BAKACE hausa novels 5

 BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣0️⃣




Ido Wardugu ya zaro, ya kai kallonsa kan hannunta wanda ke dauke da dogayen akaifu domin ba wani cire su take son yi ba sai baba sofo ya sakata gaba take yanke akaifunta sai tace nai ai susa take da su, 

Wardugu bai gama tantance meye haka ba ya ji wani irin ihun da ya yi barazanar tarwatsa masa dodon kunne, 

A tare suka juyo wajenta shi da Ayya ......


Ayya cikin yannayin tashin hankali da yaren tubanci ta ce " Wardugu Wardugu tsoro ne take ji  na manta ban fada mata ba, kuma ban riketa ba , mai yiwuwa bata taba ganninsa bama bale ta shiga;


Bak'a da jikinta ke bari gaba daya ta kwalallo idannuwanta, daurin dan kwalin nata ya kunce , hawaye tuni sun kama zarya, ihu kawai take tana ambatan innalilahi wa.ina ilaihi raj.une!


Mutanen dake kusa da su harma wa.inda ke dan nesa da su ne hankalinsu ya fara tashi du aka fara jiyowa wajen su Ayyar da ayyar tambaya da alamun tsoron a fuskokin su....

Daga can kofar masu kula da passenger wata mata mai kulawa da bukatun passenger ta fito da sauri da dan sket dinta, ta sha kwaliya, tana dan sauri tana fadin kowa ya zauna kowa ya kwontar da hankalinsa ba komai bane , sannan tana nufo wajen su wardugu;


Hannunsa ya daga na dama ya shafa sumarsa, a kasan zuciyarsa ayannawa yake wannan wani irin tashin hankali ne?  Shi Wardugu da girmansa da irin yanda duniya ta san shi, shine za.a yiwa taro da yar kauyen nan! Merde! merde! merde! 


Juyowa ya yi wajenta, hannunsa na hagu dake kusa da ita ya saka ya janyota jikinsa, ya sakata a jikinsa da hannun nasa ya karkata fuskarta gefen hannunsa na dama , ya saka hannun nasa na damar ya yiwa bakin nata mai ihu wata damka ...ai kuwa shiru kake ji ba ihu ba di kira da salamcewa sai dan mutsu mutsu wanda shima da ya kara riketa sai laf tamkar ta lafe ne a jikinsa. (WARDUGU kan keta) 


Tambaya matar nan take lafia ? Me ke faruwa??


Wardugu gannin bakuwa ce yar amerika, sai ya ciro carte dinsa da hannun hagu dinsa ya nuna mata mai shaidar ko shi waye, sannan da lebensa ya yi mata nuni da mahaukaciya ce kar ta wani damu........🤔


Ai kuwa ta shiga bada hakuri da iya yi, ta juya ta koma.

 Ayya sai faman ya cika yarinya take aman ya tsareta da ido ya ki yin maganama;


Nauyin da ya ji ta yi ne ya saka shi sasauta rikon, ba.a wani dauki lokaci ba Agaishat ta yi baci sai kace wata  baby, bacin tsoro da tashin hankali, bacin wahala, gashi daman daren jiya ba wani bacin kirki ta yi ba dan tsoro da zulumi,  sai ajiyar zuciya take saukewa du ta goge hawayenta a jikin rigar wardugu.

A hankali wardugu yake kokarin kwontar da ita jikin kujerarta, Ayya ta zabga masa harara ta jinginar da Agaishat a jikinta tana kara tabata dan tabatarwa in ba suma ta yi ba.


Murmushi Wardugu ya yiwa mahaifiyarsa na alamun bada hakuri kafin ya jingina yana duba agogon hannunsa domin tafiar idan Allah ya yarda ba wata mai tsayi bace a jirgi tsakannin Agadez da Niamey.


Allah ya sauke su lafia, Wardugu da kansa ya tuka motar da ya je da ita ya ajiye aeroport ,

Bai zame ko.ina ba sai gidan Ayya.


Suna zuwa Ayya ta yi hamdallah ta kamo Hannun Bak'a wace ke kallo da baki da hanci da ido gaba daya


Fitar da ita ta yi ta ce" mu tafi yar gidan Ayyarta


A hankali ta fito itama kamar yanda Ayya ta koya mata ta bi bayan Ayya tana waiwayen Wardugu da ya fitar da kafarsa guda waje yana ta faman yamutsa gashin kansa, wayarsa ya ciro yar karama ya dannawa abokinsa kira wato docter DOCTER MU.AZAM


Yana dagawa ya ce" Ranka ya dade oga *Wardugu Marahut* 


Wardugu ya ja tsaki ya ce" Mu.azam ni za ka yiwa rashin mutunci? Yaushe ka fara karya?


Mu.azam ya yi shiru, ......tamkarma ya kashe kiran.


Wardugu ya duba ya ga kiran na tafia, ya kara karawa a kunnensa ya ce" kai! 


Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya ya ce" abokina, ka yi hakuri ka ji? Jikina ne ya tashi aman yau nake fita asibiti in sha Allah da na huta sai na kamo hanya.


Wardugu da ya gama jin abinda ya fada, cikin mutuwar jikin da bai san ko na meye ba ya ce" me ke damun ka ne harda kwonciya hopital? (HOSPITAL) 


Mu.azam dake kallon karin ruwan da aka saka masa ya lumshe idannuwansa, jiki a mace ya ce" idan Allah ya kawo ni zan fada maka koma menene,


Wardugu ya sauke ajiyar zuciya, bai bashi amsa ba ya katse kiran ya rufo motar ya tayar dan ya samu ya karasa gidansa ya huta 


..........................


                        TIMIYA



Rana ce, karfe biyu na rana ne, aman da dan lulumi kamar yanda garin ya saba, 

A kasan innuwa suke zaune su uku suna yamutsa garin kwakwi da mai da yaji da manda (gishiri), 

Fatimata ce mai kwadawar, Ayya na yiwa maryama susa a kanta


Mariama ce ta dago ta ce" Fatimata kar ki hade yajin nan duka ki ware min a robar nan kuma kar ki zuba mai iya shi din sai mandan ya isa kin ji?


Fatimata ta amsata da kai, Ayya dake mata susa kuwa a ranta take tambayar kanta Mariama ko ta daina cin yaji ne? Kai ina Mariama da yaji ai akoy amana.


Fatimata na gama warewa, Maryama ta mike ta dauki dankwalinta ta daura, ta dauki robar ta nufi wajen tulun Anna kwaya biyu dake cike da ruwa ta dauki guda ta dora saman kanta ta kama hanyar fita,

Kallonta suke da mamaki, Fatimata ta ce" Mariama ina zaki tafi kuma? Ki bari mu ci mana.


Mariama ta juyo ta ce" ki ware min nawa, zan je wajen Sofon nan na Agaishat na dubo shi ne,


Murmushin da Anna ta jima bata yi ba ta saki, sanyi ta ji a ranta daman tana ta tunaninsa halin da yake ciki mutumen kirki


Mariama oga kennan, Mariama ba daukan raina,

Bata zame ko.ina ba sai majalisar mahaifinta,

Tana zuwa ta mika masa hannu ba alamar wasa ta ce" kudi nake so Aba,


Bakinsa ya yatsina, Mariama fa ta fara isarsa da wannan ya bata ya batan, tunda ya karbi kudin aurenta take tatikarsa, idan ya nuna ba zai bada ba kuwa a ji su, 

Rai bace ya saka hannunsa a aljihun rigarsa ya ciro dala dari ya mika mata a ransa yana adu.ar Allah ya sa ta karba kar ta ce ta yi mata kadan! 


