gode da fahimtar ki Zainab. Makaranta kika koma ne ko yaya”?
“A’a dadi ya Al Bashir ne yake koya min a gida. Nan kuwa ta takakrkare tana bashi labarin irin lesson din da take dauka a wajen maigidanta. Sun sake suna hira sai kawai jin sallama suka yi Al Bashir yaje ya tattago Abba da Umma domin su gaisa da mahaifin Zainab.
Da sauri ya mike ya isa ga Abban domin suyi musabiha. Bayan sun gaisa suka zauna. Ita ma umma ta rusunu har kasa ta gai da shi. Hakan kuwa ba karamin dadi yayi masa ba. Shi yaushe ya isa Rumaisa ta gai da bakinsa a ladabce? Ai kawai kallon contenporaries take yi musu.
Sai da suka gama gaisawa yace “kai kuma Albashir me yasa ka tattago su alhaji. Dama niyya ta daga nan ka kwatanta min gidansa in karasa mu gaisa”.
“Ai Dadi main house din is adjacent to nan gidan “in ji Zainab.
Umbola yayi musu da hannunsa yana fadin “kun ci gidanku daga ke har mijin naki. Kuma shine tun da na shigo ba zaku sanar da ni ba”.
Dariya kawai suka yi. Ganin sun ware da hira ya sanya umma mikewa ta koma gida yayin da Zainab ta shiga kitchen. Bayan ya raka umma ya dawo kuwa a nan kitchen din ya sameta. Run gomota yayi jikinsa yace “yaya surprise din nawa how much is it going to be worth”?
“hajj da Ummara”
“Na riga naje na sake zuwa”?
“sabuwar mota latest”.
“not interested”.
“a delicious meal”.
“not good enough”.
“to gaskiya ban san me zan baka ba” ta fada with disappointed look on her face.
“Ni zan fadi me nake so. I just want a memorable and wonderful time with you tonight”. Ya na mai dada rungomata jikinsa. Itama sai da ta dan yi masa peck a kuncin sa, san nan tace “ka samu ka gama. Amma yanzu barni in samu in hadawa su abba dinner. Don naga yadda suka yi relaxing suna hirar siyasa ban ga lokacin tashin su ba”.
Kamar kuwa yadda ta fada haka ce ta kasance. Ba su iya tashi ba sai da suka ji kiran sallar magariba. Dadi ya mike hade da yi musu sallama, akan daga masallaci zai wuce gida. Ba yadda basu yi ba ya dawo yayi dinner amma yaki. Al Bashir ya kalleta yace “implement plan ya Maryam”.
Nan kuwa aka shiga neman makullin motar dadi ba a ganshi ba. Ganin zasu rasa jam’I ya sa suka hakura. Ko da suka dawo kuwa ta shirya musu abinci a tsakiyar falon su uku. Da mijinta da surukin ta da kuma mahaifin ta.
An kuwa yi masa haka da sunan yaci abinci ita kuma zata ci gaba da duba makullin. Suna gamawa kuwa Al Bashir ya zaro key daga aljihunsa yana fadin “ashe Dadi kaga key din ni na saka a aljihuna na dauka nawa ne”.
Dariya Abba yasa yace ‘ya’yanka sun yi tricking dinka”.
“ai abba idan ba haka nayi masa ba zai zauna ba. Idan kuma yaki cin abincin gidan mu na san yau Zainab sai tayi kuka”.
“ja’iri kai kuma da kukan nata gwara ka bata ran naka baban ko”? in ji Dadi.
Yana sosa keya yace to ai dadi a hudubar da kuka yi min kunce a dinga kyautata yi musu. Kuma na dauka yin abin da zai hanasu kukan yana daga cikin kyautatawar”.
“Ai kaga wan nan dan naka ba zaka kashe shi a Magana ba. Shi yasa customers dinsa kance in dai ya tsara ka ba yadda zaka yi sai ka sai kaya a wajensa”. Shima Abban ya fada.
A nan dai har isha sai da yayi. San nan yayi musu sallama ya wuce. Ko da yaje gida kuwa bai tarar da momi ba tayi ficewarta gidan bikin da tayi niyya. Tun da dama a koshe yake dakinsa ya shiga ya kwanta. Mallam nema ya sanar da shi cewar ga kaya a bayan motarsa. Bayan ya shigo da su, yaga turarruka designer guda uku masu tsadar gaske da kuma variety package na shayin Tertly. Yana gani ya san aikin su Zainab ne.
Da kuwa ya buga yai mata godiya ita bama ta san da wan nan sakon ba. Mika masa wayar tayi.yana fara godiya kuwa ya katse shi da fadin “dady kayi hakuri ka barni in samu cikakken ladan kyautatawa iyayena.
Wan nan itace matsalar ka yi ta ingiza mutum just to destroy a relationship. Su kuma parties involve su zo daga baya su fahici juna su kuma yafewa juna because of strong bond da ke tsakaninsu, kai kuma ka kwana ciki da jin kunya ga kuma repercussion na ayyukan ka da kuma pay back da tabbasa sai ya zo maka.
[8/9, 14:01] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 32
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Bayan DR Abdullahi, ya samu ya daidaita da Zainab abu na gaba da Dadi ya yi shine sasantawa da mahaifansa. Suma kuwa ya taka har kauyen yaje ya basu hakuri na irin abubuwan da suka dinga faruwa. Ya dauka da ya ke ganinsu a ‘yan lokutan da yake lekasu komai kalau ya dauka sakon da yakan bawa Rumaisa ne ke isa wajensu, sai a ranar suka sanar da shi su kan ba don mijin tsohuwar matarsa Khadija ba to da sun dade da mutuwa da yunwa.
Tabbas sunje Hajji, amma ba kujerar da shi ya basu ba. Wadda abban su Hafsa ya bayar ce, wanda shi kuma bai taba raba hidimar da ya kan yiwa gidan mahaifan matarsa da kuma na aminin mahaifin nata ba.
Mallam Usman kuwa na zaune a falonsa yana lissafin cinikin kayan gonarsa, kanin Hafsa faruk ya shigo ya fada masa ana sallama a waje. Yayi mamaki kwarai ganin mai sallamar. Duk da bai san da wacce ya zo ba, amma ya yi masa tarba ta mutunci, an sauke shi da karramawar da duk wani bakon arziki ya cancanta.
Yanan sauraron yaji ta ina zai soma tashin hankali sai kuma ya ji sabanin haka. Hakuri ya dinga ba shi na yadda ya gudanar da al’amura tsakaninsu da farko. Shi ya nuna masa dama bai rike shi da komai ba. Bayan nan kuma ya dora da yi masa godiyar nauyinsa da ya taya shi dauka, saboda shi ya banzartar da shi.
Da kansa ya shiga cikin gida ya kira yaran suka gaisa. Shi kansa yaran da’arsu ta birge shi, sai fadi yake “yanzu duk wadan nan nakane”.
Ya sake nuna Hafsa yace “ita dai wan nan bata da maraba da Zainab. Ina ga kamar Khadija suka dauko”. A dakin Khadija kuwa sai da ya sha daga da ita kafin ta fito su gaisa da tsohon mijinta. Shima a dofane suka gaisa kamar mai daukar wuta.
Bayan yayi masa sallama ya tafi, Mallam Usman ya koma cikin gida yana ganin yadda Khadija ke cika tana batsewa ita ala dole an yi mata laifi. “Wai fushin na meye”? Ya tambayeta.
“Kawai tilastani da kawai zuwa gaida wan nan mutumin”.
“Dijangala tawa. Da kin san irin dauriyar da na yi kafin in barki zuwa wajensa da kin sara min. saboda Zainab kawai na barki kuka gaisa, saboda na san idan taji yazo baku gaisa ba, ba zata ji dadi ba. Amma in bani ba bakauye wake hada tsoffin masoya a guri guda”?
Da tsananin mamaki ta juya ta kalle shi tace “yanzu da wannan tsufan nawa har kake kishi”?
“ke kike ganin kin tsufa. Amma ni har yanzu a dan dasheshiyar yarinya nake ganin ki a gabana, na ga dai sakacina da ban saki kin daura nikab ba”.
Ita dariya ma abin ya bata. Tun daga wan nan lokaci kuwa zumunci ya kullu tsakaninsu. In dai zai shiga wajen iyayensa ya kan tsaya su gaisa, har kuma da tsarabar yara. Shi ma kuwa haka zai sa a loda masa kayan gona a motarsa.
Dadi kuma yanzu ya mai da ziyarar kauyensu kusan duk karshen sati, sai yanzu ya dade gane illar da Rumaisa ta yi masa. Bata barshi ya kyautatawa kowa ba sai ita da ‘yan uwanta da kuma ‘ya’yanta kawai. Tun da kuwa ya dawo kan turbar arziki zaman lafiya yayi kaura a tsakaninsu.
Ana ciki haka rashin lafiya ya sanya shi kwanciya a asibiti. Likita kuwa yayi bayani rashin cin abinci da kuma cin wanda ya dace da yanayin ciwonsa shi ya janyo masa wan nan larura. Zainab ta bashi kulawa matuka, saboda momi tafiya ma tayi wai tana da seminar. Nan kuwa karya take. Wata kawarta ce akayi wa mijin minister, shine suka tafi bikin taya su murna. Daga nan kuma ta tsaya hutuwa.
