COMPILED BY
ESHAAT SMILER
HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE
?🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 1*
Ina me farawa da sunan Allah subahanahu wa ti'allah Wanda shine zemin jagoranci rubuta wannan littafi nawa, INA me roqon Allah daya bani ikon gamawa lfy,,
Wannan lbariine da ya faru da gaske ba wai qagaggen labari bane, cikin ikon Allah zan fara kuma in gama da ikon sa.!
***
Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya CE wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba she kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta be, cike da damuwa yarinyar ta daga manta ta kalli mahaifin NATA cika da kulawa tace wllh Baba nagaji kawai ka tafi idan na huta zan tawo cike da damuwa ta ware maganar
Cike da kulawa mahaifin nata me kallonta sannan yace to rabe, amma fa ki kula sosai a nitse ta amsa da to baba, yana kaiwa nan ya juya ya nufi hanyar gida, yana tafiya Rabe ta nufi wata bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta core takalmin robar dake wafarta tana cirewa ta shin gida, bata jima da kwantawa ba bacci ya dauke ta sabda gajiyar data yi mata yawa kallo daya Zak ayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da take
A hankali iska me dadi ta fara kadawa can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar rabe daga bacci a hankali ta daga idonta zama aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci Yayi maganar aiko se shanun suka fara tafiya kamar yana tace musu suna cikin tafiya aka fara ruwa kamr wasa can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin qwarya aiko ruwan nan haka yayiwa Rave dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji 'yana magana lol
Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya aiko jikin ta yay jajir da jar qasa haka tai tayi har seda ruwan ya dauke sannan ta kama hanyar gida basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta qarasa inda bukkokin su suke da gudun ta ta qarasa bakin qofar da zata sada ta da dakin matar babanta da sallama ta shiga tare da fadin inna na dawo cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa ta fara CE mata ki fita ki bani guri shegiyar yarinya me baqin jinin tsiya har yanzu kinqi auruwa sabida baqin jininki uwarki ma a tsiyace ta qare kuma kema a haka zaki qare muddin ina numfashi,
Tunda ta fara maganar Rabe me kallonta cike da rashin fahimta dan ita harga Allah bata fahimci abinda innah Laure take nufi ba Sam kullum tana gaya mata haka amma Sam abin baya damun ta amma kuma meyasa take yawan gaya mata haka? Kuma meyasa take yawan tunani akan magar innar a yan kawanakin nan?
Cike da mugunta inna Laure ta dauki kwanon dake gabanta ta jefi Rabe dashi a gishi aiko nan da nan mini ya fara fita a goshin ta a gigice ta juya ta nemi hangar fita daga bukkar dan Neman agaji sabida gigita da tsoron jini da Rabe keda shine yasa ta nufi hanyar garken shanunsu aiko se sukayi kacibus da mahaifin ta wato malam moddibo,
Cike da tashin hankali take firta innanillahi'wainnah'ilaihirraji'un
[8:47PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 2*
Cike da tashin hankali ya nufeta tare da kama goshinta da sauri ya kama hannunta suka nufi dakinsa dan yasa mata maganin daze tsayar da zubar jinin, cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya,, amma sedai goshin ya kumbura sosai kuma Yayi jajzir kasancewarta fara, a hankali ta shiga sauke numfashi sabida zafin da gurin ke mata cikin sanyi murya baba ya fara magana Lamar haka
Rabi'atu kiyi haquri da rayuwa kamar yanda nake gaya miki kullum kuma dik abin da ze dinga hadaki da Laure ki dinga kauce mashi sbda bata da burin daya wuce ta illatamin ke, kuma sanin kanki be bani da kowa yanzu seke tunda na rasa mahaifiyarki na rasa wani bangare na rayuwata shikuma dan uwana tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa seda ga baya aka samu gawarsa a bakin hanya, run daga lokacin muka dena bin titi da dabbobin mu, tunda na rasa iyaye na ban qara samun farin ciki ba seda na auri mahaifiyarki, amma itama daga baya Allah ya karbe ta, ta rasu ta barmin ke tun kina shan nono a haka kina fara girma ina kula dake
Bayan rasuwar mahaifiyarki da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na qara aure sabida ki samu rayuwa me in ganci, cike da damuwa na kalleshi nace mai yanzu iro wace macce zan aura wadda zata Iya kulamin da Rabe??
Har ga Allah bana so ta rayu da ciwon maraici cike da kulawa malm iro ke kallon sa har ya gama mgana,,
Can kuma se Yayi murmushi yace zan baka qanwata Laure ka aura nasan zata riqeta da gaskia, badan zuciyata ta ameence ba na yarda nace zan aure ta
Da malam iro ya fahimci zuciyata bata gama amincewa da mganar auren ba se ya sake murmushi a karo na biyu yace indai ka amince ka aureta nikuma nayi maka alqawarin zan zama me koyar da ita ilimin addini cike murmushi ya qare maganar,
Batare da tinanin komai ba na amince zan auri Laure. Ashe abinda ban sani ba shine sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikina na auto ba ya qare maganar tare da matsananci kuka😭😭
A nitse Rabe ta rarrafo kusa da mahaifin nata ta rugumeshi tana kuka tare da share mai hawaye da tafin hanunta seda moddibo Yayi kukan me isarsa sannan Yayi shiru, cike da kulawa yace kinci abinci ko? Da sauri ta daga masa kanta alamar ae kuma a zahirin gaskia bata ci ba the ae ne kawai dan hankali n mahaifin nata ya kwanta
Moddibo yay murmushi yace to maza tashi ki tafi daukar karatu maza jeki kuma banda tasayawa wasa kinji Allah ya albarkaci rayuwar ki Rabe na
Ta amsa da amin sannan ta tashi ta nufi makarantar allon malm iro inda take daukar karatu
Dik da cewa su fulanin daji ne amma hakan baya hanasu karatun addini dik cikin sa' oin Rabe babu wacce batayi aure ba se ita da ruqatu sune kawai suka rage a yaran da basuyi aure ba
Rabe kyakkyawar yarinya ce kallo daya zakai mata ka fahimci hakn tana da many an idanu tare da gashin gira me yawa hancinta dogo ne sosai kamar na mahaifin ta sannan ya a da dan fadi kadan labbanta ma daidaita ne kuma suna da dan tudu kadan tanada yalwataccen gashin kai ma'ana yana da tsayi sosai, Rabe doguwa ce amma ba sosai ba kallo daya zakayi mata ka fahimci tana da kyau da diri irin na fulanin asali, Rabe miskilace ta ajin qarshe magana ma ba damunta tayi ba balle ma tayi ta sedai hakan baya hanata Haida muta ne rabe yarinya be ma'abociya fara'a da son karatu hakan ne yasa malm iron ke qaunarta sosai
Sbda tana gane karatu sosai koda wasa bata sakewa samarin rugar tasu wannan ne yasa suke cewa tana da girman kai , amma a zahiri sam ba haka bane, a nitse ta qarasa makarantar ba Wanda yazo se ita kadai tan zuwa ta ajiye allon ta ta dauki tsintsiya ta share gurin sannan ta shimfida tabarman kabar tahau ta zauna ta fara bitan karatunta dan a ranar zata wanke allon ta
Tana cikin karatun ne ruqatu ta qara so da sallamar ta amma rabe bata tsayaba seda takai aya sannan ta daga kai da murmushi ta ansa mata sallamar
Ruqatu tayi dariya tace sannu sarkin hadda shine ko ki biyo min ko?? To ai gashi nazo nima kuma nasan dan ki rigani wanke allo ne yasa kika tawo kika barni ko to ai na gane wayon naki
(cikin harshen fulatanci suke maganar nayi haka be dan me karatu ya fahimci gundarin labarin sbda idan nayi ammafani da harshen fulatanci ba lallai wani ya fahimci abinda nake labarin yake nufi ba)
Rabe tayi dariya yace ruqatu kenan keada zakiyi aure kwanan nan ai kin ma kusa ki dena zuwa makarantar
Ruqatu ta hade rai tace to ai se munyi sauka zanyi kuma yau saura sati biyu mu sauke da ikon Allah murmushi Rabe tayi sannan tace to Allah ya nuns mana sati biyun
[8:47PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page -3*
Da haka suka rufe hirar tasu saka makon qara so wan malm iro gurin cike da girmamawa suka gadashi ya amsa tare da sakin fuska yace dasu qawayen juna sukai murmushi suka sunkuyar dakai,,
Ruqatu aka fara biyawa kallonta sannan aka biyawa Rabe nata, suna kammalawa sukayi sallama da mlm suka kana hanyar gidajensu a hanyar komawar su ne sukai kacibus da Aliko Wanda ze auri ruqatu, cike da fara'a suka gaisa da Rabe ita kuwa ruqatu se boye fiska take a bayan Rabe wai ita kunya lol
Basu jima a tsaye ba Rabe tayimai sallama ta nufi gida cike da tinanin me zata tarar ta bata dawo gida ba se yamma liqis kasancewar suna da nisa da makarantar, cike da fargaba ta qarasa dakin da take kwana ta kwanta tare da sauke ajiyar zuciya,
A hankali ta firta alhamdulillah, dan har ga Allah batason haduwa da inna Laure dan tasan haduwarsu ba alkairi bane, tana cikin wannan tinanin ne taji kamar an taba mata qofa da sauri ta mike tsaye dan a tariga ta gama tsorata a, a zatonta innah Laure ce , da sallama ya shigo dakin tana ganinsa ta tafi da gudu ta rungume shi se kuma ta fashe da kuka sosai kukan ta ke taba zuciyarsa be hanata ba sda tayi me isarta sannan modibo ya share mata hawaye yace da ita kiyi haquri Rabe nasan tsoron Laure ne yake damun ki amma kiyi haquri wata rana se labari kinji ? Da sauri ta daga kanta alamar ae a hankali ya kama kafadunta ya zaunar da ita a bakin katifar ciyawar dake dakin yace daga yau nayi miki alqawarin bazaki sake kukan rashin uwa ba kinji ? Yana kaiwa nan a zancen sa yay hanyar fita da sauri ta dago tace baba kayin aure ko zan dena ganin innah Laure!
Cike da mamaki moddibo ya juyo yana kallon Rabe😳 aure kikace Rabe? Ba tare da tinanin komaiba ta daga kai alamar ae
Jikin sa a mace ya tako inda take ya dafata cike da kulawa yace dagaske kike kina son aure? Ba tare da fargaba ko shakkaba tace ae baba Ina so, harga Allah bata San me ake nufi da aure ba kawai ta fada ne dan ta samu sauqi a zuciyata
Mobabah yay murmushi yace shike nan zan kawo miki miji har gida kinji?
Da sauri ta washe baki cike da yarinta tace to babah yaushe zaka kawo shi?? Abin ma seya bawa moddibo dariya😃 itama murmushin tayi
A hankali ya kama kumatunta yace nan da 'yana kawanaki kadan zan kawo miki shi yana kaiwa nan yay hanyar fita ya tafi masallaci, itama tashi tayi taje tayi alwala tayi sallah sannan ta tashi ta nufi dakin babanta, tana shiga ta sameshi a zaune yana Hada magunguna, dayake yana bada magani irin na Gargajiya dik rugar su shi ake kira idan rashin lafiya ya samu wani cikin ikon Allah kuwa ana dacewa da maganin sa,
Da sallama ta shiga ta zauna,,,, tayi shiru bata ce komai ba ta hakan ne ya fahimci yunwa take ji be ce mata komaiba ya dakko kwanon dake gefansa ya mika mata da sauri ta karba furace da nono nana da nan ta kafa kai tafara sha yanda take shan furar ne abin ya bawa moddibo mamaki a nan zuciyar sa ta fara zargin anya kuwa Rabe taci abinci yau kuwa???
[8:48PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 4*
Tabbas ze Iya daukar komai amma fa banda horon yunwa a fisace ya tashi ya nufi bukkar Laure ko sallama be mata ba ya hauta da bala'i kan cewa ze jure komai da zatai mai amma fa Sam be yarda da horon yunwa ba
Tunda ya fara masifar Laure ke kallonsa cike da mamaki sabida tunda take da moddibo be taba daga mata murya ba balle yay mata fada, Ashe haka moddibo yake?? Tabbas ta yarda ransa ya bacci sosai shiyasa bata CE masa komai ba tunda ya fara fadan, idan tace zatayi magana to tabbas komai ze Iya faruwa Wanda kuma ba lallai yay mata dadi ba
Yana gama zazzaga mata yay gaba ya barta da fargabar halinsa
Yana futa dakinsa ya nufa da sallama ya shiga dakin inda ya bar Rabe anan ya sameta da fara'arta tace sannu da zuwa yay mata murmushi ya shafa kanta, sun jima tana yi masa shirmen hira har ya gaji yace taje tayi bacci,, ayko fir taki tafiya wai seya rakata, haka kuwa akayi har dakin ta moddibo ya kaita seda ta fara bacci sannan ya tofa mata adduah sannan yay waje
Wshe gari da zanyi safiya Rabe ta fito cikin shirinta na tafiya kiwo, sanye take da kaya irin nasu na fulanin asali,qarta kuwa sanye take cikin wani rufaffen takalmi na roba,
Dakin moddibo ta nifa da sallama sannan ta shiga a zaune ta sameshi yana Karin kumallo, da fara'a ya dubi Rabe yace qara so kusa dani mana mamana? Cike da fara'a ta qarasa jikn Baban nata cike da soyayya ta fada jikin sa
Tare sukayi Karin kumallon dashi bayan sun gama ne suka fito tare a waje sukaci karo da Laure. Aiko seta hde rai kamar taga mutuwar ta
A dan tsorace rabe ta gaisheta, seda ta faki idon moddibo sannan ta wtsawa rabe wani kallo aiko da sauri Rabe ta koma bayan moddibo ta qanqameshi bece komai ba ya kama hannunta suka fice daga Gidan
Suna fita garke suka nufa dan su fita kiwo
A nitse ta kallo moddibo tace baba yau ni kadai zani kiwo na kaga se mu raba shanun biyu kai kayi hanyar gabas nikuma nabi yamma idan muka dawo se a ga nawaye sukafi qoshi ko?
Cike da kulawa yace mata to muje sena raba mana ko, da sauri take binsa cike da zumudi zata kiwo ita kadai
Basu dai lokaci ba ya raba shanun gida biyu ya Tisa nasa yay gaba itama tayi gaba seda yay mata kashedin ta kula da kanta sosai kuma kada tabi ta hanyar da bata da kyau ma'ana banda bin titi sbda ya tsani bin titi tunda ya rasa qaninsa zakariya😭
Tafiya take cike da kwanciyar hankali daganin ta kasan tana cikin farin ciki da walwala haka sukaita yawo a cikin dajin seda suka dau lokaci me tsayi sannan Rabe ta lura lokacin zuwa makarantar ta Yayi
Dole ta kora shanun suka kama hanyar gida, koda ta dawo seta fahimci babanta be dawo ba, kuma kullum shine yake rigata dawowa daga kiwo to meyasa yau be dawo da wuri ba??
