BAKA CE hausa novels 4

 BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣5⃣





Baba cikin yannayin damuwa ya ce" me zai hana na baki auren y'a? 


A nitse ayya ta ce" Auren Ya baba? 


Baba tsoho ya ce" eh, domin shi kawai zan nema a bada yarinyar dindindin , 


Aman baba wace yarinya ce wannan?? 


Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" yarinya ce mai tarbiya mai ladabi da biyaya, yarinya ce mai nutsuwa, bata da kwaramniya, inda aka ajiyeta ta zauna kennan sai an ce ta tashi, yarinyar nan ina jinta a raina tamkar yar da na haifa, a kulun damuwana na mutu na barta a wannan hali, tana cikin halin matsi dan kawai Allah ya yita *BAK'A*  sai dai ni murnar hakan nake domin fatarta ya sa har ta kai warhaka sai dai har yanzu bata samu mijin da zai aureta ba a kauye ta girma sosai shekarunta goma sha takwas a duniya , 


Jim Ayya ta yi tana kallonsa, kafin take cewa " me dinka ce Baba?


Baba tsofo ya kalli Sarki dake kallonsa shima cike da rausayawa, da wani ne duda tsufanda in dai yana iya magana yana gane wasu abubuwan da gudu zai karbe makuden kudin da aka baza masa, sai dai shi bawan Allah ta yarinyar fake tare da shi tun tana yar shekara shida a duniya yake, irin tunanin da iyaye zasu kwana su tashi da shi na gannin yayansu sun samu mijin aure mai nagarta wanda zai kula da yayansu, toh haka baba tsofo yake kasancewa, du motsinsa itace a ransa, tambayar kansa yake ina? Ta yaya? Wanene wanda zai rike masa Agaishat mudin ranta cikin mutuntawa da kauna? Ya hanga ya hango bai samu ba, har almajirinsa ya tuntuba aman ya watsa masa kasa a ido, hakan ya saka shi dukufa wajen kai kukansa wajen Allah, yana rokonsa da ya bili masa da hanya ta inda baya zato baya tsamani, ya bilo masa da hanyar da zata zamo alkhairi gareta,,,,


Sarki ya ce" kanwar matana ce, Sunnanta *AGAISHAT* 


Kana nufin farar  buzuwa?  Ayya ta tambaya


Sarki ya ce" buzuwar ce tabas, sai dai ita wannan Bak'ar buzuwa ce, 


Ayya ta kai dubanta wajen Baba Tsofo da ya yi kododo yana kallonsu, kallonta ta maida wajen Wardugu dake tsaye ya tsareta da ido yana jiran jin me zata ce,? Ya san halin mamansa, ya san Ayya da daukarwa kai, ! 



Murya a sanyaye ta ce" Warduggggggggg..........



Fuskarsa a hade ya ce" Lalalalala, 

Daga haka ya tamke fuska yana kallon su 


Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kasa ta afka tunani (Tabas a al.adar Tubawa ba.a yiwa namiji auren dole, bake Wardugu, sannan idan namiji ya yi aure sai matarsa ta yi haihuwa kamar uku zuwa hudu kafin ya yi mata kishiya idan kuwa bata haihun ba sai ta dauki shekaru kafin ya yi mata kishiya, wannan haka ne ba ja, haka al.adar garin yake, ) Ayya ta kuma kallon su, ya zata yi? 



A hankali ta ce" baba, wannan yaron shi daya Allah ya bani a duniya, 

Sannan bai jima da yin aure ba,

Ban ki ba, ina so idan da hali a bani yarinyar a matsayin yar rikona, yar amanata, in sha Allah zata ci abinda na ci ta kwonta a makwoncin da na kwonta ko wani iri ne, kafata kafarta Har Allah ya bata miji, zan yi dukan abinda ake yiwa ko wace y'a na kaita gidan miji sannan zan bi dukan lamuranta a gidan miji mudin raina


Baba tsoho ya jima yana nazarin maganarta, baya shakun za.a bada AGaishat in dai sarki ya yi magana, damuwar shi ne: Agaishat zata so bin bakin fuska duda irin matsin da take ciki? Gida fa gida ne, sannan mahaifiyarta zata yarda da radin kanta a rabata da yarinyarta budurwa ba da wani dalilin aure ba ko dangi na jini haka kawai a tafi da ita tare da mutanen da bata sani ba? Ko wannan karon ma isar za.a nuna mata a kuma kwace mata *Y'A*?


Duda haka baba ya kai dubansa wajen sarki, 


Irin kallon da baba ke yi masa sai da ya saka ya ji kunya, ya ce" abinda za.a yi, zamu kama baba a je da shi da ku baki daya ga mahaifiyar yarinya da mahaifinta, du yanda hali ya kama zuwa ya fi aike


Sun lamunce da hakan inda Wardugu ya kama baba a hankali ya mikar da shi sarki ya kama masa suka fito yana dan dingisa kafarsa har suka karasa wajen motar inda sojan nan ya bude wardugu ya daga baba a hankali ya saka shi gidan gaba sarki ya shiga suka shishige gaba dayansu Walyn da binsa da kallon meye kuma haka? Shima kallon Ayya dai yake, 


Basu zame ko.ina ba sai kofar gidan Algabiitt


......................   .................




Anna, ki yi hakuri haka kin ji? Ki daina damuwarnan kin ji Anna?

Agaishat ta fada tana miko mata gurasa ta kasa da aka kawo sadaka gidan mutuwar


Anna ta lumshe idannuwanta bata karba ba ta bude tana kara bin yayan nata da kallo, 

Mutuwar nan da aka yi bai saka Algabiitt ya yi sanyi a lamuransa ba, ya sako Agaishat gaba dole sai ta yi shafe shafe itama ya samo mata miji kamar yan uwanta tamkar damuwarsa ta yi auren ne, 

Yarinyar bata isa ta wulga ba sai ya dura mata zagi

Ya hana a yi zaman makoki sai yayanta dake zagaye da ita

Amarya kuwa idan yau wannan ya zo ta ce dan uwanta ne , gobe sai wancen ya zo ta ce kaninta ne, ta mayar da gidan filin kawo kwartayenta ba tare da wani dar ba domin mai gidan ya bata lamuni....


