ZUBAIDAH. HAUSA NOVELS

 ZUBAIDAH🙍🏻😭

                04

*©Sameena Aleeyou..✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum... 📖📚_
  *Dedicated to all Victims of rape, never keep silence. Fight for your right, this is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselves🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾*

   "JALAL, abokin su Saleem ne wanda tun tasowarsu tare suka taso, Jalal maraya ne wanda bashida kowa sai mahaifiyarsa Annah, Annah tayi komai a rayuwarta don ganin ta inganta rayuwar Jalal tun yana yaro, kama daga karatunsa har zuwa girmansa,  haka nan ya tashi ba tareda yasan mahaifinsa ba, don Annah ta sanar dashi cewa mahaifinsa ya rasu tun yana k'arami. Annah ta jima tana yiwa matar Alhj  Kasim aiki wato mahaifiyar Salim,  tun wani lokaci da suka zauna a Gombe,  tun yaran gaba d'aya suna k'anana,  Annah ita ta rainesu gaba d'aya,  Salim Labeeb da kuma Jalal  d'inta,  wann dalili yasa lokacin da zasu komo Abuja suka taho tareda ita don tun a lokacin bata da miji ya rasu. Ta zauna da d'anta a nan BQ din gidan Alhj Kasim. 
  "Tunda yaran suka taso iyayen ke k'ok'arin rabasu da Jalal, suna nuna masu cewa shi ba daidai dasu bane,  babu yanda basuyi ba don ganin sun rabasu amma abu yaci tura dole suka hak 'ura suka k'yalesu,  amma ko kid'an babu wani abu na arziki da suke masa. 
   "Shi kuwa Jalal babban abun da ke masa dad'i shine yanda emmata da samaruka yaran masu kud'u suke zaton shima DASUKI'S ne,  ma'ana shima dan familyn Dasuki ne,  ko ina tare dasu Salim suke zuwa party shisha spot da dai sauransu.  Allah ya masa kyaun hallita gabba d'aya yafisu kyau 'yanmata  suna rubibinsa shiko na ja masu class kaman wani d'an hamshak"i ko kad'an bakace  Jalal ya had'a jini da talaka ba...wann kenan. 

 *Gombe,  Dukku*

   "Huci take kaman wata kububuwa tana watsawa  malam Habu mahaifin Umar da abokinsa malam Tanko harara,  Malam Habu suka saki baki suna kallon ikon Allah sanda  Yaya Habibu ya mik'e ya rusuna gaban Hadiza yana tambayanga shin ta amince a karb 'I baikon Zubaidah, .... Mikewa Hadiza tayi kafin ta d'ibi 'yan goron da malam Habu suka shigo dashi ta shiga juye masu a tsakar kansu, tana balbala wutan bala 'i da masifa,  ta yanda take shiga bata nan take fita ba. 
"Malam Tanko ya mik'e yana fad'in subuhanallah,  Malam Habu ya baka fad 'a mun haka lamarin yake ba, Malam Habu da kunyar abokinsa mutum mai muhimmaci a gari irin Malam Tanko ya baibayesa,  dama yasan haka ka iya faruwa, shiyasa tun farko bai so Ummaru ya nemi Zubaidah ba dukda ya aminta daehankali yarinyar kuma na tausayinta,  amma ko kad'an bashi fatan abinda zai hadasa da dilalliya Hadiza,.....  
   "Zubaidah dake mak 'ale bayan k'yaure bata san sanda ta sulale  gwiwoyinta a k'asa ba tana hawaye sanda ta jiyo irin fatattakan da Yaya Hadiza tayima iyayen Umar, shikenan itakam tasan bazata tab'a aure ba,  bazata tab'a jin dad'in rayuwarta ba,  mafarkin ta bazai tab'a tabbata ba,  takaicin yayanta da tausayin kansu shida ita ya lullub'e zuciyarta. A hankali ta k'arasa kan tabarman da ya kasance makwancinta ta kwanta tana kuka mai tsuma zuciya. 

   "Malam Habu jiki a sanyaye ya shiga bawa Malam Tanko hak'uri,  Malam Tanko yace a'a abokina baza 'a bar wann magana ba tunda yaran suna son junansu ni nasan yanda za'ayi, ka shige gida zan nemeka zuwa gobe,  Malam Habu ya masa godiya sukayi sallama kafin malam Tanko ya hau babur dinsa ya wuce. 

