ADDININA HAUSA NOVELS COMPLETE

 *ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*NOTE* *labarine ba wanda aka saba yiba, akan addininmu da yadda ake hukunci da alqur'ani da sadaukarwa zai taba zuciyar duk wani mai imani, don Allah ba mace ba namiji ina rokon kowa ya karanta inka karanta ka turawa wasu inaso ya bide duk social media da kukasan ana kai novels cos amfaninmu ne ku daure ku fahimci labarin*. 


*Ban yarda wani ko wata ta juyamin labari ba ko ta dauki wani abuba ko a siyarmin da labari ba tare da izinina ba*

09030953294.

*TRUE LIFE STORY*


*YA ALLAH INA ROKONKA KA BANI DAMAR ISAR DA SAKON DA NAYI NIYA, KA SAMIN ALBARKA A CIKIN WANNAN RUBUTUN NAWA KASA YA ZAGAYE KO INA, KUMA MU AMFANA DA DUK ABUNDA KE CIKI, NA FARA DA SUNANKA BISMILLAHI RAHMANUR RAHIM*


*SADAUKARWA GA DUK KOTUN DUNIYA MAI HUKUNCI DA ALQUR'ANI DA HADITH YADDA SHARI'A TA TANADA*


1


Bakajin komai sai ihunsu da suke magana da caca a wurin ga kwalaben giya a warwatse ga mataye da keta yawo da shigar banza duk wani rashin da'a da laifi marar kyau na hangosu a wurin wasu zina ce sukeyi wasu karta wasu shan abubuwan maye, wani babban mutum na hango wanda shekarunsa ba zasu gazawa 40 ba jin an kirasa da suna *JABEER* yasa na gane shine sunansa daka gansa kaga usulin bafillace kyakyawa da Shi saidai duk bakinsa yayi bakikirin saboda shayeshaye kwalbar giyarsa ya daga yana kwankwada yake magana cikin maye"akwai dan iskan daya isa yace bani na cinye kartar nan ba? ". 


Dariya suka kwashe da ita suna fadin"waya isa yaja dakai, makiyanka takalminka duk wanda yaja dakai to tabbas wahalarsa da rashin sa'arsane suka tsaya". 


Shima dariya yayi sosai yaja wata budurwa dake gefansa ya rungumeta yayi cikin wani daki da ita. 



Kyalanta ta dauka tare da yanawa saman doguwar rigar tata baka ta koma balarabiyar tata Jakarta ta saba ta dafa wata kyakyawar yarinya da bazata wuce shekara 10 ba tace" *Khadija* ki tsare gida bazan dadeba zan dawo kinji"


Ko kadan khadija bata damuba tunda dama bashine karona farkoba da iyayen nata ke barinta a gidaba, saidai ta kalli masu aekin gidansu ga dukiya iya dukiya saidai ko kadan bata samun kulawa ko tarbiyya gatadai musulma gaba da baya. Cikin rashin ko inkula tace"saikin dawo Ummi". 


Dariya *AYSHA* tayi ta shafa kan y'ar tata ta fita tare da yiwa mota dinta key tayi gaba. 


Khadija kam daki ta shiga ta soma kallo babu abunda ke damuwarta don shine kawai abun yinta a rayuwarta sai'in ta takaici idon mai gadi tayi gaba abunta. 



Masu aekin gidan kam abincin sukayi suka jera a dianing suka koma part dinsu basu kuma fitowa sai girkin dare. 


Aysha na isa kofar wani tankameman gidan karuwai tayi burki ta shige abunta kirari suke mata sosai sannan ta fada bisa wani katon nata da ake Kira ALHAJI, sosai suke soyewa tare dashan kwayoyi da giya. 



Wannan shine rayuwar ma'aurata biyu *JABEER da AYSHA*


Sai kusan 11 na dare sannan Jabir ya kunno motarsa cikin gidan fitowa yayi yana tangadi ga wata kwalbar wine a hannunsa, bankado kofar yayi ya shigo tare da fuduwa, Khadija dake zaune da sauri ta mike ta tallafo Abi din nata tana masa sannu ko kadan bata kyamatar rayuwar iyayen nata gani takeyi shine abu mai kyau da kowa ke aekatawa, shafa kanta kawai yayi ya mike yakai kansa daki da kyar itama ta wuce dakinta tabi lafiyar gado, sai lokacin Aysha ta shigo gidan, dakinsu ta shiga itama bata jiraba ta watsa ruwa kawai ta kwanta gefan Jabeer tuni bacci yayi awan gaba dasu. 


Kullun haka suke rayuwa, sai lokaci lokaci Khadija ke zuwa makarantar boko ba laifi ta iya fannin boko amma bangaren ADDINI ko oho don batama tabajin kalma irin Wannan ba, a kwana a tashi har tayi weac da neko, ta zama budurwa mai cikar zati shekarunta 17 a duniya, tuni Khadija ta kware fannin shaye shaye naduk ko wacce irin kwaya kuka sani cikin duniya, saidai ko kadan bata taba aekata zinaba amma ko yaushe tana like da maza zasu zauna kamar yacce zata zauna da y'ar uwarta mace, tana kazamar rayuwa zina da lesbian kawai ke bata aekatawa a cewarta bata taba ganin iyayenta sunyi Wannan ba saidai tana ganin ana rungumarsu da kuma shayeshayen da sukeyi. 


