TA AUREN MIJI*
🌰🌰🌰🌰🌰🌰
🍠🍠🍠🍠🍠🍠
*STORY WRITTEN*
*BY*
*UMMU SULAIMU*
*REAL SALMA FAROUQ*
*Nagode da adu'arku fans ta auren miji kuma naji dadi allah ya dawo dani lfy godiyata gareku bata yankewa I love u all.*
*Dedicated xeyyneb moxy ina tayaki murnar kammala novel dinki allah ya kara basira xee Zeey"*
*PAGE 7 TO 8*
Binta yai da kallo daga bisani ya haura samansa ya dau towel ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwa sannan ya fito daure da alwala cikin sauri ya shirya cikin kananan kaya sannan ya gabatar da sallah bayan ya idar ya sauka kasa ya nufi harabar gidan ya bude mota ya dauko plas din abinci da mama taba Humaira ta rakoshi dashi.
Yana shiga parlour ya taddata lokacin ta sakko daga samanta Aiko ta kame kugu ta bude baki ta fara magana" tab gaskiya anacin amanata bayan ha' inta ta da akeyi ake rabamin kulawa da tsohuwa kullum sai an biya kan adawomin gida takai ta kawo har abinci ake baka me barbade gwarama da ban dafaba bare abarni da shi........tasss kakeji ya dauketa da mari.
Waro ido 😳tayi Shaifu ni ka mara akan nayi magana akan zalincin da kakemin ba shiri tai shiru sabo da kamannin Shaifu da taga ya canja lokaci guda idanunsa sun kada sunyi jajur ga jijiyoyin Kansa da suka fara fitowa sukai rudu-rudu lalle ran maza ya baci.
"Ramla nagaji da cin fuskar da cin kashin da kikemin tunda abin har yabar kaina ya tsallaka kan mahaifiyar da ta kawo ni duniya toh kisani muddin zaki rika gigin sako mahaifiyata a al" amarina dake toh lalle kina gabda rasa igiyar auren don dama nagaji da aurenki.
Zan iyayin komai muddin za'a tabamin uwa kisani" tunda nayi aure ba kwanciyar hankali na auro jaraba mara tarbiyya.
Ganin yanayinsa don tasan ba haka yakeba komai zatayi masa baya taba kai hannu jikinta da zummar duka hasalima wani sa'in intana sababinta baya kulata kyaleta yake ko ya barmata hurin amma tunda har ya iya marinta yau to lalle zai iyai mata komai don haka ta juya ta nufi samanta tana sharar kwalla " wlhy indai sunana Ramla to lalle zakayi danasanin marina na gayama.
Duk abinda zakiyi allah ya fiki donshi yayoni ya yoki ke din me ya karasa maganar ya haura samansa ransa na kuna abincin ya bude ya faraci yayimai dadi sosai don ko ba shakka wannan girkin Humaira ta kware wajen iya girki Yana kammalawa ya nufi masallaci don yaji ana kiran isha.
Da daddare kasa bacci yayi bai damu da bacin ran da Ramla ta kunsa masaba don yasaba da wannan halin nata tunanin yanda yakasance da Humaira ne ya dameshi tun bama boobs dinta manya masu daukar ido da ya tunaba.
*Kudan karanta wannan kan muhade gobe*
*Ummusulaimu*✏[6/21, 10:19 PM] Fatima Zarah: 📝💋🍠🍠🍠🍠
*TA AUREN MIJI*
🌰🌰🌰🌰🌰🌰
🍠🍠🍠🍠🍠🍠
*STORY WRITTEN*
*BY*
*UMMU SULAIMU*
*REAL SALMA FAROUQ*
*PAGE 9 TO 10*
Tare da sulbi da sheki juyi yayi ya dauki pillow ya rungume tunanin yadda za'ai Mama ta amince da bukatarsa na bashi Humaira yake yasan ko giyar wake yasha yanxu baxai iya tunkararta da wannan maganarba.