Karba ta yi ta maida tulunta da robar saman kanta ta juya ta nufi gidan mai goro....

Nan ta sayi goro har na dala Ashirin, ta sayi man zafi na ciwon jiki ta sayi yar tsintsiya, dauka ta yi ta nufi runfar baba Sofo.


Tana zuwa ta yi salama har sau biyu kafin take jiyo muryarsa can kasa yana amsawa;

Shiga ta yi tana wara idannuwanta dan ganni da kyau domin ta biyo rana idannuwan nata duhu suke ganni.


Yana kwonce fuskarsa na dubinta, ya takure ya kara yamutsewa da cazbaharsa yana ja kuwa,


Bata yi masa magana ba ta karasa inda ta ga tulun ta jawo ta fitar da shi ta wanke shi tas ta juye ruwan nan na cikin tulun Anna, 


Ledojin da suka shihigo da kararuwa ta tatare ta fitar kafin take juyowa ta shiga share bukar inda baba sofo ya samu ya zauna yana binta da kallo da mamaki a kasan zuciyarsa; wannan ai yayar Agaishat ce, mai fadan nan, ikon Allah kawai yake fadi a kasan zuciyarsa.


Tana gamawa ta dauko robar abincin ta debo ruwa ta dawo ta darwaye hannunta ta zauna, ruwan nan ta kara yayafawa garin dan ya kara yin laushi sosai, tana yi bata ko kallonsa dan ta yi imanin ya tsareta da ido ne,............

Sai da ta kai bakinta ta ji idan mutun yace tsotsama zai yi tsaf zai tsotse abinsa ta dago da dubanta a hankali ta kai wajen baba Sofon dake kallonta ta ce"""


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣1⃣






Ta ce" ga abinci, ina magurjinka? 


Hannunsa dake dan rawa ya saka ya fitar da magurjin ya mika mata yana kallonta dai,

Mikewa ta yi ta wanko magurjin da goron, sannan ta dauko wata yar roba mai marfi da ta amso wajen mai siyar da goro ta kara darwayeta itama, ta dawo ta zauna ta saka yar farar leda a kasan abin gurzawar ta shiga gurza goron nan manya har uku; 


Robar ya saka hannunsa ya janyo, bismillah ya yi har zai fara ci maganar Bak'a ta dawo masa inda take cewa < ka ringa wanke hannunka Sofo, ka ga jiki na iya daukan dati mai yawa banda ciki ka ji sofona? >


Dubansa ya kai wajen Mariama, a hankali ya ce" Mariama?


Dagowa ta yi tana dubansa bata amsa ba,


Baba tsoho ya ce" ina kwana,


Mariama ta kifta idannuwanta ba wani dar ta ce" Lafia, still tana kallonsa


Murmushi ya yi ya yi mata nuni da kofin ruwan dake hannunta sannan ya nuna mata hannayensa.


Tasowa ta yi ta karasa, dukawa ta yi ta kamo hannun nasa ta wanke masa da kanta sannan ta kuma ciko kofin ta ajiye masa ta koma ta ci gaba da gurza goron ba tare da ta furta masa kalma daya ba.


A hankali baba ya fara cin garin nan, yana ci yana dan kallon yannayin Mariama, Mariama ikon Allah, Mariama mai albarka, 

A hankali ya ce" nima ina jin rashinta sosai, 


Mariama ta dago kanta ta zuba masa ido, murya a cinkushe ta ce" dan me ka rabata da danginta?


Sai da baba Tsoho ya hadiye wanda yake dan tsotsa a hankali ya dan kurbi ruwa ya ce" dan ta rayu cikin nutsuwa, ta samu inci kafin ta yi kaura zuwa lahira


Mariama ta ce" a wajen danginta, a kusa da mahaifiyarta ta fi samun inci Sofo! 


Idannuwansa ya dan lumshe kafin yake budewa ya ce" ta yaya? Ta hanyar ta kare rayuwarta a bakin titi? Ita ko arzikin mazan zamanin ta kasa samu idan sun shigo gari da gari dan jar fatar yayanmu ne da gashi da kyau! Ba ruwansu da tarbiya, usuli , da halaya! Burinsu shine au samu iri mai kyau ....bayan su kansu idan suka kalli kansu a madubi zasu gane cewa a da ba haka Allah ya halice su ba, kwonci tashi kuma fatarsu sai ta dawo irin tawa idan Allah ya nufa masu tsayin rai ne, 


Su da ka hadata da su din kana da tabacin a inda zasu kaita ba.a kyamar bakar fata? Mariama ta maido masa da amsa du a hargitse da yannayin bacin rai tamkar a lokacin ne za.a tafi da Bak'a,


Baba tsofo ya ce" birni da kike ji ana fadi, wata duniya ce a cikib duniyarmu mai cike da abubuwan al.ajabi, 

A birni mutane basu da lokacin dan kina da fata baka ko dan kina da muni ya kasance du idan kin zo waje za.ana kwagirar ki ko a hantare ki! Sannan birnu cike take da mutanen da kwakwaluwarki ba zata iya hasaso maki ba, idan wani ya tsana wani zai so.......Mariama, ku yi hakuri.


Kanta ta mayar ta ci gaba da aikinta, tana gamawa ta ware masa wanda zai ci a lokacin sannan ta zuba masa sauran ta kai kusa da dardumarsa ta ajiye masa ta ajiye tsintsiyar a gefe, ta fitar da sauran canjin kudin ta ajiye saman dardumar ta dauki robar Anna da tulunta ta juya,

Har ta fita ta dawo ta duka kusa da shi kanta a kasa da yaren buzancinta ta ce" ta kasance abokiyar fadana, wace idan na tashi itace kanwata ita nake cin zali, takan kwaso kayana ta wanke min, idan dare ya yi can tsakiyar dare in na je juyawa sai in jita nanake da jikina, sai in rungumeta sosai a jikina ita da marigayiya, sai gashi lokaci guda a cikin kwana goma na rasa su! su duka biyu, ita wace ta rasu ina binta da adu.a baba  wace kuwa take raye inai mata adu.a sannan zan yi iya yina dan gannin na kyautatawa wa.inda take so take kyautatawa, haushinku nake ji ku duka har Annar! 


Tana gama fada ta mike ta yi gaba abinta .


Baba sofo ya yi murmushi har cikin ransa ya ji dadin haka, ashe dai Mariama na tare da ikon allah, Mariama kennan Allah ya sa ranar da zaki hadu da yar uwarki ki bini da adu.a koda na mutu.




                       NIAMEY


              Doguwar riga fara kar ce a jikinta mai siririn hannu aman tsayinta har kasa, irin mai laushin nan ce bata da kwaliya ko das ta tafi ne ta bi tsarin halitar jikinta, 

Kamshi take bazawa du inda ta gota sai fai fuskarta ta cabe da hawaye tana biye da shi, 

Murya a raunane ta ce" WARDUGU, nice ya dace na yi fushi irin yanda ka wulakantani, ka banzatar da ni a cikin duhu a garin da ba nawa ba , a garin da na je dominka, ka fice ka barni, sannan da safe da ka dawo ko ka kali motar da ka bar ni a ciki, ka yi tafiarka wajen mamanka ni kuwa ko oho! Shine dan na tafi zaka dauki zafi da ni haka? 


