Adalilin link hausa novels complete

 [12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭ADALILIN LINK 😭*

  

  *WRITTEN BY*

*UMMYN YUSRAH*


     *EDITOR: QUEEN MEEMI* 

     

     

*DUKKAN YABO DA GODIYA SUNTABBATA GA ALLAH MAD'AUKAKIN SARKI, TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD (S. A. W).* 


*BISMILLAHIRRAHMANIRRAM* 


*Wannan Labarin k'irkirarshi nayi, don nunama 'yan'uwa illar da ke cikin wasu Link*

*Allah ya karemu da Imaninmu.* 




*Page 1*


*******

Kwance take kan gado, hannunta d'auke da waya da alama tana jin dad'in hirar da suke a wani group mai Suna *( MATAN AURE GROUP )*.



 Wata ke kwararomusu bayanin wani Maganin mata data sha yadda Oga ya gama rikicewa jiya akata.


Inda ƴan group kowa ke tofa Albarkaci bakinta. Hafsat dake kwance tanajin daɗin hirar tasu, don ita  a duniya indai zataji irin wannan zancen zata iya bata Lokacinta, don yadda zata samu k'warin Gwiwar gyara ma Oga wajen harka. 


Sallama aka yi tare da shigowa ɗin, da gudu yaranta suka haura gadon.


 Babban maisuna

Ahmad(sabeer) ya ce


 "Umma mun dawo."


k'aramar maisuna Asma'u (sabeerah) ta ce


 "Umma yunwa nakeji."


 Abbansu da ke tsaye bakin ƙofa  bai ƙarasa shigowa ba, ya zubo mata ido yana kallonta, don yasan bata d'aura girki ba. Saukowa tayi ta ce


 "Barin had'a muku tea, kafin na gama abincin."

 

Sai sannan yayi magana ranshi a ɓace 


"Habba Hafsat! ace kullum sai yara sundawo sannan kice zaki d'aura abinci! wannan wani irin Rayuwace? idan zasu tafi ba wani karyawar kirki suke ba, sannan sundawo ba abinci, kin d'auki dukkan lokacinki kinbama Waya, wannan wani irin Rayuwace? fisabilillah! bakida lokacin Gyaran gidanki, bakida Lokacin yaranki, ace  Kullum kina kan waya. Gaskiya ki gyara nafara gajiya."


Wani kallon Raini tamai ta ce 


"Uhmmmm! sai ka yi kuma, dad'in abun ba kai ka saimin wayarba, balle kamin Gori."



Ta murgud'a mai baki tayi ficewarta, ta bar shi wajen.



 Shigewa yayi ya cirema yaran kayan makarantar, sannan ya masu wanka ya shiryasu  ya sake fita dasu.


Zauna ya tadda fallor, ba tan ka ta ba  ya fice da yaran. 


Gidansu yakai yaran bayan sun gaida Ummanss ya ƙira k'anwarshi Rahma taba yaran abinci.



Umma ta ce 


"Ina ummar tasu?"


 "Tana gida, batajin dad'ine."


 "Ayyah Allah ya  bata lafiya."


"Ameen, Ummah nizan wuce sai yamma zanzo in d'aukesu."



  "Toh Allah yabada sa'a."

  

***

Bayan fitarsu sai da ta gama catin ɗin ta, kafin  ta tattara wanke-wanke ta yi, ta gyara gidan, lokacin k'arfe uku tayi, gashi ko sallar azahar batai ba, saida ta d'aura girki na dafa dukar taliya,  kafinnan ta je tai sallar azahar da La'asar Alokaci d'aya.



 Bayan ta gama girki ta juye a kula, sannan ta je ta yi wanka, kwalliya sosai, wanda tasan zai janyo hankali Abban Sabeer, abinci ta zuba a filet sannan ta koma kan kujera ta ɗora daga inda ta tsaya.


Bashi ya dawo da yaran ba, sai wajen ƙarfe takwas, yana shigowa yayi arba da ita zaune a falo, da Shigarta mai tada hankali.



Amsa sallamar  ta yi, kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai, don yasan wannan shigar da biyu ne. 


 Sannu da zuwa ta mai, ya amsa can k'asan mak'oshisa.


Tunda taji haka tasan mutumin ya shaka gashi yau so take su mori juna.


 Karb'ar Sabeerah tayi takaita ɗaki, sannan ta dawo ta kawo mai abinci kad'an yaci, don gaba ɗaya dafa dukar taliya ta fita ranshi, ita kuma bata da girki sai shi.


 Yana gamawa ya kama hannun Sabeer ya nufi ɗakinshi da shi.



Tana zaune taji yama k'ofar Key. 


Ai take tayi nutuwar zaune. 



   Ku biyo ni, don jin yadda zata kasance


  *UMMYN YUSRAH*

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*


*WRITTEN BY:*

      *UMMYN YUSRAH*


        *EDITOR BY:QUEEN MEEMI*



*GODIYA MAI TARIN YAWA GAREKU*


*AUNTY RUMA* 

*HAMEBRAH*

*MOM SULTAN (UWAR ALKHAIRI)*

*JAMEELAH K MASHI*

*AMIESTY*

*ANTY FARY NOVEL GROUP* 

*MERMUE NOVELLA*

*LABARINA GROUP*

*SIST FAREEDAH MUSA*

 *DA DUKKAN MASOYA WANNAN NOVEL INA MIKO GODIYA* 👏🏻


         *2*



          *12:30PM*


Haseeb ya d'aukosu daga Makaranta, yauma gida ya wuce dasu dake basuda nisa da makarantar, ko shiga bai ba ya ce su gaida Umman, ya koma wajen Aikin shi. 


Hafsat zaune a falo tana sana'arta,  yau anyi sa'a tagama komai, amma har yanzun wajen ƙarfe ɗaya da bai dawo da yaranba, tunda taga haka tasan ya wuce dasu gidan kakarsu, ita kad'ai ke magana ta ce


 "Uhmmmm! shi ya sani kuma nikam hutuna." 


     *Gidan Bilki*

     

Abbansu Salmane ya shigo d'auke da kayan Abinci daya sayo musu.



Sai dai abun haushi Matar tashi bata gida sai yaran ta bari da gadin Gidan.



"Salma ina Mamanku?"


"Ta fita, Abbah."


"Tun yaushe?"


"Ta jima da fita, tace zata shiga gidan Maman Nana, wai an kawo kaya har yanzun bata dawoba."


"kunci Abincine?"


"Aah Abbah."


kad'a kai yayi tsabar takaici 

"Wai yaushe Bilki zata daina wannan shegen yawon natane? kullum akazo gidan batanan sai dai tabar yara k'anana da gadin gida, ta tafi bin gidan mak'ota, Allah ya shiryeta.ke jeki ce ta zo" 


 "Tam Abbah" 


Saida ta zaga kusan Gidaje Biyar kafin ta samo ta, ta samu sai kwasar girki take tama mantada tabar yara a gida. 


"Umma kizo Abbanmu ya dawo."

 

Ai take d'umbun tsakin datakai lomarshi bakinta ya shak'eta ta zaro Ido


 "Abbanku ya dawo?"

 

"Eh, yace in ƙira ki."


 "Toh Muje."


sallama tama mutan gidan tasa kai da yar kwanon dambun ta.



 Gidan kusa dasu ta shiga tace su bata abu zata d'ebi Garwashin wuta, bayan ta d'iba tashige gida da sallamarta, tama Abban yaran barka da zuwa. 

sannan ta kama kame-kame


 "Ai na shiga ɗibar gaushi nasami matar Maƙocinmu tana kan Gwiwa, shine muka taimaka mata har yanzu bata saukaba". 



Binta kawai yayi da ido yatashi ya yi gaba, don ya rasa kalmar da zai mata magana, tunda kullum cikinta yake, fatanshi Allah yaye mata wannan yawon nata. 



*ABUBAKAR TAFAWA BALEWA TEACHIN HOSPITAL BAUCHI*


DR.Haseeb ne shida babban Abokinshi Dr. Khamees suna tattaunawa akan aikinsu,

Aminai ne sosai.



Dr haseeb Mutumne mai k'wazo wajen aikinshi k'wararren Likitan matane, mutum mai saukin kai da son mutane, sai dai sam bai yi sa'ar abokiyar zamaba. 


Bayan tashinsu daga asibiti, gidan Dr Khamees suka wuce can yaci abinci yayi sallar Magrib da Isha'i kafin ya wuce gidansu d'aukar su Sabeer. 


Bayan sun gaisa da Umman tashi tace "ya mai jikin? dazu ka sauke yaran baka shigoba."



 "Da sauki Ummah, aiki na ke na bari na ɗauki su, shi yasa ban shigo ba."

 

  "Ayyah! Allah kara sauki gobe insha Allah zanje indubata.


"Ai da kinyi zamanki gobe ma gida zan wuce dasu tunda jikin nata da sauki sosai."

   

"Toh ai shikenan idan ka koma ina gaisheta"

 "To Umma mun wuce saida safe."



CITY STORE ya tsaya yasai musu ice cream  da cakulati sannan suka wuce gona.


Falon shuru ba kowa, ɗakinshi suka wuce yaba Sabeera wani Ledar takaima Ummanta, sai dai sanda taje ta tura kofar tajita rufe ta buga k'ofar taji shuru ta dawo ta sanarma Abbanta.



 karb'ar Ledar yayi ya ajiye,  wanka ya musu sannan yayi nashi yazo ya kwanta. 


Gimbiya Hafsat tana d'aki tagama cika tayi fam, saura kiris ta fashe ta gaji da jiran dawowarsu shine ta kule daki ta rufe tanajin dawowarsu taki budewa. 


    

Bayan dawowarshi daga Massallaci ya tashi Yaran yamusu wanka, sannan sukai Alwala sukai sallah sukayi Break yashiryasu sukad'au Hanyar makaranta.

 

Yauma kamar kullum a Makare ta tashi tayi sallah ta ta had'a abun karyawa dai-dai ba, don tasan sun riga sun tafi.


Abincin da ta ajiye musu haka tazo tasamu ta dada kulewa da haushi, komawa tayi ta karya, sannan ta shiga Sana'artata wato Chattin ba gyaran gida ba wanke-wanke ba gyaran jiki ba komai ita damuwarta waya kawai. 



         


Dr. Haseeb ne zaune da Abokinshi suna hira yake bashi Labarin halin da suke ciki da hafsat. 

 

"Habba Dr! Amma bai kamata ka biye mata ba  kamata ya yi ka cigaba da hakuri da kuma mata nasiha, wala Allah kozata nutsu yanzun kai ka hau itama ta hau, tam kar fa kabata damar tacigaba da abunda takeyi kenan! Gaskiya ka sake tunani karfa ka manta mace k'aramin k'wak'walwa gareta sai ana yi ana tarota (kuyi hak'r yan'uwa mata) sabida fadawa wata hanyar."

 

Sai sannan Dr Haseeb ya gane kurenshi na fushin da yake, tabbas maganar Dr. Khamees Gaskiya ne don yaga kamar kara bata dama yayi, akan taci gaba da abun da take yi, yayi niyyar in Allah ya yadda ya koma Gida zasuyi magana. 

   


*UMMYN YUSRAH*

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭ADALILIN LINK😭*



    *WRITTEN BY:*

           *UMMYN YUSRAH* 


     *EDITOR BY:QUEEN MEEMI*




            *3*


Yau gida ya wuce dasu bayan ya d'aukosu daga Makaranta, a kofar gate ya saukesu ya juya wajen Aikin shi. 




         

Haseeb ne yashigo gidan, falo ya sameta zaune tamai sannu da dawawo ta karbi kayan hannunshi ta kaimar ɗaki, sannan ta dawo tace 


"ga abincifa akawo mane?"


 Mamakinta yake, amma kuma yasan indai tana buƙatar wani abun gareshi ladabinta dabanne. 


Abinci ta zubamai yaci, sannan ta haɗamai ruwan wanka, bayan fitowarshi yake tambayarta 


"ina yaran?"

 "sunyi bacci tun dazu." Dakinta ta wuce


Bayan yagama shirin kwanciya lokacin yana shirin zuwa ɗakinta domin tattaunawa kan matsalarsu, sai gata tashigo da shirin bacci.



"Ina shirin zuwa sai gaki."


 Dariya tai tace 


"Eh nazo tayaka kwanane" 


"kin kyauta, dama inason agana dake." 


"Toh! Allah yasa lafiya?"


"Lafiya lau.

kizauna mana". 



 Bayan sun zauna ya fara mata Magana.


