BAKA CE hausa novels 1

 BAK'A CE*


TALLAH   TALLAH TALLAH


 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                    1⃣



*WANI YANKI NE CAN WAJEN AGADEZ CIKIN JAMHURIYAR NIGER mai sunna TIMIYA*, inda buzaye ne ke rayuwa a garin indai ka ga bakuwar fata to lale bako ne ya zo kuma juyawa zai yi ,

A kauyen nan basu da ruwan pampo sai fan take, wuta bata kai can ba , 

Gari ne mai tarin ni.ima , albarkar noma garake , sannan mota bata shiga domin can cikin sahara ne sai dai a hau rakumi a samu a shiga cikin Timiya


Yan mata ne laye su hudu, 

Cikin ukun nan kowace ta kala tamkar ka lasheta dan kyau da daukan hankali sun sha digo digonsu na buzaye da katanga , sai daya a gefensu wace kanta ke sade kasa jikinta na dan rawa rawa hanayenta kawai ake ganni bakin kirin da yafen mayafinta na turkudi (tufafin buzaye ) 


Shigowa wani datijo ya yi yana dan dukawa dan tsayi ne da shi, da hannunsa yake yiwa mutanen dake bayansa nuni da su shigo domin bashida hausar kirki a bakinsa

Yana dago kansa ya hangota a cikinsu, ya juyo da dan sauri ya ga mazan nan har sun zauna

Rai bace ya nufi dakinsu wajen uwar yaran wato matarsa yana zuwa ya daga hannunsa ya dungurewa yar datijuwar kai ransa bace cikin yaren buzanci ya ce" ban hane ki turo min da wannan bakar yar taki ba? Na aurar da yaya hudu saura uku na cire wannan bakar a yayana, na sha fada maki ni a danginmu ba baki aman kika tashi kika haifo min baka? Na yi na yi ki fada min gaskiyar waye ubanta kin ce ni? Kuma dan bakin ciki an samu elhazawa masu son auren yaren kin tunkudo (turo) mini da ita ko?


Bata ce komai ba sai sada kai da ta yi, har ya gama babatunsa ya juya 


Yana komawa ya damki hannunta ya jata kiiiii suna shiga ya hankadata ta tafi tagataga ta duke nan kusa da gadon karagar mahaifiyarta kanta sade, ya aibatata sosai kafin ya juya ya koma wajen bakinsa


Kanta sade hawaye ya ziraro mata, ta dago a hankali ta kali mahaifiyarta da idannuwanta ke rufe ruf tana jin yanda zuciyarta ke suya

Murya a raunane ta ce" *ANNA* (wato mama)


Bata bude idannuwanta ba, bata amsata ba

Ta dan jima a haka kafin take mikewa ta dage rufar da ta yi tana kallon mahaifiyarta da wani irin yannayi, a gaskiya a jikin wannan matashiyar budurwa banda idannuwanta ba wani abu mai hasken fari domin kuwa tana da baki ga kuma tufafinta mai rinar da fata ne wato turkudi

Mamanta ta dago ta bude ido a karo na farko, murya shake cikin yaren buzanci ta ce" kal ki ce komi, ki yi hakuri kawai 


A hankali ta juya dan ruwa gidan baba tsoho....




Ku biyo ni garina, *TIMIYA* domin a Niger nake....   ......taku har kulun YAR MUTAN NIGERSAJIDA


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                    2⃣




A hankali take tafiya tana dan rabewa, da ta hango gugun yara sai ta labe har sai sun fice idan kuwa wasa ne suke dole sai dai ta canza hanya domin irin wulakancin da mahaifinta da wasu a cikin yan uwanta ya sanya har jama.ar garin ke wulakantata suma suna dubanta daban cikinsu....


A hankali ta karyo kwanar runfar baba tsoho


Sanda take dan karasawa domin bata son haduwa da almajiransa tun bama Ali ba wanda ya so hada shi da ita ya ci mata mutunci yayi mata kwakwaran kashedi na koda wasa kar ta yarda ta  nuna tana son sa domin shi dama ya shigo garin Timiya ne dan ya samu buzuwa fara ya aura..to tun daga lokacin sauran almajiran ke tsokanarta suna fadin ta Aliyu *BAK'A*



zaune yake cikin bukarsa, rawani ne a fuskarsa kwaurin hannun sa da na kafarsa ake gani , hakan zai nuna maka tsohon mutun ne, domin fatarsa du ta yi yaba haka gashin dake kwaurinsa du sun yi fari sol sol da su 


Waje daya kawai yake kallo, a zuciyarsa kuwa ya afka tunanin yau ina ta yi? Ya aka yi bata zo ta dauki karatu da safe ba? Bata da kawa, bata da wani mai rabata a jikinsa, mahaifiyarta kanta bata mugun sake mata dan tana tsananin tsoron mijinta a kan yarinyar 

