bakace hausa novels 5

 BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣5️⃣





Wardugu da ya mayar da dubansa gefen titi ya kai hannunsa yana shafa kansa a hankali, tabas Mu.azam yana tako shi kwanakin nan, in sha Allah shi kuwa zai yi iya yinsa dan gannin ya faranta masa...


Motar ya tayar ya dauki hanya, tafiya ce suka yi mai dan tsayi kafin suke karasowa wajen,

Daga mu.azam har Alhinayettt sun yi mamakin yanda ya yarda ya zo wajen,

Mu.azam ya ji wani girman Wardugu ya karu a idannuwansa , kaunar aminin nasa ya linku a zuciyarsa, adu.a ya yi masa da fatan alkhairi ...


Sai dai me, suna shiga da motar suka fara hango wasu abubuwa,

Yan mata ne da muguwar shiga, shiga ta kananun kaya sosai, da samari suna kai kawo suna dan badalar su,


Gaba dayansu kalon wajen suke da mamaki, Wardugu ya jinjina kansa a ransa ya ayanna, *Abinda ka zabarwa kanka kennan Uban Wardugu!* 


Mu.azam ya yi tsam ya ce" Wardugu , ko mu juya dai? Domin wajen shi har ya fara bashi tsoro irin yanda ake shiga ana fita ana wasu abubuwan, 


Wardugu ya juyo bangarensa, ya saki dan murmushi ya ce" ai mun zo  sai kun shiga, 


Ya bude ya fice bayan ya dauki hularsa casquette dan baya so kowa ya gane ko waye shi,


Jiki a sanyaye suke bin bayansa har ya karbi tikect din su hudu wanda zai basu damar leka ko.ina sannan su ci abinda ransu ke so, du tiket daya jika talatin ne, a wajen ba abinda babu, a da da aka bude shi an bude shi ne dan yara da iyayensu ranar weekend kawai ake bude shi, sannan ka.ida ne sai ka zo da mahaifiyarka ko da mahaifinka zaka shiga, ba.a barin budurwa da saurayinta shiga domin wajen an kawata shi da su piscine, su kayan lilo na zamani  wajen game, wajen hutawa, da wajen cin abinci, 

Aman a yanzu sai ta canza zani tunda ta karbi wajen da nufin zata kula masa da shi ta canza komai banda sunnan wajen, domin dalilin sunnan da ta bari doka ke tsalake su, Wardugunma bashi da labari , a yanzu wajen ba.a barin yaron da bai kai 18 shiga ba, sai gaga gagan yan duniya, sannan ba abinda ba.a yi a ciki, kan masu bushe bushen su, sai masu aikata zina a fili (wa.iyazubillah) shi kansa mahaifin wardugun bai san takamaimain abinda ake aikatawa a wajen ba, hasalima baya zama tunda abinnan ya faru da iyalansa ya ji niger din ta fice masa a rai, dan haka yake yawonsa yana kasuwancinsa a duniya, idan ya zo niger ba dan ya jima bane, koda an kawo masa korafi bai wani dubawa dan kuwa baya so ya baiwa yan tsunguri tsoma damar kawo masa korafin gidansa,


Jikin Agaishat haka yake rawa, gannin irin abinda baba sofo ke fada mata cewar ba kyau yawo jiki a bayane haka sannan ba kyau aikata zina, Ayya ma ta yi mata fadan ko a tv ta ga sun saka mace na namiji na rungumar juna ta canza tashar ba kyau aikata zina sannan ba kyau kallon tsiraicin wani banban zunubi ne ,


Wajen cin abinci Wardugu ya zame da su, domin daga nan du wani abin hange zai hango shi.

Suna zuwa suka zauna a tsararun kujerun wajen, kamshi sai tashi yake, yayan sangartatu , yayan masu hannu da shuni, da kuma masu hannun da shuni, yayan talakawan da suka zabi rayuwar hutu da zama a inda Allah ya ajiye su, sai bushasha ake ana tafiyar da lamarin cikin tsarin yan gayu.....


Menu ne aka kawo masu aka aajiye masu, nan Wardugu da kansa ke a dan duke dan kar wani ya gane shi ya dauki menu dinya kare fuskarsa da ita,


Alhinayet da gabanta ke faduwa na yannayinsa, jikinsa ya nuna ya hau, yannayinsa ya nuna ransa a bace yake, 

Ta kali Mu.azan da ya rapka tagumi bai taba Menu din ba ta kuma mayar da dubanta wajen Agaishat ta ga du a firgice take sai sada kanta take bata son kallon mutanen wajen , abin bako ne a gareta,


Hannunta ta kama ta ce" Agaishat, tashi mu je,


Ai kuwa tamkar jira take ta mike ta bi bayan Alhinayettt suka fito daga dakin cin abincin suka zauna a wata farar kujera inda suka baiwa wannan lamari baya.


A hankali yake karanta menu din, harda porc, da giya kala daban daban, sannan abinda ya fi daukan hankalinsa wani abu da aka zana fari shi kuwa aka rubuta masa kudi , shi idan dai ka dauke shi dole sai ka biya, kudi masu yawa haka, 

Kiran serveuse din mai dan bingilin sket ya yi da hannunsa, 

Tana zuwa tana wani irin juyi fa tafia ta karaso , 

Ta saman gilas dinsa ya kare mata kallo, kafin yake mika mata menu din  ya nuna mata abinda yake so,


Kallonsa take dan gane idan har dan hannun ne? Ko kuwa? Domin sunna taka tsantsan sosai bisa umarnin hajiarsu, dan ta fada masu au kula fa, kar su yarda wani mai bakin cikinta ya yi masu rami su afka, domin abin nan hoda ce, hoda ta shaye shaye, 


Jikin wardugu wando ne wanda ya dan dara gwuiwarsa, sai bakar riga wace bata da zanen komai a jikinta, sai hular baka itama wace bata nuna ko ta meye ba  ya dorata saman gashin kansa wanda yake da dan tsayi kadan ba dayawa irin na samarin nan dai na zamani, yannayinsa ta karewa kallo, girkeken namiji, bai yi mata kama da police ba, in ba police ba kuwa wa zai zo masu leken asiri? A tunaninta, dan haka sai ta ce" oga, ka kawo carte din ka ko kach zaka biya?


Wardugu dake zaune a aljihunsa ba kudi, sai dai a mota, carte dinsa kuwa idan ya bada za.a iya gane ko waye shi tun kafin ta karasa wajen, 

Yana tunanin mafita Mu.azam ya mita tasa carte din ta bank,

Karba ta yi ta karanta sunnan, 

Kallonsa take shima, a take ta ayannawa ranta yan hannu ne, wani lokacin likitoci na zuwa siyen abinnan su dai basu san ko me suke da shi ga,


Juyawa ta yi ta tafi dan kawowa , 


Wardugu ya hade jimkaken hannunsa da wanda yake bude ya shiga murza su a tare, 

Sannan yana kara bin wajen da mutanen wajen da kallo,

Table sun kai biyar da ya hango suna fan dukawa su ja wani abin da yake kyautata zaton hodar maye ne a saman plat dan karami mai ruwan zaiba mai shegen kyau kafin su dago su dora daga inda suka tsaya, 

Abin mamaki harda yan mata, kananun yan mata wanda a cikinsu sai ya yi rantsuwar akoy wace bata kai 18old din ba! 

Wajen a da kafin ya dawo haka yake etablissement privé, wanda etat gwomnati ta san da zamansa ta bada amanar a bude shi, bisa takardun fa aka gabatar a da an gabatar ne kan irin wancen tsarin na wajen hutun yara da iyayensu ranar da ba.a karatu, aman a yanzu ta sauya zani wanda shi dai da hannunsa bai saka hannun a bude haka da shi ba, 

Kansa ya girgiza, yau ko uban wa ya daure masu zasu ci ubansu! 