Wardugu da ya gama saka mabalin rigarsa ya juyo ya kare mata kallo, a ransa ya ayyana '''''rainin hankali kennan, ta dawo daga tafiarta wace ta isa da kanta , shine aka sha karamar riga aka sha wankan turare aka zo ni ga maye ga mai jira aka kawo min na karbe ko? 


Murmushi ya sakar mata kafin yake binta da wani mugun kallo irin na rainin nan, ya dauki yar karamar wayarsa ya bar ta chating din nan ya dauki ky din mota domin garin da hadari hadari baya son ruwa ya foke shi yau, ya fice ba tare da ya furta mata ci kanki ba;



Da kallo ta bi shi kafin take zama bakin bed din tana shafe idannuwanta, bakinta ta zumburo a fili ta furta" zaka sauko ne, haka kawai ka wani hada ni shakar numfashin wannan uwar taka harda wata karin malatin? Naki din wardugu! Na ki na shirya da mamanka duda baka tambaye ni ba na san hakan kake so sai dai ni a gaskiya ba zan iya jure mulkinta ba sai kaceatar wani sarki dan tana uwar General! ........hum


Wardugu bai zame ko.ina ba sai aeroport, yana zuwa ya ajiye motarsa ya shige ta wajen sojojin dake tsaron kofar bayan sun sara masa ya shige ciki ya haye wajen tarban baki


Bai kai ga karasawa ba ya ji muryarsa ya ce" mek (men), 


Juyowa ya yi, arba ya yi da amininsa, abokinsa, Mu.azam zaune saman kujera, gilas a idannuwansa ya saka costume kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai sheki take.....sai dai abinda bai masa ba irin yanda ya rame

Yana kallonsa har ya karaso inda Mu.azam ya mike tsaye yana murmushi ya bude hannayensa irin ya zo ya rungume shi ,


Ido Wardugu ya zaro ya nuno shi da yatsa ya ce" kai ko?


Mu.azam ya saki dariya yana kara kure Wardugu da kallon yaushe rabo ya mika masa hannu ya ce" Asalamu alaika amini


Wardugu ya karbi musabaharsa yana mai furta" amen wa.alaika salam amini,


Murmushi suka yi kafin suke gaisuwar larabawa, 

Wardugu ya yatsina fuska ya ce" kai dai ka cika naci, gaisuwar nan ta wani runguma ba wani sonta nake ba aman sai ka wani damki mutun kato da kai!


Mu.azam ya bushe da dariya yana biye da shi inda soja guda ya karbi jakar Mu.azam dake hannun wardugu ya shiga ja har wajen mota ya bude ya saka masu ya juya bakin aikinsa,


Wardugu ke jan motar yana dan kallon Mu.azam jifa jifa, a kasan zuciyarsa yana tare da damuwa na abubuwan da ya gani a tatare da Mu.azam wannan zuwan, ya rage magana, ya rage fara.a, ga dan cazbi a hannunsa yana dan dadanawa, ga rama da ya tafka ta mamaki sai dai fatarsa ta gyaru ta yi fresh aman ba alamun yana jin dadin rayuwa.....


 Haka har suka karasa gidan Ayya wada rabonsa da gidan kwana hudu kennan tunda ya kawo su bai samu aiki ya barshi ya zo ba , aman ita Ayyar ta ue har wajen aikin ta amshi carte dinsa ta banki wai zasu je shopping ita da sabuwar yarta, ya yi murmushi da ya tuna irin kudin da suka kaso, Ayyarsa uwarsa Ayya manya.......



Zaune Ayya take saman kujera tana kallon yanda Agaishat ke dan turo baki tana kallon Ayyar da yannayin abin tausayi, 

Daga ita dai gajeran wando da yar rigar da Ayya ta yi mata jan ido kafin ta yarda ta zauna da su dan ta shafa mata gomage a jikinta da fuskarta tamkar amarya, gefe hijab dinta ne baki dan kar kalar abin madarar ya bata hijab din Ayya ta dauko ko dan idan an yi baki, wani irin kulawa Ayya take baiwa Agaishat (Bak'a), kudi ta kashe na mamaki wajen siyen mayuka masu gyara fata ba canza kalar fata ba, sannan ta shiga kasuwa da kanta tare da Agaishat tana nununa mata abubuwa nasu na tubawa na gyaran jiki ta kwaso itacen magarya ta kwaso kayan gyaran jiki suka dawo gida, wata irin shakuwa ce ta shiga tsakannin Ayya da Agaishat, domin Ayya wayayiyar mace ce  ta yo anfani da irin yanda ta waye ta ja Agaishat a jiki tun tana tsoro tana baya baya har ya zamana sun shaku tana dora kanta saman cinyar Ayya ta yi baci ba tare da wani dar ba. 


Yauma sun tashi da niyar yin gyaran jikin ne, Ayya ta dadaure mata gashinta da abin nan na saloon wanda idan an wanke kai ake sakawa a dadaure gashi da shi dan ya nanade ya bushe, ta kwaba abin gyaran jikin nan  ta samu ta shafa mata ta yi mata hayakin mai mugun zafi wanda fuska kawai ake fitarwa, tana gamawa ta sakata ta yi wanka ta shafa mata na madarar nan suka zauna a fali sunna kallo aman ta hanata magana dan kar na fuskar ya saka fuskar ta yakune........


Mai gadi ne ya fara shigowa da jaka, Wardugu na biye da shi sai Mu.azam wa.inda shigowarsu ne ya ankarar da Ayya ta warci hijab din Agaishat ta ......


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣2️⃣







Da sauri Ayya ta samu ta rufa mata hijab din inda Bak'a ta yi mutuwar zaune a ranta tana ayana Ayya wayo daman sai da na fada maki Ayya ...........


Karasowa suka yi, Mu.azan na kallon inda aka rufe da hijab yana son sannin ko waye, 

Wardugu kuwa kallo daya ya yiwa wajen ya kawar da kai a ransa fadi yake" me Ayya ke son yiwa fatar nan da ta rine?


Da murna Ayya take kwalawa mai aikinta kira da ta zo ta dauke akwatin Mu.azam sannan ta kawo masa tarba,

Ayya ta tarbo shi tana murna ta kamo shi ta zaunar da shi sai murmushi take tana kallonsa ta ce" yarona, yaushe gamo?


Mu.azam dake jin wata nutsuwa na saukar masa ya dube duba irin na mahaifiya, a hankali ya duka kasa ya ce" Ayyana ina yini


Ayya ta kuma kamo shi ta tayar da shi tana kallonsa,  yannayinta ya fara canzawa ta kai hannunta wajen wuyansa ta ce" me ke damunka? Ya haka ka rame har haka? Ko dai ka je ka sakawa kanka ayuka ba hutu ne??


Dariya ya saki yana kallon  Ayya , kafin yake maida dubansa wajen Wardugu ya ce" freind Ayyana har yanzu akoy yannayin nan?


Wardugu ya yi dan murmushi yana kallon su,


Ayya ta yatsina fuska ta ce" ba wani nan, yanzu tashi ka je ka yi wanka ka fito zan fara yi maka dura ne tunda abin haka ne! 


Yana dariya ya mike ya kalli Wardugu ya ce" mu je ko?


Wardugu ya gala masa harara ya ce" a matsayin matarka ko dan jagorarka? 