Shi kam yana cike da zulunmin abinda ya sa bata zo ba


A hankali ta daga kasarin dakin ta yi masa salama


Murmushi ne ya subuce masa yana kallonta kafin ya amsa salamarta


karasawa ta yi tana dan tatare tataren dakin ta kai dubanta wajensa, cike da kaunar tsohon sannan idan tana tare da shi takan ji ta wani iri, bata jin tsoronsa sai soyayarsa, tsohon shi ne kawai mai yi mata murmushi a duniya,

Dan murmushi ta sakar masa ta ce" SOFO (wato tsoho)


Shima murmushin ya yi, ya dan nunota da yatsarsa, 


Ta karasa ta duka kasa ta ce" ta gode (gaisuwa kennan)


Turkudin kanta ya shafa a hankali kafin ya ce" Alharasssss


Mikewa ta yi ta gama tatare masa dakin ta dauko tsintsiyar kabar da ta yi da kanta dan share dakins ta shashare ko.ina ta dan dage kasarin ta dauki tulun ruwansa ta fice


Murmushi ya yi, ya bi ta da kallo....a kasan zuciyarsa ya ayanna" Allah ya nuna min farin cikin ki kafin na koma gareshi


Tafe take da tulunta cikin nutsuwa, tana zuwa ta duka wajen diban ruwan , wani dan kewaye ne aka yi shi ba rijiya ba, shi ba teku ba  shi dai ruwan ana jayo masu shi ne, sannan kalar ruwan jajajir ne sai kanshin laka , akoy ruwa masu kyau sai dai idan ta yarda ta je wajen sai dai ta dawo ba ruwan ba tulun domin du yawancin yan matan garin can suke zuwa dibo ruwa su kuwa sun ki jinnin ganninta a wajen


Sai da ta cika tulun ta mike ta gyara bakin zaninta da kyau ta daga ta dora saman kanta


Yanda ta bar shi zaune haka ta dawo ta tarar da shi

Ta nemi wajen Tulun ta ajiye tana dubansa cikin yaren buzanci ta ce" baka gajiya da kallon waje guda?


Bai bata amsa ba sai mika mata allonta da yayi yana nuna mata wajen zama


A hankali ta zauna ya ci gaba da koya mata karatu wanda sosai ta nisa kuma shine malaminta tunda ta san shi

Suna gama karatun ya ce" menene tambayarki ta yau?


Ta yi tsai tana kallonsa, can ta nisa ta ce" sofo, shin mutun mai bakar fata laifi ya yi aka halice shi baki?


Da sauri ya kallota, ganni ya yi kanta a sade, tana faman murza hannayenta .....yarinyar akoy zurfin ciki sosai aman wani lokacin sai ta fadi dan abinda ke ranta domin tana gannin abubuwa masu firgitarwa a rayuwarta


Hannunsa ya daga, murya a sanyaye ya ce" ko daya mutun baki da fari du daya ne a wajen Allah


Dara daran fararan idannuwanta ta dago ta sauke kan nasa da sukai dan ja sannan du sun yi yaba irin na tsohon mutun, hawayen da ya taru a idannuwanta ta yi iya kokarinta ta mayar da su , daga haka bata kara komai ba, bata bari ta yu kuka ba ta mike tsam ta fice ba tare da ta kara kalma daya ba


Ajiyar zuciya ya sauke, yana tir da halayen Agali, Agali bashi da hankali da tunani, dan kawai Allah ya yi yarinya an haifeta bak'a cikin y'ayanka sai ta zama abin kyama abin kyankyami abin wulakantawa? Ita ta halici kanta ne?



Ta jima tana tafiya kafin ta karaso gidan iya mai siyar da nono


Har kasa ta duka tana gaisheta


Iya ta amsata kafin take cewa" kin ga nonon nan yana yi min wuya, ban san me yasa idan kin dauka cinikinki baya fice dala dari da ashirin .....sai dai ki maido mini shi haka du an motsa shi sannan in baki salama  ni kam yau ki yi hakuri na sararma masu zuwa gida sara, kinga daman tausayin ki yake saka ni na  baki dan ki samu dan kudin kashewa


Kanta a kasa ta ce" ki yi Hakuri iya, zan kara kaimi wajen siyarwan  ki zuba min kadan yanda zan iya siyarwa


Kanta ta girgiza ta mike ta dauki kwarya ta zuba mata nono dan madaidaici ta mika mata, ita Allah yana ganni dan tana jin tausayin yarinyar ne aman tana da masu siyan nononta a hannu a hannu domin shannunta suna da yawa 


Dauka ta yi ta fice a gidan, tana tafe tana jin wata irin juwa na daukanta, bata karya ba, bata ci komai ba sai yanzu ta tuna

Ajiyar zuciya ta sauke ta samu gu ta dan rakube ta daga kanta sama ta afka tunani




          Mu je zuwa ci kin labarin *BAK'A CE*



🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                    3⃣



Suna tafiya ya shigo dakin,

Yanda ya barta tunda ya dungure mata kai haka ya tarar da ita

Ransa bace ya nunota da yatsarsa ya ce" ke, 


A hankali ta dago kanta ta sauke kansa tana kallon sa


Y.ayana biyu sun samu miji yan albarkana


Wani abu ta hadiye a makogwaronta, a hankali ta ce" wannan karon wa ka siyarwa yaran?