Dubansa ya kai waje, nan ya hangi su Alhinayet suna fan taba hira da Agaishat,

Idannuwansa ya tsaida kan Agaishat wanda bai ma san ya yi hakan ba, kallon me yake mata? Sho kansa bai sani ba ko yannayinta ne ya fi yiwa idannuwansa dadin kallo?

Yana tsaka da kallon nan nata aka gabatar masa da harakar gabansa harda abin ja,


Ajiye carte din ta yi ta juya, 


Wardugu ya dago hannunsa ya shiga dubawa da kyau, lale kwarai ita ce, ta ina? Ta ya aka yi take shigowa kasar?  A ina take samu? Ita ke oder ko mijinta ya canza yake samo mata? Wa yake basu? Ta wace hanya ake bi a kawo har nan? Ina polisawan dake bincike a bakin titi ba dare ba rana?, ina tsaron da yake takamar ya baza a sauran garuruwa ma bale a garin da yake ciki?, ya aka yi ya yi sake haka har wannan lamarin ya cin masa da ransa da lafiarsa? 

Yana tsaka da tunanin ne sai gata ta shigo,

Mace har mace, farar buzuwa mai shegen kyau, ta sha wasu mahaukatan sket da riga kanta ko dan kwali babu, ra sha wani dogon takalmi mai tsini, tana tare da wani balarabe ya sha jalabiyarsa hannunsa rike da makulin mota , 

Wani na biye da su da jaka baka suka shige tana dan dadagawa mutanen da sukai sabo hannu,


A hankali Wardugu ya mikowa Mu.azam ky din motar da suka zo da ita, 

Murya a bace ya ce" ka tashi ka dauki yarwn can ku koma gida, minti talatin na baku ku shige gida da abin hawan nan, ko ku je gidan su Alhinayet dan ya fi kusa da wajen nan, domin idan kame ya ritsa da ku sai kun kwana a cel! 


Ido Mu.azan ya zaro, kame a karfe uku na yama? Gashi ranar asabar ne ranar da mutane da yawa kan fita dan shakatawa, aman me ya sa zai yi kame har cikin gari bayan a cikin nan ne ake badalar?


Yar karamar wayarsa ya dauka ya dana kira,


Daga dayab bangaren aka daga ana mai fadin' Chef👮🏻‍♂️ (Sir), 


Wardugu ya ce" ina so yanzu ka yi kira wajen Gn na Gendaremeri, sannan ka hado min mahaukatana, ina son motoci masu yawa su cika gari, ina son mahaukatam su karaso nan Wardugu place, kana jina da kyau, polisai su kama du wani wanda ya yi masu shige da suspect, ba zancen takardunka ko wani abin  yau kamun yannayin mutun nake so a yi! Na fitar maka da iyaye mata wa.inda suka bayar da kwakwaran hujar daga inda suke, sai wa.inda suka kai yarensu wani wajen, bayan su a kama a cike mani cel! 


Da a vos ordre ya amsa yana katse kiran ya mike ya shiga aikatawa ba jira,


Mu.azam mikewa ya yi da sauri ya fice ya tisa su a gaba da adu.ar Allah ya kai su inda zasu je lafia kar abin nan ya ritsa da su , duda motar Wardugu ne, da lambar shaida shi ne, ba zai hana a bincike su ba domin matarsa ta saka ya dora dokar ko motarsa a ringa bincikawa a gari! .........




      Toh fa, An tabo Wardugu, an tabo tashin hankali🤔



🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣6️⃣



Bayan tafiyarsu da kamar minti ashirin, Wardugu dai na nan  zaune yana bin kowa da kallo ta kafurin bakin glass dinsa,


Mintuna tsakani sai kukan jiniyar sojoji ta fara yin salama wajen,

Da farko tunaninsu ficewa zasu yi, sai dai abin kara yi masu salama yake,


Hajia Aisata dake zaune saman cinyar karuwinta suna shagali aka dokowa waya,

Dagawa ta yi da yannayin duniyanci ta ce" Ya?


Masu tsaron kofar Wardugu Place ne daya ya yi kiranta a tsorace ya ce" Hajia me motocin sojoji ke yi a kofar nan? Na ga sai jeruwa suke suna didirowa da alama wani suke jira,


Ai bata san lokacin da ta diro daga saman kafar mutumen ta ce" me me me ka ce? Sojoji? A nan? 


Bata tsayin jin amsarsa ba ta fito da wani irin gudu ta ce" du wanda ya san da hoda gabansa ya yi gagawar rabuwa da ita ga arnawa a kofarmu!


Nan fa wajen ya rikice, mutane du suka tsorata, 

Aka fara kokarin guduwa wasu na nufar motocin su da gudun tsiya wasu na auna tsayin katangar sai dai ba halin dirawa domin ga tsayi ga abin kama barawa an zagaye wajen da ita,

Du masu jan mayan nan suka aniya gudu suna boyewa wasu na watsawa cikin ruwa wanda kadan ta rage masa ya janye abinsa, manya manyan masu fada a jin wajrn suka fara nufarta suna tambayarta me hakan ke nufi? Dama ba da lamuncewar gwamnati ta bude wajen raba masu eh yane ba? Ba wanda ya daure mata a gwamnati?! 

Ita dai ta cire dogon takalmi sai bi take table table tana kara goge dan sauran hodar da wani farin tishu ita da yarenta masu aikin wajen, 

Du sun haukace sai ihu take yiwa mutane kan wa.inda tsiraicinsu ya bayanna sosai sai fadi take su yi maza su saka kayan da ya fi wannan, 

Sannan da gudu wata bagwariyar yarinya ta fito da abaya ta kawo mata ta luluba mata daidai nan tuni sojojin sun cafke masu tsaron kofar sun fara tura su cikin motar wasu kuwa na tsare masu bi ta hanyar da wa.inda ke zuwa a lokacin,

Wani sergent ne ya kali abokinsa ya ce" yau fa akoy buro.uba a wajen nan, domin lamarin na gida ne, fadan gida ne,


Kai ya girgiza ya ce" ai ba na gida ba, ko na waye ta tarowa kanta dan oga ya yi mata tashi daya! 


A guje ta karaso table din wardugu tana babala botiran rigar tana zuwa da mamaki mamaki haushi haushi ta ce" kai waye mai hular nan ne wai? Kai ana a yi maza a kawar da komai kai kana zaune kikam , to walahi bara ku ji kaf wajen nan dan na lura hoda ta coshe tunanin ku! Du dan iskan da aka kama da ita ba ruwana, tawa kaf ta wajen nan ta bi Wc! Ta hannayen ku kuwa ban sanku bama bale na san me kuka shigo da shi, kun kuwa san wajen da girma ba lale ne sojojin su yarda da ina iya control din kowa! 


A hankali ya dago yana hangen yanda ake shan tsere da mutanen tsakar wajen fa sojoji suna yi masu cafkar fara suna yin waje da su,

Ransa ne ya kara baci , me ya kai su kokowa da su? Su saka lasifika su yi magana kan du dan akuyar da ya nemi gudu za.a watsa masa tire a gaz! Aman sai wani guje guje suke da juna harma su yi tunanin mu tsarensu ne! 


