BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣3️⃣
To tunda Wardugu ya dawo sai kuwa yan mata suka ce bismillah, ba kalar wace bata zuwa , kin dai ga yanda yake uwa kurman nan? Toh haka zasu zo su karaci haukansu sai dai su yi su gama su tafi,
Ban san ya aka yi, ta ina aka yi suke kawance da wannan mai sunna Alhinayettt wace ni hakanan nake gannin karya ne ba wani kawance may yiwuwa soyaya suke ba halin aurenta domin aurensa bai wani jima ba,
Ana haka ya amincewa yarinya daya soyayarsa, yarinyar da ta yi kundubala da sauran yan matan,
Soyaya suke ta hauka irin soyayar yayan zamani, ni ba zan shaidi yarona ba ba kuma zan ce yana aikata masha.a ba, aman a lokacin da yake kwana a gidan nan har kwana ta sha yi a wajensa dan kuwa sai da na rufe idannuwana na ci masa mutunci sannan na daina kamata a dakinsa,
Waye shi da zai rantse min ba abinda ya shiga tsakaninsu? Namiji ne, ita kuwa mace, sun kadaice a wajen da ba kowa sai su sai Allah, ai hankalina ba zai dauka ba!
Ire iren abubuwan da sukai ta faruwa kennan da yarinyar da ta gama kwana gidan mu, mamaki nake da tsoro, Wardugu ina ya zubar da kunya irin ta batube? Gaba daya wannan karatu da ya yi ya saka du ya zama wani kiritace wani tsayaye! Sam ya zubar da al.adu da dabi.un tubawa idan na yi magana sai yace ai ba wani adini bane, shi gaskiya ya girma a birni ba zai ci gaba da rayuwa irin na daji ba, ! ALLAH ya shirya,
Ana haka ya tafi karo karatu inda suka hadu da mu.azam suka kula zumunci mai ma.ana, a can ya hadu da matar da yake aure yanzu wace a lokacin ba irin azabar da bata sha ba domin shi soyayarsa tana kan *AISATA* ,
Aisata? Agaishat ta tambayi Ayya,
Ayya ta ce" kwarai Aisata dai wace ubansa ya aura,
Agaishat ta ce" aa, Ayya na shiga rudani,
Ayya ta ce" bara na warware maki,....
Haka kawai mun ci gaba da fahimtar juna alhamdulilah har wardugu ya dawo daga tafia,
Nan ya zo da maganar a tura wajen yarinya a tambayo aurenta,
Tashin farko ya dira cewar ba da yawuna ba, kuma in har ni na haife shi ba za.a yi haka da ni ba, domin yarinya bata da da.a , zan so matar da zai aura ta fari ta kasance mutuniyar kirki ko dan fadar adini ku zabawa yayanku iyaye na gari,
Nan fa aka shiga tashin hankali, yarinya ta zo har gida ta tsire ni, nan ta yi ikirarin cewa" AYYA kike ko wa? Kin dai ganni, kin ga yanda nake, nice farar mace , kwakwa! Dole na shigo gidanki ko a sarakuwarki ko a kishiyar ki!
Abin ya bani mamaki, zuciya ta kama ni na tunkareta kafin take ankara na damketa, ina faman ihun sai na nuna mata ruwa ba sa.an kwondo bane malalaciyar banza da wofi sai ga Marahut ya shigo da sauri
Kwaceta ya yi daga hannuna kafin yake fadin" ke Zannaba, baki da hankali ne? Kike ikirarin yarinya bata da tarbiya ke kina iya rantsewa waye malamin waye dalibin tsakaninta da dan naki? Ki shiga tatayinki ki daina abu tamkar wata yarinya karama!
Agaishat , a wannan rana, a gaban wannan yarinya Marahut ya wulakanta ni, ya yi min tas abinda bai taba shiga tsakaninmu ba,
Ke dai kwana biyu tamkar kura ta lafa, domin Wardugu da ya ga na nace sai kawai ya basar ya yi biris ya shiga wata sabgar gaban nasa inda ya fara kula Walyn,
Ba.a wani jima sosai ba, domin ba .a yi wata hudu tsakani ba Marahut ya zo da maganar zai yi aure,
Agaishat ban wani nuna halinmu na matan tubawa ba, na ja ajina na yi masa fatan alkhairi, na shiga rokon Allah da ya rufa min asiri kar a je dan haihuwana ya tsaya ne wani abin zai tunkaro ni,
Sannu sannu sai abubuwa ya fara bilo mani, halayen Marahut suka shiga canzawa,
Ya fara cika dare sosai a waje kafin ya shigo, ya dawo ya fara kin cin abincina sai yace baya jin yinwa tamkar wani inji,
A hankali ya kaurace min,
Na sha zuwa na duka nace da shi" menene damuwar? Wani abin na yi ne? Dan Allah ka yi hakuri , har ka manta alkawarin fa ka yi min? Marahut kace nice lumfashin ka, ka yi hakuri ka dawo min kamar da, ni ban wani hanaka aure ba, aman kar ka tayar min da hankali,
Marahut sai kawai ya yi min murmushi ya mike ya fice,
Du abin nan Wardugu bai san ubansa zai kara aure ba sai wani lokaci ya ji a gari, a lokacin ya garzayo gida da sanyin safiya ya tambayi uban, ashe auren ma a ranar sauran kwana biyu ni banma sani ba,
A wannan ranar na ga tashin hankali, na ga rikici, domin Wardugu idannuwansa sun rufe hakama na ubansa, ke sai da na fita a guje na kira direbobi da masu gadi da yaren gida du suka shigo suka yi kokarin shiga tsakannin uban da dan dan kuwa Wardugu ya rike wuka hannunsa yana ta balaki!
Agaishat, wannan bai isa ba sai da aka shigo da amarya Aisata, aisata yar buzaye, aisata yarinya kyakyawa,
A ranar wardugu ya yi dan karamin hauka, ya ja iska ya zo kusan babansa ya ce" aban Wardugu ka sake ta, ka rufa mani asiri ka saketa , kar ka yarda wani abin ya shiga tsakaninka da ita, Aba, wannan bata da tarbiya, bata da haramun! Abanna ya zaka kawo macen da ta gama talatarmin da kanta a irin yannayin da ta fado duniya ni danka a matsayin matarka? Haba Abana, me mukai maka da zafi haka?
