Dan gargajiya hausa novels complete

 [4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*

*(gargajiya ba addini bane)*




         *Na*

*Ummu Rahma* ✍🏻





 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini* 




       *1⚜5*




*BIRNIN KAHUTU*




  Kwance bahijja take cikin tsananin ciwo na nak'uda gashi babu kowa a tare ita, sai addu'o'i takeyi ga mahaliccinta na samun sassauci, can wani kuxari yazo mata ta ja jiki ixuwa kan mudubin ta ta dauko wayar ta ta danna lambar mahaifiyarta, bugu biyu ta dauka tare da karawa a kunnen ta, nan taji muryar 'diyar tata tasan ba kalau ba.


 "Umma ki yafe ni mutuwa zanyi ki rokar min Baba ya yafe min shima" Bahijja ke fadin haka inda hankalin  mahaifiyar yayi mutuqar tashi domin tasan diyar tata na tare da tsohon ciki ga ta kuma a gidan gargajiya, tana tsaka da tunani saiga Alhaji Mahmud ya fito daga wanka.


 Nan ta sanar dashi abinda me faruwa aikuwa ya zura kayan sa yace suje su ga halin da take cinki. Ya dauko motar sa suka tafi, da Isar su yace Umma ta shiga ta gano halin da take ciki, shigar ta da kamar minti biyu sai ga ta dawo a guje tana fadin Alhaji shigo mu kamo ta zuwa asibiti kan 'da ya fito gashi ko motsin kirki bata iyawa. 


Tun kan ta karasa Alhaji Mahmud yayi ciki a guje ya dauko ta suka nufi asibiti, isar su ke da wuya nurses suka kawo musu agajin gaggawa inda aka dauke ta zuwa dakin haihuwa Dan ceto ranta dana yaron.  





  A bangaren Badaru (mijin bahijja) kuma yana dawowa gida ya kutsa kai cikin gida yana muzurai shi a dole baya son raini, yana shiga yaga bata nan, nan ya fito ya shiga wurin mahaifiyar shi yake tambayarta ko ta shigo gidan, kada baki tayi tace yoo ni ina na ganta.



Suna cikin haka saiga k'anwar Badaru nan ta dawo daga aiken da aka mata, nan ta Sanar dasu cewa ai taga Umman ta sunzo sun dauketa zuwa asibiti, nan ya mulmulo wani uban zagi yace "mu za ai wa birnanci a karya mana tsarin iyaye da kakanni alhalin ni *'Dan Gargajiya* ne gaba da baya" fuuuu ya fice sai asibitin da yake tunanin nan zai samesu, aikuwa yayi Sa'a nan din sukaje danya hango surukar tasa a zaune, nanfa ya shiga cikin inda nurses suke da masu kawo yan haihuwa, nan fa Badaru ya fara tijara yana bubbuga kirji yana fadin "mu 'yan gargajiya ne ba'a mana iskanci, kawai an dauko min mata ba tare da an sanar da ko mahaifiyata ba an kawo ta nan, wannan ai reni ace mahaifiyata tana raye ace ba'a sanar da itaba saidai taji daga baya".




 Umman bahijja tace kayi hakuri mun same ta ne cikin wani hal... bata qarasa ya katse ta yana zuba rashin arxikin sa son ransa, duk abinnan dake wakana kowa ya kasa cewa Badaru komai har ma'aikatan jinyar, nan wata jajirtacciya ta taso adaidai lokacin dayake cewa uban wa yasa a kawo mishi mata asibiti, a zuciye ta dira gabansa tace ubanka ne......




Wai shin wacece wannan, kuma ya zasu kare da badaru? 



Amsoshinku na shafi na gaba.




Kuyi hakuri bana iya yin dogon shafi.





*Ummu Rahma ce*✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*



*(gargajiya ba addini bane)*




         *Na*



*Ummu Rahma* ✍🏻




 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*



     *5⚜10*



   Kai wane irin mara tausayi ne, wane irin mutum ne kai mai butulcewa rahamar mahalicci, ka ko san a halin da aka kawo ta nan zaka zo kana wa mutane rashin arziki.



 Badaru yace mata " ba ruwanki hajiya" yana muzurai kamar ya tik'i gudu a filin tsare. 


 Malama Ramatu tace da ruwa na mana saboda 'ya mace ka tab'a, kai zakaso ayiwa k'anwar ka haka ko 'yarka ko mahaifiyar ka.



 A a hajiya banda Babata wlh. Mal Ramatu tace harda ita, ita wannan da make ciwa mutunci ba uwar wata bace, duk wannan maganganun suna yin shine a hasale, Mal Ramatu kuwa kamar ta rufe shi da duka.


 Ta dora da cewa yanzu kai saboda Allah kayi daidai kenan wannan 'dabi'ar da kazo ka nuna har kana wani ikirarin kai Dan gargajiyane, to ka fada min inda ya samo asali a addini.




 Shiru Badaru yayi yana tunanin k'arfin hali irin na wanna mata, bai gama tunanin sa ba yaji ta jefo masa wani tambaya da cewa, 'yayanka nawa, Badaru kamar bazai amsa ba yace 'yata daya na biyu za a Haifa.



 Malama Ramatu tace Alhamdulillahi ka rubuta ka ajiye watarana zaizo kanka.




 Badaru zaiyi magana kenan wata nurse ta fito daga dakin karbar haihuwa dan kiran Malama Ramatu domin patient dinta ta sauka, dama ita ma mai haihuwa ta kawo, har tayi gaba ta juyo tace kuma zan dawo gareka.....




****   ****  ****



 *'KAUYEN  BANDAAS* 





 Hinde! Hinde! Hinde! Wai ina kika shiga ne ga awakai can zasu cinye ya'diyar dana zo da ita ki dafa min, jin shiru wacce aka kira da Hinde bata fito ba yasa shi 'dage labulan 'dakin nata Dan yaga ko tana ciki.




  Turus yayi ganinta tana sallah, nanfa ya hau sababi ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. 




  Yanzu Hinde saboda taurin kai irin naki sallar ma baza ki bari ta nuna ba sai kinyi ta yanzu, dama nasan za a rina, shiyasa liman yana sallame wa na taho gida dan in ganewa idanuwa, ke kullum bakya bin abinda iyayen mu suka bari saboda kinje birni kin koyo rashin biyayya, ace Juma'ar ma bazaki bari sai an dade da dawowa ba sannan kiyi taki saboda taurin kai.




 Duk wannan fadan da yake yi Hinde tana sauraran sa kuma tana jin takaicin halinsa da a komai saiya sako batun *Gargajiya*.




  Malam Maude kenan mijin Hinde daya gaji al'adu tun iyaye da kakanninsa, dan kuwa da ana sayar da al'adu wurinsa za aje, mutum ne shi mai tsattsauran ra'ayi, gashi kuma ba shi da ilimin addini mai zurfi.




 Bayan ya gama fadan sa yayi daidai da idar da addu'o'i da Hinde take yi nan ta fara bashi amsa cikin hikima da wayewa irin ta addini....





