BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣0️⃣
Dan jim Ayya ta yi, kafin take dora kafafuwanta ta fara hawa yan matatakala kwaya uku dake sadata da balbalin bangarenta,
A nitse a dake ya kuma furta" du musulmin kirki ya dace ya amsa salama koda iya abinda zai fada kennan,
Ja Ayya ta yi ta tsaya tinawa da ta yi tare take da su Mu.azam, ko ba komai bata so yarinyar da ta dauko riko, ta dauka tamkar yarta ta cikinta ta yi wani tunani a kanta, dan haka ta ja ta tsaya ta juyo a nitse tana kallonsa ido cikin ido ta ce" amen wa alaika salam,
A hankali ya kai hannunsa jikin karfen ginnin yana kallonta, matarsa uwar dansa, auren soyaya suka yi ba na hadi ba, auren fahimtar juna mai cike da nishadi, sai dai ya yi sake, ya yarda laifinsa ne hakan ta faru, a hankali ya ce" wa ya baki izinin yin tafia har kasar agadez kauyen agadez timiya ? Kika je kika yi har kusan wata biyu? Anmi wardugu banda fitar ta cikin garin Niamey yanzu kuma har kin fara yin ta nesa haka? Ba dai a so zuciyata ta huta .....
Ya karashe yana dan sada kansa,
Mamaki take, al.ajabinsa take, uhum lalema, me yake nufi da ita? Kennan yana bibiyar rayuwarta ko me?
Fuska ta yatsina kafin take fadin" gidan nan ban yarda Wardugu ya saka ko sisinsa ba dan kar watarana ka zo da takamar danka ya gina,
Marahut ya ce" bayan Allah ya halita min ziyarta inda gonata take a duk lokacin da na yi niya?
Haushi ne ya cika Ayya, yana nufin ita, dan kuwa ai matayenku kamar gonakinku ne,
Dan juyawa ta yi ta ce" ka tarda shi inda yake ba gidana ba,
Dan daga murya Marahut ya yi , domin ta tafi ya ce" ki kiyaye fita kai sake ko dan yarmu da kika dauko kar ta koyi yawo ba izinin miji idan mun yi mata aure!
Wani irin bude kofar ta yi ta rufota da karfin gaske wanda da ba dan glas din mai nauyi kuma mai karfi bane da kasa zai zubo baki dayansa.
Murmushi ya yi, a hankali ya sauko wajen su Mu.azam dake tsaye cirko cirko,
Mu.azam ya gama yarda wajen wa Wardugu ya yi gadon abubuwa,
Gashi mahaifinsa ya kai shekaru sitin da yan kai aman yana abubuwa tamkar wani bajimin matashin sarki?
Yana karasowa ya saki fuskarsa sosai ya mikawa Mu.azam hannu,
A mutunce Mu.azam ya gaisar da shi,
Marahut ya amsa yana dubansa kafin yake kai dubansa wajen Agaishat, da yaren buzanci ya ce" ina murna da kasancewa Abanki yarinyata,
Agaishat ta ji abin sabo, abin ya zo mata a bawai, ikon Allah, mutun ya wannan, ya kirata da yarinyarsa, gashi fari karkarkar ita kuwa baka kirin aman bai nuna kyamata ba, harma ya fada mata ya yi murnar kasancewarta yarinyarsa,
Baki kawai ta saki tana kallon kama, kai har yannayin girman jikin domin Ayya bata da girman jiki irin wannan ,
Hannunsa da ya dora a kafadarta na dama ya ce" sannan ki yi ta kulawa da kanki ki yiwa Ayyarki biyaya, zan yi tafia sai na dawo ...........
Agaishat da wata kwallah ta tarun mata a ido tana kallo ya fice a gidan a kafarsa domin a waje ya bar motarsa,
Yana fita ta juyo wajen Mu.azam, da tsananin murna ta ce" ka ji me ya kira ni? *Yarinyarsa*,
Mu.azam na kallonta shima da murmuahin a fuskarsa yana kallo hawayen murna ya zubo daga idannuwanta,
Cike da zumudi ta ce" kuma kuma yace ya yi murna da kasancewata tare da su, yaya Mu.azam ni *BAK'A*,
ai bai kai ga bata amsa ba ta cikashi ta shiga taka matatakalar da gudun tsiya dan zuwa fadawa Ayya cike da murna,
Sai dai tana shiga ta tarar da Ayya zaune ta hade rai tamkar an yi mata mutuwa, yannayinta ya nuna tana cikin yannayin bacin rai mai tsanani
A hankali ta shiga dan takawa dan karasawa kusa da Ayya,
Tana zuwa ta dan duka tana kallonta murya a sanyaye ta ce" Ayya, lafia?
