Dan waye hausa novels comlplete

 OVELS DAN...........WAYE 1 . DAN........WAYE ???? 1*1 . Na. ZARA'U BABA YAKASAI . . FARKON LABARI . A hankali yake tafiya cikin sanyin jiki, da alama ya sha wuya , yanayin sa zai sanya ka san nutsatstsen matashi ne. Anutse ya karya lungun daya shiga, a dai dai lokacin wata fiti nanniyar mota ta sako kai cikin lungun. Yanayin yadda ake jan motar da yadda sauti ke tashi shi ya tabbatar masa da cewa matashi ne dan uwan sa, da yake kallo daya yayima motar ya maida kansa ,yaci gaba da tafiyarsa. (Horn) din da motar takeyi ya sanya shi kallon me akeyiwa hon din??? Ai kuwa kuwa wata matashiya ya gani tana tafiya a nutse , don yadda ta nuna sam batama san matashin na yi mata hon ba. Can sai ya ga matashin ya fito a zafafe ya wanke mata fuska, ta kuwa dafe fuskar ta tana mai kallonsa. Ta zuba masa ido, tace " me nayi maka ina cikin tafiya zaka mareni ???" tunu idanun ta sun soma tsiyayar hawaye, kan kace meye wannan duk mutane sun kewaye su. Ta juya da sauri saita ga motar abayanta, sai ta juyo ta kalle, shi tace. "Me..........". Dai dai lokacin daya soma masifa, yace. "Shegiya, dana sani ma in takeki in taka banza,shashasaha kawai". Tace ,"Oho, ni ban san abinda kake cewa ba, illah iyaka na san ka zalunceni, don ban san me nayi makaba. Ina da matsala akunne na don banaji sam". "Kaji 'yar rainin hankali, zakice wai ba kya ji , gashi kina magana rambadadau". Mubarak dake tsaye yana kallon su ya taka ya ce " Abokina bahaka akeyiba, saurin hannu yakan kawo dana sani, bai kyautu ba". Ya kafa mata idanunsa yana kallonta, ya soma magana yana motsa jikinsa yadda zata fahimta, yace. "ke kinsan kinada matsala meya sanya kika fito ke daya?". Tace, "Nayi jiran surayya batazoba, ni kuma na tafi. Wannan bashi ne karon farkoba, amma ya zalunceni, domin marin mace kaskancine. Aka'idar musulunci ba a marin fuskar mace, jikin ma ba don duka akayi shiba, sai dai na barshi da Allah". Wancan mutumin yace "in baki barni da Allah ba ya zakiyi? Yar rainin hankali". Ya maido da hankalinsa kan Mubarak, yace. "Malam ba ayimin irin abinda kayi min yanzu, don na tsani shisshigi. Ke kuma ki kiyaye ni, Wallahi nasa mota na tattakaki". Mubarak ya kalle shi cikin mamakin furucinsa, yace. "Kayi hakuri, ban san abin zai bata maka rai ba. Ke kuma maza muje in rakaki, saboda gudun faruwar irin haka". Suka juya, mutumin yace "(Nonsence) dama kana son sakaine, mezakayi da musaka yadda Allah yayika da kyau haka?" mubarak da izzatu suka ci gaba da tafiya, zuciyarta na suya saboda takaicin abinda aka yi mata. Sun yi tafiya sosai mai nisa suka karaso wani tafkeken gida ta juyo tace. "Na gode , na Allah basa karewa, gashi ka kawoni har gidanmu". Yace "tow sai anjima". Har ta shige ta juyo tace. "Kai wanne irin mutum ne? Bazaka fadamin sunan ka ba?" yace , "Ni suna na Mubarak tace , "to Mubarak sai anjima". Ta juya batareda ya tambayi sunanta ba , ta shiga gida sa sauri. Tana shiga ta fadawa ummanta,tace. "kinga yau nasha mari". Ta ce, "Kiyi hakuri, ita rayuwa haka take". "Amma umma mutane basu da adalci.....". Nan ta fadawa ummanta abindaya faru surayya ta shigo ta ce, "IZZATU". Tace kinga kyaleni, ai kinsan zan fita kika fice". Tace, "Kai, kin manta ina da (text) yau?. Kiyi hakuri, afuwan kinji 'yar uwa" ta mike tayi falo, don dukansu suna tsakar gidan Mubarak yaro ne matashi, dan shekaru ishirin da bakwai. Yaro ne salihi, na gari, wanda a duk fadin unguwar su in za a fadi matashin mutumin kirki in ba asa shi na farko, ba to zai shiga na biyu. Ya samu tarbiya gurin iyayensa. Wadda suka dauki so da kauna suka dora masa, ko don shi daya suka haifane ? Oho. Iyayen Mubarak ba masu kudi bane masu rufin asirine ,don mubarak yayi (digree) dinsa, don mahaifinsa mutum ne meson sai yaga Mubarak din yayi ilimi sosai, an kuma yi sa a Mubarak din mai kwakwalwa ne. . Hmmmm tow fa yaya kuke ganin wannan lamarin .OVELS

DAN........WAYE ??? 1*2

.

Na ZARA'U BABA YAKASAI

.

.

sallamar da yayi ya sanya mahaifiyarsa wacce

mutanen anguwarsu suke kiranta da maman

mubarak,shi kuma Mubarak din yana ce mata

mah. Ta taso tana cewa.

"kai yaron nan kayi nisan kiwo, ina ka shiga ka

sanya zuciyata ta kasa zama guri daya?" ya

kwashe da dariya , yace.

"Mah, sannu da gida".

Yai dariya yace,"Nagirmafa yanzu mah, ayanzu

nakai munzalin da zan kula da ku".

Ta washe baki tace, "To Mubarak. Yaya an

dace ?" ya dan yi jim sannan yace.

"Kaiya mah,rayuwar kasar nan na bani mamaki.

Kiduba kiga kyau irin na sakamakona ,wai amma

na rasa aiki. A Nigeria ba a duba can canta illah

a duba waka sani,wanda yake ya san wani".

Mah tace "uhm kai dan nan bari .insha Allah

saika sami albarkacin Annabin Rahma". yace,

"Amin".

Tace, "Bari in kawo maka abinci".

Ya mike "A 'ah mah, bari in dauko da kaina, ai

yanzu ni yakamata kuma na dinga yi miki kina

zaune.ke dai Allah yabamu kudi in kaiki

Makka,har madina".

Tace, "Allah ya nunamin".

Shigowar malam bala tasa suka amsa

sallamarsa, ya shiga. Mah tai saurin dauko

sabuwar tabarma ta shimfida masa ya zauna, ya

cire babbar rigarsa,e Mubarak ya karba ya kai

ciki.

Ita ko mah ta soma yi masa fifita.

Malam bala ya dubi mubarak yace.

"Mutumina ya akayi ? Ina fatan an dace ?"

Mubarak ya kada kai ,yace .

"uhm baba ,yau da kaga wuyar dana sha wallah

da ka tausayamin. Tun kokon safe cikina baiga

komaiba sai yanzu nake niyyar ci". malam bala

ya dubi matar sa yace. "halima sarkin kokari,har

kin dafa".

Ta sunkuyar da kai tana dariya, yayin da yaci

gaba da sa mata albarka. ya ce, "Nafita ban bar

komaiba ina tunanin ya za ayi, sai gashi har

kinyi".

"Tow malam meye amfanin neman da nake?

Dama don kai da wannan dan nakeyi". yace,

"Allah ya biyaki".

Tace, "Amin"

shikuwa mubarak addu'arsa daya, Allah ya bashi

aiki ya sanya iyayensa suji dadi. mah ta tashi ta

kawo ma malam abinci, tare da Mubarak sukaci

suka koshi, suka kuma kama shira.

Hakika iyayen Mubarak suna son sa soyayya mai

zafi, don ko zazzabi in Mubarak yayi duk sai sun

rame. allah kuma ya taimakesu yarone

nutsatstse, don baya son yaga abinda zai taba

mutuncin iyayensa.

Sun jima suna tattaunawa akan neman aikin da

Mubarak din yakeyi,har yanzu shuru.

.

* * * * *

.

A firgice ya farka daga baccin da yakeyi, ya tofa

addu'ar da Annabi yai umarni da ayi idan kayi

mummunan mafarki'don mafarkin da yayi dole ne

ya kirashi da mummunan mafarki.

ya zuba kafafun sa a kasa yayin da yake zaune a

bakin gado,ya dafe fuskarsa da hannunsa.

Abinda

ya gani a mafarkin ya ringa dawo masa kamar

da

gaske.

Yace , "Oh! Nifa kada naje na mari aljana, yarinya

kin fitine ni, kullum na kwanta sai nayi mafarkin

ki, anya za a kwashe da gaskiya?"

Ai babu shiri yayi alwala ya dauko Alkur'ani ya

soma karatu har sai da yaji mahaifin sa na buga

masa kofa ya tashi su tafi masallaci. Ya fita

suka fita tare da mahaifin sa.

mustapha zaune yayi tagumi cikin falon

mahaifiyar sa ta fito' irin manyan hajiyoyin nan

ne' amma fa kyakkyawace ajin karshe.

Tace "lafiya kake my bo" ya kada kafada '"momi

na debo ruwan dafa kaina"

tace, "kamar ya ?"

yace , "uhm zauna ki sha labari"

ta zauna anutse ta shafi kan dan nata tace.

"Inajinka"

mustapha yace.

"Wata yarinya ce kyak kyawa momei.........".

Tasan halin wautar mustapha ko kuwa nace

shagwaba. Tasanshi yanzu zai yi kwaba,dan

haka

saitayi saurin cewa

"ita kyakkyawar sonta kake?" Yace "No momi,

tana zuwar min a mafarki......"

Dai dai nan Alhaji majid ya shigo, yana takawa

ahankali. Bawani tsoho bane don 'yan matan

zamani zasu so ace ya aure su. Sai dai shi

mutum ne mai kamun kai' ba kamar yadda masu

kudin yanzu sukeba. Domin a zahiri masu kudin

yanzu za su hana 'ya 'yansu yawo amma 'ya

'yan

talakawa suke tarawa acikin (guest house) nasu.

Wannan abu yana matukar damun a'lumma , abin

da bazakaso ayi da yarkaba shi kake yi da yar

wani.

Tow shi Alh. Majid babu ruwansa da kula mata in

ba matarsaba hajiya saratu, mace ce 'yar

kwalisa, wacce tas san yadda zata kula da

mijinta.

Ya shigo da sallama ta kalleshi a kai kaice tace.

"Au, har ka tashi a baccin ?"

.