  Haba Malam bai kamata ace har yanzu ka kasa sakin wannan ra'ayin naka ba na kimai kace iyaye da kakanni, shifa addinin Allah ba ruwan sa da wani gargajiya ko rashin ta, amma har yanzu ka kasa fahimta ta.




Ke rufa min baki, nawa kike da har kika San me duniyar ta 'kunsa, ku da baku riski al'adun mu ba masu daraja, yana fadi yana huci.




 Hinde ce ta katse shi da cewa " yi hakuri Malam, ba wai ina nufin al'adun Ku basu da kyau ba a a kawai dai akwai inda ya dace ace basuyi tasiri ba musanman akan addini.



Ka Sani cewa acikin hadisan Manzon Allah akwai wanda yai mana nuni da zuwa masallaci amma mu suturce jikin mu kar muyi fita irin ta jahilci



 Kuma ita sallah da kake fadin in barta ta nuna idan kuma na mutu kuma kafin lokacin fa.




 Nan fa yay karaf yana fadin haba Hinde ke kullum baki da magana saita mutuwa, bari inje wurin ja'e in dawo kafin maraice, kiyi maza  ki kwa'da min ya'diyar ina nan dawowa, ya shuri takalmansa yai gaba. 



  Dariya Hinde tasa Dan tasan cewa Malam Maude baya son zancen mutuwa. 


 Nan ta tashi ta fara kokarin hada masa ya'diyar sa kafin ya dawo. 





Shin ya Malama Ramatu zasu k'are da Badaru a asibiti?




*Ummu Rahma ce  ✍🏻*

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*



*(gargajiya ba addini bane)*




         *Na*



*Ummu Rahma* ✍🏻




 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*




        *10⚜15*





  Tsaye Badaru yake yana nazarin kalaman Malama Ramatu tare da jiran ta ta fito dan su 'karkare.




 Yana cikin tunanin yaji muryar ta ta dawo tana masa sallama, yayi mamakin haka duba da yanda suka rabu, abinda bai sani ba shine shi Malama Ramatu tana da saukin hali ga fahimta mai zurfi irin ta addini domin ya cancanci ayi masa sallama kasancewarsa musulmi.




 Amma a wannan karon bata dawo a hasale ba, nan ta fara masa da nasiha tana cewa " baka kyauta ba bawan Allah, ya sunan naka" jikinsa ne yayi sanyi yace sunana Badaru.




 Haba Badaru gaka a haka dai anga kamili mai nutsuwa amma kuma ka dauki wata dabi'a ka sawa kanka, duba ka gani nan duk mutane  ne kowa da abinda  yake fadi a kanka na rashin tausayi, shin Kasan bakin wani kuwa.




 Badaru yace kinsani ne Babata kawo ta fa sukayi basu sanar da Inna ta ba shine na fusata sos.....



 Malama Ramatu ta katse shi da cewa to da kuma ta mutu fa ga kan 'da ya fito ita kuma bata da karfi, in ba a taimaka mata ba Kasan abin da zai biyo baya?.




 Nan dai tayi masa nasiha ta nuna masa kuskurensa tare da mata al'kawarin zai daina, tayi murna da jin haka, Matan wurin kuwa sai kallon su ake wasu na dariya suna cewa gaskiya kin samu 'da, shidai zuwa yanxu yayi sanyi dan ya ji nasihar da aka masa.





  Suna zaune tana fada masa yadda zaiyi bayan anyi haihuwa yana amsa mata da to.




 A wannan yanayi wata nurse ta fito tana fadin " ina Wanda suka kawo Bahijja Mahmud" nan fa badaru yayi kicin kicin yana fadin "kinji ko Babata anma cire sunan ta daga Bahijja Badar...... bai 'karasa ba tace wato dai bazaka bar batun *gargajiya* ba kenan, ai a addinance mutum da suna Ubansa ake kiransa koda kuwa ya kasance ba musulmi ba, sannan yayi shiru, suna haka ne Umman bahijja ta nufo su tana fadin ta sauka an sanu 'da na miji.




 Badaru bakinsa kamar ya yage sai zabga murmushi yake.




 Bayan ta koma ciki Badaru  yace  Babata ya za ayi, nan ta fada masa ya samo wa mai jego abinda zataci sannan inda hali ya siyo wa jaririn kaya ko kala uku ne, nan badaru ya fiddo kudi ya miko mata, tace masa a'a muje dai in raka ka ka siyo (🤣).




 Malama Ramatu kenan mace ce mai gudun duniya, nan suka rankaya zuwa bakin 'kofar asibitin inda masu sayar da kayayyaki suke zauna, anan aka zabo kaya daidai da kudin Badaru domin tace kar ya matsa ma kanshi, a kullum.kayi amfani da abinda kake dashi yafi alkhairi, anan ma Badaru ya siyo musu abinci harda madara Wanda hakan ya faranta ran Mal Ramatu ganin ya dauki maganar ta.





 Nan suka dawo cikin asibitin kowa na kallon su cikin sha'awa da burgewa.




  Malama Ramatu ce ta mika wa Umman Bahijja kayan Wanda itama tayi farin ciki tayi mata godiya sannan ta wuce ciki.





 Malama Ramatu ta fito waje dan har yanzu ba a gama da patient dinta ba, tana zaman jira ta hango 'dan nata (Badaru) ya nufo ta......




****  **** ****




  Malam jauro yana zuwa ya iske Ja'e 'karkashin wata bishiya yana ta gyaran tsohon keken sa,  nan suka gaisa tare da yiwa juna barkwanci dan babu laifi akwai ban dariya ga wadannan abokai, suna tsaka da hira saiga 'dan gidan Malam Ila ya nufo su yana kuka sosai, duk suka zuba masa ido jin dalilin kukansa, nan ya sanar dasu baban shi ne ya rasu, nan fa cikin malam Maude yace 'kuuuuuuuu saboda tsoro, gashi an manyanta ga kuma tsoron mutuwa, dadin da'dawa kuma ma'kocinsa mai rasuwar.




 Nan ya daidaita nutsuwar shi suka rankaya zuwa gidan malam Ila.





 Isar su keda wuya mata suka dinga bullowa ta ko ina kafin kuce me gida ya cika dankam da mata said koke koke akeyi.....





To wai shin a wannan garin me wadannan Matan zasu aika ne?





Malama dai da Badaru fa har yanzu suna asibiti,wai shin ya zata kaya ne?.




Ku biyo bi a shafi na gaba.




*Ummu Rahma ce* ✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*



*(gargajiya ba addini bane)*



         *Na*


*Ummu Rahma* ✍🏻



 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini* 



       *15 ⚜20*


 

  *Gidan makokin Malam Ila*



   Mata ne dan'kam a gidan banda koke koke babu abinda kake jiyowa wasu harda birgima ana fadan kalmomin da basu dace ba.



 Ita kuwa matar malam Ila tayi 'kuri a gefe tun tana hawaye har ta kai ga hawayen baya iya fita saidai ajiyar zuciya. 



 Ana zaune cikin jimami da kuma dakon gama ha'da malam Ila dan mik'a shi gidansa na gaskiya, wata tsohuwa ce tayi sallama tare da shigowa tayi wa kanta mazauni, 'dauke take da 'kullin kayanta.