Ayya ta dago ta yi mata wani kallo na ta barta,
Agaishat bata fahimta ba ta ce" Ayya, *WANENE WANNAN?*
Ayya ta zuba mata wani kallon, rai a hade ta ce" ki je dakinki Agaishat!
Agaishat ta mike da sauri tana kallon Ayya kafin take juyawa da sauri ta nufi dakin nata a matukar tsorace,
Tana shiga ta karasa bakin bed ta tsaya jikinta na rawa, Ayya bata taba yi mata haka ba, dan haka hankalinta ya tashi ainun,............
Wardugu dake tsaye kan kafafuwansa tun zuwansa wajen aiki yana fama da jama.a, tun daga manyan mutane masu fada a ji da suka biyo sahun nasu, da tsagerun mutane da suka zo belin yan uwansu ko abokai, sai bayin Allah talakawa da yayansu suka kai su inda basu taba tunani ba, suma sun zo da kokon bararsu kuma cikin ikon Allah wardugu na sauraron mutane du wanda ya ga abin ba wani bane a nan take yake salamarsa da kwakwaran kashedin idan suka kuma hadewa a irin wannan waje ba zatai masa da kyau ba,
Daga karshe dai Wardugu na bincike ne cikin nutsuwa yana salamar mutanen da basa bushe bushen nan bisa kashedinsa wanda da kansa yake yiwa mutun ido da ido ba aike ba!
A hankali ya fara kawowa wajen masu zuwa dan kawai su kwale, wani saurayi aka shigo masa da shi, yana zuwa ya zube kasa ya shiga gaisar da Wardugu,
Warsugu dake kallonsa, kana ganninsa ka san ba wani dan mai shi bane, aman ya tashi ya saka kansa a rayuwar halaka idan an yi magana ace kadara, ace Allah ya dora,
A dake ya ce" tashi ka zauna saman kujera,
Da sauri saurayin ya tashi ya zauna sai sasada kai yake tamkar ya yi karya gaban sarki, tsoro yake a ransa domin a gaban idonsa akaiwa wata dukan tsiya wanda ya sa har ta sume dan kirikiri ta yi ikirarin ita ko wacece ta tofar da yawu ta dura ashar ta ci alwashin gyatiminta zai zo ya fitar da ita har sai uban gidansu Wardugu ya bata hakuri hakan ya sa su kuwa suka nuna mata da gidan maza ta shigo ba gidan yara ba, suka murza kwonji a jikinta har ta some, labarin da ya kaiwa Wardugu da ya fito a gaban mutanen nan na cel ya zuba mata ruwa da kansa wanda hakan ya farfado da ita, sai dai tana tashi ya wanka mata wani marin da ya mayar da ita duniyar suma sannan ya nunata da yatsa ya ce" ban so tonawa kowa asiri ba shi yasa na saka aka shigarmin da iyayenku daga wancen dakin wanda ba wanda zai gane in an shigo da kai wanene mahaifinka kuma me ka aikata ba, sai gashi kin tonawa mahaifinki asiri a matsayinsa na dan siyasa kin kama sunansa har kin nuna mana halin kodin! Dole mu kai kararki wajen alkali kin zagi soji!
Haka aka kwasheta aka jefata cikin cel din ya koma ya ci gaba da aikinsa dan haka ne ya sa wannan saurayin kamar ya kwonta dan kadabi,
Wardugu ya ce" yaya sunanka?
Saurayin ya kalo shi kadan ya sada kai ya ce" sunana Murtala Tasiu,
Wardugu ya gyada kai ya ce" tun yaushe kake zuwa wardugu place? Kai da wa kuke zuwa? A nawa kuke biyan kudin shiga? Du sati sati kuke zuwa? Da yan mata kuke zuwa?