*Asalinsu*
Iyayensu Mazauna garin kanone tun iyayensu gabanin su rasu mahaifin Shaifu wane ga mahaufin Humaira uwa daya uba daya runkwanta Humaira ya dawo hannun Iyayen Shaifu ne tunda allah yaiwa Mahaifiyar Humaira rasuwa wato Amina" Amina ta ruga maihaifin Humaira rasuwa mai suna Aliyu "tun lokacin da ta duro duniya allah yai mata cikawa don haka rukon Humaira ya dawo hannun Mama Maryam mahaifiyar Shaifu lokacin tana da tsohon cikin Khadija don haka ta dunga shayar da ita da madara kamin daga baya shima mahaifin Humaira Alhj Aliyu shima ya rasu sakamakon matsanan cin ciwon ciki daya kamashi da daddare da safe aka wayi gari ya rasu.
Haka Humaira suka taso da Khadija tamkar " yan biyo don suna mutukar kama komai nasu tare sukeyi tare suke zuwa makaranta insun dawo yayansu Shaifu yai musu lesson wataran kuma ammar ya chanjeshi don haka baxaka taba cewa ba mamace ta haifesu dukaba.
Sosai suke rayuwarsu cikin jin dadi har zuwa lokacin da Shaifu ya hada degree dinsa toh alokacin ne suka hadu da Ramla har matsananciyar soyayya ta kullu tsakaninsu lokacinne ya bujirowa da Alhj Ibrahim wato Mahaifinsa kan cewa yanason ya Auri Ramla shikuma a lokacin ya nuna rashin amincewar da don kowa yasan gidansu wajen rashin tarbiyya da rashin sanin girman nagaba dasu.
Sam Mama ma taki Goya masa baya don sunaso dansu ya sama musu zuri'a ta gari " amma so yariga ya rufewa Shaifu ido yakasa gane me ake hango masa zuwa lokacin sun shaku da Humaira sosai don yana ware lokaci yai wasa da kannensa sannan insunyi lefima yana cire wasa ya hukuntasu.
Ita kuma Humaira hakanne yasa take ganin kamar hakan sonta yake sbd yanda yake zagewa yayi wasa dasu tare da hira da son jin damuwarsu.
Wani lokaci Alhj Ibrahim shima ya tashi da matsananin cin ciwon ciki tamkar irin yanda dan uwansa ya tsinci kansa wancan lokacin hakan yasa duk suka karaya suka fidda rai ganin yanda yake jin jiki cikin wannan yanayin yace " yana da kudirin hada auren Aisha da Shaifu tun bayauba don haka bayason ya mutu vatare da ya cika burinsa ba kamar ya ganin ciwonnan bana tashi bane yanaji a jikinsa tamkar zaibi dan uwansa ne hakan yasa jikin kowa yayi sanyi "Shaifu ko sosai yaji baiji dadiba don Ramla itace zabinsa.
Haka yasa Mama ta kira masa Humaira ya tambayeta ko tanason Shaifu tako amsa masa da eh sbd da ita batasan Shaifu ya tunkari iyayensu da maganar wataba kuma a lokacin ta matukar jin sonsa a ranta.
Washe garin ranar a daddafe yaje ya samu liman suka yanke hukunci dashi cewa gobe azo da komai sai a daura auren za'a sanar da mutane shima ya shaidama " yan uwansa yace" bashida matsalar hakan don ya shidamusu sunanan zuwa goben washe gari kuwa aka daura Aure Humaira na farin ciki allah ya cika mata burinta na auren yayanta wanda take mutukarso.
Shaifu yini yayi zuciyarsa ba -Ba abinda yakeso kamar ya auri Ramla " Ramla batasan da yayi aureba don dama ita a Hostel take zaune ba a gidansu ba hakanne yasa ya danji sanyi" daren ranar allah ya yiwa Alhj Ibarahim rasuwa sunji mutuwar sosai don sunyi babban rashi mutum na gari ga kyauta da son zumunci gida ya hargitse sai koke koke-koke kakeji da adi'oin samun rahama.