  Wannan tsohuwa dai ba wata bace illa malamar 'kauyen bandass a cewar su,  sunanta malama Hakama, amma asalin sunanan Iya Dije, ana kiran ta da *Hakama* ne saboda duk kalma 'daya a zancen ta saita sa *Hakama*  ita ce mai shigar da matar mamaci takaba. 


*_Niko nace yau naga ikon Allah, shin takaba ma sai an shigar da mutum_* 🤔



 Ana zazzaune sai ga gawar malam Ila an fito da ita nan fa mata suka rude da wani gigitaccen kuka, haka aka fita dashi zuwa kushewar sa, malam Maude yaso ya zille dan baya 'kaunar mutuwa ko kadan balle zuwa ma'kabarta, da 'kyar malam Ja'e ya ja shi suka tafi.


 

 Anje ma'kabarta za a sanya shi a rami kenan saiga wani tsoho ya gabata yana mai cewa, ai ba ai masa addu'a ba irin wacce iyaye suke yi kafin binne mamaci, nan fa kowa yayi tsit yana sauraren shi. Tsoho kuwa ya ta'kar'kare yace su maimata abinda zai fa'di, suka ce to.


 Yace Abuna Rabbi, Abuna Rabbuka, Hasken madina walaii, ( 🤔) kowa dai ya zuba masa idanu kasancewar lokacin ilimi ya fara wadatar su ba kamar kakanninsu ba, nan dai aka matsar dashi gefe akayi yadda musulunci ya tanadar.


 Bayan sun dawo kuma aka dasa wata sabuwar al'ada.



Acikin gida kuwa Malama Hakama tana jiran a dawo daga kai malam Ila ta shigar da matar sa takaba.



****  ****


  *ASIBITI*

 


 Badaru ne ya zo wurin Malama Ramatu ya samu wuri ya zauna ya fara cewa " Ha'ki'ka Babah ta da ace za a samu iyaye irinki da anyi farin ciki, (a lokacin yasa hannu ya goge kwallar da ta zubo masa) ya cigaba da cewa da ma mahaifiya ta tana nuna min daidai da rashinsa da abubuwa basu lalace min ba Amman inaaa bana samun haka. 


 Malama Ramatu ce ta juyo Dan sauraren abunda yake fadi.......



*WANENE BADARU*



  Badaru dai matashi ne 'Dan kimanin shekaru 32.....


Ku biyoni......

  


Wai ya zata kaya ne a 'kauyen *Bandass* wurin shigar da matar mamaci takaba? 🤔 


Ya rayuwar Badaru take kasancewa ne?


Mu hadu a shafi na gaba. 



*_Congratulations Nigeria_*




*Ummu Rahma* ✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(gargajiya ba addini bane)*




         *Na*


*Ummu Rahma* ✍🏻



 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini* 



        *20⚜25*



  Badaru matashi ne 'dan kimanin shekara 32, an haife shine a can birnin kahutu, 'kannen sa hudu, uku maza 'daya mace, Allah ya wa mahaifin su Malam Datti  rasuwa tun suna yara, kafin rasuwar sa ya ba wa yaran sa tarbiya daidai gwargwado.



 Mahaifiyar Badaru mace ce mai tsaurin ra'ayi  kuma ga ta da a'kida irin ta mutan Da.


  Badaru ya taso mai biyayya ga ilimi mai zurfi musamman na addini, yana da shekara 18 ya sauke Al'kur'ani mai girma. Tun bayan kammala karatunsa na gaba da primary bai samu ya cigaba da karatu ba kasancewar mahaifiyar sa ta 'ki amincewa ya cigaba da karatu wai a cewar ta yahudanci ne, Dan ita mace ce mai akidar *Gargajiya*.



 Haka rayuwar sa ta cigaba da wakana, Idan yayi abin bajinta sai ta kushe, idan ya yi wa dangin mahaifinsa alkhairi sai ta 'dau fushi da shi, ga ta da saurin fushi haka yasa Badaru yake gujin 'bacin ranta, tun ba ya bin abin da ta ke so har ya fara ganin daidai ne.



 A haka ya dauki 'dabi'ar ta, amma wani lokacin yana kokarin gujewa hakan.


*_kalubalen mu iyaye, mu Sani cewa duk yanda muka bi da 'diyan mu to a haka za su taso, mu tuna cewa fa amana Allah ya bamu akwai ranar kar'ba, mu guji San zuciya saboda wata akida ta daban wanda ba fa'din Allah ba_*



 A haka har Allah ya sa suka hadu da Bahijja 'yar gidan Malam Mahmud suka fara soyayya, nan ma an yi dauki ba dad'i kafin ta bari ayi auren.


 Bayan auren nasu ta hana Bahijja sakat a cewar ta ba ta biyayya saboda ba ta da irin halayyar gidan, musgunawar yau daban na gobe daban. Wannan kenan......



 Malama Ramatu tace Badaru ina jinka ya kayi shiru, nan ya 'dora da cewa " mahaifiya ta ba ta nuna min abin da ya kamata in yi, idan na yiwa iyali na hidima takan nuna min cewar ba dai dai ba ne, ga yawan korafi da shiga hakki, idan na yi magana ta ce ba ni da biyayya, a dalilinta ne na fara kora 'kwaya amma ba ta ta'ba nuna damuwar ta ba, wannan rashin arzikin da nazo nayi anan ma 'bacin rai ne ganin an ta'ba min ita, ina ma..... bai 'karasa ba Malama Ramatu ta dakatar da shi.





**** ****


 *GIDAN MAKOKI* 


 Malama Hakama ce a na'de akan wata tsohuwar tabarma inda ta fara jawabi kamar haka......


  Murya a sha'ke ta fara da cewa " Allah ya jikan Ila hakika babban bango ya rushe *_(mata mu kiyaye idan an yi mutuwa, wannan kalmar ba ta dace ba a musulunci)_* yau zaki fara takaba dan haka matso nan ki ji dokokin ta



 Inna Habi ce ta matso, nan take tsohuwa ta janyo ta ta zaunar akan wata tabarmar kaba ta na cewa yauwa Habi sai hakuri yanzu dai ki maimaita duk abin da na fadi ta ce to, nan dai ta karanto mata wasu siddabaru da ban samu jiyo wa ba saboda koke-koken mata.


  Da farko dai zaki dinga yin sallah kafin lokaci ya yi (🤔), na biyu kullum ya kasance akwai tsintsiya a kusa da ke, na uku duk sanda lokacin sallah yayi butar da yake alwala a zuba ruwa aciki, na hudu duk sanda aka gama abinci a zuba a kwanon sa a bayar sadaka, ki dinga cin abinci sosai da man shanu domin takaba ta na cin 'bargo, wanka kuwa sai bayan sati 'daya kuma banda magana da karfi ra'da-rada za a dinga yin ta, kuma kar a bari gashin kanta ya fadi 'kasa ko 'daya.........


 *(ikon Allah🤔, Alhamdulillahi ala Ni'imatil Islam)*



Ku biyo ni dan jin ya za a 'kar'kare a wannan 'kauyen.



