BAKA CE hausa novels 3

 BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣1⃣





........Niamey.......




     Gidan Wardugu



Kawata, dan Allah wai da gadke kike? Gaki ga yan kaso wa.inda suka aikata mugun laifi? Gaskiya oga ya san kan mugunta



Walyn ta ja tsaki ta ce" ke, a dakin nan a nan suke fitsari, mata sai kawai ki ga an dage buje an tsirara fitsari a tsaye, basa kunya basa kyankyamin wajen , kai gaskiya Wardugu ni da shi akoy tashin hankali, ba ni ya wulakanta ba, walahi sai na rama!



Me zaki yi masa? Wardugu ne fa? Kin manta waye shi? Ko mu da muke gari bama rayuwa da shi mun san waye shi, koda kina kema jinnin tubawa ba lale ki iya da rigimarsa ba, ya hada abubuwa da yawa ne, kin ga shine da daya kwalin kwal a wajen iyayensa, shine Wardugu mai sunnan rikitatu a cikin ku, shi ne Batube, kuma shi ne Soja! Wardugu kakarfa, tsayaye, isashe, hamshakin......


Ke meye haka? Walyn ta fada tana kallon kawar tata, 

Ta ce" ya zaki tsaya kina koda min miji sai kace wata mai son min miji? Toh bara ki ji mu a yarenmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta cika wa.adin yin hakan, duka duka shekarana biyu da aure da mijina, ko na kai shekarun da yana iya kara wata Wardugu haramiyar wata mace ce a nan duniya, ban ki ba lahira idan ya dace da aljanna!



Murmushi ta yi tana kallonta ta ce" dadina da ke saurin hawa , toh yi hakuri ni ban kai abin can ba ..........



Bakinta ta tabe ta ci gaba da shafa cream dinta kan kurajen cizon sauron da suka yi mata cin balaki a cikin cel din nan, rabonta da ta saka kafarta kofa tunda abin nan ya faru, gashi ta rasa Wardugu a waya kwata kwata, !


Dogo ne fari kar, datijo ne christa sunansa Docter Lucien, kwararen likitan mata kennan wanda ya karanci abin kuma ya lakanta,


Allah ya taimaki su Anna sun samu gannin Docter Lucien a dasha kuma tausayin irin ciwon da ya gani bayan ya sha fada ya karbe su ya shirya shiga tiyata da ita a washe gari wanda cikin ikon Allah sai da ya dauki awa shida kafin yake fitowa daga dakin tiyatar da ita shi ya hada zufa hakama masu kama masa wanda ba.a jima sosai ba aka gurgurota a gadon mararsa lafia aka kaita dakin da ake kontar da masu yoyon fitsari


Jigum suke zaune suna mamakin wai asibiti ce haka, su kam tunda suka shigo garin a tsorace suke da yannayin tsarin gari, gini ne kala daban daban bene kai kasa na cin kudin masu kudin birni ....



A hankali ta shiga bukar tana dube dube kafin take kallo shi, a kwonce yake , idannuwansa a rufe kamar marar lafia


Da sauri ta karasa ta ce " Sofo?


Firgigit ya buda idannuwansa ya sauke saman kanta,


Kokarin tashi yake wanda da kyar abin tsufa ya samu ya zauna yana kallonta, murya na rawa irin ta tsufa ya ce" ina kika shiga? AGAISHAT zuciyata ta rikice na rashin gannin ki, na damu na kasa baci, kin ji har zazabi nake dan bana ganninki yata, ina kika je kwana biyu? Kin san ke nake gani ina jin dadi, kece mai daukana tamkar mahaifi, zo zo na ji me akai maki? Wa ya taba min ke ?



Karasawa ta yi tana sakar masa murmushi ta kamo hannunsa ta damka masa goron da ta siyo masa tun wancen ranar, murya a nitse ta ce" mun fuskanci matsaloli ne a gida Sofo, aman yanzu alhamdulilah mun gode Allah, Su Anna sun tafi birni Sofo, muma watarana zamu je? Zaka tafi da ni nima na ga birni? 


Ajiyar zuciya ya yi jin ba abinda ya sameta na tashin hankali, ya lalubo karfen gurza goronsa ya mika mata ta mike ta darwaye ta dawo ta raba goron hudu ta maida hankali ta gurje masa shi tas ta mika masa ai kuwa ya hambuda yana tsotsa yana dan juya kai irin ya ji dadin goron


Can ya ce" Birni garuruwa, 

A birnima akoy garin da dadi ne da shi sannan akoy wanda sam ba zaka so rayuwa ciki ba indai kai din bako ne

Birni tana tatare da abubuwan firgitarwa, murane sun yiwa abin hawa irin mashin mota yarda, sun yarda da su suna halaka su


Tagumi ta yi ta ce" suna halaka su kamar yaya?


Ido ya dan zaro ya ce" zaki ga dan birni idan zai yi tafiyar da ba wata nisa ba, ba jeji ba, ba abin tsoro a hanya ba, dan tsabar sangarta da son jiki sai ya dare abin hawa abinsa ya tafi a dan kankanin lokaci in abin ya zo da karar kwana sai ya juyeka tamkar tuwon masara nan zigib ka mace shikennan sai kiyama


Murmushi ta yi ta ce" toh ba kace ajali na tarda mutun du inda yake ba? Mutuwa ai kai ka fada min ba.a gudunta kuma ba.a boye mata, kuna Anna ta ce ita mutuwa lokaci ne idan lokacinka ya yi ba tsumi ba dabara zata daukeka ne ko waye kai ko me kake , kai ka ce min mutuwa mai yanke kauna, takan raba da da uwa, miji da mata, kuma kace min kowani bawa da ajalinsa a duniya


Tsofo yama ta murmushi yana dan barin jikin nan na tsofafi ya dungure kanta ya ce" haka ne Agaishat, Mutuwa gaskiya ce, Allah ya sa mu cika da imani

Ta amsa da amin...., ta ci gaba da fadin " ka ce a birni suna da wata kalar madara banda irin wannan tamu ta rakumi ko shanu? Ina so idan ka je birni ka kawo mini in kaiwa Anna ta sha ta ji itama

 


Kansa ya girgiza kawai, domin ya lura yau du labari ne a kunshe a bakin Agaishat, wai shi zuwa birni, shi da a yanzu salarma baya iya zuwa masalaci kafafuwa sun kiya, ga tsufa me zai je nema birni? Sai dai idan har kadarar makwoncinsa a can wannan kuwa ya san ko ta wani hali Allah zai kai shi..............



