✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*JAMA'A ASSALAMU ALAIKUM WARAH MATULLAHI TA'ALA WA BARAKA TUHU. GODIA YA TABBATA GA ALLAH S.W.T MAI KOWA ME KOMAI WANDA CIKIN IYAWAR SA DA YADDAR SA ,YA ƘADDARA NA SAKE ZUWA MUKU DA WANI ƘAYATACCEN LABARI ME ƘUNSHE DA DARUSSA IRI DABAN-DABAN NA RAYUWAR ƳAƳA MATA. NICE TAKU HAR KULLUM SIDIYA KUMA MALAMAR FARSAFA. SAI INCE KU BIYO NI...*
NOTE:
*LA'ALLA AKWAI YUWAR IN MAIDA LITTAFIN NA KUƊI NAN GABA KAƊAN. DA FATAR MASOYA NA DA MASU BIBIYAR LITTAFAI NA ZASU BANI HAƊIN KAI WAJEN NUNA MIN ZALLAR ƘAUNA??? ANAN SAI INCE ASHA KARATU LAFIYA!!!*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
_Page_ 1-5
📖_____
ƙarar mari kake ji ,Tasssss! sai kace saukar aradu. A hasale yake magana kamar wanda zai tashi sama dan tsabagen masifa. A yadda yake ta sababi kai kace wani laifin azo a gani aka masa ,har yake ɗaga jijiyoyin wuya haka.
"wai khadija wace irin wawuyar mace ce ke ,ballagaza? ban taɓa saka ki aiki kika mun a daɗin rai ba, wllh ba kida wani amfani a waje na, mace sai kace dabba, kana nuna mata hanyar aljanna tana bijirewa, to wallahi ki kuka da kanki ,ki kuma kiyaye ni kinji na gaya miki ,mutuniyar banza kawai"... Malam Ali yaƙa rasa bambamin shi yana mai nuna matar tashi da yatsa ,alamar gargaɗi...
Zube wa ƙasa khadija tayi kan guiwowin ta, kamar me kwasan gafara. A lokaci ɗaya Hawaye na kwaranya akan fuskarta. Cikin shash-shekar kuka da muryar lallashi khadija ta fara bama mijin nata haƙuri
"Dan Allah Abu Hanifa kayi haƙuri ,ka yafe min. Wallahi ba wai nayi da niyya bane, kuskure aka samu. Sanin kanka ne abu indai mallakar kane ,ko da kare ka kawo gidan nan ,to bama niba, wani can daban bazai masa kallon banza ya tashi ya wuce ba ba tare da na nuna masa kuskuren sa nayin hakan ba ,a lokaci guda kuma ,sai na nuna masa daraja da ƙimar abun ka a waje naba.
yadda abun ya faru shine, idan baka manta ba ɗazu da safe, kaine da kanka ka jiƙa kayan a ruwa ,to ina tunanin mantawa kayi ka saka musu Hypo, ka manta shadda bana saka mata hypo idan zan maka wanki??? Allah ya sa kayan ba wani jimawa sukayi a ruwa ba, kana fita na ɗauko zan wanke, ɗago su da zanyi naji ƙamshin hypo , hankali na idan yayi dubu ya tashi, shine fa nayi maza na wanke na ɗauraye na shanya. ban samu kwanciyar hankali ba Seda suka bushe na tabbatar iya hannun rigar ne kawai yaɗan taɓa ,shima ba wani sosai ba, kai kuma daka ga kayan kayi tunanin ko gaba ki ɗaya ne suka ƙoƙe. Ka ansa ka duba. Ta ƙarasa maganan tana janyo kayan dayayi wurgi dasu ƙasa.
Kalaman Khadija cike suke dason gamsar da mijin nata!
Hannu Malam Ali yakai ,ya amshi kayan. Warware wa yayi ,yana me bin rigar da kallo dalla-dalla. "Shakka babu kinyi gaskiya khadija, ni shaf na manta ,ina ta sauri in fita karna makara wajen meeting."
cikin nuna damuwa khadija tace "Allah sarki mijina! to ya taron ya kasance?"
"Alhamdulillah! Taro yayi taro ,an watse lafiya" Ya bata amsa fuskar shi ba yabo ba fallasa ,da alama fushin nashi ya ɗan sauka.
Kayan jikin shi ya fara ƙoƙarin ragewa ,da sauri khadija ta taso ta matso har daf dashi. Taimaka masa tayi ya zare kayan ɗaya bayan ɗaya. Seda ta tabbata ta maida komai mazaunin sa. Ganin cewa akwai gajiya a tattare dashi ,yasa batayi wata wata ba. Banɗaki ta shiga ,ba ɓata lokaci ta had'a masa ruwan wanka mai gasa jiki. Sosai yaji ɗaɗin ruwan, ko kafin ya fito kuma ta haɗa ruwan ɗumi da mantale ta aɗan wani rabo ,towel ne riƙe a hannun ta ,tana jiran shi ya fito ta gasa mai jiki.
Sosai Malam Ali yaji ɗaɗin gashin jikin da matar tashi tai masa. Abinci ta zuba masa, seda ta tabbatar ya warware gajiyar daya ɗauko. Dikkan su zama sukayi jigumm ,kamar masu ɗaukan darasi. Kukan Hanifa ne ya ankarar dasu. Kuka take kamar an tsikare ta... kuka take sosai, cikin hanzari khadija ta ƙarasa zata ɗauko ta ,a mamakin ta se taga idanuwan ta a rufe ,wanda ya nuna a bacci take kukan. cak ta tsaya tana ƙarewa Ƴar tata kallo ,da alama tasha kuka kafin bacci ya ɗauke ta...
Masifa Malam Ali ya fara
" wai me ya same tane? jifa irin kukan da take yi da alama ta jima tana kukan kafin ta samu bacci?"
Hawaye ya cicciko a idanuwan khadija ,cikin natsuwa take wa mai gidan ta bayani "Dama ɗazu ne da ina goge kayan ka ,nake ta jin kukan ta, ni kuma bana so in tsaida gugan ,a ɗauke wuta ,inzo ban kammala maka gugan ba ,ka dawo ranka ya ɓaci shiyasa, na bari har in gama tukunna, koda na kammala, nazo in ɗauke ta ,shine na samu har tayi bacci. Dan Allah kayi haƙuri Abu Hanifa ,wallahi bazan iya juran fushin ka ko ɓacin ranka ba daidai da daƙiƙa ɗaya, Abu khadija kace mun ka yafe mun ko zan samu rahma da rabo mai girma a wajen ubangiji na dan Allah!" ta ƙarasa maganan tana me fashewa da kuka me tsuma zuciya...
Ba kaɗan ba jikin Abu Hanifa yayi sanyi ,baran ma daya ke gasgata kalaman ta kai tsaye daga zuciyar ta suke fito wa...
MUJE ZUWA...💃🏻
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
KUYI HAƘURI NA GANIN CANZA SUNAN LITTAFIN DANAYI. HAKAN YA FARU NE, SA KAMAKON NA SAMU LAMARIN AN TAƁA LITTAFI ME WANNAN SUNAN WATO (MACE TA GARI). KAMAR YADDA LABARIN YA BANBANTA ,HAKA MA SUNAN YA KAMA TA YA BANBANTA. DA FATAR ZAKU FAHIMCE NI. NAGODE.💞
*_Page_*
📖______*5-10*
Khadija ce a zaune tana ta aikin gyaran Kayan Malam Ali, se da ta tabbata ta tsara komai yadda ya kamata, ƙananan abubuwan data san ze nema kuma ta matso dasu kusa. Manyan kaya ta ɗauko masa domin ya saka idan ya fito wanka, kasancewar yau rana ce ta jummu'a. Jin watsin ruwa a ban ɗaki ya tabbatar mata da yana daf da fitowa ,a gurguje ta fara sauko da takalman sa ,duddubawa ta shiga yi ko zata ga wanda ze hau da kayan ,se kuma wata zuciyar tace mata "A'a khadija ,kinsan halin mijin ki ,abunda zakiyi kawai shine ,ki sauko da takalman dika ki goggoge masa ,ala bashi ,idan ya fito shi seya zaɓi wanda yake so"... haka kuwa tayi ,seda ta goge takalman sa dika ,sannan ta koma bakin gado tana jiran fitowar sa koda abun da zata taimaka masa dashi.
Malam Ali ne ya fito daga banɗaki ,yana tsane ruwan jikin shi
"Sannu da fitowa". khadija tayi masa fuskarta ɗauke da fara'a. Bata jira ya amsa ba ,ta nufi lokan da take ajiye masa abubuwan buƙatun sa. Man shafawa ta ɗauko masa ,gundun wando da singileti, ta ajige akan gado. Cikin nutsuwa ta taimaka masa ya shirya.
Kaya ta miƙe masa ya saka ,sannan ta ɗauko wani turare a kwali ,da alama sabon turare ne. Tun tana fesa masa turaren yaso yayi magana ,saboda wani ɗaɗɗaɗan ƙamshi mai shiga zuci daya ji ya ratsa madaidaitan ƙofofin hancin shi. Kallon ta yayi da mamaki yace "khadija!" cikin ladabi fa amsa masa da "na'am Abu Hanifa!"
Yace "Khadija a ina kika samu turaren nan me asirtaccen ƙamshin? idan ban manta kamar shigen turaten nan da maman hafsat ta aiko miki dashi ne lokacin da mijin ta yaje umra! kodai hanci na ne?"
Murmushi sosai khadija ta saki ,kafin ta fara magana cikin tausasawa " wannan gaskiya ne Abu Hanifa. wannan karon kasan ita Abu hafsat ya biya wa taje, shine data tambaye ni me zata kawo mun tsaraba ,nace ta siyo mun wannan turaren dan nasan kana matuqar son ƙamshin turaren".
wani murmushi ne ya ƙwace wa Abu Hanifa. girgixa kai yayi kawai ba tare da yace da ita komai ba, amma daka kalle sa kasan yaji daɗi har a ran sa. Kalmar yabo ne dai baze iya furtawa ba dan kar khadija ta samu sararin ganin gadon baccin shi har raini ya shiga tsakanin su(amma fa a nashi bahagon tunanin kenan)... " ki shirya idan na dawo zamu je muyi mata sannu da zuwa" ya faɗa a taƙaice, kauda zancen yayi ,sannan yace "kawo mun abinci ,karna makara" cikin azama ta haɗo masa tire ,kunun gyad'a ne tayi da fankason alkama ,saboda shine abunda Abu Hanifa yafi so ya karya dashi. Tsiyaya masa kunun tayi a kofi ɗan ,sannan ta zuba fankaso a plate ɗan daidai. ya zauna ze fara ci kenan ,se ga waya an kira shi "toh" shine ƙarshen abunda ya amsawa me wayan dashi kafin ya kashe. tashi yayi ya ɗauko na'urar me ƙwaƙwalwa ,ya kunna ze fara aiki. Da mamaki khadija ke bin Abu hanifa da ido. cikin nuna damuwa tace "Abu Hanifa meya faru? Allah yasa lafiya?"
"A'a lafiya qalau ,wani saƙo ne zan tura" ya bata amsa a taƙaice.
tace "to aikin ze ɗauke ka kamar minti nawa?"
"Kamar mintuna 30 haka"
Nazari khadija tashiga yayi yayin da Abu Hanifa ya duƙufa kan aikin dake gaban shi. tunanin ta shine ,taya aiki ze yu ba abinci a ciki ,sannan tasan yana gamawa baze wani bi takan abincin ba, dan haka ta janyo tiren ,ta matso daf dashi ta ajiye tiren ,banɗaki ta koma ta tsaftace hannayen ta ,duk da cewa khadija mace ce me tsafta ,ta yadda bazaka taɓa ganin jikin ta ko muhallin ta da wani abu me kama da ƙazanta ba. Kofin kunun ta ɗauka takai bakin shi tare da yin bismillah, ɗan ɗagowa yayi ya dube ta ,murmushi tayi se kuma ta marairaice fuska alamar dan allah yasha. Dama kamar yana jiraye ,nan ta shiga bashi kunun ,seda ta tabbata ya shanye ,sannan ta ɗauko plate ɗin abincin ,ta shiba bashi yana ci ,a haka har seda ya ƙoshi. Hamdala tayi wa ubangiji ,sannan ta tattare kayan ta fita dasu. koda ta shigo ta taradda ya gama aikin yana shirin fita, addu'o'i da fatar nasara ta raka shi dasu har bakin ƙofa ,sannan ta koma cikin gida.
Bayan sati ɗaya, Ummu Hafsat ta kawo ziyara gidan ƙanwarta khadija(Ummu Hanifa), sosai taji daɗin zuwan ta ,da murna sosai ta tare ta. Abinci ta dafo ta kawo mata da ruwan sha,
"ummu hanifa ke bazaki ci abincin ba?" Ummu hafsat ta tambayi ƙanwar tata cike da kulawa.
Fuskar khadija ɗauke da annashuwa tace "ta ina zan samu sararin cin abinci ummu hafsat? bayan ban ga dawowar Abu hanifa ba! ummu hafsat tarbiyyar dakuka mun inata ƙoƙarin ganin na ƙarfafi kaina wajen ɗabbaƙa ta daidai gwargwado, sedai bansani ba ko ...."
"a'a ummu hanifa, karki ce komai ,nina sanki farin sani ,sedai bazan yaba miki ba dan kar guiwowin ki suyi sanyi. Akoda yaushe martaba muradun me gidan ki shine cikar martabar ki. duk abunda zaki wa mijin ki kuwa kar kiyi tunanin kin biya shi balle kiyi tunanin samun lambar yabo ,ke koda kwantawa kike mijin ki na taka bayan ki ,wallahi baki biya ba, nasiha na agare ki shine kiji tsoron allah ki kuma da aljannar ki." Ummu hafsat ta gama magana kenan ,se ga Abu hanifa ya dawo ,bakin sa ɗauke da sallama ya shigo.
a tare khadija da ummu hafsat suka amsa da "Wa'alaikumussalam warah matullah"
ƙara faɗaɗa murmushin shi yayi lokacin da yayi arba da ummu hafsat da yayi ,kafin su fara gaisawa khadija ta fara masa sannu da zuwa tare da tambayar sa ya aiki? ,jakar hannun shi ta karɓa takai ɗaki ,sannan ta kawo masa ruwan sanyi. se a lokacin ne ummu hafsat ta samu sukunin gaisawa dashi. Sosai ya nuna jin ɗaɗin zuwan nata, hira suka ɗan taɓa kaɗan ,kafin ta musu sallama....
Gidan ummu Hafsat...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______11-15*
( GIDAN UMMU HAFSAT )
Ummu Hafsat ce zaune tare da yaran ta ,tana musu karatun addini kamar yadda ta saba a kowace rana.
Duban ta ta maida kan babban ƴarta HAFSAT. Tace "Yau wani darasi zamu yi?" Cikin ladabi da girmamawa hafsat tace "Idan ban manta ba ,a lissafi yau laraba , kuma a kowace ranar laraba AT-TAUHID muke insha allah" ummu hafsat tace "jazakillahu khairan" hafsat ta amsa da "Ameen ummi" sannan ta maida duban ta kan sauran yaran ,SAUDAT, ABDUR-RAHMAN ,ABDALLAH da ƙaramar ƙanwar su AISHA, tace "Anty Hafsat tayi daidai?" dikkan yaran suka amsa da "Na'am ummi". tace to masha allah. Darasin mu na yau zeyi magana ne akan
:AMFANIN SUNAYEN ALLAH DA SIFFOFIN SU!
Farko: Lallai Allah ya wajabta ga halittu ,sanin sa mabuwayi da ɗaukaka, kuma idan bayi suka san shi to sai su bauta masa iyakar bauta.
Kamar yadda Allah (S.W.T) yake cewa : FA'ALAM ANNAHU LA ILAHA ILLALLAHU) *"to ka sani yadda sha'anin yake, ba abin bauta wanda ya cancanta a sanshi sai Allah".*
kun ga ambaton yalwar Allah yana wajabta wa bawa kwaɗayin ta. Kamar yadda ambaton azabar Allah ke wajabra wa bawa tsoron saɓa masa. Kuma haka sanin shi kaɗai ke samar da ni'ima kuma yake wajabtar da godiya a gare shi. Abunda ake nufi da bautar Allah da sunayen sa, shine cikakken sanin su , da fahimtar ma'anar su da kuma aiki dasu. Daga cikin sunaye da siffofin Allah da ake yabawa bawa akan siffantuwa dasu akwai : AL-ILMU, ARRAHMA, AL'ADLU. haka kuma akwai waƴanda za'a zargi bawa idan ya siffantu dasu ,kamar: AL-ILAHIYA (shine ya zama abun bauta) ko ATTAJABBUR Ko ATTAKABBUR (girma da ganin isa). Haka bawa ya siffantu da wasu siffofin har ma a gode masa akan su, kuma ana umurtarsa da haka; kamar su sifofin: Bauta, buƙatuwa ga Allah tare da nuna masa hakan, da ƙanƙantar da kai ,roƙo da sauran su. Waɗannan haramun ne Allah ya siffanta da su. kuma lallai, mafi soyuwan halitta ga Allah shi ne wanda ya siffantu da suffofin da yake so, wanda kuma yafi ƙi a cikin su shine wanda ya siffantu da siffofin daya ke ƙyamar su (kuma yake ƙi)."
Fatar kun fahimci inda darasin namu yasa kai? kar muyi ta tafiya ba'a gane ba, saboda ginshiƙin karatu bawai zurarawa bane a'ah fahimta ake so, dan haka zamu tsaya anan kowa yayi nazari ,idan akwai me tambaya se mu haɗu a darasi na gaba ,saboda ƙaratowar lokacin sallahn ZUHR".
"SAKALLAHU BI KHAIR WA SAKALLAHU BIL JANNAH UMMI, WA FATAHALLAHU ALAIKI", Shine abun da yaran suka furta a tare, "Ameen wa lakum" shine amsar da ummu hafsat ta basu cikin ƙayataccen murmushin ta na manya. ita ta fara tashi ,kafin yaran suka tashi ɗaya bayan ɗaya.
Da daddare dikkan yaran ta suka shigo mata seda safe kamar yadda suka saba. Autan ta aisha me shekara biyar tace "ummi Abban mu be dawo ba?" murmushin manya ummu hafsat tayi tare da janyo Aisha a jikin ta tace "Abban ku be dawo ba Aisha ,se zuwa ɗan anjima kaɗan ,me yuwa aiki ne yasha gaban shi" Aisha tace "Allah ya dawo mana dashi lafiya" kowa ya amsa da "ameen" sannan suka fita tare da ja mata ƙofar ɗakin. Awa ɗaya bayan tafiyar su ,ta miƙe tare da zura hijabi. Ɗakin su Hafsat ta fara shiga da yake kusa da nata ɗakin ,ta tabbatar sun kwanta ,sannan ta zagaya bayan ɗakin ta Zuwa ɗakin su Abdur-ralman, anan ma sun kwanta ,addu'a ta totto fa musu sannan taja musu ɗakin.
Dare yayi liƙis ,ummu hafsat ce kwance kan gado ,tana jiran dawowar mijin nata , tunani ne ya cika mata zuciya ,ganin baze fish-she taba yasa ta tashi ta ɗauro alwala ta hau kan dadduma, nafila tayi raka'a biyu sannan ta zauna tana jero addu'o'i. misalin ƙarfe biyu da rabi na dare ,se ga mijin ta ya dawo liƙis kamar wanda aka koro ,se tanɓele yake alamar a buge yake , ISTI'AZA tayi cikin tsanin firgici ,tashi tayi a guje ta nufo shi tana hawaye tare da tambayar sa meya same sa cikin tsananin tashin hankali da kiɗimewa, bangaje ta yayi iya ƙarfin sa , ta faɗi ƙasa akayi rashin sa'a kan ta ya bugi gefen gado kan kace me se ga jini, tasan ko ba'a faɗa ba tabbas musiba ya same ta ,idan da sabo kuma yaci aci ta saba ,dan sama da shekara ashirin tana tare da Abu hafsat ,amma duk daren allah idan ze shigo mata a buge yake shigowa ,yayi amai ta wanke ,kai ze ma iya neman ta zuwa shimfiɗa kuma ta amsa kiran sa babu shamaki ,sedai akoda yaushe tana kai kukan ta wajen allah ,ba kuma ƙarar shi take kaiwa gun Allah ba a'ah ,nema masa shiriya take.
duban sa tayi a tausashe tace "Abu hafsat bazan gajiye wajen nema maka shiriyar allah da yafiyar saba, nasan allah be manta damu ba". To dan me zata yi wannan maganar nan ya fara halin , dukan ta ya shiga yi ba girma ba azziki, sedai hawaye amma ba zata iya ihun ba dan kar ƴaƴan ta suji har su an kara da halin da take ciki...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______16-20*
Washe gari tun kiran sallan farko ummu hafsat ta farka, da zama da miƙe jiki ba ƙwari ta bufi banɗaki, ruwan zafi ta haɗa ta gasa jikin ta ,tare da ɗauro alwallah. Tana fitowa ta buɗe lokon gado ta ɓalli magunguna na zazzaɓi dana ciwon jiki ta haɗa tasha, sannan ta zura doguwar riga da dogon hijabi ,raka'atanul fijr ta da gabatar wa ,sannan ta tashi ta tada Abu hafsat. wani dogon miƙa yayi tare da yin salati. "Abu hafsat ka tashi lokacin sallah ya ƙarato" ummu hafsat ta faɗa cikin ladabi. "Kai ummu hafsat ,ji fa yadda kika tashe ni ina bacci na me daɗi" Abu hafsat ya faɗa kamar komai be faru ba. murmushi sosai ta sakar masa tare da cewa "kayi haƙuri ka tashi mijina ,idan ba wajabci na allah da manzon saba ba banga dalilin da zesa hannu na yayi kuskuren tada ka daga bacci ba". ta ƙarasa maganan tare da shafo gefen fuskar shi ,alamar rarrashi. murmushin ya maida mata sannan ya miƙe a kasale ya shiga banɗaki. bata bar wajen ba seda ta tabbatar ya shiga banɗakin sannan ta koma kan dadduma taci gaba da jero addu'o'i ,tana nan zaune har Abu hafsat ya fito ,a nutse ta tashi ta buɗe loka ta zaro masa farar jallabiyya da hula ,seda ta feshe jallabiyan da tararuka masu ƙamshin gaske sannan ta miƙa masa ,hannu yasa ya karɓa cikin jin daɗi yana me saka mata albarka "ameen" ta amsa shi tare da sakar masa kyaky-kyawan murmushin ta mai ƙarawa fuskar ta kwarjini da haiba... A tare suka fito ita dashi ,ɗakin su Abdur-rahman suka nufa ,tun kafin su ƙarasa ,yaran suka fito alamar tun ɗazu suka shirya , mahaifin nasu kawai suke jira. Addu'an dawowa lafiya ummu hafsat tayi musu tare da yi musu rakiya har bakin gate sannan ta koma ciki. ɗakin su hafsat ta wuce ,dan ta tabbatar ko sun tashi ,nan ma ido biyu ta same su ko wacce akan dadduma hadda Aisha. ba tare da tace musu komai ba ,taja ƙofar ɗakin ta koma nata ɗakin dan gabatar da sallan asuba.