Zaune take tsakiyar Abbas da Aliyu a club dare yayi rabi shaye shaye sukeyi ba kama hannun yaro, kallon Sadeeq tayi daya dora hannunsa saman breast dinta, tsuke fuska tayi tace a yanayin maye"kai baka ganewa ne, bance karka kuma tabamun jikiba, ka kiyayeni"ta karashe maganar tare da figan bag dinta tayiwa motanta key duki take ta ganganci ikon Allah ne kawai ya kaita gida ko kula iyayenta dake parlor batayiba ta shige dakinta a kasa ta fadi ta soma baccin asara. 



*Don girman Allah in yazo wurinka ka tura zuwa wasu groups din don kowa ya amfana*


Emmm Iyyyy

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*DON GIRMAN ALLAH NA ROKA INKA KARANTA KA TURA WASU GROUPS, KO WANI SOCIAL MEDIA DA SAKON ZAI ISA*

*TRUE LIFE STORY*

2

Rai bace Nura ya dubi Sadiq yace"kanada matsala friend kasan me Khadija ke aekatawa so nawa kasan batasan zina ba, kai kuma kaki ganewa ya kamata inma kudiri gareka kabita a hankali"


Murmushi Abbas yayi yace"ya zaka bashi shawara akan abunda kasan tamkar budewar rigima ne a tsakanin abokananmu tun yarinta zako kusa ta tabu damu"


"Saime to"Sadiq ya fada. 


Buga table din gabansu yayi yace "haba waime ya shiga kanku ne, ko kun manta tunda na kawo Khadija cikinmu na baku labarin rayuwarta da asalinta meye na batawa kanku lokaci, kadaiyi da wata but ka fita harkan Khadija cos nasan me zata iya aekatawa"Aliyu ya fada da nufin shawara. 


Tsaki Sadiq yaja yace"nuna mana kaika kawota to Dan iska kawai". 


Dariya suka kwashe da ita tare da rungume juna su duka hudun, Abbas, Aliyu, Nura, Sadiq, abotarsu babu abunda ke batata ko bacci baya rabasu gidansu daya suna matukar son junansu rawa suka ci gaba dayi da shaye shayensu a bige suka koma gida. 


Next day 


Fitowa tayi parlon sanye take da jeans black iyakarsa rabin cinyarta blue rigace mai hannun vest jikinta ko cibinta bata rufeba ga hills a kafanta gashin kanta sake yake a bayanta, zama tayi tana kurbar copee tare da tsare wadanda ta iske a parlor ALHAJI ne UMMINTA yana rungume da ita sai holewarsu suke, ajiye mug din hannunta tayi ta figi jakanta da key din mota tayi gaba ta fice zuciyarta cike da farinciki don bata ganin abunda Umminta ke aekatawa a matsayin laifi. 


Tsayawa tayi da mota ganin wurin da cinkoso da sauri ta karasa inda akayi accident din kama matar tayi aka sakata mota, mutan wurin kowa daka gansa kaga cikkun larabawa donko shigarsu ta nuna. 

Wasu matane ke gulmarta daya tace"asara daya ko biyu yar larabawa amma a haka"

Daya tace "karkuga laifinta waye besan JABEER da AYSHA ba dukiyarsu ta hana a hukuntasu da ADDININsu wanda kunsan hukuncin jiya ya wajaba a kansu amma yanzu shara'ar kudi da son rai akeyi ina za'aga daidai"


Itako batasan sunayi ba tayiwa motarta key kai tsaye gidansu Aliyu ta nufa cos duk yawanta daga club sai nan, sai in kuma su suka jata yawo. 


Tana shiga a parlor ta samesu saida ta rungumi kowa alamar gaesuwa harda Sadiq cos ita bata da riko al-adarta kenan ci gaba sukayi da holewarsu hankali kwance gata a tsakiyarsu. 



*Don Allah inka karanta ka turawa wasu, so nike sakon ya isa ko ina*


Emm Iyy luv

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*DON GIRMAN ALLAH INKA KARANTA KA TURA A WASU GROUPS DA FACEBOOK DA SAURAN YANAR GIZO*. 

 *TRUE LIFE STORY*

3

Sai  yamma likis ta fito a gidan, gidan da tasan Abi dinta na zama ta isa a kofar gidan tayi parking ta fito tare da kutsa kai a ciki, har inda yake ta isa zama tayi tare da jawo sigari a aljihunta ta kunna mata wuta, shafa kanta yayi yace"y'ar baba daga ina? "


"Gidansu Aliyu Abi na"ta fada a takaice. 

Murmushi yayi tare da mikewa yace "inkin gama ki kirani saimu wuce gida"yana zuwa nan yayi gaba abunsa. 


Yayinda aka zagayeta suka sona karta da mutanen dake wurin. 

Sai bayan isha suka koma gida, a lokaci Aysha ta dade da ficewa a gidan. 

Abinci sukaci mai rai da lafiya sannan kowa ya kama gabansa ya nufi part dinsa. 


Yaukam Jabir beyi bacciba har Aysha ta dawo, tana shigowa ta rungumesa tare da masa Sannu da gida. 


Fuska sake yake ansawa cike dajin dadin ganinta suka rungume juna suka fada bed tuni labari ya canza bako addu'a ya shigeta, sai wurin Asuba suka farka wanka sukayi tare da shaye shayensy suka kumabin lafiyar gado. 


Yau ta tashi batajin y'an fita shiryawa tayi cikin black dogon riga ta daura kyalen tayi masifar kyau ta fito asalin balarabiyarta sai zuba kanshi take, tasa masu aekinsu da suyi mata girki zatayi baki, hakan ba bako bane a wurinsu cos bayau su Abbas suka fara zuwa gidanba don saidai ma su kirasu yan gida. 