Anna murya a shake ta ce" bana so ya kashe mini wani cikin ku,


Mariama ta juyo fuska du ta yi mata ja abin kuka ta ce" to ki biyo mu mu bar masa gidan mana, dan mi ba zaki bi mu mu yi tafiarmu ba? Kin san abinda ke daure mu a nan ke ce, 


Hankalinta tashe ta ce" a duk lokacin da kuka ambata mini abubuwan nan biyu asalina da barin Algabiit bara ku ji na fada maku yau abinda nake ji! Ji nake tamkar lumfashina zai tsaya idan na ji an ce na bar inda Algabiit yake in dai ba da yawunsa ba, ji nake zan fada halaka, ji nake duniyara shi ne, ji nake in ba inda yake ba ba ni! Wani duhu ke rufe mini ido kaina ya dauki nauyi idan na takura sai na tuno wacece ni? Nakan fada damuwa mai tsanani juwa ta ringa dibana du idan aka yi maganar dangina, kun ji damuwata


Suke suke kallonta, Agaishat (Bak'a) kanta na saman cinyar Gaishat, Mariama na zaune gefensu,  Fatimata na jingine da garu tana facing dinsu,

Jiki a sanyaye Fatimata ta ce" me ke damunki haka Anna? Wannan ba soyaya bace, 


Mariama ta kallota ta ce" wace soyaya? Ai koda an yita a baya a yanzu Ya kasheta da kansa, Me ke damun Annarmu? 


GAISHAT ta buda baki zatai magana sai ga Algabiit bugum ya fado dakin yana dan dudukewa dan tsayi


Direct ya zarce gurin Anna bakinsa na rawa ya ce" sai dai su tafi da ke da tsinaniyar yar ki! Ba wanda zai kama ni, ba abinda na yi! 


Da sauri ta mike tana dafe kirjinta, tsinaniyar yarki ke mata yawo a kwakwaluwa, wacece kuma? Me aka yi? Su wa zasu tafi da su?  


Bata kai ga tambaya ba ya duko ya dago Bak'a da gashinta ya mikar da ita, 

Yawun bakinsa ya tatara mai cike da warin Sansani ya tofa mata a fuska ya ce" ga dan iskan tsohon da kike wuni wajensa tare da sojoji, to ki sani sai dai su kama uwarki


Janyeta Anna ta yi da karfi sannan ta yo fallon nasu da sauri dan jin lafia?


Gaba daya yayan nata suka biyota inda Algabitt ya labe yana leke yana kuma sauraron abinda ake fadi


Da kallo Anna ke bin su, sukai mata salama suka shiga gaisar da ita da yaren buzanci, 

Ayya ta kalli wardugu dake karewa kowa na wajen kallo, ta ce" ban san bama da wani yare zamu tatauna da ita da alama buzanci kawai take ji


Anna dake tsaye ta ji komai abinda aka fada da yaren da ba zata ce ga sunansa ba, kuma ba yaren da suka yi da likitan nan a asibiti bane............................................



🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣6⃣







Bata kai ga magana ba dogarai ke sanar da shigowar sarki falon sirikan nasa , daman da baba tsoho ma shi ke fasara tsakaninsu domin ba komai yake ganewa ba shi kuwa sarki ya zauna da tubawa 


Tunda ya shigo Anna ta sada kanta dan kunyar siriki, shima du a wani takure yake inda Gaishat ke binsa da kallo tana tambayar kanta me ya kawo shi ko bakinsa ne?


Gyaran murya ya yi ya ce" Anna, ina fatan kin san baba tsoho, wanda Agaishat ke zuwa wajensa babanta kennan


Daga inda yake ya daga murya da irin abin haushi haushi ya ce" ya zata manta kwartanta uban yarta? Ai ni dama na san dubunki sai ta cika munafuka, yau dai ga zance zai bude


Da wani irin yannayi Wardugu ya kai dubansa daga inda ake maganar, wa ke magana ta rashin da.a haka? Shine abinda yake tambayar kansa din wardugu na jin yaren buzanci  kai bama buzanci kadai ba wardugu irin mutanen nan ne masu kwakwaluwar kwashe yaren da ba nasu ba, yana jin yaruruka da dama, hakan ya bashi damar jin abinda ake fada harma wanda Algabiit ke aikowa daga daka


Sarki ya girgiza kansa kawai, ya san wanene Algabiit farin sani, kuma fa ya san harma gudumuwarsa wajen Algabiit ya tsula tsiya a garin   aman ba komai zai dauki mataki ne tun kafin ya saka a tarwatsa su baki daya


Anna da ta kasa hada ido da shi ta gyada kanta, ya zata kasa gane mutun mai daraja a idannuwanta? Wannan mutumin ko dan tsufansa a girmama shi aman Algabiit ke aiko masa da zagi haka? Ta yi imanin ba ita ba ko Algabiit din baba tsoho ya haife shi


Bak'a kuwa tunda ta kyala ido ta ga baba tsoho ta samu ta rakube jikinsa tana dan jefo masa tambayoyi a hankali da alamun tsegumi

Hannunsa ya saka ya dungure mata kanta yana murmushi, a ransa ya ayyana idan kika tafi,....nishadina, murmushina, zai tafi da ke

Sarki ya ci gaba da fadin" wadinnan mutanen da kike ganni, wannan baiwar Allahm mahaifiyar  wannan bawan Allahn ce, sannan ta taso tun daga garin da kuka kai Fatimata rashin lafia ta zo Agadez daga nan sun dauki hanya sun zo garin nan dan neman baba sofo da ya baiwa dan nata maganin huka tun yana yaro bisa alkawarin idan an samu lafia sai ta bashi abinda ya samu

Toh Sai aka tashe su Allah bai yi sun kara haduwa ba, tun daga lokacin take nemansa domin mutun ce mai son cika alkawari abin na tsaye a ranta sai yau Allah ya yi


Dan numfasawa ya yi, ya ci gaba" kin ga, ba a niger ba, ko a kasar waje masu fada a ji ne, 

Sun zowa Baba sofo da alkhairi na mamaki sai dai abin mamaki baba ya ce sam shi yanzu ba ta abin duniya yake ba, ya yafe sai dai damuwarsa *AGAISHAT CE*  

Anna ta dago da sauri ta ce " AGAISHAT? 