Bangaren moddibo kuwa yana hanyar dawo wansa daga kiwo ne se ya hangi kamar mutum a kwance da Yayi zaton ko hutawa yake amma dya qaraso seyaga sabanin tinanin sa
Yaro ne matashi sanye yake da wata tsaleliyar shadda light blue an masa dinkin jamfa kansa babu hula kansa wani qaton Sara ne hakama qirjin sa da kuma bayan sa
Jikinsa dik jini ne a jiki dik da saran dake jikin sa hakan baze hanaka fahimtar yana da kyau ba cikin sauri moddibo ya qarasa kusa dashi ya dago shi a nan ne ya fahimci yana numfashi, sabida tsabar riki cewa ma ya rasa ta India ze fara bashi taimako,, (likitan Gargajiya kenan lol)
Can dabara ta fado masa ayko da qar moddibo ya Iya dagashi ya Dora a bayan saniya daya ya daure shi a jikinta ta yanda baze fadi ba suka nufo hanyar gida
Sun jima sannan suka qara so gida ,,, a qofar gida suka hadu da Rabe dan tunda ta dawo taqi shiga Gidan ta tsaya jiran moddibo
Da sauri moddibo yace ta shiga da shanun cikin garke , ba tare da ta kula da mutumin dake bayan saniyar ba tayi gaba da qar moddibo ya kwanto shi daga jinkin saniyar Yayi hanyar dakinsa dashi, suna shiga ya kwantar dashi akan tabar marsa ya mike ya dakko boronsa dayake sa magani ya ajiye ya sake dakko wata qarya ya ajiye qaho ne a cikin qwaryan da kuma aska take moddibo ya yage rigar dake jikin matashin subahanallah abinda ya firta Neman sabida yanda yaga jini ya taru a gefan qirjinsa na dama da alama seda aka dake shi sannan aka sareshi
A nitse ya dauki askar ya daidaici gurin da bakin jinin ya taru sannan ya yanka gurin nan da nan wani bakin jini ya fara fita a hankali ya shiga goge mai seda ya gama gaba daya sannan ya shiga samai magana a jikin raunukan bayan ya gama sa masa maganin ne ya fito yana kwadama Laure kira, jiki na rawa ta qaraso tace gani mlm
Yace maza ki kawo min ruwan zafi jiki na rawa ta tashi ta hada wuta ta Dora ruwan zafin
[8:48PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 5*
Ta dan dauki lokaci kamin ta kawo ruwan zafin sabida sha'anin itace se'a hankali, dakyar ta samu wutar ta kama ba'a jimaba ruwan ya tafasa
Qwarya ta daukko ta juye masa ruwan a ciki ta nufi dakinsa dan ta kaimai ruwan. Sallama tayi sannan yay mata izinin shigowa ta shiga
Ya karbi ruwan sannan ya dakko wani farin saki yasa a cikin ruwan sannan ya dakko wani garin magani ya zuba a cikin ruwan ita dai Laure banda kallon moddibo ba abinda takeyi bakinta fal tambayoyi amma ta rasa ta inda zata fara yimai Tambayar. Suna cikin haka ne Rabe ta shigo dakin da sallama da fara'arta take kallon moddibo tace bab wannan shine mijin daka samo min din
Cike da damuwa ta qarasa maganar sabida se a lokacin ta lura da raunin dake jikinsa moddibo be damu da ya bata amsa ba sabda shi gaba daya hankalinsa yana kan wannan matashin
Kamar zatayi kuka tace baba amma wannan baqo ne ko? Ciwo yaji ? A lokaci daya rabe ta dinga jefo masa tambayoyi
Ba zato Laure ma ta jefo tata tambayar mlm a ina ka samo wannan yaron? Kai yanzu baka jin tsoron daukko shi ya zame mana masifa nan gaba?
Moddibo ya dube ta cike da murmushi yace haba Laure shin kin taba ganin inda taimako ya zama masifa? Tayi shiru batace komaiba, daya ga bata da niyar magana seya cigaba da maganarsa tin daga Hauwarsa da yaron har zuwa dakko shi da Yayi be boye musu komai ba
Nan da nan idon Rabe ya fara zubda hawaye dama su Rabe da arahan hawaye lol
Ita ko Laure ko a jikinta balle ma tausaya masa , dataga abin ya isheta ma seta fice daga dakin tana ta bambami wai moddibo ze ja musu bala'i
Shidai be kulata ba sema cigaba da gogewa matashin jiki da ruwan maganin daya hada yakeyi
Cikin muryar kuka Rabe tace baba, ya dago yana kallon ta sedai bece komai ba a hankali tace dame zan Iya taimakon ka?
Moddibo Yayi murmushi yace so nake kullum ki dinga yi masa adduar samun lfy kinji? Ta daga kai alamar gamsuwa moddibo ya share mata hawaye da hannunsa sannan yace ta tashi ta wuce daki ba musu ta mike ta tafi dakin kamar yanda yace mata
Ranar dai Rabe bata samu zuwa makarantar allo ba
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau matshinnan ya cika sati biyu a gidansu Rabe amma ba abinda yake motsi a jikinsa sedai kawai alamar numfashi, tun suna sa ran tashinsa har suka fara cire ran farkawar sa nan kusa
Yanzu Rabe CE take kula dashi itace ke zuba masa kunu a baki da ludayi tin baya shiga bakin har yazo ya fara shiga kadan kadan
Kallo daya zakayiwa matashin ka fahimci ya rame sosai akan ranar da moddibo ya kawoshi Gidan , tun ranar da aka kawoshi gdan Laure bata qara leqowa dakin ba dan acewar ta idan masifar ta zo ta afkawa moddibo da Rabe, hmmm su Laure akwai bakar zuciya lol
Wasa wsa Rabe ta shafe kwanaki bata zuwa makaranta ko kiwo bata zuwa, amma Sam hakan baya damunta sabda tsa a ranta taimakon mutum yana daya daga cikin dabi'u masu kyau
Mlm iro yazo yafi a qirga kan ta dawo makarantar ayi suka da ita amma fir taki yarda ta koma dan a ganin ta idan ta fita ko qofar gida waye ze bawa bako abinci?
Hmmm kuji fa Rabe da qarfin hali
Moddibo ne ya shigo dakin hannunsa riqe da wata saiwa ya mika mata yace maza jeki tafasata ki kawo min kinji
Da sauri ta karba taje ta hado qirare ta bada wuta ta Dora maganin ba'a dau lokaci me tsayiba ruwan ya fara dahuwa seda mutar ta mutu sannan ta juye maganin a qwarya ta kaiwa moddibo da murna ya karba yana sa mata albarka seda maganin Ya fara hucewa moddibo ya dago kan matashin ya shiga zubawa matashin abaki, dikda cewa ana zubawa wani na zubewa ansamu wani ya shiga cikin nasa, bayan ya gama ne ya shiga goge masa jiki da sauran maganin
Kullum haka suke masa har aka shafe wata ba wani ci gaba, gashi Rabe bata da aiki se kuka ga jarabar Laure ga kuma ciwon bako hakan ne yasa dik tabi ta rame se hanci da idanu
Abin yana dagawa moddibo hankali to amma bashida yanda zeyi illa kawai yayta addu'a
Laure CE ta Shiva dakin moddibo da sallama ya amsa mata da sakin fuska a dakile tace yame jiki ya amsa mata da sauqi
Moddibo ya sake murmushi a karo na biyu yace hala fita zakiyi? Da fara a tace ae dan dama ta rasa ta India zata fara tambayar sa cewar zata fita, a takice yace mata seta dawo ta gaida su iro da gwaggoji. Bata amsa ba tayi gaba bayan fitarta ne wani yaro hamisu yazo yay sallama da moddibo kan cewar mahaifin sa ba lafiya shine yace ya kirashi moddibo be bata lokaciba ya fito suka wuce har sun fita ya dawo yace Rabe ta koma dakinsa sabda maralafiyan
Da sauri ta mike tare da yi masa Allah kiyaye ta koma dakin ta zauna tunda ta zauna ta zubawa matashin ido ba tare da tace komai ba se hawaye cikin muryar kuma ta fara magana, wai kai yaushe zaka tashi ne?shin kasan yanda mukeji a ran mu? Dan Allah ka tashi ko hankalin banana ze kwanta!
Ta jima tana suru tanta kamar wata zararriya sannan tayi shiru ta cigaba da kukanta fukarta dik tayi ba idanunta suka kumbura abin ka da far in mutum
[8:49PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 6*
Ta jima tana kukan sannan bacci ya dauke ta
A hankali matashin ya fara motsa hannunsa daqar ya Iya daga hannun sa ya maidashi qirjinsa, jin da tayi kamar motsi ne yasa ta bude idanunta daqar ta maida kallon ta gareshi, ayko seta qara bude idanunta sosai alamar mamaki
To ya akai hannunsa ya koma qirjinsa? Tambayar da take mata yawo a zuciyarta Kenan
A nitse ta maida kallonta kan fiskarsa, ta jima tana kallon sa kamar bazata dena ba kamar a mafarki taga yana motsa idanun nasa ai seta qara zaro idanunta 😳 cike da mamaki
A hankali ya fara bude idon har ya gama bude shi gaba daya a kan fuskar Rabe
A firgice ya fara qoqarin tashi yana so ya ja baya sabida tsoratar dayayi
Yana ja baya ya saki wata qara sabida wani azababben zafi dayaji a gadon bayan sa , bashiri ya koma ya kwanta yana maida numfashi, da sauri rabe ta sake matsowa kusa dashi sosai sannan ta fara magana cikin harshen fulatanci take cemai kayi a hankali sabda jikin ka akwai rauni!
Tunda ta fara magana yake kallon bakinta har ta kai harshen maganar ta dikda cewa be gama fahimtar abinda take fada sosai ba hakan be hanashi qare mata kallo ba tana gama maganar ta sakar mai murmushi tare da mikewa ta fita daga dakin ,
Tana fita daki ta nifa ta dakko wani rufaffen kwano sannan ta dawo ta sake zama dab dashi ta zauna ta kuma sakar masa murmushi a karo na biyu sannan tace masa ya tashi, dataga be gane me take nufi ba setai mai nuni alamar ya tashi
A hankali ya kuma yunqurin tashi a karo nabiyu amma kuma seya kasa ze koma ya kwanta tai masa alamar a'a, da taga bashi da niyar dena kallonta seta mike ta koma bayan sa wai zata dagoshi,, cike da mamaki yake kallonta tare da mamakin qarfin hali irin nata, jibeta 'yar qarama da ita wai zata dagashi, lallaima yarinya nan yana cikin zance zucin da yake ne yaji ta cakume shi da sunan zata dagashi, ayko seya sake sakin qara sabda zafin dayaji na ciwon dake bayan sa bata damu da ihun dayeke ba har seda ta zaunar dashi,
Daqar ta Iya zaunar dashi har tana zufa
Tana zaunar dashi ta zube a gurin tana mayar da numfashi,
Dakyar ya Iya dago idon sa da suka fara canza kalah dan azaba ya kalleta lokaci daya itama ta dago ido suka bada ido,
Suna hada ido gabanta ya fadi, da sauri tayi qasa da idonta a nitse Takai hannunta kan kwanon da ta dakko a daki ta bude fura ce da nono ta miqa msa tace yasha, ya gane nufinta a hankali ya fara dago hanun amma kuma seya kasa
Data fahimci hakan seta mike daga inda take ta dauki kwanon ta matsa kusa dashi ta zauna sannan tasa ludayi ta juya ta debo ta miqa masa kusa da bakinsa, ya jima yana kallon ludayin sannan ya maida kallonsa kanta,
Tambayar dayakewa kansa itace wai shin inane nan?
Kuma wa'yannan su waye?
Wannan yarinyar wacece ita?
Waze tambaya ya bashi amsoshin wannan tambayoyi nasa?
Data ga bashi da niyar bude bakin ne seta sake miqa masa ludayin har yana taba lips dinsa , sa'a sannan ya dawo daga duniyar tinanin da yakeyi, a nitse ya bude bakin ya fara seeping, se kuma ya kauda kansa da sauri kamar Wanda ya tina wani abu,
Daqar ta samu ta lallabashi ya sha sosai.
Bayan ya gama sha ne ta dakko masa maganin sa shima ta bashi yasha , tunda ta bara bashi maganin yake mamakin yarinyar
Badan komai ba se yanda take dawainiya dashi, harga Allah ya jinjinawa jarumtar yarinyar, tana gama shafa mai maganin ta taimaka masa ya kwanta yana kwanciya moddibo ya shigo da sallamar sa aiko Rabe da gudu ta nufeshi ta rungumeshi tana fading baba ya tashi wllh ya tashi,
Kana kallonta zaka fahimci tana cikin barin ciki😃😃
Tunda ta fara magana moddibo yake kallonta da murmushi yace to yanzu kuka ya qare ko?
Da sauri ta rufe fuskarta da zarazarn hannayenta tana dariya,
Tun shigowar moddibo matashin yake kallon su har zuwa sanda Rabe ta rungumeshi, se kallon su yake cike da burgewa da alama mahaifin tane ya fada a zuciyar sa, sabda suna bala'in kama da juna!
Wai shin wanene wannan matashin??????
INA MIQA SAQON TA'AZIYAR SURAIYYAR surayyah ga Uwar dakin kuma aunty na Khadeeja candy
inayiwa sauran 'yan uwa ta'aziyar wa'yanda suka rasa fatan Allah ya gafarta mana gaba daya👏(CIBADO TAKU A KULLUM😘)
[8:49PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 7*
A nitse moddibo ya qarasa kusa da matashin ya sunkuya da murmushi a fuskarsa yace sannu da jiki kaji
Cikin harshen fulatanci moddibo Yayi maganar, ido kawai matashin yake bin moddibo dashi sabda Sam besan me yake fada ba,
Moddibo ya fahimci matashin baya jin fulatanci shiyasa yay murmushi sannan yace dashi sannu cikin harshen Hausa
Matashin ya bude baki da nufin ya amsawa moddibo amma sedai muryanshi bata fita sosai sabda mura data kamashi ( abinka da Wanda be saba da wahala ba lol)
A nitse moddibo ya fara magana kamar haka
Yaro nasan zuciyarka a cike take da tambayoyi akan mu , ko?
Kuma nasan zakaso kasan meye dalilin zuwanka wannan gurin?
To magana na gaskia itace ina hanyar dawo wata daga kiwo ne Allah ya hadani dakai kana kwance a cikin jini !!
Na Dade bana bin hanyar amma dayake Allah ya qaddara semun hadu dakai seya nufeni da bin hanyar Ashe rabon in taimake ka ne,
Safari nazata ma ka rasu amma Dana tabaka sena fahimci kana numfashi haka mukaita kula da rauni kan jikin ka har Allah ya amince mana ka tashi,
Nan da nan idon matashin ya kawo ruwa ba komai ne yasa shi hawaye ba se irin karamcin da moddibo yay masa,
Yanzu babbar damuwarsa yanzu be San halin da dadynsa yake ciki ba!