 "Gaskiya Hafsat bai kamata ace kindauki dukkan lokacinki kin ba wayaba,nbakida lokacin Yaranki, ibadarki, gidanki, baki da lokacin komai sai chattin, bai kamata kibari wata tayi rinjaye kan komai na rayuwarki ba, amma ga dukkan alamu kina neman jefa kanki hanyar da baida ceba, ibadarki tayi rauni, idan Allah yadauki rayuwarki mezaki ce?"


Jan numfashi ya yi sannan ya ci gaba



 "Bakida lokacin yaranki, kisani yaranmu amanace akanmu Allah zai tambayemu akansu mezakicema ubangiji akansu?

Zaman aure ibadane shin kina yin ibadar aurenki yadda Addini ya koyar?

a kullum nakanyi kokarin ganardake hanyar da ya dace amma sai kisa k'afa kishure,  Allah ya gani ina iya bakin kokarina wajen nuna miki hanyar data dace, bakuma zan gajiya da fadi mikiba, da sannu wataran zai miki amfani."



Nasiha sosai yamata maishiga Jiki, su Hafsy harda k'walla.


"Kayi Hakuri, insha Allah zan gyara komai zai dawo dai-dai." 


"Allah yasa." 


"Ameen."


 Gaba ɗaya sukayi Dariya daganan salon ya sauya.

   


  *UMMYN YUSRAH*

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭DALILIN LINK😭*


      *WRITTEN BY:*

                *UMMYN YUSRAH* 

       *EDITOR BY:*

             *QUEEN MEEMI*


   

             *4*


Ba Laifi Hafsat kwana 2 tadan chanza.



Bilkisu ce ta shigo gidan da saurinta, tambayar babbar ƴarta ta yi mai suna Salma ƴar shekara bakwai.


"Ke Babanku ya dawo kuwa?"


"Bai dawo ba."


"Yauwa! Sauri na ke ta yi in dawo ai."


A'isha ƴar shekara biyar ta ce


"Mama tun ɗazu kika tafi fa, kince zaki dawo da wuri, kinje kuma ki zauna, gashi sai yunwa muke ji."


"Kuyi haƙuri! Ga abinci na kawo muku,kuci kafin na ɗaura.



Bilkisu macece mai shegen son bin gidajen maƙwafta, idan ta saɓi mayafi sai an ganta, bata waiwayo gida sai ta ci ta yi hani an.



Malam Sani ma'aikacin gidan bulo, shine mijinta. Yana iya ƙoƙarinsa wajen rufa musu asiri, amma duk da haka bai hana Bilkisu hangen na waje ba.


Yara uku garesu, Salma, Aisha, sai Asiya mai shekara uku, wani lokacin duk take kwasarsu su tafi yawon, wani lokacin kuma a gida ta ke barinsu ba tare da ta yi la'akari da shekaru su da yanayin rayuwar yau ba.




Dattijuwa ce tsaye kofar gidan da yar jakar kaya da wani buhu a gefe tana tunanin ina Bilkisu taje, a wannan lokacin, ta deb'o hanya ga gajiya abun haushi tazo gida rufe. 




Bayan ta gama tunani ne ta yanke shawarar shiga mak'wabtansu ko sun san inda taje. 



Da sallama ta shiga bayan sun gaisa da Maman Maryam ta tambayeta ko Bilkisu tayi nisane tace


 "Aiko bansan inda tajeba, ki shigo mana sai indubo miki ita hala Maman tane?"


 "eh wallahi" 


"Barin dubota, don nasan bazata wuce cikin Unguwarnan ba duk yawonta." 


Wajen zama ta bata, sannan ta d'au mayafi don yaran duk sun tafi makaranta.


Gida kusan shida ta shiga bata same ta ba, haka ta hak'ura ta dawo ta sanar da Maman Bilky bata nan. 


"Toh nagode Allah yayi albarka, narasa gane Bilkisu wani irin yawo gareta, mutane da yawa idan sunzo sun koma sai suce sunzo basu same ta ba. Shin iiki takeyi ?kodai zaman gidan ya gagreta ne? Amma ace in d'auko hanya tun daga Azare ace bakowa a gidan wannan hali sam bai ba." 



"Ki hak'uri Mama sam Bilkisu ban san wani irin hali ta d'aurama kanta ba, indai garin Allah ya waye saita gama karad'e gidajen unguwa kaf! 

Har fad'a mukayi don ina mata maganar ta daina, yanzu haka ko magana ba tamin."


                                              "Humm Allah ya kyauta ya shiryeta." 



"Ameen Mama"


Maman Maryam ta gama Abinci ta zubo mata, ta ci anan tayi sallar azahar da la'asar. 



     

Bilkisu ba ita ta dawo gadan ba sai ƙarfe huɗu, yaran na biye da ita, bud'e gidan tayi suka shiga, suna shiga da sauri Murhu ta nufa tana k'ok'arin had'a wuta taga yara suna shigowa da kaya Mamanta na biye dasu.                                                          


Da Murnarta ta tafi yima Maman nata Barka da zuwa,  wani kallo ta bita dashi take tasha Jinin Jikinta.                                                                                                               


                                                                                       

  Kayan ta karb'a takai ɗaki, sannan ta d'eboma Mama ruwa tace


 "koshe nake na jima da zuwa, tun shabiyun rana na shigo gari naga gidan arufe nace hala kintafi wajen aiki?" kallon mama tayi tace 


"Aiki kuma!"


 tashi tayi ta barta da jikokinta, ta tafi d'aura girki. 



       

Mamace da Bilkisu da Abbansu salma suna zaune suna hira. Da dare, gyaran murya Mama tayi tace 


"yanzu kai 

Sani haka zaka zubama Bilki ido tana wannan yawon dabai da amfani? ace kullum kina tabibiyar gidan mak'ota, haka sauran makotan kika ga sukeyi?  

Idan kwad'ayi ke kai ki me mijinki ya rage ki da shi? yana iya k'ok'arinshi, yana muku iya  k'arfinshi, kamata yayi ace yanzu Salma da Aisha suna Makaranta amma kun barsu daga gadin gida, sai ki kwashesu yawon Gulma da kwad'ayi gidan mutane. 



Baki tunanin Lalacewar zamani kifita kibar yara k'anana kuma mata sukad'ai, a gida wani ya shigo ya lalata miki rayuwar yara, yanzu ka killace yaranma baka tsiraba balle kuma kayi watsi dasu, wallahi duk randa na sakejin makamancin haka sai dai ki fita kibarmai gida, ni kuma nama Alk'awarin Sadakin aure da lefe, kije kici gaba karki fasa, yara uku baki hankali kin ba kanki shawara mai kyau ba sai wa kikeso yazo ya baki? Nasan halin Sani yana iya k'ok'arinshi kece dai shed'an ke yawo akan ki Allah yashiryeki damasu hali irin naki." 


Kuka take Sosai


 "Mama ki hakuri wallahi ban k'arawa." 


"!Ah kici gaba, kin daiji hukuncin dana yanke." 


Malam Sani Bawan Allah hakuri yayita ba Mama"insha Allah komai zai dawo dai-dai, yara suna makaranta, ita ke hanasu zuwa na yi magana ba iyaka, sai sun fara zuwa kamar gaske, kwana biyu sai ta hanasu.



   *UMMYN YUSRAH*

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭ADALILIN LINK😭*



      *WRITTEN BY:*

              *UMMN YUSRAH* 


      *EDITOR BY:*

            *QUEEN MEEMI*



    *5*

       

       


Humm! mai hali dai bai fasa halinshi.


Hafsat kam ta koma ruwa, daga tuban muzurun da ta yi. 



Kwanan Mama biyu ta tattara takoma Azare,

Bilki kamar jira take ta tafi, don kwana biyu ɗinnan jin ta take  a taƙure,  yau jitake tamkar Sallah. 


Abbansu Salma na fita, ta shirya su Salma suka wuce Makaranta dake basuda nisa sosai da Makarantar ta gyara Gidan tsaf sannan ta goya yarta taja k'ofar tayi gaba. 



*MAFARIN LAMARIN*


Kwance take kan gado tana chattin a wayarta, taga anturo wani *GROUP LINK* mai suna *(GIDAN DADI)* ko daga hoton  jikin Group d'in kasan bana Mutanen kirki bane, hakan bai hana Hafsat bin link ɗin ba, kasancewar ta mai yawan bibiyar link.




Wasu sai Allah wadai suke ma LINK ɗin, wasu da shedan ya buga musu manga take suka hau Join d'in LINK ɗin.


Bayan shigarsu kowa ta fara gabatar da kanta, daya daga cikin Members tace 


"toh bak'i kowa ta turo hotonta ko zan sami sabuwar ƙawa." 


Take suka fara turowa, wasu sanye da Hijab wasu da gyale wasu ba Mayafi. 


Wata mai suna Ayna tace


                                                                                                           "Habba! wannan wane irin iskanci ne? pic mukace kuturo muga komai bawai kalan mayafinkuba." 


Hauwa tace 


"Habba! dad'i na da ke rashin haƙuri, ki musu uzuri, kinsan sabbin shigane meyuwa basu san komai ba ahankali zasu gane komai." 


Aynah 


 "Uhmmmm! Allah yasa donni kinsanni dason sabon zuma."


Sorphy 



 "Hhhhhhhhhhhhhh! nasanki Ayna ba dama ne wajen harka, abisu asannu zasu fahimci komai."



Shamcy Hot girl



"Munama baki barka da zuwa. 

    *GIDAN DADI*

   *GIDAN MATA MASU 'YANCI*

*GIDAN MATAN DA SUKASAN KANSU*

*GIDAN MANYAN MATA*"

            


ZEE


 "Sai Admin! wannan kirari haka!! ke dai Allahja daranki."


Shamcy


"Godiya nake Mata masu..."


Ummi


"Ku taimaka, yau banda lafiya."


Zully

"Mai ya faru?"


Ummi

"Yau ban da abokiyar rayuwa."


Shamcy

"Hhhhhhhhhh!

Ummi Dadina dake ba wasa yau ina mutuniyar taki?"


Ummi:

"Munsami matsala, ta gujene abani wata don ban iya rayuwa idan ba harka."


Hafsat:

"Assalamu alaikum!

Barkanku da wannan lokacin, ni bak'uwace ina garin Bauchi ina zaune a Gombe road Fatan zamu karu da juna."


Shamcy:

   "Muna miki barka da zuwa, muna bukatar Pic dinki."


Hafsat

"Amin afwa zuwa anjima zan turo."


Zully

"Muna jira."


Shamcy

"Ummi, kizo ga ƴar garinku, kin sami sabuwa."


Ummi

"Ganin aguje, fatar tasan harka, ba dunkum bace ba."


Shamcy:

"In bata sani ba saiki sanar mata."


Ummi

"Angama shugaba."


        


      GIDAN BILKY 


Salmace da aisha suna zaune a k'ofar gida, sun dawo makaranta gidan a rufe nan suka yada Zango, sunata wasa don inda sabo sun saba da yunwa. 


Wani matashin saurayine yazo wucewa ya gansu zaune a waje da ganinshi kasan abuge yake 


"kai me kukeyi anan?" 


"Mundawo daga makarantn kuma gidan a rufe Mamanmu batanan!" 


Duk magar da suke idonshi nakan Salma. naira Hamsin ya mik'ama Salma yace 


"kuje kusayi abu kuci maza kafin Mamarku ta dawo." 


Karba sukayi suka sa gudu shi kuma ya kama gabanshi.



     


Dr. Haseeb ne da yaranshi sun dawo daga makaranta, hannunshi ɗauke da ledar Abinci, da sallama suka shiga falon ba kowa ciki, ya leka d'akinta bai gantaba k'arar ruwa yaji abayi.



 Juyowa yayi ya cire musu kayan makaranta yace su chanza kaya sannan suci Abinci, Idan Ummansu ta fito suce ya wuce ana Jiranshi.


Tana jin tashin motorsa ta fito, ba komai take  a bayin ba, mganane kawai bataso yasa ta shige tayi zamanta. 


      


Ƙarfe goman dare, kwance take kan gado tana Chattin a sabon group d'insu (GIDAN DADI) tanajin Dadin hirar da sukeyi, abu d'aya ya daure mata kai, yadda suketa labarin dad'in da suke kwasa gun 'yan'uwasu mata, itadai Hafcy abun ya d'aure mata kai. 


     Tace don 


"Allah inada tambaya"


"Muna Jinki."

Wata ta bata amsa.


"Naji ku nace idan mace da mace suna harka ya fi dadi fiye da yadda na miji da mace sukejin dad'i, amma dai ba matan Aure cikinku?" 