Ita kuwa Zainab tun da taji haka ta daukarwa kanta, aika masa da abinci ofis mai rai da lafiya. Haka zalika ta roki Malam da ya bar Baba Laure ta dawo saboda kula da abincin mahaifinta kawai. Ya yadda amma ban da aikin kwana. Za dai tazo karfe goma na safe tayi dan abin da zata iya, saboda ita dai mai girki ce kawai ba ruwanta da shara da goge. Hakan ya mai da gidan kazamin gida.
Da can saboda samun lafiyayyen abinci da kuma tsaftar muhalli kullum jama’un momi na gidan. Amma zuciyar gidan na tafiya sai suma suka daina zuwa. Haka zakaji gidan shiru kamar ba mutane a ciki. Shi Dadi baya shiga sabgarta kwata kwata, saboda jin haushin abubuwan da ta sanya shi yayi a baya.
Ita kuwa hakan bai wani damunta. Balle dake an canza mata boss din office dinta, sai fantamawa suke a dukiyar gwamnati. Bata neman komai a wajensa bata ga kuwa dalilin da zata bata lokaci yi masa biyayya ba.
Gaba daya dadi has lost control of his house.
Ana cikin haka tenure sa as Commisioner ta kare. Ga kuma ciwo da ya sa shi a gaba. Ciwo kuma mai dan Karen tsada. Don ma Zainab ta tsaya akan magani da kuma abincin da zai ci.
Yanzu auren zainab da albashir ya doshi kimanin wata takwas. Tana kuma da ciki dan wata biyu wanda daga ita har shi ba wanda ya san da shi. Kyau ne dai tayi shi har ta gaji. Ni kaina idan na ganta mamakin irin kyan da kullum ke karuwa a tare da ita nake.
Ga sana’ar da take yi ta catering services wanda bata hulda da kananan mutane sai manyan yara. Saboda fiye da rabin customers din nata daga sashin dangin mijinta ne. balance din account din ta kuwa sai hawa kawai yake amma baya sauka. Saboda ko da wutsiyar ido ta kalli abu da sunan ya burgeta to kuwa Albashir zai tabbatar ya zama rabonta.
Nauyin danginta kuwa wani lokacin sai dai idan sun zo godiya ta samu labarin alkhairin da mijinta ya aiwatar. Saboda haka sai ta mai da hankalinta kan tallafawa ‘yan uwanta masu karamin karfi. Amma inda kasan bata daukar ko kwabo haka balance din account dinta yake.
Monthly allowance dinta wanda ko goro da kudin kitso bata saya da shi 300k ne.
A kwai ranar da suka je saloon ita da Meena. Duk saurinta kar ya dawo bai same ta a gida ba sai da hakan ya gagara. Saboda shidai ita ke nan dokarsa. Duk inda zata ya amince mata, amma fa ta tabbatar ta riga shi dawowa.
Ya tsani ya shigo gidan nan bai yi tozali da ita ba. Amma ranar akwai mutane a saloon din hakan ya sa bata gama da wuri ba. Ta main house suka bi. A falon umma ta tarar da shi. Yana ganin su ya rufe Meena da fadan da ba ita ta cancanta ba. A dan fusace yace “ke meena ina kukaje tun azahar sai yanzu kusan magariba kuke dawowa gida”.
“uncle AL B salon muka je aka gyara mana gashi”.
“a salon din ne kuka dade. Duk wanke kai yana haura minti uku ne? kun dai tsaya hira kawai”.
Dariya Meenan ta saka tace “to ai gashin anti Zee shi yafi bada wahala saboda tsayinsa. Tana sama da awa daya acikin dryer bai bushe ba”.
Ita dai bata kula su ba saboda ta san fadan nata ne ganin Umma ya sa shi ya wayance da yiwa Meena fadan. Sai kawai ta sulale ta shiga kitchen din Umman. Nan kuwa ta tsaya ta hada musu dinner. Bata shiga gida ba sai bayan isha.
Ta riga da tayi wayon da duk randa ta san ta yi masa laifi to kuwa ranar kwalliyar ta, ta daban ce. Haka zalika kwarkwasa da tarairaiyar da za ayi masa daban ce. Kwalliya ta rangada da kananan kaya, wanda suka dada fito da tsarin halittar ta.
Tana jin alamun yana kokarin shigowa tayi saurin sakkowa daga sama. Da ya kalleta sai da ya kusan shidewa. Sai kuma ya tuna ya kamata ya dan nuna fushinsa, sai ya dan dake. Murmushi kawai ta yi saboda both the first and the second reaction ta gansu.
“sannu da shigowa” kawai tace da shi. Shi ma a dan dake ya amsa da yawwa. San nan ya nemi kujera a falon ya zauna. Kitchen ta shiga saboda ta lura kamar bai ci abincin sosai ba, ga kuma dare bata son ta bashi abinci mai nauyi. Saboda haka pepper soup na ragon ruwa ta shigo da shi cikin bowl.
Center table ta jawo ta dora akai. A kan kafarsa ta zauna, sai da ta marabce shi da kyau na kusan minti uku san nan ta janye bakinta daga nasa. Ajiyar zuciya ya saki yace “kawai don kin san bana iya fushi dake shi yasa kike min abin da kiga dama”.
“Allah ya huci zuciyar ya Bala na. da iznin Allah ba za a sake maka wan nan laifin ba”.
“ke don baki san yadda nake ji bane idan na tura kofar gidan nan ban ganki kin zo tarba ta ba. Sai in ga gidan ya yi min baki”.
“in dai haka ne daga wan nan an daina zuwa salon dinma tun da ran yaya na baci yake. Ko kuma ayi wa kan kwas kwas saboda yana neman shiga tsakani na da rabin raina”.
Sai da ya saki murmushin mai nuna alamun fushi dai kam ta sauke shi, san nan ya kai hannunsa ya dada shafo gashin yana fadin “a bar min abina, saboda kallonsa yana sakani annashuwa. Idan na shafa shi kuwa har cikin zuciyarta nake samun natsuwa. Amma dai ki taimaka min in daina shigowa gida ban same ki ba”.
“in Sha Allahu an wuce wajen”.
“yawwa Putri na. yanzu me kika kawo min”?
Bata bashi amsa ba, sai dai spoon feeding din shi data shiga yi. Bayan ya gama ta dakko gwanda data yanyanka kanana tana bashi.
Washegari kuwa ta sakko ta tarar ana gyaran dan wani daki a gefen dakin masu aikinta wanda dama dakuna biyu ne. ita dai bata san me ake yi ba. Ta dai ga plumber da electrician suna aiki. Akaja ruwa aka sa Ac aka fenta dakin.
A week later cargo ya iso gidan, sai kawai gani tayi ana installing su hair dryer da su steamer kayan pedicure da dai sauran kayan da akan samu a hadadden salon. Ana gamawa ya leka yace Putri ga salon nan bana son kina sharing items da wasu”.
Sai ya zamana har su yaya Ai nan suke zuwa su da yaransu. Every weekend zasu daukko mai salon da suke zuwa ta yini a gidan sai ta gama da su dukkansu.
Bayan wan nan ya nemar mata online karatu a university ta Madina. Zata dinga daukar karatun ta online sai kuma karshen kowacce semester ta je ta rubuta exams ta dawo. An gama da wan nan sai ga su farida sun zo hutu, wanda ita farisa ma ta gama. Ita Faridan ce, ke da sauran shekara daya.
Tana dira kuwa washegari a gidan yayarta ta wuni. Tayi murna matuka da yanayin da ta samu ‘yar uwar tata a ciki. Sabanin Farisa da ke kallon komai a wulakance kamar ta ga kashi. Suna cikin hira ta ce “anya yaya Zee ba komai a tare da ke kuwa”?
Tareda mamaki tace “ban gane ba komai a tare da ni ba. me kika gani”?
“eh to ni dai to me you look pregnant. When was the last time ya had your period”?
Ta daga kai sama tayi shiru alamar tunani.
“kar dai kice min you cant remember”?
“gaskiya na manta. Ko two ko three months back”?
Cikin dariyar tsokana tace “gaskiya you are having good times da yayan nawa. Tun da har lissafi ya bata”.
Dukan wasa ta kai mata tace kin rainani”.
Da ya dawo kuwa ba tare da ta sanar da shi suspicion din kanwarta ba ta sa shi ya kaita asibiti nan kuwa labari mai dadi ya same su. Sai kuma ya nuna da dai ta hakura da karatun tun da ga wan nan ya gifta.
Rigima har gaban Umma, inda ta sasanta su da fadin yayi hakuri idan anga tana shan wahala sai ta tsaya da karatun. Haka ta soma daukar lectures dinta on line, in da zata samu degree a Islamic philosophy. Wanda kuma saboda zurfin karatun data samu a sanawiyyar da tayi, shekara biyu kawai zata dauka ta hattama karatun nata.
Farisa dai ta samo Salim ahmadu Salim. Babban yaro dan gidan senator Ahmad salim mai shunku. Ba shine babba ba. Amma shine babba a wajen amaryar da shi senator yafi so. Matarsa ta fari ‘ya’yanta takwas duk mata ne saboda haka Sharifa na zuwa ta fara da haihuwar maza, wanda sai da ta haifi hudu cif sai ta karbe gida.
