Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
▶5⃣
Ya dan gyara zamansa cikin isa ya amsa mata"Aliyyu salim maitama shine cikakken sunana""sunan ya dace da maishi"ta fadi a ranta,cikin nuna qwarewa da gwaninta ta shiga jefa masa tambayoyi daya bayan daya,sai da suka kwashi kusan awa guda sannan ta saurara masa,ta katse abun recording din nata ta jefa a jakarta,ta miqe tayi gaba abinta,saidai can qasan zuciyarta farinciki ne fal ranta,yau ta zauna daf da shi ta shaqi qamshinsa ta saurari muryarsa son ranta,shi kam bin ta yayi da kallo cike da mamaki da takaicin raininta don a gurinsa wannan raini ne.
Zaman ta tayi cikin mota tana dakon zuwansu hafsat
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dukkaninsu suna gidan alh salim,kasancewar yau ake birthday din iftihal,rabi'ah sumayya farida da fadila anty hafiza sai anty hauwa'u(babbar yar haj maimuna)duk suna bedroom din momi,fadila na kwance bisa gadon momin,dakin ya kaure da hayaniya amma banda ita,sam gun ma baya mata dadi,tun jiya da Abba yayi mata da ya ahmad suka yi masu magana ita da farida kada su kammala attachment dinau ba tare da sun kawo mijin aure ba,farida kam ko ajikinta tunda dama irin wannan damar take jira ita da masoyinta mubarak
Ta sake juya kwanciyarta hannun damanta kanta yayi mata gingirin zuciyarta a cunkushe,anty hafiza ta juyo ta kalleta "fadila ki saki ranki don Allah kiyi addu'a shine kawai mafita "fadila ta lumshe idonta hadi da sake qanqame pillow tana sake jin nauyi cikin qirjinta,anty hauwa tace "me ya sameta ne tun dazun na lura bata cikin sukuni",anty hafiza ta gaya mata hadi da cewa"na rasa irin farida kwata kwata bata kula kowa,nan da kika ganta bata da wani gwani"farida tace " anty itama fa da laifinta ya za'a ce duk mazan dake mutuwar sonta ace babu daya da ya mata"a fusace fadila ta kalleta😡"anty kinganta ko ko da ita ake magana?😫"dama zuciya kusa a kusa sai hawaye wani na bin wani😭"anty hauwa'u tace"duk ku tashi ku fita ku bamu wuri"tsam suka fice dakin ya rage daga ita sai fadilan sai anty hafiza,anty hauwa'u taja ajiyar zuciya tace"sai nake gano dacewa tsakanin fadila da Aliyyu Abban iftihal ba don kada nayi muku shishshigi ba da na hada wannan alkhairin"gabanfadila yayi matsananciyar faduwa💔 jin an ambaci Aliyyu,inama ace shine aliyyun da anty hauwa'u ke magana akai?,ina ma ace shine zai taho da neman soyayyarta?,ina ma ina ma.........taci gaba da zancen zuci
Anty hauwa taci gaba da cewa"shima anyi anyi da shi ya fidda mata tayi aure ya qi,sai jiya ya kawo wata yarinya mai zubin yare ba alamun tarbiyya a tattare da ita wai ita yake son aura,hafiza yarinyar bata da maraba da matarsa ta farko,amma sai ya kakkareta da cewar wai zaman cikin yare ne yasa aka ganta haka amma da nutsuwarta.
