zahra tawa ce*💞💞💞
Fatima Abdullahi Ibrahim *( Fatima zois*)
Bismillahir rahmanin raheem
Page1⃣
Tsaye yake a filin shi kadai yana handball cikin kwarewa tare jarumta daga ganinsa y saba,Dogo ne s osai mai yalwar fadin kirji Wanda yake dauke da six packs wanda komai tsayin mace ta tsaya a gabansa sai ya rufeta har ma baa ganinta,jikinsa duk a murde yke d alama zaiyi karfi d jarumta.kyakkyawa ne ajin farko mai cike da kwarjini Wanda duk rashin mutuncin mutum bai isa ya kalli fuskarsa ba yaci masa mutunci,yana manyan idonuwa wnda yake kara masa kwarjini tare da dogon hanci har baki,yana da dan faffadan baki mai dauke da siraran labba d fararen hokara ,fari ne sosai Wanda saboda fari har ja yake wani lokacin,a takaice dai komai na *gadanga* mai kyau ne.
Ball din yake cikin zafin nama d sauri kamar bashi kadai yake ball din ba,wani sauti naji n tashi a system din dake kusa dashi,miss jamila ce take masa magana cikin fada ba tare da shikoma ya daina abinda yake ba,gadanga yaushe ne zaka je ka dauko cells din yarinyar nan ne Tun dazu ko alamar tafiya baka yi kasan dai akwai aiki a gabanmu, magana take yi kamar bada aliyu take ba,saida yayi kamar baxai amsa ba still koma bai daina ball din da yake b matsowa yayi kusa d system din ,yana cewa miss jamila cikin tsantsar d kasaita kamar Wanda aka sa yayi magana dole,Hava miss kinsan dai tunda kin fada min zanje miye naki n damuwa y fada still bai daina ball din ba.
Miss jamila ce tace kasan nan da 20minutes zata fito aiki please ina son kayi abun d sauri mana gadanga cos wannan ba halinka bane kodan kaga mace ce?,miss jamila t tambaya tare d sake dubansa ,are no ba hka bne ynxu xan tafy kinsan yadda nike,yayin da yabar ball din yakewa miss jamila magana,cikin sauri ya nufy cikin gidan yana waving miss saiya dawo.OK my guy see you tare da blowing kiss ,shima ya maida mata tayi ending call din.
Cikin abinda baify 10minute ba ya shirya cikin shigarsa Wanda ba Wanda ya taba ganin fuskarsa duk da cewa shi din ana nemansa ruwa a jallo cos he's wanted ya gagari manyan mutane masu kudi da attajirai,kaf naija babu Wanda bai San da wanzuwa *gadanga* bah cos aikin shi shine kawai yaje wajen manyan masu kudi hamshakai d attajiran mutane,manyan yan kasuwa da dai sauran masu fada aji na kasa yaje ya dauko wani da ake bukata,baya sata baya koma kisa,asalima yawancin abinda ake turashi bincike
Wanda yakewa haka Manyan fada aji masu boye wani muhimman Abu kodai cin hanci d sauransu.
Babu Wanda ya taba ganin shi acikin wannan shigar sai mutum uku:daga miss jamila sai alhaji usman abokin babansa sai koma lady saudat Wanda take karbo abinda aka turashi ya nemo xuwa wajen miss jamila.
Domin duk wannan shakuwar dake tsakaninsa da miss jamila bai taba ganinta ba hka itama bata taba ganinsa ba aikinsu through internet suke koma basu taba samun sabani bah.miss kwararriciya a harkar zamani musamman internet Wanda saboda haka suke cemata *hacker* komai nasu thorough system suke yi Wanda da taimakonta gadanga take samun nasara.
Duk Wanda gadanga xai yiwa Abu saidai ya turamasa ta address dinsa na email idan mah da wata manufar kk nemansa miss jamilazata gani koda babu su CCTV data iya dubawa koda ta wayane da sauran hanyoyi da dama.