Mu.azam ya yi murmusho yana ji a cikin ransa ya yi missing din abokinsa da mahaifiyar abokin nasa,

Juyawa ya yi ya nufi dakin da ake sauke shi wanda yake a matsayin nasa,


Ayya ce ta dubi wardugu, da idannuwanta ta yi masa nuni da ya tashi mana shima baya gannin mutun?


Wardugu ya daga kafadu ya ki tashin yama mayar da dubansa wajen tv inda ya dauki commande ya canza tasha ya kai Canal plus sport ya shiga kallon ball.


Ji take ta fara gumi , ga kuma ta kage a yannayin zaman nata, ba.a jima ba Mu.azam ya dawo daga wankan da ya tafi ya zu suka kara kasancewa mutun biyu maza kennan,


Ayya ta tashi da yannayin jin haushi ta dunguri kan Wardugu ta ce" ta yi maka kyau! 


Wajen Agaishat ta karaso ta kamata ta mike kafarta ta yi mata tsami sosai, ta samu ta saka mata hijab din ta ce" je ki yi wanka  Agaishat ki sauko mu ci abinci .


Da toh ta amsa ta bi ta bayan kujerun ba tare da ta gaisar da su Wardugu ba,


Mu.azam da ayar tambaya ya kallo Ayya, bai yi nauyin baki ba ya ce" Ayya ina kika samo wannan?


Ayya ta karasa kusa da su sosai ta zuba jus ta mika masa shima kamar yanda ta mikawa Wardugu ta ce" Me ke damunka tukunnan yarona??


Mu.azam ya shiga dan sosa bayan keyarsa, ya kallo wajen Wardugu, ya kuma kalli Ayya.


Haka kawai wardugu ya ji gabansa ya fadi, shima kure shi da kallon yake kafin ya ajiye yar wayar dake hannun nasa ya zuba masa ido,


Murmushin dai ya kara yi masu, ya ce" na yi rashin lafia ne Ayya, kuma yanzu alhamdulilah na samu sauki,


Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" na tsorata da yannayinka, ka wani rame, ba komai haka ne idan jiki ya tabu sai a hankali  aman yanzu ka zo kennan sai na ga yarona ya koma yanda yake da koma ya fi haka kafin ka bar gidannan,


Wardugu dake kallonsa ya shafa kansa shima  kwata kwata bai yarda da maganar Mu.azam ba! Kai haba a irin yanda suka san juna Mu.azam ba zai layance masa ba


Mikewa ya yi ya nufi kofa da wayarsa a hannu inda suka bi shi da kallo, 

Mu.azam ya ce" Ayya ya tafi fa kennan??



Ayya ta daga kafadunta ta dan yatsina fuska ta ce " ya gaishe su!


Mu.azam ya yi dariya yana kallonta, a ransa kuwa dadi yake ji yannayin, kai yana jin dadin zama da su, Wardugu rikitace, mahaifiyarsa ta iya zama da shi, ta kai ta kawo ne idan tama da bukatar ganninsa a wayarsa ya yi mata activen localization, du inda yake idan ta shiga nema za.a nuna mata kawai sai dai ya ganta kuma sam baya gigin kashewa doka ce!


Suna tsaka da tataunawa mai aikin Ayya ta shinfida ledar cin abinci ta kawo abincin ta ajiye, ta kawo kayan zubawa da na sha, ta kawo su jus na gida da Ayya ke yin abinta da kanta ta saka a frij du ta ajiye, Ayya ta umarci Mu.azam da ya sauko bara ta dubo yarta.....


Wardugu ya dawo, bayansa *ALHINAYET* kawarsa ce ke biye da shi,


Salama ta yi ta shigo dakin inda Ayya ta tsaya ta saki baki tana kallon Wardugu da Alhinayet din,


Alhinayett na zuwa ta shiga gaisar da Ayya cikin yannayin ladabi da mutunta mutun,


Ayya ta dan kebe baki, ta amsata ta juya dan dubo Bak'a


Mu.azam dake zaune ta juyo ta dafe habarta ta ce" su likitoci ne a garin namu???


Mu.azam ya sakar mata murmushi ya ce" lauya, lauya, lauya mai kunce mai laifi , zamani lauya iko, lauya mai saka kato ya duka,


Kai ta dafe ta ce" wace ni, rufani ka sayani, ai ba dan an san ni aminiyar *Aboki* bace da an fige ni a Niger!


Mu.azam ya ce" kai ai rigimama ta san waye *Oga*


Wardugu ya girgiza kai yana zama ya ce" *ALHIN* ki zauna mu hau wannan abubuwan kafin ku ci gaba da kirar da kuka koya!


Alhinayettt ta je kusa da Wardugu ta zauna tana fadin" General ka duba lamarin nan je ten conjure................(plz)


Wardugu ya kaleta zai yi magana sai ga Ayya ta dawo da Agaishat,

Doguwar riga simple irin ta zaman gida ce Ayya ta bata, bayan ta saka ayya ta bata Dan kwalin rigar nufin ta yane kanta sai dai suka hau rigima kan aa dan Allah ta bata hijab,


Gannin sai su bata lokaci ne ya saka Ayyar bata hijab ta zumbula suka sauko,


Sai a lokacin Agaishat ta duka ta ce" ina yinin ku, 


Alhinayettt da Mu.azam ne suka amsa inda Wardugu ya kebe bakinsa bai wani amsa ba aman yana yi mata kallon tsaf, a ransa yake ayyana black, but ko a baki  *BUZU MAI KYAU NE* 😂😂😂😂🤪😜😜😜😜😜😜😜😜😜🤪🤪🤪  na fada a zo a dake ni🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐





May be 23......zuwa dare in sha allah, idan comment ya birge ni😄😁😆😅😂🤣


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣3️⃣



Waje Ayya ta samu ta zauna , nan Agaishat ta je kusa da ita sosai itama ta zauna ya kasance an saka baban plateau din a tsakiya,


Ayya ce ta bude inda abincin yake, tuwon tsaki ne da miyar kubewa wace aka yita da naman shanu ta sha dadawa da kayan miya 😋..ga kuma man shanu na kirki a gefe, 

Sai su fruits da aka hi masu yanka mai kyau aka sasaka cikin plat plat, sai jus da ruwa,


A hankali Ayya ta dauko abincin, Agaishat ta dauko abin zubawa, 

Cikin wannan banban plateau din Ayya ta zuba abincin ta daidaita miyar, ka.ida ne in dai ka zo gidan Ayya daidai cin abinci bata raba assiete, sai dai a hadu a ci a abu guda .......


Bayan ta zuba ta kare Agaishat ta kawo abin wanoe hannu da kuma cokula a wata yar roba,


Gaba dayansu cokulan suka dauka banda Agaishat da Ayya , hannayensu suka wanke ....


Ayya ce ta fara saka hannunta, sai Wardugu, sai Mu.azam, sai Alhinayettt, sannan Agaishat dake karamar cikinsu, hakane gidan Ayya baba ke fara saka hannu cikin kwanon cin abinci sannan yaro ke rike kwanon dan kar ya ringa yawo, ba.a magana idan ana cin abinci, ba.a dane danen waya, ba.a wani kale kale sai an gama, sannan bata yarda ana tsaka da cin abinci ana shan ruwa ko jus, sai an gama ake sha,   sannan ana cin abinci daidai ne ba.a matsawa ciki a yi mugun koshi, lamarin gidan Ayya sai yayanta (🤣),


Abincin nan ake ci cikin nutsuwa, Alhinayettt ta kure Agaishat da kallo, sam batai mata kama da tubawa ba, sannan ba bahausa bace ko daya  duda hijabin dake kanta gaban goshinta lufluf yake kwonce da gashi, girartama wani irin gazar gazar da ita, du bakinta lebenta haske ne da shi tas tas, ga girar ido ga manyan idannu, wannan cikin biyu daya ce ko bakar balaraba ko bakar buzuwa! 