Ita kuwa hajiya Bilki tuni ya mayarda ita bola ita da ‘ya’yanta. Ba ruwan sa da su. Dan teaching din da take yi shi ke rike da ita. Ita dai tana zaune a bangare guda na gidansa. Ita ba matar aure ba ita kuma ba sakakkiya ba. Sashen nata ma idan ka gani zaka dauka na masu aiki ne. ta rungumi kaddararrta ta barshi da halinsa shi da matarsa.
Tun da Salim ya tashi dan gata ne lamba daya irin gatan nan mai illah. He is very arrogant. Ba wanda ya isa ya sashi ba wanda ya isa ya hana shi. Ita kan ta Farisa Allah ne yayi wan nan auren nasu. Yayi yawon karatu kasashe kafin daga karshe ya hakura da zama a Sudan saboda ya taba dukan wata budurwa har ya kusan kasheta aka yi masa denying visa into Europe gaba daya.
Asia kuma an kama shi da drugs a Thailand da kyar baban ya fito da shi suma suka bata passport din shi. Da kyar aka samu ya tafi Sudan din, inda kuma a nan suka hadu da Farisa. Suma relationship din nasu kamar ba zai kai labari ba. Saboda haka zasu kwashi adashin tsiya ya kamata ya lakada mata duka. Ayi baram baram. Amma kwana biyu sai kuma ka gansu sun dinke kamar ba su ba.
Tarbiya dai kam babu ita a tare da shi. Abin da duk yake so shi yake yi saboda uwar da uban sun jika shi fiye da zaton mai karatu. Basa taba ganin laifinsa. A Thailanda da aka kama shi da cocaine, Allah ya sa bata kai commercial quantity ba, amma duk da haka uban ya kashe sama da dala dubu hamsin kafin ya samu aka sako shi.
To wan nan shine mijin da Farisa ta samu. Ita kuwa Farida ba wanda ya taba zuwa da sunan ya gan ta yana so, ko da samarin makaranta. Har aka sa rana Zainab bata da masaniya, balle da ke dadi ya ce ba ruwansa duk abin da ya faru Momi ita zatayi kuka da kanta.
Bincike kawai ya nuna yana son yi akan yaron ta harzuka tana gaya masa maganganu har tana cewa bakin ciki yakewa ‘yarta saboda baya son kowa ya kamo Zainab, tun da yanzu itace a gaban goshinsa. Saboda haka a kyale mata yarinyarta itama ta auri mai arziki.
Hakan kuwa akayi. Nan kuwa ta fantsama shirin biki. Da aka tashi aka basu wani makeken gida sai da kuwa ta cika falika uku da dakuna shida da kaya. Kaya kuwa na alfarma. Ga kuma hidimar biki da aka tsunduma.
Zainab tayi wa Abbanta waya yake sanar da ita zancen auren kanwarta. Taje gidan da niyyar taji me ake ciki, Momi ta zazzage ta ta koreta tana fadin bata son ganinta a harkar bikin ‘yarta. Har tana fadin “in don ganin wan nan dan kudin na mijinki ne ya sa kikewa mutane gani gani. Jira kiga inda ake harkar arziki. Shi iyayensa ban da kudi har mulki suna da shi”.
Batayi la’akri da cewar shi kudin mahaifin sa bane, sabanin Albashir da yake da halastacciyar dukiya ta halal.
[8/9, 14:16] +234 814 948 5104: FINI A UBA👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 33
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Duk abin da ake yi na shirin biki, Zainab bata da masaniya. Shi kansa dadi bai san komai ba. Ya dai san ranar daurin aure da kuma wanda zata aura. Amma ban da haka bai san duk wani shiri da ake ciki ba.
Tayi niyyar gudonmowa Momi ta nuna bata da ra’ayi bata son komai nata. Duk da haka ta bawa mahaifinta kudi naira miliyan biyu da sunan ya rage hidima. Yaya A’I ce, ta kawo katin gayyatar na bikin Salim da kuma Farisa wanda dinner ce ta gidan maza. Tare suka yi makaranta da mahaifiyar yaron, amma sanin yadda take gudanar da lamuranta ya sanya bata mua’mala da ita.
Amma ganin sune manyan garin ya sanya uwar angon nacewa sai ta gayyace ta, saboda duk uwar darin ce ita da uwar amaryar. Professional class strugglers ne. ana fito da kati, Zainab taga sunan kanwarta ajiki. Ita kuwa yaya A’I tana mitar ba zuwa zatayi ba, saboda bata son halin mamin Salim.
Umma ce tace “Maama baki da kirki yarinyar nan tana sonki tun kuna yara amma ke kin kita”.
“Umman ba son ta ne bana yi ba. Gaskiya ba zan iya hulda da ita ba. Kina ga yadda son abin duniya ya zarme mata tayi destroying gidan mijinta gabadaya. Kwata kwata ya daina kula uwar ‘ya’yansa sai ita da yaranta kawai. Ba yadda za ayi ki ga sauran yaran ki dauka wai uban su daya da su Salim. Su kullum suna yawon kasar waje amma ita kuwa tana faman yadda zata biya kudin karatun yaranta anan Nigeria.
Amma ba komai kanta ta yiwa. Gata dai nata sun samu amma tarbiyya ita kuma waccan din nata sun yi zarra. Ta dai samu duniyar, amma ni tausayin yariyar da zata auri salim din nake. Yaron kwata kwata ba shi da dadi”.
Zainab ce tace “maama kin san su da kyau ne”?
“Tun secondary muke tare da ita”.
Sai da tayi ajiyar zuciya san nan tace “Maama kanwata zai aura”.
Cike da mamaki suka maida kallonsu gareta. Umman ce tace “yanzu ke da gidanku bikin a gidanku kuma jibi za a fara amma baki sanar da mu ba”.
“umma kiyi hakuri nima ban san an kusa bikin ba. Farida dai ta sanar da ni an kusa auren amma ban san komai ake ciki ba”.
“Allah ya kyauta” inji Umma. San na ta juya wajen Yaya A’I tace zaki iya samo mata katin zuwa saboda bai kamata ace bata je ba”.
“ai ko kati dari na nema zan samu, saboda hadaddun mata take so a wajen bikin”. Take kuwa ta buga mata waya akan tana bukatar more cards for her family. Tana nan gidan kuwa sai ga driver ya zo ya kawo mata about twenty cards, amma fa dangi an hana su saboda ‘yan gayu ake so a bikin.
Umman kuma ta sanya ta ta aikawa har mamanta da kanwarta da kuma wasu friends dinta. Gayya dai suka saka tayi sosai. Bayn nan Yaya A’I ta nemi wata kawarta dake Lagos, tace mata hadaddaiyar souvenier take so kuma nan da two days take sonta. Ta aika mata details din amarya da ango da kuma sunan presenter.
Ranar Thursday za a gabatar da dinner ta gidan maza, saboda haka Zainab da tawagar ta, ta kusan mutum ashirin ta isa venue din. Da gani kasan bikin na manya ne. kuma ita dai yaya A’in ta bawa MC sunan Zainab. Har announcing arrival dinta akayi. Su kuma su ka biyo ta cikin rausaya na kidan da mc ya saka musu.
Ga kwalliyarta tadaukar hankali, kamar itace amaryar don kuwa tama fi amaryar kyau, saboda ita farisa iyayi yayiwa a kwalliyar tata yawa sai taki yin kyau. Da kyar momi ta danni zuciyarta saboda bakin cikin yadda taga Zainab tayi stealing show din bikin.
Ga kuma VIP seat da aka ware musu ita da jama’arta. San nan ga kuma dinbin souvenier mai dan Karen tsada da kyau data raba. Wani set ne na kayan wanka da ya kunshi bath robe da towel na fuska da na jiki da kuma nakai an nade su da kyau aka saka acikin wata jaka mai daukar hankali.
Duk kuwa wanda yazo fita daga gidan bikin nan sai da aka mika masa tsarabar nan. Biki dai yayi biki. Mata kuma an sha shagali. Saboda tsabar duniyanci, uwar amarya da ango suka taka rawa tare. Ga barin kudi da aka dinga yi kamar ba gobe. Su dai Zainab da convoy dinta da suka yi gracing occasion sukayi sallam suka tafi.
Washe gari ma ranar wuni umma ta sake tilasta ta akan sai taje. Tunda ta ga take taken Momi taje ta gyara dakin boysquaters inda baba Laure ta tashi. Nan ta shirya ajiye dangin mijinta. Kafin ta taho kuwa, sai da ta bada sallahun yaran da suke kamata aikin catering dinta suka hada mata variety na abinci mai yawa, saboda har da mutan kera tayi saboda suma ta san ba lalle Momi ta mutunta su ba.
To cikin hukuncin ubangiji abinci nata shi ya rufawa Momi asiri saboda wadanda taba wa aikin nata abincin sun yi disappointing dinta. Amma kusan ba laifin su bane ita ta bada dokar kar a kawo mata abinci da wuri saboda ta fi son sai mutan kauye da kuma locals sun tafi san nan ta fito da better for her special guest.
Hakan kuwa akayi. Su kuwa dangi Zainab ta ciyar da su, sanna ta bawa kowa kyautar atamfa irin ta kamfanin mijinta, san nan tayi oder hummer masu kyau domin su mai da ‘yan uwanta gida.
Sai goshin magariba kuwa aka dinga shigo da variety, amma Momi tayi rashin sa’a saboda da yawa daga mutanen da take expecting basu samu zuwa ba, saboda a ranar kuma bikin ya hade da na wata ‘yar perm sec. Saboda haka can akayiwa rubdugu. Kunsan harkar bariki ko zumunci is for the highest bidder.
