Wayasan gobe. Hausa novels

 Wa yasan gobe?

▶1⃣

safiya Abdullahi musa huguma

🌺🌺🌺🌺🌺🌺


Zaune take dirshan bisa carfet din dake mamaye da qaton dakin nata,ta tanqwashe qafafunta yayin data tallafe kumatunta da dukka tafin hannunta,lokaciguda kuma ta zubawa food flask din abincin dake gabanta ido,a zahiri idan ka dubeta zakayi tsammanin flask din take kallo sai dai sam ba haka bane zuciyarta da ruhinta sun lula wata duniya ne ta daban,da yunwa ta shigo gidan saidai sam ta kasa sa koda loma guda ta abincin a bakinta,cikin kwanakin tana cikin wani yanayi wanda ta kirashi da jarraba ko musifa dake tunkaro rayuwarta

Wannan ne karo na hudu a rayuwarta da idaniyarta tayi tozali dashi saidai ya zame mata masifa,tun daga ranar da ta dora idonta akansa wani baqon lamari ya ziyarci zuciyarta da gangar jikinta,zata iya kiran lamarin da zazzafan so wanda ya zamto mata tamkar harara a duhu,dalikinta na fadar haka kuwa shine wanda zuciyarta ke budurin a kansa baisan Allah yayi ruwan halittarta ba a doron duniyar subhana,tayi kukan tayi takaicin yadda zuciyarta tayi mata rashin adalci ta hanyar kamuwa da soyayyar wanda batasan koshi waye ba?,meye sunansa?,a ina yake?,taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta jawo flask din ta bude da niyyar taba wanu abu a ciki kota tsira daga fadan umminta,ilai kuwa tana loma ta biyu taji sallamar ummin tana daga tsaye ta dubeta tace"yanzu fadila tun shigowarki kika damemu da zancan jin yinwu amma kusan aqalla awa guda banga wani abun kirki da kika ci ba?,tadan yamutsa fuska tace wlh ummi da yunwar na shigo amma kinga na kasa ci"ummi tace ,haka dai kika iya kullum kamar wata qanqanuwar yarinya sai anyi fama dake akan cin abinci ko?,yayi miki kyau ai kinsan ulcer dai ba gidanku daya ba bare kice idan ta kamaki zata miki sassauci,tayi dan murmushi tace kiyi haquri ummi insha Allahu yanzu zan kawo miki flask din empty,ummin tadan harareta tace ai jikina kunne ne,fadila tadan qumshe dariyar da keson subuce mata,har takai bakin qofa ta juyo tace"af na manta ki shirya yanzun zaki kaini gidan alh salim kwana biyu su shiru muma shiru"tadan sosa kanta dake a tsefe saidai ta tufke shi da band tace anya ummi zan gane ma gidan?,ungo wannan ja'ira cewar ummi da ta watsa mata daquwa yace"nima in banda abbanku yace in tafi dake zaki maku siyayyar kayan make up da da driver zanyi tafiyata"tayi ko saurin miqewa tace yauwa ummi dama jiya nayi masa zancen kayan,tace ato minti goma ki sameni ina falo ina jiranki,ta amsa tana qoqarin shiga toilet dinta dake manne da bedroom din

