DAN MINISTER hausa nivels 6

 DAN MINISTER* 💅💄

           ðŸ¦šðŸ¦š





Written by *Husba'ahfama* 



 *IG officiall_husba'ahfama* 

Facebook *Real Husba'ahfama* 


Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*








                    13-14










Nabil yawahalar da shatuwa sosai Dan gaba,daya baya hankalinsa saboda wata sabuwar duniya da yaji yashiga Wanda betaba shigaba se yau ita tana kukan azaba da Kiran iya da kawayanta Babu Wanda Bata kiraba har da su amina shikuma kukan dadin da be taba jiba yake surutaikuwa Babu Wanda beyiba har da yiwa baffah godiya shatuwa da wuya tayi wuya numfashinta daukewa yayi batasan sanda nabil ya bartaba bayan komai yanutsa rungume shatuwa yayi Yana ta Mai da numfashi jiyayi gabadaya ciwan da yakeji na Mara Babu kamar an dauke Masa wani Abu me dauyi ajikinshi wani baccine me nauyi yadaukeshi be farkaba se da gari yawaye sosai Ido yabude ahankali yaji mutun ajikinshi da sauri yaduba yaga shatuwa ce kallan inda yake yahau yi abinda yafaru jiyane tsakaninsa da shatuwa yadawo Masa kurawa shatuwa Ido yayi yaga ko motsi batayi ranarne yakare Mata kallo yaga yanda ainahin kalar fuskarta take yadade Yana kallanta irin rashin mutuncin da take Masa yatuno yakuma tuno abinda yashiga tsakaninsu adaran jiya wani tsaki yasaki yatashi afusace yasa kayansa yai hanyar waje har ze fita yatuno ko motsi bega tanayiba dawowa yayi yatabata yaga kamar Bata da Rai ruwa me sanyi yadauko ya kwara Mata takuwa saki wani marayar Kara tsaki yakuma Jah yai ficewarsa ko kallan  halin  da take ciki beyiba ko  damuwa bare ya temaketa Yana dada Jin haushin kansa da yazubar da girmanshi kamarshi yaje ya aikata haka da shatuwa Kuma gashi shi yatsani Mata garin  yayama shi yashiga dakin ta tinani yake tayi har yashiga dakinshi Yana shiga wanka yaje yayi bayan yagama shiryawa kasa Zama agida yayi yai ficewarshi gurin da yake shakatawa


Baffah se da yasa aka nemo me gyaran targade yagyarawa minister targadensa da gocewar kashin da yayi yafada yaji wajan gyara Dan gurin yayi tsami sosai


Iya tinda suka dawo takasa motsa jikinta barinma hannunta gabadaya jikinta ciwo yake Mata ga hannu yaki motsuwa itama se da akasa me gyara yaduba Mata hannunta  yaga tasamu tsagewar Kashi ahannunta na dama aikuwa kafin agyara hannun ansha daru da ita Miss Miss kuwa takira sunansa ba adadi tana Masa ruwan masifa shi da nabil 


Amina ce tazo da safe baffah ne yasa tazo da mgnar da zasuyi tasamu baffah abangaran da yake sauka yasa aka Kira Masa hajiya Fatima bayan sun gaigaisa


 baffah yafara mgn yace to Kan mgnar mu na kiraku wannan shawarar da nayanke itace mafita insha allahu Kuma za a dace Amina tinda tafiyar Taki ke da mijin naki tazo zuwa kwas,din da zejeyi america kutafi tare da shatuwa tinda shi mijin naki yace tare zaku tafi Kuma sani na da gida acan america gidan nashi zaku sauka har mijin naki yagama kwas,din da zeyi na wata shida Dan Allah ki dada kokarin da kikeyi Akan Wanda kikeyi Akan shatuwa muma anan zamuyi iya namu kokarin Kan nabil har musamu abinda mukeso awajanshi Dan shiryuwarshi itace shiryuwar sani itama shatuwa hakane Dan Haka yanzu tinda kince yau da yamma zaku tashi zuwa America kije kisa shatuwa ta shirya ki hada,mata du abinda yadace ki tafi da ita gidanki lokaci nayi se dai ku tafi ko tanan karku biyo da ita Kuma karki Bari nabil yasan kece Kika tafi da shatuwa ko iya bazata San da tafiyar jikartaba Dan hakafa na yarda muka taho da iya dan Tai sallama da shatuwa Kinga karshe ga abinda yafaru itama bazata,san shatuwa tayi tafiyaba in bahakaba komai baci zeyi yanzu Fatima takira megadin gidan nabil ta tambayeshi ko nabil nanan yace bayanan yadade da fita Danhaka sekiyi sauri kije ki dauketa Kuma ko lokacin da wowarku yayi inhar dukansu Basu shiryu yanda mukesoba baza a dawo da shatuwa ba har se munga sun koma yanda mukeso 