Sarki ya ce" kwarai kuwa, Baba ya nemi alfarmar......................................................gaba daya sarki ya kwashe yanda suka yi baba da su Wardugu ya fadawa Anna dake zaune kanta na kallon kasa sauran yayanta na zagaye da ita Bak'a kuwa na jikin Baba sofo


Da sauri Bak'a ta dago ta kai dubanta wajen Anna da Sarki, ta maida dubanta wajen baba Sofo, 

Baba Tsoho ya yi gyaran murya ya ce" shakuwa, da tunani ya hana ni sakun nutsuwa Annar Agaishat, na sani bani da ikon zartar da hukunci kanta domin ban haifeta ba sannan ni ba wani shakikikin dan uwa ba

A duniya adu.ata biyu ce, Allah ya sa in gama da duniya lafia Aljanna ta zamo makomata , fatan Allah ya nuna min ta zama mutun mai cikaken inci, ta samu nutsuwar zuciya , ta samu zama itama mutun,

Anna Agaishat ta yaya hakan zai faru? A timiya mu duka bamu fi kirgo da yatsu ba, nan da kike ganina har limamin garinnnan na nemi alfarmar ya aure man ita mana aman ya nuna aa ba zai iya ba

Almajirina ma ya kiye min,

Gashi yau da gobe sai Allah, Agaishat girma take, mu kuwa gajiyawa muke kara yi,

Idan ta fito daga nan ina ta fada? Me ta ci? Ya ta yi ta samu Allah ne masanin gaibu, ni kam a matsayina da wanda take zuwa wajensa sannan ta daukeni tamkar uba nakan yi mata nasiha, nakan tsoratar da ita, nakan nuna mata karara rayuwa da abinda Allah ya bani ikon sani

Annar yara , Ba zan tirsasa maki ba, ba zan saka ki daukan abinda zaki yi ta nisawa zuciya bata da tabas, aman ina so ki yi tunanin gaba da bayan lamarin, in da hali ki dauki Agaishat ki baiwa wannan mata riko da zuciya daya, ki yi kyakyawan zato, ki saka a ranki alkhairi ne sannan ki bi da adu.a, na yi imanin koda mugaye ne Allah zai saka mata kaunar yarinyar shari ya juye wa khairi 


Wardugu ya yatsina fuska ya dubi Ayya dake zaune tana kallon su, da yaren tubanci ya ce" Ayya, yarinyar nan fa wannan mahaifiyarta ce , kuma ina jin shegiya ce shi ya sa wancen yake zazaginta haka! Ayya me ya sa suke faman rabuwa da yarinyar? Ayya 


Wardugu ya isheka haka , Ayya ta fada tana zaro masa idannuwanta, murya a kausashe ta ce" baka lura da abinda ke faruwa ne? 


Ba zato ba tsamani muryar Anna, cikin yaren Tubanci ta ce" ba shegiya bace, wannan da ka gani ya shige daki ya labe shine ubanta, yana kyamatarta ne dan ta zo duniya *BAK'AR FATA* 


Da mamaki du suke kallonta, 

Ayya ta taso ta karasa kusa da ita, hannunta ta kamo tana kallonta ta ce" batuba ce ke?????


Anna ta lumshe idannuwanta sai ga hawaye sharsharshar ta dan jijiga hannun Ayya ta ce" ban sani ba, ban san ko mecece ni ba,


Damko hannun Ayya ta yi da dan karfi ta saka idannuwanta cikin nata ta ce" ban san ko dan ina jin yarenki ba? Sai kawai nake ji zan iya sadaukar da y'ata wa ke, zaki rike mini yarinya da gaskiya?


Ayya ta ji gabanta ya dan fadi, matar na tare da wani banban lamari, Ayyan ta jijiga hannayenta itama tana kallonta ta ce" mudin raina


Algabiit dake ciki sai zaro ido yake, ya shiga ukunsa, ya aka yi Anna bata manta yaren nan ba? Aman abinda ya yi mata *Harta sunnanta ta manta*!  Domin kafin ya lulo timiya da ita sai da ya tabata ta iya yarensa, ta iya saka kaya irin nasu, ta iya yan dabi.unsu, shigewa ya yi ciki ya zauna jikinsa na dan rawa rawa 


Anna ta lumshe idannuwanta, ta ce" thank you, 


Wardugu dake tsaye ya kalo su , Inglish kuma? Inglish ta yi? 

Hai san ya karasa shigowa dakin da kyau ba sai da ya karasa, inda shigowarsa ya saka du yan matan suka tsaya kallonsa da mamaki, Bak'a kuwa ta lafe da tsoro jikin baba tsoho jikinta du yayi wani sanyi tana son fahimtar maganar tafiya da wa wai ake? Ina ai ita ba inda zata, ba zata bi wasu mutanen da bata sani ba bata taba gani ba ta je a kasheta, ya zata iya tafia ta bar yan uwanta da annarta da baba Sofo? Wa zai ringa kawo masa ruwa? Wa zai ringa saya masa gogo yana gurza masa a karfen gurje goro? Wa zai ringa koya mata karatu? Wa zai ringa ce mata itama mutun ce dan tana baka Haka Allah yake son ganninta ? 



Wardugu yana karasowa ya dan duka yana kallon Anna ya ce" di u speak Inglish?


Anna ta dago ta kale shi, ta amsa masa da kanta, a ranta tana nanata inglish? Wani yare ne shi kuwa? Ba irin wanda suke yi da matar bane kennan?


Wardugu da mamaki ya ce" ya aka yi kika iya inglish? A ina kika koya? Wa ya koya maki? Daga wani gari kika zo? 


Anna da kanta ya fara sarawa ta dafe kanta da sauri , muryarta ya fara rawa rawa ta ce" i...i...i don't know ! Ta fashe da kuka tana rungume hannayenta da sauri Gaishat ta karasa tana rungumo Annarsu itama tana kukan za.a kuma raba su da yar uwarsu? Domin ta sani ne , a yanda anna ke jin zafin irin abubuwan da ake yiwa Agaishat , a yanda aba ya tasota a gaba da man bleating kan sai ta shafa ya yi kudinta itama , anna na neman koma waye ta bashi aurenta ta tafi ta huta, ta gwamace ta tafi ta auri koma waye da aba ya yi kudinta itama kar a je ta fada irin rayuwar da fatimata ta fada ko ma wace ta fi ta


Sai da Anna ta yi kuka mai isarta, suba bata hakuri kafin take share hawayenta ta yafito Bak'a sake kukan yan uwanta da mamanta na kuka


A hankali ta taso ta nufo Anna


Tunda ta taso suka sauke idannuwansu kanta

Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayyana " Eh lale baka ce, tana da baki sosai da kuma kazanta, a rayuwar kauye dole su tsangwameta domin gari ne mai bambace bambance


Kawar da kansa ya yi, jikinsa ya yi sanyi da lamarin uwar yarinyar, tabas akoy bamban al.amari a tatare da ita, da farko ya so ya cakula abin, ya kasance an watse su yi tafiarsu ba tare da Ayya ta kwaso masu wani jangom din ba, sai dai ina yanda matar ta yi yarensa tar tar tamkar nata, sannan ta shiga turanci tamkar yarenta shima, kuma ta furta bata san bama sunnan yaririkan da ta yi, harma ta shiga wani yannayi dan za.a takurata da tambayoyi ya saka shi yin sanyi, a hankali ya furta" sai na san su waye ku! 