Marahut ya dube shi ya ce" ita ba mutun bace? Kun haihu da ita ne? Na yi niya ina sonta na aureta da kudinka ne? Ka bini a sannu Wardugu, ni na haifeka kar uwarka ta zigaka ka kauce hanya!
A lokacin ni tuni na fara gannin jiri, ni Marahut? Na sha dukan kirji nace ni mijina dan goyo ne, ba zai wulakanta ni ba, sai gashi haka ta faru, ni ba aurensa ya dame ni ba, tau da gobe ai sai Allah Allah wacece ni da zan ce ba za.ai min kishiya ba? Damuwana irin auren da ya yi, ya yi shi dan ya nuna min iyakata? Dan ya wulakanta ni? Ko wani abin ke tsakaninsa da yaronsa mai zafi haka?
A lokacin Wardugu ya fara wani irin numfashi, idannuwansa suka shiga canza launi zuwa ja, suka cicika da kwallah, ina gannin hakan na tisa shi gaba da kyar na samu muka shiga motarsa na ja muka nufi gidansa,
Muna zuwa muka tarar da Wakyn ta zo nemansa, a nan ya sauke haushin kanta domin sai da ya bala mata hannu du ya kusan canza mata halita baiwar Allah da kyar aka kwaceta,
Kin ji marabina da gidan Marahut domin akai ruwa aka yi iska Wardugu ya hau, ya gindaya rantse rantse, ya juye, nima fushi, mamaki, tsoron lamarin maza ya saka na yi watsi da shi na rungumi yarona wanda na san a duniyarnan ni ce duniyarsa ,.....
Ayya ta karasa tana dan shafa kan Agaishat,
Agaishat ta dago fuska shabe shabe da hawaye,, tana duban Ayya , ta sani bata da damar da zata iya tofa wani abin a wannan lamari domij ta yi imanin ba komai Ayya ta fada mata ba, tabas ta boye wani abin ko dan karancin shekarunta,
Sai dai wannan lamari ya tuna mata mahaifiyarta, Anna baiwar Allah, yoh ita haka rayuwarta ta kare fa, kuma bata da wani mai dauketa ya matsata daga wajen da ake cuzguna mata, ita bata san bama marainiya ce ko yar dangi, bata san daga ina ta fito ba, ba abinda ta sani,
A hankali ta mayar da kanta saman cinyar Ayya , daidai lokacin da Wardugu ya shigo dakin da salama,
Daga inda take kwoncen nan take kare masa kallo, tabas wardugu ko bashi da ko sisi sai mace ta yi haukansa, ko bashi da hali zai mitsa zuciyar mata, dan farin batube mai zamani,
Idannuwanta ta lumshe a hankali wani hawayen ya kuma zubowa daga gurbin su ta mike a hankali bayan ta share hawayen ta kai dubanta wajensa , kanshin turarensa ya cika mata hanci,
A hankali ta ce" ina yini,
Gaisuwar da tunda suka daukota daga timiya shi dai bai taba jin ra yi masa ita ba, tsumamun idannuwansa ya zuba mata ba tare da ya amsata ba, yana kallonta har ta fice a dakin dan basu waje su tatauna ta nufi wajen Mu.azam dan gannin ko ya ci abinci?
Ayya ce ta lakato shi tana yi masa murmushi tana saisaita kanta ta ce" dan gidan Ayya, sannu da dawowa,
Wardugu ya juyo da sauri yana dubanta, ya yi murmushi ya ce" Ayyana, ina yini?
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣4️⃣
Amsawa ta yi tana dubansa da madaukakiyar kulawa kafin take mikewa ta kama hannunsa,
Shima biye yake da ita suka fito daga dakin Agaishat suka nufi dakinta,
Walyn ce zaune a saloon mai suna Tawaye saloon, fitacen saloon ne na manya wanda sai ka isa kake saka kafarka,
Akifunta ake gyara mata bayan an yanyanke su an wanke su sosai aka dauko na kanti zako zako din nan aka shiga dora mata,
Kawarta dake gefenta tana karanta magazine, itama ana gyara atach din da za.a yanyara mata kitso ........
Wata mata da ta tsare Walyn da kallo tunda ta shigo ce ta yatsina fuska, a ranta ta yi murmushi tana ayyana ba laifi , matar tasa bata da laifi,
Kadan ta dan muzguta ta dubi cousint dinta dan daudu wanda suka zo gyaran gashin tare da shi ta ce" ina son aikin General a rayuwana, ina son yanda yake cin uwar kananun yan iska!
Kallota ya , ya wani yi far da idannuwansa, ya yatsina fuska tamkar mace ya ce" ke kawa, ya iya tata rashin mutunci ne fa, mutumen nan kin san da matar tsohonsa ce ya rufe? Uhum ke ni ko a lahira bama fatan mu hade da General Wardugu domin bashi da mutunci, ya iya aiki da doka, ke matarsa fa ta yarda ta kai dare a waje sai ta kwana a cel!
Daman inda take so a tabo mata kennan dan haka ta maida hankalinta sosai ta kali dan daudun nan ta ce" kawaliya matar naci ta taba daraja ne?
Walyn dake kalonsu tana kada kafarta, ta kai dubanta wajen mai saloon din, ta maida wajen kawarta da ta yi kasake itama tana jiran gannin me zata yi? sai sauran matan dake wajen da yan tsirakun ya daudun dake wajen suna suba nasu sha.anin.....
Walyn ta saki murmushi mai ciwo, ta daga idannuwanta cike da isa da takama ta ce" Wardugu kennan, mijin mace daya, jarimina mai ban tsoro, Warduguna zazafa ne, kawata kin san Wardugu baya bin kadangarun bariki? Ke na yi imanin da Wardugu na bin mata zai je ya zabo zuga zuga ne, wa.inda idan ya zaga zai dire chek ba wai ya dane karamar yar bariki ya kasa iyanta harda kason shekara sanadiyar rabuwa da mace ba!