Cike da kulawa moddibo ya dafashi yace kayi haquri yaro nasan dole zakayi kewar gida amma ka qara haquri jikinka ya qara qwari seka tafi ko ? A nitse ya amsa tare da yiwa moddibo godia,
Har moddibo ya mike se kuma ya sake sunkuyowa yace da matashin yaro ya sunan ka??
A nitse ya firta Muzaffar Abdulwahab
Moddibo yay murmushi yace dakyau, dik wannan hiran da suke Rabe na jinsu a nitse ta qaraso kusa da matashin da murmushi a fiskarta tace sunan ka dama zafar ne?
Muzaffar yay murmushi a karo na farko yace muzaffar nace ba zafar ba,
Tun daga lokacin da zafar yay murmushi har zuwa sanda ya gama magana take kallon sa ,
Ba komai take kallo ba se tsabar kyau irin nasa bata tabbatar da shi kyakkyawa bane seda yay murmushi,
Mutane dayawa suna fadar tana da kyau amma yau taga Wanda ya fita kyau da tsarin halitta,
Nima kaina seda na dan tsorata da kyansa lol)
Seda moddibo ya dafata sannan ta dawo daga duniyar tinanin da take,,,
A daburce tace baba yaushe za'a kuma bashi abinci?
Harga Allah ba abinda tayi niyar fada ba kenan tsabaragen daburcewa ne yasa ta fadi haka, sosai moddibo ya fahimci halin data ke ciki amma kawai seyay murmushi, ya fita daga dakin
A hankali muzaffar ya dago kansa ya kalleta yace ya sunan ki? A taqaice tace masa Rabe
A hankali ya kuma maimaita sunan, a taqaice yace mata thanks for everything.
Daga haka ya koma ya kwanta,, ta jima tana juya kalmar a ranta dikda cewa bata San meyace ba amma setaji Kalmar tayi mata dadi,,
Be sake cewa komaiba har yamma
Moddibo ne ya shafa masa magani sannan yasa Rabe ta Dora masa ruwan zabi ta kawo masa tana kawowa tayi waje abinta, moddibo ya tashi ya nufi inda muzaffar ke kwance a hankali ya fara kiran sunan sa,
A nitse muzaffar ya bude idanunsa a fiskar moddibo,
Murmushi Yayi masa sannan yace ka gyara zan goge ma jikin ka , a nitse ya fara qoqarin tashi amma kuma seya kasa tashin moddibo ne ya taimaka masa ya tashi zaune, wani farin saki moddibo ya qara dakkowa ya tsoma a cikin ruwan ya fara gasawa muzaffar jikinsa, dik da cewa jikinsa nayi masa ciwo sosai hakan be hana moddibo gsa masa ba
Yana gamawa ya dakko maganin shafi ya shafa masa sannan ya taimaka masa yayi alwala, sannan ya shiga rama sallolin da ake binsa ya Dade yana yi dik da cewa besan adadin kwanakin daya zauna a qauyen ba,
Seda ya dau lokaci me tsayi sannan ya idar, moddibo ne ya tai maka masa ya kwanta sannan ya dakko wani zanin saki ya lullube shi ba dau lokaci ba bacci yay a won gaba dashi
Kuyi haquri da wannan bana dan jin dadi ne👏
[8:50PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 8*
Ban garen Rabe kuwa tunda ta fita bata sake dawowa dakin ba
Sallah ta gabatar sannan ta fito ta gabatar da aiyukan da ta saba na yau da kullum seda ta gama tsaf sannan ta koma daki da nufin ta gabatar da sallar ishsha'i, bayan ta idar ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Da sauri ta mike ta cire mayafinta ta nufi katifar ciyawarta dan ta kwanta sbda sanyin daya fara busowa,
Kamar daga sama taji an banko mata cikin dakin aiko da sauri ta miqe sabda sanin ko wacece ta shigo, dan inda sabo yaka mata ace ta saba da halin Laure,
Masifa fal ranta ta shigo dakin tare da yi mata kallon wulaqanci tace to 'yar gatan gata rere to fito kiyi min ayki dakike qoqarin kwanciya, ai wllh baki isa kiyi bacci yanzu ba
Bata jira cewarta ba ta fincikota sukayi waje, wasu tarin kwanuka ta gani a jibge gefe kuma wani ruwane a cikin wata fanteka da alama ruwan ya Dade a gurin dan haka base an fada ma ya dau sanyi ba,,,
Kallo daya zaka yiwa kwanu kan ka fahimci babu datti ko kadan a jikin su kawai tsabaragen mugunta ne yasa Laure tace ta wanke mata kuma tasan sanyin da akeyi ko daki kake seka ji a jikin ka,
Ba musu Rabe ta sunkuya ta fara dauraye kwanukan tanayi jikinta na rawa sabda sanyi har taxi qarfin kwanukan laure dataga bazata Iya jure sanyi ba setai shigewarta dakin ta tabar Rabe a waje tana fama seda ta dau lokaci me tsawo sannan ta gama ta kikkife su, sannan ta wuce daki jikinta nata rawa tana shiga ta kwanta dikda cewa ta lulluba amma Sam bata dena jin sanyin ba,,
Abu kamar wasa haqoranta suka fara haduwa da juna, nana da nan zazzabi me zafi ya rufeta daqar ta samu bacci ya dauke ta
Ba ita ta farka ba se bayan an idar da sallar asuba , daqar ta samu tayi alwala ta gabatar da sallar
Koda data idarma ta kasa tashi daga inda take a gurin ta kife sabda wani irin azababben jiri data keji,
Har gari Yayi haske sosai kowa ya fara harko kinsa amma Rabe bata fito ba,
A bangaran moddibo kuwa Yayi mamaki sosai ganin har wannan lokacin rabe bata fitoba azatonsa ko bacci takeyi shiyasa be wani damu sosai ba,
A nitse moddibo ya gama gabatar da komai na karyawa Wanda muzaffar zeyi Karin kumallo dashi.
Har ya gama bega idon Rabe ba, se kuma abin ya fara damun moddibo
Bangaren muzaffar ma ya damu qwarai da rashin ganin yarinyar sbda daga jiya zuwa yau yana jin cewa ya saba da ita badan komaiba se yanda yarinyar take nuna kulawarta a Kansa
Cikeda kulawa ya dago ya kalli moddibo tare da gaishe shi, shima moddibo ya amsa da kulawa, azahiri muzaffar yaso ya tambayi moddibo INA Rabe take amma kuma daya kalli moddibo n seyaji baze Iya tambayar sa ba
Moddibo ya kalli muzaffar sannan yace yaro ya kamata ka tashi kaji abinci ka sbda ka samu kasha maganin ka ko?
Ba musu muzaffar ya fara qoqarin tashi dikda cewa ba iyawa zeyi ba,,
Moddibo ya saki murmushi yace yaro gaskia kana da qarfin hali sosai ka qara haquri ka kusa fara tashi da kanka
Tunda moddibo ya fara magana idon muzaffar yana kansa se kuma Yayi murmushi yace to baba Allah yasa , bazan gaji da qara jaddada godia ta a gareka ba sabda ka taimaki rayuwata!! Seda yayi dan shiru sannan ya sake kallon moddibo yace thank you for save my life,,, ya qarashe maganar tare da hawaye
Da sauri moddibo ya dafa kafa dunsa yace kada ka damu yaro ni nayi maka dan Allah ne badan wani ba dan haka ka dena zubar da hawayenka kaima kamar da kake a gurina kuma nayi maka alqawarin zan kula da kai har zuwa ranar da zaka koma garin Ku wajen iyayen ka ya qare maganar da murmushi,
Sosai muzaffar yake jin kalaman moddibo a zuciyar sa harga Allah dattijon ya shiga ransa, moddibo ne ya share mai hawayen sa sannan ya fara bashi kunun su irin nasu na Fulani Sosai muzaffar ke jin dadin kunun dan haka yasha sosai sannan ya cewa moddibo ya qoshi,
Moddibo yayi murmushi yace masha Allah tunda yanzu ka qoshi bari na shafa maka maganin ka se kuma kasha na shan ko?
Muzaffar yace haka ne
Seda moddibo ya gama shafa mai maganin sannan ya bashi yasha yana gamawa yace to yaro bari in je inga Rabe ko lafia naga har yanzu bata fito ba,
Muzaffar yace hakane kam yakamata a duba agani ko lfya,
Daga haka moddibo yay waje ya nufi dakin Rabe da sallama aiko tana nan a India tai sallah jikinta se rawa yake da sauri moddibo ya nufeta yana tambayar ta Meya sameta?
Ayko yana taba jikinta yace subahanallah!!
Rabe meya sameki be jira cewarta ba ya kinkimeta yayi dakinsa da ita banda hawaye babu abinda ke fita a idonta a haka ya qara so dakin da ita
Da sallama ya shigo dakin sannan ya kwantar da Iya tunda suka shigo dakin gaban muzaffar ya fadi ganin wadda moddibo ya kwantar a rude yake tambayar moddibo abinda ya sameta har yana qoqarin tashi daga inda ya ke kwance
Sosai moddibo ke kallon muzaffar tare da tsantsar so da qauna yace yaro ka kwantar da hankalin ka ba wani Abu bane zazzabi ne kawai
Harga Allah moddibo yaji muzaffar ya qara kwanta masa a rai musamman dayaga ya nuna kulawar sa a kan tilon 'yarsa gida daya!
Fatan alkhairi ga aunty na kuma Uwar dakina candy komai cibado ta zama candy CE sanadi, ngde Allah yabar qauna😘
Ina samun saqonku gareni masoya na kuma INA miki fatan alkairi, banyi zaton inada masoya haka ba!
Bazan manta dake ba Aysha musa isah(nanoni)👏
[8:50PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 9*
Murmushi moddibo yay masa sannan ya juwaya ya dakko boron sa dayake sa magani a ciki ya daukko wani farin magani ya jiqashi a kwanon sha seda ya dan dau lokaci sannan ya dgota ya bata
Ba tayi gaddama ba sabda bata qin magani
Diik abinda suke idon muzaffar na Kansu se kallon su yake yana mamakin yanda moddibo yake Iya gane ko wani qullin maganin dake cikin jakar
Ada muzaffar be yadda da maganin Gargajiya ba sena asbiti wai a cewarsa maganin Gargajiya baya maganin ciwo sedai ya qarawa mutum wata cutar( Niko nace dakyau bature lol)
Segashi maganin Gargajiya yayimai ranah, shiyasa a rayuwa kada ka raina baiwar da Allah yayiwa wani ko wata idan kayi hakan tabbas bakayi Abu me kyau ba, Allah ya kyuta
A hankali seyaji abin yana birgeshi sosai lallai ilimin baiwa ne bawai kawai ilimin sanin rayuwa kona addini bane kawai ilimi, sanin nau'ikan itace shima ilimine kinji muzaffar Abdulwahhab😊
Bata jima da shan maganin ba bacci ya dauke ta banda zufa ba abinda takeyi, muzaffar ya kalli moddibo cike da damuwa yace kayi wani Abu kagafa se gumi take kodai zamu kaita asibiti ne??
Da mamaki moddibo ke kallonsa😳 yace yaro a wannan dakin kake tinanin asibiti?
Batare da damuwar komaiba muzaffar yace ae mana
Nan da nan yanayin moddibo ya canza sannan yace yaro ga ganin nan tunda na tashi da iyayena a nan muke rayuwa asalin mu 'yan jihar Yola ne mu kuma maifan mu mu uku suka Haifa mu biyu maza se kuma qanwar mu mace guda daya wadda bansan a inda take ba a halin yanzu
Yana zuwa nan a zancensa seya fashe da kuka, daqar ya samu ya daidaita kansa sannan ya cigaba da cewa shi kuma qanina Wanda yake bina dashi da mahaifin da sauran yn qauyen mu ne mukayi hijjira daga dajin da muke ciki sbda yana fashi da suka sa mu a gaba ba Iya fashin da suke mana bane damuwar har yaran mu mata qanana suke zuwa su kwana dasu a gaban mu, wannan ne dalilin dayasa muka bar jaharmu ta asali muka komo wannan dajin dikkan mu dakake gani dik yana uwan juna ne, wata rana qanina yafita kiwo mota ta bige shi bamu sani ba , seda muka kwana biyu muna Neman sa daga baya muka tsinci gawarsa a bakin hanya,
Wata rana da yamma wasu mutane suka shigo mana nan da sunan zasuyi mana asibiti sbda muma mu samu cigaba, muka karbe su hannu biyu Ashe abinda bamu sani ba cutarmu sukazo suyi
Dayawa a cikin mu kasuwanci shanu suke yi seda suka bari kowa ya dawo daga kasuwancin sa yaxo da kudi, sannan suka far make mu suka qwace komai, sannan suka kashe na kashewa,
Tunda ga lokacin bamu qara yarda da kowa ba, kuma muka dena karbar baki koda ko daga ina suke, shiyasa tunda ka ambaci sunan asibiti kaga yanayina ya canza yaro, ya qara da cewa yanzu da mutanan rugar nan zasu samu labarin zuwanka tabbas da se sun koreka kokuma ma su kashe ka
A firgice muzaffar ke kallonsa jin kalmarsa ta qarshe wato kisa, yace to yanzu Baba meyasa lokacin da abin ya faru Baku nemi tai makon jami'an tsaro ba ???
Moddibo ya kalli muzaffar yayi murmushi irin na takaici yace yaro da fari min gwada yin hakan amma daga baya se muka gane itama hukumar se a hankali,
Muzaffar yayi shiru a zuciyarsa yace Ashe Dama a kwai mutane masu fiskantar irin wannan rayuwa??
Tabbas Allah ne ya nufi zuwansa dan ya qara ilimi akan rayuwar duniya,
Haqiqa baka godewa Allah da irin baiwar da yayi maka seka ga Wanda be kaika ba sannan kake sanin Allah yayi maka baiwa
Haka kawai seya samu kansa da jin tausayin su shiko insha Allah seya tai make su da izinin Allah
Wai ina Laure ne jma'a
Tunda garin Allah ya waye Laure ta fice daga Gidan sabda bata da wani buri yanzu a rayuwata daya wuce taga bayan moddibo da Rabe sannan kuma ta mallake dukiyar sa.
Tabdi kujifa masu karatu!