Murtala ya ce" ba.a fi shekara biyu ba,,
Ni da dan gidan Elhaji Dahiru muke zuwa,
Aa ba kowani sati ba dan kudin shigan da muke biya shima ba kulun yake da shi ba jika goma goma, sannan in mun shiga ga kudin kashewa , aa iya mu muke zuwa a can muke haduwa da yan mata kowani sati akoy a ciki,
Wardugu ya tsare shi da ido ya ce " tun daga bakin lokacin ka fara busa kodin?
Murtala ya shiga raraba ido, ya daga hannu zai fara rantse rantse Wardugu ya ce" murtala, ka fada mini gaskiya mai yiwuwa ka samu sasauci!
Murtala ya ce" oga, ka rufa mani asiri dan girman Allah, mahaifina gajiyaye ne, sai na bi abokin nan nawa yake bani wani dan abin na je na ciyar da mahifina da kanwata, kanwata bata gani, mahaifina kuwa ya tsufa, ba a son raina nake saka kafata wajen nan ba,
Wardugu ya ce" ban tambayeka labarinka ba Murtala, ban yi niyar wulakanta ba ina rokonka kar ka wulakantani, kar ka kawo mani shirme a nan , da farko dai du idan ka ga soji rikeken dan tasha ne domin tashanci koya mana ake mu shanye sai dai muna aiki da shi ne kan tsari, na jima a aikina hakan ya saka ana yi min karya nake ganewa, ka bani amsata ko mu baje basirar rainin hankalin ni da kai!.............
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣1️⃣
Da sauri Murtala ya ce" Eh eh , tun daga lokacin da muka je abokina ya siya ya saka na taba tun daga lokacin nima nake sha ,
Wardugu ya shiga gyada kai ya ce" kana iya fita,
Dan mikewa ya yi, sai ya mike sai ya dan duduka sai da wani soja ya shigo ya finciko shi ya mayar da shi cel,
Da mijin Auntyn walyn aka shigo,
Mutun har mutun, sai sasada kai yake na kunya,
Warsugu ya tsare da da ido, wai tun a nan duniya ka kasa hada ido da mutanen da basu baka ko cin wuni daya ba, ya zaka kare da wanda ya haliceka ya baka dukiya dan gannin ya zaka tafiyar da ita, ya ara mata lafia, gani da ji, ya baka ikon motsi, ya baka damar magana, ya kaika kasar da ba yake yaken yu da kulun wa.inda zasu iya tayar maka da hankali , ya baka isashen lokaci dan kawai ka bauta masa ka yi masa biyaya, sai gaka tsofai tsofai a gidan badaka tare da yar shilar yarinya ta tube kusan zindir tana maka rawa tana ciyar da kai gasashen kifi, shine zakana wani sada kai a gabana kai ga cikenken dan iska! Du wardugu ke jifansa da wani matsiyacin kallo sannan yana ayyana du haka a ransa,
Wardugu ya ce" ya sunanka malan?
Mijin aunty da mamaki ya dago yana kallon wardugu ya ce" haba haba wardugu, ai ko me ake a san na gida, a fitar da na gida, ka yi hakuri kure na aikata ba zan kuma ba , ka salame ni na koma ba tare da wani bama ya ji abin kunya ne ace ka rufe mijin kanwar babar matarka!
Baki wardugu ya dan daga na mamaki, ka ji wani dogon bayani wai mijin kanwar babar matata,
Kai ya girgiza a ransa ya yi murmushi, a fili ya kuma furta" ya sunanka malan!
Yana mai dagowa da yanayin dakewa,
Mijin auntyn walyn nan ya fara zufa, yana gagawar magana ya ce" tototo, sunana Lawali , Elhaji lawali,
Wardugu ya ce" me ya kai ka Wardugu place? Kai da wa ka je? Me ka je yi? Tun yaushe ka fara zuwa? Me ka lura ana yi a wannan waje?
Lawali ya ce" ni kam wannan waje na je ne bisa tsautsayi da rabon a yi, domin dai yarinyar nan na so na aura sai take shaida min na kaita mu sha iska, to da muka je shikenan sai muka mayar da wajen wajen zuwanmu lokaci zuwa lokaci yanzun dai an kai shekara uku,
Sannan a wannan wajen gaskiya na lura ana abubuwan da bai dace irin ahaye shaye, wannan da ka ganni tana yi wai karamin ne, eh wanda muke yi shine karamin ba Allah ja da kwana....
Ya karashe yana jinjina
Wardugu ya jinjina kai, ya ce" lawali kada daga Kokin ne?