Dago kanta ta yi ta ce " ka san me?


Ya gorgiza kai alamar aa


Ta ce" wankana sau biyu, su Mariama sun bani kaya suka saka na yi wanka 


Murmushi yake na jin dadi, bai taba yarda a duniya Allah na hada jinnin mutun da mutun haka kawai sai a kan yar yarinyar nan, 

Jinta yake tamkar jinninsa, sonta yake har bargonsa, baya son damuwarta, fatansa Allah ya bata miji na gari komai talaucinsa domin ba zata kasa ratuwa da talaka ba, a hakan rayuwarta ta ginu, gidansu ba laifi su ba talakawanan tukuf bane domin dadaya ne gidajensu ke zagaye a garin aman ita rayuwarta irin ta yayan talakawan nan tukuf ce masu wadatar zuciya,  


Tana ta zubar ta mike ta shiga dan totona dakin kamar yanda ta saba dan dudubawa da kyau ta kashe kunama, domin kunamu na cikin kasa bakaken nan wa.inda idan sukai cizo in ba.a yi gagawar shan magani ba dafin na saurin kashe mutun , sune a cikin kasar garin kamar me, yan garin sun iya rayuwa da su, domin sun san inda zasu same su sun iya kashe su tamkar yanda ake kashe cirnaku, 

Ta samu ta kashe wajen hudu ta cilar waje ta dauku tulu ta ce" sai na dawo


Hannu ya daga mata yana murmushi ya ce" Allah ya tsare ki


Yana kallonta har ta fice , ya samu kansa da zirarar hawaye, ya ce" ya Allah baka barin wani dan wani ya ji dadi, Allah ka sa , ka yarda, ka aminta , ka bani ikon gannin ta shiga hannu mai kyau kafin na koma gareka .......



                     *Niamey*



Kan Anna kasa take tafiya domin bata son gannin irin yanda mutanen ke cuwa cuwa, a can kauye shiru ne, ba hayaniya , ba komai, sannan mutanen basu fi a kirga ba, hakan ya sa du idan ta fito daga dakin da Fatimata take koda dan ta leka ta ga safiya ce rana ne ko dare ne? Sai ta rikice


Ji ta yi ta ci karo da mutun, da sauri ta dago dan bayar da hakuri sai dai me, gani ta yi ya zaro idannuwansa yana kallonta, a hankali ya nunota da yatsarsa sai dai wani abin ya ce masa Haba docter, haba docter, wacen koda jikin manyanta ya kamata ba zata koma haka ba, kuma ita batuba ce ba buzuwa ba, wannan kuwa buzuwa ce ta sha bakaken kayanta, kai bama zai yiwu ace ita bace, 


Da sauri ya ce" yi hakuri baiwar Allah


Bata san ta ina ta iya hausa ba, bata san ya aka yi ta ce" Ba komai yi hakuri kaima


Gaba ya yi yana dan waiwayenta, shi dai rabinsa da wancen dama familynta tunda aka hana masa aurenta, tun suna saurayi da budurwa, muryar wancen da wannan ba daya ba, sannan kai ka daina tunani kan matar nan mai yiwuwa matar aure ce

Da sauri ya kawar da maganar a ransa ya nufi office dinsa yana dafe kansa a fili ya furta" ya dace na ajiye aikin nan, na jima ina fama har jikin tsufa ya zo....




Tunda ta koma dakin ta yi shiru tana tunani, 


Gaishat ce ta salame sallah ta juyo tana kallon maman nata ta ce" Anna me ke damunki ne??



Anna ta dan yi jim ta dago ta ce" wani yare na yi yanzu Gaishat, wanni mutun na kade ya min yare na bashi amsa tartar tamkar na iya yaren


Da mamaki Gaishat ta taso ta zauna kusa da ita ta ce" me kuka ce?????????


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                    1⃣2⃣





Cikin yaren buzanci Anna ta maimaita mata abinda suka ce


Da mamaki take kara kallon Anna ta ce" kuma baki san sunnan yaren ba?


Anna ta girgiza kai, da yannayin damuwa a fuskarta ta ce" ban sani ba, kuma da dukan alama ba yaren faransanci bane domin likita ya yi ta yinsa a gabana ba wani fahimta nake ba, sannan ba yaren nan da muke ji wajen masu siyar da abinci a garinnan bane wato Zabarmanci, wannan yaren shima daban yake 


Gaishat ta mike tana kallon ledar fitsarin fatimata ta ga bata cika ba ta ce" Anna, ko mu koma wajen mutumen ku kara yin yaren? Anna ko haka na da nasaba da asalinki? 


Nan da nan Anna ta ji ranta ya baci, asalinta? Kennan dai yayanta ba zasu daina daga mata hankali da wannan kalmar ba, rai a bace ta ce" ina ruwanki da asalina Gaishat? Ina ruwanki? Tana gama fada ta fice a dakin don ji take zuciyarta sai tukuki take mata na bacin rai


Da kallo Gaishat ta rakata, haka ne, komai irin dadin da kake ciki da Annarsu in dai ka yi gigin neman sannin wacece ita? Zata fatatakeka ne ko waye kai komai kusancinka da ita, 

Ajiyar zuciya ta sauke ta karasa kusa da Fatimata da yanzu masha Allah sosai take samun sauki dinkinta ana kula da ita sosai, likitan karshe ne , du niger ta wannan fannin da shi muke takama!