Malama fa da 'Dan nata Badaru har yanzu suna asibiti


 Mu ha'du a shafi na gaba





*Ummu Rahma* ✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(gargajiya ba addini bane)*




         *Na*


*Ummu Rahma*

 ✍🏻



 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini* 




       *25⚜30*



 *_Afuwan masu bin lbrn Dan Gargajiya na jin shiru kwana 2_*



*_JINJINA GAREKI NABILA ZANGO ( MAI NASARA) AM PROUD OF YOU_*




 *GIDAN MAKOKI*




  ..... Malama Hakama ta 'dora da cewa, kuma kitson ma idan za ayi guda uku kawai za a ayi.




   Sannan bayan kin gama takaba za ki yi sadaka da abubuwa masu yawa dan murnar fita daga takaba.




 Duk wadannan bayanai da ake yi Hinde matar malam Maude tana jin su, takaicin rashin Neman ilimin su yana damun ta kwarai da gaske, duk da cewa Inna Dije (Hakama) ta girme masu sosai hakan bai hana Hinde yi mata gyara ba.




_Tabbas addinin musulunci sauki ne da shi kuma maslaha ce Babba, duk wanda ka ga ya aikata abu ba daidai ba to ka dawo da shi bisa turba mai kyau_




  Hinde ce ta fara bayani kamar haka....



.

 Ita takaba ba'a shigar da matar mamaci kamar yadda Inna Dije ta gabatar, da zarar an kau da mamaci ita matar tasan da cewa ibada ta hau kanta, domin shima ibada ne, za tayi takaba na watanni hudu da kwana goma, yin hakan zai bada dama a San ko tana tare da rabo (wato juna biyu) wasu malaman kuma sun hadu akan cewa za ayi amfani da zuwan jinin ta na al'ada idan mai yi sau biyu a wata ne, da zarar tayi jini uku to ta gama takaba. 




  Sannan batun shafa man shanu da cin sa kuma wannan zance ne na mutan Dá, ita takaba bata cin 'bargo, sallah kuwa akan lokacin ta za ta dinga yi ba kafin lokacin ta ba, akwai wani hadith da yake magana akan cewa *_Duk wanda ya aikata wani aiki ba daga cikin abin da aka umurta ba, za a mayar masa_* sannan idan anti kwana arba'in za ta iya zuwa gaida mara lafiya ko wurin ta'aziyar rasuwa amma banda zuwa gidan biki ko suna,  wanka kuma kullum za ta dinga yin abin ta amma ba da sabulu mai kamshi ba, wadannan su ne abin musulunci ya shar'anta.




 Wurin yayi tsit kowa na jiran yaji abinda Malama Hakama za ta ce, basu gama tunanin su ba suka jiyo muryar wata mata tana fadin " hakika abin da wannan baiwai Allah ta fadi haka yake domin da ba, a samu magana  ba ni zanyi sai kuma gashi an samu wacce tayi bayani kmr yadda musulunci  ya ya tanadar mana, hakika a zamanin baya babu wadataccen ilimi a na dora komai ne abisa tsarin *Gargajiya* wanda yin hakan ba hujja ba ne acikin addini domin ance mu nemi ilimi a duk inda yake kuma muyinamfani dashi, ni ma bazan manta da wani labari da kaka Inno ta bamu ba run Muna 'yan yara" 



*Labarin kaka Inno*

  

 Ta fara da cewa idan akayi mutuwa aka kai mutum makwancin sa, za a zo ayi mass tambayoyi kamar haka... 



Baiwar Allah mai kwanciyar tsakar 'daki meye abu daya... sai tace Allah ne abu daya. Meye abu biyu... Rana da wata ne abu biyu.... Meye abu uku ... Murahun mu ne abu uku. Meye abu hudu..... Gabas da yamma kudu da arewa su ne abu hudu. To fa bayin Allah kunji labarin kaka Inno wannan dai ya na mazaunin tambayar kabari, ina hankali zai 'dauki wannan, da duk ire-iren su. Kowa ya jinjina labarin kaka Inno harda masu darawa🤣.




 Hajiya Saude kenan yayar malam Ila, tunda suka ji labarin mutuwar dan uwansu suka zo garin kasancewar su a wani garin suke da ban.




 Nan 'yan kauyen suka yi murna jin cewa ai takabar da muusulunci ya tanadar ba irin wacce suke yi ba ce, nan kowa ya hau tambayar abin da ya shige masa duhu kyma suna samun amsoshin su.




Ana haka har aka yi kwana bakwai, hajiya Saude ta basu gudunmawa mai yawa, sunyi kukan tafiyarta domin ba laifi sun samu ilimi a wurinta, ganin haka tai musu al'kawarin dawowa idan ta samu iko tai musu nuni da su dinga zuwa wurin Hinde domin kuwa a 'dan zaman da suka yi ta fahimci Hinde na da ilimi mai zurfi sai dai rashin mataimaki.




 Nan suka yi bankwana suka wuce da al'kawarin Hinde za ta dinga basu taimako dai dai gwargwado.....




Shin kuna ganin Malan Maude da amince da haka kuwa 🤔.




Ku biyo ni a shagi na gaba.



*Sorry for the late post*




*Ummu Rahma* ✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(gargajiya ba addini bane)*



         *Na*


*Ummu Rahma* ✍🏻



 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini* 



       *35⚜40*



*_Sis Najer'art (YARIMA SUHAIL) tnz for the dedication Allah ya bar mu tare_*


*_Nabeela Zango Allah yasa kin fara WAYE NE lfy kuma ki gama lfy_*



*SHAFIN MASOYA*


*Billy luv*

*Humaira Shuwa*

*Dije ontop*

*Ina miko jinjina*


*Afuwan masoya 'Dan Gargajiya na rashin ganin post kwana biyu, hakan ya faru ne sanadin rashin lafiyar da na yi kwana biyu, amma na samu sauki, ina ji daku*





 Hinde ce ta nisa bayan malam Maude ya gama sababin sa ta juyo ta amsa sallamar Balki (wacce ta shigo).



 Malam Maude kuwa 'kin tafiya yayi ya samu gefen runbu ya ma kansa mazauni, nan Hinde ta fara yi wa gwaggo bayanin abinda Allah ya tanadar a cikin Al'qur'ani game da rabon Gado _(ayi min afuwa lokaci bazai bari muyi bayani sosai ba)_




  Bayan ta gama jawabin ta ne Gwaggo tayi mata godiya sannan ta fiddo kullin Leda daga gefen zaninta ta 'mika wa Hinde



'Karba ta yi sannan ta mata godiya ta juya wurin Balki dan jin abinda ke tafe da ita.




 Bayan sun 'kara gaisawa Balki ta jefo tambayar ta kamar haka, "Hinde ni kuwa ina son ki warware min wannan batu na sha'anin hakkin magidanci ga iyalan sa, shi ne ya kamata ya nemo abin masarufin gida ko kuwa matar gidan ce".  Malam Maude da ya yun'kura zai fita 'kwar gida komawa ya yi ya zauna Dan jin amsar da Hinde za ta bayar.