tow muma Allah kabamu mataye nagari wadda

zasu kula da mu sosai.AUSA NOVELS DAN........WAYE ??? 1*3 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Ya harare ta, ya maida hankalinsa kan Mustapha ya mika masa hannu, mustapha ya noke. "ka gani zamu bata". yace, "Allah abba in ka miko min hannu sai naji duk duniyar tayi min kadan ,sai inji wani bambara kwai". "Ya kamata ace ka saba mustapha nawa, da ai kana bani hannu ,yanzu ka daina". Hajiya saratu tace "ya yi hankali ne , ya ga rashin dacewar hakan". " Wai ko lafiya kake?" ya girgiza kai yace "abba wallahi wata kyak kyawa ce take zuwar min abacci, anya ba aljana na mara ba?" abban sa ya dubeshi yace . "meye labarin ta har ka mareta?" bai boyeba ya fada musu, cikin tsananin bacin rai hajiya saratu tace. "Wai boy yaushe zaka daina hauka ne? Kullum i na ta fama da kai amma kamar ina kara zugaka??? Tow yanzu in aljanace ai ka jaza mani" Abbansa mutum ne mai sanyin hali saboda haka sai ya lallasheshi tare da cewar mustapha yarone , zai daina. Tace, "Har yaushe ? Saurin hannu bashida dadi". Ya shafi kan mustapha daya bata ransa, yace . "Boy ,banason saurin hannu kaji? Bare ma dukan mace, wacce akafi son a tausaya mata. Domin mace daraja ce da ita kaji boy?" ya gyada kai, yace, " Abbana yarinyar 'yar rai nin hankalice, cemin tayi bataji, kuma magana radau tsabar iskanci ne" Hajiya saratu ta harare shi,tace. Ai yanzu gashi nan hakkinta ya kamaka, daga mafarki sai so kuma". Alh.majid yace, A 'a karkimasa baki ". gaba daya sukayi dariya. "bama sonta nakeba, mezanyi da dunkum? Can dai". Daga nan sukaci gaba da hira sai hajiya saratu ta gaiyacesu cin abinci, don ko kusan an shirya tebir,shi ake jira kuma ya fito. Sallamar suhaila maman mubarak taji tace . "A'a yau a gari tana dariya tace, "mah ni ce". Ta shigo ta tadda mah din tana shara, take ta karbi tsintsiyar taci gaba da yin shara ,tace .daga zuwa ?" in da sabo mah ta saba. Tana gama shara ta shiga ciki ta dauro zani, ta hau wanke -wanke suna hira . Bayan ta gama ta shige dakin mah,can ma taji shurun yayi yawa ta shigo a zaton ta bacci take ,amma sai ta tarar ta tsaftace dakinta fiye da da, dom mah tsoftace da ita, gashi ta hado kayan wani tace. "Uh, nayi zaton kwanciya kikayi, shine kika hado wanki,ke ba kyason hutu? To bani da sabulu, sai ki ajiye". tayi dariya, "Nazo da sabuluna , Mah tabi suhailat da kallo, tace " Nikam wallahi banason in ganki kin zo kina aikin wahala". Suhailat tace, "Mah, meye abin wahala? A gidama aiki nake, ni babu ruwana da masu aiki". Dole dai mah ta rabu da ita, ta sanya sanwar abinci. Tana cikin yin wankin Mubarak ya shigo yace ":wai ! Wata sabon gani". Taci na khamis , ma a'ana tasha kunu. Yace haba 'yar kanwata yaushe kika zo?" tayi banza da shi taci gaba da aikinta, ita kuwa mah tayi musu banza uwa bata jisu ba. Yace " aikin wahala ba naki bane, bar inzo in taya ki". Nanma bata tankaba . Yace kifadamin laifina sai in gyara kinji sister? Amma ban can can ci hakaba. Ta saci kallon mah, saitagama ashe bata wajen, hakan yabata damar wurga masa wani irin kallo sannan tace. "barek, kana bani mamaki". Yadan sha kunu ,yace. "Nafada miki banason kina jibgamin sunan katon aren". Tace " to niba don shi nake kiran ka da hakaba" ta kalle shi ,tace, "to nace yayana kace bako so, wai in nace maka yaya na sanya ka akwalba, to me kakeso ace?" Yace "to ga irin su HONEY,DEAR,MY LOVE da dai sauransu .koban chan chanci akirani da wadannan sunayen ba?" tayi dariya mai kara mata annurin kyau.tace. "to ai saikazabi wadda kakeso" yace ke yakamata kizabamin "shi kenan" tace. To fadamin inji Tace "kaji sanda na kira". Mah ta fito tace ,"kazo ka cikata da magana, baka barta tayi aikintaba". Yace , mah tayata zanyi" ta dan zaro ido kadan tare da girgiza kai. "Um- um nagode.zanyi abina ni daya". Yace , " Na kula ba kyaso mu samu ladan mu biyu ko???" . uhmmmmmm Mubarak da sulaihat ga kuma mustapha da izzatu kurma .ok in Free Mode. OK DANDALIN HAUSA NOVELS DAN..............WAYE ??? 1*4 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Ta murmusa tace, "Au da bakasan da wankin ba saidanazo inayi". Mah tace ,yauwa suhaila, fada masa gaskiya". Yace, " jiya nayi na baba , kema mah zanyi miki. Ita da bata iyaba. Wankin nata jika- jika ". Mah tace, "yafi min naka ". Suhaila cikin jindadi tayi masa gwalo, shine yayi murmushi yace . "Zan rama ne". A daidai lokacin da suhaila ta soma shanya .ranar agidan suhaila ta wuni ,sai dare direban yazo ya dauke su,tinin ranar sunyi shi a cikin farinciki suhaila saddiq fillo 'ya ce ga wani hamshakin attajiri wai shi Alhaji abubakar fillo, yanada matan aure uku. Hajiya hadiza itace matar sa ta lalle , ita ce uwar shuhaila. Duk 'ya 'yanta mazane su shida ras, ita ta bakwai. Suhaila ita kadai ce mace cikin dakinsu, saboda haka duk son duniya hajiya hadiza ta dora shi akan suhaila. Don yadda taci burin irin mijin da suhaila zata aura. Kunsan abin kishi, su abokan zaman ta duk sun au rar da 'ya 'ya mata, ita dai sai mazan ne sukayi aure, yanzu kuwa tasa ido taga wanne irin miji suhailan zata fito da shi. Halima mahaifiyar mubarak da hajiya dazija uwarsu daya ubansu daya. hajiya Halima tana da zumunci, don tana masifar son yayarta,itama hajiya hadizan babu laifi, don tana taimakon ta da abubuwa. Misali takan aiko suhaila ta kawo mata shinkafa,dankali,doya,taliya,har makaroni, ga kwancen kaya, wani lokacin ma har da sabo. Kuma 'ya 'yanta ta nuna musu girman kanwar ta a gurinta, don haka sun tashi suna son baba Halima kamar yadda suke kiranta. Sai dai tunda ta haifi Mubarak ya soma ce mata mah, su ma sai suka koma gaya mata mah din. Hajiya hadiza bata damu da shakuwar mubarak da suhaila ba, don ta san dole su so juna tunda 'yan uwane. Amma tunda suka girma sai ta soma tsorata da yadda suhaila ta damu da shi, don ita hajiya hadiza tafison suhaila ta auri miji mai arziki, don itama tace wane sirikinta ne. Shiyasa sam yanzu bata sakarwa mubarak fuska, tunda ta fahimci yadda yasa gaba. Suhaila saddik yarinya ce mai matukar kirki da karamci, gata da mutunta mutane .Halinta yasha bamban da mahaifiyarta. Don wani lokacin ma ita ke sanya umman nata yiwa 'yar uwarta hidima,musamman ganin su biyune rak, kuma tuni iyayen nasu sun rasu. Sai dai hajiya hadiza tafi mu amala da kawaye fiye da kanwar tata, sai dai duk da haka bata bawa 'ya'yan ta fuskar da zasu raina kanwar ta ba, amma sai ta shekara bata je gidan 'yar uwar ta ta ba. Ita kuwa Halima tana yawan zuw, da taga yar uwar tata na nuna gajiyawarta, saita itama ta janye. Don ayanzu danta Abbas bai dade da aureba, sam batasan komai akaiba, sai satin bikin ta aiko mat, ita kuma rananr bikin duk da bataji dadi ba haka ta daure taje, kuma danta da mijinta sun halarci daurin auren. Sam bata yi mata shisshigi ba wajen bikin, saboda komai na yan gayu ne, kawayenta ne akai, itama ba ta ce cikanta ba. Bayan la'asar ta bata abinda Allah ya hore mata ta tafi gida. Mah tana jin tsoron lamarin suhaila da mubarak don ta san zaiyi wuya 'yar uwar ta ta yarda da lamarin. Shi yasa sam bata kaunar taji yace zasu gidan. Ita kuwa suhaila in taje (school) in batada lacca sai ta taho gidan mah, shiyasa mah ta zuba ido don taga ya lamarin zai faru. Suhaila na zaune ita da mahaifiyarta a falo, sai tace. "umma nayi miki maganar samawa mubarak aiki naji kinyi shuru, Don Allah kisa baba ya sama masa aiki". Tace wai ke meya dameki da mubarak ne? Naga rawar kanki akansa tayi yawa ,bana son shisshigi". ta dubi umman nata tace. "rawar kafa? Kai umma ,mubarak fa nace?". tace "ko bala kikace ko halima".tayi (shock) ta dubi umman nata kamar zatayi magana,sai kuma ta fasa, wayar ta da ke yashe tana kara ta dauka ta gama amsawa sai ta kwanta tanayin 2go ita mubarak dinta. * * * * * Kamar yadda ya saba ganinta acikin mafarkinsa yauwa itace, ya farka ya tsaya yana tunani, gabansa ya ringa faduwa, abinda yakeji azuciyarsa yana ci gaba da jinsa . Yace, " Na shiga uku maganar mama gaskiyace ina sonta". Yace "wayyo! Nafada tarkon SO". Mustapha ya dade yana fadar shi bai ga amfanin soyaya ba tunda aka yaudari faisal wani abokin sa. Karamin hausa faisal yayi akan asma'u, shiya sanya yaji ya tsani mata, don yace sam basu da tausayi matukar sun gano kana son su ,shiya sanya sam bai rabar mace bare ace maganar soyayya ta shiga tsakanin su. Wannan yanayi da ya tsinci kansa yanayine da bai dace da rayuwarsaba ,basison rainin hankali, suko mata lamarinsu akwai raini. Ya dafe kansa yana fadin...... . Gaskiya harna fara jin haushin maman suhaila wlh uhmmm Allah sarki mustapha lalle akwai aiki agabanka kurma.OVELS DAN...........WAYE 1*5 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . "Allah na tuba, kada ka jarrabeni da son mace, macen ma musaka". Kai! Anya zata so shi? haduwar su da farko ya wanke mata fuska da mari ,anya kuwa zata amshi soyayyarsa? Ina ma zai ganta? Ko dai ba mutum bace? Alpha ya shigo da Sallama yana fadin. "musty, baccin me kakene? Ka manta za muje bikin kanwar anwar"? Yaja tsaki yace ,"kuje abinku, ni fa bana son sabga da mata". Allah yayi ja gwale". In da sabo sun saba ,su gasu yan son warwasawa, shi ne gidan su bashi da waigi. Duk motar dayaga dama yake hawa, amma sam shi babu chasu aransa.don a bayan idon sa cewa suke bai wayeba . Amma su alpha sun san in daukan wankane duk (group) dinsu yafisu iya sa kaya, illarsa daya mace bata gabansa. "Anya kuwa yanada lafiya?" itace maganarsu abayan idonsa, don ko irin dan biye- biyen nan da samari suke na mata shi Allah bai dora masa ba.kyaleshi da zafin rai, wannan kuwa halitta ce. Ya dubi Alpha , "da kai muke tare na mari wata yarinya?" ya girgiza kai, da " wan war ne. Yadai musty?" "zoka zauna". Yace da alpha. Bayan ya zauna yace. " anya ba mugun bakinku ya fada min ba?" yace ,"kamar ya?" ahankali ya furta mai rada ,yace. "sonta ya shiga rayuwata, ina zan ganta?" Alpha ya ware ido yana duban abokin nasa yana mamaki ,yace. "ikon Allah ,dama a rayuwar ka zaka so mace?" yace "wayeni daba zan zauna da maceba ?waye ni da zan so mace ba? Ni rainin hankaline kawai bana so, domin bazan daukaba. Ina zan ganta Alpha? Ka gaya min" Alpha yayi sauri yace, "A ina kuka ganta?" Ya dafe kai kamar mai nazari,ya furta. "titin yakasai,wajen get din makarantar shekara. Kai ! Ba anan ba, ina ga kamar titin nan daya shiga sabuwar unguwar yakasai. Kai! Inaga a nan muka hadu". Yace " zamu ringa yawan shiga anguwar ko Allah zai sa mu hadu. Kaga ,kayi wanka mu fita". " To ". Alpha ya fice, shi kuwa ya shiga wanka, ya fito ya soma shirya jikinsa. Kai mustapha in yana gayu tamkar yar budurwa, yanayin gashin sa da inda ya kwanta lif lif abin sha awa ne. Haka nan kyakkyawar fuskar sa gewayaiya, idan yana magana abin sha awa ,domin wushiryar sa kawai abar kallo ce ga shiryayyun hakora. Mustapha ya kammala ya fito sanye cikin lallausar shadda wacce taci aikin sama, anyi mata dinkin boda, hannunsa rike da hula. Ya shiga ciki mahaifiyarsa na zaune daya daga cikin luntsumammun kujeru, yace. "mamie , sannu da gida". Ta dauke kai tamkar batajiba ,gabansa yabada ra! Kada a koma yar gidan jiya . Mamie ta daga masa hannu , ya juya dai dai lokacin dayaji muryar mahaifin sa yana magana, yace. " Malam mustapha ina za a ne jikinka asanyaye?" yace, "zamu fita ni da abokaina ".mahaifin nasa yace. Yaya dai? Yace ba komai ya juya ya fice zuciyarsa kunshe da takaicin abinda mahaifiyarsa keyi masa. alh majid ya dubi matarsa yace. "Nikam kina bani takaici kina sa min damuwa alokuta da dama, saboda Allah meye boy yayi miki? Zamu bata, zaki dawo da halin ko?? Ka haifi da acikinka ka tsaneshi? Ke wacce irin mutum ne? Yaron mu yaro ne na gari , da bai gyagije ba ai da bai zama hakaba". "ka manta wuyar da nasha kafin boy ya ringa mu amala da al umma ya ajiye girman kai? Duk wannan nayi nasarar raba shi da su , to amma wannan zafin ran nasa yana matukar damu na....". Ya datse ta acikin tsananin fushi, yace . Wai ana sakewa mutum haline bare ki sake masa? Ni dai ina fada miki ita rayuwa ba a yi mata haka. Tun yana yaro baki damu da shiba har girma ma ,kada kifa dasa kiyayyarki acikin zuciyarsa, ance miki haka ake kunyar dan farin? Ke naki yayi yawa, shi daya fa muka mallaka. Tace, "To amma yan uwa sun haifamin, ko sun haifa miki ba kamar wadda kika haifa da kanki ba. Nan dai yai tayi mata nasiha akan rashin kulawar ta akan dan nata. "Ki kam bani mamaki, domin domin duniya a ayanzu kowa nasa yakeso, amma banda ke. allah kina kona min rai,zamu gauraya dake". Ta zumbura baki, "naji". Ta mike tayi ciki. Mubarak da shi da suhaila sun isa gidan hausa, inda ake kamun kawar suhaila, ko ince aminiyarta tun suna yara, kuma ga gida ga gida suke. Amarya surayya ibrahim umar ta hango..... . Tofa kaima mustapha banda rashin hakuri kayi ma mutun horn dai bai kauceba ai kasan ba kalauba amma yanzu kam zaka yabama aya zakinta ai saurin hannu bashi da kyau Allah ya tsaremu .S DAN........WAYE 1*6 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Shigowar su, ta sha kunu ta tabo kawarta nusaiba tijjani,tace. "nusy, king sai yanzu suhaila ta iso". Nusaiba tasa baki tace. "Allah ni wannan kawar taki haushi take bani, duk inda zaka ganta ita da wannan direban nata, ko ince dan rike mata jaka". Rukayya ta harari nusy ,tace zaki somako? Tace , "banson inga mace da namiji suna manne da juna matukar ba ma aurata ba". Tace ,kinada gaskiya sai dai nayarda dasu, ba yanda kike zaton suba". Nusy tace "Allah ya kyauta". Dai dai lokacin suhaila ta iso wajen. "ran amarya ya dade, da fatan ba ayi fushi da niba". Ta juya gurin nusaiba tace "yi min afuwa naga kin sha kunu". Ta dan kada kafada tace, "Ai in kina tare da wancan baza ki zo akan lokaciba". ta juya tace, " zo muje in sama maka waje". Ta kama hanunsa suka wuce inda taje ta nuna masa kujera, da yake sune manyan kawaye, ta tafi. Ya zauna yana kallon mata iri -iri ,ya hango 'yar kurma.yarinyar iya haduwa ta hadu gata da fara a. Yana kallonta tana gaisawa da jama a ya mike yaje su gaisa kafin yakarasa yaji tana fadin. "surayya ,kamu mukazo ba wai kula samariba. wai shin meyasa yanzu duk aka batamana addininmu, aka gurbata mana shi? Zuwa kamu ace sai da maza? Nikam ban da rukayya nada girma agurina da babu dalilin da zai sa nazo wajen nan". Jin haka ya sa shi ya juya, don shima ya hangi gaskiya a al amarinta. anyi kamu an tashi gfoma, kuma anyi (dinner) wacce anan kuma mubarak da mustapha suka hadu. Ko dayake su mustapha abokan ango ne, yayin da mubarak ya rako suhaila, wacce tana daga cikin manyan kawaye. Mustapha yanz zaune cikin abokansa, amma su gaba daya hankalin su na kan mata ,ko wacce shahi suke akanta. Ahankali yaji gun ya gundure shi ya mike,Amma agaskiya kyau da iya (dreasing ), da yadda ya dauki wanka ya dauki magana a gurin,yan mata sai fareti suke a (table) din da yake. Ya mike ya fita, alokacin suka hadu da mubarak ya shigo sun gaisa, yace. "kamar na sanka? Yace, "ba dai kamantaniba , ranan da ka mari kurmar nan". Take mustapha yakama hannunsa suka fice ,yace. Intambayeka mana yace, Allah yasa na sani yace, "kokasan sunanta?" yakada kai "A.a". To gidansu fa? Yace "bansaniba ,inda ka ganta inma haka na ganta". "Abokina, raina yana kuna,zuciya ta tana kunci, rayuwata ta baci duk dalilin marinta. Zan so inbata hakuri, na damu". Mubarak yace Ai shi dan adam girma ne da shi musamman aka ce mace .Ai in fada maka mace abace mai matukar daraja". "haka ne na kuma gano hakan arayuwa ta .tabbas hakan abune mai muhimmanci". Sun dade suna hira har suka yi musayar nombar waya. Gaba daya tare suka zauna ,ya nunawa manyan abokansa mubarak suka gaisa, lokacin da zasu tafi mustapha yace. Kazo mu rage maka hanya. Yace , a.a ai tare muke da kanwa na mah ce ta ciro wayar mubarak dake caji, tace. Ka ajiye waya ta dameni da kara. Ya karba yana duba (missed calls ) din sa ya gani yace . "kai ! Mustapha ne ". Tace " naso in dauka sai kuma na rasa inda zan danna". Yasa dariya yace "mah kin kusa in sai miki taki .Allah ya sa in samu aiki, duk sai na mayar da ke yar gayu". Ka dai ji da shi". Dai dai lokacin wayar tashi ta soma kara, ya daga yace ya akayi abokinaa? Yace "nayita kira da alama baka kusa". Yace "yanzu na shigo mah dina take fada min". Yace to kagaida ita kawai na bugo mu gaisa ,in kuma tambayeka labari. Don allah in har ka san inda yarinyarnan take ka taimakamin". Yace nafada maka ban san inda takeba ,amma zan cigita ". Sukayi sallama. Alpha da mustapha suna zaune kofar gidan su alpha suna hira, kanwar alpha ta fito tace yaje inji hajiya, yatashi ya shiga ciki, bai dadeba ya fito yace. Anje karbowa hajiya dinki,zan je in dawo kajirani ". Yace a,a saidai muje in raka ka". Sun iya karbar dinkin Alpha ya fice yayinda mustapha ya zauna acikin motar. Kamar ance masa ya kalli kofar shagon , itace suka fito gaban sa ya fadi don zahiri itace. . Uhmmmm harna fara tausayin mustaphaNOVELS DAN........WAYE 1*7 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . TSORO da fargaba suka dirar masa don ba sai ta soma yi masa gizo ba. Bakin sa dauke da addua yana rokon Allah ya sauwake masa wannan lalurar ,don shi a gurinsa soyayya lalurace. Yafito ya biyo su, sukuma suna son tsallaka titi,yana bayan su. surayya ta ganeshi, don ta kuma tabbatar shine wadda yan mata suka ringa nuna shi a bikin rukayya ibrahim umar, mutum mai aji sai bala in girman kai ta masa kallo shekeke dai dai lokacin ne izzatu ta kula da shi bakinta ya furta. "hasbunallah!". Suka tsallaka suka bude motarsu henesy suka shiga ,kafin ya farka sunyi mata (key) sun yi tafiyarsu. Ya dafe kai yana fadin . " ya salam!. Alpha ya kwalla masa kira ya tsallako yace. "alpha na ganta" yace wa? Yace yarinyar nan a ina? yace itace wacce suka fito yace kai muje wajen telan. Sun shiga shagon telan sun gaisa sannan suka gabatar da bukatarsu domin suna son sunan inda yam matan suke, musamman izzatu don haka ya dube su yace to saboda mezan muku bayani akansu?? Kurmace sunanta izzatu amma bansan gidansuba nine telansu. Ka taimakemu ka bamu lambar wayarta kai gaskiya intasan nina baka bazata ji dadiba. Sukace haba kataimaka kawu zizu yace kaga in na baku ban kyautaba. Wani abokin telan mai abin dariya abba alasan mutun ne mai barkwanci ga surutu yace. " alhaji nasan gidansu ni kawatace har cikin gidansu nake zuwa zan iya yi maka kamfen,amma fa biyana zakayi don kasan ba a aikin banza akano. Kawu zizu ya harareshi yayin da sani kike yace. Kagani abinda za ayi kawai ku kaishi meleysia yayi karatu. Gaba daya suka fashe da dariya har mustapha ya kule,saboda shi bayason rainin hankali. Su kuma gaba dayansu inzakayi zaman minti biyar da su to sai kayi tanadin maganin ciwon ciki. Shi alpha yasan halinsu yace abba alasan in zaka yi mana kamfen zakaje maleysia karatu Shi kam kawu zizu ya ha na lambar waya don yace bashi da ita haka suka hakura suka fita. Abba alasan yace kaji min mutum nima da zata soni sa kai zanyi. Ya basu dariya yace yar kurmafa ta hadu sai dai gayen akwai girman kai amma sun dace don har kama naga sunayi kawu zizu yana jinsu bai tankaba inda sabo ya saba da caftar su. * * * * * * * Suna tafe a mota yace Alpha yarinyar nan bazata soniba narasa ya zan fitar da ita araina. Ya shafi sumar sa tare da cije labban sa. Ya girgiza kansa yace. Mata yan rainin hankaline,Allah ya sani naso kawai iyayena suyi min aure ba wai inga mace ince ina sonta ba domin mata yan rainin hankaline, in sun gano kana son su ka shiga uku. Kaga wani mugun kallo da dayar tayimin? Daga ganinta yar tsurku ce. Alpha yace babu komai ni zansan yadda za ayi mu samu (address) dinta yadda mustapha ya gyada kai abin tausayi yana sauke alpha gida yayi cikin falon mami ya shiga ya kwanta ta fito ta ganshi ta ringa kallonsa tace "lafiya?" Yayi kasake mami na ganta yau tace wa? Yace ita din da na fada miki tace kayi mata magana ? Ya girgiza kai sai taji tausayinsa saboda gaba daya ya zama kalar tausayi yace mami baza ta soni ba. Momin ta zauna gefensa tace kayi hakuri ka nutsu saboda banason ka damu kanka kasan hausawa sunce matar mutum kabarinsa. Ka daure ka ringa cin abinci. Mami damuwata biyu ce na rasa me yasa kike min wasu abubuwa arayuwa nakam tsinci kaina da shiga kunci, mami kifada min duk abinda bakiso yanzu fa ba da bane mami ma ana na girma banason in sanyaki a damuwa. Ya kura mata ido ta dubeshi tace boy banason zafin rai yanzu ba gashi ka shiga damuwaba. Da baka nuna zafin rankaba hakan bazata faruba .inason kabi duniya a sannu. Yace mami na fahimceki zan kiyaye amma ina bukatar adduar ki domin batada hijabi ........ . Hmmmm tow nimafa zanje naga surayya ko maAUSA NOVELS

DAN ...........WAYE 1*8

.

Na ZARA'U BABA YAKASAI

.

.

Fibe star, wani gidan abinci ne daketitin gwarzo,

nan ne majilisar su mustapha inda anan suke

zaman hira. Bayan sallar isha suke zama suyi

hirar su, daga nan kowa yakama gabansa.

Mustapha ya taho zuwa majalisa sai yaga

mubarak ya yi (parking), yace.

"abokina ina zuwa?"

yace gida zani "A,A yana ganka anan kace kuma

gida zaka ?" yace "um" yace tow zo mutafi,

Amma bari inje inga wani abokina ,saboda nasan

yana jirana"

"kaje abinka banason in bata maka lokaci."

mustapha ya dan hade fuska yace. "mubarak wai

meyasa kake min haka? Ka san Allah shi yake

hada mutane ,in ba ka aminceminba shikenan ka

gaida mah".

Mubarak ya bude murfin motar ya shiga, suna ta

hira suka shiga wajen, acike yake da matasa irin

gayun nan, motoci kuwa agurin wannan na wane

waccan. Ya nemi guri yayi (parkin).

Sunfito ya samu kujera ya zauna ,shi kuma suna

magana da wanda zai gani. "mubarak bala"

ya juyo yace A'a saminu sabiu , rai kan ga rai?

Suka tafa ,sun jima suna hira sannan mustapha

ya dawo ,Nan fa suka zauna suna hira sai

shadayan dare ya kaishi gida washe gari da

mustapha yaje majalisa suka tambayeshi ina

abokinsa?

Yace "yana gidan su".

Sukace kaje ka taho mana da shi ,ya iya chafta".

Ai kuwa suka dauko shi ,tun daga ran nan ya

zama suna hira a majalisar tasu.

Rayuwa kenan mubarak da mustapha sun zama

abokai ,ta inda mustapha ya gano mubarak ba

shi da aiki. Ya karbi takardunsa ya nema masa

aiki a kamfanin mahaifinsa. Ya kuma samu

babban matsayi.

Mubarak ya samu aiki, yakuma shiga kamfanin

da

farin jini, domin yanada kirki da son al'umma, ya

kuma iya zama da kowa lafiya sannan shi bai

dauki kansa matsayin kowaba face dan talaka,

me neman rufin asiri.

