===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 1
==>Sauri take tagama watsa ruwan domin bugun
da akema qofar palon su yafara bata haushi,
tasan cewa ba kowa bane illa sumayya da
Rufayda iyayen yawo, taja tsaki.mtsww! Ta bude
murya afusace tace wai dalla cire qofar
zakuyine? Walh Nazo gurin duk zakuci
ubanku.,taga dai alamun bama jinta suke ba,
adaddafe tagama wankan tai saurin daukar towel
dinta wanda kadan yawuce rabin cinyarta. ko
gama daurawa batayiba saboda tsabar Haushi ta
bude qofar bayin ta fito tana fada. Gashin nan
nata yayi kwance agadon bayanta gashi baqi
sutuf ya kwanto har a fuskarta abinka ga farin
fata sai tayi gwanin
sha'awa ga sajen dake qarama fuskar nata kyau,
ta nufi palon tana qara goge fuskarta da towel
din jikinta,. kunfita tin dazu kunbarni agida ni
daya kamar mayya alhalin kunsan su momy basa
nan, kuma yanxu kun dawo ne zaku isheni da
nocking. yau sai kunsha ranqwashi tafada tana
kokuwan bude qofar da izzarta domin sotake da
tabude ta cafko daya dan tasan zasu iya
tserewa,
Tofa mezai faru!?ji kake tasss! Sun gabza
karo.,ta fasa wani uban qara don tsabar firgitan
datayi ga zafin buguwa, ruqota yayi da hannu
daya dayan hannun kuma yana qoqarin mulmula
mata goshinta Inda sukai karo.cike da alamun
tausayi Yake fadin oh sorry sister kinji tsoro ko,
ita kuwa har yanzu jikinta karkarwa yake sbd irin
ruqon dayayi mata gashi daga ita sai towel
.hannayenta suna dunqule akan qirjinsa ta matse
hammatarta sosai don tana gudun towel dinta
karya fadi, shi kuma hannunsa yana tsakiyar
bayanta inda ya tallabota lokacin datake qoqarin
faduwa, daqyar ta iya daga hannu daya ta riqe
hannun nasa dayaketa faman mulmula mata inda
ta buge,
cikin rawar murya kamar Wanda take shirin yin
kuka tace. Yaya afnan daman kaine? Yace eh
sannu kinji, tace dan Allah yaya afnan kayi
haquri walh bansan kai bane nazaci su rufy ne,
duk wannan maganar datake shidai kawai ya
zuba mata ido ne yana kallon bakinta wanda
yake qara
daukar hankalinshi ga sweet voice dinta daya
tirsasashi lumshe ido alokacinda ta idar da
maganarnata,. Kawai saitaga yaqara
hogging dinta da dayan hannun nasa yana qara
matseta jikinshi, qirjinta yai wani mugun bugawa
rasss!!!,ya dubeta cikin wani irin yanayi data
kasa fahimtarsa yace sis su momy
fa?,hankalinta atashe tace suntafi gaisheda
INNA ne tare da cewa yaya AFNAN sakeni mana
hawaye suka gangaro a bisa kyakkyawar
fusakarta. Hankalinshi yatashi amemakon
yasaketa saiya qara hogging dinta sosai tare da
sassauta murya yana kiran sunanta daidai
kunnenta ahankali salma!salma!salma
kitaimakeni dan Allah salma nah.,
>BUTULCI KO SO!!!.? Part 2
==>Arazane take kallonsa taga yadda idonsa ya
kada yai jajur wani irin masifaffen tsorone
yakamata gashi sai qara matseta yake aqirjinsa
yana wani irin numfashi sama! sama! Cikin tsoro
da fargaba taqara fadin ya
afnan kasakeni mana dan Allah muryarta na
rawa saiga hawaye sharrr! Haba tuni afnan
yafara kai halshensa yana lashe hawayen nata
tareda rugumeta Sosai har saida tai wata yar
qara tace na shiga uku yaya kayi haquri, tafara
ja dabaya kozai saketa tasamu ta ruga daki
amma inaaa inda tadaga qafa nan yake mayarda
tashi., yaya..yaya dan...wani irin kallo da yake
mata yasanyata daburcewa takasa qarasa
maganar, cikin wata irin murya mai tada hankali
yake fadin salma salma kintashi hankali na.
salma bazan iya rabuwa dake ba, afusace tace to
kasakeni man yaya. Ya watso mata wani irin
kallo Wanda saida tai qasa da kanta sannan
cikin rawar murya yace bazan iyaba my dia, .tuni
afnan yayo palo da ita tana tutse tutse ga towel
dinta yana neman zamewa
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 3
==>Har kiran ya katse be dauka ba.,tab da
wanne zaiji da kiran abbanshi ko da tashin
kankalin dayake ciki.,yana cikin wannan tunanin
ne kiran Abba yasake shigowa qin dauka yayi
domin hankalinshi kusan baya jikinshi,.salma!
Salma!yake fadi ahankali yana rugume da
ita,.wani irin jiri yaji yafara dibarshi da tsabar
ciwon kai!.ahankali ya dauko wayarshi daqyar ya
iya nemo numbern aunty sadiya ya danna
kira.,tai ringing harta yenke ba'a dauka
ba.,yaqara danna kira bugu biyu aka dauka
tareda sallama.,ko amsawa beyi ba.,yace aunty
kina gida ne? Eh ina gida afnan lapia kuwa naji
muryarka haka?!aunty ba lapia ba.innalillahi
tace meya faru kuma afnan bakada lapia
ne.,uhm yace aunty dan Allah kizo gidansu
salma yanxu dan Allah amma karki gayama su
umma nan zakixo kawai kitaho ne karki fadama
kowa kinji pls aunty ki taimakeni dan
Allah,.wai...kafin taqarasa maganan yakashe.
Taqara kira yaqi dauka.,afirgice tayo palo da
nufin fadama momy halinda afnan ke ciki.,koda
taxo saita tuna yace kawai tazo ne karta bari
kowa yasani.,juyawa kawai tayi da sauri dn
dauko hijabinta. Tai maza ta sanya hijab ta nufi
qofa ahankali take tafiya dan bataso momy taga
fitarta tace ina zataje.,tasamu ta fice tafara
sauri har zuwa bakin titi inda tatare me keke
nafef nahau.,har yanxu kiran afnan take amma
yaqi dauka.nan da nan suka isa gidan tasauka
tabiya me keke,tashige gidan cikin tashin
hankali ko sallama babu. Gogan naka yana rige
da salma jin dayayi an buga qofa GAM!!!.ya miqe
afurgice domin atunaninsa ko yan gidan ne suka
dawo.,nan yaga aunty ta fado palon a
60.,shikanshi saida yaqara rudewa.abin ka da
mare gaskiya ko aruwa tsuma yake.,ganinshi
tayi dagashi sai dogon wando da singlet.,ta bude
baki zatayi magana ta hango salma sharbe
sharbe kan kujera an dan rufeta da towel ga jini
dayaketa bin qafafunta.,, innalillahi wa inna
ilaihirraju'un tafada tareda daura hannu akai.,
afnan me kuma yasameta tareda qarasawa
gurin.tadafe qirji na shiga uku afnan waya
kasheta!?nan danan hawayen afnan suka qara
kwararowa tareda durqusawa yasa gwaiwowinsa
biyu aqasa aunty walh nina kasheta.nine
nakasheta da kaina ,aunty na shiga uku walh
fyade nai mata har said a ta mutu.,wa
iyazubillahi.,fyade afnan?meya kaiga wannan
aiki? afnan shikenan ka bata mana suna ta fashe
da kuka tareda dago salman shimadai kukan
yakeyi.,ta kalleshi cikin tsawa da kuka tace
katashi kaje yanxu kasamo me nafef mu kaita
asibity .,yace anty da sauran ranta ne.,ta daga
murya nace maka kaje ka kira ko.wai ma su
momy suna ina kayi wannan aikin,.walh aunty
nazo gaisheda su momy ne Ashe wai suna gidan
inna.,oh shine ka ida nufika akanta ko.,walh ba
da gangan nayi ba aunty ki yarda dani kinfi
kowa sanin wayeni kuma kinsan matsayin Salma
awajena,.mtsww tayi tsaki zaka tafi din kosai ta
mutun?da sauri yamiqe yasanya rigarshi ya fice,
miqewa tayi tacire hijab tadauki salma tai toilet
da ita tadinga wanketa tana kuka don gani take
kamar ta mutu ne,. Haka dazo ta dakko riga
tasa mata tashiga gara gurin,.sai gashi yadawo
da kanshi ya dauketa yai waje da ita sadiya tana
biye dashi abaya.,sai Horeb Hospital.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 4
==>suna isa akayi Emergency da ita,.nan danan
aka karbesu dan ganin yanda jikin nata yake .,Dr
da nurse ne tsaotsaye akanta sunata qoqarin
ganin numfashinta yadawo domin kuwa ba
mutuwa tayi ba doguwar suma ne.,wasu na kan
HQ dinta da har yanzu be danai jini ba.suka
gano anyi mata rauni ne sosai awajen nanfa
saida akai mata dinki akai mata allurori akasa
mata drift.,sannan aka akace akirawo Wanda
suka kawo ta dan tana buqatar qarin jini
yanxxun nan,.dan jininta yayi qasa sanadiyar
ciwon da akaji mata da kuma tashin hankalin
data shiga shima yataimaka wajen saukar da BP
dinta.,.nurse tafito suna ganinta suka miqe
dikkansu dan Allah ya ake ciki ta tashi kuwa?
tace kune kuka kawo Salma.eh suka fada
atare.,tace OK kuyi haquri taji sauqi sosai kuma
zata tashi insha Allahu saidai likita yace tana
buqatar jini yanxunnan.,da sauri yace muje
agwada nawa idan zaiyi adiba,sadiya tace muje
idan nashi beba aduba nawa,.suka wuce tare da
nurse aka gwada jinin afnan akaga zai iya bata
jini aka diba shima akace yadan kwanta ya
huta., ai ina yakasa kwanciyan suna fita shima
yatashi yabisu.,saidai ganinshi sukayi adakin
aunty dai tinda sukazo ko magana bata
qarayimishi ba saidai harara,.yaqarasa bakin
gadon yana fadin anty ya jikin nata. Ko kallonshi
batayiba,jiyayi yana Neman fadi saiyanemi wata
farar kujera datake bakin gadon yazauna,.yayi
wani ajiyar zuciya dayaga salman tanata
numfashi da alamun bacci takeyi.,nurse tagama
abinda take tace to dan Allah tana buqatar Hutu
karku yawaita surutu munyi mata duk abinda ya
kamata da allurori yadda zata samu tadan huta
dan ta wahala sosai kuma munyi mata dinki a
HQ dinta .,tafice abinta.,gabanshi yai wani
mummunan faduwa itama aunty haka.yanxu har
yayi mata lahaninda saida akai mata
dinki.,innalillahi kawai yake nanatawa
azuciyarsa,. aunty sadiya tana zaune a bakin
gadon tataba jikin salma tajishi kamar garwashi.
Sai hawaye kawai take shima dai afnan kukan
yake ba Wanda yacema wani uffan.,idan muka
koma bangaren gida kuwa.momy CE riqe da
hannun kahlid suka shigo gida sumayya da
rufayda suna biye da ita.suka ruga cikin gida da
gudu anty! anty!anty ina kike walh munyi miki
wayau kina bacci muka gudu mukabi su momy
gidan INNa kuma tuwon dawa mukaci da miyan
ayayo me dadi!..sumayya tace dallah kinata zuba
qilama har yanxu baccin takeyi kinsanta da
baccin tsiya.suka banko dakinta aguje suna
dariya.,adaidai lokacin momy tashigo palo riqe
da hannun Khalid.! kai ina antyn inji rufy
sumayya tace ko tana toilet ne.,aunty! aunty
suka hau qwala mata kira.,momy CE tace lapia
ina auntyn naku tashigane kuketa qwala mata
kira haka.,.sukace momy bamu ganta bane ai
adakin.,,,kamarya baku ganta ba bata toilet?.
Momy tataso da sauri tana salma!salma!.wani
irin iskancine haka ina taje tabar mana gida ba
kowa. Tafada tareda bude qofar toilet din,.,cub
mezata gani towel din salma ne yashe aqasa duk
jini.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 5
==>Da sauri tadauki towel din tabude wannan
yafi qarfin ace jinin al'ada.su Sumy da rufy kam
anyi tsuru tsuru,.ta juyo tareda daka musu tsaya
dan ubanku ina salman take? duk saida suka
tsorata.walh momy bamusani ba mudai mun fita
mun barta tana bacci.,innalillahi wa inna
ilaihirraju'un momy tahau salati tana tafa
hannu.,da sauri tayo palo tana rasa abinda
zatayi tafara zagaye gidan ita da yara sunata
leqe leqe.,su rufy kam baki yamutu tinda ran
momy yabaci daman gashi saida tace karsu biyo
ta..,bangaren su afnan kam sadiyace taciro waya
dantasan za a nemi salma bari takira tun kafin
hankali yatashi.,ta lalubo number momyn salma
takira harta yenke ba a dagaba don suna cen
suna zagaye tsakar gida har saida tai 3 miss
call.momy tace ai banga tazamaba bari inje
inkira yayanku nagaya mishi halinda ake
ciki.nanfa sukayo palo daidai sadiya tasake kira
ahanzarce momy taqarasa tai saurin daukar
wayan tareda sallama ina wuni momy lapia
sa'adiyya ko salma tazo gidanku?.shiru tayi
wasu hawaye suka zubo mata.momy taqara
cewa kinajina kuwa? Sadiya cikin kuka tace
momy muna nan tare da salma a horeb hospital
ankwantar da ita a emergency word taqara
fashewa da kuka.,,kuttt.kar kuso kuga gigicewa
agun momy subhanallahi sa'adiyya meya sameta
kifadamun dan Allah kota mutu ne?a a momy
bata mutu ba taqara fashewa da kuka ta katse
wayan,.momy kuwa jiki na bari tana fadin to
meya sameta yanxu ina salman take?sannan ta
lura ashe sdiya ta kashe..,ai tuni ta figo
hijabinta sai asibityn,.nan tabar yara tsuru tsuru
suma kukan suka kama,.Khalid ma haka yaketa
tsala ihu wai zai bita ko kulashi batayiba,.shiko
afnan tinda yaga sadiya tana
waya qirjinshi ke bugawa,daqyar ya iya cewa
aunty wa kika kira ne?ko kallonshi batayiba bare
tabashi amsa., bangaren ummansu sadiya kuwa
ummace tafito plo tana kiran sdiya
sadiya!.tashiga har dakinta amma shiru,lallai
yarinyarnan yanxu ficewa
tayi nida nabarta tadaura mana girki dan iskanci
saita fita babu ko tambaya daidai nan alhaji
yashigo da lapia hjy kiketa fada kedawa haka?
walh yarinyar nanne sadiya tafice tabar gida ni
inacen ina bacci ko tambaya batayiba,kuma
nabartane akan bari taje tai sallah ta daura girki
yanxu nafito naleqa kicin babu alamun girki
Ashe gaba daya ma gidan tabari sbd tamaidani
shakatafi.yanxu jibi qarfe 6 0pm duk inda taje
ai yaci ace tadawo,. ga gidan ba abinda aka dafa
metakeso muci?!.alhj yai ajiyar zuciya.yace
qyaleta hjy zata dawo taimin bayanin inda taje.
Sannan yace afnan fa?.tace afnan ai tinda yafice
yace zaije ya gaisheda INNA daganan sai yawuce
office wajenka yace wai kanason ganinshi.ko
beje office din bane?.uhmm alhj yace walh beje
ba kuma nakira wayanshi yaqi dauka daga bisani
ma kashe wayar yayi.tareda fadin zasu dawo su
sameni dukkansu.,momy tace allah ya
shirya.,barin daura mana ko taliya ne muci
ko?.alhj yace aa sha zamanki nayo mana
shopping saimu cinye sun tinda basuda
kirki saisuci ubansu idan sun dawo.,gaba daya
sukasa dariya tace kai alhj shikenan,.bari naje
nai wanka natafi masallaci to alhj saika fito,.