Alhinayettt dai ba wani yawan zuwa gidan Ayya ba take ba, sukan hadunsu ne da wardugu a wani wajen, yanzuma zuwa ta yi da rigimarsu ta kansu wace ta zo su yi kan irin yanda ake cece ku ce a gari na matarsama idan ta cika dare kwanan cel take bare wani banza!


Alhinayettt kwata kwata ta manta zancen ba.a magana idan ana cin abinci gidan Ayya  dan haka ta kali Agaishat da kyau, haka kawai ta yi niyar yi mata magana da buzanci dan ta gaskata zatonta, 

*ABZIN?* , ta fada tana kallon agaishat,


Agaishat da ta hadiye abinci ta kaleta itama, itama ta so ta ayanna hakan cewa wannan buzuwa ce, gannin yannayinta sai  dai bata fadi ba dan ba wajen fadin bane, 

Ai kuwa Agaishat ta washe baki itama da yaren buzancin ta maida mata cewa" eh , ke fa??


Alhinayettt zata maida mata maganar Wardugu ya tsimki hannunta na dama dake kusa da shi, sannan ya zabgawa Agaishat wata muguwar harara wace ta sakata sada kanta hannunta na rawa rawa, 


Ayya yatsina fuska ta yi bata yi magana ba, 

Sai da aka gama mai aiki ta shiga kwashewa, Agaishat na tayata kaiwa komai wajensa ta dawo ta zauna kasa kusa da kafar Ayya,


Wardugu ne ke kallon wayar Alhinayet tana nuna masa hotunnan birthday dinta da ta yi baya nan yana dan murmushi kasa kasa ya ce" Alhinayettt , ina tunanin kin girma ashe dai na daina tunanin nan?


Alhinayettt ta yi dariya ta dora hannunta saman nasa ta ce" na baka ka sha? (Irin su taba zata bashi wani labarin) 


Ai kuwa Wardugu ya dan cafke hannunta yana sauraronta, inda ya bata hankalinsa suna ta hirar su,


Ayya ce ta dan ja tsaki, ta girgiza kai tana kallon Mu.azam ta ce" kana ji? Zamani ya zo mana da abubuwan mamaki, sai ka ga mace na tafawa da namiji, tana raba jikinta da nasa wai a zuwan mutunci kawarsa, !  


Mu.azam ya zaro ido yana kallon Ayya, a fili kuwa ya furta" Lah, yana dafe bakinsa,


Wardugu da ya gama jin komai ya saki murmushi yana kallon Ayya, ya ce" Ayya, qna abota mace da namiji, abota sak ba wani soyaya ba kuwa,


Ayya ta juyo bangaren su a takaice , daman jira take wani abin ya hada su ta ce" wardugu ba abota ba dai yayan awaki! Nace yayan awaki, Ke yanzu Alhinayettt kike ko wa? Aman ke marainiya ce ko? Ina nufin mahaifiyarki ta rasu?


Alhinayettt dake kallon Ayya a dan tsorace ta ce" Aa Ayya,


Ayya ta dafe habarta ta ce" Toh abin mamaki, aman ita baku rainata kamar yanda kuka rainani ba ko? Ina nufin Wardugu baya zuwa gidan ku a matsayin aboki sai saurayi?


A tare suka kalli juna Alhinayettt da Wardugu, suka maida dubansu wajen Ayya, 


Ayya ta ce" to in ba haka ba, ya za.a yi ni ina mahaifiyarki , kato ya ringa zuwa wajenki a matsayin aboki kuma na zuba ido yarinya kin kai kin kawo min a gida? 


Wardugu ya shiga gyada kai yana kallon mahaifiyarsa, ta jima tana son aikata wannan aika aikar wa zumuncinsa da Alhinayettt, yau dai ta yi hankalinta sai ya kwonta kuma ko? 


Ayya kamar zugata ake sai magangannunta take son ranta karshe ta ce" to ni ba tsohuwar banza bace, in sonta kake ka fito a mutun ka fada ku daina boyewa Allah kadai ya san tsakanin ku! Dan haka tun wuri a fasa daukana a wata marar ilimi ana ce min wai kawa! Aa abokiyar tagwaitakarka ce Wardugu!  


Wardugu kallon Ayya kawai yake, inda Alhinayettt ta dan sada kanta kasa, a ranta ayannawa take ita bata ga laifin zumunci da suke da Wardugu ba, walahi da soyaya suke da ba haka ba, kwata kwata ba wani zance wai shi soyaya tsakaninsu, haka kawai Allah ya hada jininsu suke mutunci, Wardugu bashi da shamaki a gidan su, hakama saurayinta wanda zasu yi aure suna mutunci da Wardugu, aman haka ne itama kakarta ta sakawa zumuncinsu ido har sun mayar da ita tamkar mahaukaciya domin idan sun ga zata fice sai su shiga magana kasa kasa da yaren french ai kuwa ta kama zage zage tana fadin ita za.a munafinta? Toh gashi itama maman Wardugu kallon masu soyaya take masu bayan ita koda bindiga ba zata iya soyaya da wardugu ba domin ta san waye shi, Wardugu dan yana son ki ba zai hana ya yi maki dukan mutuwa ba, dan yana son ki baki fi hukunci a wajensa a gaban koma waye ba, hum soyayama da wardugu ai tashin hankali ce, ita mai ya kaita? Ta fi son namiji marar rigima mai bata damar ta yi rayuwarta cikin aminci........


Wardugu dake kallon Ayya tar, ya maida dubansa wajen Mu.azam ya ga sai gumtse dariya yake, 

Kansa ya girgiza ya maido dubansa wajen Ayya, da hannunsa na dama ya daga ya sara mata, sannan ya yi mata nuni da ta ci wasanfa , ta more abinta, 

Hannunsa na hagu ya mikawa Alhinayettt ta mike itama ya ja hannunta tana waiwaye tana so ta yi hira da agaishat aman ya jata kiiii sukai waje


Kusan motarta suka tsaya, 

Alhinayettt bata bi ta kan fadan Ayya ba, bata nuna damuwarta ko a fuska ba, ta ce" Wardugu, rigingimunka sun isheni haka, ya isheka malan! 


Wardugu ya shiga gyada kai yana kallonta bai bata amsa ba, 

Ta ci gaba da maga domin ta san ba amsar zai bata ba, ta ce" ta ya zaka saka Walyn kwana a cel? Wardugu ina jin zafi idan na ji ana fadin baka da sasauci, baka wasa, baka sulhu, Wardugu matarka ce fa? Ya kake so mutane su fasaraka??


Wardugu ya tsura mata ido kawai, 

Ta ci gaba murya a sanyaye" ka daina Wardugu, ina so idan na zo waje na tarda ana fadin alkhairi a kanka, ina so idan ana maganarka ta kasance ana yabonka Wardugu, ka ringa sasauci freind, 


Wardugu ya yi mata dan murmushi ya miko hannunsa ya dungure mata kanta bai ce mata komai ba, 


Alhinayettt ta ce" Wardugu ina kula samu buzuwa??


