YADDA AKE HADA FRUIT SALAD🍌
🍉
🥒
🍓
🥗
*Kafin mu fara bayanin wannan hadi akwai karin bayani kadan da nakeso nayi shine, uwargida ta fahimci cewa shi wannan hadi fa ba komai kika gani wata ta hada a nata bane kema zaki saka domin shi hadi ne kawai da zaki zabi kalolin kayan marmarin da kikeso ko maigida yakeso ki hada dasu kuma bawai yawan fruits dinne yake sa yayi dadi ba kawai ya danganta da hadin da kikayi na dacewar kayan marmarin.
*Dan haka a duk lokacin da zaki hada sai ki zabi kayan marmarin da kike bukata ko wanda kike dasu a lokacin koda kuwa basufi kala hudu ko biyar ba sun wadatar, saboda haka a yanzu a hadin da zan kawo mana na zabi wasu kayan marmari da nafiso kuma nake ganin ba zasu wahalar damu wajen siya a kasuwa ba.
*KAYAN HADI*
Ayaba
Gwanda
Kankana
Tuffa
Inibi
Yogurt ko Madarar ruwa
Sukari (Ga mai bukata).
*YADDA AKE HADAWA*
_Uwargida ta dauko ayaba kaman guda biyu ko uku ta bare ta ajiye, sannan sai ta dauko gwanda ta yanka itama ta bare ta ajiye, sai ta sake dauko kankana ta yanka kaman rabin kwallo ta ajiye, sai ta dauko tuffa ta fere bawon ta yanka biyu ta ajiye.
_Daga nan sai ta samu ruwa mai kyau ta sake wanke kayan sai tabi kowanne ta yayyanka kanana-kanana sai ta juye a kwano mai dan girma ta ajiye, sannan ta dauko inibi shima bayan ta wanke shi duk da kanana ne sai ta yayyanka shi gida biyu-biyu ta juye a ciki.
_Sannan sai uwargida ta dauko Yogurt amma anason mai dan yawa yadda idan ta juye a hadin zai shanye samansu sai ta zuba sosai ta samu ludayi ta jujjuyasu sosai sai ta dandana taji idan tana bukatar kara sukari to sai ta zuba yadda take bukata......
0 Comments