Momyce taqaraso afurgice tana tambaya kuwa
aka nuna mata word din dasuke,.tabude qofa
tashige afnan ne ya waygo dan ganin Wanda
yashigo yana ganin momy gabanshi yafadi yai
saurin sadda kanshi qasa!;taqaraso bakin gadon
tana fadin innallahi sadiya afnan meya sami
salman ne?!dan allah kufadamin mana:kuka tasa
musu gaba daya suka hau kuka ba Wanda yace
da ita uffan daga afnan har sadiya'.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 6
==>Qarasawa tayi bakin qadon ta zauna tare da
cewa sadiya harda qarin jini? Dn allah
kufadamun abinda yasameta gaba dayansu kuka
suke gani tayi babu me shirin bata amsa
cikinsu,.dan haka ta kama dube dube jikin Salma
ta duba nan ta duba cen.,itadai bataga ciwo ba
jikin salma saidai tsabar zafin jiki
dataji.,ahankali tajuya ta kalla afnan tace afnan
wai meya faru ne da ita!?.jiyayi kamar ta soka
mishi mashe a qirjinsa tsabar razanan dayayi da
tambayan nata.shjru yayi yai qasa da kanshi
kawai kamar muna fuki.,waya ta dakko
tamiqawa sadiya tareda cewa kiramun
Ahmad.,takarba ta kira sannan tamiqa
mata.,bugu daya yadauka kamar Wanda yake
jira,sannan yace momy nadawo gida naga yara
sunata kuka wai kintafi asibity salma ba
lapia?.tace eh daman nakira nafada maka ne
,.wani asibity ne momy?.nan horeb hospital ne
yace OK,.yana gamawa yafice tareda cema
sumayya ku rufe gidan yanxu zan dawo.,yafice
sai asibityn yakira momy taimai kwatancen word
din yaqarasa da Sauri.,.idan muka koma cen
gidansu afnan kuwa.,momyce ta kalli agogo
tareda cewa alhj anya yarinyar nan tanada
hankali kuwa kallafa qarfe bakwai ake nema
yarinyar nan bata dawo ba bayan fitarda tayi
bada iziniba!.alhj yace to bakiga afnan dinba
shima shiru shida yake dawowa qarfe 6, hjy tace
lallai yaran nan yau zasu gamu da bacin raina
musamman sadiya,.Yanxun haka qila gidan inna
ta nufa ko wajen salma dan nasan duk iya
yawonta kenan.,alhj yabata rai wato bataji
abinda nagayamata ba har yanxu tana
nan tana zuwa gidan kamar mayya ko.to zata
dawo tasameni ai ke kika daure mata gindin
taringa zuwa din..hjy jitayi dama bata ambata
gidansu salma ba dan har ran alhj yabaci
sosai.,nandai suka tashi danyin sallah.,,Ahmad
ne yabude qofa yashiga word dinda salma take
duk arude yaqarasa yana subhanallah momy
meya sameta ne haka?.tace gasunan su suka
kawota nayi nayi sufadamun mu sabbabin abin
amma sunqi magana saidai kuka kawai
suketayi.,asanyaye Ahmad ya kallesu sannan
yace sadiya kuyi magana mana don allah shima
kamar zaiyi kukan.,cikin kuka tace momy ku
tambayeshi yafi kowa sanin abinda yafaru nikam
bakina bazai iya fadi ba taqara fashewa da kuka
mai sauti..,nanfa afnan yafara dan Allah momy
kiyafeni momy kitaimakeni kiyafemin walh
banida burin cutar da salma arayuwa na.momy
bada gangan nayi ba kiyimin aikin gafara
momy.,daga momyn har Ahmad sototo sukayi
suna kallonshi yadda ya kofa gwaiwowin aqasa
yana kuka sosai.,Ahmad yace kufada mana
abinda ke faruwa mana kunsakamu acikin
duhu.,nanfa sadiya tace momy afnan ya lalatawa
salma rayuwa afnan yayima salma fy....kawai ta
fashe da kuka.,momy afurgice tamiqe sadiya
meyai ma salma din fadamun dan Allah., momy
ya keta mata mutuncinta har saida akai mata
dinki momy mun shiga uku., innalillahi wa inna
ilaihirraju'un suka fada daga momy har Ahmad
afnan kam jiyayi yayi mutuwar zaune.,Ahmad ne
yajuyo tareda cafko afnan ya miqar dashi yana
fadin afnan meya kaika meyasa zakai haka
afnan?gaba dayansu kuka suke wiwi,.ya kuyi
haquri Ku yafeni walh bada gangan nayi ba ya
duk hukuncin da kayimin daidai ne domin nayiwa
salma abinda yafi haka.,amma dan Allah ya
kaimin adalci .,momy tada tallabo kan salma
tanata kallonta tana Hawaye.,tace Ahmad
sakeshi.; kasakeshi nace.,ahankali yasakeshi
wasu hawayen takaici suka zuba masa.,nan tace
zauna afnan kafadamun yadda akayi ni nasan
d'ana bazai aikata abinda akace yayi ba.koma
zaiyi bazai taba kwatantashi wa salmanshi
ba.;kuttt..,momy batasan abinda yagani bane yau
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 7
==>Momy tai salati tare da cewa Ahmad riqeta
da sauri dan Allah.,Ahmad yai saurin cafko ta ai
tuni takaimai wani fizga sai gashi cen yayi gefe
guda yana tangal tangal.,ta cafko afnan dayake
malale aqasa jini yanabin fuskarsa .momy kam
salati kawai take tana fadin shikenan ta
kasheshi.,Ahmad dake baya yai saurin fizgo
sadiya ta baya har saida kanta yabuga bango
amma tana riqe da wuyan rigar afnan
tam!!.daqyar Ahmad yasamu ya matseta jikin
bango sosai.sannan
ya fixge afnan daga hannunta tuni momy tataso
tariqe afnan tareda kwantar dashi agurin tayo
gun sadiya da Ahmad yaketa faman turka turka
da ita.,suka matseta sosai suka fara tofeta da
addu'o'i.,ahankali tafara dawowa hayyacinta
Ahmad yabarta da momy tanata faman yimata
addu'a.,yafice da sauri yasamo ruwa yazo yafara
yayyafama afnan. Cikin ikon allah yafarfado
saidai yaji ciwo sosai akanshi wajen sai jini yake
fiddawa kamashi yayi sukayi waje dan asamu
atsaida jinin,.take aka karbeshi akai mishi
treatment din wajen aka rufe da bandage akaimai
alluri domin jikinsa yayi zafi sosai gashi yanata
numfashi sama sama!,nan aka daura mai drift
aka bashi gado.,.Ahmad yadawo bangaren su
momy nan yaga sadiya tana kwance kamar me
bacci"yafadama momy abinda ake ciki.',wayar
sadiya CE tai qara Ahmad yamaida dubansa gun
wayar sannan yasa hannu yadauka wayar yace
momy dadynsu sadiya ne yakira'momy tace to
dauka mana kuyi magana,.dauka yayi yakara
akunnenshi tareda sallama,.cikin fushi abbansu
sadiya yace waye kai!ina me wayar take?;Ahmad
ya sassauta murya yace abba nine fa"Ahmad
ne:yasake daka tsawa wani Ahmad din?;jiki
asanyaye yace Abba Ahmad yayan salma fa-bata
rai yayi to ina sadiyan!ahmad yace gata nan
muna tare a horeb hospital salma ne ba lapia
taxo dubata itama jikin nata yamotsa yanxu mun
samu tayi bacci ne kuma saiga kiranka_abba
yace subhanallah kuma shine bata fada mana ba
tayi tafiyarta.aida sun taho tare da hjy,yanxu
yame jikin!da sauqi Abba Ahmad yaqara dacewa
ai muna nan tare da Afnan shima anbashi gado
ya........momy tai saurin fixge wayar takashe
kiran sannan tace kana hauka ne!?me kake shirin
fada mishi to ina me gargadinka karda kasace
naji wannan maganar abakin kowa hatta
yayanka Habibullah ban yarda yaji wannan
maganar ba nagaya maka!;cikin rashin faminta
Ahmad yadubeta tare da cewa to momy ai
wannan maganar bazata boyu ba dole ne kowa
yasan abinda afnan ya aikata kuma koma me
akai mishi ai shiyaja makanshi wannan maganar
ai tafi qarfin a boyeta momy:'cikin sanyin jiki
momy ta kama hannun d'an nata hawaye suka
zubo afuskarta sannan tace Ahmad kataimakeni
da wanne kakeso naji so kuke baqin ciki ya
kasheni Ahmad kasan halin yayanka habibu
yanxu idan yaji wannan maganar me kake
tunanin zai faru ko so kake a haifi danda ba
ido;yanxu ga salma rai ahannun Allah ga sadiya
kwance afnan kwance so kake kafada yayanka
yaxo yaita hauka yanemi hanyar salwantar da
rayuwar wannan yaron ko kamanta zai iyayin
komai akan duk Wanda ya cutar da salma?!
yanxu abinda
kakeso yafaru Keenan baqin ciki yakasheni-
taqarasa maganar tareda fashewa da
kuka,.shima Ahmad kukan yafarayi'nan yazaunar
da mahaifiyar tashi kan kujera sannan ya
durqusa aganta yana kuka'yace momy na yanxu
ya kikeso ayi!?dan allah karki tada hankalinki
walh momy duk abinda kikace zanyi,.gani sukayi
sadiya tatashi ta zauna itama hawaye ne keta
faman sintiri a fuskarta da alamun ta jima tana
sauraronsu,.momy tamaida dubanta garesu
sannan tace Ahmad yace na'am.sadiya tace
na'am momy!,inaso kuyimin wata alfarma.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 8
==>momy tace ina roqonku dan Allah karbu
fadama kowa abinda yafaru kar wannan maganar
taje bakin kowa kubarta anan dagamu sai
allah,dan Allah kuyimin wannan qoqarin idan ba
haka ba abinda zai biyo baya me girma ne kuma
kanku saikunce mema yasa kuka
bayyana,.Ahmad yai wata ajiyar zuciya..,sannan
yace yanxu momy kina ganin wannan maganar
zata boyu!? wannan fa ba qaramar magana bace
yanxu idan an boyeta ya salma zata kasance
wajen
mijinda zata aura yanxu idan aka boye wannan
maganar anyi mata adalci kenan momy?!momy
tace Ahmad ba shawararka nake nema ba umarni
nake baka abinda nakeso kuyimin kenan duk
wani abinda zai biyo baya me sauqi ne akan idan
aka bayyana maganar nan.,sannan ai dole ne ma
afnan ya aura salma domin ayanxu babu Wanda
yadace da auranta idan bashi ba'.dan haka kuyi
abinda nace kuma kubar komai a wajena ni
nasan mezan fada musu!!sadiya taja wani
numfashi ta dubi momy tace momy be kamata a
quntatawa rayuwar salma haka ba momy walh
gwara ma a qyaleshi da babib din yai masa duk
abinda yaga dama domin ya cutar masa da
abinda yake matuqar tattalinta da rashin son
bacin ranta.dan haka yadace ya fuskanta
hukunci momy walh bana goyon bayan a rufa
masa asiri.,ta qarasa maganar tana kuka!,momy
ta dubeta sadiya hannunka baya rubewa kayanke
kayar kome yaronnan yayi yakamata muyi masa
adalci idan muka duba
tsakaninshi da salma bedace mujuya masa baya
ba dan ya aikata kuskure irin wannan danni na
tabbata ba halinshi bane,.dan haka sadiya kuyi
haquri kawai kubi abinda nace.,sadiya dai shiru
tayi Ahmad ne yai qoqarin cewa insha allahu
zamuyi yadda kikeso momy kuma babu Wanda
zaiji wannan maganar abakinmu dayardar Allah
munyi miki alqawari;momy tadan saki fuska tace
yauwa Ahmad allah yaimuku albarka yanxu
kiramin habibu nagaya masa muna asibiti.,kuma
inaso idan zaka tafi kuwuce tareda sadiya domin
su kwana da yaran nan.yakarba wayan yakira
yamiqa mata.,bugu 3 yayi taga an danna busy
bata damu ba tinda daman tasan baya daukar
kiranta saidai yakashe yakirata.,jim kdan kuwa
saiga kiran Habib tadau ka yagaisheta cikin
ladabi.ta amsa muryarta babu
annashuwa.,sannan tace habibu muna nan fa a
asibity salma ba lapia yanxu haka dai gatanan
sai abinda allah yaso,.what?momy meya sameta
wani asibity ne momy ina fatan dai tana nan da
ranta momy bani ita dan allah ko bata magana
ne gaba daya Habib yarikice momy tama rasa
amsar dazata bashi ajiyar zuciya kawai tayi
sannan tace muna horeb hospital ne saikazo
kawai takashe wayarta.,afurgice Habib ya nufi
daki fadeela tamiqe a tsorace tana fadin
sweetheart lapia kuwa?waye ba lapia.ko
sauraronta beyiba yaje yasaka farar jallabiyyarsa
yafito da sauri yana fadin asibity zanje yanxu
momy takirani take fadamun salma ba lapia
yanafadi yana qoqarin ficewa,.batayi mamaki ba
dan tasan yadda yakeson qanwar tashi aranta
taji haushi amma afili cewa tayi subhanallah
allah yabata lapia saika dawo kafin tarufe baki
shiyariga ma yayi waje,aranta kuwacewa tayi
allah yasa ta mutu inga qaryar iskanci.,taja
tsaki ciki ciki tajuyo ta rufe qofarta ta wuce
dyning ta zquna cike da haushi.,shiko gogan
naka tuni yafigi motarsa sai asibity,.a bangaren
su abban afnan kuwa Abba yakira yakira wayan
sadiya amma anqi dagawa tuni yafadama hjy
abinda ke faruwa sannan yace tai maza ta dauko
hijjabinta dan basuga tazama ba dan yaji ance
afnan dinshi ba lapia kome yasameshi
oho.,hankulansu duk atashe suka kama hanyan
asibity mu samman ma Abba da ko kadan
bayason yaji abinda zai cutar masa da
dansa.,suna isa saiga Habib ya iso nan suka
hadu a harabar asibityn daidai nan kuma Ahmad
da sadiya sun fito da nufin tafiya gida.,nan suka
hadu babu Wanda yatsaya wata gaisuwa Habib
yadubi Ahmad yace ina ne word din?!Ahmad yace
kuxo muje suka dunguma gaba daya suka nufi
inda salma take.,nan suka tadda doctor a tsaye
kan salma yana mata allura sannan ya cire ledan
ruwan daya qare yasa mata wani.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 9
==>Habib yai saurin qarasawa wajen jikinsa na
rawa yana fadin doctor ya jikin nata da sauqi
kuwa!?Dr yace yp zazzabine me zafi yanxu ya
rufeta nayi mata allurori yanxu yanada kyau
kubarta ta huta domin gaskiya taji jiki tana
buqatar Hutu bamason ana yawaita surutu
kubarta ta huta pls!Habib yace insha Allahu za a
kula amma Dr menene matsalar nata abinciken
da kukayi meyake damunta ne pls walh bata
saba ciwo irin wannan ba naga harda qarin jini
akai mata,.Dr yace eh abin ya danganta ne daga
irin mijin da kuka aura mata wata qila yafi
qarfinta kuma kaga qaramar yarinya CE gaskiya
kunyi mata auren wuri gashi kun
hadata da ba qauye marar tausayi yayi muku
kaca kaca da yarinya gsskia ina iya cewa harda
laifinku.,amma insha Allahu zata samu lapia
karku damu.yafada tare da bude qofa yai
ficewarsa inda yabar Habib atsaye yasaki baki
hannunsa na rawa bakinsa na motsi amma
yakasa magana gashi kuma yanada tambayoyi
domin shidai be fahimci zantuttukan likitannan
ba shin meyake nufi ne menene yasamu
salman!;momy kuwa da Ahmad da sadiya tinda
likira yafara zancen nan a furgice suke tsananin
tashin hankali yaqara ziyartar zukatansu kuttt.!!
hjy da Abba suma dai sun kasa fahimtar
maganganun Dr dan duk yasasu a duhu.,amma
shidai Abba hankalinsa be kwanta ba dan kuwa
bega afnan ba.,babban burinsa kawai a nuna
masa dan autan nashi,.Habib ne ya katse kowa
daga saqe saqen zuci jiki a sanyaye yace momy
nifa ban gane maganar Dr ba wai meya faru da
salma!?.momy ta maida numfashi sannan tace
Habibu wannan ba maganar nan bane.,yqnzudai
yakamata kuje kuduba afnan din ko ta maida
dubanta gun Abba tace alhj kuje kuduba afnan
din ko,. Habib yai saurin cewa haba momy
kifada mana abinda ya sameta mana mu fita
daga cikin rudaninda Dr yajefamu yanxu ga
salma a kwance afnan din shikuma meya
sameshi??!yaqara sa bakin gadon yataba jikin
salma agigice yajuyo yana fadin momy kinji
jikinta kuwa,.dan allah meya sameta ne idonsa
duk sun ciko da qwalla.,ta dubesu gaba daya
tace alhj muje wajen afnan din inyaso mayi
maganar a waje kaga Dr yace kar a yawaita
surutu!,alhj kan daman ya qosa yaga afnan dan
haka shiya fara bude qofa hjy tabi bayanshi
dukansu zuciyarsu cike da saqe saqe,.momy ta
kalla habib sanna tace kataso muje cen zakaji
qaddarar data afko mana yau.,amma inaso
kazamo me yadda da qaddara kuma karka tashi
hankalinka domin haka allah yaso sannan itama
ta fice sadiya da Ahmad sukabi bayanta.,da
sauri yamiqe shima yabisu yna nanata
maganarda momyn nashi tai masa yanxu a
zuciyarsa!yasan lallai akwai wani Abu me
girma,.suna shiga suka cimma afnan
kwance sai rawar sanyi yake hatta gadon dayake
kwance girgizawa yake.,Abba yaqarasa a furgice
yana fadin afnan mega sameka ne haka!,dan
allah kuyi mana bayanin abinda yasamu yaran
nan.nan danan masu saurin kuka suka fara
musamman ma wa Inda suka San abinda
yafaru,.momy tai ajiyar zuciya sannan tace
tabbas abin kuka ne yasamemu kuma dole muyi
kuka bazan hanaku kuka ba,.taqara da
cewa an tsutsemu an tsutsi salma yau anci
mutuncin mu anci mana zarafi anje har gida
anyima salma fyade na rashin tausayi.!!ta fashe
da kuka
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 10
==>Dukkansu saida suka razana da jin
maganarda momy tayi.,Habib ne yameqe hankali
tashe yace what momy fyade fa kikace salma din
akaiwa fyade!;momy tace tabbas kuwa anyi mata
fyade na rashin tausayi.dan dalilin dayasa
kukaga afnan anan wajen kenan domin kuwa
sanda abin yafaru da ita afnan yaje gidan da
nufin yagaisheni yanata sallama yaji shiru gashi
kuma yaga qofa abude sai yace bari ya leqa
falon ko muna bacci ne aiko gana shiga yaga
salma cikin wani hali juyowanda zaiyi saidai yaji
an buga mai qarfe akanshi nan take shima ya
fadi qasa sumamme,.yakai wani lokaci sannan
yafarka jini sai binshi yace domin anfasa mishi
kai daqyar ya iya qoqarin daukar wayanshi shine
yakira sadiya yafada mata ita kuma tai maza
taxo da mota aka kwasosu sai asibity nanne ma
aka gane Ashe fyade akai mata.,innalillahi wa
inna ilaihirraju'un gaba daya suka sa salati
sadiya kuwa da Ahmad suna mamakin abinda
momy ta shirya amma babu yadda suka iya dole
suyi shiru,.afnan dake kwance yana fama da
matsanancin zazzabi da ciwon kai.zuciyarsa ta
qara daukar zafi.tabbas shidai beji dadin yadda
momy ta rufa masa asiri ba,yazatai mishi
haka,wata qila data bayyana gaskiya hakan ze
iyasa ya mallaki salma amatsayin matarshi.ji
yayi kawai zuciyarsa tana qara masa quna da
zugi,shin kodai ya bayyana gaskia ne!?.,Habib
ne yataso jikinshi yana karkarwa yaqaraso
yazauna a bakin gadon da afnan yake.'ya dafa
qafarsa zuciyarsa kamar zata buga yana fadin
afnan ko kaga fuskar wanda yaima salma
wannan mugunta?pls idan kaganshi zaka iya
ganeshi!?nayi alqawari ko dan gidan uban waye
sainaga bayanshi tinda ya cutarmin da
salma!kuka ne ya kubuce masa tare da cewa na
shiga uku shikenan an lalatama sister na
rayuwa.innalillahi wa inna ilaihirraju'un",momy
ta dubi aljh tace dashi inaso sadiya taje ta taya
yara zama kafin mu koma gida yanxuma nace
tabi Ahmad su tafi,aljh yace ba matsala,ta dubi
Ahmad tace yakamata kutafi dan dare yayi sosai
anbar yara a gida,tashi kawai sukayi suka fice
ba tareda sun CE komai ba.,momy ta biyo
bayansu sukai sallama ta wuce wajen
salma,.Habib yasake maida dubansa kan afnan
yana qoqarin sake yimishi magana,.sai gani
sukayi yana wani miqewa yana nadewa jikinsa
yasake dafewa kamar wuta gaba daya sukayo
kanshi kar kuso kuga rudewa wajen Abba da
ummanshi.Habib ma yadan tsorata da ganin
yadda yakeyi.,dan haka da sauri ya miqe yace
Abba bari akira Dr.dasauri yafice sai gashi tare
da Dr umma dukta rude gani take kamar dan
nata mutuwa zeyi.harta fara kuka,Dr yayi masa
wata allura sannan yace su samu towel da ruwa
su dinga jiqawa suna goge mishi jikinshi
ahankali zazzabin ze sauka,.sannan akula kar
ana yawan surutu akanshi,.dan jininsa ya hau
saisun kula Dr ya fice,nanfa hankali yaqara
tashi!!,Habib ficewa yayi abinsa ya nufi gun
salma,yana zuwa yaga momy tana sallah
yazauna bakin gadon ya tallabo salma tanata
bacci saidai jikin nata har yanxu da zafi,.addu'a
yafarayi cikin ransa ya allah ka nunamin Wanda
ya keta haddin yar uwata.lallai an cutar mai da
yar lelenshi,umma ta idar race dashi yakamata
kaxo katafi gida ko,ya kalleta momy kije gida
kawai ki huta zan zauna da ita.,momy so nake
da zarar ta farka ta kwatantamun fuskar wannan
azzalumin;.momy ta girgiza kai tace habibullahi
abinda yafaru yariga yafaru,kaje gida abinka
nizan kwana da ita kuma Dr yace da wuya ida
zata farka yau,kuma kota farka ba lallai ne ta
iya wata
magana me tsawo ba.dan haka katashi kawai
kaje gida abinka.,,haka momy ta matsa masa
yatashi yatafi badon ransa yaso ba
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 11
==>Gari na wayewa sadiya ta kimtsa komai daya
kamata ta hada musu,.Ahmad yaxo yace idan
tashirya taxo suwuce shima zaije yaga yadda
suka kwana kafin ya wuce wajen aiki.sumayya
tasa kuka itama sai anje da ita taga
salma,.daqyar Ahmad ya lallabeta tareda
alqawarin anjima zai dawo ya kaisu idan anty
sadiya ta dawo sannan ta haqura,.suka kama
hanya sai asibity,suna shiga sukaga momy tsaye
akan salma suka qarasa da sauri,wai Ashe taga
tana motsi da qafarta ne shine duk ta rude wai
ko farkawa zatayi,.nan suka gaisa momy tace
suje su duba afnan rai abace sukaje badon sunso
ba,shima dai baccin yaketayi kamar
matacce,suka gaisa da umma sama sama Ahmed
yai sallama ya wuce abinsa,.sadiya taje ta
kawoma momynta abinci.sukaci sannan tatashi
taje ta duba salma ta dawo.,fitarta keda wuya
saiga Habib yaxo ya nufi qanwar tashi yna
tambayar momy ta farka kuwa,tace tadai dan
motsa yau da safennan,inaga da alamun
sauqi,likita yace babu wata damuwa zata tashi
cikin ikon Allah.yace ya afnan dinfa.tace shima
ba laipi kaje kadubashi mana.momy tayi tayi
yace shidai agaisheshi koyaje tinda ba magana
zai masa ba ai ba anfani,.ranar dai daqyar momy
tamatsa masa yatafi office yana maqale da
qanwarsa ko zaiga farkawanta amma shiru
hakadai yadaure ya wuce.,duk wannan abin da
ake inna bata sani ba.,aiko rufayda ta fakaici
idon sumayya ta salale sai gidan inna, tana zuwa
ta tadd inna a Palo taruga aguje ta fada jikin
inna tana haki,,inna tace yau naga arziki yannan
karyani zakiyi,daga ina kike haka kamar an
jefoki kodai kinyo tsokana ne aka biyoki.,tace a
a inna gudowa nayi sumayya bata sani ba nasan
zata iya biyoni shiyasa naketa gudu nasan
zataina nemana na barta ita kaidai.inna tace oh
kudai Baku rabo da shiririta.to ai yanxu zakiga
tabiyoki., ta dago kai a a inna ai bata isaba
tinda momy batanan kuma Khalid yana bacci
bazata fito tabarshi ba.,inna tace ina Maman
taku taje bayan jiya tabar nan!?rufy tace ai
tinjiya damuka koma gida bamuga anty salma
muna shiga dakinta mukaga jini a towel dinta
Ashe an yankata ne da bamanan shine momy ta
fita itama taqi dawowa aunty ne ma tatayamu
kwana shine....ai tuni inna ta hankadeta daga
jikinta takai mata duka ban gane an yankata ba
dan ubanki wani irin magana ne wannan ni zaki
kawoma shashanci.,rufy ta zumbura baki tace to
shine zaki dukeni ni gidama zan tafi abuna"inna
ta ruqota yanxu ina salman take?! Taqara turo
baki toba nace miki an yankata ba;,gaban inna
ya yanke ya fadi lallaima yarinyannan da gaske
take ko kuwa,.dan haka taqara jefo mata
tambaya! to ina mamanku tace ai tin jiya bata
dawo ba!,inna tasa salati innalillahi wa inna
ilaihirraju'un. Inna tayo waje tna qwalawa husna
kira!husna husna ta nufi sashensu,.momyn husna
ne tace ke bakyaji inna na kiranki husna tace ni
walh momy kinsan kiran inna yanzu haka ba
wani abin azo aji bane.,saiga inna tashigo
agigice ta miqa mata waya tace kirawomin
abubakar yanxu rafida tazo take cemin wai an
yanka salma wai mamansu ma bata kwana a
gida ba.,safiya tace wani irin an ynkata
kuma.husna ta kwashe da dariya tace umma kinji
ko yanxu shirmen rufy zaki kama,.inna tace
atafaf sai ankira mata abubakar.,husna ta kira ta
miqa mata, yana dauka inna bata bari sun gaisa
ba tace bukar
meyafaru da salma ne?!shiru yayi yana tunanin
waye yafadama ina abindake faruwa.tace kayi
shiru ina sauraronka kafadamun abinda yafaru
da salma.kame kame yafara inna..walh..inna
wayace miki.tsawa taimasa taredacewa zaka
fadamun kosaika rainamin wayau kodai salman
ta mutu ne da gaske.,yace a a inna bata mutuba
walh suna asibity tamaji sauqi inna ki kwantar
da hankalinki. Kuka inna tasa da salati shikenan
Ashe gaskiyane an kashe salma ba ason
fadamunne magana yake mata amma kojinsa
batayi duk. ya birkice gashi akan hanya yake
zaitafi asibity ba shiri ya jiyo yayo gidan Inna.,
husna da mamanta sunyi tsarko tsarko suna
kallon inna cike da mamaki.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 12
==>Zama tayi dirshan tana tafa hannuwa tana
cewa kungani ko yrinyar nan nasan haka nan
kawai bazatazo ta fada wannan maganar a
banza ba. Nasan ba hakanan ba akwai wani
abinda ake boyemin.,husna tace inna wani Abu
yafaru da salman ne?!tace gashi kuwa abubakar
yacemin suna asibity to da wuya idan salma tana
Raye., hjy safiyya tahau salati tace inna barida
asake kiranshi aji!;sai sukaji sallama abubakar
ne yashigo da sauri yayogun inna yana fadin
inna bata mutu ba tashi muje nakaiki ki ganta
.,tamiqe da saurinta tayo waje yabiyota
abaya,.husna tafito a guje tana fadin Abba nima
zanje kujirani Abba wai salman batada lapia ne?!