 A yannayin nishadi ta fito a gidansu, Abanta ya santalo Amarya yar bariki, irin a nuna masa ana son yayansa har Bak'A bata kyamata tana bata abinci bayan ya cashewa maryama kudaden da ta yi rantsuwar ba za.a shiga da matar ba sai ya bada su ......Algabitt dai na rakashewa fa amarya , yayansa na gefe suna rayuwarsu , inda bak'a ta dan samu inci na kwana biyu a gidansu domin bashi da lokacin wulakantata yana malake da amarya yan uwanta kuwa sosai suka dan sasauta mata tsanar da sukai mata


Yar waka take da yaren buzanci tana saka sunnanta a ciki, fadi take" ni bak'a yau wa zai so ni?

Bak'a nake wa zai rabe ni?

Yar bak'a haka ne sunana!

Dala biyar babu mai kaunata, 

Ta yi dariya ta ce" ni ko a baiwa an rasa mai siyana a kauye da birni,

Agaishat kij cika muni....ta fadawa kanta sai kuma ta yi murmushi tana girgiza kai kawai



Algabittt, yar firit din yarinyar da ya auro ta furta kai tsaye 


Shi kuwa da yake saman gadon karagarsa ya yi dadaya ya kallota ya amsata da um?


Tasowa ta yi tana juyi uwa bishiya ta karaso tana nuna masa gidan manta na shafawa ta ce" ka san yanzu muma a kauye mun yi ido, yarinyar nan jikanyar mai siyar da fura nake kawance da ita, ita na baiwa kudina ta siyo min wannan man,

Na ga fatar Agaishat ta dameka, baka son yarinyar dan bakinta, ni kuwa na hango kyakyawar yarinya ce ta karshe kawai bakin ne ya yi mata yawa, dan haka ga shawara wace in dai ka yarda ka takurata ta yi a hankali zata dawo farar mace itama mu siyar mu samu kudinmu mu yi tafiyarmu birni mu je mu rakashe mu hau mota mu saka gilashi mu dangwali kaji


Wata zabura ya yi daga konce yana kallonta, irin maganar ta fara shigarsa, ya fara aminta da shawarar amaryar tasa


Kara jujuya masa ido ta yi ta mika masa ta ce" ka ga bude ka gani, ai dai ka san wannan uban farin da na kara ba nawa bane wanda har kake son samun irina ............. ka yi mini ciki na haifa maka mai kyau ko? To sai fa wannan, ka bada na je na kai mata a siyo mata ta shashafa ka ga yanda bak'arka zata dawo yar dagwasssssss


Murmushi ya sakar mata ya jawota jikinsa ya ce" na yarda, in dai ta dawo fara sai in baki ki kai a siyo dan ubanta sai ta shafa ko bata so


Dan ture shi ta yi tana jin haushi a ranta, dan jaraba sai ya kama ya jajagulata shi ba wani nisa yake yi da lamarin ba du ya hargitsa mata tunani ya barta, haba ta yi aure ta bar jarumin maza saurayinta, aman yau sai ta gayato sho gidan nan


Dan dukan kirjinsa ta yi ta ce" ina so wani dan uwana ya zo mu wuni tare yau Algabiiiiitttttt 

Ta fada tana jan sunnan


Da ido ya tsareta, wai itama nan ta iya bariki, murmushi ya yi, shi dai burinsa ta dauki ciki fa? Ina ruwansa inma 2a zqi dane mata ruwan ciki, shi dai in ta yi cikin ta haifar masa kace komin jaraba ya rike abinsa ko a shekara goma ne ya saida ya kara kama daloli, shi kam haihuwar yaya mata ta yi masa rana ( wani abu zai baku mamaki a lamarin nan, irin yanda Algabitt baya kishin matarsa? To bara ku ji readers , ban ce duka buzaye ba, ba zan ce duka ba domin mahaifina buzu ne dan tsananin kulle da yake yiwa matansa ko gidan mutuwa da ta shafi gidansu zasu je shi ke kai su da kansa ba direba ba kuma ya tsaya su fito rufrufruf uwa matan ninja baka gannin komai na jikinsa ko.ina a rufe ruf ba damar ganninsu komai kusancinka da su, sai dai kuma akoy buzayen da basu san darajar matansu ba, sam basa kishin matansu, sai su ga matarsu kwonce saman bed da kato su fice abinsu ko a kwalar rigarsu, baya hana suma in an jima su taketa abinsu doki ce dan haka suke zaune da ita ba wani abin ba! Gaskiya ce a fadeta🤷🏻‍♀)


Murmushi Algabit ya yi mata ya matsota sosai cikin yannayin rada ya ce" ke , kar ki damu da fada mini fan yan uwanki maza zasu zo, in dai zaki zauna da ni ki haifa mini mata masu kyau? To na baki dama! 


Ai kuwa da murna ta rungumeshi ta shiga bashi kulawa daidai daukar hankalin tsufansa 🤦‍♀

      Wannan kennan

................................................



A hankali ya jona wayar abinda zai dafa masa ruwan zafin dan ya kada madara ya sha


Komawa ya yi jikin bed ya zauna ya shiga karanta messages din Walyn, daya bayan daya,

Na farkon farkon du yannayin ranta a bace ne, harda baya jin kunyar a ce matarsa guda ta kwana a cell? Toh garin niamey ya dauka, ita yanzu kunyar zuwa auren da zata hadu da mata take, a jejefeta da habaici ya nuna ita ba kowa bace a fadin duniya


Sai daga baya kuma ta fara nuna wai ina ya je ne? Ya haka zai yi tafiya bai yi mata salama ba? Ina ya tafi?