Da mamaki yake kallon ta, mayar masa da magana ne ta yi? Shi?

Da izgili ya karasa kusa da ita ya nunata ya ce" ke balagazar mace, ke har kin isa ki dube ni ki fda min cewar ni ina siyar da yara? A me kika dauke ni kennan? Matsiyaci? To bara na tuna maki a gidannan daidai da sansannin ( tabar buzaye) da zaki gumtsa sai kin taba tawa ba zaki iya siya ba dan bakya saye bakya saidawa zaune kike dabar ta.kar duwawu komai sai an yi maki, 

To yaranna sun samu mazaje sun yi min kyakyawan tayi! Kuma na fada maki idan har na aurar da yaran nan gaba daya ki kuka da kanki ke da yarki dan kuwa ba zai yiwu ya kasance ina ciyar da yar da ban yarda cewa tawa bace bama


Har ya gama bata kara tofawa ba , ya juya ya fice a dakin


A hankali ta zauna kusa da mahaifiyarsu, itama farinta har daukan ido yake,

Hannunta ta kamo ta rike gam ta ce" zan so ki fada mana tarihinmu kafin muma mu tafi kamar su aunty a daina jin labarin mu, ba labari ba aike ba wani motsi.....Allah kadai ya san halin da suke ciki idan suna raye! Ba yace auren wata biyu kawai zan yi, idan na cika wata biyu na kwaso masa kudade na dawo ko ya sake ni ko bai sake ni ba sarki zai hana shi shigowa garin ........ ki daure ki fada mana tarihin rayuwarmu Anna (mama)

Su waye mu?

Ina ne asalin asalin mu?

Su waye dangin mu?

Bamu da kowa ne sai mu da ku? 

Idan muna da mai ya sa ba wanda ya taba zuwa inda muke? Ina son sani ANNA


Jajayen idannuwanta ta sauke kan *Gaishat*, wai ita nan mai damar ce domin ita bata hantarar Bak'A, sannan tana kamanta bin iyayen su ba kamar sauran ba

Kwace hannunta ta yi ta hade rai ta yi mata nuni da kofa


Ta san kan zancen dan haka ta mike ta fice daga dakin


Kallonta yake tunda ya kirayeta ta zo turakarsa tana zuwa ta tube du wani abin da sunnansa sutura a jikinta, ta tsaya masa a gabansa wato gashi ka yi ka gama na koma


Kansa ya girgiza kafin yake tsareta da idonsa, ya juyar da kansa ya kuma kallota 

Can ya ce" Nadia, haka zamu yi ta rayuwa? Ke ba zaki taba saukowa ki bani kulawar da nake bukata ba? 


Saurin zubewa ta yi kasa ta ce" ka yi hakuri Uban gidana, ban san zan bata ranka ba kar ka hada ni da Ba (Aba) 


Idannuwansa ya lumshe, a gaskiya Allah ya jarabe shi da matsanancin son yarinyar, 

Yarinyar ce ko a cikin bugaje (buzaye) ta fita daban, ta hadu iya haduwa ko ba wanka Nadia mai kyau ce, dalilin haka ya amshi tayin aurenta da Ba dinta ya yi masa bisa sharudan kawar da ido da toshe kunnuwa kan karansa da za.a kawo a cikin garin kan yanda yana tafiyar da rayuwar gidansa, aman ya kasa samun nutsuwa da ita........ya kasance komai zatai masa tana yi ne dan tsoro ba dan soyaya ba


A hankali ya dagota ya jata zuwa ainahin turakar domin yanda yake kwakwarta shi kansa mamaki yake, yanzu dai shekara biyar da aurensu bayanta ma ya kara auren mace biyu ya saki gudar aman har yanzu ta kasa fice masa a rai a kulun yana mai jin zumudin kasancewa da ita.....aman ita ta kasa kontar da hankalinta ko dan matsayinsa na sarkin garin ta murza mulkinta aa tana rabe rabe ne a gidan mijinta

Nadia kennan babar yar *BA*



Ke kin san nawa ne million daya? Jika dari dari har goma fa, an ce Gaishat har million goma sha hudu mutumin ya bada kudin aurenta, 


Ke ki rufe min bakin ki, ke fa haka birge ki yake ko? Kina ganni yanda yake aurar da yayan nasa daga sun tafi shikennan ba labari, kudin ya zo bai yi masa anfannin komai ba, daga an kwana biyu ya kashe sai kuma ya fara harin wata a cikin y'ayan nasa, ai sun kusa karewa zamu ga kuma idan wada ya tsanar zai yi shelar ya siyar