Amina tace to baffah Amma aganinka iya bazata damekaba Akan kafito Mata da jikarta kasan halintafa da rigima  


Hajiya Fatima tace Nima tinanina kenan Kuma wannan matakin da kayanke Kan nabil da shatuwa baffah shine dedai Allah yabamu sa,a ni wlh daga iya har alhaji rigimar tasu dariya take bani garama nabil da shatuwa suna da dalilan abinda yafara hadasu fada tin farko Amma iya da alhaji Basu da wani dalili alhaji nabil yake tayawa fada iya Kuma shatuwa Kuma wlh Ina guje musu ranar da nabil da shatuwa zasu shirya zasuji kunya sosai mudai muna gefe kallone namu tasa dariya


Baffah yace rabu dasu gani sukayi zasu iya Ni abin takaicima sani ne mecewa indai Akan nabil ne ze ajje mukamin minister agefe in dokuwane shi da iya su doku Allah yaganar da su gaskiya; karku damu da iya danta umaru wato mahaifin shatuwa yasan komai Akan tafiyar Kuma yabamu goyan baya akai ita,kuma iya nasan yanda Zan shawo kanta har Allah yasa shatuwa ta dawo se Naga tafitarku Amina sannan zamu koma mazaigai Ni da iya Allah yakaiku lfy ku dawo lfy maza tashi kitafi Allah yai muku albarka


Amina gidan su nabil tasa direba ya kaita tana shiga taita sallama taji shuru ta dauka ko bacci sukeyi Kai tsaye dakin shatuwa tashiga ganin halin da shatuwa take ciki ko motsin kirki Bata iyawa tana kwance abin tausayi yadagawa Amina hankali tambayarta tafara me yasameta ko nabil ne ya daketa shatuwa Babu bakin mgn se kuka shima da kyar takeyi yaye bargwan jikin shatuwa da tarufu da shi tayi ganin yanda jini yabata inda take kwance yayi mugun tada Mata hankali Dakar ta rarrashi shatuwa tafada Mata abinda yafaru tsakaninta da nabil Amina taji Dadi sosai da haka tafaru tsakaninsu kafin shatuwa tabar kasar ita taiwa shatuwa wanka ta gaggasa Mata jikinta Taji tausayin shatuwa sosai ganin barnar da nabil yai Mata ita ta gyara ko Ina na dakin har zanin gadan se da ta wankeshi a injin wanki tayi du abinda yadace sannan takama shatuwa suka fito tasata amota da kayanta suka fice asibiti tatara Kai shatuwa aka dubata sannan suka shige gidan Amina yamma nayi wajan karfe shida jirginsu yatashi zuwa America baffah da Hajiya Fatima ne suka rakasu har sukaga tafiyarsu sannan suka dawo gida


Nabil tinda yaje wajan da yake hutawa tinanin shatuwa da abinda yashiga tsakaninsu yake ta dawo mishi ko Ido yarufe abinda yafaru yake gani ga fuskar shatuwa da take ta Masa yawo a idanshi kide kiden da ke tashi awajan da wakar du yau ji yayi basa Masa Dadi tinani yafara to da yafito yabarta awannan halin waye ze temaketa in tamutufa Kuma ko bakomai ai ta dalilinta yasamu lfy jiya Kuma yaji dadin da be taba jiba Daman mata na da wannan Ni,imar Haka me Dadi har da wannan ballagazar Mara mutuncin to yanzu waye ya temaketa ko tamutu fitowata daga gida  jiyayi gabansa yafadi besan lokacin da yasaki wata karaba yafara mgn kamar zararre A,A,A Bata mutuba to Wai meyasa nake tinaninta Wai meyake faruwa da nine abokansa da sauran mutanen da ke wajan kallansa suke tayi suna mamakin me yasameshi yau haka Babu me bakin tambayarsa saboda kowa yasan halinshi wajan mota yanufa da sauri ze shiga dagudu yaransa suka rufamasa baya suka bude Masa motar Yana shiga sukaja suka fice dagudu zuwa gidansa 