Dan daudun nan ne ya sheke da dariya yana duban matar da suka zo tare, wace ta ji abin tamkar saukar guduma domin mijinta ne ya jewa wata yar bariki ya ki biya sannan ya yi mata duka hakan ya sa harda su kaso, wani tukukin bakin ciki ne ya taso mata, bata tsamaci jin haka ba , abin ya dake ta,
Kallonta ta yi da yannayin bacin rai ta ce" ke Walyn kike ko wa? Kin san ko wacece ni?
Walyn ta fizge hannunta daga hannun mai saka mata farcen ta ce" ke ce katuwar yar barki marar aji! Sai me kuma?
Mikewa ta yi itama ta ce" ke din ba yar barikin bace? Ke naki a boye kike yi ko ji kike ba.a sani ba? Meye bambancinki da yar bariki? Ke kawai bakya yi dan kudi ne aman menene bakya yin? Ko dan kina rufe takunki ne baki san wa.inda kuke labewar da falasawa ba? Ki jika ki ajiye Wardugu General ya fi karfin zama da mace daya wace na sani ne bakima goge a kai shi wata duniyar ba! Zaki ga aikin gogagiyar yar bariki domin Wardugu katuwar kadara ne wanda malakarsa sai tsayaye ba isa ce zata kai ki ba mu je zuwa!......
Walyn ta yi murmushin rainin hankali kafin take bufe jakarta,
Yan jika goma goma ta fitar dami guda ta bale yar takardar dake zagaye da su wace itama sai kyali take, ta dauki bakin gilas dinta ta jefa katuwar wayarta a jaka ta juyo sosai wajen matar da sauran mutanen saloon din ta daga kudin nan ta sake su a iska wanda hakan ya saka du suka shiga wawusoso harda mai saloon din da yarenta kiwa na nema har wasu suka shiga dambacewa , aman banda wace ake kira da kankana!
Walyn ta bi kawayen da kankana ta zo da su da ido ta ga suma sai wawa suke harda yan daudun,
Yatsina fuskarta ta yi ta ce" abokin mai kanwa ba ya rasa burbudi, Wardugu ya daure min a niger tunda ya sakar min yayan banki, na kwana lafia koda Wardugu ya shiga tsakiyar yan bariki ba zata motsa ba domin kyankyaminku yake!
Ta kara taku har gabanta ta zaro idannuwanta ta ce" ki sauke girman kai ki duka ki kwashi kudi.....su kike kwadayi!
Iska ta ja ta kaiwa Walyn duka warda itama ta damketa suka shiga dukan junnansu,
Sai da suka lilisa junnan su sannan mutanen wajen suka shiga tsakanin su kowace na haki,
Walyn ce ta warce jakarta ta yi gaba inda kawar tata ta biyota da gudu tana kiran ta tsayata, aman ina cikinta take ji yana wani irin hautsina mata, bata san me ke damunta haka ba yanzu, ya kasance tana yawan jin abubuwa a tatare da ita,
Wardugu ya jima wajen Ayya, inda suka tatauna sosai sannan ta saka shi a gaba kan sai ya ci abinci,
Agaishat na fitowa ta nemi Mu.azam, sai dai bata ganshi ba hakan ya saka ta fice ta nufi wajen runfar Ayya mai wani ni.imtacen sanyi tana neman Mu.azam,
Nan kuwa ta same shi, ya kurawa waje daya ido, ya zurfafa sosai a tunani wanda yannayin fuskarsa ta nuna ba tunanin dadi yake yi ba,
A hankali ta karasa ta kuma maimaita salamar da ta yi ta yi masa tun daga dan nesa da shi,
A dan tsorace ya kalota kafin yake daidaita yannayin fuskar sa ya amsata yana mai kokarin gyara mata kujerar dake kusa da shi,
A hankali ta ja ta zauna tana dubansa, yannayinta ya nuna itama ta shiga damuwar da yake ciki,
A hankali ta ce" me ke damunka ya Mu.azam?
Daman ita yake kallo, dan haka ya bi bakinta da kallo yanda ta fadi maganar a hankali sannan a cicire domin dai tana faman koyon yarensa ne,
A nitse ta janye idannuwanta daga cikin nasa, domin kallo nr yake mata tamkar zai fada idannuwan nata take ji,
A hankali ya ce" Agaishat,
Ta dago tana dubansa, inda a take ta ji gabanta ya fadi da yannayinsa,
Mu.azam ya ce" kin san soyaya?
Agaishat ta zaro idannuwanta tana dubansa, tama rasa me zata ce da shi,
Mu.azam ya ce" kin taba yin saurayi wanda kika ji kina so?
Agaishat ta saki murmushi mai kama da na sakalci, domin ita abin har ga Allah dariya ma ya bata, A hankali ta maimaita kalmomin" *So, Soyaya, Saurayi?*
Mu.azam ya dan kankance idannuwansa ya ce" yeah,
Agaishat ta dube shi, duba na ido da ido kafin take fadin" *Ban san shi ba*!
Da mamaki yake kallon ta, bata san shi ba tace fa? Aman daga ina Agaishat ta fito haka? Ko dai masu son nata ne basu yi mata ba?
Yin wannan tunanin ya saka gabansa ya fadi, a ransa ya ayanna ya salam, kar dai a je nima ban yi mata ba,?
Muryarsa sanyaye ya ce" du a maneman soyayar ki ba wanda kika taba jin kina so?
Agaishat dake dubansa itama, bata dago ina ya nufa ba, domin dai ita ba.a taba kamanta za.a ce ana sonta ba, dan haka ta bashi hankalin ta sosai ta ce" ba wanda ya taba fada min ya ake so din ne,
Dariya ya shiga yi kasa kasa yanai mata wani duba kafin yake fadin" ba fa zolayana nace ki yi ba Madame,
Bata san kalmar madame ba, aman ta gane yana nufin wasa take yi masa, dan haka ta ce" ban taba yin saurayi ba, ko an zo zaben yan mata a gidan mu ba.a taba zabena ba, Ba yace dan na cika baki da muni, ni ba alkhairi bace dan baki ba alkhairi bane, hakan ya sa ba mai zabena bare a biya sadakina, har kanwata an zaba sai dai kafin auren ta rasu ita,
Dubanta yake har ta gama yi masa bayani da kwatance da komai dan ya gane da kyau, ajiyar zuciya ya sauke a ransa ya ayanna na godewa Allah ai da basu zabe kin ba da sun saka ni a ukunna,
A fili kuwa ya ce" wa ya fada maki baki ba alkhairi bane?