Anna ta kamo hannunta ta zaunar da ita daf da daf, ta dago fuskarta, abinda bata taba yi ba irin kusancin nan da yar tata, tana so ta yi tana mugun tsoro da kunya


Murya a raunane ta ce" Agaishat, Ina son ki


Da sauri Agaishat ta kara kallonta, 


Anna ta sakar mata murmushi ta ce" sosai, ina son ki, kuma ina so ki samu canjin rayuwa, bana so ki kare a haka bana so ki kare a ciki duhun rayuwa


Gaishat ta ce" Anna, Anna


Anna ta kallota ta ce" menen Gaishat? Kar na raba ku da yar uwarku?

Na san muna cikin jimamin mutuwa, muna cikin rudu, aman ku kun fi kowa sannin rayuwar da muke , mutanen nan na tafia in dai ba da ita ba na yi imanin ba zai barta ba tunda ya saka wannan lamarin a ransa sai ya aikata

Da wa zai hadata? Ina zata fada? Mai yiwuwa idan aka tsilira da ita wani wajen koda ta so guduwa ishrwa ta kasheta a hanya, 


Agaishat ta fashe da kuka jikinta ya kwashi rawa ta ce" Anna aa, aa Anna, kar ki bada ni haka Anna, ku kadai na sani Anna, kar ki raba ni da ku, kar ki yi mini haka Anna, ki barni ina ganninki har in mutu, ki barni ina gannin baba Sofona ina kai masa ruwa yana kiya mini karatu, ni ba ruwana Aba ya yi ta dukan nawa ba komi Anna in dai ina ganninki ina gannin yan uwanna ina gannin Baba Sofo ya isheni Anna, kar ki rabani da abinda nakeda a duniya wato ku........




To jama.a ya zama kwashe ne? ............m



🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣7⃣




Anna  zuciyarta ta yi mugun karyewa

Hawaye yana shatatar mata muryarta na rawa ta ce " Agaishat, ki yi hakuri ki bi su, ba mugaye bane


Agaishat ta buda idannuwanta da kyau ta ce" kina da tabacin ba mugaye bane? Kina da tabacin su din mutanen kirki ne??


Jikin Annan ya yi sanyi ta sada kanta

Gaishat dake hawaye itama ta matso ta dafa hannun Agaishat ta ce" Agaishat....


Anna ta dago ta ce" bani da tabacin halayensu, ba zan ce su din mutanen kirki bane kuma ba zan fadi akasin hakan ba

Agaishat, ni da na haike ki, ni da na yi rainon cikinki, na haife ki , tunda kika ji na ce ki je, toh ki je din kawai....ba zaki fahimci girman maganana ba sai ranar da Allah ya nuna maki kin haihu, soyayar dake tsakanina da ke na iya cewa ki je to ki yarda da na yi imani na barwa Allah komai ne, a nan kike ko a wani wajen dama shi ya halice ki, ko wace rayuwa zaki fuskanta shi ya kadaro maki, ni ban isa na hana ko na saka ba sai dai na yi ta kai kukana wajensa ina neman jin sanyi daga wajensa


Agaishat ta rintse idannuwanta, ita bama bin nasu ba, wannan mutumen da suke tare wanda yake tsaye tunda suka zo wanda fuskarsa bata ga saki ko tausayi a tatare da ita ba, shi take tsoro, in dai mugaye ne ta san shine mai yanka mutanen domin wannan da gani shine bamban mugun


Algabiit dake daka sai sintiri yake, haka zata tafi? Ba.a bashi komai na kudin tafia da ita ba? Koda ba yarsa bace ai shi yake ciyar da ita tunda aka haifeta, ya isa a yi shawara da shi sannan a biya shi! Sai dai yana ganin yanda wardugu ya diro daga motar nan ya nufosu, tun a lokacin ya fara sakin fitsari domin shi yama yi tunanin an zo kashe shi ne, ba zai fita gaban wannan mutumin mai kwarjini ya yi wani abin ba, aman ta yarda ta bada Bak'a haka zata gane bata da wayo! 


Bak'a na ji tana ganni, tana gurzan kuka mahaifanta da rai ba babu ba, ba aure ba ba dangi ba aka fitar da ita tana waiwayen Anna da ta koma da sauri ta shige bayi ta rufe ta shiga rizgar kuka, aka shiga da ita cikin motar da bata taba gani da idannuwanta bama bale ta shiga, 

Tana ji tana ganni matar nan ta shiga ta riko hannunta tana dan murzawa Alamar rarashi

Tana kallon baba Sofo har aka sako shi motar shima kafin da kyar sai da Wardugu ya yiwa Walyn tsawa ta shiga motar wai karni take ji na bak'a, ya shiga suka tayar tana ji tana ganni aka bar anguwarsu gidansu yara sai bin bayan motar suke suna ihun murna sun ga mota manya sai daga hannu suke har sai ta bace da ganninsu aka je kofat baba sofo aka tsaya suka sauke shi

Agaishat ta kara rikicewa gannin da gaske sun bar baba Sofo wanda ya tsaya yana daga mata hannu idannuwansa sun kara kodewa alamun kuka yake na zuci sai dai ya fi farin cikin hakan da zamanta a garin


Haka suka dauki hanya ba tare da sun huta ba ko sun sha ruwan garin ba suka dibi hanyar komawa garin Agadez


Kukan take tana fadin"" Anna, Sofo, Anna, sofo


Walyn ta ja tsaki ta ciro ecouteurs dinta ta saka a kune, Wardugu dake gaba ya rufe idannuwansa a tunaninsa zata gaji ta yi shiru ne aman ina sai kara boda Agaishat ke yi Ayya na tausarta tana bata hakuri da tubanci bata san ta dan iya hausa ba ita kuwa bata iya buzanci ba


Juyowa ya yi, da yaren buzanci ya ce" Ke ki rufe mini baki a nan tun kafin na saukeki na yi maki dukan tsiya, shiiit bakin nan naki ya mini shiru ko na ciro maki shi a hannunki


Wa ya ga hadiya, Agaishat hadiye kukanta ta yi, tana zaro ido tana kallonsu daya bayan daya tana sauke ajiyar zuciya, 

Ayya tana magana tana yi mata nuni da ta yi hakuri ta yi shiru ta daina kuka


A hankali Agaishat ke ajiyar zuciya sannan ta damke hannun Ayya wace ke rike da nata itama, tana kallonta, a nan ita kadai ta dan hangi laushi a tare da ita 


Tafiya suke suna ratsa sahara har suka baro suka debi titi,

Agasihat ko dis ba baci a tare da ita sai kallon titin da take , tsoro fal ranta haka idannuwanta suka nuna, mamaki take dama Shukoki na gudu? Domin yanda motar ke gudu sai take gannin suma shukokin gudu suke tun karfinsu


Walyn dake takure tana sakin numfashi sama sama ta shiga yinkurin amai tana kakari


Ayya ta kai dubanta wajenta da mamaki, lale walyn bata da mutunci, yanzu du irin yanda ta fafeshe su da turare tana jan tsaki kuma ta kai amai zata yi dan warin Yarinyar da suka dauko

Ta girgiza kai kawai ko ci kanki bata ce da ita ba


Wardugu dake zaune a ransa ya ayanna Walyn bata son zaman lafia, in dai Ayya ce ta isheki ba abinda ya dame ni! 