Bayan anyi Arba'in Mama ta nemi shawarar Shaifu kan yaza'ayi da maganar Humaira ya kamata ace an kai maka ita gidanka fafur yaki yace" shi abatta anan ta kare makaranta kamin nan ankarasa gyare-gyare.
Tun Humaira tana damuwa da taga kamar bai damu da itaba ta share shi ta maida hankali kan karasa karatunta don dan wasan da yake dasuma ya daina " Mama ko ta dukufa wajen gyara "yarta.
Bayan shekara daya Ramla ta dage ta tubure dole saiya turo tunda sungama karatu itafa ta gaji da yawo da hankali aure dakeso suyi.
Yazo yasamu Mama da maganar tako ki amince tace" zaiyi da auren Humaira "'yace shidai amincewarta yakeso shidai duk zai iya rikesu.
Tace" Shaifu kamar yanda Babanka bai aminceba nima zan amince ka auri wata ka cuci " yar mutaneba.
Ganin taki amincewa yaje yasamu kawunsa wan Mama ya gaya masa yace" karya damu zaizo ya sameta washe garin ranar Yoko zo" daman Maman na ganinshi tasha jinin jikinta don tason in badon girman abuba bazai zoba saidai yamata waya koya aiko tazo .
Bayqn da suka gama gaisawa ya gaya mata bukatarsa yace" inba sotake sufada wata halakarba ta amince tunda sunason junansu koma shima yai musu biyayya tunda ya auri zabinsu in allah yayi tana hannunsa sai allah ya shiryeta " haka dai mama ta amince ba son rantaba amma da sharadin Humaira ko tagama makaranta bazata zauna gidansaba.
Humaira da taji labarin ba karamin rashin da dadi tajiba amma haka Mama taita lallabata da bata hakurin da yardar allah zai karkato da hankalinsa ya gane gaskiyar abinda suke guje masa ta kara hakuri kadan tana kasa adu'a.
Cikin kankanin lokaci aka sha shagalin baki aka kai amarya daren farko Shaifu yasamu Ramla ba'a cikikkiyar budurwaba hakan yasa suka samu sabani" daga baya ya hakura ya rufa mata asiri suka dai-daita cikin wani lokaci kankani tafara sauya wasu sababbin halaye bata kulawa dashi da yayi magana saitayo kansa ga yawan fita da kawo kawayen banza ga rashin girmama "yan uwanshi cikin wannan yanayin yafara gano abinda ake gujemasa kuma yarasa gane wancan lokacin abinda yarufe masa ido ya kasa gano illar hakan.
*Continues*
Juyi ya karayi ba mifita hakan ya sanya ya mike dan dauro alwala ya kai kukansa ga allah.
Ramla tana shiga bedroom dinta ta latsa waya one ring aka dauka nan ko ta kara fashewa da kuka " Moxy kinga abinda Shaifu yai min yqu harda daga hannu ya mareni moxy har jibgata fa yayi kamar ya samu jaka" daga daya bangaren aka anshe "kutumelesi lalle wannan dan iskan Daughter yaka na aura masa " ninarasa yanda yanyi boka mai rankwal-kwal yakasa aiki a kansu wai sun jiku da ayar allah shi baya zuwa inda ayar allah take sai inda aka cire imani kuma nasan wannan munafukar uwarce sula.
Amma duk da haka karki saurara masa kicigaba da surfa masa masifa da bala"i "ya kudin danace kisamomin kinsamo min "';wlhy moxy da key dinsa yake fita dan iskan.
Yakike abu saikace ba mace ba kisan dabarar da zakiyu" toni moxy yazanyi nifa basan x nake da shiba wlhy don inya fara baya sassauta kuma muna kammalawa yake dauro alwala kobeyi wankaba bare boka yai aikinsa a lokacin ni nafison x da mai gadin gidannan "to shikenan kiyi aiki da shawarar da nabaki dazu.
To moxy ta karasa maganar tana sheshshekar kuka " kiyi hkr nace ta fada tana datse wayar *(Wa'iyazibillah wacce uwace zataso jefa "yarta cikin wannan hali)*.
