Wani al'amari mai cike da ban mamaki daya Faru da wata yarinya, yarinyar ta kasance a kurkukun mahaifinta tsawon shekaru 24,
A ranar 28, ga watan Ogusta a shekara ta 1984 yarinyar yar shekara 18 mai suna Elisabeth Fritz ta bata, inda mahaifiyar ta Rosemarie tayi ta cike fom akan yarta ta bata ta mikawa hukuma.
Anshare makonni 4 ba labarin Elisabeth inda iyayenta ke cike da alhinin rashinta kwatsam sai aka wata wasika wadda ta bayyana cewa Itafa tagaji da zama da iyayen nata hakan yasa ta gudu ta bar masu gida.
Mahaifin yarinyar mai suna Josef ya shaidawa jami'in dan sanda cewa shi besan inda yarsa taje ba, saidai yana tinanin kila yarinyar ta shiga kungiyar asiri ne saboda ta taba bayyana haka a baya.
Saidai gaskiyar zance shine Josef yasa hakikanin inda yarsu take , saboda be wuce taki 20 daga inda Dan Sandan yatsaya zuwa inda yarinyar take ba.
Yadda Abun yafaru
A ranar 28, ga watan Ogusta 1984, Josef ya kirawo yartasa zuwa wani gidansa dake karkashin kasa a lokacin da yake gyaran kofar wani daki, ya kira Elisabeth ta taya shi tana zuwa bayan shigarta dakin sai ya garkameta a dakin.
Bayan ya rufeta a dakin sai yaci gaba da yiwa mahaifiyar yarinyar karya tareda yan Sanda akan cewa yarsa ta shiga kungiyar asiri ne inda jami'an yan Sandan suka kasa gano inda yarinyar take har suka manta da batunta.
Saidai Josef bai manta da yarinyar ba yayinda jami'an tsaro suka manta maganar yarinyar.
Josef ya kasance yana shiga inda ya boye yarinyar tin karfe 9 na safe har zuwa dare yana can tareda yarsa, kuma matarsa bata nuna damuwa ba tana tinanin yana gurin aikinsa ne saboda mutum ne jajirtacce a wurin aikinsa.
Josef ya kan shiga wurin yarinyar sau uku a sati karanci, inda wasu ranakum kuma kullum sai ya shiga dakin a cikin shekarun biyun farko, alokacin kuma yafara saduwa da ita dik dare lokacin tanada shekara 11.
Bayan kwashe shekaru biyu a cikin kurkukun Elisabeth tasamu juna biyu, tazubda cikin bayan mako goma da samun cikin. Bayan wasu shekaru biyu ta kuma kara samun juna biyu , wanda ta haifi yarinya tasa mata suna Kerstin, bayan wasu shekaru biyu ta sake haihuwa ta haifi namiji Stefan.
Kerstin da Stefan sun kasance cikin kurkukun gidan tareda mahaifiyar su, inda Josef yake kawo masu abinci da ruwa dik sati , Elizabeth ta koyar da su Dan abunda ta sani na rayuwa .
A cikin shekaru 24 Elisabeth ta haifi yara biyar, daya daga cikinsu ya kasance tareda ita a kurkukun, daya kuma ya mutu Jim kadan bayan haihuwarsa, yara uku kuma sun zauna tareda Rosemarie da Josef.
Kafin Josef yakawo yaran a gidan sai da ya zaunar dasu a bayan gidansu inda ya basu wata wasika suka rike , wasikar dake nuna cewa Elisabeth ce ta yada yaran a bayan gidansu inda tace yayanta ne data haifa kuma bata iya ci gaba da zama dasu ba. Hakan yasa ta kawowa iyayenta.
Abun mamaki ganin yaran tareda wasikar sai Rosemarie ta karbe su ta kuma daukesu jikokinta ita da mijinta.
Haka Josef yaci gaba da tsare yarsa a kurkukun yana saduwa da ita kamar matar sa, a shekarar ta 2008 ne yar dake hannun Elisabeth a kurkukun ta kamu da rashin lafiya .
A lokacin Elisabeth ta roki mahaifinta da ya taimaka yakai yarta Kerstin yar shekara 19 asbiti, saboda irin matsanancin halin da yarinyar take ciki bayan Elisabeth tayi magiya sai Josef ya amince akaita asbiti .
Ya fito da Kerstin daga kurkukun inda ya kira motar asbiti, inda anan ma ya shirya sata wata wasikar dake nuna cewa Elisabeth ce ta tura yarinyar.
Bayan mako daya sai Jami'an yan sanda suka tambayi Kerstin game da mahaifiyar ta saidai bata bayyana komai ba, daga bisani suka tambayi iyalan Josef Shima ba wani Bayani, Kasancewar wasikun da suke gani sai suka shiga binciken Josef.
A ranar 26 ga watan afrilu 2008 Josef ya saki Elisabeth daga kurkukun a Karon farko cikin shekaru 24, sai tayi sauri ta isa asbitin da yarta ta ke domin dubata, inda likitocin asbitin suka sanar da yan Sandan zuwanta.
A lokacin yan Sanda suka tafi da ita domin bincike gameda lafiyar yarta da kuma bincike akan labarin mahaifinta, inda ta bayyana masu yada ta Kasance a kurkukun mahaifinta tsawon shekaru 24.
Ta bayyana cewa mahaifinta ya boyeta a wani guri inda ta haifi yara bakwai , inda ta bayyana cewa Josef shine mahaifin ya'yan nata 7.
Elisabeth tace mahaifinnata yakanzo da dare inda yakan sanyata kallon bidiyon tsiraici , daga bisani yayi lalata da ita, inda ta ce ya kasance yana lalata da ita tin tana yar shekara 11 a duniya.
Bayan yan Sanda Sun Kama Mahaifin nata , Rosemarie ta gudu ta bar gidan saboda bakin ciki da rashin sanin abunda ke faruwa da yarta tsawon shekaru 24 .
0 Comments