Cikin sauri y gama shiryawa cikin bakaken kaya Wanda ko farcensa baa gani koma komai kwakwarka baka isa ka ganeshi bah.cikin sauri y fito daga cikin gidan Wanda shi Kansa gidan zaiyi karamin estate amma a haka idan kaga gidan kamar kango saika yi tafiya mai nisan gaske acikin gidan tukunna xaka iske ainahin gidan, shima cikin gidan kamar irin tsohon gidan nan da aka Dade d tashi ga tarkace babu Wanda zaice ana rayuwar acikin gidan, Tukunna ka shiga ainahin inda yake rayuwarsa tamkar baa kasar gidan yake bah saboda tsananin kayatuwa d haduwar gidan Wanda idan n tsaya bayani har sai in gama wannan page din ba tare Dana gama ba,mai karatu na baka gari ka kwatanta yadda gidan yake😉.
A tarihin wannan gida bbu mahalukin daya taba shigarsa sai iya shida alhaji usman wato abokin babansa,Wanda shi ya daurashi akan wannan Sana'a koma y koya masa dabarun fada mai karfi Wanda ko kwarzinin jikinsa ba xaka iya tabawa komai kowa karfin ka,koma ya koya masa dabarun kare kai daga technological appliances. Shiyasa ya gagari mutane masu nemansa ruwa a jallo.
Cikin sauri ya fito yazo saidai wajen da yarinyar take hawa mota cos yau ta makara a wajen aikinta,yana tsayawa ya hangota daga nesa tana tahowa cikin gudu ga wata katuwar jaka a bayanta kamar school bag tana gudu amma kamar dawo da ita baya ake saboda jakar tana son ta tsayar Bus,abun mamaki ya bashi da yaga katuwa da ita a cewarsa tana wani gudu ,saurin connecting din Bluetooth din dake kunnensa yayi Wanda duk masifarka b xka ce Bluetooth bane cos it's new design from miss jamila tare d connecting video din komai da akeciki through his telescope glass.
miss jamila ce zaune tana cin snacks kamar wacca take ci da wani sai cika baki take cos ita bata ma d lokacin komai idan ba salla bah shiyasa idan tana cin abinci few minutes tayi ta gama,miss jamila data cika baki tana yiwa aliyu magana tace yawwa ga yarinyar nan ka duba jakar ko zaka samu matajin gashi ko brush ko nail cutter ko thumbprint nata or something like that ,OK hacker cewar aliyu tare dayin shiru ita koma miss jamila tana ganin komai cos tayi collecting telescope glass nashi d system, Bus yaga yarinyar ta shiga cikin sauri shima yabi bayanta ya shiga.
Hash😓 yaji yarinyar ta fada,yanzu har an wani cike kujerun gashi ina son zama a kujera yanzu dole saidai in tsaya ta fada tana yatsina fuska alamar ba haka taso bah cikin saurin t cire wannan katuwar jakar ta bayanta saboda gajiya,juyuwar da zata yi bata San da mutum a kusa da ita kawai saiji tayi sunyi gware har tana Neman fadowa kasa,cikin sauri aliyu ya tarota tamkar wata baby saboda rashin Nauyi,fincikar da yayi mata da karfi ne yasa tayi masauki akan faffadan kirjinsa,wani irin shock hade feeling Wanda bai taba jin irinsa ba yaji a tare dashi Wanda har yaso ya manta inda yake saida yarinyar tayi karfin halin ta fincike kanta daga jikinsa.
A tsorace ta kalle shi idonta kamar sai fado saboda tsoro wata sansanyar murya hade d zaki yaji tana cewa "am so sorry please" tare da kura masa ido sosai duk da cewar bata ganin komai kallon ta yayi ya kalli fuskarta mai dauke da manyan idano bare yanzu data tsorata ga dogon hanci har baki Wanda yake karami kamar idan tayi magana kmar baa jiba ,fuskarta rounded face ce mai dauke da dimple point Wanda ko motsa fuskarta tayi sai dimple ya fito tana da yalwar gashi a goshinta Wanda suka kwanta luf.luf tare da bakin saje baki dake kwance a gefen fuskarta girarta kam harta kusa hadewa amma siririya ce kmar Anyi sharping nata, idonsa ya sauko xuwa kasa yaganta doguwa ce sosai amma ba chan ba koma ba siririya vace baiga komai a jikinta bah saidai zarazaran yatsun hannunta Dana kasa cos dogowar rigace a jikinta Wanda idan ka kalleta zaka ce bbu komai a jikin,duk wannan kallon yayi mata cikin abinda bai wuce few seconds bah.