Dama ance yanzu ba'a maqiyin nesa , ya Allah ka shiga tsakanin mu da maqiyan mu na sarari Dana boye
Kuyi haquri wannan bana jin dadi ne👏
[8:51PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 10*
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau muzaffar ya cika wata biyu a Gidan moddibo, cikin ikon Allah ya samu sauqi sosai, kuma shaquwa me tarin yawa ta shiga tsakanin Rabe da zafar sedai bazamu fassara shaquwar da sunan so ba, sedai kawai mu kirata da yan uwantaka, sabo tirken wawa,
Washe gari da safe ne moddibo ya gama hadawa zafar komai nasa sedai rigarsa da moddibo ya tsinto shi da ita tariga ta lalace dan haka moddibo ya dakko masa wata rigar saqi irin tasu ta Fulani ya miqawa muzaffar da nufin ya sanya a jikin sa tare da wandon shaddar sa, ba musu muzaffar ya karba ya sanya rigar
Ba qara min kyau tayi masa ba dan fadar kyan da tayi masa ma bata lokaci ne
Bayan ya gama sawa ne moddibo yay gyaran murya irin nasu na dattijawa yace yaro yau dai gashi ka warke cikin ikon Allah kuma gashi har kana shirin tafiya, sedai kuma har yau bamu San kokai waye ba, a yanda muka saba dakai ya kamata musan ko kai waye. Sbda mu qulla zumunci wata rana bamu San a inda zamu sake haduwa ba
Sosai kalaman moddibo suka shiga ran muzaffar dan harga Allah gaskia moddibo ya fada
Ya kamata ya gaya musu ko shi wanene
A hankali ya fara da cewa. Ni haifaffan garin kano ne amma kuma ba'a farin kano na girma ba , ni kadai ne namiji a yaran da mahaifina ya haifa kuma ni kadai mahaifiyata ta Haifa sannan ta bar duniya
Hakan ne yasa Mayan babana suka sakoni gaba kowacce burinta taga bayana hakan ne yasa mahaifina ya dauke yabar qasar dani tun ina dan shekara goma ya kaini qasar India. Gurin wata matarsa da yake aure. Babu abinda Mami ta rageni dashi ta dauke ni tamkar dan cikinta Allah sarki mami na.
Ban dawo Nigeria ba seda na cika shekara ashirin sannan Dady ya dawo dani ba yanda beyi da Mami ta biyoshi ba amma taqi sbda wani dalili nata Wanda har yanzu taqi sanar da kowa, haka Mami tayi ta kuka da zamu dawo Nigeria
Bayan na dawo Dady ya Tara matansa da qanne na ya sanar dasu cewar zan fara aiki akamfaninsa na takalma dake abuja, Sam suka CE basu yarda ba sedai a hadamu da qanwata dake bina fadilah ai itama ta gama makarantar
Dady yayi murmushi yace shikenan babu damuwa Allah yasa haka shiyafi alkairi kowa ya amsa da ameen amma banda Hajia lami wadda Mike kira da umma, tunda aka fara maganar fara aiko na har aka gama ba tace qala ba sosai kowa ke kallonta itakuwa ko ajikinta seda ta gama qarewa kowa kallo sannan tace Sam bata yarda a tura fadilah abuja ba sbda it's mace ce kuma dik macen qwari aure iyayenta suke yi mata bawai tura ta aiki na dan haka ba Inda zata sedai ta zauna a gida
Sosai Dady ya ameence da maganganunta, dan haka ya soke zuwan fadilah badan ran mahaifiyarta yaso ba
Washe gari da safe Dady yace in shirya gobe zan wuce abuja kuma jirgin sassafe zanbi a nitse na amsa da too sannan na wuce bangarena dan na kwanta na huta
Yau umma CE da girki dan haka Dady a dakin ta yake. Da wannan damar tayi Amfani gurin canza wa Dady ra'ayi wai be kamata nabi jirgi ba ai yin hakan almubazzaranci ne kawai ya qyaleni in tuqa mota da kaina kokuma yasa ado ya Kaine
Da qar Dady ya amince ado ya Kaine a mota, suna gama mganar tacewa dady tana zuwa,
Daret dakin Momy ta nifa wato mahifiyar fadilah tana shiga Momy tayi mata wani mugun kallo sannan ta dauke kanta tace to 'yar bakin ciki meya kawoki dakina?
Umma tayi murmushi tace to sarkin jaraba labari nazo miki dashi gobe idan Allah ya kaimu su ado zasu qarawa muzaffar gudu zuwa lahira,
Momy tace ke nifa ban gane ba ,
Umma tayi dariya tace to gobe ado ze kaishi abuja a hanyar zasu kashe mana dan iska mu huta shiyasa na shiga na fita na hana fadilah zuwa sbda mu samu mu kashe matsiyaci
Nanda nan fara'a ta mamaye fiskar Momy sannan suk tafa tayi mata sallama
Washe gari da sassafe ado yazo Dady ya rakani mota tare da yimin addu'ar suka lfy nayi sallama da kowa sannan muka kama hanyar abuja seda muka wuce Kaduna sosai sannan ado ya tsaida motar a wani daji babu mutane a hanyar se motocin da suke wucewa cike da kulawa nake tambayar sa ko lfy?
Ado yay murmushi yace yallabai mtsala aka samu kozaka dan fito kafin in gyara?
Ba tare da tinanin komaiba na fito daga motar , INA fita ado ma ya fito sedai banyi aune ba naji daukar qarfe a bayana da qar na Iya juyawa dan naga waye !
Ado nagani yana qoqarin zare wuqa da gudu na yanki cikin dajin ina gudu yana bina har ya samu nasarar kamani daganan ban qara sanin inda kaima yake ba, har zuwa lokacin da Allah ya hadaka dani
Jikin moddibo ba qara min sanyi yayi ba da jin lbrin muzaffar
Harga Allah moddibo ya nuna tausayawarsa ga muzaffar
[8:51PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 11*
Moddibo yay shiru tsawan lokaci sannan yace yaro idan har na fahimceka daidai, matan mahaifinka ne suke so suga bayanka, bisa wata muguwar manufa tasu!
Mgana ta gaskia kana buqatar abokin rakiyar da ze rakaka gida ma'ana Wanda ze taya ka wannan yaqin dake gabanka👉
Sosài muzaffar ke kallon moddibo tunda ya fara mgana, sannan yace haka ne baba amma kuma waye zemin rakiyar?
Moddibo Yayi murmshi yace kayi haquri yaro ka jira zuwa gobe seka tafi kafinnan na sama maka abokin tafiyar ko?
Cike da girmamawa muzaffar ya amsa da to baba
Zaune yake cikin katafaren falonsa na gani na fada Wanda ya Tara kayan alatu na rayuwa kallo daya zakayi masa kasan yana cikin matsananciya damuwa gami da tashin hankalin Batan dansa namiji tilo
Duk Wanda ya San Alhaji Abdulwahab ya ganshi a yanzu seya tausaya masa musamman yanda ya rame yayi duhu sbda tashin hankali ko abincin kirki baya Iya ci sbda tunanin halin da dansa yake ciki
Ummace ta shigo Fallon riqe da Waya a hannunta ta nufo inda Dady ke zaune a kusa dashi tana kallon sa sosai take Mazarin fiskarsa sannan ta fara magana da salonta irin na yan duniya tace
Hba alhaji sekace ba musulmi ba? Kada fa ka manta cewar yarda da qaddara yana daya daga cikin rukunan imani fa' don Allah alhaji ka ragewa kanka damuwa sbda kasanfa baka da lfy
Tunda ta fara mgana Dady be kalleta ba amma kuma yana sauraronta kuma ya yarda da abinda ta fada,
Sedai baze gusheba gurin roqon Allah da ya baiyana masa dansa ba koda gawarsa CE ya samu ya gani yasan dole zeji sauqi a zuciyar sa
Ganinda tayi maganganunta sunyi tasiri akansa ne yasa tace ga wayarka a.s.p yanata kiranka
A nitse ya ya mika hannunsa ya karbi wayar, yana qoqarin kiransa ne wayar ta fara ruri sunan daya gani a jikin wayarne yasa ya dauka Mamie ce take kiransa,
Ya dauka suka gaisa dashi bayan sungaisa ne take tambayarsa ya jikinsa ?
Ya amsa mata da kulawa sannan Yayi shiru
Hakan ne yasa Mamie ta fahimci akwai matsalar datake damun me Gidan NATA
Sosai ta nuna damuwarta akan ya sanar da ita meyake damunsa
Fir yaqi gaya mata hakan ne ya qara tayar mata da hankali
Kafin tace wani yabu yace mata gobe kisa ahmad ya kaiki air pot ki taho Nigeria be jira cewarta ba ya kashe wayar
Hakan ba qaramin tayarwa da Mamie hankali Yayi ba se kuma ta fashe da kukan da bata San dalilinsa ba ta jima tanayi har seda kanta ya fara ciwo sannan ta haqura tayi shiru
Ban garen dady kuwa tunda ya kashe wayr umma take kallonsa cike da son qarin bayani akan wayar daya gama, dataga bashi da niyar tanka mata setace alhaji wacece wannan kuma??
Be ko kalleta ba yace matata dake qasar India itace
Dik da cewa ta girgiza Bata nuns masa komaiba
Seda ta dan jima sannan ta tashi ta fice daga falon ta nufi dakinta,
Tana shiga ta fara zarya a dakin data ga zaryar ba fishsheta zatayi ba ai seta nufi dakin Momy sbda tashin hankali ko sallama batayiwa Momy ba ta fada mata daki
A tsorace Momy ta dago tana kallonta tace haba dan Allah wllh kin tsorata no bata kulata ba ta kalli su fadeelah da suke zaune a bakin gado tace ke Ku tafi falo zamuyi magana
Ba musu fadilah ta dauki laptop dinta da wayar ta sannan ta fice daga dakin
Tun shigowar umma Momy take kallonta baki a sake tace ke wai meya faru ne?
Umma bata boyewa Momy komaiba akan yanda sukayi da Dady,
Tashin hankalin da Momy ta shiga yafi Wanda Ummah ta shiga, cike da masifa Momy tace tabdi lallai ma mutuminnan ya raina mana hankali wllh be isa ba, mu ze mayar 'yan iska ?
Ashe dama gunta yakai wancen gantalallen? Wato mun gama dashi shine ze kawo mana wata tsinanniyar ko? To wllh be isa ba bari ma naje falon nasa na sameshi wllh Yayi kadan yace zega bayan mu, fuuuuu tayi hanyar fita dagudu umma ta rugota tace ashe baki da hankali ?
Yanzu idan kikaje masa a haka kina ta jaraba ai seya zargemu akan hallaka masa dansa
Kinga kawai mujira muga zuwanta idan ta ishemu base mu kashe shegiya ba?
Da fara'a Momy tace yauwa 'yar gari dadina dake a kwai tunani. Suka tafa sannan suka cigaba da qulequllensu
Allah ya kyauta
Ni wacece da za'a sani a gaba ?? Har wacece cibado a cikin marubuta?
Wllh ni ba kowa bace illa me koyan rubutu har yanzu ban qware ba! Zefi a gareku kudena wahalar da kanku a kaina sbda in yar koyo CE, kuma daga yau ni cibado na dena rubuta sannan lbri dan haka Ku kwantar da hankalinku
No cibado ban Iya tashin hankali ba 👏
[8:52PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page -1 2*
Sun Dade suna qulle qullensu sannan umma ta nufi dakinta zuciyar ta fal farin ciki
Tunda Rabe taji batun tafiyar muzaffar hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba, amma sedai ba yadda ta Iya dama tasan dik daran dadewa dolene wannan ranar zata zo
Shiyasa bata son sabawa da mutane daga qarshe suzo su barta,
Muzaffar na fitowa daga daki hanyar garke ya nufa sabda yasan nan ne gurin zaman Rabe bata da wani gurin zuwa se nan,
Yana qrasawa kuwa ya hangeta a zaune tayi shiru da alama tinanin wani abun takeyi,
A hankali ya fara tafiya sadaf sadaf sbda baya so ta ganshi ayko yayi sa'a bata ganshiba har ya qaraso daf da ita hannunsa ya daga ya tafa aiko seta zabura zata gudu, da sauri ya ruqo hannunta yace ke tsaya matsoraciya kawai ya qarashe mganar yana dariya
Kamar zatayi kuka tace yaya zafar meyasa kake son tsorata mutum?
Cike da kulawa yake kallonta sannan yace ke kadai nake iyayiwa haka sabida ke din qanwata ce kuma inaji dake Rabi'atu ya qarasa maganar tare da Jan kumatunta.
Tunda ya fara magana Rabe take kallonsa kawai seta fashe da kuka, nan da nan hankalin muzaffar ya tashi cike da tashin hankali yake tambayar ta meke damunta!
Da kyar ta Iya bude baki tace yaya zafar idan ka tafi Dawa zan dinga hira ? Kuma Dawa zan dinga zuwa kiwoo? Ta qarasa maganar tana kuka me cin rai😭
Tunda ta fara maganar yake kallonta dan haka sosai ya tausaya mata be Iya CE mata komai ba ya jawota ya hadeta da qirjinsa yana rarrashinta , ta Dade tana kukan sannan tayi shiru,
A hankali ya zaunar da ita sannan ya fiskanceta yace, Rabbi'atu har ga Allah nima zanyi kewarki bama ke kadai ba Harda baba, amma zanyi miki wani alqawari amma se kin min alqawarin bazakiyi kuka ba gobe idan zan tafi,
A nitse ta dago jajayen idonta da suka fara kumbura tace uhmm ni se kace zaka zauna tare dani anan shine bazanyi kuka ba, cike da quruciya tayi maganar
Abin yaso ya bawa muzaffar dariya amma kuma seya dake yace haba qanwata idan kika CE haka to ni kuma babana fa?
Kinga ai ze damu tunda besan inda nake ba ko?
Da sauri tace to ba se shima yazo nan mu zauna tare ba?
Sosai muzaffar yayi dariya har yana tafa hannu
Sannan yace ai bazeyu muzo gidanku mu zauna ba sabda muna da yawa sosai, dasauri tace aini kai kadai nake so mu zauna tare dakai😔
Sosai maganar ta ke taba zuciyar muzaffar
Kamar daga sama tace nasan idan ka tafi Gidan Ku mantawa zakayi dani!
Da sauri ya kalleta sannan yace wllh bazan manta dake ba qanwat..... Bata bari ya qarasa abinda zece ba tace to kamin alqawarin komai daran dadewa zaka dawo gareni yaya zafar!
Muzaffar yace ki yarda dani mana!
Da sauri tace bazan yarda da kaiba har seka min alqawarin zaka dawo gareni wata ranah!
Batare da tinanin komaiba yace nayi miki alqawarin zan dawo gareki qanwata
Sosai abin yay mata dadi dan haka tayi dariya sosai sannan suka kama hanyar gda.
Suna tafe suna hira Har suka qaraso gida, suna shiga da Laure suka fara arba aiko da sauri Rabe tayi bayan muzaffar, beyi mamaki ba sabda yasan tana bala'in jin tsoronta, cike da girmamawa ya gaida ta a daqile ta amsa be damu da hakan ba ya wuce daki abinsa yana tafiya Rabe na take masa baya seda yaje daf da qofar sannan ya tsaya yace INA kuma zaki?