Mah tafi kowa farin cikin samun aikin mubarak,

domin sun samu rufin asiri. Ya gyara musu

dakunan su da suke zuba haka ya gyara musu

soron gidan su wadda suke fargaba karya fadi

,an sumunce gidansu an gyra ko ina.

shima mubarak ya gyara dakinsa ya shimfida

kafet. Ya kuma sa katuwar katifa.yasanya tv. Da

DBD duk na kamfanin L G har kamaramar

(generator) ya siya.anyiwa gidan fenti, mah ta

dawo kamar amarya.

Malam bala yayi farin ciki kwarai, don burinsa ya

cika, ya kuma san ko yau Allah ya amsheshi tow

mubarak zai rike mah.

Tunanin mubarak shine, tunda ya samu aikin sa

wadda zai tsaya da kafafunsa ,ai zai nemi auren

suhaila. Akwai wasu page da suke satan wannan

labarin suke sawa apage dinsu batareda iziniba

acikinsu akwai mace taskar maza dan haka

sudaina tun kafin ayi wani abu akai.

Itama suhaila ta yi farin ciki kwarai domin

mubarak yayi mata alheri mai yawa samun

aikinsa.

Mah tace mubarak, in mustapha yazo yayi mata

magana su gaisa ,domin taji kaunar sa tun kafin

ta ganshi, saboda ya nuna wa gudan jininta so

kwarai.

Mustapha na zaune a madaidaicin dakin

mubaraka suna hira yaji shigowar mah, dayake

ta

shiga makotan su dubiyar 'yan kaciya.

Mubarak yace da mustapha.

Kazo mushiga ka gaisa da mah.

Yayi murmushi yace, "kai ,ai nayi girma da shiga

gidan mutane ,kace dai ina gaida ta".

Mubarak ya bata fuska,yace.

"baraka iya shiga cikin kejin muba?"."yanzu aina

nake zaune zakamin mummunan zato"?.

"to tashi muje"

yace "um -um ,kabarshi kawaiq".

Yace , "haba abokina haka zamu yi dakai?"

sun shiga gidan sun gaisa a mutunce ,hira sosai

suka ringa yi da mah, kaunarsa taji tana yi.

Shi kam mustapha gani yake bai taba ganin

mace mai kirkin mah na, don komai ta dauko ta

bashi. Wannan ya sanya mustapha ko mubarak

yanan ko baya nan zai shiga gidan haka kuma

yana yi mata alheri sosai, haka shima malam

bala yana jin dadin abotar tasu.

Mustapha ya dubi mubarak yace.

" ina tunanin yarinyarnan ba mutum bace, domin

ta shiga rayuwata ,don bana iya bacci yadda ya

kamata".

Mubarak yayi jim yana tunani, bai son ya raka shi

tayi musu wala kanci,domin shi har ga Allah

yana

kaunar mustapha. Ba kuma yason ayi masa

wulakanci. Sannan yadda ya fuskanta yarinyar

tana fa fushi,

Don ranta ya baci da marin da akai mata. Yana

tausayin mustapha game da tarkon so daya fada.

Yayi gyaran murya yace ,"mutumina ba kun hadu

agurin tela ba"? yace "um abun ne amma ai na

mika lamarin a gurin Allah". Da yake suna gidan

su mustaphane alpha ya karaso suka zauna

Abokan mustapha duk sun tsani mubarak badon

komaiba saboda mustapha ya fifita shi akansu

kuma su abokansane tun na kuriya shi kuwa

haduwar hanya kurum shiyasa sam in sun ganshi

basu fiye maganaba kuma su basa hira da shi

mai tsayi. sai in baya gurin su ringa kusheshi

agurin mustapha shima mubarak daya fuskanta

ya rage zuwa gurinsu sai dai in shi mustaphan

yaje.

.

Uhmmmmm mubarak anya aurenku da suhaila

babu tangarda kuwa.NOVELS DAN..........WAYE 1*9 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Misalin biyar na yamma suna cikin (goslow) kamar ance ya waiga, ya ganta zaune tana duba wata jarida. Yanda ya gansu a gurin telannan, gabansa ne ya fadi daya ga tana murmushi ,baisan sanda shima ya saki nasa ba. Shikam baima san an basu damar su wuceba sai da na bayan sa yayi masa(horn) ya duba, ita tuni sun wuce. Yana jan motarsa kai tsaye shagon telan nan yayi.yayi nasara babu kowa agurin telan sai Abba Alasan. Sun gaisa yace, "Nazo gurinka ,ka taimaka ka kaini gurin yarin yarnan". Abba alasan yayi dariya yace "wai yar kurma? Cabdijam! Gaskiya zan fada maka, na san gidan su, sai dai sam bata kula maza. ka ganni da raha ta nake yi mata wasa ,tayi min (warning) din babu ni babu ita.Amma zan nuna maka gidansu,kuma zan nema maka lambarta.kabani taka in na samu zanyi maka (text) din (number). Bari na rufe shago muje in raka ka gidansu" Ya rufe shagon ya raka shi yanuna masa gidan yayi masa godiya ,ya ajiye shi,ya bashi dubu biyar yace, "Ga wannan". Da kyar abba alasan ya amsa. Yana kwance cikin dakinsa kan doguwar kujera yaji shigowar (text), ya dauka yana dubawa,sai yaga abba alasan ne ya bashi lambar. Ya buga yayi masa godiya. Yace "Abba ,Allah ya kaika maleysia". Yace, amin. Kaima Allah yabaka yar kurma. "um-um abba, zamuyi fada dakai". Yace "haba alhaji ,akan me? Yace "bakasan sunanta ba?" Yace ,sunanta izzatu Yace "don Allah adaina kiranta da yar kurma yace "to nafada maka daya sunan da muke kiranta da shi ? Yace "fadi naji" Yace, sarkin kyau To dan Allah abba ku dai na kallonta Abba ya fashe da dariya yace naji zanna kiranta da izzatunta Yace abba nayi maka wata alkairi mana yace inaji. Yace innayi nasara zakaje maleyshiya yayi ihu yace "kace yan uba zasu mutu Yace su waye yan uba ? Kawu zizu da sani kike.Allah naje maleysia karatu sake su danyi don na daina abota da su" Mustapha yayi dariya yana mamakin barkwanci irin na abba alasan. Yace "nagode abba" Ai nine da godiya Mah ita da maigidanta suna zaune suna hira yace. Halima ,hankalina ya kwanta yanzu domin mubarak ya samu aiki.abinda nakeso ya samu iyali ko naga jikokina. Taji dadi tace kamar kashiga zuciyata,amma mu barsa muga iya gudun ruwansa kasan yaran yanzu komai nasu bisa tsari suke,don rannan muna hira yake fadamin cewar shi tsarinsa yafison ya mallaki gidan kansa koda bai mallaki abin hawaba yace baya sha awar haya. Malam bala yace banda abinsa ko wadannan dakunan ai sai ya gyara. Mah tazaro ido tace, Nikam malam bana sha awar zama da sirika bare shidan zamani yace to Allah ya taimaka. Ya dubeta yace,Ai naga kamar hankalinsa ya karkata kan suhaila Gaban mah ya fadi ,shin fitowa zatai ta sanar da mijinta yar uwarta bata bukatar wannan auren ko kuwa? Tace malam mudaici gaba da addua allah ya bashi mace ta gari. Mubarak na daukar karatu wajen wani malami ,sai dayaga mustapha sai ya fahimci mustapha malamine, domin azuwansu sai da malamin ya ragi daliban sa yasa mustapha na basu karatu. Domin mustapha yayi karatu sa a sudan yayi (digree) na biyu a madina ,yana da karatu arabi da boko haka nan shi ne shugaban kamfanin babansa.don komai na hanunsa. Tun abokan sa na jin haushin mubarak har sun hakura sun zama daya . Mahaifin sa ya riki mubarak ,ya amince masa kwarai da gaske ,domin ya auna shi saiya sameshi mutum ne mai amana Suhaila na matukar kaunar mubarak domin mahaifiyarta ta nuna mata sam basu dace da mubarak ba don ita matar manyace. Mubarak kuwa me yake dashi? Tace mami ina mamaki, wai samu da rashi bana Allah bane? kuma wannan aikin nasa zai rikemu". Ta doke bakinta tace zanyi maganin ki duk kyawunki ,duk ilimin ki, ki zauna gidan karamin mutum?bazai yiwuba. Idan mubarak yazo sai momi ta hana ta fita ayanzu ya soma tunanin rabuwa da suhaila .ba don komaiba saboda yana tsoron samun matsala a zamuntarsu kuma gaba za asamu matsala koda ya aureta saboda in uwa batason aure tabbas akwai matsala shi kuwa mubarak mutum ne mai tunani da hangen nesa, gashi da hankali. Shiyasa abin yake matukar damunsa.SA NOVELS DAN..........WAYE 1*10 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Yana zaune falon mustapha yayi tagumi mustapha yafito yana tashin kamshi.kayan jikinsu iri dayane, wanda mustapha ya siyo musu da yaje cairo. Ayanzu suturunsu iri dayne. Har ya fito bai ma saniba, ya dungure shi ya ce . "mubarak, lafiya?" Ya dago yace mekagani yace kanada damuwa yace ina da ita yace ina son suhaila to amma ba zan sametaba yace saboda me? Nayi tsammani yar uwarka ce? Yace mahaifiyarta bata sona haba atunanina yar mah ce. Yace saboda banda chanji. Mustapha yayi tsaki ya dubi mubakar yace Allah ya kyauta. Anan mubarak ya sanar dashi komai yace zanje gidansu yau don bai kamata ace ka hakuraba tunda kuna son juna, ai arziki na Allah ne. Kada kaji haushina,har naji bana son mahaifiyarta domin banason iyaye irinsu. Banson uwa mai idon cin naira,gata da kudi Kai mata mu rage mugun son kudi,don hakan ke sanya yayanmu cikin mugun hali yadafa kafadarsa yace ka nutsu zanje gurin suhaila. Izzat tayi shirin kwanciya kan (bed) dinta taji wayarta na motsi ,hakan ya nuna mata cewar (text message) ya shigo. Taci gaba da gyaran jikinta sai a lokacin surayya ta shigo ta dube ta. Kai anty izzat sai kace wata matar aure ke kullum sai kin dauki kamshi ta ko ina sannan zaki kwanta tace ke ni arayuwata inason kamshi fiye da komai don ina so ko juyi nayi inji kamshi na fita ajikina. Surayya tayi dariya itakuma izzat ta kwanta ta dauki wayarta. Sakon data gani yasa ta zuwa tsakiyar gado ta sake karantawa Izzat Ita zuciya tana son wadda yake kyautata mata haka zuciya na kin wadda yake munanamata sai dai zanso ace kin kasance mai yafiya mai afuwa akan mutumin da kike ganin ya zalunceki.kinsan Allah yanason masu yafiya. Izzat tayi jirgum tana mamakin wannan sako tayi kamar ta goge sai ta barshi. Da safe da ita sallah tana cikin shafa addua wayarta ta motsa sai da ta shafa adduan ta dauko. Salam Hasken idaniyata rayuwa ta kin hana zuciyata sakat bana iya bacc. Bana iya cin abinci komai nawa ya tsaya amincewarki nake nema dafatan kin tashi lafiya kin sanya ni cikin addu a. Izzat ta jima tana karanta sakon waye wannan? A ina ya santa waya bashi lambarta? Ta goge sabon sakon harda najiyanma tana fadin bazan yi soyayya ba nayi banji dadintaba. Taci gaba da sha aninta don bata sa abin aranta ba balle ya dameta haka bata sanar da kanwartaba kuma bata gaya ma mahifiyartaba Mustapha yana zaune yana jiran ko zata aiko masa da amsa shiru tamkar ya shuka dusa. Hakan ya sanya jikin sa yayi sanyi matuka bai hakuraba kullum zai aika mata da (text) sau uku ko fiye da haka bata taba bashi amsaba. Haka zuciyarsa na raya masa yaje gabanta tadi ya sameta to ammma ya san bazata saurareshiba. Yau kimanin sati biyu kenan .yau sam bai aika mata da sako ba yau weak end baya jin dadi ya damu kwarai ya samu izzat . Ya samu momi cikin kwanliya ta juyo ta dan dubeshi tace boy lafiya? Yace banjin dadi momi ina da damuwa. Tace bazaka rasa kanka da damuba. Ni fita zanyi zan kai hajiya gidan wani mai magani (wato babarta da bata da lafiya) momi ba nace ayi hakuri da zuwa gidajen magungunan nan ba? Sai tace ai shi sauki na Allah ne bamusan a in da waraka takeba mudai fatanmu mu samu nasara. Yace to Allah ya sauwake sai kun dawo Ya kwanta baifi rabin awaba sai yaji wayar mubarak yace ya shigo cikin gida baya jin dadi yace dashi aa shidai ya fito yayi masa sannu mustapha ya mike yaje ya sa shi ya shigo. Bai taba shigowa gidanba sai yau ya ringa kalle - kalle saiga Alhaji abdulmajid ya shigo sunjima suna hira har alhajin ya fita suna falo. Izzat tun dare bata ga (text) ya shigo ba sai taji ta damu domin ta soma sabo da kalamai masu dadi da faranta rai. Da safe ma shuru har biyu,sai taji ta kasa jurewa har surayya na tambayarta yau ko lafiya?bata dai tanka mataba ta kwanta kan kujera ta dauki wayarta ta rubuta masa........... . Uhmmm wai su yar kurma ma fa ankamu .DALIN HAUSA NOVELS DAN..........WAYE 1*11 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . SALAM! Yau ko lafiya? Mustapha ya sake dubawa ya ga sakon daga wajen izzat yake ,yaji dadi sosai.ya dade yana ta maimaitawa,ya yi kamar ya bata amsa sai yaki. Izzat taji shuru har lokacin bacci,sai taji da damu taji inama ace tana da kunne lallai da ta buga taji lafiya.anya izzat bata kamuba ? Ta rufa cikin bargo ta kasa bacci, akaro na biyu ta sake daukar wayarta ta rubuta. Salam! Nadamu da insan cewa kana lafiya ?ina son insan kai waye?ka taimaki zuciyata in samu sukuni don in yi bacci. Mustapha ya karanta ya kalmashe kafafunsa yana murmushi yaji sanyi cikin ransa ya rubuta mata Salam! Ina cikin tsananin damuwa domin ciwone ya dameni zuciyata na cikin tururi.bawani bane face masoyinki .ina son ki kwanta kiyi bacci mai dadi. Sakon na samunta ta tashi ta zauna tsakiyar gado tana mai da amsa Bazan iya bacci ba bansan sanda zuciyata ta damu da kai ba bana son inyi makauniyar soyayya,ka daure insan kai waye. Yayi dariya mai isar shi ya sake tura mata. Izzat na jima bana bacci kamar yadda duk dan adam keyi,sonki ya hana ni yin walwala kullum ina cikin farbaga.ni mai laifine agurinki fatana kiyimin afuwa. Ta karanta ta maida mishi Wanne laifi kake da shi agurina ?fada min sunanka kaji? Gani bana ji da zanso inji kalamanka ko na samu sanyi cikin zuciyata. Mustapha kalmomi sunyi masa dadi matuka ya jima yana karantasu ya rubuta mata. Ki kwanta kiyi bacci kada ki makara gurin sallar asuba. Ta rubuta masa Nakasa inason nasan kai waye? Ya mai do mata Dole kisan ko waye ni domin nine baban yayan mu da zakai haifamin. Nifa kurma ce kana sona ahaka iyayenka zasu barka ka auri naka sasshiya? Ya sake maida mata Ina sonki haka fatana ki amsheni a duk sanda mukayi ido biyu. Tsaki surayya tayi ta tashi ta kashe wuta hakan ya sanya izzat kwanciya tare da kashe wayarta Shikuwa mustapha yaji shiru sai ya kwanta yana hango nasara cikin soyayyarsu ko zai yi ? Muje zuwa... Da safe har shabiyu bata bude wayarta ba sakamakon aikin da suka tashi da shi na bakin da suke yi daga gombe kaltingo sai da yamma tayi wadda ta shirya alokacin bakin suka zo kanin mahaifintane yazo shida iyalansa da yake su a can suke da zama tana bude wayarta (text) ya rinka shigowa ta zauna tana aikin karantawa tana dariya hakan ya sanya surayya ta tambayeta wai waye keyi mata (text). Tayi murmushi tace surayya wanine kuma kinsan abin mamaki ina son sa fa yazanyi in shima ya kufcemin Sai taji tausayinta tace. Bazai kufce mikiba kinsan dama ance wani hanin ga Allah baiwa ne. Ita da surayya suka fito da kamal dan kanin babansu izzat ita da kamal suna hira surayya na bayansu. Mustapha dake gefe yaji wani abu yazo ya tsaya masa awuya yana mamkin waye wannan? Sai ya dauki waya ya rubuta mata. Waye wannan dakuke tafiya da shi? Nifa mutum ne mai kishi. Duk da atafe suke saidata karanta (massage ) tayi saurin juyawa tana kalle-kalle, sai taci gaba da tafiya har suka tafi inda zasu Suhaila ce tsugune gaban ya aminu.tace,, ya aminu ina cikin damuwa na rasa ya zanyi ?shine na yanke in sameka inji me zaka ce min?.... Taci gaba na rasa me mubarak yayi wanda mami bata son sa da tace baida aiki,to saboda Allah yanzufa ka duba yanda baba halima takeso mami da kaunarta amma ita mami ta fifita kawaye akanta uwa daya uba daya. ban dama ita baba halima mai mai karfin zumunci ne ai da tuni ba sa tare,wannan wacce irin rayuwace shikenan yanzu inason mubarak wai sai dai in auri tsoho saboda yana da kudi Aminu yace kinsanfa su iyaye sai dai abisu ahankali.kihakura kibi umarninta. Tace banki ta takaba amma ni atunanina zaman aure zamane na har abada bawai zama ne na wucin gadiba inason intambayeka rayuwa zata tafi (nomal) da mutumin da baka kauna? Yayi shuru taci gaba da cewa...... .

.

.LS

DAN.........WAYE 1*12

.

Na ZARA'U BABA YAKASAI

.

.

"Taya zuciyata zata kyautata wa mutumin da

bata kauna?

Yayi shuru ta sanya kuka tace

"ka fada min ta hanyar da zan shiga Aljanna

ahaka? Wannan itace biyayyar da zan wa iyayena

a matsayina na ya mace, idan nayi mata yadda

takeso na kuma kuntata wa mijina ta ina zan

shiga Aljanna.

Naji mami batason in auri mubarak ina so ta

barni in zo da zabina".

Ya aminu yace suhaila kinsan halin mahifiyarmu

kiyi hakuri kiyi ta addua Allah ya ganar ta ita.

Mustapha ne yayi {parking}motar sa gidan su

suhaila mai gadi shi ya sanar da ita tana da bako

bataso fitowa ba.

Mustapha na tsaye yana jiranta mami ta dawo

daga anguwa yayin da tace.

Wajen wa kazo kake tsaye kai kadai?

Yace nazo gurin suhailane

mami ta kalli shegiyar motar da yazo da ita ta

kalli shigar sa tace to bari a turota

a zaune take tace ke ba kiranki akeba?

Ta zumbura baki.