*******************
*Abuja*

    "Suna isa wajen partyn pili ya dauki shewa da ihu,  manyan yara wanda duk gabaki d'aya Abuja sunansu yayi k'auri Sun samu halarta,  Tariq ya k'araso yana welcoming nasu sai wani tafe hannaye suke yanda niggas  keyi.  Tariq shine cikon na hud 'u a clik d'insu,  shima mahaifinsa nada shears a companyn *Dasuki Holdings* kampanin mahaifan Salim da Labib, ..

*Zubaidah, Jalal, Umar,  Salim, Labib da kuma  Tariq*




*Ku biyo Sameena don jin labarin gumurzumon da wad'annan matasa suka fuskanta.......... 👌🏾*
[1/23, 22:08] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

                              05

*©Sameena Aleeyou.....✍🏾*

_Queen Same Novels Forum...📖📚_

     "Alhj Kasim Dasuki, Alhj Jamil Dasuki da kuma Alhj Yusuf Maina mahaifin Tariq sai Barrister Munir Malami lawyer na company ɗinsu *Dasuki Holdings* kuma yaya ga mahaifiyar Salim Haj Farha Dasuki.
  "Zaune suke gaba ɗaya a babban parlorn taraban baƙin Alhj Tahir, magana suke na tsaida ranar auren Salim da Kausar, an tsayar sati mai zuwa za a yi bikin saka rana. Daga nan suka ɓuge da hiran kasuwanci da siyayasa. Tunda dama Alhj Tahir na neman tsayawa takaran shugaban ƙasa, nan Barr Munir ya bada shawarin a tafi chan Dukku ayi bikin saka rana hakan ba ƙaramin nasara zai kawo wa neman takaransa ba, gaba ɗaya sukayi na'am da batun Barr Munir snn ƴan garinsu zasu tabbatar shi ɗin mai ƙaunar mahaifarsa ne..... Har farfajiyar  gidan Alhj Tahir ya rakosu yanda bodyguards ɗinsu suke... Daga nan ya wuce ɓangaren matarsa uwar ƴarsa Hajiya Raliya don sanar da ita yanda suka tsai da batun auren yaran.
   "Kausar da Asmah ya samu a parlorn ƙasa suna playin PSP, gaba ɗaya suka soma gaidashi... Papa sannu da shigowa amsawa yayi da sakin fuska kafin yace ina momman taku, har suna haɗe baki wajen cewa she's upstirs, ƙarasawa yayi ya nufi stirs ɗin.
  "Kausar da Asmah suka ci gaba da game ɗinsu. Asmah cousin ɗin Kausar ce wacce a shekare baifi ta girme wa Kausar da shekera guda ba, tun dawowarsu  Nigeria Asmah take gidansu daga zuwa kwana biyu Kausar taƙi barinta ta koma dole Aunty Miemie mahaifiyar Asmah ta haƙura da zancen don tasan halin Kausar da kafiya.
  "Momma na zaune gaban dressing mirror tana gyaran fuska as usual don itakam taƙi yarda ta tsufa at her late 40s bats sahun matan nan masu barin gyaran jiki da zaran sunga shekaru ya soma ja masu,... Murmushi Papa yayi gamida rungumota ta baya,  murmushi itama ta sakar masa kafin tace" Papa how do i look like, ɗan jan hancinta yayi kafin yace as always my one you look so gorgeous manna mata peck yayi a goshi kafin suka zauna bakin gado ya soma faɗa mata yanda suka tsai da maganan bikin Kausar, nan da nan idon momma yayi raurau Kausar is her only daughter ƙaunar ranar rabuwarsu tazo dukda tasan dole wata rana hakan ta kasance.... Papa yasan kwanan zancen don haka rungumota cikin jikinsa yayi ya soma lallashinta da kalamai masu taushi, "Haba first lady you need to be very strong you know, sooner or later zaki zama mother of the country insha Allah, bama Kausar kawai ba, the whole country will be yours, and for now akwai Asmah though nasan itama tana samu miji zamu aurarta but atleast zata ɗauke mana kewar Kausar.... Jin yanda mijin nata keta faman riritata yana shagwaɓata yasata sakin murmishi gamida goge guntun hawayenta tace" Pappy you ƙnow what made me cry...." Ɗan girgiza kai yayi har lokacin tana cikin jikinsa kafin taci gaba da faɗin" I dont know why, but har raina banjin son auren Kausar da Salim duk da ɗan aminiyata ne, quite alright nasan gidan girma arziki da mutunci zata but.... Kasan yaran zamani kar Salim ya hurting mana baby girl ɗinmu...."Papa yayi murmushi gamida shafa goshinta zuwa gashinta kafin yace" Raliya insha Allah we won't regret it, bazamuyi danasanin aurar da Kausar wa Salim ba, besides they both love each other wanda kinga hakan akeso ya kasance. Yanzu abunda nake so dake, you shud start preparing we leaving in a couple of days gwara mu mu fara isa tunda mune iyayen bride, I'll make sure the house is ready from now to tomrrw, ki kira su Kausar ɗin ki sanar dasu su fara shiri, barin ƙarasa parlor inada wasu baƙin.. Gyada kai kawai momma tayi da ƙyar kafin ya manna mata kiss a chick ɗinta ya fice.
 "Wann shine rayuwar gidan Alhj Tahir, mutane ne masu Dattako da sanin ya kamata, ko kaɗan basuda ƙyamar talaka kaman Dasuki family, snn abin hannunsu sam bai rufe masu ido ba, da wann dalili yasa akasarin mutane suke mara masa baya a siyaysarsa, yayinda wasu ke ganin The Dasuki family ks iya ja masa cikas a siyasarsa sabida izzan su da ƙyamar talaka ds suke dashi.