Misalin shida na safe su Abdur-rahman suka dawo daga masallaci ,kai tsaye ɗakin mahaifiyar tasu suka nufa ,seda suka ƙwanƙwasa ta basu izinin shig ,sannan suka shiba. har ƙasa suka durƙusa suka gaishe ta ,ta amsa fuska a sake tare da saka musu albarka ,har zasu miƙe ta katse su da cewa "Abdul bana faɗa muku ba'a durƙusa wa wani bawa ba, allah kaɗai ake ƙanƙantar dakai a wajen sa? saboda dikkan gaɓɓan sallah allah kawai ake bautawa dasu ,yin hakan ga wanin allah kuwa makaruhi ne. ko kun manta ne?" cikin ladabi Abdur-rahman yace "kiyi haƙuri ummi mun manta ne ,saboda munji a karatun da kike mana kince ,tsakanin ƴaƴa da iyayen su IHSANI ne da BIRRA (wato kyautatawa da biyayya) ,to a tunani na baya cikin biyayya ɗa ya gaida mahaifansa a tsaye".
jinjina kai ummu hafsat tayi tare da cewa "Haƙiƙa kayi gaskiya ,zaku iya gurfana wa dan nuna ɗa'a ga iyayen ku ,amma banda kai guiwa ƙasa ,saboda gaɓa ce tayi wa Allah bauta. Allah yasa kun fahimce ni?" "mun fahimta Ummi" suka bata amsa. Sun zo fita sega su hafsat sun shigo ,gaishe da hafsat duka yaran suka yi a matsayin biyayya ga babban yayar su da uwar su ta hore su dashi. fuske a sake hafsat ta amsa su tare da tambayan yadda suka kwana. Ɗaya bayan ɗaya yaran suka shiga gaisawa da junan su, Aisha ce ta kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ,tace " to ni na gaida kowa ,ni kuma waye ze gaida ni?" ta faɗa tare da ɗaure fuska, dariya yadda tayi yaba ma kowa ,sannan hafsat ta janyo ta tare da ce mata " Auta ai ke nice zan gaida ki. Ina kwana anty aisha ?" lafiya qalau anty hafsat" aisha ta amsa tare da fashewa da dariya ,cikin sigar yarin ta ta gudu bayan mamanta tana faɗin " yeeh nawa antu hafsat wayo ,nice fa ƙarama ,kuma ƙarami ne ya kamata ya gaida babba" dikkan su dariya suka sa kafin su hafsaf suka ƙaraso suka gaida iyayen nasu cikin girmamawa.
A Tare dikkan yaran suka fito zuwa babban parlourn gidan ,inda suka saba bitar alqur'ani a safiyar ko wacce rana daga shida zuwa bakwai na safe.
ummu hafsat ta maida duban ta ga Abu hafsat , da yake ta faman jinjina kai ,a ran sa yake ƙara godewa allah daya bashi MACE TA GARI kamar ummu hafsat. gaishe shi tayi cike da girmamawa ,ya amsa ta fuske a sake. Har zata miƙe ,se kuma ta koma ta zauna. tare da cewa "Abu hafsat da alama kamar akwai magana a bakin ka? dan allah kar kayi ƙasa a guiwa wajen faɗamin abun da ke ranka ,idan wanda na maka lefi ne zan baka haƙuri" murmushin takaici Abu hafsat yayi tare da cewa " ummu hafsat na ɗauka zaki mun ƙora fi ne akan abunda ya faru jiya? meyasa bakya ganin aibu na? sama da shekaru ashirin ina aikata abu ɗaya na kasa canza kaina ,nasan kina haƙuri dani, kin aure ni badan kina sona ba ,ya kamata in kyautata miki amma"... murmushi ummu hafsat tare da cewa "Haba Abu hafsat ,me zesa ni kiwu in ƙyamace ka? manzon allah s.a.w yace " idan muka ga ana aikata saɓon sallah ,muyi ƙoƙarin kawar dashi da hannayen mu ,ko da harshen mu ,ko kuma a zuciya" , nakan yi amfani da harshe ne wajen nema maka tsari da miyagun ayyuka a wajen allah, kai dani bamu isa mu canza ka ba se allah ne kaɗai ya isa da wannan ,to menene na ganin aibu kuma? bayan
MASU HIKIMA SUN CE
Wanda ya san munin aibi bai sha'awar ganinsa ko a jikin wani ne, in ka ga wani na bincikar aibin wasu to dace aka yi da abinda yake da shi, kai ma ka yi a hankali."
Saboda haka mubar wannan zancen anan dan allah ,ka tashi muje nasan yara nacan na jiran mu a fara bita".
wani nannauyan ajiyan zuciya Abu hafsat ya sauka , A sanyaye ya miƙe kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki ,ya nufi ƙofar fita ,da sauri ummu hafsat ta ƙarasa ta buɗe masa ƙofar ,sannan ta rufa masa baya....
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______21-25*
GIDAN UMMU AHMAD
kofin ruwan sanyi ummu Ahmad ta kawo wa Abul Ahmad cike da ladabi ,zuƙunnawan da zata yi ta aje masa a gaban sa ,bai jira ta ƙara sa ba ,ya haɗa da ita da kofin ruwan yayi watsi dasu " baza'a sha ruwan ba ,baza'a sha ba nace " Abul Ahmad yake maimaitawa a hasale "wayyo Allah na "ummu Ahmad ta faɗa cikin tsananin gigita ,tana zaro ido ,da gudu tayo kan shi ,a tunani na ko cikumo shi zata yi da koka wa ,se kuma naga saɓanin haka. Yarfe hannu ta shiga yi tare da nuna tsantsar tashin hankalin ta a fili, rirriƙe shi tashiga yi ,tana bashi baki tare da nuna masa jinin dake fita aɗan yatsan shi babba na ƙafa sakamakon shuri da yayi da kofin glass ,ashe glass ɗin ya yanke shi ba tare da ya ankara ba, ba shiri ya zauna tare da riƙe ƙafan ,se a lokacin yake jin raɗaɗin zafin raunin na ratsa lugu da saƙo na jijiyoyin jikin shi. waige waige ta shiga yi ,tana so taga ta hanyar da zata taimaka wa mijin nata, iya hangen ta bata hango komai ba ,gashi bata so ta tashi a kan shi dan gudun ko kafin ta dawo wani abun ze iya samun shi, batayi wata-wata ba ta ciro ɗankwalin kanta 'kerrrrrrr' kake ji ta yaga shi ,ɗaukar ƙafar shi tayi ta ɗora akan cinainanta ,sannan takai bakin ta daidai inda raunin yake ta shiga hura masa iskan bakin ta 'fuuuuuuh' ,Abul Ahmad daya jinginar da kanshi a jikin kujera dan tsabar azaba ,sosai yake jin daɗin abun da take masa ,wani daɗi ne ke ratsa shi tun daga ƙwaƙwalwa har tafin ƙafa, seda ta tabbata ya rage jin raɗaɗin sannan ta samu kwanciyan hankalin ɗaure masa yatsan da ƙyallen ɗankwalin ta . Kuka take sosai tana faɗin " dan allah Abul Ahmad kayi haƙuri ka yafe mun ,wallahi duk lefi na ne ,nice nayi sanadiyyar komai ,dan allah kace ka yafe mun ko zan samu sassaucin abunda nake ji a raina. Me zan gayawa allah idan na mutu a wannan yanayin? garin kuskure na ,nayi sanadiyyar jiwa mijina rauni nida kaina" kuka take sosai ,hannayen shi take ƙoƙarin kamowa ya fincike ya shiga ɗaki abun shi ,yabar ta nan zaune dirshasha. kuka taci gab dashi a lokaci ɗaya ta ɗaga hannayen ta sama tana faɗin " Allah n tuba k yafe mun ,Allah kaji tausayi na karka kama ni da wannan laifin"... haka taci gaba da maimaitawa ,har zuwa lokacin da Abul Ahmad ya fito daga ɗaki ,a tunanin ta koya haƙura ya yafe mata ne shiyasa ta nufo shi da hanzarin ta ,hadda ɗan murmushi shimfiɗe akan kyaky-kyawar fuskar ta.
Be jira ta ƙaraso gare shiba, ya wani irin hamɓare ta ya fice abun shi. tashi tayi ta ɗauko tsintsiya da makwashi ,ta tatara glass ɗin da ya fashe ,a lokaci ɗaya ta goge ruwan daya zube a ƙasan wajen, sannan ta samu gu ta zauna.
Jim kaɗan se gashi ya shigo tare da wata irin santaleliyar budurwa, kai da ka kalli yarinyar kasan irin ƴan barikin nan nan shu'umai. Se wani karairaya take tana fari da ido ,wani kallon banza ta watsa wa ummu Ahmad ,ita kuma ta mayar mata da murmushi mai sosa ran maƙiya, shi kuwa gogan ko kallon banza bata ishe shiba ,ciki suka shiga shida karuwar shi ,suna shiga ta kalle shi tace "baby dama kana da wannan me zafin shine har mata ke burge ka a waje? " Abul Ahmad yace "lallai baki da hankali honey ,yanzu waccan shashashar matar ce me zafi". " eh mana, nidai wallahi banga makusa a tattare da ita ba" karuwar abul ahmad ya bashi amsa sannan ta ɗora da "Anyway! yanzu dai abar zancen ,dan ita tayi sake ruwa yaci ɗan kada. yanzu bari in shiga in watsa ruwa. kash baby na manta da kayan bacci na! yanzu ya za'ayi? " ta faɗa cikin siga me ɗauke hankalin me sauraron ta ,abul ahmad yace "haba wannan ai baze zama damuwa ba ,idan kin fito ga loka nan ki buɗe akwai kayan baccin matata kala-kala a ciki se ki zaɓa wanda ya miki ki saka" tace "Allah ko" yace "eh mana"... haka kuwa akayi ,tayi kamar yadda yace ,wata haɗaɗɗiyar night gown ta saka ,Abul ahmad yace "wowww! fantastic ,kinga kuwa yadda rigar tayi fitting ɗinki?" "Allah ko baby" ta bashi amsa tana wani juyi a gaban madubi, rungume yayi ta baya tace "baby inason rigar nan yamun kyau sosai" "Ah haba keda abun ki har se kin tambaya? karjiji komai kije dashi na baki" Abul ahmad ya faɗa. Cikin jin daɗi ta juyo ta rungume shi ,kissing ɗin ta ya shiga yi tana wani lashe lungu da saƙo na jikin ta ....dakatar dashi tayi, ɗan ɓata fuska yayi tare da cewa "honey miye haka? meyasa zaki rage mun jin daɗi " shafa ciki ta shiga yi alamar yunwa ,yace "wannan ba matsala bane bari insa ummu ahmad ta dafa miki ko?" har ze fita ta riƙo shi "a'ah baby ni da kaina zan dafa saboda bana son ƙazanta" murmushi ya sakar mata ,a ranshi yake cewa "tsaftar banza matata ta fiki banza" a fili kuma yace "kar kiji komai ,ki saki jikin ki kiyi yadda kike so a gidan nan ,ai komai nawa naki ne kamar yadda ni kaina naki ne" ... daɗi sosai taji ,sannan ta fita ta nufi kitchen ba kunya ba tsoron allah, kinzo har cikin gidan mace tare da mijin ta ,kin saka kayan baccin da take sakawa mijinta na sunnah ,sannan kin fito kina taku ɗaiɗaya a tunanin ki kin burge ne, kai jama’a!!!
A parlour ta taradda ummu ahmad zaune tana duba wani littafi na laraɓci me suna 'KAIFA TASLI NA ILA ƘALBI ZAUJI KI' (Yaya zaki sace zuciyar mijin ki), littafi ne mai cike da darussa irin daban-daban na yadda zaki sarrafa gidan auren ki. Murmushi ummu ahmad tayi lokacin data karanta gaɓar da malam ya rubuta "HAƘURI AKAN CUTAR WA"... sosai taje jin daɗin littafin, ta gaban ummu ahmad karuwar abul ahmad tabi ta wuce ,ashe ma tasan ko ina a gidan ,ko da yake yaci ace ta san komai na gidan tunda wannan bashi bane karo na farko data fara zuwa gidan. ko ɗaga ido ummu ahmad batayi ta kalle ta ba balle tasan mutum ya gitta ,sosai hakan ya ƙonawa feena rai(sunan karuwar kenan), tsaye take a kitchen ta rasa inda kayan masarufin yake ,ta duba iya dubawan ta ,bata ga kayan miya ba ,mangyaɗa ma babu ,balle ayi zancen kayan maggi. wani dogon tsuki taja ,sannan ta fito tana tambayar ummu ahmad cikin isa da gadara "ke! " ummu ahmad tayi kamar bata ji ba "ke wai bakya jin ina miki magana ne ko dutse ce ke?" nan ma ummu ahmad bata tanka taba ,feena taci gaba da cewa "dallah malama ni ba wani abun azzikin bane ya kawo ni wajen ki ,tambayar ki zanyi kayan masarufai na girki ,ko wancan kwalin da kike iƙirari miji be siya ya ajiye bane? A zafafe ummu ahmad ta ɗago ta mata wani kallon ban fahimci me kike cewa bane? tace "eh wancan bahagon mijin naki ,ko iya kawo mata ya ƙware wa be gwanance a iya kawo kayan abinci ba?" wani iska me zafi ummu ahmad ta furzar ,a lokaci ɗaya idanuwan fa suka kaɗe suka yi jawur kamar wacce aka watsawa wuta a ciki. kan kace me ta tsinke feena da wasu gigitattun maruka ,wanda ya sanya ta ganin taurari, ihu feena zata kwaɗa ,ummu ahmad ta katse ta "Shshshs! kar ki so kimun hayaniya agidan mijina ,zaki iya taka ni ki wuce salun alun ,zan ɗauki duk wani cin kashin ki ,amma akan mijina wacce ta haife sama ban haɗa ta dashi ba ,ki gode allah da sanayyar dake tsakanin ki da miji na ya iya ceton ki ayau, wallahi tallahi dana nuna miki kuskuren ki na kiran miji na da KWALI da kika yi ,da bazan barki ki ƙara taku ɗaya ba ba tare da na zubar miki da haƙora na zuba miki su a tafin hannu ba. Miji na yafi ƙarfin wulaƙanci koda kuwa agun mahaifiya ta ne ,wacce banda kamar ta a duniya ,to ki kiyaye ,daga yau se yau duk randa kika zo gidan nan ki tsaya iya abunda y kawo ki ,amma kar harshen ki ya ƴara kuskuren faɗan wani kalami mara daɗi akan miji na ,idan kuwa baki jibi ,tabbas zaki yi dana sanin sanin sunan miji na da kika yi ,daraja ɗaya kike ci dahar kike shigowa gida na ki fita da ƙafafuwan ki biyu ban karya kiba ,ni ɗin na kasance me son duk abunda miji na yake so, nakan kuma yi yaƙi zuciya ta idan ta ayyana ƙyamar muradun mijina ..."
iya kiɗima feena ta kiɗime ,dan kuwa daskarewa tayi ta kasa koda dogon numfashi ,sosai take ganin kwarjini da zallar rashin tsoro a cikin idanuwan ummu ahmad. Wasu mukullai ummu ahmad ta ɗauko a gefen ta ta janyo hannun feena ta ɗanƙa mata ,tare da cewa "kiyi haƙuri ,haka nake indai akan miji na ne ,zaka iya mun koma menene in ɗauka, amma shi ɗin aljannah ta ne kuma shine duniya ta ,kina tunanin mutum zeyi wasa da duniyar sane bayan a cikin ta ne mutum yake ci yasha ,ya kuma samu abunda yake so?" girgiza kai feena tayi ,ummu ahmad ta sakar mata murmushi wanda ya ƴara fito da sirrin dake shimfiɗe akan madaidaicin fuskar ta.sannan tace "to shi ɗin yafi mun duniya da abunda ke cikin ta sau ba adadi" makulli ta nuna mata tace "wannan makullin store ne ,ki duba duk wani abunda kike buƙata zaki samu aciki insha Allah" "na! nagode" shine abunda feena ta iya furtawa cikin hanzari ta karɓi makullin ta koma kitchen. indomie kawai ta iya dafawa ,saboda a tsorace take, ta jima da gama wa amma ta kasa fitowa ,idan ta leƙo taga ummu ahmad seta koma ,da ummu ahmad ta fahimci hakan ,sai ta tattara ƴan komatsan ta ta wuce ɗayan ɗakin daba kowa ,dan ta bama feena damar fitowa...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______26-30*
Ranar a ɗari-ɗari feena ta kwana a gidan ummu ahmad. a ranta take ayyana irin kwarjini na ummu Ahmad da jarumtar ta.
Da asuba an tashi da sanyi sosai, daga feena har Abul Ahmad sun rasa yadda zasu yi. Abul ahmad yace wa feena taje ta ɗora musu ruwan zafi a kitchen, amma sam feena ta kasa ko dogon motsi ,tambayar ta yayi ko meyasa? ta nuna masa ai ba komai kawai ta gajiya ne sosai ,shi yaje ya ɗora. Ba dan yaso ba haka ya tashi ta zura jallabiya ya nufi ƙofar fita, buɗe ƙofar ɗakin daze yi yaci karo da flask na ruwan zafi , da kulolin abinci, saura kaɗan yayi tuntuɓe dasu, ko be tambaya ba yasan aikin ummu Ahmad ne ,dan abunda yafi ma wannan zata iya ,beyi wata wata ba ,ya sungumi flask ɗin ruwan zafin da kulolin, ciki ya koma tare da banko ƙofar ɗakin. Kallon mamaki feena ke bin shi dashi ,tambaya ne ƙarara akan fuskar ta " A ina ka samo waƴannan daga fitar ka yanzu-yanzu kuma?" feena ta tambaya. Abul ahmad yace "A ƙofar ɗaki naci karo dasu". " to waye ya ajiye su a wajen?" feena ta tambaya ,Abul ahmad yace "wa kika san ze ajiye kuwa? mu nawa muka kwana a gidan? inace mu uku ne?" jiki a saɓule feena ta miƙe ,flask ɗin ruwan zafin ta ƙarɓa ta nufi toilet dashi ,seda tayi wanka ,sannan da ɗoro alwala ,tana fitowa ba bata bi takan komai ba ,doguwar riga da hijabi kawai ta zura ,ta kabbara sallah. Mamakin zaune ne ya kashe Abul ahmad, tun da yake da feena ,yau ne rana ta farko daya taɓa ganin ta tashi da asuba tayi sallah. Tambayar kan shi yake "to wani abu ne wannan dayayi sauƙin canza feena haka cikin sauƙi? kodai wahayi aka yi mata? Anya ma bata sha wani abu kuwa jiya ba? ko da yake duk iskancin feena bata taɓa gwada shaye-shaye ba" yaba kan shi amsa. Ganin wannan ba zata fish-she shiba ,yasa shima ya tashi ya nufi banɗakin ,tsarkake jikin shi ya fara yi ,sannan yayi alwalla ya fito, har lokacin feena na kan dadduma ,jallabiya ya saka ,sannan ya shimfiɗa wata sallayar ya tada sallah. bayan sun gama ,ya janyo kulolin abincin ya zuba musu, daƙyar feena taɗan tsats-tsakura ,dan gaba ɗaya jin ta take kamar a ɗaɗɗaure. Ranar dai basu yi isar baka isan da suka saba ba, na kaiwa azahar basu buɗe ƙofa ba ,da wuri feena ta gama shirin ta ,tace wa Abul ahmad ya tashi ya kaita ,shidai da ido kawai yake bin ta, ba musu ya tashi suka fita. Tun daga ranar feena bata ƙara gigin biyo Abul ahmad gida ba ,sedai idan tana buƙatar shi ,ta masa waya suyi mahaɗa a wani wajen daban....
*****************
Bikin Zainab ya rage saura kwana uku, dan haka dikkan yayyin ta mata suka hallara a gidan nasu. UMMU MUS'AB itace babban yayar su ,wacce hatta fara manyanta, dan aƙalla zata yi kimanin shekaru Hamsin hadda ɗori a duniya ,sedai Allah da ikon shi ,bai taɓa azurta ta da samun haihuwa ba. Se UMMU HAFSAT itace ta biyu ,UMMU JA'AFAR itace ta ukkun su, UMMU HABIBAT itace ta Haɗu ,UMMU AHMAD kuma ta biyar ,UMMU HANIFA itace ta shidan su ,Se Autar su da suka zo bikin ta ZAINAB ,wacce suke wa Alkunya da UMMU SADIQ... Gashi dikkan su sun zo da ƴaƴayen su ,saboda a sada zumunci.