   Gidan gaba d'aya ya kaure da dariya


Ummi:

      "Akwai Matan Aure cikin mu, akwai 'yan Mata. Tabbas harkar Mace da Mace yafi komai Dad'i Namiji agunmu ya fita ya nemo ya bamu shine Burinmu." 


Hafcy: 

           "Kumin Bayanin group d'in sosai don ban fahimtaba har yanzun" 


Shamcy:

              "Kamar yadda kikaga sunan wannan Gida asama, tabbas haka yake muna d'ebe ma Junanmu kewa muna Jiyar da Junanmu dad'i muna taimakon Junanmu idan hakan ya taso

Kowane Gari muna da k'ungiyarmu Babban Reshenmu yana Abuja muna Meeting Gari- Gari duk k'arshen wata kuma wajibi ne kowacce  shugaban kungiya ta zoda Members dinta akwai matan manya da masu kananan karfi cikinmu amma duk bamai gane matsayin kowa cikinmu, muna Fatan kema zaki zama daya daga cikinmu." 


Hafcy:

          "Na fahimta, Amma tayaye kuke jiyarda junanku dadi? Ko kuna tara kud'adene duk Meeting kurinka rabama Junanku wanda yake da bukata?" 


Zully:

        "Kewai dallah bakida fahimtane?" 



Zeee:hhhhhh! 

"Kawai kumata bayanin yadda zata gane sabuwace sai ahankali"


Ummi:

"Muna jiyarda Junanmu dadine tamkar yadda mace da miji sukeyi

Wannan group din na yan *LESBIAN NE (MADIGO")*

 




*UMMYN YUSRAH*

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*


        *WRITTEN BY:*

               *UMMYN YUSRAH*


       *EDITOR BY:*

               *QUEEN MEEMI*


                *6*



Ummice tacigaba da bayani. 


"idan Mutum ya Burgemu mukanyi k'ok'arin sanyashi cikinmu, idan yaƙi munada mai janyo mana da ra'ayinshi kota halin k'ak'a, muna kuma da alamar da muke gane junansu koda ko mun haɗu a gari, ta yanayin ɗinki, ɗankunne, sanya sarƙa a ƙafa ko zobe a babbar yatsar hannu." 



A haka suka ta mata bayani.


Zuciyar Hafsat ta rabu gida biyu, d'aya na bata shawarar ta yadda, daya na mata hani da hakan. 

     

Ƙarfe uku Bilky ta dawo gida, tun da taga basu Salma tasan suna mak'ota, shigewarta gida ta yi, don ta san in ta shiga gidan yanzu zata isheta da surutun ta cika yawo. 



*Hafsat*


Hafsat ta gama tunanin itama zata gwada wannan tayuwar taji yadda akeji. 


Wayarta ta d'auko ta hau Online tana bud'e Group taga anturo Pic da Video na mata yadda suke Shek'e ayarsu, take taji tana sha'awar Irin rayuwar, hira suke tasha kowacce tana yaba yadda k'ok'arin abokiyar bad'alarta. 


Hafcy:

     "Sannunku"

Ruky:

     "Yawwa sannu dai"

Ayna:

     "Amma ke bak'uwace ko?" 


Hafcy:

      "Eh"

Aynah:

         "Ayyah barka da zuwa wani gari kike? "


Hafcy:

       "Bauchi nake."


Aynah:

      "Kice Garinmu kike nima Bauchi nike, Unguwar mai kafi dai2 Jikin Gidanshi inada Aure da yara hudd'u


Hafcy:

     "Ayyah ni kuma yarana 2"


Aynah:

    "Fatan zamu k'ulla Zumunci" 


Hafcy:

      "Insha Allah" 


Aynah:

     "Muje prvt kituromin Pic naki don na fara kishinki"


Hafcy:hhhhhhhh! 

"Amma ngd"


 Tun daganna suka k'ulla gurb'atacciyar alak'a,

Ayna Gwanace sosai wajen harkar, shiyasa bata sha wuya wajen koyama Hafsat harkar ba, sukan d'auki tsawon Lokaci Awaya ko chattin suna d'ebe ma Juna kewa tare da turama Junansu Pic na sassan jikinsu. 


YAU TAKE ALHAMIS


Yauma kamar kullum Salma Sundawo daga makaranta suka shige gidan ba kowa. 


Bayan sun cire kayansu suka fito waje suka zauna suna wasa, chan Matashin Saurayin nan yazo don tunda ya fuskanci Yaran kullum akebari Gida kullum sai yazo ya basu Naira 50 susai abu idan Ummansu ta dawo suka fad'i mata tayita Murna tanamai godiya taimakon da yake Mata. 


Bayan yazo ya ciro Naira 100 yaba Aisha 


"Maza kije gun mai saida awarar Bakin hanya ta baku na Narai tamanin, sannan ki sayo muku Zobo na Ishirin, ma zaki kawo kuci, ke Salma shiga ki ɗebo min ruwa insha." 


Aisha ta tafi da gudu tana murnar yau zasuci dadi, ko nisan tafiyar bata gani, domin akwai dan tafiya daga Gidansu zuwa bakin Titi. 


Bayan tafiyarta sai da ya duba gabas da yamma kudu da arewa baiga kowa ba ya shige gidan ya jawo k'ofar ya rufe. 





*UMMYN YUSRAH*

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*



    *WRITTEN BY:*

       *UMMYN YUSRAH*


  

     *EDITOR BY:*

           *QUEEN MEEMI* 

  

*Nasadaukar da wannan page gareku dukkan masoyan wannan wannan novel din ngd😘*


   

     *7*



Ya kai kusan rabin awa a cikin gida, da gudu  ya fito yana waige-waige.



Tafe ta ke,  da gani taci kuka ta koshi, tun kafin ta karaso ta haɗu da Maryam Maƙociyarsu, tambayarta tayi 



"meya

faru kike kuka?" 



"Wani yarone ya k'wacemin Naira darina dazan siyo mana awara." 



"Ayyah ki hak'uri Allah zai saka miki, shiga gida ki gaya ma Salma" 



 Gudu ta fito arazane, kafin ta k'araso gareta ta hango Abbansu tare da wata mata sun nufo hanyar gidan.



 "Abbah sauri kazo kaga Addah Salma kwance duk  Jikin ta jini tana kwance."


 Ai kafin ta karisa bayani ya shige Gidan da gudu wacce suke tare ta rufamar baya. 



Abunda ya gani yasashi mutuwar tsaye.  



Wacce sukazo tare ita tayi k'okarin dago ta ba komai Jikinta k'asanta kam ba ko kyan gani. 

Dakinsu ta shiga ta samo Doguwar riga tasa mata sannan ta dauke ta, tace "muje akaita Asibitin nan dake kusa don ko Numfashi batayi"


Taji shuru dagowa tayi taganshi tsaye Hawayen bakin ciki ne kawai ke zuba idonshi, sai data tabashi sannan ya dawo hayyacinsa "muje akaita asibiti don sanin halin datake ciki. "


      *ASIBITIN UMAR ISAH YUGUDA*


Sanda suka isa Doctors sun tashi Aiki sai guda daya itama shirin tashin takeyi  sukai mata bayani, Aikam take ta balbalesu da masifa da irin sakacin da sukeda yaransu, tace


 "ina mahaifiyarta? "


"Batanan nima zuwana Gidan kenan na riske hakan ga Mahaifinta awaje ni yayar Mahaifintane don Allah ki taimaka."


"Gaskiya wannan case din sai an hada da hukuma sannan ayi Bincike wanda ya mata wannan Mummunar aikin".


"Don Allah ki taimakamin ki rufaman Asiri komawa ya mata hakan mun barshi da Allah mudai yanzu burinmu musan halinda Yarinyar take ciki".


Da k'yar ta yarda zata musu Aiki sannan bata bukatar asani don zai iya shafa Aikinta. 



Dr. Khady Gwanace wajen Aikinta wata Ma'akaciya ta kira ta dauki yar suka nufi dakin da zasuyima Salma aiki. 


Yaya faty ta leko gunda ɗan'uwanta yake tsaye. Hakuri tayi ta bashi da Nasihar yadda da k'addara sannan tace ya koma wajen Aikinshi idan angama komai zatamai waya, da k'yar ya yarda ya tafi badon ranshi ya soba, ya koma wajen Block dinsu tunda ya koma ya kasa komai Abokan Aikinsa sai tambayarshi suke ko lafiya yace ba komai don sun sanshi Mutum ne mai k'ok'ari waje Aikinshi Amma yanzu ya dawo ya kasa Aikata komai, da suka dameshi da tambayar yace baijin dadin Jikin shine. 


Yaya faty zaune tana jiran fitowar Dr da Salma amma shiru. 



Sun shafe wajen awa daya da mintoci kafin suka fito wani Daki daban akakai Salma aka kwantar, Sannan ta bukaci yaya Faty ta biyota zasuyi magana. 



"Gaskiya duk wanda ya mata wannan Mummunar Aikin ba Mutane mai cikakken Hankaliba, yanzu haka sai da muka mata d'inki sosai ya riga ya mata kaca2 Sai dai kuringa kula da ita sosai yanzu an mata Allurar bacci zuwa Anjima zata Farfad'o insha Allah akwai Magun-gunan da za'asiya san nan kurink'a mata tsarki da Ruwan dumi da Gishiri insha Allah zata Sami Lafiyay Allah yakare na gaba."


"Mungode sosai da taimakonki Allah biyaki ya karemiki zuri'a." "Ameen ngd."

 "Zaku koma Gidan idan ta Farfad'o sai kimin kwatancen Gidanki zan Rinka dubata acan, tunda kinga taimaka mata nayi bai Shiga Record na Asibitiba." 

 "Toh Dr Mungode da taimako" nan tamata kwatancen Gidan sannan ta wuce Gurin Salma. 


   

   5:00pm

    

Bilky ta dawo Gida tsakar Gida taga Aisha kwance wani Farin kumfa na fita Bakinta tana rike da ciki da gudu ta isa gareta tana Jijjigata Amma ina ba Numfashi, da Gudu ta fita ta shiga Mak'wab tansu don Allah Maman Abbah zaki dubamin Aisha na dawo na sameta kwance ko matsi batayi. 


Mayafi ta dauka suka fito zuwa Gidan tana dubawa tasan rai yayi halinshi. 

"Umman Salma Sai dai kiyi hakuri Aisha Rai yayi halinshi. 


Wani Uban Ihu Bilky ta zuba take Mak'ota suka fito ana tambayar ko lafiy? 

Maman Abbah ke gaya musu abunda ya faru sun tausayama yarinyar yayin da wasu kecewa ta huta wasu kuma kecewa Laifin Uwar sune Allah kadai yasan me taci.

 

" hakuri zakiyi Balki Allah Jikan Aisha yasa ta huta ko wannan kinga ya isheki ishara." 


"Ki kirawo Mahaifinta ki sanar mai don ayi Gaggawar kaita Makwancin ta kar Magrib tayi."


Bakin zaninta ta Lalubo wayar tasa number Abban Salma tamikama Maman abbah tamai magan Bayan ya d'au Wayar tace mai "don Allah yayi kokarin dawowa Gida Aisha Allah ya mata Rasuwa" 


"INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJI'U "

Kawai yake fadi. 


Bayan kashe wayar ya sanarda Abokin Aikinshi suka mai gaisuwace Allah Jikanta wasu kuma suka bishi domin yimata Sallah akaita Makwancinta. 


An kai Aisha Makwanci ta sai Fatan Allah Gafartamata yasa mai Cetone.


Asibiti ya wuce Bayan dawo wansu daga kaita nan yasamu Salma ta farka Amma kuma sai Razana takeyi Addu'a ya yita tofa mata sannan tad'an sami nutsuwa, nan take ya Gaya ma  Faty Labrn rasuwar Aisha yan zuma daga kaita suke duk dauriyarta wannan karon saida tayi kuka.


"Tabbas Bilki ta Cucemu komai ya faru itace Sila, wannan Jarabawa Lokaci guda Mungode ma Allah. 

Allah yabamu ikon Cinye dukkan jarabawar mu."


      Ameen

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*




     *WRITTEN BY:*

               *UMMYN YUSRAH*

       

          *EDITOR BY:*

                  *QUEEN MEEMI*


            *8*


Sai da tai awa guda da mintuna kafin  ta farfado, Alhamdulillah yanzu kam bata razana sai kukan da take na ciwon da take ji. 


Tunda ta dawo daidai sukayi shirin komawa gida.


           8:00pm 


Da sallama suka shiga gidan yaya faty tana dauke da Salma, Bilky ta fito daga ɗaki dauke da wani takarda da guntun kifin daya sha maganin ɓera zata kai shara, taga yaya Faty rike da Salma ita tama manta da wata Salma.