Sai daga karshe ta sauko sosai ta yi ta turo masa alamun kuka da nuna ta yi missing dinsa yana ina ne? Tana son ganninsa ta yi missing dinsa


Murmushi ya yi a fili ya ce" Hajia Walyn matar Wardugu, Walyn mai zamani, 


Girgiza kai ya yi, kai shi kansa ya sani da ace wani saunan namiji ne da tuni Walyn sai yanda ta yi da shi, kuma ba boka ba malan! 


Wayarsa ya kunna wace take kiransa, ya cireta a liste noire (Black list) ya kwonta yana sauraron ruwan zafin na karar ya dafu aman ya yi masa banza, tunani yake, wai shi shugaban revel zai yiwa haka? Ya fada masa gashinnan zuwa aman ya ki zuwa? Har ya je ya yi ta zaman jiransa wai sai daga baya ya yi masa message  cewa ba zai samu zuwa ba,? Ya sani sarai waye shi aman ai shima ya san waye shi! In ba dan tsufansa ba da sai ta tafka masa ashar din da zai gigita! 


Wayarsa ce ta shiga kara , irin kukan bindiga ratatatttatatatatatattatatatatatatattatatatatatatatatatatatatatat


Muka hannunsa ya yi ya dauko yana karanta sunnan mai kiran


Sai da ta tsinke aka sake kira kafin ya daga bai yi magana ba


Oga, bako ne muka yi, ahi kadai yake tafe cikin duhun nan, ya zo ta hanyar boye , ragar wajen nan ta shaida zuwansa domin ta kama masa hannun shine ya fito yana fada


Kai waye ya zo? Wardugu ya katse shi da kakausar murya


Murya na rawa ya ce" Shugaban Revel!


Wardugu ya lumshe idannuwansa, a nitse ya ce" ku shigo da shi fallon farko, ku juya


Da toh suka amsa suna masu mamakin mai gidansu, yana nufin daga shi sai shi zai ganna da wannan hatsabibin mutumen?  Lale Wardugu bashi da tsoro, baya dar, baya tsoron uban kowa!



Kwonciyarsa ya yi bayan ya ji wa ke jiransa, 


Can cikin tunaninsa wayar ta kuma daukan kuka, 

Da haushi haushi ya mike ya daga da kakausar muryar nasa ya ce" Hello!


Wardu.........ta fada cikin sanyin murya 


Tsai ya yi bai amsata ba


Kuka ta fashe da shi ta ce" tu me manque (i miss you)


Ajiyar zuciya ya sauke a takaice ya ce" ki bi Nuger airlines gobe ina Agadez hotel din sojoji ki sauka nan ko bana nan ki je dakina


Yana gama fada ya kashe kiran yana shafa gefen fuskarsa da sajensa


DOGON wando ya dora saman gajeran ya saka riga fara kar ta ririke damatsunansa ya fito ya nufi fallon da aka sauke bakon dare (🤣)



Yana zuwa ya shigo kai tsaye,


Mutumen dake zaune ya sha rawani ya hakimce cikin shiga ta kamala mai daukaka darajar dan adam ya dago ya tsaida kallonsa kan Wardugu, a tarihin rayuwarsa dole ya sako wannan yaro, domin shi ne mutun na uku da ya ajiye shi jira

Murya a kausashe ya ce" Wardugu ba.a tsayar da ni jira


Shima Wardugu kai tsaye ya ce" *Rhissa agbula* ba.a ajiyeni jira!


Murmushi Rhissa ya yi, ya mike tsaye suka gaisa irin gaisuwar musulunci suka baiwa juna hannu suna yiwa juna salama



Wardugu ya ce" ya zaka zo wajena ni daya bayan ka san ya dace a tatauna da kai a bainar nasi kowa na da magana da kai harda mai zuwa da maganar shugaban kasarka


Rhissa ya ce" shugaban kasarka dai, ka san ni ba nawa ba! Sannan ni kaima da na aminta ganninka dan na fafata da kai na yarda tsaurin kanka zai je da nawa, bana musanyar yawu da matsoraci, ba.a daukana a tv haka kyauta sai kace wani sakarai!



Wardugu ya girgiza kai ya ce" ya ake ciki? Wa ke son tayarwa kasata hankali? Ina suke? Menene abubuwan yakinsu? Ana jitajitar kune kuka dawo bayan kun daina aiki a niger kace niger ta yi maka kadan sata yanzu? Me yasa ake samun gawarwakin bayin Allah a gidajensu? Masu aikata min haka baki ne! Da sun san idan na damke su zasuna kururuwar na kashe su da abinda nake masu da basu shiga gonata ba!


Wardugu ya karasa yana dukan table din glass din dake falon ya yi wani jijiga aman bai fashe ba domin irin wannan mai masifar karkon ne, sai bindiga mai tsini ke tarwatsa shi


Rhissa ya mike tsaye ya ce" ba ni bane, kuma ba yarana bane, abinda ya sa na tsayar da hankalina kennan har na baro aikina na garzayo dan ganawa da kai! Kar ka shiga yaki da ni ba ni bane! Na yi bincike tsageru ne, kan harkar siyasa ne, kuma na ga makwoncinsu, suna cancanza waje ne ina son sannin tsarin canza wajen nasu, Wardugu nima sai na yi maka maganninsu 


Wardugu ya girgiza kai ya ce.....


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣3⃣






Wardugu ya girgiza kai ya ce" ka taba gannin na nemi agaji? Kokowa ai ya dace mutun yayi abinsa! Ka bani hanya kawai ka barni da sauran ai na san tsarin tsagerancin yan tsagera, idan ka yi yaki a kambacina kana so gobe su afko su aikata abinda ya fi haka? Domin sun san ba zan iya tarbansu ba? Aa ba dai Wardugu ba


Haka tataunawar Wardugu da Rhissa ta kare, kowa na ji da kansa da kuma ikirarin kansa,

Rhissa ya san abu guda Wardugu ba wai cika  baki yake ba, yana fadin abinda zai iya aikatawa ne, ya san da in dai suka yarda ya ci masu kamar yanda ya fada ne sai sun gwamace mutuwarsu da rayuwarsu a hannunsa, Wardugu ya ga damar ya fitar da su jeji su fuskanci juna wanda hakan kuwa ba zai gyara su ba!