Sosai ko waccen su ke murnar ganin ƴar uwar tata ,baran ma waƴanda ba'a jahar na Kaduna suke aure ba, murna a gurin su ,wayyo Allah ina masaki su tsoma kan su... Bayan isha'i misalin ƙarfe takwas da rabi na dare ,dikkan su suka hallara a babban parlour-n UMMI MARYAM(sunan da suke kiran mahaifiyar tasu dashi kenan. UMMI MARYAM suna ne na alkunya da yabi HAJIYA RABI'ATU tun ƴan ma tantakan ta, har zuwa lokacin da allah ya azurta ta da haihuwan MARYAM (wato UMMU MUS'AB)... wannan kenan a taƙaice.
Hira suke ta zantawa gwanin ban sha'awa na yaushe gamo. bayan sun kammala cin abincin dare ,ummu mus'ab ta sallami sauran ƙananan yaran ,ya rage daga su su bakwan su ,se manyan ƴaƴayen su mata masu aure, se kuma waƴanda aka saka wa ranar aure kamar su hafsat ,da dai sauran su. Ummu mus'ab macece data ansa sunan ta mace ta ko wani fanni. gwana ce kuma ƙwararriya wajen girke girke da sarrafa kayan mata kayan mata, duk da cewa kuwa ta soma manyanta amma baiwa da hikayoyin da allah ya mata babu ɗaya da yayi ƙasa ,se ma hauhawa data ke daɗa yi. Tunda sauran ƴan uwan ta suka ga ta sallami yaran su dake wajen ,suka san lallai yau zasu kwashi garaɓa sa ,dan duk lokacin da zasu haɗu kamar haka a gida ,takan musu daura ta ƙarawa juna sani. Ummu mus'ab macece da bata yadda koda daƙiƙa ɗaya ya tafi a banza ba ,ba tare da ta amfana ko wani ya amfana da ita ba. Gyaran murya tayi tare da yi musu sallama ,sannan tace "ina amarya?" ,zainab tace "gani ummu mus'ab" tace "to matso kusa dan yau ke nake da buƙatar gani a kusa dani" ,dariya dikkan su suka saka ,banda zainab data tashi a kunya ce ta matsa kusa da ummu mus'ab ,ta samu guri ta zauna a ƙasa kusa dasu hafsat.... UMMU MUS'AB TA SOMA BASU SHARHI KAMAR HAKA...
"_yar'uwa wannan wani hadin ne na musamman in kina yin sa ya Bi jikinki to ni'imar da Zaki samu ba karama bace._
zuma
citta
tufah
ya'yan kankana
_da farko ki samu citta ya'yan kankana sai ki daka su yayi laushi, daga nan sai ki samu tufah (apple) kamar biyu ko uku sai ki markada ta, sai ki samu zuma ki mai kyau sai ki zuba a ciki tare da Rabin karamin cokali na garin citta, babban cokali na garin ya'yan kankana, sai ki zuba ki juya su sai a rikka shan babban cokali uku safe da yamma akoda yaushe._
*_Yadda Ake Hadin Dabino_*
Wannan yana da matukar mahimmanci ga ya mace domin yana gyara ma mata jiki kuma yana saukar mata da ni'ima ko da ta kasance gabanta a bushe yake zai taimaka mata.
Zaki nemi wadannan abubuwan kamar haka;
* Dabino
* Zuma
* Tatacciyar madara
* Kanunfari
*Bayani;* Ki nika kanunfari ko kidaka ya daku sosai, sannan ki zuba busasshen dabino ki cigaba da dakawa sai ya daku sosai sannan ki samu tatacciyar madarar ki zuba cokali uku na wannan garin dabino da kanunfari a ciki sai ki sha.
Ki dunga sha lokaci lokaci zaki sha mamaki da yardan Allah.
*_Hanyar Da Mace Zatabi Don Kawar Da Bushewan Gaba_*
Bai kamata ace mace tana da busheshen gaba kuma ta zauna haka nan babu wani kokari da tayi don kawar da wannan matsalan, domin matsala ne mai girma yana iya hana ma'aurata jin dadin zamantakewar aure.
Uwar gida ki dan gwada wannan in sha Allah za a sami nasara wajen kawar da wannan matsalan.
Zaki nemi wadannan abubuwan kamar haka;
* Garin Aya
* Garin Kurna
* Garin Dabino
* Garin Habbatus sauda
*Bayani:* Zaki dukkan wa'innan garin ki hada su guri guda ki rinka diba kina sawa a madaran shanu lafiyayya (Fresh Milk) kina sha safe da yamma, har zuwa lokacin da kike ganin kin ga yayi yadda ki ke so.
In sha Allah za aga canji a lokacin saduwar aure, ke tunda ga wasanin zaki dunga jin maski a jikin ki.
*DABINO DA KANUNFARI*
_Ki bare dabino yar uwa ta ki samu kanunfari sai ki jika su a gora ko roba ki bari su jiku sosai sai ki dinga sha safe da yamma wannan hadi yana saukar da ni'ima sosai_.
_*ZAKI HADA DA KANKI*_
Ki dafa kanunfari idan ya dauko nuna saiki
zuba zuma
a ciki, bayan kin sauke ki sami garin ridi ki
zuba ki
hada nonon shanu mara tsami ki gauraya
idan yayi
sanyi ki sha......
_ki sami kanunfari da dabino ki jika sai sun_
tsima saiki
rinka diban ruwan kinasa zuma da madara
kina sha,
duk abinda aka ji na yafe kar a fada min.........
*GYARA*
ta sami sassaken baure ta dafashi da
kanumfari citta
da lipton ta hada ta tafada sai ta tace ta sa a
fridge
tarim ga sha tsimine yana da kyau
sosai
HAƊI NA MUSAMMAN
,zaki samu garin zogale ne ki jika ki ringa sha
sau biyu
a rana. Kina tashi daga bacci kafin kici komai
ki sha
ruwan zogale,sai kuma in zaki kwanta Ya
zamo na
karshe.
Sai kuma in Kina infection ki ringa seat bath
dashi
GA WANI:
Ki daka aya ki tankade sai ki samu
bushasshen dabino
shima ki dake shi, hade da mazarkwaila ki
hade su da
garin ayar. Ki sami nono ki rinka damawa
kina sha.
*KANUMFARI*
Kanunfari kaɗai kika riƙe zaki samu canji a aurenki ƴar'uwa. Kanunfari yana da powers da shi kaɗai zai iya miki maganin abubuwa da yawa na matsalolin da ya shafi jikinki. Ba wai a shayi ko girki bane kaɗai yake da amfani ba. Mai wuyan shine bama iya jure aiki da abu kullum kuma bamu san hanyoyin sarrafashi ya zama effective ba.
Kadan daga cikin amfanoninsa:
1. Yana hana warin gaba. yana sanya ƙamshin gaba, yana kuma matsesa.
2. Yana wanko ciwukan da suke tattare da wurin, yana ɗauke da antibacterial properties da suke kashe vaginal infections.
3. Yana saukar da diabetes, yana hana samuwar cholera. Yana bayar da ƙarfin ƙashi. Sannan yana boosting immune system.
4. Yana rage zafin ciwo da kumburi. Da kuma ciwon kai mai tsanani.
5. Yana taimakawa wurin samun kuzarin sex da saukar ni'ima sosai.
6. Yana rage warin baki yana iya curing gembon ciki (mouth ulcer). Yana warkar da ciwon haƙori.
Zaki iya hadiyan kanunfari ko kuma ko ki tauna shi. Sannan zaki iya diban shi ki zuba a ruwa ya kwana ki rinƙa sha kofi ɗaya da daddare kafin ki kwanta ko da safe kafin ki ci komai. Yana cleansing jiki da matse farji da kashe cutuka fiye da tsammaninki. Yana ƙara miki dadi most of maganin mata dashi a ciki.
Sannan ga mai fama da diabetes ko mai son rage kiba su jika shi tare da cinnamon (girfa) su rinƙa sha.
Yanda nake nawa haďin da nake sha ko da safe ko yamma kullum:
Ina samun ruwa a gora sai na zuba kanunfari, na zuba busashshen na'a na'a (mint), na saka girfa (cinnamon) sai na watsa Habhan ko Habbahan (cardamom). Ƴar'uwa to wani lokacin sai ina yi ina yin tsallaken ranaku. Saboda zai ƙara miki ni'ima sosai, sha'awa, ga kashe cutuka marasa adadi har da asthma yana ragewa. In kina Numfashi zaki ji iskan numfashinki na da daɗi. Haka nan bake ba warin gaba sai dai kiji wata na ƙorafi.
Mai wuyan shine ki san sirrikan sarrafa kanunfari da abubuwan da ake sarrafata. Ba wai yin tsugunon hayaƙinta tare da bagaruwa bane kaɗai amfaninta a'a akwai wasu wallahi da yawa da masu baku magani kaɗai suka sanshi. Wannan kuma ya rage ga mutum ya je ya nemo sirrikan kama mijinsa da shi ya riƙe...
Taci gaba da cewa "ba wannan ba kaɗai, ya kamata Mu zama masu girmama damuwar juna, kuma muyi kokari mu rinqa banbacewa tsakanin soyayya da sha’awa shima zai bamu daman fuskantar abokan zamanmu don fadakar da juna muhimmanci soyayya da tausayi a zaman aurenmu, a hankali zaki ce ni kuwa sai inga kaman kafi damuwa da lamarina a lokacin da kake neman wata biyan buqatarka? Zai ji kunya
Mu dasa soyayya da zama na Amana da tausayi da jin qanmu a wurin mazajenmu, mu nuna masu ba wannan bane kadai darajanmu da martabarmu wurinsu...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______31-35*
"Ummu mus'ab bata gajiya ba ,taci gaba kamar haka
*TSUMIN YAR GATA*
Dabino
Mazankwaila
Sassaqin kankana
Kanun fari
Zaki samu dabinon ki mai kyau ki wanke ki cire kwallayan saiki jiqashi idn ya jihu saiki tace ruwan didigar dabinon kuma ki zubata a blender ki markada saiki samu sassaqin kankanar ki ki wanke ki sa a tukunya ki zuba ruwa saiki dako wancen ruwan dabino da kk tace a farko shima ki juye a kai ki barshi yayi ta dahuwa idn ya dahu saiki sauke ki cire ssassaqin ki kawo wannan markadadan dabinon ki zuba a kan ruwan ki kawo kanun fari ki zuba ki daka mazankwailarki ki juye a ciki saiki maida kan wuta yaci gaba da dahuwa har yayi kauri saiki sauke ki zuba a jarkoki ki rinqa sha sau uku a rana..uhmm
*HADIN KAZA*
Kaza
Saiwar Malmo
Maggi
Zaki samu kazarki mai kyau ki gyarata ki wanketa amma karki yankan ta kawai ki cire kayan cikin ki aje ta..saiki samu saiwar malmon ki ki wanke ki saka a tukunya ya dahu saisai idn ya dahu saiki sauke ki dako wata tukunyar ki saka wannan kazar take a ki kawo ruwan saiwar malmon ki juye shine ruwan sanwa saiki dako maggi ki sa saki iya sa komae da kk so na qamshi dasu attarugu idn kina da buqata saiki rufe taita dahuwa idn ta dahu kk sauke.idn zakici ki tabbatar baki ci komae ba ita ake so a fara ci sbd tafi aiki..yar uwa zaki bani lbr
*HADIN ƊANYAR GYAƊAR MATA*
Danyar gyda
Sugar
Kanun fari
Zaki samu gyadarki mai zabuwa saiki wanke ki jiqata idn ta jiqu ki zubar da ruwan ki zuba kanun fari saiki niqi su suyi laushe saiki tace ki kawo yar sugar ko zuma wanda kk da buqata ki zuba ki sa a gdn sanyi kina shan abunki akwai babban sirri a ciki yar uwa...
*MANTA WAYARKA*
Ruwan rake
Ruwan kankana
Ruwan kwakwa
Madarar ruwa
Zuma
Zaki samu kankanar ki mai kyau ki yanka ta sai ki zaba a blender ki marka da ta tayi laushe saiki dako kwakwarki ki goge bayan ta ki yanka ta itama ki markada ta ki dako raken ki mai kyau ki zauna ki yankata qanana ki watse ta a blender ki markade ta, idn kika gama saiki dako ko wanne ki tace ki hadasu guri daya ki kawo madarar ruwanki ki zuba sai yar zuma da zaki zuba ki juya yar uwa ki sha ki zubama oga ya sha ...Za kiji baya ni...
*BITA ZAI ZAI*
Saiwar kankana
Saiwar zogale
Mazankwaila
Kanunfari
Zuma
Zaki hada saiwoyin guri daya ki wanke saiki zuba ruwa ki dora a wuta ya dahu sosai saiki sauke ki cire sai woyin ki dako kanun fari da mazankwailar ki zuba saiki mai da kan wuta yaci gaba da dahuwa idn y dahu saiki sauke ki zuba zuma ki barshi y huce sai ki rinqa sha..Oooo"
To kunga wannan kaɗai ƴan uwana da ƴaƴa na ,idan muka riƙe shi ya ishe ku ku gyara shimfiɗar mazajen mu ,bance gidan auren mu ba ,saboda ko wani namiji da irin halayyar shi ,amma idan kika san yadda zaki tafiyar dashi ,to ba kida wata sauran damuwa ,dan zaki ci riba a gaba ,haƙurin ne dai keda wahala ,se muna yi muna kai zuciya nisa. Sannan ko wacce mace da kuke ganin taci gaba a rayuwar auren ta ,wallahi ita kaɗai tasan me ta fuskanta ,babu gidan auren da ba'a samun saɓani ,komai kuɗi ko talauci ,mulki ko sarauta, shi namiji ba ruwan shi da ƙanƙantar mace ko girman ta ,sedai muce kawai Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya..."
Dikkanin su murmushi ne shimfiɗe akan fuskokin su, a tare suka amsa da "Ameen ya Allah"...
Ummi Maryam ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama tace "kuce kuna nan abun ku ,shine kuka kora mun mazajen nawa waje? to gani nazo nima a kacancana dani abunda ake rabawa" ... dariya maganar mahaifiyar tasu ya basu ,hafsat tacer " kaji fa ƴar tsohuwar nan ,to an cinyr ,se ki ja sandar kwaɗayin ki ki koma inda kika fito"... ta faɗa cikin sigar zolaya ,ummu mus'ab tace "Allah hafsat ki fita a ido na in rufe ,kin rakurawa tsohuwar nan da yawa ,ki roƙi Allah ma kiyi tsufa me kyau irin nata" dariya ce ta ƙwace wa hafsat tace "Tsufan na tafiya da sanda ne zan roƙa irin shi ,ni kam ummu mus'ab a'ah "... Daƙuwa ummu mus'ab ta mata tare da cewa "ungo naki nan hafsat" .... Murmushin manya ne shimfiɗe a fuskar ummi maryam... duban ta ta maida gun hafsat sannan tace " A koda yaushe ina alfahari daku zuri'a ta ,zan kuma ci gaba da alfahari daku daga yau har yaumut-tanadi. Wato hafsat yau ce rana ta farko da kika sa nayi sha'awar sanar daku lamarin aure ne ,badan komai ba ,nasan idan kika ji zaki so ace koda bakiyi koyi dani ba ,kiyi kwatankwacin sa..."
Mamaki ne shimfiɗe a fuskokin ƴaƴan ummi maryam. Saboda tun da suke da ita bata taɓa basu labarin zamantakewar ta da mahaifin su ba, hasalima duk lokacin da zasu bajiro mata da tambayar bata ce dasu komai ,sedai tayi ta murmushi abun da, se gashi yau da bakin ta tana so ta sanar dasu tarihin xamantakewar ta, sannan sun san shakka babu a yadda ummi maryam keda haƙuri ,dole akwai darasi da abun koyi a rayuwar zamantakewar ta, dikkan su sun ƙagu suji ƁOYAYYEN AL-AMARIN ,da ta jima tana ɓoye musu...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______36-40*
Suna cikin wannan yanayin ne HABIBA ƴar ummu habibat da JA'AFAR ɗan ummu ja'afar ,suka shigo suna jayayya, Ummu Ahamd ta kore su "Ku fita ku bamu guri ba dan allah ,kuda abun magana baya ƙare muku" ,nan take yaran suka sha jinin jikin su, ganin haka se duk jikin ummi maryam yayi sanyi ,kiran su tayi tare da tambayar su me suke so? Ja'afar kasa magana yayi sedai yayi ƴasa dakai ,Habibat ce tayi ƙarfin halin cewa "Dama musaya muke yi nida ja'afar ,yaga ina addu'a ,shine yake cewa ba'a yin addu'a idan mutum ba yada alwallah, kuma wai idan yana so a karɓi addu'an shi da wuri ,sannan wai akwai lokuttan karɓan addu'a?..."
Ummi maryam ƙara faɗaɗa murmushin dake fuskar ta tayi ,sannan ta matso dasu kusa da ita ta zaunar dasu ,ta fara musu bayani kamar haka...
"LADUBBAN ADDU'A A TAKAICE
Idan mutum yana da wata bukata ana so ya kintaci lokacin da akafi amsar addua (kamar tsakanin kiran sallah kafin tada iqama, ko lokacin saukar ruwa, ko sa'ah na ranar Juma'a(wanda take farawa daga bayan La'asar), ko daya bisa uku na karshen kowane dare, ko a cikin sujjada ko karshen zaman tahiya(a sujjada da karshen tahiya an fi so a zabi addu'ar da ta tabbata a Qur'ani ko Sunnah wadda ta dace da bukatar da ake nema), ko bayan aikata wani aiki na alkhairi, da makamantan su).
Ana so mai addu'a ya ɗaga hannun sa ya kira Allaah da sunayenSa kyawawa da siffofinSa madaukaka(musamman sunaye da siffofin da suke da alaka da bukatarSa, misali idan yana neman arziki ne sai yayi amfani da irin Ya Razzaq, Ya Wahhaab, Ya Fattaah, Ya Kareem. Idan kuma ilmi ne sai ya haɗa da Ya Aleem, da makamantan sa), Yayi ma Allaah kirari ya yabe Shi da yabon da ya dace da girmanSa, sannan bawa yayi furuci da gazawarsa da bukatuwarsa zuwa ga Allaah, sannan ya godewa Allaah kan ni'imar da yake ciki, sannan ana so ya kira Allaah da ISMULLAHILLAHIL A'AZAM - wanda idan aka kira Allaah dashi ko aka roke Shi Yake amsa Ya biya bukata( kamar _Yã Hayyu Yã Qayyūm_, ko kuma; _Allãhumma innī ash'hadu annaka antalLãh lã ilãha illã anta al'ahadus swamad allazhiy lam yalid wa lam yūlad wa lam yakun lahu kufuwan ahad_), sannan sai yayi salati ga Annabi sallallaahu alaihi wa ala alihi wa sallam, sai ya fadi wa Allaah bukatan sa yana mai kudurce cewa Allaah Zai biya masa, bayan ya gama addu'ar sai ya sake yi ma Annabi salati s.a.w.
Zai cigaba da yin addu'ar har zuwa sanda Allaah Zai biya masa bukatar sa. Domin ita kanta addu'a ibadah ce, dan haka maimaita ta yana ƙarawa bawa kusanci ne ga Allaah madaukakin Sarki.
Sannan idan aka samu jinkiri wurin biyan bukata da aka roka; baya nuna Allaah Bai amsa addu'ar ba, a'a, domin amsa addu'a yana faruwa ta hanyoyi dadama:
1- Imma Allaah Ya amshi addu'ar Ya biya ma mutum bukatar sa a take.
2- Ko kuma Ya amshi addu'ar amma sai Ya jinkirta biyan bukatar saboda wata hikma da Shi Allah din kaɗai Yabar ma kanSa sani, watakil Allaah cikin ilminSa da gamammen saninSa Yasan idan Ya baka bukatar a wannan lokacin wata matsala zata same ka ko zaka haɗu da wata tangarɗa a rayuwa.
3- Wani lokaci kuma Allah Zai amsa addu'a amma sai Ya canza ma mutum da abunda yafi alkhairi gare shi, saboda a ilmin Allaah Yasan idan Yaba mutum wannan bukatar Zata zama sanadiyyar halakar sa, ko ta zama masa sharri maimakon alkhairi.
4- Wani lokacin kuma Allaah Yakan amshi addu'ar bawa amma sai Ya tunkude masa wani bala'i ko musifa dake tinkararsa, ko kuma ya kankare masa wasu laifukan sa madadin biya masa bukatar da ya nema.
5- Wani lokaci kuma Allaah Yakan amsa addu'ar bawa amma sai Ya tanadar masa da ladanta da kuma bukatar da ya nema, Ya bashi a Lahira, ko Ya daukaka darajarsa a Aljannah, ko Ya kare shi daga shiga wuta a dalilin addu'ar.
6- Ko kuma Allaah Yana so ne ka zama ɗaya daga cikin bayinSa na kusa daShi, shi yasa Bai biya maka bukatar ka a take ba, saboda ka cigaba da da addu'a domin ƙara kusanta gareShi.
Dan haka rashin samun bukatar da aka nema wurin Allaah baya nuna rashin amsar addu'ar bawa, domin amsar addu'a Yana samuwa ta ɗaya daga cikin ababe ko hanyoyin da aka ambata, wadanda bakidayansu suna da da madogara a nassoshi na Qur'ani da Sunnah.
Sannan Baya halatta mutum ya roƙi Allaah abunda Allaah Ya hana ko Ya haramta ko Yaya tsawatar, msl kamar mutum ya roƙi Allaah akan cutar da ɗan'uwan sa, ko ya roƙi Allaah Ya sa ya ƙware wurin sata ko zamba ko maguɗi, ma'ana dai ba a roƙon Allaah akan saɓa maSa.