Gilashin idonsa ya cire a hankali ya dago da jajayen idannuwansa ya sauke saman fuskarta , murya a dake a dage ya ce " aman kuwa da kin ci amanar clients din ki *AISATA*, na ji kuna fadin client sarki ne   ke kuwa kina ikirarin ba ruwanki dan an kama shi da hoda yana zuka, 


Mutuwar tsaye ne Aisata ta yi, mutanen wajen kuwa gannin mai maganar sannan ya karasa mikewa tsaye du ya saka suka rude abinka da mai laifi suka fara neman hanyar fita, 


A rikice ta nuno shi da yatsarta ta kusan baba ta ce" Wardugu? Wardugu! Wardugu, 


Ya ce" ki ajiye yatsarki da nuna da ita, ko ki hade yatsutsanki ki nuno ni da hannun baki daya, rashin tarbiya ne nuna baban mutun da yatsa Aisata! 


Wani irin juya ta fara ji, hankalinta tashe ta ce" aman kai da kanka zaka tonawa wajen nan asiri? Ka fa san mamalakin wajen, 


Sergent Kabir da ya shigo da sauri ya zo dan jin me Wardugu zai fada kiran da ya tura nasa ya ja ya tsaya ya sara masa,


Wardugu ya juyo wajensa ya ce" ankwa! 


Da sauri ya mika masa, sannan ya kara ja ya kame,


A bainar jama.a Wardugu ya ja hular kansa ya cire ya nufota ya ce" Madame *MARAHUT AISATA* iko ya kama ki bisa laifin buda gidan badala, yada mugayen ayuka a boye, da siyar da hoda a fili kuma a bayane, ki yi shiru ko dukan abinda kika fada zai yi aiki kan ki, kina da damar tsayar da lauya dan kare kan ki ko kwato incinki.........


Yana fada ne yana sarkafa mata ankwa irin na an kamo barawo, kafi yake turata gaba da kansa ransa bace ,


Suna fitowa ya daga murya ya ce" lasifikha sergent! 


Ai kuwa da gudu aka fita aka kawo masa,


Ana kawowa tuni yan jarida sun halarta sun fara dauka abinsu, 

Wardugu na amsa daidai kunenta yana rike da ita hannunsana dama ya daga, a dake kalamai a rarabe ya ce" Duk wanda ya yi gigin guduwa daga wannan waje zai jawa kansa rigima, zamu saki batkonon tsohuwa (🤣🤪), koda kana da rashin lafia kan ka! Ku hade gaba dayanku tsakiyar wajen nan minti biyar na baku, du wanda bai zo ba tawa ce ni da shi!


Ji kake wajen ya dan lafa da iface iface, nan fa dan koke koken yan matan ya fara tashi,, wasu na dora hannayensu a kai suna ihun sun mutu sun lalace yau asirinsu ya tonu, wasu na kaico da tunanin mai tsaya masu domin dama ba wani abin iyayensu gare su ba , irin sun samu dan masu kudi ne suka zubar da tarbiya aji daraja irin ta ya mace suke bin su ana shan kida, wasu samarin sun sato motar gida ne an zo a more da yan mata haka ta ritsa su, wasu manyan mutane ne masu iyalai a gida suka baro suka dauko wata yar shilar suka zo a cashe, waje dai ya fara daukan kimtsi, waje ya yi tsit sai iza keyarsu ake ana waje da su, 


Murya kasa kasa Aisata ta ce" Wardugu, ka bar ni na kirayi abanka,


Bindigarsa karama ya daure a kugunsa kafin yake turata itama ya yi mota da ita,


A wannan rana Wardugu bai nufi gidan su Alhinayettt ba sai wajen karfe bakwai na dare,


Yana zuwa bai fita a motar su ta sojoji ba kira kawai ya yi suka fito ba tare da ya yiwa kowa magana ba suka duru a motar ya ja, inda Alhinayettt ta bi su da kallo ta koma tana shan dariyar mahaifiyarta na fadin" yau fa akoyta, Alhinayettt yau ana rigima a garinnan, kina ji shiru ? Ba galama basu fara kade kadensu ba


Alhinayettt ta yi dariya ta ce" Anna (Matar babansu ce), ai sai adu.a kawai, Wardugu Wardugu Kowa Wardugu, ni dai zan yi ta yi masa adu.ar Allah ya tsare shi........


Gidan Ayya ya kai su, wace ke zaune tsakar gida da waya a hannunta sai dokawa wardugu kira take aman ba.a dagawa,


Ai tana gannin sun sauko ta nufo wajen su sai dai bai tsaya ba ya yi gagawar juyawa ya fece abinsa, domin ya sani ne yanzu har an fara zuwa wajenta, bayan ta sani shima bai isa ba , shima yana bin dokar ne ! 


Gidansa ya yiwa tsinke,

Nan ya tarar da Mota uku a ciki bayan na kofa da aka hana shiga,

Mita daya dai ta mahaifiyar Walyn ce, biyun ne bai gane ba, dan haka ya shige bangarensa yana haharde kafafuwa yana so ya je ya zauna ya kashe du wata waya dake yi masa kuka a kunne ta hana shi sakat sai doko masa kira ake shi kuwa ba wanda zai daga kiransa domin ba wanda zai saurara, ba tonon asiri ne ya yi niyar yi masu ba, ba huce haushi ne ya yi niyar yi wa mahaifinsa ko matarsa ba, abin ne ya daje shi, ya diro masa a lokacin da bai yi tunani ba, tashin hankalinsa shi ne...ta ina ake shigo da hoda har ta gama gari haka? Ya sani ne sai sun sha masifa fa lauyoyi, inda ya san ya shige gabansu harda dan gidan banban lauya baki daya, in ya yarda ya ce a saki mutane, iyayen yara da manya masu daraja zasu sako shi a gaba ace dan da yaronsa ne ! 


Kansa ya shiga shafawa ya bude bangarensa ya shige ,


Kamar koda yaushe, sansanyen kamshi ne ya taro shi, wannan fa ba.a wasa da shi, 

Agogon hannunsa ya fara kuncewa yana kokarin karasawa cikin dakinsa na baci dan ya samu ya yi wanka,


Wardugu" ta yi kiran sunnansa tana mikewa ta nufo shi, 


Tsayawa ya yi yana kallonta, domin yanzu ya dan saka mata haushinta da yake ji na ta tafi ta bar su wai ba zata hada numfashi da yar gidan Anna ba,


Karasowa ta yi ta shige jikinsa du da yanda yake tarewa,

Murya a kasalance ya ce" Walyn bari na yi wanka , aiki na yi jikina ba tsafta,


Kai ta girgiza ta kara shigewa jikinsa tana rungume shi sosai a jikinta ta ce" baka wari kuwa Wardugu, kamshin turarenka na nan,


A hankali ya raba jikinsa da nata ya ce" aa tsaya na yi wanka, na yi zufa sosai kin ji?

Ya karasa yana mai zaunar da ita saman tsareren bed dinsa mai ruwan zeba,


Bayi ya zarce ya samu ya shige kasan shower, 

Ruwa mai sanyi ya sakarwa kansa a jikinsa dan yana son jin sanyi 

A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin sanyi mai dadi na ratsa shi, 


Sai da ya gama ya yi wanka na kirki ya dauro alwallah ya fito daga bayin , zuwa wannan lokacin har karfe tara ta kusa cikewa,


Yana fitowa , Walyn ta kara nufo shi 


Tsayawa ya yi yana kallon yannayinta, magana ke tafe da ita domin batai masa yannayin tana bukatarsa ba, 

Dan haka ya zarce ya dauko jalabiyarsa ya saka ya dauko salaya ya shinfida yana kokarin tayar da sallah,


Wardugu mana! Ta fada da yannayin damuwa,


Juyowa ya yi yana kallonta bai amsa ba,..

Ta karaso ta ce" su Mamanmu ne fa ke zaune a falona ka fito ku gaisa ,.


Wardugu yana kallonta, mamansu, har wannan lokacin?