Ba su su karasa cikin gari ba sai can wajen karfe goma na dare

Abinka da agadez ma ba wani banban gari sosai bane sai ya kasance shiru garin sai yan mata da samari wasu na tafe a kafa wasu a mota wasu a mashin suna dan yawansu na yau da kulun wasu sun nufi gidan rawa, wasu sun tafi gidan cin abinci, wasu suna yawatawa dan shan iskan gari kuma suna hirarsu


Idan ta juya can sai ta juyo nan, kallo take irin na kauyawa sosai jikinta kuwa har zuwa wannan lokacin bata saki ba, sai dai ta rakube jikin Ayya wace take kara rike hannunta dan ta saki jikinta

Direct gidan Sarki aka kai su Ayya, har ciki suka shiga da motar suka sauke su Ayya Walyn sai sauke ajiyar zuciya take ta rabu da alkakai


Har sun juya motar Wardugu ya ce" tsaya


Sojan ya ja ya tsaya ,

Wardugu ya juyo wajen Walyn ya ce" sauka ki kwana wajen Ayya


Walyn ta dago da sauri daga kakabe kakaben jikinta ta zaro ido ta ce" me me ka ce?


Wardugu ya tsareta da wani kallo na kar ki raina min wayo


Walyn ta ce" aman Wardugu , wani irin na sauka na kwana a wajen Ayya bayan ga mijina wajenka na sauka kayana a wajenka komaina na tare da kai? Yama zaka raba ni da kai ka hada ni shakar iska daya da wannan mumunar yarinyar mai siffar aljannu


Yatsina fuska ya yi, a ransa ya ce wai siffar aljannu, ko a ina ta san aljannun ita? A fili kuwa ya ce" Haka na yi ra.ayi


Walyn ta ce" Wardugu kar ka yi min haka, me na maka? Kar ka yi min irin horon nan!


Wardugu ya kalli sojan nan ya ce" sauka mu je


Sojan dai bai ce komai ba ya bude ta fita da bindigarsa yana kallon ikon Allah

Wardugu ma ya fito ya rufe ya tafi wajen sojan ya fara tafiya, sojan ya waiwaya ya ga a yanda suka ajiye motar a bakin hanya, bayan wannan matarsa a ciki, sannan tsakanin fadar da hotel din sojojin akoy tazara, kuma idan mutun ya tunkaro wajen haka kai tsaye daga bakin karfe goma na dare ordre da aka baiwa sojojin shine harbi ba ji ba gani in dai ba a mota ko wani abinda yake malakinsu ba wanda da ya tunkaro wajen akoy adadin odar da aka ce su yi dan shaida su ne wada kowace safiya ake canzawa

Shi dai biye yake da shi da sauri yana hadawa da fan gudugudu suna tafiya har suka fita daga gidan suka dauki hanya (🤔  sisi kika ce zaki iya da wardugu ko?🤣)


Walyn wani ihu ta saki a daidai lokacin da ta fahimci wardugu bara mata ya yi motar gaba daya ya tafi a kafa da ya je da ita, Wardugu ita yake wulakantawa? Toh ita kuwa ba zata shiga wajen wannan uwar tasa da wannan yarinyar mai karnin jini ba! Sai dai ta kwana a motar!  

Haka ta takure a motar nan ta ki kunna hasken waya dan a gaskiya tsoro take ta kunna waya wani abin ya lura da mutun tun bama dare da ya tsala maguna suka fara kukan jarirai ba,




Kawata, tsakaninki da Allah ke haka rayuwarki wata irin mace ce bahaguma? Yanzu yarinyar nan da kika kwaso kin san asalinta ne? 


Ayya ta yi murmushi tana kallon kawarta aminiyarta matar sarki, ta ce" mamanta ta iya tubanci


Anna matar sarki ta dafe kai ta ce" dan ta iya tubanci sai me? Dan ta iya yarenki shikennan sai ki wani kwaso yarta? Kin ce a gidansu kuka daukota


Ayya ta ce" ki gane kawata, lamarin mahaifiyar yarinyar da yarinyar ne akoy sarkakiya, wai kawai dan kalar fatarta shikenan take fuskantar tsangwama, ita kuwa uwar sai kawai ki ji tana yare kuma wai tace itama bata san sunnan yaren ba, kuma ni na yi haka ne dan cika alkawarin bawan Allahnan, baki ga yanda ya tsufa ba aman haka yake nisa lamarinta, 


Anna matar sarki ta dafe kanta da hannunta dake cike da zobunnan zinari ta kalota ta ce" ai idan kin lura yanzu wannan matsakar ta zama ruwan dare, a kauye suna kin bakar fata tare da jahilci a birni suna kiyaye bakar mace dan dogon buri irin nasu sannan suna hakan ne da dabara, kina ganni daidaiya zaki ga a yanzu mutun ya tashi ya dauko bakar mace, sai ki ji suna fadin Allah ya basu farar mace koda maya ce, banza idan ta cinye su fa? 


Ayya ta dora kafarta daya saman daya tana ajiye tufar da ta gutsura ta ce" ba ko.ina ba, ban ki maganarki ba aman nima nace maki ba ko.ina ba, 

Du macen da kika ga ana yi mata duban marar kyau ko anai mata wani gani gani ina mai tabatar maki ita ta saki kanta, 

Mace du muninta idan ta iya wanka ta iya kula da jikinta ta iya kwaliya daidai da yannayinta sai ta kara da adu.a kawai

Sannan ita bakar mace da kike ganni baiwa ne da ita, bakar mace tana da kwarjini, bakar mace nada juriya a kowani fani, bakar mace na da kyau mai fuzga, idan bakar mace ta sakar maki tsararen murmushi zaki hangi haske ne a tatare da ita, ke kawata zaki sha mamakin yar amanata in sha Allah


Anna matar sarki ta yi murmushi tana jujuya kanta ta ce" oho dai, kina kare bakar fata dan kina da ita bayan taki mai kyau ce, na rantse maki ko ni na samu taki ina so domin bakinki mai kyau ne, ba gashi ba Wardugu ya samu dan bakinki da farin mahaifinsa sai ya samu kalar fatar nan ta yan ethiopia baki ga yanda fatarsu take ba? To aman wannan yarinyar kina ganni da akace wanka ta saka kuka aman kika biye mata wai kika rakata ta yi baci a haka? Anya kuwa zaki iya wani gyarata?