(kunji uwar kwarai) 


"Lahh yaya Faty sannu da zuwa yaushe kika zo?"


"Tun rana nazo." 


"Ku shiga to, sannu da zuwa ita kuma wannan ƙatuwar ce a hannu?." 


Bata jira amsa ba ta wuce zub da sharar.



Bayan ta zubar  tazo suka gaisada yaya Fatyn, tare dayima juna ta'aziyar rasuwar Aisha. 


Nan Bilky ke gayamata


 Ashe kifin data sama b'eraye magani jiya basu ciba, shita d'auka taci yaya Faty cikin bacin rai tace


 "Hummm! koma me ke kika jawo kece silar komai, dama Mamace ta turoni in dubaku sannan inga halin naki Nanan ko kin dai na, nayi waya ma Abbansu Salma yazo ya d'aukeni a tasha muna isowa muka tarar da bakin al'amari. Burinki ya cika Bilky kin kuma kyauta kin kasa zaman gidan aurenki, kin kasa kula da tarbiyar yaranki yau an wayi gari wani azzalumin mara imani mara tausayi yama ɗiyarki fyade ƴar shekara bakwai, ya mata mummunan illar da har abada bazamu taba mantawa da shiba, duk a dalilin rashin zamanki, sai ki shirya tarar hukuncin daga wajen Mama don nasan Abban su Salma bazai taba d'aukar hannu ya Rubuta miki takardan saki ba don kun mana hallacin da bazamu taba mantawa ba." 



Tunda tafara maganar Bilki ke kuka, bata taɓa nadamar abun da take ba sai, yau take da nasanin irin rayuwar data jefa kanta ciki. 



GIDAN DR HASEEB 



Hafcy ce kwance suna waya da Aynah yanzu kam tagama gogewa a harkar, don har ziyara suke kai ma junansu. 


Da sauri ta tashi ta hau gyaran gida tayi girki sannan ta d'au gayu don darling Aynah tace mata ƙarfe huɗu tana zuwa gidanta yau su shana.



Cikin dare zazzabi mai zafi ya rufe Salma numfashin ta Sai sama2 ya keyi, sai nuni ta ke da ƙafa, da gudu Yaya Faty ta kira Abbansu Salma a dakinshi yazo ya ga yadda ta keyi kafin su iso ɗakin su ka ji Bilky ta kurma wani uban ihu tana 


"shikenan, itama ta bita wayyo Allah kutaima kamin." 



Atare suka shigo d'akin don ganin meke faruwa ɗagota sukayi a tare suna Jijjigata amma ina! rai yayi halinshi, Sai dai muce Allah Jikan Salma yasa mai cetone



Aynah tazo sun gama sheke ayarsu, lokacin yara na Islamiyya sai wajen 6:pm sukayi sallama badon sun gaji ba.



Hafcy ta goge ta zama gwana sosai kullum suna bin gidan kawayen harka irin tasu harta kai ga yanzu ko kula Dr Haseeb ba tayi balle taji wani Sha'awarshi abun yana mugun damun shi gashi yafara jita-jita wajen mutane, yadda mata ke zarya a gidansa, shi dai kam bai yadda ba tun da bai gani a zahiri ba, ya dai bar abun a ranshi yakuma kudurama ranshin insha Allah zai riƙa dawowarsa bazata.



Haka suka kwana da gawan Salma da suba bayan idar da Sallah Abban Salma ya sanar a masallaci anyi rasuwa a gidanshi zuwa karfe takwas insha Allah za'a mata sutura. 



Sakamakon Maganin Berar da sukaci a abinci shiyayi ajalin yaran nashi Gaba daya. An mai ta'aziya da Alƙawarin insha Allah zasuzo akwaita Makwancinta.



Mak'ota duk sunji lbrn Mutuwar Salma itama Dalilin cin kifi mai Dauke da Maganin Bera 



Maman Bilky da 'yan Uwanta dake Azare duk sunzo Sai dai suma ance Musu kifi sukaci da Magani ajiki don Abban Salma ya Roki yaya Faty dasu Boye Gaskiyar Al'amarin domin Maman Bilki uwace agaresu basuda kowa bayan ita idan taji Gaskiyar lamarin Tabbas zata iya Tsinema Bilky. 



    WAIWAYE ADON TAFIYA


Asalin yaya faty da sani(abbansu salma) 'yan jos ne, cikin garin mongu wani fadar kabila da akayi akasama gidansu wuta cikin dare gaba dayan al'ummar gidan suka kone, yaya faty da kaninta kawai suka tsira tsirarun mutanen da suka rage kowa ya kama hanyar neman tsira duk suka watsu cikin jeji hakan har Allah ya kawosu cikin garin Bauchi bakin tasha suka zauna lokacin mama Hadiza takawoma kanwarta ziyara datake garin bauchi zata koma tazo wucewa yaya faty tace "don Allah mama ki taimakamana da abunda zamuci, yau kwnananmu uku bamuci komai ba." nan take taji tausayinsu tace "daga ina kuke ? Ina iyayenku?" aikam nan take suka fara kuka, yaya faty ta sanar mata daga inda suka fito da abunda ya faru da danginsu ta tausaya musu matuka, ta gaya musu itama ba nan garin takeba, daga azare take idan sun yadda zasu bita zata rikesu ba musu suka amince.


Mama Hadiza tasai musu abinci ta biyamusu kudin mota sai azare.



A haka sukaci gaba da rayuwarsu cikin rufin asiri Mmn Hadiza mijinta ya rasu, tana zaune da yaranta uku biyu maza daya mace Bilky yar auta 


Haka sukaci gaba da rayuwarsu, Sani dama bamai yawan magana bane komai akayi baice eh balle aah.



Cikin rufin asiri mama hadiza ta aurar da faty anan azaren lokacin sani yana zuwa bauchi kawo kayan gwanjo duk ran jumma'a kasuwar C&C, yana samun budi sosai anan suka hadu da wani bawan Allah mai gidan block, yace idan ba damuwa yadawo bauchi da zama zai bashi wajen zama sai yarinka aiki a wajen don ya yaba da hankalinshi.


Tun daga sannan ya dawo cikin bauchi da zama har yasamu yayi gininshi yar madaidaici yaso mama hadiza ta dawo amma sam taki, tace batason rabuwa da abokan arziki sai dai yasamo mata ayi maganar aure in yaso ya sata gidan. 




Yace shibaida kowa yabar ma mama zabi a hannunta, taji dadi sosai tace idan sunyi shawara da faty zata nemashi.



Bayan tasami faty da zancen ko da wacce ta yaba da hankalinta tace "mama ai basai ansha wahalar neman mata ba, matanshi tana gida, ga Bilky mezai hana a hadasu"


"Anya faty kinaga hadin zaiyi kuwa? kinsan halin kanwartaku akwai tsiwa da rawarkai, kar azo ana dana sani, insha Allah hakan bazai faruba."




Ansha shagalin biki aka kai amarya gidan tare da gargadi da nasiha mai shiga jiki, sai Fatan Allah yabaku zaman lafiya.

[12/14, 3:12 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭ADALILIN LINK 😭*



    *WRITTEN BY:*

              *UMMN YUSRAH*


    *EDITOR BY:*

           *QUEEN MEEMI* 



         *9*


Bayan kai Bilky gidanta zaman lafiya suke da kaunar, juna har Allah ya azurtasu da yara biyu salma da aisha.



Tun daga wannan lokacin kuma halayen Bilky ya sauya, ta tsiri yawo gidajen makota wanda hakan ya haifar da mummunan al'amari. 


          

        11:00am  


Dr. Haseeb ne ya shigo gid cikin sauri, ya dawo daukar mantuwar da ya yi dakinshi ya shiga ya dauko wasu files  ya fito, yaga jaka da takalmi ya gani da kuma mayafi kan kujera, da alama bakuwa sukayi a gidan sai dai kuma gidan shuru kamar ba kowa, kicin ya nufa a tunaninsu ko suna can, wayam ba kowa, hakan yasa ya  nufi ɗakinta, tun kafin ya isa ya ke jin faɗuwar gaba.



 Murda k'ofar ya yi ya shiga, ba kowa falon, kuma ba alamar maganar mutane.


Ciki ya nufa, tun kafin ya shiga ya ke jin wani kalan nishe-nishe.



Da sauri ya juyo, yana laluben yanya, yayin da bakinsa ke furta.

 INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJI!


Ƙafar ya buɗe ya dawo babbar falo, ya zube kan kujera.



        DAKIN HAFCY


Ƙarar rufe ƙofar ne ya dawo da su daga duniyar da suka lula,wanda da sam basu ji buɗewarba.



Gaba daya hafcy ta gama razana ita kuwa Ummy haushine ya gama kamata don tana tsaka dajin dadi, gashi an katse musu.



 Juyo wa ta yi tana kallon hafcy "meye kiketa wani karkarwa kamar mazari? don kawai kin ji ƙarar ƙofa sai ki ruɗe? Idan ma mijin ki ne ba sai muje a rufe bakinsa ba, abu mai sauki har zaki wani ɗaga hankali!  Duk kin rude haka? Amma Allah sauwake, ni mikomin kayana kawai ya ragen jin dadi."


Sanya kayan ta tayi tana ta ƙunƙuni, da tazo daf ƙofa ta ce


"Idan ya koro ki kizo gidana, ina maraba dake."


Falo ta fito ta dauki jakarta da takalminta, sai da ta zo daidai gun dr zata wuce taja wani dogon tsaki, "kawai kawani ragema mutum jin dadi."


 tasa kai tayi waje gami da huro ƙwaton ƙwai da cingam ɗin da ke bakinta.



Wayarshi ya dauka ya kira mahaifiyarshi.


"Assalamu alaikum!

Umma!"


"Wa'alaikumussalam,

Ya naji muryarka wani iri lfy dai ko?"


  "Ummah ba lafiya, gani zuwa gidan."


Umma


   "Sai ka zo, ka kula da hanya."


Tashi yayi ya nufi motarshi, a guje ya figi motar.




Tana jin tashin motarshi, da sauri ta tashi ta hada kaya cikin akwati ko ina zata ohho. 


Bayan ta fito wani takarda  ta ajiye kan kujera, tayi hanyar fita sai kuma ta tsaya ta karema falon kallo, idonta na zubar da hawaye sannan ta juya ta fice bako waiwai.





    GIDAN UMMAN HASEEB 


Haseeb na kuka yana sanar ma Umma  mummunan al'amarin da ya gani cikin gidanshi.



 sallalami umma ketayi tana kumawa "wannan wacce irin rayuwa hafsat tajefa kanta? har tsawon wani lkc ta dauka tana aikata wannan mummunan aikin da ubangiji yayi hani dashi? lallai wannan tashin hankali Yakai matuka tayaya hakan ta faru? Yaushe ta jefa rayuwarta cikin sabon ubangiji haka? 


"Tabbas umma wannan illar wayace, kullum nasiha nakemata kan nacema waya, amma bata daukar maganata inajin jita2 hakan a unguwa wasuma har wajen aiki suke samuna suke sanarmin Saidai nakasa daukar mataki akan hakan, tabbas umma nayi sake."


 magana yake yana kuka 


"Ka tashi muje chan gdn naka, barinsa rahma ta dauko su sabeer daga mkrnt."



Bayan isarsu gidan falo umma ta zauna tace ya shiga ya kirota 


Tunda ya nufi kofarta gabanshi ke faduwa yanaga kamar zai kuma karo da abunda yagani d'azun, tundaga kofa ya fara karo da kaya gaba daya dakin ahar gitse bakowa ciki ya leka bayi ba kowa ciki da karfi yace "ummmmmma!!!"


"Haf...haf... haf..." kawai yazube kasa, da gudu umma tashigo warwas ta ganshi akasa da alamar dakin ba kowa gashi kaca2.



 Isowa tayi tana jijjigashi innah ba alamar numfashi, da sauri ta koma falo ta dau wayarta ta danna kiran khamees abokin haseeb.


 Yana dagawa tace "kazo gdn abokinka yanzu2." bako jiran amsa ta katse wayar ruwa ta dauko mai sanyi ta yayyafamar amma ko motsi baiba.



Khamees da sauri ya fito daga office nashi, ga tarin mutane suna layi amma haka ya wuce, don bai san dalilin kiran da akamai ba.


 Cikin gaggawa haka bayan ko awa basuyi ba da rabuwa da amininshi 

Allah dai yasa lfy?