Motar ko Gama tsayawa batayiba yabude yafito da gudu,gudu sauri,sauri yashiga gidan jiyayi gabanshi yayanke yawani mugun faduwa dakin shatuwa yashiga dagudu yaga bataciki yaje da sauri yabude bandaki yaga bakowa aciki dakin yahau kalla yaga ko Ina tsaf angyara Babu alamun mutun yakwana acikinsa kangadan yakalla yaga agyare anma canja zanin gadan gabadaya fita yayi yahau duba ko Ina nagidan nanma be gantaba dagudu yatafi wajan masu gadi Yana tambayarsu da tsawa Ina matarsa 


Jiki na Bari sukahu bashi  amsa Suma Basu gantaba ko fitarta Basu ganiba


Yace Babu wata ko wani Wanda yashigo gidannan bayan fitata yatafi da ita


Sukace eh yallabai Babu kowa Kuma mu bamuje ko inaba muna wajannan da wasu sun shigo da mungani 


Yace wlh inhar tabata kome yasameta kunsan Allah bazan barkuba Ni dakune to meye anfaninku agidan tinda baza kuyi abinda aka daukekuba korarku zanyi yau,yau dinnan bazaku dada kwanarmin agidaba dukanku se na kulleku kuje kuyi tinani ku fitomin da ita kannaje nadawo 


Gida yatafi wajan su hajiya Fatima ko sallama beyiba yabanko dagudu Yana dube dube kamar me neman wani abin daga hajiya Fatima har baffah babu wanda yai Mai mgn yisukayi kamar Basu ganshiba dakunan gidan yahau dubawa be gantaba falo yadawo wajan su baffah yazauna yakwanta Kan goguwar kujera yarike kansa yarufe Ido kamar me bacci shi yasan meyake damunsa ga wani ciwankai da zazzabi me zafi na damunsa


Baffah ne yace nabil yau ko mgn Babu bare gaisuwa Ina matar taka


Nabil besan sanda yatashi zauneba Yana kallan baffah 


Baffah yace ko dai baka da lfyne 


Nabil yace lfyta kalau Daman batazo nanba 


Hajiya Fatima tace wacece kake tambaya 


Yace aa ba mgn nayiba


Komawa yayi yakwanta


Yace mommy a Ina tsohuwar Nan ta kwana


Kafin tabashi amsa sega iya tashigo


Iya naganin nabil tace me zamanman wando Ina shatuwa ko kakuma karyata ko baka,jina Kai min shuru 


Ido nabil yabude suka hada Ido da iya batasan lokacin da taja bayaba 


Tace nashiga uku Ni Aisha kuga idan mutun kamar gauta ko dai kakuma balballata Ina Nan bansaniba 


Tashi yayi Yana hada hanya yai dakin da iya ta kwana nanma bega shatuwa ba dakin minister yatafi ya kwanta  daga yarufe Ido se yaga shatuwa gashi San ganinta yake yarasa me yasa ga zazzabi yatakura Masa se rawar sanyi yake


Hajiya Fatima ce tashigo taga halin da yake ciki tace nabil baka da lfy bayannan Kuma da abinda ke damunka ka fadamin


Yace bakomai mommy kawai dai bani da lfyne 


Tace to Alllah yabaka lfy Bari na kawoma magani tafice


Mgn nabil yahauyi shikadai kamar Mara hankali to Wai Ina taje ko an sacetane to ai babu Wanda yashigo gidana Kuma anty Amina tayi tafiya baza Kuma su tafi tareba tinda kwas mijinta zeje yi Kuma ai baffah da matsifanfiyar tsohuwar Nan baza su Bari atafi da itaba to yaushema Yar Kauye irin wannan zataje America ai ko jirgi Bata iya hawaba to waima meye nawa in tabata ba na hutaba da jarabar ta da ta wannan tsohuwar to Wai meyasa nake ta ganinta in narufe Ido ko Dan ta dalilinta naji saukin ciwan marata jiya Kai nabil manta kawai macacefa Kuma nafa tsaneta Wai meyasa naje nahada jikina da ita kazama Yar Kauye irinta tsaki yajah me karfi 


Hajiya Fatima ce tadawo 

Bashi magani tace Kai dawa naji kana ta mgn ko dai kun dada halinne Wai Ina shatuwa ana ta tambayarka kayiwa mutane shuru


Yace tana gida na barota 


Mgni tabashi yasha bacine ya kwasheshi acikin baccin Yana ta mafarkin shatuwa da Kuma garar da yasha awajanta jiya kusan rabin baccin du mafarkinta yake


Iya da baffah sun koma mazagai Dakar aka lanlabata takoma da cewa tayi se taje tayiwa shatuwa sallama Kuma akwai nasihar da ta manta batai mataba 