Tana tsakiyar mahaifan nata sunata FIra cos a duniya babu abunda sukeso sama da Khadija basason takura mata ko bacin ranta. 


Kai tsaye suka shigo parlon tare da fadin"hyy guys"


Da ihun murna ta tashi tana tarbarsu suna kashewa da juna, sannan iyayen nata suka tarbesu daga nan kuma ko wannensu ya ficewarsa wurin harkarsa. 


Disko suka kure sunacin abinci da shaye shayensu ga rawa sunayi ba jimawa bacci keson daukarsu kai tsaye dakin Khadija suka nufa suka fada a bed su duka biyar din suka soma baccin asara. 


Sai dare suka farka daga nan sukayi club don suna tunanin anan zasu kwana. 


Sosai Sadiq yake wahala da sha'awar Khadija tare dashi abun duniya dukya damesa ya kudurtawa ransa dole a gobe ya kauda sha'awarsa kota halin yaya, da Wannan tunanin ya ware sukaci gaba da sha'anin rayuwarsu. 


*Don Allah duk wanda ya karanta ya turamin zuwa wani groups*


Emm Iyy luv

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITES ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*NA ROKA INKA KARANTA KA TURA ZUWA WASU GROUPS*

*TRUE LIFE STORY*

4

Bayan wasu lokaci abubuwa da dama sun faru kuma babu wanda ya sauya da'b'i'unsa daga yadda yake saima abunda yayi gaba musamman daga bangaran iyayen Khadija. 


Da sauri ta fito rike da bag yaukam sanye take da bakar jallabiya ta yane kanta da veil black sai zuba kamshi take ta fito asalin balarabiyarta kallonta iyayen nata sukayi Aysha tace"ya naga kina sauri haka ina zuwa kuma". 


"Ae kema kinsan kwanan zancen"JABEER ya fada. 


Murmushi Khadija tayi tace"iyakata wurinsu Abbas Ummi". 


Sai kin dawo suka mata ta fito suna dagawa juna hannu sannan tayiwa motarta key ta cillata kan titi hankali kwance take tukin harta iso club inda tasan zataga su Aliyu da murmushi ta karasa suka kashe da juna suka fara fira. 



Ma'aekatan wurinne suka kawo masu wine din da sukasan sunasha cup biyar aka zuba kowa ya dauki nasa, sabanin Khadija da tace"no i'm ok", mikewa kawai tayi ta shiga fili ta fara taka rawa da wakar dake tashi, saida su Nura suka bugu sosai sannan ta turasu mota ta wuce gidansu dasu ita ke driving. 


A parlor suka zube sunata faman surutai, mikewa tayi ta nufi kitchen. 

Da ido Sadeeq ya bita kaman tsohwan maye tana lashe baki yace"wallahi yau sainayi zina da Khadija ". 


"Kar kayi kuskuran aekata haka"Abbas ya fada. 


"Kusa ido ku kallah, naga yadda wannan wasan zai kasance"cewar Aliyu. 


Rike take da fruits a plate sai small knife dake gefe zama tayi ta soma yankar Apple din dake ciki. 


Zunbur Sadiq ya mike ya soma kamata da kokowa tana shirin barka mata riga yana fadin"yau saina cinma burina gwarama ki bada kai donko babu mai karbarki". 


Sosai suke kokowa candai Allah ya bata sa'ar mikewa rai a matukar bace  tana huci bata ko ganin gabanta sai huci takeyi yayinda zuciyarta ke azazzalarta wukar hannunta ta daga ta lumata tsakiyar cikin Sadiq tajata zuwa kasan cibinsa sannan ta zaro ta kuma dab'a masa saida ta barka cikinsa sosai, take jini yayi tsartuwa ya soma malala a wurin dukta baci da jinin a hassale take fadin"waye kuma cikinku zaiyi kuskuren aekata haka gareni"lokaci daya kuka yaci karfinta ta fashe da ihu ta duke a wurin tana kuka wiwi me tsima zuciya jikinta sai kyarma yake. 


Kallon juna su Nura suka somayi a matukar tsorace sukayi waje da gudu kowa yayi ta kansa, yan sandar dake unguwar suka nuna rashin yarda suka damkesu, anan suka fadi abunda ya faru, rufesu akayi aka tada mota suka isa gidan da abun ya faru. 


Yansanda ne suka zagaye gidan sannan wasu suka shiga, gidan nanan yarda yake ga gawar Sadiq a kwance jini dukya malale parlon haka zalika Khadija tananan inda take ko motsawa batayiba hawaye kawai take. 

Mikewa tayi ta mika hannuwanta da suka baci da jini ga wukar a hannunta da tissue suka karbi wukar hannuwanta ta mika aka daura mata onka suka sakata gaba har cikin motarsu sukayi police station yayinda akayi asibiti da gawar Sadiq. 


Ganin an kulle su Nura hankalinta ya tashi tambayoyi sukayi mata ta bada statement ta kuma kara da cewa"babu ruwansu basu aekata komai ba, nina kashesa da hannuna babu taimakon kowa"


Gamsuwa sukayi da bayaninta don haka aka saki su Nura yayinda aka kulleta cikin cell. 



Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻


Emm Iyy luv

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*IDAN KA KARANTA DON ALLAH KA TURA MIN ZUWA WASSU GROUPS*

 *TRUE LIFE STORY*

5

Kai tsaye gidansu Khadija suka nufa cike da tsoran abunda zaije ya dawo ko wannensu zuciyarsa cike da tunani iri iri da kuma mumunan tashin hankali a tare dasu sunyi sa'a iyayen nata na gida, cike da fara'a suka tarbesu yayinda su kuma suke dardar da sanar dasu abunda ke faruwa. Candai Abbas ya nisa tare da fad'a masu abunda ya faru da y'ar tasu. 