Bayan isowarshi kai tsaye ya wuce cikin gidan, Sai dai kamar ba mutane sallama yy daga ciki umma tace ya shigo.


 kwance yaga amininshi ba alamar numfashi atare dashi da sauri ya isa gareshi yana tambayar umma ko lfy 

Umma na kuka tanacewa ba lfy khamees dubamin abokinka 


Nan yashiga aikinsu na likitoti kusan minti 20 kafin yasamu ya dawo allurar bcc yamai sannan suka koma falo shida umma.



"Umma lfy kuwa naga haseeb cikin wannan munnanan yanayi? bayan lfy muka rabu yazo gida daukar wasu files sai kuma inzo ingashi haka, Sannan kuma ina hafsat? 


"Khamees inafa lfy? hafsat ta gudu bayan tabka mummunan aiki." 


Take gabanshi yafara bugawa,kar dai yau sunyi karo da mummunan aikinda matar amininshi ke akatawa? 


"Ummah don Allah sanar dani mai ya faru? kar dai yau haseeb yaci karo da abunda matarshi take aikatawa?"


Juyowa umma tayi tana kallonshi 


"Dama kasanine?"


"Eh umma! munyi mgnr ko jiya da haseeb,

Akwai wata mata unguwar mu kowa yasan kazamin aikin da take aikatawa sunanta Ummy tayi sanadiyar lalacewar mutane da dama sai kuma naga hafsat ta fara mu'amala da matar, sau uku ina ganinta tana zuwa tunda nakamata na ukun na nacemata saina sanarda mujinta sai tace ba wani abu tsakaninsu kaya kawai take saya wajenta 

Munyi mgn da haseeb akan duk sanda na kuma ganinta in kirashi awaya zaizo har wajen ya tabbatarda gaskiyar lamarin. 


Umma tace "ikon Allah! ashe ta dade cikin lamarin Allah ya shiyeta da duk y'an uwanta masu wannan hali, wannan abu ne neman zama ruwan dare ne... Allah ya shirye su da mu baki daya.


ALLAH MUNTUBA BADON HALAYENMUBA


ALLAH KATSAREMU KA TSAREMANA IMANINMU ALLAH KARKABARMU DA IYAWARU


ALLAH KAMANA JAGORA ARAYUWARMU KA KAREMU DA FADAWA HANYAR SABA MAKA



nan umma ta kwashe komai ta fada mishi


"Umma toh yanzu ina zamu nemota?"


"Babu! tunda rayuwar data zaba kenan Sa dai mumata Fatan shiriya, ai ba korarta mukayi ba, ita ta kori kanta don haka taje duniyace. Wanda bai zo ba ma  jiranshi take."

[12/14, 5:53 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭ADALILIN LINK 😭*



     *WRITTEN BY:*

             *UMMYN YUSRAH*


      

 *EDITOR BY:*  

          *QUEEN MEEMI* 

        

         *10*


Wajen k'arfe hudu Haseeb ya farka Sai dai harya fad'a Lokaci guda, wanka yayi sannan yayi Sallah, kadan ya iya cin Abinci shima don Umma ta Matsamai ne. 


Hakuri tayi ta bashi da kuma Nasiha sannnan ya tayima Hafsat Addu'ar Alkhairi da fatan Allah shiryar da ita ya dawo da ita lfy."


Khamees yaje gidan Ummy ko gidan taje ba'asa metaba anje 

Gidansu nan ma batanan,



 Sallama suka ji daga waje bayan sun amsa suka bada izinin A shigo.

Wani dattijone ya shigo da ganinshi akwai dattako da Nagarta tare dashi, yana shigowa   Haseeb ya sauka y koma kasa. 



Bayan yasami waje ya zauna suka gaisa da Umma sannan Haseeb ya gaida shi.


Malam Usman kenan Mahaifi ga Hafsat 

Yace "dazu na dawo gida ake sanar min da wani Mummunan Al'amari 

Shine nazo don inji Gaskiyar Lamarin." 


Ummace tabashi lbrn komai 


Hakuri yata basu tare da nasiha sosai ma Haseeb insha Allah zansa ayi cigiyarta gidajen 'yan uwa, yanzu ka haifi Mutum ne baka Haifi halinshi ba k"arshen Duniyace tazo Masifu iri_iri an maida 

Zina, Luwadi, maɗigo, tamkar abun Burgewa ba komai bane yanzu don Mutum ya kashe d'an'uwanshi ya cire sassan Jikinshi yayi wasu sidda barun, ba komai bane Agaremu mun riga mun d'au son Duniya mun d'aurama kan mu ko kad'an mun mata da Ranar Hisabi, mun d'orama Ranmu zamu raya idan munso zakuma mu kashe idan munso, mun manta da Allah Mun maida wasu kaskantattun bayi sune masu biya mana bukatunmu Matanmu da Mazanmu mun maida Bokaye tamkar sune abun biyan bukatunmu.

Shin wai akwai abunda wani bawa zai ma wanda yafi kanema gurin Mahaliccin kane?" Inda suna Azurtawa meyasa koda yaushe suke acikin k'ask'anci? duk randa muka taka kafa wajen wani Boka munyi Babban shirkane Sallarmu na kwana 40 babu karb'ar shi.

kullum fad'akar damu ake Amma shedan sai buga Gangarsa yake akan mu, Allah kuma ya barmu da iyawarmu ya barmu da halinmu Gamu ga Duniyar muyi duk abunda mukeso karshenta kasa zamu koma zakuma muje mu tararda ubangijimu Allah ka yafemu." 


Hakuri yata basu da nasiha sannan ya musu sallama ya tafi.



Duk inda ake zaton samun hafcy anduba ba ita ba lbrnt, wayartama bata shiga haka aka hakura. 



Yau kwana ukun salma, mama suna zaune da wata y'ar uwansu ta kalli Bilky tace "Anya Hadiza ƴarnan ba za a nema mata maganin yawonnan ba kuwa? Ki duba fa ki ga yadda ta fiye yawace-yawace kamar mai mutsamutsai."


"Ba wani mutsamutsai! Iya shege ne kawai, da zunzurutun gulma da kwaɗayi da ke damunta, nasan halinta ya yi sanadiyar mutuwar yarannan, inda ta nutsu ta dafa ta basu ba abun da zai sa su bi na maganin ɓera, amma nasan me zan yi."



Sani

"A yi haƙuri Mama, mai rai baya wuce ranarsa."


"Hmmm! Sani haƙuri ai ya zama dole, Allah dai ya jiƙansu."


Duk suka amsa da Amin, banda Bilky da ke ta rusar kukan nadama.


     


An yi neman duniyar nan ba'a sami Hafcy ba, k'arshe dai aka hakura aka bar ma Allah komai.



Da kyar aka samu Dr ya dawo  dai-dai sai dai kullum yana yi mata  addu'ar shiriya da fatar dawowa lafiya, domin gani yake duk laifinsa na.



A kullum ya kalli yaransa ƙara tausaya musu ya ke.



Kwanansu bakwai suka tattara su ka yi Azare, har da Bilky, don Mama ta ce ma Sani zasu tafi ta je ta huta tun da zaman gidan ne ya isheta.



Tun da suk koma Mama ta sakar mata duk wani ɗawainiyar gidan, ko ta gama aiyukanta sai ta sake zaƙulo wani.



Taso ta sake nema ma Sani mata sai dai Aunty Faty ta bata haƙuri, don gudun kada a sake wani auren haɗin azo ana maimaita ƴar gidan jiya kuma, a barshi idan ya yi niyya a gaba zai sami matar da kansa, ita kuma muna mata fatar shiriya.


Sai da Bilky ta yi wata biyu a gida, duk ta jigata ta gaji da zaman gidan, ta matsu ta koma ɗakin ta, sai dai Mama ta kasa ta tsare.


Da ƙyar Aunty Faty ta shawo kanta ta, barta ta koma koma ba tare da ɗan rakiya ba. Ta kuma yi mata gargaɗi sosai, matuƙar ta ga wani kuskure zata yaba ma aya yaƙi ta.


Haƙuri sosai ta yi ta ba Sanin wani zuwa da ya yi.




    BAYAN WATA SHIDA



Abubuwa da dama sun faru, sai dai Fatan Allah kyauta.



Tun ana saran dawowar Hafcy, har an gaji da jiran tsammani.



Dr.haseeb har ya gaji da korafin Umma, kan ya kamata ya manta komai yanzun yasamo ma ya'ya'nshi uwa, don zamanshi ba mace baiyi tsariba. 



Tun faruwar abun yaran suke gidan Umman tun kwana biyu da kawosu suka fara kukan a kaisu wajen Ummansu .


Tun da aka ce musu ta yi tafiya, suka share zance, dama ba wani shaƙuwa ce tsakanin su ba, sun ma fi sakewa gidan Umman.


Yawan zancen ya sake Aure yasa yanzu sai ya yi kwana biyu ko uku baije gidan ba, don shi yanzu mace tsoro take bashi. 


   ATBTH BAUCHI 


Dr. Haseeb ne zaune cikin office dinshi yana duba mata masu matsala, yau kam akwai mutane sosai ga tun takwas na safe yake fama da mutane, gashi har yanzun kusan shabiyu ba alamar zasu ragu. 



Mafi yawancinsu masu matsalar Infection Sai 

Masu family planning, 

wasu sunyi amfanida kwayoyi wasu Allurai,

Wasu kuma sunsa robar hannu gashi ya jawo musu matsalar zubar jini, wasu ɗaukewar al'ada, wasu kuma haihuwar ma taƙi zuwa duk da sun bar yi.


Wasu kuma wata matsalar ta daban.


Wata kyakkyawar budurwace ta shigo cikin nutsuwa, sallama  tayi dawani sassanyar murya mai cike da nutsu, hakan ya yi sanadiyar ɗagowar Dr. da sauri, har ta iso gabansa bai bar kallonta ba.


Bayan ta zauna, ta sadda kanta ƙasa ta yi, sannan ta ce 


 "Barka da Aiki Dr"


"Barka dai" 


Miƙa  katinta ta yi, gami da yimar bayanin daga   G. O. P. D

A katurota nan 

Yace ok "meye damuwar?" 


Sunanta ya duba yaga YESMEEN TAFEESU MUHAMMAD 


A Zuciyarshi yace lallai kinci sunanki TAFEESU 


Tace "dama...! dama...!!" kanta na kasa sai in ina take.


"Nan fa asibiti kikazo don samun lafiyarki, yana da kyau ki saki jikinki kiyi kyakkyawar bayani, domin da hakan zan gane meke damunki, tunda kinga gunda suka turoki ba suyi wani rubutu game da matsalarki ba, ki aji  kunyarki agefe idan kin gama bayani sai ki maida abunki, akwai kyakkyawar fahimta da kulawa tsakanin likita da mai jinya, inaji bayanin ki."


"Dama duk lokacin da zanyi period ina yawan ciwon mara sosai wani lokacin har suma nakeyi ga shi yana zuwa da yawa."


Kintaba zuwa ganin likita Tunda kika fara jin hakan? 


"Eh ina zuwa sai dai konasha magani baya bari, sai dai in ɗaji saukin kadan."


Tana maganar ne ƙwalla na fitowa daga idaniyarta.


"Ki shuru! Wannan ba wani  matsala ba ne, barin rubuta miki magani, insha Allah zaki sami lafiya, ina dai har zaki jurema sha, ba tare da kin bari ba."


"To! Dr. Nagode."


Bayan ya rubuta ya mika mata katin, tayi godiya ta tafi. 


Wunin ranar dr. Da tunanin kyakkyawar fuska da zazzakar muryar ta ya wuni. 




Muje zuwa don jin yazata kasance 

  

Taku har kullum mai kaunarku 


   YAR MUTAN 


BAUCHI KEMUKU FATAN ALKHAIRI

[12/14, 7:38 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILININ LINK😭*


   *WRITTEN BY:*

           *UMMN YUSRAH* 


*EDITOR BY:*

       *QUEEN MEEMI*


   

    *11*


    *GARIN KADUNA*


Wasu kyawawan matane suka fito cikin wata rantsatstsiyar moto, da ka gansu kasan hutu da jin daɗi ya ratsa jikinsu, farinsu har ɗaukar ido ya ke, tsabar sun sha mai.




Kemis ɗin suka nufa, duk da ba alamar rashin lafiya a tattare da su.






Wani san k'amemen k'aton inyamuri ne zaune ciki, ga dukkan alamu shi ne mai ɗakin sai da maganin. Yana ganinsu ya washe baki, d'aya daga cikinsu tace "Oga James kawata na kawo agyaramin ita sunanta Hafsat."


Dariya ya yi, sannan cikin gurɓatacciyar hausarsa ya ce


"Kice tana so ta zama cikakkiyar babbar Baby?"