Nan dai taro ya waste ya barta da tulin abinci da sai dai a zubar ko a bawa alamajirai. Washegari kuwa dinner Momi ce itama kuma an kashe mata makudan kudi. Ga guri yayi kyau. Ga abincin an hada shi kamar ba gobe. Amma fa amarya da uwarta basu zoba sai bayan tara na dare.
Albashir dai da ya kawo Zainab ya tokare jikin kofar da take zaune ya hana ta fitowa. Fatu tana tsaye tana musu dariya na wan nan kankagewa da yake mata. Shi kuwa fadi yake yi “mh mh barni Fatu. Kinajin sanyin da ake a garin nan in barta ta fito wan nan filin. Ina ba zan iya ba”.
Bayan dai dogon zama da aka bar mutane suan jira, sai ga Momi ta shigo cikin rakiyar kawayenta ta sun sha kwalliya sun gaji, sai ya zamana kamar ma sune amaren. Da rawa suka shiga, amma basu fi minti biyar da fara rakashewaba, sai ga wata iska ta taso.
Kafin minti biyar wuri ya harzuke. Decoration sai fadowa kan mata yake. Ban Ankara ba sai na hango gwaggwarayen kan mata yana tashi a fili. Wuta ta dauke. Bakajin komai sai hayaniya. Du iskar nan bata fi minti hudu ba, amma ta’adin da ta yi saika dauka ‘yan daba ne suka kai farmaki filin. Abinci cike da chaffing dishes duk ya bude da kura.
Shi dai Albashir ya maida kofar motarsa ya rufe ya sa su Fatu suka shiga domin ya ajiye su a gida. Tun da suka dau hanya yake tintsira dariya. Har Zainab ta gaji ta ce “wai dariyar me ka keyi ne kai kadai”?
Sai da ya sake sakin wata dariyar yace “dariyar hadaddadiyar dinner da ban taba halarta irinta ba nake. Fatu baki hango Momi ba kafin a dauke wuta ta dafe dankwali tana kukan na ganin yadda akayi fata fata da hidimar da ta hada”.
Dukan wasa ta kai mishi. San nan tace “Momin tawa kake wa dariyar mugunta”?
“ni na isa in yiwa surukata dariya, murna kawai nake taya ta. Ni na isa in yiwa Momi dariya. Ai tana da value a wajena sosai. Ki tuna fa har mai gwanjo na zama saboda kawai in bi dokar ta ai kuwa kinga ina mutunta ko”? ya fadi tare da sakin wata dariyar.
Haka bayan ya sauke su fatu nan ma ya daddage wajen bawa Umma labarin crises da ya faru a gidan party. Yana dariya kuwa har da sukewa ita ma Umman na taya shi.
“kai Umman har da ke a tsokanar Momi”.
Cikin dariya tace “yi hakuri matar dan uwana. Ai duk wanda yace tukunyar dan uwansa ba zata tafasa ba, Allah ba zai sa, tasa tayi ko dumi ba. Ta dauka haka zata share kalau. Ai da saura ma”.
A can kuma cikin motar amarya da ango, masifa yake zuba mata kamar zai daketa a wajen yan fadin data fito da wuri bata tsaya bata lokaci ba ai da duk haka bata faru ba. Ita dai Farisa kukan abu biyu take. Ga na bakin ciki biki ya baci ga kuma na bakin cikin masifar da Salim yake mata.
Ya ma mai da ita gida a kawo ta washegari kamar yadda aka tsara, yace in har bata bishi sun wuce ba a lokacin to kuwa sai dai auren ya rabu. Haka ta hakura ya wuce da ita gidan sa yana duddura mata ashar kamar ba sabuwar amarya ba.
Washegari kuwa Abban su Albashir ya aiko da sakon kayan gara komai goma goma gidan su Zainab. Suma dai wan nan din ne ya rufa mata asiri, saboda duk abin data karba ta narkar da shi a ganin ta yi haddaden biki, har kuwa da kudin garar. Tayi haka da tunanin zata samu gudummowa saboda haka sai tayi almubazzaranci da kudin hannunta. Liki ma kawai ranar dinner gidan maza ta lika sama da 300k.
Washe gari kuwa da za akai garar nan bata da ko dubu dari a tare da ita. Tana cikin wan nan tashin hankali ne sai ga sakon surukin Zainab ya iso.
Momi ce ta sa Farida ta sanar da Zainab labarin wan nan sakon sai dai kuma babu kayan dangin ango. Tayi maula by stle. Da kuma an kawo tace bata so. Zainab bata yi fushi ba ta je ta sayo super goma Holland goma da shadda getzner guda goma.
Albashir ne ya debo wasu shaddoji presidenta da ya sayo wa kansa suma goma yamika yace “gashi nan ba dan halinta ba kar azo ana yi wa 'yarta gori”.
“kai Ya Al B. ni Kenan gori ka ke min na rashin zuwa da gara”?
Sai da ya jawo ta jikinsa san nan yace “ai ni dake Putri bamu yi auren don abin duniya ba. Baki aure ni don kudi ba haka nima banyi neman aurenki da kudi ba. Soyayyace zalla da mutunta juna a tsakaninmu. Kuma ke baki san irinki, idan ma da bashi a kanta aka kawo wa miji da gudu zai karba, ya kuwa dage kodago don ya fanso ki. Don a lokacin dana ke nemanki ko faskare akace in yi saboda ke zan yi shi, balle sai da gwanjo mai sauki”.
“To naji ya Bala mai gwanjo dan bani excuse inje kai garar nan”.
Dada narkewa yayi a jikinta yana fadin “saboda Allah naje daurin aure kinje yini kinje dinner kin kuma zuwa wadda iska ta wargaza, amma duk da haka sai kin kuma fita yau”.
Itama murya cike da shauki tace kayi hakuri. Nayi ma alkwarin da wuri zan dawo”.
“Ni ba wan nan damuwata ba kar kije iska ta dauke min ke. Kin ga ba wani nauyi ne dake ba, san nan …….” Dukan wasa ta kai masa ya goce cikin dariya.
To sun kai gara, amma fa sai da aka yaba musu bakar Magana, saboda sun yi lefe akwati ashirin suna expecting gara sama da haka.
Momi dai aka dawo ana bata labara bakin ciki kamar tayi yaya. Duk yadda taso tsara bikin ba haka yazo mata ba. Ga shi anji jiki, kuma kususu ba riba, saboda ko kwatar abin da aka kashe ba a samu ba. Komawar yara makaranta ma sai da taci bashi suka koma, saboda Dadi yace ba zai kara ko kwabonsa ba, saboda ya bata kudin komai nasu ta narkar da su a bikin nan.
Balle dama ya dada jin haushin labarin da ya samu a wajen Mallam ya dada bata masa rai. Shi ya shaida masa yadda akayi neman auren Zainab da kuma shawarar da ya ba wa Abashir na yayi basaja, da kuma irin yadda rayuwar Zainab ta so baci a sanadin rashin sa ido da aka ringa yi mata.
Dadi yayi nadamar rashin sanya ido a harkar gidansa kwarai da gaske, wanda kuma shine major problem din mazan yanzu. Sun dauka in dai sun tafi nema shi ke nan hakkinsu ya tsaya daga nan. Sun dauka wadata iyali materially is all that is needed. Su bar mata suna son ransu. Allah yasa mu dace.
[8/9, 14:19] +234 814 948 5104: FINI A UBA👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 34
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haka dai Zainab taci gaba da yin rayuwarta cikin jin dadi da walawala. Ga tsananin kauna da mijin ke nuna mata. Ga kuma yadda mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwansa ke tattalinta. Ko da auren Fatu ya tashi wanda kuma shi ya hada auren nata da daya daga cikin abokansa, shi yayi mata komai na hidimar auren. Mama Hajjo saboda tsabar murna ta kasa yi masa godiya, sai dai da sun hada ido ta fara hawayen murna. Ga kuma gallalen mijin da ya hada ‘yarta tata da shi.
Farisa kuwa tana zaune a gidan mijinta. Duk da dai zaman nasu ba wani dadi ne da shi ba. Yau fari gobe tsumma. Kusan duk waanda ya kamata ya sa baki ya gaji da shari’a a tsaakaninsu. Shi ba shi da hakuri ita kuma bata da kunya. Idan fadan su ya tashi haka zaka gansu kamar ‘yan daba har da fashe fashe.
Duk kayan alatun da aka narka musu sun farfasa su. Haka nan idan ya. debi cakunsa zai zo kan dan abu kadan ya rufe ta da duka. Ga dai gidan hutun nan an samu an shiga, amma fa rai da jikin ba su huta din ba. Barinta uku na sanadin dukan da yake mata.
Sai kuma daga baya ya dawo yana bata hakuri. Ita kuma tsabar sonsa haka zata hakura. Balle da ta gwada nuna wa Momi halin da take ji bata dau wani mataki ba ita dai burinta ta binne zancen kar Dadi da kuma sauran mutane suji suyi musu daraiya.
A hakama kuwa gwanda ita da Sakina. Saboda ita auren ma ya gagara gabadaya. A yan shekarun nan auren ta hudu. Ga ta da saurin samun miji, amma fa bata dadewa auren ya ke karewa. Aurenta hudu.’ya’yanta hudu kowa da ubansa. Zaman gidan Momi ya gagareta saboda last auren da Dadi ya daura mata sharadin daya gindaya mata ke nan. In dai ta fito ba gidansa ba.