               Wannan kennan


Bayan kwana biyu .......AMERICA



Docteur Mu.azam ne ke zaune yana dadana computer, 

Can ya dago kansa ya duba time, 

A hankali ya ajiye ya mike ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa 

Yana fitowa ya dauki kayansa ya saka ya saka vest dinsa ya dauki agogonsa ya daura ya fito fallonsa dan madaidaici ba wani tarkace sai kujeru da dan table da tv tankamemiya, sai hoton wasu fararan mutane mata da miji ga dukan alamu suna murmushi a hoto

Kamar yanda ya saba zuwa ya yi ganan hoton ya tsaya ya ce" Abi, amy asalamu alaikum, yauma na tashi lafia, sai dai har yanzu ya kasa hakuri ya daina fushi da ni, gashi aiki ya taso min a kasarsa banda shi da mahaifiyarsa da mahaifinsa da suka dauke ni tamkar dan cikinsu bani da kowa, 

Zan kuma gwada kiransa ku taya ni da adu.a daga inda kuke, ina mai kara yi maku adu.ar Allah ya sa kuna cikin Aljannah


Shi kadai ya tsaya ya yi zubarsa kafin yake zuwa wajen wayarsa ya zauna yana dan murmushi ya shiga doka kira


Yana kallon wayar na haske ya ki dagawa, Walyn ce ta fito daga wanka ta zo ta mike abinta saman lafiyayan bed din hotel din itama tana duba saman screnn din dan gannin wa ke kiransa yake sharewa haka?


Murmushi ta yi ta juya abinta ta shiga neman baci a kasan zuciyarta tana ayanna toh fa da shima yana gaba bare ni? 


Can dai ya daga ya saka a  handsfree


Soja kake


Ya fada yana danne dariyar farin cikin ya daga kiransa


Murya ciki ciki ya ce" Docter kake, kuma dan rainin hankali kake


Murmushi ya yi ya ce" baka hakuri ne? Baka mantuwa ne???


Wardugu ya kawar da kansa ya ce" haka, ka san ba nine na watsa taron aurena ranar aurena dan wani gudiri nawa na shirme daga shiga ka ga amarya kafin a daura aure zaka fito ka watsa taro? Kai mahaukaci ne! Mu.azam baka da nutsuwa


Mu.azam ya bushe da dariya ya ce" Wardugu, abinda ya sa na tsalako fararan fatar, na yi doguwar tafiya niger ba dan ina son na samu *BAK'A* bane?, ni bak'ar mace nake so, ita ce ra.ayina, ita nake son zaman aure da ita! Kar ka manta ni likitan mata ne, idan ka ga na kuke abu kaima ka gwada abokina


Tsaki wardugu ya ja ya ce" kiran na menene?


Mu.azam ya kuma yin dariya ya ce" kai ka dena jin haushina mana, ai ni ban shaki mahaifin matana ba


Da sauri wardugu ya kai dubansa wajen Walyn wace ke kwonce, ta ji sarai dan haka ta yi saurin mikewa tana kallonsa,

Fuska ya hade idannuwansa cikin nata ya ce" eh haka ne na shake shi, domin a lokacin ban san mahaifinta bane, kuma na tarar da shi ya zabgawa mamanta mari , idona ya rufe ban tsaya wata wata ba na shake shi, kai dan ubanka sai yanzu ka tina?????


Ajiyar zuciya ta sauke, tana tine da ranar .....dalilin wannan action din da yayi na ta haukace kansa, wardugu jarabar duniya....komawa ta yi ta kwonta ta ja bargo tana rufe jikinta 


Wardugu ya fice a dakin , yana fita ya ce" Mu.azam??



Mu.azam ya amsa da na.am?


Wardugu ya ce" kana son kashe min aure ne? Tana jinka fa


Mu.azam bai ji dadi ba aman ya ya iya har ta ji, dan tsam ya yi kafin cikin yannayin mamaki ya ce" Wardugu yamzu tsareka ake idan zaka amsa waya ko me? Lale dole na auri batuba 


Kai banza ka nutsu ka ji!!



Mu.azam ya yi murmushi ya ce" dadina da soja zagi, ni dai ka fadawa Ayyata in sha Allah ina nan ina faman gama abinda nake zan shigo Niger, ka san bani da masauki sai kusa da ita dan ita ta iya kula da cikina, zan zo ba zan dawo ba sai na samu macen aure na kuma gama abindq zai kawo ni


Wardugu ya ji dadin haka dan haka ya amsa shi da murnar hakan




Satin su wardugu hudu a garin Agadez yana faman aikinsa wanda tun Anna na fada har ta kawo ido ta zuba masa, gashi ta yi ta yi aminiyarta ta barta ta koma wani wajen ta kiya ta ki fir sai ma fada da ta dauka cewar masarautar ai girma ne da ita, ba ita ba ko baki ta kawo suna da wajen zama har lokacin da suke so a masarautar Agadez



A yau suke saka ran komawa bayan ya fada masu su kiyaye, ya basu magungunna, ya kafa masu sharuda kan lafiar Fatimata,

Jirgin da ya kawo su an basu takarda dan haka suka kai aka saka su a layin wa.inda zai mayar garin agadez bisa jagorancin docter Fannata


Sun sauka lafia inda Fatimata ke dan takawa a hankali daga nan suka nemi abin hawa dan karasawa Timiya............