Shatuwa bakin America Tasha jinyar barnar da nabil yai Mata se da tawarke sosai Amina tasata amakaranta saboda shatuwa na da kokari Kuma Babu lefi tana ganewa turancine ake fama da ita in anyimata Bata gane wani abin in angaya,Mata da turanci se ta dawo gida take tambayar Amina me ake nufi da kalma kaza da turanci in Amina tabata amsa to tarike kenan karatu kuwa tana ganewa  tamurje tadada fari sosai in ba ka santaba bazaka gane taba Amina tayi kokari sosai wajan dada wayar da ita yanzu shatuwa tazama Yar birni Kuma Yargayu acikin wata ukun da sukayi tsokanar da akasan shatuwa da ita yanzu du babu tazama saliha kamar ba itaba  yanzu Abu dayane yake damun shatuwa da Amina ta kula dashi tana yawan tinani kome take lokaci daya zatai shuru ko mgn ake Mata bazata baka amsaba Amina tayi Mata tambayar duniyarnan meke damunta se tace Babu komai


Yau Amina nazaune adaki tana shayar da yarta shatuwa tashigo ta sameta tazauna kusa da ita Amina tace yadai kanwata Naga kamar da mgn abakinki


Shatuwa tace Daman tambayarki nazo nayi Dan Allah in mutun koyaushe na yawan se Tai shuru ta sunkuyar da kai


Amina tace cigaba Mana kanwata Ina jinki meye abin Jin kunya nifa Yar uwarkice


Shatuwa tace to anty in mutun nayawan tinanin mutun mekenan kamar Wanda kasani Kuma abokin fadanka Kai tayawan tinaninsa ko in kana bacci Kai ta mafarkinsa 


Amina tace kafara damuwa dashi Kenan Kuma yanzu kana sanshi  kekuwa kanwata meyasa kikemin wannan tambayar ko tinanin gida da su iya kikeyi


Ido tarufe tana dariya tace to anty bayan su mommy Kuna waya da su iya dah  takuma,sa dariya


Amina dariya take ta dannewa Dan tagama ganota yitayi Bata gane me take nufiba tace karasa tambayarki du Zan Baki amsa


Kuna waya da Yaya nabil 


Amina tace eh to muna waya da kowa Amma nabil gaskiya ba sosaiba iyama  bama waya da ita


Shatuwa tace to in kunyi waya dashi Yana tambayarki yanake ko Ina nake ko bayayi


Tace aa gaskiya bayayi Kuma ai besan na taho da keba bemasan kina nanba


Hawayene yafara zuba daga idanta 

.Amina tace menai Miki kanwata ko na Bata Miki Rai ban saniba 


Tace aa abinne yabani haushi Ni fa anty kullin shi nake ta tinani ko bacci nake tinaninshi nakeyi yanzufa San ganinshi nake Amma shi be tabama tambayarki ko Ina nanba  Daman anty besan kin taho daniba Kuma in yashiga wani halifa Kuma fa mijinane ai bebarniba muka taho Kuma kece memin waazi Akan hakkin miji kumafa kinsan iya wlh damunshi zatayi akaina in tazo Bata ganniba


Hamdalah Amina tafara tana murna tace to akwai dalilin da yasa muka taho dake se nangaba Zaki gane me ake nufi harshi nabil din Kuma mgnar fadan da kukefa yanzu nasan muna komawa zakuci gaba da abinda kuke Kuna rabawa kanku abin kunya agaban mutane ai basan junanku kukeba Kinga kuwa ai yanzu hankalinki kema akwance yake anraboki da abokin fadanka ko


Tace aa wlh ai Ni nadena fada Kuma ko me yaimin bazan Kuma kulashiba ai kinmin fada ga Kuma waazi inaji Akan Mata tabi mijinta sau da kafa in tayi zata shiga aljanna ai shima nasan yanzu yadena gakuma iya inasan naganta anty mu koma gida Dan Allah 


Amina tace to kanwata karki damu munkusa komawa insha allahu komai yazo karshe ammafa naji Dadi ashedai anasan Dankanin nawa kanwata na San mijinta tanasan ganinshi 


Dariya shatuwa tasa tazuba dagudu tafice daga dakin tanajin kunya


Amina Kiran hajiya Fatima tayi awaya tabata labarin yanda sukayi da shatuwa itama hajiya Fatima tabata labirin halin da nabil yake ciki dukansu sunyi farin ciki sosai


Nabil tin Yana boye batan shatuwa yanzu yakasa boyewa gashi yazu tinani yamasa yawa har Rama yafara yarage walwalar da yakeyi da ko fita yanzu bayayi sosai se dai yaje dakin shatuwa yakwanta in Kuma yagaji da kwanciyar yatafi wajan hajiya Fatima yau wajan hajiya Fatima yaje yasamu kuwa babansa minister nanan suna hira 