Cikin tashin hankali JABEER ya shake wuyan Abbas yana fadin"karya kuke y'ata ba zata iya kashe mutum ba"ganin be cikin hayyacinsa yasa suka kwaci Abbas da kyar. 


Kuka AYSHA ta rushe dashi tana fadin"har lokacin fada gareka bayan kaji ance tana rufe"kukane yaci karfinta ba shiri sukayo waje ikon Allah ne kawai ya kaisu station din, sun dimauce sosai dajin case din kuma wai Khadija ta ansa laifinta, kuma babu belinta da kyar aka basu damar ganinta. 


Khadija na ganin iyayen nata ta fada jikinsu tana kuka. 


Cikin kuka AYSHA tace"haba Khadija koda kinyi laifi meyasa kika ansa kinsan cewa babu abunda zai hanaki zama gidan kaso tunda kika ansa laifinki". 


"Ummi na bansan ya zanyi ba zuciyata ce tasa na kashe Sadiq kuma ita tasa na ansa laifina nidai kawai bansan karyaba Ummi na". 


Kallonta JABEER yayi yace"aeko kinyi kuskure Khadija na ansa laifinki". 


Yar sanda macace tazo tace"lokacinku ya kare"bata jira cewarsu ba ta janye Khadija daga jikin Aysha kuka kawai suke sunaji suna gani aka kuma kulleta kuma sunce gobe za'a kaita kotu. 


A ranar basuyi bacciba banda barin dukiya babu abunda sukeyi na ganin an kashe case din amma abun yaci tura dole sukayi hakuri. 


Washe gari tunda safe suka nufi babbar kotun da za'akai Khadija kan kiceme kotun ta cika da D'an Adam kasancewar tuni yan jarida da gidajen TV sun yada al-amarin kotun ta cika makil, motar yan sandace ta kutso kai wurin saida aka tare mutane dayan jarida sannan aka samu damar fiddo Khadija, fuskarta tayi jajir idanuwanta sun kunbura dukta fada ta fita a hayyacinta kuma har lokacin yanzu hawaye basu kafeba da zubowa a kyakyawar fuskartaba, tana dago ido ta hada ido da mahaifan nata ga abokanayenta a gefe suma a rude musamman Aliyu da yafi kowa shakuwa da ita, tusata gaba sukayi har cikin kotun ta tsaya cikin akwatin da ake tuhumar mai laifi. 


Alkali ya shigo take kowa ya mike don girmamasa, anan ya bada izinin zama sannan aka karanto shari'ar su Khadija, sannan aka mika masa. 

Karba yayi tare da dubawa ya dago fuskarsa sanye da farin gilashi yace"Khadija Jabir kina da lawyer? "


"A'a bani da lawyer". 

"To kinji laifin da ake tuhumarki dashi na kashe abokinki me zakice akan haka". 


Dukar da kanta tayi ta share hawayen dake zuba tace"na aekata da wannan hannun na kashesa, ina rokon kotu data yankeman hukunci". 


Y'an rubuce rubuce yayi sannan ya dago yace "kotu ta yankewa Khadija shekara 5 gidan yari zata iya daukaka kara bayan shekara 1"yana zuwa nan ya buga tebur alamun ya tashi, take kowa ya mike, kamo Khadija akayi yayinda yanzu take murmushi wanda yafi kuka ciwo, Aysha ko kuka take iya karfinta Jabir na rike da ita, sunaji suna gani aka tafi da ita, suma a dole suka tafi gida. 


Uniform aka bata aka shiga da ita cikin gidan na mata daki aka sakata aka rufe, su biyune a dakin. 

(Kunsan su sunada wuri me kyau ba kamar Nigeria ba, kuma suna hukunci kodan waye yayi laifi). 


Kuka ta saki ta rakube gefe kanta na mugun sara mata. 



A page na gaba zamu tashi a rayuwarta na gidan yari. 



Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻


Emm Iyy luv

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITES ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*DON ALLAH INKA KARANTA KA TURA WASU GROUPS*

  *TRUE LIFE STORY*

6

   *RAYUWAR KHADIJA  A GIDAN YARI* 😭😭😭


*Abun lura da takaici na rayuwarta*. 



Yanzu kam ta ware ta rage kuka da damuwa iyayenta na ziyartarta da abokanayenta ta rungumi kaddararta da hannu bibiyu, abunda ke daure mata kai kullun zataga su Asiya suna wani abu da bata sansaba (dakinsu daya da asiya). 


Yau kusan watanta ukku Amma kullun sai sunyi abun ba laifi suna shiri da Asiya don haka yau ta yanke shawarar tambayarta, kallonsu take daga daki ta sako kanta ta karafa tana lekensu har suka isa inda sukeyin sallah. 



Bayan sun gama cin abinci ne tace "nikam Asiya inaso na tambayeki". 


Duka ta tattaro hankalinta ga Khadija tace"ina jinki". 


Numfasawa tayi tace"Asiya meye sunan abunda kukeyi kullun so biyar kuma kuje can kuita dukawa". 


Sake da baki Asiya ke kallon Khadija da matukar mamaki tace"kai Khadija banason wasa, wannan wacce irin tambayace kina cikakkiyar musulma". 