Bai bata amsa ba ya tayar da sallarsa, dama dan ya yi shafa.i da wutiri ne,


Zama ta yi har ya karasa, ya zauna ya yi doguwar adu.o.insa na tsari da komai ya mike ya cire rigar daga shi sai gajeran wando ya yi bismillah ya haye bed,


Da mamaki take kallonsa, ranta ne ya baci ta ce" aman baka ji wace nace maka tana jira ba?, 

Domin ta sani ne, yana mugun daraja mahaifiyarya, ko gaisar da ita zai yi sai ya dan duka, aman yanzu ta fada masa ta ga ya wani kwonta abinsa,


Wardugu ta kara kiransa tun karfi,


A fusace ya dago zaune , murya a bace ya ce" ba zan je na gaisar da mamanki ba, na gaji baci nake son yi ki fice mani a daki! 


Ido ta kwalalo tana kallonsa, kafin take juyawa ranta in yayi dubu a bace yake, tana son tsayawa ta ja maganar aman wani abin na hanata, dan kuwa dukan alamu sun nuna idan ta yarda ta kawo masa raini komai na iya faruwa ,


Juyawa ta yi tamkar zata tashi sama ta fita a dakin,


Karamar wayarsa ya bude,


Sheik ibrahim ya danawa kira,


An jima tana ringin kafin yake dagawa da salama,


Wardugu ya gaisar da shi da tambayarsa jama.a,


Sheik ya amsa yana mai tambayar Wardugu Aiki,


Wardugu ya amsa shi a nitse ya ce" Malan, a kara saka mu a adu.a,


Sheik ya yi murmushi ya ce" Wardugu , na ganka a tv, fatan Allah ya tayaka, Allah ya baka ikon yin aikin kirki, sai dai zan kara fada maka, a duniya karka ce sai ka birge kowa, ka yi lamarinka domin Allah, kar ka saka fushi ko gaba dan Allah ya baka dama mai girma ta jan wanda ka yi niya, ka ci gaba da kawar da kanka a kwadayi , sannan ka ci gaba da jan istighfari kana kaiwa allah kukanka ka ji?


Wardugu ya amsa a mutunce sukai salama,


A hankali ya lalubo cazbaharsa fara kar tana ta kanshin turaren  ruwa ya shiga ja daga kwoncen yana ta jan astghfari,



Me mijinki ke takama da shi a duniya Walyn? Ya rasa wa zai rufe sai aban iman? Ko dan yana auren yar yayata ai sai ya daga masa kafa, dan kawai ya kama da shi a wannan wajen, wajen ba na ubansa bane? Zance wajen sunnansa ma gare shi! Me yake tunani? Dan yana sanye da rigar iko shikennan ? Ai idan shine yau gobe ba shi bane zai ringa yiwa mutane rashin mutunci! Tunda haka ta faru muke gidannan aman ya zo ki wani zo ki ce wai ya gaji? Gajiyar kaniyarsa, mu da muke nan bamu gajin bane? To idan mijina ya kwana a cel nima na dauki alkawain sai na tozarta Wardugu sai na saka wardugu ya shiga uku, sai na


Aunty! Walyn ta fada tana daga murya sosai,


Da yatsarta daya ta ce" ke a wa? Wacece ke? Kike ikirarin tozarta Wardugu bayan Allah ya rike? Ke kin san da za.a shige shi da an shige shi ba yau ba Aunty! Wardugu baya zuwa maula, hukunci kuwa idan ya kama zai yiwa ko wani dan buro........ba, meye? Takamarki ki yi masa shari, ki hada shi da malame, ko ki same shi ta hanyar abin duniya?

Ban ce sihiri ba zai kama shi ba domin wanene shi, sai dai na miki alkwarin tunda kika fadi haka , sai dai mu mutu baki daya,! 



Mahaifiyarta ce ta kasheta da mari, rai bace ta ce" kan namiji? Kan namiji zaki ciwa kanwata mutunci? Namijin ne ya kai dan goyo har haka? Ke Wardugun da kafin aurenku ma sai da ya karya maki hannu sau biyu shine kike daga jijiyoyin wuya dan ance za.a taba lafiarsa? Kin manta dan ya kauce ki malaki wannan daula na yarda yake tata maki rashin mutunci? Idan kin canza ra.ayi na sani da wuri dan Ubanki! 


Wakyn dake yashe tun marin magaifiyarta, jikinta a mace, takan mance du wani kudirinsu idan tana tsaye gaban gwarzonta, namiji ne Wardugu, can dama tana sonsa sosai, damuwar kuna tana son kudi sosai! 








     Mu.azam, tashi ka kai ni ya sha maganin bakin nan , 

Ayya ta fada tana nuno masa wani dan kuli wai maganin baki ne dan kar baki ya fada masa


Mu.azam dake zaune kafa tankwashe Agaishat na koyar da shi bakara ya dago da mamaki yana kallo  Ayya,

A hankali ya ce" Ayya, idan muka yarda muka fita a yau fa kama mu za.a yi a rufe, sai karfe takwas na safe za.a tsayar da kamen nan, ki rufa mana asiri Ayya kin j?


Ayya ta zaro ido ta ce" dan ubansa a rufe mun, bafa zai yi baci ba sai ya sha maganin bakin nan yau yanzu yanzu dan haka tashi mu je Mu.azam,


Mu.azam ya mike yana ayyana ta faru ta kare a ransa, dan ya san in dai suka fita titi za.a kama su ne, za.a rufe su, daga shi har Ayya har Agaishat din,



...........to fah🤣🤪🤪🤪🤪✌🏼



🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣7️⃣





Mu.azam ya ce" Ayya, ki bani na je na kai masa, kin ga ko an kama ni kadai ne za.a kama,


Ayya ta ce" yo kai na d'a bane, a hada har mu a rufe, ba yace doka ta hau kowa ba? Na tabata an hada da iyayen mutane a wajen,


Mu.azam kam ya rasa ya zai yi da Ayya , ta kuwa coge kofar daki inda Agaishat ma ta fito tace ba zai yiwu Ayya ta tafi ta barta ba,


Kallon agaishat yake kasa kasa, a hankali ya ce" idan aka rufe ki Agaishana, ba zan iya hakura ba, kar ki biyo mu na roke ki,


Irin na yara ta yi masa da kafadarta irin ta kiya, tama rigayi kowa karasawa wajen motar bayan ta amshi maganin bakin na hannun Ayya,


Haka Mu.azam ya fitar da motar dake da lambar Wardugu, ya dauko carte dinsa ta shaidar shi likita ne, da carte didentité dinsa, 


Fitowa ya yi da motar Ayya ta shige baya ta hakimce, Agaishat ta shiga gaba aman a ranta a tsorace take, tana tsoron sojojin garinnan, daman ba.a saka soja a lamari a niger sai abin ya baci, su fa ba ruwansu hade kowa suke, idan ka yi masu gardama su tataka banza su barka nan zubde tamkar kayan wanki,


Tuki yake zuciyarsa kuwa sai adu.a yake, Agaishat ma adu.ar kawai take inda Ayya ke kara buga lambar wardugu aman a kashe, bata shigama bale a dauka,


Danja na tsayar da su aka haske su da cocila dall a idannuwansu,, gaba da baya sojoji suka zagaye su har mutun uku,


Na kusa da direba ne ya  kwonkwasa kofa,

Mu.azam ya bude yana dubansa,


Mutumen ya ce" motar Gn ce Oga,


Ya ce" eh na gane ai,


Ya ce" malan daga ina , kuma ina zaka je? Wa ka dauko? Sannan ka bude mana bayan mota zamu yi bincike,