Da sallama yashiga zuwa yayi yafada jikin minister yafashe da kuka me karfi yace daddy Kai da mommy ku temakeni tinaninta ze kasheni wlh Santa nake na Dena du abinda bakwaso in dai za a dawomin da ita mundena fada naje na roki baffah yace bemasan da batan shatuwa ba Kuma Allah yanzu inaga dasa hannunshi yasan inda take Ni har mommy ban yarda da itaba


Minister rudewa yayi yace alhamdulillah Allah na godemaka da kabawa nabil matar da yakeso ba wannan mahau


Kafin yakarasa nabil yarufe Masa Baki


Yace karka karasa daddy wlh bazan iya jure Jin ana zagintaba wlh Ni matata ba mahaukaciya bace da hankalinta nifa daddy ba wata matar auren da nasamo matata nake nufi Wanda baffah ya auramin Dan Allah gobe muje mazagai tare mubawa baffah hakuri ya dawomin da matata har in Kuma yaki mommy ma Taki to wlh se na Nemo gidan iya masifa na fada Mata anbatar Mata da jikarta Kuma bawasu bane su baffah ne ai nasan in taji masifarta,ma kadai ta Isa su dawo da ita Dan itama tanasan jikarta sosai


Minister Baki yasaki Yana kallan nabil bemasan sanda ya sauko daga Kan kujera yazauna akasaba Baki narawa yace nabil kakuwa San mekake fada kuwa ko dai da gaske kaima kabi layin Yan shaye,shaye abokanka inkuma ba hakaba to tsohuwar Nan da jikarta sun maka wani mugun abin sun kaika an haukatama zuciya akansu shikenan baffah zamu rasa nabil ai Dole naje har gida na ci mutuncin tsohuwa iya 


Nabil yace wlh daddy karma kafara inhar kana sona to karka yiwa iya komai Dan ran shatuwa ze baci intaji Kuma zata dada guduna Nima Kuma yanzu inasan iya kome zatai min bazan kulataba Nima kakatace nidai abinda nakeso da Kai ka tayani Nemo shatuwa mukuma je mubawa iya hakuri mubawa baffah hakuri  mukuma bazama neman matata adu inda take aduniyarnan 


MINISTER wani gumine yake ta keto Masa duda sanyin esin da ke wajan zare Ido kawai minister yake tayi Yana kallan nabil


Me hajiya Fatima zatayi inba dariyaba har da rike ciki tasaki Buda tace Allah ngdma ranar muke jira yau gashi tazo Allah karabamu da abin kunya ko wana irine Naga yanda zaayi wajan zuwa gurin iya ba da hakuri da wajan baffah da alhaji yanzu Dan Allah bakaji kunyaba tin ba a je ko inaba ai ga abinda muke ta fadamaka Ni da baffah gashi kashiga fadansu yanzu zaka dawo kaji kunya gashi dai yaro yadawo yace yanasan matarsa saura iya ita Kuma zamuga yazatayi garama ita tsohuwace akwai shiruftun tsufa Kai kuwafa ai Babu wani tsufa da kayi Allah kadawo da shatuwa lfy muyi kallo muna daga gefe yanzufa tinda kana san danka seka Rakashi neman shatuwa da bawa iya da baffah hakuri du kuma se kamanta abin kunyar da kayi nasan yanda San nabil yarufema Ido ko cewa yayi kabawa shatuwa hakuri Bata zakayi ko to karma ku sakoni Dan bansan komaiba Akan batan shatuwa shine mijinta shi zefi kowa sanin inda matarsa take to mawai yaushe ta Bata ai kullin in yazo se na tambayeshi ya matarsa se yace lfy take har sako nake bashi yakai Mata du  wayake kaiwa 


Nabil zuwa gaban hajiya Fatima yayi yace mommy Haka mukayi da ke kinface kema kina Sona Dan Allah in kinsan inda matata take ki fadamin ko wani abinda na keyine bataso du ki fadamin wlh Zan Dena 


shi dai minister har yanzo kallan nabil yake ko hajiya Fatima yakasa bawa amsa


Hajiya Fatima tace gaskiya abubuwa da dama bataso kakeyinsu Kuma ta fadamin Allah sarki har kuka take abin tausayi ko akansu ta guduma Allah masani  Kuma ai badan Allah zaka denaba kaga Kenan in kaganta ta dawo zaka koma ruwa kaci gaba da halinka da bataso Kuma dada guduwa zatayi 