   "Kausar da Asmah sai murna suke zasu Dukku dukda kakanninsu gaba ɗaya sun rasu amma skwai sauran dangi, Momsy ya maganar kayan gaskiya ki sake masu waya we need them this week, they shud make it possible this week. Momsy ta ɗan sakar mata harara kafin tace" Kausar this is not Holland fah, na faɗa maki ki rage wann rawar kan taki, ba irin auren da kika saba gani bane na turawa, wann auren fulani ne wanda aka san sansu da kunya so be careful,... Momsy tana ficewa Asmah da Kausar suka kalli junah, suna daroya ƙasa ƙasa don suma har sun ɗagota bata son Kausar ta bar gidan ne Asmah ta ɗau waya tace bari kiga na kira *Mamza beauty* (makeup artist)  na sanar mata, ke kuma pls ki kira Sarah fashion ( Fashion stylist ne a Dubai wanda zasu ɗinka kayyaykin Kausar da zatayi amfani dasu a events) ɗin ki sanar dasu.
   "Rungume pillow tayi gamida lumewa cikin hashaƙin gadon tana tuno farin cikinta Salim, ya kusa zama *Mallakinta* Asmah na mata magana ko saurara batayi ba tayi nisa wata duniyar, girgiza kai kawai Asmah tayi ganida jifar ta da pillow kafin ta fice.

 
  "Tafe suke suna tangaɗi da gani kasan sun bugu da giya,   da ƙyar suka iya fitowa daga motan ,Alhj Kasim da har loƙacin idanunsa biyu baiyi barci ba ya dubi agogon bango dake maƙale a ɗakin ya nuna ƙarfe uku na talatainin dare, yasan ba kowa bane zai shigo gidan a yanzu sai Salim, kai tsaye down stirs ya sauƙo ya buɗe ƙofar parlor, chan ya hangesu suna tafe suna tangaɗi gaba ɗayansu, Jalal na riƙe dasu don dama duk randa suka je party suka shawu toh shi ke driving nasu da shike shi bai sha yanda za'a gane sama sama yake kora wine maras bugarwa sosai shide barshi da harƙan bin mata, shiɗinma da yawa ƴan matan ke kawo  kansu wasu na zaton shi ɗin ɗan Dasuki Family ne yayinda wasu ke sonsa sabida kyaun da Allah ya masa.
   "Wani mugun kallo kawai Alhj Kasim ke binsu dashi musamman Jalal, shikan ya tsana ganin yaransu da sidecake ɗin,..... " 
   "ƴan kame kame Jalal ya soma, tuni Alhk Kasim y dakatar dashi  da faɗin" meyas baka kai shi gidansu ba ya ƙarashe maganar yana nuni da Labib, Jalal da tuni ya shaƙi kallon ƙasƙancin da Alhj Kasim ke masa, a daƙile yace " Gani nayi nan ma gidansu ne......"Jar ubancan haka Alhj Kasim yace a zuciyarsa lallai wnn talakan raini na neman shiga tsakaninsu, baiga laifinsa ba lafin su Salim ne,... Securities ne suka ƙaraso suka shiga taimaka wa Jalal, ɗaya security ɗin daga gidansu Labib yake yazo tafiya dashi don hankali mom ɗinsa ba ƙaramin tashi yake ba duk randa yayi dare a waje, duk da hakan ba sabo bane amma she couldnt get used to it har yanzu. Haka aka wuce da Salim da Labib kaman wasu mutattu don tuni bacci yayi awon gabadasu.
   "Jalal ya ɗaga gira sama kafin ya dubi Alhj Kasim yace" Have a good evening Sir , daga nan yayi wucewarsa can sashensu. Kallo Alhj Kasim yabisa dashi kafin yayi ƙwafa ya shige cikin gida.