Tace sai kije kiga wadda yazo matshine da gani

ya fito gidan ni ima. Da fatan bazaki watsa min

katsa a ido ba.

Badan suhaila ta so ba ta shirya ta fita ganin

mustapha yasa ta saki fuska tace sannu da zuwa

yace ni da tunanin lafiya nake?

Tace aa mustapha ai laifin ka ne sai kace min

kaine?

Yace ya gari tace aa muje ga guri ka zauna ta

kaishi gurin da take sauke bakinta ta kawo masa

ruwa da lemo, saannan ta zauna ta gaida shi

tace ina hasken idaniyata ka taso kai kadai?

Yace ai jiya yazo maigadin ku ya hanashi

shigowa ke kuma yanzu ba kya zuwa ki gaida

mah".

Tace ankammala karatu ya zanyi?

Ya dubeta tace tow zamu turo don asan bada

wasa mukeba.

Taji sanyi aranta

inta mahaifinta ne babu matsala matsalar a gurin

mahaifiyartane.

Tace mustapha Allah na rasa wannan matsalar

zanyi shawara da yayana.

Yace okey Allah yasa muji alheri

sunyi hira sosai daga karshe suka yi sallama.

Mubarak ne zaune gaban mahaifiyarsa suna

tattauna maganar sa da suhaila.

Mubarak yace

Dama nifa na hakura da batun auren suhaila

domin bazan auri macen da mahaifiyarta bata

sonaba.

Mah tace hakan shi yafi

yace ai mah bazan sake zuwa gidan suba har

abada tun da an sa mai gadi ya hanani sgiga.....

Kamar anjehota daga sama ta shigo mahaifiyar

suhailace tace.

Halima suhaila dai yatace to bazan bawa dankiba

domin bazan sai da akuya tazo tana cimin

dangaba ki fada masa ya rabu da yata mah tace

haba yaya nayi zaton duk dayane.

Tace aa biyune kwarya tabi kwarya.

Ran mag ya gama baci tace

shikenan yay kije ki aurawa suhaila karuna.

Ke nizaki fadawa magana?

Tace an fadamiki in wata tsiyar kike min daga

yau kidaina .don ana girmamaki si kiga kamar

tsoronki nakeji?

In kawayen naki ne suke turoki su nuna miki

wanda ya fi dacewa da suhaila

amma kin san yata ba matar talaka bace

bakiji abinda naceba ?cewa nayi taje ta auri

karuna.

Malam bala ya shigo aa hajiya hadiza lafiya?

Tace kayiwa matarka da danka magana subarmin

yata

tabdijam !amma duniya ta lalace don hadiza kinyi

faduwar bakar tasa.

Ashe bayan babu halima bazaki rike mubarak ba

dan dan uwanka?

Kai wannan abu da ban mamaki yake.

Kawai sai mama ta sanya kuka yayin da hajiya

hadiza ta fice daga gidan

mubarak dai har akai akagama bai tanka ba

amma yana jin radadin abinda hajiya hadiza tayi

masa

suhaila ce zaune office din mubarak hawaye

wani na bin wani akan yayi hakuri akan abinda

mami dinta tayi masa

yace kiyi hakuri suhaila inasonki ba wai bana

sonki ba aurena dake akwai matsala ki auri

wadda mahaifiyarki ta keso.

Inason mah fiye da komai banason a bakanta

mata domin ni daya Allah ya basu ni zan zame

musu hasken idaniya gaskiya in ana taba min su

tabbas akwai matsala.abinda nakeso dake

suhaila maganar soyayya tsakanina dake ya

wuce sai dai zumunci.

Ta share hawayenta shikenan mami tayi nasarar

taba kaunau mu wacce muka ginata tun kuruciya

anyi zalunci a tsakanin mu ta mike a zuciye ta

fita.

Surayya da izzat suna hira har da mahaifiyarsu

{text} ya shigo wayar izzat

salam

dazu na ganki ke da surayya kin saka doguwar

riga kunyi shiga tamkar arab kun shiga sahad.ko

in lissafa miki abubuwan da kika siyo?

Gabanta yafadi ayanzu ta soma tsorata anya

kuwa bada Aljani take soyayyaba komai nata ya

sani duk inda zaka ya sani.

Anya kuwa mutum ne?

Batasan sanda tace umma, anya ba da Aljani na

haduba ?

Suka fashe da dariya kudaina dariya lamarin nan

akwai ban tssoro

surayya ta karbi wayar ta kira shi yana dagawa

yace.

Hello surayya

gaban surayya ya fadi tace waye kai?

Yace masoyin izzat ne ni

mazai hana ka bayyana kana agareta

yace lokaci bai yiba

tace ya sunanka

masoyin izzat

waya baka lambarta ?kuma in tambayeka mana

yace inajinki

kai mutum ne ko aljani?

Ni mutum ne kamar ke.......

.

Uhmmmmmm tab lalle da aiki agabana irin

wannan tambayoyin damma ba sauranyinta bane

tow nikuma innaje wane irin tambayoyi zatamin

kenan

.DAN WAYE? Book 1 part 13 Posted by Bashir Sani Fesan on 25 Dec 2016 - 23:00 Mustapha ya kan turo mata da kudi awaya in ya bushi iska ya aiko da {shopping} da kayan kwalliya.sun damu da su ganshi su san ko waye don izzat da damu da shi sosai tana son sa amma bata taba ganinsa ba. Wai dama ana haka ?zuciya takan kamu da son abinda bata sanshiba? Tafiya ce ta kama mustapha zuwa cairo ya so atura mubarak don yanzu mubarak shi ma na keta hazo don yanzu ya sai filin sa ana yi masa gini.ya mallaki lifan dinsa ayanzu yayi shar da shi. Izzat ce suna tsaye bakin titi zata tsallaka ita da surayya sai taga mubarak yayi {parking},bata mantasgiba ta saki murmushi tace. Kai dama kana garu yace ke zan tambaya ya hutu? Tace yana gurinku ina mutuminki wadda ya mareki? Ta dan sha kunu kai za atambaya. Yace yace in gaida ke kuma yace in baki hakuri tace to sai anjima da alama baka so mu gaisa. Tace surayya wannan shine mutumin da nake baaki labari Allah da gaske nake zamu zo ni da shi mu baki hakuri. Tace bari mu shige kada mai gidana ya ganmu ni da kai domin yana da kishi. Suka tsallaka. Suhaila rayuwarta ta shiga kunci don ta daina ci da sha yadda ya kamata duk ta rame domin mubarak ya sake layn wayarsa kuma in taje gurin baba halima bata ganinsa ita kuma tana jin kunyar ta tambayeshi. Wata irin makauniyar soyayya ake tsakanin mustapha da izzatu don ita bata sanshi ba illah takan siffantashi azuciyarta shi kam duk wani shige da fice na izzatu akan idonsa takeyi. Tafiyar da yayi yana dawowa wanka kawai yayi ko abinci baiciba yaja mota zuwa kofar gidansu kamar ta san da zuwansa ta fito cikinkwalliya riga da wando ne ajikinta dinkin pakistan kalar {purple}ya amsheta sosai gashin kanta tufki daya tayi masa ya sakko adakin wuyanta kanta babu dan kwali.mayafintashara shara ne fuskarta asake. Yana mota yana kallon ta taji haushin rashin dankwalin da bata saba duk kowa kallon kyakkyawan gashin kanta yake. Ya ringa siffanta laushin gashin a zuciyarsa ya ringa jin uwa ya fito ya bayyana mata kansa. Ya lumshe idanunsa budewar da zaiyi ya hangota ta nufi lifan din wani matashi fuskarta cike da fara a.yana kallon su kishi ya kamashi yaji bazai iya jurewaba ahankali ya sauke gilas din motar sa ya kira wani yaro yace kai zo ya samu takarda ya rubuta waye wannan mekuke cewa na dawo ,sauka ta kenan nazo ina farin ciki na ganki da wani,na fada miki mesonki mai kishin kine mustaphanki yace maza kaima izzat yaron yace yar kurma yace eh yana kallo ya mika mata yana mai yi mata nuni da kyakkyawan motar.kamshin takardan ya doki hancinta a gaggauce ta karanta shi kuma tuni yabar wajen. Kai tsaye ta juya ta nufi gida tana jin haushin saddiq .abokintane shima kuma ya nuna yana sonta sosai ita kuma ta dauke shi a aboki don ita da tace ta hakura da soyayya. amma ta rasa yadda akayi son mustapha ya shiga cikin zuciyarta. Taji haushin kanta don da yau taga sanyi idanunta. Tana shiga ta dauki wayarta ta tura masa{text} tace barkanka da sauka cikin kasa mai ni ima zuciyata tayi nisawajen begenka kada kayi tunanin komai an halicceni saboda kai kowa zaka ganni da shi karkayi shakka kai kadaine cikin zuciyata ba wani saikai. ka daure na dawo ko zan samu nutsuwa izzat. Yana gama karantawa yaji dadi ya lullubeshi ya dinga {kissing} wayar saboda jin dadin kalamanta wai rai dangin goro ashe itama yar kurma ta iya soyayya? Ya koma gida ya shiga suka hadu da mahaifinsa yace ina kaje ne haka daga dawowarka ko gurin mubarak kaje ga su alpha sun shigo ka fita Yayi murmushi da tsallen sa ya fada kan kujera ya lumshe ido yana mai ajiyar zuciya dad dinsa yana kallon sa yace ko ta mafarkin aka gani ido biyu? Yayi murmushi yace daddy ka tayani da addua nakusa cimma burina adduarka nake bukata momi ta karaso tana fara a ta ce wani lokacin Alhaji in kana yi min fada akan yaron nan sai insha mamaki jifa dadewar da yayi amma wanka yayi ya fice ai ya zauna musake gaisawa. Daddy ya kalleta ke anje an gano surukarki zakiyi korafi mustapha yace daddy wayace maka can naje ai nina sani naga yanzu ta daina zuwa a mafarki da alama an ganta a ido biyu sai kazo ka bani labarin yadda kuka sasanta tunda ka bata mari ya ringa dariya yana shafa sumar kansa aa daddy na kasa bayyana mata kaina ina dai zuwa kallonta akofar gidansu daga daddy har mami dariya suke suna kazama gwarzo ka yarda kai namijine. Ka fita filin daga namiji baya tsoro. Sai yaji sun kara masa kwarin gwiwa,har yana jin zai iya tunkararta. Suhaila ce kwance falon gidan su suna hira da umma kishiyar mamin su sallamar yusrah taji da tsallenta ta mike ta rumgumeta tace yusrah sannu da zuwa murna suke yusrah yar babbar yarsuce da suke abuja tayi karatune a london don acan aka haife ta har ta girma shekarun su biyu da dawowa nigeria. Yusrah bata karasa suhaila ba amma kuma jininsu ya masifar haduwa don sun kulle. Babu wanda yasan tsakaninsu sai Allah.SA NOVELS DAN.........WAYE 1*14 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . . SUHAILA ta sauki yusrah yadda ya kamata sun kulle dakin suhaila ,ta bayyana mata halin da take ciki tace kinga kibini mu wuce abuja sai munemi inda yake aiki. Hakan ce ta faru sun kulla son suhaila har ta tambayi abbanta ya kuma barta. Sun shirya zuwa gidan baba halima sai da suka biya sahad suka dan yi mata siyayya sannan suka wuce kofar gidan. Wata jibgegiyar mota suka gani yusrah tace ko yana nan ne naga mota kofar gidan?tace yusrah kenan ba motar sa bace mutumin da keda lifan? Ta dan kada kafada suka shiga ciki. Dayake yammace suna zaune tsakargida kan katuwar taabarma mah ce ita da mustapha da kuma mubarak suna shan rake dai sai lokacin sukayi sallama suka amsa musu mubarak yayi kicin -kicin har mustapha ya fahimta mah tace sannun ku da zuwa ta nuna musu guri suka zauna ya mutanen gidan. Tace suna lafiya sunce a gaida ke mah da kanta ta mike ta kawo musu ruwa ta kawo musu rake tace ga rake ku sha kun same mu muna sha gaba daya hankalin suhaila a tashe yake ganin nuna ko inkula da mubarak yayi mata ta daure ta gaida su suka amsa yusrah da tunda tazo take satar kallon mustapha don tace ita wai dama maza suna da kyau. Tana kallon lafiyayyar fatar jikinsa wacce ta gogu da hutun jin dadi ga wasu irin ido da takeso a rayuwar ta. Tsoro ya kamata Allah yasa ba shi ne mubarak din ba. Suka hada ido da mubarak sai taga shi din ma babu dama don ya hadu. Mustapha ya dubi mah yace mah inaga in da anyi raken gwangwani Allah bakaramin karbuwa zai yi ba kinga mutum ya huta da tauna. Mubarak yace kai ai ka tauna rake shi ne dadinsa amma in ka kurbe ai ya zama {juice}. Mah da suhaila suna dariya yusrah ta ce. Ai abu ne mai sauki sai a ringa mace maka mah tace rabu da su santi suke mustapha ya dan kara nutsuwa yace mah ba fa santi muke ba hira ce tsakaninmu mah ta mike ta na cewa suhaila bakuwa kukayine? Tace lah baki gane yusrah yar gidan ya binta ba? tace ina zan gane ta ai bansanta ba ko ba wadanda suke kasar turawa ba? Tace itace ta wuce daki ta barsu. Suhaila ta kashe murya tace barek wai me nayi makane naga kamar ba kai murna da gani na ba. Kai mustapha kaji abinda tace mustapha ya dube ta sosai sai yaji ta bashi tausayi don ya na tausayin wadda zai afka ga zugin so don ya shiga ya san zuciya bata samun nutsuwa har sai tayi katari da abinda takeso so ba wasa ba don yasan ji da kai da girman kai da akasarin yammata suke fama da shi amma ga shi ita ke zuwa lallai tana son abokin sa. Ya dan yi murmushi ya dubi suhaila yace madam yayi murna da ganin ki mana.ta dubi mustapha tace yanzu barek baya sona ya sake layi saboda ni, baka fada masa ba kyau yanke zumunci bane?? Tabbas kinyi gaskiya saboda me ka sake layi ya dubeshi yace kai saboda Allah kaga yiwuwar soyayyarmu? Katuna girman mahaifa duk da nagari bashi da kamar su.to amma akan ki an sawa mahaifiyata damuwa ni kuwa banga amfanin soyayyar da zan yi ta bata ran mah ba. Iyaye na bani da matsala da su to amma a yanzu soyayyarki ta kawo musu matsala. ke fa yar masu kudice gwanda kije ki auri dan gidan karuna wani irin gumi ya ringa fesowa a jikin suhaila rayi shuru uwa wadda ruwa ya cinyeta. Shi kuwa mustapha sai yaji ransa ya baci da furucin abokinsa ai duk wadda yace yana sonka yafi wanda yace yana kinka. Lallai abinda yayi awai wauta da karancin tunani .ko ko tsananin bacin ransa ya nuna akan abinda akayiwa mahaifiyarsace oho yushar ta budi mustapha tayi wani irin rudadden murmushi wanda tafe yake da sakon nuna kauna tace kanajin abokinka anya akwai adalci acikin furucinsa ina ji akwai cin fuska kwarai da gaske ma ganin ba mu cancanci afada mana haka ba. Sai lokacin mubarak ya fuskanci yayi ba dai dai ba ya kuma kula da sauyin fuskar abokinsa. Suhaila ta mike tace bari in yiwa mah sallama ta aje mata ledar tace zamu tafi tace kin gai da su amma daga zuwa haka? Tace ai sauri muke ta fito tace yusrah zo mu wuce har sun isa soro mustapha ya biyo su yace babu sallama zaku wuce kayi hakuri na kula abokinka bashi da adalci ko kuma wata ya samu oho amma nidai nasan ina sonsa zan cigaba da son sa ko wani na aura wannan son yana dankare acikin zuciyata amma kuma ni suhaila bana daga cikin mata wadanda namiji zai wa gori. Zan jure ciwon sa daga yau ni suhaila in barek yasake ganina gidansu ya yanke min kafafu. Mustapha da yasan suke da laifi sai yace haba suhaila kada kuyi biyu, duk kaninku kunyi fishi in daya ya hau sai daya ya sauko sanin kankine ba laifin sa bane kiyi masa uziri . Mahaifi ai ba wasabane kin san taba mutuncin mahaifi ai ba wasa bene kiyi hakuri kuzo na kai ku koda mota kuka zo? Yusrah tace da mota muka zo sai naji ka burgeni kana da sanyin hali ya dubeta yace kece mutum na farko da kika yabeni wala Allah don baki san hali na bane.amma ki rabu dani bani da kyau ko nayi wanka . Gaba daya suka yi murmushi saboda tasan raha ne tace haba duk kyallin fuskar ka ya shafi fuskar yace kai namiji da kyalli ai abun bazaiyi kyauba mata sune aka sansu da kyalli. Sai da ya gasun shiga motar su sannan yusrah ta mika masa wayarta tace kasamin lambar ka kila mu kulla zumunci ya amshi wayar ya sa mata ta amsa tayi {saving} ya juya ya shiga ciki yana shiga mubarak ya ringa dariya yace daga rakiya sai kuma ka dade? Ya sha kunu ya suri ma kullin motarsa ya fice shima ya biyo shi.ALIN HAUSA NOVELS DAN...........WAYE 1*15 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . izzatu ce a zaune a falo yayin da surayya ke mata kitso kitson yayi kyau sosai hannunta anyi jan lalle haka kafarta tayi kyau sosai ummansu ta shigo tace. Ke surayya ko kishi bakiyi ki kalli izzat mace sosai amma ke kafa fara sol gashi kullum babu kisto tayi murmushi dai dai lokacin wasu yara suka shigo da manyan jakunkuna suka aje umma tace ku daga ina sukace wai inji mustapha surayya tayi saurin mikewa tace yana ina sukace ai yana bamu ya wuce tace ya siffar sa take? Yaro daya yace kai surayya mai kyau ne gashinsa irin na indiya ga wani irn ido kada kice nayi karya yafi salmankhan kyau daga umma har surayya suka dinga dariya to jeka mun gode. Suka soma zuge jakakkuna abin gwanin sha awa kayane masu daraja da kyau umma tace izzat kina sonsa? Ta rufe fuskarta surayya tace Allah koda can izzat bata soyayya ba wani nan mustapha ya samu karbuwa. Mustafane cikin wata lallausar shadda yar ubansu dinkin ya zauna ajikinsa aikin sama {half gown} ne yanayin gyaran gashin kansa ya dace da shi fuskarsa acike da walwala ya fito falo dad dinsa na zaune yace boy sai ina yayi murmushi yace zanje filin dagane daddy kayimin addua na daina tsoro mahaifn sa ya dinga murmushi sannan yace ina ji ajikina zata soka zatayi alfahari da samun mijin kwarai domin kai dan albarkane ya shafa kansa yana mai jindadin kalmomin mahaifin nasa ya dubi momi yace zantafi tace ka gaidamin ita ubangiji ya baka sa a yayi adduar fita daga gida haka da zai shiga motarsa yayi adduan hawa abin hawa ya nufi anguwar su izzatu. Tafe yake yana kada kansa yana bin wakar mawakiyar nan maryam fantimot da wakokinta dakeyiwa fiyayyen halitta babu wacce bashi da ita yayi alkawarin in bakinsa yazo itace zata cashe masa agurin {dinner} mustapha ya isa gidan yana jingine da motarsa kirjinsa na dam dam yan magana sukace faduwar gaba asarar namiji ya dauko wayarsa ya rubuta mata gani nazo ina kofar gidanku yau nazo mu fuskanci juna tana dubawa tayi wani irin tsalle tana kiran surayya sai dai kash surayya na bacci ta tura masa gatanan zuwa ya jirata izzatu aka shiga gyaran jiki ta dade tana ruwan ido akan kayan da zata sa sai daga karshe hanunta ya dauko wata doguwar rigar ta shadda ce hade da wani material wadda yanayin sinkin kawai inka kalla kasan yaci kudi wani shegen ta kalli ne a kafarya a kalla kudin sa dubu sha biyu yayi {matching} da mayafin ta haka da lips stick din bakinta ban da {shinning}babu abinda yake ga wani wayataccen kamshi da takeyi ta gama haduwa umman su tace izzat kinyi kyau tace nagode umma mustapha ne yazo zan fita tace sai kin da wo. Ta shige umman yayin da kusan ince umman ta fi izzat murna don ita kanta tana son mustapha duk da bata ganshiba lallai tanajin sonsa acikin ranta tana ganin ba karamin soo yake yiwa yarta ba sai dai basu san dalilin sa na boye fuskarsa ba ko da yake ai ta san duk daren dadewa in dai mutum ne dole ya fito ya bayyana kansa don ciwon so ba abin wasa bane ta fito gwadas da ita kofar gidansu ta hangi lafiyayyar mota ga wani matashi ya juya bayan sa ba a ganin fuskar sa saboda haka zuciyarta bata yakinin mustaphanta ne ta karasa cikin irin taku na rangwada irin na rantsattsun yan mata turarukan su suka hadu suka bada wani daddadan kamshi ahankali bakinta ya furta a salamu alaikum Amin wa alaiki assalam ya juyo sukayi ido hudu bakinta na rawa ta furata kaine......kaine wa? Badai kaine mustapha naba? Kai ne mutum na farko dana kasa manta cin fuskar sa agareni kaine mutum wanda ka kasa yafiya agareni. karya kake baka sona kazo ka cuce nine kawai ka cuci rayuwata ta yadda kasan yan makauniyar soyayya ta inda na kamu da so da kaunarka batare dana ganka ko naji sautin ka ba nafa maka tun farko ni din mai lalara ce bana ji zan iya magana kamar yadda kuke ciwon ya sameni da girmana mutumin daya kasa yin hakuri dani a hanya taya zai aure?kada ka manta shima aure ana hadashi da hakuri kai kuma da alama baku ko hada hanya da hakuriba. Dai dai nan surayya ta fito ta karaso cikin fara a da farincikin ganin mustapa amma yanayin da taga izzatu sai tayi turus! Ki dubeshi bai ko ji kunyar yaudarata ba ki dubeshi wai shine mustaphana bayan ya fallamin mari ta juya gida a guje surayya ta dubi mustapha sukayi cakare cakare da su uwa wasu zakaru tace sunnu ya murmusa idanunsa sunyi ja wur ya dubeta yace zanzo ace kinfiskancenidomin ki fahimci makomar rayuwata so dayane tak wallahi izzatu na bawa nasan a farkon gani na da ban kyauta mata ba inso a matsayinki na yar uwarta ki wayar mata da kai a tun sa ar dana mari abar sona hasken rayuwata na gaza samun farincikin rayuwa gaba daya na kasa sukuni sai dana binciko inda izzat take ina sonta ina kaunarta itace farin cikin rayuwata itace jin dadina ina sonta zan iya hakuri da ita a duk irin yanayin ta inasonta so mai yawa ba wai so kadanba idan ta ce bata sona lallai ne rayuwata ta tashi a aiki surayya ta dubi aji da kai irin na mustapha sai taji tausayinsa . Wai zafi biyu kenan ta sunan wani littadi ta san abin ya zamar mata biyu don ga son mustapha ga kuma kinsa a cikin zuciyarta mutum daya to wanne zai rinjayi wani . gaskiya harta fara ban haushi wlh yakamata amasa afuwa ai shima banda abinsa naka sasshiya kurma uhmmm so kenan .DANDALIN HAUSA NOVELS