Mahaifiyarsu da ta shigo da Buzu (salaya) a hannunta ta kale su ta ce" ke Amina, ki tashi maza ku je ku yi sallah, wannan maganar kun cika yinta bayan kun san ya zama abin gasa a garin nan, sai kun jaza min abinda ya fi karfina ko? Kuma da hakan bata faruwa da ku dan Ba din ku bai yarda da hakan ba, ku kun fi kowa sanni gidajen da basa haka basu fi a kirga a garinnan ba aman zaku zauna mamakin kwaya daya? Kowa ya yi da kyau kai nasa! Ku mike ku bace min a wajen nan kar ku yarda maganar nan naku ta yi tsayi ya zo ya tsige mu baki daya domin ku kun san waye shi !



Sumui sumui suka fice dan zuwa yin alwallah su gabatar da sallah



Sai yama sosai ta kamo hanyar gida,

Tana tafe ne tana dan jin dadin yannayin garin domin sanyin yama ya fara busawa sosai ita kuwa gwanar son sanyi ce sosai

Ba ita ta kai gidan iya mai nono ba sai kusan magariba, ta kai mata cinikin inda iyar ta bata dala ashirin da biyar ta yi godiya ta mike

Har ta kusa fita iya ta kirayeta ta dawo

Ta ce" kin ga , ga abinci nan ki dauka ki ci mana ni na ci na rage, sauran ki yi min halin naki sai na tabatar kina kyankyamina ne na san irin matakin da zan dauka


Fanata ce ta fito daga daki, kmar kulun cikin mahaukacin gayu mai gigitar da jama.ar garin ....Fanata dai y'a ce a wajen yar uwar iya wace ke aure a cikin garin agadez, mahaifin fanata Babarbare ne shi ya sa sunnanta ya fita daban , 

A da fannata ta kasance ita ba fara kar  ba ita ba baka ba duda mahaifiyarta farar buzuwa ce, 

Aman kasancewarta a can cikin birni, da taraya da kawaye ya saka take shafa mai wanda ya mugun karbarta ta yi fari kar kar kar harma ta fi maman nata farin, 

Fannata akoy kyau ga iya daukan wanka

Tana son garin timiya a rayuwarta domin gari ne mai cike da ni.ima 


Tunda ta fito take kallonta da mamaki,

Dubanta ta mayar wajen Iya ta ce" iya, yarinyar nan mai maki tallah ce ta girma haka? 


Iya ta ce" eh ita dai ce


Fannata ta yatsina fuska ta ce" to aman har yanzu sunnan da ake kiran nata da shi ne? Wato *BAK'A*?


iya ta amsata da kai


Fannata ta kallo wajenta ta kuma kallon iya ta ce" menene sunnanta na gaskiya ne ita wai?


Iya ta kalli Bak'a, ta kalli Fannata, ta ce" sunnan Hajia ne da ita, karfi da yaji Ba dinta ya mayar da sunnanta Bak'a har ake mata kiranye da haka


Da mamaki Fannata ta karasa kusa da ita tana kallonta,

Yarinyar fa nata wani tsararan kyau, boyeyen kyau, duda mugun bakinta ga bakin turkudi na bugajen kauye🙈🤣, ga dati da take fama da shi, aman ita tana hango wani al.amari a tatare da yarinyar, to aman me zai hana ta shafa mai itama? A sanninta ba bakon lamari bane buzu farinma ya shafa mai, kai ba buzu ba yanzu abin ya zama larabawama mai suke karawa shi yasa zaka gan su wani farfarfar da su sunna daukan ido, ba sai dan duniya ke shafa mai a duniyarmu ba, mun dauki mai mun mayar da shi abin kmgyaran fata, ra.ayi ne shafa shi idan ka shafa ba mai yi maka kallon dan duniya a karkarar mu 


Abimcinta take ci kanta a sade tana ji yanda Fannata ke aikin tambaya a kanta, tsoro take kar a je mugun kyankyaminta kamar yanda mutanen garin ke yi ya saka take son sannin ko ita wacece dan ta kara samun damar ci mata mutunci, hakan ya sa take sauri dan ta gama cin abincinta ta kara gaba , so take ta siyarwa SOFO goro na dala biyar, ta  saka dala goma asusun da take tarawa dan ta bawa Ba ko ya daina tsanarta, Gomar kuwa itama ta ci wani abin



             *AGAISHAT*

ta ji sunnanta a sama sama yana yawo, sunnanta na gaskiya aka kiraya,

Da dan sauri ta dago sukai ido hudu da Fannata,

Fannata ce ta kirayi sunnanta na ainahi ba bak'a ba.............



🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                      4⃣




A hankali ta kai idannuwanta kan Fannata dake kara matsowa kusa da ita


A hankali fannata ta saka hannunta ta dago na Agaishat, kallon hannun take tana jujuyawa, fannata ta fahimci bayan bakinta na halitarta da Allah ya yi, akoy tarin dati ga kuma karin bakin turkudi,


Da sauri Ta janye hannunta tana kokarin mikewa daga cin abincin cike da tsoron menene kuma Fannata ke taba mata hannu?


Fannata ta ce" kin ga, ba abinda zan maki 


Kallonta take da mamaki domin da hausa radau Fannata ta yi magana bayan Agaishat kadan kadan take jin hausar itama baba Tsoho ke dan koya mata dan abinda ya iya, yakan ce ba.a san gobe me zatai ba


Goshinta ta dafe ta kalli wajen iya ta ga sai faman gyara Sansanninta take(tabar buzaye), tana dan kukulewa da zare tana ajiyewa gefe tana yin kulin kadago kadago (dala biyar biyar ) 


Kurumci Fannata ta shiga yiwa Agaishat,

Ta yi mata nuni da hannayenta da fuskarta gaba daya,

Ta yi saurin taba ruwa ta nuna mata alamar bata wanka  ne?


Agaishat ta shiga faman saka tsohon takalminta na soso tana faman guduwa domin ta saka a kasan zuciyarta wannan abin zai kare ne a wulakanci da tozarci




*WaRDUGU*



Ta fada tana mai daga murya kamar zata kaiwa gabjejen mutumin dake tsaye a gabanta duka,


Ta kuma cewa" WaRDUGU Odon jidu anna indahan yuna yugusnan gwa ( tun kana yaro yake fama da kai)


Kansa ya dafe, ya kai dubansa kan agogon hannunsa, kallota ya yi ya yatsina fuska, can ya ce "Ayya (wato mama), Ayya inda medi mundu tam (wato mama ke rigimarki ta yi maki yawa)


Hannunta ta dora a goshinta ta shiga kai kawo, kai take tana kawowa, can ta dauki wani ihu ihu tamkar tana buda, ta je ta dawo ta je ta dawo, ta kallo shi cikin yaren hausarta da bata fita da kyau  ta ce"  shikennan rayuwar bariki (gayu) ta lalata min kai, shikennan na zama uwar da ina fadi ba.a saurarena, ko nima zaka kula zazafar gabar da ni ne kamar yanda ka kula da Abbanka (mahaifi)?


Hannayensa ya jimke ya daki garu da su, kafin yake juyowa wajen mahaifiyarsa, 

Taku ya yi zuwa gabanta kafin yake sada kansa, shima cikin yaren hausar sai dai tashi ta fi dan goguwa ya ce" Ayya ba dai saboda wajen wannan bugudin (tsofo) ne kike daga hankalinki harda hada kanki kike min da wannan Bugudin (wato mahaifinsa)?


Kanta ta kawar ta ki bashi amsa hakan ya sa ya mike ya fito daga falon 


Yana fitowa ya nufi wani dankareran mashin *ROUTIER* jibga jigban nan masu shegen tsada domin daga million daya abinda ya kai har million shida ne, kuma mashin ne ba mota ba...gudunsu ma daban yake da kananun mashin 


Bakin gilas dinsa ya fitar ya saka ya tayar da mashin din ya yi masa wani irin ja wanda kana ganni tamkar dambe ake da mai jan da mashin din domin mugun karfi ne da shi ga kyau


Hangame gate mai gadi yayi don kar ya jawa kansa bali wajen Wardugu


Yana fitowa daga  anguwa *Plateau* a birnin Niamey ya nufi *Francophoni*  inda gidansa yake


Yana karasawa shima tuni an hangame kofar ya shige da gudun tsiya ya silala wani waje da nan ne ma.ajiyar abinda ya shafi mashin da motoci


Dira yayi ya juya da sauri sauri ya shiga hawa matatakalar bangarensa domin bangare daban daban ne da matarsa mai sunna *GALayn* 


Wata yar karamar carte ce ya dora mai dauke da hotonsa ya dora daidai wani detecteur ya bada dan kara titeeee kofar ta bude

Caicaicaicaicaicaicai wash, gidan tubawa kamshi, wayo gidan batube ni.ima, bale mai auren gimbiya hajiar hajia, sarkin tsafta, sarkin ado, kwaliya ba dai a nuna mata ba, ta kasance cikin kamshi wanda indai kai ka ce zaka kwaikwaya sai dai ka tashi da mura (gaisuwa yar baba)


Sanyi mai hade da kamshi ne ya buso shi, sanyi mai sanyaya zuciya

Terrace din dakin fara kal kal kal haka take daukan ido ta sha guga, 

Tafka tafkan salon ( kujeru) ne irin na zamani masu kalar fari kal kal sai dan coussin kananuwa sosai su kuwa masu kalar baki kamar yanda mauquette  (capet)