*Ummusulaimu✏*
[6/21, 10:22 PM] Fatima Zarah: 📝💋🍠🍠🍠🍠
*TA AUREN MIJI*
🌰🌰🌰🌰🌰🌰
🍠🍠🍠🍠🍠🍠
*STORY WRITTEN*
*BY*
*UMMU SULAIMU*
*REAL SALMA FAROUQ*
*Dedicated by Fateen Sabi'u*
*Kuyi hakuri da abinda zakuji gareni fans kunsan ummusulaimu bata typing watan Azumi da Ramadan yazo nake dakatar da typing ko kwana2 da baku jiniba ina azumine don allah kuyimin uziri na dakatar da typing daga wannan page din sai bayan sallah saboda gudanar abubuwa da ibada cikin nutsuwa allah yasa ibadarmu karbabbiyace tare da bamu ni'imomin wannan wata da albarkatunsa kasa muga garkonsa muga karshensa sai mun hadu cikin goron sallah😄💃🏻 kada kumantafa ummusulaimu takuce ana tarefa🤝🏼😉*.
*PAGE 11 TO 12*
Kwana uku da zuwan Shaifu gidan mama bai kara zuwaba takira wayarsa har tagaji bata shiga sai ace a kashe hakan ba karamin Tayar da hankalin mama yayiba.
Sosai Humaira ma ta damu amma batasan Mama ta gane hakan yasata boyewa amma duk dare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu take kwana tana bukatar mijinta sosai amma sai dai ba hali sosai take son kara haduwarsu yai mata irin abun rannan mai dadi da kautar da tunani.
A kwana na hudune Mama ta yanke hukunci zuwa gidan don abokinsa Hafiz yazo ya shidawa Mama yaga Saifu baya zuwa aiki ya kirashi a waya sai ace a kashe ya taka yaje gidan matarsa ta surfa masa zagi harda ce masa munafiki to bansan inda yakeba hakan ya kara firgita Mama tace Humaira hado kayanki a trolley mu tafi yau zan kawo karshen Abu daman gyalewa kawai nake amma nima inason dana haifarsa nayi.
Jikin Humaira a salube ta shiga ta fara hado kaya Khadija na tayata tanai mata dariya " sai ta sheke da dariya saitace " yau su wa'e za'asha Amarci " Humaira batace komaiba banda harara da take banka mata.
Shaifu tun daren daya dawo wani azababben ciwon kai ya rufeshi daren ranar bai samu ya rintsaba gari na wayewa kwa ya kira likitanshi yazo ya dubashi tare da bashi magunguna gami da bashi shawarar ragewa kanshi damuwa gudun kamuwa da wata larurar don damuwace ta haddasa masa hakan "yinin ranar a sashinsa yayi shi don yanda yake jin kansa na sara masa kashe wayarsa yayi don bayason damuwa tare da sawa kofarsa key.
Kusan kwanansa uku kenan bai samun zuwa ko ina a daki yake yini bayajin sha'awar komai don haka inyaji yinwa yake bude fridge ya dauko yougot ya sha inyaji ya isheshi ya shiga kitchen din samansa yasamawa Kansa tea.
Ramla sam batayi tunanin zuwa part dinsa ba bare tasan halin da yake ciki rashin fitowarsa ma yabata damar cin karenta ba babbaka.
Yau ya danji sauki sosai hakan yasa yau yake masifar son ganin Humaira tare da son zuwa gaida Mama don yason kwana 2 da batajishi hankalinta zai tashi sosai mikewa yayi ya janyo wayarsa ya kunna ya dauki towel yana shirin shiga toilet yaji wayarsa ta fara ring tamkar ana jira ya kunna.
Yana duba screen din Hafiz ya bayyana a kai " kai Abokina ina ka shiga ne nakira wayarka harna gaji nazo gidanka matarka tace " batasan inda kakeba ga baka zuwa office haba ina kashiga.