Timiya.....me aka kwaba? Me aka yi me ba.a yi ba? Me ake cikin yi? Timiya gari mai abin mamaki, Timiya garin bak'a,




Duka na kawo wuka a yanka Algabitt ya yi mata bisa taki shafa man da ya fitar da kudi ya saya, 

Rai bace ya ce" sai na tsine maki in dai baki shafa man nan ba


Cikin kuka ta ce" Aba, ka yi hakuri ka ji? Bana son canza kalar fatana ka yi hakuri Abanna


Ni ban haifeki ba, ke ba abin alfaharinki bane yau har na yi hakuri na dube ki na nemi intaki aman ki butulce min? Uban wa ke hure maki kune ne ni?


Aba ba kyau, ba kyau, mu ji tsoron Allah


Hannu ya saka ya dake bakinta ya ce" ki rufe mini bakinkin nan mai bakin jaraba! Ke sai kin shafa


Kokarin shaketa yake dan ya shafa mata Mariama ta fito da gudu tana ihu tana nuna dakinsu


Dakatawa ya yi yana binta da kallon meye ke kuwa


Hankali tashe ta ce" Ashta ce, ashta ce, tun da ta ce maka in dai ka yi mata auren nan sai dai a kai gawarta kai kuwa kace sai me ba dai ka daura mata auren ba? Ita ce gata can sai wani abu take daga baya ta fasa motsi


Fancakalar da Bak'a ya yi, shi da amaryarsa suka nufi dakin da gudu


Daidai wannan lokacin Su Anna da sukai doguwar tafiya suka shigo gidan da salama bayan su Dogarai ne da suka tarbo gimbiyarsu wace sarki yake hakimce yana ji tamkar ya zo ya tarbi abinsa


Jin kururuwa ya saka gaban Anna ya yanke ya yi wani irin faduwa, cak ta tsaya tana sauraron magangannun dake tashi, ihun kuka yayanta biyu suke inda Bak'a ke jingine jikin garu ta daga hannunta ta dora saman kanta ta yi tamkar status tana kallon kofar dqkin nasu , 

Muryar amaryar Algabiitt ce ta tashi ta ce" ta kashe kanta, ta kashe kanta


Wani irin luuuuu Anna ta yi wanda ba wanda ya ganta sai faduwarta da aka ji , nan mutanen gidan suka ankara da dawowarsu wanda nan da nan gidan kai dama anguwar ta cika da dukan jama.a ana ta daga maganar, tabas Ashata ta rasu, ta rasu ne da bakin ciki, tana da ciwon zuciya ne wanda ya yi mata tashin kai tsaye, wanda amaryar Algabitt ta yi kazafin ta kashe kanta, 


         Tashin hankali!



Mota ce katuwa irin ta sojoji, direba mai iya janta kawai ya dauka kai tsaye suka karasa gidan Sarki


Ayya na zaune tana gyara akaifunta labari ya zo mata cewar ta fito su tafi


Mikewa ta yi fa hanzari tana murnar yau kam Allah ya sa , 


Tafia suke cikin mota, Walyn na zaune tunda ta cewa Ayya ina kwana bata kara magana ba sai shanshan kamshi take domin da yar tsamarsu da Ayya, gani take Ayya ke zige mata miji yana wulakantata



Tafia ce suka yi mai tsayi, cikin jeji ne sosai kafin suke shigewa sahara gaba da baya


Wani kara motar take a cikin kasar nan tana cin tafiyar wace kana ganni ka san karfi ne ke aiki


Duda a cikin mota suke aman sun yi budu budu da su domin kura sosai ke tashi sanadiyar gudun da suke a motar da kuma kasa


A hankali ya ratsa yar gadar da ta kai mutun cikin kauyen, wato *TIMIYA*..............







        YA RAYUWAR ANNA?

ALGABITTTT FA? 

BAK'A?????


SU WARDUGU DA AYYA DA WALYN ME YA KAWO SU TIMIYA??????? MU JE ZUWA ...........................................................na yi imanin da ba dan Allah na sakawa bawa hakuri da dangana a zuciyarsa a lokacin da ya rasa wani mutun mafi kusanci da shi da Anna ta samu tabuwar hankali ga wannan lamari na mijinta, kar ku manta na fada ba labarin mutun na dauko ba aa labarin abinda ke faruwa ne, (YA FARU!)......


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣4⃣





Bayan sun shiga garin timiya mutane suka ringa gudu suna kururuwa, wasu na fadawa gidajensu wasun kuwa na nufa gidan sarki wasu kuwa na kokarin neman hanyar da zata fitar da su daga garin ta barauniyar hanyoyi domin dai garin ba wani rufe yake ba


Da mamaki suke kallon reaction din mutanen, Warsugu da sojan dake jansu ne kawai basu yi mamaki sosai ba duba da yannayin garin motar lafia dai bata shiga sai ta sojoji ko kuwa motar mugayen mutane masu zuwa su kai hargitsi su kashe mutane


Kallonsa ya maida wajen Ayya wace ta dafe habarta ta wara idannuwanta tana mamakin nan yake mutumen kuwa? Aman gudun me suke?


Labari ya kaiwa sarki a yar fadarsa, 

Tabas gabansa ya fadi da jin wannan lamari, ba a taba ba, mota har nan bata fara shiga ba,

Mikewa ya yi da dukan kokarinsa ya tatara karfinsa inda dogarawa suka shiga kabara sunai masa kallon jarumi mai tausayin talakawansa da kuma kallon marigayi


Du a bayansa suke inda yake daga kafafuwansa da kyar yana kara tunkarar motar, gannin motar ta sojoji ce hankalinda ya kara tashi, domin dai shi ya san motar tunda yana shiga gari kai gaisuwa fada, kai harma ya tafi kasa mai tsarki, me ya kawo motar sojawa Timiya? Shine tambayar da yake yiwa kansa, 

To ko dai sojojin ne a cikin motar ko kuwa mugayen mutane domin idan sun kai hari ai suna karbe motocin sojawan