Agaishat ta ce" da alkhairin ne, da mahaifina bai kyamace ni ba da alkhairin ne da nima ana yi min dinkuna irin na yan uwana, da alkhairin ne da jama.ar gari sun mutunta ni a matsayina da dan adam mai daraja a cikin halitun Allah, da alkhairin ne da na yi saurayi koda mahaukaci ne a *Gida*,
Katseta ya yi da fadin" aman sai na ga kina da ilimin adini sosai, ya aka yi kika kasa imani da haka?
*Agaishat , malamata, wa ya halici fari da baki,?*
Agaishat dake dubansa ta sada kanta a hankali, kafin ta ce" Allah ne,
Shin da ya halici baki ya kawo wata ayya a alkur.ani mai girma, a hadissai ko wani litafin na adinin fake nunin bakar fatar nan da ya halita ya haliceta ne dan wani laifi? Ko mai wani laifi?
A hankali ta kuma fadin" aa, ban karanci haka ba,
Mu.azam dake dubanta ya ce" Bilal, bawan Allah, wacece kalar fatarsa? Ya darajarsa take?
Dago da idannuwanta ta yi ta ce" baba tsofo ya ce shi ne ya fara kiran sallah , ya ce mutun ne mai daraja, makusancin fiyayen halita,
Mu.azam ya gyada mata kai kafin yake ciro wayarsa ya samo hoton ka.aba ya ce" zo ki ga ka.aba a hoto Agaishat, zo ki gani...
A hankali ta matsa tana kallo, kalar bakin ya tafi da imaninta, abin ya yi mata kyau a ido, a hankali ta kai yatsarta ta dan shafa hoton,
A hankali ya ce" ba wani bawan da ya fi daraja, ya fi kusanci fa ubangijinsa sai mai yi masa biyaya, mai tsoron shi, mai kiyaye dokokinsa, a cikin nan kin ji an ce *Farar fata ta fi bak'a?*
Agaishat da take jin wani yamyamyam a jikinta na dadi ta girgiza kanta,
Mu.azam ya ce" makafi ne ko kwakwaluwar su bata ja? Ya aka yi basu yiwa abin kaunata wawa ba?
Da sauri ta kallo shi,
Kansa ya dan sada ya ce" kina da tsararen kyau, fitinanan kyau, baki da tsayi Agaishat...baki da kiba har can, yannayin jikin ki ya tafi da yannayin tsayin ki,
Bakin ki ba mai tabo bane bare shaida, gaba daya ya tafi iri daya ne baki mai haske mai nutsuwa, agaishat, fuskar ki yar doguwa ce mai dauke da dara daran idannuwan da a kowani yannayi kike su kadai sun ishi mutun, Agaishat Allah ya tsara ki da hanci mai tsayi mai yan kofofi wanda ya yi das da dan madaidaicin bakin ki,
Rashin hayanniyar ki ya hadu ya kara kawata halitar ki, ke da ba dan kar na kauce hanya ba da na fada maki sauran tsaruwar ki,
Dan dakatawa ya yi gannin yanda ta zuba masa ido, sai a lokacin ya tuna ya saki baki sai zuba yake mata,
Dan kimtsa kansa ya yi a hankali ya ce" Agaishat arrrakam (Agaishat ina son ki),
Wata irin faduwa gabanta ya yi, da wani irin firgici ta akle shi, tsoro, mamaki, surprise, murna suka hade suka saka jikinta ya dan fara rawa, So na? Ji ta yi wani nauyinsa ya diri mata,da sauri ta sada kanta kasa, kafin take mikewa da wani irin sauri ta jua inda Mu.azam ya mike yana kiran sunnanta daidai Wardugu ya yi kokarin kawar da kansa dan kar su ganshi bayan ya jima wajen,
Ganninsa ta yi yana ta faman taba labulen ayya wanda ke gyare tsaf a wajen aman kamar wanda yake gyara shi,
Kanta ta shiga sosawa kafin take dan rabar gefensa ta shige ta taka matatakalar da gudu gudu ta nufi dakin ta,
Da ido ya bita, da wani irin kallo, a hankali ya lumshe idannuwansa ya juya ya fice a dakin ya nufi wajen mu.azam da ya koma ya zauna ya dan dafe kansa da hannunsa cike da tsoron kar a je ta ki karbar sa,
Gaban wardugu ya ji na wani irin gudu wanda har ya ji wata yar zufa ta karyo masa,
A dan hanzarce ya karasa wajen amininsa yana mai cike da zulumin yannayinsa, a nitse ya kai hannunsa ya ce" Mu.azam?
Agaishat na shiga dakinta ta karasa da sauri wajen madubi, lufayar jikinta ta warware ta tsurawa kanta ido, du abinda ya fada take son gani sai dai ita bata wani gannin kyanta, , .....
A hankali ta kai zaune ta cuje abinda ta daure gashinta da shi wanda hakan ya baiwa gashin damar zubowa baki dayansa ya yi lumbuk a jikinta, hannayenta ta cusa ta fashe da wani kuka mai zafi, a hankali, muryarta na rawa ta ce" Anna, ina kike? Anna wai yana so na? Ashe nima mutun ce Anna? Anna wai ina da kyau, wai nima mai daraja ce, Anna nima na yi saurayi...........tana kukan kuma ta shiga dariya a hankali ta furta" Mu.azam, nawa😌😌😌😌😊😊😊😊😊😊😊
I.m sowi fans , jiki da jinni ne 🤦♀
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣5️⃣
A hankali Wardugu ya kai hannunsa ya taba Mu.azam, murya a sanyaye ya ce" Mu.azam?
Da sauri ya dago da kansa daga yannayin da ya afka, ya kali Wardugu da kyau kafin yake sakar masa murmushi,
Wardugu ya ce" me me ke damun ka?