yace wai waye yaxo yafadama inna ne,.husna
tace rufy CE taxo tace mata wai an yanka
salma., murmushi kawai yayi yace allah ya
shirya jeki dakko hijabinki mutafi.,dasauri taje
da dakko suka fice akabar hjy safiyya a gida.,ita
kuwa rufy tuni ta sulale tai gida abinta., basu
tsaya ko inaba sai asibity.,suna shiga momy
saida ta tsorata da ganin inna amma ta dake
tace inna waye fada miki muna nan?!tace ban
sani ba an bari saita mutu sannan agayamun
ko.tace yi haquri inna walh tin jiya hankalinmu
be natsu bane,. Inna taqarasa gun salma tana
fadin oh
ni zuwaira meya samarmin salma ne!alhj kam
juyawa yayi yanufi gun afnan yana shiga yaga
dakin ba kowa mamaki ya kamashi yawo waje
sai suka hadu da hjy tafito daga toilet tayo
alwala.,yace ina afnan din?!tace ai yana ciki
baka shiga bane yace yanxu nashiga banga
kowaba tace wani irin bakaga kowa ba muje
nabarshifa yana bacci,suka shiga tare hjy taga
wayem tasaka salati tace alhj ina yanufa ne?!
sukayo
waje arude tai hanyan word dinda salma take
yace dawo karkije tare mukaxo da inna yanxu
kinazuwa hankali zai qara tashi murasa yadda
zamuyi da ita,.tace saida nace
ma sadiya tazo tazauna dashi amma ashe bata
xoba,.yace yanxu taho muje inyaso daga baya
saimu kirasu awaya mugaya musu abinda ke
faruwa. Da sauri sukai mota suna tafe suna duba
hanya, nan bangaren salma kuwa motsawa
tafarayi gaba daya sukayo kanta suna
tsatstsaye.Salma kuwa jitake kamar awani
duniyar take jikinta duk inda tai qoqarin juyawa
saitaji wani masifar ciwo kamar anyi mata
shegen duka., momy ta zauna tana fadin salma
salma sannu kinji!"ahankali
abubuwa suka fara dawo mata tafara tuno
abubuwanda suka faru tsakaninta da yaya afnan.
Tuni tafara shure shure da qafa tana fadin yaya
dan Allah kayi haquri bazan sake ba yaya
kataimakeni nace baxan sake ba yaya.,kasakeni
tuni momy ta tallabota ta rufe mata baki tana
mata addu'oi inna tace oh wani yayan take kira
ne momydai batace komai ba saida taga salma
tadaina shure shure sannan tasake mata
baki!"ahankali salma tabude idonta taqara
lumshewa dan tarasa ina tace gashi hankalinta
be gama dawowa jikinta ba., ta sake cewa yaya!
yayana!kazo ka ceceni dan gani take kamar har
yanxu a hannun afnan take.,momy tace salma
bude idonki mana kiganmu ga inna tazo dubaki
ga antynki sadiya ga sisternki husna kubude
idonki kinji ba abinda zai sameki!"jin maganar
su kawai take sama!sama kamar wani almara!.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 13
==>Tasake bude idonta tafara ganinsu dishi
dishi!.ta qara bude idonta sosai tana kalle kalle
dan batasan a ina take bama. Wajen yayi mata
wani kala ta kalli momynta tafara magana da
murya qasa qasa kamar haka"momy nan ina ne?!
momy tace asibity ne bakida lapia shine aka
kawoki,!tai shiru jim kadan tasake cewa momy
ina yaya Afnan!?momy tace yana nan
zuwa..zakici abinci?ta girgiza kai tafara kuka a
a momy dan allah kice masa karyaxo dan allah
momy walh kasheni zeyi.,momy tai saurin cewa
to kwantar da hankalinki zan gaya mishi dena
kuka kinji"inna ta bude baki tare da cewa kaji
wani shirme duk zafin ciwonne haka!inbada
zafin ciwo afnan dinne zai kasheki!ta kalli momy
tace Aisha anya kuwa yarinyar nan tana cikin
hankalinta? kijifa surutanda taketayi tinda ta
farka;momy tace inna zafin ciwo ne kawai zata
warware insha Allahu,.inna sai qara
shashshafata take itako tanata zare ido tana
kalle kalle sai lokacin ta kula da qarin ruwanda
ake mata.,sadiya da husna suka dubeta sukace
sannu ya jikin batace komaiba tafara qoqarin
tashi ta zaina nanfa taji qugunta yariqe gam ga
wani masifaffen ciwon jiki.,anty sqdiya tace ko
adagaki ne ta daga kai alamar eh., sadiyaa tazo
da sauri ta dagota ahankali,.amma Ina jitayi
bazata iya zama ba haka takoma ta kwanta;sai
hawaye suka fara gararowa afuskarta da sauri
anty sadiya tafara lallashinta tana goge mata ita
kuwa husna tsaye tayi tana kallon ikon allah
yadda taga salma lokaci guda ta rame manya
manyan idanunta sun qara bayyana fuskarta
yazama wani siriri lebenta ya bushe aranta tace
lallai wannan ciwo yabama sis dinta
wahala.,.alhaji abubakar kuwa haka suka dinga
Neman afnan ko zasu ganshi akan titi amma
babu shi babu labarinshi haka suka figi mota sai
gida.,suna shiga palo wazasu gani afnan ne
kwance ya daura hannuwansa akan qirjinsa ya
miqe qafa daya ya daga daya fuskarshi na kallon
sama!hawaye nata faman kwarara daga idonshi.,
sunyi tsarko tsarko suna kallonshi cikeda takaici
ta wani bangaren kuma sunyi hamdala da
ganinshi Abba yaqarasa yana fadin afnan
wannan wani irin rashin hankali ne zaka gudo
gida kazauna ciwo na cinka!hjy ta nemi waje
tazauna tare da cewa kaimadai kafada.,yaxo ya
kwanta ne yanata kuka kamar wani qaramin yaro
to dukanka akayi taja tsaki..mtsww tindazu
mukebin kwararo kwararo muna nemanka Ashe
kai gida ka nufo kabar yan iska acen KO., Abba
shikam harya karaya..yace haba kibarshi
hakanan mana bakya ganin halinda yake cikine.!
tace to mu kuma ai soyayi yajefamu atashin
hankalinda yafi haka.yanxu daya fadi ahanya
mota ta takeshi aimu yabari da baqin ciki., Abba
ya dafa kan afnan yace my son me kakema kuka
ko jikinne!?nan yaji jikin Afnan zafi kamar
garwashi. Yace kinji jikinshi kuwa tashi mu
koma asibity,.shigo dake kwance duk maganar
da suke be tankaba saida yaji ance yatashi
akoma asibity.,da Sauri yatashi ya zauna yana
cewa Abba dan allah kabarni walh naji sauqi
baxan koma ba,.Abba da umma sukace atafaf
saiya tashi sun koma bazasu zauna suna kallo
ciwo yakasheshi ba; fashewa yayi da kuka kamar
wani qaramin yaro walh Abba idan kuka mayar
dani mutuwa zanyi ni bazan koma ba,duk sai
sukaji ya kashe musu jiki. Alhaji yace abarshi
tinda bayaso zaije ya karbo masa magungunan
sallama nan hjy ta kira momyn salma take fada
mata afnan ya gudo gida,. Salma kuwa tananan
tana masu kuka ita akira mata yaya Habib da
yaya Ahmad suzo su kaita gida.,bashiri momy
tasa aka kirashi! saigashi yaxo kamar Wanda
yahawo jirgin sama.yana aikinshi a office daman
hanklinshi yana wajenta saikuma yaji kira"momy
dai tarasa yazatayi kar ahaifa danda ba ido!yaxo
dasauri ya dagota murya a shagwabe tace wash
yaya bayana ciwo da cikina yaya harda kaina
ciwo yake'.saiga hawaye sun sake kwararowa:
hankalinshi yatashi yace sorry sisterna waye
yatabamin kene!;pls zaki iya gane fuskarsa dia
kidaina kuka saina daukar miki fansa!;gayamin
kinji zaki iya ganeshi?,!kuka ta sakar masa tare
da cewa ba yaya bane.....
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 14
==>momy tai saurin cewa aina gayama yayan
naki karyaxo ba shikenan ba/Habib yai shiru
daga bisani yace momy wani yayan take
magana?tace uhm walh tinda tatashi taketa
shirme nima narasa mezan mata ma;salma kuwa
kallon maman nata kawai takeyi wai itace za ace
tana shirme/kodai basu San abinda yaya afnan
yai mata bane!;to amma idan basu saniba
meyasa tagansu a asibity?kodai daman sun tafi
sun barta ne dan yazo yai mata wannan Abu?!
duk acikin zuciyarta take wannan tunanin"ya
Habib ne ya katseta da cewa..qanwata kin
ganeni kuwa?ta daga mishi kai alamar eh"ya na
shirin jefo mata wata tambayar nan yakula
Ashefa inna tana dakin kuma ya tabbata batasan
halinda ake cikiba dan yasan baza a gaya mata
wannan mummunan labarin ba!shiru kawai yayi
ya dubi inna yace ke tsohuwa meran qarfe meya
kawoki nan?'ta turo baki tace abinda ya kawoka/
ai natsayane naga iyakar gudun
ruwanka tinda kashigo ko kallona bakayiba
balantana ka gaisheni kana nan gurin qanwarka
kaime qanwa ko"gaba daya sukasa dariya momy
kuwa taji dadi da aka cenja fira dan duk
hankalinta yatashi da irin tambayoyinda Habib
kema salma!hararanda
Habib yajefoma sadiya ne bashiri ta shanye
dariyarta sanadiyyar faduwar da gabanta yayi.
Tuni ta miqe tsaye takama hanya sumi sumi tai
waje momy tace ina zakije?tace
momy..zan.danje waje ne zafi ke damuna, momy
tace zafi kuma AC akunne yake fa. Qara
daburcewa tayi tace oh sanyi nakeso nace,momy
tace eyya to dawo abinki bari akashe nima
sanyin ya dameni.haka tadawo
tazauna jiki ba qwari/tana daga kai suka qara
hada ido da ya Habib yasake balla mata harara
bashiri ta miqe zumbur harsaida momy ta kalleta
sai cewa tayi momy zanje bayi ne yanxu zan
dawo'/inna tai karab tace kinsan bayin zakije
shine kikasa aka kashe mana AC dan gulma ko/
uhm kawai tace tafice abinda.momy tace inna
kenan sarkin son AC,.sadiya kam zuwa tayi ta
nemi guri tazauna akan wata farar kujera da aka
tanadesu dan masu zuwa ganin Dr! Ta jingina
kanta da bango hawaye suka ciko idanunta
aranta tace meyasa yaya
Habib yatsane ni?!wai yayshe ne zanyi abinda ze
burge ya Habib"itadai tanason yaya Habib amma
batasan laifinda tai mishi ba bayason
ganinta;tabbas tana matuqar qaunarshi amma
gashi tarasashi amatsayin mijin aurenta;hawaye
zafafa suka dinga bin kumatunta wai yaushene
zataga dariyar ya Habib?! Salma kuwa zamewa
tayi daga jikin yayan nata ta hade rai
===>BUTULCI KO SOSO!!!,? Part 15
==>yayi yayi inna kam tace ai dole saiya kaisu
gida itada jikar tata husna'momy ma tace yayi
haquri ya kqita sannan yawuce duk inda
zashi"hakanan ya haqura suna shirin fita saiga
Ahmad tare da sumayya sunxo aiko Habib yace
shikenan maza kazo kakai inna gida allah ya
ceceni. Yanxu office zan koma ana jirana kuma
tace saina kaita gida.maza kakaita saika
dawo.ko shiga beyiba yasashi yajuya sumayya
kam shigewa ciki tayi abinta., inna dai tace oho
dai koma menene.nidai akaini gida.,sadiya kam
tagama cin kukanta taje toilet ta wanke fuskarta
tace bari tadan leqa taga mamanta !tana bude
daki taga wayam tace umma kuma tafiya sukayi
an sallamesu ne amma bako sallama.ta juyo
dukda tanajin tsoro taje taga ya Habib amma
hakanan tadaure tace bari tashiga tagayama
momy.
Topa ana wata ga wata
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 16
==>Salma tsce yaya kayima Dr mgana mutafi
gida gobe yace to iyarigima zangaya masa!
ammafa sai in kinacin Abinci sosai;ta tabe tabi
tace yaya bakaga abincin danaci ba"yace nagani
amma ki qara"mudai zamu wuce saida sfe!
Momy tace Ku gaida gida suka fice abinsu, Abba
yace salma anji sauqi sosai momy tace aikuwa
alhmdlh!/yace to Allah ya kiyaye gaba kuma
allah ya tona asirin duk Wanda yai mata wannan
cutar ita kuma allah yasaka mata/momy da ya
Ahmad sukace Ameen summa Ameen! Yace toni
zanje nasami Dr arubutama afnan magungunan
daya dace tinda yaqi zaman asibityn kuma ga
ciwo nacinsa/
Momy tace oh haryanxu jikin ko",yace eh walh
yanacen zazzabi yaqi sauka saidai yaita
hawaye_momy tace to Allah yabashi lapia,
Ameen Abba yace yafice abinsa.Salma tanata
nazari cikin zuciyarta kome Abba yake nufi oho.,
to mema yasamu afnan din?! tambayar data kasa
bama kanta amsa kenan.wato bayan yakusa
kasheta shima ciwon yakamayi kenan! Wata qila
ma da hadin bakin su momy. To amma yaza ai
su momy suyi mata haka?!kuma meyasa idan
tanaso tayi maganarshi momy ke tattarewa!
gaskia akwai wani abu a qasa Ahmad ma yace
momy zantafi sister allah yabaki lapia sai yaga
ta fashe da kuka. Hankalinsu yatashi Ahmad
yace sister lapia yaqarasa yace wani abunne ke
miki ciwo?! cikin shagwaba da shashshekar kuka
tace yaya daman da gangan su momy suka gudu
suka barni yaya afnan yaxo yakusa
kasheni..taqara fashewa da kuka
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 17
==>Asuba nayi momy tatashi tai sallah nima
tatasheni nayi sallah ta hadamin tie me kauri
tabani nasha na qoshi 6 0 daidai Dr yashigo
dubani ya cimmani inashan tie yanataimin dariya
wai na warware haka yace to ya nakejin jikina
nace mishi komai normal babu sauran wani ciwo
nace mishi saidai banajin qarfi ajikina yace ba
damuwa ahankali zanji daidai. Dr yace anjima da
yamma zai sallamemu nan nafara murna nace
mezai hana a sallameni yanxu yace sbd
inada sauran allura yanxu zeyimin anjima zaimin
sai a sallamemu momy ma tanata murna yaimin
allura yafice abinsa. nan wani baccin yasake
kwasheni.