Wlhy Hafiz inanan ina part dina yanxu haka kwana biyu banji dadiba nayi fama ciwon kai me zafi don banson hayaniya yasani kashe waya amma yau naji sauki yanxu nakeson fitowa ma.
Ayya Abokina allah ya kara sauki zanzo na dubaka kuma zan sanar a gun aiki " yawwa nagode Hafiz sai mun hadu " Ok Hafiz yace" gami da kashewa.
Watsa ruwa yayi cikin saurin ya shirya jikin farar shirt da bakin Jean ya feshe jikinsa da turare yayi kyau ba dan kadanba sumar nan duk ta kwanta fuskar nan ta kayatu da gogon hanci tare da dara-daren idanu dogone sosai farine tas tamkar balarabe inbayayi maganaba saika dauka shine.
Hanyar futa ya nufa ya jiyo kamar sallamar Mama ta Khadija da Humaira sun rufa Sallamarta baya saurin sakkowa ya shiga yi don ya tabbatar Mamace wannanne zuwanta na farko lalle dalili mai karfi yasata zuwa ya shiga rayawa a ransa.
Ramlace zaune a daya daga cikin kujerun parlour tanajin sallamarsu amma tayi Tamkar bataji ba kuma ta gane kosuwaye sarai Mamace ta kare mata kallo " tace ke isheshshiya sallamarma bakya amsawa kamar ba musulmaba ko bakisan matsayina bane.
Wani kallo ta watsa mata tace" nasani mana ba uwar Saifullahi da kannansa bane.
Au rashin tarbiyar har yakai haka lalle yanzu na kara tambatarwa.
Kin makaro da baki tabbatarba tuntuniba ta karasa tare da buntsuro baki.
Dai-dai lokacin da Saifu ya karaso ya dauketa da maruka har guda uku a jere sannan ya bita da jajayen idanuwa yana huci.
Ramla ranshin mutuncinki har ya huce tunanina ki zauna kina sa'insa da uwata ba Respect tana tsaye kina zaune ba kallon mutunci bare gaisuwa.
Dafe kuncinta tayi tana yarfa hannu don taji zafin shigar marin sosai tace' Saifu ka maran rannan ka Maran yau akan abinda baikai ya kawo ba gaban wadannan mitsi-mitsin kannanka toh kasaurari maizai biyo baya da Ramla kake zanje ta nufi upstairs kanta kai ga karasawa ta tsinkayi muryar Mama tanacewa" sai dai dana yaga alkhairi kuma yaran da kika raina har kike kiransu mitsatsai to ita zan bari ta kularmin dana don baki kassaramin da.
Eh kibar masa su dukama naga inda uwa daya uba daya zasuyi dadiro aiko bata karasaba saifu ya maramata baya cikin zafin nama tare da had a stars allah ya bata Sa'a bai kamata ba tashige room dinta ta danna key.
Wani kululun bakin cikine ya dunkulewa Humaira " a ranta ta kudiri niyyar lalle ta koyawa Ramla hankali da sannu.
Khadija kasa ta buka komai tayi don bakin ciki.
*Ummusulaimu✏*
[6/21, 10:25 PM] Fatima Zarah: 📝💋🍠🍠🍠🍠
*TA AUREN MIJI*
🌰🌰🌰🌰🌰🌰
🍠🍠🍠🍠🍠🍠
*STORY WRITTEN*
*BY*
*UMMU SULAIMU*
*REAL SALMA FAROUQ*
*PAGE 13 TO 14*
"A sukwane saifu ya dawo ransa bace yace" Bisimillah Mama zauna"yana nuna mata daya daga cikin kujerar dake parlour " Zama tayi Ranta ba dadi.
Hakan yasa su Humaira suma zama fridge ya nufa dake parlour ya dauko gorar ruwa da cup ya dawo inda Mama take ya tsiyaya mata ya mika mata 'yace Mama yi hakuri kisha ruwan nan ba nason ganin bacin ranki ko kadan rashin jin Magana yajamin shiga wannan halin.