Ya salam ya furta a hankali Wanda miss jamila da take cusa snacks a bakinta tana hadewa da kyar ta tsaya tana kallon komai tare da sakin baki da hanci tana kallo ikon Allah ya salam din daya fada ya ankarar da ita tace gadanga mai kake haka yarinyar nan pah kallonka take,sai a lokacin ya tuna abinda ya faru yayi saurin juya fuskarsa.
Yarinyar data ga haka kawai ta tabe baki ta daina kallonsa.wasu passengers ne suka fara sauka shine ta samu damar zama akan kujera,shima ya zauna a kujerar dake bayanta,kallon bayanta yake sosai daga ta juyo sai ya juya haka suke tayi har suka sauka.
Tafiya take still tana yar rawa da kmar mai jin waka, shipa abun nata mamaki yake bashi ita kenan ba zata iya tafiya ba normal saita hada da wani tana Abu kamar wata karamar yarinya,ji take tamkar ana bin bayanta amma idan ta duba bata ganin kowa,aliyu gani yayi tana Neman yi masa nisa,wani mai keke yazo wuce daya dauki wani gwangwami akan hanya ya bugawa mai keken akan tayar keken ts gaba Wanda yake saidai saitin kosa da yarinyar keken yayi kanta kmar zai bugeta nan ta jepar da jakar shikoma mai keken ya fada kan kayan mai fruit Allah yasa mai mata barna ba,sai ya shiga basu hakuri ita da yarinya ,aliyu na ganin haka ya dauke jakar yarinyar yayi wani dan toilet da ake yi abakin hanya saboda tsaro,yarinyar na juyowa taga bata ga jakarta ba saurin fara nema jakar tayi amma bata gani bah zuwa hankalinta ya tashi ,hangowa aliyu tayi da Jakarta yayi hanyar toilet din cikin sauri itama ta bishi .
Aliyu ya fito da kayan ciki yaga babu komai sai tarkacen su chocolates da biscuit iri iri da kayan make up harda su pad mah y gani sai koma jotter dasu pens duk gasu nan tarkace dai babu abun kamawa aciki, miss jamila da take kallon komai through his telescope glass tace gadanga nipah banga wani komai bah yanzu ya zaayi kenan? Kafin tayi magana tuni har zahra ta iso dai dai toilet din da yake tana haki kmar wacca ta shekara gudu,moper din dake aje a wajen toilet din ta dauko tare da sawa a jikin inda ake key wai ita a nufinta ta rufeshi,masifa take tayi tana cewa kai barawo ko yau Allah ya kama ka daga ni baza taba yiwa wani sata bah,wayarta ta dauka ta kira police tana fada musu cewar gashi wani barawo ya sace mata Jakarta suyi sauri cos gAta anan ta rufeshi har suzo,aliyu gani yayi tana bata masa lokaci cikin sauri ya daki kopar sau daya moper din ta karye tana yawwa address din gamu a toilet din bakin titin....bata karasa ba taji an fincikota wayarta ta fadi shikoma ya janyota tare da matseta a jikinsa yanda ko motsi bata iyawa ya dauki nail cutter ya fara yanke farcenta cos bai samu komai a jikin mataji da nailcutter din bah.