DAN.......WAYE 1*16

.

Na ZARA'U BABA YAKASAI

.

.

Ta murmusa tace kaje duk halin da ake ciki zan

kiraka awaya ta

uhm bazan iya tafiya ba don bansan halin da

izzat take cikiba kije ki gano min irin halin da

take ciki ki kuma kamanta adalci kada ki fada

min karya surayya baki yi kama da mutanen

banza ba.

Tace to ta juya

izzat da uka ta shiga falo ta fadawa umma tsoro

da fargaba suka cika zuciyar umman,tana

tambayar ta lafiya?

Sai kuka shine amsar har surayya ta shigo.

Umman ta dubeta meke faruwane

tayi murmushi tace ba kowa bane illa mustapha

wadda ya mari izzatu.umman ta zabura, don

babu ranan da bazata yi zancen marinba dukda

ba shine na farko ba amma tana yi masa kallon

mugu azzalumi kuma marar hakuri.

Umman tasu tace ikon Allah dama ai ance

inzakayi so kayi dan Allah hakama in zakayi ki

kayishi dan Allah makiyi na iya rikida ya zama

masoyi haka masoyi na iya zama makiyi

ta kama kan yartata tana girgizawa yayin da ta

dago tana mai furtawa ahankali ita kuma ta

nutsu tana kallon bakinta.

Kiyi hakuri kibi komai acikin nutsuwa ta yiwu

mustapha alheri ne atare dake .ki tuna komai

mukaddari ne ki sanya haka Allah ya tsara

haduwarku ta farko.

Tace umma bashi da tausayi babu ruwana da

mustapha zan yakice shi acikin raina.

Ta mike zuwa dakinta ita kuma surayya ta sanar

da umma yadda sukayi tace.jekicemasa an

rarrasheta yaje abinsa ta mike in da ta barshi

anan ta sameshi kafin ta iso shi ya karaso yace.

Yaya? Meye labari?

Tace uhmm umma ta rarrasheta yace godiya

nakeyi wa umma zan tafi sai gobe zan dawo ki

kular,in da ita ki daure ki sake rarrashinta.

Ya juya ya tafi kai tsaye gida ya isa a falon mom

ya yada zango ya kwanta.

Ya fita masallaci bai shigoba sai da akayi sallar

isha.

Afarfajiyar gidansu ya hadu da alpha yace

oh mutumina

yace ya gari

yace kai dai bari an doka andoka min guduma

aka

sun zauna gefen dakin mustapha alpha yace.

Meke faruwane? Yace alpha dama nace bazata

soniba tace nidin marar hakurine tow wai ya

zanyine kunyi {facing} din junane yace kwarai

kuwa

yace to gobe inzakaje in ganta

yace ayi haka kuwa ? Uhmmm Allah ya hadani da

mugun ciwo alpha yayi murmushi ya mike yace

zan wuce gida inje inci abinci zaka fita majalisa.

Ya kada kai .au na manta yaufa mutanenkane

zasuyi wasa ya shafa kansa yace kai anata kai

wayake ta kaya?

Alpha ya fashe da dariya yace

mata masu gari

yace af ka manta DR yakasai yace mace yar

kunama ce?

Ya sake fa shewa da dariyar mugunta yana cewa

abokin nasa

kallon ka zo hannu indai mace ce

cikin jin haushi mustapha yace jeka gida kaci

abinci ka dawo

yayi gaba yana mamakin Al amuran mustapha

izzatu a yanzu duhun da take ciki ya yaye don

tagano da wa take soyayya sai dai har yanzu

tana jin mustapha aranta.matsayi biyu ya hau

tana kinsa domin ya kasa gano matsalarta ko ko

ya gano jin kai da izza ya sanya shi ya bata

mari?

Lallai akwai artabu sosai.

Ta tashi zaune tsakiyar gado ta ringa tariyo

abubuwan da suka wuce lallai rayuwa akwai

artabu acikinta sai ta sanya kuka har ta bani

tausayi.

Tana son mustapha kam ya shiga mata zuciya

sai dai har yanzu akwai haushin marin da ya

falla

mata .

Suhaila ta shiga da muwa na rashin samun

kulawa daga barek dinta wai dama akwai ranar

da barek zai iya nuna mata halin ko in kula to

shi

ma namiji yabi maganar mahaifiyarsa bare ita

mace?

Tasan mubarak ya fita gaskiya anya zat iya

hakuri da shi maminta ta sameta tayi nisa cikin

tunani tana tayi mata magana amma bata jiba

saboda haka sai tace ke lafiyar ki kuwa?

Ta dago kai arazane tace mami ba komai

tace da komai mana ke banda tsiyarki badai kina

batawa kanki lokaci kan matsiyacin yaron nan

ba?

Ta zubawa mahaifiyarta ido tana mamakin

furucinta sai kace ba dan yar uwantaba.

Tace ki tashi ki shirya kina da bako kuma kika

sake naji wani abu sai ranki ya baci sosai sha

sha sha ana nuna miki inda zaki huta kina janyo

wa kanki wadda bai da shi ba shida kuma hanyar

samu ko kina tunanin dan abin da ya samu zai

sa na amince.nifa banda ra ayin wannan auren

gwanda ki fidda ranki akai ki gane

ta gyada kai ta fita.

Suhaila tayi dana saanin zuwanta abuja saboda

wani makocin gidan su yusrah ne tunda ya kyalla

ido ya ganta shikenan ya rikice,domin matarsa ta

rasu sakamakon hadarin mota yaronsu daya

khalid musbahu muhd dan asalin garin gombene

bafillatani.

Yana da uku uku a fuskarsa mutum ne mai fara

a

kuma ya dan manyanta

ta shirya ta sameshi a falo an cika shi da kayan

cima iri iri bata yi mamakiba saboda sanin halin

maminta.

Ta ringa watsa masa kallon raini da wulakanci

shikuma yana yi mata kallon kasan ido ya gani

amma dayake yana sonta sai bai nuna ya ganiba

yace

ranki ya dade barkanki da yini

ta shareshi sai da tayi shuru kamar bata jiba ya

sake maimaitawa sannan ta amsa

yace inata zumudin ki amma sai naga kamar

bakiyi murnan gani naba.

Ta yamutsa fuska tace

kusan haka din kenan

yaji zafin maganar sosai wayarsa ta soma

{ringing} ya dauka yace.