Sannan ita addu'a an fi so mutum yayi ta dakan shi, amma babu laifi ya faɗa wa wasu(musamman salihan bayi) su taya shi da addu'a, amma nashi tafi muhimmanci. Sannan ana so mutum Ya nemi iyayen sa su rinƙa yi masa addu'a. Sannan ana so mutum Ya tuba ga Allaah tuba ta gaskiya da nadama daga zunubbansa da laifukan sa kafin addu'a. Sannan idan ya zalunci wani lallai ya nemi yafiyar sa, in kuma hakkine to ya maida masa.
Sannan:
- Ba a hada Allaah da wani wurin roƙo.
- Ta'ammuli da haram yana hana amsar addu'ar bawa.
- Allaah Baya amsar addu'ar mai cin haram, ko shan haram, ko mai sanye da tufafi na haram.
- Ba a son gaggawa gameda addu'a, misali bawa yace ina ta addu'a amma Allaah Bai amsa mun ba.
- Ana son halarto da zuciya lokacin addu'a, da ƙanƙantar da kai ga Allaah SWT, domin Allaah Baya amsar addu'ar gafalalle....
"Allah yasa kun fahimce ni?" ummi maryam ta tambaye su ja'afar. "mun fahimta sosai ummi maryam ,sakallahu bi khair" Ja'afar da Habibat suka faɗa a tare ,haɗida nuna gamsuwa ,sallamar su ummi maryam tayi ,suka fita suna ta jin daɗi ,sannan ta maida duban ta kan ƴaƴanta da sukayi jigum-jigum suna sauraren bayanan nata...
Wani dogon numfashi ummi maryam ta sauke ,a lokaci ɗaya kuma ta zare gilashin dake manne a idon ta... Sannan ta soma basu labarin zamantakewar ta kamar haka...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______41-45*
"Kunga wannan sakiyar dake cikin ido?" dikkan su suka ɗago suna ƙarewa idanuwan ummi maryam kallo ,gyaɗa kai suka yi alamar sun gani. Ummi maryam taci gaba da cewa
"Nasan zaku yi tunanin koda shi aka haife ni ko?" tace "to wannan raunin zan iya kiran shi da ribar aure"... da mamaki kowa ya ɗago yana bin ta da ido , murmushi ta sakar musu tare da gyaɗa kai sannan tace " shakka babu abunda kuka ji ɗin haka yake. Mahaifin ku ɗan asalin jahar katsina ne, sarautar katsina ta mahaifin shine,kuma shine babba a gun sarki, sauran duk ƙannen shine ,kuma a lokacin shi kaɗai ne ya kawo ƙarfi, sauran duk yara ne.
Bayan rasuwar sarki ,kowa ya tabbatar da mahaifin ku shine ze gaji mahaifin shi ,shine kuma ze hau kan karagar mulki wato ya tashi daga Yarima me jiran gado ,ya zamo sarki ,tun daga nan dangin mahaifin shi suka ƙullece abun aran su ,dan su ko kaɗan basa so ace mahaifin ku shine ze hau kujerar ɗan uwan su, saboda haka sukayi duk abunda zasu iya na ganin sun hana a bashi wannan sarautar, kai ƙarshe ma suka kaɗa shi yabar gida, sedai aka neme shi aka rasa. Wanda idan baku manta ba nasha baku tarihin shi. To a haka dai ya faɗ yawon duniya ,daga wannan garin se kuma yayi ƙaura ya koma wani garin yana harkar fatauci ,a haka har yaje jahar Lagos, inda anan ne ya auri matar sa ta farko IYA MERO ,wacce sunan ta ne aka maidawa ummu mus'ab gata nan... se kuma Allah ya haɗa shi dani ya kuma ƙaddara auren mu dashi cikin sauƙi. Yana so na ina son shi muka yi aure. shekara na ɗaya da rabi a gidan Allah ya ƙaddara akwai rabo a tsakanin mu, Na samu cikin ummu mus'ab, ai kuwa tun lokacin dana samu cikin nan farin ciki ya ƙaura a gidan ,fitinar safe daban na yamma daban ,ba'a banni haka ba ,aka kwantar da cikin ,se da ummu mus'ab ta shekara tara a ciki kafin na haife ta, bayan wannan ma ba'a banni haka ba ,hatsaniya ya taɓa haɗa ni da ita ,na buɗe baki zan yi magana iya mero ta kwasa mun mari ,wai akan me tana magana zanyi magana ,wannan marin da tayi mun shine sanadiyyar wannan sakiyar na ido na ɗaya ,ya kuma assasa mun rashi gani sosai sedai da madubin ido. A wancan lokacin kuma ,ba'a san wani abu kai ƙara gurin miji ba ,ina tsoron in gaya masa ,bayan arai na inajin nayi ba daidai ba ,a matsayin ta na babba tana magana inyi magana ban kyauta ba ,wannan ne yasa naja baki na nayi shiru. Bayan wannan saki biyu alhaji yamun wanda bani da lefi a ciki duk ta dalilin kishiya ,a lokacin ba nida wayo ,se ta zauna ta kitsa mun zancen gizo na ƙarya ,tace idan aka tambaye ni ince baya bamu abinci ,bayan ga store ɗin mu nan cike da kayan abinci ,idan ya shigo da kuɗi ranar girki na ,ta tabbatar da ƙudi ne ,se ta iba wasu ta ƙulle ta saka mun a loka ,saboda ya zarge ni ,tasha yin haka yafi a ƙirga ,wanda shine sanadiyyar sakin daya mun na biyu. Ban manta ba ,na taɓa tara kuɗin da mahaifina ke aiko mun duk ranar jummu'a ,nayi asusu ,dana tara kuɗin suka kai na zuwa hajji ,na ɗauka na baiwa alhaji ya biya mun dan inje in sauke farali ,amma daya tashi seya je ya biya wa IYA MAIRO, dana tambaye shi dalili ,yace mun itace babba ,dan haka idan ni nafara zuwa mutane zasu zage shi ace baya adalci ,in bari taje idan ya samu kuɗi ko bayan ta dawo ne seya biya mun ,ina ji ina gani mairo ta tafi hajji da kuɗi na ,ban kuma taɓa ɗaga zancen wani yaji ba idan ba yau ba. Wannan ƙafar tawa kuma asalin abunda ya same ta ,bazan manta wata rana ,nazo sauko wa kan bena ba ,dake ko a lokacin ba ƙaramin me kuɗi ke gina gidan bene ba, nazo saukowa ,IYA MERO mero itama tazo saukowa ,ban ankara ba naji an hankaɗo ni ,na faɗo ƙasa ,wanda shine dalikin nakasar ƙafa na ɗaya na ,tun wancan lokacin ban kuma taɓa gaya wa wani ba se yau ,balle in kai ƙara ,wannan kuma ya samo nasaba ne da huɗubar da mahaifana suka mun da za'a aurar dani ,sun haneni da kawo ƙara ,sun kuma hore ni da cewa duka abunda zan gani komai wuya komai tsanani in yi haƙuri ,rayuwar aure haka ta gada"...
Nida miji na ban isa ya siyo abu a leda ya kawo mun ba ,ta fara tashin hankali kenan ,kwanciyan hankali na shine in ɗauka da leda na da nata in haɗa mata gaba ɗaya ,shine zamu samu yin bacci cikin kwanciyar hankali a wannan ranar... Da tsohon ciki na ban isa in dafa abinci da kaina ba ,duk abunda take so dole nima naso shi ,idan nayi wasa ma se in kwana banci ba. Ni fa zan ma iya ce muku ban taɓa ɗora tukunya a gidan miji ba da sunan zan yi girki ,ita take yi, amma indai aikin wahalar gidan ne kuma ya ƙare a kaina ,kama daga shara ,wanke-wanke ,kula da dabbobi ,da sauran su ,wankin kayan ta ma ni nake mata ,da nawa da nashi ,idan na gawa wanke kayan shi se ta ɗauko ta zuba manja a gaban rigar ,saboda taja mun duka... nifa ƙarshen ta ko kaya zan saka se idan iya mero ce ta ɗauko kayan ta bani tace saka wannan ,shine nake da ƙarfin guiwar saka wa. Ban manta zuwan alhaji saudiyya ba ,daya siyo mana zinari ni ɗaya ita ɗaya ,tun lokacin zinari na da daraja ,ɗaukar nawa yayi ya bata da sunan ta ajiye mun ,wai saboda ni kanna ɓatar ,daga ƙarshe da gangan ta salwantar da nawa ita nata na nan tana sakawa.
Miji wannan ban isa ya kwana a ɗaki na ba ,sedai idan ya bata kuɗi sannan ne ze shigo waje na...
Ummi maryam ajiye sandan dake hannun ta ɗaya tayi ,ta yaye rigar ta daidai cikin ta ,tace "kun ga wannan ƙonuwar? bazan manta ba ,wata rana nazo wucewa ita kuma ta gama sulala shinkafa ,seda tazo gab dani sannan ta kwaro mun shi a ciki ,a lokacin duk ban haifi ummu mus'ab ba, ita dai wannan cikin ne bata so in haifa ,amma da yake Allah keyi ba mutum ba ,bayan wahala da gwagwarmaya kuma naji daɗin zaman aure ,dan seda aka kai IYA MERO ,alhaji baya son jin koda sunan tane. Daga ƙarshe ciwon sashe ya kamata ,wanda shine ajalin ta ,kafin ta rasu kuma ta roƙi gafarar duk abubuwan da tayi mun ,wanda nasan anyi da wanda ban sani ba ,na kuma yafe matan, shima haka alhaji ,wanda ko kaɗan beso yafe mata ba ,amma sanadiyyar son da yake mun na tursasa shi har ya yafe mata ,na kuma matsa aka ɗauke ta aka kaita asibiti ,kai daga ƙarshe nice na koma asibitin ina jinyar ta, in mata wanka ,in bata abinci ,shekara na biyu a asibiti ina jinyar ta ,ba tare da na taɓa nuna gajiya wa ta ba ko kasawa, haka har kwanakin da allah ya ibar mata ya cika ,a hannu na ta rasu ,ina bata kunu da yamma..., ba kaɗan ba yaji mutuwar iya mero na kuma yi kukan da ko lokacin da aka ce alhaji yayi hatsari ya rasu ban yi shi ba...
Murmushi me matuƴar ƙayatarwa ummi maryam tayi tare da maida madubin idon ta ,sannan tace
"wannan kaɗan kenan daga abunda na fuskanta wllh ko rabin rababar abunda na fuskanta ban sanar daku, wannan na barshi ne tsakanina da mahalicci na. Nasan haƙurin da nayi bazaku taɓa iya koda kwatankwacin shiba, balle makamancin shi ,kudai kuyi naku kubarwa allah saura, dukda cewa na roƙar muku allah da baku juriya da haƙurin duk abunda zaku gani a rayuwa, zuri'a kuma indai tawa ce ,mace zata fuskanci fuskanta ,saboda na roƙar muku ,Idan Allah ze baku aljannah ,to yabaku ta dalilin biyayyar aure, duk abunda aka ce kuwa zaka sami aljannah ta dalilin shi to ba ƙaramar gwagwarmaya zaka sha b. Idan kun manta na tuna muku ,akwai wani sahabi daya zo wajen manzon Allah s.a.w yace ya roƙa masa Allah ya saka shi aljannar da saka annabi muhammad, annabi kuwa ya roƙa masa ,allah ya karɓa ,fitowar sahabin keda wuya ,yana hanyar sa ta komawa ,se yayi gamo da *KURA*, wacce itace izayar sa allah ya aiko masa, ta taune sahabin nan ƙurmumus ta taune ƙashin ,wanda annabi ya tabbatar mana da wannan kurar itace aljannar wannan sahabin....Dan haka kusa a ranku baku ga komai ba kuma ba'ayi komai ba ,sedai idan allah ya kawo muku komai ɗin da sauƙi ,wanda ina muku fatar hakan insha allah....
Ku kuma (ta nuna su hafsat da zainab) taci gaba da cewa "ko da kunyi aure ,idan kuka ga abunda ya shige muku duhu ,to ku tambayi iyayen ku cikin hikima ,saboda zamanin ya canza, duniyar na nan yadda yake ,amma mutanen cikin ta canzawa suke "...
Ummi maryam ba'a raba ta da murmushi ,yanzun ma shi ta sake sakar musu ,sannan tasa hannu ta ziri sandar ta ,tare da yi musu seda safe ta wuce ciki...
Nan ta barsu jingum-jingum kowacce da abun da zuciyar ta ke saƙa mata...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______46-50*
A ranar haka su kwana kowacce da bikin zuciyar ta, a ran su kuwa ayyana irin haƙurin ummi maryam suka yi ,shakka babu tayi haƙurin da ba kowace mace zata iya irin sa ba a wannan duniyar ,kai kafin ma a samu wata me irin kwatankwacin haƙurin ta dagar duniya ce... tun da suka ji labarin zamantakewar mahaifiyar tasu ,suka ƙara ƙaimi da ɗaukar aniyar cewa ,lallai zasu jajirce komai wuya komai tsanani ,suga sun yaƙi sheɗanin dake musu gizo a gidajen auren su...
Ranar asabar aka ɗaura auren ZAINAB (UMMU SADIQ) da ABU SADIQ... Alhamdulillahi anci an sha ,taro ya watse lafiya ,misalin ƙarfe takwas aka fara shirye-shiryen kai amarya gidan ta... kuka sosai zainab tasha kamar ba gobe na rabuwa da mahaifiyar tata ,daƙyar aka iya ɓanɓare ta daga jikin ummi maryam, ita kanta daurewa kawai take yi , dan shaƙuwa me tsanani ne a tsakanin ta da zainab ,dan ita ke ɗauke mata kewa ,bata taɓa barin ta da kaɗaici, yau ga ranar rabuwa tazo, nasihohi tayi mata sosai ,tare da rakata da addu'o'in zaman lafiya...Dikkan yayyin ta dasu aka kaita ɗakin ta ,fatar zaman lafiya suka yi mata ,sannan suka dawo gida ,anan ma zainab ba ƙaramin kuka tasha ba ,ummu hanifa ce ma ke ta mata tsiya tana faɗin "ohhho !kema ai yanzu kinji yadda muka ji ko? a tunanin ki da ummi maryam zaki rayu har ƙarshen rayuwar ki? to ki farka tun wuri ,ki kuma cire ƙawa-zuci ,kar ki bari yayi tasiri a zuciyar ki ta yadda har zaki samu tawayar kula da me gidan ki ummu sadiq ,ki kula sosai da kanki da kuma gidan ki ,duk yadfa kike jin gidan ummi maryam a ranki ,kike ganin ba gidan daya fi shi a wajen ki ,to yau gashi kin samu ,dan gidan miji shine mafificin gidan ki a duniya in ma da daɗi in ma ba daɗi, saboda haka se ki zage damtse ki kuma ci ɗammarar yaƙi da sheɗanin daya rako ki...Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a masu albarka"... kowa da kowa ya amsa da "Ameen..."
kowa da kowa ya watse, ya rage Amarya ita kaɗai a ɗakin ta ,tana jiran shigowar angon nata... Misalin ƙarfe 9 ango ya turo wa amarya text akan gasu nan zuwa. ba ɓata lokaci zainab ta tashi ta gyagy-gyara inda keda buƙatar gyara ,ta ƙara turara gidan da turaren wutar tsintsiya da aka kawo mata masu ƙamshin daɗi da shiga rai ,bata sake wani wanka ba ,saboda da za'a kawo ta tayi ,turaruka masu matuqar rikitarwa da samar da nutsuwa da baɗe lungu da saƙo na jikin ta dashi ,sannan ta ɗan ƙara gyara fuskar ta sama sama...
Ba taji shigowar su ,tun daga tsakar gida abokan ango ke santin ƙamshin da ke tashi a gidan ,basu ƙara gasgatawa ba seda suka shiga parlour ,ba lefi komai yayi tsari ,an zuba mata kaya ,bana ƙarya ba ,amma daidai gwargwado duk abunda ake kai ƴa mace dashi me kyau da tsada daidai aljihu an kai ma zainab shi... wuri suka samu suka zazzauna akan kushin ,se famar tsokanar ango suke yi ,shidai be iya cewa komai ba ,se martananin murmushin sa me ƙayatarwa dayake bin su dashi... Tashi ABU SADIQ yayi ya nufi ɗakin daya ke sa ran amaryar sa na ciki, da sallama ɗauke a bakin shi ya shiga ,zainab bata yi ƙasa a guiwa ba wajen amsa masa sallamar sa ,tare da yi masa sannu da zuwa ,duk da cewa fuskar ta a lulluɓe yake, ƙara gyara mata mayafin yayi ,sannan ya riƙo hannun ta suka fito parlour wajen abokanan shi ,nan fa kabbara ya tashi , ba kaɗan ba yadda suka fito ya ƙayatar da kowa ,nan suka shiga yi musu hotuna, ganin dare nayi yasa MALAM JAMIL (babban abokin ango) ya buɗe taro da addu'a. Nasiha sosai suka musu ,a ƙarshe suka musu addu'an samun zaman lafiya ,sannan suka miƙa masa ledodin da suka zo musu dashi ,sallama suka musu sannan suka tafi ,yaso ya raka su amma suka hana shi ,dan haka suna fita ya maida ƙofar gida ya rufe ,tare da tofa addu'o'i ,sannan ya koma ciki. Sallama ya mata ,ta amsa shi a karo na biyu ,sannan ya sake jan hannun ta suka koma ɗaki. Matsowa yayinya zauna daf da ita,,, gyaran murya yayi ,tare da ƙara faɗaɗa murmushin sa sannan ya fara godia ga allah daya nuna masa wannan rana ,ɗaya daga cikin ranakun farin ciki a rayuwar shi...
A hankali ya yaye mayafin data ke lalluɓe dashi, nan da nan yayi tozali da kyaky-kyawar fuskar amaryar shi ,godia ya sake yiwa allah ,sannan ya shiga aikin yabo ,hannu yakai yaɗan ɗago haɓar ta ,ta yadda ze ƙare mata kallo.
kunya ne ya kama zainab ,ba shiri ta faɗa jikin shi tare da ɓoye fuskar ta ,dariya abun ya bashi tare da cewa "yau ko na shiga aljannah na kasa fita ,wato dai har yanzu ba'a gama mun rowar kyaky-kyawar fuskar nan ba ko? ,to ada dai nayi haƙuri saboda saboda akwai shamaki ,amma a yanzu kam bari na za'ayi inyita kallon kyaky-kyawar kyautar da allah ya azurta ni da samu ,babu ƙarfi na balle dabara. Allah na gode maka ,Allah ga iyali na ,Allah ka tsare mun da tsarewar ka ,ka kare mun da dikkan kariyar ka ya Allah" .... a sanyaye Zainab ta amsa da "Ameen"...
Taimaka mata yayi ta miƙe ,har a lokacin tana maƙale a jikin shi ,a tare suka shiga banɗaki ,suka ɗoro alwallah ,sallah yaja su raka'a biyu ,addu'o'i sosai yayi musu tare da bawa Allah amanar auren shi...
Bayan sun kammala ,ya miƙe ya shigo da ledodin da abokan sa suka miƙa masa ɗazu ,sannan ya umurce ta data ɗauko plate da kofi... A nutse ta miƙe ta yi kamar yadda ya umurce ta ,tashi yayi ya karɓa tare da sanya mata albarka ,be zauna ba seda ya zare babban rigar shi ya ajiye a gefe ,da kanshi yake ƙoƙarin zuzzuba wa ,zainab tayi sauri ta karɓe shi ,murmushin jin ɗaɗi ya mata sannan ,ya sakar mata ,sakamakon wayar shi daya ji tana ƙara ,be kawo komai a ran shi ba ,duk da be san me lambar ba ,ya ɗauka tare da yin sallama
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______51-55*
Sallama yayi ,daga cikin wayar aka amsa mishi da "wa'aikumussalam. Malam barka dawar haka" "Barka ! dawa nake magana ?" ABU SADIQ ya tambaya, daga cikin wayar aka bashi amsa da "Kana magana da ummu hani daba bauchi. dama naji wani wa'azi ne da kayi ,shine nayi ta bibiya ,a ƙarshe sena ji ka bada lambar wayar ka ,shine nace bari in kira in yi tambaya ,to kuma kusan kwana biyu ina kira bana samu ,se yau ne allah yasa na samu..."
Ɗan shiru ABU SADIQ yayi naɗan wasu daƙiƙu ,sannan yace "Allah sarki ,to ina godia ,amma da zaki mun haƙuri ko zuwa gobe se ki sake kira ,saboda yanzu ina ɗan wani uzuri ne?" "toba damuwa malam dayau da gobe ai na allah ne ,idan allah ya kaimu goben se in sake kira"... ummi hani ta bashi amsa badan taso ba... sannan ya yanke wayar...
Duk yadda yayi da ummu hani ,xainab ta ji shi ,saboda wayar Abu sadiq irin wayar nan ne da idan kana kusa dame wayar zaka iya jin komai da akr faɗi. Bayan ya ajiye wayar ,xainab ke tambayar shi meya faru? kamar bata ji komai ba ,ba musu ya bata labarin yadda akayi ,murmushi ta sakar masa tare da ɗaukar hannun shi ta saka a nata ,tana shafawa ,nan ta fara mai magana cikin hikima
" *RAYUWA SAI DA LURA ABU SADIQ*
Ko ka san Ma'abocin Kyakkyawar Zuciya, wanda ba ya kƴamar farin cikin waninsa : Shine wanda yake yiwa kowa fatan Alkhairi ba tare da ya tsame ko tantance wasu ba.
Kuma ya fahimci cewar: Samun wasu bazai taɓa toshe ƙofar samunsa ba, Farin cikin wasu ba zai taɓa tafiyar da nasa ba, Wadatar wasu ba zata taɓa tauye Arzikin da Allah ya rubuto masa zai samu ba.