Mu.azam dake dubansa ya dan sada kai, ya kuma dagowa yana dubansa ya ce" jinta nake a raina har jikina Wardugu, sai dai ban san ba ko zata aminta ta aure ni a dan kankanin lokaci kafin mai yiwuwa ta yiwu da ni?
Wardugu ya ji gabansa ya fadi, Allah yana ganni idan da abinda ke tayar masa da hankali a yanzu bai fi rashin lafiar Mu.Azam ba, lamarin na girgiza shi in ya tuna, yakan tsinci kansa ba karfi bare laka a jikinsa idan ya tuna, .......
Duk da ya fahimci wa yake nufi aman sai ya kashe ido guda yana kallon Mu.azam ya ce" kai, soyaya ka afka daga zuwa garin mu? Fada mini wacece mai sa.ar samun abokina ?
Mu.azam ya lumshe idannuwansa ya ce" Wardugu, na kan ji wani iri idan muna hira da kai a yanzu, domin du ka canza min kan da, a da idan muna hira tamkar yaki muke, ka warto ni na tsokaneka mu yi ta shirirta har sai an shiga tsakanin mu, aman a yanzu du abinda zan maka sai na ga ka wani yi shiru ka kyale ni ko kuwa ka wani lalaba ni, malan matarka ne ni? Ko dan bani da lafia? Ni irin yanda muke da ya fi birge ni, sai ka wani dawo ladabi?
Wardugu dake kallonsa ya ji zuciyarsa ta mugun karye, hakan ya saka wata zufa ta karyo masa, a yanzu da suke zaune a haka ba mamakin shi wardugun shi ne gawar fari, aman kuma rashin lafiar Mu.azam da ta bayana kanta ne ake kiran kisan mumuke, domin dai ta hana kowa walwala tsakanin mutane ukun nan, Mu.azan din, docternsa, sai Wardugu da ya sani shima,
Wardugu ya saka hannunsa ya share gumin da yake , ya miko hannunsa kusan na Mu.azam ya ce" wa kake so? Ko yar gidan waye, ko wa take takama da shi nan duniya sai ta aure ka, kuma dole ta so ka!
Mu.azam ya kwace hannunsa yana dubansa da yannayin tausayi, ya san waye Wardugu farin sani, wannan yannayin da yake ciki yayi imanin da ace zai samu kuka da ya koka tun karfinsa ko zai samu sauki,
Goshinsa ya dafe yana dubansa, ya ce" ka daina damuwa da lafiata Wardugu,
Wardugu ya katse shi da fadin" idan muka gwada aikin nan fa?
Mu.azam ya ce" bayan ka tirsasa ni shan lemun tsami cikin ruwa masu zafi, kana tirsasani cin tafarnuwa, kuma zaka bijiro da maganar aikin da na guduwa ? Wardugu aikin nan fa mai yiwuwa shigar da za.a yi da ni a fitar maku da gawata,
Wardugu ya ce" kuma tana iya yiwuwa a fitar mana da kai ras ka sami lafia,
Mu.azam ya ce" mafi akasari idan Allah ya yi an sami lafiar ma kwakwaluwa na tabuwa, ko a samu shafewar tunani, cikin kaso dari bai fi 2/100 suke mikewa garas ba Wardugu, na fi son idan ta Allahn ce zata kasance da ni nan kusa ya kasance ina kusa da mutanen da nake so suke so na,
Wardugu ya kura masa ido, kallon cikin ido, ya ce" ba zan iya ba, zuciyata mai mugun rauni ce a kanka, ina jin rashin karfi a abinda ya shafe ka, baka yi min adalci ba idan har ka yi min haka, !
Ya mike ya dauki kys dinsa, ya dora hanayensa saman table din yana dubansa ya ce" baka isa ka min haka ba, ba zan taba barinka ka yi min haka ba! Zan nemi karin bayani ......
Juyawa ya yi ya fice inda yake jin kansa na mugun sara masa,
Mu.azam ya girgiza kansa bayan ya bi shi da kallo, a hankali ya furta" ban so ka ji ba, sai dai rigumarka ta saka ka tankalo abinda zai hana maka nutsuwa!, ya hana maka jin dadi!
Tukin garari ya yi wanda ikon Allah kawai ya kai shi gidansa lafia,
Yana zuwa ya sauka daga motar ya rufe ya nufi bangarensa kansa duke yana mai jin yanda yake sara masa,
Har zai bude ya shiga, sai ya fasa ya dubi bangaren Walyn,
A hankali ya juya akalar tafiar tasa ya nufi bangarenta yana wata irin tafia wace da ka gani zaka fahimci da karfi ne ake yinta ba dan ana jin dadinta ba,
Wardugu na shiga ya zarce falonta baba inda kamshin turaren da aka turara ya yi masa salama.
A hankali ya shige yana hangenta kwonce saman doguwar kujerar falon nata tana danna waya ranta da yannayin bace, sannan da maganin zazabi mai tafasa a gefe da alama dai ita ta sha bata jin jikinta,
Da sauri sauri ya karasa gareta yana mai cire rigar tasa ta sama ko zai ji dan sanyi sanyi ya karasa wajen Walyn da ta zabura ta mike tana dubansa da wani irin yannayi mai fasara abu uku, na farko ganninsa a bangarenta, na biyu yannayinsa ya firgitata, na uku mugun haushinsa da take ji domin yanzun ma a cikin grup dinsu na manyan mata ne ake tatauna maganar har wata na ikirarin ita walahi a duniya ba wanda ya yi mata irin wardugu halayensa na kasheta da dadi, idan ta kali hotonsa takan jita a wata duniya, tunani take wannan mutumen ya kasance hazarsa a gabanta kadai ya isheta, duda an kwabeta cewar da matarsa a gidan fa , kamar an zungureta ne an tirata domin a lokacin ne ma ta ce" Wardugu ai mijin mace hudu ne wanda Allah ya halita masa ba wani shege ba, duniya kuwa idan takamarka sauko wani a can ya kwana,
Tana wannan tunanin wardugu ya karaso jikinta, batai tunani ba ta ji ya rungumeta da karfi wanda sai da ta ji kamar numfashinta zai tsaya dan ya kanainayeta ya hana ta motsi,
A hankali ta rungume shin itama, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana shakar turaran jikinsa wanda koda ya yi zufa bata hadewa da turaran ta bayar da wari wari, turaran ke cin karfinta bama zaka gane ba sai dai idan mafi kusanci da shi ta ji gishiri gishiri a jikinsa a irin wannan yannayi 🤣,
Gajiya ta yi da tsayuwar domin daman ba wani karfin jikinta take ji ba,
A hankali ya bita saman kujerar domin shi a wannan lokacin bashi da bukatar komai sai na ya jima a jikinta , ta rungume shi, yana so ne kawai ya ji shi a jikinta ba komai ba,
Haushi Walyn ta ji, aa me wardugu ya dauketa ne? Jiya ya gama wulakantata, ya fanshi jikinta, ya tashi ya yi tafiyarsa, ta je saloon ta kwashi rashin mutunci dan shi, ta zo gida mata na wawarsa shi oga! Yanzu ya kuma dawo mata da bukatar sa? (Domin a tunanin ta , bukatuwa ce ta dawo da shi a irin wannan lokacin ),
A hankali ta zame jikinta tana dubansa yanda ya yake ringeshe jikin kujerar idannuwansa du a lumshe,
Baki ta dan yatsina, a fili ta ce" ka san yau a saloon wata karuwa ke ikirarin sai ka aureta?