Hello my boy na sauka yace yanzu haka ina tare

da auntyn naka.DAN......WAYE 1*17 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . YA dubeta yace, khalid ne ke gaida ke yace inbaki. ta amsa ba don ta soba yaron ya gayar da ita yace (next) in daddy zaizo kano zan biyo shi in ganki. inason ki,saboda daddy yace kinada kirki kinada kyau zaki kula dani tace to shikenan khalid,sai kunzo din ta bawa mahaifin nasa sukaci gaba da hira har suka kammala. Bayan ya kashe wayar yace kai khalid na sonki tace "uh" yace inason khalid saboda yaron na da hankali ga kokari ga hakuri kin san bayan rasuwar marwa nayi aure ta wahalar da shi duk sanda yaji ance zanyi aure sai yace shi kam in mayar dashi gombe . Musbahu dai ya ja ra ayinta sukai ta yin hira akan khalid. Musbahu ya samu karbuwa sosai gurin mamie ta inda yayi ta barin abin duniya har ta kai iyayensa sun zo tambaya suhaila ta samu mahaifiyarta a cikin (bedroom) dinta tace "mamie" ta dubeta yayin da take kokarin rufe zif din kayanta ta aje kayan data dauko kan gado ta mayar da hankalinta kan suhaila tace. Inajinki kinyi shuru ke nake sauraro.tace mamie gaskiya bana son musbahu mubarak nakeso .kinsan bazan iya rayuwar aure ba shi ba. Ta ce koh? To bari kiji ko uban ki atafin hannuna yake bare ke ,in kinga an fasa to kece ba ki da rai ,ke din kwalli daya mace inga samu inga rashi? Wallahi baki isa ba kada in kara jin kina yi min maganar mubarak dan matsiyata me suke da shi? Tace mamie atunanina dan yar uwarki dan kine da kenan amma a yanzu muna zamani daga kauri sai gwiwa? Taci gaba da shirin ta tace. Zanyi aganin hamima ba mubarak ba dannasan ita ke sanya shi saboda kwadayi.ina so kekuma daga yau ki sa wa ranki kin zama matar musbahu mamie na yarda zan auri musbahu a dalilin inyi miki biyayya amma ba na son sa .ina rokon alfarma agareki ki taimakeni ki hakura ka kije gidan baba halima domin zaki sake sa masoyina ya tsaneni kin san mubarak baya son damuwar mahaifiyarsa tuni shi ya fita daga harkata nice na nace. Ta harareta tamkar ta rufeta da duka don haushi tace amma kuwa kinzama sauna banda kedin yar banzace me zakiyi da shi? Ai komai kyan surarka in baka da kudi baka haduba amma zanyi maganin abin fice ki bani wuri sokuwa mai ban haushi. Mamie taci gaba da shiryawa dakanta ta dauki mota ta fita sunyi da wata kawarta larai zasu unguwa to sai dai ita laran ita yar rakiyace kuma kuma sai bayan ta fito take sanar da ita yanzu haka suna hanyar bida sun sami labarin wani malami mai zafi acan. Ta kunduma mata zagi tace. Amma kinsan inada matsala da wannan yarin yan shine kika ki gayamin.tace nima yau nasamu labarin kinsan ku masu maza kuna da matsala ba kamar mu falan baya ba tace tow shikenan in kinje kibashi waya zanyi masa bayani,inyaso ko ta banki sai in turo masa kudin tace shikenan. Tana kashe wayar ta kai tsaye gidan kanwarta ta nufa. Mubarak da mustapha suna zaune tsakar gida da yake lokacin zafine sun fito da fanka. Mustapha ya rufe idanunsa tamkar mai bacci shi kuma mubarak yana yima mah barar gyada. Mamie ta yi sallama ta shigo tana wani taku tana wani yiwa gidan kallon she keke . Halima na ganinta haka gabanta ya fadi don ta san ba da Alheri ta zo ba. sannu da zuwa ta fada ta mike shigo daga ciki ta yamutsa fuska ba zama nazo yi a wannan akurkin gidan naki ba. Jin haka ya sanya mustapha bude ido taci gaba da cewa. Na zone in gaya miki ki gayawa danki nayiwa yata miji babu shi babu ita ni bana son kwarzaba ko dole ne hadin zumuncin? Ina dacewar kaska da gwano?nazo in sanar miki ta samu miji danda ko direbanta yafi danki matsayi ita kam tana jinta ta kasa yin komai saboda tsabar mamaki mubarak na kallon mah dinsa sai yaga ashe kuka take.aiko ya zabura yace wai nine nace miki ina son suhaila? Ni ban ceba,don Allah mamie ki daina aibata min uwata tun da bama zuwa maula. Tayi sororo ta kasa cewa komai tace. Kinajin danki zai min diban Albarka? Mustapha yace ki zo ki fita don mah ta haifi karfi,yanzu zamu iya gwab gwabjeki ba ason yar taki in kin isa ki aureta, mara zumunci da zarmewar zuciya. Mamaki da storo duk sun dirar wa mamie tace. " to kai kuma awa?" "karemin kallo daga sama har kasa, ba karamin mutum bane ba alfahariba gidanki akurkine akan gidanmu. Ya nuna mah kinga wannan yanzu nake jin sonta da kaunarta acikin zuciyata ta ko bayan ran mubarak zan kular masa da mahaifiyarsa kuma ko bata haifi mubarak ba a yadda take da kuma kyan zuciya lallai kowa zai amsheta ya kuma riketa ba tareda ta tozartaba amma ke in ba naki yayan lallai kowa zai juya miki baya bantaba ganin mutum mara zumincin kiba kin san muhimmancin zumunci kuwa? Don Allah ina kiranki da murya mai karfi ki san matsayin mah agurinki kisan muhimmancin zumunci domin zumunta abace mai matukar muhimmanci.kinason shiga cikin hakkin Allah domin Allah shi yace ayi azumunci duk mai yinsa kuwa ranar kiyama zai zauna cikin inuwa wacce ba kowa ke maza ba sai mai zumunci. Mamie ta yi shuru ta kasa cewa komai illah juyawa a fusace tana kunkuni wanda ko ni berngees banji me tace ba bare nayi muku tsegumi. Mah ta dubesu tace kunada hankali kuwa ?yar uwa tace faSA NOVELS DAN...........WAYE 1*19 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Mustapha da mubarak sanye cikin lallausar shadda wacce taci aikin senegal sun masifar haduwa.suna cikin mota ash kalar shaddar tasuma ash ce suna tsaye bakin get din gidansu izzat .izzat sanye da hijab mai hannu ita kuma surayya tana sanye da riga da siket ta dora doguwar riga (after dress) akai. Sun zo sun shigesu kadan mustapha yace . Sannunku jin muryarsa yasa surayya ta juyo tayi murmushi tace a a kune? Ya gyada kai tamkar marayan da yake neman agaji tayi murmushi ya tsira mata ido ki rarrasar min rayuwata tayi murmushi taji ta amince da son da yake yiwa izzat lallai duk ajinsa da girman kansa yayi sanyi. Shi kuwa mubarak ya tsaya da izzat ta kalleshi cike da hargagi irin na kurame tace . Me ka rakoshi yayi a gurina ko kunzo ya rufeni da dukane ?na kula ku masu kunne ba ku tausayin marasa ji sam ba kwa yi mana adalci ta inda ba kwa ajiye komai ba sai gulma da munafurci ku sani in mubama jinku Allah yana jinku. To yanzu me kuke nufi dani ?so kuke ku kashe ni don na san ba wai son gaskiya ya kawo shi gurina ba yazo ya cimma wani burin sane kawai sai ta fashe da kuka ta juya ta shige gida. Kai tsaye falo ta shiga umma na kwance sai ji tayi an fada mata tace.. Izzat lafiya tace mustaphane ta rungumeta tana lallashinta. Ita kuwa surayya tana tsaye da mustapha ya bata tausayi yace yanzu ke baki shawo min kanta ba?hakika na wulakanta mata masu sona gashi nima na tsinci kaina da son wacce ba zata soni ba ina tausayin rayuwa ta. Ta kalleshi tace kayi hakuri ka san yanayin rayuwa sai a hankali na san izzat tayi soyayya da kai a waya makauniyar soyayya domin tana son mustapha haka tana kin ka adalilin marin da kayi mata ni dao abinda nake tunani shine kayi hakuri ka rabu da ita ka samu wadda ta dace da kai wani irin kallo yayi mata yace. Surayya ashe baki da hankali ba kida tausayi bakisan irin kalam da ya dace ki fadamin ba zaki iya kisan kai fa don zucita zata tarwatse ne sosai ta inda zan iya mutuwar farat daya dai dai lokacin mubarak ya karaso ta dubeshi tace ka lallashi abokinka don izzat bazata so shiba idan yana sonta na farko kurmace dole sai ya koyi hakuri zai iya zama da ita.sannan anya ma bazata satsala da iyayensa ba bana son rayuwar izzat ta shiga hadari domin ita din abar tausayi ce don da ba kurma bace daga baya ta tsinci kanta ahaka. Kuyi hakuri zan yi duk iya bakin iyawata don ganin na rarrasheta zamuyi waya ta juya agur guje tayi gida sun jima atsaye mubarak ya kama kafadunsa yace abokina kada ka damu komai mai wucewa ne kaji? Ya gyada kai dan bashi da bakain magana mubarak yaja mota suka nufi gida suna (parking)suka samu su Alpha a wani kebebben waje da suka saba zama mustapha ya fito yayi ciki mubarak ne yayi wajensu alpha yace lafiya kuwa mubarak? Yace rh tow lafiyar kenan gaba daya suka wuce dakinsa abin mamaki suna shiga suka ganshi cikin bargo yana rawar dari. Lafiya?? Suka hada baki suna tambayar sa yace sanyi nakeji zazzabi ya kamani zuciyata tayi kunci inaji ajikina rayuwata ta shiga hadari ina ji ajikina wani abu zai faru dani to menene? shi ne abinda bansaniba duk sunyi kasake babu wanda ya iya cewa kaomai jikinsa yaci gaba da bari mubarak ya zuba masa ido ya ja kafafu ya zauna a daf da shi yace abokina kada kasa kanka amatsala ka da ka damu da mace har ka yi wa rayuwarka illah yaushe ne zaka damu da wacce baka da tabbass duk yadda zaka so mace itafa bata gani ni ka ganni nan mace bata daga cikin abinda zan sanya ta araina ta dameni don ni gaba daya gaba daya tausayi rayuwar ya mace take bani. mustapha ya daga masa hannu yace kada ka rugurguzamin kwanya da maganganunka masu zafi da ciwo mace aba ce mai daraja domin ina girmama soyayya.ya zaka dinga magana kamar wanda baka fada tarkon soba ? Don Allah ka kyaleni inji da abinda ke damuna domin mace abar asotace a kula da ita abar agirmamata ce abar ayi mata komai a bata kulawa dama dukkan gata. Ka tuna mace itace ke bamu dukkan kulawa ita ke daukar ciki cikin laulayi da wahala bata bacci cikakke so da kauna ta danka wa danta ta hana cikinta ta bawa danta. Kan mace zan kwana ina baka kyautaci na ya mace kuma ban gama ba me irin wannan halin zakace kada asata arai mubarak kaso kanka da yawa ban zaci haka daga garekaba alpha yace to anji an yarda ka kwanta ka huta bari in kawo maka magani ya kudundune jikinsa sai karkarwa yake.wani matsanancin tausayi ya kama barek ya kasa tunani take ya mike kai tsaye gidansu yar kurma ya wuce yana tsaye yana neman yaro amma bai samu ba can yaga wata dattijuwa zata shiga gidan yayi sauri yace hajiya ta juyo ya kwashi gaisuwa yace najima tun dazu bansamu yaroba don Allah in kinshiga ki turomin surayya. Tace to ta shiga cikin minti uku kacal sai gata tana ganinsa tace aa dawowa kayi ? Ina abokin naka yace zuwa nayi mu kawowa kanmu maslaha wallahi mustapha ya kamu rashin izzat zai iya salwantar da rayuwarsa .yanzu haka yana cikin wani hali ki fada min gaskiya shin kina ganin ba zata soshiba?ina tsoron rayuwar sa ta samu nakasu ki bani amsa. Ta kalle shi tace mubarak ta yaya zan baka amsar da ban saniba ?saboda niba nice zuciyar izzat ba bansan meke ranta ba hakika ada nasan taso mustapha so ba dan kadan ba...... . Tabb lalle akwai aiki mustapha ta bare da kai kaima amma fa yar kurma kema kikula dan ba a walakanta masoyi .NOVELS DAN........ WAYE 1*20 . NA ZARAU BABA YAKASAI . . Domin babu abinda yafi mata dadi tamkar ta zauna tana hirar sa,tana siffanta shi.to amma kuma ta tsani mustapha saboda ya wulakanta ta ,ta jima kafin ta fidda abin da yayi mata .amma me zai hana mubarwa Allah ikon sa ma ana mu zuba mata ido? Mubarak yace mustapha yana sonta yanzu ma yana cikin wani hali ni kawai ina so ki kiramin ita tace kayi hakuri tana cikin kuka har yanzu rarrashinta umma take. Ya waina hannunsa ya dunkules ya girgiza kansa yace. Shikenan zanyi duk iya yina don ganin na ceci abokina daga fadawa tarkon so ko ince koshin wahala .zan roki Allah ya cire masa son izzat ya yi masa sauyin alheri kila sonta ba alheri bane a tare da shi shiyasa hakan ta faru ya juya a fusace don zuwan nasa bashida amfani surayya ta tsaya tana kallonsa cike da takaici ta juya ummansu tace waye yazo? Tace mubarak din mustapha ne. Lafiya? Tace eh to wai mustapha ya shiga mummunan yanayi shine yazo yaji yaza ayi ?ni kuma na ce suyi hakuri sunemi wata umma tace saboda me? Tace saboda bata sonsa umma tace karya ne kinsan izzat na son mustapha don tace bazata iya rabuwa da shi ba ya zaki ce ya hakura? Tace aa umma mutum ne yayi maka laifi ya baka hakuri kaki to ya zai yi ?ki kyaleta. Ashe duk izzat na kula da bakinsu tana fahimtar me suke cewa tace surayya ya zakice ya rabu dani? Kin san girman son sa azuciyata ?kin san yadda nake jin kaunarsa?dole in nuna masa girman laifinsa a gurina ina jin nima in na rasa mustapha hakika zan iya rasa rayuwata. Surayya tace oho miki nikam na ce ya rabu dake.ai kinga yadda yan mata ke sonsa yana share su. Zazzafan zazzabine ya rufe musty, momie tana tsaye akan sa tana kallon yadda idanunsa sukayi jajir harta bargonsa yayi zafi sosai dadynsa yace sannu ya duba agogo sha biyu da minti biyar na dare ya yiwa DR kabeer waya ya sanar masa.yace zan turo Dr yaseen ya zo ya ganshi. Alhaji abdulmajid yace bari kawai in kawoshi don jikin nasa ya dan yizafi okey shikenan alhaji sai kun iso Nusshu Clinic & maternity shine asibitin Dr kabeer shine kuma (family Doctor) dinsu asibitinnasa yana da kyau ga manyan likitoci duk wani babban likita dake kanon dabo to yana da ranar dayake ganin (patiensts) a can. Da isowarsu aka karbesu akayi ciki da su cikin kwarewa da aikin su dr yaseen ya kula da shi cikin lokaci kankani ya gano damuwa ce ta yi masa yawa don gashi har jininsa ya hau sannan bugawar zuciyar sa ya sauya nan da nan ya dura wasu allurai cikin ruwa ya sanya masa sannan ya yiwa Allah bayini.mamaki ya kama shi yace tow me ya damu mustapha? Baikoma gidaba gurinsa ya kwana ko da gari ya waye bai bar asibitinba sai wajen tara yana isa gida a zuciye ya isa dakinta wai ke wace irin macece danki mu tafi da shi cikin tsananin ciwo amma ki kirani a waya ki tambayi jikin sa kin gaza?hka ake dan fari?wallahi indai haka zakiyi yayanki ba za su soki ba wannan wane irin sha shan cine? Ta tabe baki haba alhaji ba gaka a gurin ba? To meye zanyi masa zan bashi lafiyane? Yayi kafa yace hakika yanda kike nuna rashin kaunarki ga mustapha wani cewa zai yi ba danki bane yayi kwafa ya shige. Ko ajikinta don irin mutanen nanne da basu sanya da cikin zuciyarsu.ita babu abin da ya dameta tun abin na damun mustapha har ya hakura .shiyasa yafi son baban sa?don yafi kulawa da shi ya fi bashi soyayyar iyaye. Bayan ya fito yana tsaye a farfajiyar gidan Alpha ya shigo. Alhaji yace bakatafi aikiba?yadda mustapha ya fiku kula da aiki. Alpha yace naje na dawo ne na kira mustapha a waya (switch off) jiya na barshi bashi da lafiya shi yasa na kasa hakura na dawo yace yana asibiti jiya acan na kwana yanzu ma zan zan wuce. Yace amma dady ba a sanar min ba?abune cikin dare yace shiga ka karbo abincinsa ya shiga ya fito da kwandon abinci da wasu hadaddun kuloli aciki ya sanya a bayan mota yace muhadu dady bari in dauko motata yace okey yaja motar ya tafi mai gadi ya bude masa yana cewa a gaida mai jiki ayi masa sannu ubangiji ya bashi lafiya yace amin. Ya nufi asibitizuciyarsa cike da takaicin halin matarsa ai ko dan riko aka dauko ba naka ba shakuwa wani abune. Mustapha ya tara halaye na gari wadda jama a ke yabon sa shi dai bai son raini haka akwai shi da girmama duk wadda ya girmamashi.matsalar sa daya rashin hakuri amma dole ya kawo karshen wannan halin nasa,don yanzu hakurin sa ya kure akan irin wannan halin ko in kula da take nunawa gudan jininna su tal daya . Har alokacin bacci yake ko da alhaji ya shigo ya shafi kansa yana jin kaunar dan nasa a lokacin alpha ya shigo ya zauna. Alhaji yace wa zai zauna. Yace gani mana tace office dinfa? Tace nayi signing kuma na nemi excuse. Yace zan wuce ina da (meeting) da wasu ma aikata na,amma muna fitowa zan zo inaga anjima hajiya zata zo yafice. Alpha ya kura masa ido tausayin sa ya kamashi don tun suna yara suke tare babu wanda yasan tsakanin su sai Allah haduwar mustapha da mubarak ce tasa abotar su tayi sanyi don Alpha baya son ganin mustapha ya fifita wani akan shi.shiyasa shi ko shiga sabgar mubarak bayayi amma saiyaga mubarak yana da kirki da kyan hali shiyasa saya watsar aka zama duk abokai alpha ya jima a zaune har dr yaseen ta shigo suka gaisa yace ya farka kuwa. Yace aa nidai tunda nazo bacci yake yace ai nasani domin baccin muke bukata yayi domin zuciyarsa da kwakwalwarsa su huta. Amma nasan daga yanzu zuwa wani lokacin zai iya farkawa da zarar ya farka sai ka kirani sukayi susabaha Dr yaseen ya fita sai biyu da kwata ya farka ya bude idonsa yana kallon dakin. Ya gano cewa a asibiti yake ya zauna ya kalli alpha yace tun yaushe nake anan? Yace tun jiya ya mike tsaye ya ce ina (brush) dina? . Uhmmmm gaskiya izzat tana ban haushi sai naji da nine uhmmm ruwan bagaja kawai zanje nafadaLS DAN...........WAYE 1*21 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . ya tashi ya dauko masa,ya matsa masa makilin .ya shiga ya watsa ruwa ya sanya wando (3 quater) yasa (t shirt) ya sha (tea) din da alpha ya hada masa sannan ya mike yayi sallah. Ya jima yana kan sallaya yanata addu oinsa kamar jira ake ya sha akayi sallama yan gidan su momin sane sun kai su takwas har da kakar su momin sa mai kaunar sa.ta karaso inda yake tace mustapha sannu da jiki ,ance min bakaji dadiba.na tashi hankali na don ban shirya takaba ba. Suka tin tsire da dadariya alpha yace kaji hajiya shekaru dari biyu ma nan gaba muke saran ki. Ai kam da an gaji da ku tace ni kam ko banza nayi gerona na gumba .alpha yace baki yi asaraba ki dama kunu kiyi sadaka. Dai dai lokacin faisal da anwar suka shigo. Wai har naji dadi mamie tace kana asibiti duk mun tsure ashe ma kasamu. Alokacin ya mike ya hau gefen gadon ya zauna sukaci gaba da kwasar hajiya suna dariya.da yake sun saba duk juma a suke zuwa gidanta cin dambu da danwake ko tayi musu dashishi ko burabusko har tubani ma yi musu take. Sai la asar tace to bari in koma gida in an sallameka shikenan in kuma ba asallameka ba sai gobe me zantaho maka da shi? Yace tuwon dawa miyar danyar kubewa. Alpha yace ni gaskiya hajiya ba tuwo ba. To waye mara lafiyar? Abinda nakeso shi za akawo tow maye mai ginyar? Mara lafiya ai baya cin abinci mai jinya shi yake kwasar dadi hajiya tayi murmushi tace kwa karata ni kunga tafiyata faisal yace bari nazo in kaiki gida . Tace ai ina tare da direba.ta kalli mustapha tace ina tunanin yau kanwar ka weesal zata dawo. Ya dan yi murmushi yayinda gabansa ya bada dam!yace Allah ya kawota lafiya ta juya ta fita biyar na yamma ciwon kai irin na bari dayan nan ya damu mustapha ga abokai da yan uwa wannan ya shigo wannan ya fita yana kwance yana jinsu hayaniyarsu ta dameshi a lokacin likitoci biyu suka shigo suka gaisa duk matasan suka fita. Dr yaseen ya dubi mustapha yace ya jikin ya rumtse ido yace Alhamdu lillahi ya dafa kansa meke damunka? Yace ciwon kai mai