Jiki na Bari yace wlh mommy nayiwa Allah alkawari Zan Dena danshi badan itaba tinda du kema kin fadamin Babu Kyau abinda nakeyi kecefa abokiyar shawararta kibani shawarar yazanyi na gyara ammafa wlh ko Ina iya take Sena Nemo gidanta na fada Mata halin da ake ciki dan itama ta Hura muku wuta kufito Mana da ita aini yau masifar iya ikwan Allah zata yimin Rana Kuma yanzu ita zanna gani inajin Dadi azaman shatuwa kafin aganta


MINISTER hannu binbiyu yasa yai tagumi Yana Jin ikwan Allah  


Hajiya Fatima in takalli minister taga yanda yake ta raba Ido ga gumi na ta keto Masa dariyace take dada kamata Babu halin yi saboda nabil Kar yaga tana ta dariya yadau du maganganunta azaman Wasa ko yaudara zega Kuma tasan inda shatuwa take Dan Haka ta hade Rai ta nuna batasan komaiba


Tace Ni yanzu nabil azamana na mahaifinyar,ka Kuma me baka shawara Zan baka wasu shawarwari da zasu anfaneka Amma seni da Kai 


Nabil yace mommy Ni yanzu nakeso muyu mgnar muje ko dakin,kine


Tace to tashi muje


Nabil yace daddy muna zuwa kaima da mgnar da zamuyi da Kai Kuma gobe kashirya mazagai zamu tare wajan iya da baffah


Hajiya Fatima da nabil daki suka shiga bayan sun zauna 


Tace nabil shawarar da zan baka itace ka koma isilamiya cikin biyu ayi Daya ko anemo maka malami Yana koyamaka karatu agida ko kashiga ta malam liman da ke unguwarnan daga magariba ne da Isha akwai Kuma na bayan sallar Isha zuwa karfe goma nadare kazabi Daya kana zuwa karkayi girman Kai ko wata kunya Babu kunya wajan neman ilimi daga Ni har shatuwa bamasan halayanka da kakeyi nafarko maganar Yan aikin gidannan kacire musu dokar in sun ganka suna durkusawa har se kabar wajan kacire wannan dokar in sun ganka Kuna gaisawa cikin mutunci da girmamawa Amma Banda wannan durkusan har kasa Babu Kai Babu Kuma korar wani Dan aiki dake gidannan ko karkashinka Kuma wayanda ka Kora ada ko kabatawa Rai a Yan aiki du kabisu  kabasu hakuri Wanda kaga yadace kayiwa alheri kayi Masa se maganar gudu da mota atiti babushi yanzu kudena Kai da yaranka kudena daukan hakkin talakawa Kai da su yanzu se girmamawa da Basu sadaka Kuma wannan kudin da kake rabawa abokanka suna aikata sabon Allah da kudin kadena ka koma rabawa talakawa maganar Jin kide kide du kadena ko karage ka koma Jin karatun Qur'an zuciyarka zatai sanyi zaka rage zafin zuciyar da kake dashi du in kashiga isilamiya zakaji waazi akai Kai abubuwa da dama insha Allahu du Zan na fadama ahankali kadaure kadena kazama me adalli da hakuri ga kowa kaji nabil kakoma mutunta Mata da darajasu kadena cewa ka tsanesu 


Yace to mommy du naji Kuma zanyi isilamiyar ta malam liman zan shiga nafi karuwa da wasu abubuwan sosai


Tace yauwa nabil Allah yaimaka albarka


Nabil yaji mgnar hajiya Fatima yafara zuwa isilamiya hajiya Fatima da kanta taje har gidan malam liman Tai Mai bayani Akan nabil zefara zuwa isilamiyarsa ta maza magidanta da matasa Tai Mai bayani halin da nabil yake ciki Kuma Yana  yawan temakawa da yawan yin waazi Akan zamantakewar Dan Adam ko malam liman yaji Dadi da Jin bayanin hajiya Fatima Akan nabil