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tsaf ta shirya cikin abaya baqa mai sulbi saqar qasar dubai wadda aka mata ado da jajayen dutsina masu sheqi,ta nannade tulin gashinta tayi a cuci dashi sannan tayi rolling da wani dan kyakkyawan jan mayafi,simple make up tayi amma kasancewarta tana da wani sassanyan kyau sai ta fito gwanin sha'awa,ta daura agogo na fata ja sai plate shoe da tasanyawa qafarta mai ja ne mai baqaqen igiyoyi,wayar hannunta kawai ta dauka hade da key din motarta ta sake kallon kanta a madubi,cikin zuciyarta ta qaryata masu cewa abu mai duhu baya giwa baqi kyau,duk da cewa ita din ba baqa bace irin matan nan ne masu launin fata(chaculet colour)wasu kuma suce black beauty,fatarta batayi haske can ba kuma kai tsaye ba zaka kirata baqa ba tamkar irin black american haka yanayinta yake,fadila nada wani irin kyau mai sanyi wanda tashin farko bazaka gama tantance kyawunta sai kuna tare wato qananun kyau ne da ita,ba abu mafi daukan hankali a tare da ita irin qirar jikinta cocacola shape,idanunta manya masu dauke da gazar gazar din gashi wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa gun tafiya da zuciya gami da ruhin mazaje da dama,goshinta kam irin qananun Gashinnan ne kwance luf wanda ko tayi dauri basu boyuwa,muryarta a sanyaye take cike da wani sirri wanda idan tayi magana take janye hankalin jama'a da dama,fadila tako ina Allah ya bata zubi da tsari wanda yasanya take burge mutane ba maza kawai ba hatta ga yan uwanta mata ma,sai dai gwanar miskilanci ce,sam magana bata dameta ba,tafi ganewa tayi karance karance maimakon zaman tadi,fadila yanzu haka daliba ce a jami'a bayero kano tana karantar mass com,duk da cewa abbanta yayi mata sha'awar karantar medicine ganin cewa mass com bana mutum ne mara son magana ba amma data nuna masa tafi sha'awar mass com din sai ya barta da zabinta kasancewarsa mutum ne mai sauqin kai,sai ya maida zabin nasa kan 'yar uwarta farida,alh abbas ahmad shine mahaifin fadila dan kasuwane mai rufin asiri,domin Allah ya bashi wadata irin wanda ko wane dan adam ke fatan samu ba abunda aka nema a gidansa a ka rasa,asalinsa bafulatanin bauchi ne,yana sana'ar sai da shaddodi da yadiddika cikin kasuwar kwari,yakan tura babban dansa wasu lokutan china ko india domin shigo da kayan su kuma zuzzuba a shagunansu dake cikin kasuwar,ya auri mahaifiyarsu haj amina a maiduguri cikakkiyar shuwa ce wadda Allah ya qaddari aurensu tun bayan da yayiwa manemanta dintinkau a zuciyarta,anan garin kano suka ci gaba da zama tunda anan kasuwancin nasa yake,haihuwar farko suka sami da namiji inda yaci sunan ahmad,baiyi wani tsawon rai ba Allah ya karbi abinsa,shekara daya tsakani suka sake samun wani yaron aka mayar masa da sunan ahmad din,daganan haihuwar tayi musu dif tamkar aun daina,wanda a tsakanin har amina ta soma fuskantar qananun maganganu irin na dangin miji duk da cewar ba a kusa suke ba,sai bayan shekaru goma Allah ya sake qaddara musu samun wata haihuwar,ta haifi 'yar kyakkyawar budurwa taci sunan fadila,shekara biyu tsakani Allah ya sake kawo wani rabon nan ma mace ta haifa aka sa mata farida,kasancewar fadila mara saurin girma sai suka taso kai daya da farida idan ka gansu zakayi tsammanin twince ne don kamarsu daya saidai farida tafi fadila garin jiki da kuma farar fata,tasowarsu tare yasanya komai daya ake musu hatta makaranta tare aka sanya su,sai da suka shiga jami'a ban bancin course ya raba su,shekara shidda da haihuwarsu umminsu ta sake haihuwar da namiji inda aka sa masa muhammad tun daga lokacin kuma haihuwar ta musu bankwana

Babban wansu ya ahmad yayi aure tuni da matarsa anty hafiza harsun samu albarkar twince duka mata ,rayuwar gidan rayuwa ce mai ban sha'awa cike take da son junansu suka taso girmama juna da qaunar juna,sai dai tsakanin fadila da farida akwai tsokana fada da wasa na tsakanin sakuwa da sakuwa sai dai duk da haka farida na respecting din fadila

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

S.A huguma

[10/16, 12:18 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?


Safiya Abdullahi musa huguma


🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶2⃣


Sun fito kenan daga gidan farida ta shigo da motarta layin (da yake ya ahmad yayi qoqari bayan kammala secondry sanda suka samu admission a jami'a ya sai masu yan qananan motoci rio,yace tunda fadila baqace ta dauki fara farida kuma ta dauki marun)farida ce ta soma jan burki ta tsaya don tasan halin mutuniyar zata iya shigewarta tace"ummi ina zaku je?" "Gidan alh salim kwana biyu haduwa tayi wuya shine zanje dubasu"cikin tsokana ta kalli fadila tace "wlh ummi gwara da kika banbaro kifin rijiyar nan kika fito da ita inaga tafi shekara dubu bata je gidan uncle abba ba"fadila ta watsa mata harara tace"ni sa'arki ce"ta qyal qyale da dariya tace sorry yaya fadila"fadila tayi saurin yiwa motar key suka wuce,suna tafiya a hanya suna hira jefi jefi da ummi abinsu gwanin sha'awa har suka isa gidan,gidan na jerin gidajen kundila housing estate dake maiduguri road,gidane irin na masu naira da suka ci suka tada kai,mai kula da qofa ya dage masu wakeken get din gidan cikin fara'a suka shige kasancewar akwai sanayya mai yawa tsakaninsa da ummin