Wardugu ne ya bude gefen da yake zaune ya karbe hannunsa daga rikon da walyn ta yi masa ya diro daga cikin motar tsaye kan kafafuwansa 

Jibgi, dankari, in ba wardugu ba zaka shiga kauye sai ka je da wando tree Carter?  Sai rigar sojawa irin body din nan damatsunnan hannayensa a fili, yar karamar bindiga marar karan sautin harbi ce a kugunsa inda ya rufeta da wannan rigar ta jikinsa ya saka belt kalar kayan sojojin ya daure tam abinsa

Kansa sanye da hula baka kalar wandon sai takalminsa sandal wanda ya daura abinsa 

Sun karbe shi, sun amshi jikinsa, sun kawata shi

Taku ya shiga yi da karfin jiki ya nufi Sarki da ya ja ya tsaya jikinsa na bari, ta faru ta kare, jita jitar Ashta kanwar matarsa ta kashe kanta wani ya kai birni an zo kama sirikinsa, mutuwar yau har kwana takwassss tabas wani ya kai, shikennan Alghabiitttt ya bani domin a hoto kuma a tv a birni Yana gannin wannan mutumen, an ce shugaban sojoji ne, shi da kansa ya zo kama algabiit? Algabitt ya ji haushin rayuwarsa, tunanin da Sarki ke yi kennan inda ya daskare da tare da bugun zuciyar ko wani taku na Wardugu dan nufo shi (🤦‍♀ in ba kauyanci irin na sarki ba, a rasa mai zuwa kama Algabiit karamin kwaro sai Wardugu? Za dai ka san waye shugaban sojojin nan hangensa kake!)


Yannayin shigarsa ta tabatarwa da Wardugu shi ne magabacin garin, dama irin haka idan an zo sarkin gari ko mai garin gari ko kuwa tsageran gari wanda ya gagari uban kowa ke zuwa ya tarbi mutanen, in da karar kwana a kansu ake farawa


Salama ya yiwa sarkin yana mika masa hannu sannan tar yana kallonsa ido cikin ido


Jiki na bari Sarki ya karbi gaisuwarsa yana tambayarsa hanya da zarcewa da magana kamar haka" mai gida, na san ba auren iri ka zo nema a wannan jeji namu ba? Koma wa ka zo kamawa ka yi hakuri, a yi mana sasauci kar a kashe mu, a kama iya mutumen a tafi, ni kaina inada kankannan yara da mata, idan aka tsame masu ni wa zai ji da su?


Da mamaki Wardugu ke kallonsa , aman da yake Wardugu dan duniya ne sai ya ce" Kai, baka san Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi ba?


Ai kuwa gaba daya sarki ya haukace, jiki na bari ya saki kuka ya duka kasa ya rike kafafuwan wardugu ya shiga magiya


Ayya dake cikin mota ta dake lebenta na kasa ta kali sojan nan ta ce" ka karasa da mu, na san wardugu wani lamarin ya shiga na tsawatar masa tun kafin abin ya birge shi


Walyn ce ta juyo da sauri ta kalli Ayya, a ranta ta ayanna wai ta tsawatar masa, sai son ta nuna ita kadai ta isa ta juya shi, ta ja tsaki a ranta a fili kuwa ta ce" Hum tana tabe bakinta sosai


Sojan ne ya juyo ya ce" Hajia, ki yi hakuri, nan ya ce na ja na tsaya idan na matsa bai bani umarni ba ni da shi ne


Da haushi haushi ta shiga bude motar wanda sojan bai ankara ba har sai da ya ji ta bude ya juyo da  sauri , har ta sauke kafarta guda ta ga Wardugun ya dawo da saurinsa gefen da take


Yana zuwa ya ja ya tsara mata ya ce" Ayya maman Wardugu, kece ikon mai sanya Wardugu cire wando ta kai, Ayyana kar ki yi fushi kin ji? Koma motar mu karasa sai ki yi masa tambayar ai sarkinsu ne



Da mamaki ta saki baki tana kallonsa, sarkinsu? Aman me ya saka shi kuka da dukawa ya kama kafar wardugu? 


Dan murmushi ya yi bayan ya saka mata lafayarta ciki ya rufe ya bada umarnin su karasa inda sarki yake


Suna karasawa Ayya ta bude tana shirin fitowa sarkin na karasowa ya dan risina yana gaisheta,


Ayya ta kalli wardugu ya dan sakar mata murmushi


Kai ta girgiza ta sauka sosai ta gaishe da sarkin kafin take fada masa abinda ya kawo su


Wata ajiyar zuciya ya sauke a bayane, ya ce" A garinnan Sofo mai bada magani kwaya daya mukeda, ya sufa sosai, gidansa da dan nisa da kasuwarnan sai mun shiga gari sosai


Ayya ta amsawa sarki da ba damuwa su je


A cikin motar nan sarki ya shiga inda yake dan hangen Wardugu ta madubi lokaci zuwa lokaci, ya yarda da ake cewa sarkin sojojin fa masifafe ne , bashi da dar, in ba rashin tsoro ba du irin yanda ake tsoron abzinawa da asiri shi a gabansa sai dai ma shi sarkin ya ji gabansa ya fadi maimakun na wardugun ya fadi, lale yaron ya sha ya jiku ya tada kai , rabonsa da kuka tunda aka zo masa da sakon Gaishat ta tafi baban birnin niger inda ya yi tunanin shikenan ta gudu me ta bar shi.....(wani lamarin dan gyara nvl dina ne fa, sarkin abzin ba wasa walahi🤣🤣)


Basu zame ko.ina ba sai anguwar baba Sofo


Suna tsayawa mutane suka cika wajen, tunda sun ga sarkinsu a tare da mutanen ai shikenan sai suka sakin jikinsu da su harma ake matsowa a shafa motar sai a kwala ihu da yaren buzanci a ce" nima na taba, mota mota a garinmu, mota har gidanmu, 