Wardugu ya yatsina fuska ya ce" hum, Ayya ce ta daukota wai ta yi y'a,


Alhinayettt ta ce" yarinyar ce ta birge ni, irin yanda tana buzuwa , bakar buzuwa aman bata bata bakinta ta hanyar shafe shafe ba, ina son mutun haka walahi.....

Wardugu ya daga kafada ya ce" daga kauye, can cikin kauyen kauye fa ta fito, inama ta ga man bale ta shafa? Allah dai ya sa idan ta dan waye ta zama dan kauye ya fi na birni shegantaka....


Alhinayettt ta ce " sai dai idan ba tare da Ayya take ba, Ayya ce zata wani bari haka ya faru? Yarinyar ce innocente,   dan Allah ka hada ni da ita mu zama kawaye,


Wardugu ya waro ido, a fili ya furta" kawaye? Ki kirani aboki kuma ki yi kawance da wannan? Aa! 


Alhinayettt ta yi murmushi tana kai masa dan dukan wasa ta ce" ina son ta zama kanwata ne Wardugu, ina son na kara nuna mata shafe shafe karma ta saka kanta, sannan na kara wayar da ita......


Kafadunsa ya daga irin ita ta gano, kafin yake bude mata motar ya yi mata nuno da ta shiga


Dariya ta yi ta shiga , ta kunna wato dai ta ishe shi da magana ko? 


Hannu ta daga masa, ya yi mata nuni da sai ya zo , ta tayar da dankareriyar motarta ta kama hanyar makarantar kannenta dan ta dauko su ta mayar da su gida


Komawa Wardugu ya yi, yana shiga ya tarar da su sai labari suke suna dariya abinsu, Mu.azam kuwa ya kasance du motsi sai ya kali Agaishat dake zaune tana kallon Tv kuri, ita har yanzu mamaki take mutane a cikin wannan allon suna ta magangannu suna komai abinsu, har bayan take lekawa wai ko zata gansu ta nan ta sha yiwa Ayya tambayar kuma yanzu idan suka fito fa? Yanzunma Ayya ta kuna mata wakokin dandali, kalo take tana ta sakin murmushi kumatunta na lotsawa dimple har biyu a fuskarta, wani wajen sai ta rufe fuska idan namiji ya fara rawa, sosai take dan gane hausar da suke tana kara koya ta nan, shi kuwa abin na birge shi, sannan ya yiwa Ayya tambayar wacece ita? Da french, ayyarma ta shiga kora masa bayanin komai.....ya sha mamaki, ya ji wani lamari a tare da yarinyar, yana son inganta rayuwarta......

       Wannan kennan.



Wardugu na zuwa ya ce" tashi mu je,


Mu.azam ya mike ya bi bayansa suka nufi dakin Mu.azam din , Ayya ta yatsina fuska a ranta ta ayanna mai yiwuwa ya yi fushi🤣.



Suna shiga Wardugu ya ce" c'est bon, maintenant tu me dit la verité sur ce qui t'arrive ( ya isa, yanzu sai ka fada min abinda ke damunka!)


Mu.azam ya tsare shi da kallo, a hankali ya zauna saman kujera yana kallon Wardugu, 


Wardugu ya karaso ya zauna shima, ya ce" ka san dai kana iya yiwa kowa karya banda ni! So ka fada min tun kafin na hasala Mu.azam, wata irin cuta ce wannan wanda baka taba yi a gabana ba ta zugeka haka? Me ya samu kasan gashinka ? Kana tunanin ban lura ba? To gashinan kasan gashinka a aske! Sai ka janyo sauran ka rufe, du ka zama wani iri? Ka duba fa ka gani wandon vest ne a jikinka ka dauko riga rose (pink) ka saka sai kace mace? Hannunka ba agogo, yannayinka na nuna kama tare da damuwar da ta fi karfin furucinka, ina hawa aiki karfe goma na dare, ka fada mani na juya! 


Mu.azan da wata irin murya ya ce" Cancer du cerveau  ke damuna..... (cancer ta kai)



Wani irin tsam Wardugu ya yi, ya kaste maganarsa a lokacin da bai shirya ba, 


Zurbat ya mike yana duban Mu.azam, hannayensa duka biyu ya saka ya dafe kansa, baya baya yake ja ya......


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        2️⃣4️⃣




Wani irin tsam Wardugu ya yi ya katse maganarsa a lokacin da bai shirya ba,


Zurbat ya mike, duban Mu.azam yake da wani irin kallo, hannayensa duka biyu ya kai saman kansa ya shiga yamutsa gashin kansa , baya baya ya shiga yi da kafafuwansa, bai fi taku hudu ba ya tsaya ya juya ya juyo, hanunsa ya jimke ya daki dayan da shi, 

A hargitse ya dawo wajen Mu.azam, so yake ya zauna aman ya kasa...... murya a cinkushe ya ce" yaushe, yaushe? Yaushe ka sani? Ya aka yi ka sani?????


Mu.azam ya mike yana dan sakar masa murmushi yana kokarin ganin ya saka shi ya dan nutsu aman ya kasa kama shi, dan haka ya tsaya yana kallonsa ya ce" Wardugu, har na kai wajen da gashina baya zama fa, ya jima a jikina ciwon ....nima ina gannin alamu a matsayina na likita sai dai ina turewa na ki maida hankali, ya kai ni sai na suma na yi awani a sume, na daina shiga tiyata ba yau ba, ina zuwa asibiti ne dan kar imanina ya yi rauni, ina zuwa ne dan haduwa da wa.inda suka fi ni damuwa, ina yi mana adu.a a tare, Wardugu idan na jima a gabannan na kara shekara hudu a duniya,...



"C'est faut!,(KARYA NE!)  Wardugu ya fada  tun karfi yana nuno Mu.azam da yatsarsa, 

Taku ya yi wajensa ya ce" idan kai ka fada, idanma wani sakaran likitan ya fada na fada karya kuke, karya ne Mu.azam, ku baku isa ku fadi abinda Allah ya boye ba, ba wani mahalukin da ya san ranar mutuwarsa , mutuwa bata shawara, bata fadi sai an ganta, mutuwa na zuwarwa bawa a lokacin da bai sani ba, sannan a lokacin da bai shirya ba domin a kulun bawa baya cikin shirinta,


Wardugu ya yi shiru, gaba daya ji yake jikinsa ba karfi, a hankali ya kai kasa ya zauna nan kasa, waje guda ya tsurawa ido kafin ya ci gaba da fadin" sannan Allah kadai ya san gawar fari, ba wai dan wane bashi da lafia wane lafiarsa kalau za.a ce sai marar lafiar nan ya rigayi mai lafia rasuwa, 


Mu.azam da ya karaso , a hanakli ya duka ya dora hannayensa saman na Wardugu, murya a raunane ya ce" ban taba tunanin wani abin zai girgizaka haka ba Wardugu, menene a ciki? Ko dan abin ya shafeka ne baka so ka ji? Wardugu ka yi hakuri, ka daina tayar da hankalinka kan maganar nan, nima na fada maka ne dan na ji sanyi sannan na samu wanda ya san ciwona, Wardugu ka....


Bai tsamaci lamarin ba, sai jinsa ya yi jikin Wardugu, Wardugu da dan ya tsokane shi yake ce masa sai sun yi gaisiwar larabawa, yau gashi da kansa ya rungume shi, 


Murya a cunkushe wardugu ya ce" bana so  bana so.....