Da sauri ya dago yana duban wardugu, ya ce" bilahilazi ban taba ba, ai ni ko warinta na ji juwa ke kayar da ni, ka rufa mani asiri rashin jina bai kai can ba,
Wardugu ya dago yana dubansa, wai rashin jinsa, kai ya girgiza da hannu ya yi masa nuni da ya fita,
Yana kokarin kara magiya Marahut ya shigo inda sojan nan ya biyo bayansa yana dan kame kame ya rasa me zai yi, su dai ba wanda bai san oga Marahut mahaifin uban gidansu ba, shi ya isa ya masa iyaka ne? Tun daga babar kofa ya samu shigowa ya ratso du zone na control ba.a hana shi ba sai shi tal dake tsaye dan kula da bude kofa da kuma rufewa da kyau ne zai hana shi shigowa?
Kallon Lawali Marahut ya yi kafin yake girgiza kai yana murmushi daga cikin rawaninsa,,
Kai sade Lawali ya fice domin ya ji kunyarsa ainun
Marahut ya bi tsararen tankamemen office dan nasa, bMarahut ya ce" ya aka yi ka canza kanshin turarenmu ne Wardugu? Kuma ya aka yi ba hotona a office dinka bayan kai din dan halal ne koda shege ai ado yake da ubansa bale dan halal ,
Wardugu dake ta cika takardu yana dan dana laptop bai ce da shi ci kanka ba,
Marahut ya ce" Warsugu Abanka ne fa ni ? In ba ruwanka da mutane su ga kana min haka ba ruwanka da Allah ne??
Wardugu ya ajiye biron dake hannunsa ya dan shafa kansa ya dago da kallonsa wajen mahaifinsa wanda a kamaninsu haske ne kadan ya dan fi shi domin farin wardugu ba irin cancan din nan bane,
Warsugu ya ce" Aban Wardugu ra.ayi ne ya sa na daina anfani da turaren da ka sanni da shi, sannan ni ba mace bane da zan kawo hotonka office na buga, kuma shegema mutun ne!
Murmushi marahut ya yi ya karasa wajen kujera ya zauna ya ce" to ka fido mani matata mu tafi gida Wardugu,
Wardugu ya yi murmushi a bayane shima ya ce" ba zan so shakar iskar da kuke shaka ba ko na second daya, sai dai ya zama dole ne, matarka mai laifi ce
Meye laifinta wardugu? Me ta yi da tsanani haka? Ka san yara da kin ji suke,aman ai koma me ta yi ina gannin sai mu kashe mu birne abinmu a tsakaninmu ko wardugu? Marahut ya fada yana dubansa
Wardugu ya ce" zan so haka, sai dai ka ga rashin jin nata ne ya yi kamari, tana shigo da kwaya ne tana siyarwa wannan ba boyayiyar shaida bace, abinda nake bincike kawai na samu hanyar da take shigo da ita ko wanda ke bata sai na mika su kotu koda kuwa *kai ne*, sai dai ban san ba yin hakan ko Allah zai kama ni da shi?
Da sauri marahut ya ce" Quoi? (What?), wani irin kwaya? A Wardugu place din? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, wardugu ka kara mani haske a lamarin nan
Wardugu da ya ji ya dan samu sasauci, domin a sama yake, jininsa a saman akaifa, tsoro yake kar a je rinjayar nata ya kai ta saka Marahut a wannan harka? Aman yanzu ko ba komai ya ji dan sanyi a ransa dan kuwa har gobe da sunnan mahaifinsa yake anfani,
Wardugu ka fada mani mana, Marahut ya fada yana dubansa da yannayin serius
Wardugu ya yi umarnin a kawo AISATA,
Shigo da ita aka yi, dare daya tak du ta fara fita hayacinta abinka da wada ya saba da hutu,
Tana gannin Marahut ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin da sauri ta nufi wajensa ta saki kukan kirsa,
Tana kukan ta ce" ka ga abinda Wardugu ya yi mini? Wannan wani irin tsana da cin mutunci ne? A gaban jama.a ya saka mini anker tamkar wada na yi sata, ai a tunanina ya dace komai ya fice tsakaninmu ko me na yi sai ya hukunta ni a gida ba wai a gaban duban mutanen da zasu yi min dariya ba,
Hannunsa ya saka ya dagota daga jikinsa yana dubanta, kadara, Aisata kadara ce mai wutsiya, a dalilin Aisata ya rabu da farin cikinsa da girmansa a idannuwan iyalinsa, maciya ce Aisata, Aisata zinari ce,
A nitse ya ce" me da me kuke aikatawa a Wardugu place?