Wajen qarfe 8 0 saiga yaya Habib yaxo
muryanshi ne ma yatasheni daga baccin
danaketayi.sunata hira da momy ta fadamishi
cewa anjima za a sallamemu.
Ina tashi yaya Habib ya kalleni yace sister yau
sai gida ko. Nadanyi murmushi na CE yaya
yaushe kaxo? Yace tin daxu mana ke kinata
bacci gashi mun tasheki ko. Na girgiza kai nace
daman ngaji da baccin! Yace to nima yanxu zan
wuce office anjima sai Ahmad yaxo yamaidaku
gida idan nadawo daga office zanxo muyi
magana kinji!.nace to yaya saikaxo.
Yatashi yai sallama ya wuce abinsa. Momy
taqara hadamin tie me kauri nasha nasha magani
taje toilet tahadamin ruwan wanka tace nazo
taimin Niko nace ban yarda ba saidai inyi dakai
na. Tayi tayi haka ta haqura ta qyaleni. Naje nai
wanka na yadda takemin gashin haka nima na
daddage. Nayi inayi ina kuka idan natina yadda
yaya afnan yaimin abin yanamin ciwo arai.
Ina fitowa daga toilet momy ta gyara ko
ina.nazauna bakin gado nafara shafa mai saiga
aunty sadiya ta shigo tanata yimin dariya nima
inayi mata tace rigimammiya harkin warke ko
murmushi kawai nayi. suka gaisa da momy saika
yaya Ahmad shima ya shigo ashe tare suke. Aka
gaisa Momy nata tambayan dan autan NATA dan
tayi missing dinshi gashi asibityn basa bari ana
zuwa da yara da anxo mata da Khalid ta ganshi.
Sadiya taxomin da wata doguwar rigana tace na
cenja kaya daman wancen ta isheni momy tace
Aida tabarshi ma dan yau za a sallamemu sunyi
murna dajin hakan.momy tafadama yaya Ahmad
yadawo anjima yadaukemu .wayar momy tai qara
ta dauka tareda sallama Abba ne yakirata suka
gaisa ya tambayi jikina mum tace ta sauqi
anjima ma za'a sallamemu yace to alhmdllh
daman innace tace dole saina kirawo mata salma
taji muryarta yanxudai gata..yamiqama inna
waya suka gaisa tace abani.
Na karba nace hello inna tace me sunan mamana
yajikin naki?nace naji sauqi Inna Dr ma yace
anjima zai sallamemu inna yanxu aina fiki
qarfima
Tace rufaman baki kawai saiki kama ciwo yanxu
dakin tafi kinbarfa.
To zanxo gidan naku anjiman saikin fadamun
dalili.
Nai dariya nace shikenan inna saikinxo.namiqa
ma momy wayarta suka qarashe firansu sukai
sallama .
Ahmad yai murmushi yace inna iyayen rigima.
Yace amma momy yau dai kinsan dole yaya
Habib zaixo yatambayi salma yadda abinnan ya
kasance ko?! Tace tabbas kuwa nima tunaninda
naketayi kenan.amma
aiba wata matsala bane kawai cemishi zatayi ita
batasan fuskar wanda ya aikata mata
hakanba.yaya Ahmad furka a yamutse yace
momy wai meyasa kikeson a boye maganar nan
ne bayan abune me girma kuma kinsandai halin
Abba ada ma baibari afnan ya auri salma ba
bare yanxun dayake ganin an riga an dauke
mutuncinta kuma baisan cewa afnan din bane
toya abin zai kasance.
Momy tai wani taqaitaccen murmushi tace
Ahmad kenan kana manta wanene Habib ko to
duk wani tashin hankali zaixo da sauqi akan yaji
cewa afnan ne yataba mishi salma.dan haka
dolefa sai anyi haquri amma idan mun koma
gida akwai shawarar dana yanke insha allahu
komai zaidaidaita.
Ya Ahmed yace shikenan momy.
Nida aunty sadiya kuwa bamuce affan ba illa
dana sanya rigata na kishingida akan gado
inajinsu harsuka gama.Ahmad yace Toni
zanwuce sai anjiman zandawo nadaukeku.yafece
abinsa
Cen wajen yaya afnan kuwa daqyar umma
tamatsa mishi ya karya yasha magani sannan
yace zaixo yadubani umma tace ba inda zashi ai
yanxu nafishi lapia shida aka kusa kasheshi sbd
ni to ba inda zaije idanma zaixo din toyabari
yaqarajin sauqi.
Haka nan dai afnan ya haqura dukda ma dai
yana tunanin da wuya zai iya tunkarata da nufin
gaisuwan.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 18
==>Qarfe 6 0pm likita yaxo yaimin allura dan
harna fidda rai da sallama.
Saida naganshi sannan naji sanyi amma
saiyacemin wai yanxu yamma tayi sosai saidai
gobe aiko nafara shirin kuka shine yace ai wasa
yakemin ya bamu takardar sallama yanataimin
dariya wai baby salm akwai rigima.
Tsalle ne kawai banyi ba don murna dandai
bazan iya tsllen bane amma da sainayi dan
naqosa naganni a gida.aunty sadiya kam tin
wajen qarfe 4 tawuce gida yaya Ahmad ma yaxo
yaga ba a sallamemuba yawuce abinsa.
Dan haka nace momy kawo wayarki nakira yaya
yaxo ya daukemu tamiqomin na lalabo
number dinsa nakira yana dauka nace yaya kaxo
an sallamemu yadda nai maganar harsaida
yabashi dariya yace to ganinan zuwa Ku kimtsa
kafin na qaraso,
Momy tafara shirya duk wani Abu damukaxo
dashi.
Jim kadan saiga ya Ahmad na miqe da izzana da
danufin in ruga da gudu in riga momy shiga
motar amma sai akasin hakan dan jinayi baxan
iyaba tafiyarma da yaya aka qare dan banajin
wani qarfi ajikina.dan haka nabi ahankali.nace
momy nidai Ku sameni a mota ya Ahmad yace
meyasa kika fasa gudun nace sbd kar mutane
suyita kallona ne, yace kokuma bazaki iyaba ba
kedin kinajin kunyan gudu ne.
Nai murmushi na fice abuna.
Ahmad yataimaka ma momy suka kwaso komai
suka saka a both. Suka shigo mota muka kamo
hanyan gida. nikam gani nayi ko ina
yacenjamun.
Muna isa gida su rufy da sumeey sai murna suka
rugo da gudu suna oyoyo aunty tadawo. Khalid
ya rugo ya rungumemun qafafu saida mukai
kamar zamu fadi nidashi momy ta riqeshi tace
gafara cen zaka kayarmin da yarinya wato ni
inacen ina tunaninka amma kai ba tani kakeba
ko.ta auntynka kake.
Duk mukasa dariya gaba daya muka dunguma
sai Palo tindaga qofa nakejin gabana yana
faduwa muna shiga Palo qirjina
yai wani mugun bugawa take zufa ya ketomin
naji jikina yasaki idan ban nemi guri na zaunaba
zan iya faduwa sbd ina ganin wajenda afnan ya
danneni sai nakejin kamar yanxu abinke faruwa
sai kallon wajen nake zuciyata fal da baqin ciki
da qyar naja jiki dayan kujeran 3 setter na zauna
momy ta kalleni tace lapia naga kinyi wani iri!
Nace momy walh nagaji ne duk naji
banajin dadi kuma kamarma bacci nakeji kinsan
alluran nan tanasa bacci.tace eh gaskiya ne
yanxu kiyi sallama tukuna saikici Abinci kisha
magani saiki kwanta ko.
To kawai nace su rufy duksun kewayeni wannan
yace kaza wancen yace kaza. Aunty
sadiya ta hada mana komai na Abinci mukai
sallah mukaci Abinci nasha magani natashi nace
ni yanxu zanyi sllahn isha'i. Dan bacci nakeji
momy tce to Anty sadiya tatayani kwana inyaso
gobe saita wuce gida.daman mamanta nata kira
wai taqi dawowa kuma tasan afnan baida lapia
kotaxo ta gaisheshi.
Nidai ina sallah na sanya kayan baccina na
kwanta.inna taso taxo a Daren saidai babu me
kawota dan dole ta haqura.
Ya Habib koda yaxo ina bacci dan haka ya
bayyana momy buqatarsa nason in koma
wajenshi.
Momy kam tace batasan da wannan maganar ba
babu inda zani.yayi yayi momy takafe akan babu
inda zanje dan haka yace to shikenan amma
gaskiya zaisa mana bodyguard dan bazai yiwu
adinga abinmu agida ana zuwa ana lalata
rayuwarmu ba.
Shima dai daqyar momy tayarda dan saida
Ahmad yasa baki a maganar. Haka yatashi
yawuce jiki ba qwari domin kuwa shi yafison ya
tafi dani wajenshi. Gari na wayewa saiga inna
tareda husna tin duku duku dan mu bamu tashi
bacci bama su suka tashemu.
Muryar momy najiyo tana cewa inna kece da
sassafen nan sannu da zuwa. Ina tashi toilet
nashige nai wanka inna ta shigo dakin tana cewa
ina me sunan mama saigani nafito ina dariya
nace inna gani tace ah lllai sauqi yasamu nace
ai daman na gaya miki yanxu zan iya karawa
dake.
Tazauna bakin gado nida nazauna surutunmu
yatashi Anty sadiya tana tashi kuwa suka gaisa
Kicin tanufa tafara shirya mana kayan breakfast.
Inna tace ahada damu bamu karya ba idan mun
karya zamu wuce gidan bukar dan Jiya yake
gayamun Ashe afnan ma beji dadi ba zanje na
dubashi.saida qirjina yabuga data ambaceshi
nikam yanxu ina matuqar jin tsoron ya afnan.
Sadiya ta kammala komai muna cikin break
saiga ya Habib nan yasamu inna tanatamai
surutun bashida kirki baya xuwa ya gaisheta
nandai sukaita yan wasannin da suka saba. Suka
gaisa da momy bai samu damar magana dani ba
dai sbd ganin inna hakanan yawuce yace zai
dawo da yamma.muna gama break inna tace
husna taxo su wuce dan harmun shige daki nida
ita munata hira dan haka inna tace to idan an
gama meeting din afito mu wuce, momy tace
inna kujira Anty sadiya mana Ku wuce tare. Inna
tace bayan ko wanka batayi ba nibazan jirataba
Aunty sadiya kuwa daman bason tafiya yanxu
take ba.anma momy saida ta lallabi inna TAce
anty sadiya tai maza ta shirya. Dan haka
adaddafe tasamu ta shirya suka wuce
Suna isaa....
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 19
==>Suna isa suka cimma su abba da umma a
palo suna breakfast hjy ta miqe taqaraso da
Sauri tana inna sannu da zuwa kune da safe
haka Ku zauna.
Suka zauna kan kujera inna Abba da umma
sunata kwasan gaisuwa aunty sadiya tagaisheda
momynta da abbanta. Husna ma cikin kunya ta
dubi su umma da Abba tace ina
kwana.sukadanyi murmushi tareda cewa lapia
lau. Ya Maman naki?tace lapia lau. Inna tace ni
banga afnan dinba ina yashige ne. Hjy tai dariya
tace ai yana dakinshi nyi nayi ma yafito yaci
Abinci amma yaqi sai abbanshi yaje tukun danni
an rainani.inna tace toni barinje na ganshi
daganan inyi lallashi. Sukai dariya inna ta miqe
tace taso husna muje kinsan niba gane dakin
nashi nake ba sosai.
Akunyace husna ta miqe dukda dai itama
tanason ganinshi amma tanajin kunyan su Abba.
Haka suka kama hanya inatada inna sadiya kam
tashi tayi tashige dakinta. Sun shiga dakin
amma basuga kowa ba ga dakin duk ahargitse
alamun andan jima ba a gyarashi ba.
saidai sunji alamun watsa ruwa a toilet dan haka
husna tace inna inaga yashiga wanka Ne ki
zauna kan wancen kujeran mirror din nikuma
indan gyara mishi dakin kafin yafito.yanadaga
toilet yajiyo murya Amman yarasa gane ko
waye.dan haka yaketa sauri yagama wankan.
husna kam tanata faman gyara ko ina saidata ta
kimtsa mishi tana cikin linke bargo sai gashi
yafito dagashi sai dan gajeran wando da farar
singlet gashi kwance a jikinshi kota ina.
Tsayawa yayi bakin koqar yana kallonta kamar
me shirin dukanta wani irin haushi yacikashi
aranshi yace kya gama haukanki danni walh ko
za'a kasheni ne bazan aureki ba saidai duk
abinda zai faru ya faru tinda ga inna ma yanxu
za'ayita ta qare. Yaqaraso bakin gadon ya
zauna.ya kalleta ido cikin ido ta Sauri tai qasa
da kanta batasan sanda ta saki bargon ba sbd
tsabar kunyan dataji. Tsigar cikinta duk suka
tashi. hannunta har karkarwa yake. Inna ta kalli
afnan tace wannan wanka naka kamar ana cenja
fata tin daxufa muke nan azaune.yai wani dan
malalacin murmushi yace to Inna wama yabaku
izinin shigomin daki duk kun hargiysamin daki.
Husna tai dukta tsargu dan tasan da ita yake
daqyar ta jawo jiki tadawo kusada inna
Inna tace oh abinda zakace kenan dan an gyara
maka dakin.to ai gobe ma rana ne. Husna tace
yaya ina kwana?ko kallonta beyi ba saida inna
tace bakajiba qanwarka tana gaisheka yace oh
lfy.tace ya jikin?ya harareta yace wai cemiki
akai banda lapia ne!?
Inna tace oh
Ashema lapia kake kasa muka taso tindaga gida
mukazo gaisheka to aiko kaizaka maidamu
gida.afnan yace inna ni daman inason ganinki
dan akwai magananda zamuyi
Tace to ina jinka.afnan ya kalli husna yace pls
abamu waje ko. Sumui sumui tafice tai palo su
momy sukace lfy harzaku wuce ne? husna tce a
a inna suna magana da yaya ne. Afnan ya dubi
inna yace inna dan allah ki taimakeni kisa Abba
ya auramin Salma. Walh ni salma nakeso ba
husna ba kuma salma tana sona kitaimaka kisa
baki Abba yabarni na aura salma walh inna
salma itace rayuwata yaqarasa maganar hawaye
kamar zasu zubo a idanunsa. Inna tai ajiyar
zuciya tace to afnan kasandai halin mahaifinka
ba'a iya kaudashi akan abinda yai niyya indai ba
wani ikon allah ba.
Amma zanyi maka qoqari afnan nima nafisonka
da Maman kasha kuruminka zanyima Baban
naka magana kaji ko
Afnan ya sauke numfashi ya dafa qafar inna
yace kai inna dakin gamamin komai walh.
Dan allah ki qoqarta dan walh idan ba'a
auramun salma ba akwai matsala inna.,
Tace to kaita addu'a idan Allah yasa matarka ne
saikaga anyi.
Yanxu bari naje nasamu Baban naku muyi
magana..
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 20
==>Afnan yai saurin cewa a a Inna ba yanxu ba
kobari saikin tafi gida saikisa akira miki shi
yazo kuyi maganan.tace to shikenan zan
kirashi.yanxu ya jikin naka?yace alhmdllh.
Inna tace to ai saikaxo kamaidamu gida ko tinda
kawarware. Yce to inna daman walh inaso nafita
su Abba sun boyeni agida sun hanani fita. Yanzu
bari nashirya na kaiki ammapa wancen qazamar
bazata shigarmin mota ba.inna tace wacece
qazamar afnan yace yar rakonki mana. Inna tace
lallaima yaron nan husna dince qazama to aiko
baka isaba saita shiga. Yai murmushi yanata
shirinshi.inna tamiqe tace ina jiranka a palo tayo
waje.shiko yahau shirye shirye yana gamawa
yayo palo duk suna zaune hardasu aunty sadiya
anata fira da Inna. Yana shigowa palon umma ta
dubeshi tace maza kaje dining ga abincinka cen
kuma kasha magani.
Inna tace kaisauri kagama kakaimu gida inaso
inyi bacci.,qarasawa yayi dining din yazauna
Abba ko yace haba inna ai bashida lapia kibari
idan zan wuce office saina saukeku.inna tace
shikenan ma kaizakafi lallabani dan wancen be
iya tuqi ba.yace to aini daman yanxu zan wuce
kutashi kawai muwuce.,
Suka tashi itada husna suka bishi abaya
Afnan kam jiyayi kamar ya hadiye ransa don
bacin rai da takaicin rashin fitanda beyi
ba.amma aranshi yace yau donene yafita kota
halin qaqa saiyaje yaga salmanshi.
Sadiya ta miqe zata wuce daki momy ta kirawo
sunanta tsayawa tayi ba tareda ta waigo
ba.momyn nata tace kinyima afnan din ya jiki
kuwa?!juyowa tayi tace oh sry fa ya jiki afnan?
Ji yayi wani dum kamar ta buga mishi dutsi
akai.yace da sauqi aunty amma be iya hada ido
da ita ba.ta juya abinta ta wuce dakinta.
Kadan ya iyacin abincin yasha magani sannan
unmansu tace nizan shiga inyi wanka kaima
yakamata kakoma daki ka kwanta. Dasauri yace
to umma.daman so yake tabar palon dan
yasamu ya fice.tawuce abinta
Shima yatashi yafice da saurinsa bema tsaya
daukar mota ba yanufi get dasauri me gadi
yataso yana gaisheshi tare da tambayanshi ya
jiki..dan ko ba a gaya maka ba dazarar ka kalli
afnan zaka tabbatarda yaji jiki dan yayi rama
sosai.afnan yana fita ya samu me adaidaita sahu
be sauka a ko inaba sai qofar gidansu
salma.uhm afnan kenan baya ko tunanin me
zaije ya tarar.
Said a ya isa ne yasauka ya biya me adaidaita
sahun sannan wani irin fargaba da tsoro ya fado
masa yarasa ma yazaiyi ya shiga gidan kuma
idan yashiga da wani ido zai kalli momy da
salma. Shin meye mafita juyawa zaiyi ko kuwa
dai Shiga zaiyi?!
Su momy kuwa tinda gari yawaye gidansu cikin
baqi yake yan uwa da abokan arxiki masu zuwa
gaisheda salma., suna zaune a palo momy da
salma sai Khalid sai hjy safiyya Maman husna
sai qawarta sameera sunata fira salma tadan
kashin gida akan kujera 2 setter Wanda yake
person din qofar palon. su rufy da sumayyakuwa
duk sun tafi school.
Salma ta dube baki zatayi magana muryar data
jiyo ana sallama ne ya datseta daga maganar da
take shirin yi.tareda tsantsar fargaban muryar
data ji.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 21
==>Momy ne ta amsa sallamar tare da cewa
wanene shigo mana.,afnan kam tsoro yahanashi
shigowa sai wani dan maqe maqe
yaketayi kamar mara gaskiya.koda yake daman
Mara gaskiyar
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 22
==>Momy ta juya da Sauri tafara buga qofar tana
fadin salma lapia.!ki bude qofar mana! Qara
lafewa tayi akan gadon momyn nata tana wani
irin kuka me tsuma zuciya.! Suna jiyo sautin
kukanta har palo. Momy ta juyo jiki a sanyaye ta
kalli afnan tace masa afnan kayi haquri tinda tai
ciwon nan abu kadan yake sata firgici nikaina
narasa gane kanta kwata kwata. Yanxu katashi
kaje gida kahuta dan kaima nasan bakajin dadin
jikinka kawai qoqari kayi kaxo gashi kuma
ansamu akasi yar uwantaka afirgice tace.