Haka ta hakura ta koma birged gidan ubanta da zama. Nan kuma suka dasa da matar uba. Kullum cikin tashin hankali. Zainab kuwa bata da matsala. Karatun ta take cikin kwanciyar hanakali. Idan lokacin jarrabawa yazo mijinta ya saka ta a gaba suje ta gama jarrabawa su dawo tare.
A haaka har ta gama degree dinta tana goyon ‘yarta mai sunan Ummansa suna kiranat da Amma. Dai dai ta gama degree ne kuma a lokacin bata dawo ba, Farida tayi zuwan hanzari daga Sudan. Haka ya faru ne sakamakon shayen shayen da khalil ya sanya kansa a ciki. A daure aka sako shi a jirgi a haka kuma ta shiga dashi gidan. Dadi yayi tsanannin bakin ciki da wan nan abu. Take kuwa jininsa ya hau ya yanke jiki ya fadi. Sanadin samun stroke dinsa ke nan. Momi saboda kawai bata son kowa yaji ta kaishi psychiatric ta sa aka kulle shi ta manta da shi a a wajen.
Halinta ne ya sanya kusan duk matsalar ‘ya’yan wasu a bakinta zaka ji tare da kuma nuna sakacin iyayen na abin da ya samu dansu. Kullum ita ce kadai ta iya tarbiyar yara, to yanzu da abin ya zo kanta, sai ta ke kokarin boye tata wutar mai dan Karen hayaki.
Abin da bata sani ba, ba ma acan ya koyi shaye shayen ba, tun a nan yana yi. kusan kuma duk wanda ke tare da ita ya sani itace bata sani ba. Saboda haka da wan nan ya faru sai take ganin ba wanda ya sani. Ba ta san tas asirin ta a bude yake ba. Inda ma kuwa ta dinga tallata na mutane haka itama aka dinga tallata nata.
Amma wan nan yanzu ba shi ne damuwarta ba. Maitaining status dinta a society shi ya dameta, saboda ko ba komai yanzu Dadi aljihunsa yayi kasa. Ita kuma bata yi niyyar ritaya daga karyar da ta daukar wa kanta ba. Nan kuwa ta likewa wata kawarta da akayi mijin senator akan zai samo mata aiki a Abuja.
Kullum tana zirzirga zuwa can. Har dai tayi sa’ar samun aikin. Ta kuwa tattara ta yi gaba abinta ta bar dadi da su Halim su kadai a gida. Sai kuma Khalil dake kulle a asibiti ko mai zuwa duba shi babu.
Wan nan tafiyar da Zainab tayi ta dan dade bata nan. Kuma duk wayar da suke da Dadi bai taba sanar mata abin da ake ciki ba. Sai da ta dawo ta tarar da bakin ciki kala kala.
Tayi bakin ciki matuka, na yadda ta samu Dadinta cikin rashin koshin lafiya.in ba don Mallam ba, ba ko maikula da shi. Halim da Hanif ba wani hankali ne da su ba. Duka duka shekararsu twelve ne a lokacin, ba abin da ya dame su sai dai susa video game agaba su yini wasa. Karatu duk ya tabarbare.
Haka nan ta tarar da khalil a kulle yana hauka tuburan. Da Momi ta hadu da wata kawarta tayi mata jajen Khalifa. A nan ta san ashe mutane sun san case din danta.
Yana kulle sama da wata hudu sai a lokacin ta kai masa ziyara. Dan saukin da ya samu ta dage sai an sako mata shi. Tare kuwa suka dawo gida.
Mallam Usman da yaji shi ya bada shawarar a mayar da shi wajen wani malami mai horar da yara irinsu. Haka kuwa aka dauke shi aka mayar wajen mallam Gaga.
Karatu Qur’ani sosai da sauran littafai yake biya maus. Kuma a hada da bayar da maganin shaye shayen. Tun da aka kaishi wajen nan ba wanda ya ke kai masa ziyara in ban da zainab. Ita Momi ta fake da tayi fushi saboda an dauke shi bada shawararta ba. Dadi kuma yace ba za a dawo da shi ba. Haka ne ya sanya tayi fushin karya. Nan kuwa fakewa ta yi da hakan domin kuwa bata da lokaci. Aikin da take nema a Abuja ya samu. Kuma ga shi basa zama kullum suna cikin fita aiki. Alkawarin da tayiwa Dadi da farko shine zata ringa zuwa kowanne sati, amma shi ma ya gagara. Daga baya ta fito da akidar sai dai shi ya bita su koma Abuja, yace ba inda za shi. Shi ba cikakkayar lafiya ba, tun da nasa aikin ma ya gagara yi.
Dawowar Farida shi ya dan daidaita lamuran gidan. Amma itama bata iya tsawatarwa su Halim. Saboda haka yaran suka fara komawa ba arabi ba boko. Gashi itama tun da ta dawo aiki ya sha mata kai. Kusan kullum sai ta kwana a asibiti.
Ga dai karatun ta samu masha Allah. Ga kuma babban aiki amma fa babu ko mashinshini. Abin dai bai kai ga damunta ba tukunna. Gida dai ya fashe ya zama kamar kufai.
A wan nan rana da Zainab ta kai ziyara, abin ya bata mata rai matuka. Farida ta fara aikin kwana. Wan nan ya sa su Halim basu je makaranta ba. Mallam kuma yaje garinsu gaisuwa. Sallama take ba wanda ya amsa. A falo ta tarar da Dadi ya fadi. Duk jikinsa ya baci abin ba kyan gani.
A guje ta fita ta kirawo driver ta shi ya taimaka mata suka daga shi. Sai da ya gyara masa jiki tukun na san nan suka dauke shi zuwa asibiti. Sai da tazo fita ita a zaton ta ba kowa a gidan, sai ga Hanif ya fito daga dakinsu wanda ke nuna tashin sa ke nan daga bacci. Kuma tabbas ko sallar asuba bai yi ba.
“me ya hana ka zuwa makaranat?”
Yana soshe soshe yace ‘Makara mukayi”. Har za ta sake Magana sai ta tuna da halin da Dadi yake ciki. Ba tayi masa Magana ba ta shiga mota kawai suka wuce asibiti. Tana fita ya dauki waya ya kira Momi yana gaya mata cewar Zainab ta zo ta dauke Dadi.
Da kuwa ta buga mata waya a lokacin sun isa asibitin ana kokarin ba shi taimakon gaggawa. Tana ganin wayarta da hanzari ta amsa da sallama, saboda damaa kokarin kiran ta ta ke yi. Ai kuwa bata amsa sallamar ta ta ba sai zagi da masifa.
Tana kokarin yi mata bayani ba ma ta tsaya ta saurare ta sai bakaken maganganu take ta lafta mata, har tana ce mata duk tsiyar ta bata isa ta aure shi ba, da take wani kaffa kaffa da shi. Uwarta ce kuma ita da Dadi har abada. Sai da ta gama bala’in ta sannan Zaainab ta kashe wayar. Ita da ta juya ta ga yadda Dadin ya zama taushe duk ciwo ya tsufar da shi sai abin ya bata dariya. Balle da ta tuno yadda Abbn Garrko yake kula da umma ga rayuwarsu cike da kwanciyar hankali. Sai ta dada tabbatar wa kanta ko zabi aka bawa Umma tabbas ba zata zabi Dadi ba.
An samu ya farfado. Ita tana tsoron ma ko wani stroke din ya dada samu, sai akayi sa’a sugar sa ne yayi kasa, saboda rashin abinci. Daga baya ma da Albashir yazo suka yanke shawarar fita dashi, zuwa waje.
Ba ta gaya wa kowa cin mutuncin da Momi tayi mata ba ta hada musu zuwa India. Duk abin da ta san zasu bukata sai da ta bawa momin kudin nan. Sun so hada su da Farida su tafi tare amma yanayin aikin ta ya hana. Amma abin haushi bayan sati daya da suka je ganinsa ita da Albashir, suka tarar duk test din da ya kamaata ayi masa ba a yi ba, saboda rashin kudi inji Dr.
Ita kuwa tun da tazo ta kawo shi asibiti ta shiga ta biya abin da bai takakara ya karya ba sai ta shiga kasuwa da sauran kudin. Ta kuma nuna masa ita fa dama da zasu taho ba wani abin kirki Zainab ta bata ba.
Yana ganin Zainab da Albashir sai kawai kuka ya kwace masa. Su sun dauka ma wani ciwon akace yana da shi. Zainab ma sai kuka. Albashir ne yace “don Allah dadi kayi hakuri koma menene Allah zai kawo mana shi da sauki”.
“haba Albashir da girma na zan yiwa ciwo kuka? murnar ganinku kawai nake yi.zainab matso kinji share hawayen da kike zubarwa”.
“sannu dadi Allah ya baka lafiya”. Zainab ta amsa masa. Bayan nan ta shiga tambayar sa abin da likita yace da kuma abin da akayi masa a sibiti. Bai san komai ba, saboda haka tare suka shiga wajen likita ita da mijinta. Sunyi mamakin amsar da likitan ya gaya musu na cewar kusan ba abin da a kayi masa saboda rashin kudi.