Ba tace masa komai ba ta nuna masa dakin bece komaiba ya shiga ita kuma tabi bayan sa
Ina miqa gaisuwata me tarin yawa a gareki aunty Qween 👏
Bazan mata da cikakkiyar masoyita ba (Sadiya na Abbah )😘😘
[8:52PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 13*
Yana shiga ya nemi guri ya zauna itama zaman tayi tunda ta zauna take kallon sa tun be lura ba har ya ya fahimci irin kallon da take masa, amma seya share sabda yasan indai ya kalleta dena kallon sa zatayi, shi kuma haka kawai yaji baya so ta dena kallonsa haka kawai yaji yana son hakan,
Ta jima tana kallon sa sannan ya dago ya kalleta se kuma ya kashe mata ido daya 🤪
Da sauri tayi qasa da idanunta sbda wani irin kwarjini da yay mata bugu da qarima ga kashe mata idon dayayi
Abine ya bashi dariya yace qanwata ta kaina wllh bana so ki dinga damuwa nace miki idan na tafi zan dawo wani lokacin kodan sabida ke👉
Ya qarasa maganar tare da nuna ta da hannunsa,
Sosai maganar tayi mata dadi dan haka ta saki murmushin daya qara baiyana kyawunta sannan tace na yarda dakai yaya zafar! Nasan bazaka manta dani ba kuma nima bazan manta dakai ba zafar,
Da sauri ya kalleta yace amma meyasa kike kirana da zafar ?
Murmushi tayi sannan tace sbda bazan Iya fadar sunanqanwata, sbda akwai wahalar fada,
Tunda ta fara magana yake kallon ta sannan yace oho shiyasa kike cemin zafar? Ta daga kanta alamar ae, dariya yayi sannan yace hakan dakike cemin ma yana min dadi qanwata,
A nitse ta kalleshi tace yaya zafar idan ka tafi zanyi kewarka sosai bazan gaji da gayama cewar na saba dakai ba , ni kaina bansan dalilin daya sa nake jin zafin tafiyarka a raina ba yaya zafar!
Sosai yake kallon ta tunda ta fara magana sannan yace ni kaina INA jinki a raina Rabi'atu! Ta yanda har nake jin bana so na tafi na barki! Har ga Allah naji jini na ya hadu dake, bama Iya nanan abin ya tsayaba shiyasa ma nake kiranki da qanwata ,
Bayan Mamie na da dadyna ban saba da kowa ba se ke! Dan haka kina da matsayi a zuciyata dama rayuwata gaba daya!
Yanda ta nutsu tana sauraransa seka rantse tana fahimtar abinda yake fada , ta Dade tana juya abin a ranta kafin ta jefa masa wata magana wadda seda yayi mamakinta , CE masa tayi yaya zafar dama ana Iya bawa mutum matsayi a zuciya?😳
Da sauri ya kauda tinanin ta daga maganar yace mata a'a ba'ayi, suna cikin maganar Laure ta bankade qofar dakin tace to tsinanniya fito nan kiyi min aiki
Kin shige daki da namiji kina lalata dan rashin kunya se liqe masa kike yi se kace ba BAFULATANA ba !
Karuwar banza karuwan wofi, sosai abin yayiwa muzaffar zafi a rai amma seya danne zuciyar sa, Rabe ko banda kuka ba abinda takeyi, a hankali ya matasa kusa da ita yana rarrashinta. Laure kuwa seda ta gama tijarar ta sannan ta fice ta bar musu dakin!
Sosai abin ya batawa muzaffar rai dan haka ya kasa cewa komai, cikin tatatausan lafazi yace tashi kije kiyi shirin kiwo mutafi
Tana jinsa amma setayi kamar bataji me yace ba ta cigaba da kukanta, sosai kukanta yake taba zuciyarsa dan haka seyaci gaba da rarrashinta daqar ya samu tayi shiru,
Suna cikin haka ne moddibo yay sallama a qofar dakin sannan ya shigo beyi mamakin ganin su tare ba sabda hakan ba sabon Abu bane
Da gudu Rabe ta mike ta nufi Baban nata ta rungumeshi se kuma ta sake fashewa da kuka cike da damuwa moddibo ya dagota yana kallon fiskarta yace meya faru kuma ?
Bata CE komaiba sabda kukan daya ci qarfin ta da qar ta Iya nunawa moddibo muzaffar da hannunta tace baba yaya zafar ne wai zetafi Gidan su ya barmu, ta qarashe mganar tare da cigaba da kukanta,
Murmushi moddibo yayi sannan ya dafa Kafadunta yace haba mamana , meyasa zakiyi haka?
Kadafa ki manta ke qanwarsa CE dole wata rana ze sake zuwa dan ya ganki dan haka ki dena kuka kinji mamana?
Da sauri ta daga kanta alamar ta yarda da batun Baban nata, dan hka ta share hawayenta sannan ta koma kusa da muzaffar tace yaya baba yace zaka dawo wata rana dan haka bazan sake kuka ba sbda babana baya min qarya komai ya fadamin gaskia nake daukar sa, tunda ta fara maganar muzaffar yake kallonta sosai yake nazarin yarinyar gata qarama amma tana da kaifin tunani wannan idan ta kai shekara 20 yazata kasance?
Lallai Rabi'atu tana da wayo kuma yana jinjina irin soyayyah dake tsakanin ta da mahaifin ta,
Murmushi yayi mata tare da Jan hancinta da hannunsa dikansu dariya sukayi sannan suka yiwa moddibo se sun dawo sannan suka wuce kiwo ita da yayan nata.
Gasar India
Tunda momie ta ji batun Dady na ta zo Nigeria hkan ne ya tabbatar mata tabbas akwai matsala, to meyasa Dady ze mata haka? Bayan yasan bata son zuwa Nigeria, sbda wani dalili nata!
To meye wannan dalilin na Mamie da ze hanata zuwa qasarta na haihuwa?????
Jikinta ba qwari ta mike ta shiga hada kayan da zata tafi dasu, dik wasu mahimman takardu na Dady seda ta hada su guri daya a cikin wata qaramar a kwati sannan ta kulle, dik wasu kayan da zata buqata seda ta dauka sbda ta qudurtawa kanta cewar bazata sake dawowa qasar India ba, wannan Karon yaki zatayi da wa'yanda suka rushe mata farin cikin ta na rayuwa!
Nigeria
Bangaren Dady kuwa daqar ya mike ya nufi toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin wata farar shadda me ratsin blue ammata din kin irin na dattijawa ba laifi kayan sun masa kyau dik da ramar dake jikinsa kana kallon sa zaka fahimci baya cikin kwanciyar hankali, yaa fito cikin shirin fita Momy ya samu a zaune a falo se su fadilah da zahra'au, se kuma ameerah da Fa'iza dake ta fada akan rumot , fitowar Dady CE ta katse ameera da fa'iza sukavar fadan da sukayi sbda sunsan Dady ba wasa a lamarinsa !
Dady ya kalli fa'iza dake cika tana batsewa yace dan ubanki baki da kunya ko? Zakici qaniyanki,
Daga haka yayi waje abinsa be sake cewa kowa komai ba , yana fita ya bude mota ya shiga bashir driver yaja motar suka dauki hanyar Gidan shugaban 'yan sanda wato haruna musa majia.
To se ince a suka lafiya dady👏
Bani da ta cewa sedai ince Allah ya shiga tasakanina daku!
Bani da qarfin da zan Iya kare kaina daga sharrin makiyana !
A cikin Ku babu Wanda ya halicceni balle kuma yayimin wani Abu !
Niba kowa bacce balle kusa ni a gaba .
Fatan alkhairi shine fatan cibado ga kowa, ciki kuwa Harda Ku masu yimin barazana👉😘
[8:52PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 14*
Suna isa qofar Gidan aka bude musu gate suka shige kasancewar sunsan Dady sosai
Parking space suka nufa suka ajiye motar sannan ya ta sarwa qofar da zata sadashi da falon da sp majiya yake saukar bakinsa na musamman
Yana shiga ya samu guri ya zauna sannan ya dauki wayar sa ya danna number sp majiya ya sanar dashi cewar ya qaraso,
Bugu daya ya dauka ya fada masa ya qaraso sannan ya ajiye wayar ya zubawa TV idanu,
Ba jimawa aka cikawa Dady gabansa da kayan motsa baki kala kala, kodaya Dady be taba ba sabda shi yanzu ma ko wani irin abinci ya kalla Sam baya bashi shi'awar sa, dan haka kallo daya yayiwa abincin ya dauke kansa,
A hankali sp majiya ya qaraso falon tare da sallamar sa, har ya qaraso falon Dady be San ya shigo ba har seda ya tabashi sannan ya dawo daga duniyar tinanin kudan jininsa,
A dan daburce Dady yace barka da fitowa,
Sp yayi murmushi yace haba alhji abdul dubi fa yanda ka damu kanka da tunani wllh Harka rame kayi baki kamar ba kaiba, kayi haquri ka yarda da qaddarar da Allah ya aiko maka kaifa musulmi ne , insha Allah zamu samo inda muzaffar yake da izinin Allah, tunda sp ya fara magana Dady ke kallon sa sannan yace naji abinda kace sp kuma na gamsu da bayanan ka zanyi qoqarin cire ragewa kaina tinanin kamar yadda ka shawrce ni ngde Allah ya bar zumunci,
Sp yayi murmushi yace ba komai, kada ka damu,
Kuma insha Allah zamu zage dantse wajan gano inda danmu yake da ikon Allah.
Sosai Dady yaji dadin maganganun majiya dan har ya samu nutsuwa a zuciyar sa kuma yadan sake sunyi hira kadan,
Sannan sukayi sallama da juna cikin aminci har bakin mota sp majiya ya rako dady , ya shiga mota suna masu dagawa junansu hannu,
Dady be koma gda ba se 6:00pm koda ya dawo be tsaya ko INA ba se dakinsa alwala yayi ya sake fita be dawo ba se da yayi sallar magrib
RUGAR HARDO
tunda su muzaffar suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallon Rabe dik inda tabi idanunsa na kanta,
A hankali ta bude baki tace yaya zafar meyasa kake yawan kallona?
Murmushi yayi sannan yace sabda zanyi missing naki!
Sosai take kallon sa sannan tace me Kalmar take nufi?
A taqaice yace zanyi kewarki to.
Dariya tayi sosai irin wadda bata tabayi ba a gabansa a Iya zaman da yayi dasu, daqar ta saita kanta ta dena dariyar,
Tunda ta fara yake kallonta kamar wanda zeyi kuka yace, meyasa ki dariya haka?
Murmushi tayi tace abinda ka fada ne yasani dariya senaji Kalmar taban dariya,
Hade rai yayi yace to kada ki sake min irin wannan dariyar bana so, kinji yanda kika tsorata ni?
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riqe kunnuwanta dika biyun kamar yanda yakeyi mata idan ya bata mata rai, kamar zatayi kuka ta tsuguna qasa tace kayi haquri yaya zafar badan qara ba,
Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta yace shikenan na haqura amma kadan.
Dariya sukayi dukansu, sannan suka kamo hanyar gida dabda magariba suka dawo,
Tunda suka dawo Rabe bata qara bari sun hadu da zafar ba, a cewarta wai bata so taga tafiyar yayan nata !
Daki ta nifa tayi sallah tayi addu'ointa ta shafa, amma kuma bata tashi daga gurin ba,
Bangaren muzaffar kuwa tunda suka shigo yayi sallah amma bega shigo war Rabe ba se abin ya fara damunsa, har akayi ishsha beganta ba se abin ya fara daga masa hankali,
Daqar ya Iya bude baki ya cewa moddibo dake ta faman dura madara ajarka yace, baba!
Ya a nitse moddibo ya dago yace yaro ya akayi ?
A daburce yace dama,,, dam,,,,, Rabe se kuma yayi shiru.
Murmushi moddibo yayi yace yaro INA zaton ko tayi bacci ne,
Kayi qoqari ka kwanta sbda gobe asibanci zamuyi ,
Bashi da yanda zeyi haka ya kwanta amma fir bacci ya gagari idanunsa ,
A hankali ya firta meke faruwa dani ne??
Bangaren Rabe kuwa baccinta take hankalin ta kwance babu abinda ya dameta ,
Qasar India
Mamie tana idar da sallar asuba bata tsaya ko INA ba se airports dan cika umarnin mijin nata duka 5:30am suka daga zuwa Nigeria, tun da ta hau jirgi gabanta ke faduwa komeyasa????
Ban garan su muzaffar kuwa tunda gari ya waye suka gabatar da sallar asuba suka fara shiri ba yanda beyiba dan su hadu da rabe
Amma fir taqi da abin ya isheta ma seta bar Gidan tayi tafiyarta gidansu danejo qawarta,
Ba yadda ya Iya haka suka tafi ya naji yana gani suka shiga wata a mortar shanu suka kama hanyar garin kano garin alfarma!
Dik wannan uban sammakon da sukayi basu suka isa kano ba se qarfe 4:00pm
Wanda yayi dai dai da saukar mamie a qasarta ta haihuwa!
Cike da kulawa moddibo ya kalli muzaffar yace yaro zaka gane gida ko?
Muzaffar yayi murmushi yace zan gane,
Adaidaita sahu suka tare sannan muzaffar yace malam nasarawa g.r.a zaka kaimu ,
A take me napep yace musu dubu daya !
Bece komaiba suka shiga suka tasarwa nasarawa g.r.a
Mamie na sauka daga jirgi bata wani jima ba driver yazo ya dauke ta tana cikin motar gabanta yay mummunar faduwa!
Da sauri ta firta innanillahi wa'inna ilai hirraji'un.
Qofar wani gida na alfarma muzaffar ya nunawa me napep din tare da bashi izinin shiga horn me napep din yayi amma shiru ba'a bude gate din ba ,
Muzaffar ne ya zuro qafarsa da nufin ya suka , amma se moddibo yayi carap ya riqeshi yace yaro Sam be kamata ka shiga kanka tsaye ba, dolene ka badda kamannin ka,
Cike da rashin fahimta yace ban gane ba!
Murmushi moddibo yayi ya fito da wani rawani ya CE bani kanka, ba musu ya miko masa kan NASA ya shiga Nada masa,
Watabara'kallahu'ahsanulkhaliqin,
Abinda moddibo ya Iya fada kenan sbda wani azababben kyau da rawanin yayi wa muzaffar
Gashi sanye da kayan Fulani seya koma kamar wani balarabe!
Horn suka sake yi a karo na uku sannan me gadin ya bude yana ganin baquwar fuska ai seya dakatar dasu yace daga malamai daga INA?
Moddibo ne ya bashi amsa yace daqa rugar hardo!
Ba musu me gadi ya bude musu qofar suka shige sbda kwarjinin da moddibo yayi masa
Sauka sukayi shi kuma me napep suka bashi hagginsa Harda qari, mebawa fulawa ruwa suka samu su kace dan Allah ya sanarwa da alhaji abdul yana da baqi daga rugar hardo, cike da girmamawa ya amsa tare da kaisu falon saukar baqi
Se ince fatan alkhairi mlm moddibo👏
[8:53PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 15*
Sun jima suna zaune, sannan aka kawo musu abin motsa baki.