Jiki na karkaruwa kamar mazari tana jin yadda yanke farcen NATA cikin rawar murya tace da xafy pah! Can u wait for a while aliyu ya fada.Juyuwar da zaiyi sai gani yayi ta kafeshi da ido ta cikin mirror din toilet cikin sauri yasa hannu yayiwa mirror suka daya ya fashe.numfashinta ne yaji kamar xai dauke don tsoro da firgita har jikinta ya fara saki cikin sauri ya yaga ta dakko wani magani tana kokarin sha amma saboda karkarwar da jikinta yake ta kasa har maganin na Neman fadowa cikin sauri ya karba yana tambayarta how many pins are u taking? Ta nuna masa yatsunta biyu da sauri ya dakko ya bata tare dasa abakinta, miss jamila CE ta sake masa magana gadanga mai kake yi haka tunda ka bata maganin ka tafy mna cikin sauri ya dawo daga duniyar tunanin da yake A hankalin ta fara jin nutsuwa sai sannan ta tuna abinda ya faru kafin tayi wani yunkuri aliyu ya fice ya tafy kmar wani walkiya.
Saurin tashi tayi da taji dama dama cos toilet din kmar baa shiga kullum yana a tsaftace ta tattara kayanta a jaka t fito kamar ba itace matsoraciyar nan ba
Yau na shiga uku a wajen oga isah ta fada a rants cos koda zata fada komai bazai yadda saboda yasan halinta.
Cikin sanyin jiki ta karasa wajen da take aiki,Tun daga gate taga ana mata wani kallo,Tana shigowa abokanan aikinta suka hada bakin wajen kiran *zahra* irin kiran da idan aka yi maka Kasan abun babu dama daman a cewarta yan aikin nan sunfi kowa munafurci da kara kaimin fadan murguda baki tayi tare da cewa na changa muku ne
,Oga isa najin ance zahra ya fito da gudu yana dubanta kamar zai daketa,zahra sai yanzu kika zo? Yau koma mai ya tsayar dake wanke wanken ne ko koma girkin breakfast ko wankan yara Oooh na tuna keke ne ya Lalace a hanya,kodai baki samu bus bane ? fada yana kara tsareta da idonsa don inda ka kalli yanda yake fadan saika yi dagaske wajen buye dariyarka,Kujera ya samu y daura daya akan daya ya rike dan gutun gashin bakinsa yana shafawa alamar ita pah yake jira ta bashi amsa, zahra dago da kanta tayi ta kalla kowa a wajen ita yake kallo wasu koma na kwasar dariya kasa kasa cos da alama sun saba da wannan fada da ake mata saboda tsananin son gulma har barin aiyokan da suke yi sukai suna kallon wanne mataki zai dauka,kallonta ta maido gun oga isah oga please kayi hakuri baxan sa...kafin ta karasa harya tari numfashinta tare da cewa kedin CE bazaki daina halinki bah oga Karka damu watarana nice sanadin daukakar wannan gidan labaran,kafin ta sake magana har ya tashi ya bita suna ta zagaye wajen tana oga Karka wani damu wlhy zahra dabance zakaga abinda xai faru a wannan gidan saboda ni ta fada very proudly, jotter dake kusa dashi ya jefa mata yana ke don Allah yimin shiru sai dadin baki. Yau kije gida ki huta cos ko kin zauna bacci zakimin Allah yasa koma inga Gobe baki zo da wury bah.Zahra CE ta tsaya daga zagayen da suke yi cos daman kullum ya tashi yiwa zahra fada ahaka ake yi koma a haka kaf cikin maaikatansa babu Wanda yake so irin zahra cos jininsu ya hadu koma baa shiga tsakanin fadan oga da zahra idan ba hka bah xka ji kunya ne
Dagaske oga? ta fada tana yalwata fuskarta da murmushi Wanda har sautinsa na fitowa kallonta yayi Wanda iya fuskarsa ka kalla sai cikinka ya kulle don dariya ga wani sanko da Kansa ya bayar Wanda gefe da gefe wasu tsirarin gashi ne kmar ka kirgasu,Zahra wato har ynxu ke bakisan gatse bah koh? cewar oga wani shafa wannan sidaddan salon nasa kmar Wanda ake yiwa tankal🤣 ba haka bane oga zahra ta fada tare da xuwa sit nata ta zauna.
Tuni kowa ya soma aikin gabansa,zahra CE kamar abun Kirki ta fara aiki a system dinta kafin zuwa 30minutes harta kwanta bacci kamar ba aiki tazo.