Daga yanda yake kwonce yake dubanta, a hankali ya ce" ki zo gare ni Walyn.....
Ya mika mata hannunsa,
Kafadarta ta make irin na yangar nan na mata ta ci gaba da fadin" ka saurare ni mana, ina maka hira ka wani basar,
A hankali ya kai hannunsa wajen goshinsa kafin yake mata alama da ta ci gaba, domin ya lura kwata kwata matar tasa bata lura da yannayinsa ba, bata da niyar fara sauraronsa, zata tiso abinda ke damun nata wato *kishi da isa*,
Zamanta ta gyara tana mai dubanda da kyau ta ce" ni kuwa na bata amsar cewa , Wardugu mijin mace daya ne, ba zai kula wace ta san mutuncin kanta bama bare ita karamar yar bariki, Wardugu nawa ne ni kadai!
A hankali, ba tare da wani damuwa ba ya ce" *wa ya yi miki wannan albishir?*,
Da sauri ta dubo shi, da yannayin mamaki ta ce" me kake nufi?
Dagowa ya yi yana dubanta ya ce" *Auten zobe muka yi da ke?*,
Walyn ta kara zabura da mamaki ta ce" kana nufin sai ka kula wata macen?
Wardugu ya buda idannuwansa da kyau, ya ce" *To waye ni?* , an fada maki ni ba mutun bane? ,
Yanzu sai ka ci amanata Wardugu? Sai ka dubi wata macen da sunan so?
Kallon kar ki raina min wayo ya yo mata sannan ya ce" tunda hirar kike so mu yi bari ki ji, da farko dai ni mutun ne dan Adam wanda nake tara ba goma ba wanda nake cike da laifuka , nake dauke da zuciya mugun nama, wanda na kwonta da sannin Allah ya halasta min auren hudu na jera, nake da sannin ina da wajen saka su, ina da abinda zan ciyar da su, na tufatar da su, sannan ....ya yi murmushi ya ci gaba da fadin" na sauke hakinsu saman lit (bed) ba tare da gajiyawa ba! Ke kin san wa kike aure shi ya sa kike kishi! To a haka da nake, akoy wa.inda ban yi masu ba, sam bana gabansu, bana cikin tsarin da zan samu koda gaisuwarsu ne! Walyn, ana aure dan soyaya, da tausayi, dan sha.awa, dan arziki, ba zan maki karya ba, ba zan yi maki rantsuwar ni na isa na kauce kaina daga kan *mace yar dagwas dagwas mai dorinar dukan maza ba* , ciki kuwa koda yar barikin ce da kike fadi mai yiwuwa na zama silar shiryuwarta!
Gaba daya har Walyn ta fara fita a hayacinta , ta hayayako ta ce" me na gaza da shi Wardugu da kake kiran min sunnan wata a gabana?, *Kyau, fari, tsafta, girki, iya tarairayarka,* wane na gaza a cikin nan?
Haushi ya kara kama shi, itace ke ikirarin iya tarairayarsa bayan yanzu ya shigo mata a wani yannayi maimakun ta dubi halin da yake ciki ta zauna a kusa da shi aa, sai ma ta tsankalo kabarun banza da wofi, kai da Walyn a wajen aikinsa take kai koda ficewa take ta hanyar da an kwashi yan kalo da ita da matan dake kai masa ziyara, wai kuma ta yi ikirarin ita ta san kanta ita mai kyau me memememe, *Isarta* ta hanata ta duka masa yanda ya dace, takamarta da halitarta sun hanata gane ainahin biyayar aure, sai idan baki ya bude ta shiga zubo masa abubuwa mararsa tsari, dan haka da yannayin haushin nan ya mike yana daukan rigarsa ya ce" *Kin san dadin miya ke sakawa a yi kari!*
Wai wai wai wai , shin fans zaku kuwa iya zama da mai hali irin na wardugu🤦♀🤦♀🤦♀,
Su waye wardugu ke ikirarin ko arzikin gaisuwa baya samu daga wajen su? Me ke damun wardugu?
Me ke damun kwakwaluwar Wakyn? Ta hada kyau, fari, tsafta, kanshi, girki, bata isa ta daki kirjin mijinta na ita kadai bane?🤔
Mu.azam, zai kai labari kuwa?
Agaishat Ayya, Anna, Ba, Marahut, ya labarin su ne?🤔🤔🤔
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣6️⃣
Rigarsa ya rataya a kafadarsa, ya juya da niyar barin mata bangarenta domin bai ga dalilin fa zai saka a caza masa kwakwaluwa a waje, ya zo wajenta dan samun nutsuwar zucuya itama ta caza masa, yana bauwa Walyn damarta ta mace, na ta yi korafi a kan abinda bai mata ba, ya sha duba korafinta ya nuna mata ya tuba a aikantance ta hanyar daina abinda ta kawo masa korafin a kai, sai dai abubuwa na damunsa na irin yanda ita ba abinda ya sha kanta da damuwa da damuwarsa, bata wani damu da yannayin da zata ganshi ba indai da abin fada zata rufe ido ta fada da gatsali,
Murmushi ya yi yana girgiza kai bayan ya kare mata kallo du ta fice a hayacinta daga wannan yar maganar? To idan Allah ya kadarto min kara aure yaya zamu kwashe da Walyn?