Fadila tayi hanzarin tashi don batason zancan da anty hauwa'u ta dauko yayi ma wani nisa,tayi qasa da idonta😪 tace"anty ba wai inason watsa miki qasa a ido bane a'ah,bansan ya Aliyu ba sani na da shi tun ina qarama ne wanda a yanzu na manta shi gaba daya,shima kuma nayi imanin ba sanina yayi ba,ba ta wannan ba anty a zamanin nan auren soyayyar ma ya aka cika bare auren hadi,matar cushe anty ba ta daraja,kawai ku tayani addu'a Allah yayi min zabi mafi alkhairi"suka amsa da amin suka kuma bar maganar suka shiga wata badan maganar ta bar ran anty hauwan ba
Kwana biyu da yin maganar anty hauwa na juya maganar cikin ranta sai ta kasa hadiye maganar har sai da ta niqo gari ta dawo gidan don tattatunawa da abba"tana zaune gaban abban bayan sun gama taba hira tace"abba nazo maka ne ne da wata muhimmiyar magana"abban ya bada dukkan hankalinsa kanta sannan yace"uhm ina jinki maijidda"ta dora"abba kasan fadila 'yar abba abbas tafida?"yayi murmushi irin na manya yace"banda abinki maijidda idan ban san su farida ba ai kuma bansan kuba,"tayi dariya ita da momi tace hakane abba"tiryan tiryan take gaya masa halin da yanzu fadila ke ciki game da zancen fiddo da miji,sannan ta dora"abba inason ne na haska muku abinda tuna nina ya hasko min game da wannan lamarin""uhn"cewar abba,anty mai jidda ta dora"abba Ali ya kawo muku yarinyar da azahirin gaskiya baku yadda da halaye da nagartarta ba,ali abba ya riga ya fada soyayyar yarinyar wadda da zarar kunce zaku hana shi auren ta dama ce tq zo masa ta yaci gaba da zama babu zancen aure,zai kafa hujja da cewa ai tun tuni ya kawo ku kuka qi abun"abba ya gyada kai cikin gamsuwa maijidda ta dora da fadin"to abba mai zai hana ku bashi damar ya aureta amma abba ku hadashi da fadila?,abba kai ganau ne ba jiyau ba ka fini sani kasan fadila kasan irin kyakkyawar tarbiyyar da suke da ita,mai zai hana muyi kwadayin hada zuri'a da su abba?,abba kada mu bari ta subucewa family dimmu saboda fadila macace ta gari wadda nake da yaqinin samun alkhairai masu tarin yawa da zuriyya dayyiba tattare da ita?"
Shiru sukayi gaba dayansu bayananta na ratsa su tabbas duk abinda maijidda ta fada gaskiya ne,sun gamsu matuqa da bayananta,abba yaji dadi matuqa sosai tare da sawa maijidda albarka gameda zurfin tunanin da tayi akan makomar rayuwar dan uwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari alh salim da kansa ya taka ya nufi gidan amininsa alh abbas tafida,suna babban falon sa bayan sun gam gaisawa alh salim yace"abbas nasan zakayi mamakin ganina ko da daddarennan bayan jiya da azahar ma muna tare"alh abbas yayi murmushi yace ai nasan akwai dalili,kuma ma mene a aciki don dan uwa ya ziyarci dan uwansa aduk sa'adda da yaso?"alh salim ya gyada kai yace"hakane dalili ne kuwa babba ya taso da ni"alh abbas ya vyara zama yace"ina jinka Allha yasa lpy"alh salim yace"danka Aliyyu nazo nemawa auren'yata fadila"alh abbas yace"fadila?"ya gyada kai qwarai fadila ko anyi mata miji ne?"alh abbas ya girgiza kai yana murmushi yace"ko daya wlh,rigimar da nake ma da ita kenan a 'yan kwanakinnan kenan akan sai ta fito da miji,maganarka alh ta yimin dadi sosai wlh,amma ina fatan da amincewar alin?"a'ah ko daya wannan hasashe nayi na son hada zuriyya da aminina"alh abbas ya saki dariya yace"yayi wlh wannan tunani naka yayi kyau qwarai da gaske,domin samun nagartacce kamar Aliyuna a wannan zamanim abune mai matuqar wuya qwarai da gaske,fadila'yar ka ce halak malak kuma ko wani kaso bata wlh zaka iya bashi bate aliyu,na bawa aliyu ita har abada abokina"alh salim yace"a'ah abokina kada kayi saurin yanke hukunci ba tare da kaji ta bakin ta ba ka bari su gana taga idan har yayi mata"alh abbas yace"haba salim Haba salim yaya zaka ce haka bayan kasan yarinya budurwa ubanta ne ke da ikon zaba mata mijin aure ballantana duk yaron da zata zaba mawuyacine yakai nagarta da ingancin aliyyun,ai magana ma ta qare dama dab suke da kammala attachment dinsu nafison ace da zarar sun kammala su tafi dakunansu"