Sun yi mamaki kwarai da gaske, saboda sun san cewa sun bawa Momi dala dubu talatin amma kuma ace ba kudi. Albashir bai tsaya dogon bincike ba, ya bada umarni a ci gaba da duk abin da ya kamata na nemawa Dadi lafiya. Hatta daki sai da suka canza masa. aka mai da shi VIP na asibitin.
Momi kuwa ba su suka hadu da ita ba, sai da suka kwana suka yini. A nan suka kwana a adjacent room da ke dakin. Lokacin da taje dakin da ta yasar da mijinta, aka shaida mata cewar an canza masa dakin. Tana shiga ta ga Albashir da Zainab, sai ta fara buyagin karya. Tana fadin “ai sai ka gaya min mowar ‘ya’ya ce ta zo shi yasa ka banzantar da ni. Dadin abin dai sai dai kudin amma jahilci yayi katutu”.
Har Albashir zai yi mganaa sai Zainab ta rike hannunsa, su na hada ido ta girgiza masa kai. Fita kawai suka yi suka barta a dakin. Haka kuwa akayi wan nan zaman asibiti, kullum suka je sai ta nemi maganar da zata yaba musu.
Su kuwa ba sa kulata. Sun tabbatar da Dadi ya samu kulawar da ta dace. Ita kuma ta lodi sarin kaya. Suna dawowa ta takura sai da Zainab ta kaita gidan malamin da aka tsare Khalifa. Shi ma kuwa tana zuwa da danta ta dawo.
Ba a dade ba kayan da ta auno daga Indiya suka zo. Wanda bata mori komai ba, saboda kaya dai sun iso har Nigeria, amma ana debo su daga warehouse, motar data dauko kayan ta kama da wuta kurmus komai ya kone.
Tana tsaka da wan nan bakin cikin ta dawo gida ta tarar da Khalifa wanda ya dan samu aka sako shi daga gidan Mallam, ya hada party a gidan saboda Dadi ba ya nan ya je Kera.
Ba kuwa wanda ya san ya akayi abokansa tas suka kwashe gold din da Momi ta kwashi sama da shekaru ashirin tana Tarawa. Saboda ita a al’adarta bata sayar da gold, sai dai in taga wani ya bata sha’awa ta saya ta kara. To kuwa tas suk shiga suka kwashe su.
Ranar da ta nemi kayan ta rasa ta kuma gane sacewa a kayi ga shi an nemi Khalifan an rasa, sumewa tayi da kyar aka samo kanta. Ta gama da jinyar wan nan wanda ta dau tsayin sati tana jinya, sai ga labari yazo mata na cewa Farisa sun kwashi tsiya da mijin bana har ya karya ta a hannu.
Tana masifa ta tafi da niyyar yau dai kam kashe auren zatayi ta dawo da ita gida saboda ta gaji da wan nan masifaffen aure. Uwar Salim ta kada bakitace “nima na gaji da shari’a. da kin dauke marar kunyar ‘yarki da kowa ya huta”.
“’Yata marar kunya ko danki masifaffe azzalumi. Kullum ya sha kwayarsa ya bugu ya zo ya kama yarinya da duka”.
“shaye shayen ai dan kowa yana yi. Sai dai shi da kudinsa yake yi baya satar na kowa. Ke kuwa bayan dan shaye shaye ai har da barawo kika Haifa”.
Momi ta harzuka ta daga hannu da niyyar kaiwa maman Salim mari, da kyar nurse ta shiga tsakanin. A harzuke ta karasa dakin da aka kwantar da Farisa. Abin haushi a jikin mijinta ta same ta rungume tana shagawabwa. Shi kuma yana kokarin feeding ita abinci.
“Tashi aure ke da shi na kare shi daga yau. Kotu zan shigar da kara ya baki takardarki”.
A yatsune ta dago ta kalleta tace “momi wacce irin takarda kike Magana akai”?
“takardar sakin auren ki dole ne ki rabu da wan nan kallagaggen auren”.
“Rabuwa Momi? Dama nace miki nayi aure don in rabu da mijina ne? kin ga don Allah Momi ki barni in yi rayuwata. So kike nima in koma yadda Anti Sakina ta koma. Kin zugata ta rabu da mijinta na farko, ga shi nan yanzu aurenta biyar. Kullum kuma dada ci baya take. Daga bungalow ta dawo face me I face you. To ni ban shirya rabuwa da mijin ba.
We have our fights and we make up. So meye problem dinki. Ga Farida nan ko mijin ta rasa ni kuma da na samu kina neman rabani da shi. Please Momi let me be. Kije kiji da problems dinki ni ban shirya rabuwa da mijina ba. Kuma ban neman advice dinki ba”.
Duk kuma maganr da ta ke tana rungume jikin mijinta, shi kuma sai shafa ta yake yi ko kunyar surukarsa baya ji. Daga bakin kofa taji dariyar maman salim tana fadin “to kin dai ji amsar ki a wajen ‘yarki saboda haka fice ki bamu waje. Sakarya uwa mai neman kasha auren ‘yarta”.
Haka ta baro asibitin cikin bakin ciki. Duk da kuntatawar da tayi wa Zainab bata taba maida mata Magana ba amma ga ‘yar cikin ta nan tana caccaba mata a gaban Surakarta da kuma surukinta.
Ta dawo kuma ta tarar da Sakina itama ta debo nata bakin cikin. Auren kisan wuta tayi da driver gidan da tayi aure wani Alhaji mai kudi. Karamar rigima ya dankara mata saki uku. Akan tana son komawa ta lallabi driver akan suyi auren sakin wuta. To an yi aure na sati uku amma sama da wata uku yaki saki.
Kuma ga shi da kokari har gida ya kama mata haya ciki da falo da kuma falle guda nasa a nan cikin limawa, ya kuma yi mata iznin tahowa da ‘ya’yanta guda biyar akan zai taya ta rike su. Matsalar sa muni kamar a yankar wukar. Idan ta kalle shi har gabanta faduwa yake.
Ta nemi saki yace bai san zance ba. Ta kai shi kara ta rasa hujjojin da zata bayar na ya sake ta. Kotu kuwa ta bashi aure. To yauma wan nan bakin cikin tazo take zayyanawa Momi.
Ita kam tama rasa yadda zata yi da rayuwarta. Ga Khalifa an neme shin an rasa ga kuma auren ‘yan gata yanda ya kasance. Bilkisu kuwa tayi musu ta ‘yan duniya. Ba ruwanta da kula kowa. Dama ba cikin su daya da momi ba. Ta wurgar da su ta rungumi uwarta da ‘kannenta ‘yan dakinsu.
Ganin bakin ciki da talauci zai daureta ta tattara ta koma Abuja inda ta samu sabon aiki. Nan kuwa Boss dinta ya dinga sakata tana tabargaza da kudin gwamanati.
Haka rayuwa taci gab da Garawa. Zainab ita tasa aka nemo mata Khalifa. Ta sake mai da shi gidan kangarrarun yara. Sai da kuwa ya shekara ya fito ya warke tas kansa ciki da Qur’ani. Nan ta nuna masa son ya koma makaranata. Shi kuma ya nuna yafi kaunar ya tafi Saudiyya ya karanta Islamic studies. Jin wan nan zance Momi ranta ya baci ta fara masifar Zainab ta mallaketa mata da. Ya daina jin maganrta sai ta yarsa. Shi dai bai bi ta kanta ba ya yi tafiyarsa makaranta.
Wan nan karon ma Dadi ya dan yi jinya, su baffa suka zo dubashi. Duk da dai yanzu shi dan gata ne a wajen Zainab. Hatta ruwan da zai sha za ta tabbatar ta ajiye masa. Amma yadda su Baffa suka ga gidan kamar kufai sai ba suji dadi ba. Suka tambayi Momi ya gaya musu ta koma Abuja da zama.
Baffan Nene ne yace “to kai kuma haka zaka ci gaba da zama gida ba mace”?
Shiru yayi bai bashi amsa ba. Shine ya sake cewa idan baza ka ga mun yi maka karanbani ba ai da mun baka mata”.
“Wallahi Baffa ba wani karanbani. Idan zan samu hakan zan gode”.
“ba damuwa kaje ka ganta ku gaisa. Safiya yarinyar kirkice duka duka shekarara ta talatin da biyu bata taba haihuwa ba. Mijin ne Allah ya yi masa rasuwa”.
Da alamun jin kunya yace “Baffa ni ba ma sai na ganta ba. In dai kuna ganin ta dace da ni shi ke nan ayi komai. Momi dai bata da labarin komai saboda ba wanda ya ji zancen auren. Farida ce zata sanr da ita ita kuma ta koma karatu tana Ibadan. Halim da Hanif Zainab ta mai da su wata boarding school inda ake biya musu har karatun ‘Qur’ani mai girma.
Saboda haka week end kawai tazo ta tarar da amarya a gida. Komai kuma ya canza. Dadi ango ya murmure duk furfuran nan ta tafi. Gida ko ina kal kal da shi. Tayi niyyar yin tijara da saukewa amarya Safiyya rashin mutunci, ita ma kuwa ta nuna mata ba kyalle bace. Da shirinta ta zo.
Dadi yaga zata daga masa hankali ya sake ta saki daya. A ranar ta koma Abuja cike da bacin rai. Duk wan nan badakala da akeyi Zainab bata nan ta yi tafiya saboda tana kokarin hattama degree ta na uku a tafsir. Ita kam ai ilmin ta dangin mijinta ba karamin amfana suke da shi ba.