Rai bace tana kokarin fashewa ta kuka ta ce" Wardugu, idan ka yarda, idan ka saki, ka yi saken kula wata mace sai dai a kwashi gawarwakin mu baki daya! Wardugu kamar yanda Batuben namiji zai iya suka da wuka dan an kali matarsa toh zan iya suka da wuka dan an rabe ka!
Tsayawa ya yi yana dubanta, iya gaskiyarta ta fada domin a tsaye take tana dubansa ido cikin ido, jikinsa ya ji ya dan yi sanyi, karasawa ya yi kusa da ita , ya dan sasauta murya aman a cunkushe ya ce" Walyn, bakya aiki da adini ne ke? Kin san da sunnar ma.aiki ce? Me ya sa zaki daukarwa kanki zafi haka? A haka Walyn ban ma nuna zan yin ba idan zan yi fa?
Idannuwanta ta dago dan sakawa cikin nasa domin ya darata tsayi, ta ce" na tsinci kaina a zazafar kaunarka, haka na wayi gari na ganni zundum , na shanye wulakanci kala kala dominka, kai da kanka ka sha wulakanta ni mai girma, karaya uku ka min a gabai na, du na shanye! Kai a tunaninka ba zan shanye azabar kawar da du wata tsagerar da ta tunkaroka ba? Wardugu, mahaukaciya ce ni a kanka! Sakara ce da a yaren ka! , kamar yanda ka sumar da saurayin da ya yaba maka ni, ni kuwa ka yi min marin da na yi ta ihu sai da kyar jina ya dawo dan na yi kwaliyar da aka yaba ni, haka zan iya rike makigwaron du wata yar iskar da ta yabe ka!
Kansa kawai yake dan girgizawa yana dubanta, Walyn, walyn Wardugu...ya saki murmushi ya juya,
Haushi ya kara rike mata zuciya ta daga murya ta ce" ciki kuwa harda wannan tsohuwar kilakin da ta ki aure take binka gida ma.aikata, anguwa! *Alhinayett*, ciki harda ita,
Dawowa ya yi ya tsura mata ido, kafin yake fadin" ki daina zagin Alhinayett domin mai son ki ce, tana yaki kan ki, tana yi min fada kan ki,
Karuwancin kennan! Karuwancin kennan Wardugu! Ta shiga jikinka har ka ji in ba ka kasance da ita ba , ba zaka ji nutsuwa ba!
Wardugu ya zauna saman kujerar dakin ya ce" Walyn, Alhinayett ba yar bariki bace, mutun ce mai daraja, mutunci ne tsakanina da ita, ke kin san da soyaya ne da tuni na auri abina na kilace, jimawarta ba aure kuwa Allah ne bai kawo lokaci ba, aman an kusa saka aurenta, ki daina magangannu irin haka Walyn , ke macece, ko a kan ki ba haihuwa zaki yi watarana, ba.a so mutun ya cika izgili,
Kai ta kawar ta ce" wardugu, gaskiya ne baka so? Alhinayett ai kowa ya san kilakin ka ce!
Wardugu ya mike a karo na uku kennan, ya karasa kusan Walyn yana mai binta da kallo, hannunta ya damko ya bude yana dubawa, ya riko fuskarta ya daga idannuwanta yana dubawa, ya gwale bakinta ya saka yatsunsa ya ciro harsanta yana dubawa, ya saki ya kama rigar dake jikinta ya dage sosai har biyu suka bayanna, nan ya tsura masu ido yanai masu kallon kurullah,
Cikata ya yi , ya dan taka ya tako kafin yake nunota da yatsarsa manuniya, muryarsa ya saki baki daya ya ce" Ba karuwa bace! Aminiyata ce, du wanda ya zagar min ita zan bata ransa! Kika kuma kiranta da karuwa na rantse da girman mahalicina sai na aureta koda kuwa ta tsane ni , koda mutuwa zata yi dan kina na kawota na kwana da ita saman gadon ki! Ke da ba dan ina hangen kamar mai shigar ciki ba yau da na nuna maki tsagwaron rashin mutunci! Ya ina taro ki kina raina min hankali? Walyn ni in ban kara aure ba ni ba dan babana bane!, ni ba jinin tubawa bane! Walyn dole ki zauna da kishiya in baki kona mu ba ke ba yar babanki ba ce!
Fuuuuuu ya juya ya fice yana jin kamar ya koma ya yi kwalo da ita, sai dai yana tsoron kar a je ciki ne da ita, ta ja ya yi mata lahani bayan adu.arsa kennan shima allah ya azurta shi da haihuwa, yar bakin ciki kawai take jan sa masifa salon ya biye mata idan cikin ne su barar su shiga uku!