Alj salim yaji dadin maganar yace"amma fa wani hanzari ba gudu ba,akwai yarinyar da aliyun zai hada su ya aura tare,to ya kamata a sanar da ita kasan yaran yanzu basa son abokiyar zama kaga ya kamata ta sani kafin ayi"alh abbas yayi dariya yace"shirmen banza ne iri na 'ya'yan yanzu zan sanar da ita kada ka damu,bamu buqatar duk wasu kaya na bidi'o'i"alh salim yace"a'a kaima ka sani momimta haj maimuna ba zata yarda ba yadda za'a yiwa dayar itama sai an mata"suka sa dariya gaba dayansu cikin farinciki,cike da godiya bisa karamcin da amininsa yayi masa"alh abbas yace ka daina godiya da Aliyu da fadila duk daya ne a gurina"alh salim yace"na sani amma duk da haka godiya ta zama dole duk wanda yayi ma jininka kyautar da sukutum da guda ai ba qaramin masoyi bane,cikin girmamawa da mutuntuna juna sukayi sallama
Safiyya(mra muhammad bello)
[10/16, 12:22 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶6⃣
Cikin daran alh abbas ya sanar da mai dakinsa,tayi murna qwarai don tasan amincin dake tsakanin mazajan nasu da irin tarbiyyar dake gidan alhj salim,sai dai tace wani hanzari ba gudu ba alhj ba lallai yaran su so junansu ba fa?,abba yayi dariya yace"duk soyayyar yqnzu shirme ce,ina soyayyar take zuwa?daga anyi auren ta mutu sai ki rasa ranar da tayi musu,wani auren hadin ba yafi qarko da albarka ba,ga auremmu ya isheki misali sai da aka kawo ki muka ga juna ko kin manta,gashinan haryau shekara kusan talatin da biyar ba fada bare yaji"ya dan kalleta ta sigar tsokana yace"nasan dai abu daya kikayimin kin shanye ni na kasa qaro miki abokiyar zama"kunya ta kamata tadan rufe fuskarta da tafin hannunta🙈tana cewa"kai alhaji"shina dariyar yayi😄 yana bude mata fuska yace"ai gaskiya ne"
Misalin goma na safiyar washegarin ranar alh salim da kansa ya sanya aliyu a gaba ya tuqoshi zuwa gidan aminin nasa alhj abbas don kawo sadakinsa,aliyun yayi kyau abinsa cikin shadda gezna dinkin tazarce farace qal sai maiqo take,ya saye idanunsa cikin farin glass wanda bai hanaka tozali da farar qwayar idanunsa,takalminsa baqi ne na kamfanin batozi sai baqar hula duk da bai sanya ta ba tana riqe ne ahannunsa,kana nazaratar fuskarsa zaka karanci damuwa a tattatare da shi,sam alh salim bai bi ta kansa ba don yasan kwanan zancan,ya sani cewa gata ne yake son ya yiwa aliyun wanda ko bayan ransa zaiji dadinsa.
A nutse yake murza sitiyarin motar har suka iso cikin gidan,alhj abbas da kansa ya fito yayi ma abokin nasa iso zuwa cikin gidan bayan sun gaisa da Aliyu suka barshi cikin motar,ya dan kwantar da kujerar motar yayi rigingine yana kallon yanayin ginin gidan,
Alhj salim ya fiddo da daurin bandir na dari biuar biyar rafa daya ya ajjiye a gaban alhj abbas yace "ga sadakin aliyu ga 'yata fadila"alhj abbas yace "amma ai a yimin kara ko ni na biya ai"alhj salim yace"ni da kai ai duka dayane babu komai wlh"alhj abbas yace"Allah to ya yiwa auren albarka yasa ya zamo farinciki a gurimmu da gun yaran gaba daya""ameen"ya amsa masa"auren zai kama nan da sati shida dai dai lokacin da zasu kammala attachment dinsu"alhj salim yace"anya ba'ayi gaggawa ba?""wani irin gaggawa kuma me zasu zauna su yimin agidan ?"to shikenan abbas Allah yasa ayi a sa'a""amin dama ban sanar da yarinyar ba niyyata dama yau ta sani amma munyi zancan da mahaifiyarta,to tunda ga sadakinta ga kuma mijin sai a kirata tasan komai""to ba laifi"inji alh salim