Kaf yaran family a wajenta suke daukar karatu. Babbar islamiyya ta bude sadaka. Tun tana madina Dady ya sanar da ita zancen aurensa. Ta tashi dawowa kuwa ta hadowa ango da amrya lefen na garari. Ta shirya musu dan karamin honey moon inda ta yaudare su da cewar Dadi zai koma check up.
Kafin su dawo kuwa ta sa akayi musu total renovation. Akayi musu sababbin furniture. A wan nan lokacin yaranta uku. Amma’yar shekaru takwas, sai Amir mai shekara biyar sai kuma Maama mai shekara daya. Sai koma babban bebinta da bata hada shi da kowa, watau first born dinta ke nan bala mai gwanjo.
Goggo Safiya kuwa ta kama kowa ta rike a gidan. Su Halim idan sun zo hutu nata ne. Farida kuwa dama I don’t care attitude gareta. Ba ruwanta da harkar kowa. Aikin ta kawai ta sa a gaba.
Albashir zaune a falonsa suna buga game da Amir a Xbox X dinsa Zainab tayi sallama ta shigo. Yana ganin yanayinta yace da yaron “game up. Sai gobe ma karasa”.
Yayi musu sallama ya nufi dakinsu. Yaron na fita ya jawota jikinsa tare da fadin “me ya samu Putre Salju na? na ganta yau kamar akwai abin dake damunta”.
“Farida ce ta bugo min waya tace wai EFCC sun kama Momi”.
Sakinta yayi yaci gaba da buga game din shi kadai.
“Ya Balarabe bakaji me nace maka bane”?
“naji so what. Me kike so inyi miki”?
“Kenan ba taimakon da zaka iya yi min. Shi ke nan na gode zan je in yi iyakar kokarina” ta mike irin ni nayi fushi din nan.
Da sauri ya mike yana riko ya yana fadin “yi hakuri Putri na. idan kikayi min fushi ina zan sa kaina”. Da murmushi ta dawo wajensa ta zauna a gefensa. Shi kuma yace “yanzu gaya min me kike so inyi”?
“wai da ka kirawo yallabai Sa’ad ba shine ogan Abuja ba ko da taiamkon da zai iya yi mana”.
“an gama ranki shi dade”. Waya ya kira ya sanya ta a speaker. Muryar sa’ad taji yana cewa “kaga autan umma angon Zainab baban Amma. Yau ka tuna da ni ne ko zakka ka cire ka tuna da abokinka tsohon dan sanda”?
“Ai ba wata zakka sai dai rigimar Putri da ta tashe ni yanzun nan”.
“a kace amaryar bala mai gwanjo ta murda kambunta”.
“ai ita dama kambunta kullum a murde yake. Gani kuma matsoraci ban iya yi mata musu ba”.
Dariya ya tuntsire yace “yanzu me take so ayi mata mu taimaka mu dafa maka. Kasuwar gwanjo zamu koma, koko wata sana’ar ta samo mana”?
“In bata samo sana’a ba ai ta dauko rigima. Ka tuna matar nan da ta so hana mu auren juna. Ita staff dinka suka kama”.
“subahana Lillahi. Ai kuwa aiki baiyi kyau ba. Suruka guda a hannun surukinta. Bani details din case din.
“ai ba wani details sunan ta Rumaisa a finace take aiki. Sai dai ban san nawa ta sata ba”.
“kai jama’a. yanzu Ya Balarabe don zaka taimaka min sai ka ci min fuska”?
Sa’ad ya jiyo muryarta ta speaker da Albashir ya danna. “Kin ga madam kyale shi. Bani nan da five minutes zan kiraku”.
Minti biyar din ma bata karasa ba ya kira ya ke sanar dasu abin da ya faru. Kudi ne suka fitar ita da ogan ta har miliyan hamsin. Amma unfortunately five million kawai taci a cikin kudin saboda ogan ne ya karbe sauran. Sai dai kuma sa hannunta ne a voucher so ba ta inda zata fita.
Sa’aad ya ci gaba da cewa “idan so samu ne a samu a yi refunding ko da ten ne daga cikin kudin sai a samo guarantor da zai sa hannu a sake ta. In yaso daga baya zan ga yadda za a yi ayi dropping all charges against her”.
“kana maganar 10 mill. Ni ina ga kudin da zan biya”?
Da mamaki ta juya tana kallonsa. Mutumin da don ya ginawa talaka gida ya bashi jari mai kauri ba wani abu bane a wajensa amma yana kukan bashi da as little as 10m.
Tana cikin kuka ta duba balance din account dinta. Kudin ba su kai ba. Saboda bata dade auren Sajida da kuma Faruk kannenta ba. Duk da dai 90% Albashir ne yayi komai. Ga kuma Hafsa da ta itama auren nata ba hustling saboda kanin abokinsa Mujib shi ya aureta, amma dai duk da haka an dan ji jiki. Saboda har gida suka gina masa.
Yinin ranar sam ta kasa sukuni. In ban da kuka ita da Farida ba abin da su ke yi. Ita farida tana da albashi mai dan tsoka, amma kaf hidimar anti Sakina da yaranta a wuyanta suke, saboda haka kafin wata dan abin da aka samu ya kare.
Zainab tayi rokon tayi lallashin amma sam Albashir ya kekasa kasa yace shi ba abin da zai iya yi. Daddy kuwa ko guarantor ma yace ba zaiyi mata ba. Farisa tace ita kuwa she cant waste her money on Momi saboda ita ta jawa kanta.
Albashir ya shiga wajen Umma take tambayarsa yinin yau gaba daya bata ga zainab ba, kuma bata kirata a waya ba. Kwanciyarsa yayi a kan doguwar kujera san nan yace “kyaleta umma rigima take ji shi yasa ma na fito na barmata gidan”.
“haba dan uwana. Don tana ji rigima kuma ina ce ba rarrashinta zaka yi ba. Ita fa mace ba girma take da shagwaba a gaban mijinta ba”.
“umman ba rarrashin take so ba. Wai fa matar gidansu taci kudin gwamnati shine ofis din su Sa’ad suka kamata. Kuma wai ni take so in taimaka in fito da ita”.
Da mamaki Umman ta sake cewa “baka da abin da zaka fito da ita din ne ko kuwa tsiya kawai kake ji”?
Shiru ya kasa baiwa umman amsa. “Anya dan uwana yaushe ka koyi riko haka”.
“Allah Umma don dai baki san irin muguntar da ta dinga yiwa Zainab bane. So tayi kwata kwata rayuwarta ta lalace. Hatta makaranta kin ga sai da tayi mata sanadinta”.
“Kuma da tayi mata sanadin nata sai me ya faru. Yanzu kai ilmin da Zainab take da shi ba daidaikun mata ne suka samu sa’ar yin sa ba. Ina ce ran nan kace min ERC sun nemi ta basu littafin data buga na easy fiqhu akan zasu saka shi a IRK syllabus na makarantu. Kuma duk wan nan daukakar har ace ana bakin ciki bata yi karatu ba. Ashe akwai abin da yafin ilmin addini dadi”.
“umma ni kawai haushin matar nake ji”.
“To ka daina saboda Maryam ta taba tambayarta dalilin da yasa take iya yiwa Momi alkhairi lokacin da ta kai Khalifa karatu Saudiyya. Amsar da ta bata ni kaina naji dadin ta. Tana budar baki tace idan har ta ci gaba da kullatar Momi to tabbas ba ta yi wa Allah godiya da ya hada ta zama da mu ba. Kaga kuwa idan ita tayi wan nan tunani kai ma irinsa nake so kayi. Saboda haka, kaje dan uwana in dai baifi karfinka ba, ka taimaka a fito da ita”.
Suna falonta zaune ita da Farida sun yi jigum jigum, saboda ance idan ba a zo bailing Momi ba tsakanin yau da gobe tabbas jibi kotu za a tura ta. Shigowarsa yana waya inda suka ji yana neman ticket na mutum uku zuwa Abuja, ya sanya suka saki ransu.
Sun sami jirgin karfe daya. Kafin uku suna ofis din Sa’ad. Albashir ne yayi komai, ya kuma tsaya a guarantor, amma fa yana yi yana mitar idan Momi ta gudu aka kama shi, ita ya shafa. Saboda umma da Abba suna da wasu ‘ya’yan ita kuwa shi kadai ne mijinta.
Sa’ad yana dariya yake ce masa “kar ka damu ba inda zata je. Kuma ma ina ga zan yi closing din case din yau din nan. Nan da nan asarar 10m ta hau kan Albashir. Saboda ba shi yayi niyya ba ya sa mata suna asara. Mutumin da riba ke shiga account dinsa bayan kowacce awa daya. Ko sati zai iya hada ribar 10m din.
Inda Allah ya takaita Farida bata tare dasu da ba karamin kunya zata sha ba na mitar da mijinta ke yi. Sa’ad kuwa ya taimaka matuka, saboda a ranar aka gama case din Momi.
Tana fitowa daga inda aka tsareta taga Zainab, har kasa ta durkusa tana yi musu godiya ita da Albashir. Zainab ta dago ta rungunme ta a jikinta tana bata hakuri. Abin mamaki wai yau ita Momi ke shiwa albarka.