Lallai kam wannan shine wanda rayuwarsa take kwana ta tashi cikin farin ciki a kullum, saboda yana farin ciki ne da farin cikin ƴan uwansa, ya yarda babu abinda zai iya faruwa sai da sani da kuma ikon Allah..." shiru zainab tayi ,sannan taci gaba da cewa "Abu sadiq dani dakai ,da me tambayar ba wanda yasan gawar farko , me yuwa kafin goben Allah yayi ikon sa akan mu ,idan kuma ita me tambayar allah be bata ikon sake samun ka ba fa? ta iya yuwa kuma tambayar nada muhimmancin da baza'a iya jinkirta shi zuwa wani lokacin ba, nice kaɗai zan fahimtar ka ,ita ba lallai ta iya fahimtar ka ba ,Allah yasa kamun kyaky-kyawar fahimta Abu sadiq?" .... cike da gamsuwa da bayanan nata ,yace "Naji kuma na gamsu ummu sadiq ,yanzu ya kike so ay?" ɗan marairaicewa zainab tayi ,sannan tace "inaso kamun izinin bin bayan kiran ,muji tambayar ta ta!" ,ɗan numfasawa Abu sadiq yayi sannan yace " na miki izini" tare da miƙa mata wayar ,godia sosai zainab tayi masa sannan tasa hannu biyu ta ansa wayar, tare da kiran lambar data gani a ƙarshen jerin gwanen masu kira ,bugu ɗaya biyu ,aka ɗauka tare dayin sallama ,amsa sallamar zainab tayi ,tare d gabatar da kanta " Suna na zainab ,mlm naɗan da wani uzuri ne yanzu ,amma ni matar shi ce ,ki saki jikin ki kiyi tambayar dakike so kiyi inajin ki ,insha allahu kuma zan baki amsa daidai gwargwadon sani na.. sosai ummi hani taji daɗin jin haka daga gurin zainab ,nan tashi gagaya wa zainab cewa
"Dan Allah ina son cikakken bayani ne a kan idda da takaba. sannan me ya kamata mai idda ko me takaba ta yi? Kuma meye za ta ƙaurace wa?
Ajiyan zuciya zainab ta sauke sannan ta fara bata amsa kamar haka
[1] " Idda ita ce tsawon lokacin da mace take zama bayan rabuwanta da mijin aurenta kafin ta sake wani auren. Kuma babu bambanci ko rabuwar ta dalilin mutuwar mijin ne, ko kuma mutuwar auren.
Sai dai kuma idan mutuwar auren ta dalilin saki ne, to babu idda sai in a bayan saduwa ce sakin ya auku, ban da inda ya sake ta tun kafin saduwar ta auku a tsakaninsu. Amma idan dalilin iddar rasuwar mijin ne, to a nan idda ta tabbata a kan matar, ko mijin ya sadu da ita ko bai sadu da ita ba.
[2] Hukuncin idda tana bambanta ne da bambancin matar da take yin ta:
(i) Idan matar mai ciki ce, tsawon iddarta shi ne ta haife cikinta. _(Surah At-Talaaq: 4)._
(ii) Idan kuwa tana daga cikin shekarun yin haila ne, to tsawon iddarta shi ne: Ta yi haila har sau uku. _(Surah Al-Baqarah: 228)._
(iii) Wacce kuma ba ta kai lokacin yin haila ba saboda yaranta, ko wacce ta wuce shekarun yin hailar saboda tsufa, tsawon iddarta watanni uku ne. _(Surah At-Talaaq: 4)._
(iv) Amma wacce mijinta ya rasu kafin ko bayan saduwa da ita, tsawon iddarta shi ne: Watanni huɗu da kwanaki goma. _(Surah Al-Baqarah: 234)._
[3] Wacce mijinta ya rasu ko ya sake ta amma ba ta samu labari ba sai bayan wani lokaci, to iddarta dai tana farawa ne daga lokacin aukuwar sakin ko rasuwar, in ji wasu malaman. Wasu malaman kuma suka ce: Za ta fara iddar ce daga lokacin da labarin ya iso mata.
Haka kuma don kasantuwar mace ta daɗe ba ta kusa da inda mijinta ya ke, wannan bai hana ta yin idda a bayan rasuwarsa ko a bayan ya sake ta ba.
[4] Wacce ta yi zina, ko wacce wani ya sadu da ita bisa kuskure, kamar idan yana zaton ita matarsa ce, ko kamar wacce aka ɗaura mata aure da wanda ba ta san cewa ɗan’uwanta ne na shan nono ba, haka ma duk wacce aka ɗaura mata ɓataccen aure - kamar wanda aka ɗaura ba da sani ko izinin waliyyi ba - to abin da yake wajibi a kanta, in ji malamai shi ne: *Istibraa’i* na tsawon haila guda ɗaya kawai. _(Tamaamul Minnah: 3/227)._
[5] Daga cikin hukunce-hukuncen da suka rataya ga mai idda akwai waɗannan:
(i) Wacce take iddar sakin da yake akwai kome a cikinsa tana da haƙƙin a ba ta mazauni da abinci da sauran haƙƙoƙinta a gidan mijin da ya sake ta, har zuwa lokacin da za ta kammala iddar.
(ii) Amma idan iddar sakin da babu kome a cikinsa ne, watau saki na-uku, to a nan ba ta da wani haƙƙi na mazauni ko na sauran nauye-nauye a kan mijin, sai dai ko in tana da ciki, shi ne za a kula da ita saboda cikin.
(iii) Wacce aka yi mata sakin da yake akwai kome a cikinsa, a gidan mijin za ta zauna, kuma ya halatta ta cigaba da harkokinta na ado da kwalliya. Domin Allaah ya hana a fitar da ita, ko ita kanta ta fita daga gidan. _(Surah At-Talaaq: 1)._
(iv) Amma wacce sakinta ya zama na-uku ne watau na-ƙarshe, to wajibi ne ta nisanci kaɗaituwa da wanda ya sake ta, dole ta sanya hijabi a tsakaninta da shi. Domin a yanzu ta zama *‘ajanabiyya’* a gare shi, wacce bai halatta ya kaɗaice da ita ba.
(v) Bai halatta wani ya nemi aurenta a fili ƙarara ko a fakaice ba, idan dai sakin aurenta wanda yake akwai kome a cikinsa ne, watau idan saki na-ɗaya ne ko na-biyu.
Mijinta ne kaɗai ke da ikon dawo da ita a cikin wannan halin kafin iddar ta cika. _(Surah Al-Baqarah: 228)._
(vi) Amma idan sakin na-ƙarshe ne, watau saki na-uku, to a nan ya halatta wani ya nemi aurenta a fakaice, ban da a fili a bayyane. _(Surah Al-Baqarah: 235)_
(vii) A ƙarƙashin wannan, ita ma da take cikin iddar ba za ta yi duk wani abin da zai janyo wani zuwa ga nemanta ba, kamar ta fuskar ado da kwalliya, har sai ta gama. Amma mijin da ya sake ta saki na-ɗaya ko na-biyu shi ne kaɗai za ta yi masa kwalliya.
(viii) Bai halatta wani ya ɗaura mata aure ba a cikin wannan halin, ko iddar sakin da yake akwai kome a cikinsa ne ko ba shi ba ne, har sai lokacin da iddar ta cika.
Idan kuwa har wani ya ɗaura mata auren a haka, to wannan auren ɓatacce ne, kuma dole a warware shi, a raba tsakaninsu.
(ix) Idan kuma har mijin ya sadu da ita a cikin hakan, to duk da haka dai wajibi ne a raba su, ta koma ta kammala iddar farko, sannan ta sake yin idda saboda wannan rabuwar ta biyu, a wurin malamai masu yawa.
(x) Malaman sun saɓa da juna a kan ko za su iya sake yin aure a bayan ta kammala iddar ta biyu ko ba za su iya ba. Marinjayiyar magana dai a wurinsu ita ce halaccin hakan. _(Tamaamul Minnah: 3/228)._
(xi) Idan ɗaya daga cikin ma’aurata ya kwanta ya rasu a lokacin da matar take cikin iddar sakin da yake akwai kome a cikinsa, to akwai gado a tsakaninsu.
Saɓanin wacce ke cikin iddar sakin da babu kome a cikinsa. Su kam babu gado a tsakaninsu.
[6] Idan kuwa iddar da mace take yi saboda mutuwar mijinta ne, a nan tana ƙarawa da abin da ake kira takaba. Takaba ita ce zaman da matar da mijinta ya rasu take yi ba tare da ado ko kwalliya ba. Watau tana nisantar duk kayan ado ko kwalliya a iya tsawon kwanakin iddarta:
(i) Idan mai ciki ce, za ta zauna a haka har zuwa lokacin da za ta haife cikinta.
(ii) Idan kuwa mara ciki ce, har zuwa cikan watanni huɗu da kwanaki goma daga mutuwar mijin nata.
*Al-Imaam Al-Bukhaariy (5338)* ya riwaito daga Ummu-Salamah _(Radiyal Laahu Anhaa)_ cewa: Wata mace ce mijinta ya rasu, sai danginta suka ji tsoro game da ciwon idanuwanta, don haka suka zo wurin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ suka nemi izininsa don ta sanya kwalli (tozali), amma sai ya ce:
« لاَ تَكَحَّلْ ! قَدْ كَانَتْ إِحْدَاكُنَّ تَمْكُثُ فِى شَرِّ أَحْلاَسِهَا أَوْ شَرِّ بَيْتِهَا ، فَإِذَا كَانَ حَوْلٌ فَمَرَّ كَلْبٌ رَمَتْ بِبَعَرَةٍ ، فَلاَ ، حَتَّى تَمْضِىَ أَرْبَعَةُ أَشْهُرٍ وَعَشْرٌ »
Ba za ta sanya tozali ba! Ai ɗayarku a da can, ta kasance tana zama a cikin mafi munin hali ne a cikin gidanta. Idan shekara guda ta yi kuma wani kare ya gitta, sai ta yi jifa da kashin raƙumi! Don haka, sam! Ba zai yiwu ba! Har sai watanni huɗu da kwanaki goma sun wuce!
Kuma *Al-Imaam Abu-Daawud (2302)* ya riwaito hadisi *sahihi* daga Ummu-Atiyyah _(Radiyal Laahu Anhaa)_ cewa: Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:
« لاَ تُحِدُّ الْمَرْأَةُ فَوْقَ ثَلاَثٍ إِلاَّ عَلَى زَوْجٍ ، فَإِنَّهَا تُحِدُّ عَلَيْهِ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا : لاَ تَلْبَسُ ثَوْبًا مَصْبُوغًا إِلاَّ ثَوْبَ عَصْبٍ ، وَلاَ تَكْتَحِلُ ، وَلاَ تَمَسُّ طِيبًا ، إِلاَّ أَدْنَى طُهْرَتِهَا إِذَا طَهُرَتْ مِنْ مَحِيضِهَا ، بِنُبْذَةٍ مِنْ قُسْطٍ أَوْ أَظْفَارٍ ».
Kar mace ta yi takaba na sama da kwanaki uku sai dai a kan miji: Za ta yi masa takaba na tsawon watanni huɗu da kwanaki goma. Ba za ta sanya tufafin da aka rina ba, sai dai ko tufar asbu. Ba za ta sanya tozali ba. Ba za ta sanya turare ba, sai dai a lokacin kusancin tsarki daga hailarta: Sai ta yi amfani da wani abu kaɗan na turaren *Qustu* da *Azfaا*Azfaar.
A wata riwaya (2304) kuma ya ce:
« وَلاَ تَخْتَضِبُ »
Kuma ba za ta yi lalle ba.
[7] Daga waɗannan riwaiyoyi ya fito a fili ƙarara cewa:
(i) Yin takaba na tsawon dukkan watanni huɗu (4 months) da kwanaki goma (10 days) ne, amma ba wai kwanaki arba’in (40 days), kamar yadda wasu marasa sani suke faɗi a ɓoye ga mata ba.
(ii) A tsawon wannan lokacin dole ne mai takaba ta nisanci: Sanya tozali a idanunta, ko gazal ko hoda a fuskarta. Dole ta nisanci sanya turare kowane iri, in dai ba a lokacin wankan haila ba, kamar yadda ya gabata. Za ta nisanci yin lalle ko duk wata kwalliya a ƙafafunta ko hannuwanta, kamar dayis na zamani. Kuma dole ta nisanci sanya tufafin ado da aka rina da kowane irin launi, sai dai ko koɗaɗɗu, ko kuma waɗanda ba arina su ba, kamar baƙaƙe ko farare. Ko su ɗin ma ba na ado ko kwalliya ba. Sannan kuma dole ta nisanci sanya kayan ado na zinare ko azurfa da makamantansu a jikinta, kamar a gashin kai ko kunnuwa ko hanci ko wuya ko hannuwa ko ƙafafuwa da sauransu.
(iii) Ba a hana mai takaba ta tsaftace jikinta, kamar ta yin wanka da fece gashin kanta da gyara shi, irin gyaran da ba na ado ko gayu ba, kamar dai ta ɗaure shi ko ta kitse shi kawai. Haka kuma ya halatta ta yanke ƙumbunanta, ta aske gashin mararta da hammatarta, ta goge haƙoranta ta tsaftace su. Kamar yadda ya halatta ta shafa mai a fatar jikinta idan akwai buƙata, amma ba mai kamshi wanda ke da ma’anar turare ba.
(iv) Haka nan dai ba a hana mai takaba cin duk abincin da ta so ba, daga duk nau’ukan kayan abinci da abin sha da ’ya’yan itatuwa, matuƙar dai Allaah Ta’aala ya halatta shi ga musulmi. Ko da kuwa yana da daddaɗan ƙamshi. Don haka, ya halatta ta sansana turare da hancinsa in ta yi buƙata, don ba a jikinta zai zauna ba.
(v) Sannan kuma za ta dawwama a cikin gidanta ne, ba za ta fita da rana ba sai in akwai buƙata, kuma ba za ta fita da dare ba sai in da larura. Kuma ba a haramta mata yin duk wani aiki mai shagaltarwa daga cikin shagaltarwa ta halal ba, kamar: Aikin yi wa tufafi ado, da ɗinki, da kaɗi, da sauran ayyukan da mata suke yi.
_Wal Laahu A’lam._ "...
cike da gamsuwa ummu hani ta yiwa zainab godia sannan ta mata sallama tare da kashe wayan...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______56-60*
Tsabar farin ciki ne da murna ya mamaye zuciyar Abu sadiq ,wanda ya assasa ya kasa ɓoye farin cikin shi a bayyane, ya ma kasa tantane shin yau farin cikin me yake yi? Na kasancewar shi yau Ango ko kuwa na sa'ar mata kamar ummu sadiq da yayi. kan ta ya dafa ,ya shiga jero mata addu'a kamar yadda musulunci ya koyar. Sun ciyar da juna cikin aminci da ƙaunar juna ,Se kuma aka shiga fagen jiyar da juna asalin sirri da tantagaryar madarar auratayya ,duk da cewa wannan shine karo na farko da zainab zata san namiji a rayuwar ta ,be hana ta bawa mijin ta haɗin kai sun murji amaryaci daidai gwargwado ba. Haƙiƙa tayi namijin ƙoƙari ,wanda yasa abu sadiq yaba mata kan ƙwazon ta ,Albarka kuwa iri daban daban se kalan wanda Abu sadiq ya manta ne kawai be saka mata ba, babban farin cikin daya mamaye kaso hamsin cikin ɗari na zuciyar shi be wuce daya sami matar shi a cikakkiyar budurwa ba ,bugu da ƙari ga ainahin tantagaryar abun da ake cewa ɗanɗano da ni'ima...
Da safe ,a tare suka farka ,kusan ma sun so makara ,taimaka mata yayi ta gasa jikin ta ,wankan tsarki tayi tare da ɗauro alwala ,sannan shima ya shiga yayi. Ko kafin ya fito ,ta canza zanin gado ,da ɗauke kayan shi daya cire jiya ,takai komai mazaunin shi, plate ɗin da suka ɓata ta fita dasu takai kitchen ,sannan ta dawo da kunna turaren wuta ,kan kace me ko ina dako ina na baɗe da ƙamshi. Akwatin ta ta buɗe ta zaro doguwar riga ,ta saka ,tare da feshe jikin ta da turaru ka masu sanyin daɗi. dadduma ta shimfiɗa ,tana jiran fitowar shi, da mamaki yake bin ɗakin da kallo ,ganin duk ta gyara ko ina da komai ,se kuma ya maida duban shi gare ta ,magana yake so ya mata ,amma seta masa nuni da agogon bango alamar lokaci na ƙure wa, da sauri ya ƙaraso ya jasu sallar asuba ,be wani tsawaita ba ,dan yasan Ummu sadiq ba zata jure tsayuwar ta ,duba da abunda ya kawana a tsakanin su jiya, duk ayukkan ma data yi yasan kawai tana daure ne ,amma dole akwai raɗaɗi , a ranshi yake ƙara yabawa jarumta irin nata... Bayan sun idar da sallah, sun yi addu'o'i ,cikin girmamawa zainab ta yiwa abu sadiq ina kwana da kuma ban gajiyar hidima ,ran shi fess ,ya amsa ta tare da yi mata ya jiki ,shiru ne yaɗan biyo baya naɗan wani lokaci ,koda ya ɗago se yaga idanuwan ta a kulle alamar bacci take ji ,beyi ƙasa a guiwa ba ,ya karka to ta ,ta kwanta akan ƙafafuwan shi ,tare da gyara mata kwanciyar yadda zata ji daɗin bacci ,gefen fuskar ta ya shafa tare da sumbatar goshin ta ,ba jimawa bacci sosai ya ɗauke ta, shi kuma ya fara karatu har garin ya ida wayewa tangaras...
Misalin ƙarfe 2 na rana ,ƴan uwa da ƙawayen zainab suka zo gidan ta ,an wuto mata da duk wani sauran kayan ta ,yadda suka same ta ba kaɗan ba ,yayi matuqar basu sha'awa ,suna gidan Abu sadiq ya aiko da kulolin abinci niƙi-niƙi da mahaifiyar shi ta bada ya kawo ,bayan an gama gaggaisawa ne ,zainab ke tambayar ya bata ga Ummu mus'ab ba? anan ummu hafsat ke sheda mata ai ta wuce gida tun da safe ,sakamakon kiran ta da akayi aka sanar mata mijin ta ba lafiya. Sosai zainab ta jajanta tare da kira ta a waya ta yiwa mijin fatar samun lafiya...
Bayan biki da kwana biyu ko waccen su ta koma gidan mijin ta ,dan taci gaba da bautar aure...
GIDAN UMMU MUS'AB...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______61-65*
GIDAN UMMU MUS'AB.... Tun lokacin da Ummu mus'ab ta samu labarin rashin lafiyar mijin ta ,ba k'aramin gigita tayi ba ,ikon Allah ne kawai ya k'araso da ita garin kano... YUSRA ta fara kira(sunan y'ar rik'on hajiyar kenan) ,ta gaya mata asibitin da aka kwantar dashi ,kai tsaya asibitin Maman Aminu kano ta dosa , tun daga bakin gate ta fara cin karo da y'ay'an rik'on ta ,da sauri Hajiya Zali ta k'araso tana yiwa Ummu mus'ab barka da isowa ,tambayar ta take ina Abu mus'ab? Haj zali tace ,yana Aminity ,cikin hanzari Ummu mus'ab ta k'arasa... Shigar ta wajen keda wuya ,taci karo da likita alamar ze shiga duba shi ,rufa masa baya tayi suka shiga tare, dudduba shi likitan ya sake yi ,sannan ya maida duban shi gun Ummu mus'ab ,yace "Hajiya Dan Allah iyalin sa fa?" Cikin zak'uwar son jin me ya samu mijin nata ,tace "Gani likita. Dan Allah me yake damun miji na?" Ganin yadda gaba d'aya Ummu mus'ab ta rikice yasa likitan ya fara kwantar mata da hankali " Ah wato Hajiya ,am sorry to say Alh. Ya kamu da tsananin hawan jini ,Wanda har yakai yaci k'arfin shi, iya bincike munyi mun gano ya dad'e a jikin shi kuma alamu sun nuna baya kula dashan magani..." Salati Ummu mus'ab tayi tare da Neman tsari daga musibar data ke ji a yanzu. Likitan yaci gaba da cewa "Hajiya ,alhaji na buk'atar Hutu nad'an wani lokaci ,duk wani Abu daze kawo masa hayaniya anan Dan Allah ayi k'ok'arin kawar dashi ,saboda mu samu damar yin aikin mu yadda ya kamata. Yanzu mun yi masa allurar bacci ,saboda haka akwai yiwar ya farka daga nan zuwa awa ashirin da hud'u".. Godia Ummu mus'ab tayi wa likita ,sannan ya fice yabar su. Duban tsaf Ummu mus'ab tayi wa Abu mus'ab ,nason gano ainahin abunda ke damun shi ,dukda ya manyanta ,tasan shekarun shi sun kai ya iya kamuwa da hawan jini ,amma dole akwai abunda ya assasa shi har abun yakai haka ,ba tare da d'aukan mataki ba... " yayi bak'i ya rame. Meya ke damun Ka Abu mus'ab? Bazan tab'a yafe wa kaina ba idan har na gane nima inada sa hannu a rashin lafiyar ka!" Ummu mus'ab ta fad'a ... Yinin ranar dai Ummu mus'ab wuni tayi a zaune tana rok'awa mijin nata lafiya. Abincin kirki ma ta kasa ci ,se da Haj zali ta matsa mata sannan tad'anci shima ba wani sosai ba. Kallon tausayi Haj zali tayi mata a ranta take cewa "dubi duk yadda ta damu ,kamar wacce aka ce mata baze tashi ba. Kai Ummu mus'ab akwai jarumta ,idan manta ba ,yau kusan shekaru ashirin da hud'u kenan ,tun da Abu mus'ab ya k'aro aure rabon da ya kwana a gidan ta ,hasali ma se yayi wata be lek'a taba ,idan tayi kewar shi seta shirya taje har wurin aikin shi ta same shi su gaisa ,be tauye ta da duk wani buk'atun rayuwa ba ,abinci abun sha ,sutura da sauran su ,amma rabon ta dashi kusan shekaru ashirin da had'u kenan, ban kuma tab'a jin Ummu mus'ab tayi masa k'orafi ba ,tun da tayi masa tambayar duniyar nan ,akan kodai ta masa lefi ne yace ko d'aya ,se ta barwa Allah al-amarin shi ,tasan komai yayi farko dole zeyi k'arshe amma baza 'a tabbata a haka ba. Kai namiji d'an maman shi duk a zancen zucin Haj zali ,yanzu ina matar tashi? Meya hana bata zo tayi jinyar shiba? Hmmm duniya kenan... Ummu mus'ab ce ta katse wa Haj zali tunani da cewa " Haj zali ,ina matar Abu mus'ab ? Ya banganta anan ba?"