Ayya ta ce " ki saka ido kawai.....



Sojan nan tafiya dai yake aman ba karamin gajiya ke tatare da shi ba, sai ya ga Wardugu daga kafa kawai yake yana jefawa yana kara kutsawa cikin duhun garin suna ta sauki su karasa hotel din

Ba su su karasa ba sai kusan sha biyu na dare, 

Suna karasawa Wardugu ya saka kai kai tsaye ya nufi shiga wajen da idan ka shigo harbi ne zai salamo maka ....................






           Kadan ne ku yi maneji😍😍😍😍


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣8️⃣




*Godiya ta tabata ga Allah sarkin sarauta ubangijin talikai, godiya mai dumbin yawa gareku da adu.a Allah ya saka da alkhairi ya biya ....*


*Khadijat tawa ta grup BAK'A CE* wannan page din naki ne




Ja sojan ya yi ya tsaya bai san lokacin da ya ce " Oga, zone interdite ce fa


Wardugu ya juyo yana kallonsa, ya yi murmushi ya ce " tsoro kake ka mutu sergent? 


Kansa ya dan shafa yana kallo  Wardugu,

wardugu ya kara cewa" mutuwa fa ko kana kan gadonka sai ta daukeka sergent ba gwara mu tunkareta ba?


Kara kwalalo idannuwansa ya yi yana kallon wardugu


Wardugu ya matso ya dafa kafadarsa ya yi murmushi ya ce" mu je ......


Haka suka kutsa gaban Sergen din nan tamkar ya bale ya fado dan tsoro, 

Sai dai ga mamakinsa sai ya ga sun kama wata yar raga a nan Wardugu ya bude ya shige

Shima shiga ya yi yana ta waige waige yana biye da wardugu nan ya hango ashe har sun shiga balbalin hotel din sun fice hatsarin


Wara wawar ajiyar zuciya ya sauke yana biye da wardugu

Wardugu ya rage sauri ya dan rage sautin muryarsa ya ce" nima bana so na yi mutuwar bindiga fa Sergen, ina so na mutu cikin nutsuwa kai da zabi gareni in mutu ina sallah kuma ranar juma.a, 

Aman kawai yau ranar asabar gatsai gatsai sai mu tarbi mutuwa? Da juma.a ne ma,


Ya dan yi murmushi ya yi gaba ya barshi nan tsaye yana murmushin shima, kai ogansa idan ya yi wani abin tamkar ba shi ba, wai shifa a nan wasa ya yi masa da rai🤔



Tun fa wuri ta farka daga bacin da ya saceta, sai dai ta ki motsawa tun a jiya da aka sauketa saman gado ta yi baci ta kasa ta sauko kasa ta kwonta saman farin tls din ta rufa da mayafinta na turkudi tana kallon yanda pankar sama ke juyawa har baci ya dauke, a yanzuma ta farka tun da wuri tana son tashi sai dai tsoro take hakan ya sa ta yi kuri da abin mamaki a fuskarta tana kallon pankar nan, mamaki take menene? Ya aka yi bai daina gudu haka ba? A gaban idannuwanta aka kunna , tunda ya dauki gudu bata ga ya tsaya ba, ita tsoroma take ya yo kasa kasa ya kasheta


Ayya ce ta bude dakin ta shigo da salama a bakinta


Firgigit Bak'a ta tashi ta zauna jikinta jikin garu tana bin Ayya da kallo


Ayya ta yi tsam itama tana karantarta, a kasa ta kwana du sanyin nan na kasa, sannan da alama bata yi sallah ba


Dukawa ta yi kusa da ita tana kallon yanda take jan mayafinta tana lulubawa a jikinta, 

Murya a sake ta ce" kin yi sallah?


Da ido kawai Agaishat ke bin Ayya domin bata san me take fada da yaren tubanci ba


Ayya ta yi dabara ta kamo hannun Agaishat ta mikar da ita ta jata suka nufi bayi


Suna shiga Ayya ta dauki butar karfen dake wajen ta kunna ruwa mai dumi dumi ta cika mata ta nuna mata wajen da zata iya dukawa domin ta san ba wani gane lamarin wc zarai ba tukunnan dai, ta yi mata nuni da ta yi dagara ta yi alwallah ta yi sallah , ta yi mata nuni da har rana ta fito


Da kai Agaishat ta amsata tana kallo sai da ta fita ta duka ta yi fitsari nan inda aka nuna mata ta wanke jikinta ta mike ta yi alwallah tana jin dadin yanda ruwan keda dumidumi


Tana gamawa ta fito ta ga salaya aman ba kowa a wajen dan haka ta hau ta tayar da sallah ta yi abinta cikin nutsuwa kamar yanda Baba tsofo ya koya mata


Tana gamawa ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta tana zubar da hawaye, tunani take ya Anna ta tashi? Ya yan uwanta? Ya baba sofo? Wa zai kai masa ruwa? Wa zai gurza masa goro? .    .....


Buda kofar aka yi aka kuma shigowa ,

Wannan karon matar sarki ce da wata baiwa buzuwa da kuma Ayya


Ayya ta kali matar sarkin ta ce" so nake a fada mata ina so ta yi wanka ta shirya mu tafi garinmu domin Wardugu yace jirgin karfe daya zamu bi



Matar sarki ta yi murmushi har yanzu tana mamakin daukarwa kai irin na aminiyarta, ita da ko hausar juna basu iya ba

Ta kali baiwar nan cikin isa da dakewa ta fada mata abinda zata fadawa Agaishat wace tunda matar sarkin ta fara fadi take kallonta daga zaunen da take tana fahimtar yarenta


Kafin ma baiwar ta fadi Agaishat ta kallo Ayya, a hargitse ta ce" ina zamu tafi kuma? Kar ki kaini wani wajen  kin ji? Ki barni a nan ma 


Tana fada ne tana dan nufo su Ayya dake tsaye


Baiwar ta yi saurin tareta , da yaren buzanci ta ce" ki tsaya nan, kin san ina ne kike a nan? Kina garin agadez, a garin agadezma kina masautar agadez, a masarautar agadez ma gaki gaban matar sarki uwar gida sarautar mata,

Ki koma baya ki cika umarninta 


Rakubewa Agaishat ta yi tana kallonsu, ta shiga ukunta, ya zata yi? Matar sarki kuma? Ko sarkin garinsu talaka bai isa ya yiwa matarsa ko yayansa wargi ba bale na garin Agadez 


Kanta a sade ta ce" zan yi wankan


Ayya dake tsaye ta karaso kisanta tana kamo kafadunta ta kallo aminiyarta ta ce" me ta ce mata? Sai nake gannin kamar ta tsorata? Kar ta tsorata min yarinya fa kar ta rikitata


Anna dariya ma kawai yannayin Bak'a ke bata, ta fadawa Ayya abinda aka yi


Ayya ta dafe kanta ta zabgawa matar nan harara ta ce" ku tafi abinku tunda dai ba zaku tausasa ba, idan ita sarauniyarta ce ke ni ai aminiyata ce, bana son irin yanda kike nunawa kan yarinyar nan, kina manta mutun ce itama ? 