Katashi ka lallaba kaje gida kaji! Hannu yasa
a aljuhu ya ciro handkerchiefs ya goge
hawayenda ke fuskarshi sannan ya miqi yace to
momy barin koma Allah yabata lapia jiyawanda
yayi ne ya kula Ashe ma basu kadaine a palon
ba hjy safiyya da sameera sunyi jigum jigum sai
kallon ikon Allah suke. Afnan ya sauri yakoma
ya zauna sai yanxu yatuna Ashe be gaisheda
kowa ba! Sannan ya sanda kanshi qasa yace
momy na manta bamu gaisaba ina yini. Tace
lapia qalau yajinka ya sadiya da gajiya. Yace
lapia lau sannan ya juya yagaisheda hjy safiyya
suka gaisa da sameera yai musu sallama ya
tashi yafice cikeda jimamin abinda ya faru! ,
yana fita momy ta juyo ta cigabada kiran salma
dan ta bude qofa amma shiru taqi budewa. Da
Sauri momy ta nufi dakin salma ta dakko spare
key din yakaye wajen salman taxo ta bude qofar
tashiga. Su hjy da sameera duk suka biyo
bayanta., salma na qwance ta kifa kanta a pillow
momy ta zauna kusa da ita ta janyota jikinta taji
jikin tana yadau zafi sosai tace subhanAllah
salma zazzabin kuma dawowa yayi itakam ta
runtse idonta kamar wata me barci.hjy safiyya ne
tace nifa wannan Abu ya dauremin kai.ana cikin
firq lapia kawai yarinya daga ganin mutum saita
firgice kamar taga mutuwa?!momy tace kedai
ganemin hanyan nima narasa gane kanta amma
inaga kawai zafin tsiwonnan ne har yanxu be
saketa ba. Momy ta dubi sameera tace dan Allah
sameera taimaka ki miqomin place dincen da
Kofi na hada mata tie,.sameera tace to momy
bari zan hada mata dandanan aka hada mata tie
daqyar momy tasamu ta bata sannan tabata
magani bacci ya kwaaheta. Nan su hjy sukaima
momy sallama kowa ya watse ,zuwa cen saiga
su rufy driver ya dakkosu daga school! Suna
zuwa sukai dakin salma momy ta dakatar dasu
da cewa kar Wanda yasake yashiga batajin dadi
tasamu bacci kuma zakuje kutasheta. Haka suka
tsaya duk basuji dadi ba sudai kwanan nan duk
gidan be musu dadi abokiyar firansu ba
lapia..suka nufi dakinsu suka cire uniform dinsu
sumayya tashiga kitchen ta debo musu
Abinci suka baje suka kama ci.,
Afnan kam daqyar ya iya kaiwa gida yashiga
palonsu yana dangadi kamar Wanda
yasha ya bugu.yana buga qofar palo yai sa'a
kuwa aunty sadiya tana zaune tana kallo tataso
tabude batace mishi qala ba ya wuce sashensa
yana zuwa yafada kan gado kamar Wanda
akaiwa duka! Umma tafito daga daki tace ma
aunty sadiyA wai har yanxu yaronnan bedawo ba
kuma anata kiranshi yaqi dagawa. Anty sadiya
tace umma yanxu yashigo daman yanzu zanza
nafada miki yadawo.
Umma batace komaiba tanufi sashensa ranta a
bace.
Tana zuwa ta fada dakinshi yai saurin juyowa
danganin Wanda yashigo tazaun ta dubeshi rai
ahade tace ina kaje baka iya gayamun zaka FIta
ba?inace ma wai ba abbanku yace karkaje ko
inaba!?
Afnan yace to umma yanxu shikenan ni bazan
fitaba saidai naita zama agida kamar mace
yaqarasa maganarashi ashagwabe.harsaida
yabama Umma tausayi tace to ai kozaka fitan
saika bari kaqara samun sauqi ko!yanxu dai bari
akawo maka
abinci kaci kasha magani.
Tamiqe tai kicking ta kamo masa abinci daqyar
tasamu yaci haka taita lallashisa kamar qaramin
yaro. Ranar dai haka ya yini daga tunani sai
kuka rayuwa ta juya masa baya.
Misalin qarfe 6:30mp saiga yaya Habib yaxo
yasamu salma tanata bacci nan yai sallah
sukaita fira da momy rufy da Khalid duk sun
baibayeshi sunatamai surutu. Sumayya kuwa
tana gefen momy. Sai ganin salma sukai ta
shigo dakin sumui sumui ta nemi waje ta zauna
akan kafet dinda Habib ke zaune ta lafe jikin
kafadarshi kamar me shirin yin kuka. Ya kalleta
cikeda kulawa yace sister lapia kuwa waya
tabamin ke duk naganki wani iri ne!? Tai wani
irin gajeran murmushi Wanda zamu iya kiranshi
da yaqe tace yaya ba komai.
Yace haba sister kifadamun gaskia mana! kinsan
banason naga kina damuwa naso na daukeki ki
koma gurina momy ta hana amma ba komai
yanxu haka nasamar muku bodyguard gobe insha
allahu zai fara zuwa dan haka ki kwantar da
hankalinki insha allahu babu abinda zaisake
zuwa ya cutarda rayuwarki ki natsu ki manta da
komai kinji my dia sister kinga kunkusa fara
exams dan haka ki maida hankali akan karatunki
Allah shizai saka miki kuma shizai tona asirin
duk wani me nufin cutar mana dake kinji KO!,
Runtse idonta kawai tayi sbd hawayenda ke
qoqarin gangaro mata bata iya cedashi qala ba.
Momy tai ajiyar zuciya tace ai inaga exam
dinnan ma da wuya idan zata iya har yanxu
jikinta be wani qwari ba gashi kuma batason cin
abinci.
Ya Habib yace to kingani ko sister keda kiketa
murna zaki shiga ss3 amma bazaki dage kidinga
cin Abinci kisamu lapia ba. Yanxu yaushe ne
exam din naku?! Sai lokacin ne ta iya bude baki
tai magana tace ranar Monday ne"yace to kinga
ashema jibi ne lallai kuwa idan kika tsaya sanya
za a tafi abarki idan kuwa kin dage dakun gama
exam zan cenja miki makaranta zan maidaki
Turkish kuma zan samar miki driver dazai dinga
kaiki yana dawo dake. Da sauri tamiqe daga
jikinsa tana murmushi harta manta da
damuwarda take ciki tace momy ina abinci
nah!?.kafin momy tace wani abu Sumy tai tsalam
tace to yaya ni kuma pa?"tareda turo baki kamar
alade ya hangi kashi....! x
===>BUTULCI KO SO!!!? Part 23
==>Gaba dayansu suka kwashe da dariya salma
ta dubeta tace kedai kishi kike to saidai ki mutu
dan yarinya bazanyi makaranta daya dake ba.
Yaya Habib yace to duk ya isa haka kema idan
har kika dage sosai zan kaiki duk mkarantar da
kikeso kinji yar autan mama! Ta tabe baki cikin
shagwaba tace yaya nima Turkish din nakeso
asani"kafin tagama rufe baki salma tace aiko
baki isaba walh yaya saidai asamar mata
wani".ya dubesu yace to duk Ku kwantar da
hankalinku kowa za'a sashi a inda yadace
banason rikici kunji"rufy
tace Dady muma axenja mana! Murmushi yayi
yace wato abin naku yazama qasa kenan ko;to
duk an fasa tinda abin hakane kowa ya zauna a
inda yake!.ya dubi salma ya daga maya gira
alamun karta damu sannan yace kije kici abinci
kisha magani kinji ko.ni yanxu zan wuce
gida"yasa hannu a aljuhu ya ciro kudi ya
miqama kowa nashi sannan yaba momy nata
Wanda itama batasan ko nawa bane sannan
yatashi yai musu sallama ya wuce.
Salma tatashi tai dakinta taje tai sallah sannan
ta tashi tawuce dining taga an shirya komai
kowa yaci iya cinsa.!aranta tace lallaima anraina
komai saida akaci aka rage me makon atasheni
duk an barmin kwantai"
Haka nan dai ta tuttura tinda tanajin yunwa
kuma ga abinda yayanta yace mata. Tana
gamawa momy tazo tabata magani tasha sannan
tace bari taje tai wanka ta kwanta.
Tashiga toilet ta watso ruwa sanna ta nemi wani
riga da wandonta na bacci tasa ta haye gado.
Sai lokacin tunanin wayarta ta fado mata. To
inama ta jefa wayar?! Saita tuna Ashe fa
lokacinda tatashi daga bacci taga bataga su
sumayyaba wayarta ta janyo ta kunna data ta
hau WhatsApp tana cikin chatin taji jikinta duk
babu dadi sbd tagama period kuma batai wanka
ba dan haka tace bari taje tai wanka Wanda
shine sanadin fadawanta hannun afnan. Kuma
tindaga nan batasake ganin wayar nata ba.itadai
tasan akan gado ta ajiye to kowaye yadaukar
mata waya oho!? Tambayar da takasa samun
amsarta kenan. Dan haka ta diro daga kan gadon
ta nufi dakin momy tana zuwa kafin tace wani
abu sumayya tace dama kin koma dan yau bazan
kwana a dakinki ba"tsaki kawai salma tayi tace
angaya miki ke nazo kira to dakixo da karkixo
duk daya yarinya! Sannan ta kalli momy tace
momy wayanafa waya daukarmin.? Tai murmushi
tace sai yanxu aka tuna da wayar kenan"to aiko
nima bansan inda take ba.
Ta marairaice tace haba momy pls ina aka
kaimin walh nayi missing frnd dina kuma data
na a kunne yake za aitamin magana pls momy
kibani.
Momy tace to aini ban dauka wayarki ba. Amma
ki tambayi auntynki sadiya dan naji tace tagani
kuma ta adana miki.amma bansan yadda ta
ajeba saidai kibari saitaxo.,
Tab!tai shiru tana yan waige waige saita hango
wayar momynta akan wardrobe da Sauri ta
dauka tahau lalubo numbern Anty sadiya"
Momy tace mezakiyi.?
Tace zan kiratne mana inji yadda ta ajemin.,
Momy tace ohh lallai kura tayi lapia.
Tana kira kuwa taci sa'a tana kusa. Tce hello
aunty ina yini' Lapia tafadi tana dariya tare
dacewa lallai qanwata lapia yasamu"salma
tadanyi dariya tare da cewa Anty daman zan
tambayeki ne ko kinga wayana! Tace aiko
lokacinda na kwana dakinki na ganta kasan
pillow kuma na dauka nasa cikin handbag dina
da safe na manta ban baki ba sbd tafiyar danayi
ba shiri su inna na jirana shiyasa na manta ban
baki ba kuma na taho dashi gida. Amma daman
ina shirin gobe zanxo naqara dubaki saina taho
miki dashi.,
Salma bataji dadi ba Amma saitace shikenan
Anty saikinxo din"sukai sallama ta kashe ta dubi
momy tace toni zanje na kwanta.,momy tace
sumayya maza kitashi kibita kuje Ku kwanta
sumayya ta turo baki zatai magana momy tace
ba magana nake miki ba'haka nan tatashi badan
taso ba salma kam hartayi gaba tare da cewa
dolenki dakixo
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 24
==>Asuba nayi hjy taxo ta bugama Abba qofa ya
bude tace alhj kayi sallah kuwa. Yace eh nayi
shigo daman inason magana dake. Taqaraso
suka zauna bakin gado,
Sannan ta gaisheshi.
Abba ya dubeta yace hjy jiya kinsan Inna takirani
tace eh.
Yace to bayan naje shine inna take gayamun wai
lokaci yayi dazan hada yaran nan Afnan da
salma aure.
Bayn na nuna mata qin amincewan hakan inna
tasa kuka da sauran maganganu wanda
bakai ba tushe tatayarmin da hankali intaqaice
miki zance bandawo gida ba harsaida nai mata
alqawarin hadasu aure.
Yaci gaba da cewa
To kuma kinsan wannan lamari bamai yiwuwa
bane shiyasa tindaga jiya hankalina atashe yake
narasa mafita.
Da nayanke shawarar fada mata abinda yafaru da
salma! To amma nayi tunanin halinda inna zata
qara saka kanta aciki shiyasa nace bari dai
ngaya miki yanxu mene ne mafita!?
Hjy tai ajiyar zuciya daga bisani ta dubi Abba
tareda cewa.
Toh nidai alhj dazakaji shawarata anawa tunanin
wannan ai abin farin ciki ne kuma rufama juna
asirine.
Yanxu idan akace salma wani bare zata Aura
kaga dole ne sai an fada mishi abunda yafaru da
ita kuma wannan kamar cin zarafine da kuma
tonan silili.
Idan ba tayi dace da miji me sonta bane yadinga
mata gori kenan., akan abinda itama bada
sonranta bane tsautsayine kawai ya hau kanta.
To Amma yanxu kaga afnan shi yasan abinda
yafaru da ita kuma har yanxu yana sonta
ahakan.
To alhj kaga zaifi mana rufin asiri sai ayi tuwo
na maina kenan.
Ammapa ni anawa tunanin kenan.
Wani irin kallon rashin fahimta alhj yake mata.
Yace wato ke har yanxu kina nan akan bakanki
kenan.
Yaci gaba da cewa
Daman nasan abinda zakice kenan.sbd daman
cen abinda kikeso kenan.
To Amma idan da kinson wannan hadin yanxu
yakamata ki cenja ra'ayi sbd bakisan qatonda
yai mata fyade ba.
Yanada cutar qanjamau ko bayidashi.
Wannan duk be dameki ba. Ke baruwanki da
lafiyar danki.
To idanke kina ganin wannan hadin me yiwuwane
gwara ma ki cenja tunani.
Ke ko tunanin yadda aka wulaqanta miki yarinya
ba kyayi.
To kisani bazan taba bari a kashemin yaro ba.
Shi kadai Allah ya bani na miji kuma nabari azo
a goga mishi cuta.
Towai shiyace miki ma har yanxu yana sonta.
Ai shidinma ba mahaukaci bane.
Juya kanshi yayi yai wani dan gajeran tsaki...
Mtsw...tare da cewa keda akace kibada shawara
kinxo kina wani fadin abinda bazai yiwuba.
Sadda kanta tayi qasa tace Allah ya huci
zuciyarka..Amma alhj ai shawaran na bada
bawai nace ayi dole bane.
Kuma kace kayima inna alqawari akan zaka aura
mishi salma.
Sannan na tabbata afnan shiyasamu inna yace
tai maka magana domin Jiya bayan fitanka
shima yafita.
Na tabbata hakanan inna bazata taso da wannan
maganarba saida izinin afnan.
Kaga kenan har yanxu yanason salma!.
Taci gaba da cewa.
Ni nasan daman soyayyarsu da salma bazai iya
gudunta akan wannan abun daya sameta
ba.
Kuma ya burgeni.
Sannan Wannan shine lokacinda yakamata ya
nuna mata shi masoyin gaskiya ne.
Kuma zai iya kasancewa tare da ita a kowani
hali.
Yanxu sai kayi tunani.
Danka dai yanason salma!
Kai kuma kayima Inna alqawarin hadasu aure!
Sannan wannan abun alfaharine agaremu.
Kuma rufin asirin zuri'armu ne.
Sai kaje kayi tunani ni iyakan abunda zan iya
fada kenan.
Amma ka gafarceni idan na bata maka rai.
Gaba daya jikin Abba yai sanyi da irin
maganganun umma.
Saidai har yanxu yanajin bazai iya bari Afnan ya
auri salma ba"
To amma ya zaiyi da inna!?yakasa samun
wannan amsar.dan haka ya dubi umma yace
shikenan na gode! Ni yanxu zanshiga wanka ayi
qoqari agama hada break kafin na fito.
Umma tamiqe tace to alhj saika fito.
Bata zame ko inaba sai kicking nan taga aunty
sadiya tanata hada abincin break.
Ta gaisheda momyn nata sannan tace umma ai
nashiga dakinki zan gisheki ban ganki ba.nace
ko kina dakin Abba ne shine kawai nataho
kicking nakama aiki dan yau inaso ne naje
gidansu salma.
Umma tace eyya aiko yakamata kije kidubata
kam,
Nima yau naso tambayan Abbanku zuwan .to
amma banga fuska bane dan yau ranshi abace
yake kuma hankalinshi a tashe yake.
Jiya inna tatayar masa da hankali.
Aunty sadiya ta ware ido tace topa wani abun yai
mata ne!?
Umma ta yamutsa Fuska tace kinsan dai halin
abban naku.
Wai tataso mishi da maganar auren salma da
afnan ne wai dole saiya hadasu Aure.
Shine ya nuna mata beyarda ba. Shine ta dinga
mishi kuka hankalinshi yatashi har saida yai
mata alqawarin hadasu aure.
Shine yau yatashi da bacin rai wai yaza'ai ya
aura mishi yarinyarda aikaima fyade be sani ba
kota kamu da wata cutar.
To shiyasama nakasa tambayarshi nabari saiya
huce.
Gaban anty sadiya saida yai wani mugun
bugawa.
Amma ta wani bngaren kuma taji dadin wannan
maganar.
Dan kuwa shiyafi kowa dacewa da aurenta. Bai
cuceta a banza ba.
Dan haka tace tohpa yanxu momy yaza'ayi
kenan"
Tace oho nidai nabashi shawara idan yaji
shikenan.
Aunty sadiya tace to umma Alllah yazaba abinda
yafi alkairi!
Tace Ameen dai.
Yi Sauri kigama kimtsawa dan yanxu zai fito
yayi break ya fita.
Umma ta fito tazo palo tadan kashin gid'a akan
kujera.
Abba kam yana gama kimtsawa beyi wani
jinkiriba ya nufo palo anty sadiya tana tsaye
tana shirya abinci akan dining ta duqa ta
gaisheshi ciki ciki ya amsa da ganinsa kasan
yana cikin damuwa.
Yace sadiya maza kije ki kirawomin afnan yataso
yanxu inason magana dashi.
Tace to abba.
Ta nufi sashen Afnan tafara buga qofa. Shima
lokacin ne yasamu dan bacci ya kwasheshi,
kamar a mafarki yaji ana buga qofa. Ahankali ya
bude ido yana sauraron ko Zaiji an qara.
Yaji anci gaba da bugawa.
Daqyar ya iya tashi jikinsa ko ina ciwo yake
haka yaqaraso bakin qofar ya bude.
Aunty sadiya yagani ta jefo mai wani harara
shiko yace ina kwana.
Bata amsa ba tace Abba na nemanka yanxu
kuma.
Ta juya abinta bata saurari me zaice ba.
Tana zuwa tace Abba yana zuwa.
Abba na zaune akan dining umma ta zuba mishi
abinci Amma ba abinda ya iya ci.
Saiga Afnan ya fito jiki a sanyaye yaxo ya zauna
akan Capet
Ya dubesu yace umma ina kwana.
Tace lapia lau ya jiki.?
Yace da sauqi.
Sannan yace abba ina kwana.
Wani irin kallo yajefo masa me cike da alamun
tambayoyi!.ba tare da ya amsa gaisuwanba.
Cikin zafin murya yace AFNAN..!
Firgicinda yayi saida qwaqwalwarshi da ruwan
jikinshi duk suka dena aiki.
Tsoro da fargaba suka ziyarci zuciyarsa.!
Muryarshi na kyarma yace Na'am Abba.
Abba yasake jefo masa wani hararan daga bisani
yace.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 25
==>Afnan kabani kunya. Ban taba tunanin zaka
watsamin qasa a ido ba.