"Kwarai kuwa! Amata allurar da kamin na k'arin ƙirji da ƙugu." 



"An gama Zeenah! indai da kudi komai mai saukine." 



Bayan fitowansu gida suka nufa.


Ɗan  madaidaici gida ne,

idan kashigo daga Gate akwai wajen ajiye motoci guda biyu, sai harabar gidan dake d'auke da fulawoyi sai kofar shiga cikin gidan. 


Kana shiga wani falone madaidaici yasha gyara ga kamshina tashi, ba wani tarkace cikin shi, sai Dakunan kwana biyu ko wanne dauke yake da falo da cikin ɗaki, kicin da ban ɗaki. Cikin falon akwa kicin da  store.



 Gidan ya tsaru ba laifi, ga ko ina a tsaftace, kasancewar mai gidan Zeenah akwai son tsafta gason kamshi. 



*WAIWAYE ADON TAFIYA*


Bayan barin Hafcy gida jos ta nufa gidan wata kawar lafiya, sunkai wata hudu suna tare daga baya suka hadu da zeenah awani grp nasu na y'an les mai suna AJI DADI.


Zeenah karshece wajen les tayi sanadiyar tsunduma mutane da dama, tana harka da matan manyan kasarnan har gd da motoci biyu ta mallaka yar kwalisace ta karshe. 


Tun haduwarsu da hafcy a grp suka kulla  abota, har takai hafcy ta kawo mata ziyara akan kwana biyu zatayi gidan zeenah dake kaduna, ta koma jos.


Amma sai gata har sati biyu, suna morar juna ba labarin komawa daga baya take sanarda zeenah ta gudu daga gidan mijinta yanzu intabar nan batasan inda zataba.


Tace indai ba matsala tayi zamanta anan, tunga lkcn zamanta ya dawo KD anan suke tsula tsiyarsu suke sha'anisu, ga jibgegen ƙaton kawalinsu da ke musu hanyar manyan mata, wa'inda kafarsu ta kama ƙasa.


Yesmeen ce zaune gaban Dr. Haseeb, ta dawo sakamakon wa'adin sati biyun da aka bata ya ƙare.


Bayan ya gama tambayarta yanayin jiki kuma ya sake rubuta mata magani, daga nan kuma tambayar ta canza salo, inda ya buƙaci lambar wayarta domin ƙiranta ya ji yadda jikin nata yake.


Wayarta ta ciro tana sa lamba, shi mamaki yake da yaga wayar dake hannunta yanzu.


 A ce budurwa kamar wannan tana rike karamar waya haka lallai akwai abun mamaki! don irin rawarkai da dogon baru na y'an matan yanzu ba abunda zaisa surike irin wannan wayarda ko memori batada balle ta yi, catin, lallai taci sunanta na Tafeesu.


Ringing yaji a wayanshi yaga number, 

Yayi svn sannan sukayi sallama. 



*BAYAN WATA UKU* 


Hafcy ta gama cika ta batse, kirjinnan ya gama cikowa kamar zai fasa riga ga ƙugunnan shima, masha Allah. 

Duk wacce ta kalleta sai ta kara tayi kyau sosai na gaban kwatance.


Ta zama babbar mace, kwarrariya wajen harƙa, suna kaima junansu ziyara garuruwa da dama.


Haka suma ana kawo musu, basu da wani aiki da ya wuce wannan. 



Bilky ce a kicin tana ta kiciniyar ɗaura girki, ta ƙara ƙiba ta yi kyau, yanzu kam Alhamdulillah! 

Komai ya daidaita, ta ma kanta ƙiyamullai gami da jin horon Mama, zama suke naso da kaunar juna. 




*UMMYN YUSRAH*

[12/16, 4:36 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*



        *NA UMMYN YUSRAH*



*TACEWA*

     *QUEEN MEEMI*



*12*




Dr. Haseeb dai daga gaisuwa, an koma soyayya, zance har gaban manya, abu ya kai har da sanya rana, jira kawai ake a sha biki.




Zeenah ce rungume da Hafcy, bayan sun gama baɗalarsu. 



"Wallahi zumata, ji nake kamar kar inje taronnan! Don ko kaɗan banson inyi nesa da ke, da da yadda zanyi da da nayi don guje ma zuwa."



Cewar Zeenah



Hafcy tace "daurewa za ki yi kije, kinsan babban taron  jahohine, kuma duk sharaka sau ɗaya akayi, idan ba'aga ko ɗaya cikinmu ba zasu karbi tara sosai, ga kuma auren su Meenal da Zeeta, Karina da Meenal da za a ɗaura, kinga gara ki je ki sha kallo, kafin shekarar gaba a ɗaura namu."


Wani daɗi ne ya rufe Zeenah, ta ƙara rungume Hafcy gami da haɗe bakinsu waje guda.


Sai da Hafcy ta ɗan bubbuga kafaɗarta, alamar ta sake ta.


"Ki je ki shirya fa kada ki makara, kinsan ƙarfe takwas na dare za ku fara."


"Da kin barni, ai da sauran lokaci, yanzu fa tara ne na safe, Abuja ne fa ba Lagos ba."


"Duk da haka, gara ki tafi da wuri ai, kinga kafinnan kin huta ai."


"Ke dai kawai korata ki ke na gane, ko dai kin samu wata sabuwa ce?"


"Ko ɗaya! Kin san banson tafiyar dare ne, nima kuma ba don ciwo ba, ba abun da zai zaunar da ni."



"Haka ne! Allah ya baki lafiya, kiyi kokarin zuwa ganin likita kafin in dawo. Ki kularmin da kanki."



"Zan yi yadda kika ce."


Murmushi duk sukayi, ta shafi gefen kumatunta sannan ta shige banɗaki."



Cikin lokaci ƙalilan ta fito cikin shirin tafiya, har jikin mota Hafcy ta rakota, suna maƙale da juna, da kyar suka rabu, kowa ta juya cike  da kewar juna kamar ba za a sake haɗuwa ba.




 Hafcy tayi ciki, don shiryawa zuwa ganin likita.



Zeenah kuma tayi gidan shugabarsu na KADUNA, don dukansu anan zasu haɗu, da katuwar bus dinsu na kungiya da suke tafiya gari-gari taro, yau kuma ABUJA suka nufa sai muce Allah kyauta. 



Bayan Hafcy taje asibiti, tama Likita  bayanin damuwarta, fatar bakintane ke fidda wasu kananan kuraje ga kuma, ƙasanta da ke fidda wani irin ruwa, da ƙananan ƙuraje, ga ƙaiƙayi, ga kuma yawan ciwon  ciki.


Gwaje-gwaje ya bata da kuma hoton ciki.



 *ABUJA*


Wani ƙayataccen masauƙin baƙin mijin ɗaya daga cikin su suka tsara don yin taron.



Wajen ya tsaru sosai, jiƙaƙƙun matan da suka jiƙe da naira da kuma wanda suka goge a duniyanci da kuma kawalansu maza duk sun hallara.



Taron mata ne, iri da kala, daga jahohin ƙasar nan.


Ba abun da ke tashi wajen sai kaɗe-kaɗe da raye-raye, bayan gama gabatar da taron aka shiga ciye-ciye gami da shaye-shaye na kayan zaƙi da na maye.


Bayan kammala cika ƙundu, aka shiga shirin ɗaurin aure.


Matane su huɗu zaune a wasu ƙayatattun kujeru, ko waccensu manne da juna, kowa yaci kwalliyar kece raini, nan aka shiga ɗaurin auren yayin da amare da angwayen suka kasance jinsi guda.



Hayaƙi ne ya turnuƙe waje, kafin kace me duk wajen ya kaure da tarin jama'a kowa sai neman hanyar fita ya ke yi, sai dai duhun hayaƙin ya hana ganin hanya, ga wutar lantarkin da ya haske wajen kamar hasken rana ya ɗauke.



Wutane ya kama gidan ganga-ganga, wanda aka rasa daga ina ya faro kuma meye musabbabinsa.


Tun suna iya ihu, har wutar ta lanƙwamesu, ba abun da ya rage sai burbushi.



Motocin kwana-kwana ne har uku, da ke ta aikin kashe wutan, zubar ruwan tamkar zubar fetur, sam yaƙi mutuwa, sai da ya gama ci tas kafin ya kashe kansa.




*UMMYN YUSRAH*

[12/19, 8:03 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*



      *RUBUTAWA:*

              *UMMYN YUSRAH*



    *TACEWA*

        *QUEEN MEEMI*




*13*



Kafin ka ce me, labari ya karaɗe gari, gidajen rediyo da tibi da ƴan jarida kuwa tamkar jira suke, nan suka shiga aikin yaɗa labarai na kdawsaye.



Hafcy da tun da ta dawo daga ganin likita, bata sake fita ba, zaune ta ke kan kujerar ma cin mutum ɗaya, wayar da ke hannunta ta ke ta faman dannawa, ga dukkan alamu ƙira ta ke baya shiga kuma, ta ƙira ya fi a ƙirga shiru.



"Ina Zeenah ta shiga ne haka? Sam wayarta ta ƙi shiga, lafiya kuwa? Ɗazunnan mu kayi waya fa, ba dai matsalar caji ba ne."


Ita ɗaya take sambatunta, can wata zuciyar ta ce "kema kin san Zeenah ba haƙuri ne da ita ba, tana can ta sami wata suna holewarsu shi yasa ta rufe wayarta."


Take ƙirjinta ya fara harbawa, cikin sauri ta fara ƙiran wayoyin ƴan'uwan nata da ke can don tambayar inda Zeenan take.



Duk wayar da ta ƙira baya tafiya, ta rasa meye dalili, ba kuma a kashe yake ba, miƙewa tayi ta nufi gun tibi ta kunna, juyawa tayi ta bada baya don komawa mazauninta.



Juyawar tata ya yi daidai da sanarwar gobarar da ta kama, cak Hafcy ta tsaya gami da juyowa, gabanta ne ya tsananta faɗuwa, jin yadda ake labarin wutar ta cinye komai ba tare da wani ya tsira ba.



Hatta musabbin taron sai da aka faɗa, inda mutane ke ta faɗar albarkacin bakinsu, na Allah wadai da Allah ƙara.



Suman tsaye ta yi a wajen, gaba ɗaya ɗakin juyawa yake mata, duniyar ma gaba ɗaya ta fita kanta, ihu mai ƙarfi ta rusa gami da zubewa   a waje.


"Wayyo Allah na! Me yasa? Nayi danasanin rashin zuwane, da na sani na biku muka tafi tare, domin sam zamana bai da wani amfani."



Haka ta ɗau lokaci tana ta zuba sambatu, sai kuma ta miƙe a razane, kamar wacce aka tsikara,  ja da baya ta fara yi, tare da ƙare ma gidan kallo, gami da tunano al'amuran da suka faru baya, da sauri ta fice ta bar gidan ba tare da ta ɗau koda tsinke ba.



Domin gidan ya fara bata tsoro kuma kada kuma wutan ya biyo ta nan ita ma.



Duk da dare ya fara nisa hakan bai sa taji ko ɗar na tsoro ba, tafiya kawai ta ke bata ma san inda zata ba.


Gaba ɗaya garin ya fita ranta, hanyar tasha ta nufa, duk da nisan wajen sam yau bata ganshi ba.



Tashar ba komai sai taron motocin kabo-kabo, tsakanin motoci ta samu ta maƙale zuwa safiya, don ta gwammace kwananta a nan da gidansu, tun da ta fito bariki bata taɓa tunanin gida ba sai yau.



Yanzu idan ta je garinsu ina zata dosa? Gidan mijinta ko gidansu? Ina yaranta suke? Wani hali suka shiga bayan ta? Ina Haseeb ɗin ta? Ina iyayen ta? Wani hali suka shiga bayanta?



Sai yau wannan tunanin ya faɗo mata, bata taɓa tuna hakan ba, domin rayuwa ta yi daɗi, ta manta da komai nata ta sanya sharholiyar duniya a gaba.




Anya zata koma gida haka kuwa? Idan ta je a wannan yanayin na rashin lafiya ya zata ƙare da jinyar kanta, tun da ba abun da ta ɗauka gidan.



Ko dai zata koma ta ɗauko kuɗi ne? Kai ba za ta iya ba, ta bar gidan har abada, gara ta koma gidansu na Jos ta yi jinyar kanta.



A haka ta kwana a tashi har gari ya waye, bayan ƴan tashar sun fito da aka ganta tambayoyi akai ta yi mata.