tsanani bana son surutu duk sun dami mutane. Ok sannu ko ya janyo V.P ya auna hawa jininsa yayi yace dr shuriem dan duba ka gani ko idonane bai gani dai dai ba shima ya gwada ya ja tsaki yace mustapha me yake damun ka wadda gashi har jininka ya yi mugun hawa dole masu damunka zamu hana kowa ganinka akan me zasu hana ka kwanciyar hankali? Ya duba takardan jikin gadon sa wadda (case) dinsa ke rubuce ya kara rubuce rubuce ya fita ya dawo yayi masa wasu allurai sun jima suna yi masa tambayoyi har bacci ya gaba da shi Alokacin Alhajin ya shigo suka gaisa dr yaseen yace alhaji bamu bukatar yan dubiya domin jininsa yayi irin hawan da bamaso da alama ya jima da damuwa a tare da shi don ciwon yayi karfi. Alhaji ya rangwadar da kai yace to Allah ya kawo sauki sukace amin da likitocin da alhaji tare suka fito alokacin dr shureim ya kalli alpha yace. Alpha dan Allah a hakura da yan dubiya ko in sunzo ku zauna awaje yana bukatar kadaici . Abokin ku yana fama da ciwo ku kuna ta hira da da tsautsayi sai ya fadi baku saniba duk sukayi (shock) suka wuce su dole sauran abokan suka wuce. Alpha shi kadai ne a zaune shima a waje Alhaji yace alpha wai meke damun abokin ka? Yayi shuru yace inaga akan yarinyar nan da yake sone to amma koma meye mubarak yasani.ni san yanzu na tuno da shi inaga bai sani ba da tuni yazo alhaji yace barin inje gida sai bayan sallan isha yana tafiya Alpha ya kirawo barek a waya ya sanar da shi su na nusshu hospital. Suhaila ce zaune tana kallon su yusrah suna ta faman zuba kayan rabo wasu manyan jakunkuna masu dauke da hoton ango da amarya ko wacce jaka akwai saitin kayan kamshi da atamfa da agogon bango duk dauke da hoton ango da amaryi sunyi mugun kyau . Bafilatanin gombe ne yana da uku uku irin na gombawa jikin sa amure dan gayu sosai amma in har ka kare masa kallo hakika zaka san bana yau bane amma kallo daya ba zai baiyana maka shekarun saba wasu jakunkunan set din silba ake zubawa da farantan tangaran da jug yanayin yadda ake zuba kayan rabon zai nana maka yar masu kudi ce sosai haka shima mijin ma mai kudine. Surayya ibrahim ta shigo tana fadin ina amaryar ne? Sai naji an daga barek an dan karashi da kasa kawai suhaila ta fashe da kuka tace nace bana son sa barek nakeso anki yarda za a hadani da wannan tsohon. Rukayya tayi wuri wuri don tana da tsoro sosai aa suhaila kada inzo ace nina zugaki da can baki yi kukan ba ,kiyi hakuri kila hajiyar ki ta gano miki alherin dake baki hango shiba iyaye fa babu yadda zaus yi su zaba maka abin da zai cuceka don Allah kada ki nunawa yan (school) dinmu dole akayi miki ta share hawayenta tace kowa za abani baikai kyan barek ba baikai addininsa ba bai kai shi tsoron Allah ba haka bai kaishi sona ba wannan fa maganar da kike abu ne a duhu babu wanda yasan gaskiya sai Allah.bari in mike in tafi. Yusrah tayi murmushi tace da banyi niyyar sanya muku bakiba amma yanzu rukky ace mutum yaki ci yaki sha ?duk wadda yayiwa iyayensa biyayya ba zai fadi a banza ba kema yayanki zasu yi miki.wanda kike abin nan akan sa baya sauraranki baya saukar wayarki. Kinsan wani abu rukky jiya na ganshi yayi jawur da shi yayi kiba alamar babu abinda yake damunsa .kuma rukky bantabaji ance namiji ya fada rijiya ko kashe kansa akan mace ba sai dai mace tayi wannan shirmen.to su mazan tawakkali suka fimu ko biyayya suka suka fimu ya kamata mata su farka daga wannan nannauyan baccin da suke yi. . Uhmmmmm tow nidai nawa fatan zaman lafiya mai daurewa awannan auren na suhaila amma fa yazama dole naje aurennan saboda naga yusrahVELS DAN.......WAYE 1*22 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . RUKAYYA tace gaskiya ne yusrah mace ta fi namiji zurfafa a soyayya .kuma maganarki tana kan hanya suhaila tace ana samun namiji mai zurfi a soyayya bari in tuna miki labarin laila majnun.yana cikin rukunin matafiya suna tafiya ya ga kare ya sauka daga kan abin hawan sa ya kama karen ya rungumeshi yayi masa wanka ya gyara shi da aka tambayeshi saboda me yayi haka? Cewa yayi karen yayi kama da karnukan garin su laila gaba daya suka bushe da dariya wato bama karen laila bane kama yayi dana garin su laila.lallai yayi zurfi suka bashe da dariya to kunce na mimiji baya zurfi shiya yayi? Su ai larabawane au kunaso kucemin bahaushe bai san soyayyaba? Kuna nufin kuce iyayen mu ba a soyayya suka same mu ba?aa bamuce ba kiyi hakuri ki kaddara Allah bai nufa mubarak mijin ki bane ban yardaba momi batason in auri barek insha Allah sai yayi arziki sai momi ta gano cewa dan uwanka duk lalacewar sa duk talaucinsa dan uwankane. kiyi hakuri mustapha damuwa biyu ce agareshi yadda soyayyar izzat ke damunsa ga shi kwanakin sa uku cikin asibiti amma baiga idanun momiba wai saboda me? Sai yaji idanunsa nayi masa yaji. Wai meyasa take watsi da lamarinsa?yana cikin wannan halin mubarak da mah da baban sa suka shigo yana duban su sai yaji tamkar an wanke masa zuciya cikin fara a yace mah? Tace yarona me ya dameka ka rame? Ta karashe maganar cikin nuna tausayawarsa. Tana son mustapha kwatan kwacin yadda take yiwa mubarak. Ya jikin naka?malam bala ya tambayi mustapha da sauki baba. Mah tace yaron ka da kai ina zaka samu hawan jini?komai ya faru da sanin Allah duk abinda kayi hakuri zai shige tamkarma ba ayi ba kada ka janyowa rayuwarka nakasu tun kana yaro karami ka ganni babu abinda zan sanyashi a zuciya ta ya dameni inyini ko in kwana da bacin ransa Don Allah ka zama mai tawakkali akan duk hukuncin da Allah yayi maka sai yaji zuciyarsa ta karye sai yaji hawaye na sauko masa mubarak ya dinga gogemasa yace mah na gode Allah da kuka shigo cikin rayuwata ina ji ajikina ku kun zamar min barin jikina.don Allah ku tayani da addua Allah ya yimin maganin abin da ke damuna. Malam bala yace zamuyi maka addua amma sai ka saka ta wakkali da juriya da kuma mai da komai ba komai ba. Shi kenan alokacin alpha da alhajin mustapha suka shigo suka gaisa da malam bala da mah mustapha yagabatar da su a matsayin iyayen mubarak basu dade ba suka koma suka hau adaidaita sahu sukai gida mustapha ya dubi babansa yace. Daddy yau kwana na uku acikin asibiti banga momi ba na rasa me nayi mata bata kaunta dady don Allah kafadamin gaskiya kodai ni ba danta bane daddy yayi murmushi yace. Kai daya na haifa ban taba son dan wani fiye da kaiba ko ita uwarka na fi sonka da ita don ita zan iya rabuwa da ita kaifa? Yace ina tunanin mahaifiyarka tanada aljanune wadanda suke tunanin raba ta da kai do min munsha wuya kafin da dauke ka bayan an haifeka da kyar ta baka nono kai daga karshe baka shekaraba ka dai na sha abin nan yana yimin ciwo .Alokacin abin yayi sauki amma yanzu ya dawo har yafi nada ni ina ganin kayi aure shi zai fi ma mustapha ya dora kansa kan kafadar daddy sai kuka. Ya ba zanyi hawan jini ba uwarka ta mai dakai abokin gaba ?ni kuma tawa tawa kaddarar kenan hakuri zakayi nayi fushi na raba dukiyata biyu na mallakamaka rabi lauyoyina sun sa hannu itama ta sa hannu lauyoyin ka nake jira dangi na babu wanda baya sonka ka san na birni dana kauye burina ka kyautata musu yanda tace bata son ganinka nima banso ta ganka wai a duk sanda ta ganka wani abu ke tsaya mata a zuciyarta idan na samu sukuni zan tafi turkey inci gaba da rayuwata acan tunda zama na acan yafi na nigeria yawa. Yace shikenan yanzu gashin kanka zakaci nafiso komai naka kaji my boy yayi murmushi sam yanzu ba batun izzat ne a gabansaba batun mahaifiyarsa ne agabansa ya taso cikin tsan da tsangwama da kyara agurin ta babu kulawa da tausayi tun ba ya damuwa har ya damu mijin ta da mahaifiyarta sunyi bakin iyakarsu har sakinta anyi daga baya ta dawo mahaifiyarta har rokon Allah take zuwa ayi mata wani lokacin zakagansu lafiya abun sha awa in abin ya motsa sai a (slow) lamarin ne ya motsa ga tsakaninsa da izzat abin ya zamar masa zafi biyu To muna nemar masa saukin Allah. Biki yayi biki yau bikin na masu abin ne domin sudan akaje aka dauko masu shirya amarya su hadata tayi kyau . An daura auren suhaila akan sadaki dubu dari biyar da mota yar ubansu. Amarya cike take da kunci saboda bata samu cikar burintaba kayan mata iri iri mahaifiyarta da dibga mata. Anyi fati iri daban daban amma ita duk wannan bai birgetaba,ita kawai abata mubarak dinta ko dakinsa ne na soro su zauna kafin Allah yayi masa nasa. Ta ringa ware idonta ta ga mah amma bata ganta ba kuma kafin bikin take tunawa momikada tayi fushi da yar uwarta .ita tana sonki ki gayyaceta. Suhaila bakisan halin halima ba muguwar yarinyace ba wai hakuri ne da itaba tsabar muna furcine haka tai ta hadani da iyayen mu sun fi sonta akaina ni bada basu so gashi nan ni Allah ya fi sona dan yabani arziki na kudi da yaya itafa da daya kawai ta haifa ga talauci . anya momien mustapha ita ta haifeshi kuwa kai akwai lauje cikin nadi umman suhaila wannan ba abindaya kamata ana fada ma yaro baneALIN HAUSA NOVELS DAN..........WAYE 1*23 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . suhaila tace momie wannan duk daga Allah ne ke dai ki rumgumeta babu wanda yasan gobe sai Allah. Allah yayi wa kowa Alziki . Ta ina zaiyi arziki? Ai shi da arziki sai dai in mota ta aunashi bata bugeshiba ace ya auna arziki ko an fada miki haka siddan ake arzikin? To naji momie ki daure ki sanar da ita kinga kin fita hakkinta banaso Allah ya kamaki da hakkin ta tace tow zan aika mata. Tace ko zaki bani in kai mata tace ki kaimata ko kije gurin masoyinki danta ?ke ko rabon kawayenki nace bazakiba shi yasa nasa miki tsaro kada ki ballo min ruwa suhaila ta dawo daga tunanin da takeyi tabbas momie bata aika mataba ai shikenan itakam tayi alkawarin taimakon baba halima ko don kyawun halinta. Anyi casu sosai a bikin suhaila naira tayi kuka don maroka sun kwashi rabon su .an nufi birnin tarayya unda za a kai amarya suhaila an zama ta musbahu. Mubarak yana zaune bakin gadon sa sanye yake da singileti da (3 quater),ya kunna tv don ganin labaran tara .ko minti daya ba ayiba ya fa an hasko (lovers night) din bikin suhaila. Wuta ce dauke masa ashe so wani abune mai wuyar sha ani.son gaskiya baya buya baya dannuwa tunda soyayyace da aka dasa tun kuruciya saiga shi ya rube bisa gado bai san iya adadin lokacin da ya dauka ba ya mike jiki ba kwari ya shiga gida ya zube gaban mah yace mah me yasa baki sanar min anyi bikin suhaila ba? Wane irin biki yace anyi bikin suhaila yanzu naga an sako a tv tace oh ni yasu wai me muka dauki dan uwane ? yar uwata uwa daya uba daya saboda tunaninta bani da shi shine taki gayyata ta? Ai gugu ko baiyi storon komaiba zaiyi na igiya amma shi kenan Allah yabada zaman lafiya wallahi na rabu da ita sai sanda ta neme ni. Yace ai in kinyi haka mah kun zama daya ai akwai bambanci tsakanin jahili da mai ilimi haka akwai bambanci tsakanin mai hankali da mahaukaci haka bamnancin yake tsakanin babba da karami. Tace to yanzu me kake nufi yace kibari sai bayan abin zan kaiki kiyi mata murna tace to shikenan ina rokon Allah yayi maka albarka ya sauya maka da wanda ta fita alheri. Ni na san kai dan Albarkane Allah ya bude maka hanyoyin Alheri,wanda muke tunani da wadanda tunanin mu bai zo kai ba. Yace amin ya mike jiki a sanyaye tamkar kazar da aka tsoma ta acikin ruwan zafi. Hajiya hadiza tana daga tawagar yan kai amarya don ta shige gaba abinta itace akan harkokin ta kawayenta duk wayayyune irin masu budewar idanun zamini,hajiyoyine da suka dauki rayuwar da zafi irin mutanen dabasu dauki komai da wani muhimmanci ba burinsu shine ,burinsu ya cika koda za asalwantar da rayuwar wasu sam basu dauki ran dan adam da daraja ba sukam sai a hankali hajiya marka tace ni tunda akasoma biki banga halima ba tace batasamu zuwa ba hajiya laure tace ya zata zo an hana danta auren santaleliyar yarinya irin wannan? Ai mijin suhaila ya more yarinya ta hadu ta ko ina . Tace kema dai kin fada haka taso in aurawa danta yar don ya samu aiki to albashin nasa nawane wai har ya sai lifan naji ance ya sai fili ya soma gini suka fashe da dariya to banda abin halima ai dai dai ruwa daidai kurji. Hajiya marka tace nikam inda nice ke zan janyo halima in taimaketa ta na da kirki fa.kuma sai naje har gidanta naji dalilinta na kin zuwa bikin yarta mai sonta hajiya larai ta harari marka tace ku dama aisai ahankali biki in naki ne yan uwanki ne zasu tsaya saboda kada mu handame hajiya hadiza kawa tafi yan uwa abinda kawaye suka tara miki yan uwan zasu baki? Hajiya marka tace wallahi da ciwo ko karayar arziki ta sameka babu mai tsayamiki sai naki don ni ganauce ba jiyau ba kawayen ma sai kina da shi kike mutum in babi da shi babu mai rabar ki to ai wannan batu haka yace koda kuwa ga yan uwanne to ni batun ya isheni inji hajiya marka. Kowa ya gyara ya sani kowa ya bata ya sani kanwar taki guda daya in baki yi mataba kiyiwa wa? Duk wanda zakiyiwa ba burge su zakiyiba shidan nata da kika hana kin san me zai zama ? To ki dauki yayanki ki bashi tayi dariya tace to ina ace Allah (S.W.T) ya amsa bakin ki kuma ya hada weesal ko weediyan da na bashi wadannan yaran yan feleke?? Ta ce cewa kikayi in bashi ni kuma nace Allahumma amin hajiya laure tace kin bawa suhaila abin nan kuwa wallahi na manta to dai kinsan budurwace kada ku bata abinda zai cuceta kinsan ba sonsa takeba wani hadi ne na mallaka aka ce lallai yau tayi amfani da shi dole zata bada kai kuma sai ya zama kamar rakumi da akala to allah ya taimaka. Suka rangwada guda hajiya laure ta nufi inda dakin amarya yake taje ta tare ta sai da taga ta sanye tas sannan ta juyo zuwa bangaren da aka saukesu. Dr yaseen ke rubutawa mustapha wasu magunguna saboda ansallame shi kuma cikin asibitin basu da shi inyaso ya siya a (chemist) wayarsa ta dauki kara ya duba yayi murmushi ya dauka yace dagaske kin shigo? Ina duba wani(patient) ne amma ki jira yace to ki iso daki mai lamba biyar zaki same ni. Ya kashe wayar yaci gaba da yiwa mustapha bayani. Aka yi kwan kwasa kofar aka shigo dr yaseen ya juya yana murmushi yace surayya au ke daya ce? Ina izzat din ? Tace ita muka kawo nida umma.jin an ambaci izzat yasa ya dago kai sukayi ido biyu da surayya tace . Mustapha dama bakada lafiya ?nayi ta kiran wayarka akashe. . Tow fa izzat kenan soyayyar har ta kai ga hakane inda nine mustapha wlh anfasa sallamata kenan tare zamuyi jinyaLIN HAUSA NOVELS DAN......WAYE 1*24 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . . Yaja aji sosai har saidataji haushin yanayin da yayi ya sake murmushi, mulki ya motsa tace ai ance dama mai hali baya fasa halinsa ta fada azuciyarta. Alokacin Alpha da mubarak suka shigo mubarak yace dama kunsan bashida lafiya ?tace aa nima izzat muka kawo bata da lafiya amma naga abokin naka yayi fushi ko kulani bai yi ba ai laifin wani baya shafan na wani ina maka fatan samun lafiya tace dr zo muje kaduba min yar uwata suka juya suka fita alpha da mubarak sukace wai meyasa kayi haka? Yace inaso in cire mace arayuwata ku kyaleni ina ji azuciyata zan rabu da izzat koda rabuwar mu zai haddasa mutuwata bashi kenan in kuma bai kai ba lalle ba zan yi aure ba zan kuma bar kasar nan shikenan. Lokaci daya suka kalli juna alpha ya soma hada kaya yayin da mubarak ya bisu ya ga jikin izzat .har an dora ta a gado yana kokarin daura mata ruwa ta kalleshi tace mubarak ina mustapha ta fada cikin murayr kurame da magagin bacci a hankali ta rufe idonta ya tsuguna gaban umman tasu tace ina mustapha? Yace baya jin dadi tun ran da mukaje gurin izzat amma yanzu an sallameshi. Shigowarsa shi da alpha wani daddadan kamshi ya gauraye dakin hankalinsa gaba daya ya koma kan izzat ta rame sosai ya maida hankalinsa kan dr yaseen yace. Meke damunta likita? Yace bincike muke bamu tabbatar ba sai mun gama gwaje gwajenmu sai alokacin ya kula da umma,ya risina ya gaidata ta amsa yajiki? Yace ai ya warware yanzu ma an sallame mu tace tow Allah ya kara lafiya yace amin suka fice zuwa motar alpha kai tsaye gida suka nufa dakinsa a share bello ya gyara masa shine mai kula da sashinsa yayi wanka ya hada tea ya sha bacci mai nauyi ya dauke shi ganin haka yasa suka fita bayan ya farka ya tarar da dinning area an shirya masa abinci ruwa ya sake watsawa ya jima yana murzawa kansa kalolin turaruka don Allah yayishi dan kwalisane sosai ya gyara gashin sa da wani mai dayake sake nademasa sumar sa tayi luf luf gwanin sha awa.ya taso alokacin ya kunna wayar sa ya ajiye yana jin shigowar (text) ya zauna yana cin abinci ya kammala ya shiga cikin gida. Hajiya saratu na hamshakin falonta sanye take da doguwar riga (pink colour) tayi mata kyau hakoran makkanta guda biyu masu matukar sheki ya shaki kamshin falon ta yaji sanyi har cikin ransa ya tsuguna jikin kujerar da take zaune yace. Momie barka da gida tace barka dai ya jikin naka?yace na warware ya zauna yace momi nakan yi mamaki da har na gama zamana a asibiti baki zo ba na rasa gano dalilin da kika dasa kiyayyata a zuciyarki saboda me ?kifada min laifina na daina ,bana shaye shaye bana neman mata bana neman maza bana sata. Na rasa me yasa kike kina in kuma ba ke kika haifeniba ki sanar min in nemi uwata don daddy shine ubana tana jin tausayinsa amma tana jin wani abu game da shi cikin ranta tace. Mustapha kayi hakuri haka Allah yayi ni,kullum ina addua akan lamarina,nima abin yana damuna.... Sai ta saki kuka. Kana karamin kai hawan jini, nima ina da shi. yazaro ido kema kina da shi? Tace eh mustapha nayi shekaru sha biyar da hawan jini ka yafeni nima bana so nake maka haka nida zan mutu ma dana huta. Momi mutuwafa kikace? Tace eh mana to menene amfanin uwar dake azabtar da danta? Shi ma yanzu ya yarda da maganar mahaifinsa mominsa tana da aljanu kada ki damu tace na damu kuma zanci gaba da damuwa koda kuwa zatayi sanadin mutuwata. Ya zuba mata ido yana nazarin ta yace momie ina son ki koda zaki ringa redar naman jikina kina ci zan zama mai biyayya agareki ta shafi kansa tayi murmushi tace boy dan gidan daddy ina mai zuwar maka a bacci? Tace tace bata sona sai banji haushi ba tunda wacce ta haifenima tace bata sona ta kalleshi tace karkasa na tsani yar mutane duk wanda baya sonka bana kaunarsa nace maka kai namijine ko akuruciyarka kai ba rago bane bana kai kara sai dai akawomin. Maza boy din daddy ka je ka nemi soyayyarta momie sai dai fa kurmace tace kurma? Yace tana magana sai dai bataji ciwon ya sametane da girmanta (may be )in anyi mata aiki kunnen zai bude tace