Rido (wato labulaye) yen dakin suma kalar fari ne, sai dai farin ba kar ba kamar yanda kujerun suke , shi ya fi ruwa da kalar peinture  (colern) dakin, shima an saka abinnan na daure labule baki wanda kana ganninsa ka san ba karamin kudi bane dakin ba wani tarkace aman komai ka kai dubanka ka san karshe ne sannan ya bada kala ta mamaki, 


Nan ya yada zango, ya daga kansa sama ,

Iska ya furzar yana jin yanda takalmin matarsa ke tahowa kwaskwaskwaskwas

Kamshin da take fitarwa shima na daban ne, ta shafa turaruka har ta gaji,


Tunda ta fito take kallon yannayin fuskarsa, a cikin ranta ta ayanna" wani masifafe kuma ya hargitsa min yannayin miji?


Bata yi kasa da gwuiwa ba ta karaso kusa da shi ta daga damatsunnan hannayensa ta shiga masaging a hankali tana kara kallon yannayinsa


Murya can kasa ya ce" *ADIBIRA* (Matata)


Tsai ta yi tana kallonsa kafin ta ce" qu'est-ce qui ne va pas  mon Bb? (Me ke  faruwa  Baby?)


Kansa ya kawar gefe kafin ya janye hannunta a hankali ya mike ya nufi uwar dakansa


Bakinta ta tabe, Galayn akoy saurin fushi, mace ce iya mace aman bata tunnanin zata tsaya tana wani bibiyar namiji ko waye shi balatanna wardugu? Wardugu zuma ne ga zaki ga halbi, wardugu ko a cikin tubawa tsoronsa ake, mutumin da idan ransa ya baci idan bai samu ya damki mutun ba yake suma? Mutumin da ya wawuri ogansa ya daga sama ya nana da kasa ogan nasa bama na niger ba domin a niger ba marichal, bako ne da kowa ke tsoro yana shayi, gardama kadan ta hada su General Wardugu ya daga shi ya nana shi kasa a gaban yaransa da kuma yaran general, wannan abin ya jaza masa da mukaminsa da komai shugaban kasa ya tsaya kai da fata aka tura shi daji can wajen mali sai da ya yi wata hudu ya sauko, aman maimakun abin ya yi sauki sai kara gaba da yayi, mutumin dake gaba tukura da mahaifinsa , fada yayi gwa da gwa cewa abansa ya kiyayi hanyarsa kan laifin da ya boyewa kansa sai shi sai mahaifiyarsa suka sani, ita a wa zata tsaya ta bi bayan wardugu da idan ransa a bace ka bashi hakuri yake hucewa kanka? Du irin yanda yake ikirarin shi yanzu ba ruwansa da fada da mutun na gugar jiki karya ne ! Ka yarda ka yi  gigin kai masa wargin baya ce masa komai ya ciro daya daga cikin wukaken dake jikinsa ya burma maka idan ya so a kashe shi, Wardugu nada zuciya ta ainahin tubawa....




Mu je zuwa labarin *BAK'A CE*


🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫



Na            *SAJIDA*




 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________






                      5⃣








Mikewa Galyn ta yi ta fice itama ta bi ta babar kofar danma ya san ta yi tafiyarta ta je ta kara bada turaren ruwa a jikinta ta fito ta je wajen da kys din motoci suke ta dauki guda ba tare da ta tsaya zabe ba domin kuwa kaf ciki manya ne


Tana fitowa ta shige motar ta tayar ta fice abinta wajen auren kanwar kawarta tana mai duba carte dinta ta bank dan ta tsaya ta ciro yayan banki na kari a wajen wasa.... 

      Wannan kennan



Ya yi kai kawo ya fi a kirga, ya dafe kansa yana tunanin irin nacin mamansa kan abu, ita yanzu dan wani tsoho can daban zata dame shi kan sai ya kaita, shi ya san wani bai isa ya bashi lafiya ba aman har fadi take shi ya taimake shi yana yaro, an dai dudura masa itatuwa haka kawai za.a kashe masa kwayoyin jiki


Tsaki ya ja mai karfi, ya mike ya shiga cire kayan jikinsa masu nauyi ya rage masa culotte kawai

Da dan gudugudu yake kara taka matatakalar benen bangarensa har ya karasa bangaren da piscine dinsa take


Ba tare da wani tsaye tsaye ba ya fada cikin ruwan nan ya shiga iyo tamkar wani kifi yana kai yana kawowa ba wani alamun gajiyawa a tatare da shi


Ba ita ta kai gidansu ba sai can dare har wajen karfe tara abinka da jeji shiru garin sai kukan tsuntsaye sai jefi jefin samari da yan mata ana tadi domin sukan kai har goma suna tadinsu