" Karbar ruwan tayi ta kafa baki ta shanyeshi tas sannan ta saki wani huci sannan takuma saki murmushi a lokaci guda gami da kama kafadar Saif da yake durkushe gabanta 'sannan ta fara magana fuskarnar dauke da annuri tamkar ba'a bata mataba " Kayya Saif hakika nason kai maijin maganane don duk cikin yarana nason halin kowa kafisu biyayya kawai dai nason jarrabawace ta ubangiji don ya jarraba imaninka fatana kawai allah yabaka sa'ar cinyewa ya kuma yimaka albarka amma kuma banson dalilin ramar kaba gashi yau kwana hudu bansaka idonaba Saifullah.
"'Mama kiyi hakuri banji dadi bane tun randa na dawo shiyasa baki jiniba yau naji dama shiyasa nashirya yanxun ma sakkowata chan nayi niyyar zuwa sai kuma na ganku a parlour.
Ayya Shaifullah allah ya sawwake amma ko dan gaba bai kamata bakada lfy ka kashe wayaba yanxu banda nazo wayasan bakada lfy irin hakama narasaka bansaniba amma nakawo karshen matsalar Shaifu Ga matarka nan yau na sauke nauyin dake kaina nayi imanin tarbiyar da naba Aisha zata kula dakai don irin tarbiyarta itace taka raino dayane "Shaif karka hulakantan 'ya karkaci amanarta inkaci tawa kaci kuma ta maifanka kaci kabata hakkinta matsayin matarka ka bata kulawa ka bata farin ciki ka bata nutsuwa innaganta bulbul kaine akashin hakama kaine Humaira ta kalla wadda duk jikinta yayi mugun sanyi sai wasa take da zoben dake tsakankanin hannuta kanta kasa Tace' Aisha! Sai sannan ta dago kanta a hanzarce alama tai mata da tazo tana mai nuna mata kusa da inda Shaifu ke Tsugune tunda ta fara magana " A hankali ta mike ta katasa hurin ta tsugunna kamar yanda taga Shaifu yayi 'sai sannan ya dago kansa ya kafe Humaira da idanu sannan ya kauda kai yana mejin farin cikin da yadade baijishiba.
"Hannun Shaifu ta kama ta dora na Humaira a kai tace" Ga Amanata nan Dana allah ya tayaka ruko ka kasance mai adalci tsakaninsu hakan zai baka damar shiga aljannah ka nuna mata inda zata zauna sai kazo muyi magana inason tafiya zanxu.
"Toh! Mama Saifu yace ya mike ya nufi Sashinshi Humaira na biye a bayanshi Su karasa shiga part din ko parlourn basu karasa shiga ba ko ya yawota ya rungume ta kam tamkar zai tsageta ya shige bakinta ya shiga neman laluba aiko yana cin karo dashi yashi yimasa wani irin tsotso wanda take ya kashewa Humaira jiki janta yai a hankali suka karasa parlour suka zube kan 3cter ya zame mayafin dake jikinta ya yar gefe ya shiga kokarin zuge zip din rigarta saboda huyan karamine baxai iya zura hannunsa ciki ba kuma breast din sun cika bambam kamar sa huda rigar su fito tuni yai masara zura hannunsa still bakin su na hade wani irin damka yai musu kamar mayinwacin zaki ya fara musu yani irin murza sosai tsoro ya fara ratsa zuciyar Humaira aiko kokarin kwacewa ta shiga yi iya karfinta amma ta kasa gaba daya yagama kashe mata jiki sai fusgar numfashi yake dakyar ta samu ta zame bakinta da har wani dan zafi-zafi ganin ya birkitota daga saurin juyawar da tayi yana kokarin zaro breast dinta yasata saurin kara gicciyawa " tace haba yaya Mamafa ke jiranka.
" Cikin zafin nama ya mike duk kamanninsa sun sauya donshi samma ya manta da batun Mama na jiransa kokarin gyara rigarsa ya shiga yi da dai-daita kansa ya maida mata wani kallo tare da kashe mata ido😉 ya fita.