Tana ysaka da baccinta😴 taji ana dukan saman qafafunta,ta daga kanta idanunta cime da bacci tana kallon muhammad da ya tashetan cikin jin haushin tashin nata da yayi tace masa"meye?,ba nasha gaya maka idan ina bacci ka daina damuna ba"ya hade hannayansa 🙏🏻yace"am sorry anty,abba ne ke kiranki""abba kuma?😳"ta ta tambayeshi cike da tsoro saboda ta tuna agender su,ya gyada mata kai cike da tabbatarwa,tace jeka ina zuwa"tuni ragowar baccin da take ji ya gudu daga idanunta,ta dirgo daga gadon ta shige toilet ta wanke fuskarta tayi brush sannan ta dawo cikin dakin ta daura zani kan rigar baccin ta ta fesa turare sannan ta zira zumbulelen hijabinta mai hannu,a falo taci karo da umminta tana saka turaren wuta,ta gaidata sannan fuskarta kamar mai shirin rushewa da kuka😟 tace"ummi wai abba ke kirana"ta kalleta tace"to kije mana na ganshi da alhj salim"gabanta ya qara faduwa ta juya ta bar falon
A salube tayi sallama a sitting room din,dukkansu suka amsa mata,ta samu gefan kujera ta gaida uncle abba(hka suke ce masa)kasancewar sun gaisa da abbanta tunda asuba,uncle abba ya amsa yana mai qara nazaratar nutsuwa da ladabinta,abbanta ya kalleta yace"fadila ina son ki bani aron nutsuwa da hankalinki "tace"to abba😔""kin sani cewa shekarunki sun isa ace kina dakin mijinki tunda an aurar ma da wadanda basu kaiku shekaru ba,sannan na baki dama ki fito da wanda kikeso kamar yadda qanwarki ta fiti da shi amma har yanzu baki cemin komai ba,na qyaleki har lokacin da nabaki ya qare ban tanka miki ba duk da cewa ina da iko in zaba muku miji amma na baki damarki "ta gayada kai "hakane abba yace"fadila"ta amsa "na'am""abbanki ya nemawa yayanki aurenki kuma na bashi"wata mummunar faduwar gaba ce ta risketa tamakar an daddaure jijiyoyin jikinta taji,hakan yasa ta kasa dago idanunta ta kalli kowa bare su fahimcin halin da ta shiga,ya dora da cewa "yanzu haka ga sadakinki a hannuna"jin hakan yasa ta qarasa rikicewa sauran dauriyarta tuni tayi qaura,addu'o'i ne barakatai suka dinga zuwa bakinta tanayinsu cikin zuciyarta,shikenan na rasa aliyuna?shikenan zuciyata ta rasa muradinta?shikenan mafarkina ya zama hasashe?,abinda take jujjuyawa kenan kawai a zuciyarta,duk maganganun abba ba wanda ta ji ko ta fahimta sai maganarsa ta qarshe wadda sauran qiris ta sa numfashinta ya dauke"kije kuga juna yana falon waje duk da shekarun baya kun sanshi amma saboda tsawon shekarun zaki iya mantashi ya kwana biyu baya qasar"uncle abba ne yayi saurin cewa"a'a saurara✋🏻ina da magana ke fadila gayamin gaskiya idan bakiso kina da wanda kike so"tabbasa da zata iya da ta fayyace musu sirrin dake zuciyarta ko zasu tausaya mata su bar zuciyarta taji ma da masifar da take ciki,amma ko kusa batajin zata iya kunyata abbanta,bayan ya isa da ita yana da iko da ita fiye da yadda take da iko da kanta yayi mata komai a rayuwa ya bata dama masu yawa a rayuwa irin wadda kowane mutum ke son samu,duk ma a ture wannan gefe baza iya daga iso ta budi bakinta tace da aminin mahaifinta wanda yake tamkar uba a gareta cewa batason dansa jininsa ba,hakan yasa tayi saurin girgiza kai tace"ko daya abba na gode da zabin da kukayimin,Allah ya saka muku da alkhairi"ita kanta ta jinjinawa kanta kan namijin qoqarin da tayi na furta haka,uncle abba har zuciyarsa yaji dafi matuqa tare da sake gode ma allah da zata zamo daya dqga cikin ahalin gidansa,albarka suka sa mata sannan abbanta ya umarceta taje su gana
Takai kusan minti biyar a qofar sitting room din ta kasa shiga,gaba daya a rude take zuciyarta a cunkushe take,daga qarshe taga tsayuwar batada wani amfani don haka ta tattaro dukka nutsuwarta da dauriyarta ta kutsa kai hade da sallama kanta a qasa😔 ta lalubi kujera daya ta zauna cikin fargabar wa zata daga kai ta gani,muryar da taji ta masa mata ita ta razanata da sauri ta dago kai ta gani ahin da gaske ne ko kunnuwanta da zuciyarta ke yaudararta yadda suka saba?idanunsu suka hadu da juna👀 wanda hakan ya tabbatar mata da tsammaninta,ba qaramar razana tayi ba duk da bata nuna hakan ba,A.s mai tama Aliyyun uncle Abba?,take ta jera sunayan a zuciyarta,komai tsaya mata cak yayi,tunaninta ya kasa gaba ya kasa baya,shiru daki ya dauka ba wanda ya tankawa dan uwansa wanda hakan ya sanya fargabarta daduwa,bata kuma sake kallonsa ba bare taga a wane irin