Aisata ta yi tsam kafin ta shiga cicira ido ta kali dan ta kali uban, cikin yannayin barikinta ta ce" me muke yi kuwa banda neman kudi? A wardugu place ba abinda muke yi,
Wardugu dake rubutu a takarda ya dan yi tsam ya dago ya dube su ya maida kansa ya ci gaba da aiki,
Bai jima ba ya daga wayar office din ya danna kira,
Cikin girmamawa ya gaisar da jujun kafin yake fadin" mai girma na gama nawa binciken, yanzu ana kawo maka takardu ka duba, daga nan na mika maka su kawai ,
Amsa shi ya yi kafin yake kashewa,
Marahut da ya gama fahimtar wayar da Wardugu ya yi shima yana dubansa, cikin yannayin nutsuwarsa dai ya ce" har yanzu baka daina jin haushina kan Aisata ba?
Wardugu ya juyo da sauri, ido ya zazaro baki daya kafin yake mikewa ya tofar da yawu a nan cikin office din ya ce" kan wannan? Ya fada yana nuna aisata,
Ya girgiza kai ya ce" ai koda me daraja ce bata kai na yi anfani da damata dan wulakanta ku ba, ka gane laifi ta yi, idanma baka yarda ba ai kai din oga ne kawai ka je wajen wa.inda zan mikawa takarda idan sun baka matarka ruwansu ni dai ai na tono barnar ko? Ka fi kowa sannin waye wardugu domin kaine mutun na farko da ka rikeni a duniya bayan likitar da ta fitar da ni daga cikin mahaifiyata!
Yana gama fada ya ja kys din motarsa ya dauki gilashinsa ya fice a office din yana mai jin haushin yanda mutane ke magiya kan a bari a ci gaba da yada barna!
Jikin Ayya ne ya yi sanyi bayan korar Agaishat da ta yi, a hankali ta mike ta nufi dakinta tana mai jin wani iri me ya yi zafi harda laifin wani zai shafi wani?
Tana zuwa ta shiga da salama,
Agaishat dake zaune kasa ta dora kanta a gefen gado tana jan carbi da hannunta ta dago da sauri tana kokarin mikewa tana duban Ayya,
Karasawa Ayya ta yi ta riketa ta zaunar da ita gefen gado,
A nitse ta ce" ki yi hakuri yar gidan Ayya, ba zan kuma yi maki irin haka ba ,
Agaishat ta sauke ajiyar zuciya tana dubanta,
Ayya ta ce" bara na baki labarin mu..... na fada maki wacece *AYYA?*, na fada maki waye *MARAHUT a rayiwar Ayya?*, na fada maki wanene *WARDUGU* sannan wani irin girman daraja yake da shi a rayuwar Marahut da Ayya? Yarinta bara na baki labarin da ba kowa ya sani ba................
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣2️⃣
labarin Wardugu da tushensa a gajarce
.
........ ..................
Sunana *Zanaba SHAU*, sunnan Mahaifin Wardugu *MARAHUT ELUM*, ni marainiya ce gaba da baya, na taso a hannun kakata ta wajen uwa da ta yi min saura,
Marahut dan gata ne gaba da baya, ya kasance a lokacin anguwarmu daya domin gida uku kawai ke tsakaninmu,
Tun wayona bai gama fahimtar Marahut na sona ba har na gane domin kiri kiri idan na yarda wani lokacin na yi dan shirin atampa na yafa mayafi na fito zai rufe ido ya kora ni yana masifa,
A anguwa ana girmama kakata domin mace ce da ta san girmanta, ba abinda ya shafeta da abin hannunka, ga mutunci ga zumunci,...du juma.a zaki ga an kawowa kakata abinci daga gidajen anguwar nan ciki kuwa harda gidan su Marahut inda mahaifiyarsa shuwa arab ke turowa kakata da gurasa ta kasa, irin wace ake yi a kasa ta ainahin da miya mai dadi harma ki ga an zuba tawa miyar mai magi domin a lokacin an hana kaka shan magi.