Kasa karasawa ya yi kuma ya saki Mu.azam ya mike ya fice da wani irin sauri .......


A hankali Mu.azam ya hade kansa da gwuiwarsa, , tabas mutuwa Aya ce, duk mai rai mamaci ne, tabas ba karamar ni.ima bane da Allah ya boyewa bayi ranar mutuwarsu, shi gashi, hasashe ne aka yi, likitoci sukai a kansa, rayuwar turai da za.a fada maka komai kwaro kwaro ne, sun kiyasta lokacin da suke gani zai kai a raye a doron kasa sun fada masa, wai basu fada masa rana da lokaci bama aman gashi du ya firgice ya fice a hayacinsa, 

Idannuwansa ya lumshe yana jin saukar zazafan hawayensa, zuciyarsa ce ta ci gaba da fada masa" ka zo kasar nan je dan ka kara ninninka ibadunka, ka kara yawaita sadaka da aikata abubuwan alkhairi, ka zo kasar nan ne dan ka samu ka raya sunnar ma.aiki idan Allah ya nufeka, mutuwa kowa yi zai yi Mu.azam, ka daina karaya ka yi hakuri har Allah ya yi ikonsa a kanka, 


Wayarsa ce ta dauki kuka  ya kai dubansa wajen wayar ya mike daga tsugunnin nan ya daukota ya daga,


Docter me ka yi kennan? Na zo wajen aiki na tarar da takardar barin aikin ka? Saboda ni kake son yin nesa da aikinka ko saboda na fada maka ka yi hakuri a yi maka aikin nan? ......


Kansa ya shafa yana sauraronta, masoyiyarsa wace ke nuna masa kauna, tana son Mu.azam tamkar nama daya na cikin miya, tana son kasancewa da shi, labarin rashin lafiarsa ya gigitata har itama ta kwonta, nan ne ta yi ta fadi tashi har ta gano ana iya yi masa aiki a cire wajen, aman aikin ne keda hatsari sosai, yana iya samun tabuwar tunaninsa, ko ya kasance ya shiga coma wace shigekan daga ita ba zai tashi ba, ko idan Allah ya aminta ya yi jinya sumul ya samu sauki aman shi ya kara kai da kasa ba zai harda a wani buda kansa ba a dawo kuna ba wani succes,


MU.azam ya ce" Aisha,


Aisha ta ce" ka dawo na roke ka, ka dawo tun kafin lokacin a iya yi maka aiki ya shige,


Ki yi hakuri ki daina kirana Aisha, Mu.azam ya fada da sanyin murya, ya ci gaba da fadin" nawa kuka yiwa aikin? Nawa suka fita? Karshe dai du yawanci daga dakin aikin za.a fitar da su basu san inda kansu yake ba, zasu dawo kulun a jone da inji yana taimaka masu wajen numfashi, da na.urori masu basu abinci, da masu jan fitsari da masu karban kashin su, zasu dauki lokaci a wannan yannayin har ya kasance ko a cire masu na.urorin ko dare daya su tsaya sun daina aiki, su basu dauki kadara suka yi ta ibada suna shinfida a makwoncinsu na gaskiya ba, su basu san a inda suke tsakannin duniya da lahira ba, Aisha, Allah ya dora mani, ba zan kai labari ba! Ki yi hakuri......


Yana gama fadar haka ya katse kiran, 


Docter Aisha dake kai kawo tsakannin dakinta da falonta ta dafe kai ta fashe da kuka, yar balaraba kyakyawa da ita, a fili ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Mu.azam, in sha Allah zaka warke, sai mun rayu da kai Mu.azam.......

(😔😔😔😔😔😔)


               Bayan sati uku


Ayya ce zaune tana nunawa Agaishat yanda ake gyara lale ja domin tana son kunsa mata ne, 

Bayan ta tankade shi lukui ta kawo mahanabiya ta zuba masa sannan ta zuba dan madaidaicin ruwa ta kwabe shi sosai ya yi shar da shi ta zuba dan ruwa gefe ta ajiye tana kallon Agaishat ta ce" yi ki wanke kafar mana Agaishat, kin ga yayanki Mu.azam ya ce zaku fita ku zaga gari , ni kuwa na fi so idan mun gama kunshin nan sai ku tafi....

 

    

Agaishat ta yi sauri ta shiga darwaye kafar nata ta cire ta dauke ruwan ta kai ta zubar ta dawo ta dauki abin goge kafar ta gogoge ruwan kafin take zama ta tankwashe kafafiwanta Ayya ta shiga daura mata iskwace tana fadin"ki lura dan gobe ki daura abinki kin ji Yar Ayya,


Agaishat ta gyada kai tana murmushi, a kowani lokaci a kowani yannayi ta tsinci kanta tunda ta sauke kafarta a gidan Ayya sai iyayenta da yan uwanta da baba sofo sun fado a ranta, bale yanzu Wardugu kansa da yake yawan hararata a farkp ya daina, shi dai baya shiga lamarinta aman baya hana wani shiga, Alhinayettt ma tana lekowa wani sa.in idan Wardugu na gidan su sha hira da yaren buzanci domin tana jin dadin jin yaren raurau ana hira da ita ba wani kyama, sosai Alhinayettt ke dan gwada mata wasu abubuwan, da hikima take nuna mata wasu yan al.adun yan birni sannan Mu.azam na mugumugun sakata a jiki, yana sakar mata fuska fiye da tunanin mai karatu,  idan ta kali kayayakinta, suturun da suke malakinta a yanzu, sai ta ji hawaye na neman zubo mata, tunaninta me yan uwanta suke sakawa a yanzu? Wani hali suke ciki? Jiya i yau ne ki Baba ya canza halayensa?

Sai dai takan bi su da adu.a kawai, itace kadai abinda take iya yi masu a yanzu, kuma tanaiwa iyayen rikonta adu.ar gamawa da duniya lafia, ba.a wani sakata makarantar boko ba domin shekarunta sun tafi shekara goma sha takwas har ta kusa cike sha tara, aman a gida Ayya na koya mata abinda ya sawaka sai karatun islamiya da ta kara zurfafawa sosai tana kara neman ilimin adininta.


Ayya na gama daura mata kunshin ta mike tana leka windows, mamaki take irin yanda yanzu wardugu ya ajiye kafarsa a gidan, duda ta san amininsa na nan dole za yana yawan zuwa aman abin na bata mamaki, bai jima da fita ba fa aman har ya dawo, sannan yanzu basa fada da mu.azam akasin da da sai ta shiga tsakani ko ta gindaya masa doka kan Mu.azam din kafin yake barinsa ya huta, yanzu kuwa bini bini ya shigo ya haye wajen Mu.azam su yi ta hirar da ita bata san ko ta meye ba, yanzun ma tsaye suke su uku, da yar jajar nan Alhinayettt sai hira suke suna dariya,

Rufe windows din ta yi ta juya ta fice ta bar Agaishat na zaune tana jira ya bushe ta wanke kamar yanda Ayya ta fada


Bayan kunshin Agaishat ya bushe, ta mike ta saka takalminta silifas ta yi bayi,

Wanke kunshin ta yi, jan kunshi yayi jajajir, ga mamakinta ya fito sosai a fatarta har ya haska mata  fatar kafar da hanayen,