Ajiyan zuciya Haj zali ta sauke ,sannan tace "nima rabon zanje in ganshi a wannan halin ne. Naje in duba shi ne ,na samu ba yada lafiya ,Dana tambayi me gadi matar gidan ,shine take sheda mun ai kusan watan ta Tara bata k'asar"... Shiru Ummu mus'ab tayi ,bata k'ara cewa komai ba. Haj zali kuma ta fita sakamakon kiran wayar ta da Haj ma'u tayi ,akan tana k'ofar asibitin tazo ta shigo da ita... Haj zali, haj ma'u ,haj safina ,haj kausar, Alh Audi ,Alh mus'ab comrd Bello ,dr sule ,,,,,Way'annan duk y'ay'an rik'on Ummu mus'ab ne data rik'e su tun suna yara, ta tarbiyantar dasu sannan ta musu aure ,daga ciki babu d'an d'an uwan ta ,daga y'ay'an k'anin Abu mus'ab ,na yayar shi se wa'yanda ta d'auko a gidan marayu....
******************
Da daddare a gidab Ummu Ahmad ,bayan sun gama cin abinci ,kallon tsaf tayi wa Abu Ahmad, gaba d'aya taga ya canza mata tun da feena ta dena zuwa gidan, ya koma shiru-shiru... Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta kira sunan shi a tausashe " Abu Ahmad!!! " d'an d'agowa yayi yana duban ta ,sannan taci gaba "Dan Allah inaso muyi wata magana me muhimmanci idan ba damuwa ,da fatar kuma magana ta baza ta b'ata maka rai ba?" Gyad'a kai yayi alamar yana jin ta " Wato Abu Ahmad ,nace wata shawara nake so in baka idan bazaka damu ba ,meze hana ka auro feena ka kawo ta gidan ka a matsayin mata ,da ace kuci gaba da aikata sab'on Allah ,ba gara ka aure taba ,tun da har Allah ya jarabce Ku da juna ,kuma naga ma duk a cikin sauran matan da kake nema kamar kafi shak'uwa da ita ,saboda ita nafi yawan gani a gida na ,indai hakan ze sa kayi adalci a tsakanin mu ,kuma ka dena tu'ammali da matan banza ,to ina farin ciki ,ina kuma maraba da hakan ,kuma kar kace na fad'i ne da dokin zuciya ,wallahil azim zuciya ta d'aya nake wannan maganar dakai"... Darasss das gaban Abu Ahmad ya bugi tara-tara ,da mamaki ya ware ido yana bin ta da kallon ban gane me kike nufi ba, murmushi ta sakar masa me narkar da zuciyar mak'iya ,tare da gyad'a kai... Ya san ta farin Sani ,ya kuma San me zata iya aikatawa da Wanda bazata iya ba. Kafe ta yayi da ido nason gasgata maganar ta ,a zaman da yayi da Ummu Ahmad, da yadda ya karanci rayuwar ta, abun da ma yafi wannan yasan zata iya...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______66-70*
GIDAN UMMU HANIFA!!!
Abu hanifa ne kwance zazzab'i ya rufe shi ,kallo d'aya zakawa Ummu hanifa ka d'auka ko itace Mara lafiyan. Duk tabi ta fita a hayyacin ta, tausa take mai bayan yasha magani, tana tofa masa addu'a a haka har ta samu bacci ya d'auke shi, jugummm tayi tana k'are mishi kallo, hawaye kuwa wani nabin wani, duk na tausayin mijin nata, ganin wannan baze fish-she taba yasa ta tashi ta d'auro alwalla ,sallah tayi raka'a biyu ,ta zauna kan dadduma, ba abunda take se rok'awa mijin ta lafiya... Tana kuka tana gayawa Allah, duk abunda take Ashe Abu hanifa na jin ta ba bacci yake ba, tsananin tsoron Allah ne ya kama shi. A hankali ya bud'e idanuwan shi ya zuba su akan ta, cikin tausasawa da sanyin muryar dabe tab'a yi mata ba ,ya Kira sunan ta "Ummu hanifa!" A d'an tsorace ta waigo ,tana duba inda taji an kira ta.. Abun har yaso ya bashi Dariya, murmushi ya sakar mata ,sannan ya mata alamar tazo.
A nutse ta taso tare da zare hijabin jikin ta sannan ta k'araso gare shi, hannun ta ya janyo cikin nashi ,yace " Ummu hanifa meya hana ki bacci har wannan lokacin?, tukunna ma kinci abinci " yayi tambayar kamar be San komai ba, had'ida Shafa k'asan cikin ta.
Kasa magana tayi ,se kuma tayi k'asa dakai ,a lokaci d'aya kuma hawaye ta taru a idon ta, tace "taya zan samu nutsuwar cin abinci ,bayan Wanda nake girkin Dan shi baya da kuzarin cin abincin ,Wanda shine k'arfin guiwa ta ,duk wani abunda nake yi a gidan nan ko zanyi Dan shi nake yi. Bacci kuma ba nida kwanciyar hankalin yin shi ,taya bacci ma ze kawomun ziyara Abu hanifa? Karka manta ka fini buk'atar bacci ,kaide ke fita kullum gurin nema mana abunda zamu ci ,shin kana ganin idan baka samu bacci ba da wani fuskar zan kalli mahalicci na ran gobe k'iyama in fad'a masa ,na Gaza da bautar da nake yi?"""
Murmushin jin dad'i Abu hanifa yayi tare da d'ago fuskar ta ,lokaci d'aya kuma yasa hannu yana share mata hawayen dake sauko mata, yace "na gode sosai matata da kulawar da kike bani ,hak'ik'a ke mace CE ta gari ,farin cikin ko wani namiji na gari, kin amsa sunan ki MAR'ATUSSALIHA ,ina rok'on Allah ya saka miki da alkhairi, ya kuma biya ki da gidan aljannah." Kusan Ummu hanifa kasa b'oye farin cikin ta da nuna jin dad'in addu'ar da mijin nata ya mata tayi, a sanyaye ta amsa da "Ameen tare dakai miji na". Abu hanifa yace " ki tashi ki had'a ko tea ne kisha ,amma bana so ki kwana da yunwa". D'an marairace fuska Ummu hanifa tayi kamar zata yi kuka ,bud'e baki tayi zata yi magana yace "nima to ki had'a mun amma bada yawa ba. Hankalin ki ya kwanta?" Cikin jin dad'i ta gyad'a masa kai alamar eh. Nan danan taje ta had'o tea ta dawo ,k'in shan nashi yayi ,yace idan tasha sosai sannan shima ze sha ,seda ya tabbata tad'an sha ba lefi sannan shima yasha ,kafin ya janyo ta jikin shi ,ba shiri bacci yayi awon gaba dasu...
*******************
GIDAN UMMU JA'AFAR.. Abu ja'afar ne ya fito da shirin sa na zuwa office ,d'akin Amaryar shi ya lek'a bacci ,yaga tana yi ,Dan haka beyi k'ok'arin tashin ta ,Jan k'ofar daze yi Safeena ta tashi ,murmushi ya sakar mata tare da cewa "kiyi hak'uri na tashe ki daga bacci ko? Dama zan je aiki ne, na fito naga bakya d'aki na ,shine nace bari in lek'o in gaya miki na tafi aiki" wani dogon mik'a safeenat tayi ,sannan tace "wai har ka shiru ?" Gyad'a mata kai yayi alamar eh ,sannan tace "to a dawo lafiya ,Dan Allah kaja mun k'ofa idan ka fita" ta k'arasa maganan tare da maida kanta ta kwanta. Girgiza kai Kawai Abu ja'afar yayi tare da cewa "to sarkin bacci ,ayi bacci lafiya". Sannan yaja mata k'ofar kamar yadda tace ya nufi d'akin Ummu ja'afar duk da ba yada tabbacin ze same ta a ciki ,haka kuwa akayi ,bata ciki ,sedai ko ina a gyare yake tsaf ,se k'anshin turare da yake tashi ,alamar ta dad'e da tashi, jan k'ofar yayi ya rufe ,ya nufi babban parlour ,anan ma ko ina tasss ,ya gan shi tsaf-tsaf ,kota ina k'amshi na tashi ,yara ya gani suna karya wa akan dining, cikin girmama wa suka gaida Abban nasu ,bilqees ce ta rugo da gudu ta d'ane mai jiki, tana fad'in "daddy ka toke ni" cikin hausar ta da be gama fita sosai ba ,dariya ya mata tare da d'aukan ta ,yana fad'in "to an toke ki ,sarkin rigima ,se Yaya kuma?" Tace "mud'e " wai su suje... Dariya dikkan yaran suka sa ,sannan suka mik'e tsulim ,amamatu ta tattara kayan da suka b'ata takai kitchen ,sannan ta dawo ta d'auki jakar ta ,tace "daddy muje mun shirya "... Shine a gaba su kuma suna bin shi a baya har suka iso haraba..
Ummu ja'afar ya hango ,sanye da 3quater da T-shirt, tana wanke masa mota ,da alama ma ta gama goge wa take yi , " hmmm sannu katafila sarkin aiki" Abu ja'afar yace yana mata dariya ,ita ma dariyar take masa ,sannan ta k'araso ta gaida shi cikin girmamawa ,amsa mata yayi tare da rumgume ta ,yace "I love u" "I love u more" Ummu ja'afar ta bashi amsa tare da sumbatar shi a gefen fuska... Bilqees ta karb'a sannan ya samu ya shiga mota, sauran yaran kuma suka shiga gidan baya, Addu'a ta raka su dashi har suka bar harabar gidan ,sannan ta koma ciki...
Yinin ranar Ummu ja'afar ce zata karb'a girki ,dan haka shirye-shirye ba kama hannun yaro ,dafa wannan sauke wancan ,gyara can goge nan, aikin kenan
Da yamma bayan ya dawo wurin aiki, Ummu ja'afar ce ta fara jin k'arar motar shi da gudu ta fita ,tana fad'in "oyoyo daddy!! Oyoyo daddy" ,aiko nan taja hankalin sauran yaran ,kowa ya fita da gudu ,kan kace ma sun riga ta kaiwa. D'an b'ata fuska tayi tak'i k'arasawa tana wani turo baki a shagwab'e ,yaran kuwa suka shiga yi mata gwalo ,da dariya wai su sun riga ta... Shima Abu ja'afar dariyar yake yi ,daya ga alamar dai tak'i sake fuska se yace wa yaran "oya muje mu Bama mummy hak'uri kun ga tayi fushi" dashi da yaran dika suka rik'e kunne suna fad'in " we are so sorry mummy" ,bata San sanda ta fashe da dariya ba.. Sannan taje ta karb'a jakar hannun shi tare da kaimai duka a Ka fad'a, yace "nadai ji"...
A tare suka k'arasa ciki. A parlour suka taradda safeenat ,tana aikin danne dannen waya, kallon ta Abu ja'afar yayi tare da cewa " honey baki ganni bane?" D'agowa tayi tace "sorry ina duba wani Abu ne. U're wlcm dear" ta fad'a tare da maida kan ta kan screen d'in wayar taci gaba da abunda take....
MUZE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______71-75*
A tare suka shiga d'aki ,da taimakon Ummu ja'afar Abu ja'afar yayi, wanka ,bayan ya fito ,ta bud'e loka ta d'auko masa jallabiya brown ,wacce tasha guga ,se k'amshin turare ne ke tashi. Da mamaki Abu ja'afar ya dubi Ummu ja'afar, saboda shi dai yasan koda ya fita ,ba a wanke suke ba ,balle ayi zancen guga. Duban shi yakai cikin lokan se yaga gaba d'aya jallabiyoyin ma an wanke an goge. Janyo ta jikin shi yayi tare da matse ta a k'irjin shi ,yace "oh no! Yaushe ne wai can natsar da zuciya ta har haka ne ,nidai Dana ga canji base na tambaya ba ,saboda nasan Allah ya bani 'life constructor' a gida no more worries, me canza rayuwar mutum gaba d'aya Dan ba zuciya kad'ai ba. Kinsan Allah? Nifa ina ganin cewa Anya ba ni bane d'an Autan maza ,da nafi ko wani namiji sa'ar mata kuwa? Ya kamata ki tayani murna ko" .. "Umm! To sannu me sa'a. Na tayaka murna sosai bance kad'an ba" Ummu ja'afar ta bashi amsa tare da kaimai dukan wasa a Ka fad'a. Hancin ta ya lakuto ,yana fad'in "Allah ya miki albarka matar aljannah"... " ameen" Ummu ja'afar ta bashi amsa tana sakar mishi wani uban murmushin ta ,me tafiyar da zuciyar me kallon ta. D'an matso ta ya k'ara yi ,tare da rank'wafar da kan shi alamar yana so ya sumbace ta ,d'an b'ata fuska tayi tare da taron hanzarin shi ,shagwab'e fuska yayi tare da cewa "Dan Allah mana" ... Agogon bango ta nuna masa ,tare da cewa "naji an fara kiran sallah na ,kuma na sanka sarai ,idan na biye ka sedai mu Ankara muji an gama sallah, kaje ka dawo tukunna" ,,,, sake marairace mata yayi yana fad'in " Dan Allah mana ,so d'aya fa kawai " tace "to naji ,d'aya kawai" yace " to ki rufe idon ki mana" bata wani tsaya masa musu ba ta rufe ,Dan bata so yayi asarar jam'i. Ai kuwa kamar daga sama taji ruwan kisa-kisai a fuskar ta, kafin ta bud'e ido har ya arce a guje... Dariya abun ya bata ,girgiza kai kawai tayi ,ta fad'a band'aki.
Wanka tayi tare da d'auro alwallah ,tana fito wa sallah ta fara yi ,tana idarwa ta gyara fuskar ta tare k'amsashe lugu da sak'o na jikin ta ,sannan ta nufi parlour Dan ta duba yara. Sallah taga suna yi ,Isma'il ne kawai babu a cikin su, ko bata tambaya ba kuma tasan sun tafi masallaci da Abban shi. K'arar wayar ta data ji ,yasa ta koma d'aki ,kafin ma takai wayar ya tsinke...
Har ta yi dialing zata kira ,taji shigowar Abu ja'afar, tasan ko ba'a ce Bama ze neme ta ,Dan haka ta fasa kiran. Kamar daga sama taji kuwa yana k'wala mata kira "mummy!!!mummy!!" Nan ta cillar da wayar ta fita, a cewar ta banda kiran ubangiji ,bata ga wani kira dayafi kiran mijin ta muhimmanci a gare taba. Taku d'aid'aya ta fito tana yi ,tare da cewa "na'am d'an mummy, me mummy zata baka?" Shafa ciki ya shiga yi alamar yunwa, gaba d'aya yaran se abun ya basu dariya.
Kujera taja mishi alamar ya zauna ,ba b'ata lokaci kuwa ya zauna, gaba d'aya yaran kowa yaja kujera ya zauna ,ita ja tayi zata zauna se kuma ta fasa, da ido ya bita alamar yadai? Tace " Antyn yara bata fito ba Bari inje in kira ta"... D'an b'ata fuska Abu ja'afar yayi tare da cewa "kinga ni malama yunwa nake ji ,idan da tana jin yunwa Aida kinga ta fito" Ummu ja'afar bata ji dad'in yadda Abu ja'afar yace a k'yale safeenat ba, amma ba yadda ta iya. Amamatu ce tace " lah mummy base kin je Bama ,ta sauko d'azu kina d'aki tace ,bacci zatayi kar a tashe ta cin abinci "... Wani ajiyan zuciya Ummu ja'afar ta sauke ,se a lokacin ta samu kwanciyar hankali da sukunin fara zuzzuba musu abincin.
Bayan sun kammala ,amamatu ce ta kwashe komai takai kitchen ta wanke, sannan ta dawo parlour ta zauna. Cartoon Ummu ja'afar ta kun nawa yaran ,me had'e da koyon larabci ,Wanda ake gudanarwa duk a sigar drama. Misalin Tara na dare yaran duk sun fara bacci ,tashin su Ummu ja'afar tayi ,takai su sukayi fitsari suka kwanta ,dawowa tayi ta kakkashe komai tare da tofa addu'a lugu da sak'o na parlour-n. Duban ta ta maida kan Abu ja'afar tace " ka kai bilqees d'akin su amamatu tunda tayi bacci ko?" Tashi yayi yakai ta ,rufa musu abun rufa yayi tare da tofa musu addu'a ,sannan ya kashe musu wuta yaja k'ofar, Daga nan basu zarce ko ina ba se shimfid'ar auren su ,a inda suka jiyar da junan su ainahin abunda ake kira da ZUMAR AURATAYYA... Washe gari ,bayan sun yi sallar asuba ,suka sake komawa bacci basu suka farka ba se tara na safe ,da sauri Ummu ja'afar ta sauko daga kan gado ,band'aki ta fad'a tayi wanka ,tana fitowa ,doguwar Riga kawai ta zuba ,ta nufi kitchen ,kayan kari ta had'a musu, Allah ya taimake ta ta gama cikin lokacin dan tasan 10 nayi Abu ja'afar ze farka ,kasancewar ranar weekend ne. D'akin su amamatu ta zarce ,nan ma bacci ta tarar suna yi ,da d'aid'aya da tashe su sukayi wanka ,har zata saka wa Ramla kaya(me bin bilqees)tace "mummy inji daddyn mu yau kayan sport za'a saka mana ,zamu yi exercise idan ya tashi da safe " gaba d'aya yaran suka ce "eh wllh haka yace mummy" ... Bata k'i tasu ba ,Dan haka ta Ciro musu kayan sport d'in kamar yadda suka ce ,ko wannen su ya shirya gwanin sha'awa, itama d'akin ta ta koma ,wanka ta sake yi sannan ta shirya a cikin kayan motsa jiki kamar dai na yaran. Koda ta fito a parlour ta taradda kowa hadda Abu ja'afar shima cikin shirin shi na sport ,Kanne mata ido tayi tare da jinjina mata hannu alamar tayi kyau, kuma girkin yayi dad'i. Seda ya kalli yaran yaga duk hankalin su na kan abincin da suke ci ,sannan ya maida duban shi wajen ta ,kiss ya mata daga inda yake zaune ya jefa mata ,Wanda saura kad'an ya zubar da shayin daya ke sha... Dariya abun ya bata ,kafin ta k'araso aka cika taro da ita. Bata yi yunk'urin tado safeenat ba ,dan tasan bata saukowa Karin safe ,safeenat ta fifita bacci sama da komai a rayuwar ta.
Bayan sun kammala kar yawa ,ita da kanta ta kwashe komai ta tsaftace wajen ,a haraba ta sami yaran da Abban su ,ya fito musu da k'wallo ,skip roll da sauran kayan wasa suna buga wa... Sosai suke jin dad'in rayuwar su. Misalin k'arfe sha d'aya da rabi ,Aminin Abu ja'afar ya kawo masa ziyara, sosai yaji dad'in yadda ya same su ,kunya Ummu ja'afar taji ,duba da kayan dake jikin ta ,bata jira sun gaisa ba ,ta koma ciki ,seda ta sako hijabi ,sannan ta dawo suka gaisa ,daga nan ta canza wa yaran mazuqunin wasan su ,saboda ta Bama Abu ja'afar da abokin shi Haji Ali damar yin magana ,ciki ta koma Dan da d'ora girkin rana...
A cikin hira Haji Ali ke tambayar Abu ja'afar amaryar sa safeenat. Kasancewar shi babban aminin shi na amana ,da akwai yadda da shaquwa a tsakanin su fiye da tunanin me karatu ,yasa anan take ya zayyane masa matsalolin ta da kuma banbancin ta da uwar gidan sa. Haj Ali ya tambaye sa "to kai Abu ja'afar meya kaika k'ara aure? Bayan ba abunda ka nema ka rasa a gidan ka?" Abu ja'afar yace " wallahi babu ,tsautsayi ne kawai. Nina k'ara aure ne badan na rasa komai a gida na ba ,sedan sunnah ne k'arin auren..."
"To Allah ya bada ladan sunnah " Haji Ali ya fad'a cikin sigar zolaya. Dariya dukkan su suka sa tare da shan hannu...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______76-80*
A gidan Ummu Ahmad kuwa ,tun ranar data yiwa Abu Ahmad batun ko ze auri feena, al-amurran gidan suka fara dai dai ta, ya rage k'untata mata kan wasu abubuwan ,yakan dawo gida ma cin abinci, kai wata sa'in ma fitar idan ba na dole bane yana gida baya zuwa ko ina. Hatta yawace-yawacen shi nabin matan banza kusan ya rage sosai ,badai za'ace ya dena bane ,yanzu khamsussalawat wa baya wuce shi a jam'i ,sab'anin da da kusan kullum akan zuwa masallaci se ya jibgi Ummu Ahmad ,ta kuma yi hak'urin duk wani cin kashe da zata gani ,amma alqawari ta d'aukar wa kanta ,na indai akan k'etara iyakokin Allah ne bazata taba bari zuciyar mijin ta ta Na kasa da sab'on Allah ba ,tayi imani da tun baya d'auka wataran ze d'auka ,ya zama mutumin salihi kamar kowa...