Lokacin da aka sanar da Dady zuwansu moddibo yayi mamaki sosai sbda shi bema taba jin sunan garin ba, amma dayake mutum ne shi me jama'a da kuma son mutane shiyasa be wani yi mamakin zuwan su ba, tashi yayi ya nufi falon sa na da yake saukar baqin sa,
Da sallama ya shiga falon, ya nemi guri ya zauna sannan suka gaisa da moddibo.
Kwata kwata be lura da wanda ke zaune a qasa ba,
Sosai Dady ya sakarwa moddibo fuska, a nitse moddibo ya fara magana tare da yiwa Allah godia yace da fari alhaji ka godewa Allah bisa ni'imar da Allah yayi maka a wannan rana!
Cike da rashin fahimta Dady yace ban fahimceka ba dan uwa?
Murmushi moddibo yayi sannan yayi masa nuni da muzaffar dake zaune da uban rawani a kansa gaba daya ya badda kama
Sosai Dady yake kallon dan nasa cike da so da qauna, da sauri ya nufi inda muzaffar yake da nufin ya rungume shi, haka shima muzaffar din beyi qasa a gwiwaba ya nufi mahaifin nasa suka rungume juna suna masu zubar da hawaye😭
Sosai suka bawa moddibo tausayi, sun jima suna rungume da juna sannan Dady ya cire jikinsa daga na muzaffar ya zubawa fukar dan nasa ido sosai rama ta baiyana a jikinsa sedai kuma beyi duhu ba haskensa yana nan yanda yake!
Se kuma alamar ciwon dake gefan kansa na dama Wanda be gama bacewa gaba daya ba.
Cike da damuwa Dady yake tambayar dan nasa meya faru dashi? Kuma ina ya shiga har tsawon wannan lokacin?
Muzaffar yayi shiru kamar bazece komai ba, seda ya dan nisa sannan ya gayawa Dady komai sedai be gaya masa da sa hannun su Ummah da Momy ba akan abinda ya faru dashi ba!
Har abinda ado yayi masa be gayawa Dady ba, kawai CE masa yayi 'yan fashi ne suka farauci rayuwarsu kuma sukayi yunqurin kashe shi, badan wannan bawan Allahn ba da tini na rasa rayuwata, ya qarasa maganar tare da zubda hawaye!
Da sauri Dady ya qaraso kusa da qafafuwan moddibo ya rige yana fadin ngde, Allah ya saka maka da alkhairi, haqiqa banida abinda zan biyaka dashi a wannan duniyar sedai kawai ince Allah ya biyaka da Gidan aljannah👏
Ya qarasa maganar tareda hawaye!
Murmushin qarfin hali moddibo yayi sannan yace haba alhaji dan Allah ka dena godemin sbda ni nayiwa yaro taimako ne don Allah ba dan kayi min godiya ba, dan haka ka bari godiyar ta isa haka, sedai kawai abinda zancema shine kayi a hankali sbda maqiyanka Dana danka suna tare dakai kuma sune sukafi kowa kusanci dakai!
Cike da rashin fahimta Dady yake kallon moddibo, kai moddibo ya daga masa alamar ae,
Kiran sallar da aka fara kira ne ya katse Dady daga tambayar da yaso yayiwa moddibo,
Tashi sukayi suka nufi masallaci dan su gabatar da sallar magrib,
Bayan sun idar ne suka nufi qofar da zata sadasu da Fallon,
Horn akayi daga bakin gate hakan ne yaja hankalin Dady da muzaffar, shiko moddibo shigewarsa yayi ya samu guri ya zauna, sannan ya fara nazari akan maganar da muzaffar ya gayawa mahaifin sa, to meyasa be gayawa mahaifin sa gaskia ba??
Lallai muzaffar yaro ne me sanin ya kamata kuma me gudin masifa.
Sbda gudin ta da fitina yayiwa mahaifin sa qarya dan ya fanshi kishiyoyin mahifiyarsa!
Gaskia samun irin sa se'an tona a irin wannan zamanin, haka kawai seyaji yaron ya qara shiga ransa.
Wata baqar Toyota benza ce ta sako kai cikin Gidan ko ba'a fada ba Dady yasan Mamie ce parking space suka nufa sukayi parking tana fitowa daga motar Dady ya yiwa muzaffar nuni daya shiga falon tun kafin ta ganshi,, haka kuwa akayi
Da sauri Dady ya nufi inda Mamie ke tsaye da murmushi a kwance a fiskarsa yace sannu da zuwa Uwar gida ran gida,
Murmushi Mamie tayi ba tace komaiba ta nufi bangaranta visa ga mamkinta ba ta ga qura ko daya ba harta isa falon ta ko INA tas tas ba datti daret bedroom dinta tanufa, tana shiga toilets ta shiga bisa ga mamakinta dik abinda take Amfani dasu tin daga sabulun Wanka har zuwa MacLean komai a kawai a ciki kuma dika sababbi, haka ma su towels,
Murmushi tayi sannan tace abou muzaffar kenan har yanzu kana nan yanda kake baka canza ba!
Dady ne yasa masu aiki suka shigarwa da Momy kayanta bangaren ta sannan ya nufi falon da moddibo ke zaune shida muzaffar,
Dady ne ya yiwa muzaffar izinin yakai moddibo bangaren saukar baqi dan yaje yayi Wanka ya huta
Haka kuwa akayi suna fita Dady ya nufi bangaren sa dan ya samu yayi Wanka zuciyar sa cike da farin ciki Mara musaltuwa,
Suna isa ban garen baki ya nunawa moddibo ko INA sannan suka zauna , a nan ne moddibo yake tambayar muzaffar meyasa baze tafi bangaren sa ba?
A taqaice yace Dady ne yace na zauna a nan har seya nemeni!
Lallai akwai magana a qasa se ince Allah ya huta gajia Mamie👏
[8:54PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 16*
Seda ta yi Wanka sannan ta gabatar da sallar dake kanta, ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Bangaren Dady kuwa yana shiga cikin gda dakinsa ya wuce seda Yayi Wanka ya kimtsa, sannan ya gabatar da sallar ishsha'insa, sannan ya nufi falon su momy,
Yana shiga falon ya same su dukansu akan dining sunacin abinci suda yaransu, kallo daya zakayiwa Dady ka fahimci yana cikin farin ciki, dan haka umma cike da gulma tace alhji da dikkan alamu kana cikin farin ciki, kodai an sake samun riba a company n ka na takalma ne?
Cike da masifa Momy ta fara magana tace riba? Ba wata riba da aka samu, wannan farin cikin da yake ba komai bane dalili ila zuwan matar sa, kuma wllh ka sani tunda ka jajibota cikin mu to wllh kayi bankwana da kwanciyar hankali, tana gama magana ta mike da nufin ta wuce dakinta,
Tsawa Dady ya daka mata wadda seda hanjin cikin ta ya kada yace ke kishiga hankalinki niba sa'anki bane da zaki sani a gaba kina yimin ihu, ko ba komai ni mijin ki ne kuma uban 'ya'yanki ko banci darajar kowa ba naci darajar 'ya'yana yana gamawa ya juya da nufin yabar falon, se kuma ya dawo yace idan sun gama suzo falon sa yana son magana dasu a bangaren da aka fat din Mamie kuma su zo da yaransu gaba daya sbda a kwai Abu me mahimmanci,
Yana kaiwa nan Yayi waje abinsa ban garen Mamie ya nufa da sallamar sa ba kowa a falon se qamshi dake tashi a falon sosai yake kallon falon Yayi matiqar kyau kamar yanda yake buqata, hanyar da zata sa dashi da dakin Mamie ya nufa tin kafin yakai ga dakin qamshin turarenta ya baqunci hancin dady, murmushi Yayi a zuciyarsa yace salma kenan kedai Allah Yayi miki son qamshi
Yana shi shiga ya sameta tana daura dan kwali a kanta sallamar ta amsa sannan tayi murmushi tace sannu abban muzaffar na sameku lfya ?
Dariya Yayi sannan yace Uwar gida ran gida lfy. Qalau mun godewa Allah ya gajiyar hanya?
Murmushi tayi sannan tace gajiya kam akwai ta Baban muzaffar.
Shiru suka dan yi na wani dan lokaci sannan Dady yace idan kinci kin gama shiryawa akwai maganar da zamu dan tattauna daku, gabanta ne ya fadi! da sauri ta furta innanillahi'wa'innah ilaihirraji'un, da Sauri Dady ya matsa kusa da ita ya dafata yana tambayarta meya faru?
Kuka ta saki sekace wata qaramar yarinya, beyi yunqurin hanata ba, seda tayi me isarta sannan tayi shiru,
A hankali ta fara magana ban San meyake damuna ba Sam! Koda yaushe a ' se in dinga jin gabana yana yawan faduwa, musamman ma yau ,
Lamarin nifa ya fara bani tsoro wllh, kodai wani abin ne ze faru dani? Ta qarashe maganar tana zubar da hawaye,
A nitse Dady ya fara magana yace haba salmah, har zuwa wani lokaci zaki kai kina wannan kukan?
Yakamata kisani cewa ko wani mutum da zanan qaddarar sa, kuma ko wani mutum da irin tasa qaddarar, don Allah kiyi haquri ki dena zubar da hawaye haka, insha Allah zamu samu cikar burinki da izinin Allah wata rana zamu hadu da su!
Cikin kuka Mamie ta fara magana tabbas nayi kuskure a rayuwata Abdul, gashi hakan yajamin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa,
Kuka sosai takeyi, har ga Allah ya tausaya mata dan haka yayta rarrashinta har ya samu tayi shiru,
Kicin ta nufa ta sa ruwan zafi ta hada tie sannan ta fito ta zauna a kan dining ta fara sha, tana cikin sha ameerah da zahra suka shigo falon da sallamar su cike da kulawa Mamie ta amsa sallamar tare da sakin fuska sosai baki ameerah ta saki tana kallon Mamie, zahra kuwa hankalinta yana kan Falon musamman yanda taga komai sabo ne bugu da qari ma gurin Yayi matiqar haduwa, a hankali ta furta waw gaskia falon nan ya hadu,
Ta juya da nufin ta tabo ameerah ai se sukai ido biyu da Mamie, air se itama ta tsaya tana kallon Mamie n, murmushi Mamie tayi sannan tace Ku shigo Ku zauna mana sekace baqi? Maza Ku shigo mana
Jiki a sanyaye suka shigo falon suka zauna ameerah CE ta fara gaida Mamie sannan zahra ma ta gaisheta, sosai Mamie ta sakar masu fuska suka dinga hira, a nan ne ameerah tacewa Mamie aunty gaskia ke kaykkyawa ce, daria Mamie tayi sosai dan har ga Allah ameerah ta bata daria,
A hankali Mamie ta sunkuyo taja hancin ameerah tace kema ai kyakkyawa ce,
Darirya ameerah tayi sannan tace aunty ni suna na ameerah wannan kuma zahra,
Murmushi Mamie tayi sannan tace ba suna na aunty ba Mamie zakice kinji?
Dariya zahra tayi sannan tace ke in banda baki da hankali Waya fada miki ana cewa babba kamar wannan aunty ? Ta qarasa maganar tareda nuna Mamie da hannunta, baki ameerah ta murgudawa zahra sannan tace an fada din ta qarasa maganar cike da tashin kunya,
Tunda ameerah ta fara zuba rashin kunyarta Mamie ke kallon ta, bata CE komaiba sema ja baya datayi daga kusa da ita ta koma kan daya daga cikin kujerun falon, sun jima a dan zaune sannan Mamie ta koma daki dan ta dakko wayarta a hanya suka hadu da Dady yana shirin fitowa falon shima, murmushi yayiwa Mamie sannan ya wuce ta gefanta ya nufi falon, yna shiga ya zauna a kan kujerar dake daukar mutum biyu, yana zama zahra ta sauka qasa tare da yiwa mahaifin nata barka da fitowa,
Sosai Dady yaji dadin abinda zahra ta yi shiyasa yake sonta sbda baba daya yaransa idan ka cire muzaffar a kyawawan halaye to se zahra ameerah kuwa yana zaune da alama ma bata da niyar sauka daga kan kujerar.
Tsawa Dady ya dakawa ameerah da sauri ameerah ta sauka qasa sannan ta fashe da kuka sbda tsoratar da tayi,
Ummah CE ta fara shigowa sannan Momy ta biyo bayanta se kuma fadilah dake bayan Momy n, Ummah CE tayi qarfin halin yin sallama,
Kallo daya Dady Yayi musu sannan ya dauke kai, a daqile ya amsa sallamar, sosai suke kallon falon sbda yanda ya hadu, koda wasa basu taba shigowa falon ba se yau, cike da masifa Momy ta fara magana tacewa Ummah kin gani ko? Ai dama na fadamiki gashi nan ai kin gani wllh dama na san tsugune bata qare ba, mun gudu ne bamu tsira ba da sauri Ummah ta dannewa Momy baki, tace haba zuwaira me kikeyi haka sekace wata qaramar yarinya?
[8:54PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 17*
Gaskia zuwaira baki kyauta ba, kuma gaskia ya kamata ki bawa alhaji haquri yanzunnan, ta qarashe maganar tare da kanne mata ido daya.
Nan da nan Momy ta fahimci manufarta dan haka ta sunkuya ta bawa Dady haquri,
Be ko kalleta ba ya juyar da kansa yace mata ya wuce,
Guri suka samu suka zauna, sun dan jima a zaune sannan umma tace alhaji ka kira mu amma har yanzu baka CE komai ba,
Shigowar Mamie ce ta sa umma hadiye maganar ta, da sallama Mamie ta qaraso falon kusa da zahra ta zauna , da murmushi a fuskarta tace sannan ku ya gda ?
Ummace tayi carab tace lfy qalau ya hanya? Ta qarasa maganar tana hararar Mamie,
Da kulawa Mamie ta amsa mata tare da jefa mata tambayar ta same su lfy.
A taqaice suka bata amsar lfy,
Dady yana zaune a inda yke wayarsa ya dauka a gefen kujerar daya ke zaune , ya kira wayar telho din dake dakin saukar baqinsa bugu daya muzaffar ya amsa, a taqaice Dady yace kazo falon Mamien ka Ina son Zama daku gaba daya,
Be ce komaiba ya ajiye wayar
Moddibo dake zaune kan sallayar da suka idar da sallah, bece masa komai ba se kallon sa kawai daya ke yi, jiki ba qwari muzaffar ya qaraso kusa da moddibo yace , baba wllh har ga Allah ina jin tsoron muta nan nan!
Cike da rashin fahimta moddibo yace yaro ban fahimci maganar ka ba, tsoron me kake ji?
Muzaffar yace baba INA magana ne a kan mutanen Gidan nan, ina jin tsoron kada su sake shirya min wani mugun abin!