Mu.azam ya fara bude masu motar, sannan cikin nutsuwa ya ce" ina tare da mamanmu ne, mahaifiyar Wardugu da kanwarmu Agaishat sai ni kuma amininsa ne, daga gida muka fito zamu je gida wajensa bisa umarnin mamansa,


Menene shaidarka? Sojan ya tambaya ba alamun wasa,


Mu.azam ya mika masa cartocinsa, sannan ya sauke madubin bayan ya dayan ya leka wajen Ayya, 

Kwarai kuwa itace, waye bai san Ayya ba? Mahaifiyar General,


Gaishe da ita ya yi cikin mutuntawa ya ce" yi hakuri mama muna bisa aikin mu ne, ki tabatar mana da abinda ya fada,


Ayya ta ce" eh haka ne, ina son gannin Wardugu me yanzu yanzu,


Sojan ya gyada kai yana kallonta,


Wanda ke bincika cikin motar ya shaida masu ba komai cikin motar, dan haka ya mika masa takardarsa ya basu damar su fice


Cikin ikon Allah haka sukai ta haduwa da sojojin nan suna kara titsiye su , 

Harda wanda bayan dukan bayannan nan yace ai shi bai wani san Ayyar ba a bashi shaidar da ta fi haka,

Nan fa aka sha rigima da kyar masu taya shi suka tsawatar masa ya batsu suka tafi,


Tun abin karfe tara sai kusan sha daya suka karasa gidan Wardugu nanma suka tarar da wani balakin an hana iyayen Walyn fita sai dai su kwana a nan in kuwa suka fita aka kama su toh su suka gano, sun izata sai balaki take kan wardugu ya fito ya raka su ko ya basu shaidar da zata sakasu su tafi har gida lafia,


Suma su Mu.azam sai da aka titsiye su kafin suke samun shiga gidan,


Mu.azam na tsayawa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon hajia rigima, domin Ayya ta hade rai ta yi kicin kicin da fuska tana kallon yanda suke tsatsaye suna ta magana suna tafa hannu suna balaki,


Mu.azam ya ce" Ayya, kar ki kula koya na roke ki,


Ayya ta yi murmushi ta ce" oh yarona, yanzu kai ke yi min gargadin kar na kula kowa, ai ka san bana kula mutumen da bai iya tsawatarwa zuciyarsa ba! 


Bude motar ta yi  ta sauka,


Ai kuwa tunkarar wajensu ta yi direct ba wani tsaye tsaye,


Tana zuwa ta ja ta tsaya itama tana yi masu kallon da suke mata,

Da yake akoy wuta ko.ina haske ya garwaye gidan kowa na gannin kowa ne,

Ayya bata fita sai ta shirya ko fitar da a rikice take ne, dan haka yanzuma sai baza kanshi take, ga lufayarta ta nada mai ruwan ja da baki, ta sha awarwarenta na zinariya,


Walyn ce ta ce" ina yini,


Ayya ta kai dubanta wajenta ta ce" lafia, sannan ta mayar da dubanta wajen iyayen Walyn din tanai masu kallon ido cikin ido,


Mahaifiyar walyn ta miko mata hannu ta ce" Hajaju ne, uwar gidan *MARAHUT*  ke ce da tsakiyar daren nan??


Ayya ta sakar mata murmushi ta mika mata hannun itama ta ce" wa.alaiki salam maman Walyn,  ke ce a gidan Wardugu da wurin nan haka, 


Kanwar maman Walyn ta kali Walyn ta kuma kallon sirikan biyu, ta juya bangaren Walyn tana ayyana taf, lale ana cakwakiya a gidan nan,


Ita kuwa walyn kitson kanta kawai take sosawa, susar da bata san ko ta meye ba, 


Ayya ce ta fara cika hannunta ta kuma kallon Walyn ta ce" Aa, Walyn yaron nan yana nan ne dai ko? Bara na shiga na gani Wardugu sarkin aiki! 


Juyawa ta yi ta nufi bangaren Wardugun cike da isa, sai a lokacin Mu.azam ya lalaba Agaishat ya cire mata tsoro suka fito daga motar,


Mu.azam ruwan sanyi sai ya nufi wajen su dan gaishe su,


Walyn ta daga ta watsar da idannuwanta sannan ta zabgawa Agaishat wata muguwar Harara da kallon kyama ta juya tana riko hannun mamanta suka koma bangarenta,


Agaishat dake dafe da kirjinta jin yanda zuciyarta ke dokawa Mu.azam ya kallo,


Murmushi ya sakar mata ya ce" mu je Matar Mu.azam,


Ido ta zaro kafin take daga kafa da sauri ta yi gaba tana jin wata kunya kunya da wani irin abu game da Mu.azam din, yakan mantar da ita wacece ita ta halin nuna mata itama mutun ce mai cike da cikeken inci, yana yaba kalar fatar jikinta ta hanya kawatata da kalamai masu tsari da sence, yakan ce Allah ya datar da shi samunta, ita Agaishat yar gidan Sofo? Tana so ta biye masa tana tsoron ko wasa yake mata? Tana son ta yarda tana tsoron yan birni,



Ayya na shiga ta zarce har dakinsa na baci tana fadin" ina kake janyau, ka hargitsa mana gari ka lafe a gado, tashi tashi kaima ka yi kwanan zaune dan nema kawai! 


Da wani irin sauri ya mike ya diro ya warci doguwar rigarsa yana faman sakawa ta shiga dakin,


Wardugu ya ce" Ayya, wai yaushe zaki dauna shigo min haka zaraf kawai? Me ya fito da ke a tsohon faren nan? Ya aka yi kika ratso sojawan hanyar nan? Wa ya kawo ki?


Maimakun Ayya ta bashi amsa sai cewa ta yi" baka da sutura a jikinka ne kake kwonciya Wardugu?


Wardugu ya dafe kansa ya furrta" Ya Allah, 


Bakinta ta yatsina ta ce" fito ina jiranka


Sai da ya saka kayansa ya biyo bayanta,


Yana fitowa ya ga Mu.azam, da bakuwar nan ta ayya da shi ba zai iya fadin sunnanta ba dan bai wani rike ba,


Sai dai mamaki yake, yanzuma wasu kayan ne jikinta, shi abinda ke bashi mamaki yaushe ta iya saka kayan tubawa har yake bin jikinta haka? Yaushe ta iya saka kayan kansa nema ? 


Kawar da kansa ya yi da sauri yana yatsina bakinsa yana ayyana ina ruwanka yo, ba dai Ayya ta daure mata ba?


Ayya ta karbi kulin maganinta ta umarci agaishat da ta bude frij dake nan falon ta fauko ruwan roba


Agaishat ta nufi frij tana tambayar kanta ina wajen budewar yake? Domin ba irin na gidan Ayya bane, wannan wani glass nema a jikinsa ko.ina tar tar yake ana hangen abubuwan dake ciki tar sai dai ba lale ka san wajen kunawarsa ba,


Ja ta yi ta tsaya tana kallo, 


Ayya dake jira ta kallo wajenta ta ce" Agaishta kawo mana,


Agaishat ta juyo tana raraba idannu ta ce" Ayya, ina zan bude??


Wardugu ya girgiza kansa, Mu.azam ya mike ya je ya nuna mata ya bude mata, ta nuna masa wanda take tunanin ruwan ne?

Mu.azam ya ce mata" wannan ai jus ne, gidansa da kamarsa yake yannayin ruwa, aman kin ga jerin ruwan nan,


Nan ta dauko suka dawo wajen Ayya dake ta yiwa Wardugu fadan ya kwonta bai ci abinci ba dan ba sai ta tambaya ba ta sani ne kwonciyarsa zai yi, aman kwata kwata bata sako maganar matarsa ba ko iyayenta, bata da wannan lokacin,


Wardugu dai kallonta yake, ta bude ruwa ta tsiyaye fiye da rabi ta zuba maganin ta girgiza ta mika masa ta ce" shanye,


Wardugu ya cee" Ayya meye kuma wannan

?