Ƙarya ta zauna ta shirgo musu cewar, ita ƴar Jos ce ta hau abun hawa  daga unguwar gangare zai kai ta kasuwar taminus, tun da ta hau bata san inda ta ke ba sai ganinta ta yi a can kan hanya, ta nuna da hannunta, sannan ta ci shine ta dawo tsakanin motocin ta kwana.



Ganin yadda ta fita hayyacinta ko mayafi babu jikinta, ya sanya suka yadda kuma suka kuma tausaya mata.




Motar da zata Jos aka sanya ta tare da sanar da direba da zarar ya sauƙin fasinjoji sa ya kaita har gida.



Nan motarsu ta lula sai garin Jos.



Sun iso garin Jos lafiya, Hafcy ce ta faki idon direbar ta bi layin fasinjoji masu fita.


Neman duniya direba ya mata bai sameta ba, haka ya haƙura.




*UMMYN YUSRAH*

[12/23, 7:58 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭 A DALILIN LINK😭*



   *RUBUTAWA*

         *UMMYN YUSRAH*



     *TACEWA*

            *QUEEN MEEMI*



*14*


Kai tsaye gidan Zuzu ta wuce, ta kwashi tafiya sosai, a gajiye ta isa gidan.



Ba ƙaramin mamaki ta yi ba, ganin gidan Zuzu a buɗe.



A tunaninta itama ta tafi gunrin taron ƙungiyar, tunda sun yi waya, ta sanar mata zata itama.



Dalilin zuwan ta gidan ma don tasan, Zuzu bata tafiya da key, don gidan nata bai rabuwa da mutane, hakan yasa take barin key a wani maɓoyar da su suka sanshi.



Kutsa kai ta yi, tare da sallama.


Da sauri Zuzu ta ɗago kai daga kallon tibin da take yi, yayin da wani shahararren Malamin addini ke ta zubo wa'azi mai shiga jiki da ratsa zuciya, game da iftila'in da ya faru da ƴan ƙungiyar maɗigo a Abuja.



Da gudu ta miƙe ta je ta rungume Hafcy, (idan ba kai da gaske ba, da wuya ka hango Hafcy jikin matar nan, domin gaba ɗaya ta rufe ta, sabo da tsayi da ƙiba, sai ta zama tamkar ƴar tsako a gabanta.)


 nan suka zube kan kujera, suna ta zabga kukar abun da ya faru da su.




Sai da sukai mai isar su, sannan su ka kai shiru.



Hafcy ta koma kujerar da ke gefensu ta zauna, sannan ta ce


"Na yi zaton zan samu kin tafi ai? Ashe kema Allah ya kare ki."


Matar da a haife ta kusa haihuwar Hafcy ta ce


"Ke dai bari kawai! Kwananmu na gaba, har na gama shirin tafiya aka min waya daga can dangi mahaifiyata ba lafiya, dole na haƙura da tafiyar na je na ɗauko ta, yanzu haka ma tana asibiti da ƙanwata, an bata gado."


"Kuma na ƙira wayar ki a daren bai shiga ba."


"Me yuwa matsalar zaren sadarwa ne, kin san ba ko ina ke da sabis ba."


"Shi yasa! To ya haƙurinmu da abun da ya faru?"


"Haƙuri ai ya zama dole! Hakan ya zama tamkar izina ne a garemu da sauran ƴan'uwa masu irin ɗabi'ar mu, mun gode Allah da ya barmu a raye, ya kamata mu koma ga gashi, mu nemi tuba da yafiya a gareshi, su kuma Allah yafesu."


"Amin ya Allah."


Ohho! Duniya!! Wuya mai sa a tuna Allah, su Hafcy an koma ga Rabbi.



"Kema ya kamata ki koma gida, ki nemi gafarar iyayenki."


"Zan koma Aunty Zuzu, amma fa sai na yi maganin wannan matsalar da na gaya miki."




"To! Yau kuma har da Anti?"


"Da ɗin ma ai rufewar idone yasa aka mance da girman."


Tana maganar tana sun kuyar da kai alamar kunya.


"Ummmm! Naga alama, ai kam mun tabka ta'asa sai dai Allah ya yafemu kawai, anjima idan zanje ganin mahaifiyata sai mu tafi ki ga likita a can."


"To, na gode. Amma fa ban da ku..."


"Ba damuwa, sau nawa muke taimako junanmu? Don wannan ba matsala, Allah dai ya sa a dace ya baki lafiya, nima ina ta fama da tawa matsalar."


"Ke ma?"


"Eh, kinsan wancan matsalar cutar ƙaiƙayinnan ya shafi har mahaifa ta, yanzu haka aiki za ayi a ciremin."


"Wayyo Allah! Sannu!! Mu kwaso ma kanmu da kanmu cutuka."


"Hafcy ai mugode ma Allah da a cutar kawai Allah ya barmu, ya kuma bamu ikon tuba mu koma gareshi."


"Haka ne! Allah bamu lafiya ya yafemu."



Nan sukai ta tattaunawa, har na tsawon lokaci.



Abinci suka ɗaura sannan sukai shirin tafiya asibiti, wani abun mamaki, wai yau sune har da salla, wanda idan aka ritsasu da wuya su tuna ranar ƙarshe da suka ka kalli gabas, wani lokacin ma suna aikata masha'arsu ana ƙiran salla, amma tamkar ƙaimi ake ƙara musu.



Asibiti suka nufa, bayan su duba mai jikin, kai tsaye suka nufi gun likitan da ke duba Zuzu.



Bayani sosai ta mishi game da yadda ta ke ji, gwaje-gwaje ya bata, idan ta yi ta kawo mishi zuwa gobe.



Washe gari ba ɓata lokaci ta kai ma likita sakamako, sau da ya yi shiru na tsawon lokaci yana nazari, kafin ya fara mata bayani.



"Sakamakon yawan amfani da kike da bakinki wajen biyama ƴar'uwarki buƙata hakan yasa ƙwayoyin cutar daji ya harbi wajen, hakan ya yi sanadiyar haifarmiki da yawan ƙaiƙayin gaba, wanda yawan amfani da hannu ko harshe, wanda ba kusan irin ƙwayoyin cutar da suke yaɗuwa ba ya janyo miki, hakan shi ya yi sanadiyar harbuwarsa har mahaifarki, wanda idan ba'a yi gaggawar aiki an cire miki ba, zai iya zama miki babbar matsala."


A razane gami da kuka, Hafcy ta ce

"Wayyo Allah na shiga uku! Na cuci kaina na cuci rayuwata!! Likita don Allah ka taimaka min."


"Hafcy haƙuri za mu yi, duk abun da ya faru da mu, mu muka ja ma kanmu."


"Aunty kin ji fa! Nima irin naki za'a mun."


"Na ji Hafcy, ya zamu yi? Hakan shine samun lafiyar mu."


Bata ƙara cewa komai ba, sai sharar ƙwallar da ta ke yi.



"Wannan fa ba wata matsala ba ce, matuƙar za ki da ge da shan magani komai zai zo da sauƙi insha Allahu, kullum ana faɗakar da ku game da irin wanna illolon sam bakwaji. Yanzu wa gari ya waya?"



Sosai ya ja musu kunne gami da tuna ga mummunan ɗabi'ar da suka ɗaura wa kansu.



Bayar samun lafiyar mahaifiyar Zuzu aka musu aiki, su duka, har sun koma gida suna ta shan magani sai fatar samun lafiya.






*A yi haƙuri uzurori suka sha kaina*



*UMMYN YUSRAH*

[12/24, 8:23 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭 A DALILIN LINK😭*




      *RUBUTAWA*

           *UMMYN YUSRAH*




*TACEWA*

    *QUEEN MEEMI*





*15*



Wata biyu kenan suna ta fama da shan magani, Alhamdulillah! Jiki da sauƙi, sai dai kuma, wata matsalar da ta ƙara kunno kai ma Hafcy.



Wai ana wata ga wata.


Allurar da tayi ne ya fara jawo mata matsala.



Ƙirjinta da mazaunan ta duk sun kumbura, sai jan ruwa suke kamar balo-balo, ga azabar raɗaɗi da ciwo.



Tayi kuka sosai har ta gode Allah, ta ƙara yin danasani da nadamar wannan irin rayuwar da ta jefa kanta.



Ko alhakin mijinta, iyayenta da yaranta ma ya isa ya kamata.



Tir da rayuwar bariki! Allah wadan masu rayuwa irin ta dabbobi, idan masu shiryuwa ne Allah ka shirye su, idan kuma ba masu shiryuwa ba ne, kai ka fimu sanin yadda za ka yi da su.



Dole ba shiri Hafcy ta fara shirye-shiryen komawa gida, don yanzu kam ta fara tsorata da rayuwar ta, gara ta koma gaban iyayenta idan yaso ta mutu a can.



Sun yi sallama da Zuzu bayan ta rakota tasha ta bata kuɗin moto da wasu ƴan kuɗaɗen, domin itama yanzu ta ƙare mata.



Motar su ta lula sai garin Bauchi Yakubu.



Tunda suka iso garin ta ke ga duk ya canza, (Wanda ya bar gida gida ya barshi, bariki dai ba gidan tsohon mutum ba ne, duk daren daɗewa dai sai ka waiwayo gida.)



Yau dai ga Hafcy ta dawo jaharta da ta gudu sanadiyyar son zuciyarta.



 Tunda ta baro tashi ta ke tunanin ta ina zata fara? Anya zata iya tunkarar iyayenta da wannan cutar kuwa? Bata dai isa ta koma gidan Haseeb ba, balle gidan wasu dangi nata.



Gidan Ummy ne ya faɗo a ranta, to kuma idan ita ma ta ƙone a gobarar fa? Ta tambayi kanta. Bari dai ta je ko zata dace.



A daidaita ta tsare, ta gayamai inda zata, suka lula.



A rufe ta sami gidan, da alama ma ba kowa a gidan.



Waige-waige ta shiga yi, tamkar mai neman wani abu,  tamkar anyi shara a unguwar, hakan ya sa ta shiga gidan da ke kusa da na su Ummyn.


"Assalamu alaikum!"


"Wa'alaikumussalam! Maraba da zuwa."


"Yauwa."


Bayan gaisuwa


"Don Allah tambaya na ke."


Da fara'arta ta amsa


"Allah yasa na sani."


"Wajen Ummy na zo, sai kuma na tarar da gidan a rufe."


Take yanayin kallon ta ya sauya, fara'arta ya ɗauke, cikin yatsina fuska 


"Hala ke ɗin ƙawarta ce ko?"


"E, daga Kaduna na ke, shine na zo mu gaisa kwana da yawa bamu haɗu ba."


 "Ummmm! Ta jima a gidansu ai, sakamakon kamata da mijinta yayi suna tabka baɗalarsu da wata ƙawarta, take ya danƙara mata saki uku, ya kaɗata gida. Sai ki garzaya can ki sameta."


Jikin Hafcy ya mugun sanyi, ganin yadda matar ta sauya lokaci guda, ga wani kallo da ta ke mata tamkar taga kashi (ƙyanƙyami).


"Don Allah ko kinsan gidan nasu ki kwatantamin?"


Da sauri ta kwatanta mata, tayi kitchen, tsintsiya da ruwa ta ɗauko ta hau wanke gun da Hafcy ta tsaya.


"Bamu buƙatar najasa a waje mai tsarki, kullum cikin tsarki da tsarkakewa muke fatar kasancewa."


Hafcy da ke shirin jefa ƙafarta waje, ta juyo ta kalli matar, sannan ta fice, zuciyarta cike da tunani kala-kala.



Da sallama ta shiga gidan, bayan gaisuwa ga ƴar dattijuyar ta tambayeta ko Ummy nanan? Ɗaki ta nuna mata.



Zaune ta darad da ita, hannunta riƙe da wani littafi na addu'o'i.



Waro ido Ummy ta yi cikin mamaki ta furta


"Hafcy!! Dama kina raye?"


"Ina raye, ban mutu ba."


Waje ta nuna mata ta zauna, mamakin sauyawar Ummy ta yi sosai.


Nan suka ba juna labarin bayan rabuwar su, har da yanke mahaifar da aka ma Hafcy da kuma abun da ke damunta.


"Hafcy ai mun gode ma Allah ma da ya barmu raye, yanzu kam ai mun yi hankali, neman yafiya kawai zamu duƙufa yi Allah yafe mana, amma cuta kam mun cuci rayuwarmu. Kalli nan."



Rintse ido Hafcy ta yi, don ta tsorata.


"Sanadiyar wancan baƙar rayuwar tamu ta janyo min jama'ar da sai da aka yanke min N... Na guda."



Duk kuka suke yi mai cike da nadamar rayuwa.