     "Washe gari zaune suke gaba ɗaya a babban parlorn Alhj Kasim, Ya kuma duban Hajiya Farha dake zaune gefen Hajiya Nurah mahaifiyar Labib yace" Farha  jeki taho min da yaran nan Labib da Salim suna sashen Salim, babu musu Hajiya Farha tabi umarnin mijinta ta fice kiransu.
   "Sai ihu suke suna buga game na ƙwallo ko saurarenta basuyi ba, da takaici ya isheta batasan sanda ta fincike socket ɗinba....."Whatttt!!!!! Suka fadi a tare, Salim yayi jifa path ɗin hannunsa gamida faɗin " Shitttt, why mum haba haba mum.... Rufe mun baki marassa hankali kawai Mum ta ƙasesu, Labib ya ɗan langɓe kai kana yace" We are sorry favorite Aunty, Kunnens ta janyo kafin tace" Daga yau zaka tashi daga fav son idan baku zama good boys ba, Dad na kiranku bata jira cewarsu ba tayi ficewsrta. Labib yace nasan Uncle ne dama zai sa Fav Aunt ta mana haka he will never change. Salim ya watsa masa mugun kallo kafin ya fice ba tareda yace komai ba.


   " Cikin tafiyarsu na samarin da tarbiya bai ishesu ba suka ƙaraso parlorn, gamida tsayuwa ma iyayayen tsegehe akai.
   "Alhj Jamil, ya sauƙe ajiyan zuciya kafin yace" Seat down boys, zama suƙayi da ƙyar saman carpet Alhj Kasim kuwa banda hararsu babu abinda yake. Kaman jira yake nan ya soma surfa masu masifa " When are you boys going to start acting like real Dasuki's huh?Har yaushene zaku daina alaƙa da wann matsiyacin yaron, he's not one of you ba daidai ku bane get this to your heads..... " Alhj Jamil da mamaki yake kallon ɗan uwan nasa ko kaɗan baisan kan hulɗa da Jalal zai masu faɗa ba, a'a ya ɗauka kan ɗabi'u marassa kayu da suke zai masu faɗa, to his gretest surprised sai jin akasin haka yayi, lallai yayansa yayi nisa.
   "Labib ne ya ɗago kai yanai ma uncle ɗin nasa mugun kallo ƙafin yace" Pls uncle will give us break, idan dai akan Jalal zaka mana faɗa you can keep on doing it but bazamu taɓa rabuwa dashi ba he's our childhood friend a brother from another mother....."Enough Labiiiib! Daddƴnsa ya daka masa tsawa, kafin yaci gaba da faɗin " Ma ucle ɗin naka kake faɗun magana haka, be careful kana jina, Labib yana wani hure huren hanci yake watsa wa uncle ɗin nasa mugun kallo, Barr Munir ya sako baki da faɗin"  Ni kawai a kori ysron da mahaifiyarsa kowa ya huta. Wata harara Labib ya watsa masa kafin yace" Malam ka mana shiru dalla this is family issue who invited you..." Salim ya caƙumo wuyar Labib yana huci yake faɗin " First kayi rashin kunya  wa Dad ɗin second kanayi wa Uncle ɗina, Brothern mahaifiyata how dare you Labib.... Saida aka shiga tsakanin Labib da Salim don kaɗan ya rage basu kaure da faɗa ba.
    " Alhj Kasim ya goge zufar data keto masa dukda ac dake busawa a parlorn, iyayensu matan su suka lallashesu kafin suk sanar ɗasu maƙasudin haɗuwarsu.
   "Take annuri ya cika fuskat Salim tuni ya mance wani baƙin ciki ya soma farin ciki, Yayinda zuciyar Labib taci gaɓa da tafarfasa, a cikin  ransa yake furta " _no way it can't be happening, Kausar is mine not yours Salim Dasuki_
  "ƙarasawa yayi ya ɗan daki kafaɗan Salim yayi con granulating nasa kafin ya fice cikin sauri.zuciyarsa naci gaba da tafarfasa