Wai harkayi girmanda zakaje kahadani da inna
akan salma ko?.to kasamu yadda kakeso. Domin
kuwa tayi abinda kasakata.
Kuma zan Aura maka salma!
Amma kasani duk abinda yafaru dakai kai kaja
ma kanka tinda kai bakasan ciwon kanka ba.
Baka kishin abinda akaima yar uwanka .
Dan haka zan Aura maka salma!kuma babu saki
atsakaninku har abada.
Sannan nacire hannuna akanka kaje kai duk
abinda kaga dama.
Afnan kansa na qasa ya dago kannshi ahankali
idonsa sunyi jawur ya kalli Abba kabinsa na
karkarwa yace Abba..walh..ni...kafin yaqarasa
tuni Abba ya daka mishi tsawa..get out
kabacemin da gani. Banason ganika agabana.
Agigice ya miqe kamar zai kifa sbd Sauri.
Umma ne ta kira sunan Afnan"tsayawa yayi cak!
batare da ya waygo ba. Sannan taci gaba da
cewa haba alhj dan Allah ka sassauta mishi
mana., baka ganin shima ba lapia ne dashi ba.
Abba bece mata komai ba ya miqe yadauki
jakarsa da keys din mota yai waje fuuuu!
Batareda yaci komai da aka Zuba mishi ba.
Ganin Abba ya fice afnan ya juyo ahankali ya iso
dining din yadda umma ke zaune yaja kujera ya
zauna idanuwanshi cike fam da qwalla.
Umma ta dubeshi tace Haba afnan kakwantar da
hankalinka kariga kasan halin babanku.
Fushi yayi kuma zai huce nan bana jimawa ba.
Kuma ni ina bayanka 100 bisa 100. Naji dadin
abinda ka yanke na taimakon yar uwanka.
Kuma karka sake kace zaka kalli abinda akaima
naka yar uwan domin kasamu hanyan
musgunama salma.
Dan kuwa ita babu laifinta aciki.
Inamai farin ciki da wannan lamari domin rufin
aairinmu ne gaba daya.
Dan haka ka kwantar da hankalinka ka qyale
alhj.
Yanxu dai kaci Abinci kasha magani kaga sai
rama kakeyi duk kabi ka lalace.
Nan dai taita lallashinsa har saida yaci ya qoshi.
Daman shi babban damuwarshi shine abba yaqi
amincewa.
Amma tunda sai ya amince komai zai faru me
sauqi ne.
Suna cikin firansu. Saiga aunty sadiya tafito ta
fesa kwalliya tayi masifar kyau.
Doguwar riga tasa na atanfa ya zauna daram
ajikinta taqaraso gunsu cikin takunta irin na
qasaita. Sannan taja kujera ta zauna gamida
janyo kulan Abinci tana qoqarin zubawa tace
umma Abba harya fita ne.
Ta gefen ido kuwa wata irin harara ta dinga
aikawa afnan din.umma tace eh yanxu yafita ko
break dinma beyi ba.
tace to umma nima na shirya yanzu zanci abinci
ne na wuce.
Umma tace to idan kinje dai kice ina gaisheda
me jiki kuma insha Allahu nima gobe ina nan
zuwa dubata. Afnan zai kawoni shima daganan
ya dubata.
Saida suka kalli juna aunty sadiya da afnan.
Sannan yai qasa da kanshi cike da kunya da
fargaban abinda Umma tafada. Sadiya taci gaba
da cewa toh umma zasuji insha allahu,.
Afnan ya miqe yace to aunty ki gaisheta.
Tai kamar batajishi ba. Yakama hanya yai
dakinsa. Aunty sadiya ma tatashi taje daki ta
dakko jakarta da takalminta Wanda sukai
macing da kayan gamida sa hijjab dinta taima
momy sallama ta fice.
Salma kuwa yau tatashi ta qarfinta domin
tanajin qarfi ajikinta sosai. Sauqi dai yasamu da
izinin Allah. Kwalliya kuma yadawo sabo!!.Tsaye
take gaban mirror tana taje gashinta yadda ta
sakeshi abaya, gamida dakko wani siririn hula
Wanda macing color ne da kayan datasa
tsakiyarshi a bude yake. Ta gaban hulan kuma
an rubuta (love is life!) Riga da sket ne ajikinta
Wanda yaya Habib yayo mata tsaraba daga
Dubai. Sunyi matukar amsar jikinta.
Tayi masifar kyau Wanda ba'a magana.
Ta sanya wannan hular gamida fito da gashin ta
tsakiyar hulan.
Ta qara duba mirror sannan tasaki wani
murmushi Wanda yasake bayyana tsantsar
kyawunta gamida lumshe ido domin it a kanta ta
burge kanta.
Palo tayo tana tafiyarta a nutse tana isowa palo
kafin takaga zama tajiyo sallamar aunty sadiya
nan tatsaya cak! Aunty sadiya tana shigowa ta
aika mata da wani irin qayataccen murmushi tuni
Anty sadiya ta ware idanu gamida fadin. Woww!!!
Sister irin wannan kyau haka ai saikisa inyi
rangaji in fadi aqasa. Taqara sakin mata
murmushi sannan ta ruga ta rungumeta tana
fadin kai aunty ai kinfini hadewa.
Taqara dubanta tace kai!!waneni da had a kaina
da matar manya. Wannan ai dole kidinga furgita
maza irin wannan kyau haka"Ammapa kar karki
ya fashe kidauka wai kinfini kyaune. Kin wani
zabga jan baki kamar yar hayin kogi. Gaba daya
suka kwashe da dariya.
Salma tace to aunty ni duk ba wannan ba ina
wayana!toce kwantarda hankalinki gata a jaka.
Ta karbi jakar tana kokuwan budewa. Saiga
momy tafito tana dariya tace kudai bakwa rabo
da barkwanci Indai kuka hadu.
Dariya kawai sukayi salma ta ciro wayarta tayo
daki tafada kan gado aunty sadiya kuwa nanta
baje suna gaisawa da momy. Tin kafi tacire
wayar a key take ganin saqonni daban daban
messages miss call WhatsApp.!dan haka tarasa
ina zata fara dubawa. Saita yanke shawarar bari
tafara shiga whatsapp tana shiga saqonwa zata
fara gani..uhmn..saida gabanta yafadi dan jitayi
kamar yana kusa da itane zai kamata. Afnan ne
yai mata sqo har gashi biyu..hannunta na rawa
ta danna ta shiga ga abinda saqon farko ke
dauke dashi...Amincin
Allah shi tabbata agareki yake yar uwata kuma
abar begena a kullum. Na kirawayarki baki
pecking ba bansani ba ko kina bacci ne.
Daman ba komai bane inaso na fada miki ne
daman zanxo anjima in kawo muku ziyara
kigaya momy kuma ki shiryamun kayan dadi
kinji my dear sister!! Lallai fa afnan an shirya
maka kayan dadi irin Wanda baka zata ba kuma
kaci ka qoshi..!! x
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 26
==>Da wani dogon tsuka. Mtswwwwwww!!!.gami
da cewa...!Allah shi kyauta in Auri mugu! Ai ko
maza zasu qare aduniya bazan taba aurenka ba
sbd na tsaneka tsana mafi girma.!mugu kawai"!
Tana turawa tai blocking dinsa.
Amma mezai biyo baya!?
Tunanin baya ne ya fado mata! Kalmomin da
tafada masa abaya suka dinga dawo mata kamar
anyi recording dinsu. Tabbas ta fada masa wasu
kalmomi.
a gurin da take zaune. Kuma a irin wannan
yanayin na baqin ciki,.
Lokacinda take zubarda hawaye.
Zuciyarsu ke tsananin azabtuwa da son juna!.
take masa iqirarin cewa....Haba yayana walh
hannuwa na bazasu taba iya yin blocking dinka
ba.
Kayi hquri bazan iya aikatawa ba.
Kamar yadda bazan iya guje maka ba. Haka
baxan iya daina sauraronka ba. Idan kai zaka iya
yin blocking dina to ina me baka daman yin
hakan.
To amma kasani Kunnuwana bazasu taba gajiya
da sauraronka ba. Zuciyata bazata taba daina
azabtuwa da sonka ba.
Sannan a kullum zan kasance cikin baqin cikin
rabuwa dakai.
Idanuwana bazasu taba daina son ganinka ba
akoda yaushe. Alqawari ne na dauka bazan taba
auren wani namiji ba aduniya idan bakai ba.
Ashirye nake dana rayu dakai ako wani irin hali
ni bazan taba guje maka ba.
Ina qaunarka yayana qauna irinta har abada.!
Kayi haquri yayana walh bazan iyaba"hannuwana
bazasu iya blocking dinka ba.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 28
==>INNA..ki..taima..keni muryarta na rawa! Shi
kanshi afnan yai matuwar rudewa da furgita
tsoronshi daya karta fadi ta sume kamar yadda
tayi lokacinda yaje gidansu.
Dan haka yai miqe shima akidime yake fadin
SALMA!SALMA Dan Allah ki natsu ki natsu kinji
pls SALMA! Yana qara matsowa shima jikinshi
barin yakeyi,.
Haka take qara Ja da baya tana fadin INNA..kin
ganshin.. KO.. Daidai nan ta tokare da qofa tai
wani irin qara yayinda yaqaraso a guje ya ruqota
alokacinda take qoqarin kifawa. A daidai lokacin
daya ruqota taqara sakin wasu tagwayen ihu
gamida kuccewa ta fada cinyar inna ta
qanqameta sosai tana tsusa kanta a tsakankanin
Inna,!
Gaba daya mamaki ya hana inna cewa komai
ganin jikokin NATA sun afka wani irin yanayi na
rudu Wanda takasa fahimgarsu., batasan sanda
tafara fadin."LAPIA!LAPIA meyake faruwa ne!?
Salma kuwa qara qanqameta take tana fadin
Inna kaina ne kaina inna! Cikina..ke..inna ta
katseta da cewa meya samu kan naki?
Afnan yanajin haka be tsaya yayi wata wata ba
ya zari takalmarsa yabar gidan da saurinsa. Dan
yasan idan yazauna abin saiyafi haka.
Inna ta daqo tana qwala masa kira amma inaaa
dan talikin yayi nisa! Dawo wa tayi kan salma
taci gaba da cewa wai me kuke nufi ne
daganinsa kin fara kuka shi kuma ya gudu gudu.
Kin sakani cikin wasu wasi.
Wani irin sanyi salma taji aranta alokacinda ta
waigo ta tabbatar da cewa afnan baya palon.
Miqewa tayi batare da taceda inna komai ba ta
kwanta kan kujera domin har kanta ya fara ciki
ga wani zazzabi dayke niman kamata.
Inna tai juyin duniyar NaN akan salma tafada
mata gaskiya amma ta dake akan ita kanta ne
da cikinta kawai yake mata ciwo.! Haka ta gaji
ta rabu da ita tace ai idan tai tsami maji . idan
kuma Auren ne bakwaso ai
sai inji. Salma tai saurin tashi ta zauna gamida
cewa wani rin aure kuma.!
Inna ta galla mata harara tace irin na uwaki!
Dole takama bakinta tai cit! Tadan huta nawasu
yan daqiqu tatashi tace zata wuce. Domin ita
kam yau bataji dadin zuwanba ma. Daqyar
tasamu ta isa gida tana tangadi jiri take gani
sosai dan haka tana zuwa ta zube akan kujera
jikin nan NATA ya dafe yayi zafi rauu! wasu
zafafan hawaye ne keta sulalo mata. Momyce
tafito daga sashenta gaqaraso wajenta da Sauri
tana fadin salma lapia kuwa!meya sameki?!.
Tana kai hannu jikinta taji zafi rau!tace
subhanallah zazzabi kikeji haka kuma shine baki
gayamun ba"bari nakawo miki Abinci kici nakira
driver muje asibity.
Momy ta qwalama sumayya kira saigasu sun fito
dukkansu aguje suna dariya. Ganin salma a
kwance yasa sukai tsuru tsuru momy tace ma
sumayya maza kije ki zuboma auntynku abinci
batajin dadi ne. Ba musu ta wuce kicking sai
gata dauke da pleat din kuskus taxo ta dire ma
momy sannan taje firji ta dakko robar faro daya
ta kawo momy tace to tashi kici.!
Taqarayin wani narai narai da ido tace momy
cikina ciwo yake.
Momy tace kiyi haquri kici koda kadanne. Haka
tatashi momy tafara bta abaki. Bai wuce cokali
4 tayi ba kawai sai amai momy ta tallabota da
sauri haka ta dinga kwara amai duk jikinta yai
yaushi. Momy kam duk ta rude tasamu ta
kwantar da ita sannan tamiqe dasauri taje ta kira
habib tafada masa halinda suke ciki sannan taxo
tafara gyara wajen.!ba a dauki lokaci ba habib
ya turo da driver.
Aka kwashesu sai asibity. Suna zuwa aka
karbesu cikin kulawa kasancewar habib yayi
waya tun kafin su iso..Dr ya dubata sosai tareda
wasu yan tambayoyi itakam tadinga jera mashi
amsa. Tagaya mishi cewa takai 2weaks tana
fama da ciwon ciki kadan kadan. Sannan takanji
tashin zuciya lokaci lokaci ga yawan ciwan kai.
Dan hak Dr yasa aka debi jininta da fitsarinta
sannan yahada musu wasu yan magunguna dazai
taimaka mata yace suje gida tafara sha kafin su
dawo gobe a tabbatar da result din da aka
samu.! Momy bata kawo komai aranta
ba"sabanin ni da harna fara wani tunani! Kaji
iyayen katslandan
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 29
==>A dimauce momy ta miqe tana Innalillahi wa
inna ilaihirraju'un Dr karufamun Asiri jikinta ko
ina fari yake.
Yayinda ni da Dr muka saki baki da hanci da ido
duk muna kallonta.!
Mamakin Dr shine shin meyasa momy ta furgice
haka shin bata bataraba da qaruwanda suka
samu ne ko kuwa"
Mamakin salma kuwa shine.. Wani irin ciwo ne
juna biyu dahar momy ta furgice haka take
Neman faduwa.! A tsorace ta kalli Dr tana
qoqarin yimishi tambayar wani irin ciwo ne take
dauke dashi.!
Kafin ta kaiga cewa komai sai ganin momy
sukayi ta sulele aqasa sumammiya!.
A haukace salma tai kanta tana kwarma ihu tana
fadin Dr wani irin cutane nake dauke dashi har
baqin cikinshi yake Neman ya kashemin
mahaifiya"
Shima gaba daya yagama kidimewa yayo kan
momy yana fadin kawai nace mata ne kinada
ciki shine tashiga tashin hankali haka!? Ko
bakida Aure ne dai! Allah dai yasa
ba abun kunya kika daukoma iyayen naki ba.
Cikin wata irin murya salma ke cewa Dr cikin
baby nakedashi!? Yanxu baby ne acikina
taqarasa maganar tareda shafa cikin! Dr yace
qwarai kuwa kina dauke da juna biyu har na
tsawon wata uku babu yan kwanaki!" Ai kafin
yagama rufe bakinshi sai ganin salma yayi ta
kife a qasa da alamun itama suman tayi.!
Topa Dr yaqara rudewa matuqa da Sauri ya fice
yana kiran nurse kamar wani zararre.
Dan Danna akaxo aka kwashesu gaba daya aka
basu gado. Duk iya qoqarinda zasuyi akansu
sunyi Wajen 2 hours Amma basu farfado ba Dr
duk ya gama rudewa da al'amarinsu.
momy ce ma tadinga tafarfadowa tana sake
sumewa."dan Haka Dr ya kira Habib ya fada
masa abinda ke faruwa.
Karkuso kuga daburcewa wajen Habib dan shima
kadan yarage ya sume.
Dan Haka numfashinsa ke fita wani kan wani.
Baccin yayi ta maza da shima kwasarshi zq'ayi.
A kidime ya suri motarshi ya kama hanyar
asibityn yana rafka gudu kamar wanda ze tashi
sama.!
Allah ne dai ya kiyayeshi harya isa lapia. Yana
isa ya kira Dr. Dadauri yazo suka qarasa yanda
su momy suke daidai lokacin momy ta farfado
sukayi ido hudu da Habib kawai saita fashe ta
kuka.
Yaya Habib yaqarasa gabanta shima idonshi sun
kada sunyi jawur. Yace momy dan Allah ki
kwantar da hankalinki ki natsu kar hawan jininki
ya tashi. Pls momy komai ze wuce.
Murya a sarqe momy take magana tayaya
hankali na zai kwanta wannan balq'i ya afko
mana ta Ina zan samu kwanciyar hankali. Kawai
tasake fashewa da kuka shima kifa kanshi kawai
yayi yana zubda hawaye.
Saida sukayi mai isarsu sannan momy ta juyo
tace ina salman take!? A hankali ya dago da
idonsa jawur yace momy tana nan ita bata
farfado ba Drs sunacen suna qoqari akanta.
Gashi kema kinsa damuwa sosai aranki momy ta
wanne kikeso muji. Momy ki dauka wannan Abu
kawai hukunci ne daga Allah kuma babu yadda
muka iya saidai haquri mu rungumi qaddara.
Momy tafara qoqarin tashi yaji bazata iyaba
haka ta koma tana zubda wasu zafafan hawaye.
Nan Dr yaxo yafra duba momy. Jininta har ya
hau sosai akai mata allura tasamu bacci. Habib
yakira Ahmad yafada mishi abinda ke faruwa.
Tab! Haka ya tawo asibityn a fusace da nufin
komai ma zai faru to saidai yafaru dan yau saiya
fadama yaya Habib Wanda yaima salma fyade.
Cen bangaren su hjy safiyya kuwa gidan yacika
da murna domin yaune ranar da yaya Aliyu zai
dawo. An tanadar mishi girki kala kala. Husna
ma datake kwance batada lapia yau daida ta
gyagije sbd murnan dawowar yayan nata.
An tura driver yaje ya daukoshi a airport tare
suka wuce da husna akabar momy da inna A
gida. Basu wani Dade da zuwaba jirgin nasu ya
sauka. Ya kira wayar husnan tace yaya gamu
nan a waje nida driver kai muke jira .yace OK to
ganinan fitowa. Cen husna ta hangoshi yanata
faman waige waige itako sai washe baki take
tadaga waya ta kirawoshi yana dagawa tana
yaya gashinan INA kallonka yace to ai ni....
Kawai daiya hangota tanata dariya da saurinsa
ya karaso shima fuskarsa dauke da murmushi.
Tace ya ya Aliyu kaga yadda ka qara kyau kuwa
gaskiya garin nan ya karbeka.
Yasaki kyakkyawan murmushi Wanda yaqara
bayyana tsantsar kyawunsa gamida cewa yar
Autar mama kenan. ai ni naga duk kin cenja
munne gaba daya ma. Nida na barki yar qarama
kina 8years. Yanxu ko shekarunki nawa ma oho.
Ta murguda baki tareda rangaji dakai tace kai
yaya shrkarun nawa ne ma zaka manta KO.
Yai dariya yace to yar rigima wasa nake miki.
Amma ga dukkan alamu kinyi ciwo dan naga
kamar akwai rama a jikinki.
Tandan murmusa tace yaya kenan ya akai ka
gane. Yce ko Wanda be taba ganinki ba idan ya
ganki yanzu yasan kinyi ciwo. Tace gaskiyarka
ne yaya walh yanxu ma zuwanka ne yasa na
warware sbd murnar ganinka. Yace wayyo yar
Autar umma meyake damunki. Uhm kawai tace
labarin me tsawo ne yaya yanxu dai muje gida
ka huta
Suka qarasa mota suka shiga suka dau hanya.