Oga isah ne ya fito zagaye sai ganin zahra yayi tana baccinta cikin kwanciyar hankali.zahra😡 ya fada fusace Wanda yasa kowa na wajen ya nutsu,zahra CE ta tashi tace wlhy oga yunwa nike ji shiyasa amma bari inyi sabon zubi nasan ba zaa fara drink awajenka bah please dan wuntsilo min daya mana.
Oga yace zahra tashi ki tafy gida cos naga ganki yau sai a slow Allah ya kaimu gobe. Cikin sauri zahra tattaro kayanta tare da yiwa abokanan aikinta sai gone suma hka.
Direct gida ta wuce wani hadadden gida ne Wanda ya ansa sunansa wajen haduwa daga gani naira tayi aiki a wajen.Duk haduwar gida wannan gida daga wajen Kadan Wanda a jikin gidan mah take saidai kofar shiga ba daya akwai wani ake saida duk wani kayan drinks da kake cos abban zahra ne abun yake burgeshi amma still akwai kopar da taxa sada mutum da wajen ta cikin gidan inda abbanta ya sanyawa suna *zahra tawa CE* mai karatu shima wanna ko kiyasta gidan da kanku😉
Zahra su uku neh a wajen iyayenta, abdulmalik ne babba Wanda ya gama karatun Business administration a US yanxu shi ke Jan ragamar business din abba sai zahra daga nan auta affan Wanda yake secondary by now,shikenan haihuwa ta tsaya musu amma kullum momma da zahra suna adduar Allah ya kawo musu mace, duk wani gata da tarairaya sun samu a wajen Abba da momma wato mahaifiyarta Wanda idan suna Tare tamkar wasu kawaye amma duk da haka basu bar yayan nasu sun San Grace bah cos akwai irin kallo da idan suka yi masu ba zaka CE suna wasa da dariya haka bah.Amma duk a gidan anfy son zahra kodan ita kadai CE mace.
Alhaji abubakar sadeeq shahararren dan kasuwa koma shahararran barrister yana da matarshi hajia ameena Wanda aka fi kiranta da momma yan asalin garin gombe ne aiki ne ya kawoshi abuja amma duk da haka yana kokarin zuwa gombe cos baya wuce two weeks baije yaga gida koma duk zuwan da zaiyi sai yayi musu alkhairy mai dumbin yawa ba iya yan uwansa ba harda makwabta.wannan CE yasa yake da masoya a duk inda yake.
Zahra tayi karatun mass com.a ABU Zaria tare da fitowa da grade mai kyau cos zahra badai kokari bah,amma tunda ta fara aiki a DiamondTV shikenan zahra ta shiririce Wanda daman aikin tana tana kawai.koma daman aikin iya daga Thursday zuwa Sunday ne,oga isah ne yake rike da wajen amma DiamondTV ba wani shahararran waje bane cos ba kowa bane yasan da wajen.
Zahra yarinya CE yar kimanin 23years amma a ynda take rayuwarta a sangarce da koma yanda fuskarta take baby face saika rantse kace yar 17-18 years ,doguwa CE amma tana da kirar jiki mai kyau ta gaske mah kowa cos ita CE ake kiran irin jikinsu da figure 8,akwaita da hips tare da mazaune masu daukar hankalin mai kallonta ga kirjinta a cike dai dai da jikinta wannan CE yasa momma ta dinka mata dogayen riguna masu yawan gaske tare da hijjabinsu Wanda idan tasa saita dawo karama sosai koma bazaka taba ganin Surar jikinta bah,Asali ma zaka dauka ko kwaila CE.
Zahra data dawo saida ta Dade tana saka da Warwara cos bata San abinda zata fada a gida ba ace ta dawo daga aiki lokaci baiyi bah.chan wata dabara ta fado mata saida ta shigo cikin gidan tukunna ta haye step taje falon dake tsakiyar gidan ta saki kuka mai tsoma zuciya kamar dagaske koma a lokacin kukanta take tsakanin da Allah cos yanzu ta kara tunowa da. Abinda Gadanga yayi mata......
Am sorry reader for any kind of mistake cos this is my first novel.
0 Comments