*****************************

    "Mai anguwa yaci gaba da faɗin' ni mai anguwa ni na karɓi baikon Zubaidah kina jina ya ƙarashe maganar yana duban Hadiza data sadda kai a gabansa ta cika tayi fam. Ƙiris ya rage bata fashe ba.
   "Hamma Habibu kuwa sai wsge baki yake kaman gonar audiga yanai wa mai anguwa godiya, banda hararsa babu abinda Hadiza keyi tanai masa kallon zaka shigi hannu ne. Mai anguwa yaci gaba da faɗin ya ysai da aure nan da wata mai kamawa kowa yaje yaci gaba da shirye shiryensa, kuma uffan Hadiza tayiwa Zubaidah za'a mata hukunci mai tsanani koma ya miƙa case ɗin gaban sarki, daga nan ya sallami Hadiza da Habibu suka wuce.
   "Malam Tanko da mlam Habu sukayi godiya sukayiwa mai unguwa suka ɗan tattauna kafin ya sallalmesu.


   "Tsakanin Ummaru da Inna an rasa wayafi farin ciki, tuni ya ficr ganin masoyiyarsa, mai shirin kasancewa amaryarsa......




Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:08] ‪+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

                           06


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...📖📚_


    "Zubaidah zaune bakin murhu tana kan hura wutan girki, ko kaɗan yau bata jin zafin duk tulin aikin da zatayi, snn ko kusa masifan Yaya Hadiza bai ɗaga mata hankali ba, jinta take tamkar sallah, muddin zata bar wann kurkukun dole taji farin ciki a zuciyarta, uwa uba zata ci gaba da karatunta saidai zatayi kewan Kamalu da Hammanta.
  "Wani yaro ne yayi sallama snn yace wai ana sallama da Zubaidah...... "Wulli wulli tai da idanu tana kallon yaya Hadiza dake zaune bakin ƙofar ɗaki ta cika tayi fam ƙiris ya rage ta fashe.
  "Meye kike mun kallon ƙurilla mayya jarababbiya, ai shikenan hankalinki ya kwanta za'a maki auren abinda kike so, ƙaramar karuwa kodayake ba laifinki bane kin riga kin san namiji tun a gantalinki na karuwanci......."ƙwalla suks ciko idanunta kanta na sunkuye a ƙasa, wann mummunar kalma na karuwanci da Hadiza ke jifarta dashi sosai yake ɗaga mata hankali.... Bata gama tunanin da take ba sai ji tayi yaya Hadiza ta janyo wuyarta ta jefata bakin ƙyaure tana faɗin "Wuce kije shegiya mayya kafin ki cinyeni, maza kije yaci gaba da mammatse a lungu yanda ya saba...."
  " Ko ɗan kwalliya da ƴammata keyi idan zasu wajen saurayi Hadiza bata bar Zubaidah tayi ba, haka nan yanda ta tashi daga bakin murhu da warin hayaƙin da komai ta turata waje....