"Hafcy ya kamata ki koma gida haka nan, ki je ki nemi gafarar iyayenki, shekara guda harda watanni, kina raye ba mutuwa ki kayi ba, ki je ki nemi gafarar su da na mijinki, da kuma Ubangiji, kin ganni yanzu banda aiki sai neman yafiyar Ubangiji, ga kuma islamiyyar da nake zuwa."


"Zanje Aunty Ummy, tunani na yadda zan fuskancesu."


"Ki je da zuciya guda, Insha Allah zasu karɓe ki."


Godiya ta mata gami da sallama.



Ta kusa kai awa tsaye a zauren gidan, ta rasa ta yadda zata tunƙari iyayen nata.



*UMMYN YUSRAH*

[12/26, 9:34 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*




     *RUBUTAWA*

         *UMMYN YUSRAH*



*TACEWA*

    *QUEEN MEEMI*




*16* 



Yana tsayawa da moton suka fito da gudu, hannayensu ɗauke da ledodi, yayin da suke mishi a dabo da hannun da ba komai.



Gudu suke burinsu kowa ya riga ɗan'uwansa shiga gidan.



Suna shiga, suka fito da gudu, gami da ihu, ledar da ke hannunsu duk sun zubar a wajen.



Cikin haki da alamar tsoro macen ta ce


"Yaya! Da aljani fa muka yi karo a zaurennan."



"Ke Sabira! Ai ni kam ba zan shiga gidannan ba yau. Gashi Abba ya tafi, ya zamu yi kenan?"



"Mu yi ta ƙwala ma Inna ko Baffa ƙira ko zasu ji."


Nan suka taƙarƙare suka shiga ƙwala ƙira.


Ba kowa gidan sai Inna da ke ta faman aikin gida, ta yanko ta h zaure don ɗaukar iccen da zata haɗa wuta, ta ji ƙira.


"Yau kuma Sabir da Sabira sheƙiyanci ne ya tashi kuke ta ƙwalan ƙi..."


Ganin mutum tsaye cikin zauren, ya sanya katsewar maganar ta.


"Waye nan kuma? Ba ku shiga sai ku tsaya daga zaure?"


"Niiiii! Ceeee."


"Baƙuwa ce? Ai sai ki shiga daga ciki."


Sum-sum-sum ta shige, ita kuma ta nifu gurin yaran.


"Ƴan nema! Yau kuma da salon da ku ka zo kenan? Ina Abban naku?"


"Ya tafi Inna! Ki zo ki wuce da mu, aljani ne a wannan baƙin zauren."


Cewar Sabir


Dariya sosai ta yi


"Matsorata kawai! Kai a hakanne za ka yi aikin sojan?"


"Allah Inna, sai da muka yi gware da ita ma, ki duba zaki ganta."


"Kuma idan aljanin ne sai ya tsaya muku ko? Zo ku wuce ni?"


Ƙanƙame hannayenta suka yi, gami da rintse ido, sannan suka wuce.



Tsakar gida suka tadda ita tsaye, ta basu baya, Inna ta ce,


"Kun ga abun da kukai karon. Baiwar Allah sannu ko! Hala ke baƙuwa ce."


Durƙusawa ƙasa ta yi, gami da juyowa, fuskarta sharkaf da hawaye.


"Inna Ina yin..."


Dogon tsakin da Innar ta ja, gami da jan yaran su wuce ne ya yanke mata gaisuwar.



"Ku ƙarasa ciki, barin ɗauko icce in zo."


"Inna akwai kayan da muka zo da su a zaure sun zube."


"Matsorata! Ban ɗaukowa da kanku zaku ɗauko."


"Mun daina wuce zaurennan sai kin sa wuta."


Ciki suka nufa, ita kuma ta nufi zauren ta kwaso ledodin, ta ɗau iccen ta ta yi gaba.



Hafcy kam! Iya tsayuwa ta tsayu, ta nason shiga cikin gidan don ba Innar haƙuri, amma tana tunani. Domin yadda taga fuskarta ba annuri zata iya jibgarta.



Ganin ba mafita ya sanya ta yanke shawarar shiga, koma me za'a mata a matan indai za'a huce a kuma yafe.



Suna ƙofar ɗaki kan baranda, suna hira ta shigo, har ƙasa ta durƙusa tace


"Inna don Allah ki yafeni! Na tuba ki mun rai!! Wallahi sharrin shaidan ne."


Ƙala bata ce ba, sai ma ci gaba da jan yaran da tayi da hira.


Sabir ne ya ƙure ta da ido can ya ce


"Lahhh! Mama!!"


Sabira ta kallo ta tace


"Yaushe kika dawo Mama?"



Kanta na ƙasa, bata ce uffan ba, sai ma mamaki da take na yadda sam yaran nata basu wani nuna ɗoki da murnar ganinta ba.



"Don Allah Inna ki yafeni! Wallahi na tuba ba zan ƙara ba, don darajar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama! Wallahi sharrin zuciya ne. Inn..."


Hannu ta ɗaga mata


"Dakata! Ki tashi ki fita ki barmin gida wallahi tun kafin in saɓa miki."


"Ki yi haƙuri Inna! Ban da inda zani da ya wuce na..."


Tsintsiyar kwakwar da ke gefenta, ta rarumo ta kai mata jifa, ta goce.


"Ni kike gayama ba ki da inda ya wuce nan? Da ina ki ka je? Can ɗin zaki koma ai yafi nan sau dubu." 


"Inn...!"


"Tashi kai ka miƙon taɓaryar can."


Miƙewa ya yi ya je ya ɗauko, ya miƙa mata.


"Kinga wannan? Ko ki tashi ki fita ko in rotsa miki wallahi."


"Yau kam Rayya ke da wa kike ta bolo-ƙoƙo? Har waje fa na ke jiyo ki."


"Malam bolo-ƙoƙo ai ya zama dole. Ƙaraso ka ganemin wannan mara kunyar ce ta dawo, har ta ke min rashin ta ido."



"To! Wacece kum..."


Juyowa ta yi, ganin ta ya sanya maganar tasa ta maƙale.


"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Hafsatu yau ke ce Allah ya yi dawowar ki? Allah maji riƙon bayinsa."


Gefen tabarmar da suke zaune, shima ya zauna.


"Kai! wa ya kawomin amaryata da mummunan angonnan naki?"


"Mahaifinsu ne, bai ma shigo ba."


Gaishesa suka yi, sannan Hafcy ma ta ce


"Baffa ina wuni?"


Da fara'a ya amsa mata, gami da bata izinin zama da kyau.


Inna ko sai zabga nata harara ta ke.


Kawu ne ya ce masu Sabira su tafi gidan goggonsu (ƙanwar Hafcy) da ke aure kusa da su, don su sami damar magana.



Ƙin tafiya suka yi, dalilin tsoron zauren da suke. Sai da aka rakasu sannan su ka sa kai.



Gurin ya yi tsit ba kajin komai sai nasihar da Baffan ke yi.




*UMMYN YUSRAH*

[12/30, 9:16 PM] INNAR TSALHA👵🏿: *😭A DALILIN LINK😭*




      *RUBUTAWA*

           *UMMYN YUSRAH*



*TACEWA*

   *QUEEN MEEMI*




*17*🔚


Kuka sosai take, mai cike da nadama, sosai nasihar Baffan ya ratsa duk wani sassa na Jikinta, ba abun da ta keji yanzu kamar kunyar iyayen nata, ji take tamkar ƙasar gun ta tsage ta rufta.



Ta biye ma son zuciyarta, ta yi watsi da tarbiyar da iyayenta suka bata, ta biye wa son zuciyarta ta yi wasa da damarta na samin nagartaccen miji, wanda abune mawuyaci ya yarda ta koma gidansa, abune mawuyaci ta ƙara samun mijin aure.


Tayi ma kanta babban tabon da ba zai taɓa gogewa ba, har ƴaƴa da jikoki.



Son zuciya ɓacin ta! Ta biye mata ta kuma ga illata, wanda ko maƙiyinta bata mishi fatar shiga waccan mummunar abun.



"Kaza tana take ɗanta ba don bata sonshi ba ne, tana hakan ne domin gargaɗi, ko da mahaifiyarki ta miki hakan tayi ne domin gargaɗi, don haka sai ki kula, kuma ki kiyaye, Allah yasa mufi ƙarfin zukatanmu."



Maganar da ya katse mata tunaninta kenan. Duk suka amsa da amin, sannan ya juya ga mahaifiyar Hafcy


"Rayya na ari bakinta na ci mata albasa! A yi haƙuri a yafe mata, Allah ma nason masu haƙuri da yafiya."


"Ba komai Allah yafemu duka. ya kuma ƙara shiryar da mu."


Amsawa sukai da Amin, sannan ya miƙe ya ɗau abun da ya dawo da shi, ya fice.


Matsawa ta yi kusa da Innar ta ƙara bata haƙuri, nan ta buƙaci ta bata labarin inda ta tafi, nan ta fayyace mata komai, har da cire mahaifa da kuma ciwon da ke damunta a yanzu.



Inna ta tausaya mata matuƙa, 


"Wannan shine ƙaddara ta riga fata, Allah kare gaba. Yanzu ai sai ai shirin neman magani, don ba za'a zauna da ciwo ba."



Nan sukaci gaba da tattaunawa, sai dai sam Hafcy ta gaza sakin jiki, kunya ne fal tattare da ita.



Sai dare Haseeb yazo ɗaukar su Sabir, har cikin gidan ya shigo, ya gaida su Innar, nan ya ke sanar mata da zancen aurensa.



Hafcy da ke cikin ɗaki wanda tun shigowar Haseeb ta ƙara ƙulewa ƙurya gami da jin faɗuwar gaba, take hawaye ya wanke mata fuska.



Yanzu ta ƙara tabbatar ma da kanta, ta cuci kanta iya cuta. Gashi Haseeb zai yi aure, ita ko tasan har abada ba mai auren ta a matsayin ta na ƴar maɗigo mai ritaya.


"Abbah Mamanmu ta dawo."


Cewar Sabira.


Cike da mamaki ya ke kallonta, sannan ya maida kallon ga Inna.


"Da gaske Hafsat ta dawo Inna?"


"Lahhh! Ta dawo taɗi da shirmen wannan yaran ya mantar da ni."


Hannu ya ɗaga ya gode ma Rabbi


"Ohhh! Kinga addu'armu ya karɓu Inna, Allah ya amsa ya kuma dawo da ita."


"Hmmm! Dama ai komai da lokacin sa."


"Haka ne kam!"


Ƙwala mata ƙira tayi


"Da kin barta ai Inna, hala bacci tayi."


"Anya kuwa? Kai Sabiru zo ƙira Mamar ku."


Haseeb tunanin yadda zasu haɗa ido da juna yake, ita ma haka, tana jin an turo ƙiranta ta miƙe gurin kamar mai bacci.



Zuwa yayi ya sanar tana bacci.



Nan sukaci gaba da hirarsu, don dama sun riga sun saba, Haseeb ya maida ta tamkar mahaifiyarsa, itama ta maidashi ɗa a gareta.


Nan take sanar masa da labarin Hafcy, ya tausaya mata matuƙa, ya kuma yi alkawarin taimaka mata game da jinyarta. Nan sukai sallama, ya kwashi yaran sukai gaba.



Tun suna wasan ɓuya har ta haƙura ta bayyana kanta, ta kuma nemi yafiyarsa.


Sosai ya himmatu wajen taimaka mata kan rashin lafiyarta, ana kuma ganin nasara, har gidan iyayen Haseeb taje ta nemi yafiyarsu.



Ansha shagalin bikin Haseeb da Yesmeen, auren da yake ji tamkar yafi ko wani namiji sa'a.



Bilky ma ta haifo ƴan biyunta duk maza, bayan rasa biyu da tayi sanadin yawace-yawace.


Ya sanar mata tun tafiyarta ya datse igiyar aurensu, yana mata fatar samun nagari.


*Alhamdulillah*


_Godiya ga ɗumbin masoya wannan labari, mussan Yayana El-MU (ABUL INTISAR)_


_Na gode sosai da yawan addu'o'i ku, duk da nasan albarkacin novel na samesu ba don son so ba._🤪



_A DALILI LINK tsohon labari ne da ya shekara biyu, a baya yayi masoya, haka ma a yanzu har ya ɗara na bayan, hakan ya gwadamin cewar rubutu mai kyau da ma'ana ko shekara ɗari zai yi, maishi ba zai ji shiyi ko haufin dawo da shi sabo ba._



_Allah bamu ikon gyara alƙalumanmu, ya bamu ikon rubuta daidai._




*UMMYN YUSRAH*



Post a Comment

0 Comments