"Mamako ganin kusan 10 minute bai fitoba tace Khadija tashi muje yazo gida yasameni muyi maganar " fuska Khadija ta shagwabe tace" toh Mama bari muyi sallama da Anty Humairan.
Harara ta daka mata tace" huce muje bazakuyiba in an kwana biyu kyazo kuyi abinda zakuyi ranta baisoba ta wuce suka tafi.
"Shaifu na sakkowa yaga parlourn ba kowa murmushi yayi yace" Ayya Mama afuwa na sha'afane tamkar tana ganinshin jin tashin mota ya tabbatar mishi yanxu suka fita cikin sauri ya fita amma ina tuni motar ta futa get mai gadi na kokarin rufewa parlour ya dawo yaja trolley din daya gani a parlour ya tabbatar ta Humaira ce.
*Ummusulaimu✏ina muku barka da sallah allah ya karbi ibadunmu👏🏽*
[6/21, 10:25 PM] Fatima Zarah: 📝💋🍠🍠🍠🍠
*TA AUREN MIJI*
🌰🌰🌰🌰🌰🌰
🍠🍠🍠🍠🍠🍠
*STORY WRITTEN*
*BY*
*UMMU SULAIMU*
*REAL SALMA FAROUQ*
*PAGE 15 TO 16*
"Humaira yana fita tayi saurin mikewa ko dankwalinta bata dauka ba bare mayafi ta fada daya daga cikin dakunan da ta gani jere a parlour kan bed ta fada tana maida numfashi ta shiga kokarin gyara zip din rigarta tana mamakin jaraba irinta yaya Saif tsaruwar dakinne ya dibi hankalinta ta shagala hurin kallonsa komai na bukata akwai an kawatashi da kwalliya tamkar dama don wani aka tanade shi chan kuma tai saurin mikewa ta dannawa kofar key ta kuma dawowa ta zube a bed.
" Sosai Ramla tayi kuka harya isheta harta jawo waya zata bugawa Momy kawai kuma saita fasa don tayi tunanin inta buga matama bawqni anfani tunda tace " Boka bazai iya aiki akansuba amma tayi alkhawarin saita rama rashin mutuncin da yai mata.
Jin motsin tashin mota ya tabbatar mata miciyaciyar uwar tasa ta tafi wani uban tsaki taja ta mike don wani mugun kwadayin maigadi da taji tanayi ya kware wajen biya mata bukata tunda har tabaya yana zuwar mata wani murmushi ta saki taji duk damuwarta ta kare clothes drower ta nufa ta dakko wata shu'umar Riga ta saka duk jikin ta ragane ya bayana komai dake jikinta ko pant bata sakaba ta dauki wani katon hijab ta sanya ta nufi down star Yayin da shaif ke janye da trolley din Humaira yanaja zai haura samansa da ita tsaiwa tayi tana karemasa kallo tare da kame🤔 sannan tace" Tab amma wlhy anji kunya anyi faduwar bakar tasa ka dauki "ya mace kakai dakinka na sunnah kuma matsayin kanwarka sbd ta runga baka abinda bana baka toh kaji tsoron allah dai duniya ba matabbata bace uhumm! Kodake uwarka ta daurema gindi.
Afusace ya jiyo don tunda ta fara magana ko kallonta ma baiyiba bare ya tanka cigaba ma da tafiyarsa yai amma jin kalmarta ta karshe tayi bala'in fusatashi sakin trolley yai ya fara kokarin sakkowa tare da nunata da yatsa👈🏽 Ke! Ramla be careful bazan laminci saka mahaifiyata a duk lokacin da kika tashi maganaba zan iya datse igiyar dake tsakaninmu akan mahaifiyata kisani ke bakomai bace a hurina ba banda kaddara Ramla kin cuceni kin yaudareni amma kisani mutukar baki sauyaba zaki fuskanci hukunci zuciyarsa a harzuke ya juya ya huce ya batta a gun.