Da sha.awa take kallon kunshin ya yi kyau a idannuwanta,

Ta dauki lokaci a bayi domin sai da rmta yi wanka ta fito ta je bakin madubi tana goge gaban goshinta inda ruwa ya taba kannanuwan kitson da Ayya ta dage akai mata wa.inda sai warwarewa suke dan kansu ,


Turarukanta ta zauna ta shafa na madara masu sanyin kanshi, ta shafa mai kadan a jikinta, 

Kwali ta dauka tana adu.a domin har yanzu ta kasa sabawa da saka shi da dadi sai ta yi ta fama, bayan ta saka ta caje girarta, ta dauki wani jan baki mai ruwan lebe wanda Ayya ta fada mata kadan za tana shafawa a lebenta na kasa, 

Hakan kuwa ta yi ta shafa kadan kafin take tsurawa madubin ido, tunda ta zo garin nan ka.ida ne a wuni sai Ayya ta tsareta yin wanka sau biyu wataran har sau uku, idan kuwa ta yi wanka dole ne ta zauna ta kula da du wata gaba ta jikinta, tun tana kallon haka a wani iri har ya kasance idan bata yin ba itama bata jin dadi, sannan ta yarda da mutun sai da gyara, wannan mugun bakin da take gani a jikinta a ruwan wanka ta ga yana sauka daga jikinta, tsabar rashin wanka na kirki ne da kuma karin bakin turkidi(tufafin buzaye), yanzu fatarta ta kasance bak'a mai haske, irin bakin nan mai kyau mai birgewa, ga gyara yana kara samu yau da kulun, har santsi santsi take ji fatar tata ta fara yi mata, 


Mikewa ta yi dai ta shiga fitar da riga da siket din da Ayya ta rataya jikin abin turaren wuta tun da safe kan su zata saka,

Wani ni.imtacen kanshi suke na turaren tubawa, 

A hankali ta saka slipe (pant) dinta, an ta kasa saka breziyar domin har yanzu bata iya aiki da ita ba, kai ita bata ma sonta ne , 

Kayan nan ta saka sket da riga, sun amsheta sun mata cicif a jikinta dinkin zamani ,

Tsaye take tana kallon lufayar da Ayya ta bata, ta nuna mata ta koya mata daurawa sai dai bata iya ba har yanzu (daura lufaya sai a slow), 


Gashin kanta kawai ta sakawa ribom ta saka yar bakar hular da Ayya ta hada mata da kayan ta luluba Lufayar ta fice da takalman a hannayenta dan Ayya ta nada mata da kanta,


Alhinayettt karfe nawa ne zaki je wajen auren? ,

Agaishat ta tsinci muryar Wardugu da bata da siri tana tambayar Alhinayettt dake zaune tsakiyarsu Ayya kuwa na wajen table din diner tana gyara shirin da mai aikinta ta yi mata domin bai mata ba! 


A hankali ta sauko, ta karaso tana hangen yanda Mu.azan ke sakar mata murmushi,

Karasawa ta yi sosai kafin take gaisar da su a jimila ta hanyar fadin" Ina kwanan ku,


Alhinayett ta amsata tana yaba kunshinta da harshen buzanci wanda Wardugu ya ji me take fada ya yatsina fuskarsa yana girgiza kai.


Mu.azam ya kai dubansa wajen agogo ya maido wajenta ya ce" Agaishana, yanzu ne safiya, duba karanto min karfe nawa ne? Na ga ko kin gane yanda na koya maki,


Ai kuwa ta juya wajen agogo ta shiga nunawa da hannayenta tana irgawa tana faman fada masa lokacin Ayya ta karaso ta kama hannunta ta ce" a bar y'a na gama shiryata, ita da bata yi safiyar zuwa wajen namiji ba ai ba lale ne ta gane safiya ce ko rana ko yama ! Ayya ta karasa tana murguda baki irin na tsofafin nan masu rigima ta kai dubanta kan Alhinayettt,  wato dai da Alhinayettt ake,


Wardugu ya mike ya karasa wajen Ayya, ya kasance sun saka Ayya a tsakiya shi da Agaishat wace hannunta ke cikin na Ayya tana so ta warware mata Lufayar nan ta nada mata,


Sosai ya so rage muryarsa, sosai ya yo yaki da muryarsa ya ce" kin ce baki tsufa ba? Da yaren tubanci,


Juyowa ta yi ta murguda masa baki ta ce" eh da saurana, 


Wani tsadaden murmushi ya sakar mata yana dan juya kansa, ya kamo dayan hannun nata cikin nasa ya ce" kin san du duniya ba a yi ba ba kuma za.a yi ba macen da zan so kamar mahaifiyata ko?


Ta kawar da kanta bata bashi amsa ba, ya ce" in dai kina irin abin nan sai in fara tunanin na bani Ayyana ta fara tsufa, 


Hannunta ta warce ta dungure kansa kamar yanda takan yi idan ya hasalata ta ce" ni ba wani tsufa ko rashin tsufa bane, ina jin haushin irin yanda kuka dauki al.adar yahudawa kuka mayar naku, tun da safe take gidan nan 


Wardugu ya ce" Mu.azam ya gayace mu baki daya mu raka shi ya ga gari,


Ayya ta yi tsam tana kallon sa, Mu.azam ya gayace ku? 


Wardugu ya gyada mata kai, 

Hannunta ta kai wajen wuyansa ta taba wai ta ji da zafi, 

Kalau ta ji wuyansa, ta saki ta dafe habarta da mamaki, ta ce" yaushe mage da bera suka fara shan innuwa daya har shawararsu ta fara zama daya? Me ke damunku? Shirin naku kuma ya fara bani tsoro,


Wardugu ya saki hannun nata yana murmushi ya karasa ya ce" ku fice mu je ta fito idan an gama shiryata, kai yama zaka hada mana fita da karamar yarinya? Yanzu fa dole ka saka mutun ya rike bakinsa gaban yara! 


Mu.azam dake biye da shi yana dariya  Alhinayettt kuwa da naci ta zauna sai da Ayya ta nadawa Agaishat ta saka takalminta plat, suka kamo hanya Agaishat ta mugun yi mata kyau a idannuwanta, sai ta fito kamar wata chocolate color din balaraba, ta hade ta yi wani sihirtacen kyau


Haka suka karaso suka bude bayan suma suka shiga, ita dai Agaishat kanta a kasa, irin kalon da mu.azam ke jifanta da shi ke bata kunya, sai ta rasa me ya sa yake irin kallon nan,? 


Alhinayettt ta mika hannu ta dauko wayar Wardugu ta dawo ta shiga nunawa Agaishat hotuna suna dariya,


Wardugu ya ce" ina muka nufa oga?


Mu.azam ya ce" ka kai mu Bienvenu a Wardugu place, 


Wardugu ya taka wani wawan birki, ya kalo shi ya ce" wasa kake?


Mu.azam ya ce " aa can nake son zuwa, yana mai hade rai shima ya mayar da dubansa gefen titi (BIENVENU a Wardugu place, waje ne da mahifin Wardugu ya buda da sunnansa tun suna tare suna ganewa juna kafin abinda ya hada su ya hada su su bar shi da mumunar rantsuwa a tsakani, an ce yanzu matarsa da ya aura take kula da wajen wai ita Aisata ,......mugun tsama ne tsakanin wannan family masu matukar kaunar junansu a da, kuma har yanzu da daya kwal da ya malaka dai Warsugun ne..........).....


Post a Comment

0 Comments