Wayasan gobe hausa novels

 WA YASAN GOBE?


▶3


SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA


🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Lotion kawai ta shafa bayan ta fito ta feshe jikinta da body spray ta lalubi rigar bacci doguwa har qaurinta ta zura don bacci take da muradin yi, ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta gabatar da sallar isha'i, ta dora da shafa'i da wutiri, bayan ta shafa addu'o'inta tabi lafiyar gado, a maimakon bacci yazo mata sai tunani ya mamaye gurbinsa, ba zato ta tsinci kanta da zubarwa kanta da kanta hawaye na tsananin tausayin kanta, a cikin jikinta da zuciyarta take jin ta shiga halin tsaka mai wuya, zuciyarta na bulayi da lalube cikin duhun son wanda bai ma san tana yi ba, farida ta shigo dakin hade da sallama hakan ya sanyata saka hannu tana goge hawayen cikin dabara don bata son faridan ta gani, faridan tadan kalleta jikinta yaso ya bata tamkar yar uwarta na cikin damuwa, don haka jikinta sai ya danyi sanyi ta shigo ne da niyyar tsokana don flask guda ummi ta ciko da abinci tace kada ta sauko da shi sai ta cinye Farida ta ajjiye flask din a gefan gadon ta janyo dressing chair ta zauna tana fuskantar fadilan tace"sister lafiya naga kamar fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa? ,ta qaqalo murmushi sannan tace"ba abunda ke damuna just na gajine fitar nan da nayi"farida ta girgiza kai ba don ta yarda ba tace"ok,to ga abincin ki nan ,ummi tace " kada ki sauko mata da shi sai kin cinye tana daga kwancen ta zubawa flask din ido tace"har gabana ya fadi wlh, ina zan kai wannan abincin? ,farida ta qyalqyale da dariya tace"ni dai yar aikece kuma na isar da saqo,qafafunta tayi saman tiles din daya mamaye da qaton dakin nata

Ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta zari flask din, farida ta kalleta tace " a'ah ina zuwa? "Ba tare data kalleta ba ta juya tana shirin fita sannan tace"jirani ina zuwa"farida ta bita da kallo tana dariya ciki ciki ,ta qofar baya fadila ta fita ta bulla bakin get din gidan,kai tsaye ta nufi gun idi mai gadinsu, mutuminta ne dama da hangota kuwa ya miqe yana cewa " uwar dakina"miqa masa flask din tayi tace"yi sauri ka juye idi"cikin qanqanin lokaci kuwa ya juye abincin ya bata flask din yana zuba godiya Ta tarar da fadila na waya da alama da saurayinta take, ta koma gefan gadon ta zauna tana kallon faridan har ta kammala tsaki fadilan tayi, farida tayi murmushi tana kallon flask din da fadila ta dawo dashi don tasan kwanan zancan, bata son idan zatayi waya tayi mata a dakinta,fadila ta harareta tace"bana gaya miki ki daina shigomin daki idan zaki shirmen wayarki ba? ,tace tana gyara kwanciyarta akan sofa qwaya daya dake dakin " sorry anty na"tana dan murmushi tace kiyi haquri

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tun bakwai na safe take a kitchen dama haka al'adarta take, idan bata da lecture to Itace mai shirya musu breakfast haka da rana ko da daddare,girki yana daya daga cikin hobby dinta hakan ya sanya ta zama gwana ta fannin abubuwan ci da na sha,

Awa daya da rabi ta kammala komai ta koma dakinta tayi wanka ta shirya kasancewar tara da rabi tana da lacture,dakin ummi ta shiga bata nan sai muhammad ta tarar yana kan gadonta yana bacci,dala masa duka tayi tace"tashi malalacin banza eight thirty amma kana bacci ina school din?"cikin magagin bacci yake murza ido yace"wlh nayi wanka bacci ne ya daukeni"tace"oya tashi ka shirya idan zan wuce na sauke ka na baka eight minute"da sauri kuwa ya duro daga kan gadon ya shige toilet

Bangaren abbansu ta wuce tare da diba masa breakfast dinsa ta tafi masa da shi,yana zaune kan kafet din falon hannunsa dauke da jaridar daily trust,haka yake a al'adarsa bayan ya dawo a masallaci yakan yi azkar da tilawar qur'ani idan gari ya dan sha kuma sai ya karanta jarida kafin ya fita aiki,fadila ta shigo da sallama, ya masa yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,ta dire kayan abincin ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana fadada fara'ar shi yace"sannu fadila da qoqari hala yauma anada da lacture din safen"kanta a sunkuye tana qoqarin hada masa kunun shinkafa da yasha madara tace"eh Abba",ummi ce ta fito daga bedroom din Abban hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata tana qoqarin tashi tace"abba zan tafi"ya dubeta sannan yace"ai banga kin ci komai ba haka zaki tafi?""abba zan karya a capteria idan na..........