Sosai Khadija ta natsu tace"nasan abu daya Asiya ana kirana musulma kuma ina ansawa amma bansan me yake nufiba balle nasan me kukeyi domin ban taba yiba, nan Khadija ta bawa Asiya labarin rayuwarta ". 


Hawayene jike a fuskar Asiya cike da al'ajabi take kallon Khadija tana matukar tausaya mata murya na rawa tace"yanzu wurin limaminmu ya kamata muje zaiji da matsalarki amma abunda mukeyi na farko alwala ne sai muje muyi sallah, tashi muje wurin liman". 


Wurin liman sukaje sunyi sa'a yana masallaci iso aka musu sannan suka shiga suka zauna nesa dashi tare da gaeshesa nan Asiya ta fada masa abunda ke faruwa. 


Sosai hankalinsa ya tashi tanata maimaita innalillahi wa'inna ilairir raju'un yana kallon Khadija da babu alamar damuwa a tare da ita. 


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻



Emm Iyy luv 

  09030953294.

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*IDAN KA KARANTA KA TURA WASU GROUPS*

  *TRUE LIFE STORY*

7

Sosai liman ya jinjina rayuwar Khadija domin kuwa abun tausayice be taba tunanin har yanzu akwai iyaye irin nataba da suka tura rayuwarsu data yarsu a halaka ba, nisawa yayi yace"gaskiya labarinki  abun tausayine gaki cikakkiyar balaraba amma bakisan taka maimai addininki ba, shin yanzu kinaso ki rika abunda mukeyi? "




Washe baki tayi tace"inaso kuma matukar burgeni sosai"


Murmushi yayi yace"to farko dai zaki amshi kalmar shahada, sannan ki yarda Allah dayane wanda ya haliccemu be haifaba ba'a haifesa ba". 



Girgiza kai take alamar gamsuwa da maganganunsa nan ya biya mata kalmar shahada ta maimaita, a take ya fara sanar mata abunda ya dace ta sani, na daga rukunnan musulunci, wankan janaba, alwala sallah da wasu daga cikin addu'o'i daya dace ta fara sani, satinta biyu cib ta iya sallah da karatun cikinta wanda babu algush a cikinsa, Khadija tanad kwalwar fahimta tana ganewa sosai hakan yasa liman rokon manyansu dasu barta karkashin kulawarsa domin tayi ilimi. 



Suma sun tausayawa rayuwarta don haka suka dauke mata duk wani aeki na kanta ta koma farfajiyar masallaci tana karatu kawai inta fito daga daki sai dare take komawa cin abinci kawai ke tada ita sai sallah, Alhmdllh shekararta daya ta haddace alqur'ani mai girma tantagaryar harda da babu algush cikinta fannin littafai kuwa suma ta hardace da dama kuma kullun cikin karatu da bincike take, hakan yasa kowa ke ganinta da girma donko ta zama babbar malama. 



Zaune take bakin gadonsu tashe babbar hijab da safa ta rife jikinta tsab, hawayene kebin fuskarta da tayi jajir don kuka, sallamar Asiya yasa ta dawo daga duniyar tunanin da take, isowa tayi wurinta ta dafa kafadarta tace"Khadija Allah baya dorawa bawa abunda baya iya dauka, kinyi kuskure a baya yanzu kina gyarawa toki dauka waccan kaddarar rayuwarkice". 



Kallon takaici tabi Asiya dashi sannan tace"kaddarar, kaddarafa kikace, ko sakacin iyayena, sun batamun rayuwa na tashi ba gata ba kula ba ilimi Asiya nasha giya kai harda kwayoyi daban daban naje club na zauna cikin zaratan maza ba muharramainaba nayi rawa cikinsu na mu'amalancesu kamar yan uwana mata nayi shigar banza na fidda tsiraici na bude inda ya kamata na rufe, kuma wai a kirani yar gata saboda dukiya, na tsani dukiya"kukane yaci karfinta. 



Lallashinta Asiya ta sonayi saida ta tabbatar ta natsu sannan tace"kije su Ummi dasu Aliyu sunzo". 



Mikewa tayi ta wanko fuskarta sannan ta nufi inda tasan tana haduwa da yan uwan nata, da sallama ta shiga dakin tadan zauna nesa dasu tace"ina wuninku"


A raunane suka ansa mata sannan AYSHA tace"Khadija yanzu ko munyi nasarar samun belinki, gobe zamuzo mu tafi dake". 



Sai a lokacin ta dago idanuwanta ta bisu da kallo sannan tace"nayi takaicin samun da kukayi, saidai inaso ku sani babu inda zanje bazanbar gidan daya bani abunda ku kuka gagara bani ba a matsayinku na iyayena, kuma ina maku fatan shiriya, inkunga na fita daga gidannan to saidai gawata amma na tsani zama a inda ba nanba". 


Cikin kuma AYSHA da JABEER suka nufota, saurin mikewa tayi tsaye tana ja da baya, Aliyu zaiyi magana ta daga masa hannu tace"banaso naji komai daga gareku, ku tashi ku tafi kuma Allah ya shiryeku, kuma ganin karshe kukemin domin bazan kuma hada fuskata dakuba, sai wata rana kuma koda na mutu na rahamta maku zuwa wajen gawata"tana zuwa nan ta fice abunta, umarni ta bada da kada a kuma barin kowa ya ganta ta shige masallaci ta soma karatu. 