  Balki ta ci gaba da cewa mijina baya wadata mu da kayan masarufin rayuwa kama daga sabulai izuwa cefanan su kuka da daddawa, idan nayi magana  sai yace ba hakkinsa bane, ai tun lokacin kakanninmu suke hidima da Kansu, kuma a wa'azin Hajiya Saude na ji ta fara bayani akan hakki na abokan rayuwa kuma banji karshen lamarin ba  na tafi dauko hatsi a 'kauyen yamma.




 Daga kan gwaggo har malam Maude shiru su kayi dan jin jawabin da Hinde zata sauke.




 *A GIDAN BADARU*




 Bayan komawar su Badaru ya ji nasihar Malama Ramatu inda ya siyo abubuwan bukata sosai ya jibge mata kuma yana kokarin kiyaye hakkin da Allah ya dora masa. 




 A bangaren Bahijja kuwa Ashe Malama Ramatu ta same ta kuma tayi mata nuni da cewa ita ce zata iya saita mijin ta ya dawo hanya domin kuwa mace ta na gyara mijin ta komai gur'bacewarsa kuma tayi mata alkawarin daura 'damarar saita shi in Allah ya so.



 Kwanaki sun shude ana gobe suna Innar Badaru ta dira sashen 'Dan nata dan gudanar da al'adar taron suna.




Wai ya za a yi ne a 'kauyen Bandaas?  




Innar Badaru wacce wainar zata toya ne a gidan sunan 'dan 'Danta? 



Ku biyo ni 




*Ummu Rahma*✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(gargajiya ba addini bane)*




         *Na*


*Ummu Rahma* ✍🏻



 *Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini* 


 *Jinjinar ban girma gareki NABILA ZANGO ina tayaki murnar kammala novel dinki lafiya Allah yasa a amfana da darasin dake ciki Amin*


*_Wannan shafin naki ne kyauta_*




      *30⚜35*



      *ASIBITI*



  Malama Ramatu ce ta katse shi da cewa, duk abinda mahaifiyar ka za ta yi ba ka da tamkar ta, tunda kasan abubuwan da take sa ka aikata ba daidai ba ne sai ka guji faruwar haka.



Ka kyautatawa dangin mahaifinka, ka yi wa iyalin ka adalci ta hanyar kula dasu sai ka ga Allah ya bu'da maka.



 Kayi mata biyayya kuma kayi mata addua Allah yasa ta sauko daga ra'ayin ta na baya.


 Ka zamto mai riko da gaskiya a duk inda kake..... 


 Kukan da ta ji yana yi ne ya sa ta tsagaitawa, juyowa tayi ta kallesa cikin tausayi ta 'kara masa da nasihohi masu ratsa zuciya.



 A na haka Umman Bahijja ta fito tare da nufosu, nan suka tsagaita Dan su ji da wanne uziri take tafe, nan take sanar musu cewa an basu sallama, murna sukayi gaba  'daya sannan ya nufi titi dan nemo masu abin hawa



Fitar sa kenan aka kira Malama Ramatu domin basu sallama.



 Nan dai suka rabu cikin kewar juna tare da alkawarin kai mata ziyara, dimin a dan zaman su da ita ya fuskanci mace ce mai addini da amana kuma ya dauki damarar sauka daga akidar sa ta *Gargajiya*




**** ****


     *KAUYE*


 Assalamu Alaikum! Assalamu Alaikum!  Malam Ja'e ne yake ta faman sallama a 'kofar gidan malam Maude.


 Sama-sama malam Maude ya jiyo sallama lokacin yana kishingide bayan dawowar sa saga masallaci.



Mi'kewa yayi ya nufi 'kofar gida, da zuwan sa ya tarar da Ja'e tsugunne a gefen danga.



 Nan suka gaisa tare da 'kara yiwa juna gaisuwar rashin abokin su Malam Ila. Tare da masa Addu'ar Allah ya ji'kan sa.


 Suna cikin hira sai ga wata tazo ta shige zuwa cikin gidan malam Maude bayan ta gaisar dasu.



 Shigar ta kenan Malam Ja'e yace da malam Maude "ince dai ko lafiya naga gwaggon su Mado ta bugo sammako kamar mai shirin zuwa gona"  oho ni ina zan sani tunda dai tare da kai muke zaune ta wuce, to Allah dai yasa lafiya suka ce Amin sannan suka cigaba da hirar su.  



*Cikin gidan Malam Maude* 


 Sallama gwaggo tayi taji shiru ko da ta kara shiga ta tarar da Hinde ta na sallar walaha nan ta yi wa kanta mazauni tana jiran ta ta idar.



 Cikin 'yan mintuna kuwa ta idar, bayan sun gaisa ne gwaggo ta ce wurin ki nazo Hinde, naji malamar burni tace duk mai tambaya ya zo ya sameki shine na zo in miki wata tambaya. 



 Hinde tace to Allah yasa na Sani gwaggo, tace Amin Hinde.



 Nan gwaggo tace "wai shin ya gaskiyar wannan lamarin yake, wai da gaske ne ana fitar wa da aminan mamaci ihsani kafin a raba wa magada gadon sa?


Hinde ce race a'a a cikin Al-kur'ani mai tsarki Allah yana cewa......


 Bata 'karasa ba ta jiyo malam Maude yana fadin oooo Hinde abin naki har ya kai ga haka, dama tunda naga shigowar wannan matar na ga ta dade na biyo bayan ta, na San wannan sammakon ba a banza ba wallahi, yana yi yana kumfar baki........ 


mamaki ya hana Hinde iya furta furucin da yazo mata, ana wannan hali sai ga mace ta biyu ta doko sallama

 To fa (🤣) .



Ya zata kaya ne?


Mu hadu a shafin gaba.




*Ummu Rahma*✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏻‍♂👳🏻‍♂Dan Gargajiya👳🏻‍♂👳🏻‍♂*


*Gargajiya ba addini bane*


            *40⚜45*


      *RANAR SUNA*


  Innar Badaru ce a zaune ta hakinmce a gaban Mai yanka ta na fadin yadda za a yi da fatar bayan an Fe'de, a cewar ta ai duk  na kakar yaron ce, Mutanen da ke wurin kowa yayi shiru dan gudun 'bacin ran Inna. 



 Bayan an kammala ta sa kanwar Badaru ta kinkimar mata sai 'bangaren su.



 Ana nan zaune saiga maro'ka nan sun billo,  nan fa wurin ya kaude da hayaniya, Kafina ankara Inna ta dauko jaririn ta mika wa  'daya daga cikin marokar a Cewarta me Jego ce Za tayi musu Kari (lik'i) sannan ta amshi 'danta bayan ta basu 'korai  na hatsi. 



  Kowa yayi Mamakin wannan salo na Inna kuma an rasa me cewa komai. 



 Da 'kyar dai Bahijja ta yi  yadda Inna ta ce saboda gudun fitina,  a haka dai Inna tayi ta fito da abubuwa iri iri. 