Ummi ce a gaba fadila na binta a baya har suka isa tafkeken falon gidan ,haj maimuna na zaune bisa luntsuma luntsuman kujerun dake kewaye da falon kallo suke ita da yaranta sumayy da rabi'ah,sallamar su ita ta dauki hankalin su suka juyo hade da amsa musu,haj maimuna ta miqe cikin girmamawa tana cewa lale marhabin haj kune tafe da yammarnan ,ummi tayi murmushi tace ai kuwa dai kam"ta sake fadada fara'arta tace sannunku da zuwa ai......,maganar haj ta katse ta kama baki tace"a'ah yarannan yau yaushene?,ta fadi tana kallon fadila,dukkansu sun fahimci me take nufi suka qyal qyale da dariya suka ce momi yau laraba,ta gyada kai tana cewa lallai ba shakka ta bawa ranar samu,wlh haj bazan iya lissafa yaushe rabon fadila da gidannan ba,"ummi tace"hmmmm to wlh yauma da qyar na banbarota don taji zamu biya store ne zata kwaso kayan make up shine ma qarfin biyonin"momi ta sake gyada kai cike da mamaki tace lallai yau mun tashi da bismillah haj ku zauna mun tsaya zance na barku a tsaye,dukkansu suka zauna sannan suka fara gaisawa fadila ta gaida momi a kunyace ,ta amsa mata tana cewa"kyaji kunya mana mara zumunci ,sam farida ta fiki zumunci "sumayya dake kusan sa'a ga farida tace"wlh anty fadila faridammu ta fiki zumunci"fadila ta dan harareta da taga idonsu ummi baya kansu tace"ta dai fini qafar yawo yaufa sai da zamu fita ta dawo tun azahar wai ta tafi gidan qawarta "sumayya tace "to ai zumunci taje"fadila ta dan tabe baki tace"ke ni qyaleni yawon farida yafi qarfin qafata ko ina a kano kika kwatanta mata ta sani "sumayya da rabi'ah sukai dariya suka ce "kai anty don dai ke bakison fitarne shi yasa kikace sister ta fiya yawo"

Hira suke suka tsinci qanqanuwar muryar yarinyar na sallama ,ta saki hannun wanda ya riqota da gudu ta fado falon,momi ta cewa wanda ya kawota din sannu isah,yace yawwa haj ya juya ya fice,rabi'ah tace oyoyo ifti na,muga kitson,da gudu ta fada cinyarta ta janye hular da ka rufe mata kanta da ita tana nuna mata,kalbace mai kyau twisting wadda aka lafe jelar ta da beads masu kyau,kasancewar yarinyar nada tsawon gashi sai ta kwanta lub tayi kyau har dokin wuyanta,tace anty sumy tayi kyau"sumayya tace gsky qawata ba magana "ta bata hannu suka tafa,ta miqe tayi gun momi ganin ummi yasata duqawa ta gaidata,ummi ta amsa fuskarta dauke da fara'a momi tace"har yanzu fushi ake kenan da ni shi yasa ni baza'a nuna min kitson ba"cikin magana irin tq shagwababbun yara tace "ba cewa kikayi ayimin mai zafi ba"sai kuma ta juya ta koma gunsu sumayya tana bata lbr,ummi ta kalli momy tace"wai iftihal din Aliyu ce wannan?"momi dake tsiyayawa ummi lemo a cup tace"itace mana kinga yadda ta girma ko?"ummi ta jinjina kai tace"ba shakka gata nan kuwa masha Allah,ina zaton ai ba zata wuce shekara bakwai ba ko?"momi tace "idan watan nan ya mutu sabon wata ya kama yakai ashirin zata cika shida",sai bayan sunyi magariba suka fito,tuni iftihal ta maqale wa fadila domin cikin qanqanin lokaci suka saba,don fadila ba daga baya ba gun son yara,bare iftihal yarinya ce kyakkyawa ga wayon tsiya,har bakin mota suka rakosu sumayya na yaba kyawun motocin nasu,fadila tace idan kina so ki amsa mana,sumayya ta kama baki tace rufamin asiri kada kisa yaya aliyu ya babbalani kina ganin abba zai sai mana ma ya hana wai har yanzu bamu da hankali sai randa muka qara nutsuwa?fadila tayi dariya tace "sai kace yau aka haifeku""kema dai kya fada sister cewar rabi'ah,dai dai nan ummi da momi suka qaraso momi ta miqawa fadila baqar leda tace"to ga kayan kwalliyarnan aje ayi tayi ana samo mana sueukai"a kunyace ta amsa tana mata Godiya,momin tace to sai wata shekarar kenan,fadila ta sadda kai qasa tace"a'ah momi insha Allahu zaku dinga ganina"Allah yasa inji momi,ummi tace"wai ni kuwa ina Aliyu ne,na kwana biyu rabon da na ganshi fa"fuskar momi ta canza zuwa yanayin damuwa tace"hmmmm,mtsw,ke dai bari kawai haj kwanan nan zaki jiyomu da shi,Aliyyu fir ya guji aure yaqi fidda mace yayi aure,yafi ganewa kasuwancinsa kawai nayi har na gaji hakanan abbansa kullum zancen kenan amma yaron nan sam yaqi mai dakansa"ummi tace"addu'a kawai zaku ci gaba da yi masa Allah ya kawo ta gari kada a kuma komawa 'yar gidan jiya a bata goma daya bata gyaru ba"momi ta gyada kai tace hakane,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"tace amin