Sun fara tafiya Amma gaba daya yakasa daure
Abinda yakeso ya tambaya dan Haka yace yar
Autar mama wai ina qawarki ne na dauka tare
ma zakuxo tarbana sai kikazo ke daya!.
Tadan jiyo ta kalleshi tareda cewa wa kenan!
Yadanyi farii da idonsa gamida cewa Salma
mana!. Tace oh kacemin Amarya! Dandanan
dariyarsa ta tsaya ya daure muska yana mata
wani irin kallon rashin fahimta cikin sassarqewar
murya Wanda bemasan yayi ba yace ban gane
Amarya ba!?.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 30
==>Husna tace Eh mana! Yaqara hade rai yace
Wato Aure akai mata ban sani ba.! Husna
tadanyi murmushi tace kai yaya maida wuqar ai
ba'a riga anyi bikinba ma daman ance saika
dawo!. Yadanji sanyi kadan aransa sannan ya
sake cewa to waima salman ne za'aima aure tun
yanxu! Wayema ya fada miki haka!? Tace kaidai
yaya kanada qosawa kabari idan munje gida
zakaji komai. Yace kinyi alqawari tace eh yayana
na kaina.! Haka yahaqura badan ranshi yaso ba
dan yaqosa yaji gaskiyar abinda husna tafada.
Ya qosa yaga ankai gida. Sun isa gida cikin
qoshin lapia murna kota ina. Inna kam bakinta
ko rufuwa bayayi. Ya Aliyu yaje yai wanka yaxo
dining amma duk cin abincin ya gagareshi inna
dasu momy da husna duk sun kewayeshi. Cikin
hikima yace Inna wai mamanki batasan zan
dawo bane?! Inna tace
oh Mamana Amarya ai rabona da ita tun ranarda
sukaxo nan da afnan sunataimin sakarci! Yana
qoqarin kai cokalin abinci bakinsa baisan
lokacin daya aje ba yana fadin Wani irin Amarya
kuma Inna! Tace kaidai ci abinci koma wani iri
ne ai zakaji. Gaba daya yaji ya qoshi dan haka
yamiqe tareda sakin wata yar tsaki mtsw..saiku
cinye abincinku ai.!
Gaba daya suka bishi da ido dan sun gaza
fahimtarsa. Momy tace A a inazakaje bakaci
abincinba yace nifa nama qoshi tin a jirgi. Tace
abincin jirgin wani abun kirkine! To dawo
kazauna ko zakayi amai ne saikaci abincin nan
bazamuyi wahalar banza ba. Murmushi kawai
yayi me kama da yaqe yakoma yazauna yacigaba
da tsakurar abincin. Ya kalli husna yace wai
meya samu wayar salma ne baya shiga! Tace
walh nima
bansani ba tinda tai ciwo ba'q samunta awaya
bansani ba ko wayar baya hannunta ne.! Oh tai
ciwo amma ko agayamun KO! Gaba daya sukasa
dariya sbd yadda yai maganar kamar wani
qaramin yaro! Inna tace kaji shirme banda
abinka idan an gaya maka zuwq zakayi. Yace
amma ai nakira waya nai mata sannu ko!
Anandai suka gama yan ciye ciyensu da firarsu
kowa yanufi makwancinsa domin dare ya tsala"
Wajensu momy kuwa Habib ne yadawo gida ya
kwashe su rufy yakaisu gidanshi.!fadila tayi tayi
yafada mata meke faruwa Amma yace mata
kawai momy ne batajin dadi; sannan yakoma
asibity cen suka kwana shida Ahmad. Yaya
Ahmad tinda yaje yaga halinda momy ke ciki
yakasa gayama Habib gaskiyar lamari dan gudun
qarya hurama abin wuta.! Momy tadan samu
sauqi dan qin zama tayima agunda aka ajeta
takoma gun salma saidai takasa daina kuka duk
in ta kalleta. Salma ta farka amma batasan inda
take ba har yanxu likitoci ne ke zarya akanta.
Sai fizge gizge take. Hakan yaqarasa jinin momy
ya hau sosai haka suka kwana ba barci.
Habib ne zaune akan darduma bayan ya idar
da sallah yayi jugum yana tunanin abinda Dr
yafada!.
Idan har kunason tayuwar yarinyar nan to mafita
daya CE! Kodai azubda cikin nan kokuma a nuna
mata cewar kuskure akayi wajen fadar
sakamakon!sannan kuje kucigaba da lallashinta
kuna nuna mata mahimmancin yarda da qaddara!
Sbd idan ba haka ba. duk ranarda ta fahimci da
gaske ne"zata iya shiga halinda yafi na yanxu.
Domin kuwa me ciki ba'asonta da damuwa
hawan jini zai iya kamata tun tana yar
qaramarta.
Dan Haka ko wanne daga cikin abinda kuka zaba
me hadarin gaske ne!
Wasu hawayen baqin ciki suka gangaro masa.
Aransa yace Tabbas dazaiga Wanda yaci
mutuncin qanwarshi da babu abinda zai hana
ya shaqeshi harsai ya mutu"
Wayarshi tai qara ta katseshi daga tunaninta ya
fada. Aliyu ya gani da numbernshi ta Nigeria ya
dauka da Sauri gamida yin sallama! Ya aliyu ya
gaisheshi cikin ladabi sannan yace yaya.. Hafin
yagama fadi ya Habib yace yaushe ga dawo ne
babu kodan sanarwa! Yadanyi murmushi gamida
cewa walh jiya nadawo aina dauka mama ta fada
muku zan dawo! Yace kai baka fada mana ba sai
ita" yace to babban yaya afwan yanxu dai ya
madam yasu momy! Y Habib yai shiru yama rasa
abinda zaice.! Daga bisani yace uhmm Aliyu
walh gamu nan ma A asibity salma da momy
duk basuda lapia!
Cikin tashin hankali yace subhanallah meya
samesu!?
Cikin rawar murya yaya Habib ke magana. Zan
gaya maka Amma gidanku babu Wanda yasani
Inna bata saniba momynku ba bata sani ba! Dan
Allah karka fadama kowa dan kasan inna zata
iya tada hankalinta hawan jininta yazo yatashi!
A rude ya Aliyu yaci gaba da cewa fadamun nayi
alqawari bazan fadamasu ba!
Ya Habib yacigaba da cewa fyade akaima salma
kusan wata uku dasuka wuce. Sanadiyyar barinta
da akayi ita kadai agida wani mugun yasamu
damar zuwa ya aikata lalata da ita! A wannan
lokacin salma tasha wahala sosai kwananta 3 a
asibity aka sallameta!
Shine yanxu akai gwaji akaga tana dauke da
ciki sanadiyyar haka ne Itada momy suke
kwance yanxu haka salma batasan yadda kanta
yake ba!"
Tinda aliyu yake bai taba shiga tashin hankali
irinna yau ba! Daga lokacinda yaji kalmar fyade
yayi tsananin gigicewa Wanda bai ma iya
fahimtar me Habib din yaci gaba da fadi ba"wani
irin juwa yafara dibarsa Allah yasa akan gadonsa
yake!
Shin wai mafarki ne yake! Ko kuwa gaske ne
abinda kunnuwansa ke jiyo masa!
Masoyiyarshi"abin qaunarshi" wacce yadade
yana tarairayar soyayyarta"
Wacce yarayu da tsananin qaunarta tun kafin
tasan kanta! Wacce yake burin tazamo uwar
yayansa"
Jinin jikinshi Salmat ita akaiwa fyade harma
tana dauke da ciki!?" innalillahi wa inna
ilaihirraju'un.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 31
==>Cikakken labari...! Alhaji Suleiman shine
Babban d'a awajen inna sai Alhaji Abdullahi
sannan Alhaji Abubakar Wanda a yanxu suke
kira da Abba! Haifaffun yar Kaduna ne. su uku
Allah yaba Inna kuma duk maza. Bayan rasuwar
mahaifinsu wato malam sani.
Inna ta koma wajen babban 'd'anta da zama
wato alhaji sulaiman.
Shine yacigaba da daukar nauyinsu" bayan
rasuwar malam sani da shekara1 Allah yadauki
rayuwar alhji sulaiman wajen tafiya tafiyan
neman halak da abinda zasuci a hanyar tafiyarsa
lagos ne yai Accident Allah yakarbi rayuwarsa!
Lokacin yanada matarshi daya hajiya Safiyya da
'ya'yansu biyu" wato Aliyu da husna. Tsakanin
aliyu da husna akwai tazara sosai dan harsun
fidda rai dasake samun haihuwa dan shima aliyu
sun jima basu sameshi ba!.cikin ikon Allah saiga
cikin husna anyi murna sosai!" Husna tanada
shekara 5 aduniya mahaifinsu yarasu. Daga nan
alhji abdullahi shiyacigaba da daukar nauyin
gidan harda dawainiyar makarantar Abubakar har
yakammala karatunsa'! alhj abdullahi yanada
matarshi me suna hjy Aisha wacce suke kira da
momy sunada yaransu hudu4 Habibullah Ahmad
salma sumayya! Habib shike gaba da aliyu Dan
yabashi wajen 6years sun taso tare jininsu ya
hadu sosai! Alhaji Abdullahi shiyaci gaba da
qoqari har Abubakar yasamu aiki" lokacin ne
yasamu matarshi mai suna zainab" cikin ikon
Allah tasamu ciki ta haifi santaleliyar yarinyarta
wacce aka rada ma suna sadiya!
Lokacin habib nada shekara 10 a duniya aliyu
kuma Nada shekara 4". Bayan 2years aka haifi
afnan aka sa mishi sunan mahaifinsu
aliyu!..wato Suleiman. Shine ake kiransa da
afnan.! Cikin ikon Allah habib kammala
secondary school dinshi aka turashi maleshia
acen yayi degree dinsa yadda yadawo amatsayin
Cikakken engineer.!
Lokacinda yadawo ne yayi daidai da lokacinda
sadiya ta kammala secondary school tanada
shekara 17" afnan kuma yana Ss1 shekaransa
15.
An haifi salma da husna yanda shekarau8
aduniya! Kwana 4 salma tabama husna domin a
jejjere aka haifesu" salma tun tana qaramarta
sun shaqu sosai da afnan idan yaxo gidansu
dagyar ake banbareta daga jikinsa!.
Yaya aliyu ne ma basu wani saba ba hasali ma
tsoronshi takeji danshi yanada fada kuma
bayason yawan rigima. Saidai yana masifar
tattalinta bayason yaga wani Abu dazai bata
mata rai"baya sati baixo yaganta ba tareda
tsarabar kayan ciye ciye,
Ranar wata Saturday Abba da dadynsu salma
suna zaune a palo yadda yakirashi domin
tattauna wani muhimmiyar magana.!
Dady ne ya dubi Abb yaci gaba da cewa..!.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 32
==>Ba komai yasa na kira ka ba illa wata
alfarma danake nema kuma nake ganin yadace
mu qara qulla danqon zumunci!
Ina nema ma Dan wajena Habibu auren yarka
sadiya domin na yaba da nutsuwarta kuma na
tambayi yaron nan yafitomin da wacce yakeso
Amma ya nunamun shi babu wacce yakeso
shiyasa nace toni zan duba mishi wacce tadace
kuma naga babu wacce tadace dashi kamar
sadiya. Dan haka ina nema mishi Aurenta idan
har babu Wanda takeso!
Murmushi kawai Abba yayi Wanda zamu iya
kiranta da yaqe gamida cewa Gaskiya yaya naji
dadin wannan maganar ai wannan basai kanemi
shawarata ba dan kuwa sadiya yarka CE kana da
damar zaba mata mijinda yadace da ita
ballantana kuma wannan yaro me hankali kuma
dan uwanta"
Ai kaima me bashi ne basai ka nemi shawarata
ba!
Dady yai murmushi cike da jin dadi yace a a
wannan ai haqqinka ne yazama dole na nemi
amincewarka kuma naji dadin yadda kakarbi
maganarnan yanxu saika sanarma iyalinka kuma
a tambayi sadiya idan ta amince.
Nima zan sanarda iyalina kaga idan komai ya
daidaita ma basai ankai abin da nisa ba"
yaqarasa maganar tareda qurama Abba ido!
Abba yadan sosa qeya yace gaskiyane yaya ai
dama ka yanke ranar Auren kawai tunda babu
wata matsala nidai daga gareni."
Dady yace a a baza'ai haka ba a duki kakkin
yarinya gwara anemi amincewarta dan Bazanso
arakura mata ba.
Abba yace shikenan yaya za'ayi yadda kace
amma nasanma babu wata matsala"
Nizan koma yaya duk yadda mukayi zakaji".
Dady yace to yayi kyau nagode sosai Allah yabar
zumunci.
Abba yace nikeda godiya yaya. Tareda miqewa
sukai sallama ya nufi gida zuciyarsa cike da
wasuwasi!
Lokacinda Abba yasanarma umma maganar tayi
farin ciki sosai haka ma bangaren su dady momy
tayi farin ciki matuqa kuma tabada goyon baya
Dari bisa dari!
Saidai kuma a bangaren gwaskayen babu komai
sai tarin damuwa Dan Kuwa habib hankalinshi
yayi matuqat tashi a lokacin da yaji za'a
hadashi da sadiya!
Danshi gani yake an rainashi da wannan yar
tsigigiyar yarinyarne za'a hadashi.
Saidai kuma haka nan ya daure ya amince da
zabin iyayensa batareda ya nuna qin
amincewarshi ba.
A bangaren sadiya ma haka.
Dan tayi kuka kamar ranta zai fita dan ita bawai
sonshi ne batayi ba Amma tana matuqar jin
tsoronshi dan bata cika ganin dariyarsa ba,
Tunaninta kawai ta yaya zata zauna da yaya
Habib!"
Ba'a jima ba aka tsayar da biki sati2 tunda aka
sa ranar bakin bata sashi a idonta ba sai
ana sauran kwana3 yazo shima a daddafe yake
tambayarta nawa take buqata Wanda zatai
hidima.
Tace mishi bata buqatar komai. Besake cemata
komai ba ya Ciro check din dubu dari biyar ya
miqa mata.!
Ta Amsa tareda dubawa ta ware ido gamida
cewa yaya ai wannan kudin sunyi yawa babu
abinda zanyi dasu!
Shiko gogan naka harya juya baya yana shirin
barin wajen yatsaya cak batareda ya juyo ya
kalleta ba. Sannan yace..!
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 33
==>Sannan yace idan kinyi Abinda zakiyi ki
zubar da sauran.!
Ya wuce abinsa yana qoqarin Ciro keys din mota
a aljihun wandonsa!
Yaqarasa cikin nutsuwa ya bude motarshi yacika
rigarsa da iska. Inda yabarta nan tsaye a Gardine
riqe da check din daya bata!
Wasu zafafan hawaye ne suka cika idonta fal!
Suna qoqarin gangarowa.
A zuciyarta tace yanxu A haka ne zamu zauna
toya zanyi kenan idan aka kaini gidanshi?!
Tasa mayafinta ta goge hawayenda suka wanke
mata fuska.
Sannan ta shige cikin gida cikeda tunani iri iri.
Ranar Saturday aka daura auren sadiya da habib
. yan uwa da abokan arziki an taru sai murna
ake! Kasancewar shine Wanda yafara yin Aure a
gidan.; shiko Habib ba wata gayya yayi ba dan
dayawa abokansa ma be sanar musu ba.
Dan shidai a tunaninsa wannan ba Aure yake ba
nan gaba dai zaiyi Aure.
Ankai amarya dakinta. Gida yayi kyau sosai ba
yabo ba fallasa.
4bedrooms ne akwai babbar Palo ga fadin tsakar
gida. Daga cen wani bangare kuma Swimming
poll ne da dan bukka wajen shan iska !.
Bayan biki da 1month Aliyu yafara shirin barin
qasar zai tafi qasar waje a cen zai kammala
karatunsa! Dady shiya dauka nauyin
komai"lokacin su salma da husna zasu shiga
Primary1. A lokacin da zai tafi ne ana gobe yaxo
gidan su salma yima momy sallama.
Yana Zaune a palo suna gaisawa da momy salma
tadawo daga school ta shigo da gudu da fada
jikin momy tana fadin wash momy nagaji INA
abincina"
Kafin momy tace wani abu muryar yaya aliyu taji
ya daka mata tsawa.. Ke bakyajin magana
karyata zakiyi ne!? Shiyasa nakeson Sumayya da
tafiki sanin yakamata. Da Sauri ta zame daga
jikin momy gamida juyowa ta bata rai ta dasa
mishi manya manyan idanuwanta masu kwantar
da zuciya. Ko qiftawa batayi. Tana turo baki.
Saida yadanyi murmushi acen cikin ransa!
tabbas yana tsananin son wannan kyakkyawar
yarinyar Allah dai yabashi ita yafada a cikin
zuciyarshi!. A zahiri kuwa qara hade rai yayi
gamida dubanta yace. Ke bakida kunya ni kike
murgudama baki ko?
Momy dai sai dariya take musu daman sun saba
wannan diramar . aiko yana tafiya ta fara
surutai.
Walh ni momy yaya Aliyun nan haushi yake bani
sai yaita ma mutane fada.
Da yaya afnan ne yaxo baya maun fada!
Momy tace to ai kece ba kyaji shiyasa yake miki
fada. Tace to kawai dan nahau jikinki shikenan
seyace in sauka.
Ni gara ma yatafi yaba mutane waje yaje Cen
taita musu fadan.
Momy tace tafi cen rufemun baki. Wato har ma
so kike yatafi ko. To bazai tafi dinba. Tashi
kibani waje marar kunya kawai ba yayanki bane.!
Wucewa tafi tana kumbura baki. Shiko yaya
Aliyu daga nan gidan ya Habib ya nufa .saidai
be sameshi ba dan Haka ya yanke shawarar
kiranshi a waya ko kuma ya tura mishi text dan
kuwa akwai muhimmiyar maganan dayakeso
yafada mishi.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 34
==>Haka kuwa akayi yana isa gida ya kirashi a
waya suka gaisa yace Babba yaya naje gidan ka
bansameka ba. Daman naje ne nai maka
sallama.
Nandai sukasha fira suna shirin yin sallama ne
ya aliyu yadan Sosa qeya yace yaya daman...
Sai kuma yafara uhm..uhm.. Daman.. Yaya
Habib yace mene ne kuma kaketa wani
uhm.uhm. kafadamun mana. Yadan fara kame
kame sannan yace daman.. Yaya..wata alfarma
nake nema.!
To fadamun mana mene ne inji ya Habib kenan!
Yaci gaba da magana yana sassarqewa kamar
wani marar gaskiya. Daman..yaya..so So... nake
ka kulamun..da salma.sosai. kafin nadawo pls!
Ya idasa maganar yana shafa qeyarsa!.
Yaya Habib ya fashe da dariyar da be shirya
yinta ba. Cikin dariya yaci gaba da cewa shine
kaketa wani inda inda kamar wani me
koyon magana!
Kawai dai kacemin kana ciki." To ka kwantar da
hankalinka kamar kayi baquwa ta mutu! Zan
kula maka da salma Kana dawowa zan baka
abunka!.
Sanda kansa qasa yayi kawai jikeda jin kunya
kamar yana gabanshi. Tabbas yaji dadin yadda
yayan nashi yayi saurin fahimtarshi.
Nan yaya Habib yaita tsokanarshi harsukai
sallama. Washe gari jirginsu ya daga.
Yatafi da tsananin farin ciki Dan yasan cewa a
yanxu salma tazama tashi duk sanda yadawo
Za'a aura mishi ita.
Bangaren Amarya sadiya kam zaman babu dadi
dan yaya Habib gasata yake kamar waina.
Kullum cikin kuka take Amma takasa gayama
kowa abunda ke faruwa!