 Da yammaci iyalan gidan su bahijja suka iso,  ai nan da nan Inna ta tarbe su da 'korafi Akan basuyi saurin Zuwa ba dan sallamar maroka da mai yanka (bayan Badaru ya bar mata komai) a cewar ta ai haka akeyi🤔


  Nan dai ta tilasta sai da ta raba su da 'dan wani abun, sun mik'e da shirin wucewa ciki sai ta tsayar dasu da cewa "ban ga Kun gabatar da abin da ya kamata ba" wata daga cikin tawagar ce tace kamar me Kennan Inna?.



Nan Inna ta karkace ta fara da cewa "na farko za a  bada shaddar kakan yaro duk da ba ya raye sannan sai toshin 'kanne da yayyan mijin Nata,  akwai Kuma dahuwar abincin Rana da za ta yi har tayi kwanaki  arba'in sai Kuma..........  bata Ida fadin zancenta ba suka katse ta da cewa "lallai Innar Badaru abin naki 'Kara gaba yake, to mu ba za mu iya da wannan *gargajiyar* taki ba ehe,  haba da me za mu ji.


 Nan dai ta yi ta sababi daga 'karshe Kuma ta wucewa sashen ta tana  bambami da Jiran dawowar Badaru. 




  *'KAUYEN BANDASS*



  Hinde ce ta fara bayani cikin hikima da 'kwarewa, tace " shi dai *HAKK'I* Muhimmin al'amari ne cikin aure, hakkin miji ne ya wadatar da iyalan sa da abubuwan da suke bukata tun daga kan abinci, sutura, lafiyar, makwanci kai har da abin da shafi walwalar su baki daya



  Ba tilashin mace ba ne ace ita za ta samar da wadannan abubuwa idan kuwa akai haka an tauye ta domin mata rauni ne da su, sau da dama zaka ga basu da juriya amma suna da 'dinbin tausayi da kulawa.



Malam Maude da ke gefe ya kasa kunne duk da ya ji kamshin gaskiya a jawabin da Hinde tayi sai ya basar, nan ya jefo tasa Kalmar da cewa " yanxu dai hinde in na fahimceki kina nufin ta yi wa mijin ta bore kenan ko.ya kike nufi wai"



 A'a malam ni ban ce ta yiwa mijin ta bore ba kawai dai na nuna mata abin da ke da inganci ne a shari'ance.  Shiru malam Maude yayi yayin da gwaggo ta mik'e da niyyar tafiya, sallama ta yi wa Hinde da Balki ta wuce, a soron gidan ta ci karo da Hajara 'kanwar Malam Ja'e da alama dai itama tana tafe da nata uzirin



 Jin sallamar Hajara ya tunzura Malam Maude yana fa'din " ni fa hinde ba zai yiwu ba, da sassafiyar nan ko sanwar koko baki 'daura ba kin mayar min da gida sai kace dandali.


 Allah ya huci zuciyar ka malam, yanzu zan kammala Insha Allahu cewar Hinde.


 Nan ya shuri takalman sa ya nufi tirken dabbobi. Hajara da tayi sororo a tsaye tana tunanin masifa irin ta malam Maude ta ji ana cewa 'karaso mana Jaru, ga wuri ki zauna. Bayan ta zauna ne suka gaisa sannan ta fara jawabin ta kamar haka....


  



****  ****

 

 A 'bangaren Inna kuwa sama sama aka jiyo hayaniya yana tashi nan dai kowa ya dunguma zuwa ganin me ke faruwa ne.



To faaa 


Muje zuwa



 *Ummu Rahma*✍🏻

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(Gargajiya ba addini bane)*



           *Na*


*Ummu Rahma*



*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa irin ta addini*




 *Sorry! Sorry!! Sorry!!! Fans din Dan Gargajiya, ayi min afuwa*



*Na sadaukar da wannan shafin ga dukkannin masoyan Dan gargajiya*😘😘😘😘



      *45⚜50*


 Zuwa wani 'Dan lokaci 'bangaren Inna ya cika dam, kowa yana shirin jin ba'asi.



 "Haba Laure ki dai ji tsoron Allah, haka mu kayi da ke, kin ci arziki kin mance shi ne kika kasa tuna abunda nayi miki lokacin bikin diyarki, to bari in tuna miki, samiru na saiti shida na kai miki da saitin silba (ci bari kallo) da hatsi na 'kwarya biyu da dubu guda (1) shine dan kinibibi kika dauko wata jemammiyar turmin zani da sabulu kwara hudu kika lallabo kika kawo min, ahayye wallahi da sake". (Inna ce ta ke yiwa kawarta Laure tijira akan biki wanda suka mayar dashi kamar ibada).



  Laure ta ce kiyi hakuri Innar badaru, shekarun ne suka ja shiyasa na dab manta amma zan karo miki.



  Ai dole ki mance, a zaton ki kinci lalai ko, to da sake  gara dai ki yunkuro daga shi kuma mun gama buki da ke.



 Mama Hansai (kawar Inna) da tun da aka fara wannan bidiri ta na gefe tana jin ikon Allah, bayan kowa ya natsa ne mama hansai tace da Inna " ni kuwa Innar Badaru ya bikin namu yake ne"  yauwa 'yar gari kinji masu son zaman lafiya cewar Inna.  " ai dubu uku na bhudima kacin bikin Burema da ruwa kura biyu na hudima (🤣).


  To ga wannan cewar mama Hansai inda ta mika wa Inna zunzurutun kudi dubu biyar da kunun gyadar ta a cooler mai zafu da dadin gaske, nan Inna ta amshe tana washe baki da rattabo godiya.



 A haka akai ta yin bikin suna gidan Inna kafin da yammaci kowa  ya watse zuwa gidansa.


*_kai mata mu guji wannan al'ada ta biki da mukeyi, ace duk abinda aka baka saika ninka 🤔 idan kuwa mutuwa tazo.mana to fa mun tafi da bashi kenan, Allah ya ganar damu_*



  **** ****

     *KAUYE*


  Kwanaki sun shude, abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda sauyi da Matan Kauyen ke shirin kawowa a gidajen su da kuma tarbiyar yaransu, da juma kara zuwan Hajiya saude, wanda sai da tayi kwani bakwai kafin ta wuce, nan ta kara wayar musu da kai, sunji dadi sosai daga baya kuma Hinde ta dora daga inda aka tsaya.



  Wata ranar asabar bayan malam Maude ya dawo daga masallaci ya kishingida bacci ya fara daukar sa ya jiyo kamar hayaniyar mutane a kofar gidansa bai gama tunani ba ya ji a na ta doka sallama a kofar gidansa, mikewa yayi ya fita dan ganin me ke faruwa.



  Fitarsa keda wuya ya ga mutane kusan su sha biyu kowa da alama a fasace yake.



  Sallama yayi musu suka amsa sama-sama kowa na muzurai, nan dai malam Maude yai karfin halin cewa "bayin Allah ince dai ko lafiya".  Lafiyar kenan cewar wani murdadden mafarauci da ke tare da karan farautarsa.



  Ku dakata cewar  wani dattijo da ya dan fisu sassauta fushin fuskarsa, Ya cigaba da cewa munzo ne akan batun matar ka Hinde, ta juyar mana da ra'ayin Matan mu ta Billo mana da sabon tsari , wannan mafarauci ya ce to ka tabbatar ka ja mata kunne, kuma duk ranar da muka kara ganin matan mu a nan gidan sai mun mika ku kotu can cikin birni.