Du ja sukai a lokacin da mutanen ciki suka fito gaba dayansu, suna masu binsu da kallo, girma da yannayin tsarin halitar wardugu ta basu mamaki, suna da mutane dogaye sosai sai dai ba masu fafadan kirji da manyan damatsuna haka ba, sai kuma matan dake tare da mutumen da dayen sojan, kun san dai Ayya gwadar ado ce, bale Walyn farar mace alkyabar mata, walyn farar batuba ce tas tas tas, Ayya ce ma baka domin Ayya baka ce mahaifin wardugu ne farin batube shima tas tas tas , sai sojan dake saye da kayan sojoji komai harda bindigarsa da katon takalmin nan nasu da komai sai muzurai yake


Sarki ne ya amsa gaisuwarsu kafin yake kai dubansa bukar Sofo,

Bukar kanta ta tsufa du ta zuzube sai abinda ba za.a rasa ba, ga dati sosai a dan nesa da wajen domin an yi rasuwa baka bata samu zuwa ta share masa ta gyara masa ba,

Ruwa kawai take zuwa ta dauko masa ta koma 


Nuna masu wajen ya yi bayan ya samu ya shiga ya tarar yana zaune saman buzunsa da carbinsa yana ja ya kurawa waje guda ido yana ta istighfari(Allah ka bamu nitsatsen tsufa in muna da rai wanda zai kara kusanta mu da kai ya Allah)


Gaishe shi ya yi ya juya inda sofo ke bin kofar da kallon mamaki, me ya kawo Sarki har wajena? Kuma hayaniyar me nake ji haka?


Ku shigo;


Sarki ya fada yana dubansu


wardugu ya ce" anya kuwa? Me zai hana ya fito???


Ayya ta kallo shi ta ce" Wardug.....

Da sauri ya yi gaba ya fara nufar yar bukar sofon a ransa yana ayyana ai idan Ayya ta nadaka toh fa tana yi da kai


Shishiga sukai banda sojan nan, 

Walyn na saka kanta ta yi baya tana kakarin amai da coshe hanci, a fili ta furta" kai ina , ba zan iya ba!



Ayya ta karasa a hankali kusan tsofon dake zaune ya zuba masu ido gaba dayansu yana mai binsu da kallo, ko gezau bai yi ba daga zaman da yake sannan yana jan carbinsa cikin nutsuwa 

A hankali ya amsa salamar Ayya da ta nufo shi cikin nutsuwa ta tsugunna dan nesa da shi aman suna facing din juna


A hankali ta ce" lokaci mai tafiyar da abubuwa, lokaci mai bayanna abubuwa, lokaci mai rarabe abubuwa, 

Baba tsufa ya zo haka? Allah ya sa mu cika da kyau da imani


Murmushi ya yi na gano wacece ita, tabas ya ganeta, idan ba zai manta ba shekaru sun kai talatin da suka shude ya sha kai mata magannin athsma na yaronta da bai fi shekara hudu a lokacin ba tana karbar masa aman ya ki karbar komai da sharadin sai yaro ya samu lafia


Murya na rawa baba tsoho ya ce" y'ata ke ce a garin timiya? Ya jikin yaronki? Na koma ban same ku ba sai na yi adu.ar Allah ya sa ya warke 


Ayya da murna ta janyo hannun Wardugu dake tsaye kikam ta ce" baba ai gashi, kana ganni soja ne, cikin ikon Allah magannin nan mun ji dadinsa, nima a raina kake, na nemeka Allah bai yi ba, kwanan nan na yawaita mafarkinka, a sifarka ta da hakan ya daga hankalina na saka aka nemo min inda kake, shi ne na zo na yi godiya sannan na yi salama kamar yanda na dauki alkawari, 


Baba na murmushi yana kallon wardugu wanda shima zuwa lokacin ya risina, yana kallon tsohon yana kidaya shekarunsa a ransa, ya yi imanin a kadan ya linkasa uku da rabi, 


Baba ya maido kallonsa wajenta, kafin yake bin dakin da yake zaune da kallo, ya yi murmushi bai ce komai ba


Ayya ta ce" Baba ka yi magana mana, 


Baba ya dago yana dubanta ya ce" kaya y'ata, ki dubi dakin da nake ciki a zaune a yanzu, me ya rage min? Me zan yi da arziki? Kyakyawan karshe kawai nake nema, shekaruna dari da ashirin da uku a duniya a hasashe mai yiwuwa na fi, 


Kallonsa kawai suke suna masu adu.a a ransu, adu.a suke da Allah ya datar da su da irin tsufan nan, wanda zaka yi ram da kai da carbinka, 


Jikin ayya ya yi sanyi sosai , a hankali ta zauna a kasar dake dakin tana kallonsa, murya a sanyaye ta ce" haka ne baba, Allah ya sa mu cika da imani......

Aman na so na yi maka wani abin da zai faranta maka, da zaka aminta ma da mun tafi da kai mun kula da kai


Baba tsofo da kansa ke kasa cikin rawaninsa ya dago yana kare masu kallo, ya yi imanin wannan matar da muguwa ce da bata bi bayan alkawarin da ta yiwa talaka futuk kamarsa domin ta san bai isa ja da ita ba domin zamani ya zama mai abu shi ne sarki, shi ya isa shi ke da magana ya dora doka, aman du ta manta ta tako ta ci gari da gari, ta ratso sahara du dan ta yi masa godiya sannan ta cika alkawarin da ta dauka,? Sannan ya san ba yar yankan kai bace domin ba da kansu suke nema ba kawo masu ake har gida, shi kam ji yayi gaba daya ya samu nutsuwa a zuciyarsa da shawarar sa,

Murya a sanyaye ya ce" tabas ina da bukata mau girma baiwar Allah, sai dai ban san ta inda zan fara ba, banma san ko za.a dace ba, 


Hankalinta ta maida kansa ta ce" Mecece ita?????????????........


Post a Comment

0 Comments