Ayya ta ce" Wardugu, magannin baki ne, bakin mutane, ka san baki fa ya fi maye mugunta, baki ai ba dan uwa bane, bare yau ka janyowa kanka maganar mutane


Robar ya rike a hannunsa ya ce" Ayya, bayan walahaulan da nake yi kuma dai kin bani wannan jike jiken naki?


Ayya ta ce" walahaula hanyarta daban, wannan ma nasa daban, kai harda garin hantiti nake tafe, maza shanye ka dauko min buta a bayinka na zuba maka ka yo wanka ka turaru sai mu juya,


Ido ya zaro yana kallonta, kafin ya maido dubansa wajen Mu.azam da irin kallon kai ka kawota ko?


Mu.azam ya juyar da kai wajen Agaishat dake zaune kasa yana kallonta, domin kallonta na saka shi nishadi


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣8️⃣


Bani da bakin da zan yi godiya a irin tarin kulawar da kuka nuna, da tashin hankalin da kuka nuna na wannan abin da ya faru, kunya ta kama ni, na ji kunyarku sosai na irin hada ni da Allah da kuka yi, wacece ni? Ni ba kowa bace da zan ki yin hakuri dan haka nake shaida maku ga  *BAK'A* . Daga taku yar mutan niger




Kun yi sake , kuna gani tana zuwa ta shige dan ta samu ganninsa aman mu tun da yama muke zaune, a matsayin mu na iyayen matarsa yace ya gaji ba zai fito ba, kina ganni da takama bayan ta fada mana magana ta shige abinta, 

Auntyn Walyn ke fada ranta na kara baci,


Mahaifiyar Walyn ta ja tsaki , ta ce" koma me take takama da shi ai mijin ya nuna mata iyakarta, yanzu ba da kishiyarta bace yaronta ke fada? Banza ita har ta isa ta nuna ita wata ce? Bayan an ci mata mutunci kowa ya sani?


Walyn dake zaune, gaba daya zuciyarta ke wani irin tashi, ta rasa me ke damunta kwanakin nan takan tsinci kanta a irin yannayin rashin jin dadin jiki, bata iya kara furta masu komai ba ta mike ta je dan ta saka a kara tsaftace masu wajen da zasu kwana, domin ba zata lamunci a rufe iyayenta ba, za.a samu matsala sosai,


Sai da aka sha rigima da Wardugu ya shiga wankan hantitin da Ayya ta jika a butarsa ta karfe,


Yana yin wankan ya fito yana jin yanda yake warin magannin, sai dai yana fitowa ta kuma tare shi da hayakin Hantitin nan yana ta bade shi ,


Jajayen idannuwansa kawai yake binta da su, in ba Ayya ba, wannan uwar gajiyar da ya kwaso ta zo ta tirke shi da wannan abubuwan? ,


Tana gamawa ta fita fallo da hayakin bayan ta debo turaren wutar dake jere saman coiffeuse din dakin tana tafe tana dan sakawa yana tashi a hankali,


Kansa kawai ya girgiza, ya cire jalabiyarsa ya saka rigarsa mai karamin hannun wace ta baiwa jikinsa damar bayanna ya saka wandonsa dogo fari na jalabiya saman gajeran ya fito,


Ayya dake kallon Tv, Mu.azam kuwa sai wani kara shigewa Agaishat yake yanai mata labari kasa kasa, wanin ta zaro dara daran idannuwanta, wanin ta dan yi murmushi, wanin kuwa sai dai ta rufe fuskarta da hannayenta wai kunya take ji, 


Galala ya yi yana kallon kusancinsu da kuma yannayin su, 


Ayya ce ta juyo wajensa , sai dai ranta ne ya baci gannin irin rigar da ya fito da ita, ita kam ya zatai da wannan sakarar dabi.a ta wardugu ta saka kannanun kaya? Sam ba al.adar batuben mutun bace, Batuben mutun yanda mace zata ji kunyar bayannar da jikinta haka shima namijin, sun fi saka manyan kaya sukan yi rawani ko su aza hula saman kansu, suna saka kananun kaya irin na zama aman dogon wando har kasa, riga mai mutunci su yi zanzaro abinsu, aman fa siri batube sai mata nai, shi ya saka take mamakin Wardugu, gatsai gatsai sai ya bi gari da wando daidai gwuiwa, riga mai yankeken hannu har yana wata takama, 


Rai bace da yaren tubanci ta  ce" Wardugu ! Nigey medi nubazzu ? Ay kubu nukoy ? Anna gnuduro indi hadin ?  ( Wardu! damme bakajin magana , wannan wane irin rigane ? Idan mutane suka ganka me zakace?),


Wardugu ya kalli rigar jikin nasa, kansa ya shafa wanda haka kamar ya zame masa jiki, ya juya ya sako wata riga a saman wannan duda haka bai bala boturanta ba,


Yana dawowa ya zauna yana kallon Ayya, 

Ayya ta girgirza kai ta ce" a gaskiya wannan abin sam bai yi ba, kai ba wani karamar kira ba , ka wani saka kananun kaya, yanzu haka a haka sirikanka suka ganka wardugu? Salon a fita da kai a baki ko?


Wardugu ya lumshe idannuwansa ya bude ya ce" basu ganni ba,


Me kake nufi da basu ganka ba?,


Wardugu ya daga kafada ya ce" ai na gaji ne, sai idan na huta Ayya,


Da kallo take binsa, a sanninta yana matukar jin kunyar iyayen matarsa yana darajasu, ko dan irin yanda sirikan namiji keda matukar daraja wajen mijin yarsu a al.adun tubawa, domin kuwa suna da dama sosai a kan mijin yarsu, aman yau yace wai ya gaji bai je ya gaisar da su ba? Ta so ta tsawatar sai kawai ta kyale, domin dai Walyn da Wardugu auren so suka yi, shi bai taba kawo mata karar matarsa ba, itama bata taba kawo masa karar rashin girmamata da Walyn bata yi ba, ai ido ba ma.auni bane abin duba ne, yana gani kuma yana sane, dan haka ta watsar ta mike tana duban Agaishat ta ce" ku tashi mu tafi kar mu kwana a gidan nan kun ji? 


Wardugu ya kaleta yana talabe habarsa, ya ce" Ayya, ai yau sai dai ki yi hakuri da gorin wai kin zo gidana, yau kwana ma zaki yi Ayyar wardugu,


Ayya ta zaro ido tana kallonsa, ta ce" kai, ka rufamini asiri, ni na kwana a gidanka wardugu? Aa aa, ka tashi ka mayar da mu da kanka man,


Wardugu ya dubi Mu.azam ya ce" kai, zaka bado hankalinka nan ne? Bakin karfe dayan dare dokar ba wani karbar uzuri, motocin yan tafiya kawai za.a bari su je masaukinsu, suma sai dai su waye a can, ba zai yiwu ni na karta dokarnan ba Mu.azam zaka saka baki ko sai na ...


Mu.azam ya taso yana dariya ya ce" Ayya, karfe daya saura kadan, ki yi hakuri, mutuncinki, girmanki ya fi karfin ki je cel Ayyarmu, kuma ke ke fadin ya yi aikinsa tsakani da Allah a rayuwa, ki yi hakuri Ayya,


Ayya ta yi shiru tana kallonsu,


Dubanta ta kai wajen Agaishat, ta maido wajen Wardugu, 

Kanta ta girgiza ta mike ta karaso wajen Agaishat ta kama hannunta ta ce" tashi mu je bangaren mata,


Agaishat ta mike tana biye da Ayya,


Mu.azam ya dan yi taku dan raka su Wardugu ya riko hannunsa,


Mu.azam ya dawo da baya ya ce" namiji, bangaren Walyn fa zasu je?