Murmushi moddibo Yayi sannan yace yaro kaifa namiji ne dan haka ka daure ka zama jarumi, kuma ka dage da addu'a haqiqa babu abinda yafi qarfin Allah dan haka kada ka bari tsoronsu ya samu gurbi a cikin zuciyar ka, kaji yaro? Maza kaje kiran mahaifinka, Sam kada ka nuna rauninka a gaban maqiyanka,
Muzaffar yayi sannan Ya nufi qofar fita daga Falon,
Site din Mamie ya nufa , da sallama ya shiga Fallon da uban rawani kamar wani ba Sarake, tunda ya shiga falon muta nan dakin suke kallon sa dik da cewa basu gane shi ba , ciki kuwa harda Mamie, murmushi Dady Yayi sannan ya miqa hannayensa alamar yazo gare shi , da sauri muzaffar ya nufi mahaifin nasa ya suka sake rungumar juna , umma CE tayi qarfin halin cewa wai alhaji waye wannan din da kashigo dashi cikin gida har falo?
Ga kuma uban rawani kamar wani bafade!
Momyce ta qara da cewa inda duniyar nan ba gaskia ka jajibo mana shi baka tsoron yazo ya cutar damu a gaba?
Itadai Mamie bata CE komaiba sema kallon su da take, ta Kali wannan ta kalli wannan,
Murmushi Dady Yayi sannan ya kalli Momy yace kin taba ganin inda da ya cutar da ubansa?
A taqaice tace yo alhaji nawa akayi?
A hasale yace idan kuwa kika ga da ya cutar da ubansa to wllh wannan dan ba dan halak bane,
Ynan gama bata amsa yace zoka zauna Dana ,
Umma CE tace danka kuma alhaji ?
Kodai batan muzaffar yasa kanka ya fara kwancewa ne?
Ya zaka samo wani bafulatanin daji da uban rawani kace danka ne shi?
Da sauri Momy tace yauwa gaya masa dai maman zahra,
Murmushi Dady Yayi Wanda yake dauke da manufofi masu yawa, sannan yace, babu tabin hankali balle a samu matsalar qwaqwalwa!
A yau da yamma cin nan lbri mafi dadi a duniya ya sameni,
Ba wani lbri bane illa labrin baiyanar gudan jini na wato Dana namiji tilo wato muzaffar!
Gaban Ummah da Momy ne Yayi mummunan faduwa, nan da nan gumi ya fara karyo musu dik da sanyin Ac dake dakin hakan be hanasu fitar da zufa ba,
Kallo daya zaka yi musu ka fahimci suna cikin wani yanayi!
Momy CE tayi qarfin halin cewa to alhaji INA muzaffar din yake yanzu?
Bece mata komaiba se nuna mata shi da Yayi da yatsansa,
Cike da rashin fahimta Mamie tace abban muzaffar nifa ban fahimce Ku ba wai don Allah meyake faruwa ne??
Sam Dady be boyewa Mamie komaiba tun dga batan shi muzaffar din har zuwa yanzu da Allah ya baiyana shi, da sauri Mamie miqe daga inda take ta saukko qasa Inda muzaffar ke zaune, ta Dora tafikan hannayenta a kan fiskarsa tana me zubar da hawaye tana kallonsa cike da tsantsar so da qauna tace, haqiqa INA matiqar qaunarka Dana kuma dik duniyar nan dik Wanda ze soka wllh a bayana yake muzaffar!
Dama abinda ya faru dakai kenan yasa kwana kin baya nake ji a jikina wani Abu ya faru da gudan jini na?
Ashe shiyasa na rasa kwanciyar hankali? Ta qarasa maganar cikin kika me matiqar ban tausayi!
Daqar ta tsagaita kukanta sannan tace INA matiqar sonka dana, idan wani abin ya sameka wllh har abada zanyi Dana sani!
Cike da makirci umma tace ke kinga fa bawaifa fin mu sonsa kikayi ba! Kin wani sashi a gaba se kuka kikewa muta ne, kafin kisanshi fa mumuka sanshi, tunda mu muka fara auren ubansa kafin ke,
Da sauri Momy tace gaya mata dai zata yiwa mutane kini bibi wai ita matar uba,
Mamie batace komaiba se kika da take, muzaffar ma kukan yake yana me mamakin irin qaunar da Mamie take masa !
Tabbas koda mahaifiyarsa CE irin son da zatai masa kenan,
Hawayen fiskarta ya fara goge mata da hannayensa,
Dik wannan abin Dady yana kallon su sannan yace dikkan Ku Ku dakata sbda wannan abin ba shine mafita ba, yau kowa zeji abinda na Dade ina boyewa a gare Ku
Wata qila ya bku mamaki amma kuma Sam ba abin mamki bane
A cikin masu mama kin nasan harda kai muzaffar!
[8:55PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 18*
Cike da rashin fahimta muzaffar ke kallon mahaifin nasa sedai bece komaiba,
Dady Yayi ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da magana kamar haka
Haqiqa na boye muku wani al'amari a Iya zama na daku, ya nuna umma da Momy
Sannan ya cigaba da magana,
Na gwada Ku a baya ta hanyar kawo muku Dana muzaffar tin yana shekara daya a duniya na raboshi da mahaifiyar sa na kawo muku shi,
Sbda na gwada tsoron Allah n Ku da kuma tausayin Ku,
Amma se kuka kasa riqeshi da gaskia, kuka dnga cutar da shi, abinda Baku sani ba shine mahaifiyar muzaffar tananan a Raye bata mutu ba,
Cike da tashin hankali gami da fir gita muzaffar yake kallon mahaifin nasa yace, Dady kana nufin kace min mahaifiyata tana nan da rai bata mutu ba?
Amma Dady meyasa ka rabani da mahaifiyata?
Meyasa ka zabi na rayu da wasu sabanin mahaifiyata?
Meyasa kace min mahaifiyata ta rasu? Pls Dady ka cireni a cikin rudanin Dana ke ciki don Allah
Da rarrafe ya matsa gurin Mamie ya riqe hannayenta yace Mamiena don Allah ki cewa Dady ya kaini gurin mahaifiyata na ganta koda so daya ne don Allah Mamie!
Ya qarasa maganar yana kuka sosai kamar wani qaramin yaro,
Da qyar Mamie ta saita kanta sannan tace ka kwantar da hankalin ka yarona baka da wata Uwar da ta wuce ni kaji ? Nice mahaifiyarka ba wata ba,
Momy CE tace haba malama kinga ki dakata ki barmu da almarar data muke ciki, ya za'ai kizo kisamu a gaba kina yimana kukan kirsa da makirci,
Ki rufe mana baki muji qarshen zance,
Ummah tace muma fa muna son yaron nan kawai dai tsautsayine da kishi yasa muka kasa riqeshi tun farko, shiyasa ma ya kawo miki shi amma bawai finmu sonsa kikayi ba
Kuka sosai muzaffar yake yi, dadyne ya katse su ta hanyar ce gaya musu cewar Mamie itace mahaifiyar muzaffar, kuma itace matar daya fara aure a rayuwar sa, dan haka itace Uwar gidansa kuma mahaifiya ga muzaffar!
Dikkansu seda suka girgiza musamman ma momy, sbda tashin hankalin da momy ta shiga numfashinta har sama ya fara yi,
Umma ce tayi qarfin halin zaunar da momy,
Sun jima suna alhini
Mamie qara rungume dannata tayi cike da soda qauna,
Seda suka dauki lokaci me tsayi babu Wanda yace komai ,
Fadilah CE tace momy tashi mu tafi sbda ki samu nutsuwa,
Ba musu momy ta tashi dan dama hanya take nema
Suna shirin fita umma ma ta bisu,
Suna fita ameerah tace zahra zo mutafi muma, harara zahra ta zab gawa ameerah tace ba inda zani kawai kiyi tafiyarki,
Tashi ameerah tayi tabar falon kamar zata tashi sama,
A hankali zahra ta sakko qasa daidai inda qafafun Dady suke tace Dady don Allah kayi haquri da halayen da iyayen mu suke Nuna maka nasani dole wata rana zasuyi nadama,
Tana gama magana da Dady ta juya ga muzaffar tace yaya, haqiqa ina me jajanta ma abinda ya faru dakai ina me yi maka addu'ar alkhairi a koda yaushe sbda kai dan uwa na ne kuma guda daya tilo, nasani wata rana dole Kaine zaka zama uba a garemu gaba daya,
Nasani bamuyi sa'ar iyaye ba, amma don Allah INA me roqa masu afuwa akan abinda suka aikata maka kana yaro don Allah yaya muzaffar kayi musu afuwa, tana maganar ne tana hawaye,
A hankali ta daga jajayen idanunta ta kalli Mamie tace , haqiqa ke uwa CE wadda ta cancanta a yaba mata tunda har kika Iya sadaukar da danki guda daya tilo dan farin cikin mijinki, wllh dik inda uwa ta gari Takai kinkai Mamie, dama kece kika haife ni wllh danayi alfahari dake,
Tana kaiwa nan ta miqe ta fice daga fallon tana me zubar da hawaye
A wannan rana muzaffar kwanan farin ciki Yayi, hakama Mamie da Dady
Su umma da momy kuwa kamar su mutu din bakin ciki
RUGAR HARDO
Tunda muzaffar ya tafi komai ya dena yiwa rabe dadi
Gashi yau kwanan sa daya da tafiya amma har ta rame sbda kuka , bugu da qari ga kuma azabar da Laure take gana mata, abin gwanin ban tausayi,
Tashi tayi daga dakin ta fita chan gurin garken shanunsu Inda suke zama ita da muzaffar, dutsen daya ke zama a kai ta Dora hannunta akai seta sake fashewa da matsanancin kuka me cin rai
Cikin kuka take fadin ya Allah Kaine ka bani farin ciki a lokacin da bani tsammani ba!
Ya Allah ina ina roqonka da sunayenka kyawawa, ya Allah ka cika rayuwata da farin ciki me dorewa, ya Allah ka bani ikon jure ko wacce irin jarrabawa!
Tanayi tana kuka sosai abin qwanin ban tausayi,,,,,,
[8:55PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 19*
Hka tayita rusar kukanta babu me rarrashinta, sda rana ta bude sosai sannan ta Tisa dabbobin suka tafi kiwo, haka ta dinga tafiya jiki ba qwari, inda suke zama da muzaffar idan sun gaji ko kuma zasuyi sallah, a nan ta zauna ta sake yin shiru, nan da nan ta tafi duniyar tinanin yayan nata!
A ranar dai haka ta wuni sukuku da ita
Momy ce tsaye a cikin dakinta tana ta safa da marwa da Waya a hannunta, falo naga ta nufa fiskarta a daure fadilah ta samu a zaune bata ko kalleta ba tace tashi kije ki kiramin Umman zahra, bata jira cewarta ba ta koma dakin ta
Ba'a dau lokaci me tsayi ba sega umma ta shigo dakin , Sosai take kallon Momy sannan tace nariga na fahimci me kike son gaya min tin daga qwayar idanun ki, yanzu meye mafita ? Tambayar da Momy ta jefawa umma kenan,
Bata CE mata komai ba ila daga wayar hannunta da tayi da alama wani take son kira,
Ba'a dau lokaci ba ta fara magana cikin isa da nuna gadara tace ado haka mukayi dakai?
Nawa muka baka a kan ka kashe mana wannan dan iskan?
Da kasan ba zaka iyaba kuka karbar mana kudi?
Cike da mamaki ado yace haba hajjaju, ai tin tini aka gama wannan aikin dan sda na tabbatar baya numfashi sannan na qyaleshi!
Kema kinsan Baku taba bani aiki na kuskureba,
Momy CE ta fisge wayar daga hannun umma ta kara a kunnenta cike da masifa tace har kana da bakin da zakace baka kuskure a aikin ka?
Kai daqiqin inane da zaka yarda shi a Inda mutane suke shige da fice?
To gashi yanzu ka jiqa mana aiki yaron ya dawo gida da ransa da kuma lafyar sa, kuma kasan dole 'yansanda zasu karbi bayanai daga bakinsa , dan hka seka zauna cikin shiri, at any time zasu Iya zuwa kamaka!
Ta qarasa maganar cike da masifa gamida tarin bacin rai
Umma CE tayi saurin karbar wayar tace ado kana jina?
Cike da tsoro yace ae Hajia inajinki
Maza- maza ka shirya kabar garinnan kayi nesa da kano Sam karka dawo semun nemeka, da sauri yace to Hajia, sda ta dan nisa tace masa amma dai a kwai kudi a hannunka ko?
A'a yace mata nan da nan tace yaushe na saka maka million daya a account dinka da zaka cemin ba kudi?
A daqile yace sorry Hajia na shiga rudani ne, bata sake cewa komaiba ta katse wayar sannan ta bude wayar ta cire sim din ta karya sbda gudun seta kwana!
A hankali umma ta dafa kafadar Momy tace haba zuwaira kada ki bada mata mana, ai yanzu damace tazo mana,
Cike da rashin fahimta Momy tace kamar ya ?
Murmushi tayi irin nasu na 'yan duniya sannan tace shishigewa waccan matsiyaciyar zamuyi, idan ta saki jiki damu se mu aika shegiya garin da ba'a dawowa! Koya kika CE?
Dariyar jin dadi Momy tayi sannan tace wllh kamar kinsan abinda ke raina,, suka sake kwashewa da dariya suka tafa(haqiqa kishi da rashin tsoron Allah yana kai mata dayawa ga halaka, mugun nufi bashida wata fa'ida illa yakai mutum ga na dama! Dan Allah mata mu gyara zukatan mu, kishi halitta ne kuma kowace mace tana dashi a tare da ita muddin tana da lfy, amma idan kika bishi ta hanyar daya dace wllh zaki zauna da kowa lfy, wannan abin nasu Momy Harda son zuciya gamida tarin rashin tsoron Allah, ya ubangiji Allah kasa mufi qarfin zukatan mu)
Moddibo ne zaune qasan kafet yana daure boronsa da alama shirin tafiya gda yake muzaffar ne ya shigo dakin da murmushi a kan fiskarsa yace baba,,,, se kuma yayi shiru, da sauri ya qaraso inda moddibo yake cike da damuwa yace baba badai har ka fara shiriba tin yau?
Murmushi moddibo yayi irin na dattijawan qwarai yace to yaro me kuma zan tsaya jira?
Tunda Allah ya amince mana min samu nasarar kawoka Gavan Iya yenka ai kuma nima sena fara shirin komawa gida kodan sbda Rabe na!
Nasan yanzu tana nan cikin kewata , ban taba tafiya me Nisan haka na barta a gda ba, a Iya zaman ta dani ban taba tafiyar da takaini ga kwana ba sbda tinanin halinda zata shiga idan bana nan,
Dan haka Gobe da ikon Allah zan kama hanyar gda ,ya warashe maganar da murmushi a fiskarsa
Shiru muzaffar yayi na dan lokaci tabbas yana mamakin shaquwa irinta moddibo da diyarsa, yanzu idan tayi aure ya zeyi?
