Yan Ta’adda Sun Yi Min Kwanton-bauna amma mataimakina ya ceceni>>Buratai

 Babban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya ba da labarin yadda ‘yan ta’adda suka yi masa kwanton bauna a arewa maso gabashin kasar a shekarar 2015.

Mista Buratai ya bayar da bayanin yadda aka yi masa kwanton-bauna na farko a matsayin shugaban sojoji a ranar Litinin a yayin kaddamar da wata gada da Kundin Injiniyan Sojojin Najeriya, Ede ya gina a Kuta da ke Jihar Osun.


Gadar an sa masa sunan Mista Buratai.
Da yake magana game da kaunarsa ga jihar Osun, ya ce mataimakinsa, Lamidi Adeosun, wanda shi ne Shugaban horar da ayyuka a yanzu, ya ceci rayuwarsa a 2015.
Mista Adeosun dan asalin Asamu ne a jihar Osun.
A cewar jaridar Punch, Mista Buratai ya ce mataimakinsa ne ya hada sojoji don tunkarar ‘yan ta’addan da suka kai masa hari a watan Satumbar 2015.
“Lokacin da aka mana kwanton-bauna na farko, sai ya kasance tare da ni a cikin motar, a gefena kuma na ga irin karfin gwiwar da ya nuna. Ya sami damar tattara sojoji don tunkarar ‘yan fashi,’ yan ta’adda daga hanyar.
“Lokacin da aka nada ni Shugaban Hafsun Sojoji, na hadu da Lamidi Adeosun a yankin Arewa maso Gabas, na hadu da Adeosun a matsayin kwamandan ayyuka a can kuma ya fara aikin sauya fasalin sojojin Najeriya kuma mun fara ci gabanmu ta yadda aka karya lagon kungiyar Boko Haram, “kamar yadda aka ruwaito shi yana cewa.
Shugaban sojojin ya jinjina wa rundunar Injiniyan Sojojin da suka gina gadar sannan ya kuma gode wa Olowu na Kuta, Adekunle Oyelude, saboda goyon bayan da ya ba wa sojojin yayin da suke shan suka daga jama’a.
Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya ce gina gadar zai karfafa dangantaka tsakanin sojoji da fararen hula a jihar.

Post a Comment

0 Comments