Wardugu ya ce" eh na gani,


Mu.azam ya ce" anya kuwa za.a kwashe lafia?


Wardugu ya yi murmushi, ya maida dubansa wajen Mu.azam da kyau, kallonsa yake yana karantarsa,

A nitse ya ce" me ke damunka da ita? Batai maka kankanta ba? Me ke jan ra.ayinka wajenta? Ko bakin nata?


Mu.azan ya dago da sauri yana kallonsa, Wardugu, yanzu mutun yanzu ba mutun ba,

Mu.azam ya ce" ban gane maganarka ba,

.......

........................


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣9️⃣



Wardugu ya shiga dan shafa sajensa, ya gyada kai ya mike yana dan nuna alamun zan kamaka ne ya yi ciki abinsa


Mu.azam ya bishi da kallo, ya maida kansa yana duban wajen kananun fitilu fararen dake kara kawata dakin,

Murmushi ya yi shima ya lunshe ido a ransa yake ayanna zan so na rayu da ita koda na yini daya ne


Ayya na zuwa bangaren Walyn ta yi salama , ba wani hayaniya ko nuna isa ta ita mahaifiyar mai gidan ta samu waje ta zauna tana duban Walyn ta ce" Walyn muna son daki ni da y'ata , muma kwanan gidanki yau ya kama mu,


Walyn ta mike ta nufi wani dakin ba tare da ta ce komai ba, inda mahaifiyarta kuwa sai ta fara hura hanci ance gidan yarta,


Bata jima ba ta dawo ta ce" ga dakin an gyara Ayya,


Ayya ta mike Agaishatma ta mike suka nufi dakin da aka nuna masu


Suna zuwa Agaishat bayi ta nufa ta dauro alwallah,

Da nadin nan nata ta shinfida darduma ta tayar da sallar nafila domin dare ya yi sosai ya raba, ita kuwa yanzun ta zame mata jiki sai ta yita take iya rintsawa komai dare,


Kuri dai suke zaune suna kallon juna kowa da kudirinsa a kan dan uwansa, ita auntyn walyn mamaki take ashe wardugu har mahaifiyarsa, yo har mahaifiyarsa mana gashi itama dole ta kwana a gidan?



Dare ya raba , karfe biyu da rabi yayi aman wardugu ya kasa rintsawa,


A hankali yake sando ya sauka daga bed din domin nan Mu.azam ya zo ya kwonta bayan sun sha rigimar ba zai kwanar masa a gado ba yace shi kuwa nan zai kwonta,


Yana kokarin fita ya ji muryar mu.azam ya ce" ina zaka je?


Wardugu ya juyo da sauri, ganninsa zaune dare dare saman bed din ya saka shi zabga masa harara ya ja tsaki ya ce" matarka ce ni da zaka wani motsa dan na motsa? Wajen Walyn zan tafi


Mu.azam ya zaro ido ya ce" aman Wardugu baka da mutunci, wajen Walyn fa kace, bayan ka garza rashin mutuncin nan idan walyn ta kaleka komai jarabarka lale lale bata da zuciya! 


Wardugu ya kama haba irin mamakin nan, ya ce" kai aman baka da mutunci, ohk dare ya raba kowa ya samu nutsuwa yana shara baci ni ina nan juye juye sai ta ki kulani dan na bata mata? Da a yau da asuba zan kara aure walahi talahi a masalaci! 


Mu.azam ya zaro ido yana kallo Wardugu ya fice a dakin yana wata irin tafiya na ya kumsa masa haushi,


Kai ya girgiza ya koma kwonciyarsa


Wardugu na shiga bangaren ya tarar da su still nan saman kujeru, Walyn sai gyangyadi take, mahaifiyarta ta fara bacin itama , auntyn kuwa sai dan kada kafa take ,


Dakewa ya yi abinsa ya dan yi gyaran murya irin bai ahigo din nan ba, kafin yake yin salama ciki ciki ya shigo gaba dayansa


Su duka farkawa suka yi, yanzunma ya cire rigar ta sama sai mai karamin hannun hakan ya sa iyayen Walyn din saurin kawar da kansu,


Da idonsa ya yi mata magana, da idonsa ya isar mata da sakonsa kafin yake juyawa ya koma bangarensa,


Yana fita kasa kasa maman Walyn tace" Walyn, mijinki abubuwan da ya tara suna da yawa fa, shi ne rashin mutunci, shine fada, shine rashin kunya! 


Walyn ta lumshe idannuwanta ta mike ta nufi kofa bata ce da ita komai ba


Auntyn walyn da ta kume da haushi itama bata furta su ci kansu ba ta kawar da kanta tana dan kada kafa , niya ne ta yi yau ba zata yi baci a gidan Walyn ba! 



Walyn na zuwa ta yi niyar nufa dakinsa sai dai ji ta yi ya riko hannunta ba tare da ya yi mata magana ba sun nufi dakinsa,


Suna shiga ya shiga kokarin janye zip din doguwar rigarta ta atampa,

Tana tsaye tana kallonsa ya janye ya cire mata tana kallo yake kokarin janta bayi domin mafi yawancin lokuta haka ne ida  zai sadu da ita sai sun je sun salo wanka kafin yake baje kolinsa,


Ja ta yi ta tsaya tana dubansa, kwarai ta so ta kiye masa sai dai ba zata manta wani lokaci da ta ki karbarsa ba irin yanda suka kwashi tsayin lokaci yana daure mata   ba shi ba ita a harkar har sai da ta yi ta fama kafin ya sauko,


Rai a dan dagule ta nuna ai ita ba sai ta yi wanka ba,


Wardugu ya yi kalar tausayi ya ce" walyn wardugu, me yasa ba sai kin yi wanka ba? Kinga jiki da danshi danshi ya fi dadi tabawa😌,


Kanta ta juyar ta shiga kokarin hana kanta garza masa rashin mutunci, a sama take kwarai take tausar kanta kar ta saki hanya ta hanyar karta masa rashin mutunci,


Binsa ta yi suka yo wankan,

Suna fitowa ya jata saman bed domin shima yana so ya yi ya jishi ya saku,


Da sauri sauri ya shiga romancing dinta, sai dai ya lura bata bashi hadin kai domin sai dan zile masa take, hakan ya saka shima ya zo mata kawai kai tsaye wanda hakan na wahalar da ita ainun, idan a dadi suke yakan bita a slow da dabaru ne aman yanzun shima sai ya je ya darza son ransa,


Yana samun nutsuwa ta shiga tura shi, 

A hankali ya dagata yana duban yannayinta

Rai bace ta ce" sai yanzu ka san da anfanina ko? Bayan ka gama wulakantar da ni da iyayena? Wardugu yaushe zan yi daraja a idannuwanka? Yaushe zaka daina wulakantani kai tsaye ? Dan ana fadin kai rigimame ne ai na yi tunanin kana iya zubawa kowa rigimarka banda ni! 