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻



Emm Iyy luv

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


*IDAN KA KARANTA KA TURA WASU GROUPS, DON ALLAH*

  *TRUE LIFE STORY*

8

Duka a dakin babu mai tada wani Nura kam dakeda karayeyar zuciya tuni ya soma hawaye, kowa da tunanin da yakeyi a rai, suna haka akazo aka fitar dasu dayi masu gargadin kada wanda ya kuma zuwa ganinta, kuka Ummi keyi wiwi a haka suka isa gida, Tsayawa Aliyu yayi gaban makeken hoton Sadiq yace"kaga abunda ka jawo mamu ko, meyasa kai baka daukar shawara ne, gashi yanzu komai ya lalace wannan wanne irin tashin hankali ne"rungume juna sukayi su duka ukkun suka fashe da kuka maicin rai. 



  *bayan wasu shekaru*



*Khadija ta zama babbar malama mai wa'azi kuma shugaban mata a gidan yari*


"Kiyi hakuri ki koma gida, ki zauna da iyayenki tunda kin kusa ida shekarunki gashi sunanki ya fada ga wa'anda akeso su fita". 



"Har aba Baba(liman), bazan taba barin gidannanba, saidai inka gaji da koyar danine ban saniba"Khadija ta fada. 



"Ko daya Khadija, kinada halin da kowa zai so zama dake nayi maki kwadayin hakane kawai"liman ya fada. 


"Na gode da kwadayin kayimin amma kayi hakuri na zabi zaman nan fiye da ko ina a duniya"



Babu wanda be roketa akan ta koma gidaba taki, a dole suka hakura suka barta nan. 


Yanzu kam babu abunda Khadija keyi sama da wa'azin iyaye mata da yan mata, cikin sauri ta fito donta makara shirye take tsab ta rufe ko ina a jikinta amma fuskarta a bude, cikin wasu masu tsaron gidanne suka bi bayanta aka bude masu kofa,suka shiga wasu runfuna inda taron mata yake kusa da gidan yarin tun tahowarta yan jarida keta daukar hotunanta da videos dinta kai tsaye bisa minbari ta nufa tahau tare da daukar lasifika, tana goge hawayen idonta ta nunanin yanzu duk wannan alummar don ita suka taru sukeson jin abunda zata fada. 




Kara kallonsu tayi tayi karfin halin bude taro da addu'a da sallah ya musulmai sannan ta bude baki tace"iyayena, yayyena, kannena kuji tsoran Allah, kune jigon gida kuyi ilimi ku bada tarbiyya, duniya ba matabbata bace, kada ku sayar da lahirarku akan kyalekyalen duniya, Allah daya haliccemu yayi mune domin bauta masa, ku dauka duniya jarabawace kukeyi zakuje inda zasu iske sakamakonku da gidan zamanku nahar abada, ki sani idan kikayi gudunmawar bacewar rayuwar yaranki ko kannenki ko jikokinki to Allah bazai barkiba, zai bi masu hakkinsu a ranar da babu tsimi babu diba, kada ki zama jahilar uwa da zata koyi yayanta da shan giya kwayoyi shigar banza zinace zinace, ku sani alfarman manzonmu mukeci da tuni an dade da juyar da duniyarmu, ke kanki in aka saba maki ko aka yimaki kishiya kina fushi da neman hukunci inaga anyi hakan ga mahalliccin, kada Kiyi koyi da kazamar rayuwar Khadija ta farko wanda iyayenta suka tarwatsa mata farin cikinta, abun takaici batasan ADDININTA ba bare tasan mahalkiccinta bare kuma ta bauta masa, Allah ina rokonka daka bamu iyaye na gari masu ilimi da fita hakkinmu da sanin ya dace, a fannin boko za'a iya kashe dubunnai har kasar a bari, amma a islamiyyah ana kyashin kashe dubu daya, ko'a takura wa yaro yayi karatun ADDINI, mu sani kiwo muke kuma ababen tambayane ranar gobe kiyama, ya kamata musan kanmu muyi bauta ga Allah mubawa yaronmu tarbiyya kada mu kaskantar da rayuwarmu sannan mu likata gawai kaddarace, kaddarace wannan ko sakaci, Ya Allah kasa mu hadu dakai muna masu imani a gareka da kuma kwadayin haduwa dakai, mu hadu dakai zukatanmu da gangar jikinmu suna shaukin isa gareka, Ya Allah ka bamu damar abunda muka karanta dayi maka biyayya". 



Kukane yaci karfinta sosai har tana neman shidewa ajiye lasifikan tayi ta kuma fashewa da kuka saida su Asiya suka kamata zuwa ciki dominko tsayuwa gagararta tayi bata komai sai fitar da kuka yayinda zuciyarta ke matukar kuna da tsanar rayuwar duniya gaba daya. 



Duk wanda ya halarci wannan taron kuka yake, hankalin kowa ya tashi jikin kowa ya mutu indai kana da ragowar imani a tare dakai. 



Aysha dake kallah a TV kuka take kamar ranta zai fita, ga soyayyar yar tata dake kuma azazzalar zuciyarta. 



Khadija kam kan bed ta fada tana kuka tare da kaico da irin rayuwarta ta baya ga wani irin ciwan kai daya kawo mata ziyarar, alwala tayi taci gaba da jero nafilfili da istig fari na neman yafiyar ubangiji. 




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻



Emm Iyy luv

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*


  *INKA KARANTA KA TURA WASU GROUPS DON ALLAH HAR FACEBOOK*

 *TRUE LIFE STORY*

9

Tana haka wahallan bacci yayi awan gaba da ita, Asiyace ta gyara mata kwanciyar tayi ficewarta, duk wata mace da tazo wa'azin ranar ta koma gida cike da dumbin imani da tausayi tabbas wa'azinta yayi nasarar canza mata da dama wanda suka afka kogin nadama da kuma jin tausayin rayuwarta gata yarinya karama saidai abubuwan duniya sun rikitar da ita. 