 ranar da taje ranar nabil yafara zuwa da magariba


 hajiya Fatima taji Dadi sosai yanda taga nabil yafara canja halayansa ko Jin Waka yarage sawa yanzu ko abokansa basosai yake shiga harkarsuba har gida suke zuwa nemansa Amma Haka zasu hakura sukoma jiki bakwari gashi yanzu yarage yiwa abokan nasa bushaSha kamar da ko yajema baya Basu komai baya Kuma dadewa Yan aikin gidansu kuwa sunsamu yancin kansu Babu takura tsakaninsu da nabil Babu durkusawa har kasa ga kyauta da yake ta yawan yimusu kowa yaga canji Akan nabil mutanan garima sun sheda canjawar nabi almajirai in yafita Haka yake raba musu sadaka Dan Allah yadawo Masa da shatuwa lfy wayanda da ko almajirai bayasan ganinsu  karatu kuwa alhamdulillah Yana fahimta sosai daga anbiya Masa zerike ga yawan waazi da malam liman yake tayi Kuma Yana shiga kunnan nabil sosai Kuma Yana anfani dashi motocinsu yanzu in sun taho ako Ina memakwan kade,Kaden da akeji da amotocin yanzu kuwa karatun Qur'an akeji natashi in adaki yake ko afalo abin da yake sawa Kenan karatun Qur'an ko gudu da motoci in Yana ciki yanzu andena yanzu kowa yaban nabil yake da samasa albarka ko sarkokin da yake sawa da irin shigar da yakeyi da su fentin kansa yanzu du yadena zarya kuwa amazagai Babu adadi wajan baffah Akan ya temaka ya dawo Masa da shatuwa ga ciwan mararshi yatashi sosai saboda yawan tinanin shatuwa da tinanin garar da yakwasa awajanta hajiya Fatima yanzu tafara tausayin nabil garama yayi sosai yakoma shuru shuru Babu wannan zafin ran da akasansa dashi


 da nabil yaga baffah baze bashi amsaba Akan shatuwa Kuma baze dawo da itaba yayanke shawara ko baffah be saniba bare minister yaje ya Nemo gidan iya bakaramin rashin mutunci iya Tai masaba Amma be amsa mataba wajema yanema yazauna Babu korar da batai Masaba Akan yafice Mata daga gida nabil ko akansa yaki kulata Kuma yaki tafiya Dole ta sauko ta saurareshi aikuwa nabil Nagama fada Mata halin da akeciki Tai tsalle ta dire tace batasan zanceba tahau kuka wiwi Akan se annemo Mata shatuwa nabil da yaga haka yai ta tunzurata tana dada Hawa shima har da tayata kuka su baffah sun batar musu da shatuwa


Iya tace Ashe dandaudu me zamanman wando zaka canja kazama mekirki haka har kafara San shatuwa kaima Ashe dai kaima kyakkyawane haka kaboye kyan da Allah yai maka ka koma kamar matamaza nifa da kashigo ban ganekaba se da umaru yai min bayani yace Kaine tukunna na ganeka aiyanzu Kuma Ni da Kai Babu fada munshirya tinda kanasan shatuwata saura Miss Miss Shi,ai wannan uban naka bashi da mutunci baze Dena abinda yakeba Aishi basan shatuwa yakeba Kuma nasan be damuba da batan shatuwa kabarni dshi du zamu hadu Daman da tamu dashi yanzu dai katashi mutafi wajan usuman naji inda yakai Mana ita Kai Dan Miss Miss ka fadamin gaskiya ko dai ubanka Miss Miss yasai da shatuwa bamu saniba takuma fashewa da kuka Ni wlh da magunan yace na kawo Masa wlh Zan kawo Masa ba se yasai da shatuwa ba kumafa agabanka har alkawari naimai in yafara mutunci Zan tara Masa maguna na kawo Masa har gida takuma fashewa da wani kukan

 

Nabil du dadamuwar da yake ciki se da yafara dariyar maganar iya Yana mamakin karfin Hali irin nata agabansa tana zagemai uba 


 yanzu damuwa taiwa minister yawa saboda ganin halin da nabil keciki na damuwa gashi minister najin kunyar zuwa wajan baffah yabashi hakuri akan batan shatuwa haka Dole yacire kunya yaje har gida yasamu baffah yabashi hakuri Kuma ya rokeshi Akan Dan Allah in yasan inda shatuwa take ya dawowa da nabil ita


 baffah dariya shima yafara Yana kallan minister


Baffah yace Kai sani ko dai mafarki kakeyi ko da yake ai ba kunyace da kaiba in dai Akan nabil ne komai ma zaka iya kaga abinda nake gayama Kenan yanzu gashi yadawo San matarsa Yana ta nemanta yashiga damuwa gashi kaima kadamu kazo kana tayashi neman matarsa Amma da idanka yarufe kadinga rashin mutunci da abin kunya yanzu kaima cewa zakayi ka goyi bayan auran shatuwa da nabil ko Dan baka da kunya kariga du kagama zubar da girmanka na uba a idan shatuwa yanzu ai kadada hankali kakuma dau darasi Akan abinda yafaru Nan gaba San nabil yakuma rufema Ido wlh Fatimace me San nabil bakaiba yanzufa ko shuryuwar nabil baka saniba Ni nasani baka da lokacin tarbiyarsa se ta munamai gata yanzu da ba Fatima mahaifiyarsa da kacuci  nabil har karshan rayuwarsa tashi kabani waje se nayi shawara Akan mgnarka