Babban abunda yake qara qona mata rai idan ta
tuna shine.. Ranar Daren farkonta yadda Yaya
Habib yaxo mata a bushe babu ko dan kazar nan
da ake kawoma amare Babba abin baqin cikin
ma yadda yaxo bako kunya ya tumurmusheta yai
mata hawan qawara babu wani alamun tausayi
haka yai mata jage jage saida yaga bata
numfashi. Sannan washe gari ma haka yasake
yimata akan raunin jiya. Haka ya jera kwana7 be
daga mata qafaba HQ ya kumbura yai sasul
gashi batasan yadda zatayiba
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 35
==>A kwanakin da salma tayi gidan aunty sadiya
ita kanta ta fahimci ba dadin yayan nata takeji
ba. Dan kuwa wata zubin a gabanta yake
balbaleta da fada kokuma tayi
abu ya gwasaleta.
Tun aunty sadiya tana boye mata har yakai abin
yawuce a boyeshi dan salma tagama fahimtar
komai.
Hakn yasa sadiiya tadena wani boye boye ta
kirata daki ta lallabata tace kota koma gida
karta sake tagayama wani cewa basa zaman
lapia da yaya habib.
Salma dai ranta baiso ba dan taso taje tabaiwa
momy labari. Kwanan ta 4 a gidan tace ita gida
zata koma ta gaji.
Aunty sadiya bata so hakan ba dan tana rage
mata damuwa sosai!
Haka taci gaba da zama cikin kadaici ta takura
da rashin samun kulawa wajen yaya Habib. Tana
shirye shirye komawa karatu dan ita dama harta
qosa tafara zuwa makaranta ko zata huta da
jarabar yaya Habib. Kawai saita fara laulayi.
Yaya Habib ne yakaita asibity akai treatment
dinta aka tabbatar mishi tana dauke da ciki
wata2.
Murna wajen yaya Habib ba'a magana" dan shi
Allah ya jarabceshi dason yara. Dahar yafara
tunanin ko juya ya auro sbd ya qosa yaga
jininsa!
Tun daga ranar ya Habib yafara tattalinta aiki
ma yahanata yi. Idan yaxo yaga tana wani abun
shizai karba yacigaba dayi ko kuma suyi tare.!
Ita kam harga Allah taji dadin wannan cikin dan
ya gyara zaman takewar Auren su. Itace har take
ganin dariyar yaya Habib. Ta kwanta jikinshi tayi
bacci yana tarairayarta tai amai ya wanke. Tai
mishi shawaba ya rarrasheta. Wannan abu yana
mata matuqar
dadi.! Dan ita harji take kamar ta zauna da
cikin" dan haka taita addu'a Allah yasa suci
gaba da kasancewa cikin farin ciki haka."dan a
yanxu ji take tana tsananin qaunar mijinta.
Wani irin soyayyace me qarfi ta dasu a
tsakaninsu. Lokacin da cikinta ya cika wata7 ya
hanata aikin komai abinci ma saidai a kawo
mata daga gida! Idan yadawo wajen aiki qarfe6
bashida aiki saidai ya zauna ya kwantar da ita a
yalwataccen qirjinsa yaita shafa cikinta yana
rada mata kalamai masu kwantarda zuciya. Cen
bangaren su salma kuwa duk in akai Hutu gidan
aunty sadiya take zuwa har akoma makaranta.
Saidai takan qosa tadawo wata lokacin sbd afnan
yana zuwa musu firan dare Gashi tanajin dadin
fira dashi
Shiyasa idan bata ganshi ba kwana2 batajin
dadi.
Shima kanshi wata lokacin binta yake cen wajen
aunty sadiya idan sukasha firarsu sai ya wuce
gida.
cikin sadiya nada wata8 su Afnan suka fara
shirye shiryen tafiya school shida ya Ahmad.
Inda Ahmad ya wuce sokoto. Afnan kuma ya
wuce Libya.
Salma tasha kuka sosai tafiyarsu.
Shima kanshi afnan daurewa yayi. Haka ya
rungumeta yanata rarrashinta tareda yimata
alqawarin zai dunga kira kullum suna gaisawa ta
wayar momy.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 36
==>Bayan wasu kwanakai da tafiyarsu afnan
aunty sadiya ta haifi santaleleyar yarinyarta
kyakkyawa yar blackbeauty yarinya son barka
kamarsu daya da babanta saidai shi fari ne ita
kuma black beauty ce irin mamarta.
Murna kuwa wajen yaya Habib kamar ze hadiye
babyn. Haka akasha shagulgulan suna inda
yarinya taci suna Rufayda suna kiranta da rufy.
Inna ce tazo ta zauna da ita.
Su aliyu Ahmad afnan duk an kirasu an
fadamusu sunata murna. Ranar suna akaima rufy
wani hadadden hoto aka tura musu.
Tunda aunty sadiya ta haihu salma ta dawo
gidan ta tare satinta2 ta saba da Rufy sosai
gashi yau zata koma gida dan haka taketajin
ba dadi.
Sanda yaya Habib zai mayar da ita gida ne
bayan sun shiga mota fuskar nan tata a hade. Ya
Habib ya dubeta yace yayadai yar rigima! Za'a
fara rigimar ko" ta tabe dan madaidaicin bakinta
ashagwabe tace yaya nidai banason tafiya nabar
rufy. Yace to ai momy ne tace a mayar
dake"nace tabarki tace a a!
Tace to yaya dan Allah ka sayamun waya kullum
na dinga kira inajin kukanta kaga momy bazata
bani wayarta ba.
Muguwa wato so kike tadinga kuka kenan ko.
Yafada tareda jefa mata harara cikin sigar wasa"
Murmushi tayi wanda bata shirya yiba ta dora da
cewa to yaya nidai inason inji kuma idan inason
abu zan kiraka nafada maka basai nataba wayar
momy ba"
To shikenan zan saya miki hankali ya kwanta!?
Dariya ta saki gamida lafewa a kafadarsa wayyo
yaya naji dadi Babba zaka siyamun KO.
Ya Habib yace eh Ammapa idan naga zai hanaki
kara2 qwacewa zanyi. Tace naji. Suka kama
hanya saida ya tsaya a wani blazer yasai mata
galleliyar wayarta HTC! Sai murna take kamar ta
lashe yayan nata.
Suna isa gida da gudu ta shige tana kiran
Sumy..!Sumy..!Sumy..!momy CE ta fito tana
Haba wanan kira haka kin fado ma mutane.cikin
gida babu sallama.
Saiga sumayya ta fito tana mammatse ido da
alamun itama bacci take.
Nan suka baje a palo salma ta fitoda waya.
Momy tace Sam bata yarda ba za'ayi aba salma
waya yar shekara11 nandai Habib yaita lallaba
momy harta amince Amma tace baxata dinga
tafiya dashi school ba.
Nan Sumy tafara gungunai wai itama sai ansaya
mata. Salma kam sai gwalo take mata. Habib ya
lallasheta yace qyaleta naki ma sai yafi nata
kyau sabon fitowa zan saya
miki. Nata kuwa tsohon yayi ne. Nandai tasaki
jikinta harda dariyA.
Tun daga ranar kullum sai salma takira aunty
sadiya taji kukan rufy daman yaya Habib ya sai
mata layi ya cika mata da kudi Wanda ze Dade
mata. Sannan ana bada hutu cen take zuwa taita
raino! Suyita fada da inna daman itake zaman
jego.
Haka kuma su yaya Ahmad da yaya afnan
sukeshan kira sukansu sunsan salma tayi waya.!
Ya aliyu ne kawai bata kira saitace shi yacika
fada.
Koya kira yace abata su gaisa qin karba take.
Tana zuwa school ta labartama qawarta sameera
ai yaya Habib yasai mata waya.
Itama nan tace aiko zataje gida sai babanta ya
siya mata waya.
a bangaren zaman takewar sadiya da habib
kuwa.
wani abun mamakin shine..
UTULCI KO SO!!!.? Part 37
==>Tunda aunty sadiya ta haihu yaya Habib ya
daina tattalinta idan kaga yana rawar jiki to
babynshi ne ke kuka.
Wani abun ma dan inna tana gidanne yake raga
mata. Dan har marinta yatabayi akan wai tabar
rufy tana kuka.
Tsangwama dai iri iri. Dan kyawun jegon nan ma
bata wani yi ba.
Kullum cikin zullimi take.
Ashe daman ya habib ba ita yake tattaliba
babynshi yake tattali. Tunda tazo duniya kuma
shikenan ita tazama shara.
Saidai tai kukanta tagaji tashare hawayenta.
Suna yin 40 inna ta tattara inata inata ta koma
gida.
Yanxu kam kowa yafara fahimtar sadiya ba tajin
dadin ya habib .momy ta kirasu tare tai
mishi fada sosai kasancewar tayitayi sadiya
tafada mata gaskiyar abinda ke faruwa amma
taqi.
Dan haka taita mishi nasiha akan yariqe yar
uwanshi amana idan ya cutar da ita kanshi ya
cutar domin shima nan gaba za'aima nashi.
Yadan rage mata wasu abubuwan Amman dai
babu wata soyayya da yake nuna mata.
Idan kaga yana dan lallabata to wani Abun
yakeso a wajenta.
Rufy Nada shekara1 ya habib ya hadu da wata
yarinya me suna fadeela acen qasar India suka
hadu lokacinda yaje gudanar da wasu
harkokinsa.
Ita kuma a cen take karatu.
Fadeela tunda ta qyalla ido ta ganshi taji tana
matuqar qaunarsa dan haka ta jajurce harsaida
tasamu zuciyarsa. Fadeela fara ce me
matsakaicin tsayi yar siririya tanada manyan
idanu.
Cikin dan qanqanin lokaci ta samu zuciyar yaya
Habib. Daman shi irin matar da yakeso kenan
wayayyiya yar boko wacce ta iya karairaya da
lanqwasa.
Asalinta yar Adamawa CE iyayenta Fulani ne.
Babanta me kudin gaske ne tanaji da kanta sosai
gashi an shagwabata.
Komai takeso shi iyayenta ke mata. Rayuwarta
gaba daya a qasar waje tayishi.
In taqaice muku dai ya Habib shida yajeyin sati2
saida yai 1month acen sannan da qyar tabarshi
ya dawo gida. Dan tagama yau dararshi da
kisisinarta. Dzai wuce tabashi address din
gidansu. Sukai exchange number".
inda tai mishi alqawarin itama tana nan da dawo
Nigeria nanda 2Weeks.
Ya Ahmad ya kanxo Hutu lokaci lokaci.
Ya afnan ne yaxo so daya ansha murna yaqara
zama kyakkyawan saurayi gaba daya yaga salma
ta cenja mishi dan rabonshi da ganinta ya juma.
Haka salma ta dinga murna.
Tunda yadawo yini suke a gidan inna wani irin
shaquwane yacigaba da qulluwa a tsakaninsu.
Lokacinda zai koma makaranta kuka salma taita
yi hankalinshi yatashi sosai! Haka ya xauna
yaita lallashinta. Tana kashingide a qafadarsa
murya cen qasa take fadin
=>BUTULCI KO SO!!!.? Part 38
==>Yaya yanxu tafiya zakayi kabarni! Hawaye ne
suka malalo daga kuncinta" Hankalinshi ya qara
matuqar tashi ya Sauri ya Ciro handkerchief
dinshi yafara goge mata hawaye yana Haba
salma na banason kukan nan. So kike ki
tayarmun da hankali ko. Intafi cikin bacin rai KO!
Pls kibar kukan nan kinji qanwata ta kaina"
cikin yanayin shagwaba tace. To nidai yaya
saidai katafi dani.! Yace haba salma na
makaranta fa zanje ya za'ai natafi dake kiyi
haquri kinji zamu dinga magana ta waya.
Ta daga kafada uhm..uhm..nidai saika tafi dani.!
Duk ya rasa yadda zaiyi da shawabar salma. Sai
faman rarrashinta yake yi. Sannan ya samu tai
shiru har bacci ya dauketa yasamu ya sulala ya
tafi.
Yashe gari ya wuce makaranta.
Fadeela kam tuni tadawo Nigeria ya Habib har
gidansu yaje iyayenta kam duk sunsan dashi.
Wani irin sabon wulaqanci aunty sadiya tafara
gani. Wanda ya wuce tunaninta tarasa me tai
mishi harsaida yakai abin yafi qarfinta taje takai
qararshi wajen momy.
Domin a yanxu babu ruwanshi ma da ita saidai
ya kwanta a gabanta yaita waya da fadeela cikin
dare. Basu zasu gama waya ba sai wajen 04:am
na asuba.
Su hanata bacci ga tarin takaici dayake cusa
mata saida taga sunata soyayyarsu ko shakkarta
bayayi.
Ita kuwa saidai taita kuka ga wani matsanancin
kishin mijinta dayake damunta.
Wata lokacin ma idan yaga tana kukan sai yace
ta fice tabashi guri zata takura mishi. Haka zata
dauki rufayda sukoma palo su kwanta.gashi ya
hanata ta koma kara2
'Dan kulawan dayake nuna ma rufy din ma yanxu
babu!
Wannan dalilaine yasa aunty sadiya takai
qararshi wasu abubuwanma bata fada ba.
Momy da dady suka zaunar dashi sukaimai kaca
kaca abun yayi matuqar qona masa rai wato
kamr shi har wannan tatsitsiyar yarinyarne zata
kawo kararsa gun iyayenshi. Ba qaramin target
ya shirya mata ba Amma sai yayi tunanin kada
yataso
da maganar Auren fadeela kuma ahanashi.
Dan haka yadan sassauta mata musgunawar
dayake mata amma dai bai fasa waya agabanta
ba.
Tana shirye shiryen yaye rufy ne tafara laulayi
wani cikin.
Nanfa Habib dukya rukice yafara Neman yadda
zeyi ya kawo maganar auren fadeela dan yana
gudun kar ace saita haihu shikuma ya qosa
yaganta a gidanshi.
Itadai sadiya batasan bidirin da ake yiba.tanada
fama da kanta. Tanata fama da laulayi.
Ya Habib Yaje yasamu dady yai mishi bayani
yanason yaqara Aure.
Da farko dady yaqi amincewa amma dayai tai
masa magiya ya nuna shi mata daya tai mishi
kadan. Dady yace to shikenan yanxu kabari
zamu zauna da momynka abunda muka tattauna
zakaji. Ku kasan tare dani danjin abinda suka
tattauna.
UTULCI KO SO!!!.? Part 38
==>Yaya yanxu tafiya zakayi kabarni! Hawaye ne
suka malalo daga kuncinta" Hankalinshi ya qara
matuqar tashi ya Sauri ya Ciro handkerchief
dinshi yafara goge mata hawaye yana Haba
salma na banason kukan nan. So kike ki
tayarmun da hankali ko. Intafi cikin bacin rai KO!
Pls kibar kukan nan kinji qanwata ta kaina"
cikin yanayin shagwaba tace. To nidai yaya
saidai katafi dani.! Yace haba salma na
makaranta fa zanje ya za'ai natafi dake kiyi
haquri kinji zamu dinga magana ta waya.
Ta daga kafada uhm..uhm..nidai saika tafi dani.!
Duk ya rasa yadda zaiyi da shawabar salma. Sai
faman rarrashinta yake yi. Sannan ya samu tai
shiru har bacci ya dauketa yasamu ya sulala ya
tafi.
Yashe gari ya wuce makaranta.
Fadeela kam tuni tadawo Nigeria ya Habib har
gidansu yaje iyayenta kam duk sunsan dashi.
Wani irin sabon wulaqanci aunty sadiya tafara
gani. Wanda ya wuce tunaninta tarasa me tai
mishi harsaida yakai abin yafi qarfinta taje takai
qararshi wajen momy.
Domin a yanxu babu ruwanshi ma da ita saidai
ya kwanta a gabanta yaita waya da fadeela cikin
dare. Basu zasu gama waya ba sai wajen 04:am
na asuba.
Su hanata bacci ga tarin takaici dayake cusa
mata saida taga sunata soyayyarsu ko shakkarta
bayayi.
Ita kuwa saidai taita kuka ga wani matsanancin
kishin mijinta dayake damunta.
Wata lokacin ma idan yaga tana kukan sai yace
ta fice tabashi guri zata takura mishi. Haka zata
dauki rufayda sukoma palo su kwanta.gashi ya
hanata ta koma kara2
'Dan kulawan dayake nuna ma rufy din ma yanxu
babu!
Wannan dalilaine yasa aunty sadiya takai
qararshi wasu abubuwanma bata fada ba.
Momy da dady suka zaunar dashi sukaimai kaca
kaca abun yayi matuqar qona masa rai wato
kamr shi har wannan tatsitsiyar yarinyarne zata
kawo kararsa gun iyayenshi. Ba qaramin target
ya shirya mata ba Amma sai yayi tunanin kada
yataso
da maganar Auren fadeela kuma ahanashi.
Dan haka yadan sassauta mata musgunawar
dayake mata amma dai bai fasa waya agabanta
ba.
Tana shirye shiryen yaye rufy ne tafara laulayi
wani cikin.
Nanfa Habib dukya rukice yafara Neman yadda
zeyi ya kawo maganar auren fadeela dan yana
gudun kar ace saita haihu shikuma ya qosa
yaganta a gidanshi.
Itadai sadiya batasan bidirin da ake yiba.tanada
fama da kanta. Tanata fama da laulayi.
Ya Habib Yaje yasamu dady yai mishi bayani
yanason yaqara Aure.
Da farko dady yaqi amincewa amma dayai tai
masa magiya ya nuna shi mata daya tai mishi
kadan. Dady yace to shikenan yanxu kabari
zamu zauna da momynka abunda muka tattauna
zakaji. Ku kasan tare dani danjin abinda suka
tattauna.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part. 40
==>Saiki gayamun inda Aka haramta Aure dan
matarka nada ciki! Shiru kawai tayi taci gaba da
kukanta!
Cikinta na cikin wata na5 aka daura auren
fadeela da yaya Habib. Lokacinda momy ta
fahimci aunty sadiya nada ciki taso adaga bikin
saita haihu Amma Abba yace ayi haquri kawai
abarshi. Haka akasha biki na gani na fada"many
a manyan mutane duk sun halacci bikin.
Amarya ta tare a gidanta nanfa sadiya tafara
ganin wula qanci kala kala domin ya Habib ma
babu ruwanshi da ita komai saidai amarya.
Rayuwa gaba daya taimata zafi duniya kam a
yanxu ta fahimci Habib baya kyautata ma sadiya
su dady sunyi fadar sunyi jan idon harsun gaji.
Abu sai qara cigaba yake.
Su Kansu ma kulawar da suke samu wajenshi
ada! Yanxu kafin suganshi ma aiki ne. Wata
lokacin ma sai idan sun nemeshi" baqin ciki kam
sun rasa yadda zasuyi dashi. Akwai sanda yaya
Ahmad ya sameshi yake nunamishi abinda
yakeyi baya kyautawa dan Allah ya gyara. Saida
suka kusa fada.
Domin duk Wanda yace zai zagi fadeela to zai
iya masa abinda baya zato.
A Ban garen salma da afnan kuwa,
Muna iya cewa wata alaqace me girma ta qullu
Wanda su Kansu suka Gaza fahimtarshi. Matuqar
basa tare basajin dadin
rayuwa.
A rana sai suyi waya sama da 10 sannan suraba
dare suna fira.
Sumy CE kadai tasan wannan shaquwar dayake
tsakaninsu Wata lokacin ma har fada suke cikin
dare tace ita duk sun hanata bacci.
Wata rana suna waya da daddare kamar yadda
suka saba.
Ya afnan yana kashin gide kan gadonsa yana
rungume da Teddy. Ya marairaice kamar yana
gabanta yace.


0 Comments