Kafada ta kada alamar ko inkula yana shigewa shashinsa tasa kai ta fice Garbati na hangota ya hau yashe baki don yason yau zai more kai tsaye tana karasowa dakin ta shiga wanda ta gyaramasa shi da sabuwar katifa da bedsheet zare hijab din tayi ta zube a katifar tare da baje masa kafafu ai yana shigowa yaci garo da surorinta bayyane tuni ya afka mata saida sukayi nisa wajen hargiza junansu Garbati yaja jiki.
Ramla ta kalleshi da idanunta jajur wanda ke cike da kishi sun rufe da ganin cewa abin da suke sabon allah babba tace" Garbati ya haka banyan kagama gigitamin lamari? "Da luntsumammun idanunsa ya bita ya bude dafaffen bakinsa wanda ke cike da wari yace"Bakomai kawai inaso na tambayeki ne kinsha kwayar nan kuwa? " Haba gaye nasha man ta kareshe maganar tare da gashemasa idanu gami da jawoshi suka cigaba da aikata masha'a wa'iyazibillah.
"Saifu yana shiga parlour yaga baigantaba ya fara dubawa bedroom dinsa ya fara dubawa yaga bata ciki ya koma wadda ke kusa da nasa ya murda yaji ansa key hakan ta tabbatar masa tana ciki knocking yashiga yi tanajin knocking gabanta ya shiga faduwa don tasan shine mugun tsorone ya ziyarceta lokaci guda don tason shine tsoro takeji karya kuma yimata abinda yaimata dazun jin bugun yayi yawa jiki a sanyaye ta tashi ta nufi kofar ta zare key ya turo ya shigo chan ya hangeta makure a bango ta takure murmushi ya saki don tabashi dariya ma trolley din ya dire ya nufi inda take daf da ita ya tsaya ya kama hannayenta har sunajin numfashi juna dai-dai kunnanta yakai bakinsa ya shiga mata rada " yau ga kanwa najin tsoron yayanta ya karashe maganar da zura mata harshensa cikin kunnanta yana mata wani irin wasa da lasa da hura mata iska ciki wani irin dadi taji dare da sanyi da mutuwar jiki lokaci guda ganin yafara kashe mata jiki yasa ya kama hannun ta ya maida ita bakin bed ya zaunar sannan ya kalli lumsasun idanunta data lumshe yace" Aisha Humaira bude idanunki ki kalleni nine yaya Saifunki dake mutukar kyaunar yau kusa dake allah yanuna masa ranar dake matukar jiran ruskarta.
Bude idanunta tayi ta zubesu a kansa cikin daskararriyar muryarta mai cike da shagwaba da dadin sauraro tace" Yaya karka mantafa ba Ramla abar soyuwarkace a gabankaba "Humaira ce wadda ka fifita Auren Ramla akan nata karkashin igiyoyinta.
" Idanu ya zuba mata yana kallon yanda lips dinta ke motsawa cike da sha'awa tare da mamakin wato irin nata da mamakin yanda tasan kishi haka a hankali ya bude bakinsa cikin sigar lallashi yace" Haba Aisha Humaira ba nason kina tuna baya don tahuce abinda nakeso kisani kawai ina matukar kyaunarki don da sanki nafara bude ido gabanin Ramla nakasa yadda da hakanne kawai don bangane da gaske sanki nakeba sai daga baya kuma tun bayauba na fuskanci matukar son dakikemin kema kema kuma zanbaki kulawar da zakiyi mamakin irinta kiyarda da yayanki Humaira kimin alkhawarin kulawa daga gareki.
"Kallon mamaki ta runka yi masa wai yau yayan da baya musu cikakken wasa yau shine sanyayen kalamai ke fitowa daga gareshi " jikinsa ta fada ta rungumeshi tana jinjina kai alamar yadda da batunsa nanko ya fara hautsina ta da zafafan wasanni da bata taba zaton akwai irinsu cikin aureba ganin yana neman zame mata riga yasa zillewa dakyar aiko ya sunkuceta yai toilet da ita ya batta da ware🙄.
*Ummusulaimu✏*
0 Comments