 Suna cikin wannan sa'insar suka hango wani matafiyi da alama dai bako ne, kallin sa suke yi har ya karaso kusa da su inda yayi musu sallama tare da tambayar gidan mai gari



 Kowa ya yi sakak'e kafin.daga bisani wani matashin magidanci  ya ce taho muje in kai ka Allah yasa dai kai din bakon alkhairi ne, murmushu kawai ba'kon yayi yace Insha Allahu.



Nan ya raka shi har gidan mai gari sannan aka musu iso ya barshi anan ya juya Dan komawa kofar gidan malam Maude.



 A hanya ya hadu da abokan tafiyar sa suka wuce gidajensu gaba daya.



Malam Maude kuwa a zuciye ya shige gida yana 'kwalawa hinde kira kamar ta ci bashi. ...........




Ya za ta kaya ne a gidan malam Maude?


Shin wannan bakon wanene kuma da me ya zo?

   









*Ummu Rahma*

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(Gargajiya ba addini bane)*



          *Na*


 *Ummu Rahma*



*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa irin ta addini*



      *50⚜55*



  Malam Maude yana shiga gida ya fara sababi, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.




 Ita dai Hinde shiru tayi a zuciyar ta kuma tana ayyano abubuwa iri iri dan kuwa ta 'kudiri ko da malam Maude zai dauki mataki akanta ba za ta daina bayar da tata gudunmawar ba, ganin ta yi masa shiru bata kula shi ba ya sa ya fusata ya nufi rumfar da take aikace - aikace ya sungumo randar ruwar ta ya buga da 'kasa, wannan bai masa ba ya nufi tirken dabbobi ya kunce ilahirin dabbobin ta ya kora su waje, sungumar harawar da suke ci yayi ya wulla ta bayan danga(🤣).




 Duk wannan abin da malam Maude ya ke yi Hinde ba ta tofa ko kalma daya ba, nan ya shuri takalman sa ya nufi 'kofar fita Hinde kuwa ta ce malam a dawo lafiya (🤣).



Takaici ne ya kama Malam Maude ganin duk abinda yayi ba ta yi fushi ba har da masa a dawo lafiya, waje ya fita ya samu 'kasan wata bishiya ya zauna sabida takaici sai da yayi 'kwalla, yana nan zaune yaji ana shela kowa yaje 'kofar gidan mai gari akwai tattaunawa ta musamman.



Nan dai malam Maude ya mike ya nufin gidan malam Ja'e dan su tafi tare, a hanya suka hadu shima ya fito nan suka rankaya sai gidan mai unguwa.



**** ****


A gidan Badaru kuwa bayan kowa ya watse da dare Badaru ya shigo, nan Bahijja ta nuna masa abin arxikin da ta samu, nan Badaru ya ce a kaiwa Inna a ji me zata ce.



Ba dan ran Bahijja ya so ba ta kwashi kayan ta kaiwa Inna.



Inna kallon sama da kasa ta yiwa Bahijja kafin tace "lafiya dai ko na ganki da wannan tsohon dare" ta na fadi tana yatsina fuska.



Lafiya lau Inna dama kayan da muka samu ne na zo dashi in nuna miki,  to ai kamar yadda kika sani a al'adar mu rabawa biyu za kiyi ki bar rabi ki tafi da rabi.



Bahijja ba dan ranta ya so ba tayi yadda Inna tace mata dan gudun 'bacin rai, ta sa 'kafa za ta fice Inna ta ce mata " yauwa kee gobe kar a fara suyar nan a bari sai na bullo ehee.


Bahijja da to ta amsa sannan ta fice zuwa sashen ta zuciyar ta a cunkushe da irin abubuwan da Inna ke mata.


****  ****


 *GIDAN MAIGARI*



'Kofar gidan maigari ya cika ma'kil kowa na jiran jin jawabin maigari da dalilin da yasa aka tara su 



Maigari ne ya fara jawabi kamar haka......



*Manage pls*




*Ummu Rahma*

[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*



*(Gargajiya ba addini bane)*



          *Na*


 *Ummu Rahma*




*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa irin ta addini*




        *60*

  

*LAST PAGE*



 *GIDAN MAIGARI*



'Kofar gidan maigari ya cika ma'kil kowa na jiran jin jawabin maigari da dalilin da yasa aka tara su 



Maigari ne ya fara jawabi kamar haka......

 

 Assalamu Alaikum mutanan gari na, hakika kowa zaiyi mamakin wannan kira da nayi na gaggawa, to bana so Ku tada hankulan ku ba komai yasa na tara ku ba sai don wannan bawan Allah da kuke gani a zaune a gefena ( yai nuni da ba'kon nan), yanzu zamu ji abinda ke tafe dashi.




 'Yan gari sukayi na'am da jawabin shugaban nasu sannan kowa ya maida hankalinsa dan jin da wacce ya zo.



 *JAWABIN BAKO*


 Assalamu alaikum, da farko dai sunana Malam Hudu ko in ce Almajiri, na fito ne daga yankin *KALLARE* wani sansani ne na Neman ilimi dake can gabas da kofar shigowa wannan gari naku na *Bandass*



 Hakika na dade ina son kawo muku ziyara amma ban samu damar haka ba, kasancewar komai sai Allah ya so.



 Yaa ku mutanan wannan gari hakika mafi yawan ku kuna gasgata *Gargajiya* akan *Addininku*, Ku sani cewa *GARGAJIYA BA ADDINI BANE*.



 Da yawan ku kun dauki al'ada ta kakannin da wasu ma basuyi rayuwa da su ba, idan anyi magana sai ka ji ana cewa ai *tun iyaye da kakanni*🤔 ba za ka ji ance tun zamanin sahabi wane ba da sauransu.


 Nan dai yai musu bayanai gamsassu cikin hikima da saukin harshe kamar yadda a ke so mai fadakarwa ya kasance.



 Cikin dan lokaci ka'dan da yawa daga cikin mutanan garin sun fahimci inda malam yasa gaba sa'banin malam Maude da yake ganin kamar zai aikata wani babban laifi ne in ya watsar da al'adun iyaye da kakannin sa (🤣).



 Nan fa Malam Maude ya shiga jerowa malam tambayoyi yana amsa masa cikin hikima da 'kwarewa, kafin wani lokaci malam Maude ya samu gamsuwa da jawabin malam.



 Wani daga can gefe ne ya jeho tasa tambayar yana cewa, " a cikin al'adun iyayen mu akwai masu kyau Wanda bai kamata ace mun yasar da su ba, shin zamu iya ci gaba?"  Malamin yace tabbas iyayen mu suna da kyawun 'dabi'un da ba zamu watsar ba kamar alkunya, zumunci, kawaici, dogaro da kai, kyauta, girmama yaro da babba da mayar da komai cikin sauki da fahimta, dukkan wadannan kuwa suna cikin addinin mu, wasu ne dai suke hadawa da canfe-canfe da sauran abubuwa idan anyi magana su ce *iyaye da kakanni*.