Walyn, 

Ya fada a hankali, kafin yake cin gaba" ki yi hakuri kin ji? Dare ne ki daina daga muryarki, sannan ko ba dare ba na fada maki ki daina magana tun karfi har tana fice tawa amo, mace kike, yar kwalisa ba wai wata kara zube ba, sai da na yarda da class dinki kafin na dauko ki, ki yi aiki da iliminki mana? Nifa ba ni na yi kamen nan ba! Aiki ne , doka ce ta hau du wani mai laifi,

To kawai dan nine sarkin son kai sai na ware mijin auntyn matata?,


Wardugu, kana da ikon warewar, in ka ware ba wanda zai daga maganar , kana da ikon zuwa ka fitar da shi a yanzuma ba wanda ya isa ya ja da maganar,


Wardugu ya tashi zaune, tuni hankalinsa ya fara tashi ya ce" kina nufin in na je na fido shi shikenan nine general Wardugu ba wanda ya isa ya ja da ni?


Walyn ta kale shi ta ce" karya na yi ne?


Wardugu ya girgiza kai ya ce" a niger, a duniya ba wanda ya isa ya zo ya titsiye ni walyn  aman in fa a hanyata ta dawowa daga fido shi na mutu na tarda general din baki daya? Ya zata kare min? Shikennan dan ina tsoron bacin ranki da na iyayenki sai in bata tsakanina da mahalicina? Walyn wasa kike da lamarina, kina aurena aman baki san waye ni ba! Kema kin kwana a cel bare wani tsohon dan kacare! Kin san yana me na kama shi? Tare da wa? Ku kiyaye fitina sai ku zauna lafia walyn tashi ki bar min dakina! 


Rai bace ta diro daga saman bed din ta saka rigarta ta bar pant din  a nan, sai da ta kai kofa ta ce" inma me yake yi shi a bayanne yake yi  wa ya san me wani ke aikatawa da Alhinayettt! 


Tana gama fada ta yi waje da sauri abinta,


Da mamaki ya rakata da kallo, 

Ya so abin ya bata masa rai sai kawai ya yi watsi da shi ya mike yana murmushi ya shiga ya tsaftato jikinta ya dawo falo ya kwonta


Tun karfe bakwai aka farka a gidan Wardugu,


Ayya ta fito da yarta su sai gida,

Mahaifiyar walyn ta fito da kanwarta su mijinsu,


Mu.azam ya fito cikin dakakiyar shadar wardugu sai kanshi yake bazawa,

Walyn na daki tana ramuwar bacin da suka kwana zaune suna masifa da iyayenta,


Agaishat dake zaune jikin Ayya, domin yanda ka san mage haka take, ta lafe jikin Ayya kanta a konce kan cinyar Ayya take hangen yanda Mu.azam ke aika mata da murmushi, ya aske gashin kansa ya yi irin askin nan na samari ya yi kyau abinsa sai daukan ido yake, a baza abubuwan kari a falon na wardugu hakama na walyn,


Takunsa ya shaida fitowarsa,

Tafiya ce yake cikin isa da takama,


Yana fitowa du suka kai dubansu wajensa,


Wani irin faduwar gaba ne ya samu Agaishat, a ranta ta ayana ya salam,


Wardugu ya karasa direct wajen Ayya,


Yana tafe ne yana kallon yarinyar dake kwonce saman cinyar Ayyarsa, wace irin gaisuwa zai yiwa mamansa ne? 


Yana karasowa ya ja ya tsaya, kaki ne jikinsa tun daga hular kansa har takalmansu na sojoji, sababi ne bugagu ne na manya da galolinsa a jiki na shaidar shi din waye,


Gilashin idonsa ya cire ya saka idannuwansa cikin nata,

Wani irin tsam ta ji a gaba daya jikinta hakan ya saka ta kankame hannun Ayya, 


Da ido yake nuna mata ta matsa ya yi hugin din mamarsa , aman Agaishat bata gane ba domin ba.a taba haka da ita ba,


Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya duka ya kai hannunsa ba wani dar ko tsaye tsaye ya kama hannunta ya aniya dagata daga cinyar Ayya, 


Agaishat da ta yi mutuwar kwonce🤣 ta zazaro ido tana kallonsa tartar


A hankali ya bude bakinsa ya busa mata iska wajen idannuwanta ya karasa mikar da ita kafin yake yatsina fuska, 


Ayya dake kallon ikon allah ta ce" kai daina taba min hannun yarinya ita ba irin wannan kawar taka bace! Meye haka zaka hanata hutawa?


Wardugu ya turo baki sai kace wani shagwababe ya duko ya dan yi huging din Ayya, a hankali ya ce" ni ni ne na wajenki kar ki manta Ayyana, ina kwana,


Ayya ta rungume shi itama tana murmushi ta ce" sannu da tashi Wardugu , aman ka ga yarinyata yanzu na fi ji da ita kan ku, ai ku maza ne ,


Ya yi murmushi yana kallon yanda Ayya ke kokarin maido da Agaishat jikinta,


Cika Ayya ya yi ya ce" amini abin kauna,


Mu.azam dake danna waya yana faman blok din yarinyar nan docter, domin ta whatsup sai kuka take masa ta fame shi fa walahi gatannan zuwa nigeriar ta dawo da shi a yi masa aiki, ya dan dagawa Wardugu hannu,


Wardugu ya girgiza kai ya ce" tashi ka ja ku bi bayana na raka ku, aiki ne da ni fa ka sani,


Mikewa ya yi inda su Ayya ma suka fice suka nufi mota ba tare da Wardugu ya koma bangaren walyn ba domin ya san ko ya je wata rigimar ce zasu yi  dan haka ya shige dankareriyar sabuwar rangrover dinsa ya ja gaba su Mu.azam na biyr da shi a baya,


Du inda suka zo gilas kawai yake saukewa ya yi nuni fa yana tare da motar su mu.azam har suka karaso gidan Ayya


Wata mahaukaciyar mota fara ce fake a kofar gidan, suna karasawa mai motar da ya juya keyarsa ya juyo yana kallonsu waya a kage a kunnesa


Datijo ne dogo fari kal, cikin manyan kaya yake ya yi rawani aman ya  bude habarsa, 

Gabansa ne ya yanke ya fadi gannin yaronsa cilo da ya malaka yanda ya fito daga mota ya zama cikenken namiji mai jini a hanci, 


A hankali ya hango matarsa, aminiyarsa, mai kaunarsa , ta fito daga bayan motar daya ta karaso wajen wardugu,


A hankali wardugu ya rike hannayenta yana dubanta cikin ido ya ce " mahaifiyata, ban kama matar Marahut dan na hada ki rigima da shi ko dan daukan fansa ba, ta cancanci kamawar ne, ina rokon ki da kar ki biyewa kowa ciki kuwa harda Marahut! 


Ayya ta rike kuncinsa , ta sakar masa murmushi ta ce" na sani, kaida ba mace ba mai zai saka ka yi aikin mata? Na yarda da kai Wardugu, mahaifinka kai ya zo nema ba ni ba domin ya san wacece ni, ba abinda zai hada shi da ni , ka je aikinka, sai dai ina kara jadada maka ka kiyaye bakin mutane , ka yi aikinka domin Allah , 


Wardu ya gyada kansa ya mayar da ita mota inda tuni mai gadi ya bude mu.azam da ya sada kansa kar Aba Marahut ya gane shi ya ja motar ya shige gidan Ayya


Agaishat dake zaune gaban motar a hankali take hangen Wardugu har ya shige tasa motar ba tare da ya nuna ya ga halitar wani a wajen ba ya tayar ya ja motarsa ya nufi wajen aiki


Murmushi marahut ya yi bayan mai gadi yana kokarin rufe gidan ya dakatar da shi ya tura ya shige daidai Ayya ta fito daga motar, 


Kokarin tafiya take domin ta ga shigowarsa sai dai me, 

Muryarsa ta tsinta , muryarsa mai gigitata, a hankali cikin sanyi ya ce" *asalamu alaiki anmi Wardugu!*


Post a Comment

0 Comments