Sosai muke soyaya da Marahut, duk da wani lokacin nakan zauna na yi shiru ina tunanin Marahut na so na kamar yanda nake son sa kuwa?
Hakan sai ya tayar min da hankali sosai domin Marahut dai jarumin namiji ne mai cike da abubuwan da mata ke marari har suna kai wawa, harma wani lokaci na kwatanta masa....
Tsareni ya yi da ido kawai, zuwa wani dan lokacin ya mike ya fice abinsa hakan ya haifar min da faduear gaban ko ya yi fushi ya bar ni ne?
Kwana biyu tsakani na dawo daga makarantar dare islamiya da nake zuwa a kusa da mu na tarar da kakata zaune tana jan carbinta da rufarta bata kwonta ba, ba kamar sauran lokutan ba,
Da sasarfa na karasa wajenta dan gannin abinda ke damunta sai dai ina zuwa ta rike hannayena tana kallona ido cikin ido ta ce" Zannaba, kina ta adu.ar neman Allah ya baki miji na garin nan kuwa?
Na amsata ina dubanta da wani irin yannayi ta ci gaba" an zo neman auren ki daga gidan Elum, Zannaba kin ji zuciyarki ta aminta da Marahut?
Wara irin kunya ce ta diro mani, domin fa Agaishat yata tubawa na da muguwar kunya, batuben mutun na da kunya harda ta mamaki, hakan ya saka na sada kaina kasa harma jikina ya fara rawa,
Kakata ta ce" kul, na hane ki da ki yi haka da ni, ke kawai gare ni kema ni kawai na rage maki, Allah shi ne gatanmu, zan so ace na bar ki hannu mai kyau, dan haka maza bani hankalin ki mu gama magana,
In takaice maki a wannan rana bamu kwonta ba du sai da muka dauki niyar istihara wace cikin kwana uku hankalin mu ya gama kwonciya har ma muka aminta da auren nan,
Marahut ya yi min gata , agaishat ya kai kudin aurena ya yi min kayan da aka jima ana labarinsa, aka daura aurena irin na kowace yar gata inda kakata ta bada mamaki ashe tana ajiye da sarkokin aurensu ita da mahaifiyata, ta kai aka buge akai min tafkekiyar sarka da abubuwan hannu na zinari irin na kowace batuba yar gata, sannan ta fitar da kadarorin mahaifanna harma da nata gaba daya ta raba aka yi min kayan daki sauran ta damkawa mai anguwar anguwarmu amana,
Wsshe garin auren mu Marahut ya dankara min wata makekiyar sarka ta zinari tatare da kwacakwablarta bisa al.adun tubawa wanda hausa ce cikin hausa, ba.a jima ba muka daga dan komawa bakin aikinsa inda aka maida shi domin baban likita ne kuma yana harkar kasuwanci da kiwo.....
Mun kasance cikin farin ciki, mutunta juna, da kaunar juna, muna tafiar da rayuwar aurenmu bisa tsarin islama muna kiyaye du wani abinda zai firgita mu sai dadaykun da baza.a rasa ba na yau da kulun!
A haka na samu cikin wardugu,
Mu kai rainon abinmu har na tashi haihuwa inda Allah ya taimake ni na haihu a hannun mijina a asibitin da yake aiki da taimakawar nurse..
.
Mun koma gida dan zanen sunna, nan Marahut ya gabatar da sunnan *WARDUGU* a matsayin sunnan da ya zaba,
Kowa ya jinjina lamarin sai dai ikonsa ne, dansa ne, aman sunnan Wardugu linzami ne ga mutun mai zuciya, mai fada, mai balaki, kai ba.a zama lafia da mai sunna wardugu, Wardugu! HUM, ko canfawa ne mun yi kuma yana bin mu, kwarai zahiri ne Wardugu duniya ne guda, ba sai an koya masa ba da abinsa aka haife shi.......