Haka minister yadawo Abuja jiki Babu kwari 


Iya ce da nabil sukazo har gida wajan baffah Kan mgnar shatuwa iya nazuwa tafashewa baffah da kuka tana ruwan masifa yafito Mata da shatuwa Dan Miss ne yazo yagaya Mata shatuwa tabata Kuma yasan komai har da hajiya Fatima nabil na gefe Yana Jin Dadi tinda iya tasa Baki fole afito Masa da matarsa


Baffah hararar nabil yahauyi yace to kaji Dadi ka fado Mata hankalinka se yakwanta Mara kunya Daman matar taka tana da Rana haka ban saniba ai da cewa kayi baka Santa ko kamanta na tinama to inkai yanzu kana santa itakuma in tace Bata Sanka Naga yanda zakayi Dole ai ka saketa


Kunne nabil yatoshe yace bazan iyaba wlh Babu saki Ni da ita Kuma jikina yabani itama yanzu tana sona Dan Allah ka dawomin da matata baffah wlh ba nabil din da kasani bane da 


Baffah yace bani da lokacinka se kutashi mutafi Abuja wajan Fatima tinda yau in Allah Yayarda komai zezo karshe kabar mutane su huta da Kai da kakar taka Wai iya yaushe Kuma nabil yazama jikanki kuma kuka Dena fada


Tace ai yanzu mun shirya Kuma shinake gani azaman shatuwa tinda kun batarmin da shatuwa Kuma shi ne mijinta Ashe Dan Miss Miss na da kirki Haka ban saniba bakaga yanda yake yomin siyaiyaba har kudi yake bani su umaru ma hidima yake Tai musu Ashe yafi ubansa miss miss kirki tasa kuka


Shi nabil yanzu kome iya zatace akansa shi da ubansa baya Jin haushi dariyama take bashi


Baffah da su iya Abuja suka tafi sun Isa lfy minister nagida se ganin baffah da nabil da iya yagani nabil na rime da faggwan kayanta suka shigo 


iya Kai tsaye wajan minister taje ta zauna kusa dashi tace to miss miss Allah yadawo Dani Ina shatuwa Ina matar taka Fatima itama Ina Mata kallan me kirki Ashe ka goga Mata mugun halinka ko se wani hararata kake kana zaremin Ido du baze tsorataniba ka fitomin da jikata kawai inma magunan kakeso NASA umaru yatara maka yakawo maka kafito da shatuwa kafin inmaka rashin mutunci

 

Hajiya Fatima tace yihakuri iya kijira zuwa anjima Zan rakaki inda shatuwa take kici abinci ki huta tukunna kirabu da alhaji Ni da kaina Zan kaiki


  yau su Amina zasu dawo gida nanjeria mijinta yagama kwas dinsa har ma kwanaki suka Kara bayan wata shidan da sukayi zokuga murna wajan shatuwa ga kiba tayi ga Kyau takara tadada fari sosai ga turanci tanaji yanzu sosai ga yanzu in anganta bazaace tayi rayuwar kauyeba  misalin karfe takwas na dare jirginsu ya iso nanjeria hajiya Fatima ce tatura direba ya dauko Amina da shatuwa Kai tsaye gidan minister aka shige dasu shikuma mijin Amina da yaranta gida suka shige se Amina Taraka shatuwa zata shige gidan nata mijin



Lokacin da suka dawo nabil be dawo daga isilamiyaba iyace da minister da baffah kadai agida shatuwa da taga iya har da kuka iyama kuka tafafa tana mamakin girman shatuwa da kyan da takara  iya bakin masifa yamutu se murna ake tayi jikalle tadawo 



Tace Allah sarki nabilu Yana Ina yazo yaga shatuwa ta dawo yaro Dan albarka ai ingaya Miki Dan miss miss yajansa yanzu du baya masifar Nan da yakeyi



Takalli Amina kema yannan yar Ina yabanki sallah Zaki kasa alwala Ashe kema kinbi halin Miss Miss har dake asace shatuwa


Kafin Amina Tai mgn Sega nabil yashigo dauke da sallama abakinshi cikin nutsuwa yake tafiya gawani kamshin turaransa da yacika wajan kansa akasa yashigo bema kula da suwaye afalanba shatuwa Ido takura Masa tashi tayi tsaye tana kallanshi Yana dago Kai sukai Ido hudu da juna



Post a Comment

0 Comments