Wani hadden gida da ni'imomi iriri da duk wani abu najin dadi an tarasa a cikin tankameman gida wani irin sanyin dadi da kamshi ke ratsata wanda tunda take a rayuwarta bata tabajin irinsaba ga wata natsuwa da kwanciyar hankali dake ratsata ko ina ka kallah sai kaji natsuwa ta ziyarceka, murya taji kamar daga sama ana fadin *nanne gidanki ki taho, kiji dadin da baki taba jinsaba*.  Firgigit ta farka daga mafarkin da takeyi da addu'ar tashi bacci a bakinta, cikin tsananin mamaki Khadija ke zagaye dakin nata da kallo duktayi zufa addu'a tayi ta tashi ta nufi wurin karatunta amma ta boye sirrin wannan mafarkin da tayi. 



Kamar wasa Khadija ko baccin minti biyu ya dauketa sai tayi wannan mafarkin ana kuma kawata mata da disa mata soyayyar wannan gida da take gani, saidai in bata kwantaba a matsayinta na malama tasan fassarar mafalkinta, kuma sai a sannan laifin data aekata ya fado mata a rai kuma tasan hukuncinta a musulunci, gyada kanta tayi cike da kwarin gwaiwa da aminta da shawarar da zuciyarta ke bata mikewa tayi cike da taurin zuciya da rashin tsoro ta saka hijab dinta tasa aka nema mata iso wurin malam liman, ba dadewa akace ta shiga. 


Tana shiga ta zauna nesa dashi bayan sun gaesa tace "Baba so nake ka fadamun laifin me nayi aka kawoni nan? "


Murmushi yayi yace"Khadija an kamaki da laifin kashe abokinki Sadiq kuma kin ansa laifinki shiyasa aka yanke maki hukunci". 



Girgiza kai tayi tace"tabbas nina kasheshi da hannuna, Baba kaika koyar dani ka bani tarbiya wacce na gagara samu daga iyayena, baka gujeniba ka tallafeni kamar y'arda ka haifa, kasa nayi karatu mai zurfi da sanin hukunce hukunce, inaso ka fadamun meye hukuncin wanda yayi kisa a ADDINI NA"



Izuwa yanzu kam jikin malam liman yayi sanyi don dukta rikitashi da wannan tambayoyin nata wanda yasan ta sani cikin kwarin gwaiwa yace"Khadija wanda ya kashe a kasheshi, amma kisa Kala biyune akwai na ganganci sannan akwai na tsautsayi, inka kashe da gangan a kasheka, in na tsautsayi ne kamar accident to kayi azumi sittin a jere". 


Murmushi tayi tace"Baba nina kashe Sadiq da gangan inason zuwa kotun musulunci donko na ansa laifina, ta yankemin hukunci daidai da ADDINI donna isa ga ubangijina inada tsarki bani da wani laifi gara amin hukunci a duniya ba sai naje lahira ba". 



Tunda ta fara magana hankalin malam ya matukar tashi a rude yake kallonta yace"kina cikin hankalinki kuwa, kinsan me kike fada". 


Sai a lokacin ta dago ido ta kallesa fuskarta cike da fara'a tace"na sani mana, duniya jin dadi ne mai yankewa, dama zuwa nayi ganin gari to lokacin komawata gidana na Asali yayi kaika karantar dani to banaso yanzu lokacin amfanin karatun yazo ka hanani, kuma hukunci na yanke kayi hakuri Baba banason shawarar kowa akan abunda na aekata"tana zuwa nan ta masa sallama tayi gaba. 



Tabbas abunda ta fada gaskiyane babu yanda ya iya dole ya fadawa na gaba dashi, mikewa yayi cike da al-ajabi yaje ya isar da sakonta, zuga guda akayo don lallashinta amma fir Khadija ta bijire taki sauraron kowa kai karshema kuka tasa masu ta tada hankalin kowa, dole sukabi yacce take so aka tattara kundinta aka kaita kotun musulunci, suka tsaida ranar juma'a itace za'a saurari karar Khadija. 



Ba karamin farin ciki tayi ba dajin wannan batu, murna take juma'a tazo, don kwata kwata duniyar ta fice mata akai bata kaunar zamanta cikinta, sosai ta dage da addu'o'i da ibada baji ba gani. 




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻


Emm Iyy lov

*ADDINI NA*

*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

*BY MARYAM ISMAIL*

  

*IDAN KA KARANTA KA TURA WASU GROUPS*

   *TRUE LIFE STORY*

09030953294. 

🔚🔚10🔚🔚

  

*HUKUNCIN KHADIJA A KOTU*

Yau ya kasance juma'a motocine jere guda biyu daya tasu malam liman daya kuma yan sanda ana jiran fitowar Khadija, itako daga wanka ta fito tana tsane gashin kanta da yake jike da ruwa alamun wankan tsarki tayi bata kula Asiya ba da taga tanatana faman sharbar hawaye, shiri tayi cikin shigarta ta mutunci tayi sallah raka'a biyu sannan tazo da murmushi ta kama hannun Asiya tace"banason wannan kukan naki, yanzu addu'arku nake bukata, kuma zan roka a barmu mu tafi tare don muyi bankwana, murna ya kamata kiyimin zan hadu da ubangijina"hijab ta sakawa Asiya ta jawo hannunta suka fito waje, roka tayi a barta su tafi da Asiya sai a dawo da ita, kowa yan gidan kabbara suke tare da zubar da hawaye, cikin dakiyar murya tace"duk Wanda nawa laifi ya yafemin, sai wata rana Allah ya hadamu a aljanna madaukakiya, nidai na yafewa duk Wanda ya batamun"tana zuwa nan ta kutsa kanta cikin motar akaja sukabar gidan, mutanan gidan kuwa basa komai sai kuka da rokawa Khadija gafara. 