Ummu Ahmad ta kasance bama a iya cikin gidan ta gudunmawar ta ya tsaya ba ,har a waje ma ,takan taimaka da shawarwari akan zamantakewa ,kuma kaga an dace ,saboda zuciya ta linke take da kyaky-kyawar niyya. Sautari akan gayyace ta irin taron walima ,tayi nasiha ga mata tare da sanar dasu wasu sirrika masu rik'e da ginshik'in aure...
Wata safiyar asabar ,tawa yara wanka ,ta tura su makarantar islamiyya ,Ranar ya kasance hutun k'arshen mako ne ,saboda haka Abu Ahmad Na gida be fita ba ,babu abunda ya ragu daga biyayyar auren da Ummu Ahmad ke masa ,hasalima kyautatawar data ke masa k'aruwa yayi ba raguwa ba. Misalin k'arfe goma Na safe ,se ga maman Asdar ta shigo(wata mak'ociyar ta), sallama tayi ,amma seta ji shiru ,jim kad'an Sega Ummu Ahmad ta fito ,fuskar ta d'auke da fara'a tace "maraba lale da maman asdar" da sakin fuska suka gaggaisa ,sannan maman asdar tace "Ummu Ahmad wata shawara nazo nema a wajen ki Dan Allah idan ban takura miki ba?" Ummu Ahmad K'ara fad'ad'a murmushin dake fuskar ta tayi tare da cewa "Kai haba ,menene wannan? Dan Allah ki saki jikin ki ki sanar dani ,insha allahu zan baki shawara gwargwadon yadda zan yi" shiru Ummu Ahmad tad'an yi kafin tace "amma mu shiga daga ciki ko?" A tare suka shiga parlour-n Ummu Ahmad Na gaba maman asdar Na biye da ita a baya. A kan kujera suka zazzauna ,Ummu Ahmad tace "ina sauraron ki maman asdar"... Kamar maman asdar baza tayi magana ba ,se kuma ta fara wa Ummu Ahmad bayani " Ummu Ahmad ina cikin Tsananin tashin hankali. Baban asdar aure ze k'ara ,ni macece me tsananin kishi ,bana tunanin zan iya had'a miji Na da wata macen.
Ummu Ahmad nasha wahala kafin Na saisaita kan gida Na ,shiyasa bana k'aunar wata macen tazo ta rugaza min farin cikin Dana d'au shekara da shekaru ina tattalin ginawa..." Ta k'arasa maganan tare da fashewa da wani kuka me ban tausayi...
Duk bayanin nan da maman asdar take yi a kunnen Abu Ahmad dake kwance a d'aki ,tashi yayi ya zauna, yana jinjina lamarin, kasa kunne yayi yana so yaji amsar da matar shi zata ba ta...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA✍️
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______81-85*
Wani siririn ajiyar zuciya Ummu Ahmad ta sauke ,sannan tace
"Amma in tambaye ki mana? Anya kuwa kina iya bakin k'ok'arin ki wajen sauke hak'k'insa daya rataya a wajen ki daidai gwargwado? Sannan be tab'a yi miki magana ko gyara akan zamantakewar kuba?..." D'an shiru maman asdar tayi kafin tace "to Ummu Ahmad kamar wani hak'k'i kenan? Sannan idan bazan manta ba tana matsa mai akan dan me yake so ya k'ara aure na tayar mai da hankali ,ya tab'a saka ni Na dafa masa abinci ,yace kanna saka magi a ciki ,Abun ya bani mamaki ,amma a yadda ya nuna mun babu a alamar wasa a tattare dashi ,haka naje Na dafa masa abincin ba tare da nasaka magin ba kamar yadda yace, Dana kawo mai ,se ya kuma sakani wai in dafa masa wani irin shi amma wannan in saka maggi, ban musa ba nayi yadda nace ,to bayan Na kammala nazo Na tsaya inaso inga ikon Allah, se yace mun ,inci kowanne ,Dana ci se yake tambaya Na wanne yafi d'and'ano ,nace mai kaima kasan ai abinci Mara maggi baze yi wani d'and'ano ba, bud'ar bakin shi yace ,to in k'addara ace wannan abincin Mara d'and'ano shi kad'ai muke dashi ,ya zamuyi? Se nace mai zamu daure muci ne badan mun so ba ,se yace hakane, to wancan me magin me ze zama harin mu akan shi? Nace mai zamu yi ta kai mai hari ne, yace to idan duk yadda muka yi muka kasa samun shi ya zamuyi ? Nace zamu dage kota halin Yaya muga mun same shi... Ina gama fad'in hakan se yayi murmushi tare da cemun in kwashe abincin dika ya k'oshi ,sannan kuma in gyara girki na,,, yayi shigewar sa d'aki ya barni a gurin Zuciya ta birjik da tarin tambayoyi ,Wanda Na kasa samun amsar su a gurin kowa ,se ma ganin nayi ya maida ni wata sakarya ,nima kawai se nayi facali da lamarin shi..."
Mamakin sakarci irin Na maman asdar Ummu Ahmad ke yi ,itama murmushin tayi tare da cewa "To ai kin riga kin bawa kanki amsa ,wallahi sakaryarce ke kamar yadda kika ce !" Da mamaki maman asdar take bin Ummu Ahmad da ido ,Ummu Ahmad tace "eh! Ke bari in gaya miki wani Abu ,ba wani shiga lungu ,ni'imar ki ce ta wa mijin ki kad'an. Idan kuma kince ba haka ba ,bari in warware miki komai kiji yanzu...
Wannan girkin daya saka ki kiyi ,yana baki misalin kanki ne da auren dayake so ya k'ara. Magana ce ya miki me lauje cikin nad'i. Yace miki idan abinci Mara d'and'ano kawai kuke dashi ya zakuyi ? Kika ce hakuri zakuyi dashi tunda shi Allah ya Baku ,to yana nufin ke kenan ,hakuri yake dake Dan ba yadda ze yi. Daya ce menene hayarin ki akan abinci me d'and'ano? Kika ce ,zakiyi kokarin ganin kin samu chanji ,ki d'and'ana wani sab'anin wancan, to yana nufin ze k'ara aure saboda ya samu d'and'ano awajen ta, daya ce miki idan hakan be samu ba kuma ya za'ayi? Kika ce ,lallai lallai zaki dage kota halin Yaya kiga kin samu wannan abincin me d'and'ano kinci, to wannan kuma yana nufin idan kika sa wasa d'ayan biyu ne ,kodai ki gyara girkin ki ,wato yana nufin ki gyara gonar ki ,ko kuma ya miki DA KISHIYAR GIDA..., ke idan ma kika sa wasa ,se kiyi waje ayi babu ke.... Wannan shine abunda Na fahimta akan matsalar auren ki ,Wanda duk inda zaki je ki fad'i kamar yadda kika zayyana mun ,to idan me hankali da zurfin tunani zaki zayyanawa ,shakka babu abunda Na gaya miki yanzu shi za'a gaya miki..."
Cikin tsananin tashin hankali maman asdar ta d'ora hannu akai ,tare da fasa wani d'an marayan kuka...
Ummu Ahmad bata hanata ba ,saboda a cewar ta ,duk matar data ji hakan, ba kuka kad'ai ba, idan akwai abunda yafi kuka zata yi Dan tausayin kan ta. Seda tayi me isar ta sannan Ummu Ahmad tace". Ki saurare ni dakyau maman asdar, ba kuka zakiyi ba, matuqar kika ce ba zaki yi d'ammaran d'aukan matakan gyara ba ,to wallahi kuka baki ma fara ba, saboda haka ki bud'e kunnuwan ki kiji ni dakyau..."
Tsagaita kukan maman asdar tayi, tana sauraren Ummu Ahmad ... Ummu Ahmad tace " *RAYUWAR AURE DA KIKE GANI SAI DA LURA*
Nasan lamarin mijinki zaiyita baki mamaki ganin yadda kuka shafe shekaru yana nuna miki kulawa cikin kauna, tausayi da Soyayya, amma lokaci guda sai kiga ya sauya ya juyamiki baya gaba daya.
Kirasa me kikayi masa ne, ko me ke faruwa ne haka! Kamata yayi Ki duba baya kiga a bangaren :
-Girki,
-Iya Magana,
-Tsafta,
-Sanya tufafi,
-Matsayin 'yan uwansa gareki, da kuma
-Mu'amilar auratayyar dake tsakaninku.
Shin : Me kikeyine abaya wanda yanzu kuma kika dainayinsa, ko kuma wane abune wanda ba kyayinsa abaya wanda yanzu kike yinsa?
Kisauya halayyar da kike ganin sune suka sanya mijinki ya juya miki baya, Sai kuma ki dogara ga Allah saboda shine mammallakin farin ciki, kicigaba da Addu'a tare da fadawa Allah damuwarki, Tabbas zaki kasance cikin farinciki nan ba da jimawa ba.
Tabbas rayuwar aure sai da lura, saboda cike take da qalubale da jarabawa kala-kala, Amma karki kuskura kije wajan wani malami ko wata malama masu siffar bokaye, saboda kara cusa miki damuwa zasuyi kuma sukaiki subaro akarshe kihadu da fushin Allah nan duniya da gobe Alkiyama.
Allah yakara gyara tsakanin ma'auratanmu kuma yasa mugama da duniya lafiya... "
wani siririn numfashi Ummu Ahmad ta sauke ,kafin taci gaba cewa "to ba wannan kad'ai ya kamata ki Sani ba, ga wani sirrin matso kiji..."
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______86-90*
Matsowa ummu ahmad tayi ta zauna daf da maman asdar tace "kinga TATTALIN MIJI Yar uwa ki bude kunnenki
gawani sirri...
ki samu busheshiyar kubewarki
cokali uku ki matse lemon tsami aciki da madara
kizauna ki shanye ki d'ibi kadan ki hada da
dakekken bagaruwa kiyi matsi dashi na awa daya
sai ki wanke, to fa ranar idan ana kukan agwagwa Na dad'i ,ina me tabbatar miki Baban asdar sai yayi kukan
agagwa a ranar...
Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki
yaji ki a matse kike, ba''a son lokacin da miji zai
kusanci matarsa ya wuce siririf. Don haka ya ke
da kyau mace ta rika kula da gabanta kar ya
bude. Abubuwan da ke matse mace suna da yawa
misali
Bagaruwan hausa.....ana dafa ta da ganyen
magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko
ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumin kaman
30mins a kalla sau biyu a sati...
Kanunfari ana dafa shi a sha da zuma da zafi
zafi ko ki jik'a ya kwana da safe ki tace kisha da
madara da zuma. Ana kuma dafa ta a zauna a ciki
da dumin ta ko a rika tsarki da ruwan ko kuma a
zuba kanunfari a garwashi a tsugunna shi ma sau
2 a sati...
K'wallon mangwaro idan kika fasa zaki ga dan
ciki fari haka, ana busar dashi a daka a kwab'a da
zuma arik'a matsi da shi bayan isha'I idan zaki
kwanta bacci ki wanke, ko kuma ki dafa d'an cikin
da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a
ciki shima a kalla 3x a sati...
Almiski fari ko ja ki daka kanunfari ki tankad'e
yai laushi sai ki kwab'a da miskin da man zaitun, ki yawaita amfani dashi ya na matse mace sosai, kuma yana dawwamar da hq kullum cikin kamshi....yana gyara macen da ta
haihu sosai musamman macen da jinin haihuwa ya dauk'e mata, ki fara amfani dashi har kiyi ar'bain...
ME KIKE NEMA BAYAN
SO WAJEN MAIGIDA??? Yar'uwata kigwada
wannan wallahi zakisha mamaki indai
NI'IMA ne saidai kifadama wani.
Da farko ,Ki nemi
Dabino wanda ba busasshe ba (lubiya) da, Kankana mai yashi. kici dabinon sosai sai ki sha
kankana daga baya.ki aikata haka kamar bayan
La'asar...
Na biyu ,Kisami man Hulba da pure madara
kota shanu ko peak ta ruwa sai ki hada ki aje yayi 1hr kafin ki kwanta, Idan zaki kwanta sai kisha,
ki tsaya kamar 3mins saiki kwanta...
Na uku, Kisami
lalle 1cup kisa a ruwa ki dafa, sai kijuye kisa a baho kizauna Wallahi kam zaki matse...
Ko kinsan
tsarki da Sabulu na iya causing cancer agabanki?
Musamman detol dominshi yana kashe kwayoyine
agaban macce damasu amfani da marar
amfani...kisami KALTUFA(brown venigar) kirik'a
tsarki dashi... Ba sena ce miki komai akai ba ,nasan kema zaki bama wata labari...
SANNAN ABUBUWAN DAKESA MACE
TAFITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA: Na farko akwai
- RIKO
Riko shine idan an aikatamata wani laifi kabar
abin aranka batare da kayafe ba.
Uwargida kada kizamo mai riko domin hakan ba
karamin jamaki matsala zaiyi ba, musamman idan
mijinki nada saurin fushi . Saboda haka idan abu
yafaru mudinga hakuri domin mata ansanmu da
hakuri da juriya idan akai abu to dazaran ya
wuce to amaida komi ba komi bane domin
aljannarmu tana karkashin su sai sun d'aga zamu samu shiga. Mata mudinga hakuri aduk lamuran mu
sai muga mundace..
Na biyu:
YAWON MITA
Yar'uwa kar zizamto cikin mata masu yawan
mita a gurin miji,
Abu baya wucewa ayita dawo da magana baya
wanan zai haddasamaki matsala domin zaki fita
ranshi. Idan abu yawuce to ayi hakuri abarshi
adaina tuna baya.
Na ukku:
FUSHI
Uwargida kar ki zama mai yawan fushi ko nuna ma miji kincika fushi, Karkimanta Allah da kansa "yace yanatare da
masu hakuri"shin bakison Allah yazamto yana
tare dake kowane lokaci?...
Yar'uwa kisama ranki hakuri, fushi banaki bane
domin karkashin wani kike kowayace zomu zauna
zomu sab'ane...
Hakuri shine ribarmu.
Na hud'u
RASHIN IYA GIRKI:
Da anxo maganar girki sai naji tsoro tare da jin
kunya
Haba yar'uwa yakamata ace iyayen mu
nakoyamana girki, wallahi samun yar aiki ba gata bane
Ina gatan yake kina can kwance yar aiki na saye
zuciyar mijinki da dad'ad'an abinci.
'Yar uwa mutashi tsaye mukoyi girki
kodan saye zuciyar miji
Domin namiji nason matar da ta iya girki
Zakiga namiji na gayyato abokanai zuwa gidan
shi don suci abinci saboda yasan bazata bashi
kunya ba, amma idan baki iyaba fa zai fara tunanin kara
aure wato yayi maki KISHIYA
Hmmm mata mu gyara..
Na biyar
'KAZANTA
Uwargida ayi tsafta kodon lfyr jikinki,
karki manta tsafta nadaga cikin addini , idan ba tsaftar yazakiyi ibada?
Sannan kisani tsafta nasa miji yasoki sannan yaji
bayada kamarki. zakiga kowane lokaci yana
manne dake yana shak'ar k'amshinki
Idan kuwa bakida tsafta, da yabaki kudin cefane ,baza ki k'ara ganin shi ba ,sai dare domin koyadawo ba
abinda zaigani sai b'acin rai, har ki dinga ganin cewa KO
ya daina sonki ne, aa ba daina sonki yayi ba k'azantarki
tajawo maki...
Sanan kisani k'azanta itama rukuni ce ta mabud'in k'ara aure,
wato yayimaki kishiya.
Pls kozakiyi chatting yazamto kin gyara ko ina ,sannan yazamto kema kingyara jikinki da na yaranki ,kuma idan mijin ki yadawo kibashi kulawa
abar cht.
Na shida
KULA DA SHINFIDAR MIJI:
Mata muna sakaci wajen bawa miji hakkinsa
kinaso amma kitsaya gulma wai jan aji ,ina ajin yake ?bayan yagama saninki lungu lungu ,ba inda
baisaniba ajikinki,
To wallahi ki gyara ki dinga bashi hakkin shi
yadda yakamata wanan shi zaisa mijinki yasoki
kuma ki mallakeshi...
Ummu Ahmad tace "to da wannan ,se ince miki Allah ya bamu sa'ar cinye jarabawowin gidan mazajen mu, Dan ko wani gida da kike gani ,akwai hayak'i a cikin shi ,sedai kawai ace icen wani gida yafi Na wani gida hayak'i ,kuma iya bushewar iccen ki ,iya yadda wutar murhun ki ze kama. Saboda haka ,kije ki gwada wannan ,sannan kici gaba da hakuri, ki sa gaba a lamarin ki ,kuma ki iya bakin ki ,ba kowa zaki tunkara da matsalar gidan kiba ,menene matsalar gidan ki shine sirrin auren ki. Ina kuma tabbatar miki cewa ,indai wannan matsalar ce zata sa mijin ki k'ara aure ,to matuqar kika kiyaye abubuwan Dana fad'a miki ,mijin ki shida aure ,to sedai idan Dama me ra'ayin k'ara auren ne, idan kuwa Dan abunda ya ya shafi abubuwan da muka tattauna ne ,to insha Allahu rabbi labari ze sauya... "
Godia sosai maman asdar tayi Ummu Ahmad, cike da murna da farin ciki tabar gidan...
Abu Ahmad dake d'aki yana jiyo irin baza haja da ruwan fasahar da matar shi take ta bazawa, tun yana zaune har ya tashi tsaye. Wani uban gumi ne keta wanke mai fuska ,kan kace ma ya jik'e sharkaf da zufa. Tsamo-tsamo yayi ,kamar wani figaggen zakara ,ya kasa sukuni ,a lokaci daya kuma ya rasa meke masa dad'i a duniya. Se kai da kawowa yake a tsakar d'aki. Sallamar Ummu Ahmad ce ta k'ara daskarar dashi ,gaba d'aya jin yayi ya kasa d'aga k'afar shi ko nan da can. Cikin tsananin damuwa Ummu Ahmad ta tambaye shi lafiya? Saboda yadda duk taga ya daburce.
K'asa yayi dakai ,lokaci daya zuciyar shi ta tsananta bugawa. A karo Na farko kenan da kwarjini da haibar Ummu Ahmad ta dasu a zuciyar Abu Ahmad...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______91-95*
Wani abun mamaki wai se ga hawaye shahhh! Na kwaranya daga idanun Abu Ahmad, kaida ka gani kasan hawayen takaici ne da bak'in ciki. Cikin hanzari Ummu Ahmad ta k'ara so har inda yake tsaye ,dafa shi tayi hannu bibbiyu ,tana share masa hawayen sa ,a lokaci d'aya kuma tana tambayar sa meke damun shi? Cikin sanyin murya Abu Ahmad ke magana Wanda Ummu Ahmad bata tab'a sanin ya iya shiba ,yace "Ummu Ahmad kiyi wa girman Allah da darajar muhammadur rasulullah s.a.w ,kiyi wa ,ki yafe mun duk abunda nake miki ,wallahi nasan Na zalunce ki ,hak'k'in ki baze tab'a bari inyi gaba ba ,Na k'untata wa rayuwar ki ,Na tagayyara miki rayuwa akan San zuciya irin nawa ,Na ci zarafin rayuwar auren mu ,idan Na mutu a wannan halin bansan me zanje in gaya wa mahallici Na ba. Wallahi Ummu Ahmad nayi nadamar sanin ki danayi a rayuwa ta ,balle har ace Na aure ki ,saboda ban cancanci zama mijin kiba ,ban cancanta ba. Ummu Ahmad ke ba matar wulaqantaccen mutum iri Na bane ,ke matar Wanda yasan darajar mace ce ,ya kuma San hak'k'ok'in mace ,sannan ya tanadi duk wace hanya Na kyautata mata, yake adawa dame k'untata mata ,sannan ya zama ita ta zama shi... Ummu Ahmad Na miki alqawarin duk abunda nake wallahil azim Na dena saboda Allah kuma saboda ke ,Na miki alqawarin zan zama mutumin kirki daga yau har k'arshen rayuwa ta, zan watsar da duk wani aikin ash-sha Dana ke yi. Nayi imani ba kowace mace ba zata iya hak'urin da kika yi dani, duk wani k'unk'atatawa da cin zarafi Na miki shi ,saboda ki gaji dani Dan kanki ki nema in sawwaqe miki ,amma kin cinye wannan jarabawar. Ummu Ahmad zan kasance duk yadda kike so, nidai Dan Allah badan ni ba ki yafe mun ,ba kuma Dan hali Na ba ,Dan nasan ba nida halin kirkin dahar za'a iya mun afuwa Dan shi.... Abu Ahmad ya k'arasa maganan yana kai guiwowin shi biyu k'asa tare da fashewa da wani kuka me tsima zuciya. Ummu Ahmad itama fashewa tayi da kukan, ta rasa ma kukan me take yi ,shin najin dad'in Allah ya karkato da zuciyar mijin ta zuwa gare shi, ko kuwa bak'in cikin yau mijin ta be gurfa ne a gaban ta yana rok'on ta gafara? Ba shiri itama takai zuk'enna ,hannun shi ta rik'o tana girgiza mai kai tare da cewa "bakamun komai ba Abu Ahmad, wllh ni ban tab'a qullatan ka arai Na ba ,ban tab'a kwana da bak'in cikin wani arai ba balle mijina ,Allah zaka ci gaba da rok'on ya yafe maka laifukan daka masa ,amma ni baka mun komai ba, idan da har ma za'ace kamun lefi base ka rok'e ni yafiya ba ,Na Riga Dana yafe maka duk wani abun da kamun dama Wanda zaka mun ,wannan Abu ne Dana d'aukar wa kaina tun kafin ma in aure ka, saboda haka ka tashi ,ka dena mun asarar hawayen ka ,saukar hawayen ka a gare tamkar saukar azabar Allah ne a gare ni ,ka taimake ni ka rufa mun asiri ,ka tashi Abu Ahmad".. Ta k'arasa maganan tana me fad'awa jikin shi had'ida k'ara fashewa da wani marayan kukan, Shi kanshi Abu Ahmad d'in kukan yake ,rumgume ta yayi tsamm a jikin shi kamar wani ze sace mishi ita....
