Wasu daga cikin dalilan da suka haifar da tsadar rayuwa a Najeriya



 Al'ummar Najeriya na kokawa da yadda al'amura suka sauya musamman yadda rayuwa ta sauya saboda tsadarta.

Tuni dai farashin kayan masarufi dama sauran kayayyakin amfanin yau ya yi tashin goron zabi abin da ya sa jama'a da dama suka shiga cikin kuncin rayuwa.

A yanzu haka rahotanni sun nuna cewa akwai mutanen da abin da zasu kai bakinsu na salati ma a kullum na matukar yi musu wahala.

Tun dai bayan rufe iyakokin Najeriya da gwamnati tayi aka fara samun tashin farashin kayayakin abinci musamman shinkafa da dai makamantansu.

Masana dai na danganta yanayin da aka shiga yanzu a Najeriya da wasu abubuwa da suka hadar da:

  • Karin wutar Lantarki da Man fetur
  • Cutar Korona
  • Dokokin da gwamnati ke yi a kan kudi a baya-bayan nan.
  • Ambaliyar Ruwa.
  • Tsadar takin zamani
  • Karin Haraji

Wadannan abubuwa da aka lissafo su ake dangantawa da wasu daga cikin abubuwa da suka haddasa tsadar rayuwa da ma tashin farashin kayayyaki a Najeriya.

To sai dai kuma a nata bangaren gwamnatin Najeriyar ta bayar da bayanai a kan abubuwan da take gani sun haddasa tsadar rayuwa da kuma tashin farashin kayayyaki.

  • Batun taki: Karayar tattalin arziki da annobar cutar korona ta jawo ga kasashe na nesa da kusa ya shafi shigo da ma'adinai da ake amfani da su wajen sarrafa taki.

Hakan ya sa taki ya yi tsada a noman rani har zuwa yanzu, ta yadda wadansu sun noma shinkafa sun rasa takin saka mata dole ta sa suka saida wa makiyaya shinkafar.

  • Mugunta tsakanin mutane: Akwai 'yan kasashen waje da ake gani suna yi. ana samun masu ayen abinci suna boyewa, sai dai gwamnati na daukar mataki kan masu irin haka
  • Kafa masana'antun shinkafa: An samu ci gaba wajen kafa masana'antun sarrafa shinkafa da yawa a Najeriya. Kamar a Kano akwai wajen 18 wanda kowanne a ciki yana sarrafa shinkafa daga tan 180 zuwa 400 a kowace rana. Suna daukar ma'aikata da basu gaza 200 ba.

Karin farashin man fetur da na hasken wutar lantarkin da aka yi a Najeriya sun sake jefa 'yan kasar a mawuyacin hali.

Hakan na faruwa ne a yayin da jama'a ke cikin karin matsin tattalin arziki sakamakon annobar korona wacce ta tilasta wa duniya zama cikin dokar kulle.

To sai dai kuma wasu manoma sun ce idan har aka yi girbi kaka samu amfanin gona to akwai yiwuwar cewa farashin kayan abinci zai iya saukowa.

Post a Comment

0 Comments