   "Daga can bakin bishiyar da yake tsaye ya hangeta tana goge hawayen da ya jiƙa mata fuska.. Cikin sauri Umar ya ƙaraso yanda take, tuni ta soma matsawa da baya don bata so yaji ƙaurin hayaƙin da take, gashi shi yayi tsaf ya sha gayu abinsa irin na samari daidai da ajinsa.
   " Harɗe hannaye yayi a ƙirjinsa yana kallonta, tausayinta da ƙaunarta na daɗa ratsa ɓargo da tsokarsa,.. Saida ya bari ta gama ƴan goge gogen hawayen kafin ya ɗanyi gyaran murya cikin tattausar murya ya soma faɗi" Zuɓaidah, shiru bata amsa ba har lokacin kanta na kallon ƙasa, kafe ta idanu yayi kafin ya kuma kiran sunan nata, sai snn ta ɗago koɗaɗɗun idanunta ta mar duba guda, Umar yanada ƙwarjini ta yanda duk budurwar da tayi ido huɗu dashi sai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba, gashi a yau yafi kullum mata kyau, shi ba fari bane snn ba baƙi can bane, kallo guda zaka masa ka gane asalin bafulatani ne haɗi da kwantattun sumanss da sajensa  da suks ƙara masa kyau da ƙwarjini...."Muryarsa ya katseta sanda yayi mata nuni da wani kututturen dabino yace" Mu karasa ki zauna, babu musu tabi umarninsa......" Har sun soma tafiya suka jiyo muryar Hadiza ashe tana laɓe jikin ƙyaure tana saurarensu nan ta soma faɗin "Ku ƙarasa ina, kai wani irin jarabebbe ne, baka jira akai maka ita ba sai kazo har ƙofar gidansu kana matseta, auho ashema kun saba kinji kunya Zubaidah tuna kika zaɓi zama karuwa, toh ni dai kar ki kawo min abin kunya kafin wata gudan da aka ɗiba maku ya cika taƙarashe maganar tana watsa masu mugun kallo.
   "Umar yabits da kallon mamaki, ƙarasowa gabanta yayi yanda take tsaye kafin yace" Dillaliya kike ko wa? Galala take dubansa cike da mamaki kodashike tasan Ummaru da wann taurin ran nasa zaiyi fin haka, muryarsa ya katse mata tunaninta yanda yaci gaba da faɗin" Yau ta kasance rana ta ƙarshe da zaki saka masoyita kuka, don wllhi kinji na rantse kika kuma kiranta karuwa kotu zan maka ki sai munyi shari'a daga nan har birnin tarayya, kuma da kike cewa ni jarabebbe, naji na yarda idan dai akan Zubaidah ne sai nafi jaraba ma naci, don nasan bazan taɓa ƙosawa da ita ba, ki kalleta da kyau mana, ke ai kina ganinta kinga mace ba irinki ba, nasan hassada ce tsan tsa kike da ita ba wani abu, yayi wata murmushi mai cike da nishaɗi da gargaɗi kafin yace" This should be the last warning idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira, daga haka ya dubi Zubaidah da ƙiris ya rage bata saki fitsari a jikinta ba don tsoro kana yace" Amaryata lets go, dont mind this witch, don yasan Hadiza dai ba turanci take ji ba......"Kallon Yays Hadiza tayi alamun tana jiran umarninta" Haba tuni ta soma bambami tana kunfan baki, yo har ni za'a yi ma turanci, ke Zubaida har kinyi kaurin da zaki biyewa saurayi inji ni nayi ɗawainiyar karatun naki, har shine zaki zaɓi saurayi akaina ya zageni da kalman turanci kina tsaye kina biyesa yayi maki kyau, idan dai namiji ne kije gaki gashi ..... Daga haka tasa kai ta wuce cikin gida fuu zuciyarta naci gaba da tafarfasa.... 