Haka ya koma bangarensa ya zube a falon sa ya yi ruf da ciki ya dora hannayen sa saman kansa yana yamutsawa yana tunanukan rayuwa,, walyn ba wayo , haka ya ayyana a ransa kafin ya kuma fadin....ta saka sai na kara zama da wata macen? Walyn shirme shirme🤦♀,
*Timiya*
Amai take kwararawa har kamar ta shide, inda *Ba* ke tsaye ya dan duka dan tsayinsa, da rawaninsa yana dubanta,
Gefe guda kuwa su Anna ne da yayanta yauma Gaishat ta kawo mata ziyara da dan cikinta da ya tasa kafan wanda sarki ke mugun zumudi kansa tkar shi ne dansa ma fari,
Suna kasan bishiyar gidan suna zaman su suna yar hirar su , domin yanzu da safiya ta yi Mariama ke fitowa ta gyara wajen ta shinfida tabarmar kabar da Anna ta siyo daga garin agadez ta dauki du abinda zasu bukata su koma can su yini abinsu , nan suke sallah su ci abinci, ta dauki na baba tsofo ta kai masa domin Gaishat na tsaye kan abinda zasu ci, sarki baya wasa da ta nuna tana da bukata ake kwasa a kai mata itama ta kwasa ta kaiwa mahaifiyarta, inda ta saka sarki ya yiwa *Ba* gargadin kar ya kuma kwashe masu abincin su,
Bakinsa yake motsawa ya juya ya karewa Anna kallo da yarenta su uku sun zagayeta, ya juyo wajen amarya dake maida lumfashin kadangare bayan ta gama sheka amanta,
Tabar sansaninsa ce yake gumtsa a bakinsa,
Bakin ya bude ya totofar da yawu, domin du mai shan tabar sansani ya kasance yana tofe tofen yawu, ya juyo wajen amarya ya ce" sannu *Uwar mai uba biyu*,
Kallon kasan ido ta yi masa kafin ta kada kai,
Juya kansa ya yi wajen Anna ya ce" duniya, anai min kallon ina yiwa yarana aure suna tafia birni, ke gashi kin dauki yar santal ki badata yawon kilaki!
Da sauri Anna ta kallo shi, gabanta ya fadi,
Kura mata ido ya yi ya ce" karya na yi? Ke yanzu zaki daki kirjin yarinya na hannun kirki? To ni dai in tana aiko wani abin ake boyewa ana ci Allah ya isa! Dan ko dan ciyar da ita da na yi ya isa a yaga mini wani abin ba a rufe ni da baibai hannu ba!
Gaba dayansu dubansa suke,
Ya tako da fararan kafafuwansa da sukai fari fat na kasar garin ya dubi Gaishat ya ce" ke kuwa fa? Haka zaki saka mini ko? Kin samu na aura maki sarki , ya nada ki sarauniya aman ni kika saka kafa ki ka shure ni sai wannan tsohuwar matar kike baiwa abinki ko? Ai dukan ku Allah na kallon ku! Ko hakin ciyar da ku da na yi zai bi ku,
Ya kara tofar da yawu yana duban Mariama dake bin sa da wani mugun kalli itama da sansanninta a bakinta kamar na sauran yan uwanta da Anna, ya ce" ke kuwa ke ce gagarara ko? Mai tarda ni wajen majalisa ki tirke ni gaban abokaina, ke mai karfi wace ta fi kowa iya rashin kunya, a gaban yan uba kika yi ikirarin zaki ga ubanda zai maki aure ko? Ba laifi, ba laifi Mariama, in sun zo sai mu basu gidan su saya su tafi mu kuwa mu koma zaman titi ,
Mariama ta yatsina bakinta ta kawar da kanta,
Babar rigarsa ya kabe ya ce" kudinku yanzu na fara ci, ni da ku ba shari.a domin ni na haife ku! Dole na yi maku aure na mori kudin ku! ,
Ke kuwa, ya nuna Anna da take jan dan karamin carbinta tana shamaninta ya ce" kin ji kunya, anai maki kallon saliha sai gashi kun hada baki da tsohon can kun tura yarinya nema; ana zaton wuta a makera su Annar yara sun kunata a masaka.
Yana gama fada ya fice a gidan yana ta tofe tofensa,
Mariama ta dantsa yatsarta a bakinta tana yiwa yayarsu kallo mai kama da harara, domin ita ta yi masu kashedin kar ta kuma gannin wani ya biye masa, dan ta lura hakan na masa dadi
Gaishat ta yi murmushi tana dubansu ta ce" baku lura ya fara yin sanyi ba?
Mariama dake hararar Amaryar Ba ta ce" sanyi? A wannan tsohin najad.....
Bige bakinta da Anna ta yi ya saka ta kasa karasawa tana turo baki,
Da yannayin bacin rai ta ce" in kina irin magangannun nan hankalina tashi yake, mahaifin ki ne fa, ko me ta zama adu.a ce tsakanin ki da shi, ya zaki ringa halaya irin na wace bata da tarbiya? Bana so Mariama ,
Aman Anna, kina ganni abinda yake yi fa, ke tsoronsa kike , to ni bana tsoron sa,
Kuma bakya tsoron Allah? Gaishat ta fada tana dubanta, hakin dake tsakanin ki da shi na matsayinsa na uba Allah ba zai bar maki ba, ki bi shi, ki yi masa biyaya, ki bar shi idan shi gobensa bata dame shi ba kai nasa,
Shiru ta yi tana duban fatimata dake dan zane a kasa ta ce" wacen matar ciki ne da ita fa? Kuma kum san ba cikin Ba bane,
Anna ta kwalalo ido tana dubansu, a dan harzuke ta ce" na ga mai isata yau da yaren nan, kun yi da shi ne? Bama wannan ba sa.anku ne? Du wace ta kuma gigin muguwar magana a kan mahaifin ku a gabana zamu bata da ita! Ba ruwana ban koya maku ba, baku ga ina yi ba, kuma idan na ji tsoronsa ai ba laifi ba, shugana ne, wanda aljannata ke karkashin kafafuwansa, a haka ma ya muka kare da shi bare na yi masa gatsali? Ku daina bana so!
Ta karasa tana dan dafe kanta domin har ya sara mata maganar nan da ta yi,
Da dadaya suke bata hakuri suna masu lura da yannayinta.............
Daga inda yake ringeshe yake biya bagara a fili hannunsa a kan zuciyarsa,
Sai da ya kai karshe ya samu ya dan daga ya jingina yana duban hanya dan ya san yanzu Mariama ta zo,
Yana jin dadin lamarin mariama sai dai ita ba.a hira da ita, kimkim take masa har yanzu haushinsa take ji, bata san irin yanda shima hankalinsa ke kan Agaishat ba, adu.arsa a gareta ne, da fatan saduwar fuskokinsu kafin ya koma ga mahalicinsa,
Jama.a Wardugu na neman karin aure🤣, du mai son karya kafa ta shigo layi🤦♀🤦♀🤦♀................... dan Allah aunty Alhinayett kar ki tura masa wannan page din wollah lalla batai kwari ba kar ya karya min kafar nima😟😟😟
0 Comments