yanayi yake ciki ba,sun jima a haka sannan ta jiyo alamar miqewarsa,har ya kai bakin qofa yayi taku uku ya dawo da baya,kallon nan nasa da ta fari gani a qwayar idonsa ta kuma tsaneshi shi yayi mata sama da qasa sannan yace cikin izza da qasaita"ban iya qarya ba kuma bazan fara taba saboda ke,bazan iya tafiya ban amayar da binda nake ji cikin zuciyata ba,bakimin ba baki dace dani ba,baki ma dace da tsarin rayuwata ba,ke da kanki shaidace ce idan dq zaki iyq yiwa kanki adalci bamu dace da juna ba,baki ma da zubi da tsarin da nake so gun mace,idan banda tsaurin ido ma irin naki taya zaki hada kanki da ni?kinga nayi kala da ke?gaskiya kin cuceni,god forbid ki zama matata,kada kuma ki soma yaudarar kanki ta hanyar zato ko tsammanin nan gaba zan iya sonki harki cuci kanki ki aure ni,wannan maganan daga cikin zuciyata direct take fitowa
Wani mugun takaici da baqinciki ne lokaci guda ya rufeta,tunda take babu wani da namiji da ya taba mata munanan furuci makamanta wannan,ta tuna uawan samarin da ke kara kaina a kanta,samari masu ji da kudi kyau nasaba isa da qasaita,ba wanda ta bawa dama a cikin su,wasunsu dama suke so ta basu koda ta friendship ne amma basu samu ba,samari da dama sun sha kuka a gabanta kan ta mallaka musu zuciyarta,amma yau wani daya daga cikin jinsin maza ke gaya mata wadannan kalaman,ji take a rqntq matuqar ta barshi ya tafi haka ba ta da ta mayar masa da martani ba wanda zai dade yana cizon zuciyarsa ba to ba shakka tayi faduwar baqar tasa"hey🙋🏻"tace da shi sanda ya sanya kai zai gice daga falon,ta miqe tsaye ta yi masa kallon sama da qasa ta yatsina fuska😏 ta tofar yawu a gefanta sannan tace"see you wane mashahurin maqaryacin ne ya gaya maka ina maraba da kai da zaka zo kanata soki burutsu,ni dinma ba yimin kayi ba don baka wuce dan aiken gidana ba a tsarina,amma ni nasan darajar dan adam banga a gidammu ana tozartashi ba kuma na iya darajatta zancan magabata na shi yasa ban tozarta mutumin da mahaifina ya zabamin ba,idan banda qaddar ina budurwa sabuwa dal a leda mai zanyi da bazawari ragowar wata..........
Wata iriyar wafta ya kawowa bakinta wanda ta tabbatr da ya sameta sai lebunanta sun fashe,da gudu ta bude daya qofar falon da zata kaita cikin gida ta baya ta shige ta bankowa aliyu qofar ta batshi tsaye zuciyarsa kamar zata fito saboda fushi,ya ga alamar akwai rainin wayo tattare da yarinyar,yayi qwafa cike da zafin zuciya ya fice,kai tsaye daķinta ta nufa ta kulle qofarta gam tayi zaman dirshan saman carpet dinta,wani irin kuka ta saki😭tayi qasa da kanta😪,ta rasa me zayayi farinciki ne ya kamaceta ko baqinciki?ta jima a zaune tana kukan tate da tambyat kanta da kanta shin dama baqinciki da farinciki na haduwa lokaći guda cikin zuciyar bil'adama?yau kam ta fahimci hakan na faruwa tunda gashi yau ta tsinci kanta a ciki
Aliyyunta mafarkinta na kullum?burin zuciyarta muradinta yau shine zai zama mijin aurenta babban burinta kenan dama anan duniya,sai dai kash yazo mata ta wata iriyar fuska da sigar da bata tsammatar mata ba,baya sonta baya qaunarta abin har ya kai tsananin da bazai iya boye qinta a zuciyarsa ba harsai da ya tsaya a gabanta ya fesar mata,baya ga haka ba ita kafaice zata zama mallàkinsa ba?zata yi sharing aliyunta da wata?ga ahi har waya ma ta rigata samunshi(maman iftihal)
Da qyar ta iya janye jikinta ta gada saman gadonta,ba abinda ke mata amsa kuwwa akunnenta irin kalaman aliyu,kafin azahar zazzafan zazzabi ya rufeta,sau biyu farida na shigowa dubata tana ganinta a duqunqune tayi tsammanin bacci take,a shigowarta ta uku ne tace"kai yaya fadila wani irin bacci ne haka tun ten o'clock har one thirty?"tasa hannayenta ta janye bargon tana fafin"ba sanyi ake ba ba komai ba kuma kin.......
maganar ta maqale mata sanda idonta yakai kan fadila ta zaro ido😳 tana cewa"kinga idonki kuwa?"ta juyar da idonta daya side din sannan tace"kaina ke ciwo"
0 Comments