An gama case. Sai dai kuma an sauke ta daga aiki. Tare suka juyo zuwa kano washegari. Dadi kuma yayi tsallen arziki yace ba gidansa ba. Ba irin rokon da ba su yi masa ba yace shi kam ba zai maida ita ba.
Akwai wasu kananan gidaje da Albashir kan gina masu dauke da dakuna uku a jere sai falon a karshen dakin farko da kuma kitchen da tsakar gida suna kallon dakunan daura da falon ke nan. Sai kuma daga karshen dakunan akwai dakin waje da toilet dinsa da kuma shago dan madaidaici.
Ko wacce shekara ya kan gina irinsu guda goma ya bayar sadaka. Zainab ta bude daya tasa aka wanke shi. Take ta sayo kayan gida har da su Ac aka gyara gidan sosai. Ba ita ta gama ba sai kusan magariba. A ranar momi ta tare a sabon gidan da Zainab ta bata.
“Eh haka kawai saboda mutum yaga ba a iya fushi da shi sai ya dinga min hawa kawara. To bulukutu maragatan”
Ita dariya ma mitar ta Albashir take bata sai kace Ammace take fada da Amir. Jawo shi tayi jikinta sai da ya samu daidaita natsuwarsa ya fara manta a ina yake san nan tace “kayi hakuri. Ba zan iya ganin Farida cikin tashin hankali in kyale ta ba. Momi kuma ai uwace a wajena”.
Cike da shauki yace “tsokanarki nake yi Putri. Kin san I can do koma meye for you”.
“Alhamdu lillah. Yanzu sauran ka abu daya. Yadda ka sama wa su Hafsa mazan aure nagartattu ka taimaka Ita ma Farida ka samu wani mai hankali cikin jama’arka ka hada ta da shi”.
“kai Putri akwai ki da naci. Kusan shekaru takwas ke nan kullum sai kin yi min maganra in aurar da farida. Yaya ki ke son in yi. In lokacin auren ta yazo ai za ta yi ne”.
To Momi dai daga babbar ma’aikaciya ta dawo zaman shago. Dan provision Farida ta zuba mata take sayarwa tana dan samun na batarwa. Duk da dai Zainab bata barta haka ba. Yadda ta sauke a gidan mahaifin ta haka take saukewa a gidan Momi. Amma yau da gobe sai Allah.
Sai daga baya Farida ta samu auren wani nurse in charge ne a asibitin su . Yana da kirki sai dai matarsa da uwarsa ba bayani. Masifaffu ne na nuna wa sa’a. da sun yi zai barta ta kama gidan ta, amma daga baya matar ta zuge uwar tace mata “inna idan kika barsu suka kama gida su kadai dadi zasuje suna ci mu su bar mu a anan tun da ance babbar likita ce tana da kudi. Ki sa shi ya kawo ta nan ayi komai akan idonmu”.
Haka kuwa akayi. Daki ciki da falo aka bata a gidan sa. Duk tarin da momi tayi na auren ta ya tashi a banza. Momi taso taki auren ita kuwa she is being practical tace “mh mh Momi kyale ni iam not getting any younger. Iam almost thirty”.
Haka ta lallaba tayi auren da take ganin zai zamo mata rufin asiri, sai dai fa abin da kamar wuya. Ba a raba tunuya ba. Haka dole take cefane na mutum goma sha biyar. Inna da kanne mijinta hudu. Mariya da ‘ya’yanta bakwwai. Ga kuma bazawarar kanwarsa da ‘yarta duk a gida daya.
Ba wani cikakken privacy a gidan. Duk wanda yaji ko da sartse ne ita zata kai shi asibiti ta kuma sayo magani. Cefanen gidan ita ce. Shi nasa albashin sai Innar ta karbe ta bawa useless kannensa. Dama shi kadai ne responsible a gidan. Ga ‘yar banzar rashin kunya da suke labta mata. Ga sata. Yanzu haka ta hakura da sayen waya mai tsada ta koma nokia mai torch light. Saboda in dai ta saya yau gobe kuwa zata neme ta ta rasa. Ba kuma ta isa tayi cigiya ba. Saboda ko ganin ta tayi a gidan za ace ai ba ita kadai nasara yayi wa wayar ba.
A haka ta haifi diyarta mai sunan Momi. Lokacin da ta tashi zata saka ta anursery aka ce sam ba za a raba musu makaranta da sauran yayyen ta ba. Saboda tana son Iman ta samu karatu mai kyau, haka ta hakura ta dau responsibility yaran takwas ta hada da tata tara.
She works for like sixteen hours daily just to meet her financial abligations. Ko motar hawa ta kasa saya. Duk ta tsofe kamar ba ita ba. Ranar da Zainab ta haifi ‘yarta ta hudu Khadija, taje mata barka. Haka ta tantsa yaran nan a adaidaita sahu, saboda ta dauko su daga makaranta ke nan, don ta san idan ta koma gida ba zata samu fitowa ba.
Zainab na zaune a falo ta ga yara sai fitowa suke daga adaidaita. Sai da mutum goma suka fito daga cikinsa. Take hankalinta ya tashi na ganin kanwarta ce cikin wan nan situation din. Sai da sukaci abincin dare san nan suka tashi tafiya. Ta fito raka ta driver zai ajiye ta agida, sai kawai ta tuna da sienna LE2004 dake zaune a gidan wai saboda ko da za aiki driver.
Bata san sanda ta shiga daki ta dauko key ba. Har sun gama duruwa cikin motar ta range rover tace wa “Farida sauko ungo wan nan ai dai zata kai ki point A to B. cike da murna ta shiga gida da sabuwar motar da yayarta ta bata.
Washe gari har da maigidan aka fito ana ta murnar samun sabuwar mota. Aka lalauba babu mota babu dalilinta. Ana kakabin an sace sai ga waya daga police station yazo an kama kannesa sun buge wani mutum da mota.
Haka mijin Farida ya nufi police station din. Ashe wai ta window dakinta suka shiga tana wanka suka dauke key din da daddare. Yayi belinsu Farida ta tsaya kan medical treatment din wanda suka buge. Daga ya dawo gida yana musu fada, kishiyar farida Mariya tace tana jin san da Faridan ta zuga shi.
Nan kuwa suka tarar mata. Duk da kokarin da yayi na hansu sai da sukayi mata ligif da jikinta san nan suka kyaleta. Shi ya kaita asibiti yana bata hakuri kamar yadda yake mata ko da yaushe. Shi ai yana sonta. Family shi ne wasu bunch of hooligansa.
Zainab da danyen jego ta je ta ga yadda kanwarta ta koma saboda dukan dangin miji. Ba yadda bata yi da Dadi ba yace ai shi ya fitar da hannunsa akan Rumaisa da ‘ya’yanta. Da kyar ta samu ta lallaba shi. Tare suka je gidan mijin su Farida. Nan kuwa tadage takardar kanwarta za a bata, ko kuma a raba musu gida.
Shi dai kabiru yana son zama da matarsa, saboda haka ya samu ya lallaba uwarsa akan cewa idan suka bar farida ta bar gidan yara sun daina zuwa makaranatar kudi saboda ita take biya, haka kuma dan dadin da suke ci da kuma ‘yar sutura mai kyau duk zata gagare su saboda ita ke tallafawa.
Da wan nan ya samu ya dora ta ta yarda akan Farida ta koma gidanta, amma sai tayi alkawarin zata ci gaba da dawainiyar yara ta makaranta. A nan unguwar Zainab ta samu dan gida madaidaici ta saya mata. Aka kuma yi mata iyaka da kannen mijin. In dai suna son ganinsa sai dai su kira shia a waya, amma ban da shiga gidan Farida.
A haka ta samu ta kwato mata ‘yancin ta. Ta kuma ci gaba da tallafa mata, saboda albashinta ba zai dauki nauyin dake kanta ba. Ga Sakina da yaranta biyar ga tata ga na mijinta guda bakwai da kuma ‘yar kanwarsa duk ita ke biyan school fees dinsu. Tayi aikin gwamnati tayi private duk don ta rufwa kanta asiri.
Yau shekarar Zainab da Albashir goma cif da aure. Ba tare da saninta ba ya shirya mata hadaddiyar dinner. Ya sa ta shirya ita da ‘yanmatan ta cikin wani hadaddaen lace yayin da shi da Amir suka hade a shadda suma anko babbar riga.
Sai da ta zauna a matsayin guest san nan ta fuskanci ita ce host na taron. Ba abin da ya dada birgeta irin yadda Albashir ya dada tababatar mata da soyayarrsa a gaban mutane. Allah yasa ma su yasu ne kawai matasa. Wakar da aka musu ta shimfidar fuska ranar bikin aurensu, ya zauna yayi miming da kansa ya rera mata a cikin bainar jama’a.
Ai kuwa bata san sanda ta shiga fili ta dinga falle ‘yan dubu dubu tana lika masa ba. Shi kuma ya riko hannunta yana taka rawa da ita a hankali. Nan kuma sauran abokansu suka kewaye su ana ta zuba masa kudi.
Mujib ne yayi jawabin godiya inda yake cewa “lokacin da muka je neman auren a’yan gwanjo muka je. Yau kuma mun koma mawaka after ten years. Ban sani ba nan da wata ten years idan har muna raye ban san wacce sana’a zamu fara ba. Amma dai kam iam sure of one thing. The circumstances might change but the love of Albashir and Zainab will remain where it was yesterday”.
ALHAMDU LILLAH
0 Comments