anya kuwa. Iyayenta naga suna da wadata. Tace ai shikenan ai kurma mutum ce dontana kurma sai nace kar ka aureta ai nayiwa Allah shisshigi. Ai kai zaka zauna da ita dana da ikon ka auri mace hudu fa alokacin Alhaji abdulmajid ya shigo ganinsu suna hira ya bashi jin dadi yace ikon Allah nan da anjima sai tace ita batason ganinsa Allah dai ya kawo karshen abin nima BERNGEES NACE AMEEN. Yace aa momei ce da boy dina? Hirar sukarka mukeyi kaji kurmace yayi murmushi yace wacce zakayi ta masifa batasan kanayiba oh ni mustapha naga ta kaina Allah daddy bani da fada. Kai kai kai fadi gaskiya. Suka fashe da dariya hira suke cike da so da kaunar junansu . tow wai meke faruwa da momien musty ne kam nikaina kaina ya kulle sainaji nafara tausayinta wlh ammma da haushi take bani.LIN HAUSA NOVELS DAN............WAYE 1*25 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . amarya bakya laifi ko da kin kashe yar masu gida wannan shine taken duk wata amarya akasar hausa ko ince kirari to suhaila dai amarci ya tabbata don bayan abokan ango sunzo sun sai baki tare da dire mata manyan akwatina hade da kudin da bata san iyakarsuba musbahu shima yasan bata sonsa don ta sha fada masa ita Allah ya haliccetane don mubarak shikansa shakkun yadda zai kadaita da amaryar yake?yaso ya shareta sai bakin sun koma amma daya tuna faduwar gaba asarar namiji sai ya sa kai. Tana zaune har alokacin tsakiyar gado ya ja jiki yace suhaila ya gajiyar bki? Bata tanka masaba don jinta take cikin wani yanayi ga tunanin bareak dinta ta so ace ita da bareak suka zama ma aurata amma ga yanda Allah ya hukunta. Cikin yanayin salon wadda ya saba da mace ya ringa tarairayarta tun tana gocewa ga kuma karfin magungunan da aka turka mata mijin ta ya sameta karamar budurwa wanda a tunaninsa yadda takeson barek ya gama da ita tuni ashe abun ba haka bane. Ta samu albarka daga bakin mijinta tayi kuka na takaicin halindata tsinci kanta a kirjin wani ba mubarak ba kwana tayi tana kuka har asu bahi musbahu shine ya taimaka mata tayi wanka ta shirya tayi sallah .sai sha daya su hajiya hadiza suka shigahar zuwa lokacin sharbe suhaila take kawayenta da iyayenta a gurin babu wadda ya tambayi dalilin kukan su kuwa da yake manyane sun ranfeta. Suka yi dan gyare gyaren su sannan sukayi shiri tasawo.haka aka barta daga ita sai mijinta. Mutanen gombe suma washe gari suka wace gida daga ita sai dan mijinta khalid dan shekara goma yaro ne mai kazar kazar wayayye gashi da girmama manya shiyasa ya shiga ranta sosai tana son khalid. Misalin karfe ta kwas suka iso asibitin kaf yan (group) din su dr shuriem ya kallesu ya zo shigowa yace kuba an sallamekuba mubarak yace likita korar mu ake ? Yace no ba wai korar ku nakeba ku dinne akwai cafta. Suka ce to ai ba cinya ba kafar baya yace nifa ban ganeba to ka sallami musty ka rikww mai dakinsa oh !ai ni ban saniba yaushe aka kawota yau ina AKTH ban jima da shigowa ba. alpha yace a fata muke dr shuriem ya yi dariya suka shiga tare . Surayya da izzat kadai a dakin musty ya samu gefen gadon ya zauna izzat tayi masa wani irin kallo wanda sai da yaji shi ajikinsa sannan sai ya juya baya. Yace sury ya mai jikin? Tace da sauki yace ina umma tace yanzu zasu iso ita da abbanmu ya riko hannun izzat tayi saurin janyewa tareda juyowa suka zubawa juna ido. Ya kalleta bakisona ko?? Nimai laifini. Kawai sai yaga hawaye na zuba a idonta a lokacin ya juyo yaga ba kowa duk sun fice yace. Izzat inasonki sonda ban taba yiwa wata ya maceba sai gashi kin gujeni baki sona kin tsaneni hakan ya janyo min jinina ya hau ta kura masa ido tana kallon bakinsa tace mustapha kaika dasa min kinka gashi Allah ya doramin sonka ina sonka sai dai ina shakku a yanda mata ke son ka gaka da izza anya zaka soni yace wayace miki mata na sona tace ai na gani yace kisanya aranki mustapha nakine izzat kin huce kina sona kin yafemin?? Yace in baki hakuraba ki rama marinki. Tace ya zanyi tunda ina sonka? Naso in tursasa zuciyata ta rabu da kai amma taki anya banyi son rai ba? Ina jiyewa kaina storon kada iyayenka su kuni yace iyayena bazasu kikiba domin na fada musu don bana son sai magana tayi nisa su sani ta kalle shi ido cikin ido tace suka ce me? Yace sun amince dake sai dai na ce baki sona tace waya ce bana sonka kece kika fada tayi murmushi tace to amma kafada musu kaine kaci zalina ya tsura mata ido kamar yaya? Tace ka mareni inada lalura zan yi magana a gane amma sam bana ji kai kuma na kula bakada hakuri anya zamanmu zai dai daita ta rangwadar da kai sannan tace zama dani sai mai hakuri ya kura mata ido yana jin yanda sonta yake shiga zuciyarsa ashe so na da dadi murmushi ya subuce masa nakoyi hakuri tunda kikace baki sona shiyasa ka kashe waya na ringa tura sakwanni shuru? Hakan yasa ni damuwa nake jin in na rasaka na dadu da kuncin rayuwa. Yayi murmushi dake fidda asalin kyawunsa yace. Meyake damunki harya kaiki kwanciya a asibiti? Ta nunashi kaine musty na tunanunka ya hanani sukuni kuma na rasa yadda zan manta marin da kayimin lokacin mubarak yace baka da lafiya banyi bacciba nayi ta tura sakwanni amma shuru babu bayani. Cikin zolaya yace izzat na gano tausayina kike ji kinji ance sonki zaikasheni tace hakika zuciyata ta shiga rudani don ta tsinci kanta da makauniyar soyayya wacce na nutse aciki daga karshe na afka cikin rudani sonka da kiyayyarka dole son ya rinjayi kin saboda na kula kaine mahadin raruwata. Mamaki ya kusan sumar da mustapha kai ashe izzat ta iya barin kala? Maganar gaskiya wannan da tana da kunne lallai da anyi manyan mata a fagen iya soyayya. Adaidai lokacin umman su da alhaji habib salga suka shigo ya dubi mustapha yace aa wanake gani kamar yallabai?mustapah ya ringa dariya dan ya gano izzat diyar sa ce shi kuma babban ma aikacin lamfanin suna robobine dake sharada ya risina ya gaida shi yace kardai kaine mustaphan daka marar min baby na? Yace afuwan abba nace ta rama ya fada yana shafa fuskar sa ummata dara tace ai ta hakura ko alokacin srayya suka shigo abba ya ce......... .A NOVELS DAN........WAYE 1*26 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Ke daga inakike? Tace ina zaune naga kun shige ni ina ta muku magana bakujiba mustapha ya fidda (cheque) yayi rubutu ya ajiye saboda basu sayo komaiba sakayi sallama. Mubarak yake tukin mota alpha yana gefensa shi ko musty na baya yasa hannu ya grumgumi kuje rar da bareak ke kai yace Allah abin godiya wai ni yau izzat ke cewa tanaso abinda bantaba tunanin samu ba lallai Allah abin godiya nasan abbanta ma aikacinmune alpha yace muma surayya ke bamu labarin halin da ta shiga saboda rashin samun wayarka hakane mubarak yace dama sai wani ya rasa wani yake samu sai wani ya zubar wani zai dauka kamar yaya? Yace nikuma nayi rashin abar sona rashin har abada alpha yace suhaila mutuwa tayi? Yace no tana gidan mijinta mai naira na rasa soyayyar dan Adam da kudi mutum yanason kudi kamar ransa wani ma fiye da ransa don da yawa jama a sun rasa rayuwarsu wasu bangare na jikinsu a dalilin kudi ni kuma soyayya ta da kudi bata kai hakaba domin na fison na rufin asiri kada in nema agun wani ni ina daraja dan adam fiye da kudi alpha yace mubarak yan matan yanzusun fison mai kudi fiye da kansu shiyasa samarin yanzu in kaga sun sakarwa yarinya tow lallai itama ta saki layi ban gishiri in baka manda itace rayuwar samartakar yanzu. Mubarak yace to ko in hakane gaba daya daga mazan har matan bama yiwa kanmu adalci ba.don in bamu gyaraba lallai mun dauko hanyar lalata rayuwar mu gaba daya. Domin babu yadda rayuwar al umma zata ci gaba bayan zinace zinace yana yawa acikin al umma. Mustapha yayi shuru can yaja dogon tsaki yace. Shiyasa sam bana son soyayya banda Allah ya hadani da wacce nakeso amma sonayi daddy ya zabo min wacce zamuyi dai dai alpha ya fashe da dariya yace shege musty Allah yakamaka matan daka wulakanta suna da yawa gashi sakayyar Alllah saika kamu da son kurma kai Allah buwayi gagara misali. Mustapha yasha kunu yace bana son wulakanci ai ni kurman ma ta fiye min mai baki don su ba gulma bare muna furci. Yace ai kam gashinan in kana magana tayi maka kuri da ido tamkar wacce ta warke daga makanta. Mubarak yace ai da kallo take gane me kake cewa inbata kalli bakin kaba bazata san me kake cewaba musty yace wai haj. Hadiza da gaske take kudi yafi zumunci ko?? Yace to ya za ayi yace kyaleta akwai ranar kin dallanci . Suhaila gashi dai ana cikin daula takudiri aniyar zama da mijinta don tayi bautar auew tunda duk abinda take tunkaho da shi musbahu ya gama da shi to me zatayi burga da shi ta hakura ta fauwalawa Allah (s w t) don ta kula mominta akwai son kudi to da abbansu bayi da shi zata zauna da shi? Tayi kiran duk nombobin muarak amma bata sameshiba ita kuwa baba halima batada ita tayi alkawarin siyawa mah waya don su ringa gaisawa shigowar kalid ta sanyata dawowa daga tunanin aguje ya fada jikinta. aunty mami haka yake kiranta tace boy kadawo. Ya daga kai ta soma kokarin ciremasa safa yana kokarin fidda littafinsa daga jaka yana nuna mata aiyukan da aka yi musu da (home work) din da zai yi tace ajiye su kayi wanka kaci abinci in ka dawo kaga islamiyya sai muyi. Shigowar maigidan nata ta gani tace abban khalid sannu da zuwa ta mike ta karbi jakar hannun sa ya zube kan kujera ya dafe kai yace wash! Ta maida dukkan hankalinta kansa tace badai gajiya ba. Ya dube jajayen idanunsa ya kalleta tace anya lafiya kake?ji yanda ida nunka suka rine.yace kaina kemin ciwo kada ki damu nan da zuwa gobe zan wartsake. Tace kasha magani yace kona sha ma ba dainawa zaiyiba duk sanda ya tashi sai dai in kwanta kawai cikin tausayi tace to sannu Allah ya baka lafiya. Yace amin. Juma atu babbar rana bayan sun fito daga masallacin juma ane suka nufi gidan hajiya lami kakar mustapha sun kai su bakwai al adar su matasan akwai su da zumunci akan zaga gidajen yan uwa duk inda sukaje sai mustapha yayi yayyafin naira don shi mutum ne mai kyauta. Hajiya lami tace aa sannun ku da zuwa gaba daya suna zaune a falo suna gaisawa da ita sun shiga kwasar ta. Sallamar (twince) ce ta dauki hankalinsu weesal ce a gaba wedeyan abaya yan biyu masu kama daya tamkar yayan larabawa.baban sune kwara mahaifiyarsu ma sai tayi da gaske take ganesu don komai nasu daya weesal keda dumpil daya yayin da wediyan ke da biyu shine bambancin su hatta magana, kallon su tsawon gashinsu duk dayane ,daya nada yawan magana da son budawa. Indai suka zauna suka yi shuru to babu mai ganesu ko laifi sukayi da wuya agane shi yasa lamarin su sai su. Shi dama mustapha baya shiga sabgar su. weesal ce mai nacin kaunarsa ita ko wediyan tace ita bazata auri talakaba sai mai kudi mai kudin ma sai wanda yayi suna acikin jerin masu kudin nigeria. Kai inson samune wanda yayi suna cikin jerin masu kudin duniya.OVELS DAN.......WAYE 1*27 . Na ZARA'U BABA YAKASAI . . WANNAN buri nata yasanya sam basa shiri ko kadan to amma shi kansa baya iya gane ko wacce acikinsu don sun jima ,shekarunsu uku kenan suna can kasar su baban su sai cikin satin nan suka dawo suka samu gefe lokaci daya sukace musty dafa daganan gidanku zamu munji ance kakusa zarcewa kasan yanzu tazarce ake. Ya harareta yace Ta Allah ba takuba suka bushe da dariya wesal ta gaidasu weediyan ta maze ya kalleta yace. Dama kin gaishesu duk nan babu (choosng) dinki matar manya taji dadi sosai ta sake mazewa alpha dan tsokana yace hajja wediyan ko yan rike jaka maje weesal ta mike tayi ciki cike da takaicin yar uwarta mustapha yace ya kamata hajiya ki rage buri tace wa! Nidin kai ai kudi sunyi arayuwa koya kace alpha? Shi dama dan cafta ne yace ai abin alfaharine ki fito a matar gwanna ko shugaban kasa ko minster wayyo ni ko ina fasa kai ina kanwata ce ina yiwa mutane hayaniya kina taimakon alumma. Tace no alpha nafi so in auri mai balain naira bana son shiga gwannati data bare mun zama sai labari masu masifaffan kudi dai niko in zube a falo ana yi min hidima ina kallon mabukata sun zagayeni ina ta rabon naira. Tayi ihu ta mike ta ce wayaga hajiya weediyan ka san Allah mustapha a rayuwa inason in auri mai kudi don in ta taimakon mabukata in ta bude asibitoci ko ina kaji ana fadin hajiya wediyan. Mubarak yace Allah ya cika miki burinkitunda taimako zakiyi. Amin abokin musty amma na baka weesal in kanaso itace kyautar adduarka gareni .sannan zan taimaka maka da kai da iyayenka a lokacin da bukata ta biya sannan zan dankara maka mota mai numfashi kaji?mustapha ya harareta yace weediyan ana girma ana hankali amma ke kam abin naki gaba yake. Ta dubeshi tace atarihin rayuwata talaka bai taba cewa yana sona ba kuma ni ko ya zo bazan so shiba alpha yace dazan shigo kice da gudu zan koma. Ta harareshi tace kai? Aiko ogan ku bazan yi maleji da shiba bare kai ta dubi mubarak tace kai ya sunanka ??naga kadanfi wannan nutsuwa kada ka manta na yi alkawarin weesal. Mustapha yace dayake ke kika haifeta ko ance miki bata da masoya da za ki yi kyautarta tace aa musty ko kana cikine bansaniba amma ai abin da nakeso shi takeso irin mu daya komai namu daya ne tow akan meye zan zaba mata miji ta ki?? Kai nice fa ogarta. Suka fashe da dariya tayi ciki . Hajiya lami ta mike ta bi bayansu tace oh ni zainabu naga sanda wediyan zata daina son mai naira. duka samarin suka yi dariya tana shiga faisal yace weddiyan manya ita babu ruwanta tsakaninta da Allah take furucinta anas yace kaikam barek anyi maka kyautar mata ga kyau ga gayu mubarak ya katse shi yace manta da ita yar wulakanci ce ita ce ta haifeta da zatayi kyautarta . Weesal ce da shuhuda suka shigo falon suna ta jera kayan abinci sai da suka sa komai a muhallinsa sannan shuhuda tace to gashi nan mun kammala sai kuzo muci okey sannu Suka juya a ciki ne wediyan na kishingide tana kallonsu daga baya tace in kun gama da wadancan kartin nima ku kawomin nawa sukace kin isa kai hajiya ce fa ni yanzun nan nayi kyautarki yar rainin hankali hajiya lami tace kyauta kaamar ya? Tace mubarak abokin mustapha yo ni bansanshiba sai yau amma dai naga yanada hankali haka kuma zuciyata naji ta karbeshi sai na ga kawai tunda ni me naira nakeso to bari in sadaukar dashi ga weesal amma da ba mai naira nakesoba zanyi maleji da shi hajiya tayi dariya sosai tace Allah ya kawo ni zamani rashin kunya tab ikon Allah shuhuda tace kinje da shirmanki kin dawo da tatsuniyar ki. Tace ko sai randa nace shuhuda fadi kasashen da kikeson zuwa kiji kamar mafarki hajiya lami na kallon su cike da so da kaunar jikokinta. Yayanta uku mahaifin shuhuda sannan mahaifiyar mustapha sai kuma mahaifiyar su weesal yan biyu tana sonsu sosai suna sakewa da kakar su don suna son ta fiye da kakanin su. Don suna sakewa agidanta. Mace ce wayayyiya da iya mu amala da mutane ta iya zama da kowa acikinsu. Kwanan izzat biyu aka sallameta alhaji habib salga sai yayi murna da ganin mustapha a matsayin surukinsa don samun matashi mai tashen kudi ace ba ya hulda irin ta matasan yanzu. Shi dai kyaleshi akwai fada mafada cima ai sai ka shiga huruminsa. Izzat zaune a farfajiyar gidan su zaune take da littafin kishin tsiya, tana mamakin yadda rayuwar muwadat take tafiya har hawaye taji ya zubo mata. A lokacin (text ) ya shigo wayarta ta gane hakane ta kadawar taga wayar nayi . Ta bude taga musty ne ya karaso ta shiga ciki ta sake shiryawa ta nade kanta da karamin mayafin bb doguwar rigar tayi mata kyau baka ce ajikin fara ta haska ta. Kanin ta nasir ya shigo yace na kaishi ta mike cike da yanga da rangwada ta iso gareshi tace.......NOVELS DAN........WAYE 1*28 .Na ZARA'U BABA YAKASAI . . Sannu da zuwa masoyina yayi murmushi ta zauna ta kura masa ido murmushi take sannan ta zame tace. Barka da yamma yace mum yini lafiya? Tace lafiya ya momi da daddy? Yace duk suna gaida ke tayi shuru to ina kannen ka? Nikadaine yanzu zuwanki muke jira ki bawa momi yaran da zasu debe mata kewa. Tayi murmushi ta rufe fuska alamar jin kunya alokacin surayya ta karaso ta ajiye kayan cima iriri yace aa nikam a koshe nake tace haba yallabai ai kaci ko kadanne. Yace bani insha ruwa,don inajin kishirwa. Yace surayya adaina cemin yallabai tace ai abban mu haka yakecemaka yace ai ya daina ni yanzu dansa ne. suka yi murmushi dukkansu sun jima suna hira daga baya tafi. Alhaji abdulmajid a office dinsa shida lauyan mustapha an bashi takardu ya sanya hannu.dama shi ya rage bayan tafiyar lauyan alhaji yace. To yanzu batun aurenka shine agabana yaya batun tafiyarka turkey? Yace yana nan daddy. Sunyi hirarsu ta da da mahaifi. Mustapha kwance falon mahaifiyarsa suna hira wayarsa tayi kara ya dauka yace mubarak kaine bari in fito. Hajiya saratu tace aa ina zaka tafi bayan kace yunwa kakeji? Yace mubarak ne ya zo. tace oh ni ban taba ganinsa ba yace to ai tsoron kawo shi nake kuma shi din ba mai son shiga cikin gida bane tace irin ku daya. Yace momi sai kinga yadda nake shiga gidansu na sake sosai mamarsa mace mai kirki da hakuri . Ni ina bala in kaunar mamar sa saboda yanda take tafiyar da rayuwarta. Tace Allah sarki yau dai akawo min mubarak in ganshi jake shigo da shi insha Allahu zaka kaini gurin mahaifiyarsa ai tunda naji Allahji na yabon halin sa na san yaron kwarai ne. Ya mike ya fice azaune ya sameta suka tafa ya gida ya hidima. Yace mu shiga ka gaisa da momi. Yaji matsanancin faduwar gaba shi dai baya so ya shiga,barin yadda in mustapha baya wajen ake labarin halin mamansa baya son wulakanci Amma bai isa yace baza shi ba haka ya bishi suka shige tun da uwarsa ta kawo shi duniya bai taba zaton akwai irin wadandan falukan a nigeria ba. Ta zauna kamshi da sanyi suka ratsashi ya dinga zare ido ta inda momi zata fito ai kam sai gata ta fito ta zauna batare da ta kalli mubarak ba ya tsugna ya gaidata ta kalleshi gabanta yayi mummunan faduwa,har sai data firgita ta mike ta kalleshi tace. Kaine mubarak? Yace eh ina ne gidan ku? Yayi mata bayani ,ta kalleshi a tsanake tace. Mubarak kai danane ni ce uwarka nina haifeka wallahi babu wanda ya isa ya rabani da kai sai kuma na karbeka don kai danane na cikina.nina haifeka. Gaba daya suka zabura anya kanta daya kuwa? Mustapha yace to ni kuma DAN WAYE? Kifada min mana ni din DAN WAYE? . Tofa muje zuwa amsar wannan tambaya naga littafi na biyu kukasance dani . .   COPY AND SHARED BY   MARYAM  AMEERA YOLA AND SAKINAT USMAN MAMAN IHSAN   AND JUWAIRIYA SULAIMAN



Post a Comment

0 Comments