Daqyar iftihal ta rabu da fadila harsai da ta laluba cikin motarta ta samo mata chaculet sannan ta yarda ta barsu suka tafi,basu tsaya ako ina ba sai a shop rite dake ado bayero mall,ta nufi parking space ta gyara tsayuwar motarta sannan ta kashe,ummi ta zaro kudi cikin jakarta ta miqa mata,tace maza kiyi da jiki ki fito"tasa hannu biyu ta amshi kudin tana qoqarin maida murdin motar ta rufe ne ummi tace"saura ki kwaso kayan zaqi da sanyi ki koma gida ki guji maqiyin naki abinci"tayi murmushi kawai tace baza'a siyo ba ummi ta rufe motar ta shige,cikin nutsuwa take daukar musu abinda tasan suna da buqatarsa ita da farida har ta kammala,har zata nufi kanta ta tuna bata dauki turarenta ba blue lady,cikin sauri ta koma,hankalinta yatafi ga turarurrukan tamkar ance ta kalli gefanta,tsaye yake shima yana zaban nasa kalan,yana sanye cikin shadda dinkin tazarce blue Black ce ta haska farar fatarsa matuqa,ta gefan tana iya hango qaya taccen sajensa dake kwance luf bisa tsararriyar fuskarsa,ga tsinin hancinsa nan yayi das qasan farin qal din glass dake bisa fuskarsa,kyakkyawan idonsa wanda gashin idon suka yiwa rumfa suna juyawa cikin farin glass din nasa yan karanta rubutun dake jikin kwalin turaren,kansa ba hula sai sumarsa dake kwance an dan saisayeta,ya zari turaren kwali uku cikin sassarfa ya juya yabar gun,samun kanta tayi da bin bayansa zuwa inda zai biya kudinsa ,kusan tare suka biya sai dai sam shi bai lura da ita ba ya juya ya fita ta sake bin bayansa,tafiyansa ma abar kallo ce tamkar wani saraki haka yake takawa,daga nesa tadan tsaya a harabar adana motocin don batason ya ganta,cikin aljihunsa yasa hannu ya zaro key ya bude wata baqa sidiq din mota qirar range rover ya shiga yayi mata key ya jata da gudu ya bar gun,jan ajiyar zuciya tayi gamida lumshe idonta hadi da dafe goshinta da tafin hannunta"inna lillahi wa inna ilaihir raji'un allahumma ajirni fi musi bati wa akhlifni khairan minha"abunda take ta nanatawa kenan,wannan wace iriyar musibace zuciyarta ke son jefata ba gaira ba dalili?,ta bude idonta ahankali jikinta ba laka ta soma lalubar inda tayi parking

Cikin motar tayi dif zugi da radadi take ji,ba abunda zuciyarta keyi sai zillo cike da dimbin qaunarsa,shi wa?,ita kanta bata sanshi ba,ummi nata mata hira tana cijewa tana amsa mata har suka isa gida,farida na falo ta baje kolin takardu da alama assignment takeyi,batason ta dameta da hira don haka tadan daure fuska,itama faridan data fuskanci hakan bata ce mata komai ba illa sannu da zuwa ya kuka barosu?,ta amsa mata ta haura sama inda dakinsu ita da farida yake,ta watsa siyayyar tasu kan gado zuciyarta cunkushe ta cire kayan jikinta ta fada toilet da niyyar sakarwa kanta ruwa ko zataji sanyin zuciyarta


Post a Comment

0 Comments