A hankali ta shige gidan nasu ta samu ta leka kanta 

Fitilar kwai a kunne, sai dai tana jiyo minsharin Abansu dan haka a hankali ta kutsa ta nufi dakinsu yan matan gidan


Mahaifiyarta ta gani zaune saman abin sallah, da alama ita take jira duba da irin yanda ta tsareta da ido 


Jiki a sanyaye ta karasa kusa da ita kanta duke ta ce" ANNA


Bata amsata ba sai kureta da ta yi da kallo,


Ta jima duken nan, aman bata mike ba domin ta san wani abu guda da mahaifiyarta keda na buzaye tamkar wata yar gidan sarauta koda yake du buzuwa ko buzu haka ne dadaya ne basu da shi wanda mutane ke jifansu da sun cika *Ashak* ,



Can kamar ba zatai magana ba ta ce" kin ga, ko wani hali zaki shiga, ko wace rayuwa zaki fuskanta *AGAISHAT*, ki guji sabawa mahalicin ki, ki rike mutuncin ki , ki ci gaba da hakuri watarana sai labari


Kanta take gyadawa, kuma wani dadi ta ji har cikin ranta, ko ba komai ta san a duniya bayan baba Sofo Annartama bata kyamatarta, tana kawar da kai a lamuranta ne dan gudun fitina, irin yanda Abanta ke binta da shari kwararo kwararo ya sa mutanen garima haka, ba mai kulata da daraja, ko magana za.ai mata ba.a mata ita a mutunce, ya kasance ko gaishe da mutun ta yo sai ya yi mata yatsina domin Abanta bai barta haka ba har shari ya yiwa annarta kan cewa ko dai wajen baba Sofo take zagayawa gannin irin yanda ya damu da ita ?

Wannan wutar kafin ta mutu sai da aka sha tashin hankali, baba tsoho ya yi kuka sosai aman bai daina kula Bak'a ba domin tana da mutunci yarinyar, shi Allah bai azurtashi da yin auren bama domin bashi da lafia ko ya yi ba anfani hakan ya sa yake jin yarinyar tamkar yar da ya haifa, itama tana mutunta shi tamkar mahaifinta


Mamanta na gama fadar haka ta yi shiru kanta itana a saden tamkar tana gaban sarakuwarta


A hankali ta mike ta nufi dakin su


Tana zuwa ta tarar du sun yi baci abinsu dan haka ta dauro alwallah ta shige ciki ta tayar da sallah ta shiga ramuwar wa.inda batai ba , tana so du rintsi ta ringa samun gurin sallah sai dai tana tsoron mutane da kwagirar su, yanzu za.a wulakantata dan haka take bari idan ta zi gida sai ta yi wanda bata samu ta yi ba


Tun karfe takwas na safe Aba ya fice bayan ya canza rawaninsa daga baki zuwa maroon turkudi sabo fil, ya sayi tufafi ya sayi rawanininka harda waya, ya fito sabo kudi sun fado shikennan a haka zai fada su tamkar wuta shima ya dankaro aure daga an cinye kudin shikennan ta gudu abinta


Bai jima sosai a wajen ba ya dawo,

Daidai lokacin Anna na fitar da dawar masararsa a ruwa wace ra jika dan tana son yin garin tuwo


Bai yi mata magana ba ya zarce dakinta dake baban daki idan ka cire nasa a gidan, daman dakuna uku ne, da nasa da na Anna da na yan matan gidan

Bai yi wata wata ba ya shiga kwasar kayanta yana kaiwa dakin yan matan yana jibgewa gefe guda, 

Ba wanda ya tanka shi ko ya yi mamakin lamarinsa domin sun san halinsa, haka yake du idan zai yi aure dakin mahaifiyar su yake fitar da ita ya hadeta da su ya kawo amarya, bama zai barta a dakinta ba sai dai ya hade su ya kawo amarya su sha shagalinsu ba wanda ya isa ya yi magana yanzu zai cici masa uwa ko waye


Ko kallo bai isheta ba, don ta daukarwa kanta alkawarin in dai ba mutunci ne lamarinsa toh ba zatana kai kanta yana wulakantata ba gaban yayanta. 

Sai da ya gama fitar da komai kafin yake fita ya shigo da magini

Sosai aka gyara dakin ya yi tas da shi 


Tare suka fita , sun jima sosai kAfin yake dawowa

Wannan karon kuwa masu shigo da kaya ne 


Mariama dake wanke fuskarta bayan ta shafa kurkum ta yi tsai tana bin kayan da kallo,

A gaskiya siyayar idan ka yita a kauyen ka isa ne, tun daga gado har kayan abinci na gayu ya kwaso abinsa sai dai abin haushin babu rabonsu a ciki na amarya ne, domin idan ka auri jar buzuwa ko duniya zaka kai gidansu nasu ne ba za.ai mata komai ba sai dai a kawo maka ita daga ita sai butarta (a kauye fa kar a ce inji sajida🤣)


Sai da suka gama kawo kayan tsaf Mariama ta je faban mahaifinta ta tsaya masa kerere a gabansa, somin kuwa in dai haihuwar rashin mutunci ne ya haifa Mariama ta isa ta iya tsayaya tamkar mahaifinta


Ido tar cikin nasa da yaran buzanci ta ce" Aba ya haka? Na ga ka fara kwaso kaya alamun aure zaka yi? Ya baka fitar da mu ba? Baka ba anna kudin siyayar kayanmu ba?