 Haka suka kasance tare yana wayar musu da kai har zuwa azahar inda sukayi alwala ya jagoran ce su sallah, bayan sun idar ma ya kara musu nasiha ingattaciya game da Ha'kkin iyalan su, anan da yawa suka fahimci inda fadakarwar Hinde matar malam Maude ya sa gaba inda suka ba malam Maude hakuri abisa abinda suka masa a kofar gidan sa, nan yace ba komai ai duk cikin rashin Sani ne.



 Sun kammala inda malam yayi musu akkawarin zaiyi watanni uku kafin ya cigaba da tafiya sauran garurawa kuma ya sanya musu lokutan daukan darasi, godiya suka dinga yiwa malam inda ya dakatar dasu da cewa Hakki ne a gareshi ya sanar tunda ya sani.


 Nan kowa ya yi shirin tafiya inda mai gari ya dakatar dasu da cewa ga abinci nan za a fito dashi, godiya sukayi wa mai gari bayan sun gama cin abinci kowa ya kama hanyar komawa gidansa cike da farin ciki. 



 A ranar kuwa duk matan *Kauyen Bandass* sunga canji, kowacce sai mamaki take yi, harda masu shiga gida da sabulun wanki(🤣).



 Malam Maude kuwa saida ya tsaya a bayan danga ya 'dauko harawar dabbobin Hinde da ya wullar sannan ya zagayo ya shigo gidan da sallama.



 Hinde da ke zaune a gefe mamaki ya cika ta dan rabon da Malam Maude yayi sallama tun tana amarya, bata gama mamaki ba ta ga bullo da harawa bisa kansa, saida ya sauke sannan ya fara mata bayani akan bakon malamin da akayi, kuma ya bata hakuri a bisa dukkannin abubuwan da ya mata.



 Hinde taji dadi sosai kuma tayi farin cikin zuwan wannan Malami 'kauyen su.



 Malam Maude ne ya Sosa kai yana cewa Hinde dabbobin sun shigo kuwa? Hinde ta ce aa basu shigo ba, nan yace to bari in nemo su tunda ni na kad'asu waje, dariya suka yi sannan ya fita.



Ba jimawa ya dawo da dabbobin Hinde ya mayar ya daure mata kamar yadda ya gansu, nan ya kirawo ta bayan ta zauna ne yake tambayar ta ko tana da sha'awar cigaba da koyar da Mayan 'kauyen, tace ehh malam in ka amince, nan malam Maude yace ya amince, ga waccan dan budaddiyar dangar sai Ku dinga zama a ciki, godiya ta masa da addu'o'i, sannan ya fice zuwa wurin Malam Ja'e.



Haka rayuwa ta cigaba da wakana a *'Kauyen Bandass* cikin jin dadi da aminci.




**** ****


 A 'bangaren Innar Badaru kuwa gari yana wayewa ko karyawa bata yi ba ta wuce sashen Badaru, abinda ba ta Sani ba kuwa tun bayan  fitar Bahijja a daren jiya ta kira babbar yarta Bilki Wanda syje yar wa da 'kani, jininsu ya hadu da Bilki sosai dan kuwa in ka gansu za kayi tunanin Uwa ce da 'diyarta domin Bilki Babba ce sosai. 


Bilki ba ta Barin ta kwana duk Wanda ya tabo ta ko wani nata ya Shiga tasku.



 Hausawa suka ce duk sanmakon ka wani a tafe yake kwana, dan kuwa ana idar da sallah Bilki ta sa babban 'danta ya kawo ta a Babur, tana zuwa kuwa ta shiga ciki kasancewar ranar Badaru shima sammako.yayi zuwa daurin aure a Maiduguri, yana fits suka iso.



 Bahijja ta yi murna da zuwanta nan suka gaisa sannan ta nuna mata ragowar kayan da Inna ta bar mata.



Tabdijam ai kuwa ta ba ci lalai ba saita maido dasu kaf, dauki sauran ki ajiye kafin gari ya washe.



 Inna kuwa a gadarance ta shigo gidan ko sallama babu tana kallon abin yankan da ke rataye a tsakar gidan, duk abin nan da take yi su Bahijja da Bilki suna kallonta ta Taga(window). Bats fi minti hudu da shigowa ba sai ga wani mahauci da ta aika ya zo, da sallama ya shigo, bayan sun gaisa tace ya kunto ragunan, haka kuwa akayi ya kunto su ya 'dora bisa bisa Leda.



Wancan babban ka raba shi kashi biyu ka ware gefe,'karamin kuwa ka cire 'kafafun bayan, yace to, gab da zai fara yankawa Bilki ta daka masa wata tsawa tare da fitowa, ba mahaucin ba hatta Inna da Bahijja saida suka tsorata, Inna galala tayi tana kallon Bilki Dan bata manta artabon su ba lokakin da aka kawo Bahijja gidan.


 Bilki cikin fa'da ta fara magana da cewa "shi babban na waye kuma karamin.ma ina za a kaishi". 


Ai nan da nan Inna ta birkice Dan ta San Bilki ba  ta da dama "dama babban na uwar miji ne day an kuma na uban miji" ta karasa cikin dakiya. Bilki ta ce a wanne dalilin?  Inna tace haka a keyi a al'adar su.  Bilki tace to na datse wannan al'dar akan yar uwata Ku dai da kuka dauke shi a matsayi tilas sai Ku bada himma, wlh ba yau ba na sake jin labarin an taba mata abin yanka sai an sake, wooo duk fadan Inna sai tayi la'kwas bats tanka ba, Bilki ta 'Dora da cewa kuma kayan da kika dauka ji maidosu ko in Shiga har sashen ki in debo, shidai mahauci yayi gwalam yana kaklin ikon Allah kafin daga bisani su wuce da Inna zuwa sashen ta bayan ta yi wa mahaucin umarnin ya fara yanka musu naman.



A 'bangaren Inna hatta da abin Sosa kunne Bilki ba ta bar wa Inna ba sai da ta karbo, da hantsi yan uwan Bahijja sun hallara kowa yayi mamakin ganin Bilki, nan Bahijjaa ta musu bayanin komai, wuri ya kece da dariya kowa na fadin albarkacin bakinsa.



Bayan sun kammala  suyar ne Bilki ta raba ta fitarwa da kowa nashi aka ware na Inna tare da turmin atamfa da kwalbar turaren wuta aka kaiwa Inna, Bilki ce ta kai mata aikuwa faran faran ta amsa suka mata sallama. 


Tun daga wannan ranar Inna ta sassauto ta rage wasu daga dabi'unta na *gargajiya* suka zauna lafiya.


A bangaren Badaru ma ya shiryu ba laifi Dan yakan kawowa Malama Ramatu ziyara.


A kauyen Bandass ma zama ake cikin aminci da wayewa irin ta addini.


*ALHAMDULILLAH*



Nan na kawo karshen labarin Dan gargajiya. Allah ya sa mun dauki darasi a ciki. Saimun hadu a sabon novel mai suna *HASSADA*



*JINJINA BAN GIRMA GAREKI NABILA RABI'U ZANGO

(MARUBUCIYAR ZAMANI) *



*UMMU RAHMA*✍🏻



Post a Comment

0 Comments