    "Juyowa tayi tana duban Umar, murmushi ya sakar mata kafin suka ƙarasa suka zauna.
  "cikin tattausar muryarta ta gaidashi, ya amsa yana wani kasheta da mayen kallo, ita kiwa duk kunyarsa ya rufeta musamman cewa da yayi, idan dai akanta ne sai yafi jaraba naci, wann kalmomi sun matuƙar mata nauyi, kaman yasan hakan kuwa nan yasa hannu ya karɓi ɗan karan da take wasa dashi aiko nan ta ɗago ido suka kalli juna, tai saurin sadda nata idon, 
   "Zubaidah, ki sani ina sonki ina ƙaunarki sann zanyi komai a sabida ke, nasan kalan rayuwar da kike da wann matar, daga rana mai kaman ta yau ki sani bazan sake barinta taci zarafinki ba.
  "Ɗan murmusawa tayi kafin tace" Na gode, cikin muryarta mai daɗin saurare, kaman waccd aka zabura ta miƙe tsaye, ɗan dubanta yayi kafin yace" Yaya dai ko har mun gama hiran ne, ɗan girgiza kai tai kanta na ƙasa kafin tace" A'a gani nayi kaman ƙaurin dake jikina ya dameka.
  "Tsuke fuska yayi ya kira sunanta da dakakkiyar murya, ɗago ki kalleni Zubaidah, ta ɗago tana dubansa, Umar yaci gaba da fadin" Nida ke mun zama ɗaya, bana jin ƙauri ajikinki, akasin haka nike ji, ma'ana ƙamshi nake ji, kasancewa taredake yafiye mun komai ina sonki a duk yanda kike. Murmushi tayi harda ɗan rufe fuska alamun taji kunya,.. Dariya ya ɗanyi mai bayyanar da hƙwara kafin yaxe" Oya faɗa mun kina sona... Ware idanu tayi alamun  bazata iya ba, Umar yayi murmushi kafin yace" Surbajo na nasan kinayi koh... Kasa cewa komai tayi sai murmushi.... Hira sosai suka sha a wann rana kamsr karsu rabu da juna, basu taɓa hira irin haka ba, kullum saidai su haɗu a bakin rafi taje ɗibo ruws ko kuma ta kai saniyar yaya Hadiza kiwo.

*********************

   " Salim ne tafe waya manne a kunnensa yayinda hannunsa ɗaya ke riƙe da coffee cup, "What com'on Tariq pls ka shirya yanzu yanzu, we will fetched you up sai mu wuce airport ɗin... Yeah right , see you soon. Yayi hanging up kafin ya tura ƙofar ɗakin da hannu guda.
   "Cak ya tsaya yana kallon Labib dake baccinsa hankali kwance. Kan gadon ya ƙarasa ya ɗauki pillow ya shiga dukan Labib dashi yana faɗin" Will you get your lazy ass out of bed,...
   "Labib, yayi miƙa gamida cusa kansa cikin bedcover yana faɗin" Shitt, pls mana Salim, kasan ba'a tashina a bacci i'll fall sick.
  "Salim ya shiga yaye blancket ɗin yana faɗin whatever, You know we cant miss this flight, tun jiya Daddy ya mana bucking flight ɗin Gombe mukayi missing still yauma muyi missing what will u expect, they'll get mad ai.
  "Gajeren tsaki Labib yayi kafin yace" Does it really has to be now, " Labib ya miƙe yana wangale labulayen tapƙa tapkan windunan ɗakin kafin yace" The flight is 10am and yet is almost 30mins pass 9.. Tsaki Labib ya kumayi babu salati yake hamma kafin yace" waima ina private jet ɗin Dasuki Holdings ne ba sai mu tafi dashi ba, Salim yace gaba ɗaya Jets ukun suna da prob, Daddy yace zaiyi firing masu maintenance ɗinsu, kaga idan mukayi missing wann flight ɗin tofa saidai mu tafi Gombe by road, kai ina I cnat afford to miss this flight ma, i'm dying ti see my Kausar,.. "Galala Labib ke kallonsa kafin yace" Waye ma kake tunanin zaiyi tafiya mai nisa haka by road, haba ba dai ni Labib Dasuki ba.
  "Salim yayi dariya kafin yace" Freaking Dude sai ka tashi ka shirya ai na masu Tariq da Jalal magana suna shiryaw Ya ƙarashe maganar yana jifan Labib da towel.
   Ba don yaso ba ya miƙe ya nufi bathroom..



   "Gaba ɗaya Annah bataso tafiyar Jalal Dukku ba, don tun yana ƙarami data taho dashi Abuja basu kuma leƙawa ba, tana tunanin abinda ka iya zuwa yazo, kar wata rana daɗeɗɗiyar sirrinta data ɓoye masa ya bayyana. Haka tai kusan kwana zullimi......




*Gombe, Dukku*

_Toh fah readers gasu Jalal, Labib, Salim, da kuma Tariq a garin Dukku, shin me zai faru. Shin me Annah take ɓoyewa Jalal tsawon rayuwarsa. Ku biyo Sameena don jin yanda zata kasance_


Sameena ce👌🏾

Post a Comment

0 Comments