Kun san wasu iyayen sun fi son yaya masu tsayayar nan, domin Aba yana dan shayin lamarin yar tasa domin a yanda yake gani tama fi shi rashin mutunci dan haka ya dan gyara rawaninsa irin zai yi magana ya ce" wani siyaya kuma? A sanina cikakiyar buzuwa ba.a yi mata kayan daki?


Ta yatsina bakinta ta ce" sai kuma cikakiyar buzuwa ana yi mata sutura


Karya ne Mariama, ya fada yana matsowa kamar zai doke ta, ya ce" ku ne yayan zamani kuke zuwar mana da abubuwan da suke neman fin karfin tunanin mu, ko uwarki haka aka bani ita, haka ake kai ku daga ku sai turkudin amarci da buta, kudin auren ku kuwa mu iyayen ku ke siyan maku kadara mu ajiye maku a nan wanda idan kun waiwaya zaku ji dadin su


Wani malalacin murmushi ta saki tana kallonsa 


Ya ci gaba da fadin" ke da kin ga minister ne ya turo a nemi aurenki, ya saya maki komai, sannan ke da auren wata shida ne zaki yi ki kwashe komai ki dawo mini mu more da kudi? 


Tar ta kara saka idannuwanta cikin nasa kafib take juyowa ta ga mahaifiyarta ta fara daka dawar da ta wanke ta baza a rana ta sha iska tana so ta mayar da ita gari kennan , ta kuma kai dubanta wajen yayarta *BAK'A* dake ta dirzar wankin yan matan gidan harda na su kanenta ita dai burinta idan sun tashi su bata konce, ta kuma kallon mahaifinta dake kokarin shi dole sai ya yi mata wayo, wai wani harda cewa wai ya siyar masu kadara, shi? Kudin aurwnsu bai taba wata a hannunsa ba komin yawansu zai kashe su  ne ya dawo talakansa marar mutunci, yan yatsunta biyu ta hade ta yi tap tap da su suka bada dan sauti kafin ta ce" ka kirga kudi, ina so ka bawa Anna kudi har million shida a cikin kudin da ka karba na auren mu domin na sani cinikinmu kake tamkar abin siyarwa baka amsan kasa da goma, ka bamu shida mu je birni tare da Anna mu siyo kaya mu dawo idan baka yi haka ba zan shiga duniya na saka ka a matsala kai da wanda ya kawo kudin aurena, ka san ni horonka ce 


Yana tsaye bami bude har ta fice a gidan, kallonsa ya dawo wajen Anna, da sauri ya karaso ya ce" kina jinta kika yi tamkar baki gani bayan kin san tana jin nauyin zuciyarki? Ko ke kika kitsa mata a taru a cuce ni? Har million shida? Ai kudin sun kusa karewa idan na baku haka! 


Bata bashi amsa ba ta ci gaba da dakanta , nan ya juya wajen Agaishat ya ga shi take kallo


Ke dan ubanki daina kallona da wasu tula tulan idannuwanki masu kama da na mayu, shegiya da aka kwaso cikin ki a waje aka yayaba min, dan bakin jini ko almajiri na yiwa tayi guduwa yake, zan zo in kwakwale miki idannuwan nan in baki a hannayen ki ki je ki kaiwa tsohon dan iskan nan da kike zuwa kina wuni wajen shi wama ya san ko me yake maki a bukar nan


Da sauri Annan ta juyo wajen shi, ta kai dubanta wajen Agaishat da ta sada kanta jikinta na bari, tausayin yarinyar ya kara dirar mata, nan ta kara gane shi ya sa idan ta fice take cika dare dan kar ta hadu da mutumin dake mahaifinta aman ya zamo makiyinta , ta rasa da wata kalma zata kirayi mutumin dake miji a gareta, ta san ya yi karatu, sai dai son kudinsa ya fi imaninsa yawa


A hankali ta ce" ki je kawai zan idasa maki aikin


Da sauri ta ajiye wankin ta warware mayafinta na bakin turkudi butubutu da shi ta yane jikinta gaba daya ta fice har tana hardewa tana waiwayen gidan nasa


Bakin wata bishiyar mangwaro ta zauna ta fashe da wani matsanancin kuka mai karfin gaske






             Ku mu je a labarin Bak'a ce na sajida



Post a Comment

0 Comments