Anna ta yatsina fuskarta ta ce" kin ga bara na je na ga in an kawo kayan da kika ce kina so, gaskiya ki yi hakuri ba zan iya wannan faman ba


Ayya na kallo Anna ta juya baiwarta ta bi bayanta suka tafi


Zaunar da Bak'a ta yi gefen gado wace ta takure waje guda, ta juya ta fauko wayarta ta zauna ta danna kira


Ana dagawa ta ce" kana ina?


Amsawa ya yi da" gani gefen aghali muna ratauna wata magana


To ka bari ka zo yanzu yanzu nan bangaren da aka saukeni ina ciki ina jiranka


Da toh ya amsa ya mike yana cewa Aghali ina zuwa


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                        1⃣9️⃣





Shiga ya yi ya zarce dakin Ayya ya tarar bata nan sai ya fito ya shiga dayan dakin, daman falo ne mai daki biyu,


Yana shiga ya tarar da ita tsaye , Bak'a kuwa zaune inda ta ajiyeta


Karasawa ya yi yana tambayar lafia? 


Ta amsa shi cikin kulawa ta tambayeshi kwannan iyalinshi

Ya yi murmushi dan ya san Walyn bata zo nan ba kennan wajen matar sarki ta je? 


Ayya ta ce" Wardugu, zo ka yi mana fasara da y'ata ka ji? Ina son yi mata magana yanda zata fahimta aman ban lamunce maka ka rikita min ita ba ka ji?


Da mamaki yake kallonta, daman shine dalilin kiran nasa? Kai? Yanzu Ayya ya zata yi idan baya nan toh? 


Kai kawai ya dan girgiza ya karasa inda Agaishat ta kara rakubewa jikinta ya fara rawa ta nuna alamar tsoronsa take ji


Ayya ta ce" Wardugu ka yi wani abin mana, ka ga tsoronka take ji, bana so dan Allah 


Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya kali Ayya ya kara kallonta, uwa uwa hummm


Karasawa ya yi ya dan rage tsayinsa yana kallon yarinyar, kokari ya yi ya saisaita maganarsa ya ce" me ke damun ki? 


Kallonsa take ita kuwa, irin kallon nan na kana jiran gannin me za.ai maka


Wardugu ya dan rontse idannuwansa ya bude ya ce" kin ga, mu fa ba mayu bame, ba mugaye bane kamar yanda kike tunani, mamanki tace mu zo da ke, idan kika kwontar da hankalinki kika nutsu sai ina kai ki kina gaishe da mamanki, kinga dai yanda kuka yi da ita ko so kike a mayar da ke ne??


Tsam ta yi tana kallonsa bata bashi amsa ba


Ayya ta matso ta ce" me kake ce mata?


Wardugu ya kali Ayya ya ce" ba komai


Ayya ta ce" to ka ce mata ta tashi ta shiga ta yi wanka , ko na yi mata da kaina ma


Ido Warsugu ya zaro, sai kuma ya basar, ya kaleta sosai ya ce" kin ce Sofo na koya maki karatu ko?


Kai Agaishat ta shiga daga mai 


Ya ce" yawa, kuma sofo ya fada maki tsafta na cikin adini? Sai mai tsafta zai shiga aljannah fa


Agaishat ta kara gyada masa kai, 


Ya fara jin haushin gyadegyadan kan nan, aman Ayya na wajen ta kasa ta tsare, ya tausasa murya ya ce" toh ki tashi ki shiga bayi, Ayya ta nuna maki kayan wanka ki yi wanka sosai kin ji?


Kai ta kuma gyada masa ta mike tana kallon Ayya, tunda ta ji yace za yana kaita wajen Annarta zata gwada yi masu biyaya ......


Ayya da jin dadi ta rakata bayin ta kuna mata ruwa masu dumi sosai ta bata sabulu da soso sababi, ta bude bruch da maclean ta mika mata ta yi mata nuni da yanda zata yi ,

Har ta juya ta dawo tana nunawa ta ce" ki cuta jikinki lungu lungu sannan ki wanke tafin kafafuwanki kin ji


Kai Agaishat ke gyadawa har Ayya ta gama ta fice


A hankali ta tube kayan jikinta, ta yi tsaye gaban ruwan tana kallon yanda yake zuba

Da tsoro tsoro ta tara hannunta ta janye, ta kuma tara ta janye hardai ta yarda da ruwa ne ke zubowa kuma ba zai konata ba


A hankaki ta shiga tana bismillah a ranta ta yi tsaye ruwan ya shiga kwararun mata a jikinta tun daga kanta dake da kitso kwaya daya tal har jikinta


Sai da ya gama dukanta ta dauki sabulun ta shiga gogawa a jikin soson tana jin yanda kamshinsa ke tashi tana jin dadin kamshin

A hankali ta shiga cuda fuskarta da soson nan ta cudeta da kyau ta darwaye kafin ta shiga wanke wuyanta sosai da bayan kunnayenta da cikin kunnen ta gangaro hamatarta kamar yanda Ayya ta nuna mata ta daga ta kama dirza ta yi kasa ta wanke jikinta sosai ta bi ruwan nan ya shiga darwaye mata kumfar da har ta zama baka dan tsabar datin dake jikinta, tana kallo ruwan na bin yar magudadar ruwa yana tafiya 

Ta koma ta darwaye soson ta kara yin yanda ta yi , ta shiga saba sabulun a tufkeken gashinta na buzuwar usul  ruwan nan na dareaye mata, 

Abinka da tufkeken gashi wani wajen ya wanku sama sama aman cikin kam da datinsa daskare, haka Agaishat ta yi ta wanka tana sakewa tana jin kanta wani sakayau tana kara balbaluwa a cikin ruwan nan tana jin dadinsa abinka da ba sabanba ta wanke tafin kafafuwanta da abinda Ayya ta nuna mata nanma ta ga dati sai fita yake , har yatsarta ta saka ta debo datin tana kallo da gaske dati ne ta wanke da sabulu tana daga kanta sama ruwan na shiga idannuwanta yana kara ratsa gashinta da jelar ta sako tana yawo du idan ta juya kan


Fitowa ta yi ta dauki kayanta wa.inda sai a lokacin ta ji suna wani irin bugawa da ta rabu da datin jikinta, har ta shiga tunanin ko ta wanke? Sai wani abin yace mata idan kika wanke ki saka me kuma? Mayar da kayan ta yi ta fito ba tare da ta kashe panpan ba domin bata iya ba


Ayya dake zaune tana jiranta domin Wardugu ya tafi abinsa , ta mike tana fadin" eyah Agaishat ki cire kayan nan mana


Agaishat ta yi kasakai tana kallonta


Ayya ta dafe kai ta ce" wani yare kika iya


Agaishat kin iya frencais? Angalais? Ko hausa? 