Kafadarsa moddibo ya dafa yace yaro naga daga jiya zuwa yau kanata farin ciki,
Murmushi muzaffar yayi sannan ya labirtawa moddibo komai, sosai moddibo yayi farin ciki gamida yiwa muzaffar nasihu masu shiga jiki sosai,
Jikin muzaffar haka yayi sanyi sbda nasihun da moddibo yayi masa, a ransa seyaji dama moddibo ya zauna tare dashi haka kawai dattijon ya gama shiga ransa,
Jiki ba qwari muzaffar ya miqe sbda jin kiran sallar ishsha'i, be cewa moddibo komaiba, ya nufi hanyar fita
Murmushi moddibo ya kuma yi sbda ya fahimci muzaffar fishi yayi sbda yace ze tafi gobe
Miqewa yayi shima suka nufi masallaci, daidai lokacin da Mamie ta loqo ta window falon ta bayan su ta hanga sannan ta koma taci gaba da jera abinci akan dining,
Koda aka idar muzaffar ya Dade yana addu'oinsa sannan suka shafa suka fito gaba daya,
Dai dai lokacin da Dady ma ya fito tare suka jera suna tafe suna hira anan muzaffar ke shaidawa Dady tafiyar moddibo, sosai Dady ma yaji ba dadi sbda yanda ya saba dashi a kwana daya kamar sun shekara da sanin juna, moddibo akwai sauri saboda mutane, gashi da haquri da sanin ya kamata shiyasa yake da dadin mu'amala,
Indai ya zauna dakai koda na wuni daya ne to Seka qaunace shi. Sbda dattijon a kwai shiga rai
Suna shiga Dady yacewa moddibo tunda gobe ze tafi don Allah yazo suje bangarensa suci abinci tare amma fir moddibo yaqi amincewa , haka Dady ya haqura badan yaso ba yayiwa moddibo seda safe sannan ya wuce bangaren Mamie,
Ban garen da aka sauki moddibo suka muzaffar yana biye dashi a baya har suka isa a falo suka zauna, muzaffar ne ya fita dan dakko musu abinci a bangaren Mamiensa , be jima ba ya dawo dauke da manyan food flasks guda biyu se zahra dake bayan sa hannunta dauke da flat da spoons ajiyewa tayi sannan ta koma ta daukko wani flat dauke da kosilo Wanda yaji qwai da bama ansa wata fara leda an rufe farantin da ita ta yanda kana Iya ganin abinda ke cikin flat din da sallama ta shigo ta ajiye sannan ta gaida moddibo cike da girmamawa, da kulawa ya amsa mata tareda sakin fuska, an an yake tambayar ta sunan ta murmushi tayi sannan tace zahra,
Murmushi moddibo yayi sannan yace Ashe mata nane da kanta, dukansu suka sa dariya sannan ta miqe tayi musu saida safe ta wuce bangaren su
[8:55PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 20*
Zaune suke kan dining suna cin abinci, Dady yake sanar da Mamie tafiyar moddibo da safe idan Allah ya kaimu, gaban Mamie ne yay mugun faduwa sbda sunan da taji mijinta ya ambata , take yanayinta ya sauya,
A hankali tace daga zuwansa har ze koma se kace ana korar sa?
Murmushi Dady yayi sannan yace wllh nima haka nace dashi amma fir yaqi yarda ya qara kwana ki,
Dik wannan hiran da suke itada Dady qarfin hali kawai take tinda taji sunan moddibo, sunan da bazata taba mantawa dashi ba a rayuwata
Dady ne ya katseta ta hanyar sanar da ita yayi kewarta,
Murmushi Mamie tayi sannan tace abban muzaffar kenan sekace wasu yara?
Dariya yayi sannan yace mata au yara ne kawai suke soyayyah?
Bata CE masa komaiba dan ta fahimci Neman magana kawai yakeyi,
A hankali ta ajiye cokalin dake hannunta ta miqe a taqaice tace seda safe,
Sam beyi qoqarin hanata tafiya ba sbda ya fahimci yana yinta ya canza tunda ya ambaci sunan moddibo.
Abinda ya qara daure masa kai shine meyasa bata son taji wani me suna irin hka?
A hankali ya rintse idanunsa, sbda baya son abinda ze batawa matar tasa rai, a daddafe ya kammala cin abinci, ya miqe ya nufi bedroom din shima, a zaune ya sameta da alama daga toilet ta fito, kana kallon ta zakasan tayi kuka, bece mata komai ba ya shiga toilet yayi brush sannan yayi wanka yafito, beyi mamakin ganin ta ajiye masa jallabiya ba sbda hakan al'adarta ce, murmushi yayi sannan ya sanya a jikin sa, yana gama sawa haye gado abinsa bece mata komaiba ya ka bargons da nufin ya kwanta,
Da kanta ta fahimci yayiwa megidan nata laifi dan hka ta bude baki tace don Allah kayi haquri bani da yanda zanyi ne dolece tasa,
Sanin kanka ne kasan bazan taba mantawa da me wannan sunan ba seta fashe da kuka,
Sosai me Gidan nata ya tausaya mata, dafata yayi sannan yay mata nasiha sosai tareda sake nuna mata mahimmancin yarda da qaddara,
Jikinta ne yayi sanyi sosai a hankali taba bargo ta kwanta, a nan ne Dady yake tambayar ta me take ganin zeyiwa moddibo idan ze tafi sbda nuna jin dadin abinda yayiwa dansa Wanda yasan ko duniyar nan yabashi be biyasa ba ,
Murmushi Mamie tayi me sauti sannan tace ka bari tukunna seda safen mayi maganar,
Bata qara cewa komaiba tayi addu'ointa ta tofa, ba jimawa bacci ya dauketa ,
Ban garen su muzaffar kuwa hira suke sosai da moddibo sekace ba dare ba, sun jima suna hiran sannan moddibo ya tashi ya wuce daki sbda bacci daya ke ji, kuma gashi fitar wuri yake so yayi,
Murmushi muzaffar yayi tareda dadin seda safe
A hankali ya tashi ya kashe TV sannan ya rage ywan Ac dake falon sannan ya rage wutar falon ya mike ya nufi bangaren sa, bisa ga mamakin sa seyaga an qara gyara masa dakin, ko ba'a fada ba yasan zahra CE da wannan aikin
Murmushi yayi sanan yace Allah sarki my Darling,
Wanka yayi sannan ya fito daga toilet din sanye da wata farar jallabiya, dik da cewa shirin bacci yayi amma rigar ba qara min kyau tayi masa ba, a hankali ya qraso bakin makeken gadon sa qirar Italian ya zauna yayi shiru, kallo daya zaka yimasa ka fahimci damuwa a fiskarsa,
Wani abin hannun roba dake hannunsa ya taba se kuma ya saki wani tattausan murmushi, a hankali ya firta I miss you Rabi'atu, I miss everything about you, murmushi ya sake yi a karo na biyu sannan ya hau gadonsa yaja bargo ya kwanta, ya jima yana nazarinta tareda Tina wasu abubuwa na quruciyarta gami da yawan murmushin ta,
Yajima yana aikin tinani sannan bacci yay a won gaba dashi,
Kiran sallar farko moddibo ya mike ya shiga toilet yayi Wanka yayi alwala ya kimtsa.
Masallaci ya nifa, yana shiga masallaci ya gabatar da raka'atanul fijir bayan ya idar ya dan jima a zaune yana addu'ah sannan aka gabatar da sallar asuba,
Bayan ya fito masallaci suka hadu da muzaffar suka wuce gda suna hirarrakin su,
Ban garan moddibo suka nufa ya tayashi ya hada kayan sa ya daure seda gari yayi haske sannan Dady ya shigo bangaren dan su gaisa da moddibo, bayan sun gaisa ne Dady yace masa yazo su gaisa da mahaifiyar muzaffar sannan yayi breakfast, se su wuce, murmushi moddibo yayi sannan ya CE to babu damuwa idan ka shiga seka sanar da iyalin baka shigo war tawa,
Murmushi Dady yayi sannan ya kalli muzaffar yace ka shigo dashi falon Mamie n ka idan ya kammala murmushi shima yayi ya amsa da to Dady,
Dady na shiga ya sanar da Mamie cewar moddibo ze shigo yayi mata sallama, murmushi tayi sannan tace gaskia be kamata ya tafi yanzu ba dama ya qara mana kwana 2 murmushi Dady yayi suna ta hira abinsu,
Mamie tace ina zuwa naji kamar abinda na Dora yana kamawa , kichin ta nifa dan ta sauke abinda ta Dora,
Tana fita su moddibo da muzaffar suka shigo falon, guri muzaffar ya nuwa moddibo sannan ya zauna shima hira suke dan yi da Dady jefi jefi, a haka Mamie ta fito ta samesu , ko kadan moddibo be kalli fiskarta ba itama haka ta qaraso falon fiskarta dauke da murmushi a nitse ta zauna a gefan Dady sannan ta fara gaida moddibo a nitse ya fara amsawa cike da kulawa,
Cike da tashin hankali Mamie ta dago sbda jin muryar da ko a INA take tasan mamallakinta,
Kallon moddibo take haka shima kallon Nata yake cike da tashin hankali yake nuna ta da yatsa,
Kasa cewa komai yayi dan haka kawai ya miqe da nufin yabar falon gaba daya,
Da sauri Mamie ta riqe qafafuwansa tana kuka me tsima zuciya, cikin kukan take fadin dan Allah Iya kayi haquri ka yafe min nasan nayi kuskure a rayuwa ta yanda bazan Iya gyara laifi naba! Ta qarasa maganar tana kuka sosai
Cike da rashin fahimta Dady yake kallon su haka ma muzaffar da kansa ya gama daurewa,
Cike da damuwa Dady yake tambayar Mamie shin tasan moddibo ne? Kuma meye hadinta dashi da har take fadin ya yafe mata?
Da qar ta Iya bude baki tace dan uwa nane shine yayana moddibo da mukaje nema shekaru a shirin da biyar da suka wuce, to shine wannan ta qara fashewa da kuka,
Qarfin hali moddibo yayi ya fisge qafarsa daga hannunta ya fice daga falon da sauri yana zubar da hawaye,
Ko kayan sa be dauka ba ya fice daga Gidan gaba daya,
Yana fita ya samu keke na pep ya shiga batare da ya gaya masa inda ze kaishiba !!
Seda suka fara tafiya me napep din yace mlm INA zan kaika?
A taqaice yace masa tashar mota zaka kaini, don Allah idan kasan inda ake lodin abuja ka kaini gurin sabda sauri nakeyi,
A kan titin Zaria road ya sauke moddibo sannan yasa shi a motar abuja,
yakoyi sa'a ciko ake Neman , kudinsa ya bashi sannan yayi masa godiya suka kama hanyar abuja,
[8:56PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 21*
Tun bayan tafiyar moddibo Mamie take kuka, gaba daya hankalin Dady ya gama tashi yama rasa me zeyi guri ya samu ya zauna tare da dafe kansa daya ke masa wani irin nauyi,, falon ne yayi shiru ba'a jin komai se sautin kuka Mamie, muzaffar ne yayi qarfin halin cewa Dady wannan zaman fa ba shine mafita ba fa,
Kawai tashi zamuyi mubi bayan sa, nasan ze sauraremu inayaso se'a gyara matsalar senake ganin hakan zefi da wannan zaman da muke,, cikin kuka Mamie tace nasan halin sa muzaffar yana da matiqar haquri amma idan yayi fishi yana da wuyar sha'ani!
A hankali Dady ya sauke ajiyar zuciya sannan yace abinda muzaffar ya fada shine daidai ki tashi kije ki wanke fuskarki ki shiya mubi bayansa , hakan shine mafita, haka kuwa akayi, a gurguje Mamie ta gama kimtsawa ta fito, koda ta fito bata samu muzaffar da dady a falon ba , dan haka bata tsaya jiran komaiba ta nufi waje tana fita ta hangi muzaffar a parking space yana tsaye a jikin wata ibgegiyar mota qirar ford,da alama fitowarsu yake jira, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda milk colour ammata dinkin tazarce, aikin dake jikin shaddar maroon color ne dan haka ya sanya hula maroon da ratsin milk a jiki ta kalmin qafarsa me danyasa ne shima maroon, se agogon dake hannunsa qirar Gucci, sosai yayi kyau kayan sunyi matiqar amsar jikin sa, a hankali Mamie ta qarasa inda yake kallo daya zakai mata kasan tana cikin damuwa mara musaltuwa, amma dik da haka damuwar bata hana futowar kyawun da Mamie n keda Shiva, da sauri dan nata ya matso kusa da ita ya rungumeta yace don Allah Mamie ki ya rage damuwa indai baba ne wllh ze fahimce ki, nasan shi yana da sauqin hali a Iya zaman danayi dashi , pls Mamie ki cire damuwa haka don Allah!
Batace komaiba se cire jikinta zatayi daga nasa , sannan tayi wani marayen murmushi me baiyana karayar zuciya da qarfin gwiwa tace hka dai kace yaro amma ni nasan da wuya moddibo ya yayfemin abinda nayi masa ,
Be sake cewa komaiba sbda fitowar Dady dasu umma daya gani, a nitse suka qaraso gurin murmushi Mamie tayi musu tareda CE musu muntashi lfy ?
Umma CE ta amsa mata da fara'arta , Momy kuwa ko kallon ta batayi ba, da sauri zahra ta matsa kusa da Mamie tace Mamie INA kwana ? Da kulawa Mamie ta amsa, muzaffar bece musu komai ba sbda shi gaba dayansu ma haushi suke bashi , daya ga abin nasu bana qare bane, se yace pls Dady Ku shiga muje sbda mu isa da wuri, daga haka ya bude driver seat ya zauna, yana qoqarin rufewa zahra ta riqe hannunsa da sauri tace pls yaya nima zan biku tunda ba school don Allah!
Ta qarasa maganar tare da langabar da kanta kamar wata yarinya,
Dariya ma ta bashi dan haka yace ta shiga suje da gudu ta bude qofar gaba ta shige tana yiwa ameerah qwalo,
Mamie CE ta fara shiga sannan Dady da sauri ameerah ta matso ta cewa muzaffar yaya nima, ai be jira cewarta ya daka mata tsawa yace bacemin da gani ba inda zamu dake Mara kunya kawai!
Da gudu ta bar wajen tana kuka, cike da masifa Momy tace to seme in baka je da ita ba?
Ta juya itama ta bar gurin,
Be jira cewarta ba ya tashi motar suka bar harabar gidan , suka nufi hanyar RUGAR HARDO!
Se wajen qarfe uku sannan moddibo ya isa yana hanyar sa ta shiga gida ya hangi Rabe a zaune cikin garken shanu ta rafka uban tagumi, inta take ya nifa ya kamo hannunta yana kallon fiskarta sosai yaga rama a tare da ita, ga kuma duhu da ta danyi ba komai a fiskarta se daradaran idanunta da suka sake fitowa se dogon hancinta shima daya baiyyana alamar rama, be jira cewarta ba ya ka hannunta sukayi gida, mamaki ne kwance a fiskar Laure
Dan haka tace mlm har ka dawo?
Sbda takaici ko kallonta beyi ba ya jata sukayi daki
0 Comments