Kallon mutanen dake damke da kotun take ga yan jarida da gidajen TV sun cika wurin, kamar wurin ya bare da kyar aka samu damar shiga da ita cikin kotun, aka tare yan jaridar daketa faman jefo mata tambayoyi. 



Lokacin da Alkali ya shigo kotun tayi tsit aka karanto laifin Khadija tare da mika takardar ga alkali, kallah yayi sannan ya dago da idonsa ya kalli Khadija yace"Khadija kinji laifinki kina daja ko karin bayani? ". 



Cike da ladabi tace"bana daja yamai shari'a nina kashe Sadiq da hannuna, shine nazo a yankemin hukunci daidai da yadda shari'a ta tanada. 


Allahu akbar mutan kotun ke fada tare da jinjina imani irin na Khadija Wanda ba'a samun mai Shi. 


Yan rubuce rubuce alkali yayi sannan ya dago ya fara magana kamar haka"a bisa ansa laifin da Khadija tayi hukunci a addini shine Wanda ya kashe a kasheshi, inba da ganganba to kayi azumin kaffara, itako tayi kisanne tana sane, hukuncinta ya kama kamar haka kotu ta yankewa Khadija jabir kisa ta hanyar fille wuya nanda awa biyu"buga tebur yayi ya fice daga wurin, bakajin komai sai ihun mutane da koke kokensu kowa da abunda yake fada, tun anan aka rufe mata fuska da bakin kyalle aka sakata mota aka nufi inda za'a zartar da hukunci yayinda dubban mutane suka bisu ciki hardasu malan liman da iyayenta da suka fara zaucewa. 



Filin zagaye yake anyi tsit, Asiya kam ta kasa rarrashin zuciyarta don kuka take kamar ranta zai fita, nan aka shigo da Khadija filin tare da dukar da ita, hannu tasa ta yaye rufin da akama fuskarta tace"kuban mintuna kadan nayi wasiyya". 


Gyada mata kai kawai sukayi ta mike cikin natsuwa tace"ya jama'atul Muslim, kullun maganata ta farko itace kuji tsoran Allah, kusan me kuke aekatawa kuyi kwadayin neman rahmarsa dan Adam ba a bakin komai yakeba nasiha karama dazan muku itace rayuwa cike take da jarrabawa, duk mumini Wanda yayi imani da Allah ya tabbatar sai an jarabesa, wannan fadar Allah S A W ce, kuna tunanin shikenan tunda kunyi imani ba jarabawa?, wallahi sai an jarrabemu hagunmu ko damanmu, samanmu ko kasanmu, hanya dayace ta kubuta shine mu karbi jarrabawarmu da hannu biyu, muyi imani da kaddara mai kyau ko marar kyau, duniya jin dadice mai yankewa kasan meka aekata kafin haduwarka da Allah, mutuwa bata sallama ko bankwana"hawaye kebin fuskarta "ina kuka badon hukuncinaba saidon murnar barin gidan wahala da bakin cikin duniya, yau Khadija ce tsaye a gabanku take bankwana da neman gafarar Wanda ta batawa, inna mutu kuyimin wanka ku sallaceni ku gaggauta kaini makwancina babana(malam liman shina yarda ya sani a kabari) ku yafeman". Tana zuwa nan ta dauki butan gabanta tayi alwala da sallah raka'a biyu. 



Har malam kuka yake daduk Wanda ke wurin musamman Asiya da iyayenta. 


Kai tsaye zuwa tayi ta duka inda za'a yanke mata wuya ta daga hannu sama tace"ya Allah ni baiwarka ce ya Allah, kuma kana bima Wanda aka zalunta hakkinsa, Allah na kawo karar iyayena Inaso kabimin hakkina ka mani sakayya ranar gobe, kayi masu yadda suka yimin ka hanasu jin dadin duniya ya Allah ka kuntata masu, wasiyyata ta karshe kada kubar iyeyena su kusanci gawata"dora kanta tayi tana furta " *la'ila ha illallah* "daidai nan aka sare mata wuya jini yai tsartuwa ya fara malala ta fadi kasa ragwab idanuwanta na kallon sama fuskarta sai kyalli take da alamun farin ciki. 


Kuka sosai mutane keyi, Asiya kam sumewa tayi ita da Aysha, su Aliyu kam mutuwar tsaye sukayi. 


Da kyar malan liman ya furta"Allah ya karbi bakuncinki Khadija". 



Sosai mutane ke fada kan Wanda zasuyi mata wanka, da kyar aka samu masalaha aka shiryata, kwata kwata an hana iyayenta da abokanta kusantarta, malan liman da kansa ya sakata kabari, akayi addu'a kowa ya watse. 



*ya Allah inda nayi kuskure ka yafemun, ka bamu ikon fahimtar sakon dake ciki, ka daukaka littafin nan yaje har inda banyi tunani ba, ka yafe mana kurakuranmu ka bamu ilimi mai amfani, ka gafarta mamu, mu hadu dakai muna shauki da imaninka a tare damu ya Allah*



😭😭😭😭nayi kuka iya kuka a labarin nan, kuma na tsinci abubuwa da dama 



09030953294. 



Emm Iyy luv



Post a Comment

0 Comments