Agaishat dake kallon Ayya ta ce" Ayya, hausa kadan kadan 


Ayya cikin itama dan yaren hausar nata ta ce" ouf , mun samu na gaisuwa, ki fida kayan nan ki canza wasu kin ji


Agaishat ta gyada kanta tana kallon wa.inda Ayya ta nuna mata, sannan ta juyo dan gannin a gaban Ayyan zata saka sai ta ga Ayya ta nufi kofa abinta


Ajiyar zuciya ta sauke ta tube kayan ta dauko wa.inda aka ajiye mata


Tsayawa ta yi tana kallon doguwar rigar abaya baka wace bata san ina ne gabanta ko bayanta ba sai dogon wando wanda ta daga tana ta jujuyawa irin na maza ta ayanna a ranta sai dai ba irin na mazan garinmu ba domin wandunnansu tamkar buhu........

Da daurin kirjinta tana tsayen nan Ayya ta dawo ta ga bata saka kayan ba


Nufota ta yi ta ce" aa ya baki saka ba?


Agaishat ta mika mata ta ce" Anna ban iya ba


Ayya ta yi murmushi ta shiga nuna mata ta juya ta saka wandon da kyar domin ya yiwa jikinta kadan duda fadinsa da yanda kuma yake jayuwa, 

Ta dora rigar ta kule yar igiyar dake ciki 


Ayya ta juyo tana kallonta, ba laifi kayan sun amsheta sai dai sam wankan nan bai yiwa ayya ba , gani take bata wanku ba da saura duda yanda du wani jirwayi na turkudi da fari fat din nan ya fita


Mai ta miko mata ta shafa , ta miko mata turare ta tayata shafawa 


Agaishat bata san tana sakin murmushi ba sai da ta waiga wajen madubi


A hankali ta taka ta karasa, hannunta ta mika ta taba madubin tana kallon kanta, a hankali ta juyo wajen Ayya ta ce" na gode Anna


Ayya ta karaso da dan kalabin rigar ta kama kanta da bai karasa bushewa ba ta saka mata ribom ta daure mata sannan ta nada mata dan kwalin ya zagaye fuskarta


Kwali ta dauko ta nuna mata da ta shafa , Agaishat ta ce bata iya ba , hakan ya sa Ayya ta saka mata idonta ya fara ruwa ruwa abin rashin sabo Ayya tace ta jure karta murje ta kuwa juren


Abin maskara ta dauka ta fitar da shi ta saka wani mouchoir (kyale) ta goge bakin jikin tas tas, ta dauki jagira mai ruwan baka ta gogoga a jikin abin ta samu ta caje girar bak'a,  girar ta kwonta tsaf a inda ya kamata ba kamar da farko yanda take wawatse ba 


Ayya ta juyata wajen madubin ta ce" Agaishat, Tsafta, kwaliya, ya zama wajibi ga macen da ta san ciwon kanta, ki rike wanka , ki kasance mai tsafta kin ji??


Kai Agaishat ta daga tana kallon kanta da mamaki, tamkar ba ita ba, ta sawaya hancinta ya wani tafi zuwat, wai a nan Ayya bata gamsu da wankan ba jira take dai su karasa Niamey ta dauki lamarin a hannunta..........


Karfe sha biyu da minti arbadin suka fito daga masarauta suka nufi aeroport, ita dai Ayya bata san yanda wardugu ya yi ya samawa Agaishat waje ba bata tambaye shi ba


Sauran minti biyar suka karasa, suna zaune Ayya na kallonsa yanda ransa ke bace, bata ga Walyn ba bata tambayi inda take ba domin ba wani shiga lamarin juna suke ba, bata san zuwanta ba sai da ta ganta daga ina kwana wani abin bai kara shiga tsakaninsu ba sannan dan yanzu bata ganta ba itama ba zata wani tambayi inda take ba , Allah ya basu zaman lafia ita da mijinta ba abinda ya shafeta da zamansu haka kuma ba zata shiga dan wani gyara ba! 


Ba.a jima ba suka mike domin an fara kiraye kirayen sunnaye, 

Ita dai agaishat tunda aka haliceta bata taba gannin jirgin bama bale wai har ta shigeshi

Ta dai bi bayan Ayya da ta kama hannunta ta shiga nuna mata yanda zata taka matatakalar ta hau suka hau tare tana kara rike Ayya da kyau dan kar ta fadi har suka shiga 

Kallon tsarin cikin jirgin take a ranta ta ayanna ba irin na mota ba , 

Nan Ayya ta tsaya sai da Wardugu ya shige kusan madubin domin sam ya hannata zama a nan in dai tafiar jirgi zata yi, ita dai sai dai ta yi murmushi kawai irin yanda yaron nata ke sonta ke kokarin kareta har mamakinsa take ,

Yana shiga sai ta saka Agaishat ta shige tsakiya , shi kam bai yi magana ba domin ransa a kololuwar bace yake, wai Walyn ta bi jirgin damagaran gobe ta bi na niamey ta karasa, shi zata nunawa zuciya ko? Han......


Ayya ma ta zauna ta ja ceinture ta sakawa Agaishat sannan itama ta saka bayan ta kashe babar wayarta ta android 


Ba.a jima ba aka shiga fadin a daura ceinture a kashe waya da yarurukanmu na niger da kuma french da inglish duka , bayan an gama jirgin ya fara tafiya wace suuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu ne saman doguwar hanyarsa har ya zo wajen hatsarin wato tashi da saukar jirgi ba, 


Cikin adu.a a bakin Ayya


Nan fa ake yinta domin abin tashin jirgin nan, kun san ko wanda ya saba sai ya ji cikinsa ya yi kasa bale wanda shigarsa ce ta fari kuma sha.af Ayya ta sha.afa da fada mata abinda kan iya zuwa sannan tace da ita tashi zasu yi sama, ita kuwa a kauye baba sofo ya taba gaya mata akoy harda wani abin mai tashi sama a birni sunnansa jirgi ,


Ai gaba daya ta shiga jijiga ta damki cinyar wardugu dake gefenta na dama ta damko ta ayya ta bude baki ta........






                 🤣🤣🤣🤣 ku taro su kauyawa a birni🤣😂


Post a Comment

0 Comments