***************
Gidan Ummu Habitat. Fito wa tayi cikin shirin ta Na zuwa gida dubo ummi maryam(mahaifiyar su kenan) saboda ta kwana biyu bata je ba. Sashen hajia saro(uwar mijin ta) ta shiga ,da sallama ta shiga parloun ,fuskar ta a sake. D'an gurfana wa tayi ta gaishe ta cikin girmamawa "Hajia ina wuni?" Fuske a gimtse hajia saro ta amsa da "lafiya. Gidan wace uwar kuma zaki naga kin shiryo da wata uwar jaka kamar limamiyar wanzamai?..." Bata damuwa da tambayar da Hajiya saro tayi mata ba ,Dan inda sabo ta saba. Murmushi tayi tare da cewa "zani in gano su Ummi maryam ne ,kwana biyu ban lek'o su ba". " yo da se akace dole duk kwana biyu se kinje ganin su? Tukunna ma wa kika sanar kafin ki shirya fitan ?" Hajiya saro ta tambaya. Ummu habibat tace "Ah dama Na tambayi Aba habibat kafin ya fita, kuma da safen Na shigo da niyyan idan mun gaisa se in sanar dake ,se Na tarar kina bacci shiyasa". Cike da gadara hajiya tace " eh lallai wuyan ku ya isa yanka dake da shu'aibun. Shi har yaushe yayi k'arfin guiwar daze zartar da wani hukuncin ba tare da ya sanar dani ba? Yaushe ma har wani ne ya isa yace ayi ko a bari a gidan nan Wanda ba ni nace ba?,,, to wallahi ki kiyaye ni uwar Habiba ,Ku fita daga ido Na in rufe ,shi kuma ze dawo ya same ni ,zakka Mara zuciya ,Wanda aka shanye. Nace ai ba wani sha'anin bane a can gidan naku ko?" Ummu habibat tace "eh babu komai ,dama zan je gaishe sune kawai ,saboda kwanaki Ummi maryam bata ji dad'in jikin nata ba ,har ta warke ban samu naje ba ,lokacin kin tura ni jinyar matar baba sama a kano"...
K'ara d'aure fuska Hajiya saro tayi sannan tace " to ai tunda ba komai ki hakura da zuwan kawai se wani lokacin. Yanzu ki tashi ki mun d'umame gashi can a fridge, idan kin gama kuma ,naji kamar warin b'era a uwar d'aka Na, se ki fiffito da kayan ki duba..." Ummu habibat ta amsa da "toh Hajiya" . a sanya ye ta mik'e tsayi jiki ba k'wari ,har zata fita se kuma ta tuno da iccen ta Na girki ya k'are ,dawowa tayi ta zauna tare da cewa "Hajiya Na manta ma icce Na ya k'are ,dame za'a miki d'umamen?" K'ara had'a girar sama da k'asa Hajiya tayi kafin tace "kije kitchen d'ina ni ai inada gas ,a cike ma yake jiya nasa shu'aibun ya ciko. Ki tashi kije ,zan kira shu'aibun in sanar masa iccen ki ya k'are ,ya sa a kawo..."
"To " shine abunda Ummu habibat ta iya cewa ,sannan ta tashi ta fara aiwatar da aikin da hajia ta saka ta...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
*_Page_*
*📖______96-100*
Misalin k'arfe takwas Na dare ,su habibat sun dawo daga makarantar dare, aka samu tsautsayin mota ya kad'e k'aramar k'anwar su FA'IZA, cikin hanzari me motan ya fito a gigice, mutane ne suka taru a inda abun ya faru, k'ok'arin kaita asibiti ake yi ,anan wani dattijo yake sheda musu ai ma kamar yarinyar ta rasu, koda aka duba kuwa Allah yayi mata rasuwa. Iso 'yan uwanta suka yi wa me motan zuwa gidan su. Su Habiba ne suka shiga suka sheda wa mahaifiyar tasu abunda ke faruwa ,,,,duk yadda me motan yaso yaga Ummu habibat ya bada hak'uri tare da jajen abunda ya faru, ummu habibat k'in fitowa tayi ,se ma tura mai d'aya daga cikin yaranta tayi ,tace ace masa me gidan ta baya nan ,yayi hak'uri ya dawo zuwa gobe da safe idan Allah ya kai su... Mamakin duniya ne ya cika me motan ,haka ya tafi tare da jinjina lamarin.
Habibat ce ta d'auki gawan k'anwarta takai cikin gida. Ba kad'an ba mutuwar ta tab'a ummu habibat, tayi kukan ta me Isar ta sannan ta koma yiwa fa'iza addu'an Allah yasa me ceto ce ,saboda k'aramar yarinya ce ,taso ta kira Abu habibat ta sanar dashi abunda ke faruwa, se kuma ta duba agogo ,taga tara ta gota ,tasan duk inda yake war haka yana hanyar dawowa gida ,ta kuma yi tunanin yana kan k'arfe kada garin gaya masa mutuwar yaje wani abun ya same shi a hanya ,Dan haka ta barshi bata sanar dashi ba ,tana jiran dawowar sa. A ranar Aba Habibat be dawo da wuri ba ,Dan kusan se sha biyu saura ya shigo gida. Dikkan yaran sun yi bacci se ita kad'ai. Ummu habibat bata fasa tarbon mijin ta kamar yadda ta saba ba, a wannan Daren Aba habibat ya dawo da wani matsanancin sha'awar matar shi ,Wanda ko abinci hakan be bashi daman ci ba ,muhimmancin haka yasa ummu habibat ta amsa kiran mijin nata zuwa shimfid'ar sa, wannan dalilin ya katange ta daga sanar dashi abun da ya faru. Se da asuba bayan ta tabbatar ta gamsar da mijin ta ,tukunna cikin hikima tace "Aba habibat ,yanzu ka k'addara cewa wannan gidan da muke ciki aro aka baka, kuma kafin a baka an tabbatar maka za'a iya karb'a ako wani lokaci, to ana zaune kwatsam bayan an bari ka saba da gidan ,se ga me gidan yace yana buk'atar gidan shi ,shin zaka fita ka bashi?"... Da mamaki Aba habibat ke kallon ummu habibat yace " to ai inbanda abunki ,kince fa aro aka bani ,to meyasa bazan bashi ba duk lokacin daya buqaci abun sa, sedai kawai sabo ,zanyi kewar gidan saboda Na saba dashi sosai ,amma zan rok'i Allah ya bani Wanda yafi Wanda Na rasa..." Murmushin jin dad'i ummu habibat tayi tare da cewa "nagode Allah daka fahimci abun aro ba naka bane ,da wannan nake sanar dakai Allahn daya bamu fa'iza yq karb'e ta ,ina nufin Allah yayi mata rasuwa a Daren jiya. Ban sanar dakai ba Na farko dare yayi ,bansan wani yanayi zaka shiga ba, Na biyu daka dawo nayi k'ok'arin sanar dakai amma bazan iya juya wa buk'atun ka baya ba. Idan baka manta ba ,lokacin manzon Allah s.a.w hakan ya faru da ummu sulaim(mahaifiyar Anas bn malik) da mijin ta Na biyu data aura bayan mahaifin Anas bn ya rasu, lokacin da d'an ta ya rasu ,kuma lokacin da manzon Allah yaji hadisi yazo mana cewa 'Annabin Rahma cewa yayi Allah ya albarkacin abunda suka samu a Daren jiya' ma'ana har sun samu rabo. A koda yaushe mutanen mu idan aka bada tarihi se kaji suna cewa ai lokacin manzon Allahs.a.w daban ,babu banbanci tsakanin lokacin mu da nasu ,sannan zamu iya maida kawunan mu kamar nasu koma mu fi su ,abun yarjewar allah ne ,kawai lalacewar zukata da zamani ne...To shine nayi k'ok'arin koyi da magabatan mu inga nima kozan iya. Amma Dan Allah kayi mun afuwa idan hakan be maka dad'i ba"... Ta k'arasa maganan tare da fashewa da kuka...
A maimakon ranshi ya b'aci se taga yana murmushi ,a lokaci d'aya kuma yana share hawayen farin ciki ,yace " Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama
yana cewa "Idan kaga zuciyarka bata k'yamar sab'on Allah, kuma bata samun nutsuwa da jin dadi lokacin da take aikata wani aikin alkhairi, to kasani lallai akwai wani bala'i a cikin zuciyarka, kayi gaggawan gyarata.
Idan kuma kaga zuciyarka tana farin ciki da aikin alkhairi kuma tana aikatashi, sannan tana k'yamar sabon Allah kuma tana nisantarshi, to kasani lallai zuciyarka nagartacciya ce amintacciya".
شرح صحيح مسلم ١/٣٠٠
Ke nagartacciya ce ummu habibat ,hak'ik'a ke macece ce ta gari. IDAN KA SAMU MACE TAGARI KA GAMA SAMUN JIN DADIN DUNIYA
Manzon Allah S.A.W yace: Duniya gidan jin dadi ne amma mafi Alheri da fifikon jin dadin duniya shine ka yi dacen samun mace tagari
WACECE MACE TAGARI??
Annabi S.A.W👏🏻 yace: Mace tagari itace wacce idan mijinta ya bata Umarni sai ta bi, idan yayi rantsuwa sai ta kubutar da shi daga yin kaffara, idan suna tare idan ya kalleta sai kyawunta ya sashi farinciki da sanyin ido a gareshi. Shiyasa idan ka samu mace tagari to kawai ka nemi jin dadin lahira domin na duniya kam ka samu, idan ka samu mace me irin wannan kamalar a wannan zamanin toh wallahi ka riketa dakyau ba na wasa ba. Ummu habibat hak'ik'a ke alkhairi ce a gare ni ,wallahi banida tantama ,haufi ko shakku akan yi ,ba tun yau ba kika samu dikkan yadda ta ,banga abunda zakiyi ki b'ata mun rai ba"... Shiru yad'an yi ,sannan yace "ina gawar fa'izan take?" Tace yana d'ayan d'akin mu Na suturce ta." A tare suka shiga ,ya bud'e mayafin yagan ta ,ba wani rauni taji sosai ba ,kawai zuwan ajali ne. Addu'a sosai suke yiwa 'yar tasu ,kafin ya wuce masallaci ,daga can yake shedawa mutane jana'izar k'arfe 9 Na safe. Duk abun nan da ake yi hajia saro bata nan ,saboda a ranar taje gidan k'anwar ta da d'an ta ya samu kariya ,saboda haka acan ta kwana. Ba ita ta dawo gidan ba se bayan an gama komai. Mamaki ne ya kamata lokacin data zo ta tadda gidan tinjin da mutane ,ta shiga ciki ,nan ma haka ,b'angaren ta ta shiga ,sannan ta kira habibat ,tana tambayar ta me yake faruwa ,anan take sheda mata rasuwar. Nan tasa aka kira mata ummu habibat, masifa ta fara yi inda take shiga bata nan take fita ba. Tunda Aba habibat yaga shigar ta yasan abunda ze biyo baya kenan ,Dan duk halin ta ba Wanda be Sani ba ,mugun halin ta yasa duk cikin 'ya'yan ta ba Wanda yaji ze iya zama da ita ,shi kad'ai ne me hakuri a cikin su ,kuma shine Autan su ,sannan duk a cikin 'ya'yan shine me binta sauda k'afa, wannan ne ya bata daman cin kanshi akan shi...
Koda ya shiga kai tsaye sashen mahaifiyar tashi ya wuce, ya tarar se masifa take zazzagawa ummu habibat, ta kanta Na k'asa, wai Dan me baza'a kira a sanar mata ba ,saboda be ita ta haifi fa'izan ba? To ai idan bata haifi fa'iza ba ta haifi uban fa'iza. Aba habibat Be tari hanzarin taba ,seda ya bari ta kai aya ,sannan ya fara zayyana mata duk abunda ya faru ,da irin hak'urin da matar shi da 'ya'yan shi keyi da ita. Daga k'arshe yace komai yazo k'arshe ,Dan ayau be se gobe ba ze kwashi iyalan shi su tare a sabon gidan da ya Gina. Kuka hajia saro ta fara yi a lokaci d'aya tana me nadaman abunda ta aikata. A ranar kuwa Aba habibat ya tashi ,suka koma sabon gida ,inda ze samu damar kula da iyalin sa yadda ya kamata, Dan aganin shi ci gaba da zama da mahaifiyar shi ba inda zata kai shi se wuta...
Tun daga wannan lokacin kuwa suka fara jin dad'in rayuwar su. Sama da shekaru sha shidda zuwa sha bakwai ,Ummu habibat bata San me ake cewa dad'in aure ba da 'yan cin kai se a wannan lokacin...
MUJE ZUWA
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
✨✨✨✨✨✨
🧕🧕🧕
*AN-NISA'U AHLUL JANNAH*
🧕🧕🧕
*_✨(base on true life story)_*✨
*_✨INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
*_Writing by: Sadiya Sidi Sa'id (Sidiya)✍️_*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*_Page_*
*📖______101-105*
BAYAN SHEKARA D'AYA. Sauyi tare da alkhairi ya wanzu gaba d'aya a gidajen bakwai ,kai bama su kad'ai ba ,sanadiyyar su da yawan mataye suka samu sawaba a gidajen auren su...
GIDAN UMMU MUS'AB :
Abu mus'ab yaji sauk'i sosai da taimakon Allah da kuma kulawar daya ke samu a wajen ummu mus'ab. Ya saki Amaryar shi data yi sanadiyyar shigar shi wannan halin, Wanda ummu mus'ab bata so hakan ba ,gani ba suda wani k'aramin yaro a gaban su ,duk sun aurar da 'ya'yayen rik'on su ,yasa suka tarkata suka koma k'asar TURKISH, a inda yaci gaba da gudanar da kasuwancin shi ,sosai suke jin dad'in rayuwar su ,Dan koma wa sukayi tamkar yara 'yan shekara ashirin da biyar-biyar. Duk hutun k'arshen shekara kuma sukan zo ganin gida najeriya...
GIDAN UMMU HAFSAT :
Ta aurar da Hafsat da Saudatu, a inda Allah ya dubi kyaky-kyawar zuciyar ta ,hak'uri da kuma juriyar ta ,ya karkato mata da zuciyar Abu Hafsat ,ya gane gaskiya ,ya kuma tuba ya dena duk abunda yake yi. Suma sosai rayuwar tayi musu mazak'wai...
GIDAN UMMU JA'AFAR :
Duk iya bakin k'ok'arin ta tana yi wajen kyautata wa mijin ta ,bata bada wani k'ofa da Abu ja'afar ze ga kazawar taba. Safeenat jin tayi gaba d'aya gidan Abu ja'afar ya koma mata kurkukun kafirai ,gaba d'aya ta hana kanta sukuni, Ummu ja'afar kuma tayi iya wayin ta ganin ta wayar Mata dakai akan zamantakewa ,amma ina safeenat bata ga wajen zama ba a gidan Abu ja'afar ,da kanta ta nemi ya sawwaqe mata ,taje ta nemi daidai ita ,Da farko seda Abu ja'afar ya tambaye ta ko ya mata lefi ne? tace ko d'aya, yace ko wani Abu ya had'ata da ummu ja'afar ne? Nan ma tace a'a. Anan take sheda masa bazata iya ci gaba da zaman gidan shiba ,Dan ummu ja'afar ta mamaye ko ina a gidan ,Dan haka da ita yafi cancanta ya zauna. Shida kanshi yasan dole ta nemi tafiya ,dan ko kad'an ba zata iya yin koda kwatankwacin abunda ummu ja'afar take masa ba, kuma shima yayi Dana sanin k'ara aure ,se daga baya ya tabbatar lallai mata ba d'aya bane kuma suna suka ta ra. Alkhairi ya mata ,sannan ya sawwaqe Mata kamar yadda ta neme... Tun daga lokacin be k'ara marmarin sha'awar aure ba, rayuwar su taci gaba da tafiya cikin aminci da k'aunar juna...
GIDAN UMMU HABIBAT :
Tun da suka bar gidan hajia saro ,rayuwa ta sauya musu ,Aba habibat ya samu damar kyautatawa matar shi yadda ya kamata, rayuwar su Dana yaran su gwanin sha'awa,,,,ita kanta hajia saro ta canza ,ta zamo UWAR MIJI ta gari ,duk ta zubarda makaman yaqinta, seda su ummu habibat suka d'aga ,sannan ta fara ganin ranar ta da amfanin ta...
GIDAN UMMU AHMAD :
Rayuwa ta dawo sabo ,idan kaga Abu Ahmad a yanzu kai kace bashi bane bahagon mutumin nan a da, ya zama mutumin kirki ,ya zubarda duk wani sab'on Allah da yake a baya ,shida be damu da sallar jam'i ba ,se gashi yanzu sallar jam'i guda biyar bata wuce shi, koda yaushe yana gida ,matuqar kaga ya fita ,to aiki yaje ko masallaci ,tsakanin magrib zuwa isha kuma yana d'aukar darasi a masallaci ,wannan kuma ya samu ne lokacin da yaji limamin su Na wa'azi yace
" TA YA YA?
Ta ya ya baka neman ilmin sanin Ubangijinka (Allah) baka da malamin da ka ke sanin addininka baka sauraren Karatukan malamai ba ka zuwa ka ji wa'azi sannan baka iya buɗe Alqur'ani ka karanta, baka san hadisan Annabi ba. Kuma kace zaka gudanar da rayuwar ka yadda ya kamata?? Duk zurfin ilmin ka na boko in dai ka rasa wancan to akwai matsala, dole gidadanci da rashin waye wa na addini yake shiga cikin al'amuranka, ka sani ko baka sani ba. Sannan abu mafi tsoro dak'ushe wan imani..
Allah Ta'ala ya tsare ya bamu ilmi mai amfani ya gafarta mana."
Wannan se ya k'ara zama sanadiyyar d'aukan matakin gyara. Idan ya dawo daga masallaci bayan yaci abinci ya huta ,se kuma ummu Ahmad ta tusa mai daga inda malam ya tsaya. A haka ,kan kace me Abu Ahmad ya samu wayewa ta addini ,a inda har yake adawa da sab'on Allah. Rayuwar su kamar an musu d'auraya da ma'ul wardi haka ta koma sabuwa fil...
GIDAN UMMU HANIFA :
Ita dama babban matsalar ta Abu hanifa ,saurin fushi ,da rashin ganin gwanin ta ,ga be iya yabon mace ba ,amma a hankali ta sauya masa rayuwa ,dukda tasha bak'ar wahala kafin ta samu kanshi ,amma a haka ta jure tayi hakuri har Allah ya warware komai ,suka dawo suna zaman su lafiya. Tun randa yayi wannan zazzab'in yaga yadda matar shi ke tsananin nuba masa qauna ,to daga ranar ba shiri ya koyi yadda ake zaman jin dad'i da matar sunnah. Suka dawo kamar yadda ko wasu ma'aurata Na gari ke zaman su cikin aminci...
SAI GIDAN AUTAR SU(UMMU SADIQ DA ABU SADIQ)
Shakka babu misalta irin farin cikin dake wannan gida b'ata lokaci ne ,zaman lafiyar su da yadda suke gudanar da rayuwar auren su har ya zama abun kwatance da koyi a yankin da suke... Kullum idan ummu Sadiq zata gitta Abu Sadiq Na zaune se kaji yana fad'in "MARABA DA MATAR ALJANNA"... Bayan shekara d'aya da rabi da auren su Allah ya azurta su da samun k'aruwa Na haihuwan SADIQ. Gida se ya k'ara dad'i A inda Abu Sadiq ke wa ummu Sadiq laqani da 'MADUBIN GIDA'...
*_____________________*
ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN. DIKKAN YABO DA GODIA SUN TABBATA GA ALLAH S.W.T ,DAYA BANI DAMAR FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA, NA KUMA GAMA LAFIYA . KURAKURAN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MUN, ABUNDA KUMA NA FAD'A DAIDAI ALLAH YA BANI LADAN SHI...
KUN DAI JI YADDA LABARIN YA KASANCE ,FATAR KUMA KUN D'AU DARASI.
WATO ABUNDA NAKE SON MATA MU GANE SHINE, WALLAHI BA NAMIJIN DA BAZAKI IYA CANZAWA BA ,SANNAN KUMA KO WACE MACE SARAUNIYAR GIDAN TA NE ,DUK KUMA YADDA GIDAN KI YAKAI GA LALACEWA ,MATUQAR ZAKI YI HAKURI ,KI KUMA D'AU MATAKAN GYARA WANDA ADDININ MUSULUNCI YA KOYAR DAMU ,TO KI K'ADDARA MATSALAR KI TAKAU ,SE KUMA KI DAGE DA ADDU'A ,SABODA MANZON ALLAH S.A.W YACE " ADDU'A'U SAIFUL MU'IMIN". WATO ADDU'A SHINE TAKOBIN MUMINI...
HAK'IK'A NAGA TARIN MASOYA ,NA KUMA JI SHARHI IRI DABAN - DABAN. SEDAI INCE ALLAH YABAR QAUNA. DOMIN SHAWARWARI KO NEMAN K'ARIN BAYANI AKAN WASU MAGUNGUNAN DAKE CIKI ,DAMA WA'YANDA BASA CIKI, ZAKU IYA NE MANA AKAN WANNAN LAMBAR 09064458468 ,INSHA ALLAH ZAN AMSA KU GWARGWADON SANI NA...
ANAN SE INCE ,KU TARA A LITTAFI NA ME ZUWA NAN BADA JIMAWA BA INSHA ALLAH...
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
MA'ASSALAM...🤝
0 Comments