Ina wanka a gida wajen kakata, tana kula da lamarina sosai da sosai, wata rana muka wayi gari da kyautar Allah, inda mutuwa ta sake zagayowa ta tsame min wace ta min saura a tarihin iyayena,
Ayya ta yi shiru ta share kwalar da ta zubo mata,
Agaishat da ta yi lamo ta dora kanta a hannun Ayya, Ayya ta ci gaba" Agaishat na ji mutuwar baiwar Allahn nan, domin ni ita ce duniyata, ko me na kwaso ita nake fadawa a nitse ta warware min, ta rasu ta bar ni da jaririn da a lokacin bana iya daukansa da garaje dan girmansa masha Allah, ta bar ni da dan labubun yaron da yakan calara kuka wai shima nice mahaifiyarsa, na ga rana na godewa Allah,
Agaishat ta kara jimke hannun Ayya itama tana jin yanda hawayen ya zubo mata, Ayya baiwar Allah, bata da kowa gaba da baya, ashe du yanda mutun ya kai ga malakar arziki bashi da cikeken farin ciki na yanayin rayuwar yau da kulun?
Ayya ta ce" na dawo ga marahut, bani da kowa bani da komai sai Shi a nan cikin duniya,
Bayan an yi bakwai muka juya garinmu inda na dauki girma na ajiyewa kaina na karfi da yaji na ci gaba da karatun likitana da nake yi a Ensp,
Can tsakiyar dare nakan dadaba Marahut, idan ya farka sai nace" Marahut, kar ka wulakanta ni a duniya, kai ne duniyata, kai ne farin cikina,
Yakan riko ni jikinsa ya ce" ban aure ki ba sai da na gane ke ce lumfashina, a duniya baki daya me ya kai lumfashin mutun tsada? Ba zan yi garajen gannin hawayenki ba sai na kadara!
Magangannunsa da alkawarurukansa suka saka na samu nutsuwar zuciyata harma na warware na ci gaba da shagulgulana na yau da kulun tare da yarona,
Tun Wardugu na da wata bakwai ya mike, yana tafiya da kafafuwansa digir digir tamkar dan gwari,
Du inda na yarda na je da shi idan ya damki yaro ko matashi sai an kwace da kyar,
Ya kasance ba.a gardama da shi da ya warware, yana fama da ciwon athsm wace in dai na yarda ransa ya baci toh fa a kadan mu yi kwana uku a asibiti domin athsmar nan zata tashi ne ya kasance daga ta kwonta sai ta kuma tashi domin ba zai kwontar da hankalin nasa ba,
Wardugu zuciyar mahaifinsa ne, domin daga shi ko batan wata ban kuma yi ba, muna bibjyar komai nasa tamkar ranmu, kai har bama kawaici a nuna soyayarsa,
A haka Allah ya hada mu da baba tsofo, wanda kawai salama ya yi yace yana bayar da magungunnan hausa ne,
Nan muka zanta a bayan idon mahaifin Wardugu domin baya son lamarin hausan nan wai tsoro yake ya taba masa reins,
Cikin ikon Allah ya ki karbar kudina, muka ajiye magana idan Wardugu ya samu lafia zan yi masa kyauta,
Yakan zo lokaci zuwa lokaci ya kawo mana magannin da cikin ikon Allah muke bashi da nonon rakumi sabon tatsa da sasafe, tun ina boyewa har na bayannawa Marahut shima ya kama mani domin sauki kamar da wasa Wardugu na samu a hankali a hankali har ya daina lumfashi da bakinsa ya dawo yi da hancinsa,
Agaishat na kasance mutun mai shegen son mutane, ko dan na sakawa kaina bani da kowan nan a duniya sai Allah sai mijina? Ya kasance son yaya da yawan kula zumunci da jama.a,
A haka na hadu da babar aminiyata matar sarkin agadez, na hadu da kawata ta damagaran hajia Falmata, da sauran su,
Wardugu rashin lafiarsa kawai ya warke aman halaya na nan, a haka aka tsahe mu aka maido mu garin nan inda kwata kwata baba tsoho ya bace min na neme shi na rasa har muka taso aman abin na tsaye a raina sannan ina yawan tambaya,
Kwonci tashi wardugu ya tashi da niyar shi fa soja, soja, hakan ya sa mahaifinsa ya sama mana waje a Babar makarantar sojojin niger wace ke a kwalo, wace tun yaro na karami ake kai shi shikennan shi da iyayensa sai jifa jifa,
Karatu yake, sannan kwazo yake da shi ko a filin training,
Hakan ya sa babansu yake kaunarsa harma yake zumunci da mahaifinsa
Wardugu na da shekara ashirin da biyu ya fito gagarumin comandan, jikaken saurayi, kaukauran namiji, zakin zamani, yaro da kudi kamar yanda ake kirarinsa.......


0 Comments