Ummi tayi saurin katse ta da cewa"yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take ba farida ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na rasa meke damunki anya lafiyarki qalau kuwa?",abban yayi murmushi yana dakatar da ita"dakata umminsu,fadila lafiyar ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta take"ya juya ga fadila yana tura mata cup din da ta hada masa kunun yace"maza zauna kici wani abu kada ki qara bata ran umminki kinji ko?"tamkar zata sa kuka😟 ta zauna tana cewa"to abba"yaci gaba da cewa"gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci mata,abban yayi murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani😣

Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna mota muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu ✋🏻hadi da cewa kaga malam bafa aku na dauko ba🐔idan kuma kai aku ne ka gayan"ya qyalqyale da dariya😂 yace"anty ke dai ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke burgeni ke halin ya ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace"ai da itan da kai duk zamuce ta tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai na saukeka anan" take ya rufawa kansa asiri yayi shiru🤐

Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta samu sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking din motar ta daidai ba ta nufi ajin cikin sauri

Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka da fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama'a sosai yafi kusa da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke shuke ita kuwa ma'abociyar son tsirrai ce

[8/8, 3:24 PM] LOADING......


gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take iya gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai tsintsiyar hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne ke biye da shi riqe da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga kanshi👀,hakanan gabanta yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi wa inna ilaihir raji'un"har ya danyi nesa da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta kamar ta tsinke ta fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana tsammanin jikinsa ne ya bashi ana kallonsa👀,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo jakarta ta zuge ta fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a gunbtana hutawa sai sannan ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da takalminta agogo da jakar hannu duk yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin atamfa takai aka mata dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba haka Allah ya bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada mata kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata class mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta qaraso,"fadila abbas yaufa kinyi tabargaza"abinda ta soma cewa kenan,fadila tace"kamar ya fa?"tana dubanta tace kinyi wrong parking kin toshewa A.s mai tama hanya"ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace"waye haka kika bi kika rude?'binta ta zaro ido😳 tace"kar dai kice min baki san a.s mai tama ba,hadadden guy din da duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa"fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"na gode"taci gaba da mayar da kayanta jaka

Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya👀,a tsammaninta idanunta ke mata gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da irin kallon qasqancin da yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi motarta ta bude,ta zauna a seat din tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana mata irin kallon dazun,cikin qasaita taji yace"baki da ladabin bada haquri ga wanda kika aikatawa laifi?"duk da yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta kwanta a zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta"duk da dumbin qaunar da nakeji taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na 'ya'ya mata,ta dauke kanta sannan tace"ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil'adama ba"ya saki murfin motar hadi da watsa hannayensa yace"ok,ba laifi"ya saki murfin motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi key din tasa motar daga hannun wanda suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya take motar ya kurda ya matse motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya gogeta,ya kashe motar ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa ya danyi tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun

Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number farida ta kirata"hello farida kin shigo school?"tace"eh ya akayi?""kizo ina parking space ki daukeni mu wuce"farida tace"me ya sami motar ki?""kinga idan zaki zo kawai kizo malama""ok sister gani nan"

Cikin 'yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta gabansa ta shige ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan motar,wata yar qaramar mota ce tayi parking a gabansa kusan tare suka shige motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta sakar masa tsaki hadi da murguda baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri tacewa farida"yi sauri ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun


Muje zuwa

[10/16, 12:21 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺


Wa yasan gobe?


Safiya Abdullahi musa huguma


🌺🌺🌺🌺🌺🌺


▶4⃣


Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji farida,"sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki tace"wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana ganinsu ta saki fara'a😊 cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar tamu ce"suka saki dariya😀dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera"anty hafiza tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?"fadila ta dan murmusa 😊tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji""na miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba""tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?😳""fada mata dai anty😏"cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon

Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,"to me A.S mai tama take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata😊 sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan tabe baki tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya"da sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love😜"fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa"kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta sanya ma question mark😏",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka wuni har 'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka.

to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar.

cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki"banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida😜"bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya 😂don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru

A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma'aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya zauna

sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran

Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido👀 saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa"da wa za muyi hirar ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi👀,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa😏,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan


Ku biyoni muje......


Post a Comment

0 Comments